[8/13, 4:06 PM] Masoyiya 🤗🔥: https://chat.whatsapp.com/I8iDBWAiJUS6qX9VZqRrlQ # SQUAD 2024 A WANI COMPANY BY HAUWAU OMAR CUTIE MEEYRAT MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS Page 2, Washegari tun wuri ya tashi shiryawa yayi cikin cuz Black masu matuƙar kyau da shaƙi, hannunsa riƙe da yar ƙaramar back ya fito yana tafiya cikin isa da ƙasaita ya nayin yadda yake tafiya sai ka ɗauka ta zame masa dole ne. security ne suka rufa masa baya motoci uku suka yi combai jeri suke tafiya har suka isa cikin katafaren Company mai matiƙar kyau da girma suna isa ya ɓale murfin motar ya fito left ya hau zuwa bene na biyar in da office ɗinsa yake a hankali ya murda handle ya shiga, wow shikansa office ɗin abun kallone Office ne mai matiƙar kyau zama yayi ya na cire riga dake saman kayan Zaune ya ke cikin Office talphone pole dage gefansa ya janyo wasu Numbobi ya danna da basu shige biyar ba "turomin Suhail" ya faɗa ya na aje wayar ɗago kansa yayi Masha Allah babban mutum ne wanda a ƙalla zai kai shekaru (60) haka farine tass ya ɗaure gashinsa da wani ɗan ƙaramin ribom. Nocking aka yi duban ƙofar yayi, da sauri kuma ya miƙe yana rungumar wanda ya shigo cikin office ɗin da kansa ya zaunar da shi shima ya samu waje ya zauna kallon Suhail yayi wande idansa ke lumshe wannan ɗabi'a ce ta Suhail koda yaushe zaka ga idanunsa a lumshe kamar wanda kejin bacci Suhail a salin kyakyawane kuma ɗan gayu irin dai mutanan nane da ake wa laƙabi da classic aje'butter ya na da pink leps sai ƙwayar idanunsa da ta kasance brown, gashinsa ya sauka har baya. Miƙa masa takarda dake hannusa yayi duk da yasan haka bamai yuwa bane dan yana da tabbacin tun da suhail yace ba inda zasa to bafa zaije ɗin ba murmushi yayi yana karɓar takarda sai da yagama karantawa tass kafin ya ɗaga kai yana kallon datinjon wanda ya kasance mahaifi agaresa "yanzu dad da gaske sai na tafi wance garin? da ku ka turani kadai san babu wanda nasani acen kuma ban taɓa zuwa ba why dad mai yasa?" shiru mahaifinasa yayi yana kallonsa dan ya rasa me zaiyi tasowa yayi daga inda ya ke ya zo dab da ɗan nasa yana dafa kafaɗarsa "kayi haƙuri son wannan tafiyar dole ce kai ya kamata kaje ka cigaba da kulamana da wancen Company dake nigeria banaso abun da yafaru abaya ya sake faruwa" "shikenan dad naji na kuma amince zanje mudum hakan zai faranta maka rai" wani irin yalwa tacen murmushi yayi yana sake rungume sa "Thank y my son Thank you" "Never mind dad" ya faɗa yana fita daga Office ɗin shifa harga Allah baya son zuwa ko ina ya amsa ne kawai dan farin cikin mahaifinsa wanda ya kasance gatansa. "Ayrah" "Ayrah" shine abun da Mama ke faɗa tana tsaye a jikin ƙofar ɗakin fitowa tayi tana turo baki ita ala dole an takuramata sanye take cikin atamfa maroon mai adon ganye green "ni zan fita ba daɗewa zanba kinji" "Tom Mama Allah ya tsaremin ke" tafaɗa tana shiga ɗakin murmushi Mama tayi tana fita abunta sai da tayi tafiya mai nisa kafin ta isa gidan alh hadi wanda ke nesa da anguwar su tana shiga ta isa part ɗin hajiyar, da karamawa ta tarbeta suka gaisa dan hajiya sarai matace mai matiƙar kirki da karamci abunta ko kaɗan bai rufemata idoba ta na matuƙar tausayin su Ayrah don yawanci ma anan suke samun abinci da zasuci. "Dama Maman Ayrah abunda yasa nace a kiraki wani alkhairi naji shine nace zan faɗamiki ko Allah zai sa a dace" murmushi Mama tayi tana duban hajiya sarai "Wollah kinga ɗazu ne alh ke faɗamin wai Company da suke aiki ana bukatar ma'aikata nayi matukar jin daɗin haka na ce masa kuma in Allah ya yarda zan kiraki na faɗamiki idan mun gama magana sai a samawa Ayarh ko ya kika gani?" farin ciki mara misaltuwa ne ya rufe Mama tama rasa mai zata ce murmushi kawai take tabbas wannan abun farin cikine agaresu "Nagode sosai tabbas keɗin ta dabance kuma ke mai son muce nagode sosai" Mama ta faɗa tana hawaye "haba Aminatu menene abun kuka anan shin dan nayiwa Ayrah abu shine sai kin tamin godiya karki manta Ayrah fa tamkar ya take a wajena " "Hakane hajiya tabbas Ayrah yar'kice" A hankali ya ke ɗagawa mutane da suka rakosa airport ɗin hannu har ya yi gaba ya dawo da gudu yana rungume mahaifin nasa tabbas ya san zaiyi kewa zai yi kewar Daddyn'sa "I really miss you dad" "Miss you too son ka kula da kanka kaji" ya faɗa shima yana share hawayen dake zubo masa Austiralia to Nigeria sai dai muce Allah ya sauke ka lafiya Suhail... [8/13, 4:06 PM] Masoyiya 🤗🔥: https://chat.whatsapp.com/I8iDBWAiJUS6qX9VZqRrlQ # SQUAD 2024 A WANI COMPANY BY HAUWAU OMAR CUTIE MEEYRAT MARUBUCIYAR A'ISHA LABIBA. AND NOW A WANI COMPANY. MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS *"Wannan labarin mallakin mai shine kawai ban yarda wani ko wata ya sauya min labari ta kowace sigaba idan kuma hakan ta faru bazan kyale ba"* *BISMILLAHI RAHAMANI RAHIM* *Duk kan yabo da godiya sun ta* *bata ga Allah Subhanahu wata'ala* *mamalakin sammai da ƙasai* *Allah kai daɗin tsira a bisa shugaban mu Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama tsira da aminci su tabata a garesa da Ahalinsa da sahabbansa dama wainda suka bisa a tafarki mai kyau daga yanzu har izuwa ranar alƙiyama Ep one. Yau ta kama Ranar lahadi a yau kuma duk kanin wasu ma'aikata ke hutawa a gidajensu Hadarine Sosai ya haɗo Garin yayi baƙi wata irin iskace ke kaɗawa mai haɗe da ledoji da ƙura mai baɗe idanun mutane. Gajimare ta yi wani irin baƙi tsawa ake mai haɗe da walƙiya yanayin yadda garin yayi duhu na iya tabbatar maka dacewa ruwa na iya sauka a kowane irin lokaci. tsugune ta ke a jikin bishiya ta kifa kanta a kan gwiwarta duk da wannan hadarin da ya haɗo hakan bai sa taji tsoro ba wani bawan Allah ne yayo gurin, da sauri ya karasa ya na tambayarta lafiya? Ɗago kai ta yi ta kallesa da rinanin idanunta wanda suka yi wani mugun ja daga gani kasan ba ƙaramin kuka ta yi ba Woww Masha Allah tsarki ya tabbata ga Allah subhanahu wata'ala da yayi Wannan halita farace tass gashinta ya kwanta har gadan bayanta gawani saje da ya kwanta a gefe-gefe n fuskarta tana da ɗan ƙaramin baki sai hancinta dogo mai tsini masha Allah yarinya ta haɗu matuƙa ta na da tsayi sosai ga wani uban Sharpe da ya fita a jikinta. Tashi ta yi bata ce masa komai ba ta fara tafiya jijiga kansa kawai yayi yai gaba abinsa ya na tinanin ko me yasa yarinya kamar wannan tafito tsakiyar layi tana kuka duk da wannan uban hadarin da ya haɗo wanda a koda yaushe ruwa zai iya zuba.. Tafiya take a hankali kasan cewar ita ba ma'abociyar sauri bace wata tsawa da akayi yasa tai saurin rintse idanunta tana toshe kunnanta sunan Allah ta ke ambata cikin yar ƙaramar Muryarta wadda idan ba kana kusa ba bazaka taɓa jin abun da ta ke faɗa ba,ta kai kusan 5 minute a haka kafin a hankali ta buɗe idanun na ta kamar mai tsoron wani abu Ruwane ya fara zuba kamar da bakin ƙwarya yayin da ruwan ke zuba tare da wata tsawa da ke tashi cigaba da tafiya ta yi a hankali duk da ta'taka abu a ƙafarta hakan baisa ta tsaya ba harta ƙarasa cikin ɗan ƙaramin gidan nasu dake anguwar lokogoma. Da sauri ta ƙarasa cikin ɗakin tana haki faɗawa kan wata yar taɓarma tayi dake shimfiɗe a tsakar ɗakin a hankali kuma jikinta ya fara wani irin rawa tana fitar da wani irin wahalala numfashi Gaba ɗaya ta fita hayyacinta babu abin da take ambata sai Mamah Mamah washh Allah na mutuwa zanyi shine kaɗai abun dake fita daga bakinta Fitowarta kenan daga cikin bayin buɗe ɗan yalolon mayafin dake ƙofar tayi gabanta ne yayi wani mugun faɗuwa dan-danan zufa ta shiga keto'mata duk da ruwan saman da ake ƙarasa shiga cikin ɗakin tayi da sauri jawota tayi jikinta ta rungume wasu zafafa hawaye ne ke fita daga fusakarta da sauri kuma kamar wadda aka tsikara ta tashi ta nufi cikin ɗakin wata yar ƙaramar leda ta ɗako ta nufi yar randar dake ɗakin ta ɗibo ruwa tsayawa tayi tana nazari shin taya zata bata magani bayan tin safe ruwa ne kaɗai a cikinsu? hawayene ya ƙara gangaro mata. daga hanayanta sama tayi gaba ɗaya ta kasa furta komai sai hawaye dake ambaliya akan fuskart Ƙarasowa wajan tayi a hankali ta ɗagota tana bata maganin, Kwantar da ita tayi a saman cinyarta ta na shafa sumar kanta a haka har bacci ya ɗauke su Washegari. A hankali take buɗe idanunta wanda suka mata wani irin nauyi kwance ta ganta kan cinyar Mamah da ke zaune ta jingina da bango kenan a haka Mamanta ta kwana tafaɗa tana jin wani irin tausayi mahaifiyartata da sauri ta ƙarasa jikinta ta rungume ta murmushi Maama tayi dama ta daɗe da tashi batason ta yi motsine ta tada yar'tata "yanzu Mama a haka kika kwana? meyasa baki tasheni ba?" ta faɗa idanunta na kawo ruwa "da ban tasheki ba ai gashi yanzu kin tashiko Maza tashi kije ki ɗauro alwala muyi sallah" tashi tayi a hankali dan har yanzu jikinta na mata wani irin ciwo Austaraliya Afusace ya ke maganar wanda kana gani kasan ransa ya ɓaci sosai da sauri kuma kamar wanda aka tsikara ya miƙe yana gyara zaman cuz din dake jikinsa fita yayi cikin sauri security dake wajan suka rufa masa baya daga musu hannu yayi dan baya buƙatar kowa yanzu a kusa da shi wani haɗaɗan ɗaki ya shiga mai tsananin kyau cire rigar dake jikinsa yayi ya kwanta a kan katafaran royal bed ɗin dake shimfiɗe a ɗakin gaba ɗaya kansa ya ɗau zafi ya ma rasa me ya kamata yayi shin idan haka ta kasance menene makomarsa kenan? anya zai yarda ya tafi wani guri No ya faɗa yana girgiza kansa gaba ɗaya ɗimuwa da tashin hankali sun wanzu akan fuskarsa Da sauri ya tashi yana nufar badroom, ya na shiga ya sakarwa kansa ruwa mai sanyi dan-danan kuma wata nutsuwa tafara saukar masa, lumshe idanunsa yayi a hankali ya na sakin ajiyar zuciya mai ƙarfi [8/13, 4:06 PM] Masoyiya 🤗🔥: https://chat.whatsapp.com/BW8T7i1jpeZ5QpVVl4hxuZ # SQUAD 2024 A WANI COMPANY BY HAUWAU OMAR ...CUTIE MEEYRAT MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS fallow my account Arewabooks Arewabooks@hauwauomar05 Page 4, "Ayrah" "Ayrah wai me kike har yanzu baki fito ba kin san dai ba tsayawa jiranki za'a yi ba ko" da sauri ta fito daga ɗakin tana gyara zaman zumbulele hijjab ɗin ta da ya sauka har ƙasa tayi matiƙar kyau. "Mazaki wuce kije gidan alh hadi yana cen yana jiranki tun ɗazu" da sauri ta kama hanya ta tafi har tayi gaba ta dawa tana kiss ɗin Mamanta akumatu murmushi Mama tayi tana ɗaga mata hannu "Allah ya tsaremin ke dear" "ameen Mamana" Tafiya take cikin sauri duk da ba wani sauri ta'iya ba tayi tafiya sosai kafin ta karasa gidan tana shiga taga habib da'alama shima fita zai yi da sauri ya karaso wajanta yana murmushi "a yau Ayrah ce a gidan na mu?" "eh wllh ya habib kwana biyu" "kin guje muba" ya faɗa yana dariya murmushi tayi tana sun kuyar da kanta ƙasa "ki maza ki shiga ciki dad yanan yana jiranki tin ɗazu" da sauri ta nufi cikin falon tana shiga tagasu zaune kan kujerin falon tsugunawa tayi har ƙasa tana gaidasu amasawa suka yi da fara'a "sai mu wuce ko kar muyi late dan yanzu Mdee da aka sauya baya da sauƙi kwata-kwata" Kama hanya sukayi zuwa wajan parking space shiga cikin motar yayi hajiya da kanta ta buɗewa Ayarh motar ta shiga.. Suna isa ta tsaya tana karanta sunan Company * JULIUE BERGER NIGERIA PLC* Company Juliue Berger Nigeria Plc yana hedikwata a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya. Company ya kasan ce wani kamfanin gine-gine da ke aiki a fannoni daban-daban na gine-gine, musamman a fannin gine-ginen tituna, Akwai kamfanoni da dama a Najeriya da ke da alaka da kamfanoni a kasashen waje, ciki har da kamfanin Juliue Berger Nigeria Plc. Kamfanin ya kasance yana aiki tare da kamfanoni daban-daban a duniya, ciki har da na Austiralia, don gudanar da ayyukan gine-gine da kuma bayar da kayayyaki. Sai da sukayi tafiya mai nisa kafin su isa left zaro ido tayi tana kallon alh hadi dan ita tun da uwarta ta haifeta bata taɓa ganin irin wannan abun ba murmushi yayi yana nuna mata gurin "shiga muje kinji daughter babu abunda zai miki" shiga tayi a tsorace jin sunyi sama ya sa tayi saurin rintsa idanunta tana ambatar sunan Allah Dai-dai left na biyar suka isa fita yayi tana biye da shi nocking yayi a jikin wani office mai kyan gaske, asama an rubuta General Mdee Suhail . P.a din dake zaune a Office din farko ce ta basu umarnin shiga shiga suka yi bakinsu dauke da salama zama alh hadi yayi akan kujera da sauri p.a ta miƙe tana gaidasa amsawa yayi cikin sakin fuska wani banza kallo ta watsawa Ayrah duk da bata santa ba amma gani farko taji ta tsani yarinya da sauri Ayrah ta sun kuyar da kanta ƙasa tana wasa da yatsun hannunta Tashi yayi yana ruke da hannuta suka shiga cikin katafaren office ɗin wani mugun sanyine ya daketa da sauri ta kan-ƙame jikinta suna shiga ya nuna mata wajen zama da kecen nesa karasawa yayi wajan Suhail da fara'a ya miƙawa masa hannu shima cikin girmamawa ya basa hannu sukai musabaha dan Suhail duk wulaƙancisa yana matukar girmama manya bayan sun gaisa ne yake faɗa masa ga yarinya da yace zai kawo murmushi yayi yana kallon yarinya wani irin faɗiwar gaba yaji da sauri ya kautar da idanunsa daka kanta . "Shikenan babu komai ka koma bakin aikinka zan mata inter biyu" godiya ya masa ya nufi ƙofar dan fita tashi tayi da sauri tabi bayansa "kije wacen kujera ki zauna daughter shine zai miki inter biyu" "tom Daddy" ta faɗa tana bin inda ya gaya mata zama tayi akan kujera har lokacin kuma bai dago ya kalleta ba sai da ya gama abun da yake kafin cikin wata sanyayiyar muryasa ya ce ya sunanki "Fatima Mahir" ta bashi masa itama a taƙaice Menene matakin karatunki Secondary "It's also an opportunity for job seekers, we are hiring young people here" Ya faɗa a tsawace sunkuyar da kanta tayi ƙasa dan-danan hawaye ya fara ambaliya a fusakarta Miƙa hannu yayi ya karɓi takardun hannu nata yana dubawa murmushi yayi abun ba karamin mamaki ya bataba ganin yanzu ya gama mata tsawa amma kuma ya koma murmushi "shikenan zan daukeki aiki amma kin san wane aiki zaki yi?" girgiza kai tayi alamar a'a "coffee" Zaki zama mai kawomin coffee ko da yaushe kuma ban yarda ki kaiwa wani acikin Company coffee ba in bani ba kina jina" ɗaga kai tayi alamar eh ita dai koma me zai bata ya bata in dai zata samu kuɗin da zata na siya musu abinci kuma Mamanta ta daina wankau wata takarda ya ɗauka yayi rubutu "gashinan zuwa gobe sai kizo dan fara aikinki sanan idan kin fita kicewa p.a ɗin dake zaune a Office na farko ta rakaki wajan alh hadi ki kai masa takarda" ɗaga kai tayi tana masa godiya, da sauri kuma ta fita daga Office ɗin tana fitowa p.a taimata wani irin kallo sun kuyar da kanta ƙasa tayi tana magana "dama cewa yayi kirakani wajan wanda mukazo dashi ɗazu" wani kallon banza tamata kafin tace "ke bana son iskanci da ni na shigo dake da zakice narakaki wawuya kawai" ita dai bata ce mata komai ba kuma bata ɗaga kai ta kalleta ba duk abunda suke yana kallonsu jin telephone ɗin dake kan table din nata yayi kara yasa tayi saurin ɗagawa hlo sir cikin wata irin murya mai amo ya ke bata umarni gaba ɗaya ta rikice dan bata taɓa jinsa da irin murya ba "am sorry sir Insha Allah hakan bazai kara faruwa ba" ajiye wayar yayi yana dora kansa ajikin kujera a hankali kuma ya ke lumshe idanunsa Fita tayi ita batace mata komai ba da sauri ta bita abaya sai da suka hau left ya kai su bene na 3, in da office din alh hadi yake wanda ya kasance Office ɗin da duk wani taransaction ya ke shiga "Ga office ɗin nan zaki iya shiga" ta faɗa tana juyawa abunta hankali ta murɗa handle ɗin ƙofar tashiga [8/13, 4:06 PM] Masoyiya 🤗🔥: https://chat.whatsapp.com/Ilta4xHroxoHpDTtpEW4H9 #SQUAD 2024 A WANI COMPANY BY HAUWAU OMAR CUTIE MEEYRAT MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS Fallow my account Arewabooks Arewabooks@hauwauomar05 Page 3. A hankali yake sauka daga matata kalar jirgin sanye yake cikin cuz maroon da sauri security suka nufesa gaba ɗaya suka gaidasa ɗaga musu hannu kawai yayi yana miƙa musu back ɗinsa gaba yayi suna binsa a baya har suka ƙarasa wajan motocin motoci ne yan uban su wanda babu mai hawa irinsu sai ɗan wane da wane yana shiga suka tashi motoci a hankali suke tafiya har suka isa cikin Sarah estate dage abuja haɗaɗan estate mai matiƙar kyau da girma dai dai gaban wani gida sukai horn wanda kaf estate ɗin babu kamarsa da sauri mai gadi ya wangale musu katafaren get ɗin suka shiga ya Salam tabbas wannan gidan abun a kallane gidane na gani na faɗa irin gidanan da ake kira da aljanna duniya gidane mai matikar girma. Suna yin parking ko jira security su buɗe masa baiba ya buɗe ya nufi ciki da sauri wani security a cikinsu ya ƙarasa dan nuna masa komai dake gidan suna shiga cikin katafare falon wanda aƙala yayi wani gidan mai kuɗin duka a girma ya kalli security inane part ɗina shine abun da ya faɗa a taƙaice nuna masa wani apartment yayi nufar wajan yayi ya buɗe ƙofar wani haɗaɗen falon ne mai zaman kasan sa up'chear ya nufa Tana tafe ta na murmushi gaba daya jinta take kamar anyaye musu damuwa tabbas tasan idan Ayrahta ta samu aiki zasu samu sassaucin rayuwa da salama ta ƙara sa shiga cikin gidan zaune ta ganta a tsakar gidan tayi tagumi babu abunda ke fita daga idanunta sai hawaye wata matsanan ciyar yunwa takeji gaba ɗaya ta kasa jurewa da sauri Mama ta karasa tana tambayarta me ya faru hawaye ne ya shiga sauka a idanunta ajiye abun da ke hannunta Mama tayi tana zama akan tabarma jawota tayi jikinta ta rungume "menene yake faruwa Ayarh? me akai meki ki faɗamin?" turo baki tayi hawaye na kara zuba a idonta in dai kuka ne da shagwaɓɓa dama Ayrah number 1 wajan nan "toh Mama ba yunwa nake jiba tin dazu kuma cikina sai zafi yake min" "shine kuma kike kuka haba Ayrah mai yasa bazaki yi salati Annabi ba ki sani ba komai akewa kuka ba kuma ai yakamata kisan cewa kefa yanzu babba ce" Mama ta faɗa tana jan hancinta murmushi tayi tana boye kanta ajikin Mama "maza tashi ga abinci nan na tawo mana dashi daga gidan hajiya sarai, kici na baki wani labari mai daɗi wanda zai saki farin ciki" Da sauri ta tashi ta janyo kwanan gabanta tana buɗewa shinkafa ce jallof taƙayatu matuƙa sai da taci sosai kafin ta ajiye kwanan "Mama ke bazaki ciba ne?" "zanci mana amma kifara ƙoshi" "ai na ƙoshi yanzu ma" "haka ake so" "yawwa Mama bani labarin" tafaɗa tana gyara zamanta ita ala dole zataji labari mai daɗi murmushi Mama tayi tana labarta mata duk abunda hajiya sarai ta faɗamata wani irin murna ce ta cikata da sauri kuma ta kai goshinta ƙasa tanawa Allah sujjada tabbas tasan shine yaji kokensu shiyasa Wannan hanyar tazo musu "yanzua shikenan zamu daina zama da yunwa kuma zaki daina wanki mutane ko" tafaɗa tana neman yin kuka "menene kuma haka wai bana ce kin girma ba" da sauri ta goge hawayen tana dariya ƙarasawa tayi jikin Mamanta ta kwanta *Shin wacece Ayrah* Fatina Mahir shine a salin sunanta a salin mahaifinta shuwane mahaifiyarta kuma fulanine irin fulanin nna na tashi Rugar hardo dati ruga ce mai matiƙar girma dagudu wata yarinya wada bazafi 14year tafito daga ruga tana dariya innaji ce ta nifota ruƙe da ɗan kwali "dannijo kitsayaa kisa nace" tafaɗa cikin hausarta ta fualani murmushi yarinya tayi tana kallon innaji kafin kuma ta tawo da gudu ta rungumeta ɗaura mata ɗan kwalin innaji tayi tana murmushi "yauwa yanzu sai ki maza ki ɗauka kafin su hansai su zo suna jiranki ko?" ɗaga kai tayi tana nufar in da ƙwaryar take daura mata innaji tayi ta kama janya ta fita tana yan waƙe waƙen su na fulani a hanya ta haɗu da su hansai suka jera suna tafiya, suna isa cikin kasuwar yauma Kamar kullum tana isa taga wannan mutumin a dai-dai in da take zama hansai ce ta taɓota "ke dannijo yo aradu yauma wance balaraban sai da ya tsaya a wajanki" ita dai bata bata amsa ba dan gaba ɗaya hankalinta nakan mutumin da murmushi ya karaso yana sauke mata ƙwarya dake kanta farine tass mai matuƙar kyau gashinsa ya kwanta lip ga girarsa mai matikar kyau da sheƙi mutumin dai ya haɗu sosai nuna mata wajen yayi da hannu alamar ta zauna zama tayi kuma har lokacin bata fasa kallonsa ba yanan zaune har taga ma sai da fura da nono tashi suka yi zasu tafi da sauri ya karɓi kwaryar tata "muje na rakaki ko?" bata ce masa komai ba tai gaba abunta suna zuwa dai-dai mararaba da zasu shiga rugasu ta miƙa hannu dan ya bata ƙwaryar, murmushi yayi yana dubanta "karki hanani rakaki Please ki bari na ƙarasa ladana" "a'a ? "Kayiwa Allah kabani kayana Saboda kada Baffana ya ganka" bata gama rufe bakinta ba taga Baffa ya nufosu yana kora shanu da gudu ta karasa tana rungumesa shafa kanta Baffa yayi kafin ya ɗaga idanu ya kalli wannan mutumin da sauri ya ƙarasa yana gaidasa cikin fara'a Baffa ya masa yana tambayarsa lafiya ya biyo su dannijo? ... "Da sauri hansai ta ce Baffa a radu kullum mukaje kasuwa sai ya je wajan dannijo" murmushi Baffa yayi yana kallonsa sunkuyar da kansa kasa yai "idan babu damuwa anjima kazo nan ina nemanka" Baffa ya faɗa "shikenan Baffa insha Allah zanzo nagode" sukai musa baha kama hannu dannijo Baffa yayi suka shiga cikin ruga 3 month later Biki ake yi nagani na faɗa irin bikinsu na fulani sanye take cikin saƙi blue an tufke mata gashinta waje guda sai sarƙa da ke wuyan ta da abun hannu duk na shiri a hankali suke tafiya suna waƙoƙin Fulani Baffa ne ya dubi Mahir da yasha fararen kayansa masu matukar kyau hannusa ya kama ya haɗa dana dannijo "karike min ita amana Mahir duk da nasan bazaka taɓa cutar da ita ba kasani bata da kowa sai Allah sai kuma kai a yanzu ina roƙanka ka ruƙeta da hannu biyu" Baffa ya faɗa yana hawaye, da sauri Mahir ya rungume Baffa shima yana hawayen tabbas yayi Alƙawarin bazai taɓa bari wani abu ya taɓa dannijonsa ba da gudu ta karasa wajan innaji ta rungume ta wani irin kuka take mai tsanani tabbas tasan zata yi kewar iyayen ta a hankali innaji ta ɗagota murmushi ta sakar mata,"Ki daina kuka kin ji Aminatu na Allah yayi miki albarka ina rokanki kiyiwa mijinki biyaya" ɗaga mata kai tayi alamar tom kuma har lokacin bata bar kuka ba. kama hannunta tayi ta sata cikin motar da zasu tafi dan Baffa yace babu wani wanda zai bisu daga baya aje ganin gidan nata haka kuwa akayi su kaɗai suka kama hanya zuwa ayi nayin cikin garin abuja... Rayuwa ta cigaba da tafiya Mahir sosai yake bawa matar sa kulawa wadda ke ɗauke da ciki karami. kallonsa tayi cikin shagwaɓɓa tace "Allah ni bana son cin abinci nan" murmushi yayi yana dubanta "me zakici toh"? tana jin haka ta dawo in da yake tana murmushi "ni dai mangoro nake so"Angama ranki yadaɗe gimbiya sarauta mata" murmushi tayi tana rungumesa tsam, kamar wani zai ƙwace mata shi. 6month later. A hankali ya ke dubanta da wani irin yana yi shafa cikin dake jikinta yayi yana magana "haka Allah yatsara naso ace naga abun da zaki haifa Aminatu na basa kulawa fiye da tinani ashe hakan bazai faruba ki kulamin da ɗana ko yata Aminatu ina rokanki idan ansamu mace ki samata sunan mahaifiyata" hawaye ne kawai ke ambaliya akan fuskarta "Ka daina faɗan haka yaya Insha Allah zaka tashi zamu cigaba da rayuwa kasan bani da kowa sai Allah sai kai, sai kuma abun da zamu haifa" ta faɗa tana ƙara sautin kukanta murmushi ƙarfin hali yayi yana dubanta "Insha Allah Allah na tare daku a koda yaushe" wani irin tarine ya sarƙafesa tin yanayi a hankali har ya yi masa yawa saliti yake yi kafin wani lokaci kuma yayi shiru ihu tasaka tana jijiga gashi Da guduta tafita tana kuka malam lima da fitowarsa kenan daga gidan ya ƙaraso yana tambayarta lafiya? kasa magana tayi sai nuna masa cikin gidan da take shiga yayi da sauri dan ganin mai ke faruwa innalilayi wainna ilayi rajiƙun shine kaɗai abun da yake ambata lokacin da ya taɓa Mahir tabbas Allah ya karɓi abunsa zani ya samu ya rufa masa kafin ya fita daga gidan dan samun kira mutane a suturtasa alokacin kuma dannijo ta daɗe da sumawa tabbas wannan itace sular gaddarasu wannan shine sular tarwatsa duk wani farin ciki na dannijo dama tun kwanaki da sukaje rugasu ake sanar musu tuni mahaifanta suka yi kaura daga ruga shin wananan wace kalar kaddara ce ina zata saka rayuwarta alokacin da suka dawo tayi kuka sosai da ƙyar Mahir ya lalasheta tayi shiru to shima gashi yanzu ya tafi ya barta tafiya kuma ta har abada.. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya shekaru suka shuɗe kullum sai tayi wankau suke samun abun da zasu ci ita da yarta malam liman shine yasa Fatima makarnata wadda taci sunan kakarta suna kiranta Ayrah Kuma har lokacin su kaɗai suke rayuwarsu tunda dama Mahir bai taba kaita wajan danginsa ba tin yana raye idan tamai maganr sai dan-danan ya kama hawaye hakan yasa ta daina ma masa maganar kwanci tashi akace asarar mai rai yau fatima ta yi candy wanda yayi dai-dai da tana da 17years a duniya [8/13, 4:06 PM] Masoyiya 🤗🔥: https://chat.whatsapp.com/BW8T7i1jpeZ5QpVVl4hxuZ A WANI COMPANY By HAUWAU OMAR CUTIE MEEYRAT MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS Fallow my account Arewabook Arewabook@hauwauomar Page 5, A hankali ta muraɗa handle ɗin tashiga zaune ta samasa akan kujera office ɗin ƙarasawa tayi wajan tana sunkuyar da kanta kasa murmushi yayi yana dubanta "Fatima Zarah" ya faɗa yana murmushi ɗagowa tayi tana kallonsa "zauna mana" ya bata umarni zama tayi tana miƙa masa takarda dake hannunta Karɓar takarda yayi yana dubawa murmushi yayi ya kalleta "Kema sa'a ce daughter tabbas Mdee ya karɓeki sosai tin da ake kawo ma'aikata ƙananu basu taɓa samun dama Kamar taki ba tabbas ke mai Sa'a ce" ya kara mai-maitawa yana murmushi "menene ya faru dad"? "Suhail ya baki aiki zaki zama mai kai masa coffee saboda matakin karatunki bai kai ki samun office ba sanan zaina baki salary 500th" Zaro idanu tayi waje tana kallonsa "yanzu dad ni ce zanna ɗaukar salary har na 500th?" ta faɗa tana kallonsa Sai da yamma liƙis kafin suka fito dan tafiya gida. A hankali yake fitowa daga left ɗin haɗa idanu suka yi da Ayrah da za su shiga mota da sauri ta sunkuyar da kanta ƙasa murmushi gefan baki kawai yayi ya nufi mota security ne ya buɗe masa motar ya shiga da sauri suma suka shiga suka ja motar suna isa unguwar su ya sauke ta dai-dai ƙofar gidan, "Ki shirya tun wuri gobe daughter saboda Mdee bai yarda da let ba" "insha Allah zan shirya da wuri Nagode sosai Dad Allah ya saka da alkhairi Allah yasa kafi haka" "babu komai daughter ki gaidamin da Mamanki"ya faɗa yana jan motar ta na shiga ciki da gudu ta karasa cikin ɗakin ta rungume Mama murmushi tayi tana ɗagota "washh Allah ni karki karyani" turo baki tayi gaba "ni da bani da wani nauyi taya zan karyaki Mama" "waya gaya miki baki da nauyi" ai ni na sani" tafaɗa a shagwaɓɓe "Mama albishirinki" "goro" Mama ta bata amsa "na samu aiki kuma Mdee ɗin ya ce zaina bani 500th" zaro idanu waje Mama tayi tana kallonta "nikam ban son wasa Ayrah" "wollah Mama ba wasa nake ba" Yana shiga cikin katafaran ɗakin nasa kai tsaye ya nufi badroom dan watsa ruwa sai da ya ɗau tsawan lokaci kafin ya fito daure yake da farin towel wanda ya tsaya masa iya gwiwa sai ɗan ƙarami daya ke tsane gashinsa da shi nufar wajan mero yayi ya na shafa lotion ajikin sa, ya na gama waya ya nufi wata ƙofa yanasa hannusa ƙofar ta buɗe ya salam wani ƙayatatan gurine wan da aka kaya tashi da kaya yan uban su ɓarin ƙanan kaya ya nufa treecotar ya ɗako blue da teshat White mai aɗon blue a jiki. A hankali ya fito zuwa bakin semonfull ɗin dake gidan zama yayi a ɗaya daga cikin kujerin yana shan isaka wayan shi dake aje agun ce ta fara ring da sauri ya daga yana duba mai kiransa Dad shine sunan da ya bayyana akan secreem ɗin wayar ɗagawa yayi da Salama ɗaya bangaran kuma ajiyar zuciya dad ya sauke "Suhail" ya ambata a hankali "na'am dad" "na yi kewarka sosai" "nima haka ina kewarka" "ina fata dai kana lafiya ko"? "lafiya qlau sai dai aiki da yamin yawa" "Allah sarki son Allah ya taimaka Allah ya bada sa'a" "Ameen dad" ya faɗa yana jingina ajikin kujera. sai da suka ɗauki tsawan lokaci suna waya kafin suyi salama, tashi yayi ya nufi ciki dan kwanciya saboda gobe yanada meeting da wasu baƙinsa da suka zo daga Uk. Washegari tun wuri ta tashi tashirya dan tafiya Mama ce ta miƙa mata wani foodfulas murmushi tayi tana karɓa *Mama menene wannan kuma?" "abinci ne amma ban yarda ki buɗe ba sai kinje cen tin da kinga baki karya ba" "tom Mamana na tafi sai na dawo" ta faɗa tana fita daga gidan "Allah ya tsare hanya Allah ya karemin ke aduk inda kika shiga Fatima na" Ta na fita ta tadda alh hadi zaune cikin motar shiga tayi tana gaidasa amsawa yayi cikin sakin fuska kafin yaja motar su tafi su na isa ya ce taje office ɗin Mdee dan kai masa abun da yake bukata to tace tana nufar left a tsorace ta danna ganin ta buɗe yasa tayi murmushi ta mai Kyau wanda ya kara futo da ainayin kyanta shiga tayi, tana isa tafito ta nufi ƙofar nocking tayi ciki-ciki p.a ta bata umarnin shiga haɗa ido suka yi ta galla mata harara ita dai bata ce komai ba tayi gaba abunta dan ita duk irin wannan abun ba sabawa ta yi da suba zaune ta samashi ya ɗorw kansa akan kujera idanunsa alumshe Kamar mai jin bacci "good Morning sir" "morning" ya masa mata kuma har lokacin idanunsa a rufe suke zama tayi akan kujera tana ɗora filas dinta akan table ɗin "menene wannan?" shine abun da taji ya faɗa "abinci ne Mamana ta dafamin" "okay baki breakfast ba kenan"" eh" ta bashi masa a taƙaice "buɗe muci ko bazaki saminba" zaro idanu tayi tana kallonsa bata san sanda tace "ai abincin na talakawa ne ba irin naku bane" murmushi da bai shirya yinsa bane ya subuce masa tabbas ya yarda yarinya ce karama idan banda abunta dama abunci masu kuɗi da ban na talakawa daban "Ki buɗe to naga ni zanga idan irin namu ne" a hankali ta saka zara-zaran yatsunta tana dubawa zubawa ya tsun hannu nata idanu yayi yana kallo washh Allah ya faɗa a hankali ita dai komai nata na dabane ita kuma jin yace wash Allah sai ta zata ko wani abunne ya faru sannu tace masa buɗewa wa tayi tana tura masa fisal ɗin wow lafiyayiyar jallof ɗin taliya ce wadda tasha kayan miya da cori sefun ya ɗauka ya kai abinci bakinsa wani irin daɗin abincine ya ke fuzgarsa yanaci yana lumshe idanu ita dai kallonsa kawai take sai da yaci ya ƙoshi kafin ya tura mata rogawar mazakici ya faɗa yana kafe ta da idanu a'a na ƙoshi kacinye kawai ko kina ƙyanƙyamina ne a'a ta faɗa da sauri tana jan filas din gabanta tsayawa yayi yaga yanda take tauna a hankali tabbas komai na yarinyar abun burgewa ne. P.a ce tashigo cikin Office din suna haɗa ido da Ayarh ta harareta "sir lokacin gabatar da meeting ɗinka yayi" tafaɗa tana miƙe masa takarda tashi yayi ya nufi cikin wani ɗaki dake Office ɗin after 5m ya fito cikin wasu cuz ɗin farare ƙal baƙaramin kyau yayi ba ya haɗe gashinsa waje ɗaya kama hanya yayi zai fita "taso muje ki rakani ko" tashi tayi tabi bayansa har suka fito wani irin baƙin ciki da takaici shine ya rufe p.a wai shin me wannan yarinya take nufi daga zuwanta jiya Company gaba daya ta sauyawa Mdee tunani "Tabb wllh da sake ta faɗa tana huci ita ce wace zata rakasa meeting amma yaja wata kucakar yarinya ina wollah bazai yuwu ba dole ne tun wuri ta san abunda ya kamata tayi Suna fita ya miƙa mata katardu dake hannusa left suka shiga ta kaisu ƙasa shiga mota yayi.Tsayawa tayi tana kallonsa dan ita bata san me zata yiba "shima shiga motar sai na koya miki ne" taji Muryarsa cikin dodon kunnanta da sauri ta zagaya ta shiga drive ne ya jasu zuwa wani ɓangare na Company tabbas wannan Company mai girmane tafaɗa a zuciyarta Fitowa yayi suka nufi ciki suna isa ya nuna mata wata kujera nesa da su "Kije canki zauna" nufar wajan da ya nuna mata yayi shikuma yai gaba abinsa tun tana saran zai tawo su tafi har ta fidda rai gaba daya ta galabaita bacci takeji amma tarasa ta yadda zatayi baccin. kwantar da kanta tayi akan kujera cikin yan mutuna da basu wuce biyar ba bacci ya ɗauketa. suna tashi daga meeting ɗin yayo hanyar wajan da take tun ɗazu hankalinsa na kan yarinya ya san tabbas ba ƙaramin gajiya tayi ba. Yana zuwa ya sameta tana bacci tsayawa yayi yana kallon fusakarta sai yagama Kamar idan ta rufe fuskarta tafi kyau , rasa yadda zai tasheta yayi a hankali ya fara buga kujera da take kwance buɗe idanunta tayi tana kallonsa "tashi muje ko" miƙewa tayi cikin sauri bata yi tunanin ma tayi bacci ba *Ayi haƙuri wollah ban samu damar typing da yawa ba bana jin daɗi kuma ga wayana ba chaji naso na muku page mai tsayi sosai*[8/13, 4:06 PM] Masoyiya 🤗🔥: https://chat.whatsapp.com/BW8T7i1jpeZ5QpVVl4hxuZ # SQUAD 2024 A WANI COMPANY BY HAUWAU OMAR CUTIE MEEYRAT MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS Fallow my account. Arewabook@hauwauomar Page 6. Miƙewa tayi da sauri tana gyara zaman hijjab ɗinta. kama hanya yayi ya tafi bin shi tayi abaya zuwa wajan pearking lot ɗin shiga yayi cikin motar itama tashiga suka nufi cikin Company har sun kai yace ya juya su fita gaba ɗaya daga company haka kuwa akayi sai da sukayi tafiya mai nisa kafin ya ɗago kai ya kalleta "inane anguwarku?" ya faɗa a hankali "lokogoma dai-dai gidan lima" shiru yayi dan shi baima san inane hakan ba drive ya duba "kasan in da ta faɗa?" "eh na sani sir" "maza ka kaimu cen ɗin" sun yi tafiya mai nisa kafin su isa kasan cewar unguwar na da nisa da Company suna isa ta fito zata nufi gida "babu Salama kenan" ya faɗa a takaice murmushi tayi mai kyau "nagode sosai sir" shima murmushi ya maida mata drive ne ya ja motar suka yi gaba tana shiga ciki ta samu Mamanta a bakin murhu da gudu ta karasa ta na rungumeta ta baya murmushi Mama tayi tana juyota "yar gidan Mamanta har andawo" "eh Mama yau bama da Dad su habib muka dawo ba" "dawa kika dawo" "Mdee guri namu ne na raka sa wajan meeting shine da aka tashi ya kawoni gida" "okay mun gode sosai Allah ya saka masa da alkhairi amma dai ki dunga kula" "Insha Allah Mama" Da da-dare suna zaune a ɗakin Ayrah ta ke bawa Mama labarin Company, "Wollah Mama baki ga Company ba babba nifa wallahi jiya da muka shiga sai naga kamar ba a Nigeria ba, kuma ma wai kinsa me?" girgiza mata kai Mama tayi alamar a'a "idan zaka hau sama tawani abu fa ka ke shiga sai yayi sama da kai" ta faɗi hakan tana dariya mai sauti ita dai Mama sai kallonta ta ke a duniya ta na ƙaunar farin cikin yar'tata matiƙa. Kwance yake ya rufe idanunsa kamar mai bacci gaba ɗaya ya rasa mai yake masa daɗi juyi kawai yake akan bed ɗin nasa ganin ciwon na kara masa tsanani ya sa ya yi saurin tashi daga kwanciyar bude freeg yayi ya ɗako ruwa mai sanyi tare da tablet ya kora dan-danan kuma ya fara zufa kamar wanda yake acikin zafi tashi yayi ya hau kan bed ɗin cikin muntina da basu shige biyar ba bacci ɓarawo ya ɗaukesa niko nace asuba ta gari Mdee Suhail. Washegari dawuri ya tashi ya shirya dan fita aiki sai da suka yi waya da dad ɗinsa kafin ya fita Sanye ta ke cikin wata doguwar riga mai kyau Mama ce ta daure mata gashinta da rebom ɗan ƙaramin hijjab ta saka wanda bai fi iya rabin ta ba Masha Allah tayi matiƙar kyau kyawun da duk wani namiji ya ganta dole ne ya ruɗe sunbatar Mama tayi agoshi kafinta fice daga gidan tana fita taga habib a tsaye babu dad murmushi tayi suka gaisa "amma ya habib ina dad ya ke koshi ba zai je bane"yau" ta tambayesa "a'a Daddy zai tawo daga baya, yaje wani aiki ne legos so idan ya dawo yau zaizo shine ya ce na zo na kaiki" "Allah sarki Daddy" ta faɗa ta na murmushi buɗe motar tayi ta shiga shima shiga yayi ya ja suka tafi. A hankali ta ke tafiya gaba ɗaya ta daburce sai wani irin tafiya ta ke ta marasa gaskiya, dai-dai bakin kofar ta zuba wani abu mai ƙauri kafin ta koma wajan zamanta tana sakin murmushi mugunta. Cikin tafiyarta da ta saba ta tawo dan shiga cikin office ɗin ko kallon p.a ba taiba. Da sauri ya miƙe ya nufo ƙofar yana buɗewa dai-dai zata taka abun yayi saurin dakatar da ita wani irin kallo ya watsawa p.a mai cike da tsantsar tsana da ƙyama sunkuyar da kanta tayi ƙasa "five minutes na baki ki goge abunda kika zuba agun nan sha-sha-sha kawai" ita dai Ayrah tsayawa tayi tana kallonsa dan bata san akan me yakewa p.a faɗa ba Da sauri ta ta so ta ɗako mofa ta na nufo gun sai da ta goge tass kafin ya bawa Ayrah umarnin ta shiga p.a komawa ta yi wajan zamanta wani irin kuka ta fashe dashi mai tsima rai shikenan yarinya nan ta ɓata mata duk wani shiri da ta ke da shi akan Mdee ina wollah da sa ke mudum tana raye sai ta sa ka yarinyar kuka da idanunta bazata taɓa barin yarinyar ba aje zuwa "yarinya sai shegen kyau kamar yar aljannu" ta faɗa tana jan tsuka Nuna mata wajan haɗa coffee ya yi da sauri ta karasa dan haɗa masa sai da tabi komai a hankali tana karantawa kafin ta gama a hankali ta ƙaraso gabansa ta aje masa "Thanks" taji ya ambata "sir ina so naje waje idan babu damuwa" "me zakiyi a wajen" babu komai" bai kara mata magana ba sai da ya shanye coffee ɗinsa tass dan ba ƙaramin daɗi ya mai ba telephone pole ɗin ya danna "ina son ganinki" shine abun da yace yana aje wayar kanta a ƙasa ta shigo cikin office ɗin ko kallonta baiba ya ce "ki kaita office ɗin ƙanan ma'aikata, idan kinje ki haɗani da ɗaya daga cikin su" "okay sir" tafaɗa ta na dubansa "ta so mu tafi ta cewa Ayrah" tashi tayi ta bi bayanta lumshe idanunsa ya yi a hankali ya na sakin ajiyar zuciya suna fita suka nufi wata hanya wadda zata sadasu da left ta bene hawa sukayi ya kaisu ƙasa shiga cikin wani office tayi binta Ayrah tayi suna shiga suhailat ta sakarwa Ayrah murmushi, karasawa p.a ɗin tayi wajanta ganin babu kowa sai ita kaɗai a office ɗin "dama Mdee ne ya ce na kawota nan sanann kuma na haɗaku a waya" "okay" suhailat ta ce tana murmushi kiransa p.a ta yi ya na dagawa ta miƙewa suhailat sai da suka yi magana sosai kafin ta kashe wayar ta na murmushi, kama hannu Ayrah ta yi ta na zaunar da ita akan ɗaya daga cikin kujerin "Zaki iya tafiya" ta bawa p.a umarni murmushi tayi wanda iya ka cinsa laɓɓanta tana fita daga office ɗin. "Ya sunanki?" suhailat ta tambaye ta "Fatima Mahir" "amma ana kirana Ayarh" "Wow nice name" "nikuma sunana suhailat ki daukeni tamkar ƙawarki kinji" murmushi tayi tana ɗaga kanta Hira suke sosai gwanin sha'awa duk da Ayrah bata da yawan magana amma yau sai da suka yi hira sosai lokacin sallah ne yayi suka fita dan zuwa masallaci fitowarsa kenan daga office ɗinsa ya nufi masallaci dai-dai sun nufo hanyar kanta aƙasa take tafiya jinta bugi abu yasa da sauri ta ɗako tana kallonsa wani irin kallo ya watsa mana ke baki da hankali ya faɗa a zafafe hawaye ne ya fara zuba daga fuskarta ɗaga hannu yayi a zafafa zai mareta jin an ruƙe masa hannu ta baya yasa yayi saurin juyowa yana kallon wanda ya masa haka wani irin kallo ya watsa masa yana cije laɓensa sun kuyar da kansa ƙasa yayi kus-kure ɗaya zaka yi rayuwar ka shine kus kuran marin fusakarta da ace ka aikata haka tabbas da sai dai ka zauna babu hannu har karshen rayuwarka yar fa da hannusa ƙasa yayi ya na cigaba da tafiya da sauri Suhailat ta kama Ayrah suka cigaba da tafiya suna isar da Sallah suka kama hanya dawowa ciki suna isa cikin office ɗin nasu Ayrah tafashe da wani irin kuka mai cin rai menene abun kuka Ayrah ki yi haƙuri kuma ai kinga Mdee ya zo "ke mai Sa'a ce Ayrah" Kirane ya shigo cikin photo ɗin dake wajan da sauri ta ƙarasa ta na ɗaga wayar "ki turomin ita" ya faɗa a hankali "okay sir" "tashi kije Mdee na kiranki Ayrah" "okay" ta ce ta miƙa tana barin office ɗin da salama ta shiga ciki ɗogowa yayi yana kallon idanunta wanda suka yi ja daga gani kasan tayi kuka zama tayi tana sunkuyar da kanta "Ayarh" taji ya ambati sunanta akaran farko ɗagowa tayi tana kallonsa ba tare da tayi magana ba "menene abun da ya haɗaki da shi?" turo baki tayi dan-danan kuma hawaye ya fara zarya "Ya salam" ya furta ya na dafe kansa "Please ki bar kuka bana son ji" cikn shagwaɓɓa ta ce to ba shine kawai dan mun taho da aunty Suhailat, ban sani ba na bigesa shine ya ke tamin faɗa kuma wollah babu abunda na masa" tsayawa yayi yana kallonta abun ba karamin burgesa yayi ba ganin yadda ta ke magana. "Shikenan ki tashi kije ƙasa office ɗinsu Suhailat ɗin saboda zan yi magana da wasu anan kuma kin ga maza ne bai kamata ki zauna ba gyaɗa masa kai tayi ta miƙe tana tafiya" ta na fita ta ga Daddy su Habib murmushi ta yi "Daddy yaushe ka dawo?" murmushi shima ya mai da mata yanzu nan dawowa ta kenan daughter" "sannu da zuwa" "yawa daughter ina zaki yanzu" "zani ƙasa ne office ɗin su aunty Suhailat" "Masha Allah Allah ya taimaka" "ameen dad" "maza ki je kin ji" nufar hanya tayi shikuma ya shiga da Salam ya karasa shiga cikin office ɗin zaune ya taddasa ya na latsa lapton ɗin dake gabansa zama yayi akan kujera gaisawa su kayi da Suhail "dama ba komai ne yasa na ce idan ka dawo kazo ba sai chanjin wajan aiki da ka samu zuwa Austiralia" murmushi alh hadi yayi irin nasu na manya "amma ko wani abun ne ya faru"? "A'a babu abunda ya faru mun yi duba da yanda kake gudanar da aikinka tabbas kai ɗin mai amana ne, wannan dalilin yasa muka yanke hukunci haka" yalwatace murmushi ne ya subuce masa "ina matukar godiya da wannan shaidar da Kuka min da kuma ƙarin girma sai dai wani hanzari ba gudu ba shin idan na bar ƙasarnan wanene wanda zai dinga ɗako Ayrah?" "Karka damu da wannan Insha Allah za'a san yadda za'a yi" godiya ya masa kafin ya miƙa zuwa waje dan lokaci tashi yayi har ya akai bakin ƙofar ya dakarmtar da shi "idan ka tashi tafiya karka damu da jiran Ayrah zan kai ta gida" godiya ya masa sosai sannan ya fita a office ɗin Fitowa yayi zuwa ƙasa dai-dai office ɗin da Ayrah ta ke ya tsaya ya na nocking ta sowa tayi dan buɗe ƙofar ganin Mdee tsaye a jikin ƙofar ne ya bata mamaki murmushi ya sakar mata "muje ko" shine abunda ya ambata kallon Suhailat ta yi taga ta sakar mata murmushi fita tayi ta bisa abaya. Dai-dai grand towers mall suka tsaya "muje ciki" gyaɗa masa kai tayi alamar a'a dan gaba ɗaya tsoro ya kamata "kina jin tsoron ne" ya faɗa dai-dai kunnanta ƙara gyaɗa masa kai tayi "a'a ni kawai kuje ku dawo inan" shima kwai-kwayar maganr tata yayi "a'a ni dai sai mun tafi tare" wata irin dariya ta tin tsire da ita dan ita abun ma dariya ya bata ganin yayi magana kamar wani yaro shima dariya ya ke yana kallonta. "Maza ki buɗe muje" buɗe murfin motar tayi tafita suna shiga kai tsaye ya nufi wajan wasu dogayan riguna yan uban su jida ya dunga yi kamar babu gobe wata Black ya hango cen nesa da shi sai walwali ta ke mai adon golden karasawa yayi ya ɗakota ya saka cikin basket ɗin ita dai Ayrah ta zama yar kallo dan babu abun da ta ke sai kallosa yana gama kwasar abayar ya nufi wajan Englishwest ya shiga jidar su suma yanda kasan zai haɗa lefa Ba karamin kaya Suhail ya jidaba har dangi su bra da pant sai da ya ɗibe su kafin ya nufi bangaran chocolate da beskit suma ya jida bayan ya biya kuɗi wanda a ƙala sun kai sama da 2m security gurin su ka ɗauka ledojin su ka samasa a mota a hankali ya ke takowa inda take dan ita dai ta zama mutum-mutumin tun lokacin da taga iyayen kuɗin da ya kashe hura mata isakar bakinsa yayi ya na kallonta murmushi kawai tayi ta nufi waje, shima binta ya yi a baya zuwa wajan motar, suna tafiya ta na kallonsa jin muryasa ta yi yana cewa "Shikuma kallon na menene" sadda kanta ƙasa ta yi don har ga Allah ba'tai zaton ma yana ganinta ba [8/13, 4:06 PM] Masoyiya 🤗🔥: https://chat.whatsapp.com/BW8T7i1jpeZ5QpVVl4hxuZ A WANI COMPANY BY HAUWAU OMAR CUTIE MEEYRAT MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS Fallow my account Arewabooks@hauwauomar05 Page,07. Suna isa ƙofar gidan na su da kansa ya buɗe murfin motar ya fito, drive ya sa ya ɗeba kayan zuwa soran gidan. "Amma sir naga ana shiga da kayan gidan mu aje maka zanyi ne?" murmushi ya yi ya na dubanta. "A'a ba jemin zaki yi ba mallakin kine, zaro idanu tayi waje tana kallonsa "To ni ina zan kai wainan kayan?" murmushi ya yi kawai ya shiga cikin motar su kayi gaba, tsayawa tayi ta na kallon motar har su ka ɓace mata cikin sanyi jiki ta shiga gidan tana kiran Mama Mama fitowa tayi da sauri dan gani menene ya faru Ayarh ke mata irin wannan kiran. "Lafiya Ayrah kike kira... Kasa karasa maganar tayi ganin uban ledojin a cikin soran, "Ina muka samu wainan ledojin kuma?" "Mama ki kama mu shiga ciki idan mun zauna zan miki bayani" babu musu Mama ta kama ledojin suka dinga shiga da su cikin gidan. zama ta yi akan kujera ta na sauke ajiyar zuciya, zu ba mata ido Mama tayi tana kallonta "Kefa na ke jira kimin bayani" bata labarin duk abun da ya faru ta yi, shiru Mama ta yi ta na mamakin wannan lamari kafin ta ɗago kai ta kalleta "Kina gani kuma ya miki hakan bada wata manufa ba?" tasowa ta yi ta ƙaraso in da Mama ta ke ta kwanta akan cinyarta. "Mama ki tamin addu'a inaji ajikina babu wata matsala" "Allah ya sa" "ameen" ta ce ta na rufe idanunta saboda wani irin bacci da ya ke fuzgarta Yau ta kama asabar kasan cewar babu aiki yau zaune ta ke cikin ɗakin hannuta ruƙe da beskit tanaci, Mama ce tashigo cikin ɗakin ta na kallonta "Hajiya shan zaƙi yau ansamu abunda ake so" sun kuyar da fuskarta ta yi ta na dariya "Ma za ki tashi muje gidan alh hadi, tin ɗazu ya aiko mu zo kina bacci" murmushi ta yi ta miƙa ta na gyara zaman riga dake jikinta hijjab ta saka na riga su ka fita suna tafe suna hira har suka isa gidan. a parlor su ka samu hajiya da sauri Ayrah ta ƙarasa wajan Hajiya sarai ta na murmushi ita ma murmushi tayi "A'a yau ma'aikata ne a gidan namu? sannu da zuwa lale marhabu da daughter" karasawa ta yi ta na rungumeta habib da shigowarsa kenan cikin parlor ya yi gyaran murya "Nifa na fahimci Momy kamar kinfi son Ayrah akaina Allah" ya faɗa ya na turo baki gaba kamar wani karamin yaro. tin tsirewa Ayrah ta yi da dariya ta na nunasa wollah ya habib da ka yi shagwaɓɓa ka yi kyau sosai" murmushi kawai ya yi, ya na karasa shiga cikin parlon Gyaran murya alh hadi yayi ya fara basu labarin yadda sukayi da Suhail fashewa Ayrah ta yi da kuka "Yanzu Daddy idan ka tafi ni yaya zanyi kuma dawa zan dinga tafiya"?karki damu daughter Mdee ya ce za'a san yadda za'a yi insha Allah komai zaizo da sauƙi" Allah ya sa" anan alh hadi ke faɗa musu Insha Allah ranar Monday za su wuce Austiralia kuma shi da iyalinsa za su tafi, ba karamin damuwa su ka shigaba jin haka amma babu yadda za su iya "Shikenan alh Allah ya kaiku lafiya" Ameen ya ce ya na miƙewa dan yana son ya je wani waje Saboda shirin tafiyarsu Suna isowa gidan kai tsaye Ayrah ta nufi ɗakin, ta na shiga ta kwanta gaba ɗaya sai tajima aikin ya fita kanta. Zaune ya ke akan sujerun da ke garding ɗin hannusa ruƙe da cup ɗin juice ya na sha jin gidana ya yi da kujera ya na lumshe idanunsa ji ya ke ina ma yau ba ta zo a sturdy ba, gaba ɗaya zaman gidan ya ishe shi gashi babu wani wanda ya sani bare yaje in da yake. Ayrah shine abunda zuciyarsa ta faɗa masa tabbas gidan su Ayrah ya kamata ya je har ya miƙa kuma wani tunanin ya zo masa shin idan yaje gidansu ya ce mata me? kai ina bazaije ba gaskiya, gwara ya yi zamansa shi kaɗai. tashi ya yi ya nufi cikin gidan ya na shiga ya janyo lapton ɗinsa dan kiran Daddy ɗinsa. Da fara'a dad ya ɗaga wayar murmushi ya yi ya na kallon mahaifinnasa "Allah dad ni na fara gaji da ƙasarnan, idan fa babu aiki sai dai na yi ta zama a gida kamar wani mara gata, ya faɗa cikin shagwaɓɓa" murmushi Daddy ya yi dan yasan rigima Suhail ce ta motsa "Ka yi shiru dad, yaji murya Suhail ta katse ma sa tunanin da ya tafi "Haƙuri zakayi son tinda kaga tunda ka dawo Nigeria ba'a kara samun wa ta ɓannaba, na san kana ƙokari kuma nima ina matukar kewarka. amma Insha Allah inan zanzo na kawo maka ziyara da zarar na gama da aikin dakenan" murmushi jindaɗi ya yi "Promise dad" "I promise you son" cigaba sukai da wayar ta su cikin farin ciki da kaunar juna su na gama wayar ya kashe lapton ɗin ya na lumshe idanunsa tabbas ya na natukar son mahaifansa baya iya haɗasa da komai Tashi ya yi ya nufi ciki dan ya samu yayi bacci. Cire kayan da ke jikinta ta yi ta nufi bayin na su ta watsa ruwa ta na fitowa ta tsaya a gaban wadrop ɗin ta su ta na kare mata kallo tinani kayan da za ta saka ta ke, ganin har kusan takwas ta yi ba ta fito ba ya sa Mama ta tashi ta shiga ɗakin tsaye ta ganta a jikin wadrop ɗin ta zu ba mata idanu murmushi ta yi kawai ta karasa ta na taɓata, da sauri ta dawo da kallonta kan Mama "Ke kuma lafiya? ki ke ta kallon wadrop Kamar kinga sabon abu" turo baki ta yi kamar zatayi kuka kafin ta ce "Ni to ba rasa kayan da zansa na yi ba" "Tofa yau nabanu wai Ayrah yaushe zaki daina wannan halayyar taki? ace kullum mutum in ya yi wanka sai ya ta ruwan ido, kafin ya sa kaya" Mama ta faɗa ta na janyo wata marron ɗin abaya cikin abayoyin da Mdee ya siyamata "Ingo wananan ki sa ka" karɓa ta yi ta na murmushi zura riga ta yi a jikinta wow Masha Allah yanda kasan dan ita aka yi riga, ba karamin kyau ta mataba ƙarasawa wajan mero ta yi ta shafa tirare da leps glows a bakinta kama kanta ta yi dan ɗaurewa tin ta na yi ta na ganin za ta iya harta fashe da wani irin kuka mai cin rai. ƙarasowa Mama ta yi ta kama kan ta na ɗaure mata da wani white ribom mai kyau, hula riga ta sa ka white sai belt na riga shima white ta yi rolling dashi, takalmi ta zura plat. ba ƙaramin kyau Ayrah ta yi ba yadda kasan yar turai. fitowata yi ta na ɗagawa Mama hannu. Fita ta yi waje ta na tunani ta yadda zata tari abun hawa ya kaita Company. Turus taja ta tsaya ganin wata arniyar mota kirar pontic gto(1964). Tsayawa ta yi ta na kallon motar a hankali ya sauke glass ɗin ya na sakar mata murmushi, murmushi itama ta yi ta na nufar wajan motar. Da sauri drive ya buɗe mata tashiga, godiya ta masa ta zauna "Good Morning sir" "Morning" "how are you today" "fine" ta bashi amsa a taƙaice Su na isa cikin Company ta buɗe murfin, "Ba kiji ba"ya faɗa a hankali juyowa ta yi ta na kallonsa, ganin idansa har yanzu a lunshe kamar bashi yayi magana ba "Kinyi Kyau sosai" "Thank you very much" ta faɗa ta na fita a motar shima fitar ya yi ya nufi hanyar da za ta sadashi da left, sai murmushi ya ke shi kaɗai kamar wanda akaiwa bushara 😂 Ya na shiga ya nufi office ɗinsa da fara p.a ta gaidasa ko kallon inda ta ke baiba bare ta sa ran zai amsa mata. Jiki a sanyaye ta karasa kan kujerata ta zauna hawaye ne ya fara zarya akan kuncinta. Turo kofar ta yi ta shiga bakinta ɗauke da salama da sauri ta goge hawayenta ta na gallawa Ayrah harara, sunkuyar da kanta ƙasa ta yi tai gaba abunta ta na shiga ta nufi wajan haɗa coffee dan ta san zai bukacesa zuba mata idanu ya yi yana kallon yadda ta ke komai cikin nutsuwa samun kansa yayi da sakin wani murmushi wanda shi kansa bai son manufar yinsa ba "Sir" "Sir" gaba ɗaya ya faɗa duniyar tunanin baima san ta na masa magana ba sai da ta bibuga table ɗin sannan ya dawo hayyacinsa karɓa ya yi ya na kaiwa baki ƙara lumshe idanunsa ya yi ya na kai kofin bakinsa sai da yasha sosai kafin ya ɗago ya kalleta. "Yau baki tawo da abinci Mama ba?" gyaɗa ma sa kai ta yi alamar eh "Dama ina son na maka godiya da kayanan nagode sosai Allah ya saka da alkhairi, Mama ma ta ce na maka godiya" "Babu komai na yi dan Allah so dan haka ni aganina ba abun godiya bane." "Sannan daga yau duk abunda da na baki ba na son godiya kinji" ya faɗa ya na kafeta da idanunsa ma su matukar kwarjini saurin sunkuyar da kanta ƙasa ta yi dan bazata iya jurar kallonsa ba. Da salama ta shiga ciki office ɗin wanda baida wani girma samunsa ta yi zaune ya haɗa hannusa biyu akan fuskarsa da alama wani abun yake tunani. Murmushi ta yi ta na karasawa ciki, hura masa iskar da ke bakinta ta yi "Lafiya kai kuma ka ke ta fama tunani?" murmushi kawai ya yi ya na cije leɓansa na ƙasa "Hmm wallahi har yau na kasa mantawa da abunda Mdee ya min akan yarinyar nan" "Kaima kenan daba wani abu ya maka ba" "Ni tozartani ya yi agabanta😥 "Ni da na ke matsayin p.a ɗinsa amma ko ta ni bayayi, sai wata ƙaramar yarinya" tsaki ta yi mai sauti dan a duk lokacin da ta tuna wa ta irin wutar tsanar Ayrah ke karuwa tabbas ta yi alƙawarin sai ta wahala da yarinya wahala wadda ko aljan sai yaji tausayinta bare mutum. "Wai me ki ke tunani ne? ina miki magana kin min banza kin san fa ba na ɗaukar wulakanci ko" Abdul ya faɗa a hasale "Kaifa daɗina da kai rashin haƙuri ina tunani yadda zan wahala da yarinya ne, da yadda zan rama abunda tamin" wa ta irin dariya ya sheƙe da ita ya na kallonta "Ina jinki me kike tunani kenan?" murmushi ta yi ta na gyra zamanta akan kujera. Matsawa ta yi dab da shi ta raɗa masa wani abu akune wata irin dariya su ka sheƙe da ita su duka, su na tafawa "Sai yanzu na kara yadda da ke wace" "Kai dai kawai ka kasance cikin shiri dan a koda yaushe zakajini na nemaka" "Angama shugaabar mugaye duniya" wata dariya ta karayi ta na fita a office ɗin rungumeta Hajiya ta yi su na kuka "Idan Ayrah ta dawo kice ma ta mun tafi" gyaɗa kai Mama Ayrah ta yi har sun shiga mota Habib ya fito "Aunty idan Ayrah ta dawo kice zan yi kewarta sosai, ki gayama zanzo na ɗauketa mu koma Australia tare" murmushi Mama ta yi ta na goge hawayen da ke fuskanta.. A hankali ya tashi ya nufi cikin ɗakin da ke office ɗin sai da ya kusa shiga kafin ya tsaya ya na duban Ayrah "Kije office ɗin su Suhailat, kuma bayan nan ban yarda kije ko ina ba" gyaɗa ma sa kai ta yi alamar toh fita ta yi da ga office ɗin kanta a sunkuye ganin p.a ba ta office ɗinta ya sa ta sa ki wa ta irin ajiyar zuciya mai ƙarfi, dan gaba ɗaya ba ta son ganin Suhailat Da murmushi Suhailat ta tare ta "Yau sai yanzu ake ganinki" zama ta yi ta na gaidata amsawa ta yi cikin sakin fuska "Ina kika shiga yau?" "Babu ko'ina ina office ɗin Mdee" "Okay" Suhailat ta ce ta na chanza hira "ki na son wani abu ne?" "A'a Aunty Suhailat na ƙoshi" to ai ba cewa na yi nima baki ƙoshi ba, ina nufin kamar beskit chocolate da dai sauransu" murmushi Ayrah ta yi jin an ambato kayan kwaɗayi [8/13, 4:06 PM] Masoyiya 🤗🔥: https://chat.whatsapp.com/BW8T7i1jpeZ5QpVVl4hxuZ # SQUAD 2024 A WANI COMPANY BY HAUWAU OMAR CUTIE MEEYRAT MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS Fallow my account Arewabook@hauwauomar05 Page_ 8_9 Ana tashi ta fito harabar Companyn don tafiya gida,ko office ɗin Mdee ba ta koma ba. fitowa wajan get ɗin tayi sai da tayi kusan 5minth bata samu abun hawa ba, hakan ya sa tashiga takawa da ƙafa ta na tafiya dafe kanta tayi saboda wata rana da ake gashi ko rabi bata yi ba, jin horn a bayanta ya sa ta yi saurin juyawa zuge glass ɗin motar ya yi ya na mata wani irin kallo, sunkuyar da kanta tayi ƙasa da sauri ta na wasa da yatsun hannunta Nuna mata motar yayi alamar ta shiga, babu musu ta shiga kuma har lokacin kanta na ƙasa suna isa ƙofar gidan na su ta buɗe ta fita ko magana bai mata ba yaja motarsa yayi gaba jiki a sanyaye tashiga cikin gidan na su ganin bataga Mama a tsakar gida ba yasa tayi cikin ɗakin, samunta ta yi zaune ta na karatu al'Qur'ani mai girma zama tayi ta na murmushi. Yana shiga gida faɗawa yayi saman kushin ɗin gaba ɗaya yau ya gaji lumshe idanunsa yayi ya na sauke numfashi tinani rayuwarsa ta baya da ta yanzu ce ta shiga dawo masa hawaye ne ya fara zarya akan kuncinsa tabbas bashi da wani gata sai na mahaifinsa mahaifiyarsa ta tafi ta barsa tin baisan ma menene duniyar ba haka ta watsar da shi ta tafi kawai dan basu da kuɗi alokacin. Allah kenan mai azurta bawansa a sanda ya so mahaifiyarsa taci amanar Daddysa taje ta auri abokinsa kawai dan shi baida kuɗi alokacin bata damu da rayuwar da zasu shiga ba haka ta barsu kuma har yau bata wai wayesu ba tuna irin waɗannan abubuwan ya sa ya kara fashewa da kuka mai cin rai idanunsa sun yi wani irin ja abun ka da fari nan da nan fuskarsa tayi ja a hankali ya kwanta ya na wani irin numfashi aduk sanda Suhail ya tuna waɗannan abun tofa yana shiga cikin wani irin hali ne . Tun yana numfashi a hankali har ya nemin fun ƙarfinsa miƙewa yayi ya shiga bathroom ya sakarwa kansa ruwa mai sanyi yana fitowa ya goge jikinsa da towel ne ɗaure a jikinsa ya kwanta yana rufe idanu kuma har lokacin hawaye bai daina zuba akan fuskarsa ba Wanene Suhail? Suhail Arif shine ai nayin sunansa asalin mahaifansa bature ne haka ma mahaifiyarsa Austiralia. Calvary public hospital Ihu ne ke tashi a dai-dai room 003 dake cikin hospital ɗin a hankali kuma ihu ya fara disha shewa kyakyawa mutune tsaye a bakin ƙofar idanunsa a rufe da alama yana cikin yanayi na damuwa jin kuka jariri da yayi ya sa yayi saurin shiga cikin ɗaki kwance take akan gadon na marasa lafiya daga ganin yanayi yadda take bacci zaka tabbatar da cewa a wahalce take da sauri ya karasa ya ɗauki jaririn dake gun yana rungumesa tsam a jikinsa kamar wani zai rabasa da shi sun kai tsawan muntina 20 a haka kafin ya ɗago ya kalli matar da ke kan gadon wani uban harara ta watsa masa tana jan tsaki nufar idan da take yayi da sauri ta dakatar da shi da hannunta "karka sake ka kusanci inda nake Arif saboda baka da wani amfani a gare ni cikin dake jikina ne na haife maka kuma na barmaka shi har abada bana fata ka faɗa masa yana da wata uwa wadda tai kaman ceceniya da ni talaka kawai wllh nayi nadamar auran matsiyaci kamar ka kuma ina so kasani aurena da Mahabub babu fashi" ta faɗa tana tashi daga kan bed ɗin ko damuwa da ciwon da jikinta ke mata bata yiba ta nufi hanyar fita da sauri ya karasa gabanta ya na haɗa hannuwansa biyu alamar taji tausayin su ratsesa tayi ta fita tana jan tsaki durkushewa yayi ya na fashewa da wani irin kuka mai cin rai tabbas Mahabub ya cuceshi ya ci amanarsa yanzu da gaske dama Sarah zata iya barinsa saboda kuɗi shin me yasa bata ji tausayin ɗan da yazo duniya ba yau duk wannan maganganu shi kaɗai ya ke yinsu kamar wanda aka tsikara ya miƙe ya ɗauki jaririn nufar hanya futa yayi daga hospital ɗin gaba ɗaya Haka rayuwa ta ciga da tafiya Suhail ya taso wajan mahaifinsa kullum shi yake kaisa makaranta ya ɗaukosa bayaso ko wani ƙwarzane ya taɓa masa ɗa watarana ya dawo daga school ya nufi parlon su jun haya niya yasa yayi saurin tsayawa ya na saurare "Arif kenan ban fa na zo ne dan na tambayi ya kake ko ya ɗanka ya ke ba a'a nazo ne dan naji ance kayi kuɗi shine nazo dan kabani nawa kasan tunda dai dani akasha wahala" da wani kallon ya watsamata "Tabbas baki da imani Sarah baki ko tambaye ni ya ɗan ki ba sai Maganar dukiya abar banza wannan damuwarka ce ni koma ya yake bai dameni ba to bazan bayar ba Sarah ina lokacin da bani da kuɗin gudu na ki kai kuma ki maza ki fita a gidanan kafin nasa security su fitarmin dake" ganin da gaske ya ke babu wasa yasa tayi ƙwafa tana fita a ɗakin Suhail da idanunsa ke zubar da hawaye ya tsaya yana kallonta tsaki taja tayi gaba abunta da gudu ya shiga cikin parlon yana faɗawa jikin dad ɗinsa numfashinsa ne ya fara sarƙewa da gudu dad ya ɗauke sa zuwa hospital ɗin dake cikin gidan tun daga wannan lokaci Suhail ke fama da ciwo a zuciyarsa har izuwa wannan lokaci. Wannan kenan. Sai kusan la'asar ya tashi a bacci miƙewa yayi yana ambaton sunan Allah, bathroom ya shiga ya ɗauro alwala ya gabatar da Sallah. Mama ce ta dubeta tana murmushi "yau kin daɗe Ayrah lafiya?" murmushi tayi tana bata labarin abun da ya faru "ke yanzu taya zaki iya zuwa gida dama a ƙafa karki kuskura ki ƙara wannan ganganci" "tom Mama insha Allah". "Kin san kuwa su Habib sun tafi yau ya ce na ce miki zai yi missing ɗin ki sosai kuma wai yanan zaizo ya ɗaukeki ku koma cen tare" murmushi "Allah sarki ya Habib nima zanyi Miss ɗinsa sosai Mama". Washegari da wuri ta fita dan karta ɓata masa lokacin tana fita kuwa ta gansa cikin mota ganin kamar babu drive yau ya sa abun ya bata mamaki buɗe baya tayi zata shiga jin muryasa tayi yana magana "kenan niɗin drivern kine da zaki wani shiga baya?" fasa shiga bayan tayi ta buɗe gaban ta shiga. "Dole ne kayi taka tsantsan saboda kar Mdee ya gani ta camera" murmushi yayi "haba wai bana ce miki na kashe camera office ɗinsa ba" murmushi kawai tayi suka cigaba da zuba abun ya a hankali ya buɗe office ɗinsa ya shiga itama shiga tayi ta nufi kujera ta zauna "kawomin coffee" miƙewa tayi dan kawo masa jin ta kasa tashi akan kujera sai ƙokarin tashi take amma abu ya gagara ganin tana ta ko kawa ya sa ya ce "me yake faruwa?" ɗago idanunta tayi wanda ya fara zubda ruwa "na kasa tashi" "what kin kasa tashi kamar ya ba yanzu kika zauna ba?" "Allah da gaske nake" ta faɗa hawaye ne ke ambaliya a fusakarta ganin tana kuka yasa ya miƙe dan ganin meke faruwa saka hannunsa yayi ya janyota amma ya ga ko motsi bata yiba durkusawa yayi dai-dai kujera yana dubawa murmushi kawai yayi ya nufi cikin wata drowa hannusa ruƙe da wata roba ya dawo ganin ya na zuba mata ruwa a jiki yasa ta fashe da kuka "sheet" shine abun da ya ce kin shirun tayi ta cigaba da kukanta ƙara janta yayi ta ko faɗa jikinsa wani irin faɗuwar gaba ce ta ziyarce sa sai yaji Kamar ya taɓa shork da sauri ya rabata da jikinsa ya na komawa ya zauna "kije office ɗin ƙasa zan nemaki anjima" tana sha shekar kuka ta fita wata irin dariya p.a ta tintsire da ita a lokacin da tazo wucewa ita dai bata kobi ta kanta ba ta fita abunta Suhailat ganin hawaye akan fuskarta ya sa ta miƙe da sauri tana rukota "menene ya faru Ayrah?" hawaye ne ya kara zubowa "ki yi shiru Please ki faɗamin kinga kin tayarmin da hankali" bata labarin abun da ya faru tayi shuru Suhailat tayi tana nazarin abun kafin tayi murmushi kawai ta bar magana "to kiyi shiru kinji ina ga wani abune a wajan" goge mata hawaye dake fuskartata tayi ta na cewa "yauwa ko kefa nifa sai nagama kamar idan kina kuka kinfi kyau wollah" murmushi kawai tayi tana boye kanta akan cinyarta. P.a miƙewa tayi da sauri ta nufi office ɗin Abdul ta na shiga ta tuntsire da wata muguwar dariya shima dariya yayi "albishirinki?"ta ce" goro" ya bata amsa "part one dai munyi nasara saura two" ya ce" a haba dai?" Ta ce" ai dama na faɗa wallahi Sai yarinya ta gane kuranta naso ma ace bai gane menene a kujera ba kasan nan gaba menene shirinmu?" girgiza mata kai tayi alamar a'a matsawa tayi ta raɗa masa a kune "gaskiya wannan shawara taki ta matukar yi tabbas ranar muna da shan kallo a Company nan" ta ce" sosai ma kai dai kawai a zuba eyes kaga yadda zan juya rayuwar yarinyar". Mikewa yayi ya fita office ɗin h.o.d na Company ya shiga da sauri ya miƙa ya na gaidasa amsawa yayi cikin sakin fuska dan duk cikin ma'aikata gidan babu wadda ya yarda da shi kamar h.o.d zama yayi ya na masa magana lokacin "ɗazu kafin na shigo Company an kashe Camera dake office ɗina menene dalilin haka?" "sorry sir ɗazu p.a ke faɗamin wai na bada umarni a kasheta saboda za'a yi wani gyara ne a office ɗin naka wannan dalilin yasa na kashe" ya ce" ita p.a ɗin ce ta faɗamaka haka?" "eh sir" murmushi yayi yana cije laɓansa na ƙasa "sir ko haka da matsala ne" ya ce" a'a babu wani matsala" ya faɗa ya na miƙewa yana fita ya koma office ɗinsa zaune ya ganta tana danna waya a zafafe ya ƙarasa in da take ya ɗauke ta da mari wani irin taurari ta shiga gani suna giftawa ta fuskarta "sha-sha-sha mara tunani duk ranar da kika sake maka manci haka kin ji na faɗami Wllh a bakin aikinki" zaro idanu tayi waje sai tajima gaba ɗaya zafin mari ya kauce idan ta bar aiki tasan rayuwarta ta shiga wani hali. Miƙewa Ayrah tayi suka fita daga office ɗin "Aunty Suhailat amma dai kin daɗe kina aiki anan ko?" "eh gsky na daɗe sosai Ayrah tun kafin zuwan wannan Mdee ɗin" "Alokacin wani Mdee ne azalumi. Kina so na baki labarinsa? gyaɗa kai tayi alamar eh "Okay Bari mu dawo daga sallah zan baki labarin" ta faɗa dai-dai lokacin da suka isa masallaci. Bayan sun idar da Sallah zama suka yi cikin lambu dake gefan gun "Ada idan kikazo neman aiki tofa Mdee ɗin baya taɓa yarda ya ɗauke ki aiki Sai ya lalata ki. Idan baki yarda da haka ba toh sai dai salary naki ya zama zaku raba wannan dalilin yasa yan mata dayawa a lokacin suka shiga wata rayuwa wasu daka haka kuma suka koma karuwanci. Zaro idanu tayi tana kallonta "Amma toh Aunty Suhailat ke ya kika yi?" murmushi tayi "Alokacin da na zo neman aiki Mdee ya nuna min haka babu yadda zanyi saboda ina matuƙar bukatar aiki dan dashi zan taimaki iyayena dole ina ji ina gani yake raba salary na biyu ya ban rabi duk wata hantara idan ya tashi yimin yake haka ya mai dani p.a ɗinsa dan kawai ya cimma burinsa, da yake Allah shine mai kare bawansa sai Ubangiji ya tona masa asiri aka koresa duka daga wajan aikin "Shiyasa zakiga wasu mata idan zasuje aikin Company suyita rawa kai wallahi ya wanci Company ma aikata su ko kaɗan babu Allah a ransu amma fa bana ce mike duka ba" "A'a wasu dan kin san a ko ina akwai nagari akwai na banza" "Haka ne Aunty Suhailat Allah ya sa mu dace" "Ameen ya rabbi" "Sannan ki dunga kula ba kowane zaina miki murmushi ba ki zaci sanki yake a'a wani yana da manufa a kanki ki yi a hankali sister ki san da suwa zakiyi mu'amala" Sun daɗe agun suna tattaunawa kafin su meƙe su koma ciki "Kije office ɗin Mdee ko zai buƙaci wani abun, kiga lokacin tashi yayi" gyaɗa mata kai tayi ta na nufar left ta hau Tana isa ta gansa zaune a ya na danna lapton ɗinsa da'alama kuma wani abun yake, zama tayi kan kujera sai da ya gama sannan ya ɗago ya kalleta "Yau bazan samu damar kai ki gida ba saboda ina da wani aiki so zansa drive ya Kai ki" "Toh shikenan nagode Sosai" "Ita kuma godiyar ta mece?" sunkuyar da kanta tayi batare da ta basa amsaba murmushi yayi ya cigaba da abun da yake Fitowa tayi zuwa haraba Company drive na ganinta ya buɗe mata mota ta shiga, suna isa ta sauka tayi cikin gida, ta na shiga ta kwanta akan kujera "Wash Allah Mama wollah yau na gaji da yawa" "Ke kuma aikin me kika yi da kika gajin?" "Ni fa ba aiki na yi ba kawai gajiya na yi" "Raguwa ni nataɓa gani angaji ba tare da anyi aiki ba" "Allah Mama ana gajiya" ita dai Mama murmushi ta yi ta cigaba da abun da ta ke dan tasan idan ta biye Ayrah to bazata taɓa bari ta ba [8/13, 4:06 PM] Masoyiya 🤗🔥: https://chat.whatsapp.com/BW8T7i1jpeZ5QpVVl4hxuZ # SQUAD 2024 A WANI COMPANY BY HAUWAU OMAR CUTIE MEEYRAT MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS Fallow my account Arewabook@hauwauomar05 Page_10_11 Washegari tun wuri Ayrah ta shirya tana jiran Suhail ganin lokacin sai tafiya yake ya sa ta tashi da sauri tanawa Mama bye bye. Tana fita bakin titi ta tsaida me napeep shiga tayi tana faɗa masa inda zataje. Suna isa ta fito tana bashi kuɗinsa ta nufi bakin get ɗin security da ke gun ta gaida tana shiga ciki, sai da tayi tafiya mai nisa kafin ta ƙarasa left ta hau Tana isa office ɗin Mdee taji ƙofar a kulle nufar inda p.a take tai tana tambayarta Mdee baizo ba har zata mata masifa ta tuna magungun Mdee sai kawai tayi murmushi tana ɗaga mata gira "Yes Mdee ya je wani guri sai zuwa anjima zai ƙaraso nan so idan kinga bazaki iya jiraba sai ki koma gida sai ya dawo" Bata ce mata komai ba ta juya tai tafiyarta abunta ƙasa ta sauka Suhailat ta gani da'alama kuma itama zuwanta kenan da sauri ta ƙaraso "Ayrah yau ke kaɗai kika zone? naga Kamar Mdee bai shigoba" "Eh Aunty Suhailat good morning" "Morning dear fatan kinzo lafiya?" "Lafiya qlau ta bata amsa yau kinga wani taro za'a yi a Company so karfe biyu kowa zaije gida sai bayan nan za'a dawo kamar 4:00 idan an tashi ki biyo ni muje wani waje dan shiryawa kinji" "a'a Aunty Suhailat zanje gida kawai sai na faɗawa Mam.. Kasa karasa maganar tayi ganin Mdee tsaye yana kallonsu da'alama kuma ya daɗe a wajan Nufo su yayi ya na isowa wajan ya kalli Ayrah sai kuma naga ya cenza hanya yayi gaba abunsa murmushi Suhailat tayi "Maza kije ki kaima Mdee coffee kin ji" "toh tace tana bin bayansa suna isa office ɗin p.a ta gaidasa ƙasa-ƙasa ya amsa ya na nufar na sa office ɗin. Ya na shiga ta turo ƙofa ta shiga Tunda ta shiga taga ko ɗagowa ya kalleta baiba, nufar wajan coffee tayi ta haɗa masa aje masa a kan table ɗin tayi wata tsawa ya daka mata wadda tasa gaba ɗaya hanjin cikin ta ɗaurewa "Ke wace kalar sha-sha-sha ce? kinji nace miki ina bukata ne?" ya faɗa a tsawace jikinta ne ya fara wani irin rawa dan-danan hawaye ya shiga zuba akan fuskarta so take ta bashi haƙuri amma bata da karfin haka tsaki yayi ya zauna akan kuje yana dafe kansa da hannu biyu "Ya salam" ya furta a hankali ya na rufe idanunsa shin me yake shirin aikatawa ne ohh ya Allah Da gudu ta fita daga office ɗin p.a dake zaune takaleta tana mamaki dalilin da yasa ta fito tana da gudu tana kuka. Ƙasa ta sauka tashiga office ɗin Aunty Suhailat tana shiga ta rungumeta tana wani irin kuka numfashi tane ya fara sarƙewa dalama kuma ciwonta ke ƙoƙarin tashi Suhailat hankali ta ne ya yi mugun tashi da sauri ta kwanta da ita ta fita waje a guje ko left batai tunani hawa ba ta shiga haura bene da bibiyu gaba ɗaya ta shiga damuwa buɗe ƙofar tayi ta shiga tana haki p.a tsayawa tayi tana kallon ta ko bin ta kanta bataiba ta shiga cikin office ɗin Mdee ganin Suhailat a wannan yanayi yasa yayi saurin meƙewa yana kallonta nuna masa ƙofa kawai take ta kasa magana "Menene ya faru ki nutsi ki faɗamin" "Sir Ayrah" "Ayrah sir" tun kafin ta karasa ya fita da sauri ya na sauka ya faɗa cikin office ɗin p.a na biye da shi samunta yayi kwance idanunta a rufe da sauri ya ƙarasa ya na taɓata. Ɗaukarta yayi zuwa pearking lot tun daga nesa yake ƙwalawa drive kira da sauri ya taso ya zo ya buɗe masa motar shiga yayi yana ruƙe da ita suka nufi asibiti Company suna isa asubiti da sauri Dr ya sa aka shiga da ita ɗaki gaba ɗaya Suhail ya rasa nutsuwarsa ji yayi hawaye na bin kunchisa da sauri ya saka hannu ya na gogewa ya san koma me ya faru shine sula shi yaja da baimata tsawa ba da hakan bazai faruba Mama da ke zaune tan kaɗe gari dan bata so Ayarh ta dawo bata gama girkin ba tasan hali ji tayi gabanta yayi wani irin faɗiwa a hankali ta dafe ƙirjinta tana ambaton sunan Allah laila hailla anta subuhanaka inni kuntu mina zalumin shi take ambata a zuciyarta Sai da suka ɗauki kusan 20m kafin su fito daga room ɗin. Da sauri ya miƙe ya na ƙarasawa dan jin me yake faruwa dafa kafaɗarsa Dr yayi kafin ya ce "Muje office sir" babu musu ya bisa suka shiga office ɗin nasa zama yayi akan kujera yana nuna masa shima kujera babu musu ya zauna, cire farin glass ɗin dake fuskarsa yayi ya na duban Suhail "Bakomai ne ya haifarma da wannan shiga yanayi da ba tashiga ɗinmuwa ne kasan a wasu lokuta mutum idan bai saba da abuba toh aduk lokacin da abun ya faru da shi ya na shiga gigici da ɗimuwa kuma ita yarinya ce qarama, dole ne sai an dunga kiyaye wasu abubuwa sir "Insha Allah za'a na kiyayewa, yanzu zan iya ganinta?" "why not yanzu haka tana ɗakin hutu zaka iya zuwa, zuwa anjima idan ta tashi zaku iya tafiya" godiya ya masa ya miƙe ya fita A cikin company kuwa kowa ya ya fito a office ɗinsa sun tsa-tsaya sai mai da magana ake ita dai Suhailat tana gefe ta haɗa hannuwa ta biyu a fuska babu abun da ke zuba daga idanunta sai hawaye, gashi babu damar ta bi su Mdee hospital ɗin. Yana shiga cikin ɗakin ya tarar da ita kwance tana bacci karasawa yayi gaban gadon ya zauna ya na kallonta "Am sorry Ayrah ni ne naja miki kiyi haƙuri bazan ƙaraba kinji", ya faɗa Kamar ta na jinsa hannuta ya ruke cikin nasa kiran dad ɗinsa ne ya shigo cikin waya da sauri ya ɗaga a ɗaya ɓangaren kuma dad ya masa "Hallo son kana lafiya" "Lafiya qlau dad" "Masha Allah karka manta da taron yau fa ka san taren na da matuƙar muhimmanci ko?" shiru yayi dan shi gaba ɗaya ma ya manta da wata maganar taro 'Ko baka jinane?" "Ina jinka dad insha Allah bazan manta ba" "Toh Allah yasa muma munan muna shiri" Yana katse kiran ya kira h.o.d cikin Company "Ku shirya komai da za'a bukata na taro, karku damu sai na zo no kuyi komai yadda ya kamata" "Okay sir Insha Allah za'a yi hakan" katse wayar yayi ya na duban Ayrah da ta ke bacci abunta 2hours later A hankali ta ke buɗe idanunta ganin Kamar mutum a zaune a inda ta ke yasa ta saurin karasa buɗe idanunta murmushi ya sakar mata dauke kanta tayi daga kallon nasa "Sannu ya jikin" banza tayi masa tana tuna abun da ya faru wani sabon kuka ta fara "ya ilahi ki yi shiru Please ki daina kuka nan dan Allah" "Ni ka kaini wajan Mamana bana son zama anan" "Naji zan kai ki amma sai kin yi shiru" mai makon ma tayi shiru sai ta cigaba da kukanta tashi yayi har ya kai bakin ƙofa ya ce "Taso muje ai da sauri ta duro akan bed ɗin ta bisa a baya dr suka gani na ƙoƙarin shigowa murmushi yayi "Sir kace har kun fito" "Eh" ya bashi amsa a taƙaice su na isa haraba hospital ɗin drive ya ta so da sauri "Ka koma Company ni zan kaita gida" "Okay sir" ya faɗa yana buɗe masa motar zagayawa yayi ya buɗewa Ayarh ta shiga da gudu ya ja motar dai-dai wani ɗan ƙaramin stor ya tsaya ya siya mata abun da zata iya ci tare da kayan tea Dawowa yayi cikin motar yaja suka tafi, suna isa ƙofar gidan da sauri ta buɗe zata fita ruƙe mata hannu yayi yana girgiza mata kai kwaɓe fuska tayi zatai kuka "Shiit ni bacewa na yi kimin kuka ba," ya faɗa ya na miƙe mata leda "Idan kin shiga gida ki gaida min da Mama sananan ki bari sai kinji sauƙi kya dawo aikin kin ji? Allah ya baki lpy kuma kiyi haƙuri nasan nine naja miki" "Babu komai nagode" ta faɗa ta na fita daga motar kwanta da kansa yayi a jikin kujera ya na murmushi shi kaɗai ya san abun da yake ji akan yarinya ganin har ta daɗe da shiga gida ya sa ya ja motarsa yayi gaba Kai tsaye gida ya nufa dan baijin zai iya komawa Company a wannan yanayi ya na isa ya nufi falon ya nasa Tana shiga Mama ta ta so tana tambayarta lafiya fashewa tayi da kuka tana rungumeta, ruƙeta tayi suka nufi cikin ɗakin suna shiga ta kwanta akan tabarma "Wai Ayrah menene ya faru?" "Kai nane fa ya ke ciwo" ta faɗa a shagwaɓɓe "Amma ke kam wai yaushe zaki daina kukan ciwon kai ni Allah na zata ma ko wani abune ya faru tashi toh ki ci abunci kisha magani" "A'a Mama ni na ƙoshi ta" faɗa tana miƙa mata ledar da Mdee ya bata "Ita kuma wannan ledar menene a ciki?" "Mdee ne ya siyamin kuma ma ya ce na gaidaki" "Toh Ina amsawa mungode sosai da ɗauwai niyar da ya ke" ita dai Ayrah bata sa ke cewa komai ba ta rufe idanunta Da da dare suna zaune Ayrah ta dubi Mama "Wai Mama mu Shikenan haka zamu cigaba da rayuwa mu kaɗai?" shiru Mama tayi bata ce komai tabbas itama a koda yaushe tana wannan tunani shin idan rayuwa ta ciga da tafiya haka watara na fa zata mutum alokaci sai dai yar'tata ta yi itama rayuwa ita kaɗai, ganin hawaye na zuba akan fuskarta ya sa ai Ayarh saurin nufo in da ta ke "Dan Allah Mama kiyi haƙuri idan magana ta bata miki daɗi ba" murmushi kawai tayi tana rungumeta adaran dai haka suka kwana cikin tunani rayuwarsu Washegari da wuri ya tashi ya shirya yana fitowa security ya buɗe masa motar ya shi, su na isa ya shiga office, Suhailat da dama zuwansa ta ke jira, ta tashi da sauri ta nufi office ɗinsa kanta aƙasa ta shiga da salama amsawa yayi ya ɗago ya na kallonta "Good morning sir" "Morning how are you" "fine" "Dama sir tambayarka zanyi ya jikin Ayrah" "Jikinta da sauƙi tana gida, sai bayan ta ƙara samu sauƙi zata dawo aiki" ya faɗa yana danna lapton ɗin dake gabansa "Okay Allah ya bata lafiya" "Ameen ya rabbi" godiya ta masa tana fita daga office ɗin Tana fita p.a ta tare ta "Am me Mdee ya ce akan yarinya, har yanzu tana asibiti" wani kallo Suhailat ta mata tana wucewa abunta "Mtss kada Allah ya sa ki faɗa yar raini hankali, daga gani yarinya shikenan kunbi ku liƙe mata Allah shiƙara wallahi ni na so ma ace ta mutu muga ƙarshen iskanci" [8/13, 4:06 PM] Masoyiya 🤗🔥: https://chat.whatsapp.com/BW8T7i1jpeZ5QpVVl4hxuZ A WANI COMPANY BY. HAUWAU OMAR CUTIE MEEYRAT MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS fallow my account Arewabook@hauwauomar05 Page_12_13 Yau kusan kwanan Ayrah uku agida bata zuwa aiki. Gaba ɗaya baya jin daɗin aikin ji yake Kamar akwai wani abu da yayi giɓi cikin aikin na sa. A hankali ta mike da ga kwance da ta ke ta na kallon Mama meƙewa tayi ta shiga toilet dan yin wanka, ta na fitowa ta nufi cikin ɗakin ta shirya tsaf cikin doguwa riga ta atamfa hajjab ta zura Masha Allah ta yi kyau sosai fitowa tayi ta na wa Mama bye bye ta fita sai da tayi tafiya mai nisa kafin ta samu mai napeep ɗin da zai kaita zuwa Company tana isa ta shiga ciki office ɗin Suhailat ta shiga ta na ganinta ta miƙe da sauri ta rungume ta "Oyoyo sister yau kinzo kenan?" murmushi tayi tana gyaɗa mata kai "ya jikin naki?" "da sauƙi Aunty Suhailat"ta ce" Masha Allah Mdee ya san kinzo ne?" "a'a yanzu na zo ai" ta ce"Okay maza kije zuwa anjima kya dawo kinji" fita tayi ta nufi office ɗin Mdee ɗago kai p.a tayi ta na kallonta dan ita gaba ɗaya ma ta manta da ita wuce wa tayi zuwa ciki yana ganinta ya ya yi murmushi, Murmushi ita ma tayi tana zama akan kujera ya ce" ya jikin na ki?" "da sauƙi" ta bashi amsa. Kasa tashi tayi ta haɗa masa coffee dan tana gudu abunda ya faru ranan ya sake faruwa jita yi ya ce "coffee" jiki a sanyaye ta miƙe ta nufi wajan haɗa coffee ɗin tana haɗa masa ta zo kan table ta ajiye zama tayi akan kujera tana wasa da yatsun hannunta sai da ya gama tsaf kafin ya miƙe kallonsa tayi nufar ɗakin hutunsa yayi ita dai tanan zaune har ya shige kuma bai mata magana ba ta kai kusan 20munith kafin ya fito cikin cuz brown Masha Allah yayi kyau sosai. hanyar fita yayi juyowa yayi yana kallonta ganin ba shi take kallo ba yasa ya ce "muje ko" ɗagowa tayi ta na kallonsa dan bata gane inda maganarsa ta dosaba "cewa nayi ki taso muje" babu musu ta miƙe ta bi bayansa p.a na ganinsa ta miƙe karasawa yayi "bani file ɗinnan" miƙa masa tayi har yayi gaba tace "am sir ko nazo muje tare ne?" "ban nemaki ba idan da ina da bukatar hakan da zan faɗamiki" shiru tayi bata sake cewa komai ba har suka fita zuwa waje Shiga yayi cikin motar itama ta shiga suna isa drive ya fito ya na buɗe musu ƙofa tana ganin inda suka zo ta haɗe rai haka kurum a bar mutum shi kaɗai har ya gaji murmushi yayi ya na juyowa ya kalleta dan ya ji abunda ta ce ganin ya na murmushi ya sa tayi shiru suna isa ya nuna mata wajan zama karasawa yayi wajan meeting ɗin Mrss Afif ne ya dubesa ya ce" muna bukatar gine mai kyau na zamani mun yi la'akari da kaf Company babu kamar wannan shiyasa muka kawo kwangila mu nan" haka suka cigaba da tattaunawa tun tana sa ran zai taho su tafi har ta gaji meƙewa tayi ta fita ganin ta fita ya sa hankalisa ya dawo kanta ko ina zata sai ya ji ya kagu su tashi daga meeting ɗin tana fita kai tsaye wani lambu mai kyau ta karasa lambu cike ya ke da bishiyoyi daban daban Kamar su mangoro, gwaiba, dabino banana, da dai sauransu ai ta na ganin bishiyar mangaro ta karasa da sauri ta na murmushi dan ta na matukar kaunar mangoro wani dutse ta gani agun da sauri ta karasa ta na jefawa ganin ya ƙi faɗowa gashi ta gaji ya sa ta zauna agun tana haɗe rai Suhail da fitowarsa kenan ya na nemanta security ne ya ce masa ya ganta ta shiga lambun cen nufar gun yayi ya na zuwa ya ga ta haɗe hannu biyu a kumatu ta na hawaye da sauri ya ƙasa ya na tambayarta abunda ya faru nuna masa mangoro tayi kuma har lokacin ta na hawaye murmushi yayi kawai ya kira wani security bashi umarni yayi akan ya ciro masa mangoro da yawa ya kai masa mota ai ta na jin haka ta miƙe ta na murmushi jindaɗi "toh taso muje ko" babu musu ta bisa suka fita a lambu suna shiga cikin motar ta zauna lokaci zuwa lokacin sai ta leƙa ganin har yanzu security bai tahoba ya sa ta ƙara turo baki "menene kuma toh?" ta ce" bashine har yanzu bai tahoba" "ke kuma rashin haƙuri" juyar da fusakarta tayi ta na ƙara turo baki murmushi kawai yayi security na zuwa ya buɗe boot ya saka musu zagayowa yayi "sir an saka a boot" okay ya bashi amsa drive ya ja suka fita kai tsaye gida ya kaita suna isa ya sa aka ɗako mata ledar mangoro mai uban yawa sai murmushi take kamawa tayi ta na shiga cikin gidan sakin baki Mama tayi tana kallonta ganinta ruƙe da uwar leda ta ce "ke ko Menene acikin wannan ledar?" "mangoro ne" ta bata amsa tana murmushi "wato kefa na fahimci ma ba aiki kike ba a Company wallahi kawai shirma kike" turo baki tayi ta na shiga ɗaki da abunta tashi Mama tayi tana bunta a baya zama tayi akan tabarma ta na buɗe ledar "kuma fa walloh Mama ya nuna mangoro" "eh gashinan ai nagani sai ki bada himma kisha" ɗauka tai zata kai baki "amma ai kya wanke ko?" dafe kai tayi ta na dariya "wollah ni nama manta ana wani wankewa" ta ce" dama ya za'a yi ki tuna tunda yau ala ya haɗaki da mutumnin ki" Suhailat ganin har yanzu Ayrah bata zoba kuma gashi lokacin ta shi ya kusa ya sa ta miƙe dan shirin tafiya gida ta na fitowa taga p.a ta sako daga saman "amma yawa Ayrah fa?" kallon sama da ƙasa tayi mata kafin tace "wacece kuma haka?" shiru Suhailat tayi bata sake cewa komai ba dan ta fahimci p.a bata da mutunci ko kaɗan kama hanya tayi tai wuce warta "Ayrah!! Ayrah!! ki tashi daga bacci nan kin san fa babu kyau bacci yamma ko tun da kika dawo kike ta bacci ko abinci baki nema ba" buɗe idanunta tayi ta na kallon mahaifiyata A hankali ya ke sauka daga matata kalar bene sanye ya ke cikin white cuz ya haɗe gashinsa guri ɗaya farin ne tass gashinsa ya sauka har gadon bayansa da wani irin sauri security suka nufosa suna isowa gun gaba ɗaya suka rusuna ɗago kai yayi yana kallon su ya salam kyau iya Kyau kyakyawa ajin ƙarshe sanye yake da farin glass a fuskarsa gefan sa wata mata tace wadda aƙala zata haura shekaru (45) itama fare tass kamar dai shi sanye take cikin Black abaya mai duwatsu tayi rolling da belt na abayar hannuta ruƙe ya ke cikin na haka suka jera suna tafiya gwanin ban sha'awa suna isa bakin motar aka buɗe musu suka shiga kai tsaye kata faran gida dake maitama hills estate ya salam gidane iya gida girman gidan ya zarce misali gaba ɗaya gidan zagaye yake da security ta ko ina mai gadi ne ya buɗe get ɗin da jerewa motocin suka yi zuwa cikin gidan tun kafin su gama parking ta fito da gudu ta na ihu duk da tsakanin cikin gidan da pearking lot da nisa amma hakan bai sata ta howa da gudu ba ta na murna "Oyoyo Ammina Oyoyo ya Abrad" shine kawai abun da take furtawa ta na gudu murmushi yayi kawai ya kalli Ammi itama kallon na sa tayi da sauri ta faɗa jikin Ammin ta na murmushi cen kuma hawaye ya fara zuba akan fuskarta "Ammi shine kuka tafi kuka barni ni kaɗai ko?" "ohh Jiddah toh yanzu kuma menene abun kuka ai gashi mun dawo ko?" gyaɗa kai tayi ta na kallon Abrad jan hanci ta yayi ya na cewa "rigimama Ammi" murmushi tayi ta na turo baki "nifa fushi na ke da kai" "kaina bisa wuya na idan kikai fushi da ni ina zan kama" ya faɗa ya na yin gaba abunsa dan shi bai cika yawan magana ba wananan ɗin ma yayi ta ne kawai wani haɗaɗan falo ya shiga mai tsanani kyau irin falon nane da ko gidan shugaban ƙasa ba a samunsa a hankali ya zauna a kan kujera da ke gun ya na lumshe idanunsa wani irin sanyi ne ke ratsa masa zuci yau dai gashi ya dawo Nigeria duk da badan Ammai taje ta tawo dashi bana babu abun da zai dawo da shi Ammi kama hannu Jiddah tayi suka shiga na su apartment ɗin sai surutu ta ke kamar redio dan Jiddah badai magana ba Ayrah fitowa tayi cikin ƙanan kaya masu kyau da shaƙi kallonta Mama tayi tai murmushi "kin yi kyau sosai" murmushi tayi ta na zama akan tabarma "wallahi Mama na ƙagu gobe tayi naje aiki saboda za'a bani salary na" murmushi Mama tayi "waya ga su Ayrah da salary" wata dariya tayi mai cike da nuna zallar farin ciki ta Tashi yayi ya haura sama ohh ya rabbi ashe ba komai na gani a ƙasa ba dankareren falone shima na alfarama bedroom ya shiga dan watsa ruwa Ɗaure ya fito cikin white towel iya gwiwa hannusa na ruƙe da karami wanda ya ke tsane kansa da shi Wani irin taunar cingom take mai bada sauti kallon wata ƙarama yarinya tayi wadda baza ta fi Sa'ar Jiddah ba "kinji na gaya miki wallahi kika sa ke kikaje wajan mutsiya tan cen ranki sai ya bacci sakara kawai" "rabi da ita Momy ita yarinya wallahi na fahimci tafi son Ammi" "eh ɗin nafi sonsu kuma ni wallahi duk abinda zakuce sai dai muce haka kuri ni dai wallahi Momy akullum ba zan daina faɗaminki kiji tsoran Allah ba kuma kisan zaki mutu" da sauri Momy ta bige mata baki "zaki rufemin baki ko kuwa sakarar yarinya sai anyi magana ki farawa mutane wa'azi angaya miki mu bamu san abunda ya dace ba ne?" tashi tayi ta haura sama tana ƙunƙuni "Na fahimci yarinya nan sai na shiga dukanta zata dawo hankalin ta" "kema ce Momy tutuni nagaya miki ki kaita wajan durfus kawai ya rufe miki bakinta wallahi idan ba haka ba duk wani shirinki sai ta tarwatsa sa yanzu gashi su ya Abrad sun dawo Nigeria kuma da kince ance miki ba zai taɓa dawowa ba" shiru Momy tayi ba tace komai ba dan itama al'amarin duk ya ɗaure mata kai Niko nace Allah kenan babu wani wanda ya isa yayi abunda Allah bai ba hajiyata[8/13, 4:06 PM] Masoyiya 🤗🔥: https://chat.whatsapp.com/BW8T7i1jpeZ5QpVVl4hxuZ A WANI COMPANY BY. HAUWAU OMAR CUTIE MEEYRAT. MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS Fallow my account. Arewabook@hauwauomar Page_16_17 Be ce mata komai ba ya buɗe idanunsa "Kin ɗauka na yi bacci ko shiyasa zaki gudu" girgiza kai ta yi alamar a'a "Jeki toh idan an kusa tashi sai ki dawo" "Okay sir" ta faɗa ta na fita dan zuwa office ɗin Suhailat Ana tashi ta fito dan nufar office ɗin Mdee a hankali ta tura ƙofar tashiga ganin baya cik i ya sa ta zauna ta na jiransa. Fitowa ya yi cikin wasu fararan cuz masu kyau, tsayawa ta yi tana kallonsa ganin da marron ɗin cuz ce a jikinsa yanzu kuma ya canza kenan da wasu kayan ya ke zuwa Company? ta faɗa ta na cigaba da kallonsa zuwa ya yi dab da ita ya sunkuya "Madam shi kuma kallon fa na menene?" murmushi ta yi tana saurin kawar da kanta "Tashi muje ko?" babu musu ta miƙe tabi bayansa, suna fita su ka shiga cikin motar kai tsaye ya gida su ka nufa. Suna isa ta fita dan shiga gida "Baki jiba" juyowa ta yi danjin mai zaice "Ki gaidamin da Mama" "Toh insha Allah zan faɗamata" Tsaye ya ke ajikin window apartment ɗinsa, sanye ya ke cikin treecotar black da white riga mai kyau haɗe gashinsa ya yi ya ɗaure guri guda idanunsa a lumshe ya ke wani irin jindaɗi yanayi ya ke garin lileɓe ya ke da hadari mai tafiya da iska mai sanya nishaɗi da gudu ta shigo cikin bedroom ɗin ta na kwala masa kira dafe kansa ya yi wanda ya ji ya sara masa "Ohh ya rabbi wai Jiddah yaushe zakiyi hankaline?" turo baki ta yi Kamar zata yi kuka "Toh ni ba Ammi ce ta biyo ni zata dakeni ba dan na ɗauka mata waya shine na zo gurinka, ka hanata dukana amma ka ke min faɗa ko ya Abrad" ta faɗa hawaye na zuba akan fuskarta "Dan Allah kiyiwa Allah kimin shiru Jiddah" banza ta ma sa ta cigaba da kukan ta tsawa ya daka mata, da sauri ta fita a ɗakin ta na kuka Ammi da ke nemanta ganin tana kuka ya sa ta tambayarta lafiya? karasawa ta yi ta rungumeta "Wai ke lafiyarki ne kike min kuka?" "Ba ya Abrad bane ba ya yi min faɗa" "Da ya miki faɗa ke me kika masa"? "Ni Ammi babu abun da namasa ki tambayesa" "Naji maza ki wuce ciki kiyi shiri islamiyya" babu mu su ta nufi bedroom ɗinta dan shiryawa ajere su ka fito ita da Yusra drive ne ya ƙaraso yana buɗe musu motar, shiga su ka yi hannusu ruƙe dana juna. Suna isa Jiddah ta dubi Yusra ta na dariya hararata ta yi "Mie kikewa dariya ke kuma?" "Babu komai kawai ina tuno darun da zakuyi keda ya Ustaz ne" "Toh ina ruwanki nifa Allah bana son gulma" gwalo ta ma ta ta na fita a motar da gudu, bunta ta yi itama da gudu su ka shiga gudu a makaranta Ustaz ne ya ƙaraso gurin ya na mu su magana tsayawa sukayi su na suraransa "Wai ku kullum sai kun shigo kuna gudu haba ya kamata ace kunsa kun girma fa" Jiddah ce ta turo baki "Ni dai Allah ya Ustaz ku daina cewa mun girma nawa mu ke ne nida Sis za'a na cewa mun girma" dariya ya yi kawai yai gaba abunsa dan yasan idan ya biyesuu sai sun bashi ciwon kai. Ayrah na shiga gida ta sa ki ajiyar zuciya ta rasa mai yasa a yanzu idan ta na tare da Mdee ta ke rasa nutsuwarta ganin sai murmushi ta ke kamar wata zautaciya ya sa Mama da ta ƙaraso gun ta dafata firgigit ta dawo hayyacinta "Ke kuma lafiya kike murmushi?" "Babu komai ni kawai ji nayi ina cikin nishaɗi" "Toh Allah ya kyauta" "ameen" ta ce ta na nufar cikin ɗakin na su kwanciya ta yi saman tabarma ta na kallon silin ɗakin da ya sha wuya ya ke bukatar taimako. Abincin Mama ta ajiye mata "Ki tashi kici abunci kinji" miƙewa ta yi ta na janyo yar karama samira shinkafa ce da wake da mai sai salat da aka yanka, ba Ayrah ba ko ni sai da na yi sha'awar cinta😁 bismillah ta yi ta fara ci dama wata irin yunwa ta ke ji lumshe idanunta ta yi "Wollah Mama wannan abunci na ki ya yi daɗi sosai" murmushi Mama tayi "Kodai na sa miki waigi ne" dariya ta yi ta na cigaba da cin abunci Su na tashi su ka fito dan tafiya ruwa ne ya fara zuba da sauri Jiddah ta karasa ta shiga motar jan luck ɗin ta yi ta rufe, Yusra da karasowarta kenan ta yi ta yi ta buɗe ta kasa drive ta ce ya buɗe ma ta wani kallo Jiddah ta watsa ma sa "Wallahi idan ka buɗe ma ta ko hmm" shiru ya yi ba ce komai ba "Wai sani me keke nufi ne ba cewa na yi ka buɗemin ba" dariya Jiddah ta yi ganin ruwa na ta dukanta, ganin jikinta ya fara rawa ya sa ta buɗe ma ta, da sauri ta shiga ta na ƙanƙame jikinta ko buntakan Jiddah ba ta yiba sani ne yaja motar su ka tafi. Suna isa gida da sauri Yusra ta fita ta yi apartment ɗinsu ta na shiga ta ga Momy zaune ita da Suhaima da gudu ta yi sama ta na isa ta cire kayan da ke jikinta ta sauya wasu faɗawa kan makeken gadon ta yi ta na sauke numfashi Washegari da wuri ta fita zaune ta samesa ya na danna waya zama ta yi kan kujera ta na gaidasa amsawa ya yi cikin sakin fuska suna isa suka fito a jare zuwa cikin Company tun da su ka jero p.a ke kallonsu ita ma zuwan ta kenan ta na pearking mota ta ga fitowarsu, ji ta yi hawaye ya gangaro ma ta Allah ya sa ni ta na son Suhail shiyasa bama ta so wani ya raɓesa shin ta ya zata raba Ayrah da Suhail? shine tambayar da taiwa kanta Ƙwafa ta yi ganin ta rasa mafita ta fito itama dan shiga ciki .Coffee ta aje masa akan table ɗin mug ɗin ya ɗauka ya na kaiwa baki, miƙewa ta yi dan barin office ɗin "Ina zaki" ya tambaye ta "Am dama zanje wajan Aunty Suhailat ne" "Shine kuma ba ki tambayeni ba" girgiza mai kai ta yi da sauri alamar a'a "Shikenan ki je amma karki daɗe dan anjima akwai inda zamu" "Thank you sir" ta faɗa tana murmushi Da sauri ta ke sauka daga kan stap ɗin ta na sauka ta ga p.a da Oga Abdul tsaye da'alama wani abun su ke wani kallo ya watsa ma ta ya na tsaki da sauri ta ratsa ta gefe ta yi wucewarta "Munafuka ce yarinya nan wallahi" p.a ta faɗa cikin hasala tana isa ta sameta zaune ta na dube dube a laptop. Zama tayi a kusa da ita murmushi Suhailat ta yi "Jiya ina ki ka shiga ban ganki ba" "Da wuri mu ka tafine shiyasa" "Ohk wai ni kam na tambaye ki man" "Eh ina jinki" "Kina zuwa sloon kuwa?" girgiza ma ta kai ta yi alamar a'a "Gaskiya toh ya kamata yau na kai ki saloon naga idan angyara miki gashi ya zaiyi" murmushi ta yi kawai mikewa ta yi tana kama hannuta "Zo muje kinga mu tambayi Mdee ko zai bari" tashi ta yi tabita su ka fita, su na isa Suhail ya ɗago ya na kallonsu "Sir dan Allah idan ba damuwa zamu fita da Ayrah" wani irin kallo ya ma ta da sauri ta sunkuyar da kanta "Idan kunfita kuje ina" taji ya ambata "Saloon" ta bashi amsa shiru ya yi na wani lokaci kafin ya ce "Shikenan muje na kaiku murmushi jindaɗi su ka yi su na kallon juna Baya suka buɗe za su shiga su duka "Ni ɗin drive ku ne da zaku shiga baya" "Sorry sir" "Ayrah ki shiga gaban kinji" "A'a Aunty Suhailat ke ki shiga" wani kallota ma ta wanda ya sa ta saurin buɗe gaban ta shiga, murmushi gefan baki ya yi dan dama hakan ya ke da buƙata beauty saloon su ka isa da ke garin abuja babban gurine na musamman wanda ya kayatu, akwai wajan saloon da lalle, wajan make up duk agun, fitowa su ka yi su ka nufi wajan saloon ɗin zama ya yi a gurin su kuma su ka karasa cikin wani glass "Madam gulo ce ta fito ta na tambayarsa abun da ya ke so nuna ma ta su Ayrah ya yi dake zaune cikin glass "Ki tambayesu" ya faɗa ya na ɗora kansa a jikin kujera lumshe idanunsa ya yi wani irin bacci ke fusgarsa Suhailat ce ta basu umarnin su yiwa Ayrah saloon mai kyau sannan ida sun gama su ma ta kalba kanana zaro idanu ta yi ta na turo baki "Allah ni Aunty Suhailat kar'amin kitso kedai kam anyi raguwa wallahi" "Dan Allah Aunty Suhailat" ta faɗa cikin shagwaɓɓa "Allah fa ke daina marairaice wa dan sai an miki" shiru ta yi kawai ɗago idanunsa ya yi dai-dai lokacin da ake warware mata kai masha Allah ya ambata cikin cool voice ɗinsa, cikin muntina da ba su wuce 30 ba aka gama mata komai bakaramin kyau kalba ta ma ta ba zubawa kan nata idanu ya yi tabbas yarinya Allah ya yi mata baiwa kala- kala "Sir" da sauri ya kalleta ya na mamakin yaushe ta iso nan? mikewa ya yi su ka nufi ƙofar fita su na shiga kai tsaye su ka sauke Suhailat a gida kallon Ayrah ya yi "Kin yi kyau sosai da wannan kitso" murmushi ta yi tana mamakin yaushe yaga kitson na ta "Kina mamakin yadda nagani ko?" ɗaga ma sa kai ta yi dan har ga Allah ta yi mamaki Buɗe murfin ta yi ta shiga ɗa ga ma ta hannu ya yi ya na murmushi, ta na shiga gida ta ga babu kowa a tsakar gida karasawa cikin ta yi Inna lilahi wainna ilayi rajiƙun Mai ta ke gani haka Ina ma'abota sun littfin a wani Company na ce ko kinsan har yanzu ba'a fara wasan ba ko kinsa cewa yanzu ne ƙadarorin Ayrah za su fara ohh ya rabbi ki hanzarta biya danjin yadda zata kaya Idan kinyi shirin biya 9165855674 Hauwau Umar Abdullahi opay. Ki turomin evidence ta wannan Number 09165855674 Karki bari a baki labari yar uwata.. littfina ₦300 ne babu tsada [8/13, 4:06 PM] Masoyiya 🤗🔥: https://chat.whatsapp.com/BW8T7i1jpeZ5QpVVl4hxuZ A WANI COMPANY BY HAUWAU OMAR CUTIE MEEYRAT MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS fallow my account Arewabook@hauwauomar05 Mikiya writer's Allah ya cigaba da haɗa kanmu sharin mutum da Aljan Allah ka tsaremu tabbas farin jini jama'a Allah ne ya bamu kuma muna alfahari da haka domin mu masoyan mu akullum sune mu mune su masoyan mu abun alfaharin mu. Page_14_15 "Good morning Ammi good morning ya Abrad" "Morning dear" Ammi ta faɗa. Ta na gamawa ta miƙe da sauri tana sumbatar Ammi fita tayi waje, samun Yusra ta yi tsaye ta na jiranta hararata ta yi "Wai ke kullum sai mutum ya ta jiranki?" "Sorry sisna ta faɗa ta na kama hannuta, drive na isa ta fito da sauri ko jiran Yusra batai ba. Tana gama shiryawa tafita. A ƙofar gidan ta ga motar Mdee da sauri ta buɗe ta shiga murmushi yayi yana kallonta suna isa ya fito zuwa cikin Company A hankali yake ziro santala-santalan ƙafa funsa daga kan makeken bed ɗin sanye ya ke cikin fararan sleep dress white masu matukar kyau da shaƙi badroom ya nufa dan watsa ruwa. Yana fitowa ya nufi wajan mero tabbas Abrad kyakyawa ne farine tass ƙwayar idanunsa blue sai bakinsa da ya kasance ƙarami pink color girarsa ta haɗe da sajen fuskarsa, yana da fafaɗan ƙirji jikinsa a murɗe Kamar mai gym lotion ya ɗako masu kyau da ƙanshi shi kansa salon shafa man abun kallone a wajan Abrad. Ya na gamawa ya taje kansa White ribom ya ɗako ya haɗe kansa dashi Yana gama shiryawa ya fito kai tsaye part ɗin Ammi ya isa tana ganinsa ta saki murmushi da sauri ya ƙarasa ya na kwanciya akan cinyarta wata irin nutsuwa yaji tana ratsasa shafa kansa Ammi tayi "Son ya kamata kaje wajan Momy ku ka gaidata" shuru yayi kamar bai jiba "Da kaifa na ke" "Please Ammi nifa bason shiga sabgar matarcen nake ba" "Naji ni dai nace kaje idan kuma bazaka jeba kai kasani ta faɗa tana turesa" "Sorry Ammina Insha Allah idan na fita zanje" murmushi tayi "Yawwa ko kaifa" Company Tura ƙofar office ɗin ta yi ta shiga ɗa ga idanu ya yi ya kalleta zama ta yi ta na gaidasa bai amsaba ya ciga da abun da yake. Kirane ya shigo cikin wayarsa ganin ya na murmushi ya sa da sauri kuma ya miƙe ya na yin gaba kobin takan Ayrah baiba ya kara gaba abunsa kai tsaye ya nufi airport da gudu ya karasa alokacin da jirgin ke sauka farin dattijo ne ke sakowa daga matata kalar jirgin da gudu ya nufi gun ya rungumesa "Oyoyo dad" murmushi dad yayi ya na shafa kansa kama hannunsa yayi suka nufi wajan motar, kai tsaye gida suka wuce dad zama yayi akan kujera Suhail yayi murmushi "Amma wallahi dad kamin bazata" "Ai dama na gaya maka ba zata zan maka" hira suka shiga yi "Dad amma dai nasan akwai abun da ya kawoka ko?" "Nazo ne kawai na ga ka my son Sannan akwai maganar da zamu yi da wani ne anan so ya ce min shima zai dawo daga uk yau shiyasa na zaɓi nazo nan saboda na ganka kuma naga yadda kake gudana da aiki a Company" tunawa ya yi da Ayrah da ya bari a office, da sauri ya miƙe yayi hanyar waje "Ina zaka kuma son?" "Ina zuwa dad company zani akwai abunda na manata acen ɗin" "Okay sai ka dawo" dad ya faɗa yana miƙewa dan haurawa sama Buɗe ƙofar part ɗin ya yi, ya shiga zaune ta ke ta ɗora kafa ɗaya kan ɗaya sai taunar cingom ta ke baƙace mai jiki ta na da katon baki amma saboda gyara da kuma wadata ya sa idan kaganta ba zaka gane hakan ba gefanta kuma wata yarinya ce wace aƙalla bata fi shekaru 22years a duniya treecotar ne ja a jikinta sai white riga mai adon ja yar karama hula ce akanta ba laifi yarinya ta na da kyau sai dai ita chocolate color ce. Zama ya yi akan kujera "Momy barka da safiya ya ku ke ya gida" ya faɗa duk lokacin ɗaya wani banza kallo ta masa kafin ta ce "Lafiya qlau ta na yatsina fuska, wani kallo ya watsawa suhaima da sauri ta duru kasa "Yaya barka da safiya" banza ya yi bai bata amsa ba Yusra ce ta shigo cikin falon da gudu sancewar dawowar su kenan daga makaranta ta na ganin Abrad ta karasa da sauri ta faɗa jikinsa ta na dariya shima dariya yayi "I miss you ya Abrad" "Miss you too baby ya school ɗin?" "Alhmdllh" "Masha Allah har yanzu baki daina wannan guje gujen ba ko hmm naga Ranar da zaku girma ya ranan" dariya ta yi ta na miƙewa da nufin haurawa sama tashi ya yi shima ya fice abinsa ko magana bai karawa Momy ba ya na fita taja tsaki da sauri suhaima ta miƙe ta zauna kan kujera "Wallahi Momy bakiji yadda najiba da naga ya Abrad ohh" ta faɗa ta na sauke numfashi "Ke dallah rufemin baki sha-sha-sha kawai duk ba tsoransa da kuke jibane ya kawo haka wallahi na tsani yaranan ita kuma Wannan shegiyar yar kullum ina nuna mata abunda ya dace bata ganewa" ita dai Suhaima shiru ta yi dan ta fahimci Momy ta ɗau zafi da yawa Ya na isa Company da sauri ya fito ya na shiga left, Zaune ya sameta akan kujera murmushi ya yi kawai "Ta so mutafi" babu musu ta miƙe tabisa, suna fita cikin mota ya shiga shiga ta yi itama yaja motar su ka tafi. Ya na sauke ta a gida ko magana bai mata ba yaja motarsa dan babban burinsa ya isa wajan dad ɗinsa tabbas ya san yau zai kwana cikin farin ciki gashi ga mahaifinsa "Ammi" "Ammi" shine abunda Jiddah ke faɗa ta na futowa daga bedroom "Menene haka Jiddah kike min irin wannan kira? wai ni yaushe zaki girma ne?' "Turo baki ta yi toh ni ba Abbey ne ya ce ya kira wayarki baki ɗaga ba shine ya ce na kawomiki" "Amma Jiddah fisabililahi sai ki dunga min irin wannan kiran" miƙa mata wayar ta yi ki sauri ki gama wayar Ammi ni game na ke" banza Ammi tai mata ta na ɗaga wayar sai da su ka daɗe su na waya kafin ta miƙa ma ta lokacin Jiddah ta cika fam kamar ta yi kuka, miƙewa ta yi za ta haura sama Yusra ce ta shigo cikin parlon da salama sanye ta ke cikin riga har ƙasa mai matukar kyau ba laifi Yusra kyakayawa ce sosai fara tass dan suna matuƙar kama da Jiddah gashinta ta zubo har baya, karsowa ta yi ta na faɗawa jikin Ammi "Oyoyo daughterna" "I Miss you Ammina na yi kewarki sosai" "Nima haka daughter na yi kewarki" tsaki Jiddah ta yi tai wuce warta kyale-kyalewa da dariya Yusra ta yi "Uwar kishi kawai wai Ammi ita Jiddah sai dai kita kulata ni banda ni" ta faɗa kamar zatayi kuka "Rabuda ita daughter ai bata isa ta raba ya da uwa ba" "Kinga ta so ni kiraka ni" tashi Suhaima ta yi su ka fita "Amma Momy drive zaki sa ya kimu ne?" "A'a wane irin drive dama kinga ina irin wannan tafiyar da drive ne" girgiza kai ta yi buɗe motar ta yi su ka shiga cikin sauri taja motar wani irin gudu ta ke akan titin tun su na cikin gari har su ka bar gari gaba ɗaya. "Ayrah" "Ayrah" ki tashi fa karki makara yau wane irin bacci ki ke haka sai tashinki na ke kinƙi tashi?" buɗe idanunta ta yi wanda har yanzu su ke ɗauke da bacci "Wallahi Mama yau wani irin bacci na ke ji" "Toh ya zakiyi ki tashi kar mutum yazo ya yi ta jiranki" miƙewa ta yi dan watsa ruwa. Ta na fitowa ta shirya miƙe ma ta kunu da ƙosan da ke gun Mama ta yi atsai tsaye ta ci ta fita dan tafiya ta na fita taga drive zaune acikin motar ƙara sawa ta yi ta shiga ta na gaidasa su na isa ta sauka ta yi ciki. Zaune ta samasa ya na duba wani File ƙarasawa ta yi ciki ta zauna "Good Morning sir" "Morning" tashi ta yi dan haɗamasa coffee "Ayrah" taji ya ambaci sunanta dawowa ta yi ta zauna dan tasan tunda ya kirata akwai wani abun ɗagowa ya yi ya kalleta harya buɗe baki zaiyi magana sai kuma ya cije laɓe ya na murmushi "Kawai jeki haɗomin coffee ɗin" miƙewa ta yi ta na tafiya cikin tafiyarta mai kyau da burgewa lumshe idanunsa ya yi ya na kallonta bazaka taɓa cewa ita ya ke kallo ba "My man kude ba'a ganinku sai shekara shekara" murmushi Abrad ya yi ya na kallon abokin nasa "Ina ta magana kamin shiru kaifa daɗina da kai mutum ya yi ta ma ka magana ka na jinsa" kwanciya ya yi ajikin kujera ya lumshe idanunsa ko kaɗan Abrad bai da yawan magana idan kagan shi ya na magana toh da Ammin sa ne ko kuma Jiddah da Yusra ya na matukar ji da su. Sai kuma dad ɗinsa wanda ya kasance sanyi idanunsa Gudu su ke kawai a tsakiyar falon Jiddah ce ta ce "Wallahi Yusra ki bani ni bana son haka" gwalo ta mata ta na cigaba da wulla taddy da ke hannuta ganin sun dage su na gudu akan taddy ya sa Ammi yin magana "Wai nikam dan Allah bazaku barni ba haba tun ɗazu kun sani gaba" gudunsu su ka cigaba dan su bama jin abunda ta ke faɗa su ke ba "Ai shikenan tunda na ce ku bari kunƙi bari na kira yayan ku na faɗa masa" da sauri su ka karaso gurinta suna rungumeta "Am sorry Ammi mun daina" A"u da kuna jina kenan shaƙi yanci ya sa kuka ƙi magana" Zuwa ta yi ta aje masa kan table ɗin har lokacin kuma idanunsa a rufe ya ke murmushi ta yi ganin kamar ya yi bacci ta sa ka hannuta ta na wulwulawa a wajan fuskarsa shiru ya yi kamar mai bacci, murmushi ta yi "Tunda dai ya yi bacci bari na tafi office ɗin Aunty Suhailat" gyaran murya ya yi, da sauri ta juyo ta na zare idanu Ina ma'abota son littfin a wani Company na ce shin kunsa dacewa littfi na na kuɗine shin me kuke jira saura ƙiris fa na gama free page har yanzu ba muyi komai ba cikin tafiyar littfin a wani Company ki hanzarta yin payment yar uwa saboda kar ayi wannan tafiyar babu ke kin san dai daɗi littafina da kuma ma'anarsa ba sai na faɗamiki ba shin kin shirya yin payment na littfina idan kin shirya 2318541707 Hauwau Umar Abdullahi UBA Bank Kowane mutum ance da ƙaddararsa Tabbas haka ya ke kamar yadda ƙaddara Ayrah ta fara da wani Company mai ɗauke da mabanbanta mutane masu halaye da ban da ban Ayrah ta haɗu da masoya wanda su ka nuna mata soyayya sai dai cash ashe wannan soyayyar zata zama matsala a cikin rayuwata Sister ki hanzarta kiyi payment ni na tabata bazaki Dana sani ba *Karku manta sunan littfin* *A WANI COMPANY* [8/13, 4:06 PM] Masoyiya 🤗🔥: https://chat.whatsapp.com/BW8T7i1jpeZ5QpVVl4hxuZ A WANI COMPANY BY HAUWAU OMAR CUTIE MEEYRAT MIKIYA WRITER'S ASSOCIATIONS Fallow my account Arewabook@hauwauomar Page_18_19 Da sauri ta ƙarasa shiga cikin ɗauki idanunta na zubda hawaye, jijigata tafara yi ta na kuka. Buɗe idanunta ta yi da ƙyar wanda su ka ma ta wani irin nauyi. kallonta Mama ta yi, menene ya faru da ke Mama? dan Allah ki tashi shine kawai abinda ta ke faɗa idanunta na tsiyaya da ruwa kama hannu ta yi tana matsewa a nata "Fatima" ta kirata cikin Normal sunanta "Ki yi haƙuri da rayuwa Fatima ki kula da rayuwarki ko ba na raye, kimin alƙawarin kare mutuncinki Fatima ina matukar ƙaunarki, ina jin kamar bazan tashi ba sai dai a kullum ina kuka rashin iyayena dan da na son in da su ke da komai zaizo mana da sauƙi ina matukar ƙaunarki Zarah" ta faɗa tana lumshe idanu "Mama dan Allah ki daina faɗar haka Insha Allah zaki tashi" murmushi kawai Mama ta yi da dugu ta shiga cikin ɗakin ta ɗako ledar magani ruwa ta ɗibo ta zo ta na bata gyaramata kwanciya ta yi bacci ne ya ɗauketa da sauri ta miƙe ta nufi bayi dan ɗauro alwala sallah t ayi raka'a biyu ɗa ga hannuta ta yi sama ta na kuka da roƙan Allah ya bawa Mamata lafiya Ta na idarwa ta kwanta a gefan Mama bacci ne ya dauke ta Washegari Alhmdllh Mama ta ɗan fara samun sauƙi Ayrah shara gidan ta yi tass kunu ta dama mu su bayan sun gama sha Mama ta kalleta "Ayrah ya kama ta ace kinje aiki" girgiza ma ta kai ta yi "Ki daure kije kinji insha Allah babu abunda zai faru da ni" babu yadda ta iya miƙewa ta yi ta nufi ciki ɗakin dan shiryawa ta na gamawa ta fito da hajjab har ƙasa murmushi Mama ta ma ta "Allah ya tsaremin ke a duk inda ki ke" "Ameen Mamana" ta faɗa ta na sumbatarta a kumatu tsaye ta ganshi a jikin motar da alama kuma dama ita ya ke jira tuntuni, tunda ta fito ya ke binta da kallo wani irin kallo ya kemata Wanda bai taɓa ma ta shiba dube-dube ta fara yi a jikinta dan ganin ko wani abune da sauri ya kawar da kansa ya na shiga cikin motar shiga itama tabyi yaja su ka tafi su na isa ya fito ya yi ciki ko left yau bai hauba ya nufi stap.. Shiga ya yi cikin office ɗin, dafe kansa ya yi ya na furza da wani wahalala numfashi shi kaɗai ya san abun da ke damunsa tabbas yau ce rana da ya kamata ya aiwatar da abunda zuciyarsa keson ya aiwatar ɗin. Da Salama ta shiga cikin office ɗin ɗaga kai ya yi ya kalle ta, nufar gurin haɗa Coffee ta yi da sauri ya dakatar da ita "Kije kawai bana bukata" ba ta damu ba ta nufi hanyar fita daga office ɗin ƙasa ta sauka wajan Aunty Suhailat ƙarasawa ta yi fuskarta ɗauke da murmushi "Ke Jiddah Jiddah ki tashi fa na ce" turo baki ta yi gaba tana jin haushin tashin da'a kamata wai Ammi sai ina bacci ki ta tashina" banza Ammi ta mata ta nufi kofa tai fucewarta a hankali ya ke sakowa daga bene Ammi ce ta tsaya ta na kallonsa murmushi ya yi lokacin da ya ƙaraso guri "Ammi kallon fa?" "Ai dole na kalle ka son yau na ga abun da ban taɓa gani ba, kai ne wai yau ka sa ka manya kaya? kuma ba karamin kyau su ka maka ba" dariya ya yi sosai wadda ta kara masa kyau Ammi dai kice sokike ki ce bana sa wa" "Da toh sawar ka ke ne" murmushi kawai ya yi "Anya babana ba wajan wa ta zaka ba?" haɗe rai ya yi kamar bai taɓa dariya ba dan in da abun da ya tsana a rayuwarsa toh bai wuce amasa maganar mata ba shi ya yi soyayya ma ya ce ya yi me shifa gaskiya har yau baiga wace ta isa ya sota ba, ganin ya haɗe rai kamar baya dariya ya sa Ammi cewa "Allah dai ya shiryaka Babana wai ni kam kai kullum idan aka maka zance budurwa sai ka sauya fuska shikenan sai kayi ta zama ba kai aure ba, kai kasani yanzu ka yi duba da Sa'a nin ka duk sunyi aure wasuma har ya'ya gare su" "Ammi su su kaga zasu iya wahala" ya faɗa ya na wucewa murmushi kawai Ammi ta yi tai gaba abunta dan yau ne Abieey zai dawo Nigeria Momy ce zaune a cikin bedroom ɗinta ta na waya sheƙewa ta yi da wata dariya "Ke dai bari kawai kawata ai komai na shirya shi yanda ya kamata yoh Allah na tuba taya zanyi sanya da wannan aiki idan kika ga ban aiwatar ba toh kice ni zainab an buneni ne a rami kinga a lokacin ai babu abunda zan iya" ta faɗa tana ƙara sakin shu'umin murmushi Yusra da ke tsaye a bakin ƙofar ɗakin duk taji abun da mahaifiyartata ta faɗa hawaye taji na zuba a fuskarta shin yaushe ne Momy za ta gane ta dai na irin wannan abubuwan? da sauri ta bar bakin ƙofar gudun karta fito ta ganta.. Cikin murna Fahad ya fito ya na murmushi ganin abokin na sa dan baitaɓa tunani da gaske zaizo gidan na saba kama hannusa ya yi su ka shiga cikin parlon zaunar da shi ya yi akan kujera ya nufi cikin bedroom ɗin ya na kiran Samha fitowa ta yi da fara'a "Badai har babban baƙon namu yazo ba?" "wallahi kin ga ko ya karaso' murmushi ta yi tana fita a ɗakin drinks ta ɗako da sincks ta nufi kan centar table ɗin ta ajiye ma sa "Ina yini brother" murmushi ya yi ya na kallonta "Lafiya qlau Samha ya gida" "Alhamdulillah yau dai Allah yayi munganka a gidan mu" "Ai kuwa dai" ya faɗa a taƙaice zuba ma sa juice ɗin ta yi ta na miƙe ma sa godiya ya ma ta ya na karɓa Suhailat ce ta dubeta "Kinga Ayrah bari naje office ɗin H.o.d na kaimasa wannan file kinji, yanzu zan dawo" "Toh aunty Suhailat sai kin dawo" fita ta yi ta barta a office ɗin haɗe hannuta biyu ta yi akan kuncita tun ɗazu babu abinda ta ke tunawa sai Mamata ko wane hali ta ke ciki yanzu lumshe idanunsa ya yi ya na jin wani irin ya na yi a jikinsa gaba daya jijiyoyin kansa sun tashi, p.a ce ta turo kofar tashigo sai da ta ambaci sunansa sau uku bai ɗago ya kalleta ba hakan ya sa ta ajiye file ɗin da ke hannuta ta yi ta fita ta na tunani ko menene ya faru da Mdee zama ta yi akan kujera da ta kasance mallakinta Shin kodai taje ta faɗawa Mdee tana son zuwa gida Saboda Mamata bata da lafiya? a'a gasky bazata iya ba tashi ta yi ta fita dan zuwa cikin lambu da ke Company, tana zuwa ta zauna kan fararen kujerin da ke gun lumshe idanunta ta yi ta na jin wani irin ya na yi shiba damuwa ba shi ba farin ciki ba "Ya Allah ka sa Mama ta na cikin ƙoshin lafiya" ta furta hawaye na bin gefan fuskarta "Ameen" taji an ambata a bayanta da sauri ta buɗe idanunta wanda su ke kawo ruwa Oga Abdul ta gani tsaye ya haɗe hannusa biyu akan ƙirji murmushi ya sakar Ma ta ya na zama akan kujera da ke gefanta fine girl ya faɗa ya na murmushi da shi kaɗai ya san ma'anarsa kawar da kanta ta yi da sauri kuma ta miƙe ta nufi hanya fizgota ya yi ta faɗa jikinsa, ƙoƙarin kwacewa ta ke amma ina gaba ɗaya ya ruke ta cizo ta gartsa masa da sauri ya saketa ya na dafe gun da gudu ta fita a wajan ta na haki dafe ƙirjinta ta yi ta na ambata sunan Allah Office ɗin Suhailat ta shiga ganin har lokacin bata dawo ba ya sa ta saki ajiyar zuciya mai ƙarfi zama tayi akan kujera shin wananan wane kalar bala'i ne Motoci ne yan uban su guda biyar ke shigowa cikin katafaran gidan da wani irin gudu Jiddah da ke tsaye a jikin window da gudu ta sako zuwa ƙasa a hankali ya sako ƙafarsa zuwa waje kyakyawan dattijo farine tass kana ganinsa zaka san cewa shine mahaifin Abrad saboda ya na yin Kamar su dai dai da kwayar idanunsu iri ɗaya ce rungumesa ta yi ta na murna "Oyoyo Abieeyna" "Oyoyo Mama" Abieey ya faɗa shima ya na rungumeta Yusra ce ta nufo gurin itama da buɗe hannusa ya yi ta faɗa jikinsa a hankali ya saki ajiyar zuciya ya na jin wani irin kewa da kaunar ya'ya na sa Momy ce ta fito ita da Suhaima itama rungumesa ta yi Murmushi Momy ta sa ki "urwelcome Sir" Murmushi ya ma ta ya na kallon Ammi da ke fitowa daga part ɗinta wani irin sanyi yaji na ratsasa lumshe idanunsa ya yi da sauri ta ƙaraso ta faɗa jikinsa, a tare kuma su ka saki ajiyar zuciya mai ƙarfi haushine ya ya turnike Momy da sauri ta wuce abunta, Bunta Suhaima ta yi ita ko Yusra taɓe baki tayi alamar ko a jikinta waige-waige Abieey ya fara yi tuntsirewa Jiddah ta yi da dariya dan ta san mai yake nema juyawa ya yi ya kalleta "Mamana lafiya daiko"? "Abieey na san fa wa ka ke nema toh sai dai kayi haƙuri dan ya Abrad dai bayanan tun ɗazu ya shirya ya tafi zance" ta faɗa ta na karayin dariyata mai kyau da sauri kuma ya juya ya kalli Ammi ya na son jin da gaske ne abunda Jiddah ta faɗa taɓe baki Ammi ta yi "Kadai san yarinya nan da shirma kawai dai bai san zaka dawo bane yau shiyasa ya fita kuma kaine kace kar'a sanar ma sa zaka masa bazata" baice komai ba ya kama hannuta su ka nufi ciki bunsu su Jiddah su ka yi a baya Yusra ce ta ce "Wai ke yarinya nan yaushe zakiyi hankali ki daina shirma?" turo baki ta yi gaba "Duk randa kika daina nima zan daina" Mtss Yusra taja tsaki dan gaba ɗaya Jiddah shirmanta ya ma ta yawa suna isa parlon ya haura sama dan hutawa bunsa Ammi ta yi "Nifa Ammi nasan yanzu kin daina kulamu saboda Abieey ya dawo ko" murmushi kawai ta yi tai gaba abunta dan ta san halin yaranan Suhailat ce ta shiga office ɗin ta zauna "Kin jini shiru ko siste" ɗaga ma ta kai ta yi alamar eh "Wallahi muntsaya wani aiki ne shiyasa ni kaina duk na gaji, ta so muje muyi sallah" babu musu ta miƙe tabi bayanta su na isa masjid ɗin su ka ɗaura alwala shiga su ka yi ciki, bayan sun idar Ayrah ɗa ga hannu tayi sama ta na rokan Allah akan ya bawa mahaifiyata lafiya ganin tana hawaye ta na addu'a ya suna fitowa Suhailat ta tambayeta lafiya ta ke kuka? rungumeta ta yi ta cigaba da kukan "Please Ayarh kiyi shiru ki faɗamin karki sani nima cikin damuwa" "Aunty Suhailat Mamana Mamana" "Menene ya faru da ita" "Bata da lafiya jiya da na je gida ko buɗe idanunta ba ta yi" "Ya salam shine kuma kikazo aiki yau Ayrah why' "Itace ta ce na zo yau saboda jikin na ta da sauƙi" "Okay toh kiyi shiru kinji kar mutane su ga kina kuka Insha Allah Allah zai bata lafiya" goge ma ta hawayen da ke fuskartata ta yi "Smile" ta faɗa duk dan ta sa ta cikin farin ciki murmushi ta yi _Yawwa Hajiyata ko ke fa kinga yadda ki ka yi kyau? da dariya nan kamar wa ta Ashwariya 😁" "Kai Aunty Suhailat ni ina na isa na zama Ashwariya" "Allah har kin fita Ayrah ki godewa Allah ke ɗin mai kyau ce" "Kinga zomu shiga ciki" binta ta yi su ka nufi ciki office ɗin Insha Allah anjima page 20 zai sauka wanda ya kasance page na karshe a free page shin me kike jira yar uwa har yanzu baki payment ba kin san dacewa yanzu nema wasan zai fara ohh ya rabbi Allah sarki Ayarh ko zataci jarabawoyin da suke bibiyarta sai dai muce Allah ya bata ikon cinsu Ayrah baiwar Allah *Littafi* *A wani Company* *₦300 babu tsada idan kinyi shirin biya* *9165855674 hauwau umar Abdullahi opay* *Zaki turo evidence ta wannan Number* *09165855674 * *Jinjinata agareku masoya na ina matukar ƙaunarku.❤️ Sosai kamar yadda kuke ƙaunata *MUCH LOVE LOVER'S* *_~MEEYRAT CE~✍️_* [8/13, 4:06 PM] Masoyiya 🤗🔥: https://chat.whatsapp.com/BW8T7i1jpeZ5QpVVl4hxuZ *A WANI COMPANY 🏬* *HAUWA'U OMAR* Cute Meerat. *MIKIYA WRITERS ASSOCIATION*. # SQUAD 2024. Page_20 *Last free page* Juyi yake cikin haɗɗaɗen office ɗin mai kamada fadar shugaban ƙasa idanunsa a rufe suke dan mutum na iya zaton cewa bacci yake a hankali ya furzar da nunfashi lokacin da yake buɗe idanun nasa wowwwww!! Masha Allah Mdee Suhail kenan cikakken matashi mai ji da kansa tattausan hannunsa ya sanya ya janyo telephone pole ɗin dake gefensa wasu ƴan nambobi ya danna sannan ya kai kunne cikin wata irin kasalalliyar murya mai nuna buƙatuwa akan wani abun ya furta "Ayrah!" Abinda ya iya furtawa kenan sannan ya ajiye wayar, P.A ɗin ta fahimci abinda yake nufi hakan yasa ta mike dan kiran wacce ya ambata ɗin. Wani irin kallo ta bisu dashi kamar na nuna ƙasƙanci sannan ta taɓe baki kamar ba zatayi magana ba sai kuma ta ce" keee!... dukkanninsu suka fuskanceta dan basu san da wacce take a cikinsu ba, haushine ya turniƙeta hakan yasa cikin fushi ta ce"kee ba dake nake magana ba Ayrah?" kallonta Ayrah tayi da lulu eyes ɗinta bata ce komai ba dan yawan magana ba ɗabi'arta ba ce "Mdee na kiranki Malama" ta fice daga office ɗin a fusace. Numfasawa Ayrah tayi sannan ta miƙe jiki babu kwari tayi waje. Turo ƙofar ta yi a hankali ta shiga gaba ɗaya bata jin wani ƙwari a jikinta ganin idanusa a rufe ya sa ta karasa ta zauna akan kujera murmushi ya yi wanda shi kaɗai ya san ma'anarsa sai da ya kai kusan five minute a haka kafin ya buɗe idanunsa da su ka yi wani irin ja tsoro ne ya kama ganin yanayin idanunsa ya sauya launi, miƙewa ya yi bai ce ma ta komai ba ya nufi bakin ƙofar ganin yasawa ƙofar luck yasa tsoro ya kamata dan hakan bai taɓa faruwa ba juyowa ya yi ya na kallonta ya ɗau tsawan lokaci ya na tsaye kafin ya cije laɓansa wani irin abu ya ke ji wanda bazai iya misaltawa ba shifa yau yaci alwashin cimma burinsa kuma tabbas zai bi zaɓin zuciyarsa. "Sir!! Sir!!" Murmushi ya yi lokacin da yake sake tunkarota har sannan kuma bata fasa kiran sunansa ba idanunta sun kaɗa sunyi jaa zallar tashin hankali ya wanzu akan fuskarta inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun wace irin mummunar ƙaddara ce ke neman tarwatsa rayuwarta me yake shirin faruwa ne??, Jin da tayi ta gagara yin baya ya tabbatar mata da cewa tazo ƙarshen bangone yayinda Suhail ke gabanta so close wanda har suna iya jin numfashin juna. Zufar da tagama wanketa take ƙoƙarin gogewa amma abun ya faskara bakinta sai rawa yake da alama akwai abinda takeson furtawa amma harshenta yayi mata nauyi hannayen Mdee da taji yana yawo akan fuskarta shine abinda ya ƙara tayar da hankalinta me Mdee ke ƙoƙarin aikatawa ne?, Daman ƙaddarar data kawota Companyn kenan?, wane wanda zai ceceta cikin wannan mummunan lokaci ya Rabb Ayrah ta furta cikin ranta, iskar da yake hura mata ita ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin data shiga ashe da gaske ba mafarki take ba! Da gaske *A WANI COMPANY* ne haka ta faru?, da gaske ita Ayrah ke cikin wannan mawuyacin halin?, Me zatayi wanda zata kuɓutar da kanta daga wannan masifar? Tamkar a mafarki haka zuciyarta ta ayyana mata wani abu wanda lokaci ɗaya ya yi tasiri cikin ranta har ta ɗauki hakan matsayin hanyar da zata kuɓutar da ita hakan yasa ta kalli gefenta hankali tashe glass cup ɗin da ke kan table ɗin ta janyo nufar wuyanta ya yi ya na shin-shina lumshe do yayi saboda wani ƙanshi turare da yaji wani zafin nama taji ya zo mata da sauri ta ɗaga kofi ta sauke ma sa aka da sauri ya ɗago ya na kallonta da runani idanunsa kafin ya yanke jiki ya faɗi agun dafe ƙirji ta yi tana zare idanu "Nashiga uku ni Ayrah me na aikata haka" da sauri kuma ta buɗe kofar ta fita da gudu ta wuce p.a ta sauka zuwa ƙasa ganin ta fito da gudu ya sa p.a ta shiga cikin office ɗin ihu ta saki ta na kuka "Nashiga uku ta kashe shi fita ta yi zuwa ƙasa ta na ƙwalawa security ku tareta karku bari ta fita ta kashe Mdee Inna lilahi" abun da ke fita a bakinta kenan lokacin kuma tuni Ayrah ta daɗe da fita gaba ɗaya daga Company dan gudu karma a ganta ta get ɗin baya tabi... Wani irin azababben gudu ya keyi dalilin kiran da aka yi masa tuƙin kawai yake amma a zahiri tunaninsa baya wajen sosai kwakwalwarsa ta shagaltu da tunanunnuka wanda suka yi masa ƙawanya cikin ransa,kyakkyawar bugawar da zuciyarsa ta yi ya sanya ya ja wani uban burki ji kake ƙiiiiiiiiiiiiii! a matuƙar tsorace da kuma tsananin tashin hankali yake kallon gabansa gabaɗaya tunaninsa ya tsaya cak meya aikata ne haka?, something fishy!. *_Kowacce ƙaddara tanada mafarinta kamar yanda ƙaddarar Ayrah ta kasance ƙarƙashin WANI COMPANY wanda yake da mabanbantan mutane masu mabanbantan halayya da kuma ɗabi'a Alhmdllh wannan page shine karshan free page hajiya ta ki zo ayi tafiyar da ke dan ni nasan bazaki dana sani karanta Novel ɗina ba... Shin ina Ayrah ta tafi? Mdee na raye ko ya mutu? dama Mdee ya na da wa ta manufa kenan akan Ayrah? Idan kinyi shirin biya. 9165855674 hauwau umar Abdullahi opay Sai ki turomin evidence ta wannan Number 09165855674