An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN:* *RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)* *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* *DA KUMA* *A SANADIN KAMA* Wannan littafin na kuɗi ne akan nera 200 kacal duk mai buƙata sai ya mun magana ta wannan layin 👇🏼 _08109634202_ Domin na sanar da shi yanda zai biya kuɗin. KADA KU MANTA KUMA ZAFAFA BIYU DAGA ƘAWAYE BIYU NE, IDAN DUKA BIYUN KA KE SO *A SANADIN KAMA* DA KUMA *ƘURUCIYAR SAPNAH* TO N300 KACAL, IDAN KUMA WANNAN KAƊAI KA KE SO N200 KACAL. ________________________ ________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com GODIYA: Dukkan godiya ta tabbata ga Ubangijin talikai buwayi babban sarki, wanda ya bani dama da iko na rubuta wannan littafin domin fadakarwa, cikin hikimarsa da iyawarsa. Tsira da aminci su ƙara tabbata ga Manzon tsira Annabi Muhammad (saw), da iyalan gidansa da sahabbansa. GARGAƊI: wannan labari ƙirƙirarren labari ne, na rubuta shi domin faɗakarwa da kuma nishaɗantarwa, ban yadda wani/wata ya juyamun labari ta kowacce fuska ba. Dafatar Allah ya sa wannan rubutun ya amfani al'umma. BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM Free Page 1️⃣ ↪️ 2️⃣ Y'an mata ne guda biyu a tsakar gidan, dambe su ke Sosai, hayaniyarsu ce ta fito da ita daga ɗakinta, kai tsaye gunsu ta je domin ta raba faɗan, a lokacin har kowaccen su ta ja da baya sun yi carko-carko kamar zakaru sai haƙi su ke. Tsayawa ta yi a gabansu ta na faɗar "Don Allah ku yi haƙuri." Mai da dubanta ta yi ga Babbar ta ce "Habah! Ke kuwa shamsiyya kiyi haƙuri mana, ke da ƙanwarki bai kamata ki bari aji kanku ba, don kawai ta saka kayanki ai...." Bata ƙarasa maganar ba saboda saukar wani gigitaccen mari da ta ji a kuncinta. A firgice ta ɗago don ganin waya aikata mata hakan. Idonta ne su ka sauka akan Shamsiyya ta na huci ta fara magana kamar haka "Ke Malama ki hita harkata ban kasa da ke balle ki ce za ki kwasa, banza y'ar matsiyata, da ba a san asalin balbela ba sai ta ce daga Makka ta ke, mun san komai da ki ke cewa bai kamata na yi faɗa akan ta sa kayana ba, na ga ai ba ubanki ne ya siya ba, da kuɗin yayana ne balle amin gori." Har ta juya za ta tafi, Shamsiyya ta yi saurin riƙe hannunta ta na faɗar "ina za ki tahiya? Ai ban gama ba takwan, na san dai da wannan Baban bugin na ki ki ke taƙama, wassani ma ko zaman dadiro kin ka yi gidansa a Abuja anzo an cuci yayanmu wai *A sanadin kama* aka samu wannan arziƙin..." Fincike hannunta ta yi daga riƙon da ta mata don zuwa lokacin ji ta ke kamar ta maƙure ta, kalaman sun mata zafi matuƙa, tabbas idan ta ƙara ko da mintuna biyu ne a gurin za'ayi ɓarna don a yanda ta ke ji za ta iya shaƙeta ko ta mata dukan Kawo wuƙa, sai dai wannan ya zama ƙarshen zamanta a gidan. Babban baƙin cikinta shine Innarmu ta na zaune a gurin tun lokacin da Shamsiyya ta fara mata ɗibar albarka, amma ko motsawa bata yi da zimmar hanata ba. Da gudu Mimie ta ƙarasa ɗakinta ta na matsar ƙwalla, har ta shige ƙaramin falonta mai kama da kurkuku saboda zaman sa ƙarami, ta na jiyo ihunsu su na mata dariya da izgili kala-kala. Mijinta ta tarar a zaune kan kujerar falo ya na danna wayarsa, ya ɗage labulen kofar domin ɗakin akwai zafi, da alama ya ji komai da ya ke faruwa a wajen. Guri ta nema ta zauna akan ɗayar kujera da ya ke kujera uku kawai ce a falon. Kifa kanta ta yi akan hannun kujerar a hankali ta fara rera kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro. Har izuwa lokacin ko ɗago kansa bai yi ba bare ta saka ran zai kulata har ya bata haƙuri, sai danna wayarsa ya ke abunsa. Da ya ga za ta dame shi da kukanta kawai sai ya miƙe yabar mata ɗakin gaba ɗaya. Kuka ta ke sha sosai zuciyarta cunkushe da baƙin ciki kala-kala, haƙiƙa ta riga ta saba da irin wannan cin mutuncin da mutanen gidan su ke yi mata, sai dai na yau yafi baƙanta mata rai, Daddynta wanda ta ke matuƙar girmamashi da sonsa a ranta, wanda duk duniya banda iyayenta a yanzu ba ta da tamkarsa, wanda ya kyautata rayuwarta, shi ne yau ake alaƙantata da shi ta hanyar alfasha gaskiya ba za ta iya jura ba. Abunda yafi yi mata ciwo ma shi ne Uncle ya na Zaune ya na ji amma bai yi yunƙurin ɗaukar mataki ba hasalima ko rarrashin ta bai ba, to ina ƙaunar da ya ke mata ina son da ya ke iƙirarin ya na yi mata. Shine fa wanda ta bijirewa shawara iyayenta saboda shi domin ta na ganin cewa ya fi kowa sonta, amma yau shine ya ke wulaƙanta ta. Haƙiƙa ta yi nadamar bijirewa iyayenta da ta yi a shekarun baya. Ta na kawowa nan a tunaninta ta kuma rushewa da wani matsanancin kuka. Kukanta ta ke sha sosai babu mai rarrashi, ta na cikin wannan halin ne kiran Daddy ya shigo wayarta. Dakatar da kukan ta yi tare da ƙoƙarin sai-saita nutsuwarta kafin ta ɗaga kiran. Cike da fara'ar ƙarfin hali su ka gaisa, anan ta ke tambayarsa "Ya su Momy da yaya Saheen? Na yi missing ɗin su da yawa" "Su na qlau." Ya karɓa mata, sai dai ya fahimci da akwai yanayin damuwa a muryarta duk iya ƙoƙarin ɓoye hakan da ta yi kuwa. Saboda haka ya ce "Mimiena meke damunki ne?" Cikin in.. ina ta ce "Bakomai Daddyna me ka gani ne?." "Bakomai kawai dai ina ji a jikina cewa da akwai wani abun da ki ke ɓoye mun, amma dai shikenan tunda kince bakomai, fatana shine ko da yaushe ki kasance cikin farin ciki." "Lah! Daddyna ba fa komai, ta ya ka ke tunanin zan ɓoye maka wani abu?." Ta faɗa ta na y'ar dariya kai da gani ka san ƙarfin hali kawai ta ke. "Shikenan ina Bassam, ki ba shi mugaisa." "Yanzun nan ya fita Daddy, sai dai idan ya shigo zan sanar masa." "Ok idan ya zo ki ce ya kirani, ina son magana da shi, ki kula da kanki Mimiena sai anjima." "Ok Daddyna bye, ka gaida mutan gidan." Daga haka ya kashe wayar, kamar jira ta ke ta na ganin tsinkewar wayar ta kuma rushewa da wani kukan ta na faɗar "Allah sarki Daddyna mai yawan ƙaunata, ka yi haƙuri ba zan iya sanar da kai halin da na ke ciki ba, ina tsananin jin kunyarka na ƙin jininka da na yi, ta yaya zan gaya maka cewa wanda na ƙi ɗanka akansa ya na wulaƙanta ni yanzun? Inah! Bazan iya ba." Wata doguwar ajiyar zuciya ta ja ta sauƙe sannan ta ci gaba da cewa "Allah sarki! Yaya Sameer Allah ya baka lafiya, ka gafartamin na saka rayuwarka acikin garari da na yi saboda son zuciyata, ga shi yau wanda na guje ka a kansa ya juya min baya, rayuwa ta mun ƙunci ba shakka alhakinku ne ke bibiya ta na butulce maku.." A haka ta wanzu ta na waɗannan sambatu cikin kuka har zuwa wani lokaci mai tsawo. ®®®®®®®®®®® Bassam ne ya shigo ɗakin a kufule, inda ya barta anan ya same ta sai dai zuwa lokacin ta daina kukan sai dai sheshsheƙa, ta yi zurfi a tunaninta ta tsinto muryarsa ya na faɗar "Ke! Ke!! Ke!!!." Cikin tsawa. Firgigit! Ta yi ta na kallonsa a tsorace. "Ke! Wane irin iskanci ne wannan, ki zo ki ƙunshe a ɗaki har zuwa wannan lokacin ba tare da kin ɗora mana girki ba? Sarai kin san ba na son ɓata lokaci a dukkan lamurana." "Ka yi haƙuri uncle ba na jin daɗi ne yanzu zan je na ɗora." "Da ya fi miki kam." Ya faɗa ya na ƙoƙarin zama akan kujera. Cikin hanzari ta miƙe ta nufi waje, domin ta san abinda zai iya faruwa idan ta ƙara ko da minti ɗaya ne, domin da alama an zugoshi shi isa ya zo zai balbaleta da bala'i. Tsakar gidan ta nufa gurin murahu ta na ƙoƙarin haɗa itace, a bayanta ta jiyo ana Faɗar........ Ya kuka ji readers? Wannan salonsa dabam ne da sauran, amma sai na ji daga gareku yawan Comment ɗin ku shi zai nu namin yanda ku ka karɓi abin, Acigaba ko yaya? Ga mai buƙata zai tuntubeni ta wannan number👇🏼 _08109634202_ Domin karin bayani. SHARE & COMMENT. UMMU INTEESAR CE❤️❤️❤️❤️❤️ 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN:* *RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)* *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* *DA KUMA* *A SANADIN KAMA* Wannan littafin na kuɗi ne akan farashi mai sauƙin N200 kacal, duk mai buƙata sai ya mun magana ta wannan number👇🏼 _08109634202_ Domin na sanar da shi yanda zai biya kuɗin. KADA KU MANTA KUMA ZAFAFA BIYU DAGA ƘAWAYE BIYU NE, IDAN DUKA BIYUN KA KE SO *A SANADIN KAMA* DA *ƘURUCIYAR SAPNAH* TO N300 NE KACAL, IDAN KUMA WANNAN KA KE SO ZA KA BIYA KUƊIN KARATU N200 KACAL. ________________________ ________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Free Page 3️⃣↪️4️⃣ A bayanta ta jiyo ana Faɗar "To Malalaciyar banza shi haɗa itacen shi aw-wani aiki? Da kin ka tsaya ki na abu solai-solai kamar mara lakka?." Shiru ta yi bata tamka ba, Innarmu ta cigaba da cewa "ki yi sauri ki gama ki ba mu murhu y'ar hutu, ai ki za mu yi aiki ." Daga haka ta juya ta koma inda ta fito. Girgiza kai kawai ta yi ta cigaba da aikinta ƙwaƙwalwarta cunkushe da tunani iri-iri. Sai a lokacin ta tuna da saƙon Daddy, rufe tukunyar ta yi bayan ta haɗa komai sannan ta wuce ɗakinta don sanar da shi saƙon. ®®®®®®®®®® Ɗagawar ta daga gun ke da wuya Shamsiyya ta laɓaɓo ta zabga mata gishiri mai yawa a miyar, ta rufe tukunyar kamar yanda ta same ta a farko, ta juya ta bar wajen ta na murmushin mugunta. Ƙarasawa ta yi gun Zinnira da ke tsaye can gefe ta na kallonta , hannu ta ba ta su ka tafa ta ce "Kai anma gaskiya ke iya mugunta Shamsiyya, shiyassa ni ka bala'in sonki, yau za mu yi kallon casu a gidan nan." Ƙara tafawa su ka yi su na dariya da shewa ta ce "Ai wallahi Zinnira ba ki san yanda na tsani matagga ba, ni wallahi ke kaɗai na ke so yayana ya aura na san za mu shana, da ba don mu na cin arziƙinta ba agidan nan da tuni ta bar gidan wallahi." A haka su ka ta gulmar su su na dariya. ®®®®®®®®®®® A uwar ɗakanta ta Same sa ya na kwance da alama yunwa ce ke nuƙurƙusarsa, ƙarasawa ta yi kusa da shi ta ce "Dama na manta ne ɗazu mu ka yi waya da Daddy ya ce ka kira shi idan ka dawo." Miƙewa zaune ya yi a fusace ya ce "Me zan ma shi da ya ke nema na? Ni fa wannan mutumin ya fara takura mun, ko Baba da ya ke mahaifinki ba ya mun takurar da wannan mutumin kemin Why?" Sassauta murya ta yi sannan ta ce "Na ga wata ya zo ƙarshe ƙila kuɗi ya ke so ya tura ma ka ne kamar ko wanne wata." Washe baki ya shiga yi, shi ya manta shaf da ƙarshen wata ya zo dama ya na cikin buƙatar kuɗi don haka ya ɗauki wayarsa ya shiga neman layin Daddy. Kafin ta shiga ya kalleta ya ce "Na manta wallahi, kin san Daddy akwai ƙoƙari ba ya gajiya da hidimta mana, ko ke ce *Real Mimie* iyaka kenan. Har ta tsinke ba'a ɗaga ba ya shiga nema a karo na biyu tare da Faɗar "Mimien Daddy kenan y'ar Albarka tafi abinki ki cigaba da aikinki bari mu yi waya." Ficewa ta yi daga ɗakin ta na murmushin yaƙe "Hmmm! Uncle kenan an ji zancen kuɗi daɗin baki ya tashi, Daddy bai san cewa wacce ya ke turo kuɗin saboda ita ko ƙwandala bata mora aciki ba." Ta faɗa a ranta. Ta na ida sa isowa gun girkinta su ka bushe da dariyar mugunta Sakina da ta fito yanzu daga ɗakin su ta dubi Mimie ta bushe da dariya, mayar da dubanta ta yi ga Shamsiyya ta ce "Kai gaskiya yaya amma fa ke y'ar hutu ce, duba fa tsabar hutu da sabon zaman gidan daula ko itace baki iya sawa ba ga murhu." Dukkan su su ka bushe da dariya. Ita dai bata tamka su ba duk da ta sani sarai da ita su ke, girgiza kai kawai ta yi ta cigaba da aikin gabanta. Tabbas ta tabka babban kuskure a rayuwa sai yanzu ta gasƙata zancen malam ba haushe da ya ke cewa duk abinda babba ya hango yaro ko ya hau Rimi ba zai hango shi ba, a baya soyayya ta rufe mata ido ta kasa hango abinda iyayenta su ke nuna mata ga arziƙi na kiranta amma ta rufe ido ta saka ƙafa ta murje, ta tabbatar cewa da yaya Sameer ne a matsayin mijinta yanzun tabbas da ba zai mata irin wannan wulaƙanci ba, ko dan yawan soyayyar da ya ke yiwa *Real Mimie* da kuma kamar da su ke yi, shiyasa su ka mayar da ƙaunar akanta. Da yanzu ta na kwance miƙe da ƙafa acikin sanyin A.C sai dai a mata duk abinda ta ke so bare ma har ta yi wani girki can. Haka ta cigaba da tunani da kukan zuci har ta kammala girkinta, kuloli ta ɗauko ta ɗibarwa kanta mijinta sauran kuma ta zube a babbar kula ta ɗauka ta kaiwa Innarmu. ®®®®®®®®®®® Bayan ta kai ma shi abincin ta zuba ma shi a plate, durƙusawa ta yi agabansa ta ajiye, shinkafa ce da miya. Saukowa ƙasan ya yi ya na wani ciccin magani, wai shi a dole ransa ya ɓaci na rashin gama girkin da wuri, ko uffan bai ce mata ba ya ɗauki cokali ya ɗiba abincin zuwa bakinsa. Da sauri ya furzar da lomar bakinsa, sakamakon wani zau da ya ji har cikin kunnuwansa. A gigice ya miƙe zuwa waje ya ɗebi ruwa ya na kuskure bakinsa. Su Zinnira da ke gefe su na kallonsa sai ƙunshe dariya su ke don kada ya ji. Ita kuwa Mimie tun lokacin da ya furzar da abincin ta ke binsa da kallo har zuwa lokacin da ya bar ɗakin, biyo bayansa ta yi don ganin me ya same shi, idonta ne ya sauka akan su Shamsiyya da ke famar ƙunshe dariya, nan da nan ta zargi wani abu akansu. "Me ya faru uncle?" Ta tambaye shi. Juyowa ya yi a fusace ya zabga mata wata uwar harara ba shiri ta koma ɗakinta cikin hanzari. Shima bin bayanta ya yi a kufule, nan fa y'an matan su ka bushe da dariya harda k'yalk'yalawa. Tafiya ta fara yi ta na nufar ɗakin, cikin zafin nama Zinnira ta yi taku ɗaya ta damƙo ta ta na faɗar "Ina za ki?." Dariya ta yi ka na ta ce "Bin su zan yi in ga yadda za'a kwashewa." Fiddo ido wa je ta yi ta ce "Ashe ba ki da hankali Shamsiyya? In ya gane ki hwa?." "Ke taho mutahiya in kuma ba ki zuwa banni Ni in je." Daga haka ta fusge hannunta ta ƙara gaba abinta. ®®®®®®®®®® A can cikin ɗakin kuwa bayan shigewar su Bassam ne ya rufe ta da masifa inda ya ke shiga ba nan ya ke fita ba Faɗar ya ke "Wannan wane irin abinci ne haka? Wato zaman Abuja ya lalata ki har kin manta yanda ake girki koh?" "Wai me abincin ya yi Uncle?" "Au tambaya ta ma ki ke? Ai ki na da harshe sai ki ɗanɗana ki ji." Ya faɗa a tsawance. Da sauri ta je gun Abinci ta ɗanɗana ba shiri ta furzar da shi tare da zaro ido waje, ya akayi haka? ita fa gishiri kaɗan ta san ta zuba a girkinta, nan ta tuna sanda ta ga su Shamsiyya na dariyar ƙeta ba ko shakka su su ka mata wannan aikin..... Kada ku manta wannan book ɗin na kuɗi ne akan N200 kacal, ga mai buƙata sai ya tuntubeni ta whatsapp number ɗina👇🏼 _08109634202_ Follow me on Wattpad @ UMMU INTEESAR UMMU INTEESAR CE❤️💚🧡💙💛 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)* *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* *DA KUMA* *A SANADIN KAMA* Wannan littafin na kuɗi ne akan Naira 200 kacal, duk mai buƙata sai ya mun magana ta whatsapp number na👇🏼 _08109634202_ Domin na sanar da shi yanda zai biya kuɗin. KADA KU MANTA KUMA ZAFAFA BIYU DAGA ƘAWAYE BIYU NE, IDAN DUKA BIYUN KA KE SO *A SANADIN KAMA* DA *ƘURUCIYAR SAPNAH* to N300 ne kacal, idan kuma wannan kaɗai ka ke so za ka biya kuɗin karatu N200. ________________________ ________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Free Page 5️⃣↪️6️⃣ Ɗagowa ta yi a firgice fuskarta ta bayyanar da firgici ƙarara ta ce "Wallahi Uncle ba haka na yi girkina ba, ban san ya aka yi gishiri ya yi yawa ba ka yi haƙuri don Allah ba......." Ba ta samu damar ƙarasawa ba saboda jin saukar wani lafiyayyen mari da ta yi a ƙuncinta. A tare su ka zazzaro ido shi da ita, ita ta na mamakin yanda ya mare ta abinda bai taɓa yi mata ba a rayuwa. Shi kuma ya na mamakin tayaya ya mare ta? Me ya hau kansa? Allah ya gani bai ɗaga hannu da nufin marinta ba sai don ya mata gargaɗi. Shamsiyya da ke laɓe ta taga ta na kallon bidirin da ake a falon ta bushe da wata ja'irar dariya har ta na riƙe ciki. Jiyo sautin dariyar ne ya saka ya yi saurin dubar gurin da sautin ke fitowa, cikin hanzari ta juya da zimmar barin wajen ƙirjinta na lugude, "Shikenan yau kashina ya bushe." Ta faɗa a ranta. Ke! Ta jiyo sautin muryarsa ya na daka mata tsawa, yi ta yi kamar bata ji ba, za ta wuce ya ce "Da ke na ke munafuka zo nan." Jiki na ɓari ta ƙarasa ya zazzare mata ido ya na faɗar "Uban me ki ke leƙe a tagar?" Shiru ba amsa, ya kuma daka mata tsawa a karo na biyu ya ce "Na ce uban me ki ke leƙe? Wato dama ashe laɓe ki ke mana koh?." "Ya...yaya kayi hak ƙuri." Ta faɗa cikin in Ina. Wanke ta da mari ya yi sannan ya ce "Don ubanki gobe ma kya ƙara mana laɓe, ɓace mun da gani munafukar banza." Sum, sum ta ja jiki ta bar gurin tamkar wata munafuka(ko da ya ke munafukar ce ma). Ɗakin ya koma ya na bawa matarsa haƙuri Faɗar Ya ke "Don Allah Mimiena ki yi haƙuri ban san me ya hau kaina ba har na mare ki wallahi ban aikata hakan da niyya ba, ina son ki matata amma na rasa me ya sa na ke mi ki irin haka, sanda mu na wancen gidan na birni ai ba haka zaman mu ya ke ba dawowa nan ne ya sa....." Bai ƙarasa maganar ba saboda Muryar Innarmu da ya jiyo tun daga waje ta na sababi ita don me za'a dakar mata y'a akan wata jaka, fitowa ya yi ya bata haƙuri ya lallaɓata a ka wuce gurin. FLASH BACK WACECE MIMIE? Cikakken sunanta shine Zuhriyya Sadeeq Yusuf, amma iyayenta da y'an uwa su na kiranta Zuhra. Zuhra y'a ce ga Malam Sadeeq Yusuf Bicci, haifaffen ƙauyen Bicci ne ta jihar Kano. Shi talaka ne mai ƙaramin ƙarfi sana'arsa ita ce kanikanci, da kuma wannan sana'ar tasa ne ya ke ciyar da iyalansa da duk wata buƙata ta su wacce bata fi ƙarfinsa ba. Shi Mutum ne mai wadatar zuci hakan ya sa ba ya hangen abin hannun kowa ciki harda y'an uwansa da su ka kasance ma su rufin asiri sosai saɓanin shi. Matarsa ɗaya Malama A'isha wacce ta kasance uwar ƴaƴansa wato maman Zuhra. Ta na da yayye maza guda biyu, Kabir wanda ya kasance shine babban yayansu sai Sagir wanda ke binsa, sai farida sai kuma ita Zuhran sai ƙaramin ƙanensu Ma'aruf wanda shine ƙarami daga kansa Malama A'isha bata ƙara haihuwa ba, yanzu har yara sun girma. Inda Kabir ya yi aure da matarsa mai suna Zainab su na kiranta da Anty Zee, su na da yara Uku Khalifa wanda ya ci sunan Baba wato (Abubakar Sadeeq). Siddiqa da kuma ƙaramin Lameer, Shekara Shida kenan da aurensu. Yaya Sagir kuwa ya yi aure 2years ago matarsa bata haihu ba har yanzu. Yaya farida ma ta yi aure tuni da mijinta mai suna alƙasim ta na da ƴaƴa Uku Salim, Safnah da Amir ga cikin na huɗu kuma. Sai ita Zuhran da ta ke da Shekara biyu da aure, an mata aure ne bayan ta kammala Secondary school ɗinta anan jihar kano lokacin ta na da Shekaru goma sha takwas a duniya. A lokacin Ma'aruf ya na jss3, a wannan shekarar zai kammala Secondary. Duk da cewa mahaifinsu talaka ne hakan bai saka rayuwarsu a ƙunci ba sun ta so cikin kulawa da tarbiyya mai kyau, mahaifinsu ya na iya ƙoƙarinsa gurin kula da karatunsu dukkannin su a makarantar gwamnati su ke karatu, baya wasa da abinda ya shafi ilimi, saboda haka ƴaƴansa su ka kasance ma su ilimin zamani da na addini dai-dai gwargwado. ®®®®®®®®®® Yaya Kabir malamin makaranta ne ya na koyarwa a wata Secondary school anan cikin garin Kano, shine ya ke taimakawa mahaifinsa gurin kula da wasu buƙatun gida a wancan lokaci. Duk wata idan ya karɓi Albashinsa ya ke rabawa biyu, rabin ya yi bukatarsa da ta iyalansa sauran kuwa ya siyo ma su kayan abinci ya ajiye. Yaya Sagir ma ya na iya ƙoƙarinsa duk da cewa a lokacin bai samu damar cigaba da karatu ba sai ya ke aikin ƙarfi. Da ɗan abinda ya ke samowa ya ke biyan buƙatarsa da taimakawa ƙannensa ta bangaren karatunsu. Dukkan ƴaƴan nasa Allah ya saka ma su albarka su na iya ƙoƙarin su gurin ganin sun faranta ma iyayensu, kafin shigowar Alhj. Salman cikin rayuwarsu. Alhaj Salman ya kawo haske a rayuwarsu don yanzun haka Baba ya na zaune da iyalansa a gida mai kyau cikin sukuni da walwala duk a sanadiyyar Alhj Salman. Haƙiƙa *Sanadin kama* rayuwarsu da ta y'ar su ta haskaka, haɗuwar Alhj Salman da Zuhra ya za me ma su alkhairi a rayuwa. Ga mai buƙata sai ya tuntubeni ta wannan number👇🏼 _08109634202_ Domin na masa garin bayani. Follow me on Wattpad@ ummu inteesar Vote,share & Comment. UMMU INTEESAR CE❤️💛💙🧡💚 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)* *MARUBUCIYAR:* *SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* *DA KUMA* *A SANADIN KAMA* ________________________ ________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Free Page 7️⃣↪️8️⃣ Zuhra ta kasance kyakkyawar yarinya ta gaban kwatance, ita fara ce ba sosai ba, ta na da matsakaici tsayi, siririya ce amma bata cika rama ba. Ta na da mayalwacin gashi da ya sauko a kafaɗunta ga shi da laushi da santsi, idanuwanta farare tas kamar madara. A taƙaice dai ka na ganinta ka ga bafulatanar asali. Ta na karatu a makarantar y'an mata da ke unguwar gandun albasa. Duk da cewa ta na karatu a makarantar gwamnati ne amma hakan bai hana ta mayar da hankalinta akan karatunta ba, don ita ɗin mai ƙwazo ce, ta na da fahimta sosai ga basira, Allah ya yi mata tarin baiwa wacce ba ko wace yarinya ce ta ke da ita ba. Labarin ya soma ne a lokacin da ta ke Ss1 a Secondary school. A wata ranar Laraba da misalin ƙarfe 7:45 na safe tsaye ta ke a gefen titin unguwarsu ta na neman abun hawa, sanye ta ke cikin uniform ɗinta Riga da wando, da hijabinta iya gwuiwa. Ƙafafunta sanye su ke cikin safa fara da sandals na makaranta, jakar makarantarta na rataye a kafaɗarta. Ka na ganin ta ka san ta na cikin yanayin damuwa, ta ƙagu ta ganta a makaranta, don ta kusa ta yi latti, amma ga shi ta shafe kusan mintuna goma bata samu abun hawa ba. Wata mota kirar Honda Civic ta zo wucewa a gabanta, har ya wuce sai kuma ya yi reverse ya dawo, a gabanta ya tsayar da motar. Sauke gilas ɗin motarsa ya yi tare da cewa "Assalamu alaikum y'an mata." Ta karɓa mishi da "wa'alaikumus salam." Ta na ƙoƙarin matsawa gaba. Da sauri ya ce "Ba ki ji ba y'an mata." Juyowa ta yi ta kalle sa ba ta ce komai ba. "Idan ba damuwa ki zo na rage ma ki hanya na ga kamar kin kusa latti koh?" Ya faɗa. Girgiza mishi kai ta yi alamar A'a ta ce "Ka barshi na gode." "Da dai kin shigo na kai ki domin da alama yau abun hawa na wuya a gurin nan ga lokaci na tafiya." Ta so ta yi gardama a karo na biyu amma sai ta ga idan fa ya wuce da wuya ta sami wani lift ga shi ta jima bata samu napep ba, saboda haka ta ƙarasa bakin motar ta buɗe ta shiga ta na faɗar "Nagode sosai." Murmushi ya yi ya kalleta bai ce komai ba ya cigaba da tuƙinsa cikin nutsuwa da ƙwarewa. Sun ɗan fara nisa a tafiyar ta ɗago ta kalle sa da alamar mamaki a fuskarta, da alama akwai Magana a bakinta. Shima kallon tan ya ke, ya ce "Ki na mamaki ban tambaye ki wace makaranta za ki ba koh?" Ɗaga masa kai ta yi alamar eh. Murmushi ya kuma yi a karo na biyu ya ce "Saboda na sani ne, ko ba Makarantar yan mata ta gandun albasa ba?." Kallonsa kawai ta ke cike da mamaki ta ce "Eh ita fa." Daga haka bata kuma cewa komai ba ta mayar da hankalinta akan titi ta na saƙe-saƙe a ranta. Shi kuma murmushi kawai ya ke lokaci zuwa lokaci ya na satar kallon ta "Ta na da kyau masha'allah." Ya faɗa a ransa. A haka su ka cigaba da zaman kurame har su ka ƙaraso dai-dai gate ɗin makarantar. Faka Motarsa ya yi agefen titi, sai a lokacin ta kalle sa sosai ta ce "Nagode sosai yanda ka taimakamin Allah ya taimake ka." Daga haka ta buɗe motar ta fita ta na murmushi ta yi cikin makarantar a lokacin bai fi saura minti uku ba takwas ta yi. Kallonta ya dinga yi har ta ɓace masa acikin sauran ɗaliban da ke ƙoƙarin shiga makarantar sannan ya tada Motarsa ya tafi ya na jin wani abu na masa yawo a ransa game da yarinyar har ya ƙarasa office ɗinsu da ke cikin gidan nepa na ƙofar ɗan agundi. ****************** Bayan shuɗewar kwana biyu zaune ya ke a office ɗinsu da safe ya yi shiru, ka na ganin yanayinsa ka san zuciyarsa ba ta gun aikin da alama ya zurfafa a tunani. Can ya sauke doguwar ajiyar zuciya ka na ya janyo wayarsa ya kira wata number, har ta kusa tsinkewa aka ɗaga daga can ɓangaren abokinsa ne ya masa sallama. Amsa masa ya yi a taƙaice sannan su ka gaisa ya ce "Yawwa almustapha na ce ai a makarantar y'an mata ta gandu albasa ka ke aiki koh?" "Eh a can na ke wani abun ne?." Ya mayar masa da tambaya. Bassam ya yi murmushi ya ce "Bakomai gobe zan zo da safe na same ka a makarantar akwai wata yarinya ce da na gani kuma acan makarantar ta ke, ta kwanta mun a rai." Y'ar dariya Almustapha ya yi sannan ya ce "Wow! Wannan wace mai sa'ar ce? Gaskiya har na ji na ƙagu na ganta, ya sunan matar tamu ne?" Shi ma dariyar ya yi ya ce "Kai Ni dai sai anjima, me ka ke yiwa sauri idan na zo ai za ka ji ka gani." Dukkan su su ka saka dariya sannan su ka yi sallama ya katse wayar. Ya kuma tsunduma a tunani....... Ga mai buƙata sai ya tutuɓeni ta wannan number👇🏼 _08109634202_ Domin na gaya masa yanda zai biya. Follow me on Wattpad@ummu inteesar Vote, share & Comment UMMU INTEESAR CE❤️💛💙💚🧡💚🧡 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)* *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* *DA KUMA* *A SANADIN KAMA* WANNAN LITTAFIN NA KUƊI AKAN NAIRA N200 KACAL. KADA KU MANTA KUMA ZAFAFA BIYU DAGA ƘAWAYE BIYU NE, IDAN DUKA BIYUN KA KE SO *A SANADIN KAMA* DA *ƘURUCIYAR SAPNAH* TO N300 KACAL, IDAN KUMA WANNAN KAƊAI KA KE SO TO ZAKA BIYA KUƊIN KARATU N200 KACAL. ________________________ ________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Free Page 9️⃣↪️1️⃣0️⃣ Ya Kuma tsunduma a tunaninta, a ranar haka ya wuni sukuku. Ko da ya je gida ma ba wani barcin kirki ya yi ba, saboda ya ƙagu gari ya waye ya je ya kuma haɗuwa da ita a karo na biyu, haƙiƙa idanuwansa na marin ganinta. ®®®®®®®®® Washe gari da misalin ƙarfe goma na safe ya fito a shirye tsaf, jakar aikinsa ya ɗauka domin shirin kenan daga can makarantar zai wuce gun aiki. Motarsa ya ja ya fita, bai tsaya a ko'ina ba sai a makarantar idanuwansa na mararin ganin wacce tunaninta ya hanawa ƙwaƙwalwarsa sukuni. Ɗaga waya ya yi ya kira Almustapha ya shaida masa ya ƙaraso, shi da kansa ya fito ya ja Bassam har office ɗinsa, Dama shine Exam officer na makarantar. Bayan sun gaisa ne ya kora masa bayanin abinda ya ke tafe da shi kamar dai yanda ya fara faɗa masa a jiya. Almustapha ya yi murna sosai da jin wannan daddaɗan labarin, dama sun jima su na so Bassam ya yi aure amma da an ma shi magana sai ya ce bai ga wacce ta dace da shi ba ne. Shi da kansa ya ce har Class ɗinsu don yin kiran ta, yayin da ya bar Bassam a ofishinsa ya na jiran dawowarsa. ®®®®®®®®®® Ta sha mamaki Sosai lokacin da Malam ya zo ya yi magana da malamin da ke gabatar da darasi akan cewa ya na son ganin Zuhriyya Sadeeq Yusuf. Malamin ya kira sunan ta tare da mata umurnin ta bi bayan Malam Almustapha. Ficewa ya yi daga class ɗin yayin da ta bi bayansa a tsorace, ta bar y'an aji su na y'an gulmammakinsu irin na ɗalibai. A hankali ta ke takawa kamar wacce ƙwai ya facewa a ciki, kana ganin ta ka san a darare ta ke, a haka ta ƙarasa ofis. Sallama ta yi aka amsa daga ciki tare da mata izinin shiga. Tsoro fal ranta domin ita bakinta da na malam Almustapha bai taɓa haɗuwa ba, shiyasa yau da ta ji kiransa ta firgice. Sai da ta shafe kusan mintuna uku tsaye a gun sannan ta shiga bakinta ɗauke da sallama yayin da kanta ke sunkuye a ƙasa. Tun shigowar ta ofis ɗin ya ke Bin ta da kallo tamkar maye, sai da Uncle ya ankarar da shi a inda ya ke sannan ya dawo. Kowannen su zuciyarsa halbawa ta ke da ɗan ƙarfi- ƙarfi, Muryar Uncle ce ta dawo da su inda ya ke cewa: "Abokina Ni zan fita kaɗan, ina dawowa bada jimawa ba." Daga haka ya fice daga ofis ɗin ba tare da ya jira amsar Bassam ba. Shi kuwa ya yi hakane don ya ba su dama su tattauna cikin nutsuwa. ®®®®®®®®®®® "Habah! Yan mata zauna mana." Cikin hanzari ta ɗago kanta da ya ke ƙasa tun shigowar ta, jin Muryar da ta kasa mantawa, idanunta ne su ka sauka akan kykkyawar fuskarsa yayinda ya ke ta tsabga wani tsadadden murmushi. Da sauri ta ɗauke dubanta daga kansa ta ƙarasa ta zauna akan kujera, gudun kada ta faɗi a yi abin kunya, saboda ƙafafunta da su ka ɗauki rawa. Kallon ta ya ke sosai ya kasa ɗauke idonsa akanta yayin da ta kuma Sunkuyar da kanta ƙasa. "Y'an mata, ya ki ke? Ya karatu, Ya bayan rabo?" "Alhamdulillah." Ta amsa murya na rawa. "Dafatar kin gane ni, Ni ne wanda na rage maki hanya a kwanakin baya." Sai zuwa lokacin ta yi murmushi ta ce "Hakane nagane, Nagode sosai Allah ya saka ma da alkhairi." Murmushi ya sakar mata sannan ya ce "Sunana Bassam Aliyu, Ni ɗan asali jihar Kebbi ne, amma yanzu ina aiki anan gari anan gidan nepa na ɗan agundi." Shiru ya ɗan yi don ya ji ko za ta yi magana, jin bata ce komai ba ya ɗora da cewa "ya sunan malamar." "Zuhriyya Sadeeq Yusuf, amma ana kirana da Zuhra." "Nice name." Ya faɗa sannan ya ce "A taƙaice dai Malama Zuhra bakomai ne ya zo da ni nan ba sai don na miƙa ƙoƙon barata a gare ki, tun ranar da na fara ɗora idona akanki Allah ya jarabce ni da ƙaunar ki mai yawa, idan har kin amince min ina so na je neman aurenki." Ɗago idonta ta yi da sauri tare da zazzare su da alama ta na mamakin jin kalamansa ne. Ganin hakan da ta yi ya sanya shi yin ɗan murmushi ya ce "Ƙwarai kuwa ba wasa a kalamai na idan kin amince ki bani adress tare da number wayarki, Zan zo har gidanku, domin ba na son shiga lokacin karatunki wannan ma don ya zama dole ne." Anan ta sanar mashi ita ba ta da waya sai dai ta ba shi address ɗinta, a haka su ka yi sallama tare da alƙawarin zai je har gida ya same ta. A jinsu ta koma cike da murna, ta rasa dalili haka kawai ta ke jin ta cikin tsananin nishaɗi a yanzu, ko dan ya ce ya na sonta ne oho. Shi kuma ya na fitowa ya ja Motarsa zuwa gun aiki shima ka na ganinsa ka san ya na cikin farin ciki, da alama yarinyar ta amince masa, bai yi tunanin samun ta haka cikin sauƙi ba. ®®®®®®®®®®® Washe garin ranar ya je gidansu su ka shirya kansu shi da ita sa'annan ya sami Babanta da maganar. Sosai Baba ya yi murnar jin wannan labarin sai dai ya shaidawa Bassam cewa shi ba yanzu zai aurar da y'arsa ba sai ta kammala karatun sakandare ɗinta idan zai iya jira nan da shekara biyu ba matsala, zai iya ba shi Zuhra. Duk da ba haka ya so ba, amma ba yanda ya iya ya na tsananin son ta saboda haka ya ce ya amince zai jira har lokacin in dai za'a ba shi. ®®®®®®®®®®®® Kwanci tashi ba wuya a wurin Allah, yau har ga shi sun shafe tsayin wata uku su na Soyayya, inda mafi yawan hirar su ta kasance a waya don baba Bai cika son fita hirar nan ba, itama wayar daƙyar ya bari Bassam ɗin ya siya mata nan ma sai da ya ta roƙarsa sannan ya amince. A dai-dai wannan lokacin ne su ka fara rubuta Exam ɗin third time wanda da sun kammala za'a yi hutu bayan an dawo kuma sai shiga sabon aji. Cike ta ke da farin ciki zuwan wannan lokacin domin kuwa ta yiwa Mommy alƙawarin da an samu wannan hutun za ta je mata hutu a Abuja. Hakan ya sa ta mayar da hankalinta ga karatu sosai, wayar ma ba ko yaushe su ke yi ba da Uncle dole ya mata uzuri domin shima dagewarta akan neman ilimi na burge shi. ®®®®®®®®® Bayan kammala jarabawar ne Zuhra ta shiga shirye-shiryen zuwa Abuja tuni dama Mommy ta turo mata kuɗin mota. Ranar Assabar da dare Zuhra ta na zaune a gefen y'ar katifarta,ta na haɗa kayanta a akwati. Ƙaramar wayarta ƙirar itel da ke ajiye a gefenta ta hau ƙara. Ɗaukowa ta yi ta ɗaga tare da ɗorawa a kunnenta ta na murmushi. "Ohk gani nan zuwa." Shine abinda ta faɗa, sannan ta kashe wayar ta zari hijabinta ta yi waje. A tsakar gida ta haɗu da Mama, Maman ta ce "A'ah Zuhra saurin me ki ke haka?, ina za ki?." "Uhmm! Mama dama Uncle ne ya zo za mu yi sallama kin san gobe zan tafi." Dama tun sanda ta gano abokin Uncle ne ta ke ce masa uncle domin sunansa ya yi mata nauyi a baki. "To shikenan maza ki je, amma ka da ki daɗe kin ga dare ya fara yi." Daga haka Maman ta yi ciki, ita kuma ta fita. A ƙofar gidan ta Same shi ta mi shi sallama ya amsa da murmushi a fuskarsa ya na faɗar "Barka da fitowa kyakkyawa zakaran gwajin dafin dukkanin yan matan duniya ga baki ɗaya.." Ga mai buƙatar sayen wannan littafin sai ya tuntubeni ta wannan number👇🏼👇🏼 _08109634202_ Domin na masa bayanin yanda zai biya kuɗin, kada ku manta N200 ne kacal. Follow me on Wattpad @Ummu inteesar Vote, share & Comment. UMMU INTEESAR CE❤️💛💙💚💔🧡🧡💙💚 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)* *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* *DA KUMA* *A SANADIN KAMA* WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE GA MAI BUƘATA ZAI BIYA N200 KACAL. KADA KU MANTA KUMA ZAFAFA BIYU DAGA ƘAWAYE BIYU NE, IDAN DUKA BIYUN KA KE SO *A SANADIN KAMA* DA *ƘURUCIYAR SAPNAH* TO N300 NE, IDAN KUMA WANNAN KAƊAI KA KE SO ZA KA BIYA KUƊIN KARATU N200 KACAL. ________________________ ________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Free Page 1️⃣1️⃣↪️1️⃣2️⃣ Tafukan hannayenta biyu ta saka ta rufe fuskarta alamar ta ji kunya ta ce "Kai uncle! Wannan kirarin haka, duk ni kaɗai?." Murmushin ya kuma yi ya ce "Ai kinfi haka ma Amaryata." "Allah uncle?" Ta tambaya. Ɗaga mata kai ya yi tare da kashe ido ɗaya ya ce "Sosai ma." Yan da ya yi abun sai ya bata dariya sosai ta ke dariya shima ya kama mata su na yi. Ganin ta yi ya daina dariyar nan ta ke fuskarsa ta canza daga walwala zuwa yanayin damuwa. A razane Zuhra ta kalle sa ta ce "Lafiya dai Uncle?" Shiru ya yi na ɗan wani lokaci kafin ya ce "Yanzu shikenan tafiya za ki yi ba zan ƙara ganin ki ba sai bayan sati uku?" Ɗan murmushi ta yi sannan ta ce "Yanzu Uncle saboda wannan ne ka ke ɓata ranka?, Haba dai ai bai kamata ka damu ba..." Katse ta ya yi da cewa "Me ya sa ba zan damu ba?, Bayan idan ki ka tafi Abuja wani zai iya mun ƙwace." Yanda fuskarsa ta sauya kamar mai shirin yin kuka ne ya ba ta dariya, dariya ta yi sosai sannan ta ce "In dan wannan ne ka da ka damu Uncle, ni taka ce kai kaɗai ba wanda zai iya ƙwace ma ni, kamar yanda kai ma nawa ne ba wacce ta isa ta ƙwace mun kai insha'allah." Dubanta ya yi ya ce "Dagaske?" "Sosaima my king." Sai a lokacin ya yi dariya ya ce "Yanzu na ɗan ji sauƙi a raina, kuma na yarda za ki kulamin da kanki. "Oh! Uncle ashe tsoro ne da kai." Su ka saka dariya a tare, ya ce "Yo ba dole na ji tsoro ba, na san Amaryar tawa kyakkyawa ce tamkar gold." "Kamar yanda angon nawa ya ke kyakkyawa ba." Ta na kai nan a zancenta ta ce " yawwa na tuna, ka ce za ka je birnin Kebbi koh?" "Eh insha'allah." ya amsa mata. "Yaushe za ka tafi?" Ta kuma jefo masa tambaya. "Nan da kwana biyu." Ta ce "Allah ya kaimu." "Ni zan shiga ciki." "Tun yanzu?" Ya tambaya. "Mama ce ta ce kada na jima ka ga dare ya yi." Ya ce "Gaskiya ne je ki kawai, Allah ya tsare hanya ya kai mun ke lafiya." "Ameen." "Idan kin isa can ki kira ni." Ya faɗa tare da ɗagowa daga jikin bangon da ya jingina. "To" ta ce tare da faɗar "Sai anjima hubbyna." Ya ce "Me ki ka ce?" Juyawa ta yi da gudu ta yi cikin gida ta na faɗar "Wallahi ka ji, ni za ka yiwa wayo?, Tab!. Bayanta ya bi da kallo ya na murmushi ya ja Motarsa ya tafi. ®®®®®®®®® Ta na shigewa gidan ta ci gaba da haɗa kayanta. Asubar fari Zuhra ta tashi, Sallah kawai ta yi ta haɗa shayi ta sha sannan ta yiwa iyayenta sallama. Akwatinta ta ja ta nufi tasha, ta hau motar Abuja. Tafiyar awa huɗu ce ta kai su garin Abuja, su na sauka ta kira Mommy ta shaida mata ta iso, Mommy ta ce "Dama su Ruma sun tafi ɗauko ki, su na hanya." Ba ta fi minti biyar da gama waya da Mommy ba sai ga motar su Ruma ta ƙaraso. Sosai su ka yi murnar haɗuwa da juna, shiga motar ta yi driver ya ja sai Area 1 dama acan gidan Umman ya ke. Bayan sun ƙara gidan falo su ka nufa kai tsaye. Mommy ta na zaune akan kujera ta na kallon tashar Bollywood su ka shigo ɗauke da Sallama a bakinsu. Da sauri ta juyo ta na faɗar "Wa'ailaikumus salam, oyoyo ga manyan baƙi, ƙaraso y'ata." Ƙarasawa su ka yi tare da zama akan kujerar suma, ana ƙara gaisawa. Mommy ta ce "Ya iyayen naki da y'an uwanki?." Ta ce "Qlau su ke sun ce a gaishe ki, ya su Yaya Sunil da Suhail?." Su ma qlau su ke Mommy ta faɗa. Mommy ƙanwar mamace Wacce ke Binta sunanta Hajiya khadija ta na Aure a nan Abuja, ta na da ƴaƴa Uku Sunil,Suhail sai kuma y'ar auta Rumaisa'u wacce su ke kira da Ruma, ita ɗin sa'ar Zuhra ce shekarunta goma sha shida a duniya, su na ɗasawa sosai ita da Zuhran. Mommy ta ce "Ruma je ki kawowa y'ar Uwarki ruwa da abinci ta ci ta samu nutsuwa kafin ayi zaman fira." "Gaskiya kam, don yau kam akwai fira." Ruma ta faɗa tare da miƙewa ta shiga kitchen. Bayan mintuna biyu sai ga ta ɗauke da farantin snacks da lemon kwakwa, dabino da madara. Karɓar lemon ta yi ta sha ta dubi Ruma ta ce "Ke ni wannan snacks ɗin ba yi mun za su yi ba, kai ni ga abinci kawai." Ruma da Mommy su ka saka dariya a tare, Ruma ta ce "to ta shi mu ƙarasa dinning ki ci." Su ka ƙarasa, ta ɗale kujera ta ce "Sister zuba mun abincin mana, ko ni zan saka da kaina?" "Angama rankiyadaɗe yallaɓiya Zuhra." Ruma ta faɗa ta na murmushi. Serving ɗinta ta fara yi, ihu kaɗan ta saka don ganin abincin da tafi so ne aka girka, wato dambun shinkafa haɗin zogale, tare da chicken pepper soup, sai kuma juice ɗin kankana. Bismillah ta yi ta fara cin abincin tare da kallon Ruma da ke tsaye kusa da ita ta ce "Sister wa ya girka wannan abincin?" "Ni ce, ai na san ki na matuƙar son dambun shinkafa shiyasa na miki." Ta bata amsa. "Wow! Nagode sister." Ta faɗa. Ta na kammala cin abinci ta shiga ɗakin Ruma inda nan ne masaukinta, ta yi wanka ta sake kaya zuwa na shan iska. Ta haye gado ta shiga neman layin rabin ranta, Ringing biyu ana uku ya ɗaga kiran. "Assalamu alaikum warahmatullah wa barakatuhu." Ya mata Sallama cikin sanyayyiyar muryarsa. "Wa'alaikamus Salam." Gaisawa su ka yi cikin farin ciki da annashuwa sannan ya ce "Gimbiyata kin isa lafiya?." "Lafiya qlau alhamdulillah." Ta amsa. "Ya mutan gidan? da fatar kin same su lafiya." Nan ma da "Qlau Alhamdulillah." Ta amsa masa. Daga nan kuma su ka ci gaba da hirarsu irin ta masoyan juna kafin su datse kiran. ®®®®®®®®®® Kwanci ta shi asarar mai rai, yau har Zuhra ta yi sati biyu a Abuja, tun zuwanta kullum sai sun fita ita da Ruma, sun zazzaga gidajen y'an uwa da abokan arziƙi na ɓangaren Babansu Ruma da ƙawayen Mommy , sun yawata cikin garin Abuja su biyu kaɗai da ya ke su Yaya Sunil ba sa garin a lokacin. ®®®®®®®®®®® Yau ta kama Ranar Asabar ranan ne kuma su Zuhran ke da niyyan zuwa ShopRite, su na so su je guraren shan iska. Da misalin ƙarfe uku na yamma ta shirya cikin wata haɗaɗɗiyar atamfa(wacce Mommy ta aika mata da ita har Kano) riga da siket kalar light purple and pink, ta sanya mayafi light pink, jaka da takalminta duk iri ɗaya. Juyawa ta yi ga Ruma da ke zaune ta ce "Sister mu je koh?." Wani irin miƙewa Ruma ta yi har bakinta na ɓari gurin faɗar "Wow! Sister kin yi kyau sosai fa." Murmushi ta yi ta ce "Nagode, mu je mu yiwa Mommy Sallama." Su na zuwa Mommy ta sanar ma su cewa ai ta aiki driver har yanzu kuma bai dawo ba, ko za su jira shi ne?. Ruma ta kalli agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannunta ta ja wani siririn tsaki ta ce "Bari kawai Mommy, za mu hau taxi lokaci ya ƙure." Daga haka su ka fice daga gidan. Sun taɓa tafiya kaɗan su ka tsaya neman taxi, sun yi tsayin mintuna biyar a gun ba su samu taxi ba. Su na nan tsaye su ka ga wata tsaleliyar mota ta zo ta wuce ta gabansu, sai kuma su ka ga motar ta yi reverse ta tsaya a gabansu.. Ga mai buƙatar siya sai ya mun magana ta wannan number👇🏼 _08109634202_ Domin na sanar dashi yan da zai biya, ka da ku manta N200 kacal. Follow me on Wattpad@ummu inteesar. Vote,share & Comment UMMU INTEESAR CE❤️💙💚💚💛 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)* *MARUBUCIYAR:* *SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* *DA KUMA* *A SANADIN KAMA* WANNAN LITTAFIN NA KUƊI AKAN NAIRA N200 kacal. Ga mai buƙatar siya sai ya tuntubeni ta wannan number👇🏼 _08109634202_ Domin na masa bayanin yanda zai biya kuɗin. KADA KU MANTA KUMA ZAFAFA BIYU DAGA ƘAWAYE BIYU NA KUƊI NE, IDAN DUKA BIYUN KA KE SO *A SANADIN KAMA* DA *ƘURUCIYAR SAPNAH* TO N300 NE IDAN KUMA WANNAN KAƊAI KA KE SO ZAKA BIYA KUƊIN KARATU N200 KACAL. ________________________ ________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Free Page 1️⃣3️⃣↪️1️⃣4️⃣ Haka kawai ya na zaune a office ɗinsa ya ji kamar an tsikare sa da tsinke, miƙewa ya yi ya fita ba tare da ya nemi drivernsa ba, ji ya yi kawai ya na so ya je gida da kansa, ba tare da driver ba. Ya zo wucewa a motarsa kenan kwatsam sai idanuwansa su ka gane masa abinda ya matuƙar razana sa gami da ba sa tsoro, ya kaɗu matuƙa da ganinta, amma hakan bai hana sa tsayawa ba don ya tabbatar da gaskiyar abinda idonsa ya gane masa ya saka ya yi reverse ya kuma ƙare mata kallo. Tabbas kamar ita Mimie ce amma ta ya za ta kasance Mimie bayan ta rasu tsawon shekaru uku da su ka wuce, kuma da hannunsa ya binne ta? Wannan sai dai idan wata ce mai kama da ita,amma kamar har ta ɓaci. Alhj. Salman kenan shi ne ya ke ta wannan tunanin a lokacin da ya ga Zuhra don ta yi matuƙar kama da y'arsa da ya fi ƙauna wadda ta rasu. Da wannan tunanin ya saukar da gilashin motarsa ya ce "Assalamu alaikum y'an mata." Suka amsa da "Wa'ailaikumus salam." Ya dube su ya ce "Idan ba damuwa ku shigo na rage ma ku hanya." Har su na haɗa baki gurin faɗar "Baba da ka bar shi mun gode." Ya ce "Don Allah ku shigo ai ku kamar ƴaƴana ne, bakomai don na sauke ku ka da ku ji tsoro ba zan cutar da ku ba, kuma da akwai wata magana mai muhimmanci da na ke so na yi da ke y'ata." Ya ƙarashe zancen ya na duban Zuhra ga dukkan alamu da ita ya ke zancen. "Ni kuma Baba." Ta faɗa ta na nuna kanta da yatsa. Ya ce "Eh ke." "To shikenan." Su ka faɗa tare da buɗe murfin motar Ruma ta yi wuf ta shige gidan baya, da ta ga ba ta da zaɓi dole ta shiga gidan gaba ƙirjinta na harbawa a hankali, bakinta ɗauke da addu'ar neman tsari daga sharrin mutum ko aljan. Jan motar ya yi su ka bar gun. A cikin motar ne Alhj. Salman ya ke tambayar Zuhra sunanta. Ta ce " Sunana Zuhuriyya." "Dakyau kafin mu fara magana ina za ku je?" Ruma ce ta ba sa amsa da cewa "Ita baƙuwa ce a garin za mu je shopping ne, kuma mu na so mu zazzaga guraren shan iska don ta ga gari sai dai Kamar lokaci ya ƙure." Ya ce "To ta ina za mu fara?" Yanzun ma Ruma ce ta yi kararaf ta ce "Mu fara daga ShopRite." Gyaɗa kansa ya yi tare da juyo da kallonsa kan Zuhuriyya ya ce "y'ata daga wanne gari ki ke?" "Kano." Ta ba shi amsa. Wace unguwa?" Ya kuma jefo mata tambaya. Ta ce "Tukuntawa." Miƙa hannunsa ya yi ya janyo wani envelop da ke gaban Motarsa ya ciro wa su hotuna ƙwaya uku da ke ciki ya miƙa mata ya ce "Duba ki ga kin san wannan?. Ta karɓa ta duba, zazzaro ido waje ta yi tare da kallon Ruma cikin al'ajabi ta ce "Ruma dubi wannan kamar ni, amma kuma ba ni bace don ban taɓa saka kaya irin wannan ba, kuma ban san sanda aka ɗauki hoton ba." Ruma ta kalli hoton cike da mamaki ta ce "Sister kamar har ta ɓaci." Su duka su ka mayar da dubansu ga Alhj. Da alama su na neman ƙarin bayani akan abinda su ka gani ne. Kafin ɗaya daga cikin su ta yi magana tuni Alhj. Ya riga su da cewa "Na san ku na matuƙar mamaki da ganin wannan hoton, kuma ku na so ku san wacece wannan, to wannan yarinyar dai y'ata ce da na haifa, sunanta Ruqaiya amma mu na kiran ta da Mimie, kasancewar sunan mahaifiyata ta ci." Numfasa ya yi sannan ya ci gaba da cewa "Ta rasu kimanin shekaru uku baya lokacin ta na da 13years a duniya, ina matuƙar ji da Mimie tare da alfahari da ita, kaf ƴaƴana na fi son ta, Mahaifiyarta da y'an uwanta ma su na sonta sosai, mun yi babban rashi da ya mayar ahalin gidana tamkar marayu, son da na ke yi mata ne ya sa duk inda na ke ina tare da hotunanta, kwatsam yau na taso daga office sai na gan ki." Ya na maganar idonsa na kan Zuhra alamar da ita ya ke maganar. Shiru su ka yi ba baki sai kunne. Shi ne ya ci gaba da cewa "Na kaɗu matuƙa da na gan ki bayan na tabbatar da y'ata ta rasu, kuma ni na binne ta da hannuna, kuma na yi imani da cewa wanda ya mutu ba ya dawowa, wannan dalilin ne ya sa na tsaya na nemi na yi magana da ke... Ga mai buƙatar siya sai ya tuntuɓe Ni ta wannan number👇🏼 _08109634202_ Domin na masa bayanin yanda zai biya, kada ku manta N200 ne kacal. Follow me on wattpad @ummu inteesar Vote, share& comments UMMU INTEESAR CE💙💚❤️💛💙💙 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL UMMU INTEESAR* *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* *DA KUMA* *A SANADIN KAMA* Wannan littafin na kuɗi ne akan Naira 200 kacal, ga mai buƙatar sayen wannan littafin sai ya mun magana ta wannan number👇🏼 _08109634202_ Domin na masa bayanin yanda zai biya kuɗin. KADA KU MANTA KUMA ZAFAFA BIYU DAGA ƘAWAYE BIYU NA KUƊI, IDAN DUKA BIYUN KA KE SO *A SANADIN KAMA* DA *ƘURUCIYAR SAPNAH* TO N300 KACAL, IDAN KUMA WANNAN KAƊAI KA KE SO ZAKA BIYA KUƊIN KARATU N200 KACAL. ________________________ ________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Free Page 1️⃣5️⃣↪️1️⃣6️⃣ Jikinsu ne ya yi sanyi qlau da jin labarinsa, haƙiƙa sun tausaya masa matuƙa, musamman ma Zuhra da ta yi sukuku kamar mara lakka. A tare su ka ce "Allah ya mata Rahma, ya kyauta ƙarshen mu." Ya amsa da "Ameen." Ci gaba da tuƙinsa ya yi ya na ba su labarin Margayiya Mimie da irin soyayyar da su ke yi mata. A haka su ka ƙarasa ShopRite, ba su so sun ɗebi kaya da yawa ba, saboda kuɗin hannunsu ba wani mai yawa ba ne sosai, amma haka Alhj ya dage sai da su ka ɗebe kayayyaki ma su yawa da tsada sa'annan ya je ya biya kuɗin su ka bar gun. Har zuwa lokacin sun kasa sakewa dashi a ɗarare su ke, ganin yanda ya kashe ma su kuɗi ba tare da ya san su ba, hakan ya saka Zuhra ta shiga fargaba sosai, "ko dai ya na da wata manufar ne a kansu?" Zuciyarta ta raya mata, nan da nan fuskarta ta bayyanar da alamun firgici. A dai-dai lokacin ne kuma ya nemi ta ba sa numberta. Hannu ta saka a jaka ta fiddo y'ar ƙaramar wayarta ƙirar itel da nufin duba masa lambar domin ta manta ta. Hannunta sai kyarma ya ke yayin da ta ke fito da wayar. Da mamaki ya kalli wayar hannunta ya ce "Wannan ita ce wayarki?" "Eh baba." Ta Amsa masa. Bai kuma cewa komai ba sai murmushi da ya yi, ta karanto masa number ya kwashe, ya ci gaba da tuƙinsa. Ta na cikin wannan yanayin ne kawai su ka ga ya tsayar da Motarsa a gaban wani Babban shagon siyar da wayoyi. Juyawa baya ta yi su ka haɗa ido da Ruma cikin mamaki da tsoro, dawo da dubanta ta yi a kansa laɓɓanta na motsi alamar ta na son yin magana, amma ta kasa. Murmushi kawai ya yi domin ya fahimci yanayin su kamar sun ɗan tsorata. "Ina zuwa." Abinda ya faɗa kenan ya fice daga motar tare da nufar cikin shagon. Juyowa ta yi gaba ɗaya ta fuskanci Ruma ta ce "Anyah! Ruma wannan dattijon ba wani abu ya ke nema da mu ba? Nifa na tsorata wallahi." "Nima ɗin ina mamaki sosai, amma ki kwantar da hankalinki, insha'allah ba abinda zai mana sai alkhairi, kuɗin ne kuma da alama sun zauna masa kin ga zai iya yin fiye da haka bakomai ba ne a gunsa..." Ta na kawowa nan a zancenta ta yi shiru tare da faɗar "Ga shi nan ya na fitowa, maza ki juya." Juyawa ta yi ta gyara zamanta kamar komai bai faru ba. Buɗe motar ya yi ya shigo hannunsa ɗauke da farar leda, da alama dai waya ya siyo. "Y'ata na ga wayarki." Ya faɗa. Ba musu ta miƙa masa. Buɗe wayar ya yi ya ciro sim ɗinta tare da fito da kwalin waya ƙirar iPhone 6+ ya saka mata layinta a ciki, ya kunna, sa'annan nan ya miƙo mata. Firfito da ido ta yi ƙululu kamar dunƙulen ƙuli baki na ɓari ta ce "Me zan yi da ita baba." Faɗaɗa murmushinsa ya yi ya ce "Daga yau wannan ita ce wayarki, za ki iya cigaba da riƙe ƙaramar idan kin so, ko kuma ki kyautar da ita." Kasa magana ta yi sai kakkarwa bakinta ke yi. "Ki ƙarba mana y'ata." Hannunta na kyarma ta ƙarba ta na faɗar "Nagode sosai, amma idan na je gida ta ya zan yi bayani?" "Ki gaya ma su cewa Daddynki ne ya saya ma ki Mimie ta." Ya faɗa. Daga haka bai kuma cewa komai ba har su ka ƙarasa *kelvin* guri ne na shaƙatawa mai matuƙar kyau wanda ba kowa ne ke iya shiga gun ba, sai ma su dashi. Idan ka je gurin ma sai an duba yanayin motarka kafin a ba ka tikitin shiga gun. Da ya ke Alhjn babban ɗan siyasa ne, shi senetor ne da ke wakiltar jihar Kaduna. Kai tsaye su ka shige, Zuhra ta ji daɗi sosai ta san da ba don sun haɗu da shi ba, da ba su isa su shigo wannan Wurin ba. Sun ɗauki ɗan lokaci a gurin kafin ya kwashe su su ka kama hanyar zuwa wata super market ɗin da ake siyar da suturu ma su kyau daga can kuma zai mayar da su gida. ®®®®®®®®®®® Bayan ya sauke su a ƙofar gidan ya juya don zuwa gida ya yiwa iyalansa Albishir mai daɗin gaske na kuma samun Mimiensu a karo na biyu. ®®®®®®®®®®® Fitowar Mommy kenan daga bedroom ɗinta sai ganin ta yi su na shigowa da kaya niƙi-niƙi, mamaki ne ya bayyana ƙarara a fuskarta, ƙarasowa ta yi ta na faɗar "Sannunku da dawo, ku kuwa ina ku ka samo kaya haka?, Bayan na san kuɗin hannunku bai isa yin wannan siyayyar ba. "Hmmm! Mommy kenan, ki kwantar da hankalinki, yanzu dai zauna ki sha labari." Ruma ta faɗa. Guri ta nema akan kujera ta zauna su ma su ka Zazzauna, Ruma ta shiga Zayyano mata duk yanda su ka haɗu da Alhjn har zuwa dawowar su gida, ita kuwa Zuhra fito da wayar da ya siya mata ta yi daga jakarta ta nunawa Mommy. Sosai Mommy ta yi mamaki sai dai murnarta ya fi mamakin yawa, saukowa ta yi akan center carpet ta zazzage ledojin kayan da su ka shigo da shi, don ganin meye aciki. Atamfofi ne y'an ubansu a ciki za su kai guda Shida ma su tsadar gaske sai lace guda biyu, ɗayar sauran ledojin kuwa kayan maƙulashe ne aciki danginsu chocolate, biscuits, ice-cream, cakes da sauran su. Washe baki Mommy ta yi ta ce "Ah! Lallai Alhjn nan da alama babban mutum ne akwai karamci agunsa." A ranar ta kira iyayenta ta sanar da su labarin abunda ya faru ɗazu, sun yi murna kuma sun ɗan ji tsoron abin kaɗan. Mama ce ta ce mata "To Zuhra ki dai bi a hankali kin san sanin halin mutum sai Allah, barin ma wannan zamani da ya rikice, don haka ki kula kuma ki tsare mutuncinki." Godiya ta mata sannan ta katse kiran, ta na gamawa ne kiran Alhj Salman ya shigo wayar. New number ta gani da ba ta yi niyyar ɗauka ba, komai ta tuna? Kawai sai ta ɗaga kiran. Gaisawa su ka yi sosai, sa'annan ya bawa matarsa su ka gaisa itama, anan ya ke sanar mata jibi zai turo driver ya ɗauke su zuwa gidansa, don haka su zama cikin shiri..... Ga mai buƙatar siya sai ya tuntubeni ta wannan number👇🏼 _08109634202_ Domin na masa bayanin yanda zai biya kuɗin. Ka da ku manta N200 ne kacal. Follow me on Wattpad@ummu inteesar. Vote, share & Comment. UMMU INTEESAR CE❤️💚💔💙💚💛❤️ 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)* *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* *DA KUMA* *A SANADIN KAMA* Wannan littafin na kuɗi ne akan Naira N200 ga mai buƙata zai biya kuɗin karatu N200 kacal ga mai buƙata sai ya tuntubeni ta whatsapp numberna👇🏼 _08109634202_ Domin na masa bayanin yanda zai biya kuɗin. KADA KU MANTA KUMA ZAFAFA BIYU DAGA ƘAWAYE BIYU NE, IDAN DUKA BIYUN KA KE SO *A SANADIN KAMA* DA *ƘURUCIYAR SAPNAH* TO N300 KACAL, IDAN KUMA WANNAN KAƊAI KA KE SO ZAKA BIYA KUƊIN KARATU N200 KACAL. ________________________ ________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Free Page 1️⃣7️⃣↪️1️⃣8️⃣ Yau ta kama Ranar Litinin a ranar ne kuma Alhj zai turo mota a kai su gidansa. Kwance su ke a kan gadon Ruma su biyun su na barcin safe, Mommy ce ta shigo ɗakin ta tarar da su sun yi rashe-rashe akan gadon, barci su ke sosai da alama dai su na jin daɗin barcin. Ta da kanta ta yi ta kalli agogon da ke sarƙafe a bangon ɗakin ta ga har 10:30am ta yi. "Subhanallah! Wai har lokaci ya tafi haka." Ta faɗa tare da ƙarasawa gaban gadon ta na ƙwala ma su kira. "Ruma! Zuhra! Ku ta shi lokaci ya tafi." Ta faɗa ta na ɗan bubbugarsu a cinyar ƙafa. A maimakon su miƙe sai ganin ta yi kowaccen su ta juya tare da gyara kwanciya, da alama ma ba su san ta na yi ba." Toilet ta shiga ta ɗebo ruwa a cup ta zo ta yayyafa ma su. Ai kuwa su ka yi firgigit su ka tashi a tsorace su na zazzare ido, kamar ma su neman wani abu. "Sannun ku kasa Sarkin barci, har lokaci ya tafi haka ba tare da kun shirya ba?, bayan kun san ƙarfe goma sha biyu na rana Alhj ya ce zai turo driver a ɗauke mu." Ware ido su ka shiga yi su na duban agogo, cikin hanzari su ka sauko daga kan gadon. Zuhra ce ta yi saurin cewa "Ki yi haƙuri Mommy wallahi ba mu san lokaci ya tafi haka ba, barci ne ya ɗauke mu." "Ai ba laifinki ba ne laifin wannan kasar ne na san ita ta koya miki wannan barcin asarar." Ta faɗa ta na nuna Ruma da yatsa, ta ɗora da cewa "ku yi sauri ku je ku shirya lokaci na ƙurewa, kun ga ni har na gama shiryawa." Su ka fice ba tare da sunce komai ba, Zuhra kuwa ta cika da mamakin yanda ta ga Mommy na zumuɗin tafiyar nan, ko da ya ke wataƙil don mijinta baya gari ne kuma ta jima bata fita ko'ina ba shiyasa yanzun da ta samu dalilin fitar ta ke zumuɗi. ®®®®®®®®®®® A ƙofar gidansu sha biyu ta yiwa drivern Alhj, kiran Alhjn ya yi ya sanar masa tuni ya ƙarasa ƙofar gidan. Alhjn ya kira Zuhra ya shaida mata driver na jira a ƙofar gida. A tare su ka fito su da Mommy kowaccen su ta sha wanka na kece raini. Zuhra sanye ta ke cikin doguwar rigar yadi mai kyan gaske kalar dark blue ta yane kanta da mayafi ƙarami kalar red, ɗan kunne, takalmi da jakarta kala ɗaya da mayafinta,ta yi matuƙar kyau sosai. A hankali ta taka zuwa gaban motar ta shiga yayin da Mommy da Ruma su ka shiga gidan baya, drivern ya ja Zuwa gwarinfa domin acan gidan alhj Salman ya ke. Zahiri duk Mommy tafi su zumuɗin wannan tafiyar, ko su da su ka taɓa ganin Alhjn ba su kaita rawar jiki ba. ®®®®®®®®®® Su na shiga gidan kai tsaye parking space ya nufa, sai da ya dai-daita tsayuwar motar Sannan ya kashe ta tare da kiran Alhjn ya sanar masa sun ƙaraso. Ya ce da shi ya shigo da su ciki. Tun daga ƙofar shigowa gidan su Zuhra aka sake baki ana kallo, hatta Ruma da Mommy sai da su ka zama ƙauyawan gaske gurin kallon kyau da tsarin gidan. Drivern ne ya ce da su "Bismillah Hajiya ku zo mu je ciki." Gaba ya yi su ka biyo shi a baya su na kalle-kallen yanda aka ƙawata gidan da furanni ga baloons an ɗaɗɗaura kamar dai ana shirin yin wani biki. Su na isowa ƙofar babban falon gidan driver ya ja ya tsaya, ya kalle su ya ce "ku ƙarasa daga ciki, ni iyakata nan." Ya na gama faɗa ya juya ya koma, tun daga ƙofar su ke jiyo wani cool music na ta shi a hankali. A hankali su ka fara takawa zuwa cikin falon a ɗarare domin ganin duhu da su ka yi a gun. Su na ƙarasawa tsakiyar falon kawai sai su ka ga haske ya mamaye ilahirin katafaren falon, wanda tsayawa misalta ma ku kyau da tsaruwarsa ma ɓata lokaci ne, sai dai ku ƙiyasta dakanku. Hasken ya bayyana tare da sautin mutanen gidan yayin da su ke faɗar "Welcome back to your home Mimie." Dukkansu su ka tada kai su na ƙarewa mutanen da ke cikin falon kallo, Alhj Salman ne a tsakiyar mutanen guda biyar, huɗun duka maza ne ɗayar ce mace da alama ita ce matarsa, sauran kuma ƴaƴansa, domin kallo ɗaya za ka ma su ka fahimci cewa jininsa ne su, kasancewar dukkansu su na kama da shi ne ɗayan ne kawai ya ke kama da mahaifiyarsa. Dukkan su tsaye su ke a gaban wani zungureren cake dogo wanda zai yi tsayin yaro ɗan shekara huɗu zuwa biyar. Alhjn ne ya ke tahowa cike da fara'a sai murmushi ya ke ya iso gabansu ya na ma su sannu da zuwa. Da sauri sauran mutanen su ka ƙaraso cike da al'ajabi su ka yiwa Zuhra ƙawanya su na kallon ta, tabbas ta yi matuƙar kama da y'ar uwarsu, maganar Daddy ta tabbata da ya ke cewa idan su ka gan ta za su iya rantsewa ita ce ƙanwarsu Ruqaiya. Sun ɗau tsawon lokaci su na kallonta cike da fara'a a fuskokinsu kafin daga bisani Mamy ta janye ta ta na faɗar "Kurwar y'ata kur, sai dai ku ci kanku ku sha baƙin ruwa." Ga baki ɗaya yaran su ka kalleta mai biwa babban ne ya ce lallai Mamy har an fara gaya mana magana akan ƙanwarmu don kawai mun kalle ta?, Mu ba ƴaƴanki ba ne kenan?" "Eh ɗin, dole a gaya maku haka irin wannan kallon haka kamar za ku haɗiye ta." Dukan mutanen da ke gun su ka saka dariya. Ƙarasawa ta yi ta zaunar da ita akan kujera, sai a lokacin ta waigo ta kalli su Mommy da ke tsaye agun ta ce "Don Allah ku yi haƙuri Hajiya mun bar ku a tsaye mu na ta murnar ganin daugther mu, ku ƙaraso ku zauna." Mommy da ke tsaye agun kamar an dasa ta tsabar mamaki, sai a lokacin ta iya daga ƙafarta ta ƙarasa gun kujera ta zauna. Zuhra kuwa kasa gane a wanne yanayi ta ke ciki ta yi, tsabar mamakin ganin yanda mutanen gidan ke rawar jiki akanta da yanda kai tsaye su ka mayar da ita ta su. ®®®®®®®®® Bayan gama gaishe-gaishe aka miƙe gaba ɗaya domin gabatar da bikin da su ka shirya mata na dawowa gida, domin su a ransu jin su ke kamar Mimie ce ta yi tafiya ta dawo bayan shekaru uku. Ga baki ɗayan su su ka nufi gun cake ɗin da aka yi saboda ita, a hankali kiɗan da ke tashi ya karaɗe falon gaba ɗaya. Zuhra ce tsaye a gaban cake ɗin Ruma na tsaye daga gefenta sai kuma Mamy da Alhj da sauran ƴaƴansu su ka tsattsaya a gefen su. A dai-dai lokacin ne Camera man ɗin da su ka kira ya ƙaraso, saboda haka ya fara kashe masu hotuna yayinda Zuhra ke yanka cake ɗin fuskarta ɗauke da fara'a sosai. Da ta yanko na farko ta sanyawa Alhj a baki aka saka tafi Camera man na daga gefe sai aikin ɗaukar hotuna da vidio ya ke, ta yanko a ƙaro na biyu ta sakawa Mamie a baki nan ma aka ɗau tafi, a haka saida ta bawa Kowa na gidan cake ɗin a baki suma su ka bata. Bayan kammala yankan cake ɗin ne aka shiga gudanar da bikin na murnar dawowarta, a haka baƙin Mamy da ta gayyata su ka fara zuwa, su ma y'an samarin gidan sun gayyato abokanansu mafi kusa da su. Anci ansha biki ya yi kyau, wuni ɗaya aka shafe ana wannan shagali kafin daga bisani baƙin su ka tafi, ya rage saura y'an gidan, da su Zuhra. ®®®®®®®®®®® Wajajen ƙarfe shida da rabi Mommy ta dubi Mamy ta ce "to hajiya mu za mu tafi yanzu kin ga yamma ta yi, mungode sosai da karamci." Mamy ta kalle ta ce "Ah! Haba dai, tun yanzun? Ga shi ko gabatarwa junan mu da kanmu ba mu yi ba ana ta shagali, ya kamata dai ku tsaya asan juna tukunna, sannan ina neman Alfarmar a bar mana Mimie anan ta yi mana kwana biyu don Allah." Murmushi Mommy ta yi ta ce "To shikenan an zama ɗaya ai." Anan Alhj ya gabatar da kansa da yayansa ga su Mommy ya ce "Ni sunana Alhj Salman Mukhtar Nni senetor ne da ke waƙiltar jihar Kaduna, Ni ɗan asalin jihar Kaduna ne, wannan ita ce Matata Hajiya Fariha ita ma yar asalin jihar Kadunan ce, Sai yarana guda Shidda, wacce ɗayan ta rasu ita ce wacce mu ke so Zuhra ta maye mana gurbinta, waɗan nan su ne Maza biyar da su ka rage mun, Sameer shi ne Babba yanzun shekarunsa 27 sai Saheen ya na da 24 years, sai Samar ya na da 21 years Salim ya na da 18 years , sai Margayiya Ruqaiya (Mimie) ta na da 13 years a lokacin da ta rasu, sai Auta Sagir ɗan 5years." Shiru falon ya yi ana saurarar Alhjn yayinda ya ke koro bayani...... Ga mai buƙata sai ya mun magana ta wannan number👇🏼 _08109634202_ Domin na masa bayanin yanda zai biya kuɗin N200. Follow me on wattpad @ummu inteesar. Vote, share & Comment. UMMU INTEESAR CE❤️💔💚💙💛💙💛 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)* *MARUBUCIYAR:* *SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* *DA KUMA* *A SANADIN KAMA* Wannan littafin na kuɗi ne akan Naira N200 kacal. Ga mai buƙata sai ya neme Ni ta whatsapp numberna👇🏼 _08109634202_ Domin na maku bayanin yanda za ku biya. KADA KU MANTA KUMA ZAFAFA BIYU DAGA ƘAWAYE BIYU NE, IDAN DUKA BIYU KA KE SO *A SANADIN KAMA* DA *ƘURUCIYAR SAPNAH* TO N300 NE IDAN KUMA WANNAN KAƊAI KA KE SO ZAKA BIYA KUƊIN KARATU N200 KACAL. ________________________ ________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Free Page 1️⃣9️⃣↪️2️⃣0️⃣ Bayan ya gama bayanin ne Mommy ta ɗora da bayanin kanta da matsayin Zuhra a gunta ta ce "Ni sunana Khadija musa, ni ƙanwar mahaifiyar Zuhra ce uwa ɗaya Uba ɗaya, nice na ke bin Yaya A'isha,ina da yara guda uku, wannan ita ce y'ar Autata Rumaisa'u, sauran bayanin kuwa nasan Zuhra zata maku acikin zaman da zata yi anan." Da haka aka kammala jawaban, Mommy ta miƙe ta na faɗar "Ruma tashi mu tafi, Hajiya sai watarana saduwar alkhairi." Har Ruma ta miƙe ta kamo hannunta ta riƙe gam ta na faɗar "Mommy don Allah ki barmun y'ar uwata anan idan har ki na so nima na zauna, idan ba haka ba sai dai mu tafi tare." Jin wannan zancen ne ya saka cikin sauri Mamy ta ce "Me ya yi zafi haka Mimiena, ki yi haƙuri zata ta yaki zaman ko da ace ba zata yi hakan ba sai an biyata kuɗi to ina mai tabbatar miki da cewa ko nawa e zamu iya sadaukarwa saboda farin cikinki." Juyawa ta yi ta kalli Mommy ta ce "Ina neman alfarma ta biyu, don Allah ki taimaka ki bar Ruma anan su zauna tare zata fin jin daɗin zama tunda ga y'ar uwarta anan zata fi sakewa." Shiru ta yi na yan wasu daƙiƙu kamar mai tsoron wani abu . Mamy ce ta kuma cewa ki yarda damu Hajiya ba zamu cutar da yaranki ba, mu ba macuta bane hasalima soyayyar da muke yiwa y'ar mu Mimie ba zata bari mu iya cutar da duk wani mutum makusancinta bare wacce ta ke tamkar ita." Dogon numfashi Mommy ta sauke kana ta ce "Hmmmm! Ba fa haka nake nufi ba Hajiya, kawai ina tunanin idan na barsu su biyun anan ni wa zai ɗebe man kewa agida Ni kaɗai tamkar mayya." "Ki dai ƙara haƙuri Hajiya." Ta faɗa ta na juyawa zuwa cikin Bedroom ɗin ta can bayan wasu mintuna sai gata ta fito hannunta riƙe da wasu zungura-zunguran ledoji guda biyu ta miƙa hajiyar ta na faɗar "Ga wannan Hajiya ki gaida gida mungode sosai Allah ya bar zumunci." Shima Alhajin hannu ya saka a aljihu ya ciro bandir na ɗari biyar-biyar guda biyu ya miƙa mata, ba musu ta karɓa ta na ta zabga godiya ga wani lallausan murmushi kwance a fuskarta, aka saka driver ya maida ta gida. ®®®®®®®®®®® A mota ta ke ta zancen zuci ita kaɗai ta na faɗar "Kai Alhamdulillah, gaskiya wannan yarinyar Zuhra Allah ya zuba mata farin jini ga shi tun zuwan ta sai alkhairai na ke ta samu, Haka Musaddiq ya ta kawo mana abun arziƙi saboda ya na sonta, ita kuma ta ƙi fahimta, yanzu kuma ga alhajin nan da alama za'a shana, ko ni da ba don kada su ga rashin hankalina ba, ai da ni za'a yi kwana biyun na more, na gode Allah ma da Zuhra ta buƙaci zaman Ruma a tare da ita ko ta nan na rage zafi tunda y'ata zata moru." Sauke ajiyar zuciya ta yi ta cigaba da zancen zucinta "Ga shi yarinyar nan ta kusa tafiya bai fi saura kwana biyar ba ta koma Kano, inama-inama ace Ruma ce ta samu wannan gatan tabbas da na fantama nima, amma yanzu ta ya zan iya hana Zuhra komawa gida tunda acan ta ke karatunta?, Kuma tabbas idan ta koma duka wannan kulawar da arziƙin da na ke samu a dalilinta kan iyayenta zai koma." A haka ta wanzu ta na ta tunani kala-kala har drivern ya sauke ta a gida ta shiga. ®®®®®®®®®® Su Zuhra kuwa ana nan baje a falo, sai hira mutanen gidan ke mata amma har zuwa lokacin bata sake jiki da su ba, sai Ruma ce ta ke tamkasu, gata kam sun sha shi, ko motsi su ka yi sai ɗaya daga cikin mutan gida ya matso don jin ko lafiya. A ranar dai yara mazan gidan ba inda su ka tafi duka su na falon ana hira sun tasa ta a tsakiya har wuraren 11:00pm na dare, kowa idon shi na kanta musamman yaya Sameer da ko kyaftawa ba ya yi ya na jin ƙaunarta har cikin jinin jikinsa. Fara mitsittsika ido ta yi alamun ta fara jin barci, yayin da Ruma ta fara gyangyaɗi, su ko mutan gidan ba su da niyyar tashi, tuni Sagir ya yi barci a cinyar Mamy. Ganin haka ya saka Mamy ta kalle samarin na ta ta ce "Ku tashi ku je ku kwanta dare ya yi kun ga ƙanwarku ta fara mitsitsika ido." Miƙewa su ka yi a tare dama sun fara jin Alamun barci Saheen da Samar su ka haɗa baki gurin cewa "Good night Mamy& Daddy." Su ka haura sama zuwa ɗakunansu, Shi ma Salim miƙewa ya yi ya bi bayan su, Sameer ne kaɗai ba ya da niyyar tashi agun. Mamy ta kalle shi yayin da ta ke ƙoƙarin tada su Zuhra su je su kwanta, ta ce "Kai ba ka jin barcin ne ka tsaya a nan?." Sosa ƙeya ya yi sannan ya ce "Uhmm! Dama zan tashi ne ina jira ne Lovely sis ta farka na mata sai da safe sannan na tafi." Murmushi kawai Mamy ta yi ta lura cewa Sameer duk ya fi su zaƙewa gurin nuna soyayyarsa wa sabuwar Mimiensu. Tada su ta yi a hankali Ruma ta buɗe idonta yayin da Zuhra har ta miƙe tsaye kasancewar lokacin ne barcin ya fara surarta bai yi nisa ba. Kallonta Sameer ya yi ya ce "Good night lovely sis." Daƙyar ta iya buɗar ba ki ta ce "Good night." tsabar barci da ke idonta. A haka su ka watse kowa ya nufi sashensa, Mamy ta raka su ɗakin da ta saka aka gyara masu... ®®®®®®®®® Shi kaɗai ne kwance a ɗakinsa kan makeken gadonsa, amma barcin ya ƙi ya ɗauke sa, da ya rufe idonsa ita ya ke gani tana gifta masa fuskarta ɗauke da murmushin da ke ƙara ruɗar da shi, sai juyi ya ke ya rasa yanda zai haƙiƙa so ya masa Shigar sauri, domin abinda ya ke ji akanta ya tsarce soyayyar yan uwantaka, sai dai soyayyar aure, domin a lokacin da Real Mimie ta ke raye ba ya jin irin wannan feelings ɗin akanta...... Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number👇🏼 _08109634202_ Domin na masa ƙarin bayanin yanda zai biya. Ka da ku manta N200 ne kacal. Follow me on Wattpad@ ummu inteesar. Vote, share & Comment. UMMU INTEESAR CE❤️💛💚💙💔💚 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)* *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* *DA KUMA* *A SANADIN KAMA* Wannan littafin na kuɗi ne akan Naira 200 kacal, ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number👇🏼 _08109634202_ Domin na masa bayanin yanda zai biya. KADA KU MANTA KUMA ZAFAFA BIYU DAGA ƘAWAYE BIYU NE IDAN DUKA BIYUN KA KE SO *A SANADIN KAMA DA *ƘURUCIYAR SAPNAH* TO N300 NE, IDAN KUMA WANNAN KAƊAI KA KE SO ZAKA BIYA KUƊIN KARATU N200 KACAL. ________________________ ________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Free Page 2️⃣1️⃣↪️2️⃣2️⃣ A haka Sameer ya kwana cike da mafarki iri-iri akan Zuhra. Washe gari da tun da safe ma su aiki su ka kammala komai na break fast su ka gyaggyara guri kamar dai yanda aka saba. Mamy ce ta fito Sanye da wa su kayan barci riga da wando ma su kyau da tsadar gaske, cikin hanzari ma'aikatan su ka zube a gabanta su na kwasar Gaisuwa. Fuskarta cike da fara'a ta amsa ma su tare da kallon biyu daga cikinsu ta ce "Fariha da ke da Maryam ku je ɗakin Mimie ku kai mata break fast ɗinta acan, sa'annan bayan sun tashi ku gyara ɗakin, daga yau ku ne ma su hidimarta har zuwa lokacin da zata tafi kun ji koh?" Waɗanda aka ambata da waɗannan sunayen su ka ɗaga kai sama alamar gamsuwa su ka ce "Insha'allah Hajiya za'a yi yanda ki ka ce mun gode sosai." Cike da zumuɗi su ka miƙe za su nufin ɗakinta, domin sun tabbatar kakarsu ta yanke saka tun da aka mayar da su ma su kula da y'ar gatan gidan sun san za su fantama, albashinsu ma ninkuwa zai yi. Har sun fara tafiya Hajiya ta dakatar da su da cewa "Ku dakata." Tsayawa su ka yi cak, tare da juyowa su na jiran umurni. "Idan ku ka same ta bata tashi daga barci ba kada a tayar da ita ba na so a takuramin yarinya, ku tabbatar kun faranta mata ta hanyar yin duk abinda ta umurce ku da yin abunda ta ke so." Ɗaga kai su ka yi alamar gamsuwa su ka ce "insha'allah, wannan shi ne aikinmu." juyawa su ka yi su ka nufi cikin, yayin da Hajiya ta juyo ga sauran ta ce "Ku duka kowa ta san aikinta ba sai na jaddada ma ku ba, abu ɗaya na ke so ku sani shi ne kun dai ga ga y'armu Mimie Allah ya dawo mana da ita a karo na biyu, ku tabbatar ba ku yi abun da zai baƙanta mata rai ba, domin idan haka ta faru kun san kwanan zancen ba sai na gaya ma ku ba, ku tashi ku tafi." Miƙewa su ka yi jiki a saɓule su ka fice kowaccensu a ranta ta yi fatar ace ita ce mai kula da Mimie. ®®®®®®®®®® A cikin ɗakin kuwa Zuhra ce ta fara farkawa da misalin ƙarfe bakwai da rabi na safe, dama ita bata fiye nauyin barci ba, kuma da lokacin Sallah ya yi komai barcin da ta ke za ta tashi ta yi, mussanman sallar asuba bata taɓa wuce ta ba, bayan ta gama ne ta koma barci shi ne sai yanzun ta farka. Kallon Ruma ta yi ta ga ko motsawa ba ta yi ba bare ta saka ran za ta tashi, saukowa daga kan gadon ta yi ta nufi bathroom, wankanta ta tsala sa'annan ta fito. Sai dai me? Ta yo wankan amma ba ta san ina za ta samu kayan da za ta saka ajikinta ba, tun da ba su zo da shirin kwana anan ba. Ta na nan a tsaye ta na tunanin mafita ko dai kayanta za ta mayar? Kawai ta ji an turo kofa an shigo, ga shi iya towel ne a jikinta, saurin durƙusawa ta yi ta ƙanƙame jikinta ta na kyarmar sanyi saboda sanyin a.cn da ke ratsa ta. Cikin hanzari su ka ƙaraso kanta a ruɗe su na faɗar "Rankiyadaɗe lafiya dai? Da fatan ba ki ji ciwo ba." Sai a lokacin ta ɗago ta na faɗar "Bakomai qlau na ke, don Allah ku nemo mun kayan da zan saka." Ai tun ba ta gama rufe bakinta ba, Maryam ta fice da sauri, can bayan mintuna Kamar biyar sai ga ta ta dawo riƙe da wata leda ta miƙa mata. Wani tsadadden material ne aciki, ficewa su ka yi daga ɗakin dan su haɗo mata abincin break, kafin su dawo kuwa ta saka kayan. Duk wannan bidirin da ake Ruma bata ma sani ba barcinta ta ke sha, dama ita haka ta ke Allah ya yi ta da mugun son barci ita ko ƙasusuwanta ma ba sa ciyo saboda kwanciya. Bayan sun ajiye mata sun tabbatar bata buƙatar komai su ka fice daga ɗakin. Nan fa Zuhra ta tada kai ta dubi girman ɗakin da ake kira da nata, da kuma kyau da tsaruwarsa, da yadda ake tarairayarta a gidan. Ta kuma tuna yanda gidan iyayenta ya ke da yanda ita ce mai kula da duk wa su aikace-aikacen gidan, anan kuma ga shi ita akewa hidima. Dogon numfashi ta ja ta sauke, a bayyane ta ce "Alhamdulillah, Allah nagode ma ka da irin wannan baiwar da ka mun, Allah ka ƙaro mun daga falalarka." Shiru ta yi na ɗan lokaci komai ta tuna oho, sai ganin na yi ta miƙa hannu ta ɗauko wayarta. Numbersa ta kamo ta danna masa kira, har ta tsinke bai ɗaga ba. A ranta ta ce "kodai Bai tashi daga barci ba ne.." Kafin ta ƙara sa zancen zucinta ta ga kiran shi na shigowa wayarta, ɗagawa ta yi ta na faɗar "Amincin Allah ya tabbata ga angona farin cikin zuciyata." Murmushi mai sauti ya yi kafin ya ce "Ameen tare da ke mai sona, ya ki ke ya kwana biyu? shiru ake jin ki Hajiya Mimie, kin yi kuɗi kin ɓoye." Y'ar dariya ta yi ta ce "Lah! Ka ji Uncle ban son sharri fa, ni ce na ɓoyen?." Shima dariyar ya yi ya canza ma su salon hirar da cewa "To ya abujan ya su Mommy da Ruma?" "Qlau su ke Mommy na gidanta, Ruma kuma ga ta a kusa da ni barci ta ke." Ta amsa masa. Da mamaki a fuskarsa ya ce "A'ah bangane ba ku ku na ina ne?, Ki na nufin bakwa gida?." "Eh haka na ke nufi, mu na gidan Daddy ne ko ince Alhaji Salman daga zuwa kawo ma su Ziyara su ka riƙe mu sai Mommy ce ta koma gida, ba ka ga yanda su ke nan-nan da ni ba, ko Ni ce Real Mimie ɗin sai haka, gaskiya su na son Margayiya Mimie da yawa, anyah! Kuwa za'a samu iyayen da su ke son y'arsu sama da su a duniya kuwa?" "Hmmm! Ikon Allah, ke kam Allah ya kashe ya baki, kin ji daɗinki." Ya faɗa sannan ya ɗora da cewa "Wai sai yaushe ne za ki dawo?" "Saura kwana biyar, kai fa.?" Ta mayar mai da tambaya. Ya amsa da cewa "Ai ni tuni na dawo Kano, sati ɗaya na yi a gida saboda yanayin aikina, kuma na gaya maki, ina ga daular da ki ke ciki ne ta mantar da ke." Ya ƙara sa zancen ya na dariya. A haka su ka cigaba da firarsu a waya har zuwa lokacin da su ka yi Sallama, sai a lokacin ne kuma Ruma ta farka. Kallonta Zuhra ta yi ta ce "Barka da tashi sarauniyar barci ta duniya, da girman kujerarki, ga break fast nan tun ɗazu ke ya ke jira." A dai-dai lokacin ne Sagir ya faɗo ɗakin da gudunsa tare da yin tsalle ya ɗale cinyar Zuhra ya na faɗar "Good morning my lovely sister." Murmushi ta yi ta na faɗar "Morning sweet bro." Tare da shafa sumar kansa don haka kawai ta ji yaron ya na matuƙar burge ta, ya shiga ranta nan take. A dai-dai lokacin ne kuma Mamy ta ƙaraso ciki ta na faɗar "Wai miye haka ka ke yi Sagir? zo mu je, ka da ka takurawa Yayarka." Jin haka ya saka ya ƙara lafewa a jikinta kamar wata mage. Mayar da dubanta ta yi ga Zuhra ta ce "Barka da safiya daddy's girl, dafatar kin tashi lafiya, don Allah ki yi haƙuri ya zo zai takura ki koh? Wallahi tun da asubar fari ya farka ya saka rigima, shi sai a kai sa gurin Sisternsa, daƙyar Sady ta lallaɓa sa ya koma barci." Murmushi ta yi ta ce "Ayyah! Mamy, ai bakomai shi ai ƙanina ne." Ba su an kara ba kawai su ka ji motsi daga ƙofa, Mamy ta juya don ganin ko waye yayin da Zuhra ta ƙura masa ido domin itama bata ankara da zuwansa ba sai yanzu, amma da alama ya jima tsaye agun. ®®®®®®®®®®® Ita kuwa Mommy tsaye ta ke a gaban gas ta na Shirya break fast, Amma kallo ɗaya za ka mata ka fahimci hankalinta baya kan girkin, ta yi nisa a tunani. Mafita kawai ta ke nema ta yanda za ta yi ta zaunar da Zuhra anan domin tsakani da Allah ba ta so wannan daular ta fita daga hannunta, "to ko zan riƙe ta anan ne idan ya so sai ta ci gaba da karatunta anan?" "Shawara mai kyau" wata zuciyar ta faɗa mata nan da nan ta kashe gas ɗin ta kwashe dankalinta da ta gama soyawa, wanda ke cikin man kuwa anan ta bar shi ta yi waje don kiran yayarta a waya. A falo ta dire kayan tare da ɗaukar wayarta ta dannawa Mama kira. Mama na ɗagawa su ka gaisa sosai cike da fara'a sannan ta fara inda-inda ta na son ta roƙe ta su bar mata Zuhra, amma ta na jin tsoron ka da su ƙi amincewa. Can dai ta dake ta yi ta maza ta ce "Am, Yaya dama ina so na roƙi wata alfarma Allah ya sa zan samu." "Insha'allah, indai zan iya kuma bai fi ƙarfina ba zan miki." Murmushi ta yi ta ce "Yaya dama ina so na roƙi Alfarmar ku bar mun Zuhra a hannuna, na yi ma ku alƙawarin zan kula da ita sosai tamkar yan da za ku mata." "Khadija me ki ke nufi da mu bar ma ki Zuhra? Kin san dai ta na karatu anan koh? Kuma bata riga ta kammala ba, ta ya ki ke ganin za mu bari ta rasa karatun da daƙyar da taimakon Allah mu ke ɗaukar nauyinsa?" "Uhmm! Indan wannan ne ba damuwa yaya ni zan saka ta makaranta mai kyau anan, ina mai tabbatar mi ki za ta samu ingantaccen ilimin da za ta taimaki Rayuwarku gaba ɗaya anan." "To na ji ba ma wannan ba Khadija, kin san yarinyar nan fa ta na da miji, ta na gama sakandare aure za mu mata, kafin wannan ma ita kaɗai ce ta rage mun y'a mace a gabana ita ke taimaka mun gun ayyukan gida da sauran su, idan ki ka ɗauke ta ya zan yi?" "Ka da ki damu yaya Ni zan iya ɗaukar maki y'ar aikin da za ta taya ki aiki a gida, ni dai buƙatata kawai ki bar mun Zuhra don Allah, don Allah yayata, ni da ke fa duka abu ɗaya ne." Jikin Mama ya yi sanyi sosai, haka kawai ta ji ta kasa amincewa da Khadijah tabbas da kwai lauje acikin naɗi tun da har Khadija ta dage haka, amma sai ta ce "Shikenan ki kira Babanta a waya ki sanar mai, duk yan da ku ka yi da shi ki sanar min." Ta na gama faɗa ta kashe wayar ba tare da ta tsaya saurarar godiyar da ƙanwar tata ke mata ba. Murmushin cin nasara Mommy ta yi ta ce "Habah! Ko ke fa khadijatu? Amma ta ya yarinya za ta samu arziƙi ta dalilinki ki bar ta ta tafi ta kai wani gurin dabam, ina ai ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa." Wani murmushin ta kuma yi wanda ita kaɗai ta san fassarar kayanta sa'annan ta zauna ta fara cin abinci ta ta na ƙissima irin abubuwan da........ Ga mai buƙata sai ya tuntubeni ta whatsapp numberna 👇🏼 _08109634202_ Domin na masa bayanin yanda zai biya. Follow me on Wattpad @ummu inteesar. Vote, share & Comment. UMMU INTEESAR CE💚💙💛❤️💚 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)* *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* *DA KUMA* *A SANADIN KAMA* Wannan littafin na kuɗi ne akan Naira 200 kacal. Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number👇🏼 _08109634202_ Domin na masa bayanin yanda zai biya kuɗin. KADA KU MANTA KUMA ZAFAFA BIYU DAGA ƘAWAYE BIYU NE, IDAN DUKA BIYUN KA KE SO *A SANADIN KAMA DA *ƘURUCIYAR SAPNAH* TO N300 NE, IDAN KUMA WANNAN KAƊAI KA KE SO ZAKA BIYA KUƊIN KARATU N200 KACAL. MASOYA NA A DUK INDA KU KE INA MATUKAR K'AUNAR KU,ALLAH YA BAR ZUMUNCI. ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Free Page 2️⃣3️⃣↪️2️⃣4️⃣ Ta fara cin abincinta ta na ƙissima irin abubuwan da za ta yi da zarar burinta ya cika na riƙon Zuhra. Bayan ta kammala ne, ta kira Baban Zuhra a waya ta sanar mai da buƙatarta. Kai tsaye ya nuna mata rashin amincewarsa ba wani nuƙu-nuƙu. Sosai ta ji haushin hakan a ranta ta ke cewa "Ku ji mun wannan mutum na saka shi a inuwa ya na ƙoƙarin tura ni rana, tun da ya ga alkhairi ya doso ni ta dalilin y'arsa shi ne zai mun baƙin ciki, to wallahi ba ka isa ba Habu, in ka san wata ai ba ka san wata ba." Dogon tsaki ta ja ka na ta bar gun cike da ɓacin rai. ®®®®®®®®®®® "A'ah! Sam me ka ke yi tsaye agun? Ƙaraso ciki mana." Ƙarasowa ya yi da fara'a sosai a fuskarsa ya na faɗar "Good Morning Mamyna." "Morning dear Sam, dafatar ka tashi lafiya." "Alhamdulillah, qlau na ta shi Mamyna." Ya faɗa tare da mayar da dubansa ga Zuhra fuskarsa cike da murmushi mai ƙayatarwa ya ce "Barka da Safiya Sweet sis." Murya a kasalance ta karɓa masa da "Barka dai." Saboda yanayin yanda ta ga ya ƙura mata ido ba ya ko kyaftawa. Daga jiya zuwa yau ta lura cewa ya fi kowa tsinannan kallo duk a gidannan. Kafin ta gama zancen zucinta ta tsinto muryarsa ya na faɗar "Sweet sis me ku ke jira ne har yanzu ba ku yi break ba." "Uhmm! Za mu yi yanzun." Ta amsa masa. A lokacin ne kuma Ruma ta gyara zamanta ta na faɗar "Ina kwana yaya Sameer, na ga kamar ka manta da ni saboda ganin sisternka?" Ta faɗa ta na dariya kaɗan-kaɗan. Firgigit ya yi tamkar wanda ya farka daga dogon barci kallon ta ya yi ya ce "Yi haƙuri y'ar uwarmu, ba wai na manta ki ba ne dama... Dama....ina so ne na..." Ya na maganar idonsa na kan Zuhra duk sai ya daburce ya rasa ma me zai ce. Dariya sosai Ruma ke yi yayin da Mamy ta yi murmushi ta ja hannun Sagir ta ke kan cinyar Zuhra za su fice daga ɗakin domin ta fara ɗago jirgin ɗan nata, har ta kai ƙofa ta juyo ta na faɗar "Mimiena don Allah ku sauko ku ci abincin ka da ya yi sanyi, don Allah ka da ku bari na dawo na samu ba ku ci ba, shiyasa na saka aka kawo maku har nan domin ku fi sakewa." Ta na gama faɗa ta juya ta fice still ta na riƙe da hannun Sagir da ke ƙoƙarin ƙwace hannunsa daga riƙon da ta masa. Mamy na ficewa shima ya bi bayanta a daburce ganin an fara yi masa dariya, ba ya so ayi saurin kwaɓo jirginsa shiyasa ya fice, saboda ya tabbatar muddin ya na ganin Mimie a gabansa ba a bunda ba zai iya aikatawa ba, saboda ƙaunarta da ta masa dirar mikiya a zuciya. @@@@@@@@@@ Bayan kwana biyu da zuwan Zuhra gidan Alhaji Salman, ta saki jiki sosai domin ta sakankace cewa su ma su ƙaunarta ne, ko da iyayenta ne sai haka su na ririta ta sosai, haka y'an samarin gidanta su na matuƙar son ta ita kuwa ta na girmama su sosai. Fatarta ta murje ta yi kyau sosai acikin kwana biyun nan saboda canjin cima da kuma hutu da ya zauna mata, ko Ruma da ta ke y'ar rakiya ta ƙara kyau sosai har bata so su bar gidan. ®®®®®®®®®®® Shi kuwa Sameer wata irin ƙauna mai zafi ce ta shiga zuciyarsa, sosai wutar soyayyarta ke ruruwa a zuciyarsa. A ranar ne kuma Mommy ta kira Mamy a waya ta ke tambayarta "Yaushe ne su Zuhra za su dawo?" "A yau ne ya kamata su dawo domin kwana biyu ki ka ce." Anan Mamy ta kuma roƙarta da ta ƙara ma su kwana biyu don Allah. "Hmmm! Hajiya ba na so na ce miki a'a, amma ya kamata su dawo haka kin ga yarinyar nan saura kwana biyu ta koma gida akwai shirye-shiryen tafiya a gabanta." Mommy ta faɗa. "Hajiya ka da mu yi haka da ke don Allah ki ƙara haƙuri, ba ki ga yanda iyalan gidan nan ke cikin farin ciki ba saboda dawowar Mimie cikin rayuwarmu, da son samun mu ne ma a bar mana ita anan gaba ɗaya amma na san da wuya iyayenta su amince, amma ki ƙara haƙuri don Allah, insha'allah nan da kwana biyu za su dawo." "Uhmm! Shikenan Allah ya kai mu amma gaskiya dan ke ce kawai shiyasa zan bar su su kuma kwana." "Shikenan Nagode sosai Hajiya, ki turomin da account number na ki yanzu." Ta na gama faɗa ta yanke kiran. Mommy kuwa murna duk ta gama cikata, har hannunta na ɓari gun tura account number ɗin, don ta tabbatar kuɗi ne za'a turo mata. Can kamar bayan mintuna biyar da turawar sai ga alert ya shigo wayarta daga account ɗin Mamy. Naira dubu hamsin ne, sai da ta yi y'ar ƙara kaɗan don murna a bayyane ta ce "Hmmm! Lallai ma Habu, wato wannan arziƙin ne ka ke mun baƙin cikin samu?, Kar ka ji komai ni na san me zan yi a kai." Ta ƙarashe zancen, leɓenta ɗauke da wani busasshen murmushi wanda ita kaɗai ta san fassararsa, ƙwafa ta yi tare da jan dogon tsaki, ta nemi guri ta zauna ta na ayyano abubuwan da ya kamata ta yi, domin ta shiga cikin dukiyar Alhaji Salman ta wataya. ®®®®®®®®®®® A can Kano kuwa mama ce ta ji shirun ya yi yawa, Mommy ba ta kuma kiran ta akan maganarsu ba, hakan ya sa ta ɗaga waya ta kira ta. Har ta tsinke ba ta ɗaga ba, ta kira ta ya kai sau uku amma ba ta ɗaga ba, mamaki ne ya cika ta me wannan matar ke nufi da ƙin ɗaga wayarta? Ko dai ta na fushi ne?, To me aka yi na fushi?. Mama ta shiga jerowa kanta tambayoyin da ba mai amsa mata su, hakan ya sa ta haƙura ta ajiye wayar tare da komawa kan aikin sana'arta ta ɗan wake da ta ke. ®®®®®®®®®®® Ita kuwa Mommy ta na sane ta ƙi ɗaga wayar domin dukkansu haushi su ke ba ta har yayar Tata tun da sun hana mata riƙon y'arsu. A ranta ta ce "Jibi-jibin nan zan tattaro ma ku y'arku na maida ma ku, Nagode Allah da ya sa nima ina da tawa y'ar, da ba ni da ita ne abun zai fi yi mun ciwo, dama shi talaka tsiyarsa kenan ka saka shi a inuwa ya yi ƙoƙarin turaka rana." Ƙwafa ta yi sannan ta ce "Za ku sha mamakina, domin wannan karon ko kwanɗalata ba za ta yi ciwo ba gurin hidimarku da ta y'arku, za ku san kun yi da khadijatu." Ta ƙarashe zancen ta na huci. A ranar ne kuma Sunil da Suhail su ka dawo daga tafiyar da su ka yi. Mommy na ƙoƙarin yi ma su sannu da zuwa, su kuwa ko wannensu ƙoƙarinsa ya ga Zuhra sai raba ido su ke. A tare su ka haɗa ba ki gurin faɗar "Mommy wai ina Zuhran? Ko har ta koma ne?. Harara ta zuba ma su ta na faɗa "Bansaniba, wannan wane irin iskanci ne ina ma ku sannu da zuwa amma ku na tambayar wata can dabam." A tsorace su ke kallon mahaifiyar tasu, fuskarsu ta bayyanar da mamaki ƙarara, to yaushe Mommynsu ta sauya haka? Ita ce fa ta koya ma su ɗokin y'an uwansu tun su na yara, amma yanzu don sun nuna kuma sai ta yi fushi?, Tabbas da wani abu a ƙasa, ruwa baya tsami banza. Daga haka su ka ba ta haƙuri su ka wuce ɗakinsu don watsa ruwa.. A dai-dai lokacin ne kuma kiran Zuhra ya shigo wayarta. Kallon wayar ta yi tare da zubawa screen ɗin harara kamar dai Zuhran ta ke gani a ciki, har ta tsinke bata ɗaga ba, domin zancen gaskiya ita yanzu har Zuhran haushi ta ke bata matuƙa, ta matsu su dawo ta tattara ta ta mayar gidan faƙiran iyayenta kowa ya huta. ®®®®®®®®®®® Washe garin ranar Sameer ne ya farka daga barci a razane duk ya ruɗe sai maimaita faɗar "Innalillahi wa inna'ilahir raji'un!" Ya ke, kallo ɗaya za ka masa ka gano cewa a gigice ya ke, da alama ya yi wani mummunan mafarki ne, gaba ki ɗaya ya gama jiƙewa da gumi duk da a.c da ya ke ƙure a ɗakin nasa. Cikin hanzari ya sauka daga kan gadon ya nufi banɗaki don watsa ruwa. A ransa ya ke cewa "Ya zama wajibi a gare ni, na sanar da Mimie yawan ƙaunar da na ke mata kafin ta tafi gobe, domin gujewa faruwar abinda na gani a wannan mummunan mafarki." Ko me Sameer ya gani a mafarki? Me zai faru tsakanin Mommy da y'ar uwarta bayan komawar Zuhra garinsu? Hmmmm! Sai ku tare ne a page na gaba don cin amsar Waɗannan tambayoyin. Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number👇🏼 _08109634202_ Domin na maku bayanin yanda za ku biya. Follow me on Wattpad @ummu inteesar. Vote, share & Comment. UMMU INTEESAR CE❤️💛💚💙💛💚💛 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)* *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* *DA KUMA* *A SANADIN KAMA* Wannan littafin na kuɗi ne akan Naira 200 kacal. Ga mai buƙata sai ya tura kuɗin ta wannan account ɗin. Account name: Rukayya Ibrahim lawal Account no:0431343346 Gt bank. KADA KU MANTA KUMA ZAFAFA BIYU DAGA ƘAWAYE BIYU NE IDAN DUKA BIYUN KA KE SO *A SANADIN KAMA* DA *ƘURUCIYAR SAPNAH* TO N300 NE, IDAN KUMA WANNAN KAƊAI KA KE ZA KA BIYA KUƊIN KARATU N200 KACAL. ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Free Page 2️⃣5️⃣↪️2️⃣6️⃣ A daren ranar Mamy ce Zaune a gefen gado, yayin da Daddy ke kwance akan gado da shirin barci da alama ya fara jin barci. Mamy ce ta ce :Alhaji gobe ne fa yarinyar nan za ta koma gidan Mommynta Saboda jibi za ta koma gida, ya kamata ka yi wani abun, gidan nan kowa na cikin damuwa saboda tafiyar da za ta yi." Da damuwa a fuskarta ta ke zancen. Ajiyar numfashi ya sauke cikin alamun fara jin barcin ya ce "Haba Mamyn yara ki daina damun kanki a kan wannan, ni na san me zanyi, Ni da kaina zan maida ta gida Kano jibi idan ya so sai na roƙo alfarma gun iyayenta ko za su bar mana ita na ɗan wani lokaci." Ganin jikin Mamyn ya yi sanyi qlau, ya saka shi miƙewa zaune ya ce "Haba my wife, ki kwantar da hankalinki, ki kwanta yanzu ki yi barci, na miki alƙawari komai zai tafi dai-dai insha'allah." Ba ta ce komai ba sai ajiyar zuciya da ta sauke ka na ta kwanta akan gadon cike da tunani iri-iri. ®®®®®®®®®®® Kashe gari wuraren ƙarfe goma Sameer ya ɗauko ƙasa cikin shigar ƙananun kaya jins da red t-shirt, ba hula akansa anma ya yi matuƙar kyau da ya ke shi fari ne sai kayan su ka amshe fatarsa sosai. Kai tsaye ɓangaren Mimie ya nufa, don tun da ya ga ba ta falon ya tabbatar ta na ɗakinta. Tarar da su yay su na fira ita da Ruma, ga tulin tufafinsu da su ka samu a gidan su na jerawa a akwati. Da sauri ya ƙaraso ciki baki na ɓari ya ce "me kuke haka?" Bai jira sun amsawa ya ware murya ya na kwalawa su Maryam kira "Maryam! Maryam!! Fariha! Fariha." Daga can ƙasa su ka jiyo ana ƙwala ma su kira da gudu su ka hauro sama har su na yar rige-rige. Cikin fushi ya kallesu ya ce "Wannan ba aikinku ba ne?" Yay tambayar ya na nuna masu kayan hannun Mimie da yatsa. "Eh ranka yadaɗe." su ka faɗa baki na ɓari." "Shine kuma dan ku na isassu ku ka bar ƙaramar yarinya da aiki irin wannan?." "Ayi haƙuri yallaɓai wallahi ba mu san za ta yi ba ne." Su ka faɗa tare da ƙarasawa gunta su ka janye akwatin su ka fice daga ɗakin domin ba za su iya tsayawa gu ɗaya da oga Sameer ba saboda kwarjininsa. Zuhra da Ruma kuwa tun lokacin da ya shigo ɗakin su ke kallonsa cike da mamakin abin da yayi yanzun. Guri ya nema ya zauna akan ɗaya daga cikin kujerun da ke ɗakin sannan ya dubi Zuhra ya ce "My sister akwai Magana mai muhimmanci da na ke so nu yi da ke." Jin hakan ya sa Ruma ta miƙe ta nufi hanyar fita daga ɗakin. "A'ah! Ina za ki kuma sister?" Cewar Mimie. Murmushi ta yi sannan ta ce "Zan sauƙa ƙasa ne gun Mamy." Daga haka ta yi ficewarta ba tare da ta sake cewa komai ba. Shi ko Sameer Sosai ya ji daɗin abinda Ruma ta yi, haƙiƙa kanta na ja tun da har ta fahimci cewa ya na son kaɗaicewa da Mimie, haka kawai sai ya ji ta burge shi. Bayan fitarta Zuhra ta sunkuyar da kanta ƙasa ta na wasa da y'an yatsun hannunta, yayin da ta ke zaune a kan carpet. "Sweet sister!" Ya kira ta cikin sanyayyiyar muryarsa. Ɗagowa ta yi ta na kallonsa. Shiru ya gifta na wani ɗan lokaci, can ya ce "A yau ɗin nan zan sanar da ke sirrin zuciyata, na sani kin riga kinsan cewa Margayiya Mimie ƙanwata ce uwa ɗaya Uba ɗaya kuma ina matuƙar ƙaunarta, amma ina so ki sani soyayyar da na ke mi ki ta na da banbanci da tata." Da sauri ta ɗauke idonta daga na sa ta kuma Sunkuyar da kanta ƙasa. Bai damu da hakan da ta yi ba ya ci gaba da cewa "Daga zuwanki zuwa yanzu na tabbatarwa kaina cewar na faɗa soyayyarki, saɓanin yanda na ke tunani daga farko, a farko na ɗauka cewa soyayyar y'an uwantaka na ke maki, sai a yanzu na tabbatar cewa, Soyayyar aure na ke ma ki." A razane ta ɗago idonta ta na kallonsa da mamaki a fuskarta, bakinta sai motsi ya ke alamar ta na son yin tambaya amma ta kasa. Murmushi ya yi ya ce "Ƙwarai da gaske, ina matuƙar sonki, ina ji a raina idan ban same ki ba Zan shiga wani mummunan yanayi, ki taimake ni ki so ni Mimie, ina so ki dawo cikin ahalinmu har abada." Ganin ba ta da niyyar ba da amsa ya sa ya miƙe ya bar ɗakin cikin wani irin yanayi da mutum bai isa ya fassara sa ba, shin farin ciki ne ko akasin haka." Zuhra kuwa ta shiga ruɗanin jin maganganunsu, tabbas ta na cikin wani yanayi, yanzu ya za ta yi kenan? A haka Ruma ta shigo ta Same ta. ®®®®®®®®®®® Da Azahar driver ya ɗauke su zuwa gidan Mommy. A ƙofar gidan ya sauke su sa'annan ya fito ma su da akwatinsu daga but ɗin motar tare da wasu kayan arziƙi da Mamy ta haɗosu da su. A falo su ka sami Mommy zaune ta na kallo cike da mamaki ta ke kallonsu, wai yaranta ne su ka yi kyau haka? Lallai hutu abu ne na musamman. Da sauri ta taso ta rungume Ruma ta na faɗar "Oyoyo my daughter." Su ka rungume juna su na murna. Zuhra ce ta ƙarasa jikin Mommy ta na faɗar "Oh! Mommy ta Ruma kawai ki ke kin manta da y'ar lelenki Zuhra." Mommy zame jikinta ta yi daga na Zuhra ta na taɓe baki, ba ta ce komai ba, ta ja hannun Ruma ta zaunar da ita kan kujera su na cigaba da hirarsu. A ranar Abbansu Ruma ya turowa Mommy kuɗi dubu talatin ya ce abawa Zuhra ta yi kuɗin mota kamar yanda ya saba idan ta zo. Amma saboda tsabar hassada irin ta Mommy ta kuɗurce a ranta ba zata bata kuɗin duka ba, tunda ita Habu zai yiwa haka. Daga Zuhra har Ruman mamaki su ke irin wannan sauyin hali da Mommy ta yi lokaci ɗaya, "To me ya faru bayan tafiyarsu?" Ranar dai a haka aka kwana cikinsu ba wanda ya gane kan Mommy. Shigowar su yaya Sunil da dare ne kaɗai ya rage mata damuwar da ta ke ciki. Washe gari Tun bakwai na safe Mommy ta tattarowa Zuhra Komai nata ta ajiye a falo, sannan ta wuce ɗakin Ruma don ta da Zuhra. Bayan ta shirya Mommy ta ba ta dubu biyar wai ta yi kuɗin mota. Cike da mamaki Zuhra ke kallonta can ta ce "Uhmm! Mommy da kin barsu kin manta tare da Daddy zamu tafi?" Ba musu ta kwashe kuɗinta ta mayar jaka, dama ba da niyya ta bayar ba don kawai ka da duniya ta zarge ta da rashin kirki ne ta gwada bayarwar. Shiru-shiru har takwas da rabi Daddy bai zo ba, Mommy ce ta yi gajin haƙuri ta ce "Wai nikam sai ƙarfe nawa ne za ku tafi?" "Uhmm, nima bansani ba Mommy bari na kira shi." Zuhra ta faɗa ganin ana mata kora da hali. Wayarta ta ciro ta danna mai kira bayan sun gaisa ta ce "Yawwa Daddy na ce ƙarfe nawa ne tafiyarki? Na fa shirya." Murmushi mai sauti yay ya ce "Yar gidan Daddy kenan, Sarkin zumuɗi, to ki ƙara haƙuri kaɗan nima shirin na ke nan da 30mins za ki ganni." "Ohk Daddy sai ka zo." Daga haka ta kashe wayar. Mommy kuwa sai taɓe baki ta ke ta na wurga mata harara. Ita dai bata kuma magana ba domin daga jiya zuwa yau jinta ta ke kamar kan ƙaya, gidan yayi mata zafi saɓanin da, da ba inda ya fi mata daɗin zama sama da nan. Sai ta ke ganin kamar Mommyn ta tsaneta, kuma bata san me ta yi mata ba. ®®®®®®®®®®® A can gidan Daddy Kuwa da misalin 9:12am ya fito a shirye tsaf domin tafiya zuwa garin Kano. Iyalansa ne gaba ɗaya su ka yo ma su rakiya cike da alhinin tafiyar Sisternsu. Har zai shiga Mota Sagir ya rugo da gudu ya riƙe babbar rigarsa ya na faɗar "Daddy ni dai zan bika, ka kaini gun sisterna." Mamy ta je ta janyo shi jikinta ta na lallaɓasa, amma fur ya ƙi daga karshe ma ya saka ma su kuka, shifa lallai sai an tafi dashi gidansu yayarsa. Ganin ya ƙi daina kuka da rigimar ya sanya Daddy ya ce Mamy ta je ta haɗo masa kayansa, ai kwana biyu ne kaɗai zai yi ya juyo. Shi ko Sagir faɗawa motar ya yi ya na murna yayin da Mamy ta shiga ciki don cika umarnin mijinta. Sameer sai kallon autansu ya ke ya na murmushi sai ya ji inama ace shi ma ya na da dama irin ta Sagir, tabbas da ya aikata hakan. Can bayan wani ɗan lokaci sai ga Mamy janye da akwatin Sagir, aka saka ma su but, drivern Daddy ya ja su ka bar gidan. Sai ɗaga ma su hannu su Saheen ke yi. Kai tsaye su ka wuce Area 1 don ɗaukar Mimie. A ƙofar gidan su ka faka ya kira ta a waya sai gata ta fito su Mommy harda to mata rakiya. Ta ƙarasa gaban motar Daddy ta na mishi sannu da zuwa tare da Faɗar "Alhaji mun gode da karamci, Allah ya ƙara girma mun gode, mungode, Allah ya kai ku lafiya." Kuɗi ya ciro bandir ɗin 500 guda ɗaya ya bata, ba kunya ta amshe ta na washe haƙora........ Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number👇🏼 _08109634202_ Domin na masa bayanin yanda zai biya kuɗin. Follow me on Wattpad @ummu inteesar. UMMU INTEESAR CE❤️💛💚💙💔💛 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)* *MARUBUCIYAR:* *SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* *DA KUMA* *A SANADIN KAMA* Wannan littafin na kuɗi ne akan Naira 200 kacal. Ga mai buƙata sai ya tura kuɗin ta wannan account ɗin: Account name: Rukayya ibrahim lawal Account no:0431343346 Gt bank. KADA KU MANTA KUMA ZAFAFA BIYU DAGA ƘAWAYE BIYU NE IDAN DUKA BIYUN KA KE SO A SANADIN KAMA DA ƘURUCIYAR SAPNAH TO N300 NE, IDAN KUMA WANNAN KAƊAI KA KE SO ZAKA BIYA KUƊIN KARATU N200. ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAH RAHMANIR-RAHIM* Free Page 2️⃣7️⃣↪️2️⃣8️⃣ Ɗaga Zuhra hannu ta ke ta na faɗar "Ki gaida gida da iyayen naki, Allah ya sauke ku lafiya." Ruma da ke tsaye jikin motar ta na bankwana da y'ar uwarta sai hawaye ta ke ta na ɗaga mata hannu. A haka drivern ya ja su ka bar ƙofar gidan. Tafiya su ke a nutse, banda sanyin a.cn motar ba abinda ke tashi, Sagir ne ya ke ta damunta da surutu, Daddyn na jinsu sai dariya ya ke masu, anan shima ya sako bakinsa a hirar ta hanyar ƙara tambayarta wasu abubuwa da su ka shafi tarihin rayuwarta., Ita kuwa ta na bashi amsa. Tafiyar awa uku da rabi ce ta sada su da garin Kano kasancewar motar da su ke ciki lafiyayya ce, sabuwar mota ce dal ƙirar Land cruiser prado. Ita ce ta ma su kwatancen hanya har su ka ƙarasa unguwarsu, su na zuwa ƙofar gidansu ta cewa driver "Nan ya yi ai mun zo gidan." Cike da fara'a a fuskarta ta yi zancen. Cike da mamaki Alhajin ke ƙarewa gidan kallo a ransa ya na mamaki "Ashe akwai mutane da ke rayuwa a irin wannan wajen." Driver ne ya zagayo cikin sauri ya buɗe ma su motar, ta sauka cikin zumuɗi ta na faɗar "Daddy bari na je na sanar masu mun ƙaraso." Daga haka ta nufi cikin gidan da gudu, Sagir na ganin haka shima ya bita a baya da gudunsa. Fitowar mama daga banɗaki kenan, ta na riƙe da buta a hannunta, ta ga yarinya ta shigo gidan da gudu ɗauke da Sallama a bakinta. Kallon yarinyar ta yi ta ce "Lafiya dai yarinya, biyo ki akayi ne da ki ka faɗo mana gida da gudu haka?" Dariya sosai ta yi ta ce "Kai mama ki na nufin baki gane Zuhranki ba?" Sai a lokacin ta ƙare mata kallo tabbas ita ce da sauri ta rungumeta ta na faɗar "Allah sarki Zuhrana ki yi haƙuri banganeki bane, tabbas zaman Abuja ya karɓe ki, kinga yanda ki ka mulmule ki ka yi haske kuwa?, Kin ƙara kyau." Zame jikinta ta yi ta na faɗar "Allah mamata?" "Ƙwarai da gaske." Maman ta bata amsa. Af mama kinga har zan sha'afa, kin san fa tare mu ke da Daddy ya na waje, shine na zo sanar daku, Baban namu yana nan kuwa?." "Allah sarki! Gashi kuwa babanki ya na gun sana'arsa Kira mun shi a waya na sanar masa, bari na shimfiɗa tabarma je ki shigo da alhajin." Sai a lokacin su ka lura da Sagir da ke tsaye a bayan Zuhra. Mama ta ce "Wannan yaron fa?" Da murmushi shimfiɗe a fuskarta ta ce "Ƙanina ne ɗan autan Daddy." Ta faɗa ta na janyo shi a cikinta. Kafin ta ƙarasa ƙofar gidan ta kira baba a waya ta sanar masa sun iso. Kayan aikin da ke hannunsa ya watsar tare da miƙewa ya sanar da yayansa su kula da gurin shi zai je gida yanzu. ®®®®®®®®®®® A ƙofar gida Zuhra ta same sa har gumi ya fara karyo masa saboda zafin rana, ta ce "Ayyah! Yi haƙuri Daddyna na Barka ka sha zafi koh?, Muje daga ciki." Ba ta jira amsarsa ba ta juya ya bita a baya, tun shigarsu zauren gidan ya ke ƙarewa gidan kallo, kallo ɗaya za ka yiwa gidan ka gano waɗanda ke rayuwa ajikinsa talakawa ne, filasta ce kawai a bangon gidan ko fenti babu, simintin gidan duk ya tashi ta wasu ɓangarori na gidan. A haka su ka ƙarasa ciki,yayin da ya ke cike da al'ajabin yadda su ke iya rayuwa acikin wannan gidan. A kan tabarma ya zauna su na gaisawa da Mama. "Sannu da zuwa Alhaji, ya hanya? Ya iyali?" Mama ta faɗa cikin sake fuska. "Alhamdulillah, iyali kuwa su na nan ƙlau." "Alhaji mungode da ƙoƙari fa, Zuhra ta na ta bamu labarin abubuwan alkhairin da ku ke mata, mun gode, mungode Alhaji." "Ah! Bakomai wallahi, ai yiwa kaine ita ɗin tamkar y'a ta ke a gurina." Har mama zata ƙara magana su ka jiyo Sallamar Baba da ya ke shigowa gidan yanzu. Ƙarasowa ya yi ya na miƙawa Alhaji hannu. Duk da cewa daga wurin kanikancinsa ya ke, ko wanke hannu bai yi ba ya zo, hakan bai hana Alhaji miƙa masa hannunsa su ka yi musabiha ba. Nan fa Baba ya zauna aka cigaba da gaisawa, yayin da Zuhra da mama su ka tashi zuwa cikin ɗaki. Kuɗi mama ta bata N1000 ta ce "Kinga na manta ba a siyo lemo ba, maza kije kantin ɗan liti ki Karɓo masa lemo mai sanyi da ruwan roba." Karɓa ta yi ta fito tsakar gida, har ta kai ƙofar fita Sagir ya biyo ta da gudu. Alhajin ya ce "Ai fa yanzu aiki ya same ki Mimie, duk inda za ki sai ya bi ki." Yar dariya ta yi ta ce "Ai bakomai Daddy autanmu ne fa, dole a masa yanda ya ke so." Ta na gama faɗa ta sunkuce shi su ka bar gidan." Mama kuwa kitchen ta koma ta harhaɗa sauran abubuwan da su ka rage ta kawo ɗaki ta ajiye ta na jiran dawowar Zuhra. Bayan ta dawo ne Mama ta fito da abincin da aka shirya saboda shi kawai a tiren silver babba, cikin wasu kuloli ma su damar kyau da ta aro a maƙwafta kasancewar ita bata da su, a ɗakin Zuhran ta dire kayan. Baba ya ja shi zuwa cikin ɗakin domin ya ci abinci. Ba laifi sun yi ƙoƙari sosai gurin karrama baƙon na su domin a abincinsa harda kaza biyu a ciki. Su na cikin cin abincin ne wayar Alhaji ta hau ƙara. Ɗagawa ya yi tare da faɗar "Assalamu alaikum." Jim ya ɗan yi alamar ana magana a ɗaya bangaren, can ya ce "To madallah, kayan sun haɗu kenan? Nan ma ya ɗan yi shiru can ajima ya ce "Shikenan Kabir yanzu zan turo maka da address ɗin sai ka aiko mun da kayan, ba na son ɓata lokaci fa kasani." Daga haka ya kashe wayar,ya cigaba da cin abincinsa don ba laifi abincin ya yi daɗi sosai, dama Mama gwana ce a ɓangaren girki. Su na gama cin abincin su ka wuce masallaci don gabatar da sallar Azahar. Bayan dawowar su daga masallaci ne saƙon Alhaji ya iso. Dawowarsa kenan daga gun abokanansa dai-dai kan layinsu ya ga wata babbar mota cike da kaya ta na tafiya a hankali da alama su na neman wani guri ne, cigaba da tafiyarsa ya yi har ya zo ƙofar gidansu ya shige abinsa. A dai-dai lokacin ne kuma Alhaji ya gama waya da Kabir ya sanar mai kaya sun iso kwatancensa sai dai ba a gane gidan ba. Ƙarasawa yaron ya yi ya gaida mahaifinsa da baƙonsu har ya miƙe baba ya Kira sunansa "Ma'aruf!" "Na'am baba." Juyawa ga alhajin Baba ya yi ya ce "Alhaji ka kwatanta masa mutanen sai ya je ya zo da su." Kallon Ma'aruf Daddy ya yi ya ce "Za ka ga wa su mutane a wata babbar mota mai cike da kaya su za ka...." Ai tun bai gama rufe bakinsa ba ya ce "Wata ƙatuwar mota wacce ta ke cike da kayan abinci koh?" Da mamaki a fuskar Daddy ya ce "Eh ita, ko ka gansu ne?" "Na haɗu da su a farkon layi su na tafiya a hankali, bari na je kafin su kai kayan wani guri mu shiga uku." Ya faɗa cikin yarinta da rashin wayo, ya fice da gudu. Jim kaɗan sai ga su sun ƙaraso tare, aka fara sauke kayan abincin. Alhaji da Baba ne su ka fito ƙofar gida baba ya tara yara aka fara shiga da kayan ciki sai godiya ya ke ta yi Wa Alhaji, harda hawayen farin ciki. Tun da ya ke a rayuwa bai taɓa tunanin zai ajiye irin wannan kayan abincin a gidansa lokaci ɗaya ba. A kwai wani ɗaki a gidan wanda ke jikin kitchen da basa amfani dashi, sai tarkace ne kawai a ciki a ciki a ka saka kayan abincin. Da la'asar Daddy ya hau Motarsa ya ma su sallama za shi ya kama ɗaki a hotel inda zai kwana. Nan ma Sagir ya ƙi ya bi Daddy ya laƙewa Zuhra, bisa ga dole Alhaji ya haƙura ya tafi. ®®®®®®®®®®® Y'an uwa da abokanan arziƙi ne su ka cika gidan su Zuhra a na ta yi mata sannu da zuwa..... Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number👇🏼 _08109634202_ Domin na masu ƙarin bayani. Follow me on Wattpad @Ummu inteesar. UMMU INTEESAR CE❤️💙💚💛💔💙 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR) *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* *DA KUMA* *A SANADIN KAMA* WANNAN LITTAFIN NA KUƊI AKAN NAIRA 200 KACAL. GA MAI BUƘATA SAI YA TURA KUƊIN TA WANNAN ACCOUNT ƊIN: Accnt name: Rukayya Ibrahim lawal Accnt no:0431343346 Gt bank. Ko a tura katin Mtn ta wannan number 08109634202 KADA KU MANTA KUMA ZAFAFA BIYU DAGA ƘAWAYE BIYU NE IDAN DUKA BIYUN KA KE SO A SANADIN KAMA DA ƘURUCIYAR SAPNAH TO ₦300 KACAL, IDAN KUMA WANNAN KAƊAI KA KE SO ZAKA BIYA KUƊIN KARATU ₦200 ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Last Free Page 2️⃣9️⃣↪️3️⃣0️⃣ Haka ma yaya farida da matar yaya Kabir duk sun zo sai murna ake. Washe garin ranar da su ka zo da misalin ƙarfe sha biyu na rana Daddy ya zo gidansu Zuhra domin su tafi banki a buɗe mata account dama ya sanar da ita ta shirya kuma ta nemi ɗan rakiya. Saboda haka ko da ya zo ta gama shiryawa dama tuni yaya Kabir ya zo, zuwan Daddy kawai su ke jira, don haka koda ya zo mota kawai su ka hau suka wuce Gt bank. Cikin ƙanƙanin lokaci aka gama komai take anan Daddy ya yi mata transfer kuɗi dubu ɗari zuwa account ɗinta, su ka juyo gida. Jin kanta ta ke yi kamar tafi kowa ce yarinya Sa'a a rayuwa, wannan kuɗin da ya tura mata jin su ta ke tamkar miliyan goma sai ta ke ji yanzu ita da iyayenta sun samu waraka daga talauci. A kwana biyun da su ka yi Sagir ya shaƙu sosai da Zuhra da kuma ɗan uwanta Ma'aruf, saboda yanda su ke kula da shi da tarairayarsa tamkar ƙwai. Kwana biyu Daddy ya yi a garin Kano sannan ya yi shirin komawa. A ranar da zai tafi ya tara iyaye da y'an uwan Zuhra domin neman wata alfarma a gunsu. ®®®®®®®®®®® Ga baki ɗayan su zaune su ke akan wata ƙatuwar tabarma a tsakar gidan, kowa ya hallara in ka ɗauke Ma'aruf da ya janye Sagir ƙarami su ka fita zuwa wajen abokanansa. Anan Daddy ya dubi Kabir ya ce "To yaya babba sai ka buɗe mana taron da addu'a." Ba musu Kabir ya yi addu'ar aka shafa, sannan Daddy ya fara jawabi kamar haka " Da farko dai abinda ya sa na nemi mu taru anan shine, ina neman Alfarma guda biyu a wajenku, duk da na san ta farkon za ta yi matuƙar wuya amma zan roƙa." Ɗan dakatawa ya yi da zancen ya na kallonsu, Ganin duk sun zura mashi ido Alamar shi su ke saurare ya saka shi nisawa sannan ya ɗora da cewa "Alfarma ta farko shine ina so ku bar mun Mimie ta dawo hannuna domin ta maye mun gurbin Real Mimieta, na yi ma ku alƙawarin zan riƙe ta da amana, idan hakan bai samu ba to ina roƙon ku da ku ba mu damar zama iyayenta na biyu ta yadda za mu dinga sanin duk wani abu da ya shafi rayuwarta, in ya so duk aka yi hutu sai ta je mana, wannan abun zai sanya iyalina cikin tsantsan farin ciki." Tun da ya fara magana ba wanda ya ce ƙala, jin Alfarmar da ya nema ya sanya jikin Baba ya yi sanyi domin har ga Allah ya san ba zai iya barin Zuhra ta koma hannun wa su ba, domin da ya na buƙatar hakan da ba wanda yafi cancanta a baiwa riƙonta sai ƙanwar mahaifiyarta, tun da kuwa ya hana ta tabbas ba ya jin zai iya bawa Alhaji duk da ya na matuƙar jin nauyinsa. Ganin kowa ya yi shiru kuma ga Baba da alama ya zurfafa a tunani ya sanya Daddy ya ce "Ka kwantar da hankalinka malam Habu, idan ba zai yiwu ba ni na haƙora ka da ka ji kunyar faɗamin gaskiya." Dogon numfashi Baba ya ja ya sauke sannan ya ce "Ka yi haƙuri Alhaji ba wai ban yarda da kai ba ne ko kuma ba na son baka Zuhra ba ne a'a, dalilin da ya sa ba zan yi hakan ba shi ne kafin ka nemi wannan Alfarmar, ƙanwar Mahaifiyarta Khadeeja da ke Abuja ta nema ban yi mata ba, ka ga yanzu idan ta samu labarin na ba ka Zuhra tabbas ba za ta ji daɗi ba, don Allah Alhaji ka yi haƙuri, ka da ka ga kamar na maka butulci." Haƙiƙa Daddy ya ji zafin hanashin da aka yi sosai, amma ya masa uzuri domin ya san yanda zafin rabuwa da ɗa ya ke. Murmushin yaƙe ya yi ya ce "Kar ka ji komai Malam Habu, sai alfarma ta biyu da na ke nema ina fatar zan samu." "Insha'allah Alhaji." Ya amsa. Gyara zamansa ya yi sannan ya ce "Alfarma ta biyu kuwa ita ce daga yau ina so ku dinga kiran Zuhra da Mimie domin ina so ta maye min gurbin y'ata Mimie." Cikin hanzari Mama ta ce "Ah! Wannan ai ba damuwa tun yanzun ma za mu fara faɗa." Anan Daddy ya yi godiya sosai sannan ya sanar da su cewa ya na so ya haɗa auren Sameer da Mimie domin ƙarfafa zumunci. A razane Zuhra ta ɗago ta kalli Daddyn su na haɗa ido ta kuma sunne kai ƙasa. Iyayenta ma da yayyenta haka su ka ji maganar a bazata. Lura da yanayinta yasa Daddy ya ce "Ki kwantar da hankalinki y'ata, shine ya sanar da ni ya na sonki, amma duk da haka ba zan takuraki ba, ba tursasawa idan kin gama shawara ma yi magana daga baya." Daga haka ya tashi ya ma su sallama zai tafi, a dai-dai lokacin ne kuma Ma'aruf ya dawo gidan tare da Sagir. Nan fa kallo ya koma sama domin Sagir saka rigima ya yi shi ba inda za shi, zai zauna da Sisternsa anan, aka yi-aka yi fafur ya ƙi, sai da Daddy ya kira Mamy a waya ya gayamata tare da bawa Sagir wayar. Komai ta gaya masa oho, sai ga shi ya amince zai bi Daddy su koma gida. Anan ya masu Sallama Dukansu su ka ɗunguma zuwa kofar gida don su ma sa rakiya. Motarsa ya hau driver ya ja zuwa abuja, a ransa ya na da ƙudurin canza ma su gida, amma so ya ke sai komai ya dai-daita tukunna. Tun daga ranar aka fara kiran Zuhra da Mimie kowa haka ya ke kiranta, domin a ɗabbaƙa Alfarmar da aka yiwa Daddy. Bayan tafiyar Daddy Zuhra ta shirya zuwa gidansu Raliya domin ta kai mata kayan arziƙin da su ka samu a matsayin tsaraba. Raliya ƙawarta ce tun a primary ajinsu ɗaya kuma kujera ɗaya har yanzu su na tare kuma aji ɗaya duk da cewa Raliyan ta girme ta amma sun shaƙu sosai. Ta na matuƙar tausayawa rayuwar ƙawartata, kasancewar mahaifiyarsu ta rasu shekara uku da su ka wuce, kuma mahaifinsu mai ƙaramin ƙarfi ne kamar babansu, ga shi har zuwa lokacin bai ƙara aure ba, sai su kaɗai a gida, yayarta ɗaya ƙannenta huɗu duk ita da yayarta ke kula da su. Sai da ta ɗibar mata komai na kayan abincin kama daga kan shinkafar har kayan maggin sannan ta nufi gidansu. ®®®®®®®®®®®®® Bayan wata Ɗaya Zaune ta ke a tsakar gida akan ƙaramar kujerar katako ta na wanke-wanke. A zahiri wanke-wanken ta ke amma kallo ɗaya za ka mata ka fahimci cewa hankalinta ba ya gun, ta yi nisa acikin tunanin wannan sabon al'amari da ya tunkaro rayuwarta, mafita kawai ta ke nema. Ta na nan a haka bata ankara ba sai ji ta yi an dafa kafaɗarta, ta juyo aɗan razane sai ta ga ashe ƙawarta ce. Da mamaki a fuskarta ta ke kallon tasleem tare da cewa "Tasleem! Yaushe ki ka zo ne? Ban fa ji shigowarki ba." Tasleem ta ce "Dama yaushe za ki ji shigowa ta? Tun da ki na nan ki na wannan sababben tunanin na ki, ni na rasa meke damunki ne, Soyayya hauka ce, da za ki mayar da kan ki haka?, Ke kenan kullum tunani.?" Ɗan murmushi ta yi bata ce komai ba, Tasleem ta cigaba da cewa "Na san dai ki na tunanin Rayuwarki ne wato Bassam, Wai ni kam ƙawata wane irin so ne ki ke yiwa Bassam haka?" Ta tambaya tare da janyo wata kujerar da ke kusa da ita ta zauna kusa da Mimien. Sai da ta ɗauraye kular da ke hannunta ta kife a cikin kwando kafin ta yi murmushi ta ce "Ba za ki gane ba ne ƙawata, ina son Bassam fiye da komai a rayuwata, ni kaina ba zan iya kwatanta iya adadin son da na ke yi masa ba, Abun da nasani shine duk duniya ba wani fa namijin da na ke so sama da shi, duk da cewa ba shi ne na farko da ya furta min kalmar so ba, Amma akansa na fara soyayya, kuma ba wanda na kamu da tsananin sonsa har na amincewa zuciyata ba zan iya rayuwa idan ba shi ba sai Bassam." Murmushi sosai Tasleem ta yi ta ce "To ƙawata Allah ya bar ƙauna ya sa shine abokin Rayuwarki na har abada." Miƙewa ta yi adai-dai lokacin da ta kammala aikin da ta ke tare da ɗauke kwandon ta na washe baki ta ce "Ameen ƙawata Allah ya bar mun ke." "Ba zai bar ni ba wallahi sai na mutu." Ta faɗa Ƙyalƙyalewa da dariya ta yi ba ta ce komai ba. Miƙewa tsaye Tasleem ta yi tare da Faɗar "ke ba fa zama na zo yi ba, dama zan je gidan yaya Khalil ne, shine na ce bari na biyo mugaisa,kin san tun dawowar ki daga Abuja ban samu shigowa ba saboda muna exam ne, amma zan samu dama na yi miki zuwa na mussanman." "Nagode sosai ƙawata sai kin zo, mu je na taka mi ki koh?." Ta faɗa. "No da kin barshi tare muke da direba." Tasleem ɗin ta faɗa. Duk da haka ba ta hak'ura ba sai da ta raka ta har k'ofar gida. Mimie ta ce "Nagode sosai ƙawata a sauka lafiya, Allah ya kiyaye hanya." Ameen ta ce tare da shigewa cikin motar direba ya ja su ka bar ƙofar gidan. ®®®®®®®®®®® Juyawa ta yi ta koma cikin gidan ta cigaba da Aikace-aikacen ta dama Mama ba ta nan ta fita saboda haka ba kowa a gidan sai ita kaɗai tsintsiya ta ɗauka ta share tsakar gidan gaba ɗaya da ya ke gidan ba wani mai girma ba ne sosai cikin mintuna ƙalilan ta kammala Sharar. Ruwa ta ɗiba a bokiti ta nufi banɗaki ta yi wanka, tana fitowa ta ɗora Alwala kasancewar lokacin Sallar Azahar ya yi. Ɗakinta ta shige ta saka kaya tare da zura dogon hijabinta ta shimfiɗa Sallaya ta tada Sallah. Sallamewar ta keda wuya ta ji ƙarar wayarta ƙirar iphone 6+ da ke gefe ɗaya a kusa da ita. Da sauri ta ɗauki wayar don ta riga ta san mai kiran ko bata duba ba, Bassam ne ke kira. Murmushi ne ya bayyana a fuskarta yayin da ta ke ɗaga kiran, Wayar ta kai saitin kunnenta tare da yin Sallama. A ɗaya bangaren Bassam ne ya Amsa Sallamar cikin zazzaƙar muryarsa mai kama da sautin kanari. Faɗaɗa murmushinta ta yi su ka gaisa sosai daga nan kuma su ka fara kashewa juna zuciya da tausasan kalamai masu ratsa zuciya sai da su ka shafe kusan minti Arba'in su na wayar kafin su ka yi Sallama da juna su ka datse kiran. Dogon numfashi ta ja, haɗe da faɗawa akan ƙaramar katifarta ta tsunduma kogin tunani "Oh! Allah ga Mimie, Allah ka dube ni da idon rahama." Ta faɗa a bayyane. Bakomai ne yasa ta faɗin haka ba sai dan tunawa da ta yi cewa Daddy Ya na so ya haɗa ta aure da babban ɗansa wato Sameer, kuma ba za ta iya tozarta Daddy ba, ba ma yadda za'ayi ta ƙi jininsa Tun da ya so ta ya nuna mata gata ya ɗauke ta tamkar y'ar cikinsa (Real mimie) da ya haifa, ita kam ta na jin kamar ta karɓi zaɓin sabon Abbanta da ya nuna mata gata fiye da kowa a duniya, to amma ya za ta yi da zaɓinta babban masoyinta a duniya? Dole ne dai ɗaya za ta aura acikinsu ko dai Sameer ko Bassam. Ta na kai nan a tunaninta ta kuma jan dogon numfashi tare da dafe kanta da Tafin hannunta ta na faɗar "Oh! Ni Mimie ina mafita?, Allah ka fitar da ni daga wannan matsalar." Mirginawa ta yi akan katifar ta na cigaba da cewa "Amma fa ya kamata na yi tunani sosai tsakanin masoyan nan nawa guda biyu, waya kamata na aura ne?" Ajiyar zuciya ta yi kana ta ci gaba da tunaninta. Sameer dai ɗan Alhj ne kuma ko da bai faɗa ba ta san shine zaɓinsa tun da ba zai ƙi ɗansa ba, amma fa ya gaya mata ba tursasawa idan dai har bata son Sameer ka da ta ji kunyar gaya masa don ta na ganin cewa Sameer ɗansa ne, ai itama y'ar tasa ce da ya ke ji da ita wacce ta ke a matsayin Mimiensa y'a ɗaya tilo da ya ke da kuma ya ke ji da ita tamkar Rayuwarsa, sai ga shi mutuwa ta masa yankan ƙauna. Ya yi baƙin cikin matuƙa a lokacin mutuwarta, amma yanzun da ya sami wace take a madadinta sai ya ji baƙin cikinsa ya gushe to me zai saka ya tursasa Mimiensa? Ya gaya mata cewa idan da wanda ta ke so ta sanar da shi, shi zai shige mata gaba ayi komai na auren. Sai dai ita fa ta na matuƙar jin kunyar Alh Salman, ta ya za ta buɗi baki ta ce ba ta son ɗan cikinsa? Inah! Ba zai yiwu ba. A zahirin gaskiya kallon yaya ta ke masa ba masoyi ba ba zata iya aurarsa ta bar Bassam ba, idan ta yi haka tamkar ta yaudari masoyinta Bassam ne. Duk da cewa iyayenta suna ƙarfafa mata gwuiwa ta auri Sameer domin ƙin aurensa kamar butulcewa Alhaji ne, amma inah! Sam ita ba za ta iya ba ko alama... Ta na ganin daurewa kawai za ta yi ta fuskanci Daddy ta sanar da shi gaskiyar lamari cewa....... 🤔🤔tirƙashi! Idan baku manta ba a farkon labarin kunga Mimie a gidan Bassam ana gallaza mata. Tambayar anan ita ce: Shin ina yawan ƙaunar da ya ke mata ta tafi? Me yasa ya juya mata baya? Ina kuma labarin Sameer? Tayaya ta auri Bassam ta bar zaɓin iyayenta? Domin jin cigaban wannan ƙaryata cen labarin sai ku biya kuɗin ku 200 ba yawa. Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number👇🏼 _08109634202_ Domin na masa ƙarin bayanin yanda zai biya kuɗin. Ka da ku manta wannan shine last free Page duk mai buƙatar jin cigaban wannan labarin sai ya biya kuɗin da ₦200 kacal ba yawa, a tura katin ta number da ke sama. Follow me on wattpad @ummu inteesar. Vote, share& Comment UMMU INTEESAR CE💚💙💛💙 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)* MARUBUCIYAR SOYAYYAR MEERAH Y'AR GANTALI RIKICIN MASOYA *DA KUMA* *A SANADIN KAMA* WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL. GA MAI BUƘATA YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202 KA DA KU MANTA WANNAN PAGE ƊIN NA WANDA SU KA BIYA NE SU KAƊAI, IDAN KA SAN BAKA BIYA BA KADA KA KARANTAMUN DOMIN HAƘƘI NA NE, IDAN MA KA BIYA KUƊIN KADA KA FITARMIN DA LITTAFI DOMIN KUƊIN KARATU KA BIYA BA MALLAKA NA BAKA BA. ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Page 3️⃣1️⃣↪️3️⃣2️⃣ Cewa ita fa gaskiya Bassam ta ke so shine cikar burinta kuma farin cikinta. A haka ta wanzu ta na ta tunanin mafita har bata san ta shafe tsawon lokaci haka ba, sai da ta ji kiran sallar la'asar. Miƙewa ta yi ta tada Sallah dama da arwallarta, a haka Mama ta dawo ta same ta. ®®®®®®®®®®® A haka rayuwa ta cigaba da gudana ko yaushe Mimie na cikin zullumi da tunanin mafita don gudun kada a rabata da masoyinta.. Dama tuni an koma hutu don haka ta cigaba da zuwa makarantar ta kamar lokutan baya sai dai yanzu rayuwarta ta samu sauyi ba kamar da ba, domin yanzu su na da wadataccen abinci da suturu masu kyau sakamakon shigowar Alhaji Salman cikin rayuwarsu. ®®®®®®®®®® A bangaren Mommy kuwa ta gama cika fam! Fashewa kawai ya rage ta yi, domin yanzu wata tsanar Mama da ƴaƴanta ta ke ji, domin a ganinta su suka hanata damar cika burinta na shiga cikin daular dukiyar Alhaji Salman. Bayan tafiyar Mimie Mommy bata kira su ta ji ya su ka sauka ba, duk ta watsar da su saboda hassada, yanzu babban target ɗinta shine ya za'a yi ta aurar da y'arta Ruma a gidan Alhaji Salman?, Domin a gaskiya ba zata iya ƙyale wannan daular ta wuce ta na ji ta na gani ba, saboda haka akai-akai takan kira Mamy su gaisa a waya, shima Alhajin haka wani lokaci ma har su mata kyautar kuɗi, domin su nuna musu ta ke duk duniya ba wanda yafi ta son Mimie. ®®®®®®®®®®® Alhaji Salman kuwa ya na matuƙar son ya ga aure ya ƙullu tsakanin Mimie da Sameer domin ta dawo cikin iyalansa kamar baya, amma ba ya son ya takura ta, hakan ya saka ya yi gum da bakinsa ya ƙara bata dama daga nan zuwa lokacin da za ta yi candy. Mamy da ta ji zancen soyayyar da Sameer ke yiwa Mimie ba ƙaramin daɗi ta ji ba, don haka a kullum ta kai goshinta ƙasa sai ta roƙi Sarkin talikai da ya ƙaddara wannan aure na yaranta. ®®®®®®®®®®® Zancen soyayya tsakanin Mimie da Uncle Bassam ɗinta kuwa sai ma abinda ya ƙaro, ya na tarairayarta gami da bata kulawa baya son damuwarta ko kaɗan. Wata rana da dare Mimie na kwance akan katifarta (sabuwa da ta siya da kuɗin da Daddy ya tura mata) Kawai sai wayarta ta hau ruri, acikin magagin barci ta lalubo wayar ta katse kiran tare da koma kwanciya, domin ta tsani abinda zai katse mata barci mai daɗi irin wannan. Wayar ce ta kuma ruri a karo na biyu a ɗan fusace ta ɗaga wayar ta ɗora a kunnanta bata ce komai ba, still idonta na rufe. Daga can ɓangaren Sameer ne ya ce "Assalamu alaikum warahmatullah wa barakatuhu, da fatar ban katsewa sweet sis daddaɗan barcinta ba." Zumɓur ta yi ta tashi zaune ta na waro ido a ranta ta ce "Yaya Sameer?" "Meyasa zai kirani kuma a wannan lokacin?." Mamaki ta ke sosai, domin wannan ne karo na farko da su ka fara magana a waya. A daƙile ta amsa mai da cewa "Wa'alaikamus Salam, Yaya Barka da dare." "Yawwa Barka dai, kin fara barci ne?" "Eh." Ta basa amsa a taƙaice. Ya ce "Ayyah! Sorry sweet sis, na katse maki barci amma ki yi haƙuri a bar ƙaunata zuciyata ce ta azalzalamun akan son jin muryarki har ta saka na manta cewar yanzu dare ne, mai yiwuwa kuma Sweety barci ta ke." Kalamansa sun bata mamaki duk da cewa bai kamata ta yi mamakin ba domin ya riga ya sanar da ita cewa ya na sonta. Mamaki da fargaba ne ya hanata maida masa da amsa. Shi kuwa jin shirun ya yi yawa ya saka ya kashe wayarsa domin a zatonsa ko barcin ne ya wuce da ita tunda dama ta fara. Murmushi ne kwance a fuskarsa yayin da ya katse wayar, ko ba komai dai ya yi farin ciki tunda ya ji muryarta kuma ya tabbatar ta na lafiya, a bayyane ya ce "Allah ka mallaka mun zuciyar wannan yarinyar, Allah ka bani ita a matsayin uwar ƴaƴana, ameen." Ita kuwa bayan katse wayarsa barci ne ya ƙauracewa idonta ta rasa ma tunanin me za ta yi, tabbas ta na cikin sarƙaƙiya, ƙwaƙwalwarta na dab da tsayawa cak akan tunanin mafita, to ita yanzun wa za ta aurah, Sameer ko Bassam? Dogon numfashi ta ja tare da mirginawa ta sauka daga kan katifar ta je ta ɗoro Alwala ta tada Sallar nafila ta na roƙon Allah da ya kawo mata mafita acikin wannan lamarin (dama Mimie yarinya ce mai ibada sosai, wannan na daga cikin ɗabi'unta duk lokacin da wata matsala ta tunkaro ta, tana mayar da dukkan lamuranta ga Allah ta hanyar yin nafilfili da riƙon Allah domin ya kawo mata mafita) A kullum iyayenta su na ƙara ƙarfafa mata gwuiwa da bata shawara akan ta auri Sameer ko don halaccin da iyayensa su ka mata, amma har zuwa yanzu bata jin za ta iya barin Bassam domin a ganinta ba zata taɓa jin daɗin rayuwa in ba shi ba. ®®®®®®®®®®® Bayan shekara ɗaya da rabi, abubuwa da yawa sun faru a ciki kuwa harda sabon gidan da Alhaji ya siya ma Baba a unguwar geza, gidan bene ne babba, dai-dai wanda zai ishesa yin rayuwa da iyalansa cikin farin ciki, wancan gidan na Tukuntawa Baba ya saka yan haya aciki, yanzu kam alhamdulillah komai ya wadata agaresu. Yan uwan baba da su ka guje shi saboda talauci da ya ke fama dashi, yanzu duk sun laɓaɓo sun bashi haƙuri su na neman yafiya a gareshi na gudunsa da su ka yi abaya don suna ganin sun fi shi arziƙi(Rayuwa kenan, dama duk lokacin da baka da shi to kai ba kowa bane, yan uwanka ma gudunka su ke amma daga lokacin da ƙofofin arziki suka fara buɗe ma kuma sai ka dawo kaine abun girmamawarsu.) A lokacin kuwa Zuhra ta na Ss3 a shekarar za ta yi candy, har yanzu dai ta na nan a makarantar y'an mata ta gandun albasa, ba yadda Daddy bai yi ba ta bari a canza mata makaranta amma ta ƙi, acewarta ko a makarantar gwamnati mutum ya ke zai iyayin karatu idan ya so." Zahirin gaskiya ba ta so a raba ta da ƙawarta Raliya da su ka ta so tare tun ƙuruciya, sosai Zuhra ke son Raliya ta na kyautata mata, barin yanzu da su ka fara samun abun duniya komai ta kwasa Raliya ta ke kaiwa, ba ƙaramin daɗi Raliyan ke ji ba, domin su ma sun shaida cewa su Mimie sun samu. Ko da yaushe Daddy da Mamy cikin turawa Zuhra kuɗi su ke a account domin yanzu sun ƙara shaƙuwa fiye da da, domin a shekaru biyun da su ka gabata duk hutu a Abuja ta ke yinsa, sai hutu ya ƙare ta ke dawowa kano. Saboda haka yanzu koda yaushe tana cikin yin vidio call da su yaya Saheen da Salim a laptop ɗinta ko a wayarta. Lokacin da ya rage baifi saura sati uku ba afara weac a lokacin ne kuma yaya Sameer ya tayar mata da ƙayar baya akan zancen aurensu, shima Daddy a lokacin ya tuntuɓe ta don son jin shawarar da ta yanke, a bangare ɗaya kuma ga Bassam sai zumuɗi ya ke akan alƙawarin su ya kusa cika harma ya sanar da iyayensa domin su zo neman aure. Nan fa hankalin Mimie ya tashi ta rasa yanda za ta yi, gabaki ɗaya hankalinta a tashe ya ke gashi har zuwa lokacin ta kasa samun mafita. Ana cikin wannan halin ne wata rana da daddare iyayenta su ka yi kiranta zuwa falon Baban nata domin su nusar da ita akan wannan lamari. Zaune ta ke a ƙasa kan carpet ta sunkuyar da kanta ƙasa yayin da Baba ya fara magana kamar haka:Zuhra ina so ki nutsu sosai ki saurare ni, lokaci ya yi da za ki sanar mana wa za ki aura acikin manemanki biyu, kin sani dole ɗaya za ki aura don haka wa ki ka zaɓa?" Sunkuyar da kanta ta yi ƙasa idonta ya fara tara ƙwalla ta na tunanin ita ta ina ma za ta fara? "Muna sauraron ki" mama ta faɗa. Buɗi baki ta yi daƙyar ta ce"Baba ni......... Follow me on wattpad @Ummu inteesar UMMU INTEESAR CE❤️💔💛 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)* *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* *DA KUMA* A SANADIN KAMA ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Page 3️⃣3️⃣↪️3️⃣4️⃣ Daƙyar ta ce "Baba ni a gaskiya gani na ke kamar idan ban auri Bassam ba na yaudare shi kuma gaskiya ni...." Maganar ce ta laƙe a kasan maƙogwaronta ganin a gaban iyayenta ta ke. Baba ya tari numfashinta da cewa "Ai dama tun farko ba mu mai alƙawarin cewa za mu ba shi ba, kuma ba mu ƙarbi komai nasa ba, don haka ba yaudara, zan kira sa na bashi haƙuri." Ɗago kai ta yi zuciyarta na rawa ta ce "Amma Baba gaskiya ni fa kallon yaya na ke yiwa yaya Sameer ba zan iya aurarsa." Mama ce ta cafe zancen da cewa "Yaro man kaza, idan bakya sonsa yanzu, a hankali idan kuna tare za ki so shi amma da kunya, mu gayawa Alhaji cewar ba za ki auri dansa ba, don haka ki haƙura kawai." Hawaye mai zafi ne ya fara bin kuncinta ganin ana neman raba ta da mutum da ta shaqu dashi sama da kowa, kuma mutumin da ta shafe shekara biyu wutar ƙaunarsa na ruruwa a ranta, gaskiya ba za ta iya ba. Ta na ganin za ta ajiye kunyar nan kawai ta fito musu da abinda ke ranta. Gyara zamanta ta yi ta sunkuyar da kanta ƙasa ta ce "Baba, Mama ku yi haƙuri ka da ku ce na maku rashin kunya, Amma gaskiya Ni dai Bassam na ke so shi kaɗai zan iya....." Mama ce ta katse mata zance yayin da ta ke cewa "La'ilaha ilallah! Malam ka ga yaran zamani koh?" Ta faɗa ta na tafa hannu tare da kallon baba. Numfashi ya ja "hmmmm" sannan ya kalli Mimie ya ce "Zuhra! Ɗago idonki ki kalleni." Ba musu ta ɗago madai-daitan idanuwanta masu haske ta zuba mi shi su. Ya ce "Zuhra kin sani cewa mu iyayenki ne, mu muka haife ki muka sha ɗawainiyar rainonki tun kina jinjina har kawo yanzu da ki ka zama budurwa, kin sani cewa ba yadda za'a yi mu zaɓa maki abinda zai cutar da ke saboda muna sonki sosai." Ɗan tsagaitawa ya yi yana kallonta don ya ga ya ta ƙarbi zancen. Sai dai ita tuni ta sunkuyar da kanta ƙasa hawaye na cigaba da yin sintiri a kumatunta. Bai damu da hakan ba ya ci gaba da cewa "Sau tari Kakan so abu ya kasance ba alkhairi bane a gareka, ko ka ƙi Abu ya kasance shine alkhairi a gareka, shiyasa ake so duk lokacin da mutum zai yi wani abu makamancin wannan to ya yi istikhara ya mayar da lamarinsa ga Ubangiji. Don haka a matsayina na mahaifinki ina mai ba ki shawara da ki auri Sameer ko don karamcin iyayensa a garemu, idan ki kai mana haka zamu ji daɗi sosai ni da mahaifiyarki kuma kin mana biyayya, amma zaɓi ya rage na ki ba zan maki auren dole ba." Ya na kai nan ya yi shiru alamar ya kawo ƙarshen zancensa. Tun lokacin da ya fara maganar ta ke jin kanta ya na mata masifar ciwo kamar zai fashe, kalamansa sun matuƙar gigita ta da bata mamaki har ta fara zargin iyayen nata kodai...? Don haka ko da ya kai ƙarshen zancensa miƙewa kawai ta yi tare da dafe kanta ta fashe da matsanancin kuka yayin da ta ke barin gun ta na faɗar "Ni dai wallahi uncle Bassam na ke so, za ku iya rasa ni idan....." Bata ƙarasa zancen ba sakamakon kukan da ya ci ƙarfinta. Da mamaki iyayen nata ke Binta da kallo abun na ba su mamaki da tsoro ace wai y'arsu ce a gabansu ta na gaya masu haka? Yarinyar su mai matuƙar kunya, ladabi da biyayya ita ce yau ta ke faɗa masu haka a gabansu? Tabbas akwai aiki ja a gabansu. ®®®®®®®® Ita kuwa bayan shigewar ta taƙinta anan ƙasan tiles ta sulale ta na kuka mai cin rai, "Meyasa su Baba za su yi mana haka? Anyah! Sun ɗauko hanyar adalci kuwa? Meyasa su ke son rabani da Bassam bayan su da kansu su ka ba mu damar zama masoya? Da ba su yarda za su basa ba ai da ban faɗa tarkon sonsa harna shaƙu da shi haka ba? Sai yanzu da na kai ƙoluluwa a kan bishiyar ƙaunarsa za su nemi yado ni ƙasa? Wannan abun ba zai taɓa yiwuwa ba wallahi, ba zan yi biyayya wa wannan maganar ba, indai akan Sameer ne na san yanda zan yi." Ta na kai nan a tunanin zucinta ta rarrafa ta janyo wayarta da ke kan bedside drower ta shiga neman layin Sameer don yau so ta ke ayi ta ta ƙare domin ba zata taɓa saɓuwa ba bindiga a ruwa. Har ta ƙaraci burarinta bai ɗaga ba, nan fa ta ƙara ƙuluwa a bayyane ta ce "aikin banza wai a hakan ka ke so a baka ni, bayan ka kasa kula da wayarka ma bare ni. Su ƴaƴan ma su kuɗin nan me su ka ɗauki kansu ne?" Ta na cikin wannan mitar ne sai ga shi ya biyo kiran, ɗagawa ta yi a gadarance ko sallamarsa ba ta tsaya amsawa ba ta ce ....... Ku yi haƙuri da wannan kun san daga tafiya na ke so agajiye na ki wallahi shiyasa, don kawai na ga shirun ya yi yawa na ce bari na maku. Follow me on wattpad @ummu inteesar UMMU INTEESAR CE❤️💔💛💔❤️ 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)* *MARUBUCIYAR SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* *DA KUMA* A SANADIN KAMA WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE DON ALLAH IDAN KA SAN BAKA BIYA BA KADA KA KARANTA MUN. IDAN MA KA BIYA DON GIRMAN ALLAH KADA KA FITARMIN DA SHI DOMIN KUƊIN KARATU KA BIYA HAƘƘIN MALAKA NAWA NE ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAH RAHMANIR-RAHIM* Page 3️⃣5️⃣↪️3️⃣6️⃣ Ta ce "Don girman Allah Sameer ka yi haƙuri ka janye maganar aurena da ka ke so ka yi, tun kafin haɗuwata da kai an tsayar mun da miji amma soyayyarka ta na neman zame mana Barazana a rayuwar soyayyarmu..." Saurin dakatar da maganar ta ta yi gudun ka da ta yi kwaɓa. Sameer kuwa tsikar jikinsa ce ta fara tashi, hankalinsa ya dugunzuma ba ki na kakkarwa ya ce "Ke ma don girman Allah ki yi haƙuri Sweety wallahi ba zan iya rayuwa ba ki ba, ban san cewa kina da wanda ki ke so ba, da na yi yunƙurin hana zuciyata faɗawa tarkon soyayyarki, amma yanzu ba ni da zaɓi da ya wuce aurenki ina matuƙar sonki ba zan iya rayuwa ba ki ba." "Nima haka Sameer ba zan iya rayuwa ba Bassam ba soyayyarsa a gare ni bata da iyaka, ko da na aure ka ba zan iya kallon ka a matsayin miji ba, sai dai yaya don haka ya na da wuya na iya maka biyayyar aure, ka ga kuwa zan rayu cikin halaka ne don Allah ka yi haƙuri ka sanar da Daddy ka janye." Jikinsa ne ya soma kakkarwa bakinsa na ɓari zuciyarsa cike da damuwa ya ce "Sweety Wallahi ina son ki ban san yaushe na kamu ba, amma na sani cewa idan ki ka guje ni rayuwata za ta zama mara amfani, idan ma na rayun kenan, amma ba damuwa idan haka ne zai sakaki farin ciki zan yi ƙoƙarin aikatawa, domin ki rayu cikin farin ciki zan iya haƙura da nawa farin cikin" Daga haka ya kashe wayar zuciyarsa cike da ƙunci ya zube kan tiles tare da dafe saitin zuciyarsa. ®®®®®®®®®®® Ita kuwa bin wayar ta yi da kallo, haƙiƙa ya matuƙar bata tausayi domin ta san zafi da raɗaɗin so, amma idan ta aure shi tamkar ta daɓawa cikinta wuƙa ne, domin ita za ta cutu, saboda yanda ya ke jin bai iya rayuwa idan bata itama haka ta ke ji akan Uncle. Da wannan tunanin ta ajiye wayar ta ɗoro Alwala ta fara karatun Alqur'ani, nan da nan kuwa zuciyarta ta fara yin sanyi. ®®®®®®®®®®® Har zuwa lokacin Bassam bai san me ake ciki ba domin ta kasa sanar masa, sai dai da yawan lokuta ya kan gan ta cikin damuwa idan ya tambaya sai ta ce Bakomai, amma zuciyarsa ta kasa nutsuwa da hakan. A kan haka ya shirya wata rana ya zo hira gidansu da dare. Isowar Motarsa ƙofar gidan ya yi dai-dai da ƙarasowa motar Baba. Hon drivern ya ke ta tsabgawa amma ba Alamar za'a buɗe gate ɗin, ganin haka ya saka Bassam ya yi saurin ƙarasawa ya shiga ta ƙaramar ƙofa ya zuge ma su gate ɗin, bayan sun shige ya mayar ya rufe, sannan ya ƙarasa gun don gayar da Baba. Baba na fitowa ya nufi hanyar cikin gida ba tare da ya kalli Bassam ɗin ba. Da mamaki Bassam ke binsa da kallo, ganin ya na neman shigewa ya saka ya ɓoye mamakinsa ya yi sauri ya tarad da baba ya ce "Barka da dare Baba." "Yawwa Barka dai." Baban ya bashi amsa ba tare da ya kallesa ba, ya yi shigewarsa. Shi dai mamaki ya gama cika sa tambayoyi ne fal a ransa ya rasa mai ba sa amsa. Waya ya ɗaga ya kira Mimiensa, ya na nan tsaye cikin mamaki sai ga ta ta ƙaraso da murmushi a fuskarta ta ce "Barka da zuwa kyakkyawan mijina." "Yawwa sannunki da fitowa sarauniya" Ya faɗa jiki a sanyaye. Kujerun roba guda biyu ta ɗauko ta saka ma su acikin gate ɗin sannan ta dawo ta ce masa "bismillah." Ƙarasawa ya yi ya zauna har yanzun dai a sanyaye ya ke. Lura da hakan da ta yi ya sa ta kallesa ta ce "Uncle ya dai na ga jikinka a sanyaye?" Murmushin yaƙe ya yi ya ce "Ka da ki damu ba wani abu." Ganin ya na ƙoƙarin ɓoye mata gaskiya ya sa ta yi narau-narau da ido ta ce "Don Allah menene ko Babana ya gaya ma ka wani abun ne?" Girgiza kai ya yi ya na faɗar "A'a bai gayamin komai ba, akwai abinda ya ke son ya faɗa kenan? Ko shiyasa na ga ya..." Zaro ido ta yi ta ce "Don Allah me ya maka?." "Bai mun komai ba, amma na ga ya sauya mun ina gaida shi ya na kawar da kai kamar na masa wani laifin, idan kin san dalilin haka ki gaya mun gaskiya na shiga damuwa." Sunkuyar da kanta ta yi ta na ƙoƙarin goge hawayen da ya fara gangarowa a idonta. Kafe ta ido ya yi kasancewar da akwai haske a gurin ya na ganinta sosai. Sosai hankalinsa ya tashi ganin ta na sharar ƙwalla ya ce "Don Allah ki gaya mun menene?." Cikin raunin murya ya yi zancen. Share hawayen ta yi sannan ta ɗago ta ce "Ina cikin damuwa sosai, haƙiƙa Soyayyarmu ta na cikin barazana, domin ana neman raba ni da kai ƙarfi da yaji kuma ni......" Bata ƙarasa ba saboda sabon kukan da ya zo mata shi ma hankali a tashe ya dube ta ya ce "....... Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number 08109634202 Follow me on wattpad @ummu inteesar Ummu inteesar ce💔❤️❤️❤️❤️❤️❤️ 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘAMIN RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)* *MARUBUCIYAR SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* DA KUMA A SANADIN KAMA WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN N200 KACAL GA MAI BUƘATA YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202 IDAN KIN SAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA MUN, IDAN KA BIYA MA KUƊIN KARATU NE KA BAYAR, HAƘƘIN MALAKA NAWA NE DON HAKA BAN YARDA KA FITARMIN BA. DON ALLAH A KIYAYE. ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAH RAHMANIR-RAHIM* Page 3️⃣7️⃣↪️3️⃣8️⃣ Ya ce "Menene? Ki sanar da ni da gaggawa don Allah." Cikin rawar murya ta ce "Ana so a raba ni da kai masoyina ta hanyar aurar da ni ga wani, don Allah ka yi wani abun." Wa su sababbin hawaye ne su ka sake tsiyayowa daga idonta su na sartu akan kumatunta. Cike da tashin hankali ya miƙe tsaye daga zaunen da ya ke ya na faɗar "Waye ke son shiga tsakanina da burina? Wa ake son ba wa ke?" "Sameer ne ɗan gidan Alhaji Salman." Ta ba sa amsa. Wata uwar zabura ya yi ya ce "What!? Dama ba don Allah su ke ɗauke da ɗawainiyarku ba, dama su na da wata manufa a kai kenan?" Huci ya yi sannan ya koma ya zauna bai ce komai ba sai ma dafe kansa da ya yi da hannayensa. "Meye mafita yanzu?" Ta jefo mai tambaya. Ya ce "Mafita ɗaya ce ki samu baba ki sanar da shi ni ki ke so, ki tuna fa shekara biyu na shafe ina rainon soyayyarki a zuciyata, sai yanzun da ta yi ƙwari kuma za ki bari a raba mu?" Cike da rashin madafa ta ce "Na sanar da su haka, amma sun ce ba za su iya yiwa Alhaji butulci ba, dole na haƙura da kai." Dogon numfashi ta ja ta sauke kana ta ce "Mafita ɗaya ce ta rage mun, idan ina son fita daga wannan matsalar, sai dai abun da kamar wuya in iya..." Har ya sare ya sallama cewa ba zai kuma yin farin ciki ba a rayuwa matuƙar a ka raba su, jin wannan zancen da ta yi ya saka ya yi saurin jefa mata tambaya "Wacce hanya ce ta rage? " Ɗago idanunta da su ka fara sauya kala zuwa ja ta yi ta ce "Mafitar ita ce na kira Daddy na sanar da shi cewa ni kai na ke so? Domin ya gaya mun ba tursasawa na kawo wanda duk na ke so shi zai shige mun gaba a yi komai, wannan hanyar ita kaɗai ta rage amma ka san kamar da wuya na iya...." Saurin dakatar da ita ya yi ta hanyar cewa "Kawai ki ajiye kunya ko jin nauyi ki aika ta idan ba so ki ke ki rasa ni ba." Ya faɗa kamar mai shirin yin kuka sannan ya ɗora da cewa "Na yi mi ki alƙawarin zan kula da ke da dukkan ƙarfina, zan yi iya ƙoƙarina don kare ki a ko'ina, ba zan bari a cutar da ke ba." Ya ƙarasa faɗa cikin raunanniyar murya, daga haka ya miƙe cike da karayar zuciya, ko sallama ya kasa yi mata kawai sai ya juya a hanzarce ya fice daga gidan. Ta na ganin haka ta miƙe da gudu ta shige cikin falo idonta na ambaliyar hawaye. ®®®®®®®®®®® Sameer kuwa tun ranar da su ka yi waya ta ƙarshe da Mimie ta sanar da shi ba za ta aure sa ba, ya ke cikin tashin hankali, abinci ma yanzu ba sosai ya ke ci ba, ya rage fita sai dai ya ƙule a ɗaki ya yi ta kukan zuci. A ransa ya ke cewa "ya Ubangiji ga bawanka, ka san halin da na ke ciki, kai ka jarabce ni da soyayyarta, Allah ka sassauta mun raɗaɗin da zuciyata ke yi." Mamy ce ta shigo ɗakin nasa ta Same sa kishingiɗe akan gado, kallo ɗaya za ka masa ka fahimci ya fara fita a hayyacinsa. Cikin hanzari ta ƙarasa kusa da shi ta na faɗar "Menene Sam? Kamar da zan shigo na jiyo muryarka ka na magana, ga shi na ga kai kaɗai ne a ɗakin, akwai wata damuwa ne?" Saurin ta shi zaune ya yi ya na ƙoƙarin ɓoye damuwarsa ta hanyar ƙaƙalo murmushi ya ce "Ba fa komai Mamy me ki ka gani ne?" Kallon tuhuma ta masa sannan ta ce "Na ga ko abinci ka rage ci kwanan nan, sai aukin kulle kai a ɗaki,tabbas akwai wani abun, Ni fa mahaifiyarka ce, ni nafi cancanta ka sanarwa matsalarka kafin kowa." Nannauyar ajiyar numfashi ya sauke ka na ya ce "Mamy na gaya miki ba komai ki yarda da ni, ni Ko me zan ɓoyewa mahaifiyata a duniyar nan?" Ya faɗa ya na riƙo hannuwanta. "Hmmm! To shikenan, Nagode Allah tun da ba matsala, ni bari na tafi dama na zo duba lafiyarka ne." Bayan fitarta ya ja dogon numfashi tare da kwanciya kan gadon ya na faɗar "Ki yi haƙuri Mamyna ba na so ki shiga damuwa ne, amma na tabbatar za ku iya rasa ni idan aka wayi gari Mimie ta auri wani, na san ba zan iya jurewa ba." ®®®®®®®®®®® Mommy ce kwance a gadonta da dare, ta na tufka da warwara, hanya ta ke nema mafi sauƙi da za ta shigar da y'ar ta gidan Alhaji Salman, sannan ta na son ta tunkuɗe Zuhra da iyayenta daga wannan daular, domin tabbas idan ta rasa suma dole sai sun rasa. Babban takaicin ta shine abinda ta ke gudu ne ya faru, domin zuwa wannan lokacin ta daina samun Alkhairai sosai daga gidan Alhaji domin da alama sun manta da ita, haka ma musaddiq ya ma daina zuwa gaida ta bare ta saka ran samun abun hannunsa, ga ta da tsinan nan kwaɗayin abun duniya, duk da gwargwado su na da irin na su kuɗin." Ta na kai nan a tunaninta ta ja dogon tsaki tare da yin ƙwafa a ranta ta ce "Ku jira ni ɗaya bayan ɗaya zan ɗau fansa a kanku, mussanman kai Habu domin kai ne silar komai da ya faru, matsiyaci kawai." Tsakin da ta yi ne ya farkar da Abban Ruma daga sumammen barcinsa. Juyowa ya yi ya ce "Lafiya dai khady? Me ki ke yiwa tsaki a tsohon daren nan? Dama ba ki yi barci ba?" Ya jefo mata tambayoyin a jere. Fuskarta ba yabo ba fallasa ta ce "Ba na jin barcin ne, ina zuwa bari na je kitchen na sha ruwa." Ficewa ta yi daga Bedroom ɗin, zuciyarta cike da hassadar y'ar uwarta da tunanin hanyar da za ta bi ta ƙuntata mata don ta rama. ®®®®®®®®®®® Bayan sati ɗaya ansha artabu da Mimie akan ta a jiye burinta ta zaɓi zaɓin iyayenta amma fur ta ƙi, yayyenta sun yi iya ƙoƙarin su gun nuna mata illar bijirewa umurni ko shawarar iyaye, yaya farida har misalai ta bata da aurenta da alƙasim wanda da can ba shi ba ne zaɓin ta ba, Abbansu ne ya zaɓa mata shi, da ta yi haƙuri ta yiwa mahaifinta biyayya sai ga shi yanzu ta na ganin alkhairan da ke tattare da auren. Duk wannan misalin bai saka Mimie ta sauko ba, tuburewa ma ta ƙara yi a kan lallai ita sai zaɓinta soyayya ta riga da ta gama rufe mata ido, har bata iya hango illar saɓawa iyaye, tuni ta manta tarbiyyarta da tsananin biyayyarta ga iyayenta a da. Har fushi sai da Mama ta yi da Zuhra na tsawon mako ɗaya ba ta kula ta, amma bai sa ta karaya ba. Haka ma Abbanta ya daina kula ta daƙyar ma ya ke amsa gaisuwarta, a bangare ɗaya kuma ga Bassam ya daina kiranta tun lokacin da ta shaida mai ba za ta iya sanar da Daddy Ba ta son ɗansa ba, idan ma ta kira shi tambaya ɗaya ya ke mata, kin sanar da shi? Da ta ce a'a ya ke katse wayar. Abu duk ya taru ya caɓe mata, ta shiga damuwa sosai, ga waec na ƙara matsowa amma ta kasa karatu. Kuma ta kyautata zaton Bassam Ya na cikin wani hali na kaɗaici da damuwa. Ganin idan ta yi wasa za ta iya samun matsala harma a bangaren karatunta, hakan ya sa ta yanke hukuncin kiran Daddy kawai za ta yi komai ta fanjama fanjam, koma me zai faru ya faru gwanda a yita ta ƙare kowa ya huta. Tashi ta yi daga zaunen da ta ke a falo, ta shiga ɗakinta tare da ɗaukar wayarta ta dannawa Daddy Kira. Ta na shiga kuwa ba ɓata lokaci ya ɗaga ya na faɗar "Assalamu alaikum daddy's girl ya ki ke?" Jiki a mace ta amsa masa Sallamar tare da cewa "Lafiya qlau." Cikin raunanniyar murya ta ke magana. "Subhanallah! Y'ata me ya same ki ne? Ya na ji muryarki kamar ki na cikin damuwa? Sanar da ni menene? Da alamar tashin hankali a muryarsa ya ke maganar. Samun kanta ta yi da kasa ba shi amsa kawai sai ta fashe da kuka mai cin rai. Ai kuwa Daddy ya ruɗe iya ruɗewa sai tambayarta ya ke yana fadyar "Innalillahi wa inna'ilahir raji'un! Me nene? Waya taɓa y'ar Daddy?" Kara karyar mata da zuciya zancensa ya yi kawai sai ta kashe wayar, ta cigaba da gursheken kukanta. Hankali a tashe ya kuma kiranta, ganin har sau uku ya na kira amma ta ƙi ɗagawa, hankalinsa ya sake dugunzuma kawai sai ya kira Mama a waya da har zai kira babba sai ya tuna wataƙil ya na gun aikin yanzu haka ya saka ya mayar da kiran a number Mama. Bayan ta ɗaga sun gaisa ya ke tambayarta me ya samu Mimie ne ya ji ta na kuka?" Mama kasa cewa komai ta yi, ya ce "Ki kai mata wayar na rarrashe ta." Jiki a mace ta ƙarasa ɗakin Mimien ta bata wayar ta fice a ranta ta na jinjina girman rashin kunyar yarinyar ashe har za ta iya kuma kiran Alhaji ta kai masa kukanta bayan ta ƙi jininsa? Gaskiya ƴaƴan zamani ba su da ta ido." ®®®®®®®®®® Karɓar wayar ta yi cikin sanyin jiki da rasa makama. Daddy ne ya ce "Y'ata idan har kin ɗauke ni matsayin uba ina so ki sanar da ni me ke damunki, na mi ki alƙawarin ko menene zan yi iya ƙoƙarina gurin samar ma ki mafita, idan kuma abun yafi ƙarfina sai na taya ki da addu'a." Kalamansa sun ƙara mata ƙwarin gwuiwa ta na ji wannan shi ne lokacin da ya dace ta gaya mai matsalarta. Sai ta buɗi baki za ta yi magana kuma sai ta kasa. "Ina jinki y'ata." Daƙyar da siɗin goshi ta buɗi baki ta ce "Dama baba ina da wanda.... Am dama... Dama...." Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number 08109634202 Follow me on Wattpad @ ummu inteesar UMMU INTEESAR CE❤️💛💚💙 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)* MARUBUCIYAR SOYAYYAR MEERAH Y'AR GANTALI RIKICIN MASOYA DA KUMA A SANADIN KAMA WANNAN LITTAFIN NA KUƊI AKAN 200 KACAL GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202 DON ALLAH IDAN KINSAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA MUN, IDAN MA KIN BIYA KUƊIN KARATU KAWAI KI KA BIYA HAƘƘIN MALAKA NAWA NE BSN YARDA KI FITARMIN BA. ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Page 3️⃣9️⃣↪️4️⃣0️⃣ Kasa ƙarasawa ta yi sai ta kuma rushewa da kuka. Iya tashin hankali Alhaji ya gani ranar rarrashinta ya shiga yi, sai da ta yi shiru sannan ya ce "Ki faɗa mun ko minene insha'allah zan samar maki shi ko ɗan farin cikinki." Cijewa ta yi ta ce "Dama Daddy ina da wanda na ke so na aura tun kafin haɗuwar mu, shine su Baba su ka ce ba zan aure shi ba tun da ga yaya Sameer, kuma wallahi Daddy zan shiga matsala in har ban aure shi ba." Murya a raunane ta ƙarasa maganar. Duk da cewa Daddy ya ji ba daɗi akan wannan maganar da ta faɗa ma sa yanzu, amma farin cikinta ya fiye ma su komai saboda haka ya ce "Ki kwantar da hankalinki y'ata, in dai wannan ne ba ki da matsala, zan kira babanku mu yi magana, daga yau Sameer ya janye shi ma nasan ba zai so damuwar yar ƙanwarsa ba, ya sunan surukin nawa ne?" Ya ƙarasa maganar da sigar zolaya. Dariya ta yi cike da kunya ta ce "Bassam." Ta na gama faɗa ta kashe wayar ta na sauke ajiyar zuciya lokaci ɗaya wani nishaɗi ya dirar mata. Number Bassam ta lalubo a wayarta domin ta ma sa Albishir mai daɗi. Cikin Sa'a kuwa ta na kira ya ɗaga tambayar da ya saba yi mata yau ma ita ya yi. Sai da ta yi ɗan murmushi sannan ta amsa masa da cewa "Albishirinka!" Cikin rawar baki ya ce "Goro." Ta ce "Yanzun nan mu ka gama waya da Daddy ya ce sun janye saboda farin cikina ya fiye ma su komai, ya ce ma zai kira Babanmu ya sanar mai." "Kai! Alhmdulillah, gaskiya na ji daɗin wannan Albishirin naki, kin ga shikenan sai na turo magabata na a gama magana, nan da wata ɗaya a ɗaura mana aure." Ya faɗa. Y'ar dariya ta yi sannan ta ce "Da wuri haka uncle? "Ko ya yi nisa ne na rage? Ke yanzu irin wannan tashin hankalin da mu ka shiga kwanan nan da ba don Allah ya taƙaita ba ai da na shiga tara." Dariya kawai ta ke masa bata kuma cewa komai ba, daga haka su ka cigaba da wayar su har zuwa lokacin da su ka kashe wayar. ®®®®®®®®®®® Abuja Mommy ce tsaye a kan Ruma ta na surfa mata masifa a dalilin ta ce ba zata gidan Alhaji Salman ta kwana ba, wanda hakan na ɗaya daga cikin shirin da Mommyn ke yi domin nemarwa y'arta muhalli a gidan. "Haba Mommy! don Allah me yasa dole sai na je can na kwana, bayan Zuhra bata nan?" Harara Mommy ta watsa mata ta ce "Kin ji ki da wani shashanci, yanzu ne lokacin da ya kamata ki shiga rayuwar y'an samarin gidan domin samun soyayyarsu." Ita dai Ruma ban da kallon Mommy ba abunda ta ke, tuni Mommy ta sauya mata ta zama wata iriyar mace, saɓanin yanda ta san ta a da. "Maza ki je ki yi wanka, ga wannan kayan su na ke so ki saka, ina nan ina jiran ki." Ta faɗa ta na miƙa mata wata arniyar doguwar abaya ɓaka wacce ta ji ado stone a gabanta. Baki a hangame ta karɓa ta wuce cike da tsananin mamaki "to wai me Mommy ke nufi da ni ne?" Bayan ta fitowarta ne Su ka je gidan Daddy ita da Mommy drivernsu ne ya kai su, a mota take mata huɗubar yadda za ta ɗauki hankalin samarin gidan. Ita dai Ruma ba ta ce uffan ba har su ka ƙarasa gidan. ®®®®®®©©© Daddy kuwa bayan sun kammala waya da Mimie ya kira Baba a waya ya ke sanar masa cewa Sameer ya janye daga neman auren Mimie, sa'annan idan za'a zo neman aurenta ya sanar masa. Baba na jin haka ya rayo aransa tabbas wannan aikin Mimie ne ita kaɗai za ta iya faɗawa Alhaji wannan zancen.. Lallai yayan zamani ba su da ta ido, yau ko za su haɗu shi da ita ne, a kunyace ya karɓa masa da to, sannan ya sauka daga layin. Miƙewa ya yi a fusace ya fice daga shagon kasuwancinsa (wanda alhajin ya siyar masa tare da bashi jari). Kallon yaran shagon ya yi ya ce "Ni zan tafi gida ku kula da shagon, idan lokacin tashi ya yi ban dawo ba ku rufe." Da to suka amsa su na masa sauka lafiya, Motarsa ya hau ya wuce gida kai tsaye, ya cika fam! Ba abunda ya ke so kamar ya buɗi ido ya gansa a gaban Mimie, tabbas yau sai ta fuskanci hukuncin abinda ta aikata, shi za ta zubarwa mutunci akan wani banzan yaro? ®®®®®®®®®® Ya na gama faka motar ya shige falon fuskar nan a haɗe tamkar bai taɓa dariya ba. Da Mama ya fara cin karo a falon "kira min Mimie." Shine kaɗai abinda ya faɗa. Ganin yanayinsa ya bawa Mama tsoro, hakan yasa ta ce "Lafiya dai Alhaji?" "Kira mun ita dai idan ta zo ai za ki ji." Jiki a saɓule ta je ɗakin Mimie ta yi kiranta a lokacin suna maƙale a waya ita da Bassam. Haka kawai ta ji gabanta na faɗuwa da jin wannan kiran, hijabinta ta sako sannan ta fito. A lokacin tuni mama ta dawo falon, dama ta na isar da saƙo ta juyo don jin me y'arta ta yi. "Sannu da zuwa Baba ga...." Bata samu nasarar ƙarasa zancenta ba, saboda saukar wani gigitaccen mari da ta ji a kuncinta na dama. "Mu za ki maida mutane banza ko Zuhra? Ashe ba mu isa da ke ba?...." Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number 08109634202 Follow me on wattpad@ummu inteesar UMMU INTEESAR CE❤️💚💙💙 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘAMIN RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)* MARUBUCIYAR SOYAYYAR MEERAH Y'AR GANTALI RIKICIN MASOYA DA KUMA A SANADIN KAMA WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202 DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE Page 4️⃣1️⃣↪️4️⃣2️⃣ "Zaɓinki ya fi namu koh?, To mun gode Allah ya saka da alkhairi." "Ashe rashin kunyarki har ta kai haka? Ina tarbiyyarki, ina iliminki, ina biyayyarki duk ina su ka je ne?" Mama da tuni kanta ya gama ɗaurewa, kuma har zuwa lokacin ba ta fahimci laifin y'ar tata ba, sai dai ta san cewa ba yadda za'a yi Malam ya mare ta ba tare da ta masa komai ba, domin shi ba fitinanne ba ne, ko faɗa bai cikawa yaro ba sai da babban dalili. Kallonsa ta yi tace "Malam me kuma ta yi ne?" A cikin wani irin wani yanayi ta yi zancen. Baba ya na huci ya ce "Kin san wai yarinyar nan kiran Alhaji ta yi ta gaya mai ba ta son ɗansa, saboda rashin mutunci?" A razane Mama ta ɗago ciki na kyarma ta ce "Me nene? Lallai Zuhra kin baɗa mana ƙasa a ido, ke ba ki duba halacci da karamcin wannan mutumin a garemu ba, kika mai haka?" Mimie da tun lokacin da Baba ya mare ta ta durƙushe idonta na tsiyayar da hawaye sai a lokacin ta iya buɗar baki daƙyar ta ce "Ku yi haƙuri iyayena, soyayyar Bassam ta makantar da gani na, na ga ku na shirin raba ni da shi ne, wanda idan hakan ta faru tamkar kun ƙwace makullin farincikin rayuwata kun yi wurgi da shi ne, sanar da Daddy shine kaɗai mafita kuma....." Cikin tsananin fushi Baba ya daka mata tsawa "Ya isa haka!, Ki je ki yi abinda ki ke so amma ba hannuna a ciki." Ya na gama faɗa ya yi fuu ya fice cikin fishi, bin bayansa Mama ta yi itama rai a matuƙar ɓace. ®®®®®®®®®®® Bayan Mommy da Ruma sun je gidan Alhaji Salman, Mommy ta sanar da Mamy cewa ta kawo mata Ruma ne ta yi kwana biyu don ƙarfafa zumunci. Sosai Mamy ta nuna jin daɗinta wanda daga gani iya fuska ne bai kai zuci ba. Anan Mommy ta tafi ta bar y'arta cikin tunani da al'ajabi, huɗubar Mommy ta tuna lokacin da su ke tahowa a mota inda ta ke cewa "Ki buɗe kunnenki da kyau ki ji ni, ba shashanci zan kai ki ba, zan kai ki ne domin ki siye zuciyar ɗaya daga cikin samarin gidan, ga kayan nan na saka miki a jakarki idan kin je su na ke so ki dinga sakawa, kaya ne masu ƙayatar da kwalliya, duk ɗa namiji lafiyayyan da ya gan ki a cikin shigar dole ki burge shi, saura ya rage na ki ki san yanda za ki yi ki ja ra'ayinsu ki dinga naniƙe musu, ki yi duk abinda ki ka ga za ki iya, ni dai burina ki cafko zuciyar ɗaya daga cikinsu daga nan sai ki bar komai a hannu na." (Wa'iyazu billah wai uwa ce ke yi wa yarta wannan huɗubar saboda son abun duniya, Allah ya kyauta.) ®®®®®®®®®® Sameer kuwa damuwa ta zame masa mugun ciwo a zuciya, domin duk ya ƙwarjame ya rame, a ranar da Daddy ya kira shi ya sanar da shi cewa ya yi haƙuri da auren Mimie domin ta na da nata zaɓin kuma shi ya goyi da bayanta, ya roƙi Allah ya zaɓa mai mafi alkhairi, har suman zaune sai da ya yi. Amma ba yadda ya iya haka ya haƙura domin shima ya fi son farin cikin nata akan kwanciyar hankalinsa. Tun daga lokacin Sameer ya zama abun tausayi kullum likitansu na hanyar zuwa gidan Alhaji domin duba lafiyarsa. Mamy duk ta shiga damuwa ta na cikin wannan damuwar ne kuma Mommy ta kwaso Ruma ta kawo mata, haka nan ba yadda ta iya ta nuna murnarta a fuska, amma a zuciyarta damuwar ciwon ɗanta ne fal aciki. ®®®®®®®®®® Bassam kuwa ya na ta shirye-shiryen angwancewa, ga shi ya na son turo iyayensa amma Baba bai bada fuska ba. Ita kuwa Mimie kowa ya fita sha'anin ta duniya ta mata ƙunci a haka su ka fara waec bata da kwanciyar hankali har yayyenta duk sun share ta, gaisuwarta kaɗai su ke amsawa ita ma sai sun ga dama. Gidan yaya Farida kaɗai ta ke zuwa ta ji ɗan sanyi-sanyi, to can ɗin ma Baba ya hanata zuwa yanzu. Ana cikin haka iyayen Bassam su ka ce za su zo kawo kuɗin aure, ta je da kanta ta samu Mama a sanyaye ta sanar mata. "Ki je ki faɗawa babanki ni ba ruwana a lamarin." Mama ta faɗa. Jiki ba ƙwari ta fice ta samu Baba a ɗaki ta sanar mai daka mata tsawa ya yi ya ce "Ki ɓace mun daga nan mutuniyar kawai, ki je ki nemi wani uban amma ba ni ba." Cikin rashin madafa da mutuwar jiki ta miƙe ta bar ɗakin, zuciyarta ta riga ta ƙeƙashe a kan komai za'a yi ba za ta canza zaɓinta ba duk rintsi. Mafita ɗaya ta rage mata ita ce ta kiran Daddy, don haka ba ɓata lokaci ta kira shi ta na kuka ta sanar mai abunda Baba ya ce da kuma halin da ta ke ciki a gidan. Lallashinta ya yi ya sanar mata da kwantar da hankalinta insha'allah zai zo da kansa har Kano don yin magana da baba. A cikin kwanakin kuwa Daddy ya dira Kano, lallaɓa Baba ya shiga yi, daƙyar ya shawo kan Baban sai dai duk da haka ya ce shi ko ƙwandalarsa ba za ta yi ciwo a auren Zuhra da Bassam ba. Murmushi kawai Daddy ya yi ya ce "A haka ma mungode saka albarkarka kawai mu ke nema, ni ne zan yi komai na auren y'ata insha'allah." Daddy da kansa ya kira Bassam ya sanar mai ya turo iyayensa, dama abu ga mai jira domin tuni ya shirya komai dama kawai ya ke jira abashi don haka ya na komawa gida ya sanar da Alhaji sale(Aminin babansa ne da ke zaune a nan Kano, a hannunsa Bassam ya ke.) Tun kan Daddy ya bar garin su ka kawo kuɗin auren Mimie tare da sadaki gaba ɗaya kuma ta ke a gurin a ka saka rana wata ɗaya, da ya ke shima Daddyn Amaryar a shirye ya ke shiyasa ba'a samu wata tangarɗa ba. Bayan an kammala da wannan ne Daddy ya koma Abuja, ya je ma su da Albishirin da ya zamewa Sameer gobarar zuci. ®®®®®®™™™ Murna a gun Mimie da Bassam kuwa ba'a cewa komai sai albarka su ke sakawa Daddy da masa fatar dacewa da alkhairai duniya da lahira...... Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number 08109634202 Follow me on wattpad @ummu inteesar UMMU INTEESAR CE❤️❤️❤️❤️❤️ 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘAMIN RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)* MARUBUCIYAR SOYAYYAR MEERAH Y'AR GANTALI RIKICIN MASOYA DA KUMA A SANADIN KAMA WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202 DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE Arewa writers association Page 4️⃣3️⃣↪️4️⃣4️⃣ A cikin wata ɗayan da aka saka ne ta yi Candy, lokacin da ya rage bikin saura sati ɗaya Mama ta kira Mommy ta sanar mata duk da cewa ba'a son ranta za'a yi auren ba, kuma y'ar uwar tata ta share ta tun lokacin da aka hana ta rikon Mimie hakan bai hana ta sanar mata ba domin acewar ta itama ta na da haƙƙi ya rage nata ta zo ko akasin haka. ®®®®®®®®®®® Abuja Lokacin da ya rage saura kwana goma bikin, su Mamy ne da Daddy ke ta tsare-tsaren yanda bikin zai kasance domin wannan karon duka iyalan gidan za su je bikin shalelensu. Duka ahalin gidan, su na zaune a makeken falonsu, amma banda Sameer da ke kwance a ɗakinsa ya na jinya, anata hirar yanda tafiya Kano za ta kasance wannan karon, domin tuni Daddy ya tura kuɗin komai na kayan ɗaki a account ɗin yaya Kabir an siyar mata komai. Sameer ne ya sauko daga bene a hankali ya nufo inda su ke zaune, ka na ganinsa ka san cewa baya cikin hayyacinsa, ga shi duk ya rame ya yi baƙi.. A hankali ya ƙara so gun kamar mara lakka ya nemi guri ya zauna ya na faɗar "Mamy & Daddy barkan ku da dare." "Yawwa Barka dai ya ƙarfin jikin?." Su ka amsa a tare. "Alhamdulillah jiki da sauƙi." Ya faɗa. Saheen da sauran ƙannensa su ka gayar da shi ya amsa sannan ya ce "Hirar me ake? Tun daga sama na ke jiyo dariyarku." Mamy ta ce "Muna hirar yanda tafiyarmu kano bikin ƙanwarka za ta kasance ne, ka yi ƙoƙari ka shirya ina tsammanin duk gidan nan kai ne kaɗai baka shirya ba domin kwana uku ya rage tafiyar mu." Wani busasshen murmushi ya yi wanda iyakacinsa fatar bakinsa ya ce "Uhmm! Ai Mamy ina ga tafiyar nan ba da ni ba." Fiddo ido waje ta yi ta ce "What? To saboda me? Kenan idan Real Mimie ce a raye ba za ka je ɗaurin aurenta ba?" Gyara zamansa ya yi ya na cije baki da alama ya na shan wahala a zuci da gangar jiki Ya ce "Ba haka bane, tafiya zan yi ne." Bai jira jin me za ta ce ba ya juya ga Daddy, a dai-dai lokacin da ta ke tambayarsa Ina za ka je ne? Bai bata amsa ba sai kallon Daddy da ya yi ya ce "Daddy ina neman wata alfarma a gunka, don girman Allah ka ba ni dama na bar ƙasar nan kafin cikar makon nan, ina so zan je wata ƙasa na ƙarasa masters ɗina acan." Kallonsa kawai Daddy ya ke, bai yi yunƙurin katse shi ba sai da ya dire zancensa sannan Daddyn ya ce "Karatu a waje kuma da gaggawa haka? To miye Dalili? Na ɗauka a can baya kai ne ka ƙi wannan, lokacin da na so tura ka ka yi digiri a India me ka ce?" Ƙara matsowa ya yi kusa da Daddy ya yinda duka Mutane falon su ka zubo mai ido don son jin dalilin wannan tafiyar ta gaggawa. Ya ce "Daddy da ba na da buƙatar yin nisa da ƙasata, haka ban son barin mahaifata, amma yanzu tafiya ta kamani dole, akwai buƙatar na yi nisa da ƙasar gaba ki ɗaya ko zan manta da Mimie da abinda ya shafe ta duk da na san abu ne mai matuƙar wahala na iya manta ta, amma ba zan iya zama a ƙasar nan a ɗaura aurenta da wani ba alhali ina raye, don Allah Daddy ka da ka hanani." Ya na zancen idonsa na ciccikowa da ƙwalla kamar zai yi kuka. Shi kaɗai ya san raɗaɗin da zuciyarsa ke masa. Cike da tausayi da kulawa Daddy ya dubi ɗan nasa ya ce "Shikenan ka je ka fara shirin tafiyar Allah ya tsare ya kiyaye mun kai." Godiya ya shiga yi, yayin da Mamy ta ce na san yanda ka ke ji, tabbas ba daɗi amma ka jure ka cire abun a ranka ka rungumi azkar insha'allah komai zai zo ya wuce kamar ba'a yi ba." Miƙewa ya yi zai koma ɗaki Sagir ya ce "Yanzu yaya tafiya za ka yi ka bar ni?" Murmushi kawai ya masa ya juya Daddy ne ya kira sunansa, na manta ban tambaye ka ba wace ƙasar za ka?" "Ban riga na yanke shawara ba Daddy, idan na gama zan sanar maku." Ya faɗa murya na rawa, ya na gama faɗa kuma ya bar falon. Ga ba ki ɗaya jikin mutanen gidan ya yi sanyi da wannan al'amari, sun tausaya masa matuƙa. ®®®®®®®®®®® Amarya Mimie kuwa sai shirye-shirye ake ba kama hannun yaro, su yaya Farida da su Mama talatu ƙannen Baba su ka maye gurbin Mama a bikin domin su ke gudanar da komai da Ya kamata ta yi. Ana saura sati ɗaya su Mamy su ka ɗira a Kano, su kam Mama ta tarbe su iya tarba da sakin fuska domin a cewar ta su kaɗai ne baƙinta a bikin, amma kowa ya zo zuwan kansa ya yi. ®®®®®®®®®®® Sameer kuwa a ranar da su ka dira Kano a ranar jirgin su ya cira zuwa Dubai, ko makarantar da za shi bai sani ba, kawai ya tafi ne don ya bar kasar, ya tafi da zimmar idan ya na zaune a can sai ya nemi makarantar da ta dace da zarar anfara ɗaukar sabbin ɗalibai. Ya bar gida cike da ƙunci, haka sallamarsa da iyayensa ta kasance cike da alhinin rabuwa da ahalinsa. ®®®®®®®®®®® A ranar da su ka sauka Mimie anan ta kwana tare da Mamy sun sha hira sosai, anan ta ke tambayar Mamy, "Nikam Mamy ina yaya Sameer ne? Shi kaɗai ne ban gani ba acikin yayyena." Mama da ke gefe ta na jin su sai harara ta ke watsawa Mimie, aranta ta ke mamakin irin wannan rashin kunya ta Mimie, ki ƙi mutum kuma ki dawo ki na tambayarsa? Ita ko kunyar Mamy bata ji da ta ƙi ɗan ta? Murmushi Mamy ta yi ta ce "Uhmm! Ai yaya Sameer ya tafi Dubai gun ƙaro karatu, da a tare zamu taho amma sai tafiyar ta faɗo dai-dai da lokacin, shima yau ya tafi." Ƙirjinta ne ya buga da ƙarfi dam! A zuciyarta ta ce "Na shiga uku, ka da dai ya tafi ne saboda zan yi aure." A fili kuwa murmushin ta yi itama ta ce "Ayyah! Shiyasa ashe ban gan shi ba, shi ko yaya Sameer haka ake tafiya ba sanarwa?" Dariya Mamy ta yi bata ce komai ba, a haka su ka kwana su na hirarsu gwanin burgewa. Mama ta so ta kore Mimie daga ɗakin domin haushin da ta ke bata, amma Mamy ta ƙi ta ce ita sai a bar mata y'arta su kwana tare za su yi hirar yaushe gamo. ®®®®®®®®®®®® Gidan Malam Habu ya cika da jama'a y'an biki duk da ba su yi wata gayya ba, amma hakan bai hana y'an uwa da abokan arziƙi cika gidan ba. Su Mamy tuni an zama yan gida sai hidima ake. Yaya Saheen, Salim da samar kuwa a gidan yaya Kabir su ke kwana can ne masaukinsu, domin Anty Zee a gidan Mama ta tare saboda hidima..... Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number 08109634202 Follow me on wattpad @ummu inteesar UMMU INTEESAR CE❤️❤️❤️❤️ 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘAMIN RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)* MARUBUCIYAR SOYAYYAR MEERAH Y'AR GANTALI RIKICIN MASOYA DA KUMA A SANADIN KAMA WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202 DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE Arewa writers association Page 4️⃣5️⃣↪️4️⃣6️⃣ A haka shagalin bikin ya cigaba da gudana, anyi shagali iya shagali kama daga kan party, kamu da Dinner ba abunda ba'a yi ba ko wanne biki ya ƙayatar domin an yi bukukuwan irin na ƴaƴan manya da ya ke Mamy da Daddy na garin duk wani abu da za'a nema don cigaban shagalin bikin a aljihunsu ya ke fita. Tun ana saura kwana Uku ɗaurin aure iyayen amarya da wa su daga cikin danginta su ka je birnin Kebbi domin gyaran ɗakin Amarya da ya ke a can garin su Bassam ɗin za'a kai ta can ya yi gidansa, da ya so ya zauna da ita a Kano ko da a gidan haya ne saboda nan ya ke aiki, amma fafur mahaifiyarsa ta ƙi ta ce dole sai a garin zai zauna kusa da ita, bisa ga dole ya bi umurninta. ®®®®®®®®®® Su mama Habeey (ƙanwar baba) da Mama sadiya (ɗaya ƙanwar Mama da ke garin kaduna ta na aure) su ne su ka je birnin Kebbi domin gyaran ɗakin Amarya kuma ba za su dawo ba har sai an kai Amarya. Har zuwa lokacin Mommy ba ta zo bikin ba kuma bata turo ɗanta ko ɗaya ba, Ruma ta so zuwa kamar me amma Mommy ta hana, bisa ga dole ta haƙura ta kira Mimie a ɓoye ta mata Allah ya sanya alkhairi. Sai dai Mommy ta turowa mama kuɗi Naira dubu talatin ta account ɗin yaya Kabir, wai ba zata samu damar zuwa ba a cewar ta. Kuɗin ma ta turo ne don ka da a zarge ta da rashin zumunci kuma don kada duniya ta zage ta ace auren yar yayata guda ba ta ce ba, kuma ba ta yi aike ba shiyasa, amma hassada ce fal a ranta. Da ma ta ji daɗin rashin auren Sameer da Mimie ta yi. ®®®®®®®®®® A bangaren abokan ango na jihar Kebbi ma tun ranar Alhamis su ka diro garin Kano da su aka yi dinner. Ranar Assabar da misalin ƙarfe takwas da rabi na safe dubbunan mutane su ka shaida ɗaurin Auren Bassam Aliyu da Amaryarsa Zuhuriyya Sadeeq Yusuf akan sadaki Naira dubu hamsin. Murna a gurin Bassam ba'a cewa komai domin sai da ya yi sujudus-shukur a gurin ya godewa Allah da ya nuna masa wannan rana. Da misalin ƙarfe goma sha ɗaya na rana aka kawo motocin ɗaukar amarya daga gidansu Bassam na nan Kano. Nan fa aka zo fitar da Amarya, Mimie ta sha kuka kamar ranta zai fita, Mamy ce ta janyo ta, ta kaita har uwar ɗakan Mama, a gaban Mamar ta durƙusar da Mimie ta ce "To Hajiya ga y'ata nan na kawo ta ki mata huɗuba zan sadata da ɗakin mijinta." Mimie kuwa banda kuka ba abinda ta ke sai yanzu ne ta ke jin kamar ta fasa auren nan saboda ba ta son yin nisa da iyayenta ga shi ba'a son ransu aka yi auren ba ta na tsoron me zai biyo baya. Mama da ta ke zaune kan gado daga ganin ta ka san ta na cikin alhinin rabuwa da y'ar tata, ta ja numfashi ta sauke sannan ta ce "Hmmm! To Hajiya ni me zance? Duk abinda zan faɗa an riga da an faɗa mata sai dai na tunatar da ita abu ɗaya." Mayar da dubanta ta yi ga Mimie ta ce "Zuhra ki riƙe Allah a ranki, ki sanya tsoron Allah a cikin dukkanin lamuranki, rayuwar aure ibada ce ba wasa ba, ki yi haƙuri ki yi biyayya ga mijinki, duk da cewa ba'a son ranmu ki ka yi wannan auren ba amma hakan ba zai hana mu yi miki fatan alkhairi ba, Allah ya ba ku zaman lafiya mai ɗorewa." Ta na kai nan ta kuma jan dogon numfashi ta sauke yayin da Mimie ta cigaba da rusa kuka kamar ranta zai fita. Cikin ƙarfin hali Mama ta dubi Mamy ta ce "Hajiya za ku iya tafiya ka da ku makara, Allah ya tsare ya kaɗe fitina." Mamy ta ce "Ameen mungode da addu'a." Miƙewa ta yi ta ja hannun Abar sonta su ka bar ɗakin, falon Baba ta kaita acan su ka tarar da Daddy da kansa ya raka ta har gaban Baba don neman gafara da yin sallama. Ko kallonta Baba bai yi ba, acan ƙasan ransa damuwa ce fal ta rabuwa da y'arsa duk da ya na jin haushin yanda ta bijirewa Umurninsa. Daddy ne ya katse mai tunani da cewa "Ga y'ata na kawo ka mata huɗuba, yanzu za ta tafi ɗakinta." Kawar da kai Baban ya yi ya ce "Kai ne Abbanta ai, kuma kai ka aurar da ita ga wanda ka ke so, don haka duk abinda zan faɗa na san ka riga ka gaya mata don haka ta tafi kawai Allah ya tsare." Jikin Daddy ya yi laƙwas da jin zancen Baba, kawai sai ya yi shiru ya ma rasa me zai ce ma, sai yanzu ne ya tabbatar ran Baba ya kai ƙololuwar ɓaci da auren. Juyawa ya yi ga Mimie da ke ta ruzgar kuka har jiyojin kanta sun yi ruɗu-ruɗu ya riƙo hannunta ya ƙara matsowa da ita daf da Baban sannan ya ce "Daddy's girl ki durƙusa ki bawa Babanki haƙuri, Babanki ya na fushi da ke sosai." Durƙusa ta yi ta kama ƙafafun Baba cikin kuka mai tsanani, murya na rawa ta ce "Babana don girman Allah ka gafarce ni ka yafe mun, sai yau na tabbatar da na tafka babban kuskure a rayuwata na bijirewa umurnin ka da na yi, amma aikin gama ya riga ya gama, da na sani ƙeya ce kuma tuni na barta a baya, don girman Allah ka yafe mun, muddin na tafi ka na fushi da ni tabbas ba zan ga dai-dai a rayuwar aurena ba." Ta na kai nan a zancenta ta kuma rushewa da wani marayan kuka, duk sai ta bawa Baban tausayi, sosai tausayinta ya ɗarsu a ransa don haka ya buɗi baki kamar wanda a ka yiwa dole ya ce "Na yafe miki tashi ki je, Allah ya miki albarka." Kasa miƙewa ta yi har lokacin ta na riƙe da ƙafafun Baba sai da Daddy ya zo ya janye ta yayin da ya ke ƙoƙarin shanye ƙwallar da ta taru a idonsa don tausayin da su ka ba shi su duka. Falon ya tarar da Mamy ya hannunta mata y'arta, dama tuni sun yi mata ta su huɗubar don haka Mamy da sauran iyayen Amarya su ka nufi motocin da za'a kai Amaryar dama tuni aka shirya amarya cikin shiga ta alfarma, shadda Maroon ce a jikinta sai alkyabba fara da aka ɗora mata akai, a haka su ka fito waje da ita hannunta na riƙe acikin na Mamy sai shasshekar kuka ta ke. Anan parking space su ka tarar da su yaya Saheen Mamy ta ja ta har gabansu don su yi Sallama anan su ka ƙara sanyayar mata da gwuiwa, ba ma kamar zancen Samar da ke cewa "Allah sarki my sister, shikenan yanzu kin yi nisa damu koh? Shikenan yanzu rayuwar yaya Sameer ta tabbata a cikin duhu da ɗemuwa ta rashin ki a matsayin mata koh? Allah sarki yaya Sameer Allah ya ba ka ikon jure wannan ƙaddarar." Hawaye ne su ka sauko a kuncinsa, yayinda ita ma Mimie ta kuma fashewa da kuka, da har an samu ta tsagaita sai ga shi ya famo mata ciwon. Mamy ce ta dakatar da shi ta hanyar ɗaga masa hannu ta ce "Ya isa haka Samar, ba na kawo y'ata don ku saka ta kuka ba ne sai don ku yi sallama, amma me ye haka ka yi kenan? Dawo da abinda ya wuce ba shi da amfani." Daga haka ta ja hannun Mimie zuwa cikin motar da aka tanada don Amarya. Dama tuni ƙawayen Amarya da y'an uwa da abokan arziƙi y'an rakiyar Amarya sun gama shiga Mota ita kaɗai ake jira, don haka ta na shiga direbobin su ka ja aka fara fita daga gidan domin zuwa Birnin Kebbi.. Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni 08109634202 Follow me on wattpad @ummu inteesar 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘAMIN RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)* MARUBUCIYAR SOYAYYAR MEERAH Y'AR GANTALI RIKICIN MASOYA DA KUMA A SANADIN KAMA WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202 DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE *AREWA WRITERS ASSOCIATION* Page 4️⃣7️⃣↪️4️⃣8️⃣ Ba su suka isa birnin Kebbi ba sai wajajen ƙarfe takwas na dare, a hakan ma wai don motocinsu lafiyayyi ne,kuma ba abinda ke tsayar da su sai sallah. Da isar su garin ko gidan Amarya ba'a tsaya ba, motar amarya da ɗaya daga cikin motoci uku na y'an rakiyar Amarya suka ɗauki hanyar Kalgo local government don zuwa gidan iyayen Bassam, acan za'a fara kai amarya gaisuwar iyayen miji kafin a miƙa ta ɗakinta, yayin da sauran motocin biyu su ka wuce gidan Amarya inda su Mama Habeey ke can su na dakon ƙarasowar su. Dama tuni an kammala gyaran gidan na Amarya ita kaɗai ake jira komai ya yi zam-zam don kuwa Daddy ya narƙar da dukiyarsa gun gyara ɗakin y'ar lelensa Mimie. ®®®®®®®®®® A ƙofar gidan su Ango motocin su ka yi parking inda Mamy ta fito daga motar Amarya ita da Raliya da gwaggwo talatu (ƙanwar baba,yar yayan mahaifinsa). Mamy ce ta riƙo hannun Amarya, su Raliya na take ma su baya har zuwa cikin gidan, sauran matan ma su ka fito su ka bi su a baya. A ɗan madai-daicin ɗakin Innarmu (mahaifiyar Bassam) su ka yi masauki, tarad da ita su ka yi tare da y'an uwanta da su ka zo taya ta murna. Ba laifi sun samu tarba domin ko ba komai an masu shimfiɗar fuska wacce y'an iya magana ke cewa tafi shimfiɗar tabarma. Bayan gaishe-gaishe iyayen Amarya su ka damƙa amanar y'arsu hannun iyayen ango, bayan wani lokaci aka kawo masu abinci da abin sha su ka ci su ka ƙoshi, su ma direbobin su Shamsiyya su ka kai masu na su abincin a ɗakin da aka masu masauki. Ko kafin a ankara dare ya riga ya yi domin har 10pm ta yi, don haka Innarmu ta ce dole su kwana anan domin ba za su koma birni cikin daren nan ba, ko ba komai Amarya ta gaji Saboda zaman mota ga kuma tafiya mai tsayi da su ka yi, dole su na buƙatar hutu, su bari da safe sai akaita ɗakinta. Haka kuwa aka yi anan su ka kwana, Amarya da ƙawarta Raliya tare da su Shamsiyya ƙannen ango su ka kwana a ɗaki ɗaya, sai nan-nan ake da ita. ®®®®®®®®©©® Ango kuwa tun lokacin da aka tashi walimar tayashi murna da abokanansa su ka haɗa masa, ya addabi mutane da maganar tafiya Bk, har wasu daga cikin abokanansa su na yi masa tsiya wai ya cika azarɓaɓi ko da ya ke badamuwa shi sabon shiga ne a harkar. Shi dai dariya kawai ya yi ya ce "na ji ai bakomai kowa da haka ya fara, azo a tafi don Allah Amarya na jirana." Dukkansu su ka saka dariya da haka su ka ɗebi motoci shida abokanansa na can dama wasu daga cikin abokan aikinsa su ka masa rakiya zuwa gidansa. Sun ma riga Amaryar yin gaba don haka tun su na hanya ya ke damun abokanansa direbobin motocin y'an Amarya da kira, "kun ta so? Ku na ina ne yanzu? A tuƙan Amaryata a hankali." Shine kaɗai abinda ya ke famar nanata masu, har su ka gaji su ka daina ɗaukar kiransa. Don haka angon ma ya riga Amaryar isa gari, shima gidansu ya fara zuwa ya sadu da y'an uwansa su ka taya shi murna, daga bisani ya wuce gidansa don jiran Amarya. Ganin har goma ta gota ba su ƙaraso ba ya sa ya shiga damuwa, ya fara neman layinta, ya kira ya fi a ƙirga bata ɗaga ba sai kawai ya kira number Antynsa Lami ita ta ke sanar mai Innarmu ta ce anan za su kwana, sosai ya ji haushi amma ba yanda ya iya haka ya haƙura, ya san dai komai ta daɗe sai an kawo masa ita. ®®®®®®®®®®® A bangaren Sameer kuwa ya na sauka masaukinsa a ƙasar Dubai kawai sai ya saka layin ƙasar ya shiga neman layin Daddy, anan ya sanar masa ya sauka lafiya, shima Daddy ya sanar masa suna gidansu Mimie. Tun daga ranar ko da yaushe su kan yi waya da shi su duka, don ma su na cikin taro ne ba sa samun sakewa sosai. A ranar da aka ɗaura auren Mimie bayan komawar su masauki, Samar ya kira yaya Sameer a waya su ka gaisa kamar kullum,bayan sun gaisa Sameer ke cewa "Ku na nan lafiya dai koh? Kun koma gida ne ko har yanzu ba ku gama shan bikin sisternku ba?" Ya ƙarashe maganar cikin murmushin yaƙe. Samar ma murmushin ya yi ya ce "Uhmm! Yaya ba mu tafi ba muna Kanon, ai ɗazun nan ma aka ɗaura auren, yanzu haka Mamy sun je Bk don raka Amarya ɗakinta." Ɗif, wuta ta ɗaukewa Sameer, nan take damuwa da tashin hankalin da su ka ɗan ɗaga masa ƙafa na kwana biyu su ka dirar masa, kasa magana ya yi saboda yanayin tashin hankalin da ya ke ciki "Shikenan ta tabbata na rasa ki Mimieta? Ke wani ɓangare ce ta jikina ba zan iya rayuwa baki ba, ko da na rayu to zan rayu ne bisa ga mummunar ƙaddara, kuma rayuwata za ta kasance mara armashi tamkar miyar da ba gishiri." Ya faɗa a ransa. Bai san cewa ashe afili ya faɗa ba sai da ya jiyo sautin Muryar ƙanin nasa cikin damuwa ya na faɗar "Ka yi haƙuri Yayana, komai ya yi zafi maganinsa Allah, mu kanmu muna cikin irin wannan damuwar, ada muna farinciki Mimie ta dawo gare mu a karo na biyu ashe ba haka ba ne, duk wanda ka rasa ta silar mutuwa ka riga ka rasa shi kenan sai dai ka samu makamancinsa..." Ya na kai nan ya ji wani irin kuka ya zo ma sa kawai sai ya katse kiran. Shi kansa Sameer ya shiga wani hali, don haka ya gyara kwanciyarsa akan kujerar da ya ke tare da rumtse idonsa ya na cigaba da karanto *Innalillahi wa inna'ilahir raji'un* a zuciyarsa... ®®®®®®®®®®® Washe gari da misalin ƙarfe goma na safe aka sada Amarya da gidan mijinta. Ango da dama ya gama ƙosawa a kawo masa Amaryarsa ya na jin dirar motarsu ya fito waje. Anan ya samu ya keɓe da Raliya ya haɗa kai da ita domin ta kawo masa Amaryar ɗakinsa ba tare da sanin kowa ba. Haka kuwa aka yi daƙyar ta samu ta yi dabara ta fito da Mimie zuwa ɗakin Bassam, su na shiga ta dawo da baya ta rufo ƙofar ta baya, ta wuce abinta ta na dariya. Da sauri Mimie ta juyo ta na zare ido ta miƙa hannu don buɗe ƙofar amma inah! Ta kasa buɗewa. Jin ƙarar taku a bayanta yasa ta yi saurin juyowa, wa za ta gani?, Uncle ne ke nufo ta da murmushi kwance a fuskarsa sai ƙamshi ya ke zubawa. Ba ta san ya aka yi ba kawai sai ta samu kanta da jin tsoro, fargaba duk ta bi ta ishe ta, ƙirjinta sai lugude ya ke, a ranta ta ke mamakin Raliya ashe wayo ta mata kenan haɗa baki su ka yi don ta kawo ta nan?. Ba ta gama zancen zucinta ba ya ƙara so daf da ita ya na faɗar "Sannu da zuwa kyakkyawar Amaryata, ina miki Barka da shigowa wannan gida mai albarka, gidan da na ke fatar ki tsinci farincikin da za ki rayu da shi har abada." Ja da baya kawai ta ke ta kasa magana ma, yanzun ma shi ne ya yi dariya ya ce "Haba! Ka da ki tsora ta da angonki mana princess, kin san ba zan cutar da ke ba, kawai na yi missing ɗinki da yawa ne shiyasa na kasa haƙuri har jama'a su watse na saka aka kawomin ke nan." Haka dai ya ci gaba da tsokanarta harta ɗan ware ta na murmushi. To da ya ke a yau ne dukkannin su za su juya don haka Mamy ta shiga neman Amarya don su yi sallama ga mamakinta ba Amaryar ba Raliya ƙawarta, anan ta shiga neman dukkansu, can ta hango Raliya a waje ta ce "Ya'ta ina Amaryar ne nemo min ita, kuma ki zo ki shirya yanzu za mu tafi." Da to ta amsa. Ita ce ta je ta dawo da Mimie, su ka yi Sallama sannan su ka juya su ka bar Amarya cike da fargaba har hawaye sai da ta yi, da za su tafi..... Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number 08209634202 Follow me on wattpad @ummu inteesar Ummu inteesar ce❤️❤️❤️❤️❤️❤️ UMMU INTEESAR CE❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤ ️ 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘAMIN RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU-INTEESAR)* MARUBUCIYAR SOYAYYAR MEERAH Y'AR GANTALI RIKICIN MASOYA DA KUMA A SANADIN KAMA WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202 DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE *AREWA WRITERS ASSOCIATION* Page 4️⃣9️⃣↪️5️⃣0️⃣ A haka kowa ya watse aciki kuwa har da su Mama Habeey da su ka kwana uku anan. Aka bar Amarya ita kaɗai sai fatar Allah Ya ba su zaman lafiya. Bayan wata biyu da kai Amarya Mimie ta na zaune a gidanta cikin kwanciyar hankali da jin daɗi damuwarta ɗaya ce ita ce komawar angon nata Kano domin aikinsa, sati uku kawai su ka yi a tare hutun angoncinsa ya ƙare bisa ga dole ya koma Kano ya bar ta a gidan ita kaɗai, sai dai ya kawo mata ƙannensa y'an mata guda biyu Shamsiyya da Sakina domin su taya ta zaman gidan. Bayan tafiyarsa aka fara ɗaukar sabbin ɗalibai a jami'a don haka ta kira shi ta sanar masa, bai yi gardama ba domin kuwa dama can kafin a ba shi ita sai da Daddy ya sanya masa sharadin barin ta ta ƙarasa karatunta kuma ya amince da hakan. Waya su ka yi ita da Daddy ta shaida masa anfara bayar da admission a jami'a, don haka Daddy ya turo mata kuɗi Naira dubu ɗari biyu account nata, ya ce ta saka mijinta ya nema mata makarantar da ta dace da ita sai ta yi amfani da kuɗin gun hidimar makarantar idan sun ƙare ta sanar masa. Godiya ta yi masa sosai, bayan sun gama wayar ne ta nemo layin Bassam ta shaida masa, sosai ya nuna jin daɗinsa tare da yiwa Daddy addu'a. Anan ya sanar mata zai san yanda za'a yi a nema mata admission ɗin duk da baya gari. Waya ya yi da ɗaya daga cikin abokanansa da ke nan Birnin Kebbin ya shaida masa buƙatarsa anan ya ce ba damuwa ya sanar mata ta shirya takardun shi zai yi iya ƙoƙarinsa. Bayan wani ɗan lokaci Al'amin abokin Bassam ya kammala komai, lokacin fara karatu kawai Mimie ke jira. Universityn da ta ke cikin local government na Kalgo anan za ta yi karatun, hakan ba ƙaramin daɗi ya yiwa Bassam ba domin ko bakomai cikin garinsu ne za ta yi karatun, daga nan zuwa gidansu Naira hamsin ne kuɗin Babur, ya san hakan zai sauƙaƙa mata wasu abubuwan. A lokacin da ta cika wata huɗu a gidan ta fara attending school, inda za ta karanci Medicine. Ko da yaushe ta kan je makaranta,yayin da su Shamsiyya su ke zaune a gida, su ne masu yi mata duk wani aikin gidan kafin ta dawo, sai dai ta zo ta tarar an gama girki ci ne kawai nata. Kullum kwanan duniya ta kan yi waya da angonta abun alfaharinta, a rana sai su yi waya sau goma ko ƙasa da hakan, ta na jin daɗinta har ta sakankance cewa ta samu gurin zama na har abada, kuma zaɓintan dai tabbas shi ne alkhairi a gare ta, ragowar fargabar da ta ke ji akan yin aure ba tare da amincewar iyayenta ba duk ta gushe a zuciyarta, ba ta san cewa akwai sauran rina a kaba ba, ba ta san cewa tarin matsaloli da tashin hankali su na gaba ba. ®®®®®®®®®®® Sameer da ya je Dubai da niyyar karatu sai Dubai ta kasance masa gurin jinya, domin tarin damuwa da ɓacin rai da ya ke ciki ya fara haifar masa da matsala a zuci da gangan jiki, mussanman ya nemi likita acan mai kula da lafiyarsa, kullum ciwonsa daɗa yi gaba ya ke, ya kasa samun mafita, ya na so ya manta da ita amma ya kasa. A waɗannan wata huɗun da ya yi duk ya zama abun tausayi, maimakon ya yi kyau, sai ma ya daɗa lalacewa. A ranar da ya ji ya samu sauƙi ya ɗan warware a ranar ya fita domin fara zuwa ɗaukar darasi domin tuni ya kammala duk wani process na makarantar. Khalifa University da ke babban birnin Dubai wato Abu dhabi, ita ce makarantar da ya fara attending domin yin masters ɗinsa a ɓangaren Medicine. A ranar farko da ya fita acan ne ya haɗu da wasu aboka nai su uku biyu y'an Nigeria ɗayan kuma ba indiye ne, daga farko ya ƙi ya kula su, amma a haka suka cigaba da bibiyarsa har zuwa ranar da ya amince musu, ba tare da sanin cewa wata rana za su saka shi yin dana sani mara amfani ba a rayuwa. ®®®®®®®®®® Bangaren Mommy kuwa ta cigaba da cusawa Ruma mummunar aƙidar tsanar Mimie da kuma saka ta bibiyar rayuwar ƴaƴan Alhaji Salman, sai dai ita Ruma ba ta ɗauki ko ɗaya daga cikin wannan akiɗar ba, sai dai a fuska ta ke nunawa Mommy kamar ta amince kuma ta na yin abunda ta saka tan. Ita kuwa Mommy ganin ba cigaba ta wannan ɓangaren ya saka ta je gidan wata aminiyarta Hajiya hafsat, domin ta bata shawaran yanda za ta ɓullowa lamarin, inda hajiyar ta sanar Mata cewa ta na da wani Malama, sai dai ba'a nan ya ke kusa da su ba, idan ta amince za ta kira shi a waya domin asan yanda aka yi aka cusa Soyayyar Ruma a zuciyar ɗaya daga cikin yaran. Da farko kamar ba za ta amince ba, Hajiya hafsat ta dinga mata huɗubar tsiya, da hakan ta yaudare ta har ta amince, ita kuwa ta ɗora ta a keken ɓera. ®®®®®®®®®®® Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number 08109634202 Follow me on wattpad @Ummu inteesar UMMU INTEESAR CE❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)* *MARUBUCIYAR:* *SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* *DA KUMA* *A SANADIN KAMA* WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202 DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE *AREWA WRITERS ASSOCIATION* Page 5️⃣1️⃣↪️5️⃣2️⃣ A haka Mimie ta cigaba da karatunta cikin kwanciyar hankali da nutsuwa, duk da cewa mijinta baya gari amma ba ta da wata matsala ta kuɗi ko makamancin haka, kasancewar Daddynta ya na tura mata kuɗi a account ɗinta duk wata, hakan ya sa ba ta ɗaurawa mijinta lalurar komai, abinci kuwa sai kalar wanda su ke son ci ita da ƙannen mijin nata, yayin da mijinta ke zuwa duk bayan wata biyu ya yi sati biyu ya koma bakin aikinsa. Sosai ta ke jin daɗin zama da ƙannen mijin nata domin su na yi mata biyayya Sosai, kuma su ne ke mata duk wasu aikace-aikacen gida, iyaka ta kwanta ta huta sai karatu su kaɗai ne aikinta acikin gidan, kasancewar Shamsiyya sa'ar ta ce hakan ya yi mata daɗi sosai, tamkar ƙawaye haka ta ɗauke su. Haka zalika idan ta je Kalgo Innarmu sai nan-nan ta ke da ita, ko kuɗa bata son ya hau kan Mimie saboda yanda ta ke nuna mata soyayya da kulawa. Ganin irin wannan ƙaunar da uwar miji da danginta ke nuna mata ya saka ta saki jiki da su ta ke sakar masu Naira, bata jin ƙyashin yi masu komai, tuni ta manta da rashin biyayyar da ta yiwa iyayenta a lokacin auren, ta ɗauka ta ci bilis, kuma bata tunanin akwai wata mummunar ƙaddarar da ke tafe a rayuwarta ta gaba. A ranar da ta cika shekara ɗaya da rabi a gidan miji a ranar ne ta fara fuskantar matsala daga ɓangaren uwar mijinta, domin Innarmu ta fara sauya mata fuska, yanzun bata murna da ganinta ko kaɗan, zancen da Innarmu ta yi mata a ranar shi ya fi komai ɗaga mata hankali. Da yake aranar sun je gidan ita da su Sakina, ta na zaune a ɗakin Innarmu, innar ta shigo ta kalle ta a ɗage ta ce "Wai ni yarinyagga har yanzu baki samu ciki ba? Ko dai wata ƙwaya ki ka sha ta hana haihuwa?" Sunkuyar da kanta ƙasa ta yi gabanta na tsananta faɗuwa ba ta dai ce komai ba. Innarmu ta kuma matsowa tare da zama kusa da ita ta ce "Ki amsa min tambayata." Ƙara sunkuyar da kanta ta yi ɗakyar ta ce "Inna Wallahi ba na shan komai, Allah ne dai bai kawo ba." Ta ƙarshe cikin raunanniyar murya. "To in ma ki na sha ki dakatar, ina so ki sani cewa ɗana Bassam shikenan ni ke da shi ɗa namiji wurina, dan haka ina ɓukatar jininsa a matsayin jikokina kahin in mutu." Ta faɗa cikin yanayin faɗa-faɗa. Jikin Mimie ya yi sanyi laƙwas da ganin yanayin Innarmu A ranta ta ke cewa "Na shiga uku, su waye ke ƙoƙarin shiga tsakani na da sirikata, na san an cusa mata wannan aƙidar ne." Wunin ranar dai kwata-kwata Mimie ba ta ji daɗinsa ba, da yamma ta ja su Shamsiyya su ka koma gida, jikinta ya yi sanyi qlau, damuwa ta fara shigarta nan ta ke ta tuna da iyayenta, aranta ta ce "Allah ya sa ba sakamakon bijirewa iyayena ne na fara gani tun yanzu ba." ®®®®®®®®®®® DUbai Kishingiɗe ya ke akan wata kujera irin waɗannan ake ajiyewa bakin swimming pool. Idonsa sanye da wani makeken baƙin glass ya kafe ruwan da ido, hannunsa riƙe ya ke da wani glass cup ƙarami da alama lemo ne a ciki. A gefensa na dama Wisam ne zaune riƙe da kwalbar barasa ya na kwankwaɗa, a gefen hagu kuwa Zaroon ne zaune Shi ma da kofin barasar a hannunsa, yayin da Rajbir ya ke cikin swimming pool ɗin ya na wanka abinsa. Shi kuwa Sameer zaune kawai ya ke kamar an dasa shi agun, da alama damuwa da tunani sun gama zama jikinsa, domin a yanzun ma baya hayyacinsa ya tsunduma tsulum a kogin tunani, har sambatu ya ke yanzun ma faɗar ya ke "Why Mimie? Meyasa ki ka mun haka? Ga inda kika kawo ni a yanzu, kin yi silar barin mahaifata, Why?, Shin ashe laifi ne don na ƙaunace ki?. Cikin wani irin yanayi mai wuyar fassarawa ya ke furucin. Cikin Muryar y'an maye Wisam ya ce "Haba guy, ni wallahi ka na ba ni kunya, yanzu akan mace ka ke wannan abun? Ga maganin damuwa na baka ka ƙi ka sha, ban san meyasa kaƙi ka waye ba." Zaroon ne ya cafke zancen da cewa "Ka bar shi kawai, tun da baya so sai ya zauna damuwa ta kashe shi, tun da haka ya ke so." Shima cikin Muryar y'an ƙwaya ya yi zancen. Rajbir da ya fito daga cikin ruwa yanzu ya nufo su ya na goge jikinsa, faɗar ya ke "Sam tun daga nesa na hangoka, na san yanzu ma damuwar ce?, karɓi wannan ka sha, ka na sha za ka nemi damuwar ka rasa." Ya faɗa tare da karɓar kwalbar giya a hannun Wisam ya na miƙa masa. Sameer kuwa jin su kawai ya ke domin shi baya tunanin zai iya aikata saɓo irin, wannan bai taɓa shan giya ba, kuma ba ya son ya sha. Tunawa ya yi da hadisin Manzo Sallallahu alaihi wasallam inda ya ke cewa "Kullu muskirun khamrun, wa kullu muskirun haramun." Ma'ana (Duk abinda ke saka maye giya ne, kuma duk abinda ke saka maye haramun ne.) Haka kuma ya tuna ayar da ta yi magana akan haka, nan ta ke ya ji ba zai iya aikata wannan saɓon ba. Kimanin watanni takwas kenan da haɗuwarsa da su Wisam, da farko ya ɗauka yaran arziƙi ne shiyasa ya amince musu, sai bayan ya shaƙu da su sannan ya fahimci halayyar su ta shaye-shaye da neman mata, ga shi ya kasa rabuwa da su amma kuma shi baya aikata ɓarnar da suke yi, kullum ya na neman tsari a gurin mahaliccinsa daga sharrin su. Rajbir ne ya dawo da shi daga tunanin ya na miƙa masa kwalbar giyar, karɓa ya yi ya ajiye a gefe. A haka su ka cigaba da masa huɗubar tsiya, su na nuna masa ya sha ko sau ɗaya domin maganin damuwarsa. Cikin rashin Sa'a su ka yi nasarar cafko zuciyar Sameer tare da karkato da shi zuwa gurɓatacciyar hanya. Nan ta ke ya manta da hadisin da ya tuna ɗazu ya karɓi kwalbar ya ɗaga ya kwankwaɗa sai da ya ku san shinye ta sannan ya ajiye. Wani shu'umin murmushi su ka yi dukkansu, murmushin mai nuni da alamun cin nasara. "Ko kaifa?" Yanzu ya ka ke ji?" Su ka haɗa baki gun tambaya. Ganin ya yi mankas abunka da sabon shiga kawai sai suka janye shi zuwa ɗakinsa, suka kwantar dashi. ®®®®®®®®®®® Ita kuwa Mommy bisa ga huɗubar ƙawarta ta saka a ka kira mata Malam a waya, ya haɗa masu maganin sanya soyayya a zuci, Hajiya hafsat da kanta ta je har ƙauyen da ya ke ta karɓo tare da zabge masa kuɗin aikinsa ta juyo. Daga can kai tsaye gidan Mommy ta wuce ta kai mata, ta yi mata bayanin yanda za'a yi amfani da shi. "Danƙare maƙari! To yanzu ni khadija ina ma za mu ga abincin ɗayansu bare a saka masa har ya ci?, Duk da wanda na so yin aikin akansa ya bar ƙasar, amma sai a juya ga ƙaninsa ai duk ɗaya ne." Mommy ta faɗa yayinda ta ke karɓar kullin maganin. "Ke kika san yanda za ki yi, har a samu ya ci, amma ya na ci angama magana." Hajiya hafsat ta mayar mata da amsa. Dogon numfashi Mommy ta ja ta ce "Wannan ja'irar yarinyar na san ko na saka ta ba za ta aikata ba, amma bari zan nemo mafita, yanzu zuwa yaushe ya kamata ya ci maganin?" Da haka su ka cigaba da tattaunawarsu har zuwa lokacin da Hajiya hafsat ta bar gidan. ®®®®®®®®®® Zuwa wannan lokacin damuwa ta fara yiwa Mimie yawa ganin su ma su Shamsiyya sun fara juya mata baya, yanzu iskanci su ke mata iri-iri, sai ta je makaranta ta dawo ta tarar ba abinci kuma ba su gyara gidan ba, idan ta tambaya sai su ce ba su dafa da ita ba, iya cikinsu su ka yi, aiki kuma ba za su yi ba, domin ba bayi aka kawo mata ba, a haka za ta yi haƙuri ta yi aikin dole, idan ta na son ganin gidanta tsaf. Duk wannan abin da ake Bassam bai sani ba ya na Kano zaune abinsa, sai dai idan su na waya ya na yawan tambayarta ko lafiya ya ji Muryarta tamkar tana cikin damuwa, sai ta ce ba komai kawai yanayin karatun na su ne, ko ta ce gajiya ce. Anan cikin haka ya shirya ya zo hutu gida inda ya tarad da ita cikin damuwa sosai, juyin duniyar nan ya yi ta ƙi gaya masa akan dole ya haƙura. Dama da ya shigo garin su Sakina ke komawa gida sai zai tafi su dawo da yake su zauna gari banza ne, daƙyar Shamsiyya ta gama Secondary, Sakina kuwa tun ta yi jlce ta ƙi komawa makaranta wai ba za ta iya wahalar boko ba, da ya ke innar tasu ma ba wani wadataccen ilimi ne da ita ba sai ta ƙyale ta. A yan kwanakin hutunsan nan ta na cikin jindaɗi da nishaɗi domin ya na ƙoƙarin faranta mata. Ya na zaune a ɗakin matarsa aka kira shi daga Kano aka shaida masa cewar Shagonsa na kasuwar Rimi inda ya ke siyar da takalmi da jakunkuna ya yi gobara komai ba a tsira da shi ba. (Da ya ke ya na taɓa kasuwanci tun lokacin da ya ke karatu a Kano, abokin babansa da ya ke zaune a gidansa ya saka shi a cikin kasuwancinsa, zuwa yanzu yana da shaguna biyu ɗaya a Rimi ɗaya a kwari, sai dai ya zuba yara ne aciki tunda shi yana aiki a nepa.) "Innalillahi wa inna'ilahir raji'un!" Ita ce kalmar da ya ke ta maimaitawa, anan ta ke tambayarsa lafiya ya shaida mata abunda ke faruwa, ta ji matuƙar ba daɗi na wannan hasarar da mijinta ya tafka. Ko da ya je gida ya sanarwa Innarmu maimakon ta jajanta masa sai cewa ta yi "Ai ga irinta nan, ka tai ka kwaso ma kanka mai hwarar ƙahwa, da alama kuma juya ta, dan tun da ta shigo gidanka hay-yanzu ko ɓari ba ta taɓa yi ba, bayan nan kuma ga hasarori an hwara tafkawa." Cikin yanayin faɗa take zancen. Bassam ne ya ce "Haba Innarmu, ba laifin ta ba ne fa, ƙaddara ce, kuma ni na yi imani da ita, kuma maganar haihuwa da kike, ai ita kanta haihuwar nufin Allah ce idan ya ƙaddara zan......" "Kai ruhemin baki, shashashan banza." Innarmu ta katse mi shi zancen ta ɗora da cewa "Ita ta san ƙwayar da tassha ta hana ɗaukar ciki dan ta yi karatunta hankali kwance, mu mun san tciyar y'an boko." Ganin abin na shiri hakan zame masa ɗan zane ya saka ya fice daga gidan rai a jagule... Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number 08109634202 Follow me on wattpad @Ummu inteesar UMMU INTEESAR CE❤️❤️❤️❤️❤️ 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)* *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* DA KUMA *A SANADIN KAMA* WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202 DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE *AREWA WRITERS ASSOCIATION* ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Page 5️⃣3️⃣↪️5️⃣4️⃣ Wata rana Zinnira ta shirya daga gidansu ta zo gidan Bassam domin sun yi waya da su Shamsiyya su ka shaida mata suna nan. Da yamma liƙis ta zo gidan a lokacin Bassam ya na nan, wai zo ku ga iyayi agun Zinnira, sai wani yauƙi ta ke. Dama can tun bata kai girman haka ba Allah ya jarafce ta da son ɗan yayar mahaifinta wato Bassam, ta na jarabar son sa, har kowa ya shaida hakan a familynsu, amma shi Bassam kwata-kwata baya nuna ma ya san me ta ke. Da ta juya sun haɗa ido da Mimie sai ta zabga mata harara,shi kuwa idan ta juya garesa sai ta yi masa murmushi. A haka ta ƙaraci iyayinta da habaici da hare-harenta, bayan magariba ta tattara ta koma gidansu da ya ke cikin garin, bayan ta ƙara yiwa su Sakina huɗubar tsiya akan su cusgunawa matar yayan nasu a lokacin da baya gari. Bayan kwana biyu ya na shirye-shiryen komawa Kano Innarmu ta kira shi zuwa gida, da ya je ne ta ke ce masa "Dama ba komi yassa nikkiraka ba, sai dan wata magana mai muhimmanci da muka son mu yi." Gyara zamansa ya yi akan ledar ƙasa dake shimfiɗe a ɗakin ya na sauraronta. Innarmu ta cigaba da cewa "Dama na ga kana yawan tahiye-tahiye ka na barin matarka can binni gashi babu kowa kusa da ita, sai su Shamsiyya, ga shi duk su na taron zani-zaka, ƙurciya na cin su, kuma nan an banni shiru, shina nicce me zai hana ka maida Matakka gidan ga?, in yasso gidanka na binni sai ka sa y'an haya, ka ga dannan ma ya hi mata sauƙin zuwa makaranta." Gyara zama ya yi ya na cewa "Amma Innarmu, miye amfanin gidan da na ke da shi kenan, idan iyalina ba za ta zauna ciki ba?, Kuma nan na ga ya matse ba wani ɗaki da za ta iya zama aciki, ku kanku bai wadace ku ba." Cikin tsawa Innarmu ta ce "Kama min bakinka, ba ga wancan tsohon ɗakin na babanku ba, tunda yarrasu ɗakin ya ke ruhe, sai a buɗe shi ka ƙara gyarawa kasa Matakka ciki." Da mamaki a fuskarsa ya ɗago ya na cewa "Amma Innarmu ɗakin fa ƙarami ne kuma....." Bai samu damar ƙarasawa ba saboda tsawar da ta daka masa ta ce "Ka ga ɗan nema mai shegiyar gardamar tciya? To tashi ka ban wuri hukunci na riga na yanke kahin ka wuce Kano za ta dawo nan umurni ne ba shawara ba, ya rage naka ka bi ko akasin haka." Ta na gama faɗa ta miƙe ta shige uwar ɗakanta ta bar shi a gun sake da baki. Shima miƙewa ya yi cike da damuwa ya bar ɗakin, a ransa ya ke mamakin me Innarmu ta ke nufi da hakan? Da farko ta tursasa shi zama birnin Kebbi, yanzu kuma ta na yunƙurin nuna ƙarfin ikonta ta hanyar tursasa shi zama gidan family abinda baya burge shi kwata-kwata. Jiki a saɓule ya bar gidan. ®®®®®®®®®®® Dubai Bayan farkawar Sameer daga bugaggen barcin da ya yi sakamakon kwankwaɗar barasa, ko da ya farka ya dawo hayyacinsa, da ya tuna abinda ya faru kawai sai ya fashe da kukan nadama. Ya yi kuka sosai tare da Allah wadai da halin su Wisam shi kam tarayya da su bata amfane sa da komai ba, sai jefa shi a halaka da ta yi. Ya na cikin wannan halin ne Rajbir ya shigo ɗakin, ganin ya farka kuma ya na kuka ya saka ya buɗe shi, cikin harshen turanci ya ke cewa "A'ah! Mutumin ka farka ne? Me ya faru ka ke kuka?" Cikin zafin rai da ɗaga murya Sameer ya mayar masa da amsa da yaren da su ke amfani da shi idan za su yi magana da juna wato turanci ya ce "Bansaniba, tambayar me kake bayan kuka jefa ni a cikin wannan halin na saɓawa mahaliccina?" "Oh sam! Wannan fa ba damuwa ba ce shan barasa ai ba laifi bane.." Dakatar dashi Sam ya yi ta hanyar ɗaga masa hannu ya ce "A addininka hakan ba laifi ba ne, amma a addinina wannan haramun ne, kun cuce ni, daga yanzu na daina yarda da ku, don Allah ku fita rayuwata ku koma masaukinku." Ya na gama faɗa ya miƙe ya shige toilet ya bar Rajbir nan sake da baki. Tun daga ranar ya fara share su, ba yanda bai yi su bar masa gidansa ba su ka ƙi, a haka suka lallaɓa shi har su ka shawo kansa ya kuma faɗawa tarkonsu a karo na biyu, tun daga lokacin ya afka cikin baƙin tarkonsu daga lokacin rayuwarsa ta zama ta mashaya,har ta kai da ya fara tunanin Mimie ya ke buɗe bakin kwalba ya tuttula, a haka rayuwarsa ta gurɓace duk silar soyayyar Mimie da ke cunkushe a zuciyarsa. Har zuwa lokacin kuma ya kasa manta ta ko da ya sha giyar. ®®®®®®®®®®® Ɓangaren Mommy kuwa ta samu nasarar saka maganin a cikin abincin Saheen ta hanyar Nafisa mai kula da gyaran ɗakinsa, da duk wani abu da ya shafe shi. Hakan kuwa ta faru ne a lokacin da Mommy ta je gidan Alhaji Salman, kamar yanda ta saba, domin ta mayar da gidan tamkar gidansu. A lokacin ne ta samu keɓewa da Nafisa su ka haɗa kai, ta bata maganin tare da kuɗi dubu goma ladan aikinta, ita kuwa saboda kwaɗayi ta karɓa ta tafi. Mommy ba ta bar gidan ba sai da ta tabbatar an saka masa a abinci ya ci. Tun daga ranar Saheen ya susuce yake jin kansa cikin wani irin yanayi shauƙin soyayya na fizgarsa, shi da kansa ya saka Direbansu ya kai shi gidan su Ruma ba tare da sanin kowa ba, ya je ya furta ya na son ta, da ya ga kamar bata so har kuka ya saka mata. ®®®®®®®®®®® Bassam ya samu Mimie ya gaya mata hukuncin da mahaifiyarsa ta yanke, jikinta ya yi san yi laƙwas amma bata nuna ba, a haka ta nuna tsantsan farin cikinta, bayan kwana biyu su ka yi parking duk wani abu nasu, su ka koma gidan Innarmu da zama. Washe garin ranar da suka tare gidan, Bassam ya juya zuwa Kano yayin da ya bar matarsa cikin damuwa da zullumi, haƙiƙa ta na hangowa kanta matsala a zaman gidan saboda yanda mutan gidan su ka fara juya mata baya... Ga mai buƙata ya tuntuɓeni ta wannan number 08109634202 Follow me on wattpad @ummu inteesar UMMU INTEESAR CE❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️ 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)* *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* DA KUMA *A SANADIN KAMA* WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202 DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE *AREWA WRITERS ASSOCIATION* ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Page5️⃣5️⃣↪️5️⃣6️⃣ A haka ta cigaba da haƙuri halayyar mutan gidan da suke cusgunawa rayuwarta a duk kwana duniya,aciki kuwa har da su Sakina da suka manta da tarin Alkhairanta a gare su suka rufe ido suna mata tijara iri-iri. Damuwa ta taru ta mata yawa ga shi ɗakin da ta tare ƙarami ne, daƙyar uwar ɗakan ta ɗauki gado da walldrop ɗin ta,sai madubi shima daƙyar ya samu mazauni a ɗakin, ɗan filin tsakar ɗakin da ya rage bai wuce inda mutum sai saka Sallaya ya yi Sallah ba, ga shi ba toilet a ciki. Falon kuwa saboda matsatsinsa daƙyar kujeru ƙwaya uku suka zauna a ciki, sai ƙaramin showglass ɗinta, ɗan filin da ya rage ba zai ishi kwanciyar mutum biyu ba, dole aka bar sauran kayan nata acan wancan gidan da suka taso, haƙiƙa ta na cikin ƙunci sai a lokacin ne ta tuna da auren bada yardar iyayenta aka yi ba, shima wanda ya mata auren don ba yanda ya iya ne, amma ta san ba don ya na so ba. Kusan ko da yaushe ta na waya da su Mama,yaya Farida da su yaya Kabir da matansu, Baba ne dai idan ta kira sai ya ga dama ya ke ɗagawa, nan ma da sun gaisa ya ke kashe wayar bai damu da tambayar lafiyarta ko yaya zaman su ita da mijin nata ba, don har zuwa lokacin ya na jin zafin abinda ta masa, ga wata mahaukaciyar kunyar Alhaji Salman da ya ke ji tun lokacin da abun ya faru, Mama ce ma ta ɗan sauko ba laifi tun da ita ta na tambayar lafiyarsu kuma ta sake su yi hira. Haka ma ta na waya da su Daddy Mamie, da su yaya Saheen, watarana su na waya da Daddy ta ke tambayarsa "Daddy wai ni kuwa yaya Sameer fa? Shiru ake jinsa ya shige Dubai ya manta da y'ar ƙanwarsa." Ta ƙarashe da sigar zolaya. Dariya Daddy ya yi ya ce "Cab! Wai kina nufin bai kira ya taya ki murnar aurenki ba? Na fa tura masa number na ce ya kira ku gaisa." Shiru ta yi ta na tuna lokacin da suka yi waya da shi ta ƙarshe da irin maganganun da ta gasa masa a lokacin da idonta ya rufe da Soyayyar Bassam, "Tab! Ta ya ma zai kira ni bayan duk wannan abun da na masa?" Ta faɗa a ranta. Tunawa da ta yi ashe ta na kan waya ne ya sa ts kirkiro murmushi ta ce "Ai kuwa Daddy bai kira ba, ina ga mantawa ya yi turon numbersa na kira shi." Ta faɗa cikin dakiya don ba ta so ya fahimci canjin yanayi daga gare ta. "Ohk, bye sai anjima, ina da wani aikin da zan yi." Daga haka ya katse wayar, ko ɗagawa bata yi daga gun ba, saƙonsa ya shigo wayarta. Nan take ta danna masa kira jiki a saɓule, ta na ji wayar na ring amma bai ɗaga ba sai da ta kuma kira da ya ke can ƙasar har dare ya fara. Shigowa lokacin ya na zaune a falonsa cikin yanayin damuwa da tunaninta, ko yaya ya rufe idonsa hotonta ya ke gani, lokacin bai jima da gama sallar isha'i ba, ya zauna agun cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa. Ƙarar wayarsa da ke kusa da shi ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya shiga, ganin new number ne ya saka ya ƙi ɗagawa, sai ga wani kiran ya shigo, lura da ya yi cewa in bai ɗaga ba ba za'a daina kira ba, ga shi kuma number Nigeria ce da alama wani ne daga familynsa hakan ya saka ya ɗaga tare da karawa a kunne. "Assalamu alaikum." Ta faɗa cikin sanyayyiyar muryarta mai rikita tunani. Shi kuwa Sameer wata irin super ya yi ya miƙe tsaye tare da ƙara kallon sensor na wayar, tabbas ko ba'a faɗa masa ba, ya san Mimiensa ce ke magana domin ba zai taɓa manta muryarta ba, tunda kullum ya kan ji a mafarki. Mai da wayar kan kunnensa ya yi ya na faɗar "Baby da gaske kece,Sweet sis, anyah! Ba mafarki na ke ba." Ya faɗa cikin wani rikitaccen yanayi. Mamaki ne ya cika ta "Ashe ya gane ni? Taya ya yi saurin gano ni haka? Wannan na nufin bai manta da ni ba kenan?" Muryarsa ta dawo da ita daga tunani inda ya ke cewa "Baby ko ba ke bace? ko abinda na saba ji a kunnena ne yau ya zo min a kiran waya? Lallai na fara zaucewa." Ya faɗa cikin rawar murya. Jin haka yasa ta tattaro duk wata nutsuwarta, daƙyar ta haɗo kalmomi ta ce "Ni ce yaya Sameer, Mimienku ce, ya kake? Ya karatu? Da fatar kana nan lafiya." Cikin mutuwar jiki ta ke zance domin a kunyace take, saboda ba ta manta irin cin kashin da ta masa ba, a lokacin da yake neman aurenta. Komawa ya yi ragwaf ya zauna kan kujerar ya na faɗar "Sweety ba lafiya ba, ina nan ciwon son ki ya murƙushe ni, ba ni da aiki sai tunaninki, ba na iya karatun da ya kawo ni, Dubai ta kasance mun gurin jinya a maimakon gurin karatu, na shiga wani mugun yanayi Baby, na sani yanzu ki na can zaune ɗakinki cikin farinciki yayin da na ke cikin damuwa, idan ba ki manta ba a baya na gaya miki muddin ba ki aure ni ba tabbas zan iya rasa raina ko na rasa hankalina, to hakance ta faru ina daf da rasa hankalina Baby ki taimake ni..." Daga haka ya fashe da kuka cikin wani yanayi mai ban tausayi. Hakan ya kashe mata jiki sosai, lura da ta yi cewa idan ta cigaba da saurararsa tabbas su na daf da faɗawa halaka musamman shi, hakan ya sa ta fashe da kukan tausayinsa tare da kashe wayar ta ajiye. Cigaba da kukanta ta yi, a zuciyarta ta ke cewa "Shin yaya Sameer ya manta cewa ni matar aure ce ya ke faɗar waɗannan kalaman." Nan ta ke ta ji ta yi nadamar biyewa son zuciyarta, ga shi ta saka wannan bawan Allahn cikin tashin hankali da ɗimaucewa. "Kaicona ni Zuhra, Daddy baka cancanci wannan sakayar daga gare ni ba, yaya Sameer ku yafe min." Ta faɗa ta na cigaba da kukanta. ®®®®®®®®®® Sameer kuwa jin ta na kuka ya saka shi gigicewa faɗar "Ya ke Baby kuka ki ke?" Jin ta yanke kiran ya saka shi fara neman layinta hankali a tashe ya na kuka. Kusan sau biyar ya na kira amma bata ɗaga ba, hakan ya saka shi faɗuwa a ƙasa ya na cigaba da kuka ya na sambatun kiran "Sweety meyasa ki ka mun haka? Me na rasa da ki ka ƙi ni? Me wanda kika aura yafi ni da shi?" Wisam da Zaroon da su ke zaune a falon kowannen su ya na rungume da budurwarsa, kallonsa su ke cike da tausayawa. Wisam ne ya tashi, ya je gabansa ya fara rarrashinsa faɗar ya ke "Haba Sam! Me ye haka? Ka zama namiji mana, akan mace ne ka ke wannan kukan? Ka da ka ba ni kunya mana." Maliha budurwar Wisam ce ta ce "Haba my love, ka tausaya masa mana, shi kaɗai ya san me ya ke ji a zuciyarsa, ina ga kamar ba ka gama fahimtar miye so ba." Zaroon ne ya taso shima ya ƙarasa wurin su ka tayar da shi zaune, Zaroon ya dubi budurwarsa ya ce "Janan ba ni kwalbar barasar nan." Ɗaukowa ta yi ta na kwarkwasa ta iso gun ta miƙa masa. Buɗe bakin kwalbar ya yi ya miƙawa Sameer ya na faɗar "Karɓi wannan Sam, ga maganinka ka na sha shikenan." Ai kuwa ba musu ya karɓa ya kwankwaɗa tare da komawa ya lafe jikin kujera ya na cigaba da sambatun kiran sunan Mimie. ®®®®®®®®® Saheen kuwa ya gama susucewa kullum ya na gidan Mommy maƙale, abin har ya fara bawa Ruma tsoro, "Anyah! Mommy ba wani abun ta aikatawa Saheen ba kuwa?" Wannan tambayar ce ta faɗo ranta. Ras ƙirjinta ya buga da ƙarfi "in kuwa hakane tabbas Mommy ta cika mai son zuciya." Haka Saheen ya ke yiwa Mommy ɓarin kuɗi, ita kuwa Ruma tausayinsa ne ya saka ta fara kula shi. Farincikin Mommy kasa ɓoyuwa ya yi har sai da ta kira ƙawarta Hajiya hafsat ta shaida mata magani ya ci, su ka yi ta murna anan ta ke labarta mata irin barin naira da Saheen ke mata da ɗan abin hannunsa, kafin ta shiga dukiyar Mahaifinsa. ®®®®®®®®® A haka lokaci ya cigaba da ja, a wani zuwa da Bassam ya yi gida anan ne komai ya ƙara rikicewa Mimie, domin bayan komawarsa Kano ya tafka hasarori waɗanda ba sa faɗuwa duk ya fara tsiyacewa motar da ya ke hawa ma ya na gaf da zuwa gida aka sace ta. Da dawowarsa gida ya sami matarsa da zancen ta taimaka masa da kuɗi ya ja jari koda aro ne ya na so ta ba shi, ita kuwa saboda tausayin mijinta ta ba shi dama anan ta ke cewa "Uncle ai dukiyata taka ce, da ni da duk abinda na mallaka mallakinka ne, ka yi yanda ka ga ya dace." Ai kuwa ya yi farin ciki sosai, da wannan damar ya yi amfani ya je ya siyar da tarin kayanta da su ke a can gidansa ajiye ya karɓi kuɗi da zimmar ya na komawa Kano zai siyo wa su kayan a fara kasuwanci. Tun dawowar su gidan nauyi ya dawo kansu, domin duk wani cefane na gidan shi ke yi tun da babansu baya raye, matarsa kuwa ta kasance ita ke yin duk wani girkin da za'a ci agidan, sai dai idan ta gama ta kai masu na su, sauran kuma ta ci ita da mijinta. Duk wannan abin da ake bata sanar da kowa ba ta yi haƙuri ta jure, sai da ta ga abun ya fara yawa ne ta sanar da Mama ta na kuka tare da neman addu'ar ta da yafiyar ta. A wannan dawowar da ya yi ne kuma Zinnira ta zo ta tare a gidan, nan fa abubuwa suka ƙara caɓewa Mimie, domin baƙar magana da habaici kam kullum sai ta sha shi, kasancewar Zinnirar na matuƙar son Bassam tun kafin ya yi aure, shi ne bai ba ta fuska ba. Ana haka ne ta nemi izinin zuwa ganin gida daga can kuma ta na so ta wuce Abuja gun Mommy da kuma gidan Daddy, ba musu mijin nata ya amince mata, amma ita kaɗai za ta tafi kasancewar bai jima da zuwa ganin gidan ba lokacin komawar sa bai yi ba, dama can sun samu hutun makaranta. Da haka su ka yi sallama ta wuce Kano satin ta ɗaya anan ta wuce Abuja gidan Daddy ta sauka domin tunawa da ta yi cewa yanzu bata da gurbi a zuciyar Mommy, amma a ranar ba ta kwana ba sai da ta je gidan Mommy ta kwana biyu, a can ne ta ga irin susucewar da Saheen ya yi akan Ruma. Ta yi murna sosai da wannan haɗin, acewar ta idan ba ta auri yaya Sameer ba ga yar uwar ta za ta auri yaya Saheen ta san wannan haɗin zai rage ma su damuwar da ta jefa zuciyoyinsu aciki. A daddafe ta kwana biyu gidan saboda hantarar da ta ga Mommy na yi mata. ®®®®®®®®® Rashin sani ya fi dare duhu, da Mimie ta san cewa wannan tafiyar tata za ta bawa maƙiya damar shiga tsakaninta da mijinta tabbas da ba ta yi ba. Domin a lokacin da ta bar shi gida ne, Zinnira ta je gida ta karɓo magani hannun Mamanta wanda su ka karɓo gurin boka na karkato da hankalinsa zuwa gare ta ta kawowa Innarmu, su ka saka masa acikin abincin da ya fi so wato dambun hatsi aka basa ya ci, tun daga ranar ya fara mantawa da al'amarin matar tasa, kuma ya fara jin sabon al'amari game da y'ar uwar tasa...... Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number 08109634202 Follow me on wattpad @ummu inteesar UMMU INTEESAR CE❤️❤️❤️❤️❤️❤️ 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)* *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* DA KUMA *A SANADIN KAMA* WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202 DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE *AREWA WRITERS ASSOCIATION* ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHI RAHMANIR-RAHIM* Page 5️⃣7️⃣↪️5️⃣8️⃣ Tun ta na Abuja ta fuskanci sauyi daga mijinta, domin ada kullum sai su yi waya sama da uku, amma a y'an kwanakin da ta yi a garin sai a kwana a yini bai kira ta ba, sai ita ce ta ke kiransa, nan ma suna gaisawa sai nemo wani uzurin ya faɗa mata, a kan dole take ƙyale shi. Bayan da Mamy bata yi ba don ta gaya mata damuwarta amma ta kafe a kan cewa ba komai, a haka ta ƙaraci zamanta a Abuja ta juyo zuwa birnin Kebbi. Ba ta ƙara shiga tashin hankali ba sai da ya zo ganin gida ta ga ya daina kula ta kamar da, sai ma wulaƙanci da ya ke mata, bashida wani lokaci ta sai na y'an uwansa. A gabanta zai je ya kira Zinnira su zauna a falonta su na hirarsu su na dariya. Hakan ba ƙaramin daɗi ya ke yiwa Zinnira ba, anan ne ta ke samun damar gasawa Mimie magana cikin ruwan sanyi, kuma a gabanta ta ke kanainaye shi da kalaman soyayya. Ba yanda ta iya dai dai idan abin ya dame ta ta shige ɗaki ta yi ta kuka har ta gode Allah, ta rasa wa za ta tunkara da matsalarta, a duniya bata da waɗanda su ka wuce su Baba,Mama,Daddy da kuma Mamy amma kuma rashin kunyar ta ba ta yi ƙwarin da za ta iya fuskantar ɗayan su da damuwarta ba, yaya Farida ce ta faɗo mata a rai, aikuwa ta kira ta tana kuka ta zayyane mata komai. Rarrashinta ya shiga yi kafin daga bisa ni ta ce "Komai ya faru dake ke ki ka ja Mimie, da kin karɓi zaɓin mahaifanki ina da yaƙinin da baki shiga wannan tashin hankalin ba, amma ba damuwa zan dinga taya ki da addu'a, ke dai abinda na ke so dake ki ci gaba da haƙuri kuma ki nemi yafiyar iyayenki akan saɓa musu da kika yi." A haka suka cigaba da tattauna matsalar ta na bata shawarori har tsawon wani lokaci kafin su katse kiran. ®®®®®®®®®® Bayan kamar rabin shekara da tarewar ta gidan abubuwan su ka ƙara tsananta a gare ta domin yanzu Uncle har zagin ta ya ke tas, kuma baya ganin laifin y'an uwansa akan duk wulaƙanci da suke mata. A bangaren Sameer ma ya na can cikin wani mawuyacin hali mai wuyar fassarawa, kuma ya ci gaba da shaye-shayensa ba tare da sanin iyayensa ba, Allah dai ya kare duk abinda ya ke baya neman matan banza. DAWOWA DAGA LABARI Bayan komawar Innarmu ɗakinta, ya ci gaba da rarrashin matarsa har ta ware, to kun san tsakanin mata da miji sai Allah, nan da nan ta sauko su ka dawo kamar ba abunda ya faru. Da ya ga hankalinta ya kwanta ne ya shirya ya fita, ya bar ta anan ta na tunanin rayuwar da ta tsinci kanta a ciki. Ita yanzu ga baki ɗaya auren ya fice a ranta, ba wai don ba ta son mijinta ba sai don damuwar da take ciki, tunawa da ta yi cewa aure ibada ne kuma zaman bautar Allah take da neman aljannarta a gidan, hakan ya sa ta haƙura ta cigaba da daurewa. Idan ta je makaranta ne ma take samun sassauci domin a can ne za ta haɗu da course mate ɗinta ai ta taɗi ana dariya, amma tana dawowa gida shi kenan ƙuncinta zai dawo. Akwai wata course mate ɗinta (Samiha) da suka shaƙu sosai ita ce ta lura da yanayin damuwar da ƙawar tata ke ciki, ta taya ta jimami kuma ta ba ta shawarwari gwargwadon yanda za ta iya, haka ta cigaba da takatsan-tsan a zaman gidan don ma tana da juriya sosai. ®®®®®®®®®® Lokaci ya sha kwanaki sun shuɗe bayan shekaru biyu, zaune take a ɗakinta abin duniya ya dame ta gorin haihuwa kawai ake mata, Innarmu faɗar ta ke Mimie ta ƙi yarda ta haihu ne saboda karatunta da yabawa muhimmanci akan komai. A haka ta duƙufa da addu'a kullum dare ta na kai kukanta a gurin mahaliccin bayi ta na neman sassauci da mafita a gunsa. Kallo ɗaya za ka mata ka ɗauke kai domin duk ta ya mutse ta lalace abinka da zaman ƙauye ga kuma uban aiki da take sha ba hutu. A shekarar da ta gabata Mamy da Daddy sun zo don duba lafiyar y'arsu, yanda su ka same ta ba ƙaramin ɗaga musu hankali ya yi ba, a haka su ka koma su ka bar ta a gidan mijinta don ba yanda za su yi, amma Mamy ta sha kuka, ko da suka koma Abuja ma hankalinta bai kwanta ba, saboda haka ta duƙufa da yiwa Mimie addu'a, domin ta na jin soyayyar yarinyar har cikin jininta. Shima Daddy ya saka malam ana ta yiwa Mimiensa addu'a da roƙon Allah a kan ya kawo mata sauƙi a cikin rayuwarta, domin duk da ba ta faɗa masu komai ba, a yanayin da suka ganta ma ya isa shaidar cewa ta na cikin tasku. ®®®®™™™ Bayan dawowarsu daga Birnin Kebbi ne Daddy da Mamy suka shirya don zuwa dubo Sameer, saboda tun lokacin da ya tafi hankalinsa Daddy ya ƙi kwanciya, ga shi har ya gama masters ɗinsa shekara uku amma ya ƙi ya dawo gida sai ya cigaba da zamansa a Dubai, inda Daddy ya yi-ya yi ya faɗa masa dalilin hakan amma ya ƙi sai cewa da ya yi, ya ji daɗin zaman ƙasar ne shiyasa. Wannan dalilin yasa suka shirya yi masa zuwan bazata, dama already sun san ya na Abu-Dhabi kuma sun san address ɗin gidan don haka su na sauka kai tsaye suka wuce can ba tare da saninsa ba. Abin da su ka tarar ya matuƙar ɗaga masu hankali, wani irin shork ne ya kama su to yaushe rayuwar ɗan na su ta gurɓace haka ba su sani ba? Ƙarasawa su ka yi cikin falon kai tsaye, idanun Daddy su ka ƙanƙance, cike da masifa ya dubi su Zaroon da ke zaune rungume da y'an matansu su na aikata masha'arsu tare da shan barasa, ya daka masu tsawa tare da Faɗar "Get out from here nonsenses." Su kuwa kamar ba da su ya ke magana ba don ko kallonsa ba sa yi, abinda su ka saka agaba kawai suke yi. Ran Rajbir ne ya yi mugun ɓaci ya buɗi bakinsa ya ce "Who Are you?, Kai wanene da za ka zo ka na yiwa mutane shouting aka?" Sameer da ke gefe riƙe da kwalbar barasa ya na sha, shi ne ya taso ya na layi irin na y'an maye ya ce "Your highly welcome my Dad, Mamy i miss You alot." Cikin Muryar mashaya ya ke zancen har ya ƙara so gun su, Daddy ne ya kife shi da wani wawwan mari, luuu ya yi ya faɗa jikin Mamy sharaf, ya na mashalo Mamy kuwa sai hawaye take wani na korar wani, tsananin tausayin ɗan nata ne ke ratsa ta, a haka ta riƙe shi gam! Sai hawaye ya ke. Daddyn ne ya juya ya fatattaki su Rajbir da y'an matansu su ka bar gidan ya na ja masu Allah ya isa tare da yi masu gargaɗi akan kada su sake shiga rayuwar ɗansa. A buge su ka bar gidan ba arziƙi, ya juyo ga Sameer ya ce "....... Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number 08109634202 Follow me on wattpad@ummu inteesar UMMU INTEESAR CE❤️❤️❤️❤️❤️❤️ 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)* *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* DA KUMA *A SANADIN KAMA* WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202 DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE *AREWA WRITERS ASSOCIATION* ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Page 5️⃣9️⃣↪️6️⃣0️⃣ Ya ce "Sameer yaushe ka lalace haka?, Wannan ita ce tarbiyyar da muka baka? Ka ban kunya Sameer! Ka ban kunya!!" Ya na gama faɗa ya zauna shirim kan kujerar falon ya na share gumi da handkerchief ɗin da ya ciro a aljihunsa, sai maimaita kalmar "Innalillahi wa inna'ilaihir raji'un ya ke." Mamy kuwa ƙara rungume ɗan nata ta yi sosai a jikinta tare da neman guri ta zauna shima ta zaunar da shi, ta saka hannunta ta na share ƙwallar dake idonta. Shiru ya ratsa na ɗan lokaci baka jin komai sai sanyin a.c haɗe da warin giya dake tashi a ɗakin. Can Sameer ya zabura da ƙarfi ya miƙe ya na dube-dube har ya kai ƙofar falon ya leƙa waje, sannan ya dawo ya na tangaɗi cikin Muryar maye ya ce "Mamy ina ku ka baro mun ita? Ta ƙi ta shigo ciki, ki ce ta shigo in gan ta ko na ji sauƙi." Shiru ba wanda ya tamkasa duk sun yi jugum-jugum dasu. Dawowa ya yi kusa da Mamyn ya zauna ya na kuka kamar wani ƙaramin yaro, acikin kukan ya ke cewa "Mamy ku gayawa y'arku Allah ina son ta, idan ban aure ta ba zan iya mut..tuwa ma, kawai ku aura min ita zan daina abunda nake na rantse." Ya na gama zancen ya langaɓar dakai kan cinyar Mamynsa, kai daga ganin yanayinsa ba sai anga yama a buge yake ba. Daddy ne ya miƙe ya je pridge ya ɗauko gwangwani madara ya hude, ɗaga bakin Sameer ɗin ya yi ya tsiyaye masa, ba musu ya shanye ta tas. Shanyewarsa ke da wuya barci ya yi awon gaba da shi. Ɗora shi suka yi akan three-sitter sa'annan suka gyara masa kwanciyarsa, Mamy ta miƙe jiki a saɓule ta shiga gyaran falon da ya yi dagaja-dagaja da datti yayin da Daddy ya fita harabar gidan cike da damuwa. Bayan dawowarsa cikin hayyacinsa ne suka saka shi gaba da faɗa, su na yi masa nasiha a kan rayuwa tare da tsorartar da shi daga azabar Allah. Cikin kuka ya ke ba su haƙuri tare da jaddada masu cewa shima ba laifinsa bane damuwa ce ta masa yawa da kuma zugar mugayen abokanansa da suka ɗora shi a kan hanyar da bata ɓullewa. To dama an ce tsakanin ɗa da mahaifi sai Allah, nan take suka yafe masa tare da jaddada masa ba za su bar shi a nan ba, domin idan su ka bar shi ba susan wane hali zai shiga ba, bayan shaye-shaye da neman mata da yake. Anan ya rantse masu a kan baya neman mata shaye-shayen ma ƙaddara ce ta saka. ©©©©©©©™™™™ Mimie na cikin wannan halin ne, Cikin iyawar Allah wata rana sai ta tashi da laulayi sai amaye-amaye take, komai ta ci sai ya dawo mata, nan take Innarmu ta fahimci ciki ne da ita. A can cikin zuciyarta ta na farin ciki za ta samu jika amma a fili sai ta nuna rashin damuwa, domin zahiri soyayyar Zinnira ta mamaye zuciyar Innarmu(ko da yake aikin asiri ne) da yake shekara ɗaya baya kenan da Bassam ya auri Zinnira sai dai ba'a ƙauyen take zaune ba, ta na birni gidan da ya yi burin rayuwa da Mimiensa a ciki, anan a ka kai ta domin tun da lokacin bikin nasu ya ƙaraso ya sallami y'an haya ya sake gyara gidan tsaf don sanya amaryarsa. Bayan auren ba irin rawar kan da su Shamsiyya ba su nuna ba, baƙar magana da habaici kam ta sha su, a ranar da za a kai amarya gidan ya cika maƙil da y'an biki, Mimie ce ta zo wucewa cikin dakakkiyar shaddarta bowa sai ƙamshi ta ke zubawa. Sakina ce ta dubi Shamsiyya tare da yin karaf ta ce "Yaaya irin wagga kwalliya haka sai ina? Lallai babu laihi shaddakki mai tcada ta, sai dai matsalat baki gaban mijinki don ko ganin ki bai son yi, yau ya ɗauki sabuwar amarya dal, ba irinki ba da kit tsuhwa tun baki da ko ɗa guda ba." A take y'an matan dake wajen suka bushe da dariya. Shamsiyya ma dariyar ta yi ta ce "Ke dai bari ƙaunata, dole ki ga na ɗauki irin wanga wanka, kin san ɗiyar masu arziƙi nike, ga shi kuma dadirona babban sanata na ko uwayena basu turomin kuɗɗi ba shi ya na turo min..." Ran Mimie ne ya yi mugun ɓaci da jin zancenta, duk haƙuri irin na Mimie ranar kam sai da su ka kai ta bango, idonta ne ya rufe har bata san lokacin da ta ƙaraso gun ta wanke Shamsiyya da mari ba, ji kake tas, tas, tas, ta wanke ta da lafiyayyun mari har guda uku. Cikin firgici Shamsiyya ta miƙe zumɓur dafe da kunci ta na neman wanda ya mata wannan marin da sai da ta ga taurarin wuya. Ido huɗu suka yi da Mimie ta na huci kamar zakanya, ta nuna Shamsiyyan da yatsa ta na faɗar "Ke ƙaramar y'ar iska, idan kina cin ƙasa ki kiyayi ta shuri, shiru-shiru fa ba tsoro ba ne, daina ganin duk abinda kuke na saka maku ido, zan iya jure ko wanne wulaƙanci da duk abinda za ku min, amma ban da zagin iyayena, mussanman mutumin da ya zame mini gata, ya ke goyon bayana acikin kowanne yanayi, ba zan taɓa jurar na ga ana cin mutuncinsa ba a gabana na yi shiru, a baya kin yi na ƙyale ki amma na fahimci ba ku san zuru ba, to duk wacce ta kai shegiya ta kuma gwada zagin Daddyna ta gani." Ta na gama faɗa ta yi fuu ta bar gun cikin ƙonar zuciya ta shige ɗakinta tare da banko ƙofa, ta faɗa kan kujera tana kuka mai cin rai. ®®®®®© A can waje kuwa har bayan mintuna biyar Shamsiyya bata dawo a hayyacinta ba, ta kaɗu iya kaɗuwa, "Ashe dama Mimie ta iya rashin mutunci haka? Ita dai tun zaman su da ita tsayin shekaru uku kenan bata taɓa jin ta faɗawa wani baƙar magana ba bare ta tada murya sai yau. Sakina ma ta jijjiga da wannan al'amarin, cikinta ya ɗuri ruwa sosai, dai-dai lokacin ne inna ta fito ta na faɗar "Minana ka hwaruwa?, ina ɗaka nijjiyo hayaniya." Anan y'an matan dake wajen su ka labarta mata. Nan take ta hau ruwan bala'i, ta je ƙofar ɗakin Mimie ta na ta zazzagawa sauran mutan wajen su ka kama mata, ba su suka bar wajen ba sai da su ka lisafe mata haƙoranta tas sa'annan. Ranar ta sha kuka kamar ba gobe, don duk ɗibar albarkar da suke ta na jin su, sauƙinta ɗaya yau ta samu ta fara ɗebe takaicinsu, da baƙin ciki ya karta a ránar. Tun ranar yaran suke shakkar yi mata rashin mutunci. Bayan tarewar amaryar Bassam ne suka tattara suka koma gidan da zama, ai kuwa sun ga rayuwa, domin a farko ta bi su lab-lab-lab komai yi masu ta ke lokacin da ta ke amarya, bayan kamar wata uku da auren, Zinnira ta fara sha masu ƙamshi ta na ɗaɗɗauke kai, irin ita ba sa'ar su ɗinnan ba ce, haka ma ba ta wani ganin girman Innarmu a zuciyarta, dama tun farko neman shiga ne yasa ta bita. ©©©©©©©©© Abuja A can Abuja kuwa tuni shirye-shiryen aure sun yi nisa tsakanin Ruma da Saheen, domin ita tausayinsa take ji ba da wasa ba, ta daɗe da gano cewa Mommynta asiri ta masa domin da kunnenta ta ji su lokacin da suke tattauna maganar a waya. Wannan tausayin ne ya rikiɗe ya koma soyayya, don haka ta amince da auren, su ma su Daddy ba musu suka amince ganin cewa abun na gida ne duka. Mommy kuwa kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha haka ta ji. Lokacin da ya rage saura sati ɗaya bikin, Ruma ta saci hanya ta je gidan wata ƙawarta domin ta samu ta yi waya da Mimie da su Mama, don Mommy ta kasa ta tsare ta ce ba za'a sanar masu ba, sai dai su ji a dangin ango, ko su zo a matsayin dangin ango don sun fi ƙarfi can ®®©®®®® Ko da Mimie ta samu labarin ta yi murna sosai, a nan ta kira Uncle ta sanar da shi, daƙyar ma ya ɗaga wayar don zuwa lokacin komai ya ƙara jagulewa tsakaninsu. Ko da ya ɗaga ma bata samu amsar arziƙi ba don cewa ya yi "Ko Alhaji Salman ɗin ne ya koma saurayi za a yi aurensa ba za ta je ba, bare wani banzan ɗansa." Ta ji ciwo sosai a ranta amma sai ta dake ta ce "Pls Uncle ko dan Ruma ka daure ka bar ni na je." Nan fa ya fusata ya ce "Na ce ba za ki ba, ko da Hajiya khadija za a aurar ba Ruma ba, ke bari ki ji ƙarshen zance ko da Malam Habu bakanike da Malama A'isha mai ɗan wake ne su ka koma matasa za a aurar da su ba za ki je ba kin ji na gaya miki." Sosai zagin nan ya mata ciwo nan take ta fashe da kuka tare da kashe wayar gaba ɗaya. Haƙiƙa a yau da ba ta ɗauke da ruwan cikinsa, da a yau ɗin nan sai ta bar masa gidansa, ko da kuwa a ce idan ta je gida iyayenta za su koroto ne, ta gwammace ta shiga uwa duniya da ta zauna a na zagin iyayen da suka yi silar zuwanta duniya, kwata-kwata ma ita aurensa ya fice mata a rai, duk da idan ta ce ta daina son sa ita kanta ta san ƙarya take. A ranar ta kira Babanta a waya ta saka mi shi kuka ta na neman gafararsa shi da mahaifiyarta.... Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number 08109634202 Follow me on wattpad @ummu inteesar UMMU INTEESAR CE❤️❤️❤️❤️❤️ 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)* *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* DA KUMA *A SANADIN KAMA* WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202 DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE *AREWA WRITERS ASSOCIATION* ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Page 6️⃣1️⃣↪️6️⃣2️⃣ A nan suka tabbatar mata da sun yafe mata, tare da yi mata addu'ar Allah ya yaye mata ƙuncin da ta ke ciki. ®®®©©©© Shekara ɗaya kenan da auren Zinnira da Bassam amma ita ma ko ɓatan wata bata yi ba, haka ya saka innarmu cikin damuwa da alhini, har ta fara fitar da rai ga samun jika sai ga ɓullowar ciki a jikin Mimie. Ga wani sabon salon iskanci da Zinnirar ta tsiro da shi, ko da Bassam ya zo gari sai ta hana shi zuwa Kalgo, da yake ta riga ta asirce shi ko kara ta ɗora baya tsallakawa, a haka ta gwaguye ɗan arziƙin da ya fara dawo masa ita da innarta mai shegen kwaɗayin abun duniya. Su Sakina sun ga rayuwa domin zuwa lokacin Zinnirar da suke rawar ƙafa a kanta, ta saka yayansu ya masu korar kare daga gidan, bayan ta masu rashin mutunci ta zage su tas. Da kukansu da hawayensu suka dawo gida, ko da Innarmu ta kira shi, hana shi ɗagawa ta yi, da Innarmu ta ga bai da niyyar ɗagawa sai ta kira Zinnira, nan fa Zinnirar ta dage ta cinyewa Innarmu mutunci tsaf, ko raga mata bata yi ba, don arziƙin zumuncin dake tsakanin innar da babanta, har da ce mata "tsohuwar banza, wacce take son lalata rayuwar ɗanta da kanta." Ranar Innarmu ta ci kuka har ta bawa uku lada, ta yi nadamar yarda da ta yi aka haɗa kai da ita aka gurɓata rayuwar tilon ɗanta namiji. Bayan ta gama kukanta ta kira innar Zinnira ta sanar da ita ɗibar albarkar da ta mata, maimakon ta bata haƙuri kawai sai ta bushe da dariya ta ce "Ta min dai-dai Lantana, ke dama tunaninki haka za mu ƙyale ki, mun dai gode miki da kika taimaka muna da kanki a ka mallake muna ɗanki, ga shi ke kanki mun raba ki da shi, yayan naki ma ko da ke hwaɗa mai baida abin yi don na gama da shi shi ma." Ranar Innarmu ta yi nadama mara amfani, tare da tsinewa Hajiya Rabi(maman Zinnira) albarka. ©©©©©©®™™™™ Acikin shekara ɗaya da rabin, Zinnira ta tubure musu, ba irin cin kashin da bata masu, rashin mutunci sai wanda ta manta, ga shi har lokacin bata haihu ba. A na tsaka da haka ne watarana Allah ya toni asirinta. Bassam ya zo gida hutu kamar ko da yaushe, bayan ya fita gun abokanansa a cikin birnin, sai da yamma liƙis ya dawo, ya na shigowa ya tarad bata falon hakan ya sa kai tsaye ya nufi Bedroom ɗin su. Cak ya tsaya a bakin ƙofa jin maganganun da take faɗa a waya. Bakomai ya saka shi cin birki ba, sai don jin da ya yi ta na faɗar "Kai innata shiyyasa ni ka mugun son ki wallahi, ke san kan sheri, ke ga yanzu mun raba shi da uwatai da y'an uwa nai gaba ɗai, yanzu abu biyu yar-rage muna, mu samu a raba shi da shegiyar matan nan ta shi, don wallahi na tsane ta, dama na ɗaga mata ƙahwa na saboda azzikinta da muka ci, dan rabin kuɗɗinsa duk nata na shiyassa, amma yanzu anhwaninta ya ƙare, a sa ya saki y'ar banza." Shiru ta yi alamun ta na sauraren abunda innarta ke faɗa, can kuma ta bushe da wata mahaukaciyar dariya ta ce "Kai inna! Wallahi ke ma hi ni mugunta, yanzu dai gobe ina nan shigowa gobe sai mu koma wurin boka Kokau, don ya cika muna ayyukan mu." Nan ta ke hawaye suka fara gangarowa a idanunsa, ya saka hannu ya share. Ita kuwa Madam ɗin bata ma ji shigowarsa ba, saboda hankalinta gaba ɗaya ya na kan wayar da ta ke da mahaifiyar ta. Ta na kammala wayar ta juyo ta gan shi tsaye ya na bin ta da kallon tsana. Hannu ta ɗora a kai tare da saka ihu, saboda tunawa da ta yi cewa boka ya ce duk ranar da suka bari wani ya ji wannan sirrin, ban da su da za su yi aikin tabbas asirin zai karye, musamman idan suka bari wanda a ke aikin a kansa ya ji ko ya gani to ba shakka suna cikin hatsari don bayan karyewar asirin, su jira bala'ukan da za su biyo baya a rayuwarsu. Kuma a haka suka amince tsabar sun yi nisa basa jin kira. Ihun ta ci gaba da yi tana kuka tare da riƙon gafararsa. Kallonta ya yi cike da tsana sannan ya ce "Zinnira ko ban miki Allah ya isa ba, tabbas sai kin ga abinki, domin ko alhakin raba ni da mahaifiyata a ka bar ki da shi ba za ki iya ɗauka ba, ballantana har sakawa da kika yi na cutar da matata, amanata, tabbas sai kin ga abinki, ki je na sake ki saki biyu, kuma ba gyaran aure tsakaninmu." Hankalinta ya kai ƙoluluwar tashi ihu kawai take ta na roƙonsa, amma ko sauraronta bai yi ba, ya bata umurnin ta tabbatar ta bar masa gidansa kafin ya dawo, daga haka ya fice ya bar mata gidan." A ɗimauce ta nufi gidansu ta na kuka. ©©©©©©©©©© Ita kuwa Mimie tun bayan da iyayenta suka tabbatar mata da yafiyar su agare ta, ta fara ganin haske a rayuwar aurenta domin an rage kyarar ta da hantarar ta da a ke a cikin gidan, sai dai har yanzu da sauran rina a kaba. ©©©©©©©©©© Bayan wata tara, wata ranar lahadi da safe Mimie na kwance a ɗakinta ta na fama da ciwon mara mai tsanani. Shamsiyya ce ta shigo ta tsaya a kanta ta na famar rafka mata kira amma saboda zafin ciwo ko jin ta bata yi ba. Bata yi aune ba ta tsinto muryar Shamsiyya na faɗar "Ke! Wai ba ke aka kira tun ɗazu ba?,ki na ji ke ƙyale mutane, matsiyaciya kawai mai ƙaryar arziƙi." Ita dai bata ce komai ba har ta zo ta wuce budurwar. A hankali take takawa bayanta kamar zai tsage, (saboda cikin jikinta ya yi girma da yawa) a haka ta ƙarasa gun Innarmu dake zaune ta na ƙulla yaji ta ce "Inna gani.". Wani kallon banza innar ta watsa mata sannan ta ce "To hitsararra na gan ki ai, da uwakki ta na san ba ki tsayawa kanta haka, amma da yake ni ke rena ni shiyassa kin ka wani tsaya ƙiƙam akaina." Mimie dai ba ta ce komai ba, don in da sabo tuni ta saba da wannan cin mutuncin da mutan gidan ke mata, wai ma don yanzu abin ya yi sauƙi ne. Innarmu ta kalle ta a gyatsine ta ce "Maza ki aza muna sanwa ga rana harta take kina ɗaki kwance, ke ga....." Bata samu damar ƙarasawa ba saboda ƙarar da wayarta ƙirar Nokia ta yi. Ɗaga wayar ta yi tare da ɗorawa a kunne. Can ta ce "Eh ni ta." Shiru ta ɗan yi can ta zabura tare da dafe ƙirji ta ce "Mee!?. Wane asibiti?, Wayyo Allah! ɗana Bassam." Wayar hannunta ce ta suɓuce ta faɗi ƙasa, da sauri ta miƙe zuwa ɗakinta ta na kuka. Mimie kuwa gabanta ne ya tsananta faɗuwa, "to me ya faru da mijinta ne ko hatsari yayi?" Zuciyarta ta bijiro mata da wannan tunanin, tunowa da ta yi ya kira ta ɗazun ya sanar da ita yau zai dawo. Daƙyar ta ɗaga ƙafarta ta bi bayan Innarmu don jin me ya faru. A dai-dai lokacin da ta iso ƙofar ɗakin, ta jiyo muryar Innarmu na faɗar "Sakina yayanku ne ya yi haɗari, kan hanya tai ta dawowa gida, yanzu haka ya na asibitin binni rai ga hannun Allah, maza kira Shamsiyya ku taho mutahiya." Ta faɗa cikin kuka. "Innalillahi wa inna'ilahir raji'un! Bassam! Uncle! Mijina!" Abunda ta iya furtawa kenan tuni ganinta ya ɗauke sai ji kake tim! Ta faɗi a kan cikinta. Da gudu Innarmu ta ƙaraso gun tana salati cikin kuka ta ke faɗar "Innalillahi wa inna'ilahir raji'un!, Shamsiyya yi sauri ki kirawo babanku Isah ya taho da mota tai akai ta asibiti." Ba musu Shamsiyya ta fice da gudu ta je ta kira sa, bayan kamar minti ashirin sai ga su, da gudu suka shigo gidan a ka cicciɓe ta tare da sakata mota. Asibitin da a ka kai Bassam can suka nufa da ita, har zuwa lokacin bata dawo hayyacinta ba, don tun lokacin da ta faɗin ta suma. Likitoci sun tabbatar masu da cewa dole sai an mata tieter, ba za ta iya haihuwa da kanta ba saboda ta jigata sosai. Bayan an shigar da ita ɗakin tiater ne suka juya zuwa ɓangaren da Bassam ya ke, nan ma ba'a basu damar ganinsa ba saboda a lokacin likitoci ne suka duƙufa a kansa don ceto rayuwarsa. Haka suka nemi guri suka zauna hankali a matuƙar tashe, duk sun yi jugum-jugum da su, kowannen su sai addu'a ya ke a ransa a kan Allah ya bawa majinyatan lafiya. Bayan awa ɗaya aka kammala tieter, likita ya fito, nurses biyu mata su na biye da shi a baya a nan likitan ya yiwa Innarmu albishirin cewa an samu y'an biyu maza, daga haka ya wuce zuwa office ɗinsa. Nurses ɗin ne suka nemi da a basu kayan da za su shirya jira-jiran da mahaifiyarsu a ciki, a nan suka sanar masu cewa sai an je annemo da ya ke ba fitar nutsuwa suka yo ba. Innarmu ta ce da Sakina wadda ta kasance tare da ita agun "Yi sauri ki biya ta wurin su Babanku Isah, ki ce mai na ce ya kai ki gida ki ɗakko kayan haihuwa, idan kika je ki duba ɗakinta na san ba su rasa aje su." Da "to." ta amsa, ta wuce a hanzarce, da yake sun baro shi tare da Shamsiyya a can ƙofar ɗakin da a ka kwantar da Bassam... Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number 08109634202 Follow me on Wattpad @ummu inteesar Vote share and comment UMMU INTEESAR CE❤️❤️❤️ 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)* *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* DA KUMA *A SANADIN KAMA* WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202 DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE *AREWA WRITERS ASSOCIATION* ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Page 6️⃣3️⃣↪️6️⃣4️⃣ Ƙarasa ta yi ta kira Baban suka wuce zuwa Kalgo don ɗauko kayan. Bayan wucewar su a ka yiwa Shamsiyya izinin shiga ganinsa, sai da ta je ta kira Innarmu sannan suka shiga tare don duba lafiyarsa. Kuka kam sun sha shi saboda ganin yanayin da Bassam ɗin ke ciki, wasu daga cikin gaɓoɓin jikinsa duk sun kakkarye, haƙiƙa ya na cikin zillah. ®®©© Ɗaya daga cikin Nurses ɗin ce ta je ta samo madai-daitan towel guda biyu, ta naɗe jariran a ciki bayan angama shirya su, domin Allah ya jarafce ta da son 'yan biyu, mussanman identical twins(tagwaye masu kama da juna) shiyasa yaran suka shiga ranta sosai. Bayan dawowar Sakina daga gida ne a ka shirya yaran a cikin kaya iri ɗaya, ita ma Mimien suka taimaka mata ta shirya, sai ga su sunyi ras abinsu. ©©©©©© A can ɗakin da a ka kwantar da Bassam, Innarmu ce ta matso daf da shi ta na kuka ta na roƙa masa lafiya a gun mai kowa da komai. Ko waye kai idan ka ga halin da Bassam ya shiga dole ka zubar masa da ƙwalla matuƙar ka na da imani. Buɗe idonsa ya yi ya fara rarraba su ko'ina na cikin ɗakin, alamar ya na neman wani abu, can ya dawo da dubansa a kan innar, daƙyar ya buɗi baki ya ce "Innarmu ina matata?" Cikin yanayin damuwar da take ta bashi amsa da cewa "Tana nan asibitin, bata jima da haihuwa ba." Tun da ta fara maganar ya ke kallon ta don jin me ya kawo matarsa asibiti, bayan ta dire zancen ne ya yi hamdallah a zuciyarsa, daƙyar ya kuma cewa "Me a ka samu." "Y'an biyu maza." Innar ta amsa. Wai Wai Wai!!! Zo ku ga murna a gun Bassam, duk da cewa ya na kwance cikin azabar ciwo, amma hakan bai sa fuskarsa ta kasa bayyanar da farincikinsa ba. A nan ya roƙi Inna Alfarmar ta je ta kawo masa matarsa da yayansa ya gan su, tun da shi ba zai iya tashi ba bare ya je, kasancewar kunkurunsa da ƙafarsa suna ɗaya daga cikin gaɓoɓinsa da suka karye. Ganin basu da wannan damar ta ɗauko masa ɗaya daga cikin waɗanda ya nema ne, ya saka Baba isa ya je ya sanar da likitan buƙatar majinyacin nasu. Sai da aka sha artabu kafin likitocin su yarda da wannan ƙudurin nasu, nan ma sai da su ka ji daga bakin majinyacin, ganin yanda ya ke ta masu magiya ga kuma halin da yake ciki na rashin tabbas ya sa suka amince da buƙatarsa. ©©©©©™™™™ Akan kujerar guragu aka ɗora ta, kasancewar ba ta iya tafiya da kanta saboda wahalar da ta sha gun haihuwa, nurse ce ke tura ta har zuwa ɗakin da ya ke. Sakina da Shamsiyya ne suka ɗauki jariran su ka bi su a baya. Su na isa nurse ɗin ta saki kujerar tare da juyawa ta fice daga ɗakin. Tashin hankali ne ya ziyarce Mimie, ganin mijinta kuma masoyinta kwance magashiyan, baya ko iya kyakkyawan motsi. Nan da nan idanunta suka fara ambaliyar ruwan hawaye, ta ma kasa cewa uffan tsabar firgicewa. Su Sakina ne suka ƙaraso ɗakin riƙe da ƴaƴan, Inna ta karɓi ɗayan yaron, ta je saitin fuskar Bassam ta nuna masa ta ce "Ga ɗanka guda." Shamsiyya ta matso da ɗayan kusa da na farkon yadda zai iya ganinsu sosai, shi kuwa sai murmushi ya ke a ransa ya na ƙara godewa Allah da wannan kyautar da ya masa ya na gaf da barin duniya, domin ya na ji ajikinsa cewa tasa ta zo ƙarshe. Sosai ya ke jin ƙaunar yaransa na ratsa shi, da yake yaran duka da shi suke kama, komai da komai nasu iri ɗaya, ba inda suka bar shi har a kalar fata. "Allah ya maku albarka." Shi ne kaɗai abinda ya faɗa ya na ta famar murmushi. Bayan sun tabbatar da ya ga yaran da kyau, suka janye daga gun. "Matata fa?" Ya tambaya. Sakina ce ta je ta ƙara matso da Mimie daf da shi, dai-dai inda zai iya hangotan daga kwance. Kallon ta ya yi ido cikin ido, sannan ya fara magana a wahalce ya na neman gafarar ta faɗar ya ke "Ki gafarta min uwar ƴaƴana, haƙiƙa na san na cutar dake, na ci amanar soyayya a baya lokacin da sihiri ke ɗawainiya da ni, ki yafe mun ki roƙa min gafarar su Abba da Alhaji Salman, ga amanar ƴaƴana nan na bar miki, na san za ki ba su tarbiyya mai kyau, don Allah ka da ki ce za ki rama abinda muka miki a kan ƴaƴana, pls ki yafe mun, Ni tawa ta zo ƙarshe." Ya na maganar numfashinsa na sassarƙewa, sheɗarsa na yin sama da ƙasa. Kuka take sosai ta ɗago da rinannun idanunta ta kalle shi ta ce "Na yafe maka Uncle, na yafe maka uban ƴaƴana, na yafe maka...." Murmushi sosai ya yi a dai-dai lokacin da sheɗarsa ta zo daf da maƙogwaro ya ce "La'ilaha illallah, Muhammadu Rasulullah......" Ya na zuwa nan rai ya yi halinsa. Innalillahi wa inna'ilahir raji'un! Tashin hankali ba a sama ka rana, nan fa Mimie ta haukace, ta kai hannu tana jijjiga shi ta na faɗar "Uncle! Uncle ka tashi, wallahi na yafe maka ka tashi Uncle, ka tashi mu shimfiɗa sabuwar rayuwa mai cike da farin ciki tare da ƴaƴanmu. A ɗimauce take zancen, ganin baya motsi kuma idonsa ya kakkafe yasa ta juyo ga Innarmu wacce take ta faman salati ta na kuka ta ce "Inna ki ce ya tashi wallahi na yafe, ki faɗa masa." Sosai innar ta ji tausayin Mimien na ratsa ta, kawai sai ta zo ta rungume ta suka ci gaba da kukan. Shamsiyyan ce ta yi ƙarfin halin zuwa ta kira likita itama ta na kuka sosai. Ya na shigowa ɗakin ya ga abunda ke faruwa, kawai sai ya shafe masa fuska tare da jan mayafi ya rufe masa fuska. Ai kuwa Mimie na ganin haka ta tabbatar ya mutu, kawai sai ta kuma saka ihu tare da sumewa a kan kujerar da take.... Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number 08109634202 Follow me on Wattpad @ ummu inteesar UMMU INTEESAR CE❤️❤️❤️ 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)* *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* DA KUMA *A SANADIN KAMA* WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202 DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE *AREWA WRITERS ASSOCIATION* ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Page 6️⃣5️⃣↪️6️⃣6️⃣ Iya tashin hankali Innarmu ta gani a ranar. A haka suka tura keken tare da mayar da Mimie ɗakin da take jinyar a ciki, likitanta suka kira don ya duba ta. Ko kafin ta farfaɗo har an wuce da gawarsa can gida don masa sutura. Dogon suma ne ta yi, don haka bata farfaɗo ba sai wajajen tara na dare. Bayan ta dawo hayyacinta ta cigaba da kukanta cikin dasasshiyar murya, rayuwar soyayyarsu ta baya da farkon aurensu kawai take tunawa, duk ta fita a hayyacinta. Innarmu dake zaune gefe kusa da ita rungume da hassan, ita ce ta dubi Shamsiyya ta ce "Ɗauki wayatta ki kira min innatta, ya kamata su san halin da a ke ciki." Ba tare da budurwar ta amsa ba ta miƙa hannu ta ɗauko wayar tare da miƙawa Sakina, da ido ta mata nuni da ta kira. Da yake Sakinan ita ce mai ɗan dama-dama, sai kuwa ta shiga jerin numbobin ta na dubawa. Can ta gano number da a ka rubutawa *Mamata* ai kuwa ta danna mata kira. Bugu biyu a na uku a ka ɗaga kiran, sallama ta yi, bayan ta gaishe da maman. Cike da mamaki Maman ta tambaya "Wacece? Ina Mimien?" A ɗan tsorace take zancen. Cikin matuƙar ƙarfin hali Sakina ta ɗan yi busasshen murmushi ta ce "Mama! Sakina ta ƙaunar Bassam, dama na kira na in sanar miki Anty Mimie ta haihu ɗazu da rana, amma c.s anka mata." Sosai mama ta yi murnar jin wannan labarin duk da ba komai take ganewa ba, saboda Hausar Sakinan ba ta kanawa ba ce. Cikin rawar baki Mama ta ce "Kai masha'allah, me a ka samu?" "Y'an biyu maza." Ta ba ta amsa. Nan fa murnan Maman ta daɗu, amma da ta fahimci kamar akwai yanayin damuwa a tattare da Muryar Sakinan, sai ta ce "Masha'allah! Allah ya raya, amma ina Mimien ban ji ta ba, ko da wata matsala ne, na ji muryanki wani iri." Guri ta nema ta zauna ta na matsar ƙwalla ta ce "Ita dai da dama, ga mu nan asibiti domin ta jiggata Sosai, amma kuma yayan ne...." Sai kuma muryarta ta fara rawa. Cikin tashin hankali Mama ta ce me ya sami yayan naku Sakina?" Cikin kuka ta ce "Bayan haihuwarta, ko awa ɗaya ba a yi ba, yaya ya rassu." Duk da cewa ba a son ranta a ka yi auren ba, amma ta girgiza sosai da wannan mutuwar. Cikin tashin hankali ta ce "Innalillahi wa inna'ilahir raji'un! Allah ya jikansa da rahama, yanzu ina Mimien? Don Allah idan ta na kusa ki ba ta wayar." Tashi ta yi ta je bakin gadon Mimie dake kwance cikin wani yanayi ta na sauraron wayar ta su, ta miƙa mata wayar. Karɓa ta yi amma bata iya cewa komai ba, ta na jin maganar Maman tata kawai sai ta fashe da matsanancin kuka. Lallashin duniyar nan Mama ta yi, amma kamar zuga ta take, duk yanda ta kai da son su yi magana Mimie bata ce uffan ba, sai kuka a kan dole ta kashe kiran, cikin wani irin yanayi na rashin jindaɗi. ®©©©©©©©© Kano Ƙarfe goma na dare Baba ya shigo gidan nasa, ya samu matarsa cikin wani yanayi na jimami. Tambayarta ya yi "Lafiya dai Maman Zuhra? Me ke damun ki?" Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce "Mimie ta sauka ɗazu, an samu y'an biyu maza." Da fara'a a fuskarsa ya ce "A'ah to ai wannan abin farinciki ne, miye abun tada hankali a nan?" Cikin raunanniyar murya ta ce "Allah ya yiwa mijinta rasuwa bayan wasu mintuna da haihuwarta." Sosai ya ji wani shock ya ja shi, amma gudun kada ya karyar mata da zuciya sai ya ce "Allahu akbar! Allah ya jikansa da rahama." Ameen ta faɗa. Ya ce "Addu'a za ki yi masa Maman Zuhra, yanzu addu'ar mu kawai yake buƙata, amma damuwa ko kuka duk ba su da amfani." Da haka ya samu ya ciwo kanta, a nan suka zauna hira, cikin hirar ne suka yanke lokacin tafiya birnin Kebbi. Washe gari Mama ta kira Mamy ta sanar da ita abinda ke faruwa da kuma ranar da za ta tafi, a nan Mamy ta ce ta bari su tafi tare ranar talata a maimakon ranar Litinin da ta saka. Bayan ta gama waya da Mamyn ne ta kira Mimie, wannan karon Mimien ce da kanta ta ɗaga suka gaisa, don yanzu an samu ta daina kukan sai dai kukan zuci da ba ta tunanin za ta iya daina shi har ko yaushe. Sosai Mama ta mata nasiha, tare da janyo hankalinta a kan ta yi haƙuri da rayuwa a duk yanda ta zo mata. Bayan ta gama ne ta nemi da a haɗa ta da Innarmu a waya ta mata Gaisuwa tare da Barka. Mimie ta yunƙura ta zauna tare da miƙawa innar waya ta ce "Innarmu ga Mamana za ta miki gaisuwa." Jiki a sanyaye innar ta karɓa, don yanzu wata irin kunyar yarinyar da iyayenta take ji, saboda sanin abinda ta aikatawa yarinyar a baya. Gaisawa suka yi sannan ta mata gaisuwar mutuwar da kuma barkar haihuwar sannan ta kashe wayar. ©©©©©©© Haka kuwa a ka yi ranar talata tun safe Mamy ta taso zuwa garin Kano, da misalin ƙarfe sha biyu ta iso, abinci kawai ta ci suka ɗau hanyar zuwa Bk. Sai dare suka isa, kai tsaye asibitin da a ka kwatanta masu su ka nufa. A can suka tarad da yaran cikin ƙoshin lafiya sai abinda ba a rasa ba, domin innarmu da ƴaƴanta su na iya ƙoƙarinsu gurin kula da Mimie da yaran. Mimie ta ji daɗin zuwan Mamanta da kuma Mamynta sosai, hakan ya ɗauke mata wani ɓangare na damuwar da take ciki. Kwanansu biyar a asibitin a ka sallame su, ganin jikin nata ya yi kyau, Innarmu da kanta ta bawa su sakina maƙullan gidan Bassam na birni suka buɗe shi tare da gyarawa, a ka kai Mimie can don yin wankan jegonta cikin kwanciyar hankali da nutsuwa. ©©©©©©© Ranar juma'a su Baba, Alhaji Salman da Saheen suka zo don suna da kuma yin gaisuwa. Kalgo suka fara zuwa suka yiwa Innarmu da y'an uwanta gaisuwa sannan suka dawo gidan Mimie. yau ta kasance ranar Asabar a yau ne kuma za a yi sunan y'an biyu, tun da sassafe Innarmu ta je bayan gida inda turken dabbobinta ya ke, ta saka a ka kamo manyan raguna biyu tare da madai-daicin santa wanda ta ƙwallafa ranta a kansa, ta bayar a ka yankawa jariran tare da masu suna. Yara sun ci sunan Aliyu da Bassam wanda Mimie da kanta ta zaɓawa yaran suna. Hassan shine Aliyu wato takwaran baban Bassam, sai kuma Hussain wanda ya ci sunan mahaifinsa, amma ana masu inkiya da *Affan* da *Afeef* Duk da ba wani shagali a ka yi ba, saboda mutuwar mahaifin yaran, amma hakan bai hanawa mutane yin tururuwa zuwa ganin yaran ba. Washe garin ranar su Baba suka koma tare da Mama saboda ayyukansu, amma a nan suka bar Mamy tare da Sagir ƙarami domin ita sai Mimie ta yi arba'in za ta taho tare da ita gaba ɗaya. Bayan Mama ta koma Kano ne ta tura ƙanwarta Halima( da yake ita bazawara ce y'ar ƙanin babansu Maman ce da take zaune gidansu dake nan Kano)zuwa Bk don ta taya Mamy zama. Bangaren Innarmu kuwa yanzu ta na masifar son Mimie, ji take ina ma yanzu ne Bassam ya ke raye tare da matarsa? Da sun ga gata, amma inah! Mutuwa bata barin wani don wani. Kullu nafsin za'iqatul maut (dukkan rai sai ta ɗanɗani mutuwa) Don haka ta sakawa ranta dangana, yanzu sosai take kula da Mimie duk da y'ar tazarar dake tsakanin su, amma duk bayan kwana biyu take zuwa birni don duba lafiyarsu. Sannan ta ajiye ƙanwarta (Rashida) da Shamsiyya a can domin su riƙa taimakawa su Mamy. Sosai Mimie take mamakin sauyawar Innarmu, duk da cewa ba abun mamaki ba ne, saboda yanzu ta fahimci wancan lokacin asiri Zinnira ta masu, yanzu kuma ya warware. Wata rana da Innarmu ta je gidan, da kukanta take roƙon Mimie a kan ta gafarta mata abinda ta mata, hakama su Shamsiyya sun nemi yafiyarta, kuma duk ta yafe masu, yanzu komai ya dai-daita ba sauran tashin hankali. Bayan sati Uku, komai ya lafa an nutsu, Mamy ta je da kanta ta sami Inna da maganar gadon yaran, su na so a raba a bawa yaran na su, ba don komai ba sai don haka Shari'a ta tanada, domin so suke su tafi da Mimie gida ta ƙarasa takabarta a can. Ta yi hakan ne domin karɓarwa yaran haƙƙinsu, amma kwata-kwata su ba kuɗin ne a gabansu ba domin indan kuɗi ne kam ba za su nemi hakan ba don su na da shi har ba su san yawansa ba. Ba musu Innarmu ta karɓa mata tare da cewa "insha'allahu Hajjiya za a yi yadda yak-kamata, gobe-gobenga zan biɗo malammai, don su zo a san yadda za a yin rabon. Amma don Allah kak-ku raba mu da Mimie ku batta nan don Allah." Girgiza kai Mamy ta yi ta ce "A'a innar Sakina ba za a yi haka ba, dole ne mu tafi da ita, domin ta na gama takaba aure za ta yi." A firgice innar ta ɗago kamar za ta ce wani abu game da hakan, kuma sai ta fasa. Jiki a sanyaye ta ce "To don Allah Hajjiya ku bam-muna yaran, ke ga yanzu su ɗai su ka rage min jinin Bassam tunda shi ya mutu." Ta ƙarashe zancen kamar za ta yi kuka. Mamy ta ce "Hmmm! Mu bar muku su ku kashe su, yanda ku ka so kashe uwarsu da baƙin ciki koh?" Ware ido Inna ta yi da sauri, haƙiƙa bata ji daɗin zancen nan na Mamy ba, amma ta sani wata rana dole sai haka ta faru tun da su su ka ja. Cikin rawar baki ta ce "Hajjiya ku yi hanƙuri don Allah, abat tuna baya, ya riga ya wuce kuma insha'allahu za mu riƙe su da amana, ki tuna su ɗin jinina na, tayaya zan bari a walaƙanta su?...." Ga mai buƙata sai ya tuntuɓeni ta wannan number 08109634202 Follow me on Wattpad @ummu inteesar. UMMU INTEESAR CE😍😍❤️🌹🌹🌹 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)* *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* DA KUMA *A SANADIN KAMA* WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202 DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE *AREWA WRITERS ASSOCIATION* ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Page 6️⃣7️⃣↪️6️⃣8️⃣ Bayan sun gama tattaunawar ne Mamy ta koma gidan Mimie. Innarmu ta shiga damuwa amma ba yanda ta iya dole ta haƙura da koma me za a musu, domin tsuntsun da ya ja ruwa dama shi ruwan kan doka. Har zuwa lokacin Zinnira da innarta ba su zo yiwa Innarmu gaisuwar mutuwar Bassam ba, hakan ba ƙaramin ƙona mata rai ya yi ba, damar abin dai yayan nata shi ya zo ya mata Gaisuwa kai tsaye ya juya abinsa. ©©©%%%%%©®®® Bayan wani ɗan lokaci malamai suka zo aka raba gadon Bassam, domin tuni Alhaji Sale ya siyar da komai da yake mallakin Bassam a kano, da kansa ya zo ya kawo kuɗin, lokacin da ya zo gaisuwar Bassam ɗin. Da yake ba wanda ya san zancen dukiyar Bassam da su Zinnira suka kwasa lokacin da take gidan, domin bai sanar da kowa ba, shi kansa bai san da wani abun ba, hakan ya sa ba wanda ya waiwaye su da zancen dukiyar Bassam, domin da ma ita Zinnirar ba ta da gado tun da ba ta da ko ƙwai a gidan, kuma bata masa takaba ba. An raba masu gadon kamar yanda Shari'a ta tanada, an bawa Innarmu kashi ɗaya bisa shida na dukiyar, yayinda a ka bawa Mimie kashi ɗaya bisa takwas na dukiyar, sauran kuma aka barwa tagwayen kasancewarsu maza. Bayan kammala rabon gadon ne a ka damƙawa mahaifiyar yaran nasu, aciki kuwa har da wannan gidan da suke zaune a ciki, don haka a ka siyar tare da bata kuɗin. Account a ka buɗewa yaran na musamman a ka zuba masu dukiyar gadonsu a ciki. A ranar da Mimie ta cika kwana hamsin da haihuwa a ranar Mamy ta ɗauke ta suka je yiwa Innarmu bankwana domin a washe garin ranar za su wuce Kano. Innarmu har da kukanta a kan ka da a raba su, amma inah! Haka ta haƙura dole, a nan ta ƙara roƙar gafara a gun Mimie su Sakina ma suka ƙara roƙar gafara sun sha kuka a ranar rabuwar su, Ba ma kamar Shamsiyya da tafi zaƙewa a lokacin da suke kan ganiyar rashin mutuncinsu. Mamy ta yiwa Innarmu alƙawarin za a dinga kawo mata y'an biyu lokaci zuwa lokaci don su ma su saba da dangin babansu. Haka rabuwar su ta kasance cike da alhini. Ranar wata Laraba suka wuce Kano, anan Mamy ta bar Mimie ta wuce Abuja. ©©©©©©© Tun washe garin Ranar da Mimie ta haihu, Abba ya kira Sameer ya sanar da shi ƙaruwar da aka samu, domin har zuwa lokacin Sameer baya Nigeria, wancan karon sun so su dawo da shi daga Dubai don ganin halin da ya shiga, amma sai ya dinga roƙar su a kan su yi haƙuri, ba zai iya komawa Nigeria ba, amma zai canza ƙasa domin ya nisanta da gurɓatattun abokai irinsu Rajbir, tun daga lokacin ya wuce Saudiyya ya na zaune a birnin Madina, dama ya gama karatun zaman dole ne kawai, tunda zaman Nigeria ya gagare shi. Ya yi murna sosai a zahiri, amma a baɗini ya ji ba daɗi ya so ace shi ta haifarwa waɗannan yaran har guda biyu, amma sai ga shi ƙaddara ta canza al'amarin. Anan ne kuma Daddy ke sanar masa cewa Mijin Mimien ya rasu. WOHOHO! Maimakon Sameer ya shiga jimami, sai wannan labarin ya zame masa tamkar Albishir, ji ya yi kamar an masa bushara da gidan aljanna, ya na ji cewa lokaci ya yi da farin cikinsa zai dawo tamkar da, ya na jin Allah ne ya dube shi da idon rahama shiyasa ya ɗauki rayuwar Bassam domin ya dawo masa ita a lokacin da ya gama fidda rai ga samun ta. Har sai da Daddy ya fahimci farincikin ɗan nasa a bayyane. Murmushi kawai ya yi ya kashe wayar, a ransa ya na yiwa ɗansa fatar samun nasara a karo na biyu, ya na masa fatar dawowar farincikinsa. %%©©©© Tun daga ranar Sameer ya fara shirye-shiryen dawowa Nigeria domin lokaci ya yi da zai dawo mahaifarsa. Cike da annashuwa yake shirinsa na dawowa, kallo ɗaya za ka masa ka san ya na cikin yanayi mai kyau. Nan fa Sameer ya haukace da siyayya komai ya gani mai kyau jibgowa Mimiensa da kuma twins ɗinsa yake, ku san duk rabin kayan tsarabar da ya siya nasu ne. ©©©©©©%%% A wata ranar Litinin da misalin ƙarfe uku na rana jirginsu ya sauka a filin jirgin Abuja. Cike da nutsuwa ya ke tako step ya na saukowa daga jirgin, ya yin da Saheen da Salim suke ɗan nesa da shi su na kallonsa cike da murnar sake saduwa da ɗan uwan nasu da suka yanke ƙauna da samun hayyacinsa. A haka ya ƙaraso gunsu suka rungume juna su duka suna murnar haɗuwa. A mota Sameer sai kalle-kalle ya ke, ya na ganin yanda garin nasu ya sauya, shekara biyar kawai da yayi ya dawo, ya ga sauye-sauye a birnin nasu. Haƙiƙa Abuja ta cika Babban birni mai kyau da tsari, ko ina gwanin burgewa. Haka yata kalle-kallensa har suka kusa isa gida, a nan ya kalli Saheen ya na tsokanarsa da cewa "Yaya Saheen baban Boy, ya boy ɗin namu da kuma Mamansa?." Y'ar dariya Saheen ɗin ya yi,bai ko amsa tambayar ba, ya ce "Kai yaya Sam! Yau kuma ni ne yayan naka?." Shima Sameer ɗin dariya ya yi ya ce "Eh, ai yanzu kai ne yayana tun da har Ka na da ɗa da mata ni kuma ba ni da, ka ga kenan yanzu ni ne ƙaninka." Ya ƙarasa zancen ya na ɗan murmushi da alama murmushin na jin ciwo ne. Dariya suka saka dukkansu, Salim dake zaune a bayan motar ya na sauraren dramar y'an uwansa sai murmushi yake saboda sun burge shi, sai a lokacin ya ce "Ai kar ka wani damu yaya Sam, kai ma kwanan nan za ka angwace, za mu sha shagalin aurenka da Mimienmu." Da sauri Sameer ya waigo bayan, ya na kallon Salim ya ce "Waya gayama haka?" "Ni na faɗa domin yanzu haka Mamy ta na can kuma kwanan nan za ta zo maka da ita, ina da tabbacin wannan karon ba za a samu matsala ba insha'allah." Murmushi kawai Sameer ya yi bai kuma cewa komai ba, ya juya ya cigaba da kallon gabansa, domin ya fahimci y'an uwan nasa su na so su saka masa rai ne da samun abinda zai yi wuyar samu a gare shi. Lokacin da ya ke saurayi mai ji da kyau da ƙuruciya ga Naira ma ba ta so shi ba, sai yanzu da duk ya yamutse kuma ya ƙara shekaru? A haka ya ci gaba da saƙe-saƙensa har suka ƙarasa gida. Rashin Mamy a gidan ya saka Sameer ya ji gidan ya yi wani iri, amma duk da haka ya ji daɗi sosai da ya dawo ya riski ɗan ɗan uwansa kuma takwaransa, wato Sameer ƙarami ɗan Ruma da Saheen." Kasancewar Sameer Ya na matuƙar son yara hakan yasa kullum Sam ƙarami ɗan 3months ya na cinyarsa ya na wasa da shi. Ko da Mamy ta dawo Abuja ta sami Sameer a gidan, sosai ta ji daɗin ganin yanda ya samu nutsuwa kuma da alama ya shiryu ya daina halayyarsa ta baya wato shan giya. ©©©©©©®®® Har zuwa lokacin Mommy bata bar Saheen ya huta ba, kullum ta na cikin ƙwaƙule masa aljihu, ga shi tun da ya auro Ruma ku san kullum ta na gidan, kasancewar Abbansu Ruma ba mazauni ba ne, kullum ya na hanyar wani gari ko wata ƙasa don kasuwancinsa. Duk wannan abun Saheen ba ya ganin aibun Mommyn kuma duk abinda take so shi a ke yi, da yake dai aikin asiri ne shiyasa. Sosai a bun ke damun Ruma yanda mahaifiyar tata ke takura masu, amma ba yanda ta iya dole ta yi haƙuri, domin dai duk yanda ta lalace ita ce dai mahaifiyarta kuma bata da madadinta a duniya. A haka ta cigaba da haƙuri da halayen mahaifiyar tata, kullum ta na roƙa mata shiriya a gurin Allah. ©©®®®©©©© Mimie ta zazzaga dangi na uwa da uba da kuma gidan yayyenta duk ta kai masu ziyara, ba wanda bai yi murnar ganinta ba, ga twins Allah ya zuba masu farin jini duk inda ta je kamar alashe su saboda ƙaunar da a ke nuna masu. Bayan wata ɗaya da zuwan Mimie Kano, hankalinta ya kwanta ta murmure jikinta ya yi kyau, haka ma Affan da Afeef sun yi kyau abinsu. A ranar da suka cika Wata uku a duniya, Mimie ta shirya ta je Abuja gidan Daddynta don kai masu ziyara. Murna a gun iyalan gidan ba a magana, Ba ma kamar Sameer da yake jin kamar ya haɗiye ta ita da jariranta saboda ƙauna. Ruma ma ta yi matuƙar farinciki da zuwa y'ar uwar tata a karo na farko bayan aurenta. Nan fa suka shiga murnar ganin junansu. Ita kuwa Mimie kunyar yaya Sameer take ji sosai, shiyasa muddin ta ji motsinsa a falo ba ta fitowa sai ya bar gun. Lura da hakan ya saka wata rana Yaya Sameer ya rutsa ta a ɗakinta dake gidan. Ta ɗan tsorata da ganinsa, su na haɗa ido ta sunkuyar da kanta ƙasa ta na wasa da hannun Afeef dake kwance kusa da ita a kan gadon. Matsowa ya yi ya na murmushi ya ce "Mimienmu sannu da zuwa." Shiru ta yi bata ce komai ba. Faɗaɗa murmushinsa ya yi ya ce "Da ma na zo ne na miki sannu da zuwa, tun da na ga alamar kunyar yayan naki kike ji." Ita dai ba baki sai kunne kuma har lokacin bata ɗago ba. Sunkuyowa ya yi ya ɗauki Affan dake kwance ya na wasarsa, ya ɗaga shi sama ya na murmushi ya ce "To ni bari na je, dama ina son ganin ƴaƴana ne, kuma kin ɓoye man su a ɗaki kin ga ko dole kenan na biyo sahu." Daga haka ya nufi ƙofar fita riƙe da yaron a hannunsa, ya na faɗar "Idan kin gama jin kunyar ki sanar da ni akwai maganar da na ke so muyi.." Ƙirjinta ne ya fara bugawa da ɗan ƙarfi, a ranta ta ce "Na shiga uku, me kuma zai faɗa yanzun?...." Follow me on Wattpad @ummu inteesar 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)* *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* DA KUMA *A SANADIN KAMA* WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202 DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE *AREWA WRITERS ASSOCIATION* ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Page 6️⃣9️⃣↪️7️⃣0️⃣ Haka ta ci gaba da tuna abinda ta yiwa yaya Sameer a baya har tsawon wani lokaci kafin ta tashi daga gun. @@@@## Bayan sati biyu da zuwan ta Abuja, wata rana da misalin ƙarfe goma na safe Sameer ya sauko daga sama ya same ta a falo ita kaɗai sai waya riƙe a hannun ta na karatun wani novel mai suna cikin waye? na marubuciya Fatima sunusi Rabi'u (Ummu Affan) sai share hawaye take kasancewar jarumar littafin ta bata tausayi matuƙa. Matsowa ya yi daf da ita ya tsaya, ya yi kusan minti biyar tsaye a kanta ya na kallonta, amma bata ko san yana yi ba,saboda ta yi nisa a karatunta. Da ya ga alamar idan bai yi magana ba ba za ta san da tsayuwarsa agun ba, ya saka ya tafa hannayensa guda biyu. Firgigit ta yi ta kalle shi a ɗan razane domin bata ji isowarsa gun ba. "Kukan na mene sweet sis?" Ya tambaya. Share hawayenta ta yi ta ce "Ba komai Bro, jarumar littafin ce kawai ta ban tausayi." Guri ya nema ya zauna a lokacin da yake faɗar "Da ma sistern tawa ta na da tausayi, amma ta kasa tausayawa yayanta a lokacin da yake tsananin buƙatar hakan?" Sunkuyar da kai ta yi wani hawayen na gangarowa yayin da shi kuma yake kallonta ta ce "Ka yi haƙuri yaya a wancan karon soyayya ce ta rufe min ido na kasa hango girman kuskuren dake cikin abinda na aikata, haƙiƙa na maku butulci, amma insha'allah wannan karon a shirye nake da aikata duk abinda zai gyara kuskurena na baya." Wani sanyi ya ji a ransa, ya na ganin lokaci ya yi da zai shigar da buƙatar a karo na biyu. Wani lallausan murmushi ya yi ya ce "Ki share hawayenki sister ni na yafe miki, kuma a yanzun ma za ki iya gyara kuskurenki idan kin so." Da sauri ta ce "gaya min abinda zan yi don tabbatar da hakan." Ƙara murmusawa ya yi sannan ya ce "Za ki gyara shi ne ta hanyar karɓar soyayyata a karo na biyu, za ki gyara shi ne ta hanyar yarda da ni a matsayin mijinki na sunna.." Sai da gabanta ya faɗi da ta ji kalamansa, amma bata fatar ta kuma aikata wani kuskure a karo na biyu, saboda haka ta ce "Ashirye na ke da gyara kuskure na, don haka na yi maka alƙawarin zan wanke maka dauɗaɗɗiyar zuciyarka da na yi silar ɓatawa da ruwan zallar soyayya, zan shafe maka ita da ƙyallen ƙauna domin dawo da ita a asalin yanda take kafin na gurɓata ta." Ba ƙaramin farinciki Sameer ya ji ba, ya ma kasa magana sai bakinsa dake rawa daƙyar ya buɗi baki ya ce "Alhamdulillah!" A yau wani irin farinciki yake ji wanda rabonsa da jin makamancinsa tun kafin shekara biyar da suka gabata. Gyara zama kawai ya yi a gun yana ta kallon ta, har ta ji ta tsargu ta tashi ta gudu zuwa ɗaki. Sai ranar ne kuma Sameer ya gabatar mata da tsarabarsa da ya yo masu a saudia ita da yaran. A wannan ranar Sameer bai kwanta ba sai da ya shaidawa Daddy halin da a ke ciki, shima Daddy a ranar ya samu Mimie a ɗaki ya tambaye ta, ta tabbatar masa da hakan, ya yi farin ciki matuƙa don haka a ka yanke cewar da ta gama iddarta za a sanar da iyayenta sai a yi maganar auren. Bayan wata biyu da rabi Mimie ta kammala iddarta, a ranar kuma ta juya zuwa Kano, tun kan ta isa kanon Daddy ya kira Baba ya shaida masa halin da a ke ciki, shi ma Baba ya yi murna sosai ya na ta sakawa Mimie Albarka. Bayan sati ɗaya a ka biya sadaki da komai na aure a ka saka rana nan da sati uku masu zuwa. A cikin satin farko a ka kawo lefen Mimie a Kano, lefe ne na gani na faɗa akwati goma sha biyar Sameer ya danƙaro mata, irin wanda ko a aurenta na fari bata samu irinsa ba. Mutane sun yi ta al'ajabin wannan abun, Ita kanta Mimie ta yi mamakin irin wannan kayan duk da ta san akwai abun yin fiye da haka, amma sai da ta kira Sameer ta na tambayarsa "Yaya miye haka?" Ya ce "name fa?" "Irin wannan kayan haka sai kace za ka auri wata budurwa?." Ta tambaya. Murmushi yayi mai sauti ya ce "Sweetyna ai kin fi wata budurwar a gurina, matsayinki baya da misali, shiyasa ma na yi zaman jiranki har zuwa wannan lokaci." Da alamun mamaki a fuskarta ta ce "To yanzu da ƙaddara bata ɗauke Uncle Bassam ba sai ka yi yaya kenan?" "Da a haka zan cigaba da zama har zuwa lokacin da tawa mutuwar za ta riske ni, domin ba zan iya rayuwa da ko wacce 'ya mace ba bayan ke." Jinjina kai kawai ta yi bata ce komai ba. A haka suka cigaba da hirar har zuwa lokacin da suka kashe wayar. ©©©©©© A bangaren ango shirye-shirye suke sosai, domin wannan shi ne karo na farko da za su aurar da babban ɗansu, bugu da ƙari kuma auren za a yi ne da 'yar lelensu, don haka dole a yi biki mai ƙayatarwa. Ranar da ya rage saura kwana biyar bikin, wasu daga cikin dangin Mamy da Daddy na kaduna suka je Abuja don taya murnar wannan auren. Bangaren Mimie ta ce ita ba wani shagali da za ta yi saboda ita a yanzu ba budurwa ba ce. Jin hakan ya saka Mamy ta turo wasu daga cikin 'yan uwanta zuwa Kano a ka ɗauki Amarya zuwa Abuja don gudanar da shahararren shagalin da suka shirya a can. Sameer kuwa ya ce shi komai na auren, so yake a gudanar da shi kamar yanda a ke gudanar da na saurayi da budurwa, don shi a ransa haka auren yake. Su yaya Farida, Anty Zee(matar yaya Kabir da Anty yusrah (matar yaya Sagir) ne suka yiwa Amarya rakiya har Abujan, da yake wannan ne karon farko da za su je gidan Daddy. Raliya ma ta je duk da cewa ta yi aure shekaru uku da suka wuce, amma sanin amintakar da ke tsakaninsu ya sanya mijinta bai hana ta zuwa Abujan ba. Ranar Asabar da yamma liƙis ango da tawagarsa suka ƙara Kano domin ɗaurin aure. Washe gari Ranar Lahadi Dubbunan mutane suka shaida ɗaurin auren Sameer Salman da Zuhuriyya Sadeeq Yusuf a kan sadaki Naira dubu ɗari. Ɗaurin auren da ya samu halartar manya baƙi kama daga kan sanatoci, gwabnoni da manyan 'yan kasuwa abokanan Daddy har ma da 'yan uwan Daddy da Mamy na Kaduna da abokanan arziƙinsu. Ranar murna agun Sameer ba a magana, wannan rana ce ta farin cikin Sameer, don haka ya yanke aransa duk wanda bai zo masa wannan ɗaurin auren ba acikin abokansa tabbas ya san zaman da zai yi da shi. Bayan an gama shagalin ɗaurin auren da kamar awa huɗu jama'a suka ɗunguma zuwa Abuja don gudanar da sauran shagalin, su kuma baƙin Daddy kowa ya juya zuwa jaharsa. Lokacin da suka isa garin Abuja a na ta kiraye-kirayen sallar la'asar, don haka suka tsaya suka yi salloli sa'annan suka ƙarasa masauki. Bayan magriba a ka shirya amarya cikin wata tsadaddiyar Gown mai masifar kyau dark blue, ta yi kyau matuƙa fuskar nan ta sha make-up, dama abu ga jinin Fulani sai ta fito kamar yar tsana. Idan ka gan ta sai ka rantse bata taɓa haihuwa ba, saboda gyaran da ta sha. Shi ma ango ya shiryo tsaf cikin dakakkiyar shaddarsa dark blue ya sha babbar riga, mota ɗaya suka hau zuwa hall ɗin da za a yi dinner, sauran motoci suka rufa masu baya. Su na isa parking space direban ya kashe motar, bayan samari da 'yan mata sun fir-fito, amarya da ango suka fito. A tare suka jero zuwa hall ɗin sai ƙamshi suke zubawa. Ka na ganinsu ka san sun dace da juna sosai. Ƙarasawa suka yi cikin hall ɗin suka zauna, samarin ango suka kewaye su a na ta ɗaukar hotuna. Bayan an natsa Samar ya fito domin bayar da taƙaitaccen tarihin soyayyar ango da amarya. Bayan ya karɓi speaker ya dai-daita tsayuwarsa ya fara jawabi da turanci ga abinda yake cewa: "Labarin soyayyar ango da amarya labari ne mai taɓa zuciya don haka nake so kowa ya nutsu don jin wannan labari." Shiru ya yi na ɗan lokaci sai da ya tabbatar kowa ya nutsu sannan ya ci gaba da jawabinsa kamar haka: "Soyayya ce mai cike da raɗaɗi da sanya ƙunci a zuciyar ɗaya daga cikinsu, yayana ya kasance ya na matuƙar ƙaunar amaryarsa fiye da tunanin mai tunani, shekara biyar ya kwashe ya na cikin ƙunci da raɗaɗin rashin masoyiyarsa tare da jiran ranar da za ta dawo gare shi, duk da baya da tabbaci a kan za ta dawo masa kuma bai saka rai ba, ya faɗa a cikin wani mawuyacin hali da ya sanya shi a cikin ɗemuwa da gigita, saura ƙiris ya rasa hankalinsa gaba ɗaya. Ya nisanci ƙasarsa da familynsa da kowa nasa duk a dalilin rasa soyayyarta da ya yi a karo na farko, saboda ƙaunar da ya ke yi mata ya sadaukar da farin cikinsa domin nata farincikin, ya janye zancen neman aurenta domin ta auri wanda take so." Ya na zuwa nan a jawabinsa idonsa ya fara zubar da ƙwalla, share hawayensa ya yi da handkerchief dake hannunsa, sannan ya ci gaba da cewa "Tun da nake ban taɓa ganin soyayyar gaskiya irin ta yayana ba, haƙiƙa shi gwarzon sadauki ne mai haƙuri da juriya, ga shi a yau Allah ya dawo masa da sumammen farincikinsa ta hanyar maido masa da wacce yake tsananin ƙauna, ya kuma samu soyayyarta da ya rasa a baya, haƙiƙa mai haƙuri ya kan dafa dutse har ya sha romonsa." Ya na kai nan a zancensa ya ajiye abin maganar tare da juyawa ya na sharar ƙwalla. Suma jama'ar gurin haka suka yi ta goge ƙwalla, waɗanda suke da saurin kuka kuwa harda hawayensu. Amarya Mimie ma sai da ta goge ƙwalla daƙyar ta iya haɗiye kukan da ya zo mata, sai kallon Sameer take, Ashe haka ya sha wuya a kanta? Da kansa ya janye maganar aurenta don ta rayu cikin farin ciki? Haƙiƙa ya kai akira shi da nagartaccen masoyi. Yaya Farida harda kukanta da ta ji wannan labarin. Dinner a ka yi ƙayatacciya, an ci an sha an yi bushasha da Naira kafin daga ƙarshe a ka tashi daga Dinner kowa ya koma masaukinsa..... Follow me on Wattpad @ummu inteesar. UMMU INTEESAR CE🌹🌹🌹🌹 UMMU INTEESAR CE🌹🌹🌹🌹 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)* *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* DA KUMA *A SANADIN KAMA* WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202 DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE *AREWA WRITERS ASSOCIATION* ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Page 7️⃣1️⃣↪️7️⃣2️⃣ A ranar kuma amarya ta tare a ɗakinta, da yake a cikin gidan a ka yi ma Sameer ɓangarensa. Ya so ya je wata unguwar ya siyi gida, amma Daddy da Mamy suka ƙi, sune suka nace a kan sai dai ya ajiye musu 'yarsu kusa da su, inda suke jin motsinta, domin basa son ta yi nisa dasu a karo na biyu, suna fatar ta dawo cikin ahalinsu kenan har abada, don haka a ka gyara masa wani sashe na cikin gidan kamar yadda Saheen ya ke zaune a gidan, sai dai kowa part ɗinsa dabam. An ƙawata part ɗin Sameer ɗin sosai, wannan karon ma Daddy ne ya zuba mata kayan furnitures, duk da Baba ya ce wannan karon su za su yi gyaran ɗakin ɗansu da kansu, suma sun zuba mata kaya dai-dai ƙarfinsu, duk da haka Daddy sai da yayi wani abun. An gyara mata sashenta sosai, ta samu gyara irin wanda ko farkon aurenta ba a mata irinsa ba, tabbas ta ga bambancin auren da a ka ɗaura da son ran iyaye da kuma wanda a kayi ba tare da son ransu ba. Washe garin ranar da amarya ta tare su yaya Farida suka juya zuwa Kano. Sun so su wuce da twins kamar yanda Mama ta buƙata, sai dai fafur Sameer yaƙi, ya ce shi sai a bar mi shi yaransa domin ba zai yarda a raba su da mahaifiyarsu ba, gashi ma su jira-jirai ne 'yan wata biyar, ba a ma gama shayar da su ba. ©©©© Wannan karon kam, Mommy ta zo bikin Mimie da ita a ka yi komai saboda kwaɗayi. Yaya Farida ta yi mamakin ganin yanda Mommyn ta yi kamar bata san su ba, sai harkokin gabanta take, lallai Mommy ta yi nisa acikin ciwonta na hassada. Don haka ko da suka koma Kano ma sai da ta bawa Mama labarin yanda Mommy ta nuna masu halin ko'in kula. Ita kanta Mama sosai take jin zafin yanda 'yar uwartata ta wofintar da ita, kuma take wulaƙanta ta, amma ta zubawa sarautar Allah ido. ©©©©©©%%©© A can Abuja bayan komai ya natsa, Sameer ne zaune a falonsa ya na bin Mimie da ido, yayin da take kai kawo tsakanin kitchen da dinning area ta na jejjera kulolin abinci. Kallonta ya ke cike da so da ƙauna. "Sweety!" Ya kira ta. Juyowa ta yi fuskarta ɗauke da murmushi ta ƙaraso tare da durƙusa a gabansa ta na faɗar "Ga ni ranka ya daɗe." Shi ma murmushin ya jefe ta da shi, "Tashi ki zauna a nan." Ya faɗa ya na nuna mata kan kujera kusa da shi. Zama ta yi ta na murmushinta mai burgewa, ya dube ta sosai ya ce "ke ba kya son hutawa, kin fi son kullum ki ta aiki, sai kace wacce ba ta da 'yan aiki?" "Ai na saba da aikin ne yaya, idan na zauna haka ba na jin daɗi, kuma taya zan bari 'yan aiki su yiwa mijina girki? Ai ba zai yiwu ba." Gyara zamansa ya yi ya ɗage gira sama irin ya ci serious ɗin nan ya ce "Daga yau ba na son na ji kin sake ce mun yaya, suna mai daɗi nake so ki mun." 'Yar dariya ta yi kaɗan ta ce "Sorry yaya, au na manta ka yi haƙuri Hubbyna." Ta faɗa ta na kama kunnenta da hannu biyu. Dariya su ka yi dukkan su ya buɗi baki zai yi magana kenan Mamy ta shigo falon da sallamarta, ta na ɗauke da Afeef a hannunta ta ce "Sannunka da aiki Sam, wato ka riƙe mun "ya da surutunka ka hana ta ta zo ta bawa jikokina abincinsu koh?" Miƙewa tsaye ya yi ya na faɗar "Sam ni ba ruwana a wannan maganar Mamy, laifin 'yarki ne, ita ce ta tsiri girki, nima yanzu maganar da zan mata kenan kika shigo." Daga haka ya wuce cikin bedroom ɗinsa ya na murmushi, Mimie ta taso ta durƙusa gaban Mamy cike da ladabi ta ce "Barka da rana Mamyna." "Yawwa sweet daugther, tashi ki karɓi yaron nan ki shayar da shi kafin na kawo maki ɗayan." Miƙewa ta yi tare da karɓar yaron, ta koma kan kujera ta zauna ta na shayar da shi yayin da Mamy ta juya ta fice daga sashen. @@@@@@ A bangaren Ruma abin da mahaifiyarta ke yiwa mijinta ya fara isar ta, don haka wata rana da dare a na zaune a babban falon bangaren Mamy ana ta hira, kowa ya na gun inka ɗauke Saheen da ya yi daren dawowa gida yau. Ruma ce ta kalli Mamy ta ce "Mamy ina son na bawa a halin wannan gidan wata shawara idan ba damuwa." Murmushi Mamyn ta yi ta ce "Ki faɗa kai tsaye 'yata." Janye idonta ta yi daga duban Mamy ta sunkuyar da kai ta ce "Ina ganin ya kamata a ce kun nemi maganin tsari da kuma na karya sihiri, domin a irin shahara ta Daddy da zamansa babban ɗan siyasa ga shi kuma ɗan kasuwa, na san ba za a rasa magauta 'yan hassada waɗanda dukiyar da shaharar ta tsokale masu ido ba, wani zai iya jefar sa ko ya jefi ɗaya daga cikin ƴaƴansa da sharri don haka nake bada shawarar a nemo maganin sihiri saboda...." Kasa ƙarasa zancen ta yi domin a ganinta hakan kamar fallasa asirin mahaifiyarta ne, sai dai ta na son mijinta kuma ta na tausaya masa dole ta nemo masa mafita. Muryar Mamy ce ta dawo da ita daga tunanin da take, inda take faɗar "Gaskiyar ki ne, cigaba da zancenki saboda...?" "Uhmm! Dama yaya Saheen ne nake ganin kamar da sihiri a jikinsa, saboda susucewarsa ta yi yawa, da za a nemo wannan maganin sihirin da kowa sai ya sha a huta." Ta faɗa. Daddy da yake sauraren ta tun sanda ta fara zancen, sai yanzu ya ce "Gaskiyar ki Rumaisa'u, haƙiƙa kin cika mai hangen nesa, ni da kaina na hango susucewa a tattare da Saheen, insha'allah zan nemo mana magani." Mamy ce ta karɓe zancen da cewa "Habah! Ai dole ma ki gaji Ruma, a ce mutum kullum ka na naniƙe a cikin gida? Daƙyar fa ya ke fita, yau ma sa'a a kayi ya fita har ya jima haka, ko gida fa ya raka ta ba ya barin ta, a haka zai zauna har sai ta tashi su taho tare, haka ranar da ƙawayenta suka zo, na shiga sashenta na tarar da shi zaune tare da su a falo ya ƙi ya ɗaga ya basu guri Habah! Ai abin ya yi yawa, wannan sai dai aikin asiri....." Follow me on wattpad @ummu inteesar UMMU INTEESAR CE🌹🌹🌹🌹🌹 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)* *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* DA KUMA *A SANADIN KAMA* WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202 DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE *AREWA WRITERS ASSOCIATION* ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Page 7️⃣3️⃣↪️7️⃣4️⃣ Daga haka suka ajiye hirar aka zaro wata ana yi, washe gari bayan Daddy ya je office yake labartawa abokinsa Alhaji sunusi maganar neman maganin asiri da suka yi jiya a gidansa. Alhaji sunusin ne ya kira wani babban malamin addini don ya basu addu'ar karya sihiri. Cikin abinda bai fi kwana biyar ba ya haɗa masu ruwan Ayatus-shifa kusan jarka ɗaya, ya ce abawa kowa na gidan ya sha ya shafe jikinsa safe da yamma. Godiya ya masa tare da bada abun sadaka, ya saka aka kai masa ruwan gida. A ranar da aka kawo ruwan, a ranar suka fara amfani da shi, musamman Saheen duk an fi ba shi mai yawa. Bayan wasu lokuta ya ji canji a jikinsa, shi da kansa ya yarda cewa a baya ba ƙalau yake ba. Bayan kamar sati biyu da suka fara amfani da ruwan addu'ar, wata ranar talata Mommy ta zo gidan tun sha ɗaya na safe kamar yanda ta saba yi duk sati. Kai tsaye ɓangaren 'yarta ta shiga, bata same ta ba, da ta tabbatar bata sashen nata sai ta fito, da har za ta wuce part ɗin Mamy sai ta yi tunanin ko ta na ɓangaren Mimie ne? Tunda aka kawo Mimie gidan bata taɓa leƙa bangarenta ba, yau ɗaya sai ta ji ta na so ta ga me waɗannan matsiyatan suka sakawa 'yarsu a ɗaki? Domin tun lokacin da ta share su bata kuma bi takansu ba, bare ta san sun samu arziƙi yanzu. Falon ta faɗa kai tsaye bako Sallama, ai kuwa Ruman na ciki, domin a falo ta same ta tare da Mimie su na hira, ga Affan riƙe a hannunta ta na masa wasa, yayin da Afeef ke cinyar Mimie ya na shan mama. Tsayawa ta yi ta na ƙarewa falon kallo ganin yanda ya tsaru, kuma aka ƙawata shi da kayan more rayuwa iri-iri. Nan take ciwon nata na hassada ya motsa a ranta ta ce "Kambuu... Yaushe waɗannan talakawan suka samu galihun siyen wannan kayan? Sai dai in su Alhaji ne suka mata." Nan fa ta ƙara jin tsanar Mimie na ƙara ratsa ta, kenan hakan na nufin sunyi galaba a kaina? Ai ba za ta saɓuba, goben nan zan koma gun malam a aikace mun ku." Ta faɗa a ranta. Miƙewa suka yi dukkansu su na faɗar "Laah! ga Mommy, sannu da zuwa." Ko kallon side ɗin da Mimie take bata yi ba ta dubi Ruma ta ce "Ke don baki da hankali shine za ki baro part ɗin ki ki dawo na wata ki zauna?" Ruma ta buɗi baki za ta yi magana ta gwatsale ta, ta hanyar faɗar "Ni don Allah shige mu je wawuya kawai." Har za ta wuce riƙe da Affan Mommy ta daka mata tsawa "Ki ajiye mata tsumman ɗanta ki wuce..." Jiki a saɓule Ruma ta ajiye shi, tana jin zafin abinda Mommy ta yiwa 'yar uwarta a yanzu, ta juya suka fice a tare. Sosai Mimie ta ji zafin abinda ƙanwar Mahaifiyarta ta mata a yanzu, ita ba wulaƙancin ne ya dame ta ba, kamar yanda ta kira ɗan Bassam da suna tsumma, a take tunanin mahaifinsa ya dawo mata a rai, tabbas da ya na raye da ba za a wulaƙanta masa ƴaƴa haka ba. Komawa ta yi ta zauna ta rungume yaron ta na kuka sosai, a haka Sameer ya shigo ya same ta, ya yi ta rarrashi duk da bai san waya ɓatawa shalelen zuciyarsa rai ba. ©©©©© Bayan shigarsu part ɗin Ruma Mommy ta nemi da ta zubo mata abinci da nama. Jinjina kai kawai ta yi ta shige kitchen ta ɗauko mata, domin zuwa yanzu lamarin mahaifiyar tata ya fara bata tsoro. Tana cikin cin abincin ne Saheen ya shigo gidan a hanzarce da alama ya zo ɗaukar wani abu ne. Ganin Mommy ya saka ya tsaya ya gaida ta fuskar nan ba yabo ba fallasa, domin shi yanzu mamakin ma yake me ya hau kansa ya auro Ruma? Shi dai ba sonta ya ke ba, amma saboda darajar yaron dake tsakaninsu, da kuma zumuncin dake tsakaninta da Mimiensu ya haƙura ya ci gaba da zama da ita. Sa kai ya yi zai shige cikin bedroom Mommy ta kira shi "Saheen!" Tsayawa ya yi cak, tare da juyowa ya ce "Lafiya dai?" Ta yi mamakin furucinsa amma sai ta haɗiye mamakin ta yi murmushi ta ce "Dama ƙawata ce Hajiya hafsat za ta aurar da 'yarta kuma bani da kuɗin da zan bata gudunmawa, shine na ce bari na zo na gayama na san za a samu a...." Tun bata ƙarasa ba ya ɗaga mata hannu ya na faɗar "Dakata Mommy, ina ganin girmanki a matsayinki na ƙanwar mahaifiyar Mimie da ba don haka ba, yanzun nan sai na sakar miki 'yarki ku tafi tare. A kan me za ki mayar da ni kamar wani Atm machine, kullum cikin tatsata kike kamar kin samu wata shanuwa? To daga yau na daina baki ko sulena, wanda kika ci a baya ma ya isa." A hasale yake zancen ya na gama faɗa ya sa kai ya wuce abinsa. Tun da ya fara jawabinsa Mommy ta saki baki ta na kallonsa, tama kasa haɗiye guntun naman dake bakinta tsabar mamaki, a bayyane ta ce "Aiki ya ɓaci? Shirina ya wargaje kenan? Malam baka mun adalci ba da ka bari sihirin nan ya warware da wuri haka, tun ban gama cika burina a kan Alhaji Salman da iyalansa ba." Har ya kai ƙofar ɗaki ya jiyo ta ta na sambatu cikin alamar tashin hankali, juyowa ya yi ya na faɗar "Dama Allah ba azzalumin sarki ba ne, kuma ya na kallonki duk abinda kike yi, ya aramiki lokaci kaɗan ne, yanzu kuma ya toni asirinki." Ɗan tsagaitawa ya yi kafin ya dubi Ruma ya ce "Na sake ki saki ɗaya." Ya dawo da dubansa ga Mommy ya ce "Ke kuma ga Atm card ɗinki nan na sakar miki ita ku je, Allah zai saka mana." Ya na gama faɗa ya fice daga gidan gaba ɗaya, da alama ya fasa ɗaukar abinda ya kawo shi. Hannu Ruma ta ɗora a kai ta na kuka take faɗar "Shikenan Mommy burinki ya cika sai ki tashi mu bar masa gidansa." Ta na gama faɗa ta shiga ciki ta ɗauko Sameer ƙarami, tare da mayafinta, sai ƙaramin akwatinta da ta janyo ta fito waje. Ita kuwa Mommy dasƙarewa ta yi a gun, tama rasa me za ta yi? Kuka za ta yi ko takaici zata ji? Fitowar Ruma yasa ta miƙe jiki ba ƙwari ta wanke hannunta suka fita, amma ta lashi takobin sai ta rama wannan wulaƙancin da Saheen ya mata. Ruma kam tsabar damuwa da take ciki yasa ta manta da zaman wata Mimie ko Mamy a gidan bare ta masu sallama, bin bayan Mommynta ta yi suka bar gidan. ©©©©©© Da la'asar bayan Mimie ta gama sallarta ta fito zuwa sashen Ruma don ta ga ko Mommy ta tafi? Sai dai me? Bata tarar da kowa ba a haka ta ƙaraci sallamarta, da ta tabbatar ba kowa ta wuce sashen Mamy. Nan ma bata tarar da ita ba, kasa haƙuri ta yi har sai da ta tambayi Mamy "Wai ni kam Mamyna ina Ruma ta shiga ne?" A nan Mamyn ke shaida mata bata shigo ba, hankalinta ne ya tashi ta shiga neman layin Ruman sai da ta kira ta ya fi sau biyar amma bata shiga ba, nan hankalinta ya tashi fiye da da. Bayan dawowar Saheen ne ya shaida masu abinda ya faru, ya sha faɗa agun Daddy da Mamy sosai, suka ce gobe ya je ya dawo da matarsa, ai ba ita ta masa laifin ba, sai dai ya basu haƙuri da cewa su yi haƙuri ba zai iya dawo da ita yanzun ba, sai Mommy ta gane kuskurenta, akan dole suka ƙyale shi domin 'mai ɗaki shi ya san inda ɗakinsa ke yoyo.' Mimie ta yi mamaki matuƙa na jin halin shirkar da ƙanwar Mamanta ta faɗa don kawai hassada. Ta na tausayawa makomar Mommyn tasu. @@@©©©© Bayan wata huɗu Sameer da Mimie su na cikin farinciki da kwanciyar hankali, aurensu abin burgewa ne da kwatance ga kowa. A lokacin ne Sameer ya yi mata zance komawa Bk domin su nemi a mata transfer zuwa Abuja ta ci gaba da karatunta a nan, tunda dama saura shekara biyu. Daga nan kuma sai akai twins dangin babansu su gan su. Ta yi murna sosai da wannan tunanin na mijinta, don haka ta fara shirin tafiya ba ƙaƙƙautawa.... Follow me on wattpad@ Ummu inteesar UMMU INTEESAR CE🌹🌹🌹🌹🌹 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)* *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* *RASHIN GATA* DA KUMA *A SANADIN KAMA* WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202 DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE *AREWA WRITERS ASSOCIATION* ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Page 7️⃣5️⃣↪️7️⃣6️⃣ A ranar wata Alhamis suka je Bk ita da Sameer da kuma twins, direban Daddy ne ya kai su. Gidan Innarmu suka sauka, domin Mimie bata da wanda ya wuce Innarmu a Bk, su kaɗai tasani. Innarmu ta yi murna da ganin jikokin nata yanda suka yi kyau abinsu. A can Mimie ta riski labarai kala-kala masu daɗi da akasin haka. Ko da ta je ta tarar an aurar da Shamsiyya ga wani magidanci mai shekaru arba'in, wata biyar kenan da auren, itama Sakina ana gaf da aurenta. Washe garin Ranar da suka sauka, suka je Jami'a domin yin abinda ya kawo su, kuma sun samu abinda suke neman, don haka suka juyo zuwa gidan Innarmu lokacin yamma ta riga ta yi. Suna dawowa hutawa kawai ta yi ta ci abinci, Sakina ta raka ta gidan Shamsiyya don ta ganta. Sosai Shamsiyya ta yi murnar ganin Mimie da ƴaƴan yayanta. Mimie kuwa har da ƙwallarta don ganin irin taskun da Shamsiyya ke ciki. Babban gida ne irin na family ɗinnan, mijinta ya na da mata biyu ita ce ta, gashi da ƙanne 'yan mata da kuma yaya matasa, sosai ƙannen mijin da kishiyoyi suke takura mata, cin mutunci har irin wanda bata san da shi a duniya ba yi mata suke, ga aiki da ake jibga mata kamar jaka. Ganin wannan halin da Shamsiyya ke ciki ya tunawa Mimie rayuwar aurenta da ta yi a baya, da yanda Shamsiyyar ta takura ta, tabbas Allah ba azzalumin sarki ba ne, domin ga shi ya saka mata ta wannan hanyar duk da ta riga ta yafe har cikin zuciyarta. Kallon Shamsiyya ta yi ta ce "ke kuwa Shamsiyya a haka kike jure zama da waɗannan mutanen?" Nan fa Shamsiyya ta fashe da kuka ta na faɗar "Ki yahe min Anty Mimie, na san sakamakon abinda na shuka ne na ke girba, a baya na wulaƙanta ki yau gani ƙannen miji suna walaƙanta ni na kasa yin komi, wannan ishara ce ga masu hali irin nawa, don Allah ki yahe min." Zancenta ya sanyayyarwa da Mimie jiki, duk sai ta bata tausayi don haka ta ce "Da ma ni tuni na yafe muku, Allah ya yaye miki damuwarki." Ba su suka baro gidan Shamsiyya ba sai bayan magriba. A hanyarsu ta dawowa ne Mimie ke tambayar Sakina labarin Zinnira. Sai da ta ja dogon numfashi ta sauke, sannan ta shiga bata labarin yanda rayuwa ta dawowa Zinnira da halin da take ciki na rashin lafiya ita da mahaifiyarta. Ta tausaya masu matuƙa don haka ta dubi Sakinan ta ce "Gobe ki shirya da wuri kafin mu wuce sai ki raka mu, mu dubo su." Da to ta amsa haka suka cigaba da hirarsu, Sakina ta na goye da Affan a bayanta har suka isa gida. Washe gari tun ƙarfe takwas suka shirya tare da shiga motarsu driver ya ja, Sakina na nuna masa hanya har suka isa gidansu Zinnira. Da sallamarsu suka shiga gidan, tun a ƙofar shiga ɗakin Mimie ta toshe hancinta, saboda wani ɗoyin bala'i da ya daki hancinta. Su na shiga suka same su akwance ita da mahaifiyarta, kallo ɗaya zaka musu ka fahimci su na cikin wani hali na azabar ciwo da raɗaɗi, jikinsu duk wasu marurai ne sun ja ruwa sun cika fam, wasu ma sun farfashe har da tsutsotsi ke zazzaga ta wani ɓangaren. Ɗakinsu kuwa ba komai sai ledar ƙasa da alama komai nasu ya ƙare garin neman magani. "Sannu Mama ya jiki?" Suka faɗa a tare Kai kawai ta ɗaga masu. "Sannu Zinnira." Mimie ta faɗa cikin tausayawa hawaye na gangaro mata. Daƙyar Sameer ya iya buɗar baki ya gaida su, sai alla-alla yake a tashi a tafi, domin cikinsa ya fara hautsinawa saboda a zaɓar ɗoyin ruwan maruran. Daƙyar Zinnira ta yunƙura zaune, tare da sakin wata ƙarar azaba saboda fashewar wani maruru a lokacin da take zama. Kallon Mimie ta yi idonta na zubar da hawaye ta ce "Don Allah ki yahe muna Anty Mimie, na san wannan ciwon shine ajalin mu nida innata, domin muna girbar sakamakon abinda muka shuka ne." Shiru ta ɗan yi na wani lokaci kafin ta cigaba "Mu at silar lalacewar farincikin rayuwar aurenki a gidan Bassam, duk abinda su Innarmu ka miki bayin kansu na ba, aikin sihiri na, wanda mu munka ƙulla shi don a hidda ke daga gidan ni in shiga, shi ma Bassam mu munka tahi wurin boka munka sa ya raba soyayyarku, sannan mun saci kuɗɗinai, waɗanda duk rabinsu naki na, amma a yau babu ko sisi duk sun ƙare wurin neman magani." Ta na gama faɗa ta fashe ta kukan nadama, tana ƙara neman yafiya a gun Mimie. Mimie ta tausaya masu matuƙa cikin kuka take faɗar "Na yafe maku duk abinda kuka mun na yafe, sai dai wannan ya zama ishara gareku, domin Allah ba ya yafe haƙƙin wani, kuma ya na karɓar addu'ar wanda aka zalunta, yau wa gari ya waya? Ni na yi aure na samu wani mijin wanda ya fi Bassam kamar yanda kika gani ke kuma fa?." Ta ƙarashe zancen ta na kallon Zinnira. "Na yi hasara, na cuci kaina." Zinnira ta faɗa cikin kuka. Kuɗi ta ciro a jaka bandir ɗin ɗari biyar, ta ajiye a gaban Zinnira ta ce "Ga wannan ku siyi magani." Daga haka suka miƙe suka fice, dama tuni Sameer ya bar gidan ya koma mota, saboda ba zai iya jure wannan azabar ba. A mota Mimie ta sha kukanta, dama can kuka baya mata wuya. "Allah sarki rayuwa! Allah kenan, sarki buwayi gagara misali ikonsa ya na kan komai, wai yau ni ce maƙiyana a baya suke kuka su na roƙon gafarata?, gaskiyar 'yan magana da suka ce mai haƙuri kan dafa dutse har ya sha romonsa." Mimie ce ke wannan tunanin a fili kuwa cewa ta yi "Kai! Allah ya raba mu da aikin danasani." Sameer ya amsa da Amin. Su na isa kalgo suka ajiye Sakina, ta yiwa Innarmu Sallama tare da ɗaukar kayanta ta fito waje gun mota. Har bakin mota Innarmu ta raka ta, ta na ta yiwa Sameer godiyar riƙe mata jikokinta da ya yi da amana, tare da masu addu'ar samun zaman lafiya mai ɗorewa. "Ai duk mai son Uwa dole ya so ƴaƴanta." Ya faɗa tare da ciro kuɗi a aljihun wandonsa ya miƙa mata. Ta karɓa ta na godiya. Suka yi Sallama suka hau mota sai Abuja. Bayan wani ɗan lokaci da dawowarsu daga Bk, ta koma bakin karatunta, yayin da Sameer ya ke zaune a gida zaman jiran aiki. ©©©©© Bangaren Mommy kuwa zaman Ruma a gida ya fara damunta, yanzu kimanin wata biyu kenan ta na zaune a gida amma bai zo ya maida matarsa ba, don haka ta shirya ta je gidan Hajiya hafsat domin ta raka ta gidan malaminsu a mata aikin da Saheen zai maida Ruma ɗakinta. Bayan sun je ne ta kokawa malamin nasu cewa wancan asirin da ya masu ya karye, kuma duk ɗan abinda ta samu daga hannun sirikin nata ta cinye, ga shi ya daina bata abinsa, har ma da guzurin saki ya haɗo 'yarta da shi. A nan malamin malamin tsibbun nasu ke mata bayanin sai dai ta yi haƙuri, domin yanzu akwai tsari sosai a jikin ahalin gidan gaba ɗayansu, ba wanda za su iya taɓawa. Nan fa suka yi cin mutunci tsakaninta da malamin, ta gaggaya mai maganganu, wai ya ci kuɗinta a banza, dama yasan aikinsa ba mai garantee bane don haka bata yafe ba, har da ce masa ɗan akuya, shi ko ya ce ta je za ta gani. Haka suka baro ƙauyen da yake, Hajiya hafsat na cike da tsoro, domin kalaman malamin nata sun ruɗar mata da ciki, ta san shi sarai zai iya yin komai akan wannan maganar, sai ƙirjinta ke harbawa da ƙarfi dama kuma ita ke tuƙi, su na shigowa garin Abuja kan babban titi motar ta ƙwace mata. Tun daga nan ba su kuma sanin inda kansu ya ke ba sai farkawa suka yi suka gansu a asibiti. Ko da labari ya riski Ruma hankalinta ya tashi matuƙa, da kukanta ta isa asibiti don ganin halin da Mommynta ke ciki. A asibitin ne ta kira Abbanta ta shaida masa, haka ta kira su yaya Sunil da Suhail, daga makaranta suka wuce asibitin don ganin Mommynsu. Abbansu ma washe gari ya zo. Su ma iyalan gidan Alhaji Salman sun girgiza, mussanman Mimie duk ta fi su shiga damuwa. Kowa na gidan ya damu inka ɗauke Saheen domin shi kam, ko a kwalar rigarsa. Washe garin ranar da suka samu labarin, da yamma suka je asibiti don dubiya a can suka tarar da Abban Ruma, anan ne kuma asirin Mommy ya tonu, domin Abban Ruma ya tambayi dalilin fitar da ta yi ba tare da saninsa ba har hakan ta faru. A nan Hajiya hafsat ta fallasa asirin duk wata badaƙala da ƙulle-ƙullen da suka yi tare, ta kuma roƙi gafarar Alhaji Salman da iyalansa. Abban Ruma ya ji zafi da raɗaɗin wannan abu matuƙa, take a gurin ya sake ta saki ɗaya, domin a cewarsa ba zai zauna da mushrika ba. Ya na sakinta ya juya abinsa, a ranar ma ya bar garin. Ƴaƴanta sun yi kuka har sun gode Allah. Mimie ta kira Mamanta ta na kuka, ta shaida mata halin da ƙanwarta ke ciki. Mama ta tausayawa ƙanwar tata matuƙa, don haka ta shaidawa Mimie zuwa jibi za su zo Abujan ita da Baba insha'allah, daga nan ma sai su ga ɗakinta. Bayan kwana biyu Mama da Baba suka zo Abuja, har lokacin Mommy na asibiti domin ta samu gocewar ƙashi a wasu gaɓɓanta. A wannan zuwa nasu ne komai ya dai-daita, a nan asibitin Mommy ta nemi yafiyarsu, cikin Sa'a kuwa dukkan su suka yafe mata, komai ya wuce kamar bai faru ba. Mama ta shirya da 'yar uwarta suka dawo kamar da. Bayan kwana biyu suka koma Kano. Mommy kuwa ta cigaba da jinyarta yayin da Ruma ke kula da ita. A cikin zaman jinyan da take ne wata rana Saheen ya zo har asibitin ya duba jikin Mommy, ya kuma ce ya mayar da aurensa da Ruma. Nan Mommy ta nemi ya fiyarsa ya kuma yafe mata. Bayan wani dogon lokaci aka sallame ta daga asibitin ta koma gida. Tun daga lokacin Mommy ta tuba, ta koma ga Allah ta na rokon gafararsa na shirkar da ta aikata a baya. @©©©© Mimie kuwa ta ci gaba da karatunta cikin kwanciyar hankali da nutsuwa yanzu ba ta da sauran wata damuwa, duk matsalolinta sun kau, tsakaninta da mijinta kuwa sai son Barka. Bayan shekara ɗaya Sameer ya samu aiki a ƙasar Dubai, don haka ya fara shirye-shiryen tafiya, amma ita Mimie a nan Abuja zai bar ta har ta kammala karatunta, wanda ya rage saura Shekara ɗaya. Twins kuma yanzu shekarunsu biyu, sun yi wayo abinsu har su na magana da gudu a ko'ina. A ranar wata Laraba Sameer ya yi Sallama da iyayensa da 'yan uwansa domin a ranar ne jirginsu zai cira zuwa Dubai. Bayan tafiyarsa Mimie ta sha kuka, domin ganin take kamar ba zai dawo ba, tunawa ta yi da lokacin da suka rabu da Bassam lafiya ƙalau, cikin ƙaunar juna sai gashi an dawo mata da shi cikin wani mawuyacin hali kuma ya mutu a gaban idonta, wannan abun ya tsaya mata a rai sosai, duk lokacin da ta tuna shi, sai ta zubar da ƙwalla tare da masa addu'ar samun gafara. To yau ɗin ma haka ne a bayyane ta ce "Allah ya jikan ka, Uncle, Allah ya maka rahama uban ƴaƴana, ka tafi ka bar ni da marayun ƴaƴanka, a yau wanda ke kulawa da su ma ya tafi, banda tabbacin sake haɗuwa da shi.." ta faɗa ta na rushewa da wani sabon kukan...... Follow me on wattpad @ummu inteesar RUKY I LAWAL CE🌹🌹🌹 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *A SANADIN KAMA* 👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻👰🏻 *DAGA ALƘALAMIN: RUKAYYA IBRAHIM LAWAL (UMMU INTEESAR)* *MARUBUCIYAR: SOYAYYAR MEERAH* *Y'AR GANTALI* *RIKICIN MASOYA* DA KUMA *A SANADIN KAMA* WANNAN LITTAFIN NA KUƊI NE AKAN NAIRA 200 KACAL GA MAI BUƘATA SAI YA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 08109634202 DON ALLAH IDAN KA SIYA KADA KA FITARMIN HAƘƘIN MALAKA NAWA NE *AREWA WRITERS ASSOCIATION* ________________________________ *AREWA WRITER'S ASSOCIATION* _________________________________ *💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦* _________________________________ https://www.facebook.com/104534761033461/posts arewawritersassociation@gmail.com *BISMILLAHIR RAHMANIR-RAHIM* Page 7️⃣7️⃣↪️7️⃣8️⃣ 🔚🔚🔚🔚🔚🔚 Bayan tafiyar Sameer da kamar sati uku Mimie ta fara laulayi, ashe ko da Sameer ya tafi ta na da ciki wata ɗaya, sai dai duk a cikinsu ba wanda ya lura, sai yanzu ne ta lura da hakan, amma sai ta yi gum da bakinta bata faɗawa kowa ba, har shi Sameer ɗin gudun kada ɗoki ya sa ya kasa gudanar da aikinsa cikin nutsuwa. ©©©©©© A Dubai kuwa Sameer ya na gudanar da aikinsa cikin ƙwarewa da jajircewa, ya bada himma sosai ga aikinsa, domin yanzu zaman Dubai ya na masa daɗi ba kamar da ba. A yanzu ba yada damuwar komai, kullum ya kan yi waya da ahalinsa da kuma matarsa. ©©©©©© A bangaren Mimie kuwa ta ci gaba da renon cikinta da kuma tagwayenta ba tare da ta nuna gazawa ba. Mamy ce ta lura da yanda yanayin Mimien ya canza, abinka da manyan mata nan da nan ta fahimci cewa Mimie tana da ciki. A nan fa Mamy ke cewa "y'ata ko dai mun samu ƙaruwa ne?" Da murmushi a fuskarta ta ɗan dubi Mamy ta ce "Ta me fa Mamyna?" Ba wai don Mimie bata gane ba ne ta yi wa Mamy wannan tambayar, a'a sai dai don ta na tsananin jin kunyarta ne. 'Yar dariya Mamy ta yi ta ce "Yata kenan, ina nufin ko kina da ciki ne?" Ba ta amsa tambayar Mamyn ba sai ma sunkuyar da kanta ƙasa da ta yi, a nan Mamy ta fahimci hasashen ta ya zama gaskiya. Cikin matuƙar jin daɗi ta ce "Masha'allah! Allah ya nuna mana lokacin fitowar wannan Babyn lafiya, wannan daddaɗan labari ne, kin gayawa Sam kuwa?." Gyaɗa kai ta yi alamar a'a. Mamy ta ce "No wonder, shiyasa ban ga ya fara zumuɗi ba, ai ko ya kamata ya sani." Sai lokacin Mimie ta ce "Mamy na san halin Yaya Sameer ne, yanzun ana gaya masa, zumuɗi zai hana shi gudanar da aikinsa cikin nutsuwa shiyasa na yi shiru." Daga haka suka ajiye wannan maganar suka zaro wata chapter. A taƙaice dai Sameer bai samu labarin cikin Mimie ba sai da cikin ya kai wata biyar, a nan ma ba faɗa masa ta yi ba, shine ya lura da hakan lokacin da suke vidio call. Shine ya ke tambayar "Sweetyna yaya kodai mun samu ƙaruwa ne?" Bata ce komai ba sai murmushi da ta yi, a nan ya tabbatar da zarginsa, ai kuwa ya hau murna, farincikinsa ya kasa ɓuya. Tun daga ranar baya da aiki sai jibgowa Babynsa kaya, komai ya gani mai kyau na jarirai sai ya siyi wanda zai yi dai-dai da sawar maza ko mata ya ajiye, daga wannan ranar ne kuma ya fara irgen watannin da suka rage na haihuwa sai zumuɗi ya ke. Lokacin da cikin Mimie ya shiga wata na tara, Sameer kasa haƙuri ya yi har sai ta haihu sannan ya koma Nigeria, don haka ya harhaɗa kayansa ya dawo Nigeria zaman jiran Babynsa. A ranar da cikinta ya cika wata tara da sati biyu, ta haifi 'yarta ƙatuwa masha'allah. Sameer ya yi matuƙar farinciki da haihuwar nan, da yake a asibiti ne ta haihu, su Mommy da Ruma sai Mamy sune tare da ita a ɗakin bayan an gama shirya su ita da jaririyarta. Sameer ne ya shigo ɗakin fuskarsa cike da annuri, ba ya da burin da ya wuce ya ga fuskar 'yarsa. Cikin hanzari ya isa gun Mamy dake riƙe da 'yar a hannunta, ya miƙa mata hannu, ba ko kunya ya ce "Mamyna miƙo mun 'yata naji ɗuminta." Harararsa Mamy ta yi, ta nuna masa Mommy dake zaune a gun da ido, alamar ya gaida ta. Amma inah! Shi yanzu ba Gaisuwar ba ce a gabansa, 'yarsa yake muradin ji a tafin hannunsa, don haka ya yi mirsisi. Ita ko Mamy ganin ya yi kunnen uwar shegu da nuninta sannan yaƙi janye hannunsa, ya sa ta haƙura ta miƙa masa 'yar tana mai jin kunya, "yayan zamani basu da kitsen ido." Ta faɗa a ranta. Cikin azama ya karɓi 'yar ya rungume ta tsam a ƙirjinsa, sai ko ga hawaye shaaa! Faɗar ya ke "Alhamdulillah! Allah abin godiya, ashe ina da rabon ganin wannan 'yar" Matsawa kusa da Mimie da ta fito daga toilet ɗin ɗakin ya yi ya na faɗar "Sweety ashe da rabo a tsakaninmu? Ashe rabon wannan 'yar ne ya saka na nacewa soyayyarki? Shi kenan yanzu mun kuma zama jini da tsoka, dama can kina a cikin ahalinmu." Da alama ya ma manta da mutane a ɗakin. Ganin haka ya saka Mamy da Mommy suka bar masu dakin, Mamy na sharar ƙwallar tausayi, saboda tunawa da ta yi da rayuwar da ɗan nata ya shiga a baya. Tun a asibitin Sameer ya yiwa 'yarsa huɗuba da sunan *Rukayya* wato sunan ƙanwarsa Margayiya Real Mimie ta ci, za su dinga kiranta da Little Mimie. Bayan Mimie ta huta sosai aka sallame ta daga asibitin suka koma gida. Tun ranar da ta haihu Mommy ta tare a gidan, domin acewarta ita ce za ta kula da 'yarta da kanta kafin ƙarasowar mutan Kano, da yake har lokacin Abbansu Ruma bai sauko ba bare ya mayar da aurensa. Ana saura kwana uku suna 'yan Kano suka zo. Ranar suna aka yi shagali sosai, Naira ta yi kuka domin kam an kasheta a sunan 'yar gata, a gurin zanen sunan ma maroƙa sun yagi rabonsu. A wannan ranar gaba ɗaya iyalan gidan alhaji Salman su na cike da tsantsan farin ciki, kuma sun yiwa Allah godiya da ya dawo masu da walwalarsu a lokacin da basu yi tsammani ba. Da farko ya aiko masu Zuhra a matsayin wacce za ta zama jagoran dawo masu da sumammen farincikinsu, yanzu kuma ya azurta su da samun 'yar da take kama sak da Mimiensu daga tsatsonta, 'yar kuma da ba su da a familynsu, ba abinda za su ce sai dai su ƙara godewa mahaliccin bayi mai jinƙai da Rahama ga bayinsa. Bayan watse taron suna da kamar sati biyu, Daddy ya yi-ya yi Sameer ya koma bakin aikinsa amma ya ƙi, ya kafe shi lallai ba inda zai je sai tare da matarsa. Mamy kuwa ta yi tsayin daka akan cewa ba inda zai je da Mimie har sai ta yi kwana tamanin da haihuwa don haka ya je kawai. Wasa-wasa ƙaramar magana ta zama babba domin yanzu kusan wata ɗaya kenan amma Sameer ya ƙi ya koma, daga gun aikin nasa ma sai kiransa ake a na buƙatar ya dawo amma ya ƙi. Ganin haka ya saka watarana da yamma Daddy ya sami Mamy akan maganar, ya ce "Mamyn yara, ki yi haƙuri ki bawa Sam matarsa ya tattara ya tafi, domin wannan al'ada ce ba fa addini ba, kuma ma ai ta yi arba'in ɗaya, idan ma baki amince da hakan ba, sai Mommynta ta shirya su tafi tare hakan zai fi mana kwanciyar hankali." Da farko Mamy ta so ta yi gardama, amma kasancewar wannan ba dabi'arta ba ce yin musu da maigidanta, don haka ta haƙura ta ce "Shikenan Alhaji tun da ka faɗi haka, sai a nemawa Mommyn nasu visa ta bi su can, tun da ma ai batada miji a yanzu." Da wannan shawarar suka kawo karshen maganar tafiyar, kowa ya fice zuwa yin sabgar gabansa. Da dare Mamy ta kira Sameer ta shaida masa shawarar da suka yanke ita da Daddynsa. Bai Musa ba, saboda shi ma zai so matarsa da 'yarsa su samu kulawar da ta dace a wannan stage ɗin, wanda shi ba zai samu damar yin hakan ba saboda aikinsa. "Nagode Mamy Allah ya ƙara girma, sai a gayawa Mommyn ta shirya da wuri koh?" Ya na gama faɗa ya miƙe don zuwa makwancinsa. Alhaji Salman da kansa ya nemarwa Mommy visar, ta kuwa shirya tsaf, bayan sati biyu ta yi Sallama da ƴaƴanta ta bi su ƙasar Dubai. Da yake zuwa lokacin Mimie ta kammala digirinta, ta yi komai ta haɗa takardunta kawai ta bi mijinta ƙasar Dubai. %©©©© Bayan saukarsu a Dubai, Rayuwa mai daɗi suka shimfiɗa cike da so da ƙaunar juna, ganin twins sun yi baki sosai domin yanzu shekarunsu uku, hakan ya saka Sameer ya nemo masu makarantar nursery mafi kusa da gidansa a can, ya saka su. Bayan wani ɗan lokaci, Mimie ta shiga jami'ar da ya kammala, don yin masters ɗinta A nan. Su Mommy an zama mutanen Dubai sai shanawa take abinta, a zaune take ta na tunani "Allah karimun, yau gata a cikin dukiyar Alhaji Salman ko ta ce ta ɗansa ta na watayawa yanda ta so, tabbas da ta san da zuwan wannan ranar da ba ta yi gangancin faɗawa shirka ba, ashe gajin haƙuri ta yi, ta fitar da maitarta a fili, ashe wannan lokacin da take fata har ta kauce hanya akansa zai zo mata cikin sauƙi da ta kwantar da hankalinta. "Astagfurullah! Astagfurullah!! Allah ka yafe mun haƙiƙa a baya ina cikin ɓata mabayyaniya." Ta faɗa a fili. ©©©©©%%% Bayan kamar wata uku da komawarsu Dubai wani tashin hankali ya Kunno Kai acikin rayuwarsu. Bakomai ba ne ya ɗaga hankalin dukkanninsu face rashin lafiyar Sameer, a hankali ciwon ya fara shigar shi, abun ya fara mai da yawan kasala, wasa wasa ciwo sai daɗa gaba ya ke, domin yau kusan satinsa biyu kenan ba ya fita aiki, sai dai ya ba da uzurinsa akan cewa ba shi da lafiya ne. Duk da cewa a zahirin gaskiya ba wannan ne karo na farko da Sameer ya fara fuskantar irin wannan matsalar ba, tun bayan tafiyarsa Dubai a karo na biyu bayan aurensu kenan ya fara jin wannan yanayin, sai dai a tunaninsa ko gajiyar aiki ce da sauran abubuwan da ba a rasa ba. Amma zuwa yanzu ya tabbatarwa kansa cewa akwai wata cutar da take addabarsa, don haka ya yanke shawarar zuwa ganin likita. Ya na daga kwance kan gadonsa ya kalli Mimie dake zaune a gefensa ta na sharar hawaye ya ce "Ki daina kuka Sweety, cuta fa ba mutuwa ba ce, yanzu dai dauko wayata ki kira mun Abokina doctor Sadeeq, ki ce na ce ya zo ya kai ni asibiti." Ya ƙarashe maganar daƙyar da alama ya na shan wuya sosai. Hawayenta sun kasa tsayawa, bata iya cewa komai ba, sai janyo waya da ta yi ta dannawa doctor Sadeeq kira. Bugu biyu ana uku ya ɗaga, ta shaida masa saƙon abokinsa, cikin hanzari ya fito daga asibitin ya nufo gidan Sameer. Ganin yanayin Sameer ɗin ya ruɗar da shi saboda haka ba jinkiri ya saka shi a mota, Mimie ma ta faɗa motar hankali a tashe, Sadeeq ya tada motar cikin hanzari ya nufi asibitinsu. Yayinda suka bar Mommy a gida ita da yara sai masu aikin gidan. Gwaje-gwaje da aune-aune aka hau yi masa, sannan aka shiga ba shi agajin gaggawa, kafin fitowar sakamakon binciken. Hankalin Mimie a tashe yake ta kasa tsaye ta kasa zaune, sai zarya take a harabar asibitin ta na kuka, gani take kamar za ta rasa shi kamar yanda ta rasa Bassam a rana mai kamar ta yau. Bayan wani lokaci sakamakon gwaji ya fito nan take aka gano cutar hapatatis a jikinsa(wato ciwon Anta) a nan doctor Sadeeq yake mata bayanin hakan ta faru da shi ne sakamakon shan giya da ya ɗau lokaci ya na yi a baya. Hankalin Mimie idan ya yi dubu ya tashi, miƙewa ta yi daga kan kujerar office ɗin da take zaune, ta fara kai-kawo a filin ɗakin ta na kuka, doctor na ƙoƙarin mata bayanin mafita amma ina! Bata saurare shi ba sai ci gaba da kukanta ta ke ta na faɗar faɗar "Shikenan, yanzu kai ma yaya Sameer haka zan rasa ka kamar yanda na rasa Uncle? A baya na rasa uban ƴaƴana, yanzu kuma zan rasa wanda ya tarairaye su kamar ƴaƴan cikinsa, kuma zan rasa uban 'yata a karo na biyu? Ka da ka mutu kabarni a ƙasar da ba ni da kowa sai kai da ƴaƴana, Ya Ubangijina kada ka ɗora min ƙaddara da ba zan iya cinyewa...." Kuka ne ya ci ƙarfinta ta kasa ƙarasawa sai komawa da ta yi ta zauna a inda ta tashi daga farko. Anan doctor Sadeeq ya shiga rarrashinta, daƙyar ya ciwo kanta da kalaman tausasa zuciya domin ya tausaya mata matuƙa. A nan ya tabbatar mata cewa akwai mafita, mafitar kuwa ita ce a yanzu za'a ɗora shi akan magani domin cutar bata riga ta yi nisa ba, idan ya shanye maganin bai ji sauƙi ba za'a masa aiki. Ta ɗan nutsu amma ba don hankalinta ya kwanta ba, ranar a asibitin ta kwana, duk da doctor Sadeeq ya shaida mata su na masu kula da mara lafiyar ta je gida kawai, amma haka ta kafe sai da ta kwana, sai dai ta yi waya ta shaidawa Mommy halin da ake ciki, ita kuwa Mommy ta kira Mamy da Mama ta shaida musu domin su taya su da addu'a. ©©©©©© Hankalinsu Daddy ya tashi fiye da tunani, a lokacin da labarin rashin lafiyarsa ya riske su daga nan suka duƙufa da addu'a ba dare ba rana. Daga ƙarshe Daddy kasa haƙura ya yi sai da ya shirya shi da Mamy suka je Dubai don duba lafiyar ɗan nasu. Alhmdulillah sun same shi jikin da sauƙi, amma hankalin Daddy bai kwanta ba don haka ya saka hannu kawai don a yi masa tieter, tunda wannan ita ce mafita ta ƙarshe da ake hangowa kafin abin ya yi nisa. Daddy da Mamy ba su baro Dubai ba sai da suka tabbatar an yiwa Sameer aiki ya ji sauƙi, da yake a can suna da kwararrun likitoci, an ɗora shi akan magani ya na sha, likitoci suka tabbatar masu da cewa insha'allahu cutar ta tafi kenan, muddin zai tsare magani don dama kaɗan ta fara kama hantarsa. A tare suka juya zuwa Nigeria da Mommy bayan ta share watanni a can. Bayan Sameer ya ji sauƙi rayuwar ta komo kamar da mai cike da annashuwa. Ruma ma ta kuma haihuwa ta biyu, ta samu ɗa namiji da ya ci sunan Salman ake masa inkiya da (Ashraf). ©©©©©©©©©©© Bayan Shekaru biyar Sameer ya zama ƙwararren likita a ɓangarensa, a wajen Mimie ma haka ne tuni ta gama masters ɗinta ta fara aiki a asibitin da mijinta ke aiki, kowannensu ya yi kyau abinsa, duniya ta zamar masu sabuwa kamar basu fuskanci wani ƙalubalai ba a baya. Mimie ta sake haihuwar ɗa namiji wanda ya ji sunan Abubukar Sadeeq suna yi masa inkiya da (Abba) kasancewar sunan babanta aka sakawa yaron. Affan da Afeef sun girma sun zama 'yan samari, yanzun su na cikin shekara ta tara kenan a rayuwarsu, su na primary4 amma wayon yaran ya wuce na shekarunsu, a lokacin ne kuma Little ta cika shekara biyar ta na nursery 2 yayin da Abba yake da wata tara a duniya. Sameer ya zama magidanci mai shekaru arba'in da ɗaya a rayuwarsa yayin da Mimie take da shekaru 31, kamar yanda gangar jikinsu da shekarunsu ke ƙaruwa haka kauna, soyayya da shakuwarsu take ƙaruwa. Ko waye kai idan ka ga iyalan Sameer dole su birge ka, don kuwa Sameer ba ya nuna bambanci tsakanin ƴaƴansa da na Bassam, duk da cewa ya na tsananin ƙaunar little a rayuwarsa sai ya ɓoye hakan a ƙasan ransa, domin a zahiri ya fi nuna ƙaunar 'yan biyu, hakan kuwa ba ƙaramin daɗi yake yiwa Mimie ba. Da yammacin wata ranar Lahadi dukkanninsu su na gida kasancewar ranar hutu ce. Alhaji Sameer ya na zaune a falo ya na karatun jarida, Mimie kuwa ta na kitchen ta na girkin rana, Affan ne ya shigo ɗakin da gudu yayin da Afeef ke binsa a baya, ƙarasowa yayi gaban Sameer ya zauna ya na faɗar "Dad don Allah ba ni ne Aliyu B. Aliyu ba, shi kuma Bassam B. Aliyu?" ya ƙarashe zancen yana nuna hausaininsa. Murmushi manya Sameer ya yi kana ya daga kai alamar tabbatarwa ya ce "Hakane." "Yawwa Daddy wai to me yasa a makaranta ake kiran little da Rukayya Sameer amma mu sai a ce mana B Aliyu?, Ga shi kuma kai sunanka Sameer ko Dad?" Afeef ya watso masa tambayar da ba zato ba tsammani. Jikinsa ne ya yi sanyi ƙalau, hakan ya saka ya miƙe tare da ajiye jarida ya shige ɗakinsa ya rufo ba tare da ya ba su amsa ba. Mimie dake kitchen ta na jin duk abinda suke faɗa, goge hawayen da ya zubo mata ta yi, ta na ganin lokaci ya yi da za su koma Nigeria domin sada su Affan da ahalinsu, saboda tun zuwansu ƙasar nan su Innarmu basu kuma ganinsu ba, har labarin mutuwar innarmun ya riske ta. Kashe gas ɗin ta yi ta sauke miyar, sannan ta nufi ɗakin mijinta mai tsananin tausayi da jinƙan marayun ƴaƴanta, ta masa magana akan tafiyarsu Nigeria. "Hakan shi ne dai-dai, ki bari sai mu ɗauki hutu daga gun aiki sannan mu saka rana." Ya na gama faɗa ya shige toilet don watsa ruwa. Mimie kuwa ta na nan a inda ya bar ta ta na tunanin rayuwa, ta na ƙara godiya ga Ubangiji buwayi gagara misali, wanda ya halicci bayinsa ya sanya wani sashensu yake kama da sashe, cikin hikimarsa da iyawarsa ya sanya siffofinta suka yi kama da na 'yar bayinsa masu jinƙai da tausayin talaka. Ga shi yau *A SANADIN KAMA* Rayuwarta da ta iyayenta da ƴaƴanta ta haskaka, ita kam tsakaninta da Margayiya Mimie sai dai addu'ar dacewa da rahamar ubangiji, domin a silarta ta samu wannan gatan da bata taɓa hasasowa ba ko da a duniyar mafarkinta. Tabbat bi hamdillah, duka_duka a nan na kawo ƙarshen wannan ƙayataccen labarin mai cike da faɗakarwa tare da wa'azantarwa da fatar masu karatu kun ɗauki darasi a rayuwar Mimie da sauran jarumai littafin. Ina rokon Allah ya yafe mun kuskuren dake ciki ya ba ni ladan faɗakarwa. Sai mun haɗu daku a cikin sabon littafi na, wanda zai zo da sabon salo littafin da zai ɗarsa tausayi da tsoron Allah a zukatanku *HALITTAR ALLAH CE* Shine sunan littafin ya na nan tafe very soon. Mai son farin cikinku ce. RUKY I LAWAL🌹🌹🌹🌹🌹 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels