[7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga ELEGANT ONLINE WRITER'S Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S PAGE 1 Bismillahirrahmanirrahim Kaiwa Waccan Tsohuwar Bazawarar Abincinta, Fati ta faɗa Gami da gyatsine Fuska, Umaima ta ƙyalƙyale da dariya sannan ta ɗauki ɗan Abincin ta nufi Ɗaki da shi. Aameenat Ta na zaune ta zuba Tagumi ta na jiyo su amma ba ta da bakin cewa ƙala. A can gefe Umaima ta ajiye Abincin Sannan ta ce "Ga shi nan in za ki ci" rausayar da kai tayi sannan ta taso zata ɗauka seda tazo gaf da Abincin Umaima tayi maza ta ɗauke tana cewa "Ahayye ƙwalelanki ƙaramar bazawara" "da kin zauna a gidan miji ai da kinci" Fati faɗa tana ya mutse fuska, dariya suka kwashe da ita suka tafa. hawayen da suka cika mata Ido ne suka samu damar gangarowa fuskarta wani kallo Umaima ta watsa mata sannan taja Fati suka fice suna waƙe waƙen su na fitsara . wani sabon kuka ta fashe dashi tana cewa "kacuceni bazan taɓa yafe maka ba azzalumi" ganin kukan baze amfane ta ba yasa ta tashi ta nufi ɗakin wanka ruwa ta watsa ta fito ta shirya cikin doguwar riga Abaya yaluwa taji duwatsu masu sheƙi da walwali tayi kyau sosai madubi ta kalla wasu hawaye masu zafi suka fara gangarowa da sauri ta kauda kai tana tauna laɓɓan ta kafin ta tashi ta nufi ƙofa Mama ce tace " zawar zawar ce yau tafito kenan" "haba kekuwa Mama ba dole a fita neman bazawari ba" dariya Su ka sa Kafin Mama ta ce "Allah ya raka taki gona" Aaminat ta murmusa ba tare da ta yi magana ba ta yi hanyar fita, a ƙofar gida ta coge ta na leƙawa, kasancewar yamma ce ga iska na kaɗawa a hankali a hankali ya sa yanayin ya yi mata daɗi sosai, yaran layin da su ke Ƙwallo ta ke kalla, a zahiri idanunta su na kansu amma a cikin ranta tunanin Yau da Goben Rayuwarta kawai ta ke yi, "Wace irin Rayuwa ce Ƴan Adam su ka ɗorawa kansu??, ba sa tunanin ita Ƙaddara ba kai kake tsarawa kanka ita ba??" tunanin da ya fi yi mata yawo kenan, ta na cikin tunanin ta ji saukar Ƙwallon a Fuskarta, ta yi baya cikin sauri gami da dafe fuskar tata, hawayen azaba ne su ka fara tseren zubowa kan kumatunta, yaran su ka yo yuuu akanta wasu suna "Don Allah ki yi haƙuri" wasu kuma su na cewa "Wallahi Walid ne ya jefo miki ita" Goge hawayen ta yi ta ɗago fuskarta ta na kallonsu, murmushi wanda ke ƙara nuna zallar haƙurinta ta yi kafin ta ce "Na haƙura" Sauran su ka Ɗauki Ball ɗin su ka koma wasa. Abdulkareem ne ya tsaya Ya na Kallonta cike da tausayawa, "Yaya Aamimat!" ya kira sunanta cikin sigar Tambaya, cikin sauri ta zuba masa idanu, sai a lokacin ma ta san ya na gurin domin kuwa a kowacce daƙiƙa tunani ne tsarin rayuwarta, "Abdulkareem sun ci gaba da wasan ba kai" ta faɗa ta na masa ɗan murmushi wanda ya ke bala'in sumar da Zinariyar Zuciyarsa "YaYa Aameenat ban ji daɗi ba, wallahi dan dai Walid Ƙaninki ne kuma ba'a shiga faɗan dangi banda haka da sai kinga yadda zan yi da shi, don ni da a raina ki gwara a mutu har liman, ban damu da rashin kunyar Yayyensa Ƴan Matan nan ba" Ita har ga Allah ya takura mata, don kuwa ganin tsaurin idonsa ta ke yi ta yadda ya ke iya zama ya na tsara mata kalamai kamar irin Namiji Ɗan 35-37 Years ɗinnan, ashe nan Bai fi 20 Years zuwa 21 22 ba, yadda ya ke iya jefa ƙwayar idonsa a cikin nata ya fi komai bata takaici, shi don bai sani bane amma ba ƙaunar ganinsa take ba. Jin ta yi shiru ya sa shi yin dariya ya ce "YaYa Aaminat haƙurinki ya na bala'in Taɓa Zuciyata!" ya ƙarasa maganar gami da ɗora ɗan yatsansa akan Ƙirjinsa saitin Zuciyar tashi, haɗa hannunta ta yi guri ɗaya alamar roƙo, cikin sassanyar muryarta ta ce "Abdulkareem don Allah ka koma ku ci gaba da ƙwallonku Me yasa sai ka dame ni ne???" "Ba na gajiya da kallonki ne" lokacin da ya yi maganar ya juya mata baya har ya ɗanyi tazara da inda take, ta saki baki ta na kallon bayansa, ɗan ƙaramin tsaki ta ja kafin ta juya ta koma ciki aranta ta na cewa "Ciki ba daɗi waje ba daɗi Abdulkareem ka fiya shiga rayuwata, Mara kunya da tsayayyun idanunka" Ta na shiga Mama dake shara ta ce "A'ah Zawar me mu ka samu ne naga kin shigo baki na motsi??, ko mun yi sabon kamu ne??" Girgiza kai ta yi alamar "a'a" ta ratse ta shiga ɗaki, Mayafinta ta fizge ta jefar sannan ta shiga gyara ɗakin, daga fitarta har Su Fati sun yi abinda su ka saba, sun yi wa ɗakin batsa batsa, ta na aikin ta na Tunanin Kamal wanda ta kasa mantawa dashi, zuwa yanzu ita kanta shaida ce WATA TSIYAR A Jinin Ɗan Adam take, Ba ta taɓa tunanin haka za ta gindaya tsakanin Rayuwarta da Kamal ba. hawayene suka fara sunturi a kuncinta sosai take sheshshekar kuka tana girgiza kai, jiri ne ya fara ɗibarta tayi saurin dafa bango ta na ambaton Allah, a daddafe ta iya ƙarasa sharar dan ta zamar mata dole, fita tayi tsakar gidan ta fara haɗa kwanuka domin wanke su ba tare da ɓata lokaci ba ta kammala wanke wanken ta shiga ɗaki ta saki labule domin bata son yin kaciɓus da samarin gidan dan kuwa basason ganinta guri tanema ta zauna tana jen carbi. dariyar da taji ce tasa ta ɗagowa Umaima ce da ƙawarsu Nafisa da Fati suke mata dariya "Oni ƴasu dama haka zawarci kebsa bawa ladabi"? Nafisa faɗa tana riƙe haɓarta wani murmushi Fati tayi sannan tace "to zawara se a bawa ƴan mata waje ko, ta baro gidan miji ta zo ta dami mutane" bata musa ba ta tashi ta nufi ɗakin Umma, duk da ta san balalle ta barta ta shigar mata ɗaki ba kai a ƙasa ta ƙarasa kofar ɗakin, Umma ta watso mata harara gami da cewa "Sannu Aameena karki shigo min ɗaki, ki ɓata min, ɗakin naku aikin me yake yi??" "Su Fati ne a ciki" Umma ta ce "Ai ba ƙarfinki su ka fi ba, ni dai ba a ɗakina ba, yanzu na gama share shi" jiki a sanyaye taja ƙafafuwan ta tanufi kicin, karo taci da Umar ya shigo ta sunkuya tace "Ya Umar ina wuni" be ko kalleta ba ya wuce abin shi hakan yayi mata ciwo sosai Amma inda sabo ta saba haka ta tura ƙofar kicin ɗin ta shiga ta zauna tare da saukar da wata ajiyar zuciya yunwa takeji gashi babu da mar dafa abinci domin in mutan gidan suka sani baza taji da daɗi ba. rabonta da abinci tun karin safe ta galabaita sosai dankuwa duhu duhu take gani.. Rai a ɓace ya shiga gidan bebi ta kan kowa ba ya nufi ɗakin su "Abdulkareem"! tafaɗa cikin kwantar da kai batare da ya juyo ba ya tsaya cak bece ko mai ba a hankali ta ƙarasa inda yake ta ɗan shafi gefen fuskar shi tare da hura mai iska da bakin ta batare da ya ɗagoba yace "Ummi ina jin bacci" "maza kaje in katashi ka sanar min da wuri don rabonka da abinci ka daɗe, ka fi ganewa tsalle tsalle" be ce komai ba ya cigaba da tafiya murmushi tayi tare da bin ɗan na ta da kallo tana sa musu Albarka tare da addu'ar Allah ya ƙara haɗa mata kan su mazan da mata ya tsaresu daga sharin magauta. ɗakin wanka ya shiga yawatsa ruwa ya na fitowa ya nufi firji gorar ruwa ya ɗauka ya sha sannan ya sauke ajiyar zuciya gami da dafa ƙirjinsa.... CommenT Shere FisabilillaH © INDO CE & AUTAR JARUMAI [7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga ELEGANT ONLINE WRITER'S Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S Shafi 3 Matashin ya saki baki da Ido ya na Kallon Abdul, shi kuwa ya karkaɗe kwalar rigarsa da aka riƙe ya yi gefe ya na muzurai. "Me kake nufi ne?? ka yi min laifin kuma sai ka sa a Ɗaure ni?" Abdulkareem ya ce "Ɗan Halak ka fasa, ai kasan yadda doka take, ka riga ka ɗau doka a hanunka ka ga ba ka da dalilin ƙorafi akaina tinda ka rama, Ka ja saɓa ko mu saɓeka da kanmu." Cike da taurin kai Matashin ya ƙara cewa "Wai kai da me kake taƙama ne haka?, gani ka ke kamar ƙarfinka ɗaya da ni ko??" "Ka zo a gwada Gwani mana, na gaya maka dalilin da ya sa na bari ka dokeni amma banda haka da ba za ka bar layin nan lafiya ba daga kai har Motar taka." ya na gama faɗe ya bar wajen ya nufi inda ya wurga Takalminsa, Matashin kuwa ganin an fi ƙarfinsa ya sa shi jan Motarsa su ka bar wajen. Sai a lokacin Aaminat ta samu ƙwarin guiwar matsowa kusa da shi, cike da ɓacin rai ta ce "Ka na Shaye-shaye ne Abdool?? ko kuma dama Mahaukaci ne kai ba mu sani ba??" Rikitattun idanunsa ya zuba mata kafin ya ƙyalƙyale da dariya sannan ya ce "YaYa Aameenath!! Ba za ki Fahimce ni ba yanzu, don Allan ki shige gida ki dena tsayawa kan hanya kar a sabauta Mana Rayuwarki." idan Abdulkareem ya yi mata wani abin komai na jikinta dena aiki ya ke sai iya Zuciyarta, yau ma kamar kullum sai ta zama kamar bishiya ta saki baki ta na kallonsa, aranta kuwa irin Manyancensa ta ke tunani. Siyama takama hannunta gami da cewa "Tawo mu tafi ki bar wannan Tantirin Yaron, idan ma Nasiha ki ka yi masa ba zai fasa halinsa ba, ace rigimar da ba da kai ake ba dole sai ka shiga?" muryarsa ce ta dakatar da ita "Ke!! me kike da suna ne?? Siyama ko? to Anti Siyama dai Sabi da darajar masu daraja, ki fita idona in rufe tsakanina da ke daban tsakanina da Yarana daban tsakanina da sauran Ƴan Adam daban hallau tsakanina da YaYa Aaminat ya fi kowane tsakani da na ambata muhimmanci, Tsarin rayuwata ne a haka, ki kula da kanki." zuwa yanzu Siyama itama ta rasa bakinta hakan ya sa ta ja hannun Aaminat ƙiiiiii su ka shige ciki. Abdulkareem ya ja tsaki kafin ya wuce gida ya na famar mita. "Aaminat! Aaminat"!! ko kin fiso a kiraki da sunan da ki ka fi dacewa? Bazawara iye Mama ta faɗa tana bankaɗa labulan ɗakin a kwan ce take tana aikin nata na kuka dariya Mama tayi tace "eh lalle ne zawaru samun guri kina gani dai Fati basa nan ki tashi kiyi girki kuma in kika gama ba ace ki iba ba" da kai ta amsa mata ganin bata da niyar magana yasa Mama ta juya da lukutayen kafafuwanta. ciwo kanta yake yi kamar ze faɗi gashi babu me bata magani gas ɗin ta kunna ta ɗora girkin, ta zauna a Kicin ɗin tana tunane tunane ya rayuwar ta zata kasan ce?? shin cikin zawarci zata mutu ko kuwa za ta yi Aure? waze Aureta mutane suna gudun bazawara?, kuka ne ya kufce mata dede lokacin da Umma ta danno kai kicin ɗin sosai Umma take jin kukan har cikin ranta kamar bazata kula ta ba se kuma ta kauda kai gefe tace Aaminatu lafiya ki ke kuka haka??" ba ta kula ta ba taci gaba da gursheƙen kukan ta Umma ce ta kama hannun ta da cewa ba ki da lafiya ne?" kai ta gyaɗa mata alamar eh shuru Umma tayi tana kallon Aaminat da duk ta rame cike da nuna damuwarta akan ta tace "kije Umar ya kai ki asibiti kinji, ke ce bakya jin magana Aamina kin kashe Auren kuma kin ƙi yin wani, darajar Ƴa mace fa Aure ne" to kawai tace mata daka haka bata ƙara cewa komai ba har Umma ta fita. A haka ta gama girkin ta zuba a kula ta ajiye batare da taci ba ko ta ɗiba ta nufi ɗakinsu, gado ta faɗa taja ƙaton bargo ta rufa tana rawar sanyi jitake tamkar kan ta ze faɗi sabi da tsabar ciwon da ya ke yi mata. Zaune suke a Falon Ummi suna fira Abdulkareem ya ɗan daki kafaɗar Abdurrahim yace "kana sha" "amma kaɗan" cewar Abdulmajid dariya suka sa Abdulmajid ya hantsulo daga kan kujerar da ya kashingiɗa, yace "kai anayi muna dariya jiya naga wata Cika ta ci wanka za ta je gaiyar soɗi ta ji fenti an sa mata wannan hodar tasu fuskarta jajir amma wuyan kamar an babbaka kan rago" wani ihu suka sa suna dariya Abdulkareem ya dafe kai yace "Jar uba jiya kuwa naga anyi yasar wata rijiya a wata unguwa da nasani na ɗebowa su Nana Fareeda su bursuna" ta zabga masa harara ta murguɗa baki tace " A haka ake gani a ƙyasa ehhe" dariya suka yi "haka zakaga wata ƙafa karsan karsan fuska kuwa taci kwailin" Nana Fareeda ta ɗago tana kallon su tace "nide ai ba bilitin nake ba balle ku ce" Abdulmajid ya ce "waya sani ko kina ɗanawa" Abdurrahim ya ɗan dafa kai yace "gaskiya an ciki wasa" Abdukareem kuwa kallon ta yayi ya ɗan yamutse fuska yace "wani goshinki kamar jirgi" zaro ido tayi ta shafa goshin nata taji hakan yake ko kuwa kuka tasa tana kwashe littattafan ta da gudu tayi sashin Ummi tana kuka kan Ummi tafa ɗa tana cewa Ummi kinga su Auta ko se tsokana ta suke murmusa wa ta yi tace "kamar baki san halin su ba kike musu kuka kuka?" "To ai ni tsokana ce ba na so, kuma na ce su bari sun ƙi. Ummi ta murmusa gami da rausayar da kai. Abdulkareem ne ya miƙe gami da cewa "Ni fa Abokaina su na jirana bari in yi waje." Abdulmajid ya ce "To Abokin Abokai, sai ka shigo." bai ce komai ba ya yi hanyar fita. A Garden ya tarar da Dadda ya na zaune shi kaɗai ya na ƴan aikace aikacensa, har ya wuce Dadda ya ce "Babban Mutum" shafa kai ya yi gami da cewa "Wai Baba sai da ka ganni??" Murmushi Dadda ya yi ba tare da ya ce komai ba, Abdulkareem ya ƙaraso ya nemi kujera ya zauna gami da cewa "Barka da Dare Dad ba ka kwanta ba??" "Lafiya lau! kwanciyar me zanyi bayan na aje ku kuma ku ba ku kwanta ba??, An sanar min wani ya mareka waye shi??" zaro ido ya yi ya na cewa "Waye ya gaya maka??" gyaran murya Dadda ya yi hakan ya sa Abdul ya yi saurin gyara zamansa domin kuwa a tsarin Daddy ba a Maido masa Tambaya ba tare da an bashi amsa ba "Wallahi Dad Glass ɗin Mota na fasa masa" a ɗan mamakance Dadda ya ce "Babban Mutum!!?? Me yasa to??" "Wata Yarinya ya ɓare ne shine nima na ɓare mar Glass ɗin ka ga mun yi ragas" "Wace yarinya ce??" "To dai ga ta nan dai Baba Ƙanwar Abokina ce, to kuma kasan ba na ɗaukar Hau. Daddy ya ce "Tooo!! Ina fatan an kaita Asibiti ita Yarinya" "Ahh!! Dadhh!! ba ina nan ba wai? kasan za a yi komai akan tsari ai" ya yi maganar cikin sigar shagwaɓa, Dadda ya ce "Tashi ka je inda za ka tafi, amma ka dinga kulawa fa" miƙewa ya yi gami da cewa "To" Ya na fita su ka sake sabuwar hira don jiran zuwansa dama su ke yi. Aaminat washegari ta tashi da sauƙi dama yawan kuka ne ya haddasa mata ciwon kan, bayan ta yi bacci kuma ya lafa. Ta na zaune ta na wanke-wanke Umma Sa'a ta yi sallama, amsawa ta yi ta na murmushi ta ce "Umma Sa'a Sannu da zuwa" a yatsine ta ce "Yauwa Aaminat, wanke-wanken ne don lalacewa sai kusan Azhar ake yinsa? akwai girɗeɗiyat mace kamarki a gida amma don baƙar ƙazanta sai yanzu ake yin wanke-wanke?? ba dole ma Aure ya mutu ba" A sanyaye Aaminat ta ce "Wallahi Umma Sa'a ba hakan ake yi ba, yau ne don ba ni da lafiya ban yi da wuri ba" "Ke dalla rufen baki, ai ke yanzu rufin asirinki ki yi Aure kuma ki gyara ƙazantarki don ba mijin da zai yarda da wanke-wanken Azhar, kin ga yanzu ma IV na Auren Ƙanwarki na kawo amma ke sabi da kin sa ido a Duniya ba za ki yi Auren ba" "Ni fa Umma ba ku fahimce ni bane, wallahi gabaki ɗaya mummunar fahimta ku ka yi min, ni ban taɓa ƙin Aure ba, me zai sa ma na ƙi Auren??" ©️ INDO & AUTAR JARUMAI [7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga ELEGANT ONLINE WRITER'S Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S Shafi 2 Bismillahirrahmanirrahim Wato ya lura Duniya idan ba ka tsaya mata ba ita kwanta maka za ta yi, mutum ne mara gaskiya amma ba za ka yi magana ba sai ka zama tsinanne. Da wannan tunanin ya kwana, washegari tin safe ya shirya Ya nufi Kasuwa. Yau da daddare Aaminat ta na zaune ta na Azkhar Umaima ta shigo ta na dariya "Abba ya ce ki zo" ta faɗa ta na ɗan tsoshe bakinta sabi da dariyar da take yi. "To ki ce ina zuwa" ta faɗa ta na ƙoƙarin tashi, ba ta ɓata lokaci ba ta nufi ɗakin Abban bayan ta ƙara gaisheshi a karo na biyu ya ce "Maza ki shirya ki fita Allah ya kawo Manemin Aurenki, kuma kar in ji kar in gani, in ki ka sake ki ka koreshi za ki gamu da ɓacin raina, ko bakya so ki haƙura haka nan don zaman banzan naki ba shi da amfani." "To Abba" ta faɗa kanta a ƙasa. Mama ta yi wani ɗan murmushi gami da cewa "Kamar gaske" ba ta kalli inda ta ke ba ma bare ta tanka mata. Ɗakinsu ta koma ta shirya har ƙasan ranta daɗi take ji gami da Addu'ar Allah i sa mutumin kirki ne ya ce zai Aureta ta huta da tsangwamar Al'umma, Fati ce ta matso kusa da ita ta tsaya ta na ƙare mata kallo kafin ta tuntsire da dariya, "Gaskiya sai kin yi Jagira" Aaminart ta ce "Ke ni ba zan yi ba" Fati ta ja tsaki kafin ta ce "Ƙazamar Mace." Aameenat ta murmusa dan dai ita ba ta iya sa'insa ba kumama Fati ba Abokiyar yinta bace, amma ko Mama Mahaifiyar Fatin ba za ta taɓa kaita tsafta ba. cikin sauri ta shirya ta fita, ya na zaune kan kujerun da aka aje ɗaya ta shi ɗaya ta-ta, ta ƙarasa da sallama, amsawa ya yi ya na murmushi ya ce "Zauna mana." Ta zauna sannan ta gaishe shi ta yi shiru, bai ce ba ba ta ce ba su ka shiga zaman kurame, Agogon Wayarsa ya duba ya ga dare ya fara yi gudun kar ya makara ya sa shi cewa "Sunana Salis Bara'u, an bani labarinki ne aka ce in zo mu gana ko zamu daidaita kuma ina fatan hakan." ɗan murmushi ta yi ba tare da ta ce komai ba ''Duk da nasan sunanki amma ina son ƙara ji daga gareki. "Aaminat" ya yi murmushi ya ha cewa "Suna me daɗi, an ce min Shekararki Ishirin da Biyar, to amma wace makaranta ki ke zuwa? nasan har yanzu anata neman ilimi ne" ya ƙarasa maganar ya na wani mugun washe baki, in ta fahimta dai ba'a gaya masa gaskiyar cewa ita Bazawara ce ba kenan! jinjina kai ta yi cike da mamakin halin ɓoye-ɓoyen nan na Abba gashi wai a dole sai ya Aurar da ita sai bi yake ya na tallanta. "Yanzu ba karatu nake ba ai Zaman Zawarci na ke yi. "Bab.. ban..gane ba Zawarci kuma? tsokanata ki ke yi?" murmushin takaici ta yi kafin ta ce "Ba Zolaya bace ita ce gaskiyar ni ban iya ɓoye-ɓoye ba gwara kasan wadda ka Aura, in har za ka iya ka so ni don Allah ba don wani abu ba, amma ni Bazawara ce." gyara zama ya yi gami da sauke gwauron numfashi kafin ya kalleta ya ce "Ki na da Ƴaƴa ne??" "Ba ni da ko ɗaya. "To ki sanar min abin da ya sa ku ka rabu ke da Mijin naki. shiru ta yi ta na tunani kafin ta girgiza kai ta ce "Ba zan iya ba." tsaki ya zabga ya gyara zaman Hularsa ya tunkuɗota gaba sannan ya fara magana "Ai in na Aureki na ƙi cin Biri na ci Dila kenan, Matata Ma ta fiki Yarinta don dai kawai Ƙazama ce shi yasa na ke son ƙara Aure, amma da in Auri Bazawara ai gwara in zauna da Ƙazamar Matata har zuwa lokacin da zan samu Budurwa, wa ya san ma irin abin da ki ka yi Wancan ɗin ya sakeki? ai duk wanda ya ɗebarwa kansa Bazawara ya ɗebowa kansa aiki, me za ka samu a Kale in banda takaici, ni ba zan iya Auren sauran wani ba, ki gayawa Abbanki in zai sa ayi tallarki a dinga gayawa Mutane gaskiya, don a zamanin nan ko anzo dole a tafi don ba me yarda ya Auri Bazawara." ya na kaiwa nan ya miƙe ya kakkaɓe tijararriyar rigarsa ya yi hanyar fita. Aaminat kuwa tin da ya fara hawaye su ka shiga tsere akan fuskarta, tashi ta yi ta shiga Gidan da gudu, a hanya su ka yi tawo mu gama da Umar, ya daka mata tsawa da cewa "Kehh!!!!! menene hakan ko ciwon hauka ya kamaka ki ne??" Kukan da ya ke cin ƙarfinta ne ya samu damar fitowa, cikin shashshekar kuka ta fara cewa "Kowa sai ya ce ba zai Auri Bazawara ba sai ka ce ita ta tsarawa kanta Ƙaddara?, idan ba su Aure mu ba a haka za mu Mutu cikin fuskantar ƙasƙanci da wulaƙanci kenan??, nima fa ban sani ba Ya Umar ban san Kamal zai yi min haka ba, Ban sani ba wallahi, kowa ya tsaneni har iyayena da ƴan Uwana, wallahi Tallahi ba ni da laifi, don son raina ba zan taɓa zaɓar irin wannan Rayuwar ba, Abba ya kawo min Mutane da yawa amma sai su ce ba za su Auri Bazawara ba." Kukanta ne ya ƙara ƙarfi ta toshe bakinta da gefen Gyalenta sannan ta kutsa kai cikin gida. "Aamina!!! Aaamina!!!" Ya Umar ya shiga watsa mata kira Bata tsaya ba taci gaba da tafiya, ta na shiga ta yi gamon katari da su Abba Umma Mama da sauran Yaran curko curko a tsakar gida don kuwa sun ji muryarta lokacim da ta ke yiwa Umar Magana. Mama ta ce "An yi abin da aka iya ko?" ganin kowa ya tsirata da ido ya sa ta yi saranda ta kasa wucewa, Abba ya ce "Kukan me ki ke wa mutane?" "Abba shima cewa ya yi ba zai Auri Bazawara ba" Abba ya doka tsaki kafin ya ce "Ai tinda ba ƙaunar Auren nan ki ke ba sai ki zauna, ga ki ga gidan nan, kullum aikinki kenan ki ce sun ce ba za su Aureki ba idan kuma na tambayesu sai su ce Ƙarya ki ka yi musu, ai ga gida ga ɗaki sai kita zam." Umma ta ce "Allah i kyauta". daga haka ta bankaɗa labule ta shige ɗaki, Mama ta riƙe haɓa gami da cewa "Lallai Makircin yarinyar nan ya ƙara girma, ga yadda ta shigo da kuka kamar wadda ya sokawa wuƙa a Zuci??" Goge hawayen ta shiga yi cike da ɓacin rai ta ce "Wallahi Abba ba ni da laifi ba gaskiya su ke faɗa maka ba, ni dai ina neman Alfarma don Allah idan za'a ƙara kai Tallata a faɗa musu gaskiyar ni Bazawara ce, idan ba haka ba ko anyi Auren Wallahi dole a rabu don ba a ginashi a Tubalin gaskiya ba tin farko." a fusace Abba ya ce "Ɗan Iska ki ke neman maidani?? Kina nufin so nake na yaudaresu?? to tinda ba ƙaunar Zawarawa ake ba ba sai ace ke Budurwar bace ai Ƙaryar kare kai Halak, shashasha Mara kan gado." ya na gama faɗe ya yi fuuu ya bi iska su ka yi waje. Mama ta ce "Ai kin gani, mun yi nasihar har mun gaji, ki ta korar samari Aamina wai ni ko Namijin Aljani gareki ne???" Umar da ya dafe bango ya riƙe ƙugu ya na saurarensu sai a lokacin ya ce "Ta na fa da gaskiya Mama, fisabilillahi ko wanene ba zai taɓa lamunta ya Auri mace da sunan Budurwa ba bayan kuma Bazawara ce, kuma ko dama ace ni ne ko kuma Anas Ɗan uwana, nasan ku kanku iyayenmu ba za ku taɓa amincewa ba, mu sai mu haƙura amma ku iyayen ku zage sai kun nemawa Ƴaƴanku Ƴanci, Maganar gaskiya Ƙaramta ce wai a gayawa Mutum Budurwa ce ya zo ya tarar da wannan Kakar su wanen, kuma Bazawara ma" ya na kaiwa nan ya buga tsaki ya fice, Aaminat ta faɗa ɗaki ta ci gaba da kukanta sample sample. Mama da su Fati su ka gama tsugunguninsu su ka tashi. washegari Daga Abba Umma Mama ba wanda ta gaisar ya Amsa sabi da fushin da su ke da ita. tin da ta gama Ƴan wanke-wanke da shararta ta shige ɗaki ba ta ƙara ko leƙe ba sai in za ta yi Alwala, sai yamma liƙis ta ji ciwon Jiki duk ya isheta don kuwa zaman guri ɗaya ba abin da ba ya haifar mata har ciwon kai, tashi ta yi ta sola wanka sannan ta fito ta shirya cikin doguwar rigar Atamfa, mafici ta ɗauka ta na kaɗawa ta ji daɗi sosai da ta ɗan motsa jikinta. Siyama ce ta yi sallama a tsakar gida ba tare da ta jira wani ya bata izinin shigowa ba ta danno kai don tasan in ta tasu ce ba za su barta ta ga Ƙawarta ba, Da sallama ta shiga ɗakin kafin ta ce "Aaminat Mutanen ɗaki." Aaminat ta yi dariya kafin ta ce "Na ji daɗin ganinki wallahi dama ni kaɗai nake zaune gashi su Fati ma ba sa nan bare in ji surutansu." Siyama ta ce "To surutan su Fatin har abin daɗi ne?" "Ai motsi ya fi laɓewa Siyam's." Siyama ta jinjina kai kafin ta ce "Ba fa zama zan yi ba, tashi mu je Gidanmu." ba gardama ta miƙe ta zura hijab sannan su ka fice. Kafin su ƙarasa gidan Aaminat ta ce "Wai don Allah Siyama akwai wani aibu babba ne a tare da Bazawara?" cak ta tsaya gami da cewa "A'ahh!! tsaya kin ji na faɗa ne??" "Ke fa daɗi na dake Saurin rigimewa, bance kin faɗa ba tambayarki na yi ko kin ji labarai a wasu gurin, na ga kowa ƙyamata ya ke, kamar ma zargina ake." Kafin Siyama ta yi magana sai jin Hucin Mota su ka yi ta yo kansu da Mugun gudu, Su ka tsallake da gudu zuwa gefe. Me Motar Ko ya kula ya ci gaba da gudunsa. Cikin Zafin nama Abdulkareem ya wawuri wani rangwamemen dutse ya wurga akan Glass ɗin Motar ya yi tsawa kwatsa-kwatsa, me Motar ya ja burki Ƙuuuuu, sannan ya fito a fusace, Majalisar tasu ya kalla cike da hargagi ya ce "Uban waye ya jefe min Mota ??? Ba ku da hankali ko?? ba ku san darajar Mota ba ko?? to wallahi ko waye sai an biyani Glass ɗina!!" Abdulkareem ya miƙe ya gyara kafaɗu sannan ya nufi gaban Matashin ya tsaya, a dake ya ce "ni ne na Fasata sai me??" "Sai Ubanka ya biyani, Mahaukaci ne kai?? ka san darajar Mota kuwa???" "Kai Malam kar ka sake ka zagi Ubana, kuma an fasa banza ba za a biyaka ba in ka na da ƙarfi ka ƙwata. Fass Matashin ya kwaɗawa Abdulkareem Mari, shafar fuskarsa ya yi kafin ya murmusa ya ce "Na gode" Cikin Sauri Aaminat da Siyama su ka yo riiiii zuwa gurin domin raba faɗa, Abdulkareem ya yi saurin cire Takalminsa ya wurga gabansu, cikin Ɗaga Murya ya ce "YaYa Aaminat kar ki tsallake layin da Takalmin nan yake." Aaminat ta zazzaro ido ta na kallonsa, shi kuwa ya yi kamar ba shi ya yi maganar ba, haka kawai sai ta tsinci kanta da komawa baya a memakon ta ƙarasa. Matashin ya ce "Godiya nace kai min?? ina ne gidan Ubanka??, kai Yaran nan ina ne gidan Uban wannan Yaron??" ya faɗa ya na Kallon su Haisam Cokali, sai ya ga sun sa masa ido kawai kowa ya ƙi magana, maida hankali ya yi akan Abdul ya na tambayarshi gidansu, duk Tambaya ɗaya Mari Ɗaya shi kuwa Abdulkareem aikinsa ya ce Ba zai faɗa ba, a ƙalla ya yi masa mari ya kai Shida kafin Abdulkareem ya ɗaga masa hannu gami da cewa "Kar ka Ƙara dukana". "Idan na ƙara za ka rama ne??" "Ka dai ji maganata kar ka Gani" "Ai dama ance Talakawa baƙin ciki garesu, shi yasa za ka fasa min Mota, To idan na bar unguwar nan ba tare da an biyani ba Allah i Tsine min." Abdulkareem ya yi dariya kafin ya ce "Ai ka mari kuɗinka kuma, Fuskata fara ce kyakkyawa a ƙalla duk Mari ɗaya Dubu Biyar ka ga ka Mari Dubu Talatin kenan, don haka Sai ka Zareta, ina nufin ka Zari ƙafarka in dena ganinta anan, Sakarai Mara wayo, a ganinka Namiji kamar ni zai zauna ka mareshi ne har haka sabi da na fito daga gidan Mahaukata? nasan Shekaru kawai za ka ban amma ba uwar da za ka nuna min, Na bari ka Mareni ne sabi da wadda ka so Kashewa Darajarta ta fi Ƙarfin Kuɗi ya Siya shi yasa na Sa jikina Fansa, idan kuma ba ka haƙura ba dik da haka ka kira POLICE wannan Katangar itace ta gidanmu, anan in ka yi gaba akwai Get A baya ma Akwai Get ta ko ina in ka je za ka iya shiga ka sa a zo a kamani Ni kuma Zan sa a Ɗaureka!!!" Salma ta ce IN ba COMMENT ba Posting🤷🏾‍♀️🤷🏾‍♀️🤷🏾‍♀️ © INDO CE Tare da AUTAR JARUMAI [7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga ELEGANT ONLINE WRITER'S Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S Shafi 4 Bismillahirrahmanirrahim "To in ba haka ba me ze sa ki ƙi Auren?" "Allah Umma sa'a da ace zaku fahimce ni da zaku gane gaskiya" "ke dalla can jinake Abban ku kallum cikin nemo mi ki manema yake?" ta ƙarasa maganar tana tafiya ɗakin Mama. "Yau kuma su Umma Sa'a ne a gidan namu?" "wallahi kuwa kin ganni ina su Fati da Umaima?" "suna ɗaki inaga bacci suke" aikuwa gara su huta tunda ga me aiki nan Aaminat" Umma ce ta shigo ɗakin da sallama suka amsa "Umma Sa'a sannu da zuwa ina wuni ya hanya?" "lafiya lau na sameku lafiya" Mama tayi zaram ta ce lafiya lau" Umma ce ta ta shi ta nufi ɗan ƙaramin Falonsu firji ta buɗe ta ɗakko ruwa pure water ta zuba a faranti ta nufi ɗakin Mama da shi, "garuwa kisha" ta faɗa tana ajiye farantin a gaban Umma Sa'a. Fati ce tashigo ɗakin ganin Umma sa'a yasa ta ɗan kyaɓe baki sannan tace "ina wuni" "lafiya lau ƴan mata masu tashe" suka yi dariya, Umaima tace "wallahi Umma Sa'a na daɗe ina son ki zo se gaki" "wai ina gari da Bazawarar ku? naji ta shuru kamar bata gidan ta na nan haka take kullum tana ɗaki" tsaki Fati tayi tace "abin takaicin ma ta fiya ƙazanta" Mama ta muskuta gami da cewa "to kunga ta ina Aure ze zauna kowa ma ta Aura se ya sake ta dan kuwa mazan yanzu basa son ƙazamar mace" haka suka ci gaba da fira akan wai Aaminat ita ke korar maneman ta acewar su me kuɗi take so. Aaminat kuwa da ta gama wanke-wanken ta ga gidan kamar kango duk su na ɗaki su na hira ta ɗauki gyalenta ta fice zuwa gidan su Siyama. Kamar daga sama ta ji Muryar Abdul ya na cewa "Ina zuwa YaYa Aaminat??" tsaki ta ja kafin ta ce "To ka aikeni ne??, kai ma ai abin tambaya ne me yasa yau ba ka je Kasuwa ba??" Ya ɗan shafa kai kafin ya ce "Ina da wani Case ne a Layin nan, wani kiwo ne da nake to kwana biyu banga abin da nake kiwon ba shine na tsaya jira ko sai da rana Rabo na zai rantse." ba ta ce komai ba ta ci gaba da tafiya, cikin sauri ya sha gabanta ta yi saurin ja da baya ta na wararo masa ido "Abdulkareem! wai don Allah ba ka gane ka shiga haƙƙina ne?? ba ka san ka na shiga rayuwata ba idan ka na yi min magana ka na katsalandan a cikin lamarina??" Murya ƙasaƙasa ya ce "Ki yi haƙuri YaYa Aameenat kinsan Zuciyar ɗan Adam kowacce da irin rauninta, da zan iya fita daga sabgarki da na yi tun kafin ki fara fusata da ni amma na kasa." ya ɗan tsagaita kafin ya ɗora da cewa "Ni hakan shine raunin tawa Zuciyar, ba na iya yi mata shamaki da shiga Gonarki, sai dai ki yi haƙuri da ni, yanzu ma tambayarki na ke son yi don kuwa naga kamar ba ki da lafiya." "Eh ba ni da lafiya ina ciwon kai ne, kuma na warke yanzu ba wata damuwa, ka bani hanya in wuce. "Zan ba ki hanya Aaminat amma sai na gama maganata, kin sha magani? ko kuma kin ga likita??" kamar za ta fashe da kuka ta ce "Abdulkareem Ciwon kaina ne, abin da bai shafeka ba ne wannan, idan na sha ba ka da asara idan ban sha ba baka da ita, me yasa?? me yasa ka ke son illata rayuwata ne Abdulkareem??, shin ba ɗaya daga cikin ƙannena na layin nan bane kai?? ka na tunanin akwai bambanci tsakaninka da su Bilal ne??" Zuciyarsa ta yi wani mugun rauni idanunsa su ka canja kala su ka cicciko da hawaye, cikin sanyi ya kalleta sannan ya ce "Tabbas ba ni da bambanci da su Bilal ni Namiji ne su ma Maza ne, kuma ba na ganin bambanci tsakanin ni da Anas da Umar Yayyenki, Aaminat ina son in tsayawa rayuwarki fiye da yadda Umar Zai tsaya miki, kar ki yi min mummumar fahimta, wallahi ko da sau ɗaya ban taɓa yin banzan tunani akanki ba, sai dai ina tunana ɗaukaka gobenki, Ba zan iya denawa ba har sai in na dena numfashi a Duniya ko da kuwa za ki jefa ni cikin rijiyar azaba, ni kaina ina jin ba daɗi idan na ɓata miki rai sai dai bansan me yake damuna ba da na kasa denawa, ta yuwu ma na haukace ne!" Ya ƙarasa maganar ya na murmushin da ya bawa hawayen idonsa damar sakkowa. girgiza kai ta yi cikin sauri, bakinta na rawa ta ce "Abdul ba ka haukace ba amma akwai wata cutar da take damunka, ka roƙi Allah i yaye maka ita domin za ta illata rayuwarka, ni kuma ba za ka iya tsaya min ba Allah ne kaɗai abin jinginata shine ya ke shiga lamurana, Iyaye ko Ƴan uwa ba wanda zai iya tsayawa Aaminat bare kai Yaron Maƙota, ka cire wannan tunanin daga Zuciyarka Abdul." ta na kaiwa nan ta ratse ta kusa da shi cikin gudu-gudu sauri-sauri ta shige gidan su Siyama, tin a Soro ta fashe da kuka ta ƙarasa ta na yin kayanta Anti ta ce "Subhanallah meke faruwa haka Aameenat??" zama ta yi gami da cewa "Nima ban sani ba Anti, bansan meke damuna ba amma nasan Ƙaddarorina a rayuwa su na da yawa." Siyama ta fito daga ɗaki ta na gyara kallabinta, sai da ta zauna sannan ta ce "Haba Aameenat na gaya miki wannan kukan ya yi yawa wallahi, komai kuka komai kuka?? ki samawa kanki Ƴanci daga wannan koke koken don Allah, a Duniyar nan fa kowa ki ka gani da kalar damuwarsa kowa ya na yawo da Jarrabawarsa to idan ki na kuka ta yaya za ki iya fuskantar Jarrabawarki har ki cinyeta?, ki yi shiru don Allah." gyaɗa kai ta yi ta na ƙoƙarin tsaida kukan sai dai da ta goge Ƙwallar da wata ta zubo. Abdulkareem tin da ta yi gaba ta barshi ya kasa gaba ya kasa baya, Haisam Cokali ne ya iso gurin cike da iyayi da kwainane irin nasa ya ce "Master Allah i sa dai lafiya don wallahi gani na yi idanunka sun kawo ruwa." Abdulkareem ya numfasa ba tare da ya ce komai ba ya koma jikin gatangar gidansu ya jingina gami da zubawa guri ɗaya ido, Haisam Cokali ya ce "Wallahi daga gani yau Maza sun sha fama don kuwa gabaki ɗaya rauninka ya gama baiyana Oga" tsaki Abdulkareem ya ja kafin ya ce "Cokali zan Ɗauraye hannuna in kikkifa maka Mari wallahi". cikin sauri ya riƙe haɓa gami da cewa "Ni Ɗan nan rufani ka saya ni, abin ai bai yi zafin haka ba, maida wuƙar Allah i bada haƙuri ni tafiya ma zan yi." Abdulkareem ya ce "Haisam wai don Allah ka lura akwai wata cuta da take damuna?? ni ina ganin kamar lafiyata ƙalau ko ina alamun hauka?" Haisam ya tuntsire da dariya ya yi shewa ya tafa hannuwa sannan ya ce "Master namu Allah ya barka, to ai ni duk layin nan a Samari dai har ƴan shekara Talatin banga me hankali kamarka ba, kumw lafiyarka ƙalau tinda ba zazzaɓi ba ciwon kai." girgiza kai ya yi a sanyaye ya ce "Ta na da gaskiya sai dai na kasa gane kowane irin ciwo ne, nima kaina na san ba ni da lafiya". "Allah Sarki Master, don Allah sa ranka a inuwa ka je ka yi Sallah, ba ka jin Masallacin gidanku ma anyi kira??" Gyaɗa kai ya yi ba tare da ya ce komai ba, ya nufi cikin gidan. bai bi takan kowa ba ya yi Alwala ya bi Jam'in Sallar bayan an Idar ya shige cikin gida. ba shi ya fito ba sai yamma liƙis lokacin har an gama kasa Ƙwallo shi ake jira, ya na fitowa kuwa su ka fara. Sun yi nisa cikin wasan Nana Kadija ta tawo tsogal-tsogal ta sha ado cikin wando ja Da baƙar Riga iya guiwa wadda aka yiwa adon duwatsu ta yi Rolling da ɗan ƙaramin Mayafi Ja, sai Glass No Respect baƙi ta haɗe girar sama da ta ƙasa, tsaki ta ja ganin sun cika layin su na Ƙwallo kamar mallakinsu, Walid ne ya kula da zuwanta ya ɗaga murya ya na cewa "Ku tsaya a wuce!" Banza su ka yi masa har sai da Abdulkareem ya ce "Dalla ku dakata mana ko bakwa gani ne?" su ka tsaya su na kallonta, ita kuwa ta girgiza sannan ta ci gaba da takawa kamar me tsoron Ƙasa, sai da ta zo saitin Abdulkareem sannan ta ja wani dogon tsaki ta tsartar da yawu ta bashi wani banzan kallo sannan ta yi gaba. cike da mamaki ya bi ta da kallo ya na cewa "Kaii!!?? ke zo nan, ni za ki kalla ki yiwa tsaki harda tsartar da yawu?" ta juyo a fitsare ta ƙare masa kallo sannan ta kuma wani tsakin, Muktar ya ce "Haba Master ba da kai take ba da mu take fa, ƙyaleta kawai." Fuska ya haɗe ya ce "Ku tara min ita in ji in ni sa'anta ne." Walid ya ce "Me za ka yi mata to? ka ƙyaleta mana ai ba da kai take ba." "Wallahi in ta bar sashin nan ba ku tare ta ba sai ran kowa ya ɓaci" ya na rufe baki su ka bi bayanta su ka sa ta a tsakiya, ya yi tsalle ya tsinko ƙaramin reshen bishiyar da suke ƙarƙashinta ya gyarata sannan ya nufi inda suke, Sai tsiwa take zuba musu bakinta ya ƙi mutuwa gashi sai keɓe baki take yi ita a dole ƙyamarsu take. buɗa masa su ka yi ya shigo tsakiyar ganinsa da bulala ya sa ta zaro ido ta na cewa "Wai meye hakan??" bulalar ya shiga sauke mata a gadon bayanta, tin ta na mazewa har ta fara kuka ta na roƙonsa, sai da ya daka iya son ransa sannan ya ce su bata guri, su ka buɗa mata hanya, Abdulkareem ya ƙara zuba mata ɗaya gami da cewa "Ƙetare Ƴar Bantan Uba ta Danƙi Harawa." Nana Kadija ta tsallake da gudu, duk ta watsar da iyayin nata ta fara gudu, ba ta tsaya ba sai da ta shige gida, ta je da kuka yare-yare. Abdulkareem kuwa ko a jikinsa ya ce su ci gaba da Ƙwallon. sai bayan sun tashi ya koma gida ya tarar da ita har lokacin kumburi take, ta yi murjai-murjai. Ummi ta ce "Babban Mutum me ya haɗaka da Nana Kadija??" "Au wai zuwa ta yi ta ce na daketa??, to me yasa ba ta gaya miki abin da ta yi min ba?" Ummi ta ce "Ba tambayarka na yi ba?? ka kama Budurwar Ƴa a gaban Yara ka zaneta haka ake yi??" "To Ummi tin da ba ta da kunya ai wallahi fin haka ma za ta samu, wai fa kallona ta yi ta min tsaki ta tsartar da yawu, ƙarshe dai kinsan cewa za ta yi wai ina wasa da ƳaƳan Talakawa, to ina ruwanta? ki ga ta na yawo a layi kamar figaggiyar tantabara ita a dole Ƴar Masu kuɗi, na bi kuɗin da gudu ba Silifas, sai na karya mata ƙafa idan ta ƙara yi min irin wannan iskancin" Cike da tsiwa ta ce "Eh ɗin ni na fi figaggiyar tantabarar ma, aikin kawai ba dole ma ka sa a dinga raina mutane ba ka na shiga cikin ƙazaman can kuna wasa, wai Ummi ba za ki hana shi wasa da su ba? Kuma wallahi Ummi indai ya ƙara dukana sai na rama ai jiki bai fi jiki ba, kwata-kwata shekara uku fa ko huɗu ka bani shine za ka maidani kamar ƴar cikinka, to wallahi ba ka isa ba." "Idan kin gama surutun sai ki tashi ki rama yanzu ai ga jiki ga tsoka, ko da minti Ɗaya na girmeki ai na girmeki dai, kuma ni Namiji ne a Matsayin Ubanki nake ɗaukar kaina." rasa abin cewa ta yi don haka ta ƙara fashewa da kuka, Ummi ta ce "A gaskiya Auta ni kaina raina ya ɓaci, abin ya isa haka Nana Kadija fa ta girma, Sakuwarka ce fa, ka dena Dukanta don Allah musamman dai a waje gwara ma a cikin gida ya fi rufin asiri, ba ka san ma idan mace ta girma dena dukanta ake ba?" "Wannan ƴar Ummi tinda ba ta yi hankali ba ai kuwa ba ta girmi duka ba." ya faɗa gami da yin gaba ya basu guri don ya gaji da jin gunjin kukan nata. Ummi ta ce "Allah i shiryeka to" Nana Kadija ta ce "Wallahi Ummi bakwa son yi masa faɗa ne shi yasa duk ya bi ya addabi kowa." Murmusawa Ummi ta yi kafin ta ce... © INDO & AUTAR JARUMAI [7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga ELEGANT ONLINE WRITER'S Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S Shafi 5 "Ba ya aikata abu mara kyau, shi yasa za ki ga kamar ba a son yi masa faɗan ne, ba za ki gane hakan ba sai kin sawa kanki nutsuwa. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya a kowane ɓangare ba wani sauyi. Aaminat Kullum jiya i yau ne ba ta da lokacin farin ciki, ko da ba ayi mata komai ba idan ta yi tunanin rayuwarta ita kaɗai sai ta kama kuka. Yau su na zaune su na hira Abdulkareem ya ke cewa, "Wai Kwanan nan naga Walid ba ya yi min magana, ko wasa ake yi da shi idan na shigo sai ya fita, me yasa haka???" Kowa ya ja bakinsa ya yi har sai da Abdulkareem ya ƙara maimaita tambayarsa sannan Amiyo ya ce "Ni fa ba zan ɓoye maka ba wallahi, munafukan ba sa son gaya maka gaskiya shi ya sa ka ji sun yi shiru." Abdulkareem ya ce "Yauwa Mutumina zo ka zauna kusa da ni." Amiyo ya furmutsa tsakiya ya zauna sannan ya ci gaba da cewa "In gaya maka, ba ramar nan ka zane ƙanwarka ba? to ai shine ya ke jin haushinka wai shi sonta yake". Abdulkareem ya yi dariya kafin ya ce "Ita Ƙanwar tawa ya ke so??" Amiyo ya ce "Ƙwarai da gaske, kar ka ƙara kar ka raga hakan ne ya sa ya ke ta jin haushinka." Abdulkareem ya ce "Lallai ma yaron nan, bar ni da shi zan ji da lamarinsa." Muktar ya ce "Kai kuma da tsinin bakinka ya gaya muku sirri amma ka zo ka kwashe ka faɗa." "To zaman munafurci da cin Amana kake so ayi da ni? aa ba zan iya ba" Abdulkareem ya ce "Kar ka damu Amiyo gwara da ka faɗa min ai, wai ni kam Ya akai naga Chokali yau ba iyayin nan? "Cokali Cokali!" wai lafiya ka zabga ta gumi?" Bilal ya tambaye shi, kallon shi kawai ya yi ya ƙara maida kai ƙasa, Amiyo ne ya ɗanyi ƙasa da kai yace "Babarsu ce ba ta da lafiya" da sauri Abdulkareem ya dafa Abokin na shi cike da damuwa ya ce "Haba Haisam mene amfanin zaman mu waje ɗaya in har ba za mu magance matsalarmu ba? kamata yayi ka sanar min tun wuri mu kaita asibiti" tashi yayi ya run gume Abdul yana kuka "nagode Allah ya ƙara arziƙi " Abdulkareem ya murmusa "karka ƙara yi min godiya, babu godiya tsakaninmu maza kaje ka ce su shirya za mu tafi Asubiti" da ' to" ya amsa sannan ya nufi gidan nasu, ɗaki ya shiga ya tarar da Sumayya ƙanwarsa se faman kuka take tana shafa mata ruwa cikin rawar murya ya ce "ki kintsa Inna za a kaita asibiti" to tace tana tashi. tuni Abdulkareem ya fito da mota yana jiran fitowarsu Sumayya ce ta rungumo ta suka fito murfin motar ya buɗe suka shiga da Inna, Haisam ya shiga gaba shima ya shiga ya tada motar ya fara tafiya cikin nutsuwa duk da sauri yake amma hakan be hana shi bin hanya a hankali ba se faman jerawa Inna sannu ya ke har suka isa A.I HOSPITAL Asibitin Daddansa duk da babu wanda ya sani cikin Abokan na shi. danda nan aka bawa Inna gado likitoci guda uku ke kanta suna ƙoƙarin ceto ranta. "Ummi ki ƙara kiran shi na kira ba a ɗauka inaga baya kusa ne" Nana Kadija ta faɗa cike da damuwa, wayar ta ta ɗauka kai tsaye ta danna wa shalelenta kira dede lokacin Abdul ya buɗe ƙofar motar ze ɗauki waya ganin sunan Ummi ya baiya na akan fukar wayar yasa yayi saurin ɗauka ya kara a kunne, Muryar Ummi ce ta daki dodan kannan shi tana cewa "ɗana kana ina? ina ka shiga?" "Ummi ina Asibiti Maman Cokali ce bata da lafiya" "ayya Allah ya bata lafiya waye kuma Cokali?" "Haisam Aboki na Ummi" "to jikin da sauƙi ko?" "eh Ummi mun ma kusa tahowa in sha Allah" "to Allah ya ƙara lafiya se kun dawo kakula ka ji?" "to Ummi. daga haka su ka yi sallama ya koma ciki Cike da fustara da rashin kunya Fati ta ke cewa "wallahi sekin biya ni kuɗina wa yace ki ɗaukar mini?" Aaminat ta ce "dan Allah kiyi haƙiuri ranta nayi in na samu zan baki" "taɓ baki isa ba yanzu zaki biya ni kuɗina ko mu daku" jin Fati ta kira dakuwa yasa Aaminat zaro ido ta sani zata aikata, Umaima ce ta shigo dakin tana cewa "ke ƙaramar Bazawara zaki biya ko se mun fara salawaitun bala'i ne" "kuyi haƙuri zan baku in anjima" "wallahi yanzu zaki bani kuɗina ko na faɗawa Abba kin satar min kuɗi" "Haba Fati kin sani bana sata kar kiyi min ƙazafi zan biyaki kuɗinki, yanzu ba ni da su ne in da akwai ai da ban kai ga ɗaukar nakin ba" "to biyani" rausayar da kai tayi tana tunanin inda zata samu kuɗi ta biya Fati tunawa tayi da Siyama ta yi saurin miƙewa ta na faɗin Alhamdulillah. Fati ce ta cakumi wuyan Aaminat ta na cewa "ina za ki je baki biya ni b? wallahi babu inda zakije se kin biya ni!!" ta ƙarasa maganar cike da bala'i. cikin muryar kuka tace "zanje gidan su Siyama na aro na biya ki" "koma ina ne muje tare" kibari na kawo miki karki bini dan Allah" murgu ɗa baki tayi tace "maza ina jira ki da wo" Umaima tace "kuɗi ne de se kin biya shi ehhe" Aaminat ta ce "To sakar min wuya sai in tafi." "Abin ya ci tira ma bayan takura har da sata Alawadai da wannan zawarci, azo a damu iyaye a damu ƙanne yanzu ma an fara sata, Ba dan Allah ya tona miki asiri ba da tuni shi kenan kin sha ni na warke" Fati ce ta ke zazzaga masifa hannunta riƙe da ƙugunta har wani ɗan girgiza take yi, Aaminat ta share hawaye kafin ta ce "Kar ki fitar da ran kema Allah zai jarrabeki Fati, nima ban taɓa tunanin hakan ba gashi ta faru da ni." "Allah i kyauta ya kare hawala, ai wallahi ni nafi ƙarfin zawarci na riga na bashi baya, ke dai da baki da daraja ke Allah ya ɗorawa amma ni wallahi ko tawo mu gama ba zan taɓa yi da shi ba, ya ƙare dai akanki. Umaima ta ce "Ato wallahi fa" Aaminat ba ta ƙara ce musu komai ba ta fita domin samo rancen ta biyata ta huta. Fati da Umaima kuwa zancenta su ka dasa Umaima ta ke cewa "Ni fa wallahi har ba na so ma ta ƙara yin Aure yanzu kinsan sabi da me?" Fati ta ce "Sai kin faɗa, ni dai na fi so naga ta kauce ta bamu guri don wallahi wannan kashe mana kasuwa za ta yi, ba dan ita ba ma ai da yanzu batun Aurenmu ake yi, amma komai sai dai ace Aurenta ita kuma na lura Tafi son me Ido a tsakiyarka (Duniya)" Umaima ta ce "Ke baki kwashe ba dalla, ni aikin da take yi mana ne ya sa ba na son Auren nata, kinga ba ruwanmu da wanke-wanken safe ba na Yamma, girki ma ba kullum ba, share-share kullum sai dai ta yi mu ɓata, shi yasa fa ba na son ta tafi." Fati ta yi dariya gami da ɗakawa Umaima duka a cinya ta ce "Shegiya ke kin gano laƙabin ashe, wallahi fa haka ne, nima sai yanzu na gane amma fa kamata ya yi mu muna da samarinmu Aurenmu za mu yi ita kuma ta na yi mana aiki, kin ga sai ta ƙare a Aikin wanke-wanke, kinga wannan Bikin da za ayi na Ƴar Umma Sa'a? wallahi dagewa Za mu yi mu samo Samari masu aji da kuɗi a Wajen Dinner nan kin ga ai mijin Umma Sa'a ya na da Ƴan Kuɗaɗensa, nasan shima wanda Bilkin za ta Aura hakane, to a ciki za mu ƙure wanka mu zaɓi santalele mu yi wuf da shi" Su ka yi shewa su ka tafa kafin Umaimai ta ce "Wallahi kanki ya na kawo wuta My Sister, ayyiriri!!! ai sai dai ki ji ana mana buɗa, ni kuwa za ta iya zuwa bikin nan ma?" "Sabi da me ki ka ce haka?" "To ai naga ba ta ƙaunar shiga jama'a itama kanta kunyar kanta take. Fati ta ce ''Ba lallai ta je ba kuwa, musamman Dinner ɗinnan, yo mutum ne kamar mujiya ba farin jini." Umaima ta ce "Allah i sittira to" Shigowarta ce ta katse musu hirar, ta miƙawa Fati kuɗin gami da cewa "Ga shi nan ai ba a rasa masu tausayi, tin da ku ƴan uwana ba ku tausaya min ba na samu me tausayina." Fati ta yi mata kallon tara saura kwata ta ɗiba ta watsar ba tare da tace uffan ba, Umaima ta ce "An dai ji, tinda kin biya kin huta da kin yo aman su a gurin nan" cike da takaici ta ce "Umaima uwa ɗaya uba ɗaya mu ke ni dake amma kin ɗauki Tsana kin ɗora min sabi da jarrabawa ta same ni, wai ba ku san ƙaddara ba?" Umaima ta buntsira baki gaba ta murguɗe ɗankwalinta ta ce "Ai ba wani ne ya ce ki kaso Auren ki zo ki dame mu ba." "Wallahi da kunsan waye Kamal da ba za ku dinga cewa na kashe Aurena ba" ta yi maganar ta na sharar ƙwallah, cike da rainin hankali Fati ta ce "Allah sarki!" shiru ta yi musu su ka ci gaba da ƴan maganganunsu. Yau ta kama ranar Wunin Bikin Bilkin Umma Sa'a, sai yamma liƙis ta shirya kowa ya tafi ya barta don babu ma wanda ya ce ta shirya kawai dai ta yi ra'ayin zuwan ne duk da ba a gaiyaceta ba. Riga da Sket na Atamfa ta saka sun kama jikinta sosai, ta yi ɗaurin ture ka ga tsiya ta yafa mayafinta akan kafaɗarta, kamar ko da yaushe iya Kwalli ta saka sannan ta zura Plat Shoe ɗinta, kayan duk sun takure ta kamar ta cire har ta koma za ta canja wata Zuciyar ta ce kibar kayanki, ta ɗauki mukullin gidan ta rufe sannan ta fito. a hankali ta ke tafiya kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki, tunanin Kamal take yi, ko shakka babu ya taka rawar gani wajen tarwatsa mata farin cikinta, indai ana samun maza irinsu to fa kowace mace ma za ta iya fuskantar rayuwa ta garari kamar yadda itama ta fuskanta. firgita ta yi sabi da jin muryar Abdulkareen a dodon kunnenta "Haba YaYa Aaminat don Girman Allah ki koma ki canja kayan nan, wallahi sun yi miki ƙanƙanta kamata ya yi ki dena saka su ma. Bakinta har rawa ya ke wajen cewa "Bab.. ba.. bazan canja ba, ina ruwanka da ni?" ya ɗan yi dariya kafin ya ce "Ba ruwana da ke kawai karambani ne, ina za ki je ma??" Ta ɗan murguɗe baki ta ce "Bikin Ƴar Ƙanwar Abbanmu ake yi" Idanu ya zuba mata ya na binta da wani sihirtaccen kallo, sai murmushi ya ke wanda bai ma san ya na yinsa ba "Kin iya murguɗa baki YaYa Aaminat" tsaki ta yi gami da ci gaba da tafiya ta na tuhumar kanta ma dalilin da ya sa ta tsaya saurarensa. cikin sauri ya tare hanyar ta fuska a haɗe ba alamun wasa ya ce "Aaminat bar ɗaukar zancena a wasa fa, idan ƙanwata ce ke ba zan bari ki fita da kayan nan ba bare ke YaYata, don Allah ki koma ki canja sai ki tafi." "Ba fa zan canja ba" "Ni kuma indai ba za ki canja ba nima ba zan barki ki wuce ba wallahi sai dai ki fasa zuwa bikin, kin ji har na rantse" "Wai ina kake so in sa kaina Abdo..." ɗaga mata hannu ya yi cike da manyance ya ce "Na gama magana Aaminat, ki yi haƙuri ki dinga sitirta min kanki." ya na rufe baki ta ɗauki hanyar komawa gidan zaizaizai ta na tafiya ta na haɗa hanya bakinta ɗauke da Addu'a a cewarta neman tsari take da sharrin Abdulkareem, duk ilahirin jikinta ya ɗauki tsuma, ai kuwa indai gaskiya ne abin da Zuciyarta ta ke gaya mata akansa ai kuwa Kamal ya sa ta tafka babbar asara a rayuwa, ya yi mata tozarcin da ba lallai a samu tozartacciyar mace irinta ba.... ©️ INDO & AUTAR JARUMAI [7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga ELEGANT ONLINE WRITER'S Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S Shafi 6 Bismillahirrahmanirrahim Sabi da takaici sai ta ji kamar kar ta je Bikin ma, Doguwar riga Abaya ta ɗakko ta ƙare mata kallo aranta ta ce Wannan dai duk jarabarsa ai ba za ta kama jikina ba, Sakawa ta yi sannan ta Ɗakko Hijab ta saka a cewarta ta ma fasa saka mayafin, ta ƙara fesa turare sannan ta fito cikin sanyi jikinta duk ya mutu, ta cikin mirror ya hangota, ganin yadda ta zuba Hijab ya sa shi sakin murmushi, kwata kwata ba ta lura shine a Motar ba sai da ta zo wuce ya yi Hon da ƙarfi, ta maruƙar razana da artawa za ta yi da gudu sai ta cije, ya fito ya na dariyar shakiyanci, har ya je ya yi shirinsa cikin Ƙananun Kaya Baƙin Wando da Farar riga me ɗan ƙaramin hannu, "YaYa Aaminat zan je gidan mai shiga in rage miki hanya" ya yi maganar ya na murmushi gami da kasheta da fararen idanunsa, cikin sauri ta girgiza kai ta ce "Ba zan shiga ba" Takawa ya yi cikin nutsuwa ya matsa kusa da ita idan ya matso sai ta matsa har sai da su ka kai bango sannan ta tsaya ta zuba masa ido don ganin ƙarshen tsagerancin nasa, asalin ƙwayar idanunta ya ke kalla wanda yake iya karantar abubuwa da dama daga cikinsu, cikin wata kasalalliyar murya ya ce "Allah Aaminat idan ki na yawan yi min gardama zan nuna miki bambancin Wa da Ƙanwarsa, ki shiga ko na sa ki da kaina, ki ka tsaya kina kallona." cike da takaici ta ce "Wai kai ko kunyar faɗen sunana kai tsaye ba ka ji? aƙalla fa na yi ƙani na biyar ko shida da kai, amma don rashin kunya kake min abu kamar wani Babana don wannan isar taka ta fi ƙarfin YaYa, ba fa zan shiga Motar nan ba sai dai ka yi duk abin da za ka yi, akan na bi ka gwara na fasa zuwa, ba za ka jaza min bala'i ba yanzu ace kuma bin maza na koma yi" Ido rufe take maganar cike da son nuna iyakar gaskiyarta, shi kuwa ya yi shiru ya zuba mata ido ya na wani Sassanyan murmushi, sai da ta gama surutun ta ƙara kallonsa ta ga ko gezau bai yi ba, ta ƙara jan dogon tsaki ta ratsa ta kusa da shi za ta wuce ya yi saurin riƙo hannunta gami da cewa "Ohh Aaminaathhh!!" yadda ya kira sunanta ya mugun taɓa Zuciyarta ta tsaya cakk gami da rintse idanunta ta cije gefen leɓenta, zagayowa ya yi gabanta ya na ƴar dariya ya ce "Me yasa ki ke son ɓata min lokaci har ma da ke kanki, Aaminat tin da ki ka fito sai kin je kuma ni zan kai ki" shiru ya ɗan yi kafin ya saki wani malalacin murmushi ya ce "Komai naki har Zuciyata! kina bala'in girgizani a duk motsinki Aaminathh!!" "Kai Master hannun YaYa Aaminat ɗin ne a cikin hannunka???" Bilal ya jefo masa tambaya cike da mamaki, cikin sauri ta fizge hannunta cike fa baƙin ciki da takaici, ji take inama za ta iya ta kikkifa masa mari ko zai gane ba sa'arsa bace, shi kuwa da ta fizge hannunta sai ya saki murmushi ya shafi sumar kansa sannan ya ce "Bilal wai unguwa zan je shine ba zan rage mata hanya ba." Bilal ya ce "Yaya Aaminat ki yi haƙuri ki shiga mana, kin san shi kin san gidansu ai ba zai sayar da ke ba, ni bari inzo in raka ku ma." tsaki ta ja kafin ta shiga gidan baya don ta lura sabi da naci za su iya cinyeta, Abdulkareem ya dafa kafaɗar Bilal cikin muryar raɗa ya ce "Ba za ka je ba munafuki" Bilal ya yi dariya ya ce "Na ji , wallahi sai in ce kar ta bi ka ma" talle masa ƙeya Abdul ya yi ya na dariya sannan ya shige gidan direba ya fige motar. Tasan dama ba gidan man zai je ba don haka ko da ta ga ya ƙi tsayawa ba ta ce masa komai ba, shi kuwa ya na tafiya ya na waiwayenta daga baya ma sai ya saita Mirrorn cikin motar zuwa kanta. "Wace unguwa za ki je??" "Ba na so fa ka kaini inda dangina za su ganni tare da kai su dinga zagina, gwara ka ajiye ni in tafi a Napep" "Tin ina ɗan shekara goma sha biyar na iya Driving kawai ba a bani mota ne, sannan a gidanmu akwai motoci sai wadda naso nake hawa, kuma duk bayan wannan sai na barki ki tafi a Napep bayan gani ba aikin da nake yi? kema kinsan ai a tsarina babu haka, kawai neman ɓata bakinki ki ke yi, tin da nace zan yi kinsan sai na yi." Dogon tsaki ta rafka gami da zuba tagumi ta ɓoye fuskarta a cikin hijab, ya yi murmushi kafin ya ce "Ya Aaminat! Wallahi in kina murmushi har kusan suma nake yi," cikin sauri ta ɗago kai ta na cewa "Iye???? Abdul me ya ke damunka ne??" dariya ya yi kafin ya ce "Kin ga dai na sa kin ɗago duk da kin ɓuya, kinga bambancin babba da yaro kenan" "Ni kake kira yarinya??" "A haka nake ɗaukarki Aaminat domin ina da muradin zamo miki bango a Rayuwarki" baki na rawa ta ce "Abdulkareem Rijiyar Zaki za ka kaini don Allah ka dena lelewa da ni akan titi kar ka ɗauki raina kafin na je bikin nan, wallahi nayi da na sanin fitowata zamana a gida ya fi Alkairi, yanzu na tabbatar kai Mahaukaci ne, meye haɗina da kai??" "A zahirance ba alaƙa a tsakaninmu ta jini ko ta wani abun ba abin da mu ka haɗa, sai dai shi Allah babu rawansa baya damuwa da matsayin wani ko wani sai ki ga ya haɗasu Alaƙar, ni dai ina jin akwai alaƙa a tsakaninmu kece dai bakya jin haka, a gurina Ba ki da bambanci da Nana Kadija Nana Fareeda Nana Hauwa'u, dake da su duk ƙannena ne." "Ciwon Zuciya ne ajalina na tabbata, abin duniya ya yi min yawa, ka rufa min asiri ka barni na rayu da baƙin cikin da yake damuna kar ka ƙara min wani tashin hankalin, ka tausaya min ka cire ni daga sahun Ƙannen nan naka don girman Allah" murmushi me taɓa Zuciya ya yi kafin ya ce "Ba ni na sa ki da kaina ba, kuma ba ni da ikon cire ki, ki tayani da Addu'a indai cutata me warkewa ce zan warke in kuma ba zan warke ba to fa ba na jin zan iya bari ki zauna lafiya ko ina ki ka shiga, ki ɗauke ni a matsayin ƙaddararki Aaaminathh!" "Abdulkareem Na tsaneka!!" ta faɗa tare da fashewa da kuka, Murmusawa ya yi ba tare da ya ce komai ba, Zuciyarsa banda ƙuna ba abin da take yi, a take idanunsa su ka canja launi. ba wanda ya ƙara magana har su ka isa unguwar sannan ya ce "Idan za ki iya ki kwatanta min in ba za ki iya ba sai mu zauna tare a motar don ni ba na gajiya da kallonki ko da gaban tsana za ki yi min." ta san aikata hakan ƙaramin aikinsa ne don haka ta murje idanunta ta kwatanta masa. har ƙofar gidan ya kaita ya na tsayawa ta buɗe ta fito, cikin sauri ya fito ya zagayo inda take ya na cewa "Aaminat don Allah in da wata damuwar ki kira ni, duk lokacin da za ki tafi ma kawai ki neme ni." girgiza kai ta yi kafin ta ce "Ina Addu'ar kar Allah ya kawo min ranar da zan nemeka don kaina." ya ɗan yi murmushi gami da cewa "Na ji Aaminat, amma ni ba zan yanke ƙauna ba , na ce wata rana za ki neme ni." Fiddausi ce ta kasa yin shiru ta ƙaraso wajen hannunta riƙe da haɓarta, "Aamina?! tabbas ba shakka, ke aka aje a wannan Motar lunƙumemiya??" Abdukareem ta zubawa ido cike da takaici take binsa da kallon ka ga abin da ka ja min, ya rausayar da kai gami da cewa "Ki yi haƙuri YaYa Aaminat na yi miki shi....." ɗaga masa hannu ta yi kafin ta yi gaba, Fiddausi ta kalle shi kafin ta ce "A kawo maka ruwa Yallaɓai??" a taƙaice ya ce "Sauri nake aikena aka yi shine naga Auntynmu na rage mata hanya." "Laaa Abdulkareem me ya kawo ka Bikinmu?? ko dama kasan ana bikin ne??" Fati ce ta yi magana cike da mamakin ganinsa. "Ke ni wa na sani a cikinku, YaYa Aaminat na kawo, an aikeni ne shine na rage mata hanya" a take annurin fuskarta ya ɗauke ɗiff ta taɓe baki ta ja hannun Fiddausi. Zagayawa ya yi ya shiga mota ya na mamakin sa ido irin na mutane, ya na ankare da tinda ya zo ya tsaya kowa idanunsa na kansu, har ya koma gida tsaki yake ja gabaki ɗaya duniyar ta yi masa zafi, Abdulkareem Na Tsaneka idan ya tuna kalmar sai ya ji kamar ya yi hauka sabi da zafinta da yake ji. Tin da ta shige gidan duk wani abu da za'ayi ta na ciki ta ƙi fitowa, ta na kallon mutane har zuwa ake ana leƙota ana ɗan nunata, ita dai ba ta ce komai ba sai dai in abin ya yi mata ciwo ta ɗan matse hawaye, jiran tafiyar su Umma take yi su kuwa sai Goman dare sannan su ka tashi tafiya, lokacin da su ka iso gida Sha Ɗaya sauran Ƴan Mintina, ta ji daɗin hakan don kuwa duk Fitinannun yaran layinsu sun shige gida har shi kanshi Gogan, tinda ta yi siff ta shige gidan makonci kawai ta nema don anan ne za ta samu damar yin kukanta ba tare da kowa ya sani ba. Yau Abdulkareem ya na zaune shi kaɗai sauran Yaran kowa ya tafi uzurinsa wasu makaranta, Walid ne ya tawo ya na taku a ƙasaice kamar wani Yaron Giwa shi a dole babban Mutum, sai da ya kalli Abdulkareem sannan ya watsar ya wuce, Abdulkareem ya miƙe ya riƙe hannunsa kam sannan ya ce "Kai daga ina kake??" "Ina ruwanka? ka aike ni ne? ba na son shishshigi ba kwarjini" Wani kyakkyawan Mari Abdulkareem ya tsinka masa sannan ya ce "Da ni kake gaba ko?? sabi da na doki ƙanwata da ba daga gidanku ta fito ba, ni za ka nunawa rashin hankali?? ashe kasan abin da ciwo? ranar nan da ka dokawa YaYa Aaminat Ƙwallo don ban nuna ɓacin raina ba shine kai za ka yi Gaba dani sabi da na doki Ƙanwata ko??" cike da rashin kunya irin tashi ya ce "Eh an buga mata ɗin ai naga YaYata ce ko, wallahi ka ƙara dukana sai dai mu daku." wani lafiyayyen marin ya ƙara zuba masa sannan ya ce " Na ƙara maka kuma zan ja maka kunne, rashin kunyar da ku ke yiwa Aaminat ta isa haka, nima ina jin zafi bansan ba daɗi ba sai da ka fara gabani wai akan ka na son Ƙanwata, to wallahi ka shiga hankalinka da kai da ita duk ina iya karya muku ƙafafu na zauna lafiya, nima ina jin zafin da ka ji a duk lokacin da kuka wulaƙanta Aaminat kawaici kawai nake muku" Walid ya yi tsaki kafin ya ce "To wai kai me kake nufi?" "Ban damu da sai ka san me nake nufi ba inda ka fahimci akan abin da nake magana, kuma wallahi tallahi ka je ka yi min munafurci ko a gida a Layi sai na lahira ya fika jin daɗi, ni zan rabaka da farin cikin rayuwa ne har ka koma ga Allah, kuma na ƙara yi maka magana kai min banza ka ga in ban sauke maka na tauna ƙashi ba." Walid ya zumɓuri baki, yasan an fi ƙarfinsa don haka bai yi ƙoƙarin wani abu ba, ya na sakinsa ya wuce gida ya na gungunai da kumfar baki. Mama ta bankaɗe labule ta fito ta na cewa "Wa ya taɓa ka???" "Wancan Dan Iska Abdulkareem ɗin ne har da marina ya yi ba abin da na yi masa kuma." "Kanbutar Duma???, sai na sa an ci uwar Abdulkareem ɗin nan sannan zai fita idona in rufe, Umar! Umar ! maza kira min Umar ai ya dawo" Walid ya fita kiran Umar Mama kuwa ta ci gaba da zazzaga masifa, Umar ya na zuwa ta ce "Wannan Abdulkareem ɗin nake so ka ci min Ƙanwar Tsohuwarsa, ya raina min Ƴaƴa yanzu Fati in ka ga wulaƙancin da yake sa yara su yi mata sai ka sha mamaki, yanzu ka ga ya kama min Auta ya mammara ba tare da laifin komai ba, to wallahi in ya na da ƙarfin damtse ai doka ta fishi, ni zan iya yin shari'a da shi tinda ba shi da hankali" Umar ya yi murmushin takaici kafin ya ce "Mama indai Mari ne kawai ayi haƙuri don kuwa Kinsan Waye Alhaji Aminu Mai Kasuwa, ya na da kuɗi kuma ya ɗaurewa ɗansa abun shi yasa ya ke tata iskancinsa, ba za mu iya nuna masa yatsa ba gwara ma ki yi haƙuri, Shari'ar da ki ke taƙama da ita ba za ta goyi bayanki ba bare har ki ga ribarta, ba iya ku ya ke yiwa ba ya gagari kowa a layin nan, ki na gani fa ko Ball da su ke yi a layin Matasan Layin sun yi ƙoƙarin hanawa daga nan har gaban hukuma yaron sai cewa ya yi ai idan ana so su dena sai dai a basu babban Filin Ball, kuma lokacin manya ne su ke yin wasa a a wai sai dai manya su haƙura su ba yara, ance su dinga yi da rana ya ce ai su ba cima zaune bane su na sana'a kuma suna neman ilmi ba su da lokaci sai da yamma, dole fa muna ji mu na gani mu ka ƙyalesu, Kina gani a layin nan manyan samari ƴan shekara Ishirin da Bakwai ma ba za ki gani ba bare ƴan talatin sabi da tsabar bala'in yaron nan duk sai dai su bar unguwar nan su shiga unguwar maƙota sannan su kafa Majalisa, yanzu babu samarin da za ki gani sai yara ƴan sheka Ishirin zuwa ƙasa, Mama wallahi yaron nan tantiri ne fiye da tunaninku, kaff yara masu tasowa ya lalata su ba sa ganin kowa da gashi sai shi. Mama ta ja tsaki sannan ta ci gaba da yayyafin masifarta sai ma ta koma cewa don ba Ita ta haifi Umar ɗin ba ne ya sa ya ƙi ƙwatarwa Ɗanta haƙƙi, shi kuwa Umar sai ya bar mata gidan Umma ma ta na jinta ta yi shiru, Aaminat kuwa ta na son yin magana akan rashin kunyar Walid ɗin amma idan ta tuno waye Abdulkareem sai ta ja bakinta ta tsuke. ©️INDO & AUTAR JARUMAI [7/26, 2:46 PM] INDO: https://chat.whatsapp.com/DkGGck6Es6l4w7KMwiaGVZ *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga ELEGANT ONLINE WRITER'S Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S Shafi 7 Bismillahirrahmanirrahim Fati ce ta fito daga ɗaki ta na cewa "wallahi Mama karki yarda, ai ɗa befi ɗa ba haifar shi ki ka yi shima haifar shi akai" cikin baƙin ciki da takaici Mama ta ce "kina gani fa na kira Umar ya je ya rama masa sabi da ba ni na haife shi ba yaƙi ya kama ƙalabusan banza, shima yaron ai ɗan iska ne dama ƴaƴan masu kuɗi haka suke iskanci iri-iri" Aaminat ta kasa jurewa sai da ta shiga zancen, "Haba Mama shi fa yaron nan anan gurin babu ruwan shi Walid ne da shegiyar tsokana, na san halinsa ba kunya ce da shi ba" "to? lamarin hada zawarawa dama?" Fati ta faɗa tana riƙe baki kafin ta ƙara cewa "ai dole ki ce haka tun da yana ce miki Anti kuna sheƙe ayar ku" dole tasa Aaminat ta fito daga ɗaki tana dafe kirji Umaima ta ce "ko bahaka bane kike ɗafe ƙirji?" wata shewa Fati tayi kafin ta ce "Hee!! ni naga abun mamaki Mama Ranar bikin Bilkisun Umma Sa'a fa Abdulkareem ne yakai ta a Mota" Mama ta yi salati tana tafa hannu tana cewa "innalillahi wa'inna'ilaihirajiun Aamina dama haka kike?" Fati tace tafi ma haka ku ne baku sani ba, ai wallahi Allah ne kaɗai ya san abin da su ke aikatawa ita da Abdulkareem ɗinnan" Umma da ke jin maganar su kamar ana zuba mata wuta ajiki bata san lokacin da kuka ya kufce mata ba tana cewa "Aaminatu da abinda zaki saka min kenan? kin san dai na baki tarbiya shine za ki dinga biyewa wannan Ɗan iskan Yaron da kowa ya san bai da kyakkyawar Ɗabi'a?, na gaji da baƙin cikin da ake sa ni a gidan nan, wallahi na gaji" jiri ne ya ɗebeta luuu tayi ƙasa cikin hanzari da tashin hankali Aaminat ta sa hannu ta tallafo Umma ta na cewa "Wallahi Tallahi Umma ni ban taɓa aikata komai ba, babu wani abu tsakanina da Abdulkareem, hasalima ni na tsane shi kawai sharri ne aka son yi min" Umaima ta fashe da kuka tana cewa "wallahi baza mu yarda ba in ta mutu ke ki ka kasheta macuciya muguwa, ba wani sharri da akai miki ai kowa ya ganki, indai da ke mutuniyar kirki ce ai ba za ki kashe Aurenki ba" cikin tashin hankali take faɗin haka Aaminat kuwa ta shiga matsanancin hali, Temakawa Umman ta yi ta shigar da ita Ɗaki ta kwantar da ita saman Gado, cikin kuka ta ci gaba da cewa "Don Allah Umma ki yarda da ni, in banda Ƙaddara ba abin da zai rabani da Mijina, ba son raina bane kamar yadda kowa ke faɗa, Umma ni ba zan aikata kuskure ina ji ina gani ba." cike da takaici Umma ta ce "Ba ni da baƙin ciki da damuwa sai naki, tin da ki ka dawo gidan nan ba ni da kwanciyar hankali, komai akaina ya ke ƙarewa, Ko me aka faɗa akanki ba zan ƙi yarda ba, Aaminat abin naki ya yi yawa, ba zan iya jura ba baƙin cikinki zai kashe ni." wani sabon kukan ya ƙara sillewa Aaminat cikin rawar murya ta ce "Wallahi ba sa ƙaunata ne kawai sabi da baƙar Ƙaddarata, ki dena yarda da su abin da suke faɗa ba gaskiya bane." Umma ta ce "Aaminat tashi ki bani guri, ki fita kawai ki barni, ni ba zan taɓa samun kwanciyar hankali ba har sai kin bar gidan nan kin tafi gidan Miji." Aaminat za ta yi magana Umma ta katse ta da cewa "Ba na son jin komai, ki tashi ki bani guri." Aaminat ta tashi jiki a sanyaye, sabuwar Ƙiyayyar Abdulkareem ta na ƙara ɗarsuwa a Zuciyarta, dama tasan sai ya ƙara jawo mata wani bala'in sannan hankalinsa zai kwanta, ɗakinsu ta koma ta tsakure a gefe ta shiga rera baitin kuka. Abdulkareem Kowa a Falon hira ya ke cikin nishaɗi amma banda shi, ya yi shiru ya na tunanin Aaminat rabonsa da ganinta tin ranar Bikin Bilkisu hakan ya sa duk ya shiga damuwa, abin da ya fi tashin hankalinsa ma rabuwar da su ka yi baram baram bai san a halin da ya jefata ba. Abdulmajid ya ƙare masa kallo kafin ya ce "Kai tunanin me ka ke ne?? ba na son ɗorawa kai wahala, kai dai ba ka da wani haufi a rayuwa sai dai in kai ka jawowa kanka abin da zai sa ka tagumi." ya ɗan murmusa cikin son kauda zancen ya ce "Ba abin da ya dame ni, kawai jina nake kamar an yi min dukan tsiya, wai yaushe za mu je Abuja ne??" Abdussalam ya ce "Wallahi Ƙarya yake, ku tuhume shi, na lura kwanakin nan ba iya yau ba ma duk ya bi ya wani firgici, ku ce ya ɗaga rigarsa ku ga yadda ƙashin haƙarƙarinsa su ka fito, duk ya bi ya rarrame amma don kafiya idan ance akwai abin da ya dame shi sai ya ce aa." Ƙasa ya yi da kai don kuwa ba shi da ta cewa Zuciyarsa ta wani mugun karaya, yanzu kuwa ya ce musu Aaminat ya ke so ta dalilinta ya shiga wannan halin, Allah ne kaɗai ya san abin da zai faru, Abdurrahim ne ya katse masa tunanin da cewa "ka Sunkuyar da kai Hakan na nufin dai da gaske ka tsumbula kanka cikin Aradu." girgiza kai ya yi zai yi magana hawaye suka fara zuba sharrrr, ya yi saurin sunkuyar da kai ya na ƙoƙarin goge su. Abdussamad ya tashi ya dawo kusa da shi ya zauna, cikin lallami ya ce "Abdulkareem, ba ka da wasu tamkar mu Ƴan uwanka, mu ne dolenka, kar ka ɓoye mana abin da ke damunka ka faɗa mana." Ummi da ta ke binsu da ido sai a lokacin ta ce "Gaskiya ne Auta, ka faɗa ko da da temakon da zamu iya yi maka, don nima na lura abin har ya fara yawa musamman a cikin wannan Ƙadamin." Murmushi me tafi da hawaye ya yi kafin ya ce "Ba zan iya cewa ga abin da ya ke damuna ba, don Allah ku zuba min ido kawai Sabi da ba ku da abin da za ku magance min damuwata" kallon kallo su ka yi kafin Abdulmajid ya ce "Abin har ya yi tsauri ne haka?? Auta ko ba a haiyacinka kake ba? ka na tunanin duk cikinmu akwai abin da zai gagara mu yi maka??" Ya rausayar da kai kafin ya ce "Ba za ku taɓa Fahimta ba YaYa, ita fa rayuwa komai matsayinsa daban, wani abin da kuɗi ake sayensa wani kuwa ko da kaine mafi kuɗi a Duniya sai ya gagareka ba za ka iya saya ba, kuma a rayuwa ba za ka ce ko da yaushe sai dai ka yi farin ciki ba, akwai Launi kala-kala a Cikin rayuwa, hakan ya na daga cikin jarrabawar ɗan Adam, duk cikar ka da kaiwarka akwai abin da ka rasa kuma ka ke da burin samunsa, don Allah a rufe wannan maganar." dukkansu sakin bakuna su ka yi su na kallonsa cike da mamaki da kuma nazarin inda kalamansa su ka dosa sai dai sun kasa fahimta me yake nufi, Nana Kadija ta ce "Ya Audu ya na da gaskiya fa, a cikin kalamansa babu na banza, a rufe zancen kawai." goge hawayensa ya yi sannan ya dalla mata harara ya ce "Ban hana ki kirana Audun nan ba??" "To ai naga Sunanka ne" "Ki na buƙatar rasa haƙoranki ko??" ta yi farrr da ido ta ce "Ba zan rasa komai ba ai dai sunanka ne kuma ba zan dena faɗe ba." filo ya ɗauka ya wurga mata ta doka tsalle ta koma kusa da Ummi, ya yi ƙwafa kafin ya miƙe ya ce "Ni waje ma zan fita" Abdussamad ya ce "Sai ka dawo!" tin da ya fita magana sai ɗaiɗai a Falon sakamakon da da suka cika shi da surutu, kowa nazarin kalaman Abdulkareem ya ke har Ita Kanta Ummi, abin da su ke ta tambayar kansu shine menene ya sa shi faɗen hakan? Tin daga ranar da Fati ta faɗi cewa Abdulkareem ya kai Aaminat gidan biki komai ya ƙara rincaɓe mata, Umma ta ɗauki Fushi da ita Mama kuwa tsakaninta da ita sai dai habaici da nuna ƙyama a cewarsu itama ta iskance, Ba ta da aiki sai na kuka sai kuma aikace aikacen tsakar gida wanda ba mai yi sai ita, Ta na son fita amma ta na tsoron ta yi mugun Katari da Abdul, yau dai ta yanke shawarar fita da tsakar rana don ta san a Lokacin yawanci ba ya zama, Ta yi sallama aƙalla biyar kafin Siyama ta amsa ba tare da ta kalleta ba hankalinta na kan wayar hannunta, Aaminat ta ce "Siyama meke damunki haka ne? sai sallama nake kamar ba ki da kunnuwa" ajiye wayar ta yi ta ja numfashi kafin ta ce "Hmm ba a magana Ƙawata, wai Ina ki ka shiga ne kwana biyu?, wani littafi nake karantawa Abin tausayi wallahi, kin ganni nan yanzu na gama sharar ƙwalla, Anti ba ta nan sai ni kaɗai a gidan kuma ba ni da aiki, ai gaskiya Novel ya na temakawa sosai sabi da ya na ɗebe kewa, dan dai bakya ra'ayinsa ne da kin rage wannan koke-koken naki." Aaminat ta ce "Novel wannan ai sai ke Siyama, amma kuma shi ne har da kuka? me ya yi zafi haka?'' "Hmm! ai dole na yi kuka, kema sai kin koka in ki ka ji abin da ke faruwa." "To wai ya sunan littafin? me ya faru kuma?" Siyama ta ce "Sai kin gyara zamanki in kina so sai in baki labari." Aaminat ta murmusa kafin ta ce "Na daɗe ban yi hira da mutane ba ma bare na yi nishaɗi, kema kin dena shigar min, yanzu dai bani labarin ko zan ji daɗi." Siyama ta gyara zama sannan ta ce "Ke ni wallahi ba na son mugun kallon da Mamanku take min, ga habaice habaicen jaraba, yanzu dai ki saurari labari, Sunan Littafin DOGON YARO Marubuciyar sunanta Ayeesha Abdulkareem INDO CE ." © INDO CE & AUTAR JARUMAI [7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga ELEGANT ONLINE WRITER'S Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S Shafi 8 Aaminat ta ce "Ni fa ban tambayeki sunan Maru buciya ba." Siyama ta yi dariya sannan ta ce "Eh na sani, amma ai labarin sai ya fi daɗi, ki na ji, Sunansa Muftahul-jannah ya na da yayye da yawa amma Ba Mamansu ɗaya ba, shi ƙanwarsa ɗaya mace Jannatiee, duk yawan yayyen nasa ba sa ƙaunarshi kamar mujiya haka su ka tsane shi, sai dai Babansa ya na son shi sosai itama Ummanshi haka, kullum ƙiyayyar da suke masa ta na ƙara yawa, gasu da son Zuciya da son abin Duniya, su na mugun jin haushin Babansu ya dinga nunawa Jannah Ƙauna amma ba yadda za su yi sabi da komai na baban nasu Jannah ne akan gaba, a kasuwancinsa ma Jannah ya ɗora duk da shine ƙaramin cikinsu, wai kin san abin Tsoron?" Aaminat ta girgiza kai, Siyama ta ce ''Wai sabi da Jahilai ne da su da iyayensi Mata su ka haɗa kai su ka kashe Mahaifinsu sannan su ka sa aka yiwa Ƙanwarsu Jannatiee fyaɗe, sannan su ka ɗorawa Jannah laifin, yanzun haka a halin da ake ciki kenan, sun jefa shi cikin gararin rayuwa, sun rabashi da Babanshi kuma sun yi masa sharri, sun haɗa masa azabu iri-iri shiyasa na ji kawai na fara kuka, yanzu anje sai Shari'a ake yi, sun ce ba za su yarda ba sai an ƙwatar musu haƙƙinsu a gurin Jannah, ki ji fa wani zalumci? ni cewa ma na yi anya kuwa Ƴaƴansa ne?? Yanzu Jannah ba shi da kowa sai Allah sai Ummanshi, Ƙanwarsa ma ta rasa tunaninta, ban san waye zai cece shi daga wannan Ƙangin Wahalar ba." jikin Aaminat ya yi sanyi, sai da ta ɗan yi gyaran murya sannan ta ce "Kai!! rayuwar nan fa akwai abin tsoro a cikinta, kasan yau ba ka san gobe ba, yanzu sabi da son Zuciya aka kashe masa Babansa, shi kuma tashi ƙaddarar kenan, ni kuma Allah ya haɗani da Kamal duk ya bi ya tarwatsa min farin cikina." Siyama ta yi dariya kafin ta ce "Allah Sarki Ƙawata, wato har labarin ya tsuma miki Zuciya, gaskiya akwai abubuwa da yawa a cikin Littafin, abin akwai ruɗani, ga ban tausayi, masifu iri-iri ya na ganinta Dogon Yaro, sun sha kai masa hari za su kashe shi Allah ya temake shi ya rayu, ƙila ma sai sun kashe shi ɗin don ko a Kotun nan nasan sai sun Yarda shine ya kashe Mahaifinsa kuma ya yiwa Ƙanwarsa Fyaɗe." Aaminat ta ce "Haba Siyama ta ya za ki ce haka bayan kinsan Allah ya na tare da me gaskiya?, ai tinda ya riƙe gaskiyarsa ba za su yi nasara akansa ba in sha Allahu." Siyama za ta yi magana Amiyo ya yi sallama, amsawa ta yi gami da binsa da ido don jin abin da ya kawo shi. ya ce "Siyama wai Master ya na son yin magana da ke." ido a zare ta ce "Master??? fa ya na nufin Abdulkareem." ya ɗaga gira ɗaya gami da cewa "Yessss!!" da mamaki ta ce "Amiyo zan ci ubanka ni kake ɗagawa gira?, to wai me zai ce min ne? ni fa ban yi masa komai ba bana son salawaitun Bala'i irin na Abdulkareem." Aaminat ta ce "Don Allah Siyama dena ambaton sunansa a gabana, ba na so." Miƙewa Siyama ta yi ta wawushi mayafinta ta yafa ta nufi hanyar fita ta na cewa "Allah i sa ba munafurci ku ka haɗa min ba, bansan hawa ba bansan sauka ba, nasan ba mutunci ne da shi ba." ya na raguɓe a jikin bango a ƙofar gidan ya yi wani sumul kamar ba shi ba. Siyama ta na fara'a ta ce "Guda ba Tsagi ba, Allah i sa lafiya ce ta sa kake nemana." murya a cunkushe ya ce "Ta ɓangarenki lafiya amma a gurina zan iya cewa ba lafiya ba." "To fa me ya faru??" ta faɗa cikin mamaki, "Siyama Aaminat! wallahi na yi mata laifi, tin daga ranar ban ƙara ganinta ba shi yasa duk na firgice wallahi, ta dena fitowa amma nasan idan ki ka ce ta zo gidanku za ta zo hakan zai bani damar ganinta." Siyama ta na shirin jirga masa Ƙarya Amiyo ya tari numfashinta da cewa "Master ai YaYa Aaminat ta na gidan su Siyaman, yanzu na ganta." Siyama ta kifa masa wata shegiyar harara, ya buntsire baki alamar ko a jikinsa. a marairaice Abdulkareem ya ce "Siyama don Allah don Darajar Ma'aikinsa ki yi min Izini in ga Aaminat, wallahi akwai damuwa idan ban ganta ba." ganin ya na neman fashe mata da kuka ya sa ta cewa "A'ahh ni fa ba na ƙi bane, kasan ni Ƙawarta ce ta yarda da ni, ka ga bai dace na yaudareta ba." "Ba za ta ga laifinki ba laifina za ta gani, ni kuma duk na yarda da hakan, idan ba za ta fito ba ki ba ni dama in shiga ciki don Allah." Siyama ta rausayar da kai kana ta ce "Zan jarraba kiranta idan ba ta zo ba sai ka shiga, amma ba da yawuna ba." "Na ji daɗi Siyam's , hankalina duk ya bi ya ɗaga na kasa control na kaina Laifi na yi mata kuma ina son bata haƙuri." Siyama ta juya ba tare da ta ce masa komai ba, a ƙasan Zuciyarta kuwa mamakin ƙarfin halinsa take, ba shakka yanzu ta fahimci mugun son ƙawar tata yake, a gefe guda ta na murna da hakan don kuwa za ta so Ƙawarta ta kauce daga Cikin Uƙubar da take, a gefe guda kuwa tsoro da fargabar rigima take don ta san Abdulkareem bai wuce Shekara ishirin da Ɗaya ba bai zama lallai iyayensa su amince ya yi aure a yanzu ba bare ma ya Auri Bazawara a matsayinsa na ɗan masu kuɗin nan. da wannan tunanin ta shiga cikin gidan ko zama ba ta yi ba ta isar da saƙonsa don tasan ƙarshe ma ko ta zauna sai ta tashi ta koma don Aaminat ba za ta amince ba, wani mugun kallo Aaminat ta watsa mata kafin ta ja tsaki ta ce "Siyama ba na son ki shiga sahun masu son lalata min rayuwa, ni kaina na kasa gane meye Manufar Yaron nan a kaina, ya na yi min wasu irin abubuwa da su ke bala'in rikita tunanina, ina tsoron ya bi Sahun Kamal don ba shakka Abdulkareem ba shi da burin da ya wuce ganin ya jefani cikin iftila'i da Azaba, indai har don gaskiya ki ke ƙawance da ni kuma ki na tausaya min to kar na ƙara jin sunansa a bakinki bare ma wani saƙo daga gareshi." Siyama ta numfasa sannan ta juya, ya na tsaye ya zubawa ƙofar gidan ido da alamu jiran fitowarsu yake ko ita ko Aaminat, Siyama ta ce "Guda Wallahi dogon Sharaɗi Aaminat ta ja min don haka ka temaka ka fitar da ni daga cikin zancen nan ba zan iya ba." bai ce uffan ba ya kutsa kai hanyar shiga gidan Siyama ta bashi hanya ya wuce gudun kar ya mazgeta don har ga Allah tsoronsa ta ke ji. Aaminat ta na zaune a inda Siyama ta barta ta ji sallamarsa, cikin sauri ta miƙe ta na binsa da idanu cike da mamakin ganinsa, lallai rashin kunyar tashi ta ƙara yawa, abin har ya kai ya shigarwa mutane gida, katse mata tunanin ya yi da cewa "Aaminat ki yi haƙuri kuskurena ne amma ba zan ƙara ba..." dakatar da shi ta yi cike ɓacin rai ta ce ''Ya isheka Abdulkareem!! yanzu me ka yi? ka biyoni har cikin gidan mutane ka ga an samu shaidar cewa binbininka nake yi, ka fita kafin ranka ya ɓaci" "Ai raina ya gama ɓaci Aaminat tin da har na ɓata miki naki ran." fassss ta wanke shi da wani lafiyayyen mari, ta na kuka ta fara cewa "Na gaya maka na tsaneka, ka nacewa rayuwata sai kace ni kaɗai ce mace a layin nan? idan da gaske ka na tausayina ne me yasa ba ka tausayawa sauran Matan? Azzalumin yaro ka sa Umma sai fushi take da ni, ka ƙara min wata jarabar yanzu ance bin maza nake duk sabi da kai, na ce ka fita daga rayuwata iya zalumcin da ka yi min ya isa haka kar ka ƙara da wani, na tsaneka na tsani ganinka ko da sunanka na tsani ji." Sai da ta gama magana sannan ya sauke hannunsa daga kan kumatunsa da ta mara, idanunsa sun kaɗa sun yi jawur sun wani ƙanƙance, Zuciyarsa bugawa take yi a fusace tamkar za ta ɓalla ƙirjinsa ta fito, "Aaminat ba ki ji ba daɗi ba da ki ka saka hannu ki ka mareni?? Meye laifina don na shigo rayuwarki? shin na taɓa nuna miki halin banza ne? me na aikata da na cancanci wannan hukuncin daga gareki Aaminat?? kenan don sun yi miki Ƙazafi sai ya zama ni na sa su ko kina zaton zan iya aikata abin da su ke tunani ne? Aaminat na gaya miki gaskiyata ba zan iya fita daga rayuwarki ba kuma na zamo Ƙaddararki ba yadda za ki yi dani." shiru ya yi sabi da wani marin da ta ƙara zabga masa, jikinta sai rawa ya ke yau ta kai maƙurar fusata, cikin rawar murya ta ce "Ƙaddarata ma ta fi ƙarfinka balle ni, mugun nufi gareka a kaina ba alkairi ba, kuma ba za ka taɓa yin nasara ba, ko ina bin maza ma banga abin da zan bi a jikinka ba ba ka isa ba ka yi kaɗan, na gaya maka ka ƙyale ni tin kafin ka kai ni maƙura ka ƙi ji, yanzu na kai ƙarshe wallahi in baka bar gidan nan ba ko me na samu sai na buga maka na illata maka rayuwa ko ma na kashe ka!!." "I LOVE YOU Aaminat komai zafin azabar da za ki yi min har Abada ina sonki, Soyayya itace manufata akanki kuma na yi ɗamara da ita ba zan fasa ba, in kin so kar ki dena marina don ba na jin zafinsa ma kan yadda nake jin zafin kalmar ƙiyayyar da ki ke tofa min, kuma ko da za ki mutu ko ki kashe ni Ina Sonki, akanki idanuna sun riga sun rufe ba abin da ba zan iya aikatawa ba ki sa wannan a tunaninki." ya na kaiwa nan ya juya ya fice, Siyama da Amiyo su ka bashi hanya. tafiya yake amma bai san inda ya ke tsomala ƙafarsa ba sabi da ɓacin rai, ya na da haƙuri kuma ya na da Zuciya sannan ya na da zafin rai, hakan ne yasa idan ya burkice ya ke fita daga haiyacinsa, kai tsaye Bedroom ɗinsa ya nufa ya faɗa kan gado. Aaminat kuwa jiri ne ya ɗebeta ta yi luuuu zuwa ƙasa, ta faɗa jikin bango sannan ta zame ta yi zaman ɗaɓaro, kukan da take ma ta dena ta zubawa guri ɗaya ido ita ba a sume ba ita ba a daidai ba. Hankali tashe Siyama ta yo kanta ta na cewa "Aaminat!! lafiyarki ƙalau kuwa?? ki rufa min asiri ki tashi." jijjigata ta shiga yi ta na cewa "Aaminat! Aaminat don Allah ki tashi ai ya tafi." Wasu zafafan hawaye ne su ka samu nasarar gangarowa gefen idanunta, cikin disashshiyar murya ta ce "Siyama Abdulkareem shine ajalina, nasan dama ba zai taɓa ƙyale ni ba har sai ya gama yi min illah." Siyama ta girgiza kai ta na sharar ƙwallah ta ce "Ba haka bane Aaminat, kinsan a rayuwa kowa da irin fahimtarsa wani ba ya ganewa amma nasan wata rana zai fahimce ki zai dena shiga rayuwarki." Aaminat ta yi shiru sai kuka mara sauti da ta ke yi. Siyama ta tashi da sauri ta nufi Firji ta ɗakko mata Fiyowata duk da ba wani sanyi gareshi sosai ba, miƙa mata ta yi gami da cewa "Ki sha ruwan nan nasan Zuciyarki za ta ɗan yi sanyi, don Allah ki yi shiru ki dena kuka, wallahi ita damuwa ba yin kanta take ba sai dai in mutum ne ya so yinta, ki cire shi daga tunaninki bai isa ya yi miki abin da Allah bai yi ba, mu yi ta addu'a Allah zai kawo mana ƙarshen matsalarmu, ki yarda da ni Aaminat ni fa Aminiyarki ce." ruwan ta karɓa ta sha ba da yawa ba ta ajiye sannan ta ce "Temaka min in koma gidanmu Siyama." Siyama ta tashi ta miƙo mata takalmanta ta gyara mata zaman hijab ɗinta sannan ta temaka mata zuwa gida. ©️ INDO & AUTAR JARUMAI [7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga ELEGANT ONLINE WRITER'S Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S Shafi 9 Ya na kwance Kan Gado ya ɗora Filo ya rufe fuskarsa kamar me bacci, Nana Kadija ce ta shigo ta na ƙwala masa kira, "Auta kai Auta! Auta!!" tsaki ya yi yace "Ki tafi bana son takura" "babu inda za ni se ka tashi" "nace ki tashi ko?" "haba kai kuwa wata gulma nazo in ɗan gutsura maka" "Nana ki fita kar na mareki" cikin tsiwa tace "Mari? ka daɗe baka mareni ba kawai daga magana se mari ɗan halak ka fasa, Don ka ga ma ina lallaɓaka" banza ya yi mata ya toshe kunnensa da hannun shi yana cije leɓe, masifa ta ci gaba da yi tana tafe tafe wai dole ma ya tashi ko su daku, ganin be ce komai ba yasa ta saduda ta fara tunanin ko bashi da lafiya, fita tayi da gudu ba ta daɗe ba ta dawo da magani a hannunta, ta zauna kusa da shi sannan tace "Ya Abdulkareem ga magani" ta shi ya yi ya zauna sannan ya kamo hannun ta yace "lafiya ta lau, ina son hutawa ne yau shiya sa, kinji zuwa anjima in na tashi se mu dakun" murguɗa baki tayi tace "oho de ruwa ya daki babban zakara" murmusawa yayi gami da cewa "to koma mene ki je zuwa anjima ma yi shi" jiki a sanyaye ta ce "Amma Ya Audu gaskiya fa ko lafiyarka ƙalau akwai abin da ke damunka, ranar nan su YaYa Abdulmajid sun tambaya na hau bayanka na yi ɗare-ɗare amma yanzu na ga abin ya yi yawa wallahi." "Na rantse da Allah Kadija kawaici kawai na ke miki, idan ki ka ji Biyar ɗina a kumatunki inaga za ki fi fahimta ta, na ce miki ba na son hayaniya. ba ta ce komai ba ta fita saƙol jikinta ya yi matuƙar sanyi dan ba haka ta saba ganin shi ba, kai tsaye ta nufi ɗakinsu tana tafiya tana tunane tunane. Aaminat ta yi kukan har ta gaji sai dai na zuci, sabi da bakin ciki da damuwa Zuciyarta a koda yaushe zafi ta ke yi, don kuwa kalaman Abdul sunyi matuƙar tsaya mata Aaminat I LOVE YOU in ta tuna wannan furucin se ta ji kamar ta haɗiyi Zuciya ta mutu, zuwa yanzu ji take duk duniya babu wanda ta tsana sai su biyu Daga Kamal sai shi, a cewarta Kamal ne ya yi mata silar da har Ƙanin Ƙaninta ya dubi tsabar idon ya ke gaya mata Kalmar So. kuka ne ya kufce mata yayin da take riƙe da carbi tana Azkhar, ta shiga rera shi tana roƙon Allah i yanke mata wahala ta huta koda sauƙinta shine Mutuwarta ta zaɓi hakan" Fati ce ta kalleta ta tuntsire da dariya ta ce "Haba Zawar dariya ma wahala ce bare kuka, za ki gaji ki dena ne" dariya suka sa ita da Umaima kafin Umaima ta ƙwace carbin gami da cewa, "Dalla tashi ki ɗora mana girki kin wani zauna kamar wata Malama se jan carbin munafurci ki ke yi" Aaminat ta kalleta cikin muryar kuka ta ce "meyasa kike min haka?? karki manta ni fa yayarki ce Uwa ɗaya Uba ɗaya ko wani ya gujeni sabi da ƙaddara ai ke be kamata ki gujeni ba, kuma ƙaddara ta na kan kowa!!" shewa suka saki kafin Fati tace "ai muda ƙaddara se kallo daga nesa dan kuwa zaran ba Kalar Yadin bane na gaba yayi gaba wallahi mu ai babu lissafin ƙaddara cikin rayuwar mu" Umaima ta ce "Wallahi ni banga wata ƙaddara a tare da ke ba, kashe Aure ki ka yi don ki dinga tara samari masu kuɗi kuma sai aka yi sa'a ba a gamu ba, in da ba son zawarcin ki ke ba ai da kin yarda da waɗanda Abba ya ke nemo miki." wani kallo Fati tayi mata na kinyi asara gami da taɓe baki ta ce "Wallahi fa kin yi gaskiya Umai." wani kukan ta saki sabo tana da nasanin zuwanta duniya. jin Sallamar ya Umar ce tasa su tashi dan kuwa yana jin motsin su ze fara faɗa meyasa ba suje makaranta ba, fitarsu ta bata damar ci gaba da kuka me taɓa zuciyar me saurare. Tin tana hawaye har sun ƙafe idanuwanta duk sun kumbura sunyi jawur sai ya ji su ke mata kamar an watsa musu dakakken barkono, ga matsanan cin ciwon kai. Su na zazzaune kan Babban Carpet wanda suke shimfiɗawa su zauna, Salim ya lura da tunda suka zauna hankalin Guda baya jikinsa sai ya ji shima jikinsa ya yi sanyi, "Ɗan Ummi ya dai?? tunanin me kake kai da ka Tara an Tara maka, kuma tunanin me zakayi??" murmusawa yayi ba tare da yace komai ba ya bisu da kallo. Cokali ne ya ɗan matso kusa da shi sannan yace "wato ainahin me yake faruwa ne kwana biyu ka dena walwala ɗan abincin da kake fito mana da shi ba kullum ba yanzu" "kai de kamar maye haka kake kaje kaci na gidanku mana" Jabir ya faɗa yana tallewa Haisam ƙeya ganin Abdulkareem ba shi da niyar yin magana ya sa suka fara musu wasu suce bashi da lafiya wasu suce muskilan cin shi ne ya motsa, jin hayaniyar ta su tayi yawa yasa ya tashi yana cewa "ni zan shiga cikin gida in na fito to in kuma se gobe to" gabaki ɗaya suka tsaya da surutun cakkk suka bishi da ido suna mamakin canzawar Master ɗin su lokaci ɗaya, cikin sanyin jiki Haisam yace "wai laifi mu ka yi maka ne?? kwana biyu kadena zama cikin mu kullum kana gida ko baka da lafiya ne??" gargiza musu kai yayi alamar lafiyar shi lau, "to se munji ka nima gida zan tafi" Jabir ya faɗa cike da damuwa, marmushin yaƙe yayi ya ɗaga gira ɗaya sannan ya juya, Walid ne ya dakatar da shi ta hanyar cewa "Guda ko de rabuwa zakayi ne damu??" cakkk ya tsaya shi bai tafi ba shi ba dawo ba kuma bai bashi amsa ba, Walid ya ƙaraso inda yake, ya na shirin yin magana Abdul ya riga shi, ya na murmushin karfin hali yace "Ba haka bane Ɗannan me ya yi zafi da zan rabu da ku bayan ku sashi ne na rayuwata? wai ni kam ina yayarka ne??" Walid ya ɗan ya mutse fuska kafin yace " tana gida bata da lafiya, kuka ne aikinta kullum, duk ta bi ta damu ni bansan me akai mata ba, gashi su kuma ƴan gidanmu kowa harkar gabansa ya ke yi an rasa me kaita Asibiti ma ba wanda ya damu da ita, ni wallahi duk jikina ya yi sanyi bansan me ta yi musu me tsanani haka ba, wai ko Abba babu ruwansa da tambayar ya ta kwana ya ta tashi" rassss gaban Abdukareem ya faɗi har ƙasa, ya wararo ido ya na kallon Walid, ci gaba ya yi da cewa '' Wai kowa ya zare hannushi daga kanta, ni fa Da na zata laifi ta yi musu ashe kawai sabi da Ta rabu da Mijinta ne, ƙila ma ba ta da laifin komai." cikin dauriya Abdulkareem yace "to kace ina mata sannu kaji? to yanzu idan ka ce za ka rakata wajen likita ba za ta yarda ba?" Walid ya ce "Hmm! ba za ta yarda da ni ba don na riga na ɓata wasana tin farko sabi da rashin kunyar da nake mata, kuma gani na yi su Umaima na yi, ni kuma na zata abin kirki ne, tin daga ranar da ka yi min magana akanta na gane kuskurena." Abdulkareem ya ce "Okay Ƙyaleta kawai, Allah i bata lafiya." yana gama faɗin haka ya ci gaba da tafiya zuwa cikin gida. kai tsaye Babban Falo ya nufa ya tarar da ƴan uwansa su na hira ba abin da ya yi tsalle ya tsinka musu mari, ɗan ƙaramin tsaki yayi ya nemi guri ya zauna kusa da Ummi batare da yace musu komai ba, "Ya Audu ko sallama babu??" Nana Kadija ta faɗa cikin sigar tsokana, sai a lokacin ya tuna da be yi sallama ba, ya sunkuyar da kai yana wasa da zobukan yatsunshi "Ya Audu magana fa nake" harara ya watsa mata sannan yace "Dije kar ki takura min" "ni kake cewa Dije?" "an faɗa Dijen gala Ƴar Gona" turje turje ta fara yi tana cewa "Ummi ki na ji de yana cemin Dije kin ƙi ki hana shi" murmusawa Ummi tayi kafin tace "ke kuma ki ka ce masa Audu banyi miki magana ba se shi sabi da kece Zinariya ko??" Abdulmajid ya ce " Yaran nan in ki ka bi ta tasu Ummi sai bakinki ya yi ciwo, Ko Nana Fareeda da Nana Hauwa'u da suke ƙananu ba sa faɗan nan da su ke yi, kuma na lura rashin duka ne ya ke damunsu, yauwa kai tin ɗazu mu ke jiran shigowarka mu ci Abinci kazo ka tsaya cecekuce da wannan me ƙaton kan" murmushin baƙin ciki da ta kaici yayi sannan yace "wa ya ce ku tsaya jirana?? ni na ƙoshi" sakin baki sukayi suna kallonsa kafin Abdussalam ya ce "Ƙalubale Gareka Ɗan Uwa, Nana Kadija ta ce ruwa kawai kake ta kurɓa sai Juice a duk tsawon yau Yaro in za ka zauna ka ci Abinci ka zauna don in ka dawo ƙashi ba ruwan wani." ya ɗan ɗangale kafaɗa alamar ko a jikinsa. Ummi ta ɗan muskuta gami da cewa "haba Autana ba'a horon yunwa ka ci Abinci ka ji Babban Mutum!" tingira kai ya yi a shagwaɓe yace "nifa bana son cin Abincin sabi da Aam" ɗiffff yayi yana muzurai, a ran shi yace taɓ yau na kusa zunguro sama da kara. Abdussalam ne ya katse masa tunani da cewa "sabi da me ka ce??" Abdurrahim ya ce "Tabbas nima na ji zai faɗi wani abu ya fasa, ni dai nasan da abin da ya ke ɓoyewa, wallahi ku tashi mu yiwa Yaron nan Cali-cali yau ya faɗa mana menene a ransa ya ke sa shi rama ta wuya." Ummi tace "kun samin ɗa gaba ku ƙyale shi ni zanji me yasa ya ƙin cin Abincin" rarrashinsa suka shiga yi da ƙyar ya ce zai ci Nana Kadija tace "nasan yadda zamuyi maka se kayi lauma uku se muyi ɗaya" tafawa Nana Hauwa'u sukayi da Abdurrahim Nana Farida tace "kanki yana kawo wuta kamar fulogi" haka suka sashi gaba in yayi Cokali uku se suyi ɗaya tun yana ƙoƙarin ci har ya gaji ya ɓare baki ya fara kuka wai so suke su kashe shi cin yayi yawa. Ummi ta galla masa harara taɗan hade fuska tace zauna se Abincin ya ƙare zaka tashi" komawa yayi ya zauna ya ci gaba da kuka Abdulmajid ya ɗan yi dariya yace "taɓ Jariririnmu babu lafiya gidan ya koma kamar gidan mutuwa an dena dariya" Abdussalam ya ce "Ni fa duk ba wannan ba." su ka haɗa baki wajen cewa "To me????" © INDO tare da AUTAR JARUMAI [7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga ELEGANT ONLINE WRITER'S Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S Shafi 10 Bismillahirrahmanirrahim "Maganar gaskiya ba zuba masa ido za mu yi ba don ba shi da lafiya, ga yadda ya ke yiwa mutane kuka kamar an tsoma shi a wuta, kun manta tsabar kwainane da Manyance irin nashi ne? gaskiya ya kamata mu kai shi wajen likita ko da likitan Mahaukata ne" Abdussalam ya yi magana cike da son nuna gaskiyarsa, Nana Fareeda ta ce "Kuma wallahi haka ne YaYa Abdussalam." Abdulmajid ya ce "Ni gardama ce ba na so shi ya sa na zaɓi na zuba masa ido tinda haka ya ce, ko ka manta ya ce mu zuba masa ido kawai?" Abdurrahim ya ce "To ai amfanin hankali kenan don ya faɗa tinda mu da hankalinmu ai ba biye masa za mu yi ba." Ummi ta ce "Gaskiya nima abin ya dame ni sosai, kuma ya na yawan zazzaɓi yanzu, amma sabi da kafiya Magani ko Ɓalli ya ƙi sha." Goge hawayen ya fara yi ya na cewa "Na dena zazzaɓin kuma dama lafiyata ƙalau, da fa hankalina ta ya zan zauna da cuta." Abdussalam ya ce "Da sauƙi dai hankalin naka don in da da shi da yanzu ba wannan maganar ake yi ba, kukan nan da kake yi ma ba dalili ya na ɗaya daga cikin Ƙarancin hankalin." ya ja numfashi ya busar kafin ya ce "Ka na nufin Mahaukaci ne ni??" "Ahh ba wai ina nufin Mahaukacin gaske ba, hauka irin na Ƙuruciya nake nufi don ya na da yawa a tare da kai. Abdulmajid ya haɗe fuska ba alamun wasa ya ce "Abdulkareem ba na son shirme ka tashi mu je ka ga Likita, idan kuma ba haka ba ranka zai ɓaci ka san ba na son Hau." "To ai dama ba cewa na yi ba zan je ba" Abdulmajid ya miƙe tare da cewa "Abdussalam Ɗakko Mukullin Mota kai kuma Abdurrahim ka tawo min da Abdulkareem." Abdulkareem ya miƙe ya na cewa "Ni ba sai an tafi da ni ba zan biyoka." Abdulmajid ya murmusa ya na tunanin wai a hakan ya ce ba Ƙuruciya a tare da shi ya na magana ya na kuka kamar wani ɗan shekara Uku. Da su ka dawo bai saurari kowa ba ya wuce Bedroom don kuwa duk haushinsu ya ke ji kamar ya bubbugesu. Dadda ya dubesu a tsanake sannan ya ce "Na shigo gida na tarar duk bakwa nan ance Babban Mutum ba lafiya." Abdulmajid ya ce "Eh Dadda yanzu mu ka dawo ai." "Me Likita ya ce game da shi?" Abdulmajid ya zauna sannan ya ce "Wallahi Dadda abin akwai ɗaure kai wai damuwa ce ta fara yi masa yawa har Ƙunci ya harba masa zazzaɓe-zazzaɓe.'" Dadda ya zare Glass ɗin idonsa cike da mamaki ya ce "To fa? ikon Allah kenan, Babban Mutum da wace irin damuwa haka?" Abdussalam ya ce "Kullum sai mun tambaye shi me ya ke damunsa amma ba amsa sai dai ya ce ba komai, kuma ni banga abin da akai masa ba." Abdurrahim ya ce "Ko dai a cikin Yaran da ya ke Abota da su matsalar take??" sai a lokacin Ummi ta ce "Kai a'a gaskiya Yaran nan duk ba wanda zai sa Abdul damuwa haka sai dai wani abin, zurfin ciki gareshi ne shi yasa, mu taya shi da Addu'a kawai." Dadda ya Jinjina kai ba tare da ya ce komai ba. Yau Aaminat ta tashi da zazzaɓi me zafi da ciwon kai, yau ko aikace-aikacen tsakar gida ta kasa yi sai dai ta kwanta in ta gaji ta tashi, fatan ta ɗaya Allah i jefo wanda zai temaka mata ko da ƙwayar Magani ne. Tana cikin wannan halin Siyama ta yi sallama bayan ta gaida Umma ta shige ɗakinsu Aaminat, da sauri ta ƙarasa kanta ta na cewa "Aaminat me ya faru ne? ba dai zazzaɓin ki ke ba naga jikinki na kakkarwa." A wahalce ta ce "Siyama ba ni da lafiya ki temaka ki karɓo min maganin zazzaɓi in Anti ta na da shi." Siyama ta ce "Ai wannan Rashin lafiya taki ta fi ƙarfin zama, a tsaitsaye ta ke ƙarar dake gashi yanzu har ta kaiki ƙasa, ba zan iya jura ba ki tashi mu je Asibiti." "Ba zan je ko ina ba Siyama, ba na son fita sabi da ina tsoron na yi gamo da wannan mummunan Yaron. "O'o Allah Me Baiwa, ke kuma ki na wannan zazzaɓin amma tunaninki ma kar ki fita ki ga Abdulkareem to in kin ganshi zai ɗauki ranki ne??, wannan fa banzan tunani ne, me yasa ki ke da gardama ne? gaskiya ki tashi mu je yanzu za mu dawo, nan fa ƙaramin Asibitin nan na tsallake za mu je ba wai nesa ba. "To zazzaɓi fa nake ta ya zan iya tafiya? ni dai ki ƙyale ni in ba za ki ban maganin ba. Siyama ta miƙe ta kwance ɗankwalinta ta fita ta jiƙo shi sharaf sannan ta dawo, Aaminat ta miƙawa gami da cewa "Karɓi ki shashshafawa jikinki zazzaɓin zai ragu in sha Allahu sai mu je Asibitin." ba ta yi musu ba ta karɓa ta yi yadda Siyama ta ce duk da ba daɗi. Cikin kayanta ta duba ta ɗakko mata Hijab ta zura mata sannan ta ɗakko mata takalma, ba ta zauna ba ta ce "Ai jikin ya yi sanyi tashi mu tafi." "Ni wallahi da ƙyale ni ki ka yi Siyama, ki ka sani ko Ajalina ne ya yi in mutu in huta?" cike da takaici Siyama ta ce "To inaga Ajalin naki ne, kuma zuwa Asibiti ya zama dole ko ki tashi ko in sa Abdulkareem ɗin ya ɗakko Motar gidansu ya zo ya kai ki da kansa, kinsan ba kan gado gareshi ba har cikin gidannan zai shigo ya taitayeki, Allah i sa ma ya na nan." ta ƙarasa maganar ta na ƙoƙarin fita daga ɗakin, da sauri Aaminat ta ce "Wallahi Siyama ba na son irin wannan, haba don Allah ba tashi zan yi ba shine za ki fara ambato min sunan Shaiɗanin Yaron nan?." Siyama ta ce "Da ki zauna ma". riƙe hannunta ta yi sannan su ka fito, Umma ta ce "Ina za ku je ne??" Aaminat za ta yi magana Siyama ta yi saurin cewa "Ba ku san ba fa da lafiya ba Umma? Asibitin tsallake zan rakata ai, don abin ya ci tira." Umma ta rausayar da kai gami da cewa "To Allah i yaye." Ko kulata Siyama ba ta yi ba su ka ci gaba da tafiya. Sun yi sa'a su na zuwa Wata Malamar Asibitin da ta ga jikin nata ba daɗi ta ce su shiga wajen Likita don samun temakon gaggawa. Bayan sun shiga Ɗakin Likitar ta yi mata nuni da kujera gami da cewa "Zauna." zaman ta yi ta na maida numfashi duk ya bi ta gaji ga tafiya ga rana. Likata ta ce "Meke damunki??" "Zazzaɓi da Ciwon Kai sai kuma wani ciwo a ƙirjin...." sallamar wani matashin Saurayi ce ta katse mata magana, Likitar ta fara fara'a gami da miƙewa tsaye ta na cewa "A'ah marhabin da Manya, Yallaɓai yau ku ne a Asibitin namu?" Fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce "Hajiya Maimuna mu ne da tsakar ranar nan." Hajiya Maimuna ta ce "Sannu da zuwa; ke patient Allah ya temake ki ga Babban Likita sai ya duba ki don na ga larurarki babba ce, kin zo a sa'a." ya ɗan shafi sumarsa ya na dariya gami da cewa "Kai Hajiya Maimuna, ba daɗewa zanyi ba fa, wani Patient zan duba shi yasa ma ki ka ganni." Hajiya Maimuna ta yi dariya gami da cewa ''To ai Dr aikinku ne temakon Al'uma kar mu yi haka yau, temaka mata." ya ce "Idan na fito sai a turo ta." Hajiya Maimuna ta ce "To Mu na godiya." bai ce komai ba ya ɗauki abin da zo ɗauka sannan ya fice, Hajiya Maimuna ta zauna kafin ta ce "Na fa yi miki murnar ganin DR Yarima Ƴar nan." a marairace Aaminat ta ce "Ni fa ban damu da ganin Babban Likita ba, Allah shi ke yayewa don Allah ki saurare ni ba na son jira, ko a zaunen nan ma wahala na ke sha" Hajiya Maimuna ta ce "Minti nawa ne zai gama ya dawo kanki?, ke ba za ki gane komai bane; ki ga yadda ki ka wani ɗauke gabaki ɗaya, ki na fa da babbar matsala Yarinya, koma Kujerar nan ta gefe ki bawa Al'umma guri, don ma kin samu zai ganki shine za ki yiwa mutane iyayi." cike da takaici Aaminat ta miƙe ta koma gefe ta zauna, ta na jin Hajiya Maimuna ta na cewa "Zazzaɓin naki ya samo asali gwara ki zauna a ɗora ki akan layin magani daidai da larurarki." ba ta ce mata komai ba don kuwa itama ta shiga sahun waɗanda ta ke jin haushinsu. Ta daɗe ta na jira sannan wata Ƴar Budurwa ta shigo da sallama, bayan Hajiya Maimuna ta amsa ta ce "Dr Yarima ya ce a tura masa wadda ki ka ce." Hajiya Maimuna ta ce "Ga ta nan, rakata " a yatsine budurwar ta ce "Ki taso" Aaminat ta tashi ta mara mata baya. ya na zaune ya harɗe ƙafa akan kujera sai danne-dannen waya ya ke, ko ɗago kai ya kallesu bai yi ba, Budurwar ta bata gurin zama sannan ta fice. Aaminat ta ce "Zazzaɓi da ciwon kai nake sallame ni sauri nake." ɗan murmushi ya yi ba tare da ya kalleta ba ya ce "Ba shi kenan ba, faɗi gaskiya." Sai a lokacin ta tuna zafin da ta ke jin Zuciyarta na yi ta zaro ido tare da tambayar kanta ba dai Ciwon Zuciya bane?, Sai a lokacin ya ɗago ya zuba mata idanu gami da cewa "Zuciyar ta na ciwo ne??" tsuke bakinta ta yi ta kauda kai, sai a lokacin ma ta tuna ashe a zahiri ta yi magana; banza ya yi mata ya ci gaba da danna waya ganin haka ya sa ta ce "Zafi nake jin ta na yi haka kamar Ciwo ko da yaushe sai na dinga jin Ƙunci." ya ce "To Hawan Jini gareki ko Ciwon Zuciya??." da sauri ta ce "Kai Malam ba na son neman bala'i cewa nayi zazzaɓi nake." ya yi dariya kafin ya ce "A alamunki ba ki da faɗa amma zafin ciwo ya sa kin fara; kan ki ya na juyawa ne ko kuma jiri?" ta gyaɗa kai alamar eh, ya ce ''Ina Mijinki ??" duk da ba lafiya gareta ba sai da ta harare shi sannan ta ce "Meye haɗinka da shi???" "Kamata ya yi na yi magana dashi akan lafiyarki mana." "To ba ni da Miji yanzu a gaban iyayena nake, kar ka ɗakko min abin da ba zan iya ba kawai ka rubuta min maganin zazzaɓi." tuntsirewa ya yi da dariya kafin ya ce "Wallahi zafin nan naki ya na bani armashi Aaminat!; Dole fa sai kin yi gwaje-gwaje, gobe ki dawo." ganin ta zaro masa ido ya sa shi cewa "Ya dai?" ta ce "Wa ya faɗa maka sunana??" idanunsa ne su ka ƙara girma, lallai ya kusa ya yi ɓaramɓatama da sauri ya ce "To kin taɓa ganin anga Likita a Asibiti ba tare da an bada suna ba?" ta yarda da hakan don haka ta ce "Yanzu sai me? gida nake son tafiya." Rubutu ya yi a Farar Paper sannan ya miƙe gami da cewa "Mu je Pharmacy ki karɓi magani." ba ta yi musu ba ta bi bayansa, da kansa ya harhaɗa maganin sannan ya ce ta biyo shi kuma ya ƙi bata maganin, ba dan ranta ya so ba take binsa zaizai duk inda ya yi ta na biye da shi, Siyama ta na kallonsu cike da mamakin ta yadda akai lokaci ɗaya Ƙawarta da Dr Yarima su ka zama kamar da can sun saba, ganin za su fice daga Asibitin ya sa ta miƙe ta bi bayansu cikin sauri. Wajen Motarsa ya nufa ya buɗe mata baya gami da cewa "Shiga na raka ki gida." banza ta yi masa kamar ba ta ji shi ba, Siyama ta yi zuruf ta shige ta na cewa "Mun Gode Dr Dama da kyar ta iya zuwa wallahi ka temaka." "Ke kuma daga ina?" "To ai ni ce na kawota Asibitin ni ƙawarta ce; ke Aaminat idan ba za ki shigo ba sai ki daɓa a ƙasa, ai kinsan Dr Yarima dai kuma kowa ya san shi ba sace ki zaiyi ba kuma bai yi kama da mutanen banza ba bare ko ki ce." Dr dai ya na jinsu nashi aikin dariya kawai don kuwa yanayin Tirjiyar Aaminat ya mugun sa shi a kwalba. Sun daɗe a tsaye ita da shi sannan ta ji wahala ta shiga Motar, ga rana ga rashin lafiya. Su na tafiya DR da Siyama su na hira yawanci tambayoyi ya ke mata akan abin da ya shafi Aaminat da rashin lafiyarta, Ita kuwa sai bashi amsa take yi daki-daki. ©️ INDO Tare da AUTAR JARUMAI [7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga ELEGANT ONLINE WRITER'S Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S Shafi 11 Bismillahirrahmanirrahim Hirar tasu ta na bala'in Ƙona Zuciyar Aaminat don ita gani take duk sun dameta. abin da ya bata mamaki har ƙofar gidansu ta ga ya je tsaf ba tare da wani ya yi masa kwantance ba, ta tambayi kanta ta yadda hakan ta faru amma sai ta basar don kuwa ba wannan ne a gabanta ba. Siyama ta buɗe murfin Motar ta fita ta na cewa "Ni fa ban san da yaren da zan yi Godiya ba Yallaɓai." Ya yi murmushin gefen baki, daidai lokacin da Aaminat ta ke shirin fita daga Motar ya ce "Ƙawarki ta na da Mutunci sosai, ba ruwanta da faɗa ga sauƙin kai, a taƙaice dai ta haɗu ta ko'ina." Tsam ta tsaya kamar wadda ya ɗaure har sai da ya gama maganar sannan ta ja sangalalen ƙafafunta ta yi gaba. Cikin Hanzari ya fito har tuntuɓen harshe ya ke garin kiran Sunanta, ta tsaya sauraren abin da zai ce ba tare da ta waigo ba, "Aaminat ki kwana a shirye kuma cikin zaɓi biyu, ko in zo ƙofar gidanku in ɗauke ki ko ki zo Asibiti ki sameni." sai a lokacin ta juyo hawaye sun cika kwarmin idonta, cikin rawar murya ta ce "To duk na meye? ba dai Magani ne ba to ai ka bani." ya girgiza kai gami da gyara tsayuwarsa, cikin muryarsa me cike da nutsuwa ya ce "Aaminat ki na buƙatar test ai na faɗa miki tin ɗazu, ba zan iya zuba Ido ina kallo ki cutu ba don ni likitan Al'uma ne ko kuma in ce na waɗanda ba za su iya ba, temaka miki a wannan Ƙadamin kamar Alhakin da ta rataya a wuyana ne, Allah i ƙara lafiya." ya na kaiwa nan ya saka Baƙin Galashinsa wanda ya rufe kyawawan idanunsa sannan ya juya cikin takunsa irin na Cikakken Namiji wanda ya amss sunansa, Ƙasaita nutsuwa ɗagwarmashi ƙwarewa, kaɗan daga cikin salonsa. Haka kawai Aaminat ta tsinci kanta da tsayawa kallonsa ta kasa gaba ta kasa baya kamar tsohuwar Bishiyar da ta daɗe da kafuwa a guri, sai da ta dena ganin biɗi-biɗin motarsa sannan ta samu ƙwarin guiwar shigewa ciki, ta na jefa ƙafarta ta tsorata sabi da jin dariyar Siyama, ta saki baki ta na kallonta cikin sirkakken yanayi, takaici da kuma mamaki. Siyama ba tare da ta dena dariyar ba ta ce "Iskancin Loko; ka ga Dr da patient ɗinsa?" ta ƙarasa maganar tare da riƙe haɓa alamun mamaki. Aaminat ta ja dogon tsaki sannan ta wuce ciki ba tare da ta cewa Siyama ko Ƙwal ba. Washegari Da misalin Ƙarfe 10:00am ta na zaune ta buga tagumi bayan ta gama haɗiyar Maganinta, takaicin shan maganin duk ya isheta don kuwa ba ƙaunarsa ta ke yi ba. Siyama ce ta yi sallama fakatan-fakatan ta shigo ta tsaya ta riƙe ƙugu kafn ta ce "Aaminat! fita idona in rufe, na aiko Walid ya ce ki fito mu tafi Asibitin sabi da gardama kin ce ba za ki je ba ko?" Cikin matuƙar takaicin rawar kan Siyaman ta ce "Allah i yaye miki Siyama, ni dai ba na samu sauƙi ba? to ban ga me sa ni na fita ba yanzu, ni ba na son temakonsa; ba wani gwajin da za a yi min." Siyama ta gyara ɗaurin ɗankwalinta ta tunkuɗo shi gaba ta fara tattafa hannaye gami da cewa "To wallahi ko Mutuwa za ki yi sai dai ki mutu bayan mun je Asibitin!" ta na kaiwa ƙarshen maganar ta maida hannun kan ƙugunta ta riƙe gami da cellaro ƙafa ɗaya gaba, Aaminat ta tsaya kallonta ta na tunanin ta yadda akai ta zama Ƴar Buyagi haka. Cikin sigar rarrashi Aaminat ta ce "Siyama ki fahimce ni don Allah, ba ki san komai ba a halayen Maza shi yasa ki ke dagewa akan sai na bi shi, temakon nan zai iya zamewa wani sabon babin Baƙin ciki na rayuwata, ki yi haƙuri ki bar ni zan lallaɓa Ya Umar ya kai ni Asibitin duk wani abin da za a yi sai a yi min." Siyama ta sassauta murya sannan ta ce "Nima ki fahimce ni Aaminat, tare da ni fa za mu je, kin ga in ma tsoron zargi ke ke yi kin fita tinda da ni, idan kuma ki na tsoron Dr Yarima ne ina me shawartarki da ki dinga kyautatawa mutum zato, jiya ki ka fara haɗuwa da shi kar ki yi masa zaton da shi ba haka yake ba, ki nemi Kariyar Allah in kin yi haka ba abin da zai faru in sha Allahu. Aaminat ta yi shiru ta na nazarin kalaman Siyama, ta daɗe ta na tunani kafin ta tashi ta ce "Ɗakko min Hijab ɗina Dogo, a shirye nake tinda ba kwalliya zan yi ba ni." Siyama ta ce "Ki ma yi kwalliyar mana, Mutum ba lafiya ba sai Ƙilinbo iri-iri kamar rainon Jinnu." Aaminat ta yi mata banza don kuwa ta lura akan Guiwa Ƙawar ta-ta take. Su na fita Ƙofar gida su ka yi Tozali da Fallatsetsiyar Mota Fara kar da ita, Siyama ta ce "Alhamdulillahi, dama ina tsoron tafiyar Ƙasan nan, Allah ya kawo shi." a ɗan Fusace Aaminat ta ce "Wai way....." kasa ƙarasa maganar ta yi sabi da IDO HUƊU da su ka yi ita da shi, ya zuba mata Brown Eyes ɗinsa masu zaiba-zaiba, suƙut ta haɗiye Yawu tare da sauran Kalamanta. Ya haɗe Cikin Riga Baƙa me ɗan Gajeren Hannu da Wando Blue (Bulu), ya wani Coge a jikin Mota ya na ɗaiɗaita idanu akanta. Ganin ta tokare ta kasa tafiya ya sa Siyama ta ja hannunta kiiii ta na cewa "Yanzu in biye miki za mu yi sai Wankin Hula ya kaimu Dare." Sai da ta tura ta cikin Motar sannan hankalinta ya kwanta, ta kalli Dr Yarima da yake dariya Ƴar ciki-ciki cikin yanayinta na shiririta ta ce "Yallaɓai Ina kwananka? ga ta nan na fito da ita da ƙyar, Allah ya sauwaƙe min da tuni Na yanka Kazar Wahala na Fige na cinye." sai da ya tuntsire da dariya sabi da jin kalaman nata, ta taɓe baki ta yi masa kallon ba ka dameni ba sannan ta shige Motar, Dr Yarima ya Zagaye ya shiga Mazaunin Direba ya fara Tuƙi cikin nutsuwa. Aminu Kano Teaching Hospital Su ka nufa, su na zuwa ba ɓata lokaci ya yi abin da zai yi su ka fito daga Aminu Kano zuwa AA Hospital. Cikakken sunan Asibitin shine, AMEENU ABDULLAH HOSPITAL a nan ma gwaje-gwaje aka yi mata sannan ya tarkato su ya dawo da su gida. sallama su ka yi bayan ya jaddada musu gobe zai dawo tare da Bayanan Gwajin nata, Aaminat dai sai gyaɗa kai da girgizawa ba Baki, Siyama kuwa ita da shi babu gwani a fagen Magana idan ya faɗi Ɗaya za ta shirya masa goma shi kuma zai ƙara mata da wata ɗayar Zazzafa, ta ari bakin Aaminat wajen yi masa godiya sosai da nuna farin ciki akan Temakon da ya yi musu. Sai da su ka shiga cikin gida Aaminat ta kasa Aradun Mita, motsi kaɗan sai ta yi maganar surutunsu, da Siyama ta gaji sai ta bar mata gidan. Washegari Gwajar ɗin wayarta ce ta ta fara ƙara, ta janyota Zuciyarta cike da takaicin kiran ko ma waye, sai da ta katse wani kiran ya ƙara shigowa sannan wayar ta taɓu da ƙyar don kuwa ta fara cin sensor, ta yi sallama a ɗaya ɓangaren Dr Yarima ya amsa, Sai da ta kusa yarda wayar sabi da ɗan firgitar da ta yi na wucin gadi, ya yi mata bazata ba ta taɓa tunanin za ta ji shi ba, don kuwa da hannunta ba ta bashi lambarta ba, kai tsaye ta ɗorawa Siyama laifin. "Aaminat ki na tare da ni??" ya jefo mata tambayar cikin lallausar murya, gyaɗa kai ta yi a sanyaye ta ce "Eh." ya ce "Na zo fa, za ki fito ne ko na haɗu da Siyama kawai?" cikin sauri ta ce "Ya ma fi sauƙi, ka haɗu da ita yanzu aiki na ke yi." ya yi murmushi me sauti ba tare da ya ƙara magana ba ya katse wayar, Siyama da ta hakimce a kujerar ɗan zaman banza ya kalla kafin ya ce "Yau ba zan samu ganinta ba, don haka mu yi magana." ta maida hankalinta kansa sannan ta ce "To Dr ina jinka." "Da na yi tunanin fa Hawan jini ne ke shirin tasarwa Ƙawarki, bayan bincike kuma na gane Ƙarancinsa ne ya fi damunta sabi da yawan ciwoce-cowoce da take, amma inda matsalar ta ke, ta fiye sa kai a damuwa hakan kuma ka iya janyo mata Taɓuwar Zuciya anan gaba; ya na da kyau ki kula da ita yadda ya kamata ki dinga sa ta shan magani sannan ki dinga ƙoƙarin hana ta zaman tunane tunane da damuwa; za ki iya ganina kwatsam na zo ganinta a koda yaushe don haka ki zauna cikin shiri domin ke ce abar dafawata. Siyama ta zuba tagumi ta na kallonsa, sai da ya gama dogon bayanin sannan ta rausayar da kai ta ce "Allah Sarki Aaminat, dama na yi tunanin haka shi ya sa na damu akan mu je Asibiti, mun gode da temakawarka Yallaɓai, ai ka yi mana mutunci idan ka dawo ganinta in sha Allah za ka ganta." ya saki lallausan murmushi gami da cewa "Na gode." buɗe murfin Motar ya yi ya fita, itama Siyama ta fita, a gidan baya ya ɗakko Ledar Magunguna ya miƙo mata ta karɓa gami da ƙara masa wata Godiyar. Sai da ya tafi sannan ta shiga gida ta kaiwa Aaminat Magungunan tare da kora mata jawabi, jikin Aaminat ya yi sanyi Salam da ta ji abin da ke damunta, Siyama ta ce "Ya ƙara da wasu dokin ma fa, kuma ya zama dole ki kula ni zan dinga ku la da ke ma, ga shi ko Abinci ba ƙaunar ci ki ke ba." Cikin rauninnZuciya ta ce "Siyama Abinci ne sai ka ce ba na gidan Mahaifina ba, da gori da gore-gore ake ba ni shi kullum ko da ni na girka." Siyama ta rausayar da kai gami da cewa "Allah i kawo ƙarshen abin." Bayan wani lokaci Aaminat jiki ya yi ƙwari ta samu lafiyarta, Siyama ba ta yi mata da wasa wajen ɗura mata Abinci da magani da sauran abin da ya kamata kuma takan zauna ta dinga bata labarai ko kuma ta karanta mata Littafan da ta ke karantawa. hakan kuwa ya matuƙar samawa Aaminat nutsuwa duk hayaniyar kanta ta yi sauƙi, ƙarin farin cikin nata kuwa, Abdulkareem da ba ya shiga shirginta tin lokacin da ta fara rashin lafiya za ta iya cewa Ba ta yi IDO HUƊU da shi ba (Sunan Wani littafi nawa IDO HUƊU me ban tsoro) hakan ya sa ta farin ciki sosai ta saki jikinta. Fitowarta kenan daga gidan su Siyama kamar daga sama ta ji ya kira sunanta, Gabanta ya yanke ya faɗi, a ranta ta ce Shi kenan baƙar ƙaddarar tawa ta dawo. "Aaminat na samu wasu baƙaƙen labarai da ba su yi min daɗi ba." ©️ INDO tare da AUTAR JARUMAI [7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga ELEGANT ONLINE WRITER'S Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S Shafi 12 Bismillahirrahmanirrahim Aaminat ta doka tsaki kafin ta ce "To sai me? ko a bakina ka ji baƙaƙen labaran? ina da asara ne ni ko sun yi ma ko ba su yi ba?" Ya yi murmushin takaici gami da cewa "Hmm!!! Aaminat! a tunanina kinsan martabar SO kuma kina sauraren Huɗubar Manya na cewar ka so me sonka, a bakin kowa za ki iya jin wannan furucin me yasa ba za ki ɗauki wannan Nasihar ba? Wallahi ba na wasa da soyayyarki tsakanina ga Allah ina sonki kuma ina son Aurenki; ko da a yau ki ka Amince a Ɗaura a shirye nake, kinsan na riga na mutu akan sonki amma ki ke saurarar wani gaja da bai son inda ke masa ciwo ba?" a fusace Aaminat ta nuna shi da yatsanta manuniya gami da cewa "Kaii!!! ka shiga taitayinka wallahi ka kama kanka tin kafin ka tsinci Juma'arka a Laraba, banda ba ka da kunya wai ka kalli tsabar idanuna ka ce ka na sona? kai ba dan nasan daga gidan Daraja ka fito ba da ka sha wankin Rashin Mutunci a gurina, duk haƙurina ka fara kaini ƙarshe zan rufe ido in yanka maka tikitin rashin Mutunci" ta ƙarasa maganar ta na raka shi da wani mugun kallo wanda ya ke ƙara murtsika Zuciyar Abdulkareem, a take idanunsa su ka sauya kamanni, ya girgiza kai alamar a'a sannan ya ce "Aaminat Ko a yau nace zan Aureki zan iya sai dai ba na so na Aureki ta hanyar tilastawa domin ina matuƙar Tausayinki kuma ina darajaki in banda haka da ko ta wane hali sai na Aureki." "Sabi da Auren abin banza ne? me ka ɗauke ni ne? ka yi kuskuren raina Ƙarfin Ƴa mace wallahi, ina fa da Ƴanci Abdulkareem!" ya yi murmushi gami da shafar ƙeyarsa ya ce "Hmm!! Aaminatu tawa, kin yi kuskuren raina Hatsabibancin Ɗa Namiji musamman akan abin da ya ke so; Ta sigar lumana na ke so komai ya faru don haka na ara miki lokaci ki gama sha'aninki ki dawo gareni." Mewtch!! ta buga tsaki ta yi gaba ta na cewa "Saurararka ma ɓatawa kai lokaci ne." "Aaminath I Love U!"ya faɗa tare da raka bayanta da ido, duk da ta ji furucin nasa har cikin ranta amma ta ƙi juyowa ta ci gaba da tafiya gabanta na wata muguwar faɗuwa a kai a kai. a diririce ta shige gida dan kuwa zuwa yanzu jikinta har rawa yake bata bi takan kowa ba tashige ɗaki, "Aaminat! Aaminat!!" Mama ta ƙwala mata kira tana ce wa kina ina zonan ki karɓi wankinnan da su fati suke dama ke ya kamata kiyi dan kuwa su yanzu su ke zamaninsu" "Yasalam" ta furta tana dafe kanta wata sarawa yake mata jitake kamar ta mutu ta huta sede babu yadda zatayi haka zataje tayi wankin, ta shi tayi tana haɗa hanya labulan ta bankaɗa zata fita taji sallamar yaya Hamza da sauri ta tsaya tana zazzaro ido danda nan bugun zuciyarta ya ƙara tsananta. "Ummi ya kamata ki ɗauki mataki akan ya Abdul dan kuwa komai ƙara ta'azzara yake dan ɗazu kuka natarar ya nayi" Nana kadija ta faɗa fuskarta cike da tsagwaron damuwa, numfasawa tayi kafin ta ce "nima nalura kullum lamarin nashi ƙara taɓarɓarewa yake ya dena cin abinci kuma na rasa meke da mun shi" shuru suka ɗanyi na wani lokaci kafin Hauwa'u ta ce "Ummi nakira Anti Maryam ta ce suna hanya" tsaki kadija tayi tare da cewa "wai ke kina hauka ne yanzu se kija tazo itama ta biyemai mukasa gane kansu" Ummi kuwa ta faɗa duniyar tunane tunane, Abdulkareem Abdussalam Abdurrahim Abdulmajid suka shigo tare da sallama cikin shiga iri ɗaya riga da wando baƙaƙe sunyi bala'in kyau sosai yayin da tsantsar kamarsu ta ƙara bayyana, zama sukayi kusa da Ummi Abdulkareem ya tada kai da cinyar Ummi Abdulmajid kuwa gefenta ya kashingiɗa Murmusawa Ummi tayi tare da ce wa Allah yayi muku albarka ya shirya mini ku Allah ya karemin ku a duk inda kuke Allah ya kauda idon maƙiya daga kanku" da Ameen suka Amsa baki ɗaya shuru ne ya ratsa na ɗan lokaci kafin Kadija ta ce "Na ga ka yi jan Ido Mutumina, wallahi ka rame." Cikin takaici da baƙin ciki ya zuba mata harara aransa ya na tunanin tsawwalawa irin ta ta duk ta bi ta dame shi a memakon ta barshi da Iyo a Kogin azabar da Aaminat ta jefa shi.. ya fara tunanin Kalmar da zai bata martani Abdussalam ya riga shi da cewa "Ke kuma Jar Munafuka ko? ba ki da magana sai can na yi masa ciwo sai ka ce jikinki." cikin sauri Abdulkareem ya ce "You're Right, I Like You Wallahi." Nana Kadija ta cika baki da iska gami da ɗauke musu kai cike da takaici, a ranta tana cewa "Ai gaskiya na faɗa kuma na damu da damuwarsa ne ba wai takura masa na ke yi ba." Abdulmajid ya ce "Zaginmu ki ke ne??" Zaro ido ta yi cikin sauri ta ce "Ni na isa?" Abdulkareem ya yi ƙwafa kafin ya ce "In Mutum ya isa ya gwada mana." ta raka shi da hararar ƙasan ido ba tare da ta ce ƙala ba. Hira su ka ci gaba da yi ana yi Abdulkareem da Nana Kadija su na faɗa kamar tagwayen Kaji. danda nan Mama ta sauya fuska ta koma kalar tausayi ta ce "yanzu nikike faɗawa haka daga cewa kizo ki tayani wanki???" dafe ƙirji Aaminat tayi tare da zaro ido tabbas Mama azzaluma ce tafaɗa cikin ranta, wata tsawa Hamza ya daka mata gami da ce wa "mahaifiyar tamu kikewa rashin kunya dan ubanki kodan ba uwar ki bace" murya na rawa ta fara magana "wallhi ya Hamza banyi mata rashin kunya ba yanzu ma nafito daga ɗaki" Mama kuwa jin Hamza yana sauke ƙwandon bala'i ya sa ta fara matse hawayen makirci, Abba ne ya shigo da sallama da sauri Mama ta ce "yawwa Alhaji nagaji ka zaɓa koni ko ƴarka dan kuwa na gaji da futsarar da Amina take mini" ran Hamza kuwa in yayi dubu ya ɓaci jiyake kamar ya nakasa Aaminat yahuta Abba kuwa haƙuri ya shiga bawa Mama, Umma kam kuka me ƙarfine ya kufce mata, ta rasa meyasa Mama ta tsaneta ita da ƴaƴanta kodan ita bata da ƴaƴa da yawa, itama ta gaji da cutarsu da ake agidan dan kuwa yanzu Abba ko ta ita bayayi, jikake tassssss Abba ya wanke Aaminat da mari ya na ce wa "ke wace irin yarinya ce??!! mara tarbiya kin ƙi zaman aure sabida Uwarki da ta ɓataki kullum baki da aiki se tayar da masifa da bala'i to kinyi na farko kinyi na ƙarshe daga yau se yau na rabaki da duk wata alaƙa da zata haɗaki da iyalina kuje can ku ƙare keda Uwarki!!! Ni dai ban taɓa haifar Ɗa na yi nadama ba sai ke, a gidan Miji ma ba ki fasa iskanci ba Aaminat ina ki ke so ki kai Alhakin mutane? Da Mijinki fa ki ka dinga neman Mazan wasu kuma ya sake ki kin dawo ki na tayar min da hankali a Gidana Aaminat ki je don kanki, na yi bakin ƙoƙarina don naga na nema miki wani mijin kin yi Aure kin gyara rayuwarki amma duk kin Fatalar sabi da idonki a tsakar kai ya ke, Ba komai ki je don kanki" yana gama faɗin haka yajuya fuuuuuu ya fice daga gidan don kuwa in ya zauna ba abinda zai tsintsa sai ɓacin rai. durƙushewa tayi awajen tana wani kuka metsuma zuciya tayi da nasanin rayuwar ta a duniya wani juyi take ganin gidan yana yi. Hamza kuwa har yanzu ranshi aɓace yake ganin yadda Mama take matsar hawaye "shikenan haka zamu zuba ido ta dinga yiwa Mama rashin kunya to wallahi haƙurinmu ya ƙare" Fati ta faɗa tana goge hawaye A hassale Aaminat ta ce "mukuma tamu uwar fa ta mutu sabida baƙin cikin da kuke ƙunsa mata???!!! ko a tunaninku bata jin zafin abinda kuke wa ƴarta kodan kunga tana kauda kai tana bawa uwarku girmanta?????!!!" "ke dan uwarki mu kike faɗawa haka??!" cike da ɓacin rai da baƙin ciki Aaminat ta ce na faɗa sede kakasheni nagaji da wulaƙancin ku yau sede ayi duk wadda za'ayi" wani zazzafan mari ya kifa mata ya ɗaga hannu zeƙara mata yaji an riƙeshi da sauri ya juya dan ganin waye idon shi yayi tozali da Omar, rai a tsananin ɓace ya ce "kayi kuskuren marinta da farko amma yanzu na iso wajen ba za ka ƙara ba, Zawarci fa ba hauka bane, Idan ita ƴar iska ce ƴan iskan nawa ku ke tare da su kuma ba kwa nuna musu ƙyama sai ita da take jininku sabi da Asararru ne ku? Kun lalata mata ƙaunar da ke tsakaninta da Mahaifiyarta har ma da mu ƴan uwanta, Ba Uwar kwabo sama da taku uwar kai ma ka sani." Hamza da yake wani huci kamar yunwataccen Zaki ya fizge hannunsa daga riƙon da Umar ya yi masa ya cafki kwalar Umar ɗin ya na cewa "Uwarka itace Uwar Kwabo domin ita ta ɗora yarinya a turbar Karuwanci, kuma ƙarya ka ke ka ce mu muka ɗora Uwarka akan tsanar ƴarta ai ta na da hankali ko mahaukaciya ce da za mu faɗa ta yarda?" Fati ta ce "Ƙila dai Mahaukaciyar ce." Wani lafiyayyen Mari Aaminat ta saukewa Fati a kumatunta, Fati ta ƙwalla ƙara gami da rintse ido sabi da azabar da ta risketa lokaci ɗaya; Aaminat da jikinta ya ke kakkarwa ta ce "Wallahi tallahi ki ka ƙara zagar min Uwa sai na lahanta rayuwarki, Kai kuma Hamza na dawo kanka, Ni Karuwa ce na faɗa na ƙara Idan akwai wanda nake bautawa sai ya hanani Karuwanci, Miji ɗaya ya yi min kaɗan don hakan na ke neman wasu ka gane?? Ƴan Iska Ƴaƴan Baƙar mace!" yuuuuuu Yaɓar!!!! Mama ta yi zaman Ƴan Bori a gurin ta na cewa ''Na shiga uku na Lalace wannan Ƴa ta zageni ta zage Mutuncina, ni ki ke kira Baƙar Mace duk baƙina ai ban kai baƙin Halin Hasiya ba, Allah zai min sakayya Azzaluma Hasiya kin haifi bala'i da Masifa Allah ya isa Tsakanina da ku." jin haka ya ƙara ta'azzara Fusatar Hamza ya yiwa Umar wata Muguwar Shaƙa wadda ta sa numfashinsa ya fara rikirkicewa. Umma da Umaima su ka ƙara ɓarke baki su ka ci gaba da kuka, Aaminat kuwa idanunta sun ƙeƙashe hawayen ma babu, tsananin Fusatar da ta yi ya sa take jin kamar ta kama su ta yi musu mugun dukan ko Mutuwa ko Rayuwa, Fati Sai zubo Maganganu ta ke yi amma Aaminat ta yi mata banza don kuwa Hamza ta ke Hari. ©Autar Jarumai & INDO [7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga MIKIYA ONLINE WRITER'S Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S Shafi 13 Cikin kuka Umma ta ce "Aaminat! Umar! indai kun tabbata ni Mahaifiyarku ce to na ce ku bari domin ni, ku kuma Hamza ku yi haƙuri komai ya wuce ba na son tashin hankali." a hasale Hamza ya ce "Ba zan haƙura ba har sai mun kece raini ni da Wannan Yaron." Umar ya ce "Yaro ya na bayan uwarsa don ni ba yaronka bane, kuma in ka isa ka fito waje mu yi Wallahi sai na saɓa maka kamanni kawai zan ƙyaleka ne sabi da Umma ta sa baki." ya na gama faɗen haka ya hankaɗa Hamza da ƙarfi, ya yi baya taga-taga, daidai lokacin Abba ya dawo gidan, cikin ɓacin rai ya ce "Au ku na nan ɗin dai ba ku dena ba??, kowa ya ɓace min da gani ko ranku ya ɓaci, shashashan banza da ba ku san ciwon kanku ba, don fita sai ku zo tsakiyar gidana ku kama yi min tashin hankali iye?, to ba zan ɗauka ba, idan na ƙara jin labarin wani ya taso fitina sai na saɓa masa, marasa mutunci shashashai." nan fa ya ci gaba da faɗa ta inda yake shiga ba tanan ya ke fita ba. Umar da Hamza su ka yi sum-sum su ka fice su Aaminat ma su ka gudu ɗaki, Fati kuwa ɗakin Mama ta gudu su ka dasa Labarin Aaminat, Fati ta na bawa Maman labarin yadda ta so ayi ba ta so faɗan ya ƙare iya haka ba. Aaminat kuwa banda kuka ba abin da take yi bayan ta shiga ɗakin. Haka aka ci gaba da rayuwa a gidan salin alin kowa ya dena shiga harkar kowa tsakanin Ƴaƴan Umma da na Mama, Musamman Umar da Hamza, Fati kuwa tsakaninta da Aaminat sai dai baƙar magana da habaice-habaice, Aaminat kuwa duk hakan ba ya damunta burinta ɗaya ne ta ga ta bar gidan don haka ta zage da Addu'a tuƙuru. Umaima kuwa duk jikinta ya yi sanyi, daga ita har Umman, sai yanzu su ka gane shigo-shigo ba zurfi Mama take yi musu ta cusa ƙiyayyar Aaminat a Zukatansu har ta sa su ke tsangwamarta. A ɓangaren Mama kuwa ƙiris take jira ta samu abin yi ko ta samu abin da za ta laƙƙabawa Aaminat sharri, kullum cikin masifa da kumbure-kumbure take ba dan komai ba sai don ganin Umma da Umaima har ma da Umar duk sun koma jikin Ƴar uwarsu sun dena nuna mata ƙyama kamar yadda su ke yi Da. Yau ta kasance Ranar Laraba, an tashi da Sanyi gami da Hazo sosai kasancewar Yamma ce ya sa sanyi ya ƙara yawaita. DR Yarima Sanye yake cikin Riga da wando Ƙananu dukkansu Farare sai Baƙar Jacket da baƙin Takalmi ya rufe idanunsa da baƙin Glass, hannunsa sanye da agogo golden. cikin nutsuwa ya ke takawa har ya isa wajen Motarsa ya buɗe ya shiga mazaunin Direba, ya na so ya tayar da ita domin tafiya amma ya kasa sabi da dogon tunanin da Zuciyarsa ta tafi yi. ba kowa yake tunani ba face Aaminat wadda komai nata yake matuƙar burge shi. "So ka ke ka ce ka kamu da Sonta?" ya tambayi kansa, da sauri ya zaro ido gabansa ya yanke ya faɗi, ko shakka ba ya yi kuma hakan ne, bai taɓa kawo cewa abin da ya ke ji zai iya zama so ba sai a yanzu wannan tunanin ya faɗo masa, girgiza kai ya yi gami da cewa "Ba zai yuwu ba, ba zan zama maci Amana ba, Kar ka yi gangancin haka." a sarari ya yi maganar duk da cewar shi kaɗai ne a gurin. Cikin sanyin jiki ya shiga tuƙa Motar, ba ya son zuwa Gida Ammi ta tsare shi da tambayoyi don haka ya nufi gidan Kakanninsa a cewarsa sai ta yi tambayar da dalili. *Ku Dakata Mana✋🏽🤸🏾‍♀️Saurin Me Kuke🤔 sai ka ce Za'a ci da Rabonku🤔😍* Assalamu-alaikum Masoyana kowa da kowa Barka da Warhaka. *Na zo muku da Kyakkyawan Albishir Me Matuƙar Muhimmanci. Shahararren Business Center Ɗinnan da ku ka sani me Suna HALYJASHERU Sun yi muku gwaggwaɓan Tanadi na Kyawawan Kaya Masu Kyau ga Rahusa, ina Farin cikin Sanar da ku Cewa Ku Garzaya HALYJASHERU Ku Ƙulla Kasuwanci da su Za ku yi Matuƙar Farin ciki.* *HALY-JASHERU venture's* *munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba Algus da ha'inchi kayanmu daga Ethiopian ne.* *prdct dinmu, muna Ethiopian MAGIC HAIR OIL, ANTI DANDRUFF SHAMPOO, SERUM BODY CREAM, HAND CREAM.* *Da Magungunan chututtuka Kala Daban-Daban, Da Magunguna Na SIRRIN MATA Masu Matuƙar Kyau da Iganci Gami da Kara Lafiya ajikin Ɗan Adam.* *HALY-JASHERU CENTER Ba mu tsaya iya haka ba, Muna Da Distributor a Ko Ina a Fadin Ƙasarnan Har ma da ta Ƙetare Domin Kuwa abin ba na Wasa Bane, Domin Tallafawa Ƴan Uwanmu Muka Ware Aji na Koyar da Harkokin Kasuwncinmu ga Masu Buƙata, a kan Naira 3000 kawai Muke Koyar da Wannan Sana'o'i Domin Temakon Al'uma, Da Fatan kun yi farin ciki da hakan domin Mu Farin Cikin Costomers Shine Namu. Ku Tuntuɓi C.E.O Ta Wannan Lamba 07046665338 ko 07061664264 INA GAISUWA GAMI DA GODIYA MASOYANA* A Falon Farko ya tarar da E,iya ta na zaune kan kafet ta na Azkhar, ta sha Hijab wanda ya karɓi fusukarta ta yi kyau sosai, zama ya yi kan kujera ya saka guiwar hannunsa na dama akan cinyarsa sannan ya buga tagumi ya zuba mata ido cike da shakiyanci. Da farko banza ta yi masa sai da ta ga ya na neman sawa ta ƙware sabi da kallo ta yi sauron kammala Azkhar ɗin ta yi Addu'a sannan ta kalle shi cike da sababi ta ce "Kai in ba a san asalinka ba sai a ce Mayene Wallah!" ya tintsire da dariya gami da cewa "Hajiya E'iya Matata ta kaina, gani na yi kin yi kyau sosai shi ya sa nake kallonki." "Aff!! Ƙarya ka ke yi, da dai bansan halinka ba sai ka shogama ni." dariya ya yi sannan ya ce "To Ina wuni" ta ce "Da ban wuni ba ai da ba ka ganni ba." ya ce "Daɗina da ke Sababi wallahi, Ina ƴan ƙannen nawa?" ta taɓe baki sannan ta ce "Ƙannenka sun tafi Yawon Ta Zubar" cikin sauri ya ɗora hannunsa akansa gami da cewa "A'uzubillah!!" ya furta ya na dariya, ci gaba ya yi da cewa "Wai ba na ce ki dena cewa Yawon ta zubar ɗin nan ba? kin fa san me ake nufi da hakan" "Na sani sarai kuma ba zan dena faɗe ba, yawo ba dalili ina ya ga amfani? gaskiyar ce ba kwa so kuma sai na faɗa, tsabar iskanci fa Huzaif Baby ya ke kiran kansa." Dr Yarima ya ƙara Kecewa da dariya ya na cewa "Wallahi ba ki da dama Matar nan, shi ya sa fa da tunani ya yi min yawa na gudo wajenku don nasan anan ne zan samu farin ciki, in banda rikicin tsufa don ya cewa kansa Baby ai ba wani abu bane, kema ai Babyn ce." ya ƙarasa maganar cikin sigar zolaya, ta riƙe haɓa da sauri gami da cewa "Ni!!!!? rufa ni ba da ni ake wannan Tumɓelen ba, ba na so, in haifi ubanka ka ce min Baby banda ka raina ni?" Miƙewa ya yi ya na cewa "Ina Budurwata? na lura yau a fusace ki ke ma." ta ce "A'a zauna mana, ko ruwa ban baka ba fa, ka ce ka na neman Budurwa bayan ga mata? zauna maza za ta zo ta sameka ta na Sama ƙila ma kwalliya take maka." ya koma ya zauna tare da cewa "Ai daɗin budurwa kenan in ciki ta ƙi sai a fita waje." ta taɓe baki murya ƙasa-ƙasa ta ce "Ka ji da shi dai." Ɗakko masa ruwan ta yi a gora tare da kofi ta dire masa sannan ta koma ta zauna. shiru ne ya biyu baya kafin ya buɗe baki zaiyi magana Inni ce ta katse shi da cewa "Ah marhaba da zuwanka Saurayina." ya saki murmushi gami da cewa "Yauwa dama ke nake nema, tin da na shigo kin ganta nan banda faɗa ba abin da mu ka yi, kai amma gaskiya kin yi kyau Budurwar Mijin Wata." ya faɗa ya na kallon E'iya taɓe baki ta yi ta kauda kai. shi da Inni su ka sa dariya, Inni ta ƙaraso kusa da shi ta zauna, bayan sun gaisa su ka ci gaba da hira. Sai misalin ƙarfe 9:53pm ya shiga gida, Mamy ta na zaune a Falo ta na kallo, ya na ganinta ya yi ƙasa da kai ya na shirin zillewa sashinsa, "Yarima!!" ta kira shi ba tare da ta kalle shi ba. tin daga yanayinta ya fahimci a cike take fam, shafar ƙeyarsa ya yi a ransa ya ce "Shi kenan rigima ta tashi." ƙarasawa ya yi, ya gaisheta ta amsa kadaran kadahan sannan ta ci gaba da cewa "Tin Yamma ka ce min za ka ɗan je can kuma ga shi har goma, ina ka je? me ka zauna yi?" "Gidan su E'iya na je." mewtcss!!! Mamy ta ja tsaki kafin ta ce "Wai me ya sa ni ba za ka ji maganata ba sai dai ta ubanka??? ban haneka da zuwa wajensu ba wai??" a rayuwa Yarima ya na bala'in takaicin ƙiyayyar da Mahaifiyarsa ke nunawa Kakarsa ta wajen Uba, ya rasa me ta yi wa Mamyin da ta tsangwameta haka har ta kai ga hana shi zuwa wajensu, "Mamy su ɗin fa Kakannina ne ai ba komai bane don na je na gansu, don Allah ki dena irin haka kema fa uwa ce, yanzu idan Ƴaƴana su ka yi miki haka ai ba za ki ji daɗi ba." Mamy ta saki baki gami da cewa "Auu?? lallai ma, ni ka ke faɗawa haka??" ya ce "Ki yi haƙuri kawai ina takaicin hakan ne." Ta jinjina kai gami da cewa "Danƙari Maƙari" bai bari ta ci gaba da wata maganar ba ya miƙe tare da yi mata sallama ya sanar da ita ba zai ƙara sakkowa ba. Ko amsawa ba ta yi ba ta bi shi da ido har ya ɓacewa ganinta. Bayan ya watsa ruwa ya yi shirin Bacci sai kuma tunane-tunane su ka sake yi masa sallama, bai iya rintsawa ba har sai da ya yanke hukunci zai gayawa Aaminat ya na sonta kuma ya tsara zuwa gidansu gobe. Sai mu ce Asbha ta gari. (To masu Karatu ya yi Bacci kuma ku kwanta kafin gobe mu garzaya Gidan Alhaji Aminu Mai Kasuwa don jin Halin da Abdulkareem yake ciki😍) *Ayeesha Abdulkareem INDO* Ta na me farin cikin Sanar da ku cewa An Fara Karanta Littafinta WATA HANYA a Gidan Radio Garanti Mita 94.7 Ku Kasance da Abdullahi Muhammad SALBAS Domin Jiye Kunnuwanku irin Faɗakarwa Da Nishaɗi da ke cikin Wannan Littafi. Kar kuma Manta Sunan Marubuciyar Ayeesha Abdulkareem INDO, Garanti Radio 94.7 Ƙarfe 5:30pm Daidai Share Fisabilillah ©️©️ INDO tare da SALMA AUTAR JARUMAI [7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga MIKIYA ONLINE WRITER'S Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S Shafi 14 Washegari. Abdulkareem ne kwance kan Gadonsa ya lulluɓe gangar jikinsa da bargo fuskarsa ce kawai a buɗe sai muzurai yake ba alamar walwala a tare da shi. Tunanin irin Yankan ƙaunar da Aaminat ta ke yi masa yake yi gashi duk yadda ya nemi hanyar da zai dakatar da hakan ya kasa samu, ya rasa ta inda zai bi ya shawo kan matsalar. Nana Khadija ce ta yi sallama ba tare da ta jira ya amsa ba ta shigo ta zauna a gefen gadon, fuskarta a ɗaure ba alamun wasa, ko kallonsa ba ta yi ba ta ce "Sai wani ɓoye-ɓoye ka ke yiwa mutane, idan ba ka gayawa wani ba a cikinmu ai ka gayawa wani, ko an gaya maka ana iya samun maganin cutar da ba'a santa ba? ni na san akwai wani abu a Zuciyarka amma sai raina mana hankali ka ke yi." "Ke har wani hankalin da za a raina gareki?" ta ce "Ka ga ni fa ba wai na zo mu yi faɗa bane; na zo ne da batun sirri tsakaninmu, banda abinka in ka gaya min ai ka samu abokiyar jaje ko da ba za mu iya yin maganin abin ba. Nazari ya ɗan yi kafin ya ce ''Ba na son gaya muku ne duk ku tayar min da hankali." "Faɗi indai ni ce ba ni da matsala. "Kinsan Aaminat? ta gidan su Waleed. ta zaro ido gami da cewa "Me ta yi maka?" "Ni ne na yi mata laifin domin kuwa na kamu da sonta, a da kawai tausayinta nake ji amma yanzu abin ya wuce nan, ina son ganin farin cikinta ko ta wane hali, amma ita ta ƙi ƙaunata ƙarshe ma nema take ta ba wani damata ya yi amfani da ita. jikin Nana Khadija ya yi mugun sanyi murya a sanyaye ta ce "Amma Ya Abdulkareem kai ma ka san hakan da kamar wuya ya akai ka bari hakan ta faru?" ya ce "Ni ma ban sani ba, amma kema kin sani ba a yiwa so shamaki, ki bar zancen nan kawai tin da kin ji, ki tayani da Addu'a kawai, tashi ki ban guri yanzu nima zan fito." miƙewa ta yi jiki a sanyaye ta yi hanyar fita, duk hankalinta ya tafi a tunanin ta yaya Abdulkareem zai iya Auren Sa'ar Yayan yayansa? ta yaya ma Iyayensu za su yarda?, da wannan tunanin ta koma Falo ta nemi guri ta zauna sannan ta ci gaba da tufkawa da warwarewa. "Yaya Aaminat kin karya kuwa?" Umaima ta faɗa tana zubawa Aaminat ido "Umaima meyasa yau kike tambaya ta na ci abinci??" murmusawa tayi sannan ta ce "da da yanzu ai ba ɗaya bane" murmushin ita ma tayi kafin ta ce "to na karya Umma ta zuba mini abin kari" "ai na zaci baki karya ba shiyasa" "Umaima kina son wata abaya tawa??" ina so mana kogi ai bai ƙi daɗi ba" "sawa ɗaya nayi mata naji ta fita daga raina" "nikam ina so wallhi dama akwai wani takalmi naki ko kibani ko mudinga sawa tare" tintsirewa tayi da dariya Umaima ta zaki baki tana kallon ta ta ce "yaya Aaminat dariyar mekike??" "kece kika bani dariya wai ko na baki ko musa tare" "A'a to bazaki bani ba" Aaminat ta ce "A'a zan baki mana ai baki taɓa tambaya ta abu na hanaki ba, kin manta lokacin da ina budurwa kafin nayi aure wata ranar se na zo sa abu se naga kinyi ɗagwass-gwass a ciki" dariya sukasa Umaima ta ce "rayuwa kenan dan ma sharrin shaiɗan ya ratsa da zigar Mama da Fati suka sa na juya miki baya amma ki yi hakuri ki yafe ni don Allah, yanzu na gane kuskurena" dandanan annurin fuskar Aaminat ya ɗauke ta ce "ba na son naji kina irin wannan magan-ganun ai baya tawu ce ni na yafewa kowa" rausayar da kai Umaima tayi ta ce "ai nadena daga yau" "kyaji dashi de" Aaminat ta faɗa fuska ɗauke da murmushi dariya Umaima tayi kafin ta ce "wai kina da labarin wani sikarin guys da yace yana sona??" "A'a bani da labari se kin shaƙamini" "Ummm ai nake faɗamiki shiɗin maƙura ne wallhi gashi kyakkyawa" "Allah ƙanwata kice kin kware masa?" dariya ta ɗanyi ta ce "ai dole sabida tsabagen kyanshi gashi ɗan wanka babu ruwan shi" Aaminat ta riƙe baki ta ce "lallai Autar ɗakinmu haka kika kama da wuta??? ya fini kyau kokuwa?" dariya suka sa cike da nishaɗi Umaima ta ce "ai kowa da matsayi shi kin fishi kyau" haka suka cigaba da hira suna dariya da nishaɗi. Misalin ƙarfe 4:30 na yammaci Yarima ya shirya cikin dakakkiyar rantsats-tsiyar shadda fara ƙal har ɗaukar ido take baƙar hula dara yasa baƙin agogo baƙin takalmi yayi kyau sosai fitowa yayi Falo a ya na taku ɗaiɗai, Ammi na zaune ta na kallon TV dama aikinta kenan ko Abi ne yadawo bata kulawa da shi abinci ma sede ƴan aiki su kai masa ko Yarima, ɗan ƙaramin tsaki yayi sannan ya ce "Ammi ni zan fita" "Allah ya tsare kuma saura kabiya gidan kakannin ka" ya ce "Ameen" yafice zuwa harabar gidan Kai tsaye wajen ajiye Motoci ya nufa, wata tsuleliyar mota baƙa ya hau me tsadar gaske yanufi Gadon Ƙaya gidan su Aaminat. *Ku Dakata Mana✋🏽🤸🏾‍♀️Saurin Me Kuke🤔 sai ka ce Za'a ci da Rabonku🤔😍* Assalamu-alaikum Masoyana kowa da kowa Barka da Warhaka. *Na zo muku da Kyakkyawan Albishir Me Matuƙar Muhimmanci. Shahararren Business Center Ɗinnan da ku ka sani me Suna HALYJASHERU Sun yi muku gwaggwaɓan Tanadi na Kyawawan Kaya Masu Kyau ga Rahusa, ina Farin cikin Sanar da ku Cewa Ku Garzaya HALYJASHERU Ku Ƙulla Kasuwanci da su Za ku yi Matuƙar Farin ciki.* *HALY-JASHERU venture's* *munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba Algus da ha'inchi kayanmu daga Ethiopian ne.* *prdct dinmu, muna Ethiopian MAGIC HAIR OIL, ANTI DANDRUFF SHAMPOO, SERUM BODY CREAM, HAND CREAM.* *Da Magungunan chututtuka Kala Daban-Daban, Da Magunguna Na SIRRIN MATA Masu Matuƙar Kyau da Iganci Gami da Kara Lafiya ajikin Ɗan Adam.* *HALY-JASHERU CENTER Ba mu tsaya iya haka ba, Muna Da Distributor a Ko Ina a Fadin Ƙasarnan Har ma da ta Ƙetare Domin Kuwa abin ba na Wasa Bane, Domin Tallafawa Ƴan Uwanmu Muka Ware Aji na Koyar da Harkokin Kasuwncinmu ga Masu Buƙata, a kan Naira 3000 kawai Muke Koyar da Wannan Sana'o'i Domin Temakon Al'uma, Da Fatan kun yi farin ciki da hakan domin Mu Farin Cikin Costomers Shine Namu. Ku Tuntuɓi C.E.O Ta Wannan Lamba 07046665338 ko 07061664264 INA GAISUWA GAMI DA GODIYA MASOYANA* be ɓata lokaci ba ya ƙarasa Unguwar wayarsa ya ɗauka ya danna wa Siyama kira bugu biyu ta ɗauka tare da sallama ya sanar mata ya ƙaraso "to" kawai ta ce ta tashi ta yafa mayafinta tayi waje sai gidan su Aaminat. Ta zaune tana rera karatun alƙur'ani maigirma cikin nitsats-tsiyar muryar ta me daɗin saurare. zama Siyama tayi Aaminat ta taƙaita karatun dan ganin Siyama ta yi addu'a suka shafa Siyama ta ce "kin fa yi baƙo" "nayi baƙo kuma wanene?" ta faɗa cikin sigar mamaki Siyama ta rausayar da kai ta ce "ke de kizo muje" "kinga nifa babu inda zani sekin faɗa min kowaye" "Yarima ne" rassss!!! taji gabanta ya faɗi takasa cewa komai se kallon Siyama da take to meya zo yi wajenta ta tambayi kanta Siyama ta ce "yana kira fa kihanzar ta"! taɓe baki tayi kafin ta ce "wai na hanzar ta sabida ga ubana ya zo ko??" Siyama kuwa roƙon Aaminat ta shigayi tana magiya akan tafita, Siyama ta ce "tunda bazaki ba bari na faɗawa ya Omar shiya tilastaki koma dole kije" tana shakkar ya Omar sosai dan kuwa ba shi da wasa hakan yasa ta ce "zanje base kin faɗawa Ya Omar ba amma da sharaɗi bazan daɗe ba!" Siyama ta ce kokefa harkinfi kyau yanzu" Aaminat ta kai mata duka ta ce "dani mummuna ce??!" "A'a karki kaini inda Allah be kaini ba" ta shi tayi ta zura zumbulelen hijabi ta feshe jikinta da turare meƙamshin gaske, Siyama ta ce "sekizo muje ai ko" ƴar dariya tayi gami da cewa "sekace wata babata se wani magana kekemin sama sama" Siyama taja hannuta ƙiii zuwa ɗakin Umma, cikin jin kunya Aaminat ta ce "Umma zanje nayi baƙo" Umma ta ce sekun dawo kukula kunji ko Allah yayi muku albarka" Siyama da Aaminat suka amsa da Amin. Ɓangaren Yarima kuwa yana jikin motar sa ya jingina ya harɗe hannayen sa a ƙirjin sa kanshi a ƙasa kamar tsohon munafuki sallmar da yaji ce ta dawo dashi hayyacin sa yayi saurin ɗagowa karaff suka haɗa ido da Aaminat wani kallon kallo suka shigayi babu kiftawa dariyar da Siyama tayi ce ta dawo dasu hanyyacin su, Aaminat tayi saurin kauda kai gefe, sannan ta ce "i...ina wuni" wani tattausan murmushi ya sakar mata gami da cewa "lafiya lau" wani sihirtaccen kallo yabita da shi yana wani limshe ido wani tartsa-tsi yakeji zuciyar sa nayi sede ya ɗaura ɗamarar bayyanawa Aaminat soyayar shi. Siyama ta ce "To ni dai sai anjimanku." Yarima ya ce "Na gode Siyama ki gaida Aunty." ta ce "To" Maida kallonsa ya yi ga Aaminat kafin ya yi gyaran murya sannan ya ce "Aaminat kin bani dama na bayyana soyyata agareki??" rasss-rasss!!!!!! gaban Aaminat ya faɗi tunanin Abdulkareem ne ya keto mata, Yarima ya ɗan ƙara takawa yaje gaf da ita kana ya ce " kitaimaki wannan bawan Allahn da idanunsa su ka rufe akan sonki Aaminat." shiru ya ɗan yi kafin ya ci gaba da cewa "Ina sonki!!! ba na so ki ce min a'a don Allah ki yi tunani me kyau akaina." a hankali ta ɗago kanta ta zuba masa idanu Zuciyarta na wani irin tsalle, ba shakka idan ta ce Ba ta burgeta ta yi ƙarya, haka idan ta ce ba za ta iya son shi ba ta yi babbar ƙaryar da ƙarshe ta zo ta ji kunya, sai dai akwai wani hanzari ba gudu ba, Abdulkareem kawai take tunani don ba ta san yadda za su ƙare ba, bayan haka kuma ta gaji da sanya shi ƙunci duk ta dalilinta. tattausan murmushi Yarima ya sakar mata wanda ya ratsa dukkan sassan Zuciyarta, tayi saurin yin ƙasa da kanta yayin da itama murmushin yake neman kufce mata. murmushi me sauti yayi kafin ya ce "kin amince da Soyayyata???!!!" murya a harɗe ta ce "Zan yi shawara" ya ce "shikenan kiyi shawarar amma dan Allah karki sanarmi mummanan saƙo" bata ce komai ba ta juya zata tafi taji ya ce "kitsaya muyi sallama mana ko" cakk ta tsaya batare da ta juyo ba, ya juya mota ya ɗakko wata ƴar ƙaramar leda sannan ya nufota, miƙa mata ya yi gami da cewa " ga wannan waya ce da layi aciki inna koma gida zan kiraki" ƙin karɓa tayi ta ce "A'a kariƙe kayarka nima ina da ita" "nasan kina da ita shiyasa na baki wannan" ajiyar zuciya ta sauke aranta ta ce "wannan bawan Allahn yafiya ta kura" ya ce "Don Allah ki karɓa ba don ni ba, sannan duk shawarar da ki ka yanke ki kirani da ita kar ki barni ina tunane-tunane." karɓa ta yi gami da godiya sannan ta wuce cikin gida. seda ya ga ta shige gida sannan ya juya ya nufi motar shi cike da farin ciki da kuma zullumi kar Aaminat ta ce bata son shi.... INDO tare da Ƴar Uwa Salma Auta [7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S Shafi 15 Tana shiga gida ta faɗa kan gado tare da sauke wata nannauyar ajiyar zuciya. Siyama ce ta shigo ɗakin tare da sallama, Aaminat ta amsa tare da cewa "dama so nake naje gidanku yanzu se gaki," Siyama ta ce "Yariman ya tafi??" wani kallon sheƙe-ƙe Aaminat tayi mata gami da cewa "to in be tafi ba a ɗakin nan kikeso ki ganshi? ba daga ƙofar gida kike ba?" Murmusawa Siyama tayi ba ta ce komai ba ganin haka yasa Aaminat cewa "Siyama Yarima yana sona nace zanyi shawara ki bani shawara" rausayar da kai tayi sannan ta ce "ni a ganina Yarima bashida wani aibu mutum ne me dattaku da kuma sanin ya kamata sabida haka ki amince masa kawai" shiru ta ɗanyi kafin ta ce "Siyama kiyi tunani ya Abdul zeji idan har naso wani ba shi ba kuma shi ya fara cewa yana sona sannan Yarima" tsaki Siyama tayi kafin ta ce "kinga kema kinsan kina son Yarima kuma me zesa kidinga tunanin Abdul shifa ba sonki yake ba kawai tausayin ki ya keji kuma shi Abdul inde har Yarima ze saki farinciki to ze iya haƙura ya barwa Yarima" shiru ne ya ɗan ratsa na wani lokaci kafin Siyama ta ce "ni zantafi" "ince mai ina sonshi??!" "ruwa ya rage naki" "Siyama wai meyasa kike wani fushi-fushi ne??" murmushi ta ɗanyi ta ce "ba fushi nake ba kede kawai in Yarima ya kiraki to kice mai kin amin ce dan Allah ba don nu ba, nima kaina ina so in ga kin fita daga wannan halin, ace mutum ba shi da aiki sai tunanin bara anci wake" "in sha Allah zan faɗa mai ki de tayani da addu'a Allah yasa Alkairine" "Ameen" Siyama ta ce sannan ta fita. Misalin ƙarfe tara na dare kira ya shigo wayar Aaminat ta ɗauka zuciyar ta na wani bugu-bugu sallama yayi mata, ko ba a faɗa ba tasan Yarima ne "Assalamu alaiki sarauniyata fatan kina lafiya" ta amsa da cewa "Wa'alaikumussalam lafiya lau" shiru ne ya biyo baya kafin Yarima ya katse shirun da cewa "kina farin cikin shiga rayuwarki da nayi kuwa??!!" murmushi me sauti ta ba tare da ta ce komai ba, hakan ya bashi damar ci gaba da magana "amincin Allah ya tabbata gareki a duk tsawon rayuwarki masoyiyata, ina so ki faɗa min ko da hankalina zai kwanta numfashina ya dena sassarfa, shin kin aminta da soyayyata???!!" rasss!!!!!! taji gabanta ya faɗi ta yi shiru ta na zazzare ido, jin ya ƙara maimaita tambayar yasa ta tattaro nutsuwar ta fara magana cikin in ina "na...na.amince" "Alhamdulillah Allah kai ne abun godiya Allah na gode maka da ka mallaka min zuciyar da nadaɗe ina muradin samunta".. bayan ya gama godiya ga sarki Allah ya ci gaba da cewa "Ina Sonki Aaminat !! Ina fatan kema ki so ni da dukkan Zuciyarki" wani murmushi me sauti ne ya kufce mata shima murmushin yayi, ta ce "ina jin bacci se da safe" sukayi sallama cike da farin ciki da jindaɗi. haka rayuwa taci gaba da tafiya na wani lokaci kullum Yarima da Aaminat ƙara shaƙuwa suke.... *Ku Dakata Mana✋🏽🤸🏾‍♀️Saurin Me Kuke🤔 sai ka ce Za'a ci da Rabonku🤔😍* Assalamu-alaikum Masoyana kowa da kowa Barka da Warhaka. *Na zo muku da Kyakkyawan Albishir Me Matuƙar Muhimmanci. Shahararren Business Center Ɗinnan da ku ka sani me Suna HALYJASHERU Sun yi muku gwaggwaɓan Tanadi na Kyawawan Kaya Masu Kyau ga Rahusa, ina Farin cikin Sanar da ku Cewa Ku Garzaya HALYJASHERU Ku Ƙulla Kasuwanci da su Za ku yi Matuƙar Farin ciki.* *HALY-JASHERU venture's* *munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba Algus da ha'inchi kayanmu daga Ethiopian ne.* *prdct dinmu, muna Ethiopian MAGIC HAIR OIL, ANTI DANDRUFF SHAMPOO, SERUM BODY CREAM, HAND CREAM.* *Da Magungunan chututtuka Kala Daban-Daban, Da Magunguna Na SIRRIN MATA Masu Matuƙar Kyau da Iganci Gami da Kara Lafiya ajikin Ɗan Adam.* *HALY-JASHERU CENTER Ba mu tsaya iya haka ba, Muna Da Distributor a Ko Ina a Fadin Ƙasarnan Har ma da ta Ƙetare Domin Kuwa abin ba na Wasa Bane, Domin Tallafawa Ƴan Uwanmu Muka Ware Aji na Koyar da Harkokin Kasuwncinmu ga Masu Buƙata, a kan Naira 3000 kawai Muke Koyar da Wannan Sana'o'i Domin Temakon Al'uma, Da Fatan kun yi farin ciki da hakan domin Mu Farin Cikin Costomers Shine Namu. Ku Tuntuɓi C.E.O Ta Wannan Lamba 07046665338 ko 07061664264 INA GAISUWA GAMI DA GODIYA MASOYANA* sanye take cikin riga Abaya marun tayi rolin ɗin mayafin tayi bala'in kyu sosai duk da bawata kwalliya me hayaniya tayi ba amma tsan-tsar kyawun ta ya ƙara baiya na dama Aaminat fara ce ƙal dan Umma ta biyo a fari. mudubi ta kalla fuska ɗauke da murmushi ta ɗauki turare ta feshe jikinta sannan ta zira takalmin ta, Umaima da bata iya shiru ta ce "yaya ina zuwa haka kinyi kyu wallhi" murmusawa tayi ta ce "gidan su Siyama zani" Umaima ta ce "bari nazo muje" kafin kace meye wannan ta yafa mayafin ta, Aaminat ta ce "kai kin fiya son yawo wallhi" "nide muje" fita sukayi ƙofar gida kamar daga sama taga Abdulkareem sanye cikin shigar ƙananun kaya riga fara da wando baƙi yayi bala'in haɗuwa yajingina da tamfatsetsiyar motar sa me tsadar gaske ya harɗe kafa tare da kauda kai gefe, Aaminat kuwa zuwa yanzu ta gama tsinkewa da Abdul ido ta tsira masa babu ƙiftawa, jikinta se rawa yake tabbas ta sani yau haƙurin Abdul ya ƙara kuma seta ɗanɗa na kuɗar ta, a hankali ya fara takun shi me cike da ƙasaita da jin kai da kuma zarra, seda ya zo gaf da ita sannan ya tsaya da hannu yayiwa Umaima Alamar ta bar wajan, jikin na ɓari ta saki hannun Aaminat ta fece, wani tattausan murmushi yayi me cike da baƙin ciki da takaici, sannan ya fara motsa kyakkyawan bakinshi ya ce "Aamaint ina sonki amma ba kiyi la'akari da haka ba kike soyayya da wani wanda baki san kowaye a wajena ba,.. ya ɗan numfasa kafin ya ce ko be faɗa miki muna da alaƙa da shi ba?? Aaminat kinci Amana ta kuma ina so kisani har yanzu ina so ki kuma muddin ina raye bazaki Auri yarima ba,.." "nikam naga rayuwa" ta faɗa cikin ranta wani tsallle zuciyar Abdul take kamar zata fito waje dafe ƙirjin shi yayi tare da cewa "Aaminat ina sonki soyayyar ki tana azabtar dani tabbas zan iya rasa rayuwa ta daga ranar da akace kin Auri wani wanda bani ba".. ya zuba guiwoyin shi biyu a kasa ya karyar da murya cikin sanyi da kuma raunin zuciya ya ce Aaminat ina sonki ina ƙaunar ki kece duk wani farin ciki nawa ido na ya rufe bana ganin kowa seke kunne na ya toshe bana jin komai idan bake ba duk wani mafarki na kece ina sonki soyyayar da ni kaina bansan iya adadin ta ba, son da nake miki ya shafi rayuwar gidan mu dan kuwa yanzu ta sanadiyyar soyayyar ki gidanmu ya canza, Aaminat bata san lokacin da zuciyar ta ta karye ta fara kuka tana cewa, "Dan Allah Abdul karage wannan makauniyar soyayyar da kake min inna ce bana son ka nayi ƙarya amma Abdul shifa Aure ba wasa bane, kaifa yanzu baka isa mizanin da zaka Auri mace kamar ni ba in kuwa ka aure ni to ka tar watsa rayuwar ka karka manta ni BAZAWARA ce" ta ƙarasa maganar tana wani irin kuka me tsuma zuciya, Abdul kuwa ya kasa koda motsa ɗan yatsan shi ne, har yanzu guyawun sa na ƙasa ya sunkuyar da kai, hawaye masu azaba da kuma zafi suna sauka daga idon sa zuwa ƙasa, sun ɗauki tsahon lokaci a haka kafin Abdulkareem ya ta shi ya juya, seda ya taka sau uku sannan ya ɗan tsaya ya ce Aaminat kisa aranki duk tsanani duk wuya sena Aure ki!!!!!!!!!" yana gama faɗin haka ya juya ya shige motarsa ya bata wuta, da gudu ta shiga gida tana kuka ta wuce ɗakinsu... *Ayeesha Abdulkareem INDO* Ta na me farin cikin Sanar da ku cewa An Fara Karanta Littafinta WATA HANYA a Gidan Radio Garanti Mita 94.7 Ku Kasance da Abdullahi Muhammad SALBAS Domin Jiye Kunnuwanku irin Faɗakarwa Da Nishaɗi da ke cikin Wannan Littafi. Kar kuma Manta Sunan Marubuciyar Ayeesha Abdulkareem INDO, Garanti Radio 94.7 Ƙarfe 5:30pm Daidai Share Fisabilillah *©INDO Tare da SALMA AUTA* [7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION Shafi 16 Mama da Fati Suna zaune a tsakar gida suna Taɗi, ganin Aaminat ta shigo tana kuka yasa su jindaɗi Mama ta sheƙe da dariya gami da cewa "Allah sarki bazawara yau ma saurayi ya gudu" Fati ta ce "dama waze Auri bazawara se tsoho ko talaka" Mama ta ce "kekuwa ƴata daga me jirgi se me mota" suka sa dariya kafin su ci gaba da hirar Aaminat. Aaminat kuwa ta daɗe ta na kuka ganin ba zai kaita ko ina ba ya sa ta share ƙwallarta. Yarima da Abi zaune suke a falon Abi suna taɓa hira Abi ya ɗan yi gyaran murya kafin ya ce "Yarima ina neman shawarar ka" Yarima ya tattaro dukkan nutsuwar shi sannan ya ce "Abi ina sauraren ka" Abi ya murmusa gami da cewa "dama ina son ƙara Aure ne shi yasa nake neman shawarar" rassss!! gaban Yarima ya faɗi Abi ya ce "nasan bazakaji daɗi ba a ce na yiwa mahaifiyar ka kishiya amma idan kayi haƙiri komai ze dedeta" murmushi Yarima yayi sannan ya ce "Abi me zesa kace zaka ƙara Aure yanzu bayan girma ya fara kama ka??!" "Abubakar ina son ƙara Aure ne sabida halaiyar Hajiya Hafsa, kai ma ka san ba ta ƙaunar Mahaifiyata" Yarima ya ce "shikenan Abi ina goyon bayanka kuma ni zan taya ka cukucukun Auren" "nagode ɗana" Yarima ya ɗan yi dariya cike da zolaya ya ce "Abi wace amaryar" "Zainab sunan ta tana aiki ne a ƙarƙashin kamfanina kuma na yaba da hankalin ta da nutsuwar ta" Yarima ya ɗanyi murmushi me sauti gami da cewa "Allah yasa Alkairi, kuma ka sanar wa Ammiee kuwa???" "A'a yau de na yanke zan sanar mata duk da nasan hankalin ta ze tashi amma zanyi ƙoƙarin fahimtar da ita" cigaba su ka yi da tattaunawa, Yarima har ya fara tsara yadda za'ayi komai. zaune suke a tafkeken Falon Ummi suna hira cikin nishaɗi gami da ƙaunar juna, "Ummi wai nida ya Abdul wayafi wani kyau??" Nana khadija ta yi tambayar ta na wani mole baki don ta ƙara tatso kyaunta, dariya su ka sa kafin Abdurrahim ya ce "Allah sarki Nanaro wai gasar kyau zakiyi da Abdul??!" cokalo baki tayi kana ta ce "so nake Ummi ta raba mana gardama wai ya ce ya fini kyau ni kuma na ce na fishi" dariya Abdul yayi gami da cewa "Kadija ai kinsan de nafiki" "haba de taya namiji zefi mace kyau??"! Nana Farida ta faɗa cike da nuna gaskiyar ta, ita kuwa Ummi ta kasa cewa ko mai se ido da take binsu da shi gami da murmushi, tana ƙara godewa Allah da ya a zurtasu da ƴaƴa masu haɗinkai da kuma son junansu, "Ummi ki raba mana gardamar nan yau dai" Abdulmajid ya faɗa ya na dariya, numfasawa tayi kana ta ce "nide a ganina baku da banbanci kamarku ɗaya kamar an tsaga kara babu wanda yafi wani kyawu" dariya su ka sa, Kadija ta tumɓuro baki ta ce "ni dai bana kama da shi gaskiya na fi shi kyau" Abdussalam ya ce ƴar zafi ce ta isheki" Abdulmajid ya ce ke kuma me cewa mata sunfi kyau shiyasa naga ai suna ƙarin kyan suje su lafta hoda wai su adole mata" Ummu ta gyara zama gami da cewa "dan Allah kudena musun nan haka" "mundena Ummin mu" Abdul ya faɗa yana kwantar da kai a kafaɗarta. *Ku Dakata Mana✋🏽🤸🏾‍♀️Saurin Me Kuke🤔 sai ka ce Za'a ci da Rabonku🤔😍* Assalamu-alaikum Masoyana kowa da kowa Barka da Warhaka. *Na zo muku da Kyakkyawan Albishir Me Matuƙar Muhimmanci. Shahararren Business Center Ɗinnan da ku ka sani me Suna HALYJASHERU Sun yi muku gwaggwaɓan Tanadi na Kyawawan Kaya Masu Kyau ga Rahusa, ina Farin cikin Sanar da ku Cewa Ku Garzaya HALYJASHERU Ku Ƙulla Kasuwanci da su Za ku yi Matuƙar Farin ciki.* *HALY-JASHERU venture's* *munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba Algus da ha'inchi kayanmu daga Ethiopian ne.* *prdct dinmu, muna Ethiopian MAGIC HAIR OIL, ANTI DANDRUFF SHAMPOO, SERUM BODY CREAM, HAND CREAM.* *Da Magungunan chututtuka Kala Daban-Daban, Da Magunguna Na SIRRIN MATA Masu Matuƙar Kyau da Iganci Gami da Kara Lafiya ajikin Ɗan Adam.* *HALY-JASHERU CENTER Ba mu tsaya iya haka ba, Muna Da Distributor a Ko Ina a Fadin Ƙasarnan Har ma da ta Ƙetare Domin Kuwa abin ba na Wasa Bane, Domin Tallafawa Ƴan Uwanmu Muka Ware Aji na Koyar da Harkokin Kasuwncinmu ga Masu Buƙata, a kan Naira 3000 kawai Muke Koyar da Wannan Sana'o'i Domin Temakon Al'uma, Da Fatan kun yi farin ciki da hakan domin Mu Farin Cikin Costomers Shine Namu. Ku Tuntuɓi C.E.O Ta Wannan Lamba 07046665338 ko 07061664264 INA GAISUWA GAMI DA GODIYA MASOYANA* yau ta kasance ranar Juma'a se shirye shiryen ɗaurin Auren Alhaji Saadiƙ (Abi) ake yi. Ammi kam ta kasa zaune ta kasa tsaye se sintiri take hankalin ta ya gama tashi, in ta tuna befi saura awa ɗaya ayimata kishiya ba seta zabura kuka kam Ammi tayi shi gashi ta ɗauki lefin ko mai ta ɗorawa Yarima da su E'iye da Inni a cewar ta su suka sa shi. Abi ya shirya tsaf ya nufi sashin Ammi ƙofar ɗakin ya tura yaji gam a rufe ƙonƙwasawa ya shigayi yana ɗan kiran sunanta, ya kusa minti goma yana aikin abu ɗaya bata buɗe ba haka ya juya jiki a sanyaye, ya nufi ɓangaren Yarima a zaune yake yana danna waya Abi yayi sallama zama yayi a gefen gadon ya ɗan kalli yarima ya ce Allah shine sheda ta naje ɗakin Hajiya Hafsa dan yi mata sallama amma taƙi bude ɗakin har na gaji" jinjina kai yarima yayi gami da cewa "karka damu Abi dan bata buɗe ɗakin ta ba kaide kawai kaiyi ta addu'a Allah ya kauda fitina" jikin amace Abi ya ce "Allah yayi maka albarka ɗana" murmushi ya ce yanzu lokaci yana ja tashi muje ya faɗa cike da ƙwara-rawa Abin na shi guiwa tashi sukayi suka nufi ma'ajiyar motocin gidan yarima ne me tuƙa motar Abi kuma yana wajen ɗan zaman banza suka ɗauki hanyar Dorayi. bayan wani ɗan lokaci suka isa Dorayi misalin ƙarfe 12:00 dubban mutane suka sheda ɗaurin Auren Alhaji Saadiƙu Yahya da Zainab Yunus, ciki kuwa hada Alhaji Aminu mai kasuwa, Babban Aminin Alhaji Saadiƙu. bayan an kammala komai kowa ya watse. ƙarfe biyar na yammaci aka kawo Amarya Zainab gidan Alhaji Saadiƙ, ƴar aikin gidan ce tayiwa ƴan kawo Amarya jagora zuwa ɓangaren Ammi, ɗaya daga cikin ƴan matan ce ta murɗa ƙofar ɗakin Ammi da niyar sushiga, abin mamaki ƙofar arufe haka suka ƙonƙwasa amma ba a buɗe ba, juyawa sukayi izuwa sashin Amarya basu daɗe ba suka gama abinda zasuyi suka bar gidan. haka rayuwa taci gaba tafiya a kowane ɓangare babu sauyi wani lokaci farin ciki wani lokaci baƙin ciki, Siyama da Aaminat suna zaune a ɗakin Anti suna hira Walid ya shigo da sallama "ya Aaminat kije inji Guda" rasss!!! rasss!! gaban Aaminat ya shiga faɗuwa, ta kalli Walid ta ce "kace bana garin kaji" dariya yayi gami da cewa "Banda abinki taya zan cewa mutumin da duk wani motsi naki ya sani bakya gari ya yarda bayan ya ganki ɗazu zaki shigo gidan nan" wani huci tayi gami da kallon Siyama, Siyama kuwa ta kauda kai gefe, "ki tashi ko nace mai kin ƙi zuwa yazo da kanshi" faɗar Walid, muzurai ta shigayi zuciyarta tana bugu ganin bata da mafita yasa ta tashi ta na cewa "shikenan tawa ta ƙare Abdul yaga zuwan Yarima jiya" Siyama ta ce nide babu ruwa na da rigimar ku da Abdul keda shi" Aaminat ta ɗan kalli Walid ta ce "dogon munafuki shine ka wani ɗakko tsawo ka tawo kirana" tintsirewa yayi da dariya ya ce "muje ya ce na tisa ƙeyarki gaba na kaiki har gabanshi" fitowa tayi yasa ta gaba suka yi waje, yana ƙofar gidan yaja ya tsaya yana jiran fitowar su, suna ƙarasowa ya kalli Walid ya ce "nagode ƙanina" murmushi Walid yayi bece ko mai ba ya tafi. gyara tsayuwa yayi gami da zuba mata narkakkun idanunsa, yaɗan matsa kusa da ita sannan ya ce "Assalamu'alaiki" murya ciki-ciki ta ce "wa'alaikumussalam" murmusawa yayi kafin ya zuba hannayen sa cikin aljihun sa na wando ya ce "Aaminat gargaɗi nazo yimiki" dan da nan jikinta ya ɗau ɓari, ya kula da yadda Aaminat take shakkarsa kuma ya na matuƙar jin daɗin hakan, ya ɗan shafa sumar kanshi kafin ya ce "daga yau se yau karki kuskura ki ƙara tsayawa da wani ɗa namiji idan har bani ba!!!!!! kuma ki sanarda wannan kucakin cewa na hanaki tsayawa da shi, karya ƙara zuwa inda kike in kuwa yazo to zansa a kusa rabashi da numfashin sa... ya ɗan tsagaita kafin yaci gaba da cewa "kuma idan na ƙara kiran wayarki kika ƙi dauka ko kika kara katse min kira to tabbas zan ɗauki tsatstsauran mataki akanki, wanda dagani harke bazamuji ɗaɗin sa ba!!!!!!" Siyama ce ta fito daga gidan cikin baƙin ciki da takaici tace "wai kai wana irin maye ne ance ba a sonka to ka haƙura mana tunda bata sonka ko ana dole ne!!!!!!!?????" wani lafiyayyan mari ya sakar mata, tayi saurin dafe wajen hawaye na zuba, cikin tsananin bacin rai ya ce "Siyama inde akan Aaminat ne zaki iya kirana da abinda yafi maye muni bazan damu ba amma kuskure ne kice na haƙura da Aaminat dan kuwa bazan iya hakan ba..., Aaminat kuwa kuka take tana cewa "haba Abdulkareem a haka kake sona kana sani kuka kana ƙaramin baƙin ciki???!!!!! aduk lokacin da na haɗu da kai idan banyi kuka ba to sena share hawaye to wannan shi ne soyayyar taka iyee????!!!!" ta ƙarasa maganar cikin shashshekar kuka ©️INDO tare da SALMA AUTA [7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION Shafi 17 Abdulkareem ya ce "Ba haka nake so ba ke ce ba kya iya hana kanki kuka, amma ni kullu yaumin burina naga farin cikinki, sani ne ba ki yi ba amma na fi kowa jin zafin kukan nan naki." Kasa magana ta yi ta cigaba da rera kukanta, Abdulkareem ya ce "Ki tafi gida, kuma ki kula da gargaɗina." Dama jiran ƙiris take ya na faɗa zaizai ta wuce hanyar gidansu, Siyama kuwa ya na jiyowa kanta ta yi saurin juyawa za ta koma cikin gida, ya dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta, juyowa ta yi kanta a ƙasa ta na wasa da ƴan yatsunta jikinta sai tsuma yake. Ya ɗan matsa gaf da ita ya na binta da zara-zaran idanunsa murya ƙasa-ƙasa ya ce "Siyama ki yi haƙuri ba a son raina na yi hakan ba, ina da zafin rai ne wani lokacin, kuma kin zo min da maganar da hankalina ba zai iya ɗauka ba, ba na jin akwai wanda zai iya sa ta farin ciki bayan ni, ni ne na dace da rayuwarta." ba tare da ta ɗago kai ba ta ce "Haka ne, ni na haƙura, amma ya kamata a ce yanzu Aaminat ta san gaskiya." Abdul ya ce "Na cika da fargabar abin da zai biyo baya shi yasa nake tsoron sanin nata, amma zan yi shawara." gyaɗa kai ta yi alamar eh, bai ƙara cewa komai ba ya juya itama ta shige gida. Tagumi ta buga ta na tunanin irin shirmen da su ka tafka, Allah i sa komai ya zo da sauƙi shi ne addu'arta a halin yanzu. Yarima Cikin shirinsa ya fito Falo ya na tafiya ya na gyara zaman agogon hannunsa, muryar Yayarsa Raheena ce ta sa ya fara slow ya na zazzare ido, idanunsa su ka sauka akanta suna tsaye ita da Ammee su na tattaunawa Khausar Ƴarta ta na gefe ta coge ta na danna waya. Ƙarasawa ya yi gurin cikin sanyin jiki Zuciyarsa fal mamakin haɗewar da Ammee da Raheena su ka yi lokaci ɗaya saɓanin Da da Raheena ta fita daga sabgar kowa na gidan a cewarta Duk sun fi son shi akanta don haka ta yi fushi ta fitar da kanta daga cikinsu, amma yau sai gasu sun haɗe kai, Addu'a yake Allah i sa ba Kishiyar Ammeen su ke son cutarwa ba. Lura da zuwansa ne ya sa su ka yi shiru da zancen da suke yi, Ammee ta kalle shi a fizge ta ce "Menene?" ya ce "Zan fita ne, Aunty Raheena yaushe ki ka zo?." a yatsine ta ce "Meye naka a ciki? ai gidan ubana ne ina da ƴancin zuwa a duk lokacin da naga dama." ya ce "Ba ina nufin wani abu bane, Allah i baki haƙuri, kuma dama ba ni na hanaki zuwa ba ke kika sa kanki." Ta buga tsaki kafin ta ce "Allah wadaran ɗan da yake zigawa a yiwa uwarsa Kishiya ni ban taɓa ganin irinka ba; ai ga irinta nan Ammee kun fifita shi a kaina yanzu ga abin da ya jawo miki nan." Ammee ta rausayar da kai ta taɓe baki gami da cewa "Umm!! kin ga ranar Duniya, amma dai kinsan ni ina sonki ai Mahaifinku ne dama me nuna bambanci wai shi ya fi son Namiji." Yarima ya ce "A'a ba ruwansa fa Ammee wallahi itace kawai ta ɗorawa Zuciyarta haka amma shi dukkanmu ya na sonmu." a hantare Ammi ta ce "Kai dallah gafara shashashan da bai san ina ke masa ciwo ba, kai ai anyi Mahaukaci tinda har ka fifita wata akan Uwarka , ka je ka rungumeta nima ina da tawa ƴar." Yarima ya kasa cewa komai ya yi gaba zungui-zungui Ammee da Raheena su ka rufa masa baya da harara, Khausar ma ta bi bayansa da kallo kafin ta zabga tsaki. Raheena ta ce "Ni fa in fayyace miki gaskiyata Ammee na tsani Abubakar tin da ya zo Duniya na dena jin daɗin rayuwa, sai ma da na fita daga cikinku ne na samu nutsuwa, gashi duk wani abu da za ka yi masa don ya ƙuntata ba ya tasiri akansa." Ammee ta rausayar da kai gami da cewa "Uhm!! Allah i kyauta dai, Nima ai yanzu kinga ya yi min sabi da Namiji ɗan kunama ne, shi yasa ake cewa in ka haifi Namiji wata ka haifawa, yanzun haka kwalliyar nan da ya yi ya cokara hula in ba sa'a ba wajen wata zai tafi." Raheena ta yi tsaki gami da keɓe baki, har cikin ranta neman makasar Yarima ta ke yi don a cewarta shine duk wata damuwa ta-ta, ci gaba su ka yi da tattaunawa, sun daɗe a wajen kafin Ammee ta raka Raheena wajen Mota dama fitowa ta yi za ta tafi shine aka tsaya ana ƙara tattaunawa. Yarima..... a ƙofar gidansu Aaminat ya tsayar da motarsa, zazzafar iska ya furzar hankalinsa duk ya rarrabu kashi-kashi wani kan Aameenat wani kan Ammee da Raheena har ma da Abi da Matarsa wadda yake kira da Aunty Zainab ko Aunty. waya ya cira ya turawa Aaminat kira kamar ba za ta ɗauka ba sai kuma ta ɗauka gami da sallama, ya sauke ƴar ajiyar Zuciya sannan ya ce amsa sallama ya ci gaba da cewa "Na zo fa." da sauri ta ce "Ka zo??" ta yi tambayar ƙirjinta na bugun shalugude... Ya ce "Kin manta na ce miki zan zo ne?" da sauri ta ce "A'a ban manta ba na zata dai ka fasa,, gani nan zuwa." ta na faɗen haka ta yi ƙitt ta kashe wayar, Yarima ya bi wayar da kallo ya na mamakin abin da ke damunta. Cikin sauri-sauri ta ɗakko gogaggen Hijab ɗinta a sif ta saka ta fesa turare, ba ta saurari inda kayan kwalliya su ke ba bare ma ta yi tunanin za ta yi, cikin sauri ta fita ta na alla alla ta je ta bashi haƙuri tare da uzurin rashin lafiya don kar Abdulkareem ya ƙyalla ido ya gan shi. A hanyar soro ta yi katari da Abba ya na ƙoƙarin shigowa, ta raɓe gefe cike da ladabi ta ce "Sannu da shigowa Abba." bai amsa ba sai ma cewa da ya yi "Na samu labarin wani ya na zuwa gurinki, to ki gaya masa wata ɗaya ya rage masa idan Aurenki zai yi ya fito a wata ɗayan nake so in aurar da ke." Zuciyar Aaminat ta bada Durummmmm!!!! Abdulkareem ne ya fata faɗo mata, ba shakka idan Abba ya ce dole a wata ɗaya zai aurar da ita ya jefata a masifa, Abba ne ya katse mata tunanin nata da cewa "Ko ba ki ji ba??" ta ce "To Abba in sha Allah zan faɗa." ya jinjina kai sannan ya wuce ciki, Aaminat ta yi waje cikinta ya na ƙugi da rugugi na tsoro. Yau ma kamar kullum ya na tsaye a jikin mota ya na jiran fitowarta, kanta a ƙasa ta ƙarasa inda yake tare da yi masa sallama ya amsa ya na murmushin ƙarfin hali. shiru ne ya ɗan biyo baya na wani lokaci kafin ya ce "Mun gaisa da Abba ai." ta yi murmushi gami da cewa "Na ji daɗin hakan." Ya ɗan gyara tsayuwarsa kafin ya ce "Na zo kuma na yi shiru, hankalina ne duk ba a kwance ba, ni ba na son fitina wallahi ko yaya take." da ɗan mamaki ta ce "Fitina kuma?" ya ce "Aff! yi haƙuri don Allah wallahi abin da ya shafi cikin gidanmu ne kinsan mata da kishi kuma Abi ya yi sabon Aure." Aaminat ta rausayar da kai cike da tausayawa ta ce "Allah sarki, am..um... dama ni kam zan ce maka ka yi haƙuri yau ba ni da lafiya ne so na ke na yi sauri naje na kwanta." "Subhanallah! me ke damunki? ai ba kwanciya ya kamata ki yi ba magani ya kamata ki sha. ido ta zaro a ɗan razane, har ga Allah ta manta cewa shi ɗin likita ne take neman jibga masa ƙaryar rashin lafiya, Yarima kuwa ya kafeta da idanunsa da su ka fara kawo ruwa, cikin inda-inda ta ce "Au..ai..am. dama fa ba wata rashin lafiya ce me girma ba da zarar na yi bacci shi kenan, don Allah ka yi min uzuri, amma kafin haka dole ne in isar maka da saƙon Abba, ya ce in gaya maka indai Aurena za ka yi to ka turo manyanka su yi magana." ta ƙarasa maganar kanta a ƙasa cikin ɗan jin kunya. Yarima ya ja numfashi kafin ya ce "Aaminat! nima ya gaya min haka kuma ya ce nan da wata ɗaya yake so komai ya faru, Aaminat ki yi haƙuri da jin abin da zan gaya miki, ki ɗauka hakan ƙaddararmu ce baki ɗaya." Ɗan numfasawa ya yi sannan ya ci gaba da cewa "Ba ni ne asalin Masoyin naki ba Abdulkareem ne!" rasss gabanta ya faɗi ta yi zaram ta ɗago kai ta zuba masa idanu cike da rashin fahimta, ya gyaɗa mata kai cike da son tabbatar da gaskiyarsa, "Abin da kunnenki ya ji shi na faɗa, Abdulkareem Aminu Mai Kasuwa, yaron da ki ke rainawa ba ki ɗauka a matsayin Namiji na shine ya turo ni gareki, na yanke hukuncin faɗa miki ba tare da ya sani ba domin dole-dole wata rana gaskiyar za ta fito kuma ko ba haka ba ma a yanzu ake buƙatar hakan domin shi Abba mijinki yake nema ba ɗan Aike ba." tasssss!! Aaminat ta wanke shi da mari cikin kuka ta fara magana "Ashe kai mayaudari ne macuci maci amana?! me na yi wa maza ne da suke son tarwatsa rayuwata? shin menene laifina a Duniyar nan da ƙaddarata ta fi ta kowace mace muni? ashe kai ma ba so na kake ba ashe kai ma yaudara ce ta kawo ka gareni!! Kaicona, ni dai ban yi sa'ar zuwa Duniya ba. Marin da ta yi masa ne ya bawa hawayen da suka cika kwarmin idonsa damar zubowa ya dafe kumatunsa ya na binta da idanunsa wanda su ke masa suya tamkar an watsa masa gaurashi. sai da ta gama magana sannan ya samu damar motsa bakinsa ya fara cewa "Idan ki ka ce haka kin butulcewa Allah gami da ni'imominsa gareki, ke zawarci kawai ki ka yi amma wata tin tana ƴar ƙarama aka keta mata haddi aka yi mata illar da ba wanda zai yi sha'awar aurenta, wata kuma sai da ta girma ta na burin samun miji na gari aka keta mata haddi ƙarshe ki ganta har da Ɗa bayan ba ta taɓa aure ba, wata kuma ta na so ta yi Auren amma har shekarunta su wuce ƴan-matanci ta koma babbar mace Allah bai kawo mata mijin Aure ko da sau ɗaya ba, amma duk da haka Aaminat ki ce taki ƙaddarar ta fi ta kowace mace muni?? shin kinsan adadin dubban Matan da suke jiran zuwan Namijin gaske irin Abdulkareem cikin rayuwarsu? tabbas Aamimat samun miji nagari kamar Abdulkareem a zamanin nan sai an tona, shine me sonki da gaskiya me son farin cikinki ko da kuwa shi zai kwana da baƙin ciki, ya na son ganin dariyarki ko da shi zai kasance ya na kuka a koda yaushe;, Aaminat wallahi ni kaina da na shigo rayuwarki ba don ni shaida ne akan irin son da yake miki ba da ban fara aikata hakan ba, ya so share miki hawaye da tafukan hannunsa amma kin ƙi amincewa kuma ya san kina buƙatar temako hakan ne ya sa ya turo ni gareki, idan ba ki manta ba a ranar da ki ka fara ganina na gaya Hajiya Maimuma cewar na zo ganin wani Patient ne , ba kowa bane face ke, Asibitin Aminu Abdallah mallakin Abdulkareem ne da sunansa aka gina shi kuma ya zaɓe ni a matsayin Babba me kula masa da Asibitin,, shi ɗin Ogana ne kuma Abokina, Babana Abokin Babansa ne; ya gujewa Abinci ya sa kansa a damuwa ya jawowa kansa Cuta duk sabi da ke, yana bala'in tausayinki; Aaminat na roƙe ki ke ma ki tausaya masa ki jiƙansa ko da sau ɗaya ne ki nuna masa Halacci, ki ƙaunace shi ko da Zuciyarki ba ta so, shi ɗin mutum ne me sauƙin kai kuma ya na sonki, za ki yi farin ciki indai har ki ka zaɓi rayuwa da shi, amma in ki ka bari kika rasa shi tabbas kin tafka asarar da ba za a iya kwatanta ta ba, wannan shine saƙona na ƙarshe a gareki Aaminat!,, ni kuma da na zo miki a matsayin ɗan yaudara ki yi haƙuri ki yafe min ba don halina ba." ya ƙarasa maganar ya na shashshekar kuka kamar ba namiji ba namijin ma Garƙeƙen saurayi. Ba iya suma ko mutuwar tsaye ba in da gaba da nan Aaminat ta gama kaiwa, idanunta ne kawai ke zubda hawaye yayin da ta kafe su akan Yarima, gangar jikinta kuwa sun dena aiki don in ba ka saurari bugun Zuciyarta ba ba za ka ce mutum ce me rai da lafiya a tsaye ba. *©️INDO Tare da SALMA AUTA* [7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION Shafi 18 Yarima ya ƙara da cewa "Ki kasance me ɗaukar ƙaddara a duk yadda ta zo miki, ba komai ne ake so kuma a samu ba, ita rayuwa ta gaji haka, ina yi muku fatan Alkairi." ya na gama faɗen haka ya juya ya shiga Motarsa ya ci gaba da tafiya ya nufi gidan su Abdulkareem. Umar ne ya ƙaraso kusa da Aaminat da ke tsaye cokam ta ƙi gaba ta ƙi baya, "Wuce ciki!" ya faɗa cikin sigar umarni, sai a lokacin ta ja dogon numfashi ta sauke tare da fashewa da kuka ta fara tafiya a hankali a hankali kamar karyayya. a gefen Katifarsu ta zauna ta haɗe kai da guiwa ta ci gaba da rero baitin kuka, ba abin da take tunowa sai Abdul sama da ƙasa ya mamaye tunaninta a wannan lokacin. Ba zato sai jin muryar Omar ta yi ya na cewa "Ke fa duk yadda ki ka ɗauki Duniya ba haka take ba, abin kuka ba ya yi miki wahala kamar wadda ba ta san ciwon kanta ba, ki na da dama amma kin ƙi amfani da ita ga ci gaba kina maida kanki baya tsabar kin san takan shiririta, duk fa ƙarancin shekarun mutum indai Namiji ne kawai ki sa a ranki Namiji ne, domin in azzalumi ne komai yawan shekarunki ko da kin yi sa'ar mamarsa ba zai yi duba da ƙarancin shekarunsa ba hakan zai zalumce ki kuma ya nuna miki ya isa ya kai a kira shi Namiji, babban kuskure ne Mata suke tafkawa na Raina ajin Maza da faɗa musu cewa ba su kai ba hakan ya na tunzura yara ƙananu su aikata abin da ba shikenan ba ƙarshe su barku da mugun tabo, amma ya rage naki ki yi shawara da Zuciyarki sai ki yanke hukunci." Ya na kaiwa nan ya fice ya bata guri, ta bi bayansa da ido tsaiii, ta daɗe ta na kallon ƙofa ta na tunani iri-iri kukan ma ba ta san lokacin da ya ɗauke ba, gajiyar da ta yi da zama ya sa ta zamewa ta kwanta ta ci gaba da tufka da warwara. Yarima a harabar gidan ya tsaya ya turawa Abdulkareem kira, ya na ɗauka ya ce "Likita Bokan Turai." murya a cunkushe Yarima ya ce "Abdul ina Parking Space ɗinku ka zo ka sameni in kana gida." rasss gaban Abdul ya faɗi sabi da jin muryar Yarima sak irin ta wanda ya ci kuka ya ƙoshi. Tashi ya yi ba tare da ya ce ƙala ba ya zabari silifas ɗinsa ya na jin Nana Khadija ta na tambayar inda zai je ya yi mata banza. Yarima ya na tsaye jikin Motarsa ya jingina hannunsa ɗaya harɗe a ƙirjinsa ɗayan kuma ya na kan ɗayan ya tallafo haɓa da shi. Abdul har shirin tuntuɓe yake wajen ƙarasowa inda Yarima yake, ko tsayawa bai ba ya ce "Lafiya kuwa Yarima?" ya girgiza kai gami da sauke nannauyar ajiyar Zuciya Sannan ya ce "Ba zan ce lafiya ba, Mahaifin Aaminat ya na buƙatar Aurar da ita cikin wata ɗaya ya nemi iyayen Masoyinta, ni kuma ban yi ƙasa a guiwa ba na gaya mata gaskiya domin rufewar shine kuskuren." tamkar Mutum ya yi gware da Babbar Mota Gingimari haka maganar Yarima ta zo wa Abdulkareem, cikin rawar baki da rashin sanin abin yi ya ce "Yanzu kana nufin ta san ni na turaka gurinta??, kuma a wata ɗaya Abba yake son aurar da ita? anya baya shan wani abu kuwa? ko an ce masa haka ake auren sama taka?" Yarima ya ce "Ya yi bazata kuwa, amma a shawarce wannan dama ce ta sameka ka san yadda za ka yi ka aureta don ba na so ka rasata, idan aka ƙara kawo min kai ba lafiya Allurar Dogon bacci zan yi maka ka yi shekara baka farka ba kowa ya huta da rigimarka." ya ƙarasa maganar cikin sigar zolaya, Abdul ya ce "I'm seriously, ban san wanda zan tinkara da maganar ba, to amma zan yi tunani sosai, na gode da temakonka." Yarima ya jinjina kai kafin ya ce "Ni zan wuce, ka kula sosai." Ya na gama faɗen haka ya shiga motarsa ya fice. Abdulkareem ya shiga zagaye a gurin a matuƙar rikice, ba zato ya ji an cafki kwalarsa, ya juyo da zafinsa don ganin wanda ya yi masa hakan, karaf su ka yi IDO HUƊU da Abdulmajeed fuskarsa a murtuke ba alamun wasa, cikin kakkausar murya ya ce "Mu je ciki dan ubanka yau ka yi mana bayani da bakinka." bai saurari maganar da Abdulkareem yake ba ya ja shi zuwa babban falo, har Dadda ma ya na zaune. a tsakiyarsu ya ja dinga kafin ya fara magana a mugun fusace, "Ashe munafukin yaron nan tayar mana da hankalin da yake wai aure yake so, amma shine ya ke ta ƙumi-ƙumi, yanzu banda tsaurin ido i na Abdulkareem ina shi ina aure yaron da ko gama iya sa riga bai yi ba?" tsananin mamaki ya cika kowa da yake gurin musamman Dadda da bai taɓa zaton ɗan da yake wa kallon me hankali zai iya yin hakan ba. Cikin sigar tambaya ya ce "Aure!??" *Ga wata Muhimmiyar Sanarwa, Ku daure ku tsaya ku karanta* *Assalamu-alaikum Masoyana kowa da kowa Barka da Warhaka. *Na zo muku da Kyakkyawan Albishir Me Matuƙar Muhimmanci. Shahararren Business Center Ɗinnan da ku ka sani me Suna HALYJASHERU Sun yi muku gwaggwaɓan Tanadi na Kyawawan Kaya Masu Kyau ga Rahusa, ina Farin cikin Sanar da ku Cewa Ku Garzaya HALYJASHERU Ku Ƙulla Kasuwanci da su Za ku yi Matuƙar Farin ciki.* *HALY-JASHERU venture's* *munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba Algus da ha'inchi kayanmu daga Ethiopian ne.* *prdct dinmu, muna Ethiopian MAGIC HAIR OIL, ANTI DANDRUFF SHAMPOO, SERUM BODY CREAM, HAND CREAM.* *Da Magungunan chututtuka Kala Daban-Daban, Da Magunguna Na SIRRIN MATA Masu Matuƙar Kyau da Iganci Gami da Kara Lafiya ajikin Ɗan Adam.* *HALY-JASHERU CENTER Ba mu tsaya iya haka ba, Muna Da Distributor a Ko Ina a Fadin Ƙasarnan Har ma da ta Ƙetare Domin Kuwa abin ba na Wasa Bane, Domin Tallafawa Ƴan Uwanmu Muka Ware Aji na Koyar da Harkokin Kasuwncinmu ga Masu Buƙata, a kan Naira 3000 kawai Muke Koyar da Wannan Sana'o'i Domin Temakon Al'uma, Da Fatan kun yi farin ciki da hakan domin Mu Farin Cikin Costomers Shine Namu. Ku Tuntuɓi C.E.O Ta Wannan Lamba 07046665338 ko 07061664264 INA GAISUWA GAMI DA GODIYA MASOYANA* Abdulmajeed ya ce "ƙwarai kuwa, yanzu na ji suna zanzen shi da DR Abubakar ba su san ina gurin ba, ga shi nan sai ya yi muku bayanin wadda zai aura kuma ku shirya don kuwa uban ƴar ya ce wata ɗaya ya bashi, fitinannen yaro kai! ko ina shi ina aure?" Dadda ya ce "Sake shi to" sakin nasa ya yi Abdulkareem ya gyara rigarsa Zuciyarsa na tsalle, ba tare da tangarɗa ba ya ce "Aaminat nake so ta layin nan Ƴar gidan Alhaji Shu'aibu." Ummi da su Farida su ka sanya salati da sallallami, Abdussalam da Abdurrahim kuwa sai sakin baki su ka yi suna kallonsa. Dadda ya ce "Na san Baban nata amma ban santa ba." cikin ɓacin rai Ummi ta ce "Wata Yarinya ce ba budurwa ba ma bazawara, yanzu sabi da Allah Abdulkareem aikin da za ka janyo mana kenan? ka na nufin ka watsar da duk tarbiyar da muka baka ne ko me?" cike da takaici ya ce "Ki yi haƙuri Ummi amma sam wannan ba rashin tarbiya bane, Ita ma fa macece kuma wadda take lokacinta, don ita bazawara ce ba ya na nufin shikenan ba ta da galihu ba, Daddy don Allah kar ka hanani abin da nake so wallahi ni ita nake so kuma ina son aurenta a cikin wata ɗayan da babanta ya ce." Dadda ya ninke Jaridar hannunsa ya zare Tabarau ɗinsa ya zubawa Abdul ido har na ɗan lokaci sannan ya jinjina kai gami da cewa "Danƙari, Babban Mutum ni ba zan zauna ina jayayya ko sa'insa da kai ba, kawai ban amince ka yi aure yanzu ba ko Bazawara ko Yarinya Ƴar goye ma duk ban amince ba, kai da Aure sai nan da shekaru Goma lokacin ka gama kafa kanka kasan inda ke maka ciwo, idan kuma za ta jiraka hazawasalam ni dai na gama maganata." Cikin fitar haiyaci Abdul ya yi saurin durƙusawa kan guiwarsa hankalinsa a matuƙar tashe ya fara magana ba tare da tunanin cewa Mahaifinsa ne a gabansa ba "Dadda ni fa Namiji ne kuma namiji ba ya kaɗan, me zan buƙata a rayuwa bayan wanda Allah ya bani?, ya bani hankali da nutsuwa kai da kanka babban Mutum kake kirana, sannan ina kasuwanci ina da shaguna a kasuwa bayan Asibitin da Ka Mallaka min, ina da ilimi kuma ko da na aureta ban girmin ƙarin ilimi ba, Dadda ka temaka ka canja min wani Punishment wannan ya yi min tsauri hankalina ba zai iya ɗauka ba." sai a lokacin Abdurrahim ya ce "Abdulkareem anya kuwa ba ka fara shan wani abu ba? Daddan ya na faɗa ka na maida martani sabi da ka rasa hankalinka?" ya girgiza kai kafin ya ce "Ka kirani Mahaukacin dai amma Please kar ka kuma ce min ina shaye-shaye, Dadda komai ka ce in yi zan yi amma don Allah karka hanani Aurenta, itama Aaminat abar a tausaya mata ce ku temaka ku bani dama na inganta rayuwarta." Dadda ya miƙe rai ɓace ya ce "Tabbas hankalinka ya gushe ɗin ne shi yasa kake tunanin ma zan canja maganata, ka fi kowa sanin ni kaifi ɗaya ne mutum me tsatstsauram ra'ayi da kuma magana ɗaya, abin da zai yuwu shi nake amincewa da shi ba wanda ba zai yuwu ba, kar ka ƙara tinkara ta da wannan maganar idan kuma ka yi hakan fushina ya tabbata gareka; don muna nuna maka so ba shi yake nufin za mu barka ka dinga katoɓara iya son ranka ba." ya na kaiwa nan ya gangara sashinsa cike da fushi da takaicin haukan Abdulkareem, don a cewarsa hauka ne kawai. Ummi kuwa da abin duniya ya isheta sai ta fashe da kuka itama ta tashi ta yi nata ɓangaren. Su Abdurrahim su ka tasa Abdul gaba su na yi masa faɗa da nasihohi, sai dai a nashi ɓangarem in ta shiga ta kunnen hagu ne sai ta fito ta dama. ©INDO tare da SALMA AUTA [7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION Shafi 19 Sai da suka gaji da yi sannan kowanne ya saɓe ya bar Abdul a gurin. Bedroom ɗinsa ya nufa zuciyarsa cike da baƙin ciki da takaici, gabaki ɗaya haushin kowa yake ji musamman su Abdulmajeed masu bakin yiwa mutum faɗa. Haka ya kwana cikin takaici ko baccin kirki ya kasa yi sai juye-juye yake yi. a ɓangaren Abubakar (Yarima) ma haka ya kwana ba kwanciyar hankali, baccin sai ɓarawo. Aaminat ita ma haka ta kwana sai kici-kici take ta kasa baccin daga ta kwanta sai ta tashi, sai ma ta ga daren ya yi mata tsayi da yawa sabi da ta ƙagara garin ya waye. Washe gari kuwa tin safe Abba ya na fita itama ta fita zuwa gidan su Siyama. Bayan ta gaida Aunty ta wuce ɗakin Siyama Ta na zaune bakin katifarta ta zuba tagumi da hannayenta duka biyu. Aaminat ta ƙarasa ta zauna jiki a sanyaye ta ce "Siyama kin ji abin da ya faru dani? ashe wai Abdulkareem ne ya turo min Yarima." Siyama ta ja numfashi kafin ta ce "Hakan ba baƙo bane a gurina domin kuwa nima da sa hannuna a ciki, Abdul ne ya roƙe ni na yi masa wannan Alfarmar, a lokacin da na ce dole sai na kai ki Asibitin nan ai shi ne ya sa ni, ina ganin fa kar ki tsaya tunanin wani abu daban Aaminat, Abdulkareem ya na sonki tsakaninsa ga Allah ba don wani abu ba." jikinta ya ƙara yin sanyi salam ta yi shiru ta ja tunani, sun daɗe a zaune curko-curko ba me cewa ƙala sannan Aaminat ta ce "Gaskiya in haka ne ban kyauta masa ba, duk abin da yake yi don ya fitar da ni daga cikin damuwa ne, yadda nake ɗauka duk ba haka yake a zahiri ba." Siyama ta sauke nannauyar ajiyar Zuciya sannan ta ce "Na godewa Allah da ya baki ikon fahimta, yanzu abin da za ki yi kawai ki ba shi haƙuri kuma ki amince da soyayyarsa idan ba ki yi haka ba kuwa ni ba ruwana, ba gori ba ko me zai faru dake nan gaba ba zan ƙara damun kaina ba." Aaminat ta ce "To ni ta ya zan ba shi haƙuri??" Siyama ta ce "Ba ni wayarki in sa miki lambarsa ki kira shi, yanzu ba tare da ɓata lokaci ba." Ba musu ta miƙa mata wayar ta karɓa ta jera mata lambobin sannan ta bata wayar ta. Karɓa ta yi ta tashi jiki ba ƙwari ta koma gida, tin da ta zauna take tunanin kiran nashi sai dai in ta kira ba ta san ta ina za ta fara ba. Abdulkareem Sai 10:00am ya fito lokacin duk yayyensa su Abdussalam sun bar gida su Khadija ma su na makaranta sai Ummi ita kaɗai a Falo ta na zaune kamar korarriya, ita ba magana ba ita ba aiki ba ta na dai zaune kurum sai aikin tunani take. Kusa da ita ya zauna ya gaisheta ta amsa masa ƙasa-ƙasa, ganin ta na ci masa magani ya sa shi tambayarta abin da ya faru. Cikin takaici ta ce "Abin da za ka ce kenan? har ka manta tayar mana da hankalin da ka yi jiya?" Ya rausayar da kai kafin ya ce "Meye abin tashin hankali Ummi? daga na yi zancen Aure ba fa ƙaramin yaro ba ne ni, i'm twenty something years old fa kuma ina da komai da zan iya riƙe mace." Wata harara Ummi ta zabga masa wadda ta sa shi raina kansa, cikin matuƙar takaici ta ce "Abdulkareem shiga taitayinka, mu ba sa'o'in wasanka bane, mu za ka zo wa da rashin hankali cikin gida? da ƙuruciyarka ka ɓata ta ta hanyar Auren Bazawara?, to bari ka ji ni ko 15 years indai budurwa za ka aura daidai kai ba zan damu ba, amma ina raye ba ka isa ka auri budurwar da ta girmeka ba ma bare wata Bazawara da Allah ne kaɗai ya san tsiyar da ta tufka wancan mijin nata ya rabu da ita, ni dai ba a zuriya ta ba in za ka yayewa kanka ka yaye tin kafin dare ya yi maka." Ya buɗe baki zaiyi magana ta dakatar da shi da cewa "Na gama maganata, ba na son jin komai, na riga na faɗa ban amince ba kuma idan ka yi ko bayan raina ban yafe ba, tinda na lura kai zuma ne sai da wuta, kar ka ji irin baƙin cikin da na kwana da shi jiya na furtawa da ka yi cewar za ka auri bazawara, wannan ai zubda kima da mutuci ne, to ni ba na son jin komai a bakinka indai ba cewa za ka yi ka janye ba, kuma ni me iya fita shirginka ce indai ka ce za ka bujire mana." Sakkototo ya saki baki ya na kallon Ummin ta shi, a ransa ya na tsaka da mamakinta bai taɓa zaton za ta iya yin abin da ta aikata ba, kenan itama ta na ɗaya daga cikin waɗanda suke ƙyamar Bazawara? to wai me yasa hakan? Tambayoyi ne suke masa yawo a tunaninsa sai dai ba shi da amsarsu ba shi da mai bashi don haka ya tashi ya zabari mota ya bar gidan. *Ga wata Muhimmiyar Sanarwa, Ku daure ku tsaya ku karanta* *Assalamu-alaikum Masoyana kowa da kowa Barka da Warhaka. *Na zo muku da Kyakkyawan Albishir Me Matuƙar Muhimmanci. Shahararren Business Center Ɗinnan da ku ka sani me Suna HALYJASHERU Sun yi muku gwaggwaɓan Tanadi na Kyawawan Kaya Masu Kyau ga Rahusa, ina Farin cikin Sanar da ku Cewa Ku Garzaya HALYJASHERU Ku Ƙulla Kasuwanci da su Za ku yi Matuƙar Farin ciki.* *HALY-JASHERU venture's* *munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba Algus da ha'inchi kayanmu daga Ethiopian ne.* *prdct dinmu, muna Ethiopian MAGIC HAIR OIL, ANTI DANDRUFF SHAMPOO, SERUM BODY CREAM, HAND CREAM.* *Da Magungunan chututtuka Kala Daban-Daban, Da Magunguna Na SIRRIN MATA Masu Matuƙar Kyau da Iganci Gami da Kara Lafiya ajikin Ɗan Adam.* *HALY-JASHERU CENTER Ba mu tsaya iya haka ba, Muna Da Distributor a Ko Ina a Fadin Ƙasarnan Har ma da ta Ƙetare Domin Kuwa abin ba na Wasa Bane, Domin Tallafawa Ƴan Uwanmu Muka Ware Aji na Koyar da Harkokin Kasuwncinmu ga Masu Buƙata, a kan Naira 3000 kawai Muke Koyar da Wannan Sana'o'i Domin Temakon Al'uma, Da Fatan kun yi farin ciki da hakan domin Mu Farin Cikin Costomers Shine Namu. Ku Tuntuɓi C.E.O Ta Wannan Lamba 07046665338 ko 07061664264 INA GAISUWA GAMI DA GODIYA MASOYANA* Ya na cikin tafiya ya ji wayarsa ta fara tsuwwa, ya duba ga mamakinsa sai ya ga lambar Aaminat, da sauri ya ɗaga tare da ƙoƙarin tsayar da motar a gefen titi. Sallama ta yi ya amsa cikin sauri sannan ya ci gaba da tambayar lafiyarta. Shiru ta ɗan yi kafin ta ce "Na kiraka ne don na baka haƙuri akan duk abin da na yi maka, ina fatan za ka manta da komai." daga jin muryarta za ka san ta na cikin sanyin jiki gami da tsoro tsoro. Abdulkareem ya saki murmushin farin ciki gami da cewa "Kullum cikin manta abin da ki ka yi min na rashin daɗi nake, kuma kullum farin cikin da ki ka sa ni nake tunawa na tin kafin ma na furta miki kalmar so, ina fatan nima kin yafe min akan turo miki wani da na yi, bayan haka kuma ina so ki faɗa da bakinki cewar yanzu kin yarda ni masoyinki ne ko da kuwa ke bakya sona." Murmushi ne ya suɓuce mata ba tare da ta shirya ba, "Eh na amince kai masoyina ne, kuma ni ba ka yi min laifin komai ba." Kusan tare su ka sauke zazzafar ajiyar Zuciya, Abdul ya lumshe ido ya na godewa Allah. Jin ta ce "Sai anjima" ya sa shi sauri cewa "Tsaya mana, daga kira kuma sai ki ce sai anjima? nifa na fita ne amma sai na ji kamar in dawo, ko kina wani aikin ne?" zaro ido ta yi ta ce "Ahh gaskiya kar ka dawo." Ya yi murmushi gami da cewa "Me yasa?" ƴan kame-kame ta fara yi masa don haka ya ce "Ba komai zuwa dare dai za ka ganni in Allah ya yarda, ki tanadar min kyakkyawan murmushin nan naki ma kawai ya ishe ni." Ba ta iya cewa komai ba sabi da wata ƴar kunya da ta rufeta, don kuwa ta na sane da cewa shi ɗin Ƙaninta ne, a ganinta abin kunya ne ta saki jiki ta yi soyayya da shi. Shi kuwa hakan bai dameshi ba. Tuna baya Lokacin da Abdulkareem ya yi rashin lafiya su Abdulmajeed su ka kai shi Asibiti da daddare. sai da su ka yi waya da DR Yarima ya sanar musu ya na asibitin Ameenu Abdullah sannan su ka nufi can don dama shi ne Family Dr ɗinsu. Bayan ya gama bincikar lafiyarsa ya ce su bi shi Office ɗinsa. Hakan su ka yi nan yake musu bayanin damuwa ce ta sako Abdulkareem ɗin gaba, jin hakan ya tsuma musu zuciyarsu don ba su ga wani abin damuwa a Duniyar Abdulkareem ba. Dr Yarima ya miƙe gami da cewa "Kai ƙaramin mai gida zo mu je in gana da kai." Abdulkareem ya tashi ya na ƙasa-ƙasa da ido don ya lura fa kallon tuhumar da suke jefa masa. Bayan sun fita sarari inda ba mutane Yarima ya tsaya ya na kallon Abdul sannan ya ce "Kai ya ne?" Abdul ya bashi hannu suka tafa ya na cewa "Likita Bokan Turai, ba ka so a Mutu ba ka so a Zauna Lafiya." Yarima ya yi dariya ya na cewa "Ai ku ne ku ka ɗaure mana abin, kai wai meye a ciki ne? faɗa min gaskiya me ya sa ka jawowa kanka ƙunci?? soyayya ka fara yi ko?" Abdul ya ce "Malam ina ruwanka ba na son sa ido it's my life." Yarima ya dara kafin ya ce "Ba ruwana amma da ruwan Alhaji Mai kasuwa, zan iya gaya masa gaskiya har ma na ƙara da duk abin da na ga dama." Abdulkareem ya shafi ƙeyarsa gami da cewa "Ka matsa da yawa; kuma hakane wallahi soyayya na faɗa, amma ba wannan ce matsalar ba Yarinyar ta ƙi yarda da ni ne, ni kuma ina baƙin cikin ganinta cikin damuwa ina so na kawar da wannan tsarin a rayuwarta amma ita duk ta ƙi yarda, yanzu haka ba ta da lafiya amma ta ƙi yarda da temako na, amma yanzu komai ya zo da sauƙi kai ne za ka temake ni." Yarima ya zaro ido ba tare da ya bi ta kan sauran zancen ba ya ce "Ta ya? kai da masoyiyarka kuma ni meye nawa a ciki?" Abdul ya ce "Ta na da gardama fiye da kima don haka nake so ka je mata a sigar likita daga nan sai ka fara jan hankalinta, har ku fara soyayya, amma fa ka bi a hankali idan ka kuskure min sai an ji ni da kai har Kotun Ƙoli." Yarima da mamaki ya cika shi ya ce "Kai, gaskya yaro yaro ne, ni ba zan iya wannan kasassaɓar ba, ka dai nemo wata mafitar." Abdulkareem ya ce "Ba ni da wata mafita sai kai, ka fahimta mana, ni fa wallahi bala'in tausayinta nake ji, ba wai na damu akan dole ta so ni bane, kawai ina sonta ne don na sanya ta farin ciki na gaji da ganinta cikin damuwa da wani mugun hali na rayuwa, daga tausayinta ma na ji gaba ɗaya ita nake son Aura, don Allah ka yi min alfarmar nan Dr in ba da haka ba za ta iya rasa ranta a banza domin ta fi ni faɗawa rashin lafiya." Yarima ya yi shiru ya na nazari har na wani lokaci kafin ya ja numfashi, ba tare da hakan ya kwanta masa a rai ba ya amince don kawai Abdul ɗin ya nemi temakonsa ba zai iya ƙin yi masa ba. Abdul ya yi matuƙar farin ciki da amincewar Yariman, su ka rabu da haka da cewar za su ƙarasa plan ɗin ta waya. Hakan su ka yi Abdul ya zauna ya tsara Siyama da Yarima kuma su ka aiwatar kamar gaske. Ci gaban labari kamar yadda ya ce za ta ganshi da daddare bai yi ƙasa a guiwa ba ya je, ta sha surutu sai dai ta kasa sakin jiki da shi. Abdul kuwa samun kanta ya sa ya manta da rigimar cikin gidansu, har sai da ya ko ya ga suna yi masa gani-gani sannan ya tuna akwai ƙura. Tin daga wannan lokaci Abdulkareem da Aaminat su ka haɗe, ya na gwada mata soyayya iya iyawarsa, a nata ɓangaren kuwa tunanin halin da Yarima yake ciki take yi, haka kawai ta ji duk ta damu da shi, gashi ta na tsoron kiransa ya gayawa Abdul ta kira shi hakan ya jawo mata matsala don haka ta haƙura ta ci gaba da tunaninsa ba dare ba rana. a ɓangaren Yarima kuwa tin daga ranar da ya rabu da Aaminat duk ya rasa nutsuwarsa, ba dare ba rana ba aiki ba rashin a kowace daƙiƙa ita yake tunani, a gefe guda kuwa yayarsa Raheena da Ammee sun saka shi gaba da tsangwama, ga sharri iri-iri da Raheena ta ke binsa da shi don kuwa har cikin ranta ta tsane shi. ©️INDO tare da AUTAR JARUMAI [7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga MIKIYA ONLINE WRITER'S Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S Shafi 20 "salamu alaikum" Abi yayi sallama ganin yarima be amsa ba yasa ya ƙarasa inda yake, dafa kafarɗar shi yayi, da sauri Yarima ya ɗago tare da zazzaro ido, Abi ya murmusa gami da cewa "Abubakar lafiya ina sallama amma hankalinka baya jikin ka!!!!???" "Abi babu komai" "A'a da wani abu faɗamin" rausayar da kai yayi ya ce "Abi dama... dama.. wata matsala ce" "matsala kuma" ya faɗa cikin sigar tambaya, kafin ya ce "faɗamin" ajiyar zuciya Yarima yayi gami da cewa "Abi maganar gaskiya wata yarinya ce Abdulkareem mai kasuwa yake sonta kuma Bazawara ce bata sonshi, shine ya turani wajen ta a matsayin ina sonta rana ɗaya mahaifinta ya ce nafito nan da wata ɗaya ze Aurar da ita ni kuma na laburtawa asalin masoyin ta yanzu ban san yadda suke ba" tunda Yarima ya fara magana Abi yake binshi da kallon mamaki, gyaran murya Abi yayi kana ya ce "Abubakar maiyasa kuka aikata haka????.. ƙuruciya da shirme ya rinjayeku kunje kun ai kata ba dai-dai ba" Abi ya ƙarasa maganar cikin damuwa, Abubakar ya numfasa kafin ya ce Abi yanzu a bin damuwar shine ina son Aaminat nima" rassss rassss gaban Abi ya buga ya dubi Yarima ya ce "dama baka da tunani ka rasa hankalinka ne kasan kuwa me kake shirin aikata wa ????!!!!! cin amana fa karka manta shima fa ɗana ne nida mahaifin shi tamkar wa da ƙani muke fa!!!!" ƙasa yayi da kai yana goge ƴar ƙwallar da ta gangaro kumatun sa Abi ya ce "kayi haƙuri ɗana, karka bari zuciyar ka tayi maka ɗanyan aiki kaji kaida Abdul ɗaya ne a waje na ba zan iya dannewa Abdul haƙƙin shi ba banda haka da na yi wani abu a kai" murmushin ƙarfin hali Yarima yayi ya ce "Abi ni dama bazan iya cin a mana ba ko makamancin haka ba, kuma zanyi ƙoƙari har naga Abdul ya mallaki Aaminat" murmusawa Abi yayi yace tare da cewa "ka kawar da tunanin komai kaji Allah yayi muku Albarka baki ɗaya" "Amin" yarima yace, suka kamo wata hirar suka ɗora, zaune yake ya buga tagumi yana tunane-tunane Nana Kadija ta shigo da sallama zama tayi kusa da shi, gami da cewa "ya Audu komai fa ƙara zafi yake, ya kamata ka janye maganar Auren nan" wani dummmm!!!! yaji a ƙwaƙwalwar sa tayi, yayi saurin dafe kai, cikin sanyi da damuwa Nana ta ce "yanzu haka Ummi kuka take domin kuwa Dadda ya dora mata laifi ya ce duk ita ce ta ɓata mai yara" a kiɗime ya dube ta ya ce "Ummin ce take kuka???!!!" "eh" "yasalam bari naje wajen ta" da sauri Nana ta riƙeshi ta ce "ko kaje bazata kula kaba nima har nagaji da magana batace komai ba" komawa yayi ya zauna Kadija ya ce "yanzu mafita zamu nemo" ya ce "Dole hakan za'ayi don ba zai yuwu na bar Aaminat cikin wannan halin ba, kuma zan iya yin abinda ba zai yiwa kowa daɗi ba" a gigice Nana ta kalle shi ta ce "nashiga uku ya Abdul a hayyacin ka kake kuwa? me za ka yi kuma haka? don Allah ni dai karka jawo mana abin da ya fi ƙarfinmu ka yi haƙuri" cikin ɓacin rai ya ce "wai ba kince mafita zamu nemo ba??? to mu nemo mana" a jiyar zuciya ta sauke kana ta ce "lokaci yanaja kuma Dadda da Ummi kara sama suke a ganina kaje ka sanarwa da Uncle Rabi'u", da sauri ya ce "Alhamdulillah Allah na gode maka shikenan matsalata kau" Nana tayi dariya kana ta ce "duk kabi ka zauce a kan Bazawara" dan da nan ya ɗaure fuska ya ce "kinga ke fa matsalarki ba a abu da ke sai kin ɓatawa mutum rai" dariya tayi gami cewa "kwana biyu baka da lokacin da zamu ɗanyi faɗa ko yanzu da nace maka Audu babu abinda kace shi yasa na ce haka amma kayi haƙuri" murmushi ya ɗanyi kana ya ce "to yanzu dai zanje nasami Uncle Rabi'u kuma kinga shine sama da Dadda dole Dadda ya risina" amma fa matsalar ɗaya ce kai ma kasan Dadda kaifi ɗaya ne" cije gefen laɓɓan sa yayi kana ya ce "Allah ya dafa ma lamarin kawai shi ne" daga haka suka cigaba da tattauna wa *Ga wata Muhimmiyar Sanarwa, Ku daure ku tsaya ku karanta* *Assalamu-alaikum Masoyana kowa da kowa Barka da Warhaka. *Na zo muku da Kyakkyawan Albishir Me Matuƙar Muhimmanci. Shahararren Business Center Ɗinnan da ku ka sani me Suna HALYJASHERU Sun yi muku gwaggwaɓan Tanadi na Kyawawan Kaya Masu Kyau ga Rahusa, ina Farin cikin Sanar da ku Cewa Ku Garzaya HALYJASHERU Ku Ƙulla Kasuwanci da su Za ku yi Matuƙar Farin ciki.* *HALY-JASHERU venture's* *munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba Algus da ha'inchi kayanmu daga Ethiopian ne.* *prdct dinmu, muna Ethiopian MAGIC HAIR OIL, ANTI DANDRUFF SHAMPOO, SERUM BODY CREAM, HAND CREAM.* *Da Magungunan chututtuka Kala Daban-Daban, Da Magunguna Na SIRRIN MATA Masu Matuƙar Kyau da Iganci Gami da Kara Lafiya ajikin Ɗan Adam.* *HALY-JASHERU CENTER Ba mu tsaya iya haka ba, Muna Da Distributor a Ko Ina a Fadin Ƙasarnan Har ma da ta Ƙetare Domin Kuwa abin ba na Wasa Bane, Domin Tallafawa Ƴan Uwanmu Muka Ware Aji na Koyar da Harkokin Kasuwncinmu ga Masu Buƙata, a kan Naira 3000 kawai Muke Koyar da Wannan Sana'o'i Domin Temakon Al'uma, Da Fatan kun yi farin ciki da hakan domin Mu Farin Cikin Costomers Shine Namu. Ku Tuntuɓi C.E.O Ta Wannan Lamba 07046665338 ko 07061664264 INA GAISUWA GAMI DA GODIYA MASOYANA* "ya Aaminat kinsan kuwa Mama ce ta ziga Abba wai yace a wata zai Aurar dake" sakin baki tayi tana kallon Umaima, cikin mamaki ta ce "wai sai yaushe Mama zata bari nasha ruwa??! ta kurar tata tayi yawa kinga yanzu ta ƙara jefani a masifa" tsaki Umaima tayi gami da cewa "ai wallahi ko samun mata kamar Umma da wahala a gabanta fa ta faɗa amma ta kasa cewa komai saida ta dawo ɗaki naji tana kuka dana tambaye ta sai tace babu komai, saida na matsa mata sannan ta faɗa mini kuma tace karna faɗa miki ni kuma yau na faɗami" wani numfashi Aaminat taja ta sauke tare da gargiza kai" ta ce Ummm Mama kenan haryau bazata karaya ba ai gashina ƴata da tafi fifi-tata yanzu ita ce take mata fitsara iri-iri amma taƙi ganewa" Umaima ta ɗan gyara zama gami da cewa "nifa wallahi ina ganin Auren ki da Abdul kamar ba zaiyuwu ba" Aaminat tayi wani murmushi mai kama da yanzu aka fara kana ta ce "nima ina wannan tunanin amma innna tuna waye Abdulkareem sai na kauda tunanin hakan" murmushi Umaima tayi kana ta ce "nimafa na faɗa komar so yanzu in na kira Abdurrahim baya ɗauka kuma baya kirana" rausayar da kai Aaminat tayi kana ta ce "kinga ai dama haka komai yake, keda Fati baku da aiki sai yaudarar samari gashi kema anyi miki saikiji da daɗi ko babu" ƙasa tayi da kai cike da nadama Aaminat ta ce "amma kita addu'a Allah zai cire miki sonshi" "to" tace suka cigaba da hirar duniya, tuni Abdulkareem ya shirya tsaff ya ziyarci gidan Uncle Rabi'u ya zayyane masa duk a binda kefaruwa, Uncle Rabi'u ya ɗan gyara zama gami da cewa "to duk naji bayanin da kayi mini in sha Allah yau da yammaci zanje Abuja amma nan da kwana uku zanje nasame shi" Abdul ya murmusa, Uncle ya dafa kan Abdul gami da cewa "karka damu kaji in sha Allah ko mai zai dai-dai ta Allah yayi muku albarka" "Amin" Abdulkareem ya ce tashi yayi gami da cewa "Baba ni zan koma a gaida su ya Abbas" har zaka tafi???" "eh Baba zanje in zagaya masana'antar mu" Baba ya ce "to Allah ya tsare ka gaida ƴan uwan ka" "Amin" ya ce ya fita inda ya ajiye motar sa, Bayan kwana uku Yarima ya shrya tsaf yayi kyau sosai babban Falo ya nufa yana tafe yana tunane-tunane harya ƙarasa falon zama yayi akan kujera sannan ya dubi Ammi ya ce "Ammi ina kwana" "lafiya ƙalau" ta faɗa fuska babu yabo babu fallasa, tashi yayi ya ce "Ammi natafi" "ina zaka???!!!" ko ɗarrr baiji ba ya ce "gidan su E'iye" wata muguwar harara tabuga mai tare da ya mutse fuska, juyawa yayi zai tafi ta ce "waɗannan kakan nin naka mayune sun kama kurwar ka yaro tun kana ƙarami nake nesanta ka da su amma sun liƙema" ran Yarima in yayi dubu ya ɓaci, dan haka yaci gaba da tafiya ko waiwayon ta baiyi ba yanaji tana surfa masifa amma yayi ficewarsa, Bai ɓata lokaci ba ya ƙarasa gidan su E'iye kai tsaye Falon Inni ya nufa yana tafe yana kiran sunan ta cike da tsokana, fitowa tayi daga ɗakin dake cikin Falon tana cewa "sannu da zuwa saurayi na" murmushi yayi gami da zama ya ce "budurwa ta nayi kewarki kwana biyu" murmushi tayi kana ta ce "Allah sarki rabin raina ai kana zuciya ta" dariya ya ɗanyi gami da cewa "ina E'iye" Inni tace "inaga dai tana ɗakin ta ai yanzu rana tayi" shiru ne ya ɗan ratsa na wani lokaci kafin Inni ta ce jikalle na baka da lafiya ne???? naga ka rame" murmusawa yayi gami da cewa "A'a lafiya ta lau kawai dai jiki da jini" "to saika faɗa mana mara jini ajika"! E'iye ta faɗa gamida ƴar dariya juyawa yayi ya kalle ta ya ce "ko sallama bakiyi ba amma kunnan ki yaji abinda nace" murmusawa tayi kana ta ce "ai kunacan kuna soyewa kaida budurwar ka nayi sallamar baku amsa ba" dariya yayi ya ce "to mata ta irin wannan kishi haka" "Allah ya kyauta nayi kishin ka ni yanzu ma ba Auren ka nake ba nasake ka" "subhanallahi dama mata ce take sakin mijin ta" dariya tayi ta ce "ni dai bana Auren" shima dariyar yayi cikin jin daɗin barkwancin da suke shida kakan nin na sa, Inni ta ce "Habu zaka kaini nayi siye'siye??!" "kai Inni banason tsokana ki daina cemin Habu" dariya ta ɗanyi ta ce "to ai sunan ka ne" "to kishirya kuma bazamu da E'iye ba karta samana ido" dariya sukayi sudika, Inni ta shirya tsff tashe hijab ɗinta suka kama hanyar shopping, INDO CE &&& Salma Auta [7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga MIKIYA WRITER'S Association Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S Shafi *21* Basu ɓata lokaci ba suka kammala siyayyar da zasuyi suka koma gida, kashingiɗe yake a kan kujera yana waya cikin nishaɗi da farinciki sai faman fara'a yake sam ya manta a inda yake ya ce "Aaminat Ina sonki, so na har a bada, in dai inaraye bazan bari kisake kukan baƙin ciki ba" wani ni'imtaccen murmushi ta saki, kamar tana ganin sa, ya ƙara da cewa "Aaminat kece ƴa mace ta farko da nakejin bazan iya rabuwa da ke ba"! "yazama dole karabu da ita kuwa" rassss!! rassss!!! gaban sa ya buga yayi saurin katse kiran yana muzurai, Abdussalam ya ɗan yi murmushi mai cike da ma'anoni ya ce "yaro man kaza" ƙasa yayi da kai, Abdussalam ya zauna gami da cewa "Auta mai yasa ka koma haka???, naga Uncle Rabi'u yazo duk da ban san dalilin zuwansa ba amma na alaƙanta zuwan da kai kaika ce ya zo ko" cikin sanyi ya ce "eh ni nace yazo ya sami Dadda", kallon sa ya ɗanyi cike da tausayawa ya ce "Abdul kayi haƙuri ka taushi zuciyar ka, kabi Umarnin iyayenka" har ga Allah Abdussalam baya jin daɗin yadda suke yiwa Abdul saidai acewar su hakan shine zaisa ya janye maganar sa ta Auren Aaminat, a raunane ya ce "Ya Abdullah ina sonta wallahi ku tausaya mini ku dubi halin da ɗan uwanku yake ciki, ita ɗin abar tausayi ce ina tausaya mata, kutayani ƙoƙarin shawo kan su Dadda," wani lafiyayyan mari ya zuba masa, sai da yaga taurari sun gifta, cikin ɓacin rai ya ce "ni zaka dinga faɗawa kana sonta dan baka da hankali, cikin kwanaki kaɗan ka canza mana gida komai namu ya canza kuma duk ta silar wata matsiyaciyar yarinya," ƙasa yayi da kai dan kuwa ko kashe sa Abdussalam zaiyi baya jin zai iya ɗaga mai murya, rai a ɓace Abdussalam ya bar wajen, tunda Uncle Rabi'u yazo suke ƙarda da Dadda akan yabar Abdul ya Auri wadda yake so, saidai Dadda ya kafe ya tsaya tsayin daka a kan ra'ayin sa, Uncle Rabi'u ya gyara zama gami da cewa "bai kamata ka hana yaro abinda yake so ba, tunda yace Aure yake so to ka rabu da shi mana yayi kuma ai ba haramun bane dan ya Auri bazawara", Dadda ya rausayar da kai, cikin girmama yayan nasa ya ce "bawai na hana shi Auren bazawara bane, No, Ina buƙatar ya ƙara hankali ya san inda ke masa ciwo, ga Abdulmajid ga Abdurrahim ga Abdussalam duk ba wanda ya taɓa zuwa min da zancen Aure sai ƙaraminsu wai Abdulkareem, maganar Gaskiya Yaya ina girmamaka ne shi yasa nake bi a hankali amma ba zan iya bari ɗana ya yi aure ya na da shekara ashirin da ɗaya ba, don bance ya kai da biyu ba ma, ka yi haƙuri in sha Allahu indai ya ƙara hankali to wannan ba ni da matsala ko wa zai aura indai ba mara tarbiya bace" cike da gamsuwa Uncle Rabi'u ya ce "Eh na fuskanceka sosai kuma in sha Allahu zan ƙara yiwa Yaron nasiha, zan nuna masa cewa haƙurin ma ya na da amfani, amma ku tayashi addu'a kawai Allah i zaɓa masa alkairi idan yanzun ne idan sai nan gaban ne." murmusawa Dadda yayi gami da cewa "In sha Allah za mu ƙoƙarta, na ji daɗi da ka fahimce ni." murmushi Alhaji Rabi'u yayi ya ce "to Allah yayi mana mai kyau, kuma dan Allah ku daina fushi da ɗana shifa yaro ne," ƴar dariya Dadda yayi gami da cewa "ai ɗan na ka yana da kafiya sam ya koma tamkar bashi ne wanda nake kira da Babban mutum ba!" Alhaji Rabi'u ya ce "toni zan koma sai akira min Abdulkareem ɗin" Dadda ya ce "to" sallama sukayi da Alhaji Rabi'u cikin fara'a da sakin fuska Dadda yanufi ƙofar da zata sada sa da labun gidan, ba a ɓata lokaci ba Abdulkareem ya shigo Falon kai a ƙasa, zama yayi a ƙasan kafet, ya ce "Uncle gani" murmushi Uncle Rabi'u yayi sannan ya ce "Abdul kayi haƙuri kasa Allah a ranka kaji ka maida komai ba komai ba, mahaifinka yaƙi Amincewa da maganar Auren ka, nayi iya ƙoƙari na amma ban sami nasarar shawo kanshi ba amma ina ganin kayi biyayya wa iyayen ka," wasu hawaye ne masu zafin gaske suka fara tsere a kumatun Abdul, "kayi haƙuri ka daina kuka kowa da tashi ƙaddar idan Allah baiyi matar ka bace to babu makawa sai kun rabu,...." ya ɗan tsagaita kafin ya ce "ka sanar da yarinyar cewa mahaifinka bai amince ba idan tana da wani tace ya fito" zuwa yanzu Abdul ya fara fita haiyacin sa, kuka yake razgawa tamkar ƙaramin yaro Uncle Rabi'u kuwa sai faman rarrashin sa yake, "Abdul kaifa musulmi ne ka ɗauki ƙaddara a yadda ta zo ma, ka gode wa Allah da ya wadata ka, ta ko ina ka kana da damar da zaka taimaka mata, ita rayuwa dama haka take wani lokaci farin ciki,.. wani lokaci baƙin ciki, kuma a rayuwa Ɗana ko a da ma ba yanzu da zamani ya juya ba, Ba komai ake so kuma a samu ba ɗana, ka tuna waɗanda su shuɗe kafin mu, ko ba ka sauraren tarihi ne? gashi za ka ga su na son abu to kuma ba shi Allah yake basu ba, wasu lafiya suke nema sun rasata, wasu ƴan uwa suke so gashi ba su da su, wasu ƴaƴa suke buƙata kuma me kyautar bai basu ba, wasu kuɗi ne abin son su amma Allah bai yi da rabonsu ba, za ka ga wasu ido ne ma basu da shi, wasu ba su da damar jin magana duk da suna da kunnuwa, amma duk a haka muke raye kuma muke farin ciki da abinda Allah ya bamu, to ita rayuwa a haka take, ta yuwu ita ba matarka bace shi yasa hakan take faruwa" cikin kuka ya ce "Uncle nagode da nuna damuwar ka akaina Allah ya saka da alkairi kuma in sha Allah zanyi ƙoƙarin ganin nayi wa iyayena biyayya koda hakan zaiyi silar rayuwa ta" yana gama maganar ya ƙara fashewa da wani matsanancin kuka mai tsuma zuciya, cike da tausaya wa Uncle ya ce "Abdul kasa a ranka haka Allah ya rubuta Aaminat ba matar ka bace kaji kataya ta da addu'a Allah ya bata miji nagari wanda zai riƙeta da gaskiya da Amana!" daker ya iya ɗaga harshen sa ya ce "na..na..na..nagode!!!!" jiki a matuƙar sanyaye Uncle Rabi'u ya tashi sannan ya dafa kan Abdul ya ce "Allah ya baku ikon haƙuri da juriya da kai da ita Allah ya haɗa kowa da rabon sa na alkairi, katashi ka koma sashin ka ka daina kuka domin kuwa kukan ka yana karyar min da zuciya" bai ce ko mai ba sai aikin kuka da yake babu ƙaƙƙautawa jiki a mace Uncle ya nufi ƙofa, *Ga wata Muhimmiyar Sanarwa, Ku daure ku tsaya ku karanta* *Assalamu-alaikum Masoyana kowa da kowa Barka da Warhaka. *Na zo muku da Kyakkyawan Albishir Me Matuƙar Muhimmanci. Shahararren Business Center Ɗinnan da ku ka sani me Suna HALYJASHERU Sun yi muku gwaggwaɓan Tanadi na Kyawawan Kaya Masu Kyau ga Rahusa, ina Farin cikin Sanar da ku Cewa Ku Garzaya HALYJASHERU Ku Ƙulla Kasuwanci da su Za ku yi Matuƙar Farin ciki.* *HALY-JASHERU venture's* *munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba Algus da ha'inchi kayanmu daga Ethiopian ne.* *prdct dinmu, muna Ethiopian MAGIC HAIR OIL, ANTI DANDRUFF SHAMPOO, SERUM BODY CREAM, HAND CREAM.* *Da Magungunan chututtuka Kala Daban-Daban, Da Magunguna Na SIRRIN MATA Masu Matuƙar Kyau da Iganci Gami da Kara Lafiya ajikin Ɗan Adam.* *HALY-JASHERU CENTER Ba mu tsaya iya haka ba, Muna Da Distributor a Ko Ina a Fadin Ƙasarnan Har ma da ta Ƙetare Domin Kuwa abin ba na Wasa Bane, Domin Tallafawa Ƴan Uwanmu Muka Ware Aji na Koyar da Harkokin Kasuwncinmu ga Masu Buƙata, a kan Naira 3000 kawai Muke Koyar da Wannan Sana'o'i Domin Temakon Al'uma, Da Fatan kun yi farin ciki da hakan domin Mu Farin Cikin Costomers Shine Namu. Ku Tuntuɓi C.E.O Ta Wannan Lamba 07046665338 ko 07061664264 INA GAISUWA GAMI DA GODIYA MASOYANA* Abdul kuwa yana wajen ya kasa koda motsa ɗan yatsan sa ɗaya ne da nufin tashi" baya jin zai iya rayuwa gani yake tamkar numfashin sa a duniya ya zo ƙarshe, ya daɗe a haka kafin ya tashi jiri ne ya fara ibarsa, yayi saurin dafa kujera yana wani numfashi sama-sama cikin hanzari da tashin hankali Ummi ta nufo wajen da gudu tana ƙarasowa ya ɗaga mata hannun sa dake rawa, Alamar da katar wa, tsayawa tayi cakkk kamar wadda a ka riƙe, Nana Kadija ce ta nufo wajen tana kuka, hannu ta miƙa mai ya kama, ta jashi suka bar wajen da ido Ummi ta bisu cikin tashin hankali, ta rasa abinyi hakan yasa ta juya gudu-dugu sauri-sauri tanufi inda Dadda yaka Aaminat kuwa wannan furicin ne yake mata yawo aka yazama dole karabu da ita, ta kasa zaune ta kasa tsaye sai zarya take haka kawai zuciyar ta, ke raya mata Abdul yana cikin tashin hankali hakan yasa hankalin ta ya ƙara tashi ko tsakar gida ta kasa fita tana ɗaki kuka kam tayi ta gaji kanta har ya fara ciwo "maiyasa duk wanda ya shiga rayuwa ta saiya haɗu da ƙalubale dama gidan su Abdul basa ƙauna ta" wannan tambayar take yiwa kanta saidai bata da amsoshin su hakan yasa ta koma ta kwanta tayi lamo tana jiran Siyama ko Umaima su leƙota, Yarima yana zaune a office wayar sa ta fara ringin da sauri ya ɗauka don gani mai kira sunan Abdulkareem ne ta fito a kan wayar jiki a sanyaye ya kara a kunnan sa tare da sallama "salamu'alaika" "kana ina??!! muyar Kadija ta daki dodon kunnan sa, ya ce "lafiya??? ina Abdul ɗin??!" murya a cunkushe ta ce "tambayar ka nayi kana ina??!!" "ina Asibiti" "to ka hanzarta zuwa gidan mu" tana gama faɗin haka ta katse kiran, sororo Yarima yayi ya kasa gaba ya kasa baya "mai yake faruwa" ya furta a fili zimbur ya tashi cikin hanzari ya fice daga office ɗin ya nufi ma'ajiyar motar sa yana zuwa bai jira komaiba ya faɗa motar ya jata a guje, ya bar Asibitin, Ummi ta sanar da Ddda abinda ke faruwa murmusawa yayi gami da cewa "ki ƙele sa zaiyi zai gama" sakin baki tayi tana kallon Dadda, shi kuwa ya harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya yana karatun jaridar sa, juyawa tayi zata tafi yayi saurin cewa "zoki zauna" babu musu ta koma ta zauna, hankalin ta yana kan Abdul saidai babu yadda zatayi ya zama dole su hane sa da abinda yake shirinyi, Yarima yana zuwa yayi parking kai tsaye ya nufi ƙofar da zata sada sa da sashin Abdul, yana tafe yana tunane-tunane ya saƙa wancan ya warware wannan har ya ƙarasa ɗan ta ƙaitacan Falon, rasss rasss gaban sa yayi wata mummunar faɗuwa ganin Abdul a dur ƙushe a wajen, cikin hanzari ya ƙarasa wajen ya ɗaga Abdul yana cewa "Abdul mai yake faruwa" cikin sarƙaƙƙiyar muyar sa ya ce "Abubakar taimoko zakayi mini a karo nabiyu" "taimako??" ya maimai ta cikin sigar tambaya, baki na rawa Abdul ya ce "ka taimaka mini ka Auri Aaminat" zindummmmm!!!!!!! gaban Abubakar ya yanke ya faɗi tare da zazzaro ido ya kalli Abdul, Abdulkareem ya ɗaga masa kai a lamar eh ©️INDO &&& Salma Autar Jarumai [7/26, 2:46 PM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga MIKIYA WRITER'S Association Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S Association Shafi 22 Aruɗe Yarima ya ce "Abdul anya kuwa kaine??, ka kuwa san mai kake faɗi??!!!" rintse ido yayi yana jin zuciyar sa tana wata muguwar ta fasa kamar zata fasa ƙirjin sa ta fito waje, dafe kai yayi tare da sakin yarima ya tafi taga-taga zai faɗi cikin zafin nama da hanzari Yarima ya riƙo Abdul, zaunar da shi yayi a kujera sannan ya nufi firji ya ɗauko ruwa mai sanyi, ya buɗe gorar ruwan sannan ya kafa a bakin Abdul, kamar magani haka yake jin ruwan, saida ya sha ruwan sannan kuma ya fara sauke ajiyar zuciya, Abubakar kuwa hankalin sa yayi mugun tashi, cikin wata iriyar murya Abdul ya ce "Abubakar kai kaɗai ne zaka iya taimaka mini ka Auri Aaminat, dan kuwa a yanzu bani da halin Aurenta kuma mahaifin ta zai iya Aura mata duk wanda ran sa yaso hakan kuma zai cutar min da ita!!!" ya ƙarasa maganar cikin marai-raicewa, "A'a bazan iya Auren Aaminat ba Abdul" hawaye sai zarya suke a fuskar Abdul yayi murmushe mai cike da bayyanar da ciwo, ya ce "Yarima kaima bazaka iya Auren (BAZAWARA) ba ko " girgiza kai yayi ya ce "A'a bawai bazan iya Auren bazawara ba, Abdul ka na son Aaminat fa, ni zan temaka maka ka aureta a kowane hali, don Allah kar ka ce min ka haƙura zan yi maka komai, idan na aureta gani nake kamar na ci amanarka" Ya ƙarasa maganar ya na goge hawayen da suka fara sauka kan kumatunsa. wani murmushi yayi mai cike da raɗaɗi, ya ce "hakan ba yana nufin kaci Amanata bane, ni fa musulmi ne don me ba zan iya yin tawakkali ba? ba na son saɓawa iyayena don haka na haƙura da ita, duk son da nake mata iyayena sun fi ta muhimmanci a gurina; ba abinda nake so gareta wanda ya wuce in ganta cikin farin ciki in cireta daga cikin ƙunci, kuma na san za ka iya, ka yi min alƙawari za ka yi don Allah ba tare da tunanin wani abu ba" Yarima ya ce " na san da hakan kuma hakan ya na da kyau, amma ta ya zan iya Auren Aaminat bayan kai take so?? kuma kai ma ita kake so No bazan iya hakan ba," zamewa yayi daga kan kujerar da yake a kai ya zuba guiwoyin sa a ƙasa sannan ya dubi Yarima ya ce "na roƙeka ka tausaya mini ka taimaki baiwar Allahn nan Aaminat badan ni ba dan girman Allah ka Aureta koda zuciyar ka bata so," zuwa yanzu ƙafafuwan Yarima sun gaza ɗaukar sa hakan yasa shima ya durƙushe a gaban Abdul yana wani irin kuka mai taɓa zuciyar me saurarensa, dakyar Abdul ya iya fizgo muryar sa ya ce "Yarima ka aminta zaka Aure ta??????!!!!!!" cikin kuka Yarima ya ce "tabbass a da na so ta amma yanzu sam banajin zan iya rayuwa da Aaminat" Abdulkareem ya girgiza kai ya ce "Abubakar kaifa Aminina ne,, kai kaɗai ne zaka iya taimako na dani da Aaminat ka tausaya mata" Shiru ya yi ya na tunani har na tsawon wani lokaci sannan ya ja numfashi ya sauke sannan ya ce "na aminta zan Auri Aaminat don farin cikin ka" taune gefen leɓensa yayi sannan daga harshe da ƙyar ya ce "kayi mini alƙawarin bazaka taɓa bari Aaminat tayi kuka akan komai ba ka yi min alƙawarin za ka yi mata kowane irin gata" Yarima ya ce "zanyi ƙoƙarin cika maka burinka" wata zazzafar a jiyar zuciya ya saki sannan ya miƙe da niyar shiga bedroom ɗin sa, Yarima ya kalle sa cike da tausayawa, tabbas Abdulkareem yana cikin wani halin na rayuwa ko mutuwa, duk wani mai imani yaga yadda Abdul ya koma tamkar zautacce saiya tausaya masa, tashi Yarima yayi ya nufi inda ya Ajiye motar sa yana tafiya yana haɗa hanya tamkar wanda yasha giya, Abdul kuwa yana shiga bedroom ɗinsa ya faɗa kan gado yana wani irin matsanancin kuka mai tsuma zuciyar duk wani ɗan Adam me imani, ya daɗe yana kuka kafin ya tashi, da jan ƙafa ya shiga toilet ɗin dake ɗakin, ruwa ya watsa ya fito zama yayi a gefen makeken gadon sa tare da riƙe goshin sa, wata farar takarda ya ɗakko tare da biro, ya runtse ido yana kiran sunan Allah, rubutun ya fara, ya nayi yana kuka hakan yasa ƙwallar sa ke zuba kan ta kardar saida ya kammala rubutun sannan ya lankafe ta ya ajiye a gefen sa, wata ta kardar ya ɗauka yayi rubutu sannan ya ajeta agefe ita ma. *Ga wata Muhimmiyar Sanarwa, Ku daure ku tsaya ku karanta* *Assalamu-alaikum Masoyana kowa da kowa Barka da Warhaka. *Na zo muku da Kyakkyawan Albishir Me Matuƙar Muhimmanci. Shahararren Business Center Ɗinnan da ku ka sani me Suna HALYJASHERU Sun yi muku gwaggwaɓan Tanadi na Kyawawan Kaya Masu Kyau ga Rahusa, ina Farin cikin Sanar da ku Cewa Ku Garzaya HALYJASHERU Ku Ƙulla Kasuwanci da su Za ku yi Matuƙar Farin ciki.* *HALY-JASHERU venture's* *munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba Algus da ha'inchi kayanmu daga Ethiopian ne.* *prdct dinmu, muna Ethiopian MAGIC HAIR OIL, ANTI DANDRUFF SHAMPOO, SERUM BODY CREAM, HAND CREAM.* *Da Magungunan chututtuka Kala Daban-Daban, Da Magunguna Na SIRRIN MATA Masu Matuƙar Kyau da Iganci Gami da Kara Lafiya ajikin Ɗan Adam.* *HALY-JASHERU CENTER Ba mu tsaya iya haka ba, Muna Da Distributor a Ko Ina a Fadin Ƙasarnan Har ma da ta Ƙetare Domin Kuwa abin ba na Wasa Bane, Domin Tallafawa Ƴan Uwanmu Muka Ware Aji na Koyar da Harkokin Kasuwncinmu ga Masu Buƙata, a kan Naira 3000 kawai Muke Koyar da Wannan Sana'o'i Domin Temakon Al'uma, Da Fatan kun yi farin ciki da hakan domin Mu Farin Cikin Costomers Shine Namu. Ku Tuntuɓi C.E.O Ta Wannan Lamba 07046665338 ko 07061664264 INA GAISUWA GAMI DA GODIYA MASOYANA* Kadija ce ta shigo ɗakin da ka ganta kasan taci kuka har ta gaji zama tayi a kujerar da ke kusa da gadon, murya a cunkushe ta ce "ya Abdul dan Allah ka daina sakanka cikin damuwa ai kin gama ya riga ya gama sai haƙuri ka fauwala wa Allah, ka kai kukan ka ga Allah" bai ce ko mai ba ya bita da kallo, hannu yasa ya ɗauko takardar da yayi rubutu sannan ya miƙa mata ya ce "ki kaiwa Walid ya kaiwa Aaminat" hannu tasa ta karɓe ya miƙo mata ɗayar ya ce "ki aje a inda su Dadda zasu gani" "to" tace tana bin sa da kallon tausayi, tashi yayi ya fara takawa ɗaya bayan ɗaya sanna ya tsaya batare da ya juyo ba, ya ce "SAI ABINDA ALLAH YAYI" rasss raaass gaban ta ya yanke ya faɗi cikin tashin hankali ta ce "ina zaka???!!!! bana so murasa ka" tafiya ya cigaba dayi ta shiga roƙon sa ya faɗa mata inda zaije batare da ya tsaya ba ya ce "India" wani kuka ta saki, tana so ta dakatar da shi sai dai bata da dama, tanaji tana gani ya ɓacewa ganin ta, Da taimakon Allah Abubakar ya isa gida ya daɗe a mota yana aikin kuka kafin ya fito kai tsaye ya nufi sashin sa, kayan jikin sa ya rage sannan ya watsa ruwa ya fito, komawa yayi ya zauna tare da runtse ido, Anti Zainab ce ta shigo ɗakin da sallama, ciki-ciki ya amsa, ta ƙaraso hannun ta ɗauke da filet da abinci zama tayi gefen gado gami da cewa "mijin E'iye lafiya kuwa naga kamar kayi kuka kuma ba kaɗan ba???!" bai ko kalli inda take ba ya ce "babu buƙatar Abinci ki koma da shi" sakin baki tayi sakaka tana kallon sa, tunda take agidan bai taɓa faɗa mata magana irin wannan ba ko makamancin ta, ganin bata da niyar tafiya yasa ya ce "dan Allah Anti kiyi haƙuri ki tafi" zaro ido tayi ta kalle sa ta ce "babu inda zani sai naji ko mai yasa ka kuka" tabbass yau da ba Antin sa bace da sai ya lakaɗa mata duka, "dan Allah ka faɗa min kasani ko nataya ka nemo mafita????" bai ce mata komai ba, taci gaba da magiya, da naci, hakan yasa ya zaiyane mata komai tundaga farko har izuwa ƙarshe, ta tausaya wa Abdul jikin ta yayi sanyi ƙalau hada matse ƴar ƙwalla, ta ce "Abubakar ina ganin ka taimake sa ka Aure ta dan Allah" rausayar da kai yayi ya ce bazan iya zama da wadda Aminina ya fiso a duniya ba" murmusawa tayi ta ce "kenan bazaka iya taimaka masa ba aduk halinda yake ba???" shiru yayi ta ce "zan sanarwa Abi yaje suyi magana da mahaifin ta" bai ce komai ba ya bita da idanu, tashi tayi gami da cewa "kaci Abincin nan ko kaɗan ne" wani mugun kallo ya maka mata, tayi saurin da wowa ta kinkimi Abincin tayi waje kuyi haƙuri babu yawa A A &&& Auta [7/26, 3:03 PM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION Shafi 23 Abdulkareem bai jima da fita ba Kadija ta kaiwa Walid takardar da yace ta kaimasa ya kaiwa Aaminat Aaminat tana zaune A ɗaki jikinta yayi sanyi salam ta zabga uban tagumi Walid yayi sallama amsawa tayi, Walid yace "gashi inji Guda yace abaki!" rasss gabanta yafaɗi, karɓa tayi tace "Walid wani abunne ya faru ko???" jiki a sanyaye ya ce "nima ban sani ba amma ɗazu Abdulkareem yazo yayi mana sallama yace zai nesanta kansa da gida", juyawa yayi ya fita daga ɗakin Aaminat kuwa ta riga ta gama saduda ta sallama , dama tunda taji mugun firicin Abdussalam ta saduda, warware takardar tayi ta fara karantawa kamar haka Assalamu'alaiki, fatan alkairi gareki, Aaminat kiyi haƙuri ki ɗauki ƙaddara haka Allah ya rubuta ni ba mijinki bane, Mahaifina yace bai amince na Aureki ba, amma dan Allah na roƙeki ki taimaki rayuwata ki Auri Aminina Abubakar zai kula dake tamkar yadda zan kula dake, ina son ki Amma ƙaddara ta gifta tsakanin mu, ina cikin wani mugun hali ki tayani da addu'a ina miki fatan alkairi tare da farinciki na tsawon rayuwarki. tuni hawaye sun wanke mata fuska, da sauri ta ɗauki waya ta kara akunne bugu ɗaya aka ɗauka, cikin muryar kuka da tashin hankali, ta ce "me...meyasa zaka barni alokacin da nake tsaka da buƙatar rayuwa da kai wallahi ina sonka" ƙit ya katse kiran sai a lokacin zafafan hawayen da suka cika ƙwarmin idon sa, suka sami damar sakkowa, ƙasa yayi da kai yana ambaton sunan Allah don samawa kansa sauki. zuwa yanzu Aaminat ta gama fita hayyacinta kuka take mai tsuma zuciya Umma da Umaima kuwa sai faman rarrashin ta suke, Umma tace "kiyi haƙuri ki ɗauki ƙaddara haka Allah yaso daku" haka suka cigaba da rarrashin ta, Mama da Fati kuwa ransu fafess sai nishaɗi suke suna ɓaɓɓaka dariya Mama ta kalli Fati kana ta ce "ni dama banaso ahaɗa bikinki da na Bazawarar can wallhi, sai gashi saurayin ma ya fece" dariya suka sa hada shewa, Abi ne zaune a Falon Anti Zainab, Yarima ya shigo kai aƙasa, zama yayi kusa da Anti Zainab gami da cewa "barkan ku da dare " Abi ya ce "yauwa" Anti Zainab ta muskuta gami da cewa "Abi dama tun ɗazu nakeso zamuyi magana da kai" ya ce "to ina jinki" "dama batu ne akan Abdulkareem" Abi ya murmusa sannan ya ce "Abdulkareem yayi mini bayanin komai gaskiya abinda Aminina yayi bai kyauta ba, banji daɗi ba," Anti ta ce "to ya za'ayi sai haƙuri nima ya bani tausayi wallhi" tashi Yarima yayi, Abi ya dakatar dashi ta hanyar cewa "zo mana Abubakar" dawowa yayi ya zauna, Abi ya ce "Abdul ya roƙeni na taimaka masa na nema maka Auren Aaminat domin yana ganin zaka iya maye gurbin sa arayuwarta" ƙasa yayi da kai, Abi ya ƙara da cewa "kuma na yanke hukunci zuwa jibi iyayanka su Alhaji Kabiru zasuje gidan su yarinyar saika faɗa mata ta sanar da mahaifin ta" cikin rawar murya ya ce "to" ya tashi ya nufi sashin Ammi, Washegari da safe ahankali Dadda yake sakkowa daga benen dake tsakiyar Falon gaban sa ne yayi wata muguwar faɗuwa ganin hawaye shaɓe-shaɓe afuskarta, da sauri ya ƙarasa inda take sai alokacin ya lura da takardar dake riƙe ahannun ta, hannu yasa ya karɓi takardar sannan ya zauna kan kujera ya fara karantawa, kamar haka "Salam Daddana da Ummina, tabbas ban taɓa zaton haka daga gareku ba, nayi tunanin zaku iya cika duk wani buri na ɗanku ashe ba haka bane, dama ƙaunar da kukemin ba har cikin zuciyar ku bace???? Uhmmm ban taɓa tsammanin hakan ba, nayanke hukuncin nesan ta kaina daku, nabar ku lafiya" wata zazzafar iska Dadda ya furzar cikin dakakkiyar muryar sa ta jajirtaccen Uban da ya amsa suna Uba, ya ce "kar hakan ya dameki kuma hakan ba zaisa na sauya ra'ayi na ba" yana gama faɗin haka ya juya zuciyarsa na wani mugun tar tsatsin azaba tabbass a zahiri bazaka taɓa iya gane iya tashin hankalin da Dadda ya shiga ba, a baɗini kuwa zaka iya cewa yafi kowa shiga tashin hankali dan kuwa tafiya yake a harabar gidan amma baisan inda yake jefa ƙafarsa ba, *Ga wata Muhimmiyar Sanarwa, Ku daure ku tsaya ku karanta* *Assalamu-alaikum Masoyana kowa da kowa Barka da Warhaka. *Na zo muku da Kyakkyawan Albishir Me Matuƙar Muhimmanci. Shahararren Business Center Ɗinnan da ku ka sani me Suna HALYJASHERU Sun yi muku gwaggwaɓan Tanadi na Kyawawan Kaya Masu Kyau ga Rahusa, ina Farin cikin Sanar da ku Cewa Ku Garzaya HALYJASHERU Ku Ƙulla Kasuwanci da su Za ku yi Matuƙar Farin ciki.* *HALY-JASHERU venture's* *munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba Algus da ha'inchi kayanmu daga Ethiopian ne.* *prdct dinmu, muna Ethiopian MAGIC HAIR OIL, ANTI DANDRUFF SHAMPOO, SERUM BODY CREAM, HAND CREAM.* *Da Magungunan chututtuka Kala Daban-Daban, Da Magunguna Na SIRRIN MATA Masu Matuƙar Kyau da Iganci Gami da Kara Lafiya ajikin Ɗan Adam.* *HALY-JASHERU CENTER Ba mu tsaya iya haka ba, Muna Da Distributor a Ko Ina a Fadin Ƙasarnan Har ma da ta Ƙetare Domin Kuwa abin ba na Wasa Bane, Domin Tallafawa Ƴan Uwanmu Muka Ware Aji na Koyar da Harkokin Kasuwncinmu ga Masu Buƙata, a kan Naira 3000 kawai Muke Koyar da Wannan Sana'o'i Domin Temakon Al'uma, Da Fatan kun yi farin ciki da hakan domin Mu Farin Cikin Costomers Shine Namu. Ku Tuntuɓi C.E.O Ta Wannan Lamba 07046665338 ko 07061664264 INA GAISUWA GAMI DA GODIYA MASOYANA* su Abdussalam suma suna ɗaki suna nasu zaman makokin, babu mai iya cewa ɗan uwan sa ƙala saidai kallon kallo su Farida kuwa sunyi kuka mai isarsu sun gaji, Kadija kam tun daren jiya ta haɗa kayan ta tsaf ta koma gidan Uncle Rabi'u, "Aaminat ki daure kici abincin nan, ki fauwala wa Allah komai" Umma ta faɗa cike da damuwa, Umaima kuwa tana gefen Aaminat ita da Siyama sun zabga tagumi sai muzurai suke, haka kowa ne gida suka wuni cikin baƙinciki, Bayan kwana biyu su Alhaji Kabiru da Baba Usman sukaje gidan su Aaminat suka gana da mahaifinta da ƙaninsa Baba Auwalu, cikin kamala suka bawa Yarima Auren Aaminat, Haka rayuwa ta cigaba da garawa a kowane ɓangare. Gidan su Abdulkareem kuwa har zuwa yanzu babu wanda yasan inda Abdul yake agidan sai Kadija ita kuma tayi musu ƙaura daga gidan Alhaji Aminu kuwa yayi cigiyar yayi neman amma shuru, Yau ta kasance ranar lahadi saura sati ɗaya bikin Aaminat da Abubakar (Yarima) Ammi tana zaune a falon ta ta zabga ta gumi, Yarima yayi sallma, zama yayi kusa da ita gami da cewa "Ammi lafiya kuwa???, naga kwana biyu bakya walwala" hawaye ne suka fara shatata tayi saurin kauda kai, "Ammi meke faruwa haka dan Allah ki daina kuka banason ganin kukan ki," cikin muryar kuka ta ce "mahaifinka ya juya min baya sam ya daina saurara ta ko magana nayi masa baya kulani rabon da yazo sashina har na manta kullum sainayi kuka mai isa ta" ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kama hannunta ya ce "Abi yace mini ba zai iya zama da wadda bata ƙaunar iyayansa ba, shine dalilinsa na juya miki baya" hawaye ta sharen gami da cewa "Allah natuba kayafeni wallhi duk zigar su Hajiya Bilki ce suka ce karna bi iyayan mijina wai E'iya ta fiye tsugudidi da munafurci ga masifa, sun cuceni gashi sun rabani da miji na" ta ƙarasa maganar tana kuka Abubakar yasa hannu ya share mata hawayen sannan ya ce "tunda Allah ya ganar dake gaskiya ina ganin kije ki nemi yafiyar su mahaifiyar tasa daganan saiki faɗa musu abinda yake faruwa tsakanin ku da Abi ɗin zasuyi masa faɗa kuma zai ɗauka, banda abinki dama Amma kema fa uwa ce idan na yi Aure matata ta tsaneki kamar yadda ki ka tsani su E'iya nasan ke ba ma za ki iya haƙura ba" rausayar da kai tayi ta ce "Ai Ƙaddara ce yaro, ni bansan hakan kuskure bane, kana ganin su Hajiya E'iye zasu yafemin abinda nayi musu harfa kiransu nake da mayu, kaicona nayi asara" ta ƙarasa maganar tana kuka mai ƙarfi, cikin ƙwarin guiwa Abubakar ya ce "zasu yafe miki in sha Allah, ki shirya na kaiki gidan" "to" tace cike da tararradin zasu karɓeta ko kuwa, bata ɓata lokaci ba ta shirya tsaf suka ɗauki hanyar gidan su E'iye cikin mintina ƙalilan suka ƙarasa gidan Yarima yayi gaba Ammi na biye da bayan sa kai tsaye sashin E'iye suka nufa E'iye da Inni suna zaune a Falo sukaji sallama, fuska babu yabo babu fallasa Inni ta amsa, Abubakar ya ce "yadai Budurwas naga kin wani haɗe fuska" zumɓura baki tayi ta ce "naga ka shigo mana da baƙuwar fuska ne" murmusawa yayi ya ce "Ammi ce tazo ta naimi yafiyar ku" Ammi kuwa kanta yana ƙasa sai sharar ƙwalla take, Abubakar ya ce "ni bari naje wajen su Huzaifa" Ammi ta zauna murya na rawa tace "dan Allah ku yafe mini na tafka babban kuskure da ban ɗaukeku da daraja ba, dan Allah ku gafarce ni badanni ba dan Allah na roƙeku" ajiyar zuciya E'iye ta sauke a ranta ta ce Alhamdulillah Allah kaine abin godiya, Inni kuwa tashi tayi zata bar wajen, Ammi tayi saurin durƙushewa agaban ta ce "dan Allah ba danni ba ku yafemin dan girman Allah" E'iye ta ce "nayafe miki Allah ya yafe mana baki ɗaya" Inni ta sake ajiyar zciya ta ce "nima na yafe miki kinji ai ɗa na kowa ne, ina fatan Allah i shiryi duk masu irin halinki" Ammi bata san lokacin da ta fara murmushin farin ciki ba, ta ce "Na gode Allah i saka da Alkairi.... Indo and Autar Jarumai [8/1, 1:28 PM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION Shafi 24 E'iye ta ce "ya zaman gidan naku komai lafiya ko!???" da sauri Ammi ta girgiza kai ta ce "da sauki dai, Abi ya juyamin baya yanzu ko magana bata haɗani da shi sai kallo amma karku ga laifinsa nice da laifi dan kuwa mugun halina ne ya ja mini" E'iye ta ce "sabhanallahi mekikayi masa har haka!??" murya ƙasa-ƙasa ta ce "rashinyi muku biyayya ne kuma yanzu na gane kuskure na wallhi nayi nadamar abinda na aikata, duk nice silar rabuwar Abubakar da ƴar uwarsa, nidai banyi dacan hali ba" cike da manyance E'iye ta ce "kinga dama haka duniya take abinda ka shuka shi zaka girba, ko akan Abubakar zaki gane Allah ɗaya ne, tun yana goye yake ƙaunar mu har ya girma kinsha jifanmu da munanan kalamai, amma yanzu komai ya wuce, zankira Alhaji Saadiƙ ɗin" ta ƙarasa maganar tana ɗaukar wayar ta ta dannawa kira Abi bugu biyu ya ɗauka, cike da girmamawa yayi sallama, ko amsawa batayi ba ta ce "ka hanzarta zuwa ina nemanka" rasss gaban sa ya faɗi cikin rawar murya ya ce "lafiya kuwa" "inkazo kaji" ta faɗa tana sauke wayar, bayan ɗan wani lokaci Abi ya ƙaraso gidan kai tsaye yayi ɓangaren E'iye, sallama yayi a Falon turusss yayi ganin Hajiya Hafsa tayi muzu-muzu gaida su Inni, yayi rai a ɓace ya kalli Ammi ya ce "meya kawoki gidanmu kokinzo ki haddasa mana fitina agida???? to kisani makircinki babu inda zaije"... numfashi yaja ya cigaba da cewa "idan kin manta ni ban manta ba, lokacin da sukaje gidanki kikasa akayi musu korar kaji kikace ke baki sansu ba, dama zama kawai nakeyi dake amma yanzu zamanki yaƙare agi...." "ka dakata karka yanke hukunci cikin fushi" muryar Inni ta dakatar dashi E'iye ta ce "bawai nakiraka bane dan ka dawoda bara bana ba, nakirakane domin inaso ka daina abinda kake ka ka koma ga iyalinka, indai akanmune ka fita shirgin matarka to kakoma, ta nemi yafiyarmu kuma munyafe mata, saura kai" ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa "tinda kun yafe mata nima na yafe mata Allah ya yafe mana baki ɗaya, kuma darajarku da ta ɗanta ta ci" suka amsa da amin, shurune ya ɗan ratsa na wani lokaci kafin Abi ya ce "nizan koma sai anjima zan dawo" Inni ta ce "to Allah ya kaimu anjiman, nima zan fita nayo siye-siye kar naje Amarya tafini kyau" dariya sukayi Abi ya tashi E'iye ta ce "ai bamu gama magana ba" komawa yayi ya zauna, ta ce "inason da kaida Hafsa ku haɗa kan ƴaƴanku da yarabe" Inni ta ce "gaskiya dai yakamata wannan gabar da take tsakanin su tazo ƙarshe" "to in sha Allahu zamuyi hakan, Allah ya saka da alkairi," kallon Hajiya Hafsa yayi ya ce kikira Rahina kice ina nemanta yau ɗinnan," cikin jin daɗi Ammi ta ce "to" sallama yayi musu sannan ya fita," Yarima ne ya shigo Falon yana tafe yana haɗa hanya Inni ta ce "saurayin ya dai naga kamar bakajin daɗi" zama yayi gami da cewa "kin fiya ƙaga min cuta banace muku Dr baya rashin lafiya ba???" E'iye ta maka masa harara gami da cewa "shiyasa naga ai Dr kullum sai yayi kuka," dariya yayi ya ce "to su E'iye kinshin ya motsa" badole ya motsa ba zakayi mini kishiya kuma kace dagani ka gama Aure" Haba uwar gida nimafa ba ason raina zan miki kishiya ba" dariya suka sa, Ammi cikin raita ta ce "dama haka suke gudanar da rayuwarsu nake ƙoƙarin shiga tsakanin su???" Inni ta muskuta gami da cewa "ai tare zaka Aure mu nagaji da zaman budurci" dariya sukayi suka cigaba da hirarsu cin farinciki, "Wai a haka za'a kaiki gidan mijin ko gyara babu" Siyama ta faɗa Aaminat ta ce "gyaranme zanyi" "Au bazakiyi ba kenan" Aaminat ta murmusa ta ce aini agyare nake koda yaushe" dariya Siyama tayi ta ce "kyajidashi dai" Umaima ta ce "Siyama gobe fa zamuje rabon katin gaiyata" "Allah ya kaimu kowa a layinnan sai mun bashi," "kedai bari har maƙiya sai mun gaiyata wallhi ɗazu ma naje fagge wajen mai ɗinki na karɓo" Aaminat ta ce wai ku baku da aiki saina zancan wani biki can" "iyeeee lallai to kokina so ko bakya so sai mun cashee" Siyama ta faɗa tana murguɗa baki Aaminat ta bita da kallo, "Siyama nifa da sosamu ne wallhi da gobe zan fara shagali" Siyama ta ce "to uwar zumuɗi" dariya sukayi, Aaminat ta ce "dan Allah ku bani katin nan na bawa su Bilal" Siyama ta ce "taɓ ai'dasu ake komai suma zasuyi tasu gaiyatar, sune ƴan shigo da Amarya fa" ɗigimi wai shigo da Amarya saikace wata mage" "kinga sai wani babbasarwa kike munfa san komai wallhi" "mekuka sani???, ƴar rainin hankali kawai" Umaima ta ce "ba saikinji ba" "to karku faɗa" dariya sukasa, Aaminat ta ce "wallhi ko kwana biyu tinanin Abdulkareem kawai nake" "Allah sarki rayuwa ɗazu naga ƙanwarsa Farida" Aaminat ta tayi murmushi mai tafe da hawaye, "kinga matsalata dake komai kuka saikace wata kaza" Aaminat ta ce "ina tunanin halinda Abdulkareem yake ciki ko yana ina???" Umaima ta rausayar da kai gami da cewa "haba yaya Aaminat ki daina damuwa na san yasan ankusa bikinku kuma inaga yana nan yana farinciki dan kuwa shi rayuwarda kike ce baya so kuma ai Amininsa ne zai Aureki kuma shiya nemi haka" ƙwalla ta share ta ce "Allah ya bamu haƙuri da dangana," suka amsa da Ameen,, Abi Ammi Anti zaina Rahina Abubakar zaune suke a babban Falo. Cikin nasiha Abi ya ce "ke Rahina na kira ki ne akan tsakaninki da ɗan uwanki daga yau sai yau karki kuskura na ƙara ganin kina nunawa ɗan uwanki ƙiyayya, idan baki riƙeshi da daraja ba wazai riƙe miki ɗan uwa kin kuwa san irin baƙin cikin da nakeji idan naga kina nunawa ɗan uwanki ƙiyayya????! babu dare babu rana addu'a nake Allah ya haɗa min kanku Amma ke ce babba kuma kece babbar banza ciki ɗaya amma ace baki da maƙiyi sai wanda kuke uwa ɗaya uba ɗaya anya kuwa kina da hankali????!" Yarima kuwa banda sharar hawaye babu abinda yake, kansa na ƙasa, Ammi ta ce "duniya abin tsoro wata rana in mune wata ranar bamu bane, yanzu itace damarki ki gyara kusakuren ki" "kin kuwa san waye yayi nasarar ceto rayuwarki lokacinda kikayi hatsari???, to ɗan uwanki ne wanda kika ɗauka maƙiyinki, shi ko da yaushe ƙaunarki yake, amma kallon da kike masa daban, sau da yawa ba tare da kin sani ba shi ke temaka miki, wai me ya yi miki ne haka?" da sauri ta ɗago suka haɗa ido da Abubakar yayi saurin yin ƙasa da kai yana goge ƙwalla, itama maida kai ta yi ƙasa ta kasa cewa komai, jikinta ya yi mugun sanyi, Ammi ta ce "Wallahi Rahina da ni da ke duk duniya ce take ruɗarmu, amma ko iya abinda ki ka yiwa Abubakar ba ki yi nasara akansa ba su kaɗai sun isa ishara, bai yi miki laifin komai ba, kuma duk nice na fara nuna miki hakan sabida shi yana nunawa kakanninsa ƙauna ki nemi yafiyarsa don Allah" ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka, Anti ta ce "rashin sanine, ki godewa Allah da ya ganar dake tin yanzu" cikin kuka Rahina ta ce "Abubakar ka yafemin dan Allah wallahi sharrin shaiɗan ne" cikin muryar kuka ya ce "yaya wallahi ni ban taɓa ƙullatarki ba kullum burina naga mun zauna inuwa ɗaya muna zumunci da juna" tashi tayi taje gaf dashi sannan ta durƙusa ta ce "ina neman yafiyar ka kayafe min duk abinda nayi maka" hannu yasa ya share mata hawayen sannan ya kalle ta ya ce "na yafe miki nima ki yafe min" cikin kuka ta ce "na yafe maka dukda bakayimin komai ba" Abi ya ce "Alhamdulillah Allah kaine abin godiya" Ammi kuwa murna take sosai sai sharar hawayen farin ciki take, Abi ya miƙe gami da cewa "lokacin sallah yayi" tashi suma sukayi kowa ya nufi inda zai ɗaura Alwala" INDO TARE DA AUTA [8/1, 1:28 PM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION Shafi 25 Yarima yana dawowa daga masallaci ya nufi ɗakin sa, zama yayi gefen gado ya zabga tagumi, wayar sa ce ta fara ruri da sauri ya ɗauka ya kara akunne, "salamu'alaikum" "likita bokan turai bakaso a mutu bakaso a zauna lafiya" dariya yayi ya ce "mai gaiya mai aiki sai dakai uban gida" dariya sukasa Abdulkareem ya ce "ya shirye-shirye???" "shiri kuma saikace wasu mata" "Au sannu maza" Yarima ya ce "sai yaushe zaka dawo ne, nifa nagaji da zuwa duba mutan gidanku" "dawowa kuma ai sai abinda Allah yayi idan kana son ganina ka zo inda nake" "kana nufin bazaka halacci wajen ɗaurin Auren ba!??" "eh bazan zoba idan nazo ai nadawo gida kenan kuma nasan Dadda zai halacci wajen" "dan Allah ka daure kazo wallahi bazanji daɗi ba in bakazo ba" "kana ruwa nace fa bazan zoba" Yarima ya rausayar da kai ya ce "wallahi mutan gidanku duk sun rame yaufa kwana uku Dadda baya fita bashi da lafiya" dariya Abdul yayi gami da cewa "zuwana ba zaisa Dad yaji sauƙi ba, dan ba danni ya kwanta rashin lafiya ba" "dan kaine kuwa Dadda babu inda baya neman ka amma ya kasa gano inda kake" Abdul yayi murmushi mai ciwo ya ce "Allah ya bashi lafiya kawai, ni yanzu Allah ya taimakeni na dawo cikin nutsuwa ta, kullum ai'kina karatun Alƙur'ani mai girma" "to Allah ya taya mana" daga haka sukayi sallama, Abdul ya ajiye wayar yana murmushi yanzu abu ɗaya ne ya rage masa, yaga ƴar uwarsa Kadija, "Fati wallahi ko banso Auren ki da waccan banzar yazo ɗaya ba" wani banzan murmushi Fati tayi ta kalli ƙawar ta Nafisa ta ce "kinsan kodame kurna tafi magarya ƴaƴa," "kuma kinsan wazata Aura??" Fati ta girgiza kai ta ce "koma waye nasan sai dai ya biyo bayan Ahmad, dan kuwa idan kuɗi ne Ahmad ya tara an tara masa," dariya suka yi gami da tafawa, "inaga ma bazawari ne ko mai mata" "to dama ai bazawara sai bazawari," "hahahaha" Nafisa tayi wata dariya kamar wata mahaukaciya, Fati ce ta tashi gami da cewa "zoki rakani gidan su ruma" "to" tace suka tashi suka nufi hanyar fita, "Ummi dan Allah ku dauwo mana da ɗan uwanmu yau kusan kwana ashirin da wani abu, ba muga Abdul ba" "kuyi haƙuri muna bamu san inda yake ba gashi yanzu hankalina kullum ƙara tashi yake nayi da nasani, yanzu bansan awana hali ɗana yake ba" Nana Farida ta share ƙwalla gami da cewa "laifinku ne keda Dad baku tsaya kun fahimtar da shiba nasan da kunjashi ajiki kun nuna masa bakuso ta sigar salama da duk haka bata faru ba" Ummi ta muskuta tare da rausaiyar da kai, Nana Hauwa, ta miƙe gami da cewa "Allah sarki rayuwa gashi ai kuna da nasani" Abdurrahim ne ya shigo Falon hakan yasa Hauwa komawa ta zauna" "sannu da hutawa Ummi" ya faɗa yana zama, Ummi ta ce "yawwa" "haryanzu dai babu labarin Abdul nifa nafi tunanin yabar india dan kuwa nayi neman na rasa shi" "shikenan su Dadda sun rabamu da ɗan uwan mu" Farida ta faɗa tana fashewa da kuka, Ummi kuwa ta kasa koda magana, Nana Hauwa ta ce "Allah ya baiyana shi aduk inda yake" suka amsa da "amin" Kadija zaune take a ɗan matsakaicin ɗakin su na gidan Uncle Rabi'u, waya ta ɗauka tare da danna kira bugu ɗaya ya ɗauka cikin jin daɗi da farinciki ya ce "Dijan gala yakike" dariya tayi gami da cewa "lafiya ƙalau wallahi" "za kizo ɗin" "eh ya Abdul in sha Allah da yammacin yau zan sauka a Abuja" "Allah ya kawoki lafiya amma idan kikazo kije gidan Anti Maryam zanzo nan ɗin" "kana ganin babu matsala idan Anti Maryam kazo, kuma zata iya faɗawa su Dadda" murmushi yayi kana ya ce "a tasani kuma bazata faɗa ba ɗazu ma naje gidan" "yaushe zaka koma" "Jibi kinsan dan naga ya kike nazo kuma da mun gaisa zan ɗaware" "to sai nazo ɗin yanzu ma na faɗawa Mami nace zani wajen Anti Maryam kuma kwana zanyi nace amma karta faɗawa su Ummi" "Allah ya kawoki lafiya" daga haka sukayi sallama cikin farinciki da annashuwa, "Abubakari kwandon sikari" Anti Zainab ta faɗa tana dariya "kai Anti dan Allah kidaina tsokana ta," zama ta yi akan ɗayar jujerarda ke kallon sa, ta na dariya ta ce "idan uwa bata tsokani ɗanta ba waye zai tsokane shi" dariya yayi gami da cewa "yaya ta tafi ne" Anti ta ce"A'a" Rahina ce ta shigo falon ta zauna Yarima ya ce "yanzu nake tambaya kin tafi" "A'a yanzu nakira Abban Kausar nace masa sai bayan Biki zamu dawo kuma ya amince" murmusawa yayi kana ya ce "Allah ya kaimu amma kun ɗiba da yawa kobaya ƙasar" "eh bayanan amma zai dawo ɗaurin Aure" murmushi yayi ya ce dakince ya barshi basai ya dawo ba" kallon sa tayi cikin jindaɗin yau gata ga ɗan uwanta suna magana, ta ce "ai dole ma yazo bikin fa ƙanina ake" sukayi dariya kana suka ci gaba da hira jefi-jefi don kuwa ba wani sabawa su ka yi ba" kiran sallar magrib Kadija ta sauka a tafkeken gidan babban yayansu Abdurrahman kai tsaye ta kutsa kai falo, tare da sallama, da gudu ƙaramar ƴarsu Islam ta taso ta rungume ta tana cewa "Oyoyo-Oyoyo" jin haka yasa Anti Maryam fitowa daga kicin ɗin dake falon, cikin murna da dariyar farinciki ta ce "sannu da zuwa ya hanya" "Alhamdulillah" Kadija ta faɗa tana zama kan ɗaya daka cikin kujerun Falon, waya ta ɗakko ta dannawa Abdul kira, yana ganin kiran ya ɗauka, cikin farinciki ya ce "ina harabar gidan yanzu zan shigo," "ok" maida kallon ta kan Anti Maryam tayi ta ce "ina wuni" dariya Anti Maryam tayi sosai ta ce "saida kika gama wayar" "Au wallahi na sha'afa burina naga ya ɗan uwa yake" sallama yayi yana cewa "yau gani ga tsigai dariya sukayi, ya kalli Khadija ya ce " Khadi ya hanya" "lafiya lau sai godiyar Allah" "nayi kewarku wallahi kewarku" kaidai bari harfa rashin lafiya nayi" "Allah kice ruwa ya daki babban zakara" "sosaima dan kuwa naji jiki" dariya suka sa Anti Meri kam sai faman kaiwa da komowa take ta cika gabansu da kayan alatu iri-iri, Abdul ya kurɓi shayi sannan ya kalli Anti ya ce "Anti kushirya fa kunkusa Aurar da Dije" "Ah haba dagaske waye sirikin namu" dariya yayi Kadija ta maka masa harara, ya ce "ai gaskiya ce tun ina gida nagane kuna soyewa da Omar" "kace sunan sa Omar" "eh mana kuma na bashi" tsaki Kadija taja ta ce "kowa yafaɗa maka ma oh'ho" "nina sani da kaina sau da yawa ina lura da lokacin da kike dawowa daga makaranta" "to kaji daɗi ai ka faɗa" "sosaima gashi har ƙiba nayi" dariya suka sa cike da farinciki,, har wajen shaɗaya suna aikin abu ɗaya, daga baya kowa ya nufi makwancin sa Abdul ma a gidan ya kwana kasancewar gidan babba ne. washe gari tunda safe Kadija ta kama hanyarta ta komawa gida, Abdul ma ya shrya yayi wa Anti Maryam sallama, da niya shima gobe zai tafi Qatar, Yau biki ya rage saura kwana uku ko wane ɓan gare shrye-shiye babu kama hannun yaro inda Anti wato maman su Siyama da ƴar Autar su Umma suka zage dantse wajen shirya Aaminat, Mama da ƙawar ta sun zage wajen ganin Bikin Fati yafi na Aaminat (Bazawara) inda suke shige da fice na ara aren bashika dan kuwa kashe kuɗi suke sosai, Ɓagaren su Anti Rahina ma shiri ake sosai wajen ganin sun tsara biki, Ya Omar ne zaune a ɗakin Umma ya zabga tagumi hannu bibiyu, sallamar Aaminat yaji hakan yasa ya ɗan saki fuska, ya amsa ƙarasowa tayi kusa dashi ta zauna, cikin nutsuwa da girmamawa ta ce "ya Omar anya kuwa ƙalau kake naga ka zabga tagumi ko bakajin daɗi" murmusawa yayi gami da cewa "karki damu ƙalau nake kawai banason hayaniya ne" "haka ne bakason hayaniya amma naga kamar yau kana cikin damuwa" "eh hakane ina cikin damuwa amma ki bar zancen kawai" "sabida me zakace nabar zancen" rintsa ido yayi kana ya ce "Aaminat banajin daɗin yadda Abba yake yiwa Umma" "nima abin yana damu na wallhi" Ya Omar ya ɗan ja numfashi tare da sauke ajiyar zuciya ya ce "karkiso kiji irin cin zarafin da Abba yayi wa Umma yau har zagin ta yayi kuma duk ta sanadin Mama ne" ya ƙarasa maganar kamar zai fashe da kuka, cikin rawar murya Aaminat ta ce "Allah Sarki, ai Allah yana kallo kuma zai saka mana" ta share hawaye sannan ta cigaba da cewa "ita rayuwa haka take kowa da tasa irin ƙaddarar," "Aaminat ina zamu saka kanmu Mama ta sako mu gaba, yanzu naji tana cewa Abba wai nima bin mata nake, haka kema tayi miki sharri tasa muka tsaneki" cikin kuka Aaminat ta ce "taje dan kanta Allah zai saka mana, kuma in Allah ya yarda kamar yadda tasamu a ƙunci itama saita shiga ƙunci da azaba ta duniya" Ya Omar ya ce "yanzu haka Abba yace bazai ƙara yi miki kayan ɗaki ba" Aaminat tayi murmushin takaici ta ce "wannan kuma dama bana buƙata suje suriƙe kayansu, ai muma Allah ya azirtamu dan kuwa Umma tana da masu yi mata ko babu komai nasan Baba Usman zaiyi mini" shurune ya ɗan ratsa kowa ya faɗa daniyar tunani, Umma ta shigo ɗakin da sallama, murya a dashe dagaji tasha kuka, Aaminat ce ta amsa, Umma ta zauna kan gadon ta sannan ta kalli su Omar ta ce "kutashi yaya Usman yazo zamu bishi" "zamu bishi kuma??" Omar ya maimaita cikin sigar tambaya Umma ta ɗaga masa kai alamar eh "maiyafaru Umma" Aaminat ta faɗa, Umma tayi gyaran murya ta fara magana da cewa "ƴan uwana sun yanke shawarar baza'ayi taron biki anan ba sabida gudun rigima, kunga dangin Mama zasuzo Bikin Fati kuma sai sun tada fitina, ƙarshe kuma tazo ta ƙare akanmu shiyasa su yaya, suka ce muje gidan yaya Usman ayi taron kuma duk wani abu da ake buƙata ya ɗauke mana ya ce shizaiyi komai shima ai ƴarsa ce" cikin farinciki da jindaɗi Omar ya ce Alhamdulillah wallahi naji daɗi Allah ya saka masu da akairi Aaminat kuwa taji daɗin hakan amma bata nunaba saima sunkuyar da kai datayi Indo &&&& Salma [8/1, 1:28 PM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION Shafi 26 Umma ta murmusa ta ce "Aaminat ko kinfiso ayi Bikin anan" "Aa Umma canɗin sai yafi kwanciyar hankali" Umma ta tashi tana cewa "Aamiant kije ki kira Siyama da ita zamu tafi" "to" tace Umma ta fita, Aaminat ma tashi tayi ta zira hijabi ta nufi waje, Basu ɓata lokaci ba suka kwashi duk wani abunda zasuyi amfani da shi suka kama hanyar Gidan Baba Usman. ɗaurin aure saura kwana ɗaya kenan kowawane ɓangare ya kacame, sai ai'kace-ai'kace ake ko wane gida ya cika da dangi ko ta ina gidan su Yarima ma yayi taff da mutane sai hada hada ake, haka gidan Baba Usman ma dangi sun taru ba ƙarya manya da yara kowa ya nata shagalinda. Gidan su Fati ma biki yayi biki, inda su Fati suke ta sherye-shiryen fita Dinner Nafisa ƙawar Fati ce ta shigo ɗakin su Fati ko sallama babu sai uwar shewa da ta saki, tana cewa "Amarsu ta ango yau saura kwana ɗaya mu kaiki" Fati ta tashi tsaye gami da cewa "dama ke nake jira kizo ki tayani zaɓar kaya dan wallhi so nake nayi shiga ta kece raini" "haba ai karki ɗaga hankalinki zaki fita da fitarki dan akwai ban-banci tsakanin Bazawara da Budurwa" Walid dake zaune aɗakin ya dubi Fati ya ce "wai Fati maiyasa ba ki da tunani ne,??? ita Aaminat ba sa'ar gasarki bace don kuwa zaran bakalar yadin bane" "dakata munafiki ina ruwanka damu ko kafiso mu zauna muna gani Bikin Bazawara yafi nawa??, to wallahi karka sake wannan tunanin nafi ƙarfin Aaminat ko ta ina" tashi yayi ya ficewarsa, ya barsu suna zage-zage da masifa. Ammi ce zaune a kan kujera a Falon ta tana latsa waya, Anti Zainab ta shigo da sallama, Ammi ta amsa tare da cewa "Anti ina Yarima ya shige ne tin ɗazu nake neman sa" "kinsan sa baya son hayaniya kuma gidan namu ya fara cika" "to banda abinsa ai shiya tara taron" Anti Zainab ta zauna kusa da Ammi tana cewa "washh wallahi na gaji" "sannu ai da gajiya" Kausar ce ta shigo da sallama, Anti ta amsa gami da cewa "daga ina haka naganki da kaya niƙi-niƙi???" "daga wajen mai ɗinki nake " "kije ki watsa ruwa kizo kici Abinci" "to Anti" Ammi ta miƙe gami da cewa "bari naje madafa naga ya aikin yake tafiya" "to nima yanzu zanzo" Anti ta faɗa tana kashingiɗa, "Aaminat tana kwance a ɗakin su Iman tana kuka taji wayarta tana ruri, banza tayiwa wayar ta cigaba da kukanta, saida kiran ya katse wani ya shigo sannan ta ɗauki wayar batare da ta duba maikiran ba, karawa tayi akunne, batare da tayi magana ba, "Salamu'alaiki" murya a daƙile ta ce "Amin wa alaikassalam" murmusawa yayi, gami da cewa "Aaminat kin shirya ne" "A'a" "saboda me baki shirya ba shida tayi fa" "nifa nace maka babu inda zanje" "Aaminat kiyi haƙuri dan Allah kije in bakije ba bansan yadda zancewa dangi na ba kuma nace musu zaki je" ɗan ƙaramin tsaki tayi, "Aminat dan Allah ki tausaya min kije," "nifa bazani ba ai ba wannan ne Aure na nafar koba kaga ai ba saina wani je ba" wata zazzafar ajiyar zuciya ya sauke tare da rintse ido, sun ɗauki minti yakai biyu babu wanda yayi magana, Yarima ne yayi ta maza yace "shikenan tunda bazaki ba saiki zauna, kiyi abinda kika ga dama tinda ba a'isa dake ba," yana gama faɗin haka ya kashe kiran rai aɓace, dan kuwa Aminat ta fara ɓata mai rai, kusan kwana biyar yana fama da ita amma taƙi yarda, Aminat kuwa kuka ta ƙara fashewa dashi, dai-dai lokacin Siyama Umaima Iman suka kutso kai ɗakin, turusss sukayi ganin Aaminat ta zage tana ɓarzar kuka, da sauri sukayi kanta suna cewa "maiyafaru??" banza tayi dasu, Umaima ta ce "ya Aminat baki da lafiya ne ko wani abu akayi miki??" cikin kuka tace "babu komai" "to maiya faru kike kuka??" share hawaye tayi tare da cewa "Yarima ne wai sainnaje gurin Dinner kuma ni banason zuwa" sheƙewa sukayi da dariya ta saki baki tana kallon su, Simaya ta ce "amma kin bani dariya, akan haka kika zauna kina ta kuka sai kace wadda akace za'a kashe" Aaminat ta shiga goge hawayen gami da cewa "kukan ma baza'a bar mutum yayi mai daɗi ba, sai an takura masa" "iyeeee kukan ma hada mai daɗi ko???" tsaki tayi taja ƙaton bargo ta rufa, wayar ta ce ta fara kuwwa ya duba mai kiran da mamakin ta sai taga wata number ba irin ta ƙasar nan ba, saida ta kusa yankewa sannan ta ɗauka, tare da sallama, amsawa yayi, cikin nutsuwa ya ce "maiyasa bazakije wajen shagalin bkinki ba" wani dummmm taji zuciyar ta tayi, adiririce ta ce "A...a...a....Abdul kaine" "nine Yaya dan Allah kiyi mana alfarma kije dan Allah" tana dariya dariya kuka kuka ta ce "to zani amma bazan daɗe ba, Abdul ka dawo don Allah" "to kitashi kishirya kuma dan Allah ki daina wahalarmin Aminina bana jin daɗin hakan, idan lokacin dawowata ya yi zan dawo" wasu sabbin hawaye ne suka fara sabuwar zarya akan tausasan kumatunta, ta ce "to zan daina" "to Allah ya sanya alkairi ya kauda fitina amma kin ɓatawa Abubakar rai kikira sa ki bashi haƙuri" "to" ta ce daga haka sukayi sallama, Umaima ta kalli Aaminat ta ce "gaskiya ki rage abinda kikewa yaya Abubakar gobe iyanzu fa kina gidan sa," "nima dai haka nagani haka kawai saita dinga tsangwamar bawan Allah" Aaminat kuwa banda cokalo baki babu abinda take, Ameeera ce ta shigo tana cewa "ga mai kwalliyar nan ta ƙaraso", "to ki ƙaraso da ita nan ɗaki" Iman ta faɗa Siyama ta kalli Aaminat, cikin sanyin murya ta ce "kije kiyi wanka lokaci yana ja", tashi Aaminat tayi ta shiga wanka, bata jima ba ta fito daga wankan, zama tayi akan ƴar ƙaramar kujera, ta fara shafa mayuka masu ƙamshi da tsada, tin kafin ayi mata kwalliyar ta ɗau harama don kuwa ta sha gyara, fatarta ta yi suɓula sai ƙyalli da walƙiya take ta yi wani ɓulɓul, tana gamawa "Umaima ta kalli mai kwalliyar ta ce kije ki fara yimata", Aaminat ta ce "nifa ba saianyi mini Make-up ba" "ai kuwa dolenki ayi tunjiya kike faman wahalar da mutane dan iskanci, komai akace saiki ce ke bazakiyi ba to dole sai anyi kwalliyar nan" "yauwa maman Humaira tin ɗazu take ta butsewa taƙi yarda" wadda aka kira da maman Humaira ta ƙara ɗaure fuska babu alamun wasa, ta ce "maza ki farayi mata,"... ta makawa Aaminat harara ta ce "idan kika kuskura nadawo na tarar, baki zauna anyi miki ba sainayi rugu-rugu dake ja'ira" tana gama faɗin haka ta juya ta ficewar ta, dan dole aka fara yiwa Aaminat Make-up anayi tana butsarewa, ko ta cokalo baki gaba tana mita,, Fati ta shirya cikin tsadadden Leshi marun doguwar riga gown sai walwali take tayi kyau sosai san kowa ƙin wanda ya rasa, cikin yauƙi da yanga da jinkanta, take takawa har suka isa kofar gida inda aka aje motar ango da abokansa, kofar maya aka buɗe mata ta shiga, Direban ya fara jan motar a hankali suka ɗauki hanya, cikin ɗan lokaci aka gama Make-up ɗin Aaminat wata riga Umaima ta miƙo mata, ta ce "kiyi kisa" batare da tace komai ba ta karɓi rigar ta fara sawa, Dogowar riga ce Baƙa da yarfin golden, mai irin buguzum ɗin nan irin ta indiawa, tayi mata mugun kyau tamkar wata sarauniyar kyawa-wa, takalmi golden tasa da wata ƴar ƙaramar jaka mai ƙyalli da sheƙi, wani ɗan ƙaramin mayafi, Siyama ta miƙo mata, ta karɓa ta yana a saman kanta, Iman da Umaima suka ɗauki wasu tsadaddun turaruka masu mugun ƙarfi da ƙamshi suka fara fesa mata kamar bazasu daina ba, Siyama ce ta kama hannunta cikin sanyi ta ce "muje ko" tirjewa tayi taƙi ta fiya, Siyama ta saita dai-dai kunnan ta ta ce "Aaminat kiyi haƙuri ki bamu haɗin kai dan Allah, karkiyi gardama," wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke,, sannan ta fara ɗaga ƙafar ta cikin nutsuwa, ahankali take takawa, kamar mai tsoron takawa, a haka suka isa babban ɗakin da Umma take ita da ƴan uwan ta da sauran mutane, suna shiga ɗakin ya kaure da buɗa, ahankali ta ƙarasa inda Umma take, kai ta kifa akan cinyar Umma, Umma ta shafa bayanta ta ce "Aaminat Allah yayi miki albarka ta shi kuje" ƙin tashi tayi saida Umaima ta kama hannun ta ya ɗagata, bayan anyi kamu, suka nufi ƙofar fita, Aharabar gidan suka tsaya, inda wata jibgegeyar mota mai tadar gaske take Baƙa ce motar daganin motar kasan ba ta ƙanana mutane bace, wani kyak-kyawan saurayi ne ya buɗe ƙofar baya, kasan cewar duhu ya farayi hakan yasa bata lura da mutu ko babu ba ta shiga motar cikin nutsuwa, ahankali ta rufe murfin ƙofar, sannan ya zagaya ya shiga mazaunin Direba, su Siyama ma tasu motar suka shiga,, cikin nutsuwa Direban ya fara jan motar suka fita daga get ɗin gidan, saida suka hau titi, sannan Aaminat taji motsin mutum akusa da ita, matsawa tayi, gefe, wani ni'imtaccen murmushi ya saki, tare da lumshe ido, waya ya ɗauko ya kunna fitilar wayar, ya haska Aaminat yana wani tattausan murmushi, cikin nutsuwa ya kai hannun sa ya yaye gelen da ta rufe fuskarta, hawaye ne shaɓe-shaɓe kwance afuskarta, cikin tattausar muryarsa mai daɗin sauraro ya ce "sorry ki daina kuka, banason ganin zubar hawayen ki," wani numfashi taje ta sauke tare da, sauke nannauyar ajiyar zuciya, wani maraitaccen murmushi ya sakar mata, sannan ya miƙo mata tissue, ya ce kishare hawayan ki bana son ganin ki kina kuka dan Allah ki daina karki sa kanki ciwon kai,..." ya numfasa kafin ya ce "Aaminat dan Allah ki karɓa ki shara hawayan ki, kidaina kuka karki ɓata kwalliyarki," ƙin kaɓa tayi saima wasu hawayen da suke ƙara shararowa, cikin nutsuwa, Yarima ya fara share mata hawayen yana hura mata iska da bakin sa, hakan yasa ta fara jera ajiyar zuciya akai-akai, gyaran muryar da Sabir yayi ce ta dawo da Yarima cikin hayyacin sa,, Sabir ya kwashe da dariya gami da cewa "ya Abubakar dama ka iya soyyaya haka,???" tsaki Yarima yayi ya ce "kai ina wasa da kai???" "A'a wallahi salon nakane yake matsa ni" "kai Sabir ka fiya sa ido, dama hankalin ka yana kanmu ka saki tuƙin ko??" ƴar dariya yayi ya ce "ai dama shiyasa nace ni zan jaku" "ai kuwa idan na ƙarajin tarinka saina..." muryar Aaminat ce ta katse masa magana, jin tana cewa "kun isheni da surutu" murmusawa yayi ya ce "ranki ya daɗe tuba muke, mun daina" shiru tayi batace komai ba hakan yasa suma sukaja nasu bakunan suka tsuke, Ɓan garen su Fati kuwa suna isa aka fara cashewa ana rawa kamar ba gobe, cikin mintina ƙalilan suka ƙarasa ƙaton hall ɗin parking sukayi, a tafkeken filin wajen, Siyama da Ameera ne suka ƙaraso wajen tare da sauran ƴan matan, gaba ɗayansu sunyi ankon material pink ɗinkin dogayen riguna fitet, sunyi bala'in haɗuwa maza kuma su Bilal da sauran ƙannan ta na layinsu irin su cokaki Jabir Walid Salim Ahmad Amiyo da dai sauran sunyi ankon yadi mai tsada Bulu Black suma fa sun haɗu huluna ma iriɗaya ɗinki iri ɗaya, Sabir ne ya fito ya zagayo ya buɗe murfin motar, tuni masu photo sun zagaye wajen, sai ɗauka suke, a hankali da nutsuwa ta zuro ƙafa ɗaya waje, saida ta ɗan kwashi sakanni kafin ta zuro ɗaya ƙafar sannan ta miƙe, Yarima ma fitowa yayi yana wani ƙasaitaccen taku, ƴan matanne suka shiga gaba, mazan kuma suka tsaya abaya, Yarima da Aaminat kuma a tsakiya, ahankali suka fara tafiya, kamar basa son taka ƙasa, daga ita har Yariman wani jinkai da izza ne ya ziyarci zukatan su hakan yasa suke taku ɗaya bayan ɗaya, suna ƙarasa tafkekiyar ƙofar ɗakin taron suka ƙara sauyw taku, wani ƙasaitaccen taku suke da izza zarra mulki, MC kuwa dan da nan ya saki waƙar shigowa da Amarya da Ango, a tare suke jefa ƙafarsu in suka ajen ta hagu sai sun ɗaki sakan uku kafin su ƙara jefa ɗayar, danda nan kallo ya koma sama inda kowa na wajen yake kallon su, guri ya ƙara kacamewa kowa yana farinciki, tabbasss biki yayi biki biki ya tsaru waje yayi waje kai dagani kasan akwai banbanci tsakanin Fati da Aaminat iya wajen zaman su Aminat ma aljannar duniya ne wasu mugaye kujeru ne na gani na faɗe nasa maƙiya jin haushi, ahankali suka ƙarasa wajen zaman Amarya da Ango, kamar yarda su Umaima suka tsara yadda Amarya zata zauna, haka suka zagaye wajen tamkar Sarki zai zau na, mazan suka baza malin malin ɗin su ta yadda babu wanda zaiga zaman Amaryar da Angon ta, zama sukayi sannan su kuma ƴan shigo da Amarya suka jeru a layi maza da mata suka fara rawa,, Dangin Ango ma ba abarsu abaya ba haka akaita ɓarin kuɗi Anti Rahina ma tayi liƙi kamar ba gobe haka abokanan ango kowa na wajen farin ciki yake da nishaɗi, su Kausar ma da sauran ƴan mata na dangin Yarima sun fita da fitar su suma sun zubga ankwan su iri ɗaya material fari ƙal, wajen ya ƙara haduwa, abin burgewa, misalin ƙarfe 12:00 na dare kowa da ya halarci taron ya koma gida Amarya ma tako ma, gidan su Yarima kwanan aiki kenan wani ƙaton fili ne na cikin gidan wanda ake ta girke-girke an ɗora kangama kangaman tukwane sai hada hada ake, Gidan Baba Usman ma ba daga nan ba aiki ake tuƙuru ana kaiwa ana komowa, Aaminat kuwa tuni tayi wanka tabi lafiyar gado, su Ameera Iman Siyama Umaima Hasana da Usaina sai fama surutai suke suna shewa da kagansu kasan suna tsaka da farinciki, Ɓan garen su Fati ma aiki aketayi, 🤕🤕🤕🤕🤕🤕🤕 wai da gaske dai Yarima ne zai Auri Aaminat ba Abdulkareem ba,😭🫣 Indo &&& Auta [8/9, 1:33 PM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION Shafi 27 Washe gari misalin ƙarfe 10:30 ƙofar gidan su Aaminat ya cika da ƴan ɗaurin Aure sai hada-hada suke, ɓangaren mijin Fati ma sun taru ba laifi. Yarima ya shirya cikin bugaggiyar shadda ruwan toka mai haske, kai maza fa sun ɗau harama yayi wani fitinennen kyau in kuka ga Yarima sai kun girgiza sabida tsabar haɗuwar da yayi, a hankali yake tafiya tamkar baya tafiyar kansa a ƙasa kamar munafuki sai fici-fici yake da ido, ɓangaren Abba ya nufa, Ammi Anti Zainab suna tsaye da alama wani abun suke tattaunawa, sallama ya ɗanyi murya ciki-ciki. Anti Zainab ta dube shi ta ce "Allah ya sanya alkairi ya baku zaman lafiya," baice komai ba sabi da kunyarsu da ya keji, Ammi ma addu'a tayi masa tare da nasihohi, daga haka sukayi sallama. *Ga wata Muhimmiyar Sanarwa, Ku daure ku tsaya ku karanta* *Assalamu-alaikum Masoyana kowa da kowa Barka da Warhaka. *Na zo muku da Kyakkyawan Albishir Me Matuƙar Muhimmanci. Shahararren Business Center Ɗinnan da ku ka sani me Suna HALYJASHERU Sun yi muku gwaggwaɓan Tanadi na Kyawawan Kaya Masu Kyau ga Rahusa, ina Farin cikin Sanar da ku Cewa Ku Garzaya HALYJASHERU Ku Ƙulla Kasuwanci da su Za ku yi Matuƙar Farin ciki.* *HALY-JASHERU venture's* *munada kayayyaki masu kyau da inganchi ba Algus da ha'inchi kayanmu daga Ethiopian ne.* *prdct dinmu, muna Ethiopian MAGIC HAIR OIL, ANTI DANDRUFF SHAMPOO, SERUM BODY CREAM, HAND CREAM.* *Da Magungunan chututtuka Kala Daban-Daban, Da Magunguna Na SIRRIN MATA Masu Matuƙar Kyau da Iganci Gami da Kara Lafiya ajikin Ɗan Adam.* *HALY-JASHERU CENTER Ba mu tsaya iya haka ba, Muna Da Distributor a Ko Ina a Fadin Ƙasarnan Har ma da ta Ƙetare Domin Kuwa abin ba na Wasa Bane, Domin Tallafawa Ƴan Uwanmu Muka Ware Aji na Koyar da Harkokin Kasuwncinmu ga Masu Buƙata, a kan Naira 3000 kawai Muke Koyar da Wannan Sana'o'i Domin Temakon Al'uma, Da Fatan kun yi farin ciki da hakan domin Mu Farin Cikin Costomers Shine Namu. Ku Tuntuɓi C.E.O Ta Wannan Lamba 07046665338 ko 07061664264 INA GAISUWA GAMI DA GODIYA MASOYANA* Harabar gidan ya fita, inda su Sabir suke suna jiran fitowar sa, Sabir ya maka masa harara, cike da zaulaya ya ce "kaje ka nemi waje kayi zaman ka sai an ɗaura Auren da wani ko" "cakwakiya ai ko da me suke yawo saiya sake ta an ɗaurawa yayan mu" Sulaiman ya faɗa yana harɗe ƙafa, Yarima kuwa ko kallon su baiyi ba ya wuce ya shige mota abin sa, suma binsa sukayi, suka shiga, Sulaiman ya zauna a mazaunin Direba, cikin nutsuwa ya fara jan motar har suka ɗauki hanyar Unguwar gadon ƙaya, Basu ɓata lokaci mai tsawo ba suka isa, layin ya cika taf da mutane sai kayam-kayam suke bayan mintina ƙalilan aka shaida Ɗaurin Auren, ABUBAKAR SAADIQ YAHAYA, tate da AAMINAT HABIBU SALEH, sai AHMAD ZAKARIYYA, tare da FATIMA HABIBU SALEH. ma sha Allah Aure ya ɗauru, nan aka shiga gaggaisawa da mutane ana rabon goro da alawa na ɗaurin Aure, Fati da yayyan ta mata su uku Hajara Faiza Alawiyya, suna ɗaki suna jin an ɗaura Aure suka sa shewa tare da ta fawa, Haja ta kalli Fati ta ce "yarinya kin Auri mai kuɗi ki taka duk wanda ranki yakeso," ko dangin sa bance kiraga musu ba, karki ragawa kowa ko da uwarsa ce in ba haka ba rainaki zasuyi" Faiza ta faɗa tana zazzaro wa Fati ido, Fati ta yi wani shu'umin murmushi gami da cewa "karku wani walar da kanku wannan Mama ta daɗe tana faɗamin," "dama nasan zata faɗamiki amma ki kula da wannan maganin gobe da safe kiyi amfani dashi wajen girki," "to" ta ce Nafisa ce ta shigo ɗakin tana cewa "uwar gida a gidan Ahmad," Fati ta saki murmushi tare da cije gefen laɓɓanta, dariya suka sa hada shewa, Nafisa ta ce "ki tashi muje waje za'ayi photo da Angwaye" zaram Fati ta miƙe tare da gyara mayafinta, tabi Nafisa suka fita, Ɓangaren su Yarima kuwa ba'ajima da ɗaura Aure ba sukayi ta fiyar su, Aaminat tana zaune a ɗaki Siyama ta shigo da sallama, murya a sarƙe ta amsa, zama Siyama ta yi, gami da cewa "Aaminat wai bakya son Yarima ne," wani yarrrr taji ta kanta yayi, tunanin amsar da zata bawa Siyama ta shigayi, jin Aaminat bata ce komai ba, yasa Siyama cewa "bakya son sa ko?" ƙasa ta ɗanyi da kai, cikin sassanyar muryar ta mai daɗin sauraro ta ce, Siyama in nace miki banason Yarima nayi ƙarya, abu ɗaya ne yake hanani sakewa da shi tunanin Abdul ina ganin kamar munci amanar sa," dai-dai lokacin ya Omar ya kutso ɗaki da alama yaji maganar da suke, ƙarasowa yayi, sannan ya zauna akan wata kujera madaidaiciya, Aaminat kuwa tuni jikinta ya hau rawa ta sani ya Omar ba wasa, Siyama ma ta kasa ɗaga ido ta kalle shi, gyaran murya yayi gami da cewa "Aaminat dama baki da hankali, yanzu fa kina da haƙƙin wani akanki, mai yasa kike tunanin wani wanda ba muharramin ki ba????,"... ya ƙarasa maganar yana tsira mata ido, jin batace komai ba yasa ya ƙara cewa "Aaminat karki kuskura in ƙaraji kince kunci amanar sa, ba haka cin amana yake ba, hassali ma shi da kansa Abdul ɗin ya roƙe ki da ki Auri Amininsa, to kinga ai sam hakan baiyi kama da cin amana ba". karyar da murya yayi kamar mai shirin kuka ya ce "Aaminat dan Allah kiriƙe Auren ki da daraja ki riƙi mijinki, kiyiwa mijinki biyayya dan Allah karki bari duniya ta ruɗeki," cikin kuka ta ce "na gode yaya, Allah ya saka da alkairi, kuma zanyi duk abinda kace, zanyi biyayya agidan Aure na, har na tsahon rayuwata," murmusawa yayi gami da cewa "Allah ya baku zaman lafiya, Allah ya kaɗe duk wata fitina," suka amsa da Amin, tashi yayi ya fita,, Siyama ta maida kallonta kan Aaminat ta ce "na tayaki murna Allah ya baku zaman lafiya, Allah yasa gidan zaman ki ne," "Amin" ta ce suka shiga fira da Siyama, duk da Aaminat ba wani magana take ba sai murmushi ko eh da ummm, Misalin ƙarfe uku na rana Ko wana ɓan gare sun sanya anko ko ta ina biki ake ana nishaɗi Ammi da Anti Zainab sunyi wankan dakakken leshi ruwan kwai sunyi bala'in kyau, Kausar ce ta zo wucewa ta taga su Amma sai faman kici-kici suke a ɗakin Abinci, tsayawa tayi cike da zaulayar kakannin na ta ta ce "su Anti fa an zage wai adole ana Aurar da ɗa" dariya sukayi, Anti ta ce "Kausar baki ƙyale kowa ba," dariyar itama tayi, sannan ta wuce ɗakin Ammi, ta sauya kaya, Da yamma gafda za'akai Amarya Gidan su Fati faɗa ya ɓarke tsakanin dangin Abba da na Mama, saka makon ɓatan wayar ƴar ƙanwar Abba, Mama sai zage-zage take kamar mahaukaciya wai an ɗorawa dangin ta sata, haka sukaita turnuƙu ana bala'i, ɗaya daga cikin dangin Abba ta ce "ai Bara'atu kinyi asara ƴaƴa a lalace, ke a tambaɗe, Abinci agidannan gagarar mu yayi saidai kuci keda gaiyar tsiyarki," ta ƙarasa maganar tana huci, rai a ɓace Bara'atu (Mama) ta ce "ni kike cewa atambade to wallahi ƙaryar ki, ni zaki duba kicewa ƴaƴa a lalace,??.. to ai basukai na wadda ta ɗora ƴaƴan akan karuwanci ba, garani na basu tarbiya," wata shewa dangin Abba suka sa,, Jamila ƙanwar Abba ta kalli Umma gami da cewa "to tsohuwar munafuka ai anyi walƙiya mungan ki, yanzu munsan sharri kikewa Umma agidan nan kuma da tanan ƙaryarki ki hanamu Abinci," sakin baki Mama tayi sakaka tana kallon su, ta kasa cewa komai, hakan ya ƙara turnuƙeta, su Alawiyya da ma suna cen suna nasu faɗan, Mama kuwa ganin batayi nasara ba, yasa ta nufi ɗaki, fakan-fakan sharaf-sharaf tana kuka, dangin Abba kuwa tuni sun haɗa kayansu sunce barin gidan zasuyi, kaɗan ne suka zauna suma don ya zama dolen su ne, Umman Nazir Autar su Umma da Anti maman su Siyama, sai Aaminat da take cikin shirin Atamfa mai kyau da tsada, riga da zani, sai ƙaton mayafin da aka rufeta ruf,, tana zaune agefen gado tana kuka, Umman Nazir ta ce "Aaminat kibi mijinki, kibi duk abinda ya ce indai hakan bai saɓawa addini ba, kiyi biyayya wa iyayan mijinki yanzu sune iyayanki, kinji, ki kyauta tawa dangin Mijinki,, kar inji kar ingani kinyi abinda bai kamata ba kinji ko," Auta ta ce "komai yayi zafi maganin sa Allah duk abinda za'ayi miki, toki kauda kai wata rana sai labari, mahaƙurci mawadaci, kiyi koyi da halin mahaifiyarki ki zama mai haƙurin gaske ki jure ki cije," Banda kuka ba abinda Aaminat take, Anti ta muskuta gami da cewa "nasanki da kafiya wani lokacin, to ki daina kinji, yi nayi bari na bari, karki kuskura ki ɗauki zigar ƙawaye duk abinda zasuce miki kiyi watsi da shi, kibi mijinki sau da ƙafa, kinji ƴata" haka sukaci gaba da yi mata faɗa, da nasihohi, masu ratsa jiki, Maman Humaira ce ta shigo da sallama suka amsa, Anti ta duba gami da cewa "masu ɗaukar Amarya suna jira ance ku fito da ita," "to yanzu ma kuwa in sha Allahu ga mu nan", Anti ta faɗa, Maman Humaira ta juya zuwa wajen ƴan ɗaukar Amarya, Siyama ce ta shigo ɗakin tana kuka, Aaminat tana jin kukan Siyama ta ƙara fashewa da kuka, da gudu Siyama ta rungume Aaminat tana wani kuka mai tsuma zuciya, cikin muryar kuka Siyama ta ce "Aaminat yanzu rabuwa zamuyi zaki tafi ki barni," Aaminat kuwa ta kasa koda magana sai kuka, ko ɗaga harshe ta kasa, da sunan tayi magana, Umman Nazir ce ta kama hannun Aminat, Auta ta janye Siyama, sukansu su Umman Nazir ɗin saida suka share hawaye, duk wanda yaga yadda Siyama da Aaminat suke ɓarzar kuka saiya tausaya musu, gashi sun shaƙu, "dan Allah kudaina kuka kunji kuyi haƙuri rabuwa ta zama dole saidai ziyara," wani kukan Aaminat ta ƙara rushewa da shi, Umman Bazir taja Aaminat, dan kuwa daƙirewa tayi, Ɗakin da Umma da su Baba Usman suke, suka shiga da Aaminat, durƙusawa tayi kan guiwoyinta tana kuka kamar ranta zai fita, cikin tausayawa Umman Nazir ta ce "kiyiwa mahaifiyarki sallama ki nemi yafiyarta," cikin sarƙaƙƙiyar murya mai cike da ban tausayi ta ce "U ....u....u...umm..umma ki yafemin!!!!!!" cike da jarumta Umma ta ce "ba kiyi min laifin komai ba Aaminat Allah yayi miki albarka, Allah ya baku zaman lafiya" mutanen ɗakin suka amsa da Ameen,, Anti ta ce "to Umma zamu tafi da Aaminat ɗakinta kuyi sallama," murya na rawa Aaminat ta ce "Um...umma zan tafi ki yafe min dan Allah," "Allah ya tsare hanya, ya kaiku lafiya," hannun Aaminat suka kama zasu tasheta saidai sukeji ta riƙe, Umma gamm, haka sukaita ƙwarbe da ita kana suka samu nasarar raba Aaminat da Umma, kai tsaye mota suka shige kowa ya shiga mota suka kama hanyar gidan Amarya, Ɓangaren Fati ma tuni an tafi da ita, Basu ɓata lokaci ba suka ƙarasa gidan su Yarima jagora akayi musu zuwa ɓangaren Ammi, gaisawa sukayi sannan sukayi ƴan addu'oi, Anti ta ce "ga Amana nan mun kawo muku, idan tayi ba dai-dai ba ku gyara mata ku nuna mata, dan Allah, duk abinda tayi in me kyaune kune in mara kyaune kune, mudai ga Amana nan mun baku," Anti Zainab ta muskuta gami da cewa "in sha Allahu zaku samemu masu gaskiya da ruƙon Amana, kuma in Allah yayarda mun zama ɗaya ƴarmu ce", cike da gamsuwa sukayi sallama suka raka Aaminat ɗakin ta dake wani sashi na gidan, Basu daɗe ba kowa ya kama gaban sa suka koma gidan, Siyama Umaima Iman Ameera, su kai ɗaina agidan suna taya Aaminat zama, Bayan na ɗan wani lokaci suna zaune agefen Gado sukaji sallama, amsawa sukayi sannan suka bashi izinin shigowa, Sabir yana ƴar dariya ya ce "ƴan mata, mai guri yazo sai mai tabarma ya naɗe," tsaki Siyama tayi gami da cewa "ai ba cewa mukayi zamu zauna ba," dariya yayi dama kunnasu yake sonyi kuma ya kunna, "kuma babu wadda zamu mayar, wayace baku bi manya kun koma gida ba" Siyama taja tsaki cike da baƙinciki Iman ta dube shi ta ce "kaga malam ka tattara ya naka ya naka ka bamu waje musha iska," dariya yayi cike da tsokana irin tasa ya ce "ni ai gidan mune kune zaku tattara komatsanku ku bar mana gida",.... zai ƙarayin magana yaji Sallamar su Yarima, da sauri ya ce "yanzu dama zan fito" Sulaiman ya ce "na mata na mata kawai tun ɗazu daga aike kanemi waje kayi zaman ka," ɗan sosa sumar kansa yayi, su Umaima suka gaida Yarima, Siyama kuwa ko kallon sa batayi ba, ta figi Jakar ta ta na "cewa sai ku tashi mu tafi tunda ba gidan ku bane," ba musu suka tashi, Yarima ya ɗan murmusa gami da cewa Iman "mai akayiwa Siyama ne" murmushi tayi gami da cewa "wai fishi take ka rabata da Aminiyar ta," murmusawa yayi gami da cewa "haka dama rayuwar take sai haƙuri," batace komaiba tabi bayan su Umaima, Yarima ya dubi su Sabir ya ce "to ku kuma mai kuke jira," dariya suka sa, sannan Sabir ya ce "babu abinda muke jira tafiya zamuyi" "to sai ku tafi" Yarima ya faɗa yana hararar su, fita sukayi, Sabir ya wuce harabar gidan, yana zuwa ya tarar su Siyama sun shiga motar Iman sun tafi sai ƙyellinsu ya hango ta get, baiji daɗin hakan ba so yayi sun ƙara casuwa, hakan yasa ya juya y nufi ɗakin da suka sauka, Ɓan garen su Yarima kuma saidai na ce Asuba ta gari,, Indo ❤‍🩹 Salma [8/9, 1:33 PM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION Shafi 28 Bayan Biki da kwana uku kowa da ya halarci taron Bikin ya koma gidan sa, su Umma ma sun koma gida taro ya tashi lafiya Alhamdulillah, Sanye take cikin dakakken leshi fari ɗinkin buba yaji adon duwatsu masu sheƙi da ƙelli, a hankali da nutsuwa take sakkowa daga benen dake ƙaton Falon, wanda yaji kayan more rayuwa, da kayan alatu iri-iri, komai na Falon pink da fari ne, kama daga kan kujeru kwalliyar Falon, komai pink da fari ne, kai Falon fa ya haɗu iya haɗuwa ya tsaru, Ma sha Allah, zama tayi akan ɗaya daga cikin luntsuma-luntsuman kujerun Falon, kai dagani kasan an zuba kuɗaɗa na tashin hankali, wani tattausain murmushi ne ya kufce mata, har saida fararen haƙoranta suka baiyana, sallamar da akayi ce ta fargar da ita tayi saurin haɗe fuska, ƙarasowa yayi cike da jin daɗi da farin ciki, ya ce "wa na kama???" ya faɗa yana dariya, murmusawa tayi kafin ta buɗe baki ta ce "yanzu ma ai baka kamani ba," "haka zakice ko??" "A'a nifa banyi magana ba," "mai kika ce??" ya faɗa yana zuba mata wani sihirtaccen kallo mai rikitarwa, murya ƙasa-ƙasa ta ce "ce wa nayi sannu da zuwa" dariya yayi gami da cewa "Aaminat wato kin rainani ko" "ni na isa in raina ka," murmusawa yayi, batare da ya ce komai ba, shirune ya ɗan ratsa na wani lokaci kafin Yarima ya ce "ni zan wuce Asibiti kije sashin su Ammi ki zauna kafin na dawo" "to" ta ce tana tashi, kallon ta yayi gami da cewa "saura kuma inna dawo kiyi zamanki ki ƙi zuwa," dariya tayi, yaɗan harareta harara mai tafe da saƙonnin so, kala-kala, wani murmushi ne ya kufce mata tayi saurin rufe fuskar ta da tafukan hannunta, juyawa yayi ya fara tafiya cikin nutsuwa, bayan sa tabi, ma'ajiyar motocin gidan ta rakashi, sannan ta juya ta koma, . .Fati tana zaune a hamshaƙin Falon ta tana latsa waya, Ahmad ne ya shigo, wani kallo yayi mata mai cike da ma'anoni, sannan ya zauna kusa da ita, cikin yauƙi ta ce "Baby na sannu fa" "yauwa ya gidan,??" "lafiya" wani musmushi ya kumayi mai cike da tsantsar ma'ana, tashi yayi zai wuce ta ce "gaskiya mota nakeson ka siyamin," "mota kuma??" "eh mota ko bazaka siya ba?" murmusawa yayi gami da cewa "yaufa kwananki uku agidan nan, mai ki ke ci na baka na zuba, Habibti na" cingam ɗin bakinta ta tauna tare da "cewa shikenan" haka sukaci gaba da ƴar hira tana nuna masa son duniya ƙarara, shima ya na nuna mata na sa salon. Atsaye suke cirko-cirko, kowa yana tunane tunane, Nana Hauwa ce ta dubi Abdussalam gami da cewa "anya kuwa Abdul zai dawo garemu, kusan wata ɗaya kenan baya garemu kuma duk ta silar ku ne" ta ƙarasa maganar tana sharar hawaye, Abdussalam ya jata jikinsa cikin sigar kwantar mata da hankali ya ce "sorry Nana ki daina kuka, in sha Allah komai zai dai-daita, kuma muna ta addu'a Allah ya juyo da hankalin sa gida" Nana Farida ce ta tashi daga kusa da Dadda ta ce "kalli fa Ummi bata da lafiya, ya zama dole in muna son rayuwar mahaifiyar mu mu nemo ya Abdul," Abdurrahim ya girgiza kai kana ya ce "ta hanya ɗaya zamu sami Abdul" Abdulmajid ya ce "wace hanya ce???" "ta hanyar roƙon Kadija ta faɗa mana inda yake domin kuwa ina da tabbacin ta san inda yake" da sauri Dad ya tashi zaram yana zaro ido ya ce "haka ne Maza ku kira ta " "to" Abdullah ya faɗa yana nemo number Kadija, kira ya danna mata bugu huɗu ta ɗauka da sallama, hankali tashe ya ce "don Allah kadija ki taimaka ki faɗa mana inda Abdul yake karki ce baki san inda yake ba, hakan na iya silar rasa mahaifiyar mu," ya ƙarasa maganar kamar zai yi kuka, Kadija kamm tayi suman zaune ta kasa koda magana ne, jin ya ƙara cewa "Kadija Abdul shine rayuwar mu baki ɗaya dan Allah" yasa tayi fifgigit, cikin muryar kuka ta ce "Abdul yana india, dole ce tasa na faɗi inda yake," "Kadija kidawo gida Abdul ma zai dawo" hawaye ta share tana tuna lokacin da su Dadda suka murzawa idon su toka suka hana Abdul Abinda yake so, "Kadija yanzu in sha Allah zamu shirya tafiya, kuma hada ke gobe zamu je inda Abdul yake mu dawo dashi gida", wata nannauyar Ajiyar zuciya ta sauke gami da ce wa "ganin nan zuwa yanzu" sallama sukayi, Abdulmajid cikin jindaɗi ya ce "Alhamdulillah mun kusa dawo da Autanmu," kowa na ɗakin farin ciki ya hauyi ciki kuwa har da Dadda Ummi ma murmushi take tana miƙa saƙon godiya ga sarki Allah buwayi gagara misali, Washe gari da sassafe Jirgin su Dadda Abdussalam Abdulmajid Nana Kadija, ya tashi izuwa ƙasar india, Umma na zaune a ɗaki ta kammala karatun Alƙur'ni mai girma ta na yin addu'a, wayar ta ta fara ruri, ta mayar da Alƙur'anin mazaunin sa, sannan ta juyo inda wayar take kafin ta ƙaraso wayar ta katse, ɗaukar wayar tayi sannan ta zaune a gefen godo, kira ne ya ƙara shigowa wayar, ta ɗauka da sallama, "Assalamu'alaikum Ummana ta kai na," "Aminwa'alaikisalam," ta faɗa tana murmushi, cikin farin ciki da jin daɗi, Aaminat ta ce "Umma ya kuke ina kewar ku wallahi, dan Allah kice ya kawoni" "A'a Aaminatu kefa ba yarinya bace, ki zauna agidan ki kinji ko?" turɓune fuska tayi, kamar tana ganin Umma ta fara magana cikin shagwaɓa, "ni Umma na zan gani yaufa kwana huɗu rabo na da Umma na" "to kinga kwana huɗu ai bakyazo gida ba kuna zaune lafiya," "nifa Umma ji nake tamkar nayi shekaru ban ganku ba" Umma ta murmusa, Aaminat ta ƙara cewa "ina su Walid da Umaima suzo dan Allah" "A'a bazasu zo ba, kedai ki nutsu ki zauna agidan mijin ki banda yawon banza" "kai Umma kin sanni fa ko a nan bana zuwa ko ina sai gidan su Siyama, anan kuma wa na sani, gidan da ko yara babu, ni duk na gaji, jinake kamar akan ƙaya neke, wata tsawa Umma ta darka mata ta ce "ba ki da hankali gidan mijin naki kike kira kan ƙaya? to karki sake na ƙara jin wannan maganar a bakin ki" tsitt Aaminat tayi baki na rawa ta ce "Umma dan Allah kiyi haƙuri bazan ƙara ba, kinji Ummu na" tsaki Umma taja, sannan ta ce "sai anjima" tana gama faɗin haka ta katse wayar, Aaminat kuwa ajiyar zuciya ta sauke. Koda su Dadda suka isa masaukin Abdul, basu sha wahalar shawo kansa ba, kwanansu ɗaya suka juyo gida. Zaune suke Falon kowa sai farin ciki yake kamar ba gobe, Ummi kam tunda taga ɗan Autan ta sai ta nemi cuta ta rasa sai rashin ƙwarin jiki, Abdussalam kuwa sam ya kasa sakewa da Abdul dan kuwa bai manta lokacin da yake marin Abdul ba da maganganu mara sa daɗi, Dadda ya dubi Abdul ya ce "babban mutum" Abdulkareem ya ɗago da runannun idanun sa ya zubawa Dadda su, Dad yayi gyaran murya gami da cewa "Abdulkareem kayi haƙuri mun sani bamu kyauta maka ba, amma mu muna gyara goben ka ne, inaso ka sani ita rayuwa ba komai ne muke nema mu samu ba, wani abun muna neman sa ido rufe, amma sai Allah ya hana mu kuma duk dan ya jarraba mu ne, wani abun kuma zakuga bamu nema ba Allah ya bamu,"...... zuwa yanzu Abdul yayi ƙasa da kansa sai sharar hawaye yake, Dadda ya ce "komai na rayuwa haƙuri ake dashi, saika ga mai haƙuri ya cimma duk wata nasara, da yasa gama kuma Aure nufi ne na Allah idan Allah yayi matarka ce to babu makawa sai ta zama matar ka, idan kuma Allah baiyi ita ce matar ka ba to ko anzauna za'a ɗaura Auren sai Allah yayi yadda yaso, sai Auren ya warware,, Abdul ina so ka zama cikakken musulmi mai yarda da ƙaddara aduk yanda tazo maka, ka daure ka cinye wannan jarrabawar" ɗakin yayi shiru sai shash-sheƙar kukan wasu daga ciki kakeji, tashi Abdul yayi ya durƙusa a gaban Dadda ya fara magana cikin da kakkiyar muryar sa mai daɗin sairaro, ya ce "haƙiƙa ka cancanti zama uba domin kuwa kaine cikakken da ya amsa sunan sa uba, ka jajirce akan iyalin ka ka tsaya tsayin daka don ganin anbi maganar ka, domin kuwa samun uba kamarka da kamar wuya, Dadda kaiɗin uba ne wanda bakowa ne yake da kamar ka ba," ya ƙarasa maganar yana faɗawa jikin Dadda, bayansa Dadda ya shiga bubbugawa, cikin nutsuwa, har saida Abdul ya samu nutsuwa sannan Dadda ya miƙe ckin farin ciki da jin daɗi, ya ce "Babban mutum kazo ka tayani fira," "to" Abdul ya ce ya tashi yabi Dadda sashin sa, Bayan sati biyu komai ya dai-daita a gidan su Abdul sun manta da komai sai farin ciki Abdul ma Alhamdulillah bashi da aiki sai karatun Alƙur'ani mai girma gami da Azkhar. INDO & AUTA [8/9, 2:01 PM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION Shafi 29 Ɓangaren Mama kuwa waɗanda ta ciwa bashi sun hanata sakat arana mutum biyar sa zo karɓar bashin da taci musu, yau ma kamar kullum tana zaune, a tsakar gida, Hajja Lantana tayi sallama, gaban Mama ne yayi wata muguwar faɗuwa, kasa amsa sallamar tayi, Umma ta amsa, Hajja Lantana ta kalli Mama kallo mai cike da razanarwa, ta ce "to koriyar munafuka Allah ya kamaki, yau ɗinnan zaki biyani kuɗi na, dan wallahi indai kika ga na bar gidan nan to da kuɗi na in kuwa ba haka ba, zanzo da mota na kwashe kayan ɗakin ki,!!!!!" tuni Mama ta fara zufa, jiki na rawa ta ce "dan Allah kiyi haƙuri idan na samu da kaina zanzo na kawo miki!!" wata shaiɗaniyar dariya Lantana ta saki lokaci ɗaya kuma ta murtuke fuska kamar ba ita tayi dariyar ba, hakan ya ƙara rikita Mama ta fara sharar gumin wahala, Umma kam tana so tayi magana amma ta kasa sai ido, Lantana ta daki bango, cikin hargowa, ta ce "zaki biyani kuɗina ko saina sa an kamaki, dan kuwa wallahi akan kuɗi babu abin da bazan iya ba,!!!" ta ƙarasa maganar tana tafe-tafe cikin muryar kuka Mama ta ce "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un na shiga uku, duniya ta ruɗeni,"...!!! "bakiyi salati ba sai kinganki a office ɗin ƴan sanda" sakin baki Mama tayi tana kallon Mara da tashigo, Mara ta kalli Mama sama da ƙasa sannan ta ce "yaro man kaza, rashin sanin wace ce Mara shiya kaiki cimin bashi ki ƙi biya, bana yafiya kuma bana ɗaga ƙafa, yanzu haka tafe nake da ƴansanda, zakije ofishin ƴan sanda ki biyani kuɗi na,, Lantana ta kwashe da dariya gami da cewa "tirƙashi ana wata ga wata, nima dani za'a ofishin nan a ƙwatar min ƙaƙƙi na!!" hannu Mama ta ɗora aka ta fashe da wani gigitaccen kuka ta na cewa "Allah na tuba ka yafemin Alhakin Aaminat ma kadai ba zai barni na sha ruwa ba, na zalumci baiwar Allah nayi mata sharri iri-iri, ni yau tawa ƙaddarar ta zo, nayi kuskuren cewa babu ni babu ƙaddara, gashu ƴar tawa ma ta gujeni kamar ba ni na haifeta ba don ta samu duniya, waiyo Allah na yau zasu tozartani!!!" haka Mama ra fara suntiri a tsakar gidan tana rusa kuka, Umma ma sharar haweye take domin kuwa idan kaga halin da Mama ta shiga sai ka tausaya mata,, cikin rashin imani Mara ta cukumi Mama da ƙarfin tsiya ta jata ƙiiiiii!!!!, Mama kam kuka take tana sambatu, har suka fita waje, mutane taf a layin kowa ya zubawa su Mama Ido, Walid yana zaune a cikin su Abdul, baisan lokacin da wani kuka mai ƙarfi ya kufce masa ba, haƙuri suka shiga bashi, Abdulkareem kuwa kauda kai gefe yayi, Haka sunaji suna gani aka tafi da Mama, Umma kam ta rasa yadda zatayi sai faman sintiri take. Walid kam duniyar tayi masa zafi saiyayi kamar ya daina kuka, sai ya ƙara fashewa da sabo, Bilal ya dubi Abdul ya ce "dan Allah Guda ka taimaka, ka fito da Mama," sai a lokacin Abdulkareem ya kalle su, ganin sun zira masa ido yasa shi cewa "yakira yayarsa ya sanar mata mana," Walid ya kalle shi ya ce "indai Fati ce tayi hannun riga damu ta juyawa kowa baya kusan sati ɗaya kenan Mama tana kiranta, wani lokaci da ta ɗauki kiran tace kar atakura mata, wani lokaci, ma bata ɗaukar kiran," ya ƙarasa maganar kamar zai ƙara rushewa da kuka, kowa yayi zumu-zumu yana kallon Abdulkareem, shi kuwa ranshi fess, saidai bai bari Walid ya gana hakan ba, Jabir ya numfasa gami da cewa "to yanzu ya za'ayi??" Abdulkareem ya murmusa kana ya ce "yakira ɗayar yayar tasu mana," da sauri Walid ya ce "wai yaya Aaminat,??" "eh ita" sauke ajiyar zuciya yayi sannan ya ce "banajin yaya zata iya taimakawa Mama, domin kuwa alhakin ta ne yake bibiyar Mama" Abdul yaja tsaki gami da cewa "dalla ka kirata an faɗa maka ba'a yafiya, zata yafe mata kuma zata fito da ita ka kira ka sanar mata," yana gama faɗin haka ya tashi, ya nufi gida, yana cikin tafiya yaji garam sunyi karo, ahan kali ya ɗago kansa ya zuba mata wani masifefen kallo, jiki na rawa ta ce "dan Allah kayi haƙuri, wallahi ban kula ba," tsaki yayi gami da cewa "ina idanunki suke, ko aka suke, kina tafiya amma hankalin ki na wani wajen, ƙasa Siyama tayi da kai, ƙirjinta yana wani bugu, Abdul ya kauce ya fara takawa, cikin ƙasaita,, Walid yana kiran Aaminat ya zaiyana mata komai, numfasawa tayi, sannan ta ce "Walid ka kwantar da hankalin ka, kaji zanzo in biya duk bashikan da Mama taci yanzu," cikin farinciki ya ce "ya Aaminat samun kamarki da wahala, kin manta duk wani sharri irin na Mama kan manta munanan ƙazafin da tayi maki," murmushi tayi mai ciwo ta ce "hannun ka baya ruɓewa ka yanke ka jefar, Mama uwa ce gareni, kuma tana cikin wani hali, kaga dole zanyi ƙoƙari naga na fitar da uwa ta" "haka ne yaya Allah ya saka miki da alkairi," "amin" daga haka sukayi sallama, Yarima ta kira ta sanar masa, yaso ya hana ta amma da ya tuna ko wace Mama a wajen Aaminat sai ya amince, bata ɓata lokaci ba ta shirya tsaf cikin Atamfa riga da zani, ta zindima hijab ɗinta har ƙasa, sannan ta fito ta umarci Direba ya kaita, inda zataje. basu ɓata lokaci ba suka isa, ofishin ƴan sandan, tana shiga ta hangi Mama a cikin ɗan wani ɗaki, tayi muzu-muzu kana gani kasan ta wahala, gaisawa sukayi, cikin mutuntawa, sannan Aaminat tayi musu bayanin duk Abinda ya kawo ta, Mama kuwa tana ganin Aaminat ta ƙara rushewa da kuka mai cike da nadama da danasani, saida suka ɗauki lokaci suna magana da ƴansandan sannan Aaminat ta biya su Mara da Lantana kuɗin su, tayi ƴan cike-cike aka fito da Mama, Aaminat ta juya zata tafi taji, an rungumota, cikin muryar kuka, Mama ta ce "Aaminat ki yafe mini na zalumce ki, ni kuma ga tawa ƙaddarar, ta sanadin Fati na shigo wajen nan amma Fati bata damu dani ba," ta ƙarasa maganar tana kuka, Aaminat ta kama hannun Mama ta jata suka fita, murfin mota ta buɗe ta ce "Mama ki shiga muje ki rakani duk inda ake binki bashi abiya su," Mama tana kuka ta shiga motar. haka suka dinga bi gida gida ta biya su kuɗin su, sannan suka wuce gidan Aaminat, saida Mama tayi wanka taci Abinci, ta ƙara nemar yafiya, Aaminat ta ce ta yafe, tasa Direba ya maida Mama gida, Washe gari da safe Abba ya shirya tsaf zai fita, Mama ta fito daga ɗaki, simi-simi "dan Allah kayi haƙuri Alhaji, ko kallon ta baiyi ba yayi gaba abin sa, Mama ta rushe da kukan nadama da da na sani, Umma ce ta fito daga ɗakin Abba ta fara rarrashin Mama, Abba yana fita yaci karo da wani bawan Allah, baki sake Abba ya tsaya yana binsa da kallon mamaki, da al'ajabi, mutumin yaja ƙafa ya ƙarasa inda Abba ya tsaya, ya ce "Abba Kamalu ne, nazo ne na nemi yafiyar ka da Aaminat dan Allah kuyafe min, cikin mamaki Abba ya ce "Kamalu kaine ka koma haka,???!!!" "nine duniya ta ladabtar da ni, haƙika na cutar da baiwar Allah wadda batasan komai ba sai gaskiya da Amana, Abba duk wasu munanan magan ganu da na faɗa akan Aaminat wallahi ƙarya nake sharrin zuciyane," ya ƙarasa maganar yana kuka, Abba kam ya kasa koda motsa ɗan yatsa ɗayane sai ido, Kamal ya kara cewa "maganar tana bin maza agida na itama sharri ne ƙazafi ne, nayi hakan ne dan na tozarta ta na rabu da ita, na Auri wata, sai gashi wadda na Aura ɗin neman yar uwata take, ina azabtuwa awajen ta ta rabani da duk wani abu da na mallaka, hatta iyayena ta rabani dasu," ran Abba in yayi dubu ya ɓaci ji yake kamar ya shaƙe Kamal ya huta, cikin ɓacin rai "Abba ya ce haƙika ka cuce ni kasa na juyawa ƴar ciki na baya, ƴar da tafi kowa ladabi da biyayya, tafi duk sauran ƴaƴana tausayamin, amma kasa na juya mata baya nake azabtar da ita, amma kaje kaida Allah ni nayafe maka," cikin kuka Kamal ya ce "haƙiƙa nine silar rushewar farin cikin ƴar ka, ko bakomai duniya ta hukunta ni yanzu na rasa duk wani abu na farin ciki, ina fuskantar tsanani," ya ƙarasa magnar yana shash-sheƙar kuka, Abba ya juya zai tafi, zuciyar sa cike fal da baƙin ciki da takaici, tabbas yayi gangancin yarda da abinda Kamal ya faɗa masa lokacin da ya saki Aaminat, cikin sauri Kamal yaja ramammun ƙafafuwan sa, ya tari Abba cikin muryar kuka ya ce "don Allah kayi min hanyar da zan nemi yafiyar Aaminat," cak Abba ya tsaya zuciyar sa tana wani irin tuƙuƙi, Kamal ya haɗa hannayen sa waje ɗaya ya ce "don girmin Allah na roƙeka ka taimaka min na nemi yafiyar ta wallahi in ban nemi yafiyar ta ba ruhina ba zai samu salama ba," Abba ya kalle shi sannan ya ce "yanzu Aaminat tana ƙarƙashin ikon mijin ta ni bazan iya yi maka hanyar da zaka gana da ita ba saida izinin Mijin ta," "na yarda kanema min alfarma awajen mijin ta in nemi yafiyar ta," Abba ya sauke ajiyar zuciya ya kalli Omar dake tsaye, yana jinsu, ya ce "Omar ka kira Abubakar ka sanar masa, in ya Amince ka rakashi, amma karka kuskura ya shigar masu gida," cike da girmamawa Omar ya ce "to Abba amma ni bazan iya ɗaukar wannan ƙazamin mutumin ya mashin ɗina ba," "kayi haƙuri ka raka shi, dole ce tasa" badan yaso ba ya ce "to" Abba ya wuce yashiga motar sa, Omar kuwa sai jan tsaki yake yana zabgawa Kamal harara, Dr Yarima ya kira yayi masa bayanin komai, Yarima bai musa ba jin ance Abba ne yasa akirashi asanar masa, hakan yasa ya amince amma bawai dan yaso ba, Omar kuwa takokin yadda zai ɗauki Kamal yake amashin ɗinsa acewar zai ɓata masa mashin, ganin bashida zaɓi ne yasa ya ce Kamal ya hau sutafi, yana hawa Omar ya figi mashin ɗin, Basu daɗe ba suka isa, aharabar gidan Kamal ya tsaya, Omar yashiga ya ce da Aaminat ta fito, amma bai faɗa mata kowaye ba, batare da tunanin komai ba ta zira hijabi ta bi bayan ya Omar, suna ƙarasawa harabar gidan tayi turusss ganin Kamal, rai a ɓacen-ɓace ta juya da niyar komawa, Omar ya ce "kiyi haƙuri ki tsaya ki saurare sa," "Babu abinda zanji daga gare sa sabi da haka kace ya tattara mummunar fuskar sa ya barmin gida ko nasa ayi masa korar kare" tana gama faɗin haka taci gaba da tafiya, Omar ya sha gaban ta ya ce "karki manta da cewa muma munayi wa Allah laifi kuma munemi yafiya ya yafe mana" tsayawa tayi tana huci, Kamal kuwa kuka yake yana cewa "dan Allah ki gafarce ni ki yafe min duk abinda na aikata miki dan Allah, "kaje na yafe maka duniya da lahira, Allah ya shirye ka," tana gama faɗin haka ta juya tayi ciki, "Ahamdulillah Allah na gode maka, da kanuna min wannan rana, Aaminat da mahaifinta sun yafe min," Kamal ya faɗa yana jan siraren ƙafafuwan sa, Omar ya kalleshi ya ce "inna ta gaida Ashsha," Kamal ya juyo ya kalli Omar yana goge hawaye, Omar kuwa yana gama faɗin haka ya zuge ƙofar gilashin ya shige cikin tafkeken Falon, INDO &💗 SALMA[8/12, 6:24 AM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION Shafi 30 Zama yayi ya kalli Aaminat dake razgar kuka ya ce "ke kuma kukan me kike!!" share hawayen tayi ta ce "nifa ba kuka nake ba" "kice dariya kike," sakin baki tayi tana kallon ya Omar, tsaki yaja gami da cewa "nifa wallahi haushin mutumin can nakeji kuma kika zauna kina yi masa kuka" "wai kai ana maganar mutane kana sako zaburarru," dariya yayi batareda yace komai ba, shiru ne ya ɗan ratsa na wani lokaci, Aaminat ta katse shirun da cewa, "Bari in kawo maka abinci" "ke nifa da tafiya zanyi amma tinda kin matsa ba komai" miƙewa tayi tana cewa " Ya Omar nawa niko ta Allah" harara ya maka mata, ƴar dariya tayi, ta nufi kicin, Bata jima ba ta dawo da wasu jibga-jibgan kuloli, na alfarma, ajewa tayi, ta buɗe ta zuba masa a wani ƙayataccen Filet, ta kalle sa ta ce "kuma sai ka cinye dika," "ke mai kika maida ni ne???" dariya tayi, batare da tace komai ba, saida ya ɗan kwashi ƴan mintina yana latsa waya, sannan ya fara cin abincin, Aaminat kuwa sai murna take tana mai ƙara godewa Allah, aranta ta ce "duniya juyi-juyi yau gani ga yayana agida na," ta ƙarasa zancen zucin tana murmushi, ƙaɗan yaci ya ce ya ƙoshi dama don karta ga ya ƙi ci ne, tana ya ƙara ci yana ya ƙoshi, ya miƙe ya ce "ni kinga tafiya ta sai wata rana," yanzu tafiya zakayi??" "A'a kwanciya zanyi," ya ƙarasa maganar yana dariya, ita ma dariyar tayi, ya nufi kofa, bin bayan sa tayi domin yi masa rakiya, sallama sukayi, ya hau mashin ɗinsa ya ɗaware, Abba kam tunda ya isa kasuwa, ya kasa komai sai tunanin Aaminat, kozata iya yafe masa, ko bazata yafe ba, wannan tunanin ne yake tayi masa juyi a ƙwa-ƙwalwa, in ya zauna sai ya tashi, sai zarya yake, Hamza ma tunda Abba ya bashi labarin komai, jikinsa yayi sanyi salam har dare yayi Abba ya koma gida, jikinsa amace, tunda ya koma yake zazzagawa Mama ruwan faɗa, banda kuka babu abinda take, Umma ce ta samu nasarar, bashi haƙuri kuma ya haƙura, washe gari ma koda Abba ya tashi bai nunawa Mama bambanci ba sai nasihohi da ya haɗa su ita da Umma yayi musu, Bayan wata ɗaya. Fati ce zaune, ta zabga tagumi sai hawaye take, kallo ɗaya zakayi mata kasan tana cikin mawuyacin hali, ta rame ta ƙanjame, tayi wani ragwaf-ragwaf kamar tsohuwa, saitayi yun ƙurin tashi saita kasa, tun safe take zaune awajen har shabiyu na rana tayi, amma ta kasa koda motsawa, in tayi kamar zata tashi sai jiri ya ɗebeta ta koma tayi jagab, tana cikin wannan halin Ahmad ya shigo, hannunsa riƙe da waya ya manna ta akunnan sa yana waya cike da jin daɗi, wucewa yazoyi ta gefen Fati, tayi saurin cafke ƙafarsa, ya harbatsar da ita gefe, cikin rawar murya ta ce "Allah ya isa tsakani na da kai macuci kawai, ka yaudareni kaci amana ta," cikin zafin rai ya dubeta ya ce "kekika yaudari kanki, duniya ta rufe miki ido kika kasa gane asalin waye ni," cikin kuka da taurin kai ta ce "mugu Azzalumi Allah saiya saka min, yau kwana biyu baka bani ci ba baka bani sha ba ga duka na rana daban na dare da ban," ta ƙarasa maganar tana wani galabai-taccen kuka, shi kuwa ko ajikin sa, yayi gaba, cike da tsiwa da rashin kunya Fati ta ce "Allah ya isa mugu kawai ɗan is...." marin da ya kifa mata ne ya hana ta ƙarasa maganar, ya ƙara sharara mata wani azababban marin mai rikitar wa, saida taga taurari sun gifta, shiɗewa tayi ta kasa kukan, cikin ɓacin rai ya ce "niki ka zagi, an faɗa miki ni ɗan asara ne da zaki zagi iyaye na, na ƙyaleki, to ki sani ni iyayena basu ce jeka ka gani ba,.." ya numfasa yaci gaba da cewa "ƴar iska ta wuce ke, wato kin samu duniya kin banzatar da iyayen ki, to kisani nine ajalin ki muddin baki daina ɗagamin harshe ba," cikin mawuyacin hali da azaba, Fati ta fara magana muryar ta dakyar take fitowa ta ce "Ahmad kayimin duk abinda ka gadama, Allah ne ya jarabce ni, bazan taɓa ganin laifinka ba, sakaiyar Aaminat ce da waɗan da na cuta na yaudare su, duniya kenan, kaico na da na kasance, mai son zuciya, duniya ta ruɗeni, na afka inda ajali na yake," ta ƙarasa maganar tana gursheƙen kuka, Ahmad jikin sa yayi sanyi, ya nufi inda Fati take, yana ƙoƙarin kamata ta ce "A'a Ahmad bancan-canti ka taimake ni ba, kaɗan na gani daga cikin abinda na aikata, amma don Allah idan Allah yayi na koma gareshi ka nema min yafiyar ƴar uwa ta Aaminat da iyayena, kane mamin yafiya a wajen mahaifiya ta da na juyawa baya," zuwa yanzu Ahmad tausayin Fati ya gama mamaye zuciyar sa, ya matsa kusa da ita ya ce "kiyi haƙuri da abinda nayi miki duk da nasan ba a son raina nake azabtar da ke ba" murya na rawa ta ce "baka da laifin komai, hakan jarabta ce daga uban giji, kuma ta silar hakan nayi na damar abinda na aikata abaya,!" Ahmad yayi murmushi, ya ce "Fati kin gane gaskiyar abinda kika ai kata ba dai-da bane!!!??" ta gyaɗa kai, alamar eh, "to ni da kaina zan taya ki roƙar ƴar uwarki ta yafe miki, kuma zata yafe miki," share hawaye tayi ta dubbeshi, ta ce "banajin Anty Aaminat zata iya yafe min, domin kuwa abun da na aikata mata ya munana, kuma ko ba komai yanzu nasan Aaminat ta wuce inda nake zato" "hakane amma ina mai kyauta-ta zaton zata yafe miki in sha Allah, gigiza kai Fati tayi tana ƙara tuno irin cin zarafin da tayi wa Aaminat abaya, Ahmad ya ce "kitashi kiyi wanka" ƙoƙarin tashi ta farayi, Ahmad ya taimaka mata ta tashi, ya raka ta banɗaki, tayi wanka, kafin ta fito ya haɗa mata shayi, tana fitowa tasha shayin sosai dan kuwa muguwar yunwa takeji, Ahmad ya kalle ta ya ce "Fati kinsan me" ta ce "A'a" ya ce "maganar gaskiya ni ba mai kuɗi bane hassali ma iyaye na a ƙauye suke, ni nataso ne a makarantar allo, daga bisani na samu aikin shara da bawa fulawoyi ruwa a gidan su Abubakar mijin yayar ki, daga baya suka maidani Direban su hakan yasa na iya mota, kuma nake hawa mota kala-kala, kikayi zaton ni mai kuɗi ne, a ranar da muka haɗu dake ma aike na akayi," ya numfasa, kana ya ɗora da cewa "gidan nan ma da muke zaune mallakin Yarima ne, banawa bane bamu da gadon sa, lokacin da na faɗa masa zanyi Aure ne ya bani wannan gidan na zauna na wani lokaci," tuni hawaye sun wanke fuskar Fati, tabbas duniya makaranta ce, ta gama ruwan idon da yaudare yaudare ƙarshe ga inda Allah ya jefota, share hawayen tayi ta ce "naji kuma na yarda zan zauna da kai, amma don Allah tunda kasan inda Aaminat take kayi min Jagora, na nemi yafiyar ta," ajiyar zuciya ya sauke, kana ya ce "karki damu yanzu zamuje kuma zata yafe miki," Fati ta miƙe tana cewa "muje yanzu" shima tashi yayi ya mara mata baya, Aaminat tana zaune ta harɗe ƙafa, ƴar aikin ta tashigo, ta ce "ranki ya daɗe kinyi baƙi," "baƙi kuma" Aaminat ta maimaita cikin sigar tambaya, Na'ima ta ce "eh ranki ya daɗe, kuma naga kuna shigen kama da ita," Aaminat a ranta ta ce "ko suwaye su Umaima da Siyama dai jiya sunzo to ko Iman, ce" afili kuwa ta ce "ki saukesu a Falon baƙi kice ina zuwa" cike da girmamawa ta ce "to" ta nufi inda su Fati suke, Aaminat kuwa ɗaki ta nufa ta sako ƙaton hijab sannan tayi Falon Baƙi, da sallama ta shiga ɗakin, rassss gaban ta ya faɗi, lokacin da idon ta ya sauka akan Fati, ja baya tayi tana watsawa Fati wani irin kallo, "mai ya kawo ki inda nake ko kinzo ki ƙarayi min wani ƙazafin, kina so kice na ai kata wani abun ne?!!!" ta ƙarasa maganar cikin hargowa da ɗaga murya, Fati kuwa wani kuka ta saki, mai cike da nadama da danasani, ta ce "don Alla.....!!!" Aaminat ce ta katse ta da cewa "mai kike so kice dani mai zaki ce ki tattara yanaki-yanaki ki barmin gida, azzaluma, kawai, butulu!!!" cikin kuka Fati ta ce "nazo ne nanemi yafiyar ki koda bazaki yafe min ba, ina roƙonki da kiyi min gafara ki yafe min duk abinda nayi miki don Allah, kitaimaka min" ta ƙarasa maganar tana durƙushewa agaban Aaminat, tuni jikin Aaminat yayi sanyi, ta shiga share hawayen ta, Fati kuwa kuka take tana ƙara nemar gafarar Aaminat, cikin kuka Aaminat ta ce "Fati na yafe miki kinji ke ƴar uwata ce, ki daina kuka," ta ƙarasa maganar tana rugume Fati, kuka suka shigayi, babu mai rarrashin ɗan uwan sa, Ahmad ma matsar hawaye yake, Aaminat ta share hawaye ta fara rarrashin Fati har saida tayi shiru, sannan ta ƙara nemar yafiyar Aaminat, Aaminat ta ce "na yafe miki, na daɗe ina jiran wannan ranar tazo, ranar da zamu haɗe kanmu," Fati tayi murmushi mai tafe da hawayen farin ciki, sai a lokacin Aaminat ta lura da Ahmad, suka gaisa, sallama yayi musu da niyar da yamma zai dawo ya ɗauki Fati, Fati taji daɗi sosai, duk wunin ranar, da yamma Ahmad ya dawo ya ɗauketa suka koma gida, Haka rayuwa taci gaba da tafiya ko wane ɓangare farin ciki ya wanzu, Akwana a tashi rayuwa tana ƙara shuɗewa sanyi zafi damuna rani bazara waiza tana ƙara juyawa, Yau ta kasance ranar Juma'atu Babbar rana, Aaminat tana zaune a ɗakin ta, ta zabga tagumi, idon ta yayi jawur, Yarima ya shigo ɗakin da sallama, ta amsa ciki-ciki, zama yayi kusa da ita, ya kama hannun ta, ya ce "mai yafaru, naga kina kuka,??" kauda kai tayi gefe, yasa hannu ya rungumota ya kwantar da kanta cikin ƙirjinsa ya ce "bana son ganinki cikin damuwa, ki sanar min maiyake damun ki," murya asarƙe ta ce "inason na ga ɗana amma har yau shiru Fati har ta haihu," murmusawa yayi cike da son kwantar mata da hankali ya ce "haba abar ƙauna ta, kar hakan ya dameki kinji, wani jinkirin alkairi ne, bamu san alkairin dake tattare da mu ba," ajiyar zuciya ta sauke cikin shagwaɓa ta ce "kullum haka kake cewa" murmushi yayi yana shafa kanta, ya ce "abinda nake so dake kidaina sa kanki adamuwa, Allah ne kaɗai yasan iyakacin alkairin da yake tare da hakan," murmushi tayi tare da cewa "amma inaso naga jarirai," ƴar dariya yayi ya ce "wani lokacin kamar yarinya haka kike, wato jarirai kike so ko" murguɗa baki tayi ta ce "eh jari-rinaye nake so" ta ƙarasa maganar tana tashi, fizgota yayi gami da cewa "ina zaki ki barni bayan ke nake jira" turɓune fuska tayi kamar gaske ta ce "nika cika ni" murmusawa yayi gami da cewa "to shike nan na ƙyale ki, kije inda zaki , daɗin ta ina da wata matar," ƴar dariya tayi ta ce "wai E'iye" "A'a ba ita ba" turɓune fuska tayi ta fara dire-diren ƙafa, shikuwa banda dariya babu abinda yake. Misalin ƙarfe 8:00 na dare Abdussalam, Abdurrahim Abdulmajid Abdulkereem, Nana Kadija Nana Hauwa Nana Fareeda, Ummi Dadda, zaune suke A babban Falo suna hira cike da jin daɗi, Ummi ta muskuta gami da cewa "Auta anya kuwa lafiyar ka ƙalau," "lafiya ta ƙalau mana mai kika gan?i" ta murmusa gami da cewa "banga komai ba kawai naga baka magana kwana biyu," Dadda ya ce "kinmanta Babban mutum kenan,?? ai ba kasafai ya fiya magana ba," Ummi ta ce "nifa ba Dadda na tambaya ba" dariya suka sa, Nana Fareeda ta ce "yau zamuga Dad da Ummu a rana" dariya sukayi cike da jin daɗi, Dadda yayi gyaran murya hakan ya tabbatar musu zaiyi muhimmiyar magana, kowa ya maida hankalin sa kan Dadda, Dad ya ce "dama magana ce akan Kadija mahaifin Omar ya sameni da maganar Auren su, to sai nace masa ya ɗan bamu lokaci, saboda inaso a haɗa Auren da naku," gaba ɗayan su suka sunkuyar da kai ƙasa, cike da jin kunya, Abdulkareem kuwa yana so yayi dariya ko guda ɗaya ce amma ya kasa, Kadija kam tunda taji inda Dad ya dosa ta miƙe tayi ɗaki, Ummi ta gyara zama kana ta ce "to Alhamdulillahi, saiku sanar da iyayan matayan naku, za'azo ayi maganar manya" Dadda ya ce "nayi magana amma kaf cikinku babu wanda yace komai," Abdulmajid ya taɓo Abdussalam, cikin raɗa ya ce "kaine Babba kai zaka fara magana," wata uwar harara ya zabga masa, Ummi ta ce "kufa muke jira kuyi magana a ina abokanan haɗin naku suke???" Abdurrahim ne yayi ta maza, ya ce "Dadda idan munyi shawara zamu faɗawa Uncle Rabi'u" ya ƙarasa maganar yana sosa ƙeya, Abdulkareem kuwa dariyar da yake dannewa ce ta samu nasarar kufce masa, ya farayi ba ƙaƙƙautawa, Dadda ma saida ya murmusa, Ummi kuwa sakin baki tayi tana kallon sa hada leƙa fuskarsa don ta tabbatar dariyar yake, sai da yayi mai isarsa sannan ya dubi, Abdussalam dake faman shafa kai ya ce "zamusha biki harda yada zani," sai yanzu Ummi ta tabbatar bai fuskanci inda zancen Dadda ya dosa ba, Abdussalam kuwa kallon sa yayi azuciyar sa yace "lallai yaro man kaza, kana taka Dadda na tashi," afili kuwa cewa yayi, "zaku yaga kantin kwari ba zani ba," Abdulkareem kuwa ko ajikin sa, sai nishaɗi yake, Dadda ya dubi Abdulkareem, ya ce "kai kuma in kayi shawarar waza kafaɗawa,??" danda nan annurinn fuskar Abdulkareem ya gushe, ya saki baki yana bin Dadda da kallo, Dad ya ce "eh dakai nake" Abdulkareem ya ce "No Dadda, ni babu Aure a tsarin rayuwa ta," Dadda ya murmusa ya ce "hakan ne yasa na nema maka Abokiyar haɗi, kuma mun gama magana da iyayen ta, ina fatan bazaka watsa mana ƙasa a ido ba," zuwa yanzu Abdul ya saduda, ya sallama Nana Fareeda ta ce "kuce zamu yaga zani" "ke rufe mana baki mara kunya ana magana kina magana," Dadda ya faɗa fuska aɗaure, Abdulkareen kuwa sai mi-mi yake da baki, Dadda ya ce "ka amince wa hakan,??" yana so ya ce shi bai amince ba amma ya kasa, Abdurrahim ya ce "tunda kukaji yayi shiru ai ya amince, kawai kunyarku yakeji, " Dadda ya ce "to Alhamdulillah Allah kaine abin godiya, addu'a sukayi kamar yadda suka saba in sukayi zaman tattaunawa, kowa yanufi makwancin sa Abdul kuwa yana so ya tambayi Dadda wa zai Aura masa amma ya kasa, INDO & Salma Auta [8/14, 10:55 AM] INDO: *AAMEENAT* (Bazawara) Littafin Haɗaka ne💪🏾 Ayeesha Abdulkareem *INDO* Daga MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION Tare da Salma Abdulkareem *AUTAR JARUMAI* Daga JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION Shafi 31 Washe gari da safe Ummi tana kicin ita da Nana Kadija, Abdulkareem ya shigo da sallama, amsawa sukayi, Ummi ta ce "ɗan Ummin sa ka tashi lafiya," ƙasa yayi da kai ya ce "Ummi ina kwana" murmusawa tayi ta ce "lafiya lau ƙaramin ɗa," wata ƴar ƙaramar kujera yaja ya zauna, gami da cewa "Ummi wai kinaji kina gani Dad ya ce Aure zai min kuma ni ban san ko wace zai Aura min ba" Ummi ta murmusa kana ta ce "kayi haƙuri da komai, kaji zaka santa kuma nasan zaka sota, ka taushi zuciyar ka, kayiwa mahaifinka biyayya kar hakan ya dawo da bara bana, a baya kowa bai ji daɗin abinda ya faru ba,.." ta numfasa taci gaba da cewa "ina so kazama ɗan da ake kira ɗa, ka bawa mutane mamaki, kabi duk abinda mahaifin ka ya ce," share hawaye yayi kana ya ce "in sha Allahu zanyi biyayya wa mahaifina zan bi duk abinda ya ce," shafa gefen fiskar sa tayi, cike da kulawa ta ce "kaje wajen ƴan uwan ka" "to" ya ce sannan ya tashi, kai tsaye yanufi ɗan ta ƙaitaccen Falon su, tsayawa yayi shi bai shiga Falon ba shi bai juyo ba, Abdurrahim ya ce "Ango kasha ƙamshi," tsaki Abdul ya ja ya ce "to ya ranka, ko kana baƙin cikin zamu angwance tare" "kutt lallai yaro ya girma iyeee," Abdulmajid ya faɗa yana dariya, Abdussalam ya ce "karku takurawa Auta Dad ya subirbiɗa ku" dariya suka sa, Abdulkareem ya ƙaraso inda Abdussalam yake, ya kwanta ya tada kai da cinyar sa, fira suka shigayi suna dariya cike da ƙaunar junansu, Ɓangaren Dad ma cikin kwanaki ƙalilan suka gama maganar Auren su Abdussalam, duk inda sukaje neman Aure an basu cike da gaskiya da amana, nan aka saka bikin wata biyu. Yarima ne zaune kusa da Inni yana zuba mata tsiya iri da kala, Aaminat kuwa banda murmushi ba abinda take, tana matuƙar son ganin sharholiyar su Inni, E'iye ce tayi sallama, suka amsa, Inni ta ce "bashakka Mijin ki ya juya miki baya kina gani har wata ƙiba yake," dariya E'iye tayi gami da cewa "ai naga alama, tunda yayi sabon Aure ya sakeni" Yarima ya ce "waya ce na sakeki, ina ni ina wannan ɗanyen aikin," dariya sukayi baki ɗaya, Inni ta kalli Aaminat ta ce "ke kin yarda tsohuwa ce kishiyar ki??" Aaminat tayi ƴar dariya, ta ce "yazanyi ai tare na gansu," Yarima ya ɗan harare ta ya ce "eh tare kika ganmu ko zaki raba mu ne" "ai bazaku rabu ba" dariya sukayi cike da nishaɗi. Akwana Atashi ba wuya agurin Allah, kwanakin da aka ɗiba na Biki sun zo, yau ta kama Asabar inda ake ta shirye shiryen ɗaurin Aure, ta ko ina gida ya cika, sai hada-hada ake yi. Umaima ce zaune ita da Aaminat da Fati, suna hira, cike da farin ciki, Aaminat tana tayi wa Umaima ƴan faɗa da nasihohi, da dubaru na zaman Aure, Umaima kam jikinta yayi sanyi salam, in ta tuna gobe zata bar gida sai jikinta ya ƙara sanyi, Ɓangaren gidan su Abdulkareem ma ba'a mgana gida ya cika taf, ciki kuwa hadda su Ammi da Anti Zainab, sai shagali ake, Washagari misalin ƙarfe 11:30 Dubban mutane suka shaida ɗaurin Auren Abdussalam Aminu mai kasuwa da Iman Usman Kabeer, Abdurrahim Aminu mai kasuwa da Umaima Haruna, Abdulmajid Aminu mai kasuwa da Salma Rabi'u, Abdulkareem da Husna, Habibu, Omar Haruna da Kahdija Aminu mai kasuwa. Alhamdulillah, Anɗaura Aure lafiya, taro ya tashi lafiya. ana idar da sallar magrib a nufi kai kowace Amarya ɗakin ta tare da ƴan uwa da abokan arziki. misalin tara na dare Abdulkareem ne zaune a ɗakin Dadda, Abdulmajid ya shigo, yana cewa "Auta lokaci yana ja ka tashi mutafi," Abdul ya yamutse fuska gami da cewa "kuje mana ni sai gobe" "haba Auta yazaka ce haka ƴar fa mutane ce ka barta ita kaɗai ta kwana agida," Abdussalam ne ya shigo tare da sauran ƙannan nasa, Abdul suka sa gaba sunayi masa faɗa da nasiha, dakyar suka samu ya tashi, sukaje sukayi wa su Ummi sallama da su Dadda, saida sukayi musu faɗa sosai da rarrashi da jan hankali, sannan suka tafi, Abdul sai ɓarza kuka yake yi, su ma kansu su Abdulmajid sai da su ka yi kuka amma ba kamar Abdul ba. kowa Abokanan sa sun rakashi gidansa. Abdussalam, da Iman suna gabatar da sallar nafila da godiya ga Ubangiji suka haye gado domin bacci. Abdulmajid suna zauna shida Salma sun idar da sallar nafila, ya kalli Salma dake gyan-gyaɗi cike da so da ƙauna ya ce "Salma kici abinci sannan mu kwanta na san kin gai." ni na ƙoshi" wani tattausan murmushi ya sakar mata gami da cewa "To ba komai" ta tashi ta ɗane gado tare da addu'oi na bacci. Abdurrahim da Umaima cikin kwanciyar hankali gami da so da ƙauna su ka kasance a cikin wannan dare na musamman a garesu. a ɓangaren Omar da Kahdija ma hakance ta kasance. Abdulkareem yana zaune akan kujerar Falo, ya lumshe ido, yayi nisa a duniyar tunane-tunane, Husna kuma tana daga gefen sa sai sharar hawaye take, kuka take mai cin rai amma bakowa ne zai san tana kukan ba, dan kuwa kuka ne mara sauti, shikan shi Abdulkareem ɗin baisan tanayi ba, Washe gari da safe kowa ya tashi shida Amaryar sa cikin farin ciki da annashuwa, kowa na kula da masoyinsa, "Husna" ya kira sunan ta cikin sarƙaƙƙiyar murya, cike da ladabi ta juyo tare da risinawa, ta ce "na'am" murmusawa yayi gami da cewa "Siyama kina sona ko dole akayi miki,??" ya watso mata tambayar gami da tsira mata idanu, ƙasa tayi da kai kana ta ce "ina sonka na daɗe da sonka acikin zuciya ta kawai ina kauda kai ne, ko alokacin da kake son Aaminat lokaci lokaci nakanji ina kishin hakan, ko da yaushe addu'a nake Allah ya nuna min ranar da zan zamo mata agare ka, sai dai kash baka sona" ta ƙarasa maganar tana sharar ƙwalla, da sauri yasa hannu yana share mata hawayen cikin nutsuwa ya fara magana da cewa "ba wai bana sonki bane, nayi tunanin mahaifina ne yasa iyayen ki sukayi miki dole shiyasa, ko jiya da naji kina kuka nayi tunanin bakya sona ne" ya numfasa, kana ya ce "ina sonki Siyama ba tun yauba sai daga baya na gane ina sonki," wani murmishin farin ciki ne ya kufce mata, ta sa tafukan hannayen ta ta rufe furkar ta, wani ni'imtaccen murmushi ya sakar mata, yana kallon, kyawawan hannayen ta da sukaji lalle, ƙoƙarin tashi take taji ya ɗauke ta calak, ya nufi uwar ɗaki. (😳kutt!!! Abdul!! Indo ta tsorata😳) Bayan sati biyu da biki duk wani wanda ya halacci taron ya koma gida. Ɓangaren Yarima da Aminat ma soyayya ba kama hannunn yaro, Haka ɓangaren Abdulkareem da Siyama ko da yaushe suna manne da juna, tsakanin Abdulkareem da Aaminat kuwa sun manta da sun taɓa wani abu wai shi soyayya, zumunci suke sosai dama Abdilkareem da Yarima Aminan juna ne Siyama da Aaminat ma tamkar ya da ƙanwa, Ɓangaren Fati ma da Ahmad sun watsar da duk wani abu, sun kama ga Allah rayuwa suke cike da son juna, suna da ƴa guda ɗaya wadda taci sunan Aaminat ana kiranta da Meenal, Ɓangaren Kamal ma Alhamdulillah rayuwa tayi kyau, Umma da Mama ma sun haɗe kansu tamkar wani abu bai taɓa faruwa ba, Alhaji Aminu mai kasuwa da Alhaji Sadiƙ, Amintar su kullum ƙara gaba take duk inda kaga ɗaya to ɗayan ma yana nan, Ammi da Anti Zainab ma rayuwa suke tsaftatacciya. Anti Rahina ma da su Yarima harda su Abdul kai ahaɗe yake ita ce Babba ita da Anti Maryam, ko wane ɓangare kagan su gwanin ban sha'awa, in ba faɗa maka aikai ba bazaka ce ba dangi ɗaya bane. Bayan shekaru bakwai, Allah ya azurta Abubakar (Yarima) da Aaminat da ƴaƴa kyawa wa guda biyu, mace da namiji, na farkon yaci sunan Abdulkareem ƙanwar shi kuma taci sunan E'iye Rukayya ana kiran ta Nihal, Ma sha Allah, saidai muce Allah ya ƙaro zuri'a mai Albarka da kwanciyar hankali na har a bada, Ɓan garen Abdurrahim da Umaima ma sun Haifi ɗa ɗaya Samid. Abdulkareem da Husna (Siyama) Allah ya basu kyautar ƴaƴa biyu, ta farkon mai sunnan Ummi Kareematu tana amsa suna, Najwa, Nabiyun kuma yaci sunan Mahaifin Siyama, Habibu, ana kiran sa, Abba, Alhamdulillah su Ya Omar da Kahdija Allah ya basu ƴa, ɗaya taci sunan Umma Fa'izatu ana kiran ta, Neehla, Abdussalam da Iman ma Allah ya basu kyautar ƴaƴa Biyu, ɗaya yaci sunan Dadda yana amsa, Hanif, Sai Hanifa, Abdulmajid da Salma ma suna da ɗa ɗaya, wanda yaci sunan Uncle Rabi'u. Haka rayuwa taci gaba da tafiya ko wane ɓangare sai Farinciki da ƙaunar Juna, Ziyara kam ba kama ƙafar yaro, lokaci lokaci sukan haɗa kwarya-kwaryan taro, ƴaƴan suma sunyi shaƙuwa sosai da ƴan uwan su, SAIDAI MUCE ALLAH YA ƘARA ZUMINCI DA HAƊIN KAI BAKI ƊAYA. Alhamdulillah Alahamdulillah (Mun taƙaita labarin nan sabida wasu ƴan dalilai da abubuwa da su ka yi mana yawa, mu na fatan kun yi farin ciki da karantawa wannan Littafi, Allah i bamu ladan Alkairan cikinsa, kusakuren cikinsa kuma Allah i yafe mana baki ɗayanmu) INDO&AUTA