https://chat.whatsapp.com/LH7GN3pMRE26T5G5xcTmmw *🌹A JINI TAKE🌹* *(IZZATA)* By _*Zarah Maitama (Mhiz Innocent)*_ _Bismillahir rahmanir raheem_ _*CHAPTER ONE*_ Page _01 __La'asar ce sakaliya dan kuwa rana ma ta kusa faɗuwa. Babu laifi akwai iska, irin iskar nan me daɗi, duk da ba lokacin sanyi bane, se dai yanayin garin sosai yayi kyau da kuma daɗi. 'Yan mata ne guda biyu ke tafiya sanye cikin hijab dogo har ƙasa kala ɗaya. Ɗayar da niƙab a fuskarta ta saƙala jaka a kafaɗarta, yayin da ɗayar ke sanye da hijab kawai. Hannun wadda ke sanye da niƙab riƙe yake da wani ƙaramin kyakkyawan yaro, fari ƙall da shi, wanda ba ze wuce 5years ba sanye cikin uniform, wanda hakan ya alamta min cewar daga Islamiyya suka dawo. A hankali na kai dubana zuwa fuskar wadda babu niƙab a fuskarta, kwata_kwata kyakkyawar fuskarta ta babu annuri, da alama wani abun ne ya ɓata mata rai ko kuma akayi mata. Se dai duk da yadda fuskarta ta ke a haɗe hakan be hanani ganin tsagwaron kyawun fuskarta ba, wadda idan ba dan shigar da ke jikinta ba da kai tsaye zan iya kiranta da balarabiya, dan kuwa komai na ta yayi kama da nasu, dara_daran idanu masu ɗauke da baƙar ƙwayar ido me matuƙar ɗaukar hankali da wani irin ƙyalli, dogon siririn hancinta da ke zaune ɗass akan fuskarta kamar an zama, se kuma ɗan ƙaramin red lips ɗinta me matuƙar kyau wanda shi ne yafi komai ƙawata fuskarta. Har suka ƙarasa gida babu wadda tace da er uwarta komai. Babban gida ne me kyau sosai, duk da ba wani ƙyale ƙyale ne a gidan ba amma kasancewarsa me girma da kuma yanayin ginin gidan na zamani ne yasa ya ƙawatu matuƙa. Tun a parlour AFAAF ta jefar da jakar hannunta da tun da suka fito daga makaranta ta kasa maƙalata a kafaɗa se riƙeta tayi a hannu, wucewa ɗaki tayi kamar wadda aka kora. Ammi ta bi ta da kallo kafin ta dawo da kallan nata kan AFRAH dake kwance niƙab ɗinta tace "Ke lafiya kuwa? Yau kuma me aka yiwa Afaaf?" Dariya wadda aka kira da Afrah tayi daidai lokacin da ta ida kwance niƙab ɗin fuskarta, wanda hakan ya bani damar ganin kyakkyawar farar fuskarta wadda kallo ɗaya na mata na gane ita ɗin er biyun Afaaf ce, dan kuwa kamarsu ɗaya sak, kamar yadda Afaaf ke da manyan idanu haka Afrah ke dasu, dogon hanci da ƙaramin baki me kyawun gaske haka Afrah ke da shi, ba dan tsayawa nayi ina kwatanta muku kamanninta ba da bazan iya gano wani banbanci a tsakaninsu ba, saboda kamarta su ta ɓaci, banbancin da zan ce na gano guda ɗaya ne shi ne, saɓanin Afaaf da ke ɗauke da baƙar ƙwayar ido ita Afrah brown ne da ita me maiƙo. "Tubarkallah Masha Allah!" Shi ne abin da na faɗa sanda na sake tabbatar da lallae waɗannan en biyun irin waɗannan da ake kira da identical twins ne, se dai su waɗannan nin sun fita daban ta hanyoyi da dama, a ƙiyasce ba zasu wuce 17 years ba, kowaccensu na da kyawun jiki me kyau, hatta kuma da jikinsu ba zaka iya banbance wani banbanci ba dan kuwa dukansu basu da ƙiba. "Ammi ita da Gwani ne.." Afrah ta faɗa da siririyar muryarta me daɗi wadda ke ɗan rawa a duk sa'ilin da take magana, zaka ɗauka tsoro ko wani abun makamancinsa ke sanya muryarta ta rawa, se dai ba haka bane, haka muryarta ta take a halitta, hakan kuma shi ke ƙara ƙawata muryarta ta ta sake zama ta daban. "Gwani kuma? Me ya faru? Wani abun ta sake yi?" Ammi tayi tambayar a jere. Girgiza kai Afrah tayi kafin tace "A'ah Ammi, kawai dai an chanja mana malami ne, yanzu Gwani AFFAN ne malamin ajinmu." "Auu shi ne take fushi saboda makarantarta ce ko kuwa me?" Ammi ta faɗa a ɗan zafafe. Se da Afrah ta ɗan yi kalar tausayi da fuskarta gudun kada Ammin ta fusata sosai sannan tace "A'ah fa Ammi, ita abin da ya ɓata mata rai yadda ya aiko wai a faɗa gobe ze fara da karɓar hadda." Tsaki Ammi ta ja tana girgiza kai, wannan hali na Afaaf na ƙona mata rai wani lokacin, kamar ba za tace komai ba se kuma tace "Idan ta so kada tayi, zata haɗu da ni ko da Abbanku." Daga haka ta miƙe ta bar parlourn. Bin ta da kallo Afrah tayi ba tace komai ba se dauke ajiyar zuciya da tayi sannan ta dawo da dubanta cikin ɗakin kana ta miƙe ta wuce ɗakinsu. .. Se da Afrah ta gama komai sannan ta koma kan gado, ta ɗauko Qur'an ɗinta dake cikin jaka ta buɗe ta soma karantawa. Tana cikin yin karatun Afaaf ta fito daga toilet da alama wanka tayi, ta ƙarasa ta shirya cikin kayan bacci sannan ta dawo kan gadon tana ƙoƙarin kwanciya. Rufe Qur'an ɗin Afrah tayi sannan tace "Me za ki yi?" Se da ta harari gefe sannan tace "Bacci zan yi." Karo na farko kenan da na fara jin muryar Afaaf wadda itama cikin ikon Allah muryarta su iri ɗaya ce, dan idan wata a cikinsu ma tayi magana ko da ka sansu ba zaka banbance ba se dai idan ka ga fuskarsu. "Malama ki ɗauki Qur'an ki yi karatu, kin san dai halin Gwani." Se da ta tura baki sannan tace "Ai yau so nake na ƙure shi wallahi, mutum se faɗin rai da nuna shi wani ne bayan ba kowa bane. Ban da tsabar iyayi meye na wani cewa ze karɓi hadda a ranarsa ta farko a ajinmu? Ni babu haddar da zan yi." Ta faɗa tana neman waje zata kwanta. Da sauri Afrah ta riƙota tace bayan ta haɗe rai "Lulu ki fita a idona wallahi. Gwanin kike faɗa wa haka? Ki tashi malama ki yi karatu kin san dai ba ɗaukar iskancinki ze yi ba." "Don Allah Didi ki ƙyaleni." Afaaf (Lulu) ta faɗa a ranta tana sake tuna wannan ƙarfa_ƙarfar da Gwanin ke ƙoƙarin yi. Cika hannunta Didi tayi kana ta haɗe fuskarta waje ɗaya ta cigaba da haddarta a zuciya. Ita kuwa Lulu kwanciyarta tayi, se dai yanayin yadda ta ga fuskar Didin ya hanata yin baccin. Tsaki ta ja a hankali ta miƙe zaune tana tura baki. Ita kuwa Didi ko kallanta ba tayi ba, duk da dama ta san Lulun ba zata iya kwanciya tana fushi da ita ba. Sauka Lulu tayi ta ɗauko Qur'an ɗinta ta koma kan gadon itama, bata kalli Didi ba ta soma karatunta a zuci, se dai ba haddar take yi ba, dan kuwa ta riga ta ƙudurcewa kanta ba za tayi haddar ba, se dai kawai ta shiga muraja'a hankalinta kwance. Ta riga Didin idarwa, da ta ga har lokacin bata kalleta ba se ta ɗora kanta akan kafaɗar Didin da itama take kan aya ta ƙarshe a maimaita haddar da take yi. Se da ta idar sannan ta saka hannunta ta buge kan Lulun. Tura baki Lulu tayi kafin tace "Kai Didi, nayi karatun fa. Kiyi haƙuri." Murmushi Didi tayi dan itama ba wai tana fushi da Lulun bane kawai dai ta ɓata ranta ne dan tayi karatun, dan haka tace "Toh na ji, amma dai ki dena abin da kike yi musamman akan Gwani Affan, ni ban san me ya tare miki ba!" Taɓe baki Lulu tayi dan ita sam bata da buƙatar jin magana akan Gwanin, ko a makaranta ne kuwa ballantana a gida. "Haka kawai fa Didi, ɗaga kansa yayi yawa kuma..!" "Ni kam ya isheni haka nan Afaaf, ke kodayaushe zancenki kenan!" Riƙo hannun Didi Lulu tayi kafin tace "Pls Didi mu bar maganar nan, Allah kuwa raena ɓaci yake yi." "Naa ji." Didi ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa. Langaɓar da kai Lulu tayi kafin tace "A'ah fa Didi, ta yaya zan san kin haƙura.. Smile.." ta faɗa tana murmushin da ya sake fiddo da ainahin kyawunta. Itama Didin murmushin tayi wanda hakan ya sake ruɗani akan tsananin kamarsu da ta sake fitowa fili, dan komai na su iri ɗaya ne hatta da murmushin kuwa. ... Washegari wajen ƙarfe 2 da rabi Didi ta gama shirin Islamiyya, tana kallan Lulu da tun dawowarsu daga boko ta kwanta a kan gado ita a lallai bata da lafiya. Kasancewar sun makara ne ya sanyata saurin ɗaura niƙab ɗinta a jikin ƙaton mudubinsu me kyau sannan ta ɗauki jakarta ta fito. Kallanta Ammi tayi tace "Har kun shirya? Ba zaki tsaya ki ci abinci ba?" "A'ah Ammi sauri nake yi, kada na makara. Idan na dawo zan ci.." "Toh Allah ya tsare.." ta ƙare maganar tana kallan hanyar ɗakinsu "Ina Afaaf ɗin?" Kallan ɗakin tayi sannan tace "Ammi wai bata da lafiya.." Kafin Ammin ta sake cewa komai Abba ya shigo cikin ɗakin da sallama. Dogon babban mutum wanda kallo ɗaya zaka masa ka san twins ɗin nan shi suka biyo, dan kuwa shi ma a kallan farko zaka gano kyawun da yake da shi. Dukkansu suka amsa masa sallamar kafin Little ya tafi ya rungume shi. "Abba sannu da zuwa." Afrah ta faɗa. "Yawwah Didi an shirya ne?" Ya faɗa mata sunan da yawanci en gidan ke kiranta da shi, wanda har shi ɗin ma wani sa'in ya kan kirata da shi. "Ehh Abba.." "Toh Allah ya bada sa'a.. A'ah ina Afaaf?" Ya tambaya shi ma. A wannan karon ma se da ta sake kallan ƙofar ɗakin nata sannan tace "Abba wai bata da lafiya." "Ji min ja'irar yarinya, sauƙin ze sameta ne tana daga kwance.. Kai Little maza je ka tasota ta sha magani sauƙin ze sameta acan." Babu musu kuwa Little ya zura da gudu zuwa cikin ɗakin. Da ƙarfi ya soma kiran "Lulu! Lulu!!" Yana saka hannu ya soma yaye ƙaton blanket ɗin da ta rufa da shi. Duka ta kai masa sanda ya sake buɗe murya ya kira sunanta. Be kuma saurara ba ya ɗora da "Abba yace ki fito mu tafi makaranta." Ya faɗa da muryarsa me daɗi duk da akwai ɗan tsami kaɗan a cikinta. Dukan da ta masa ne ya sanya shi kai hannu ya riƙe wajen yana kwaɓe fuska "Allah se na faɗa wa Abba.." ya faɗa yana shirin yin gaba.Da sauri ta riƙo shi ta ɗan sassauta fuskarta kaɗan kafin tace "Ka je kace bani da lafiya.." maƙe kafaɗa yayi yana faɗin "A'ah.." Tsaki ta ja dan ta san in dae ta biyewa wannan yaron se dai faɗan da Abban ze nata ya ƙaru, hakan ne ya sanyata sakinsa kawai ta shiga shiryawa tana sake cika tana batsewa. Ta san halin Abba sarai, gudun kada ya gane ciwon ba na gaske bane ya sanya ta yin kalar tausayi da fuskarta hadda aro ƙwallar ƙarya cikin idanunta sannan ta fito, a hankali tace "Abba sannu da zuwa" ta faɗa da muryarta da ta sake yin rawa fiye da yadda take. Cikin tausayawa yace "Yawwah. Bari na ɗakko miki magani ki sha se ku wuce" Tun da dai ta san makaranta ce dole se taje tun da Abba ya saka baki ya sanyata faɗin "A'ah Abba ai na sha, ciwon kai ne dama kuma ya warke" "Toh madallah. Se kun dawo Allah ya tsare." Didi da Little kaɗai suka iya amsawa ita kuwa Lulu ta kasa faɗin komai dan gaba ɗaya hankalinta ya tafi kan yadda zasu ƙarke ne da Gwani bayan ba tayi hadda ba, duk da yadda hankalinta ke a kwance da rashin yin haddarta ta amma yanzu se da ta ji wani tsoro tsoro na neman kamata tayi saurin basarwa tana sake cika tana batsewa. Ita kuwa Didi dariya kawai take yi a ɓoye dan kada Lulun ta gani yanzu se ta sake fusata. "Yau ba zaki biyawa Masoyiyarta ki ba?" Didi ta faɗa tana kallan Lulu sanda suke dab da wuce gidansu ƙawar Lulun. Hararar gidan tayi kamar shi ne ya mata laifi sannan tace "Ehh ɗin.." ta faɗa tana wuce gidan ma da sauri. Ba tace komai ba Didi se bin bayanta da tayi suka cigaba da tafiya. Sakin hannun Didi Little yayi ya koma kusa da Lulu yace "Ki riƙeni kin ji!" "Ba za a riƙe ba" ta faɗa tana maka masa wata uwar harara, dan yau ɗin gaba ɗaya haushin kowa take ji, musamman ma Little ɗin da kamar shi ne ya janyo mata, da yace bacci take da yanzu tana can a matsayin mara lafiya tana bacci hankalinta kwance. A yanzu kam dariya Didi tayi sosai ta cikin niƙab ɗinta, ta janyo hannun Little suka cigaba da tafiya. A haka har suka ƙarasa makarantar.. *** *** Gida ne da ya amsa sunansa gida, ƙato wanda idan baka sani ba daga kallan farko zaka iya kiransa da ƙatuwar plaza. Haɗaɗɗen gida ne wanda tsayawa faɗar irin haɗuwar da yayi ɓata baki ne, dan kuwa anyi ɓarin kuɗi kamar me, an gina shi cikin tsari da ƙwarewa kamar ba a Nigeria ba. Ko daga Compound ɗin gidan kaɗai se an tashi kanka saboda yadda ta matuƙar ƙawatu da abubuwa kala kala se dai marasa hayaniya. Idan kuwa tun farko dama a cikin Compound ɗin ka tsinci kanka to fa ba zaka taɓa cewa a Nigeria kake ba. Ƙaton parlour ne da ya lamushe kujeru saiti uku a gefe guda na cikinsa, wanda anan ne aka zuba kayan ado da ƙawa aka ƙawata haɗaɗɗen parlourn da ko na shugaban ƙasa albarka, parlour ne da ya amsa sunansa parlour, parlour ne da a karan farko zaka iya kiransa da aljannar duniya saboda matuƙar haɗuwar da yayi. Akan ƙaramar kujera wani kyakkyawan babban mutum ne dake sanye cikin wata dakakkiyar shadda da kallan farko zaka mata ka san ta lamushe kuɗi na musamman, fuskarsa kuwa a kallan farko baka isa ka ƙayyade adadin shekarunsa ba, saboda yadda jin daɗi da kuma hutu suka lamushe kaso masu yawa daga cikin shekarunsa. Kyakkyawan babban mutum wanda aƙalla ya bawa 50 baya, idanunsa saye suke cikin glass me matuƙar kyau da tsada, wanda yake amfani da shi idan ze yi wani aikin da ya shafi Computer ko waya. A yanzu ma idanunsa na kan hamshaƙiyar waya ne yana dannawa cikin ƙwarewa. A nutse take takowa cikin parlourn, duk da yanayin shekarunta da suka tura hakan be hanata cin kwalliya kamar yarinya er shekara 20 ba, ƙafarta saye cikin wani hill shoe, sanye kuma cikin rantststiyar atamfa me shegen kyau da tsada, ta sha ɗauri irin wanda ake kira da ture kaga tsiya. A haka take takowa zuwa cikin ƙaton parlourn da kafin ƙarasowarta inda mutumin nan ke zaune ta ɗauki sakanni masu yawa. A nutse ta nemi waje ta zauna cikin kissa da kisisina tace "Barka da wannan lokaci Yallaɓai." Se da ya ƙarasa abin da yake yi cikin waya kamin ya ɗago ya kalleta bayan ya ɗan zame glass ɗin fuskarsa yace "Barka kadai.." "Aiki ake yi ne?" Ta tambaya tana gyara zama akan haɗaɗɗiyar kujerar da ke kusa da tasa. "Ƙwarae kuwa. Kin je kin duba abokiyar zaman naki? Bata ji daɗi ba." Se da ta taɓe baki sannan tace bayan ta yamutsa fuska "Zan dai shiga, amma yanzu magana ce ta kawoni akan Boy." Ƙarasa cire glass ɗin yayi ya ajje a gefe kamin ya juya ya kalleta sannan yace "Yaya muka yi da ke?" Girgiza kai Hajiya Salma tayi kana tace "A'ah fa Yallaɓae, ka sake kwantar da hankalinka ba wani abun yayi ba. Akwai manufofi da dama da suka saka na takura se ya tafi ƙasar waje karatu, misali raba shi da Abokansa na nan ɗin waɗanda yake biye musu, acan kuwa idan babu su na san dole ze rage wasu abubuwan. Kawai dai zuwa nayi in ji ko zaka tura a ɗakko shi ne?" Sauke ajiyar zuciya yayi, bayan yayi murmushi sannan yace "Kamar na faɗa miki zan cire hannuna daga wannan maganar koh? Babu yanda ban yi dake akan fitar AREEF ƙasar waje ba kika dage, yanzu ma se kiyi komai da kanki." "Haba kai kuwa me yasa za kace haka? Ta yaya zan yadda Boy yayi karatu anan bayan ga 'ya'yan manyan mutane na ta fita waje suna karatu wasu ma sun koma da zama acan. Se nawa ɗan ƙwalli ɗaya takk, ace yayi karatu a cikin ƙasar nan. Yanzu yallaɓae mu ba abin kunya ba ne a garemu ace ɗan gidan ALHAJI MATAWALLE guda yana karatu a cikin ƙasar nan bayan babu sa'anninsa? Wannan ma ai salon raini ya shiga tsakaninsa da 'ya'yan talakawa ne.!" Ta ƙare tana yatsina fuska kamar wadda ta ga kashi.. https://chat.whatsapp.com/LH7GN3pMRE26T5G5xcTmmw *♡☆A JINI TAKE☆♡* *(IZZATA)* By _*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_ *CHAPTER ONE* Page_02 __Kallanta Alhaji Matawalle ke yi har ta ƙare zancenta. Ya girgiza kai yana ɗaukar juice me sanyi cikin tambulan ya kai bakinsa ya ɗan kurɓa kana ya sauke. Baya son zancen nasu yayi nisa dan be ƙarasa aikin da yake yi ba, ya kuma san idan har be amsa mata ba ba zata tafi ta bar maganar ba, shi kuma ya riga da ya tsara mutanen da zasu je taho da Areef ɗin. Se dai a kodayaushe baya nuna mata yana bin bayan yadda take shagwaɓa Areef ɗin, take so ta dinga nuna yafi kowa a cikin garin saboda kasancewarsa ɗan wanda yafi kowa kuɗi a garin a wannan lokacin. "Ki je zamu yi maganar.!" Ya faɗa bayan ya kalleta fuskarsa a ɗan cunkushe, baya ma so yayi mata magana akan irin maganganunta marasa daɗi da kullum basa ƙarewa alan talaka, yayi maganar, yayi faɗan har ya gaji. "Amma Yallaɓae da gaske ka damƙa komai a hannuna?" Girgiza kai yayi kafin yace "Na ɗauki wannan aikin, ke dai kawai ki shiryawa dawowarsa." Murmushi me ƙayatarwa ta saki har cikin ranta tana jin daɗi, musamman idan ta tuna yadda tilon ɗan nata ze dawo bayan tsawon shekarun da ya ɗauka a harvey Mudd College da ke California U.S. Ba ta kai ga cewa komai ba Alhaji Matawallen ya sake faɗin "Ki saka a gyara masa part ɗinsa." Da sauri ta soma faɗin "Yallaɓae halin Boy ɗin ka manta? Ni da kaina zan gyara masa, idan ba haka ba yanzu zaka ji yace ɗakin yana warin 'yan aiki." A wannan karon ma se ta ƙare maganar tana yamutsa fuska. "Allah ya taimaka" yayi gaggawar katseta. "Ameen. A huta lafiya." Tayi maganar tana miƙewa ta fice daga ɗakin. Bin ta da kallo yayi kafin ya dawo da dubansa cikin ɗakin yana girgiza kai, a kodayaushe al'amuran Hajiya Salman ƙara ƙaimi suke yi, shi har mamaki take ba shi da ta yadda ya cire hannunsa akan tafiyar Areef ƙasar waje. Bayan ta manta waye shi wajen kula da tarbiyyar Areef ɗin, shi ne take tunanin ze bar shi sakaka haka a can wata ƙasar ba tare da yana sakawa ana duba shi ba? Ya sake girgiza kai kawai yana maida glass ɗinsa ya cigaba da abin da yake yi cikin wayar. .. Wayarta da tayi ƙara ta kalla, ganin kiran wadda ya shigo wayar ya sanyata ɗagawa tana cigaba da taku ɗai_ɗai. "Hello Auntyn Areef" shi ne abin da Hajiya Salma ta faɗa. Murmushi wadda aka kira da Auntyn Areef tayi kana tace "Na'am, toh ya ake ciki?" "Cikin satin nan Boy ze dawo!" "Woww!! Amma gaskiya na ji daɗi ki ce na kira a daidai." "Aikam dai. Bari zan kiraki akwai abin da zan yi yanzun." Babu ɓata lokaci suka yi sallama da ƙanwarta ta daidai lokacin da ta ƙaraso bakin ƙaton part ɗin abokiyar zamanta. Se da ta ɗan tsaya kamar me son ganin wani abu, se kuma ta ɗan saki ƙaramin tsaki kana ta cigaba da takawa zuwa cikin ɗakin. Haɗaɗɗen ɗaki ne da ya ƙawatu da Furniture masu kyau da tsada, komai kuma na cikin ɗakin milk da coffee ne irin masu ɗaukar idon nan. Ƙaton parlour ne se dai duk girmansa be kai na Alhaji Matawalle ba. Daidai lokacin da ta shiga ɗakin ta tsinci muryar Atine (Er aikin kishiyarta) na faɗin "Ranki ya daɗe cikin satin nan Yallaɓae Areef ze dawo." Kafin Hajiya Sa'adah ta bada amsa, Atine suka yi 4 eyes da Hajiya Salma, duk se ta duburburce, ta miƙe a sukwane, a hankali ta zo ta gifta ta gefen Hajiya Salman ta fice daga ɗakin. Wata banzar harara Hajiya Salman ta bita da shi kafin ta ja ƙwafa ta ƙarasa shigowa ɗakin. Kyakkyawar farar bafulatanar da ke zaune kan kujera sanye cikin wata haɗaɗɗiyar atamfa me mugun kyau ɗinkin doguwar riga, ta juya ta kalli inda Hajiya Salma ke tsaye dan ganin abin da ya saka Atine fita haka babu faɗar dalili, se taga Hajiya Salma na cigaba da takowa zuwa cikin ɗakin. Murmushi ta saki duk da na ƙarfin hali ne kasancewar ta ɗan kwana biyu bata ji daɗi ba. "Ki ƙaraso mana" Ƙarasawar tayi ciki se dai bata nemi waje ta zauna ba, ta ɗan ajje numfashi kafin tace. "Har an kawo miki gulmar yarona ze dawo kenan?" Ta tambaya tana kallanta. Ɗan murmushi Hajiya Sa'adah tayi kana tace "Ba gulma ba ce, kawai dai ta faɗa min ne ko da ban sani ba" Jinjina kai Hajiya Salma tayi tana ɗan taɓe baki "Eyyah, don Allah Sa'adah ki fita a harkar ɗana, ban san wannan ɗin wane irin abu ne ba. Ka da kice zaki shirya masa wani abu, dan yana da uwar da zata shirya masa, baya buƙatar na shishshigi. Don Allah ki kama kanki ki bari idan kika haifa se kiyi rawar kan akansa." Tun da ta soma magana Hajiya Sa'adah ke kallanta, ba tayi mamakin soma maganar da tayi ba dan dama ba yau ne karon farko da ta ke faɗa mata makamancin waɗannan maganganun ba, se dai yau ɗin mamakin yafi kamata sosai musamman da har se da ta shigo ɗakinta sannan take jifanta da waɗannan kalaman. A nutse ta buɗe baki duk da yadda take jin wani irin ɗaci a cikin bakinta, maganganun Hajiya Salman tabbas sun daketa sun kuma taɓata sosai "In Sha Allah." Shi ne abin da ta iya furta wa sannan ta ɗauki wayarta tayi stairs ɗin da ke cikin ɗakin nata. Tsaki Hajiya Salma ta ja tana bin ta da kallo, a ranta tana fata da addu'ar Allah yasa ta bar mata ɗanta, ta dena wannan shishshigin ta bari idan ta haifi na ta se ta yi duk abin da za ta yi. ... A ɓangaren Twins kuwa ko da suka isa makaranta kai tsaye aji suka nufa, lokacin babu wanda ya shigo ajin, da yake ajin ba baya ba wajen sanin ya kamata se kowaccensu ta ɗauki Qur'an ta soma bitar haddar da za a karɓa yau ɗin. Kallan Lulu Didi tayi tace a hankali saboda karatun da ake yi "Ki maimaita karatun mana" ta faɗa ganin ta ɗauki wani hadith tana dubawa. "Didi na iya fa, ba se na maimaita ba." Sanin Lulun na da kaifin hadda ne ya sanyata yadda da hakan, ta rabu da ita, ita kuma ta cigaba da karatunta. Duk da yadda idanun Lulu ke kan hadith ɗin da take karantawa amma gaba ɗaya hankalinta ba ya kai, duk taurin kanta se take ji kamar ta ɗauki Qur'an ta yi haddar, amma se ta ji zuciyarta ta ƙeƙashe, hakan ne ya sanyata jan tsaki da siririyar muryarta ta cigaba da karatunta. Dukan da aka ɗaka mata a kafaɗarta ne ya sanyata saurin juyawa bayan ta ɗan saki ƙara saboda yadda dukan ya shigeta. "Masoyiya!" Ta faɗa tana buɗa baki. Galla mata harara wadda ta kira da Masoyiyar tayi kana tace "Ni zaki wa rashin mutunci koh? Ya miki kyau" ta faɗa tana neman waje ta zauna kusa da ita ta haɗe rai. "Ke dallah makara fa muka yi, na ɗauka kin tafi" Lulu ta faɗa tana kallan Fateema Kabeer wadda ta kasance babbar ƙawarta a Islamiyyar ta su. .. Sanye cikin wata lallausar brown ɗin jallabiya, sumar kansa saye cikin irin wannan naɗin da larabawa ke yi a wajen goshi zuwa bayan kansu. Kyakkyawa ajin farko, fari me ɗauke da wasu idanu masu mugun kyau, manya masu ɗauke da baƙar ƙwayar ido me shegen kyau, wata irin gira ce da shi wadda take a jere kamar wadda aka saita ta ta zauna akan fuskarsa ta matuƙar ƙawata ta, hakan ya sa har haɗewa da junansu se da suka yi, saboda se da suka bada wani irin shahararren kyau a tsakiyar goshinsa. Bakinsa ɗan ƙarami ne kamar na mace, kuma ja kamar wanda yake shafawa jan baki ko wani abun makamancinsa, se dai sam ba haka bane. Hannunsa ɗauke da wasu littattafai na Addini kasancewarsa ɗaya daga cikin manyan Malaman Addini a makarantar, ba ma a makarantar kaɗai ba hatta a yankin yana ɗaya daga cikin manyan Malamai, duk da ƙarancin shekarunsa da ba zasu wuce 25 ba amma da yake gada yayi daga wajen mahaifinsa da ya kasance Babban Malamin Addini a garin. Se hakan ya sake siyo masa soyayya daga wajen mutane da dama, ba ga mata ba ba ga maza ba, kowa ƙaunarsa yake. Se dai kuma shi ɗin mutum ne me matuƙar bauɗaɗɗen hali, idan dai har ka fahimce shi a bai_bai ba zaku taɓa zauna wa lafiya ba, zamanku baze taɓa daɗi ba, se dai kuma idan har ka fahimce shi shi ɗin mutum ne me matuƙar kirki da sanin darajar ɗan adam. Abu ɗaya ne yake sakawa a kasa fahimtar inda ya dosa kasancewarsa miskili na ƙin ƙarawa, hatta da magana bata dame shi ba, za a iya masa wani abun ko kuma ayi abu a gabansa amma ba ze ta tanka ba. Sam baya ɗaukar raini, ba ya ma bada fuskar da za a raina shin shi yasa ba a taɓa jinsa da wata ɗaliba ko ɗalibi ba, dan idan dai har ze shiga aji abin da ya kai shi ne kaɗai yake yi, daga nan ba lallai ma wata magana ta shiga tsakaninsa da wani ba. Sallamarsa da muryarsa me amo da daɗin sauraro yayi cikin ajin, se dai kasancewarsa mutum mara fara'a a halitta ya sa fuskarsa a cunkushe take, dan kuwa za a iya kiran Gwani Affan da "Sad Man" Gaba ɗaya ajin suka haɗa baki wajen amsawa, se ya sako kansa cikin ajin cikin nutsuwarsa da tayi matuƙar haɗuwa da tsarin halittarsa. Ɗan lumshe manyan idanunta Lulu tayi tana jin yanda ƙirjinta ya buga sanda ya shigo cikin ajin, tsoron da ya lafa mata tun ɗazun yanzu ya dawo sabo, amma saboda ƙeƙashashshiyar zuciya irinta ta se ta sauke ajiyar zuciyar tana tsara abin da zata faɗa idan ya zo kanta a karɓar haddar. Tsayawa nayi ina kallan ikon Allah sanda na ji bakinsa ya furta "Ina Hafsa Abba?" Dan ban taɓa tunanin za a iya yi masa Hausa ya ji ba ballantana ya furta da bakinsa saboda daga yanayin halittarsa har shigarsa da larabawa yayi kama, se dai maganar da yayi ce ta sanyani fahimtar tabbas bahaushe ne, se dai a cikin hausawan irin na daban ɗin nan ne, wanda za a iya cewa sun samu komai, musamman ma dai a wajen Gwani Affan da aka ba shi kyau, da kuma ilimin Addini, se dai kamar kowanne ɗan adam ba za a rasa wani abun da ya rasa ba, ban san a wajen Gwani Affan ko akwai abin da ya rasa ba dan ni dai a fili ban gan shi ba. Zumbur Hafsa Abba ta tashi bayan maganar da Gwani yayi, tace a hankali "Malam ga ni!" Ba tare da ya kalleta ba ya jinjina kai sannan ya fita daga ajin, bin bayansa tayi zuwa wajen tana ɗan gyara tsayuwarta. "Se gobe idan Allah ya kai mu zan kar6i hadda! Ki sanar da en ajin" "Toh Malam" Daga haka ya juya ya soma takawa dan barin wajen cike da nutsuwa, se da ya ɓacewa ganinta sannan ta juya ta koma ajin ta sanar da su saƙon shi. Lulu kaɗai tayi farin ciki da hakan, dan kuwa gaba ɗaya en ajin farin ciki suke da dawowar Gwanin ajinsu. Haka dai ba dan sun so ba suka haƙura. Yau ɗin sosai take cikin farin cikin tun da suka fito daga makarantar murmushi yaƙi barin baby face ɗinta. Didi na lura da ita kuma ta san dalili amma bata kulata ba. Maganar da Fatima Kabeer ta yi ne ya sanyata kallanta "Masoyiya baƙuwa na miki magana tun ɗazu." Juyawa Lulu tayi ta kalli wadda Masoyiyar ke magana a kanta, itama ita take kalla tana murmushi, yaƙe tayi kana tace "Sannu!" Daga haka bata sake cewa komai ba. Daidai lokacin da suka zo zasu rabu, se suka yi sallama da yake ita baƙuwar zuwan makociyarsu Fatima Kabeer ne ya sa suka yi hanyarsu. "Wallahi ƙawar nan ta ki ta min Fatima, kyakkyawa da ita kamar ita tayi kanta" Murmushi Fatima tayi tace "Allah koh?" Ba tare da tunanin komai ba Abida tace "Wallahi kuwa dama zaki haɗani da ita!" Kallanta Fatima tayi cikin er rashin fahimta da maganar ta ta sannan tace "Ban gane ba?" Dariya Abida tayi kana tace "Mu yi ƙawance mana" "Uhmm ai ga ki ga ta, dan in dai Masoyiya ce wallahi dizgaki za ta yi" Se da Abida ta tsaya ta kalli Fatima har se da Fatiman ta tsargu sannan tace "Shi kenan!" Daga haka babu wadda ta sake cewa komai suka cigaba da tafiya. _Claremont California U.S Tunnel Rd Berkeley East Bay Hotel_ .. Haɗaɗɗen ɗaki ne da ke cikin East Bay Hotel wanda ya amsa sunansa ɗaki me kyau, ado da ƙawa, ya matuƙar ƙawatu da wasu Furniture 'yan ubansu. Kiɗa ke ta shi a cikin ɗakin cikin wata ƙatuwar speaker da ke gefe guda, sosai waƙar ke tashi da ƙarfi kamar ba mutum ɗaya ke ji ba. Babu kowa cikin ɗakin bayan speaker da ke cigaba da aikinta. Taɓa ƙofar toilet da na ji anyi ne ya sanyani saurin kai idona wajen. Farar ƙafarsa da ke cikin wani takalmin wanka itace na fara hangowa lokacin da yake zame takalmin kafin ya kai ga fitowa gaba ɗayansa. Singlet ce a jikinsa se towel ɗin da ke ɗaure daga ƙugunsa yayin da ya ɗora wani akan kafaɗarsa. Yanayin rigar da ke jikinsa itace ta fallasa halittar ƙaƙƙarfan jikinsa da ke ɗauke da wasu lafiyayyun kwantattun gargasa baƙa wuluk, wadda ta zauna ɗass akan farar fatarsa da ta gaji da gyara, hutu gami da jin daɗi. Ƙarasawa yayi gaban mudubi yana ɗan kaɗa kansa dake ɗauke da tulin suma wadda aka yiwa gyara na musamman, hakan ne ya bani damar ganin kyakkyawar fuskarsa da ke ɗauke da wasu shu'uman idanu, wanda kallo ɗaya idan yayi wa mutum ze iya rikicewa, ba ga mace ba hatta ga maza idanunsa kan firgita wasu mazan, idan kuwa mace ta bari ya ɗora shu'uman idanunsa akanta idan dai har bata rikice ta faɗa ƙaunarsa ba toh ba za ta bari ta sake iya haɗa idanu da shi ba saboda yadda idanun nasa suke kamar suna ɗauke da wani maganaɗisu ne, a iya idanunsa kaɗae an ƙure kyau, dan kuwa idanunsa na ɗaya daga cikin abin da ya kwashe kaso masu yawa daga cikin kyawun da Allah ya bashi, se kuma dogon siririn hanci da ke zaune akan fuskarsa kamar an zana. Duk da yanayin yadda kiɗan ke tashi da ƙarfi hakan be hana shi rage sautin ba se ma buɗe baki da yayi ya shiga bin sautin waƙar da se ka rantse shi yayi ta saboda yanda yake bin kowanne waje cike da ƙwarewa da muryarsa me daɗin sauraro. Ya ɗauki wajen rabin awa yana shiryawa sannan ya gama cikin wata haɗaɗɗiyar riga da crazy jeans da suka matuƙar yi masa kyau. Wata er ƙaramar abin hannu me kyau da tsada ya ɗauka ya saka a hannunsa da shi kansa yake ɗauke da kwantacciyar suma me matuƙar kyau. Wayarsa da ke ajje kan gado ta shiga ruri, se a lokacin ya ƙarasa ya rage sautin kiɗan da ke tashi, wanda da alama ba dan kiran da aka masa ba ba ze rage sautin ba. A nutse ya koma ya jingina da jikin mirror shu'uman idanunsa a ɗan lumshe kamar yadda suke a halitta, shi ba irin manyan idanun nan gare shi ba, basu da girma can kuma ba ƙanana ba ne se dai tasirinsu da kuma kyansu na musamman ne kamar yadda shi ɗin ya kasance na musamman. "Bad!" Shi ne abin da Lucky da ya kira wayar ya faɗa bayan ɗaga kiran da Areef yayi. "Yeah Lucky, What's going on?" Yayi maganar da muryarsa da ita kanta ta daban ce, me daɗin sauraro gami da wani amo da ke ɗauke da ita. "Amm ka jirani harkar nan ta samu zan kawo maka har ɗaki." "Nop, Let's meet at school couz mutanen Dad na nan." Da mamaki Lucky yace "A'ah Bad kada kace min tsoro kake ji?" Ya tambaya dan ya san halin Bad Man ɗin. Wani murmushi Areef ya saki kamar ba zece komai ba se kuma yace "Lucky! Just let's meet there" ya faɗa yana taune lips ɗinsa na ƙasa idanunsa a lumshe.. Me son karanta A JINI TAKE (IZZATA) har ƙarshe ze tura ₦300 ta 8124818273 Zahra'u Yusuf Ishaq Opay. Shedar biya ta 08124818273. https://chat.whatsapp.com/LH7GN3pMRE26T5G5xcTmmw *♡☆A JINI TAKE☆♡* *(IZZATA)* By _*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_ *CHAPTER ONE* Page_03 "Ohk mu haɗe a can ɗin." Lucky ya faɗa. Zare wayar daga kunnensa Bad yayi lokaci ɗaya yana ɗaukar karin waƙar da yanzun ke tashi cikin ɗakin. Soma takawa yayi dan barin wajen, wayarsa da ya ajje ta soma ƙara. Ɗan ƙaramin tsaki ya ja yana miƙa hannunsa kan tulin kwantacciyar sumar kansa, kamar ba ze dawo ba, se kuma ya dawo ya ɗora idanunsa akan wayar. Ɗan lumshe idanunsa yayi yana murza goshinsa kaɗan, ya san idan har ya ɗaga kiran Mom ba zata bar shi ya fita da wuri ba, shi kuma gaba ɗaya hankalinsa ya tafi wajen kayan da Lucky ɗin ya samo musu a sirrince. Wayar na dab da tsinkewa ya ɗaga duk da sautin kiɗan da ke tashi har lokacin se dai ba kamar ɗazun ba, hakan be sa shi ya kashe gaba ɗaya ba. Cike da soyayyar ɗan nata tace "Boy!" A hankali yace "Yes Mom!" "Kana lafiya? Ya zaman kaɗaici?" Wani miskilin murmushi ya saki wanda ya matuƙar ƙawata kyakkyawar fuskarsa haka waɗannan idanun nasa se suka ƙara yin wani kyau na musamman. Kafin yace komai ta ɗora da "Ai dai ya kusa ƙarewa, ka fara shirye-shiryen ne?" Ɗan shiru ya sake yi dan shi kam da za a bi ta tashi da ya cigaba da zama a ƙasar nan yanda ze cigaba da cin karansa babu babbaka, babu me saka shi babu me hana shi, amma se ya basar kawai yace "Yeah Mom!" Murmushi Mom tayi sannan tace "Ni fa na fara shirye-shiryen dawowarka tun yau, hope dai ba zaka wuce jibi ba?" Kamar me nazari ya ɗan yi jimm, lallae tabbas yau ɗin dole ne yawa kansa charge me lasisi, dan ya san idan har ya dawo Nigeria Daddy se yafi sakawa an saka masa ido fiye da yadda yanzun ake saka masa. "Ehh ba zan wuce ba" shi ne abin da ya faɗa, kafin Mom ɗin tace komai ya ɗora da "Amm Mom, zan ɗan shiga school ne. Zan kiraki later" Sauke ajiyar zuciya Mom tayi sannan tace "Ohk Boy." Ko ajje wayar be yi ba bayan katse kiran Mom kawai ya jefata cikin aljihu sannan ya fice daga ɗakin jikinsa se tashin ƙamshin turarensa me matuƙar daɗi yake, wanda in dae ka shaƙa se ka so ka sake shaƙa saboda daɗinsa. Angry face ɗinsa ya sake tattarowa waje ɗaya ya ɗorata akan fuskarsa, cike da izza da isa yake takawa bayan ya sakko daga stairs inda ɗakin da yake ciki yake. Kai tsaye ya ƙarasa inda motarsa take, duk da uban mutanen da ke zagaye da ita hakan be hana shi saka hannu da niyyar buɗewa ba. Wani baƙin mutum me sanye da baƙaƙen kaya yayi ƙarfin halin faɗin "Yallaɓae ina zamu cewa Mai gida ka je?" Dakatawa yayi daga niyyar buɗe motar da yayi, a yadda ya dakata kawai ba zaka yi tunanin ze amsa ba se kuma ya ɗaga waɗannan idanun nasa ya kafe wanda yayi maganar dasu. Da sauri ya janye saboda yadda ya duburburce lokaci ɗaya. "Aikin da aka sakaku kenan?" Ya tambaya cikin tsare gida kuma cikin basarwa. Ɗaya daga cikinsu wanda da alama duk tare suke shi ne yace "Sorry Ranka ya daɗe. Sabon ɗauka ne be san yanda abin yake ba." Be tanka ba duk da yaji abinda ya faɗa ɗin se buɗe motar da yayi ya shiga ya tashi motar ya bar Hotel ɗin zuwa makaranta. Ɗaya daga cikin mutanen Daddy ne ya bi bayansa a bisa umarnin Daddyn. Be kuma bar shi ba har se da ya tabbatar ya shiga cikin makaranta sannan ya dawo, dan su basu taɓa tunanin tantirancin Areef ɗin ya kai ya dinga shan wani abun a cikin makaranta ba, shi yasa daga zarar sun gan shi a makaranta hankalinsu ke kwanciya. A inda suka saba haɗuwa yayi parking na motarsa, saboda yanda ya taho a guje ya sa ya ɗan tunkuɗi wani keke yayi gefe sannan ya faɗi ƙasa. Duk da ya ga hakan amma be saka shi yayi yunƙurin yin wani abun ba, se ma ɗauke kansa da yayi kamar be gani ba ya sauka daga motar hannunsa ɗaya saye cikin aljihun wando. Lucky da ya hango shi ya ƙaraso yana kwashewa da dariya. Hannu ya ba shi suka tafa kana yace har lokacin yana dariya "Mutumina gaskiya kai shege ne. Wai bayan duk waɗannan mutanen se da ka fito?" Ɗan murmushi ya saki wanda na fahimci murmushinsa kodayaushe baya wuce wannan miskilin murmushin da kamar ya san kyau yake masa idan yayi. Kamar ba ze ce komai ba se kuma yace "Mu je kawai Lucky!" "Bad Man!" Lucky ya sake faɗa yana jinjina basirar abokin nasa da yace su haɗu a makaranta. .. Da sallama ɗauke a bakinsa ya shigo cikin soron gidan wanda Abeey ke zaune da wasu ɗalibansa yana karantar da su. Dakatawa yayi anan ɗin ya zame takalmin ƙafarsa sannan ya zauna akan tabarmar da ke shimfiɗe a wani ɓangare na soron gidan kasancewarsa me yalwar girma sosai. "Barka da wannan lokacin Abeey" "Barka dai Affan, ka dawo lafiya?" Dattijon mutumin da kana kallansa zaka san shekaru sun ja masa sosai ta faɗa, se dai duk da haka hakan be hana shi karantar da ɗalibai ba wanda kusan kullum cikin hakan yake. "Alhamdulillah" ya faɗa a nutse lokaci ɗaya yana karɓar hannayen masu miƙo masa suna gaisawa cikin mutunci. Be daɗe a soron ba ya miƙe zuwa ɗakinsa da ana shiga tsakar gidan yake. Kai tsaye toilet ɗin da ke cikin ɗakin ya faɗa yayi wanka, ya ɗauki wajen minti 20 sannan ya fito ya sake shiryawa cikin manyan kaya, sosai kyawunsa ya sake fitowa musamman da ruwan da be gama bushewa ba na jikinsa ya sake kwantar da kwantaccen sajen da ke zagaye akan kyakkyawar fuskarsa, ɗaya daga cikin abin da ke sake ƙawata fuskarsa kenan. Se da ya gama shiryawar sannan ya koma ya zauna akan madaidaicin gadonsa ya ɗauki littafan da ya shigo da su ya shiga dubawa yana ware waɗanda ze fara yiwa ajinsu Twins wanda yanzu su ne babban aji. Sallamar Ummeey cikin ɗakin nasa ne ya sanya shi ɗaga manyan idanunsa ya kalli bakin ƙofar. Murmushin da ban taɓa gani akan fuskarsa ba ya wanzu, se a lokacin na sake fahimtar lallai murmushi ma wani abun ne, dan kuwa wani shahararren kyau Gwanin ya ƙara yi, kai ba zaka taɓa ɗauka shi ne a waje ba a yanzu da yayi wannan murmushin. "Sannu da zuwa Ummeey" ya faɗa yana miƙewa daga inda yake. "Yawwah sannu ka dae Affan.. Ka ci abinci?" Ta haɗe tayi maganar lokaci ɗaya. Girgiza kai yayi yace "A'ah Ummeey zan dai ci tukunna" Itama girgiza kan tayi dama ta san halin Affan ɗin, shi ba damuwarsa ba ce ya yini be ci abinci ba, se dai idan ita ta tilasta shi, hakan ne ya sa idan dai ta fita unguwa toh tana dawowa zancen abincin take fara masa dan ta san da wuya idan ya ci. "Ajiye littafan nan, yanzu zan kawo maka." Bata jira yace komai ba ta wuce Kitchen. Ajiyar zuciya ya ɗan sauke, a ransa yana sake godewa Allah da irin wannan uwa da ya ba shi, dan haka se ya koma kawai ya zauna har Ummeeyn ta dawo hannunta ɗauke da abincin ta ajje masa. Babu musu ya ɗauka ya soma ci ko dan faranta ran Ummeeyn. Se ma ta zauna tana masa fifita shi kuma yana cin abincin. ... A harabar gidan driver ɗin da ya saba kaisu makaranta ya saukesu. Dukkansu suna sanye ne cikin Uniform na makarantar boko me kyau, kalarsa nutsatstsiya ce sam babu hayaniya, ga kuma yanayin yadda ɗinkin da aka musu yake me kyau, wanda aka yi shi cike da ƙwarewa. A gajiye dukaninsu suka shige cikin ɗakin nasu da sallama, yayin da Little ya faɗa ɗakin a guje yana kiran Ammi. Ammi da fitowarta daga kitchen kenan ta amsa sallamar tasu lokaci ɗaya tana riƙe Little da ya rungumeta. "Ammi mun dawo." Ya faɗa bayan shi ma ya rungume Ammin. "Sannunku da dawowa yaran kirki" tayi maganar tana ɗago shi suka ƙaraso zuwa cikin parlourn. A tare Twins suka zube akan kujera sannan kusan a tare suka ce "Washh!" Se da Ammi ta zauna sannan tace "Da alama kun gaji?" Yamutsa fuska Didi tayi tace "Wallahi kuwa Ammi" "Toh maza ku tashi ku watsa ruwa, ku zo ku samu ku ci abinci." Ta ƙarasa maganar tana kallan malalaciya Lulu da har ta kwanta akan kujerar ɗakin. Se dai da yake ta ji maganar Ammin ya sanyata miƙewa ta bi bayan Didi suka wuce ɗakinsu. .. Parlour ne madaidaci wanda adon da aka masa ya dace da zubinsa, ya matuƙar ƙawatu da kayan da ke cikinsa. Daga kan kujera wata matashiyar budurwa ce da aƙalla za ta yi 20years, zaune cikin riga da wando wanda ta ɗaga shi zuwa ƙasan gwuiwarta. Hannunta ɗauke da waya tana dannawa yayin da kunnenta ke saƙale da bluetooth, da alama waƙa take ji dan kuwa lokaci lokaci ta kan tsaya ta ɗan jinjina kanta sannan ta cigaba da danna wayar. Ba wata kyakkyawa bace se dai ba za a kira ta da mummuna ba, dan kuwa tana da kyawunta daidai misali. Kanta babu ɗan kwali se zallar gashinta da ba shi da wani yawa da ta ƙulle shi a saman kanta. "Jadwa!" Maganar da naji daga gefe itace ta sanyani juyawa dan ganin wadda tayi ta. Babbar mace ce wadda aƙalla ta bawa 40 baya, ko kuma 40 ɗin ciff, se dai idan har kace daga yanayin shigarta zaka faɗi shekarunta toh se dai ka ce ba tafi ashirin da wani abu ba. Dan kuwa wani riga da wando falazo ne a jikinta, yayin da ta saka wata hula a kanta wadda ta zameta har wajen rabin kanta a waje yake. Hannunta ɗauke da waya ta ƙaraso cikin ɗakin ta saka hannu ta cire bluetooth ɗin kunnen Jadwa guda ɗaya. Se ta juyo da sauri, ganin Maminta ne ya sanya ta faɗin "Ohh Mami! Kin saka nayi loosing." Ta faɗa tana yamutsa fuska. Neman waje Mamin tayi tana faɗin "Kin ƙure uban volume, idan kin gama ji se ki tashi ki yi sallah." Se da ta sake yamutsa fuska kafin tace "Tohm" ta cigaba da danna wayarta. Se kuma ta juyo ta kalli Mamin da take danna waya tana ɗan tauna chewing gum ɗin da ke bakinta. "Mami wa za ki kira ne haka?" "Ammin twins!" Se ta juyo sosai tace "Mami me ya faru?" Ta faɗa daidai lokacin da Mamin ta kai wayar kunnenta sannan ta amsa mata da "Ki jira ki ji!" Babu musu kuwa ta gyara zama tana kallan Mamin. A ɗaya ɓangaren kuwa Ammi na zaune kan kujera, Didi na kusa da ita tana koyawa Little home_work. Wayar Ammin da tayi ƙara ne ya sanya Lulu da tafi kusa da ita ɗauka ta miƙawa Ammin ba tare da ta kalli me kiran ba. Karɓa Ammi tayi ta ɗaga wayar, suka gaisa da Mamin sannan ta ɗora da "Ina Twins su ke?" Murmushi Ammi tayi kana ta amsa da "Ga su a kusa da ni" Kamar Mamin na kusa da Ammi tace "Na san wannan maƙalalliyar uwar miskilanci tafi kowa kusa da ke a yanzu haka" Kamar kuwa ta sani hakan ne, kuma da yake sun ji abin da ta faɗa ɗin se Didi ta ɗora kanta akan kafaɗar Ammi tana tura baki da murmushi akan fuskarta. Hannu Ammi ta saka ta shafa kan Didi sannan tace "Aikam dai.." "Ina Lulu?" Ta sake tambaya. Da sauri Lulu ta taso daga inda take dan dama babu ƙarya suna ɗasawa da Auntynta su. Karɓar wayar tayi daga hannun Ammi suka gaisa sannan Mami ta ɗora da "Yaushe zaki zo?" Kallan Ammi tayi sannan tace "Idan an yi hutu!" "A'ah babu wani hutu, ki zo kawai tunda idan kika zo ɗin zaki dinga zuwa makarantar anan ɗin ma, Uhmm?" "Toh Mami" Daga haka ta miƙawa Ammi wayar, suka sake magana sannan suka yi sallama. Abba da ya shigo kafin su yi sallama yace "Sadiya ce?" "Ehh.." Kafin Ammin ta gama faɗar abin da tayi niyya Lulu tace "Abba zan je gidan Mami pls.." se da ya nemi waye ya zauna yana riƙe da hannun Little sannan yace "Makarantar fa?" "Abba ai za a dinga kaini a can ɗin ma" Kallan Ammi Abba yayi dan jin abin da zata faɗa, se dai ba tace komai ba hakan ne ya sanya shi faɗin "Ita ce ta nemi ki je ne?" Ɗan shagwaɓe fuskarta tayi sannan tace "Ehh Abba" "Ki shirya, gobe idan Allah ya kai mu se na saukeki acan ɗin." Cikin jin daɗi tace "Toh Abba." Ta faɗa a ranta tana tuna yanayin rayuwar gidan Aunty Sadiyan, da take babu takura, komai ka ga damar yi daidai ne, ta san idan ta je can ɗin babu me tilasta mata yin abin da bata ga dama ba, hatta da karatun ma idan bata yi niyyar yi ba ta san Mamin ba zata takura ta da se tayi ba, shi yasa take matuƙar ƙaunar rayuwar gidan Mamin. Kallan Didi tayi da har lokacin kanta ke ɗore akan cinyar Ammi tace "Didi wankin kan." "Ba za a yi ba" Didi ta faɗa tana galla mata harara. Rau rau tayi da idanunta tana kallan Didin, ta san ko me zata yi Didin ba zata bi ta su tafi tare ba, dan ita ɗin miskila ce irin ta sosai ɗin nan, ba kasafai ta fiya son shiga cikin mutane ba idan ba dole ba, shi yasa kullum tana gida kusa da Amminta. Se dai kuma ta wani ɓangaren zata ɗan ji daɗi, dan kuwa idan har Didin ta bi ta suka tafi gidan Aunty Sadiyan tare, zata zame mata cikas, ta san ita ɗin me sakata tayi ne. Ɗan sauke ajiyar zuciya Ammi tayi ba dan ta so zuwan Lulu gidan Aunty Sadiya ba, se dai komai lalacewar Aunty Sadiyan ita ɗin ƙanwar Abbansu ce, saboda haka ba zata iya kallansa tace masa Lulun ba zata je gidanta ba saboda yanayin tarbiyyarta sam be dace ba. Se dai koma me ake ciki ba zata bari Lulun ta wuce sati ɗaya bata dawo gida ba, dan haka kawai take ji hankalinta be kwanta ba tun da akayi maganar zuwan Lulu gidan nata.. Me son karanta A JINI TAKE (IZZATA) har ƙarshe ze tura ₦300 ta 8124818273 Zahra'u Yusuf Ishaq Opay. Shedar biya ta 08124818273. https://chat.whatsapp.com/LH7GN3pMRE26T5G5xcTmmw *♡☆A JINI TAKE☆♡* *(IZZATA)* By _*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_ *CHAPTER ONE* Page_04 ___Ba su daɗe a parlourn ba Didi ta miƙe tana kallan Ammi tace "Ammi bari na je na kwanta, bacci nake ji." Kallanta Ammin tayi na tsawon sakanni kafin tace "Tohm" Daga haka ba ta sake cewa komai ba ta wuce ɗakin nasu. Da narkakkiyar fuskarta Lulu ta bita da kallo sannan ta dawo da dubanta kan Ammi. "Ammi haushina fa take ji." Ta faɗa tana tura baki. Girgiza kai Ammi tayi kana tace "Ai dai kin san halinta dama." Tasowa Lulu tayi daga kan kujerar da take, ta dawo wadda Ammin ke kai. Ta kamo hannunta har lokacin fuskarta a narke tace "Ammi don Allah ki rakani in rarrasheta." Ta faɗa da iya gaskiyarta, dan kuwa tafi kowa sanin halin Didin musamman idan tazo tafiya wani wajen, ta dinga nunƙufurci kenan, kuma ko me za a mata ba za ta bi Lulun ba. Duk da itama Ammin ba son zuwan Lulun take gidan Mamin ba, amma za ta so su je tare da Didi, domin kuwa duk da kasancewarta mahaifiyarsu ita me iya buɗe baki ne ta faɗi cewar Didin tafi Lulu hankali. "Ni ba inda zan je." Ammi ta faɗa. "Don Allah, Don Allah, Don Allah." Lulu ta faɗa kamar za tayi kuka. Murmushi Ammi tayi tana miƙewa ta saka hannunta kan kunnen Lulu ta ja lokaci ɗaya tana faɗin "Ke dai koh!" Se ta saka hannunta ta riƙe kunnen tana ɗan sakin ƙara a hankali gami da murmushi. A kwance take akan gadon na su idanunta a rufe kamar me bacci, se dai ba baccin take ba, amma dai jira take ya ɗauketa. A nutse suka ƙarasa cikin ɗakin. Ammi ta nemi waje ta zauna yayin da Lulu ta zauna a kan gadon, kusa da Didi da ke kwance. Motsin da ta ji a kusa da ita ne ya sanyata saurin buɗe ido, se ta ga Lulu a zaune, ta galla mata harara hadda murguɗa baki. Langaɓar da kai tayi gefe tana ƙiƙƙifta ido, duk Ammi na lura da su hakan ne ya sanyata murmushi tana girgiza kai. "Didi tashi.." Ammi ta faɗa, itama langaɓar da kan tayi kafin tace "Ammi bacci fa zan yi." "Tashi dai." Ammi ta sake faɗa tana riƙota kamar zata ɗagata. Se a lokacin ta miƙe ɗin da taimakon Ammi. "Ki shirya ku tafi tare zuwa gidan Mamin taku." Ammi ta faɗa bayan ta gama gyara zamanta akan gadon. Girgiza kai tayi da sauri sannan tace "A'ah ni kam Ammi." "Pls my Didi" Lulu da ke gefe ta faɗa a narke. "Na ƙi ɗin" ta faɗa tana jefa mata harara. Dama Ammin ta san ba zuwa za ta yi ba, idan ma aka takura se dai ta dami kanta dan haka se tace "Toh fushin na meye?" Se da ta ɗan yi shiru sannan tace "Toh Ammi ba komai fa." Ta ƙare tana cuno baki. "Kin tabbatar?" Ammi ta faɗa. Kafin ta kai ga cewa komai Lulu tace "Allah kuwa Ammi ba wani nan, fushi take da ni fa." "Ni ba wani fushi da nake fa." "Toh in ga alamar hakan." Ammi ta faɗa tana murmushi. Ba tare da Lulu ta ankara ba se ji tayi Didin ta rungumeta. Cikin farin ciki itama ta rungumeta tana murmushi. Ammi ma da ke gefensu murmushin tayi a ranta tana sake addu'ar Allah ya ƙara haɗe mata kan 'ya'yanta. ... Washegari se bayan sun dawo daga makaranta sannan Abba ya ɗauki Lulu da ta gama shiryawa tsaff da kayanta zuwa gidan Mamin. Tun a ƙaton compound ɗin gidan suka haɗu da Mami sanda ya ida parking ɗin motarsa. Mamin na sanye cikin wata doguwar riga ɗinkin hijab bubu da mayafi fuskarta ɗauke da glass, hannunta kuma ɗauke da wata ƙaramar jaka. Cikin farin cikin ganin nasu tace "Oyoyo! Sannunku da zuwa." Ta faɗa da murmushi kan fuskarta. Fitowar da Lulu tayi ne sanyata buɗe mata hannu tana faɗin "Welcome my dear." Babu ɓata lokacin Lulu ta ƙarasa jikin Mamin suka rungume junansu kowaccensu ɗauke da murmushi a kan fuskarta. "Toh ko dai na koma ne?" Abba ya faɗa yana murmushi. Itama murmushin Mami tayi tana sakin Lulu kafin tace "Haba dai Yaya. Barkanka da zuwa, ka zo mu ƙarasa ciki mana." Girgiza kai Abba yayi yana ƙarasowa inda suke lokaci ɗaya yace "A'ah akwai inda zan je, naga kuma kema fita za ki yi. Saboda haka mu gaisa anan." "Kai Yaya haka za a yi?" "Hakan kuwa za a yi" Abba ya faɗa yana murmushi. Gaisawar kuwa suka shiga yi, saboda Abban sauri yake ya sanya babu daɗewa ya wuce. Ita kuma Ammin ta saka hannu ta ɗauki jakar Lulu sannan suka soma takawa zuwa cikin gidan. "Mami da kin bari na ɗauka." Lulu ta faɗa. Hararar wasa Mamin ta jefa mata kafin tace "Ke ban son iyayi." Dariya suka yi kusan a tare daidai lokacin da suka shiga cikin parlourn. Har ɗakin Jadwa Mamin ta kai jakar Lulu. Jadwan na kwance kan gadon tana danna waya, kamar ko da yaushe kunnenta ɗauke da ear piece. Sam bata ji shigowarsu ba, se da Mami ta saka hannu ta karɓe wayar sannan ta juyo da sauri dan ta san dai sun riga sun yi sallama da Mamin kafin ta fita. Tana juyowa se taga Lulu a tsaye tana murmushi, da sauri ta diro daga kan gadon lokaci ɗaya tana faɗin "Oyoyo.." ta faɗa tana rungumeta. Murmushi Mami tayi tace tana kallansu su duka bayan sun saki junansu, se kuma ta maida dubanta kan Lulu tace "Lulu za ki je makaranta ne yau ɗin?" Girgiza kai tayi tana tura baki, tace a hankali "A'ah Mami, daga zuwana kuma?" Dafa kafaɗarta Mami tayi tana faɗin "Kwantar da hankalinki my dear, ba wanda ze miki dole. Nemi waje ki kwanta ki huta, gobe se ki je." Cikin farin ciki tace "Yawwah Mamina." Itama murmushin tayi kana tace "Jadwa ki kula da ita kafin na dawo. Duk abin da take so a sama mata shi, ina dawowa kuma zan ɗora daga inda kika tsaya." Sunkuya wa Jadwa tayi irin alamar girmamawan nan sannan tace "An gama Mami." Tayi maganar tana dariya. Dukansu dariyar suka yi. Mami ta sake yi musu sallama ta fice daga gidan. .. A ranar da Didi taje makaranta tana ta jiran zuwan Lulu amma shiru bata zo ba, bata damu ba tunda ta ga yau ta je gidan Mamin, dan kuwa ze yi wuya idan ba Mamin ce za tace yau ɗin su yi hira ba tunda dai yau ta zo. Aikuwa ta sha tambaya a wajen Abida, har se da ta gaji. Dan haka kawai ta ji yarinyar ba ta birgeta ba, rawar kanta ya fiya yawa, se wani rawar kai take akan Lulun da sau 1 ta taɓa ganinta. Idan ma da ta san halin Lulun da bata din ga zaƙewa haka ba, dan ba abu ne me wahala a wajen Lulun ta dizgata ba, dan wani lokacin halinta se ita. ... "Kin gama shiryawa?" Mami ta faɗa tana kallan Lulu da ta fito cikin Uniform ɗin da kamar kodayaushe ana ƙara mata kyau ne idan ta sakasu. "Ehh Mami." "Toh mu je!" Mami ta faɗa tana yin gaba yayin da Lulu ta bi bayanta. Compound ɗin gidan suka nufa kai tsaye suka hau motar da zata kaisu inda zasu je. Har bakin makarantar driver ya kaita ta sauka sannan ya ja Mami da ze kai unguwa. Kai tsaye ita kuma Lulu ajinsu ta wuce cike da zumuɗin ganin twinnynta. Aikuwa tana shiga ta sameta zaune kamar kodayaushe a inda suka saba zama. Da sauri ta rungumeta tana faɗin "Didina" Cike da farin ciki itama Didin tace "Luluna" se ta koma ta zauna tana ɗage niƙab ɗin fuskar Didin lokaci ɗaya tana faɗin "Bari na ga ko kin rame saboda bana nan." Hannunta ta bige kafin tace "See u. Kwana ɗayan koh?" Kafin Lulu tace komai se ga sallamar wani Malami nan ya shigo cikin ajin, hakan ne ya sanyasu yin shiru bayan amsa sallamarsa. "Masoyiya fa?" Lulu ta tambaya ƙasa_ƙasa. "Ba ta zo ba, itama mutuniyarki bata zo ba" Didin ta bata amsa itama ƙasa_ƙasa. Cikin rashin fahimta tace "Wace mutuniyata?" A hankali Didi tace "Ki yi shiru zan faɗa miki" Daga haka babu wadda ta sake magana. Se dab da za a tashi sannan aka aiko cewar duk wanda be bayar da hadda ba jiya ya je ya bada, wanda ma yayi fashi shi ma ya je. Kallan juna Lulu da Didi suka yi, cikin sarewa ita dai Lulu tayi shiru tana jiran ganin wasu sun miƙe, se dai shiru bata ga kowa ya miƙe ba. A'ah abin dai kamar haɗa baki se ya kasance ita kaɗai ce wadda bata bayar da haddar ba, haushi kamar ya kasheta, takaici kamar ta yi kuka. Se kawai ta gyara zama a inda take zaune fuskarta a haɗe "Lulu ki tashi ki je, meye amfanin abin da kike yi? Haddar ce baki iya ba ko me?" Didi ta faɗa tana kallanta. Se da ta sauke numfashi sannan tace "A'ah fa Didi kawai dai.." "Kawai dai me? Ki tashi ki je kawai." Miƙewa tayi ba tare da ta kalli kowa ba ta fice daga ajin kyakkyawar fuskar nan ta ta a haɗe. A filin makarantar ta hange shi zaune da wani a gefensa, da alama magana suke yi. Gefen fuskarsa kaɗai ake iya hanga wanda hakan ya matuƙar bayyana kyawunsa musamman da fuskarsa take a juye. Sosai wata zuciyar take zugata akan kada ta je, kawai ta koma, se kuma wata ta zugata akan kawai ta je, ai ba wani abun taje nema wajensa ba. A nutse ta cigaba da takawa zuwa inda yake ɗin, se da taje inda take da tabbacin ze ganta sannan ta tsaya kanta na kallan gefe tayi shiru, dan ta san ya ganta, kuma shi ne ya nemi ta zo ba ita ce ta zo wajensa neman wani abun ba. A nutse Gwani ya cigaba da tattaunawa da mutumin nan, sam be nuna ya san akwai wanzuwar wata halittar a wajen ba. Hakan ba ƙaramin baƙantawa Lulu yayi ba, ga shi yana wani magana a hankali daga shi har wanda suke maganar, se dai shi ta shi ko sautinta ba a ji saɓanin ɗayan da ake iya jiyo sautin tasa muryar. A hankali ta ɗan saki tsaki tana runtse idanunta, wannan faɗin ran nasa da nuna shi wani ne bayan shi ɗin ba kowa bane yana ɗaya daga cikin abin da ke sanyawa bata yinsa ko kaɗan. Uwa uba kuma yadda kowa ke son shi, kowa ke nan nan da shi, se take ɗauka duk suna yi saboda kyawunsa ne da ke yaudararsu, shi yasa ita sam be taɓa birgeta ba se ma haushinsa da take ji daga shi har mutanen da ke son shi, dan gani take yadda suke son na shi ne yake sanyawa baya ganin girman kowa, baya tsayawa inda Allah ya ajiye shi. Tafi ƙarfin minti 5 tsaye a wajen, zuwa lokacin ta gama fusata, duk da Malaminta ne amma se take ganin kamar idan ta buɗe baki ta masa magana, ko da ba a tausashe ba ne ba ze ɗauka itama ta yaba da shi ɗin ne, kamar yadda kusan kowa yake yi. Ji take kamar ta tafi ba tare da tace komai ba, yayin da wata zuciyar ke faɗa mata ta masa magana ba ze ɗauki komai ba, haka dai ta daure, ta cije ta haɗa rai ta juya ta kalli inda suke tace murya a cunkushe "Malam, ga ni!" Se a lokacin ya ɗaga kyawawan idanunsa ya kalli inda take tsaye, cikin er basarwa yace "Assalamu alaik." Daga haka ya maida kansa wajen mutumin suka cigaba da magana. Runtse idanunta tayi tana jin wani irin takaici da kunya da haushi duk sun taru sun rufeta. Me yake nufi da ita? Kafira ce ita ko me yake nufi? Ƙirjinta har wani bugawa yake saboda tsabar takaici da haushi. Yanzu duk da irin wannan dizgin da rashin kirkin da yake a haka ɗalibai da yawa ke son shi, a haka suke cigaba da mu'amalantarsa kamar wani mutumin arzik'i. Yadda zuciyarta ke tafasa ta san ko ta buɗe baki ma ba abin da zata iya faɗa, dan haka se da ta ƙara wajen minti 2 tsaye a wajen. Se da ta ji ta ɗan soma dawowa daidai sannan ta sake juyawa cikin rashin mafita tace "Ga ni!" Sarai ya jita, ba ya kuma san yayi shiru dan ya san hakan be kamata ba, se dai kuma yanda take magana kamar da sa'anta ko ma ƙaninta ya ga lallai ya kamata ya koya mata hankali, dama ya daɗe da gane take_takenta tun ba yanzu ba. Toh a yanzu kuma da ya zama malamin ajinsu shi ba ɗaukar kowanne hauka ze yi ba, dan haka ya zama dole ya taka mata birki. A nutse ya sake ɗaga kansa a karo na biyu ya dubi inda take ba tare da ya kalli fuskarta ba yace cikin basarwa "Ba a koya miki sallama ba? Toh ki je ki koya se ki dawo!" Daga haka ya miƙe a nutse hannunsa ɗauke da wani littafi ya bi bayan wanda suke magana dan ya riga shi tashi. Bin sa tayi da kallo tana jin yadda zuciyarta ke tafasa tana mata zafi, wani irin baƙin ciki da ɓacin rai duka suka haɗu suka tarar mata. Kawai se ta ji ƙwalla a cikin idanunta, gaba ɗaya ta gama muzanta, ya gama yarfata, ya gama wulaƙantata. Se ta buɗe ido ta fara duba gefe da gefenta ko da akwai wani a kusa da ita. Fatan ta guda ɗaya Allah yasa babu wanda ya ga wannan cin mutuncin da yayi mata, ga shi kuma wani ƙarin baƙin cikin ya tafi ya barta a wajen, wato ga mara aikin yi, idan ta gaji da tsayuwar se ta ƙara gaba. Ganin da tayi kowa da abin da yake yi, se kuma waɗanda ke fitowa daga aji saboda an tashi, se dai da alama kowa harkar gabansa yake yi, ya sanyata soma takawa a hankali kamar babu laka a jikinta tana jin yadda gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, haushi da takaicin Gwanin na sake cikata. Gaba ɗaya ta ƙi barin zuciyarta ta huta, se tunanin abin da ya faɗa mata ɗin take cikin wannan muryarta sa me kauri da daɗi. Duk da kalaman da ya faɗa ɗin basu da yawa amma ita a wajenta ji tayi kamar an gama muzanta ta muzancin da ba a taɓa yi mata ba, wai yau ita ɗa namiji ke faɗawa magana. Cigaba da takawa ta cigaba da yi har zuwa sanda ta ƙarasa ajinsu, ko lura da masu fitowa ma ba ta yi ba, se da Didi ta kamo hannunta tace "Kee!" Se a lokacin ta kalli Didin da idanunta da ƙwalla ta gama taruwa se dai taƙi bata damar zubowa saboda kada wani ma ya gane akwai abin da aka mata, bare ma a tambayeta kuma idan ta faɗa ɗin ita ce zata ji kunya. "Me ya faru?" Didi ta tambaya tana kafeta da idanunta. Duk da basa ɓoyewa junansu komai amma yau ɗin so take kawai ta kwanta tayi bacci ta manta da abin da ya faru ba tare da kowa ya sani ba, dan haka tayi ƙarfin halin faɗin "Kaina ke ciwo!" Duk da bata wani yadda ba, amma ta san koma mene idan ta matsota zata faɗa mata ne, hakan ne ne ya sanyata faɗin "Ki wuce gida, kina zuwa kuma ki sha magani kin ji koh?" Didin ta faɗa cikin kulawa. Jinjina kai Lulu tayi kawai se ta cigaba da bin Didin da ke riƙe da hannunta suka fito. Suka yi sallama cike da kewar junansu sannan Lulu ta shige cikin motar da ta zo ɗaukarta, yayin da Didi ta kama hannun Little suka tafi gida. Tun da ta shigo Jadwa ke binta da kallo, ganin ba a irin yanayin da ta saba ganinta ba yau ɗin ta ganta a ciki. Hakan ne ya sanya lokacin da ta nemi waje ta zauna kan gadon, se itama ta zauna tana kallanta tace "Sistor wai me ya faru?" Murmushin yaƙe Lulu tayi kafin tace "Babu komai fa. Me kika gani?" Yamutsa fuska Jadwa tayi tace "Kin ga yanzu dai babu Didi a gidan nan, idan zaki faɗa min damuwarki mu haɗu mu yi maganinta toh. Idan kuma ba zaki faɗa min ba se in san inda kika ajjeni." Kallan Jadwan Lulu tayi kamar ba za tace komai ba se kuma tace "Babu komai fa nace miki" ta faɗa fuskarta a haɗe saboda tuna abin da ya faru ɗazun. "Akwai ɗin kenan. Just tell me, mu haɗu mu yi finding solution." Jadwa ta faɗa bayan ta tauna chewing gum ɗin bakinta ya bada sautin 'ƙaƙas'. Ji tayi kamar yanzun ne Gwanin ya faɗa mata maganar, ji take kuma kamar yanzun ne ya shayata a tsaye kusan mintina nawa. Kamar za ta fasa ihu tace "Jadwa ki ƙyaleni don Allah. Malaminmu ne ya ɓata min rai." Cikin rashin fahimta Jadwa tace "Ban gane ba? Kin je wata makaranta ne hajjaju? Yaushe kika fara zuwa University bani da labari?" Kallan rainin hankali Lulu ta bi Jadwa da shi jin maganar da tayi ɗin irinta rainin hankali, se kawai tayi mata shiru fuskarta a haɗe cikin zuciyarta na cigaba da tafasa. "Common Babe, Allah kuwa ban gane me kike nufi ba" Jadwan ta faɗa tana riƙo hannun Lulu. "Idan nace miki Ya Sayyadi zaki gane? Toh shi ne ya gama yarfani da girmana da mutuncina." Kallanta Jadwa ta cigaba da yi tamkar wata sabuwar halitta, se kuma daga baya kawai ta sheƙe da dariya hadda riƙe ciki. Haushi gami da tuƙuƙi suka sake cika Lulu, se ta miƙe a fusace zata bar ɗakin, Jadwa tayi saurin riƙo hannunta. Fuzge hannun tayi kamar zata rufe Jadwan da duka. Ganin hakan ne ya sanya Jadwa miƙewa tana maida dariyarta ta soma faɗin "Sorry my love. Tun farko ce min zaki yi Malamin Islamiyya. Ni da kika ce min Malami na ɗauka wani shahararren Malamin University ne, shi yasa nake dariya. Kin ga mu je mu zauna." Ta faɗa tana jan hannun Lulun. Yanzu dai se ta bita ɗin suka zauna. Da rarrashi ta haƙura ta bata labarin abin da ya faru ɗin. Se da suka ɗauki wajen minti 1 bayan gama bada labarin sannan Jadwa tace "Wai kina nufin Malami, Malamin ma Malamin Addini shi ne kika zauna yana ƙoƙarin manna miki hauka?" Jadwa ta faɗa cike da mamaki wanda ya gaza ɓoyuwa har akan fuskarta.. Me son karanta A JINI TAKE (IZZATA) har ƙarshe ze tura ₦300 ta 8124818273 Zahra'u Yusuf Ishaq Opay. Shedar biya ta 08124818273. *♡☆A JINI TAKE☆♡* *(IZZATA)* By _*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_ *CHAPTER ONE* Page_05 ___Shiru Lulu tayi, dan ita maganar ma da Jadwan ke yi sake tunzurata take yi, tana sanyawa tana tuna abin da ya faru ɗazun, tana kuma sake sakawa tana jin Gwanin yayi mata ƙarshen cin mutunci. Kamar ba za tace komai ba se kuma can tace muryarta a cushe "Toh da wa nake nufi?" Ɗan lumshe ido Jadwa tayi tana furzar da iska daga bakinta. Tayi shiru na tsawon mintuna kamar me tunani, dan hadda sunkuyar da kai tana jinjina kai. Se can ta ɗago kai ta kalli Lulun, ta sauke ajiyar zuciya kana ta soma faɗin "Wallahi kin bani mamaki Lulu. Kamar ke big gurl ace kin zauna kina saka damuwar wani ƙaramin alhaki a cikin ranki? Me aka yi akayi Malami? Malamin ma na Addini? Me yake taƙama da shi? Kuɗi? Ɗan gidan uban waye shi? Na san babu yadda za a yi ya kasance ɗan gidan wani hamshaƙi se dai na matsiyata. Ke kuma fa? Kyau, aji, kuɗi duk kin haɗa, toh meye zaki tsaya kina ɗaura damuwar talakawa a kanki?" Se ta ɗan dakata anan, ta sanya hannu ta kamo hannun Lulun sannan ta ɗora da "Kin ga kiyi amfani da halinki a wajen nan Lulu. Shi ɗin ba kowa bane, saboda haka duk wani abu da kika san ze haɗaku da shi ki ƙaurace masa. Ke hatta haddar ma ki dena bayarwa, kar kiyi tunanin ze takura miki akan se kin bayar, idan dai har kika bi abin da nace miki toh ba ze takura ba, tun da dai ai yin haddar ba dole bane. Dan haka ina so in sake tabbatar miki da in dai kika bi waɗannan hanyoyin toh ze kama kansa ne, ya gane ke ɗin ba sa'arsa bace." Shiru Lulu tayi tana saurarar maganar Jadwan tun da ta soma magana, har ta ƙare. Tabbas duk wata magana da ta faɗa ɗin ta riƙeta hakan ne ya sanyata tsayawa tana warwaresu dalla_dalla dan ta sake fuskantarsu yanda ya kamata. Anya kuwa abin da Jadwan ta faɗa shi ne mafita? Ko kuwa dai tayi ƙoƙari ta bi abin da Jadwan ta faɗa ta gani ko hakan ze yi aiki, dan tabbas itama zata ji daɗi idan kwata_kwata wata harka ta dena shiga tsakaninta da Gwanin. "Amma Jadwa..!" Ta faɗa a raunane, narkakkun oily eyes ɗinta na wani irin sheƙi kamar waɗanda aka zuba musu zaiba. Numfashi Jadwa ta sauke tace bayan ta girgiza kai "Uhmm wai Lulu yaushe kika chanja ne haka? Ko dai ba so kike ki kawo ƙarshen izzarsa ba? Ko da ze gwada wa wasu ya kasance banda ke a ciki?" Se ta jinjina kai kawai. "Toh abin da na faɗa shi za a yi. Shi ne kawai mafita. Ke ko ma dai kin manta abin da ya miki ne?" Ajiyar zuciya Lulu ta sauke tana ɗan lumshe idanunta sannan ta buɗe tace "Haka za a yi Jadwa!" Shi ne abin da ta faɗa bayan murmushi ya suɓuce akan fuskarta. Se a lokacin ta ji tabbas abin da Jadwan ta faɗa yayi daidai. Za kuma tayi amfani da shawarar Jadwan ta gani ko za a dace. "Thank you so much sistor." Lulu ta faɗa. Itama murmushin tayi sannan tace "Ko babu komai na sakaki murmushi bayan da wancan Malamin Addinin ya ɓata miki rai." Dariya Lulu tayi jin da tayi har Jadwan ta laƙabawa Gwanin sunan "Malamin Addini" "So yanzu dai ki zo mu buga game. Ki manta da wancan useless person ɗin." Babu ɓata lokaci Jadwan ta ɗakko wayarta suka shiga yin game ɗin, Jadwan na sake iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta saka Lulun ta manta da abin da ya faru. ... Tsaki ta saki tana miƙewa tana ajje wayar akan kujera sannan ta miƙe. Kai tsaye ɗakin Jadwa ta wuce inda ta tabbatar suna can. Aikuwa suna can ɗin zaune suna game lokaci ɗaya suna shan yankakken fruits ɗin da ke cikin wani plate. "Game ɗin ce?" Ta faɗa tana ƙarasowa cikin ɗakin. "Wallahi kuwa Mami" Lulu ta faɗa tana tashi zaune daga kishingiɗen da take. "Toh yayi kyau.. Jadwa tashi.." tayi maganar tana neman waje ta zauna. Tashi Jadwa tayi akan gadon. Ita kuma Lulu ta ja hularta da ta saɓule ɗazun a gefe ta ɗora akan nata. "Gobe zaku wakilceni wani biki. Na yi niyyar zuwa se dai kuma abubuwan sun haɗe min, ga bikin er gidan Honourable, so yafi zama min dole na je nata, dan haka se ku shirya." "Ammi ban san zuwa ko ina ni fa." Jadwa ta faɗa tana yamutsa fuska. "Bare kuma ni!" Lulu ta faɗa tana ɗan tura baki. Harara Mami ta jefa musu dukansu kafin tace "Ban san shashanci malamai. Umarni ne na baku. And ku yi shiga me kyau wadda zaku janyo min mutunci, manyan mutane ne zasu je wajen, may be ma ku samo min sirikai." "Kai!!" Lulu ta faɗa tana waro manyan eyes ɗinta gami da buɗe baki. Tare duk suka saka dariya na yadda Lulun tayi. Jadwa tace tana dariya "Mami tamu ta gargajiya." "Ban san shirme Jadwa" Mamin ta faɗa tana murmushi lokaci ɗaya tana jefa mata harara. "Shikenan Mami zamu je ɗin." "Ai ko baku yadda ba ma dole se kun je." Mami ta katse Jadwa da faɗin hakan. .. Washegari wajen ƙarfe 8pm ne Didi da Ammi na zaune a parlourn. Tasowa Little yayi daga inda yake zaune ya ƙaraso wajen Ammi yace yana tura baki "Ammi don Allah Lulu ta dawo" ya ƙare kamar ze yi kuka. Kamo hannun shi Didi tayi tace tana murmushi "Har ka fara missing nata?" Se ya jinjina kai yana sake langaɓar da kai gefe. Kumatunsa Ammi ta ja lokaci ɗaya tana faɗin "Idan da tana nan da tuni kun yi faɗa yafi sau a ƙirga, amma daga tafiyarta har ka fara kewa." Shi dai kallan Ammin kawai yake yi. Se ta saka hannu ta ɗakko wayarta da ke ajje a gefenta. "Ammi kawo na kira." Didi ta faɗa cike da zumuɗi. Miƙa mata wayar tayi, da sauri ta shiga ta soma lalubo number Mami ta kira, se dai a karon farko aka faɗa mata ba zata shiga ba. Se ta yamutsa fuska cikin rashin jin daɗi. "Didi ba tace komai ba." Little ya faɗa yana kallanta. "Little wayar ta ƙi shiga." Ta faɗa a hankali dan itama ba ta ji daɗi ba kwata_kwata. Shi dai be fahimci abin da take nufi ba hakan ne ya sanya shi sake faɗin "Didi ki kirata" "Tohm zan kira." Ta faɗa tana janyo shi jikinta. A ɓangarensu Lulu kuwa, kiran wayar da Mami tayi musu ne ya sanyasu soma shiryawa. Jadwa ce ta fara shiryawa cikin wata shegiyar straight gown ta atamfa wadda ta matuƙar kama ko ina na jikinta, ta ɗauki wani yalolon mayafi ta ɗora shi a gefen kafaɗarta. Ɓangaren Lulu kuwa ko da ta gama gyara fuskarta se ta ɗauki wata doguwar rigar abaya me kyau ta saka, da yake Abba ba daga nan ba wajen siya musu kaya masu kyau, hakan ne yasa wannan ɗin ma me kyau ce ta sosai. "Don Allah ki yi sauri Lulu." Jadwa ta faɗa tana juyowa. Sakin baki tayi tana kallan Lulu ganin ta cikin doguwar riga sakakkiya ta yafa mayafin da shi dai ƙarami ne, tayi matuƙar kyau kamar ka saceta ka gudu. "Wai kina nufin a haka zamu tafi?" "Ban gane ba?" Lulu ta faɗa sanda girarta ta tattare waje ɗaya ta ɗan yi ƙasa. "Kalleni fa Lulu, waye ze kalleni be sake kalla ba? Kalli yanda na shigar na fitar, don Allah ki saka gown kema." "A'ah fa ni kam na gama shirina." Lulu ta faɗa tana ɗauke kai. "Please..." In ji Jadwa. "Idan in cire kayan na yi kwanciyata ne toh" Lulu ta faɗa tana gyara zaman mayafin jikinta. "Shi kenan ki tashi mu tafi toh!" Se a lokacin sannan Lulu ta miƙe suka fita zuwa parlour. Ba su dai suka fita daga gidan ba se wajen 9 driver ya ɗaukesu zuwa wajen dinner. CALIFORNIA U.S Zaune suke su biyu akan kujerun da ke kusa da na juna, kowannensu hannunsa ɗauke da wani ɗan ƙaramin cup da idan mutum ruwa ze sha da shi be fi yayi ƙaramar kurɓa ɗaya da shi ba. Wani ke zuba musu wani abu daga cikin kwalba, daga ya gama zubawa kowannensu se ya kai bakinsa ya shanye. Goge baki Lucky yayi yana ajje numfashi lokaci ɗaya yana wani lumshe ido wanda hakan ze nuna maka a buge yake, yace "Bad komai ya isheni.. na fara ganin.. ba daidai ba." Yayi maganar a rarrabe kamar me koyan yadda ake magana. Be ce komai ba se sake miƙa cup ɗin yayi aka sake zuba masa ya kai bakinsa, se da yayi hakan kusan sau 5 sannan ya soma sauke numfashi idanunsa da suka yi ja a rufe. Se kuma ya shiga buɗesu kamar waɗanda aka sakawa gum aka manne. "Ka da da kayi Over dose Dude." Lucky ya faɗa yana kallan yadda Bad Man ɗin ke ta bankawa cikinsa abubuwa, duk da dai dama ya saba yin mankas amma yau ɗin ya ba shi mamaki. A hankali ya sauke idanunsa akan Lucky, dan shi kam da wuya ya sha abu yayi loosing hankalinsa, dan kuwa hatta maganarsa kaɗan take chanjawa, se ka iya rantse wa ma babu abin da ya sha idan ba waɗannan idanun nasa ka kalla ba, waɗanda ke sake ƙanƙancewa su sauya kala. "Leave me pls! Gobe zan koma Nigeria, ina ƙaunar abubuwan wajen nan." Ya faɗa bayan ya janyo maganar da ƙarfi, sannan ya sauke numfashi lokacin da ya kai ƙarshen maganar. "Zaka yi missing Dude." Dariya yayi har yana komawa jikin abin da ke bayansa, har kuma zuwa lokacin idanunsa a ɗan lumshe suke se dai ba a rufe ba "Karka damu." Ya ƙare maganar yana sakin wani murmushi. A can gidan na Alhaji Matawalle kuwa yau ɗin gaba ɗaya gidan sun tashi ne da shirye_shiryen dawowar Bad Man. Gaba ɗaya Mom ta kasa zaune ta kasa tsaye, duk hankalinta ya rabu ne kan masu girki, da kuma mabanbantan abubuwan da ake ta gabatarwa a gidan duk dan dawowar ɗa ɗaya tilo ga Alhaji Matawalle. Yanzun ma haka fitowarta kenan daga part ɗinta za tayi aike supermarket. A daidai part ɗin Hajiya Sa'adah ta dakata saboda yanda ta ji wani uban ƙamshi na tashi daga sashen. Ta san dama Hajiya Sa'adahn ba baya bace wajen iya girki, dan kuwa idan tayi girki tuni ze baɗaɗe ko ina da ƙamshi, shi yasa ma ita bata yadda da 'yar aiki ta mata girki ba. Se dai yau ɗin haka kawai take ji wannan girkin Hajiya Sa'adahn tayi shi ne ba dan kowa ba se dan Areef. Lallai dole ta sake tashi tsaye, ta sake ɓillo da hanyoyin rashin mutunci ta juye shi a kan Hajiya Sa'adahn duk dan ta fita daga harkar ɗannata. Dogon tsaki taja a ranta tana saƙa ko wannan ɗin wane irin shishshigi da naci ne haka?. .. Ƙarfe 6pm jirgin da ya ɗakkosu ya sauka a filin jirgi na Malam Aminu Kano. Sanye cikin ƙananan kaya, riga da wando jeans, hannunsa riƙe da wata trolley, yayin da ɗayan hannun nasa ke ɗauke da haɗaɗɗiyar jaka me kyau ko a ido. Farar fuskarsa wasai take, se dai saɓanin yanda take a da yau ɗin cike take da annuri na son ganin Mom ɗinsa da Daddynsa. Duk da kuwa yanda kafin ya taho ɗin yake jinsa duk a takure, amma da ya tsinci kansa a cikin Nigeria, Nigeriar ma Kanon dabo tumbin giwa duk se ya manta da wannan ɗin. Kansa babu komai se tulin kwantacciyar sumar da ta sha gyara da maya mayai masu matuƙar tsada, haka zalika sajensa da ya taho tun daga kansa shi ma a kwance yake luff luff gwanin kyau. Annurin da ke kan fuskarsa ya sake bayyana waɗannan sihirtattun idanun nasa masu kyau da suka ɗan ƙanƙance suka sake kyau. Wasu manya manyan motoci ne na gani na faɗa masu mugun kyau da tashin kai, birjik a cikin airport ɗin, wajen guda 10, dukkansu kuma ɗauke suke da sunayen Matawalle, wanda hakan kaɗai ze nuna maka ko daga ina motocin suke. Ɗan lumshe idanunsa yayi kafin a hankali ya furta akan laɓɓansa "Bismillahi.. Na dawo fa?!" Ya faɗa fuskarsa na komawa ainahin yanda take babu fara'a. Ya kai wajen minti ɗaya tsaye a hakan kamar ba ze je ko ina ba, se kuma ya soma takawa a hankali cikin tafiyar nan tasa me cike da mazantaka.. Ayi manage da wannan pls.. *♡☆A JINI TAKE☆♡* *(IZZATA)* By _*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_ *CHAPTER ONE* Page_06 __ Cike da nutsuwa da kuma takatsantsan duka motocin ke tafiya akan titin, kowannensu na kiyaye duk wani abu da ze janyo fushin Bad Man, ko kuma na mahaifiyarsa. Dan in dai har ta Alhaji Matawalle ne ko da laifi suka yi se dai yayi musu faɗa shi ma cikin dabara. Se dai ita Hajiya Salma abu kaɗan zasu kuskure ta juye musu kwandon rashin mutunci, wani lokacin har da barazanar rasa aikin da mutum ze yi. Toh bare kuma yau ɗin da suke ɗauke da shalelenta, ɗa ɗaya tilo da ta ɗauki soyayyar duniya ta ɗora masa, hakan ne ya sa suke takatsantsan kada a samu matsala. A hankali ya ɗaga idanunsa ya kalli titin da suke wucewa kamar masu tausayinsa saboda yanda drivern ke tafiya a hankali. Ya ɗan furzar da iska kaɗan sannan ya buɗe baki yace "Malam! Wane irin driving ne wannan?" Da sauri drivern yace bayan ya sunkuyar da kansa ƙasa kaɗan "Sorry sir, Hajiya tace mu yi driving na ka a nutse shi yasa muke kiyayewa. Sorry sir." Ya faɗa cikin girmamawa. Ɗan shiru yayi, ba dan ba dan ba fatali ze yi da maganar nan, se dai kuma tun da har Mom da kanta tace hakan, bari ya bari. Jin da drivern yayi yayi shiru ne ya sanya shi cigaba da driving din, yayin da Bad ɗin sam ji yake kamar yayi mene, dan shi sam be saba da irin wannan driving ɗin ba kamar na en ƙwaya. Jerin gwanon motocin da suka soma tsayawa a parking space ne ya alamtawa Mom cewar lallai masu ɗakko mata ɗanta sun iso, hakan ne ya sanyata fitowa cike da zumuɗi ta ci ado kamar wadda ake biki, cikin wani tsadadden lace me shegen kyau. Ita tun da suka tafi hankalinta ke kansu dan dai Alhaji Matawalle yace a bar drivers kawai su ɗakko shi ne, ba dan ta so ba dan Alhajin na da power a gidan ya sa ta haƙura. Da sauri drivern ya fito ya saka hannu ya buɗe murfin gidan baya, inda Bad ke ciki, daidai lokacin da Mom ta iso wajen. Se ta saka hannu ta ƙarasa buɗewa tana jin wani irin farin ciki mara misaltuwa. A hankali ya zuro ƙafafunsa zuwa cikin gidan, ƙafarta sa dake cikin wani tsadadden haɗaɗɗen takalmi sau ciki, me matuƙar kyau da tsada. Cikin sauri Mom ta rungume shi tana faɗin "Oyoyo my Boy." Ta faɗa tana ɗan shafa bayansa a hankali idanunta a rufe ciki da kewar ɗan nata. "Noo pls Mom, Na girma fa yanzun. Ni yanzu ba yaro bane, look at me mana, Boy ɗinki ya zama Big.." ya faɗa kamar ba shi ba. Murmushi tayi daidai lokacin da ta ɗago tana kallansa tace "Noo, kai yaro ne a wajena har yanzun.." ta faɗa tana murmushi tana kallan kyakkyawar fuskarsa da ta ƙara kyau na musamman. "Mommm..!" Ya faɗa yana jan ƙarshen sunan. "Let's get in." Ta faɗa hannunta riƙe da na shi. A hankali suka soma takawa zuwa cikin gidan. Cikin ƙanƙanin lokaci en aikin gidan suka soma shigar da kayansa ciki, wasu kuma na cigaba da ayyukansu. "Bari na gaida Mommah!" Ya faɗa sanda suke dab da wuce part ɗin Hajiya Sa'adah. Wani kallo Mom ta watsa masa, daga zuwansa har ze fara ƙona mata rai? Da ƙyar ta furta "Ba za ka je ba!" "Reason..??" Ya faɗa sanda ya dakata hannunsa cikin aljihun wandonsa. "Ka dawo koh? Ka da ka ɓata min rai daga dawowarka." Shiru yayi yana kallan Mom ɗin, so tana so tace masa har zuwa wannan lokacin tana nan dai kamar yanda take? Ya ɗan sauke ajiyar zuciya sannan yace "It's ohk.." Ƙaton parlourn Mom din suka wuce, dan Daddy baya nan yayi tafiya yau da safe. Zama yayi akan kujerar ɗakin ya ɗan lumshe idanunsa kafin ya furta a hankali "I missed komai na nan.." murmushi Mom tayi kafin tace sanda ta zauna a gefensa "Mu kuma mun yi missing na ka.." Buɗe lumsassun idanunsa yayi, waɗanda daga lumshesu har sun sake shanyewa, yace yana kallanta "Wanka!" Shi ne abin da ya faɗa kawai. Miƙewa Mom tayi tana faɗin "Let's go, se kayi a nawa.." girgiza kai yayi hannunsa cikin sumar kansa yace "No Mom, I prefer to do it on my own.." "Ohk mu je na rakaka.." Tashi yayi daga kan kujerar yace bayan ya ɗan yamutse fuska "Ki zauna Mom, I will be back.." Ba dan ta so ba tace "Ohk.." Amma duk da haka bata ƙyale shi ba se da ta raka shi har ƙofar sashensa, cike da takatsantsan kada a san da dawowarsa cikin gidan. .. Wani ƙamshi ne ke tashi tun daga bakin sashen nasa, ƙamshii me daɗin shaƙa. A nutse ya saka hannu ya buɗe ƙofar da zata sada shi da parlournsa. Haɗaɗɗen parlour ne wanda ke ɗauke da tsala_tsalan kujeru ash colour, komai na ɗakin ash ne, light and dark ash, hakan ba ƙaramin ƙawata ɗakin yayi ba, se ya zama na musamman, yayi matuƙar haɗuwa. Be bi ta kan parlourn ba kai tsaye ya wuce bedroom ɗinsa. Ban sani ba ashe parlourn ba komai ba ne amma fa idan aka haɗa shi da bedroom ɗinsa. Wani irin bedroom ne wanda ko a ƙasar waje mamallakinsa se ya kasance wani shege ne, ballantana anan. Haɗaɗɗen bedroom wanda ya wadatu da kyawawan furniture masu shegen tsada, kyau da kuma ɗaukar ido. Wani shahararren gado ne da ke gefe ɗaya kame ya sha wani lallausan zanin gado, da pillows kai ba kace gadon mutum ɗaya ba ne. A gefe guda wata ƙaramar kujera ce er ubansu da ke ɗauke da ƙananan pillows, gabanta kuma da wani centre table me kyau. Wajen TV kuwa daban yake, wanda ke ɗauke da wata ƙatuwar TV kamar wadda mutanen cikinta zasu iya fitowa. Lolz 😹 A can gefenta kuma wata wuta ce ke ci a wani keɓantaccen waje, irin wadda ke bawa ɗaki ɗumin nan, tana ci a hankali babu hayaniya. Kai tsayawa ma faɗar abubuwan da ke cikin bedroom ɗin ɓata lokaci ne, saboda yadda ya ji kaya. A hankali cikin takunnan nasa me kyau da ɗaukar hankali ya ƙarasa wajen labulen da ke zagaye da ɗakin, ya saka hannu ya yaye ɗaya, nan take glasses ɗin da ke a wajen suka bayyana, wanda bayan glasses ɗin wasu uban shuke_shuke ne masu matuƙar ƙayatarwa da ɗaukar ido. A hankali ya ɗan sauke numfashi yana lumshe ido lokaci ɗaya kuma yana shaƙar ƙamshin da suka cakuɗe waje ɗaya da iskar da ke kaɗawa me daɗin shaƙa. Ya kai wajen minti 2 a haka sannan ya koma gaban wata muguwar wardrobe da tsayawa faɗar yadda ita kanta ta haɗu ma ɓata lokaci ne, ya buɗe ya ɗauki jerarrun kayansa da aka shirya su ciki kana ya wuce toilet. Kamar yadda bedroom ɗin ya haɗu haka shi kansa toilet ɗin ya haɗu kamar ba banɗaki ba. Yayi wajen minti 30 kafin ya fito ɗaure da towel babba, jikinsa babu abin da ke tashi se ƙamshin sabulunsa me daɗin ƙamshi da ya haɗe da ƙamshin jikinsa da kodayaushe baya barinsa. Kasancewar be hautsina kansa ba ya sanya shi ɗaukar comb ya taje shi sama sama, sannan ya shirya kansa cikin wasu riga da wando kana ya feshe jikinsa da turaruka masu ƙamshi sannan ya nemi waje ya zauna. Wayarsa ya janyo kai tsaye ya shiga wajen message, ya turawa Mom gajeren saƙo kamar haka "Sorry Mom, ka da ki ji ni shiru, zan ɗan yi bacci kaɗan.." daga haka ya ajje wayar a gefensa, ya haye lallausan gadonsa kana ya ja blanket yana rufe jiƙaƙƙun eyes ɗinsa da har yanzun akwai ruwa a lashes ɗinsa. .. Da mamaki ta kalli Jadwa tace "Baƙuwa kuma? Anya ni?" "Aikam dai wajenki ta zo, may be daga gida aka mata kwatance." "Ohk" ta faɗa tana saukowa daga gado ta ɗauki wani ƙaramin mayafi ta ɗaure sassalkan gashin kanta da ke a buɗe kuma a tsefe. Ƙarasawa tayi da sauri tana faɗin "Oyoyo Masoyiya!" Ta faɗa tana rungumeta. Rungume juna suka yi cikin farin cikin ganin junansu kafin suka saki juna kowaccensu ta nemi waje ta zauna. "Sannu da zuwa." Lulu ta faɗa tana murmushi. Murmushin itama Fatima Kabeer ɗin ta maida mata da shi sannan tace "Yawwah Masoyiya, se kika ganni a gidan nan kawai." "Wallahi kuwa, amma fa na ji daɗin zuwan nan naki." Kafin Lulun tace komai Jadwa ta fito daga ɗaki sanye cikin riga da wando kamar koda yaushe, ta ƙarasa ta rungume wata budurwa da ta shigo ɗakin. Itama budurwar rungumeta tayi, Jadwa na faɗin "Oyoyo Ƙawata." Kallansu Fatima tayi dan yadda suka bata mamaki, yanayin yadda suke rungumar ma kaɗai ba irin tamu ce, irin ta turawan nan ce da ake sumbatar gefen kumatu. Juyawa tayi ta kalli su Lulu tace "Hey sannunku." "Yawwah" suka amsa kusan a tare, sannan suka wuce ɗakin Jadwa. "Kee!" Lulu ta faɗa tana kallan Fatiman. Se da ta sauke ajiyar zuciya bayan ta juyo sannan tace "Masoyiya!" "Na'am" Lulu ta faɗa. "Life style ɗinku ba iri ɗaya da ta en gidan nan ba ce, kalli yanda suke abu kamar wasu turawa, kalli shigar er gidan, ina baki shawara da don Allah kar ki biyewa wannan yarinyar, ki din ga kaffa kaffa a komai. Amma kiyi haƙuri idan ba ki ji daɗi ba." Ta faɗa da ita gaskiyarta. "Toh na ji." Harara Fatima ta jefa mata sannan tace "Ai na san halinki ne, ni dai na faɗa miki." Ba dan bata so ta ja maganar da nisa ba da ta tambayi Masoyiyar meye aibun shigar Jadwa? Su suna rayuwa ne babu ruwansu da kowa, rayuwar 'yanci suke gabatarwa a gidan nan, kowa yayi abin da ya ga dama, babu me takura masa. Ba sa saka ido akan kowa, kamar yanda ba sa so a saka musu ido. Ba ta wani daɗe ba Fatiman ta yiwa Lulu sallama ta tafi, cikin jin daɗin zuwan nata Lulu ta rakata har gate sannan suka yi sallama ta koma cikin gida. .. Kamar za tayi kuka tace "Little don Allah ina ka jefa min shi?" Ta faɗa tana cigaba da duba cikin ɗakin. "Yana can fa." Little da ke shirye cikin Uniform ya faɗa yana nuna mata gefen gado. Sake dubawa tayi, kamar ɗazun dai yanzun ma babu komai a wajen, hakan ne ya sanyata kallan Little ɗin ta galla masa harara daidai lokacin da Ammi ta shigo cikin ɗakin. "Afrah wai me kuke yi ne har yanzun ba ku fito ba?" Ammin ta faɗa tana ƙarasowa cikin ɗakin. "Ammi Little ne fa ya ɗaukar min niƙab, kuma be san inda ya jefa ba!" Kallan Little Ammi tayi tace "Ina ka jefa mata?" Se da ya tura baki sannan yace "Na manta" Maida dubanta kan Didi Ammi tayi tace "Kin ga wuce ku tafi, kada ku makara, zan duba miki In Sha Allah kafin ku dawo." Kamar za tayi kuka tace "Tohm." Tana jin duk babu daɗi, saboda ta saba fita da niƙab ɗin zuwa ko ina, idan har dai ba boko ba. Hannunta riƙe da na Little suke tafiya, se hira yake mata yana tsalle_tsallensa, ita dai amsarta duka bata wuce "Ehh ko A'ah" gaba ɗaya hankalinta ya tafi kan makarantar da take Allah Allah su isa saboda rashin niƙab. "Fatabarakallahu Ahsanal Khaliqin." Ya faɗa yana sake buɗe idanu dan cigaba da kallan wannan kyakkyawar halitta da a ganin farko ta tafi da shi. A karon farko ya ayyana wa kansa tabbas ya samu matar aure, dan a yadda ya ji zuciyarsa ta harba daga lokacin da yayi arba da Didi. Saurayi ne da aƙalla ze kai shekara 29 baƙi se dai ba can ba, babu laifi kyakkyawa ne, yana cikin manyan kaya masu haɗe da babbar riga, hakan ce ta kara masa kwarjini, yana kame cikin motarsa me kyau, shi yake driving da kansa, se dai ganin Didi da yayi ya sanya shi dakatawa. Ganin alamar tana neman kuɓuce masa ne ya sanya shi saurin cigaba da driving ɗin cikin takatsantsan ya soma binta. Sam bata lura da wata mota da ke binsu ba har suka isa makaranta. Ko da taje makarantar ma duk se take jinta a takure, dan ta gama sabawa da niƙab ɗin musamman a Islamiyya. Lulu da ke kusa da ita tace "Didi wai duk kin kasa sukuni akan wannan abun." "Ina ruwanki?" Didi ta faɗa tana murguɗa baki. Murmushi kawai Lulu tayi tana maida dubanta kan Abida da ta juyo daga bench ɗin gabansu tace "Hajiya Afaaf, kin dai ƙi zama ƙawata. Amma na fi tunanin Masoyiyarki ce ke hanaki kulani." Kallan juna Lulu da Masoyiyar suka yi se suka saka dariya. Ɗan cizar leɓenta na ƙasa Abida tayi kafin ta rufe idanunta sannan ta buɗesu a lokaci guda, Allah ma ya gani ba tun yau ba Lulun ke matuƙar birgeta, tana birgeta yadda ya kamata, se dai ta ga ita ɗin ba ta wasa bace, amma za tayi iya ƙoƙarinta wajen ganin tayi wani abun da ze sa su soma samun kusanci har ta saki jikinta da ita, kafin ta fito mata a mutum, se dai za ta bi komai a nutse ba za tayi gaggawa ba. Babu daɗewa Gwani ya shigo ajin kamar ko da yaushe cikin irin shigar nan da ya saba yi wadda ke matuƙar yi masa kyau da sake fito da ainahin kyawunsa da kwarjininsa. Daga shigowarsa kowa ya nutsu. Babu ɓata lokaci ya nemi waje ya zauna. Kamar ko da yaushe se ya soma karɓar hadda kafin yayi littafi, hakan ne yasa ya fara karɓa babu ɓata lokaci. Da yake a jere kawai yake karɓar haddar, yana gama karɓar ta Didi, se Lulu da ke kusa da ita ta gyara zama ta cigaba da zamanta tana ɗaɗɗaure fuska irin dan kada ma ya ga fuska bare yayi mata magana. Se dai ga mamakinta se jinsa tayi yace, bayan wajen rabin minti "Kee!!" Bata juyo ba duk da tayi tunanin da itan yake, se dai ta nuna kamar ta ɗauka da wata yake. Da sauri Masoyiya tace ƙasa_ƙasa "Lulu da ke fa yake.." Se a lokacin ta juya, bata kalle shi ba tace cikin dakewa "Ban iya ba!" Shiru ne ya biyo bayan maganar da tayi, dan babu wanda ya taɓa tunanin abin da za tace kenan. Jin alamar kamar be ji bane ya sanyata sake buɗe baki za ta yi magana daidai lokacin da yace "Tashi ki fita!" "Ni?" Ta faɗa tana nuna kanta kamar da gasken bata san da ita yake ba. A karo na biyu bayan ɗaukar wasu sakanni ya sake furta "Fita!!" Ya faɗa idanunsan nan cike da fushi, haka zalika muryarsa na fita da wani amo na ɓacin rai, yana jin a wannan lokacin idan dai har tace zata nuna masa rashin tarbiyya a gaban kowa ze hukuntata, hukunci me tsanani ma kuwa. Gaba ɗaya en ajin kallansa suke yi cike da mamakin yanda ya chanja ɗin lokaci guda, kowannensu ya san shi ɗin tsayayyen namiji ne wanda baya ɗaukar raini, baya bayar da fuskar da za a raina shi, se dai yau ɗin ya sake nuna musu real Affan ɗin ne. Kanta ta ɗauke duk da yanda ƙirjinta ke bugawa amma ta riga ta ɗaukar wa kanta alƙawarin babu wanda ya isa ya wulaƙantata musamman ma kuma Malamin makarantar islamiyya. Hakan ne ya sanyata yin shiru tana ɗan lumshe idanunta. Gaba ɗaya en ajin kallanta suke yi, wasu na mamakin taurin kai irin nata, yayin da wasu da suka santa suke jinjina yadda ta iya yiwa Gwanin taurin kai. A hankali Didi ta runtse idanunta tana ji kamar tayi kuka saboda takaicin abin da Lulun ta aikata. Cikin dabara ta kai ƙafarta kan ta Lulun ta taka sosai, har se da Lulun ta juya ta kalleta, suna haɗa ido Didi ta girgiza kai, kyawawan idanunta cike da ƙwalla. Da sauri Lulu ta ɗauke kai, dan sarai ta gane abin da Didin ke nufi. Sam bata son ɓacin ran Didin se dai ita bata bin bayan dizgi ko waye kuwa ze yi mata ba zata ɗauka ba. Se dai cikin dakewa da basarwa ta miƙe a hankali ta soma takawa hannunta harɗe a ƙirji, fuskarta a haɗe ta fice daga ajin. Duk da abin nan da ya faru har ta fita ɗin ba ka jin motsin kowa, ko na surutunsa, kowa ya bar maganar ne a ransa, imma dai idan Gwani ya fita su tattauna ko kuma idan aka tashi. Kwantar da kanta Didi tayi akan bench ɗin gabanta tana sauke ajiyar zuciya. "Why Lulu?" Ta faɗa akan laɓɓanta har zuciyarta tana jin babu daɗi sam. Se dai a wannan karon tana ganin dole ne ta faɗa wa Ammi abin da Lulun take yi dan ayi wa tufkar hanci tun yanzun. Da sallama ya shiga Office ɗin me makarantar, ya nemi waje ya zauna fuskarsa a cunkushe babu fara'a, da yake dai dama can ba wata fara'a gare shi ba so yanzu ma idan ka ganshi ba zaka gane a wane yanayi yake ciki ba, se dai shi kaɗai ya san yadda yake jin ɓacin rai a yau ɗin. "A'ah Malam Affan, Barka da zuwa." Malam Ahmad ya faɗa yana murmushi. "Yawwah." Ya faɗa a nutse. Baya san ɓata wani lokaci hakan ne ya sanya shi faɗin "Amm, wata magana ce.." "Toh Ikon Allah, ina jinka." Malam Ahmad ya faɗa yana kallansa cike da mamaki, dan kuwa ba kasafai Gwanin ke zuwa da wata maganar ba. A nutse ya soma faɗin "Magana ce a kan er uwar Afrah Muhammad Aji, na koreta daga ajina!" Numfashi Malam Ahmad ya sauke yana tuna Afaaf ɗin, tabbas ya san yarinyar ba ta ji, amma be taɓa tunanin har zata iya yiwa Gwani wani abun da ze sa har ya koreta ba. Ya riga ya san Gwanin ba ze yanke hukunci babu ƙwaƙwƙwaran dalili ba, dan haka tambayarsa dalilin yin hakan ma kamar ba shi da wani amfani, dan haka yace "Kayi haƙuri Malam Affan, kayi haƙuri. Wallahi ka san yarinyar muna fama da ita, ba dan ma muna da tsayayyun malamai ba. Duk da yarinya ce amma gani take kamar kanta ɗaya da kowa, amma In Sha Allah zamu san yanda za a yi a yiwa tufkar hanci." Furzar da iska Gwani yayi lokaci ɗaya yan ɗan lumshe idanunsa kafin ya buɗesu yace "Ka yi haƙuri Malam Ahmad, amma se dai ko ni na zauna a ajin, ko kuma ita ta zauna ni na bar ajin.." Wajen second 30 Malam Ahmad ya soma faɗin "Da ka duba al'amarin nan Malam Affan, ka yi haƙuri, ba wai dan ina sama da kai a cikin makarantar nan ba ne, dan ka san idan Addini ne kai ɗin number ɗaya ne. Ba komai ne ya sa nace kayi haƙuri ba se dan kai ɗin na daban ne, kai ɗin me iya zama da ɗalibai ne masu kowanne irin hali sannan ka chanja su cikin ƙanƙanin lokaci. Zaka iya zama da wannan ɗalibar Malam Affan, kamar kuma yadda nake fata ta chanja, ta koma kamar er uwatta. Se dai a wannan karon ba ze yiwu a barta haka ba, zata iya kasancewa mahaifinsu be san abin da take aikatawa ba, saboda mahaifinsu mutumin kirki ne na sosai. Dan haka zan saka a sanar da shi muna son ganinsa, idan ya so se ku yi magana da shi." A wannan karon shiru Gwani yayi sanda ya gama saurarar maganar Malam Ahmad ɗin sannan ya gyara zamansa a kan kujerar da yake kai.. *♡☆A JINI TAKE☆♡* *(IZZATA)* By _*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_ *CHAPTER ONE* Page_07 "Shi kenan!" Shi ne abin da Gwani ya faɗa yana miƙewa, ya miƙawa Malam Ahmad hannu suka sake gaisawa sannan ya fice daga Office ɗin. A tare suka fito daga cikin makarantar, se dai Didi ba tace da Lulu ko uffan ba, wanda hakan ke alamta mata fushi take da ita. Ita kuma a yanda take jin zuciyarta dama yanzun ba za ta iya cewa komai ba. Idan kuwa tayi ƙoƙarin furta ko da kalma ɗaya ce to kuka ne ze ƙwace mata, and idan hakn ta kasance kuma ba zata taɓa yafewa kanta ba, hakan ne ya sanyata sake haɗe fuska waje ɗaya tana iya ƙoƙarinta wajen ganin ta riƙe kanta kukan be taho ba dan kada ta yarfa kanta. "Se da safe." Didi ta faɗa ba tare da ta kalleta ba, daga haka tayi gaba hannunta riƙe da na Little. Binta da kallo Lulu tayi, mamakin yadda tayi fushin na sake kamata, bata taɓa tunanin akan Gwani Didin kan iya fushi da ita ba. Da dai ta ga alamar da gaske Didin take ta tafi kenan, se ta soma jan ƙafafunta kafin ma en ajin na su su gama fitowa tayi inda motar da zata ɗauketa ke tsaye. Daidai lokacin ya ɗago kai cike da sarewa, dan a yanzu kam be taɓa tunanin ze iya ganinta ba, ya gama fidda rai, bayan daɗewar da yayi a wajen ta sama da awanni. Se dai me? Yana ɗaga kai ya hangi Lulu na neman shiga motar. Cikin matuƙar farin ciki ya furta "Alhamdulillah!" Yana tayar da motarsa. Babu daɗewa driver ya ja motar da Lulu ke ciki ya soma tafiya, cikin ƙwarewa shi ma ya soma binsa har zuwa sanda suka isa gidan Mami. A bakin gate ɗin ya tsaya yana kallan gidan, ba dan akwai abin da ze yi yanzu ba, da tun yanzun ze fara zuwa wajen nata, se dai kuma ance gaggawa aikin sheɗan ne, dan haka gwara ya bari zuwa goben se ya zo. Hakan ne ya sanya shi tashin motarsa ya bar layin cike da farin cikin samun gidansu Lulun. Ko jakarta Lulu bata iya ɗauka ba ta fice daga motar da gudu. "Subhanallahi, daughter me ya faru?" Mami ta faɗa tana miƙewa tsaye, babu ɓata lokaci Lulu ta ƙaraso ta faɗa jikin Mami tana fashewa da kuka. "Na shiga uku ni Sadiya, Lulu me aka miki ne? Waye ya taɓa min ke?" Se da tayi me isarta sannan ta buɗe baki ta soma korawa Mamin abin da ya faru tana jin kwata kwata babu daɗi. "A gaban en ajin ya yagaki haka? Shi be san wacece ke ba? Be san kin fi ƙarfinsa ba shi ne ze miki haka? Toh makaranta ce kin dena zuwa daga yau, zan yi magana da Yayan." Mami ta faɗa a kufule. Cikin jin dadi Lulu tayi murmushi kafin tace "Ko Mamina?" "Ƙwarai kuwa ɗiyar albarka, ai kin fi ƙarfin wulaƙancin kowanne ɗa namiji ballantana kuma malamin islamiyya. Kada ki damu daga yau kin dena zuwa makarantar nan." Miƙewa tayi duk da yanda take jin zuciyarta na zafi amma sosai taji dama_dama da maganganun Mamin, ko babu komai sun sanyaya mata zuciya, hakan ne ya sanya ta wuce ɗaki. .. Ko sallamar da yayi a ciki_ciki yayi ta, Ammi da ke zaune kan kujera ta amsa sallamar tana kallansa. Se ta miƙe tana faɗin "Sannu da zuwa" "Yawwah, maza ɗauko min takaddun nan zan fita ne." "Ikon Allah, sake fita kuma zaka yi?" Ammi ta tambaya, se dai ganin yanayinsa kamar a ɗan fushi ya sanyata faɗin "Allah dai yasa lafiya!" Ajiyar zuciya Abba ya sauke sannan yace "Ni dama na san kiran nan da aka min a makarantarsu yaran nan akwai wani abun, dan kuwa basu taɓa yi min haka ba. Ashe ban sani ba kara suke min, suna ta ɗaga min ƙafa ban sani ba. Ashe yarinyar nan tana can tana ƙoƙarin zubar min da mutunci da kimata wajen malamanta, bata duba girmansu, darajarsu da kuma kimarsu, tana yin abu kamar bamu bata tarbiyya ba?" Abba ya ƙare cikin fushi kamar Lulun na gabansa. "Hasbunallahu wa ni'imal wakeel!" Shi ne abin da Ammi ta faɗa tana komawa kan kujera ta zauna. Se dai kafin ta gama tunanin ballantana ta kai ga cewa komai ta jiyo muryar Abban na faɗin "Zuwa zan yi na ɗakkota, ta dawo ta cigaba da zama a gidan nan, a gabana ina kallan abin da take yi hankalina ze fi kwanciya. Sannan kuma tun a can ɗin wallahi zan hukuntata tun da bata da kirki." Se a lokacin Ammi ta miƙe tana girgiza kai tace "A'ah Abba kayi haƙuri don Allah, kome zaka yi mata ka bari ku dawo gida tukunna, sannan ka ɗan sassauta fushin nan naka kafin ka fita, ka san fushin ba shi da wani alfanu.." Sauke ajiyar zuciya Abba yayi yana faɗin "In Sha Allah.." A ɗaya ɓangaren kuwa su ukun ne zaune a parlour suna kallo a ƙatuwar TVn da ta ƙawata parlourn. Jadwa da ke zaune kujera ɗaya da Lulu ta juya ta kalli Mami sannan tace "Mami wae yaushe Abbu ze dawo?" "Baki na fiki koh?" Mamin ta faɗa tana jefa mata harara. Kafin Jadwan ta kai ga cewa komai se ga sallama daga bakin parlourn. Jin sallamar me gadinsu ne ya sanya Mami faɗin "Shigo!" Duk kuwa da irin shigar da ke jikinsu hakan be sanyasu tashi sun ɗauki ko da mayafi ne sun rufe jikinsu ba ko dan kasancewarsa ba muharraminsu ba. Babu daɗewa kuwa se ga shi ya shigo cikin ɗakin. Ya durƙusa har ƙasa yana faɗin "Hajiyoyi barkanku da wannan lokaci.." "Barka dai" Jadwa da Mami suka amsa da hakan, yayin da Lulu hankalinta gaba ɗaya ke kan TV saboda ana haska wani favourite movie nata ne. "Me ya faru?" Mami ta katse shi da faɗin hakan. "Kun yi baƙo ne, yana ƙofar gida, yace yana buƙatar ganin wata daga cikin gidan nan, nafi tunanin irin baƙin nan naki ne hajjaju, shi yasa nace bari na zo na faɗa miki!" "Yana tsaye a bakin gate kuma?" Mami ta faɗa tana kallansa. Se ya girgiza kai yace "A'ah da yake a mota yake, toh har yanzun ma yana ciki.." "Ohk, ka faɗa masa ya shigo, ka kai shi ɗakin baƙi, gani nan zuwa." Mami ta faɗa tana miƙewa. Babu musu ya miƙe yana faɗin "Toh Hajiya." Ɗaki Mami shiga, babu daɗewa ta fito, kai tsaye ta wuce ɗakin baƙi. Da sallama ta shiga cikin ɗakin, hannunta ɗauke da wayarta, ba yau ne karon farko dama da take karɓar baƙi kala_kala ba, musamman akan aikinta, se dai yau ɗin bata san da zuwan wannan ɗin ba, abin da ya bata mamaki kenan. Sanye yake cikin shadda, ɗinkin babbar riga kamar ranar farko, yau ɗin ma sun amshe shi babu laifi, yana kame a cikin kujera. Amsa sallamar yayi sannan ya juyo yana kallan me shigowar. Kusan a tare suka faɗi sunan junansu kowannensu cike da mamakin ganin ɗan uwansa. "Kaseem!" Mami ta sake faɗa tana ƙarasowa cikin ɗakin. "Kai ne a gidan nawa?" Ta tambaya tana neman waje ta zauna a kan kujera. Duk da yayi mamakin ganinta a gidan hakan be hana shi faɗin "Wallahi kuwa ni ne Madam." "Ikon Allah, toh ya kake? Ya aiki?" Ta tambaya. Nan dai suka gaisa cike da sabo sannan Mami tace bayan shuɗewar wasu sakanni ba tare da kowa yace komai ba "Anya kuwa gaisawa da ni ka zo yi?" Murmushi Kaseem yayi yana ɗan gyaran murya sannan yace "Madam ina ganin fa da alama kina dab da zama sirikata.." buɗe ido Mami tayi kafin tace "Woww, da gaske?" Se da ya jinjina kai sannan yace yana murmushi "Ƙwarae kuwa, dan kuwa a jiyan nan na ga ɗiyarki, na kuma ga nan gidan ta shigo, hakan ne ya sanyani biyo sawu." Cikin matuƙar farin ciki Mamin tace "Woww, amma gaskiya na ji daɗi, na yi farin ciki Kaseem." Ta faɗa tana jin wani irin daɗi na ratsata, dan kuwa tun da yayi maganar ita Jadwa kawai ta hango ta kuma san ita yake nufi, idan kuwa har Jadwan ta amince to fa shi kenan ta samu mijin aure na nunawa sa'a, dan kuwa Kaseem ɗin akwai abin hannu. Be ce komai ba ban da murmushi da ya sake yi. Sakkowa daga kan kujerar Mami tayi tana faɗin "Bari na kira maka ita." Ɗan zamowa yayi daga kan kujerar da yake kai yace "A'ah da kanki kuma." Ya ƙare yana murmushi. Itama murmushin tayi kana tace "Toh mene ne Kaseem? Kada ka damu." Tayi maganar tana ficewa daga ɗakin. Ajiyar zuciya ya sauke yana jin lallai tabbas komai ze zo masa da sauƙi In Sha Allah. Cikin matuƙar farin ciki da jin daɗi Mami ta faɗo dakin fuskarta murmushi yaƙi barinta tun ɗazu. "Maza maza tashi ki je kin yi baƙo." Mamin ta faɗa tana dukan ƙafar Jadwan. "Baƙo kuma?" Jadwa ta faɗa cike da mamaki, dan dai ita ta san ba suyi da kowa ze zo wajenta ba. Jinjina kai Mami tayi tana faɗin "Ƙwarai kuwa, tashi.. Lulu maza tashi ki tayata shiryawa kin ji?" Ta ƙare maganar tana kallan Lulu. Babu musu kuwa Lulu ta miƙe daga kan kujerar tace tana kallan Jadwa "Mu je!" "Kin ji ki kema, in je ina?" Tsaki Mami ta ja kafin tace "Shashasha sakarya, da alama yau kin yi babban kamu, kamun da idan dai har ba wasa kika yi ba kin yi dace da smaun miji me kuɗi kuma na gari.. Ina Kaseem da kika sani a baki?" Da sauri Jadwa tace "Ehh.. ehh.." "Toh shi ne yazo wajenki." Mami ta faɗa. Da sauri Jadwa ta diro daga kan kujerar tana faɗin "Kai Mami.." Hannunta Mami ta kama tace "Maza mu je ki shirya pls, ka da a ɓata masa lokaci" Yanzu kam babu musu Jadwan ta bi Mami zuwa ɗaki. A wannan karon ita dai Lulu taɓe baki tayi kawai ba tace komai ba se bin bayansu da tayi. Wasu haɗaɗɗun kaya Mami ta fitowa da Jadwa su, babu musu ta ɗauka ta saka, sosai kayan suka mata kyau, suka zauna ɗass a jikinta, ta ɗauki ƙaramin mayafi ta saka sannan ta shafe fuskarta da powder. "Ki ɗan yi kwalliya mana ko yaya ne!" Mami ta faɗa tana kallan Jadwan, dan ita dai tafi so ta ƙure wanka a yau ɗin. "Mami haka ma fa ya isa." Ta faɗa tana ajje turaren da ta gama fesawa. Da sauri Mami ta karɓa tana faɗin "Shashasha, har kin gama sakawa? Ni gyara min na sake feshe miki jiki da shi, so nake na ji ko ina na jikinki na tashin ƙamshi." Ta faɗa tana sake feshe turaren a jikin Jadwa.. Ku yi manage da wannan pls, mu haɗe gobe idan Allah ya kai mu. *♡☆A JINI TAKE☆♡* *(IZZATA)* By _*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_ *CHAPTER ONE* Page_08 ___Ita dai Lulu binsu kawai take da kallo, se kace waɗanda aka ce an musu albishir da wani abun na musamman, ko kuma za su je su ga wani abun na musamman ne. Sosai Mamin da ita kanta Jadwan suka bata mamaki, duk yanda suke amma a kan namiji sun bi sun ruɗe kamar ba su ba. Ɗan taɓe baki kawai tayi tana bin Jadwa da kallo sanda ta zo gaban mudubi tana juyi tana kallan jikinta. Zagayeta Mami tayi tana murmushi tace bayan ta ɗaga yatsanta ɗaya alamar jinjina "U look so take away.." Murmushi Jadwa tayi sanda take faɗin "Awwwn, Mami ki bar zugani haka nan." Komawa Mami tayi ta zauna kusa da Lulu sannan tace "Heyy! faɗa mata tunda ni sa'arta ce" yaƙe kawai Lulu tayi kamar ba za tace komai ba, se kuma tace "Sosai ki ka yi kyau fa.." "Mami, bari na je, kada yayi ta jira." Jadwa ta faɗa bayan ta sakarwa Lulu murmushi. "Toh se kin dawo." Mami ta faɗa, ita kuma Jadwa ta fice daga ɗakin. A hankali take takawa tana wani rangaji kamar agwagwa, ƙafarta dake ɗauke da hill shoe tana bada sautin 'ƙwas_ƙwas'. Ɗan lumshe idanunta tayi sanda tazo dab da shiga ɗakin tana sauke numfashi, dan bata taɓa ganinsa a fili ba. Da sallama ɗauke a bakinta ta shiga ɗakin, cikin matuƙar farin ciki yadda yake tunanin ze yi arba da kyakkyawar fuskar da ta hana shi bacci tun ranar da ya soma ganinta ya ɗaga idanunsa ya sauke a kan Jadwa da ke cigaba da takowa cikin ɗakin. Shi da ya buɗe baki da niyyar amsa sallama cike da karsashi duk se yaji jikinsa yayi matuƙar sanyi, hakan ne ya sanyashi ƙarasa sallamar a hankali. Ba tare da ta kalli inda yake zaune ba, ita a lallai dole me kunya, ta nemi waje ta zauna sannan tace "Barka da zuwa. Ina wuni?" Ta ƙare maganar tana ɗago wa ta kalle shi. Ƙaƙalo murmushi yayi yace "Yawwah, barka dai." Se dai duk hankalinsa yafi tunanin meyasa ya ga daban da wadda ya gani a jiya? Toh ko dai rakiya tayo ne? Abar ƙaunarta sa na ciki? Hakan da ya tuna ne ya sanya shi ɗan gyara zama sannan yace "Sannu koh? Ya makaranta?" Wani irin daɗi ne ya ziryarceta tace bayan itama ta gyara zama tace "Alhamdulillah." "Madallah." Ya faɗa. Daga haka se shiru ya mamaye ɗakin, ita tana jira yace wani abun, yayin da shi kuma yana jira ne ya ji tace 'yar uwarta ta na nan zuwa. Jin shiru ya sanya shi faɗin "Amm sisterta ki fa?" Ya tambaya yana murmushi. Da mamaki ta ɗago ta kalle shi, se kuma ta ɗan basar tace "Sisterta kuma?" Ta tambaya a mamakance. Yanzu kam shi kansa abin ya bashi mamaki, shi dai ya san tabbas ba wannan ya gani ba, amma ya tabbatar wadda ya gani gidan nan ta shigo kuma yanzu an turo masa wata a matsayin ita ya gani. Shi kam sam ba ze yadda yayi saki na dafe ba, hakan ne ya sanya shi faɗin "Amm, na haɗu da wata ne tana shirin shiga Islamiyya, so na bi bayanta na ga kuma gidan nan ta shigo." Cikin mintuna ƙalilan Jadwa ta ji jikinta yayi wani bahagon sanyi, duk wannan kunyar da ta aro ta yafa ta ji tana warewa zuwa na ta wajen. Se kawai ta basar tace "Ohh lem me call her." Ta faɗa tana miƙewa. "Ohk.. Thanks sistor.." ya faɗa yana murmushi gami da binta da kallo sanda take ficewa daga ɗakin. Haushi ita kuwa ya sake cikata, wato har da wani kiranta da sister duk wannan uban kashe kalar da tayi. Cikin sauri da kuma takaicin da ya cikata take tafiya har zuwa parlourn. Jefar da mayafinta tayi a kan kujera, tana tuna yanda mutuncinta ya gama zubewa a wajen Kaseem ɗin. "Kee! Me ya faru?" Mami ta faɗa tana ƙarasowa cikin ɗakin. Saboda yanda take jin zuciyarta na wani irin zafi yasa ta kasa furta ko kalma ɗaya se ajiyar zuciya da take ta saukewa. "Oh ni Sadiya, ba dai wannan banzan halin naki kika nuna masa ba?" Mami ta faɗa bayan ta zauna. Shirun dai Jadwa tayi har lokacin tana tuna wannan cin mutuncin. "Wai ba za ki min magana ba ne?" Mamin ta faɗa a ɗan zafafe, dan zuwa yanzun ta fusata. "Mami dama kin san ba wajena ya zo ba amma kika ce na je? Ba kya tsoron mutuncina ya zube?" Hannu Mami ta saka ta dafe ƙirji kafin tace "Ke ban san shashanci mana, kamar yaya? Toh idan ba wajenki ya zo ba, wajen wa ya zo? Ko ina da wata ɗiyar ne bayan ke?" "Lulu!" Jadwa ta faɗa kai tsaye. Shiru Mami tayi tunda Jadwan ta ambaci sunan Lulu. Daga lokacin da Kaseem yayi zancen ya ga wata a gidanta ita sam ta manta da Lulu, kawai Jadwa ta hango, ashe ta manta akwai wata a gidan bayan Jadwa. Ajiyar zuciya ta sauke tace tana jinjina kai "Tirƙashi!" "Mami ba tunani zaki tsaya yi ba fa, nace masa zan kira masa ita ne, and am sure yanzu haka jiranta yake." Jadwa ta faɗa. Kallanta Mami tayi tace "Ina zuwa!" Ta faɗa tana miƙewa ta fice daga ɗakin. Daidai lokacin da ta fito yayi daidai da lokacin da motar Abba ta shigo gidan. Se kawai ta ƙarasa wajen, daidai sanda ya fito daga cikin motar. "Sannu da zuwa Yaya." Ta faɗa bayan ta ɗan rusuna. "Yawwah." Ya faɗa ba yabo ba fallasa. Hakan da Mami ta lura da shi ne ya sanya ta ji duk jikinta yayi sanyi, se ta kalli Abban da ke faɗin "Ina yaran suke?" "Suna ciki.." ta ɗan dakata anan sannan ta ɗora da "Ka shiga Yaya, ina da baƙo ne. Zan je na sallame shi yanzun nan se na zo." "Toh ki yi da jiki." Da "toh" ta amsa tana yin gaba, yayin da ita kuma ta shige cikin parlourn. Duk jikin nata a sanyayen dai ta ƙarasa ɗakin da Kaseem ke ciki, yanzun ma ya ɗauka ze ga Abar begen tasa ne se ya ga Mami ta shigo. Se da suka sake gaisawa sama_sama sannan Mami tace "Wato Kaseem ka taki rashin sa'a dan kuwa yarinyar da kake nema bata nan, kuma yanzu haka Yayana yazo. Amma In Sha Allah zamu yi magana da kai ko da ta waya ne se na haɗaka da yarinyar.." Ba dan ya so ba ya amsa da "Toh, na gode sosai Madam, Allah ya kai mu. A gaishe min da Yayan." "Toh ze ji. Ka gaida gida." Ta faɗa sanda yake dab da ƙarasawa bakin ƙofa. Se da ya fice da motarsa daga gidan sannan ta sauke ajiyar zuciya tana dawowa cikin gidan. A parlour ta samu Abba zaune ta ƙarasa suka sake gaisawa sannan ta miƙe tana faɗin "Bari na kirasu, da alama basu san da zuwanka ba." Be ce mata komai ba ta shige ɗakin. "Lulu fito ga Abba ya zo." Ta faɗa bayan ta shiga ɗakin. Da sauri ta ɗauki hula ta ɗora a kanta tana faɗin "Don Allah Mami?." Ta faɗa tana jin wani irin daɗi, dan ba ƙarya tayi missing Abban nata sosai. Murmushi Mami tayi kana tace "Ke dai fita ki tabbatar." Se ta fice daga ɗakin da sauri cike da zumuɗin son ganin Abban nata. "Abba sannu da zuwa." Ta faɗa sanda ta zauna a kusa da shi tana murmushi. Se ya kasa ƙin amsa mata saboda fushin da ya taho da shi yace "Yawwah.." "Abba na yi kewarku sosai." Ta faɗa tana kwaɓe fuska da iya gaskiyarta. "Je ki ɗakko kayanki ki wuce mu tafi." Abba ya faɗa, ita sam bata kawo komai game da maganar Abban ba, hakan ne ya sanyata miƙewa dan zuwan Abban ya sa ta tuna yanda tayi kewar gida. "A'ah Yaya lafiya kuwa?" Mami ta faɗa tana riƙo hannun Lulu. Abin da ya dakatar da ita kenan, se kuma itama ta juya tana kallan Abban "Ba lafiya ba. Daga yau ta gama zuwa ko ina, gwara ta zauna a gabana na dinga ganin duk wani abu da take yi." Da sauri dukansu suka buɗe ido suna kallan Abban. Anya kuwa da gaske Abban yake? Me Lulun tayi? Me aka ce masa tayi? Jan hannunta Mami tayi dan zama a kan kujera, se ta zame ta zauna a ƙasa, yayin da Mamin ta zauna a kan kujera tana kallan Abba tace "Me aka ce maka tayi Yaya? Me ya faru?" Shiru Lulu tayi tana jin yanda jikinta ke rawa, musamman yanda ta ga lokaci ɗaya yanayin Abban ya chanja kamar ba shi ba, har idanunta se da suka kawo ƙwalla, dan kuwa kafin Abban yayi fushi da su ana daɗewa. "Ashe abin da take yi kenan a makaranta? Ni zata zubarwa da mutunci? Afaaf ni zaki zubarwa da mutunci?" Abba ya ƙare maganar yana kallan Lulu. Zuwa lokacin oily eyes ɗinta sun gama cika taff da ƙwalla ƙiris ya rage ta zuba. Sosai ƙirjinta ke bugawa, tana tsoron fushin Abban, dan a lokacin da yayi fushi se ka ji ka tsani kanka. Kafin ya sake cewa komai Mami tace "Wani abu aka ce maka tayi Yaya? Hala basu faɗa maka abin da suke yi mata ba? Wallahi nan yarinyar nan ta dawo gida tana kuka kamar wadda akama mutuwa. Ni maganar ma da nake cewa nayi zan maka magana a cireta daga makarantar, ko anan unguwar ne in sama mata wata ta shiga, tunda dai ba iya makarantar ce kawai a duniya ba. Wallahi cin kashin da suke wa Lulu yayi yawa, nan ta zauna tana faɗa min abubuwan da ake mata kamar nayi mata kuka. Haka kawai sun tsaneta babu gaira babu dalili." Ta dakata anan. Kusan second 10 sannan Abba yace "Kin gama?" Shiru Mami tayi tana yin ƙasa da kanta, dan ta san ma'anar wannan tambayar tasa. "Nace kin gama?" Ya sake tambaya. "Ka yi haƙuri Yaya.." shi ne abin da ta faɗa. Se a lokacin ya sauke ajiyar zuciya sannan yace "Ke! Tashi ki je ki shirya ki fito mu tafi." "Amma da baka tafi da ita ba don Allah. Idan ma wani abun tayi ni me iya yi mata faɗa ce." Ta faɗa sanda Abban ya miƙe. Ya san idan yace ba zata dawo ba be kyauta wa Mamin ba, dan haka yace "Zata dawo tukunna. Amma yanzu kam se na ga kamun ludayinta." Shi ne abin da Abban ya faɗa yana yin gaba. "Shi kenan. Na gode." Mami ta faɗa. Se ta juya ta kalli Lulu bayan fitar Abba ta kama hannunta zuwa cikin ɗaki. Janta tayi cikin jikinta ta rungume kana ta soma faɗin "Ka da ki damu kanki, halin Abban naku ne baki sani ba? Shi faɗansa kin san dai na lokaci ɗaya ne koh? Daga zarar ya wuce shikenan. Saboda haka ki samu ki bashi haƙuri, zan zo gidan da kaina na ɗaukeki mu dawo." Ita dai Lulu saurararta kawai take yi ba dan tana fahimtar abin da take faɗa ba. Da kanta Mamin ta haɗa mata kaya, har lokacin Jadwa na baccin takaicin da ya ɗauketa. Har compound Mami ta rakosu cike da kewar Lulun. Haka dai suka shiga mota, ta ɗaga musu hannu suka bar gidan. Ita dai Lulu ta kasa ko da ƙwaƙwƙwaran motsi ne dan har lokacin jikinta a sanyaye yake da Abban. ... A ɓangaren Bad Man kuwa, tun lokacin nan da ya kwanta bacci, se da ya ɗauki fiye da awa 3 sannan ya tashi. A nutse ya shiga buɗe sexy eyes ɗinsa da suka sake lumshewa saboda baccin da yayi, su a maimakon su yi rashin kyau, se ƙara kyau da suka yi na musamman. Ya kalli cikin ɗakin da yake kamar ne neman wani abu. Se kuma a hankali ya zura ƙafarsa ƙasan gado, ya saka takalmi sannan ya sauko yana ɗan lumshe ido, tun yanzu har ya soma missing na kayan maye, dan haka ya zama dole ya samarwa kansa mafita. Kai tsaye toilet ya faɗa, ya ɗauki fiye da 30min yana wanka kamar me shirin chanja fata, sannan ya fito yana ta zuba wannan ƙamshin nasa kamar na ko yaushe da ke ratsa zuciyar me shaƙarsa. Kamar ko da yaushe yanzun ma cikin riga da wando ya shirya, se dai wannan karon ma cikin crazy jeans ya shirya. Ya riga ya saba duk sanda ya fito daga wanka ya kan tsaya ya chanja ɗan kunnen da yake sakawa, yana shirin juyawa wajen da ya saba ajje su, se ya tuna nan ɗin fa ba California ba ne. Ɗan ƙaramin tsaki ya saki yana sake jin rayuwar Nigeria na sake fice masa a rai. Kawai se ya ɗauki face cap ya ɗora a kan kyakkyawar sumar kansa da ke kwance kamar wadda aka shafawa mai. Tsaff ya gama shiryawa, ya fito sak a Bad Man ɗinsa, se dai abubuwan da ba'a rasa ba waɗanda be yi amfani da su ba dan kasancewarsa a Nigeria. Ɗakin Mom ya wuce kai tsaye, dan ya san ta daɗe tana jiransa. Idan yaso in ya fito se ya je wajen Mommah su gaisa. Shi ya riga ya saba, ko ina ze shiga kai tsaye yake shiga babu sallama, hakan ne yasa yanzun ma a haka ya shiga, hannunsa ɗaya cikin aljihun wandonsa. Wannan ɗin sam ba damuwar Mom bace, tunda dai ya shigo shi kenan. Dan haka tasowa tayi cikin jin daɗin ganinsa tace "Oyoyo my Boy, yanzun nan nake so na zo na tasoka, baccin haka ba ka ci abinci ba ya isa." Ɗan murmushin gefen baki yayi wanda ya mugun ƙawata fuskarsa sannan yace "So gani dai.." ya faɗa yana soma takawa. Sallamar da aka yi daga bakin ƙofar ne ya sanya Mom kallan ƙofar, yayin da shi kuma ya cigaba da takawa cikin tafiyarsa me cike da kuzari. Cike da mamaki take kallan Hajiya Sa'adah da er aikinta Atine da ke shigowa cikin ɗakin. Wani irin takaici da baƙin ciki ne suka kamata lokacin da ta hangi warmers a hannun Atinen. Daidai lokacin da yake ƙoƙarin zama idanunsa suka sauka a kan Hajiya Sa'adah, se ya miƙe da murmushi kan fuskarsa ya ƙarasa inda Mommahn ke tsaye, yana zuwa ya bata side hug yana faɗin "I missed you Mommah." Daskarewa Mom tayi ta kasa ko da ƙwaƙwƙwaran motsi ne. Murmushi Mommah tayi tace "Missed you more Areef. Ka dawo lafiya?" "Yeap!" Ya faɗa a gajarce bayan ya koma gefe ya tsaya yana kallan wayarsa da kira ya shigo cikinta. A hankali Mommah ta ɗaga ido ta kalli Mom da har lokacin take tsaye, ta riga ta san halin Hajiya Sa'adahn, duk yadda aka yi wani abun take shirin yi. Ita bata san me tayi mata ba, bata san me yasa bata san alaƙarta da ɗanta ba. Ita har ga Allah, Allah ma ya ga zuciyarta tana ƙaunar Areef ɗin ne da zuciya ɗaya, amma Mom ɗin ta kasa fahimta, dan ba tun yau ba take raba duk wata alaƙa da zata shiga tsakaninsu, se kuma aka samu sauƙi ya tafi ƙasar waje karatu, shi ne abin yayi sauƙi. Tana so ko yaya ne ta yiwa Areef ɗin wani abun na burgewa a matsayinsa na wanda ya dawo gida daga can wata ƙasa, se dai ta san ba lallai mahaifiyarsa ta bar shi ya shiga ɗakinta ba. Hakan ne ya sanyata ɗakko abin da tayi masa ɗin zuwa ɗakin nata, ta ba shi a gabanta. Atine da ta gaji da tsayuwa ne ya sanyata faɗin "Hajiya na ajje kayan ne?" Jinjina kai Mommah tayi tana kallan Mom tace "Barka da wannan lokaci." Se ta maida dubanta kan Atine tace "Ki ajiye ki fita." Cike da girmamawa Atine tace "Toh Hajiya." Ta faɗa tana yin gaba. Cikin hanzari Mom ta saka hannu ta janyo hannun Atine da ƙarfin gaske tace cikin ɗaga murya "Gidan uwarki zaki je?" Taga_taga Atine tayi kamar zata faɗi, tana ƙoƙarin ganin ta tsaya a kan ƙafafunta amma hakan ya citira, se kuwa ta yi baya, hakan ne ya bawa warmers ɗin da ke hannunta damar faɗuwa a ƙasa da ƙarfi. Cikin lokaci ƙanƙani faɗuwar da suka yi ya bawa abin da ke cikinsu damar tsarwatsewa cikin parlourn.. *♡☆A JINI TAKE☆♡* *(IZZATA)* By _*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_ *CHAPTER ONE* Page_09 ___Kusan a tare dukkansu suka kai dubansu inda abincin ya zube. Ɗan runtse idanunta Mommah tayi har cikin ranta tana jin ɗacin abin da Mom ɗin tayi. A hankali ta mayar da kanta kan Atine da ke zaune a wajen kamar wadda aka koro, tayi zuru_zuru, cike da mamakin abin da Mom ɗin tayi, da kuma tausayin Mommah da ta tabbatar ta shafe awanni da dama tana yin girkunan nan duk dan Areef ɗin. "Mu je." Mommah ta faɗa cikin sanyayyiyar muryarta me cike da nutsuwa. Bata jira Atinen tace komai ba tayi sauri ta fice daga ɗakin. Se a lokacin sannan Atine ta ɗaga ƙafafunta itama ta fice daga ɗakin ba tare da ta bi ta kan warmers ɗin ba. Ɗan lumshe ido Bad Man yayi yana cije lips ɗinsa na ƙasa, se kuma ya ɗan furzar da iska daga bakinsa sannan ya sauke ajiyar zuciya ya soma takawa dan ficewa daga ɗakin. Sam Mom bata lura da shi ba, se da ya wuce ta gabanta har ya kusa fita daga ɗakin sannan ta gan shi. Cikin sauri ta bi bayansa tana faɗin "A'ah, Areefullah ina zaka je?" Ta ƙarasa maganar sanda tazo dab da shi. "Pls ki bani hanya." Yayi maganar gaba ɗaya fuskarsa a cunkushe babu fara'a ko misƙala zarratun. Cikin kwantar da murya tace tana ɗan murza hannunsa "It's ohk..it's ohk Uhmm?" Ta faɗa cike da rarrashi. "Pls Mom." Ya sake ambata ba tare da ya kalleta ba. Da dai ya fahimci ba matsawar za ta yi ba, kawai se ya zagayeta ya fice daga ɗakin ya barta tsaye a wajen. "Oh my goodness.." ta faɗa tana yarfe hannunta. Ta riga dama ta san halin Bad Man ɗin amma bata san wannan ɗan abun da tayi ze fusata shi haka har ya ƙi cin abinci ba. "Munafukar mata!" Ta faɗa tana jin yadda ɓacin rai ke taso mata musamman idan ta tuna da Hajiya Sa'adah. Yana fitowa Compound ɗin yayi daidai da lokacin da Daddy ya sauko daga cikin motarsa. Se ya ƙarasa a nutse fuskarsa na sassautawa daga ɗauretan da yayi kamar ba shi ba. A nutse ya ƙarasa ya rungume Daddyn yana faɗin "Welcome Daddy.." "Welcome my Son.." Daddy ya faɗa yana ɗan dukan bayan Bad Man ɗin. "Ina zaka je?" Daddy ya faɗa bayan sun saki junansu. Ɗan shafa sumar kansa Bad Man yayi kafin yace "Amm, zan ɗan fita ne.. in zaga gari.." Jinjina kai Daddy yayi yace "Hakan ma yayi. Buh zuwa anjima ina so muyi hira sosai.. Amma yanzu let's go to mosque, kaa ji ana kiraye_kiraye.." Babu musu yace "Ohk.." daga haka be sake cewa komai ba. Kai tsaye masallacin suka wuce, wanda ke cikin tafkeken gidan nasu. Tare suka yi Sallahr cikin ƙaton masallacin. Cigaba da zama suka yi na tsawon mintuna, har lokacin Daddy addu'a yake, yayin da Bad Man tun kusan minti nawa baya ya idar da tasa addu'ar. Kallan Daddy yayi, sannan ya fito da wayarsa ya duba tym. Ya san idan dai har ya ƙara mintuna a gida ba ze samu abin da yake so ba. Dan haka cikin muryar nan tasa yace bayan ya ɗan ranƙwafo kusa da Daddyn. "Daddy! Tym na tafiya.. Zan tafi.." se da Daddy ya kai ƙarshen abin da yake kafin ya kalle shi yace bayan yayi murmushi, a ransa yana farin ciki da yadda ya ga Areef ɗin nasa ya girma sosai yayi kyau, kuma da alama babu wani shashanci da yake yi, dan kwata_kwata yanayinsa be nuna ba. In banda askin da ke kansa da cikin ruwan sanyi ze san yanda ze yi ya sauya shi. Yanzun ma ya bar shi ne dan ya san hakan ba komai bane a can ƙasar da ya baro. "Ohk.. Akwai yara za a haɗaka da su.." Cikin rashin fahimta yace "Yara?" "Yeap, yara mana.. waɗanda zasu kula da kai.." Se da ya soma ƙanƙantar da idanunsa sannan yace "Kula da ni fa kace Daddy? Ba na buƙatar kowa. I can take care of myself couz am matured enough.." ya faɗa cike da jin haushin yanda burget ɗinsa ke neman rugujewa. "Ga ka ga su ai Areef.. Je ka fita.." Daddy ya faɗa yana gyara zamansa ya cigaba da addu'oinsa. Har wani huci yake sanda ya miƙe ze fita daga masallacin. Tafiyarsa ta sake mugun ƙawatuwa saboda yanayin da yake ciki na fushi, se ya koma tafiya cikin wani irin taku kamar wanda baya son yin tafiyar. Se dai da yake tafiyar cike da kuzari yake yinta kasancewarsa ƙaƙƙarfan namiji ya sanya tafiyar tayi armashi. Kai tsaye wajen motarsa ya nufa ya buɗe ya shiga, ya ɗan lumshe idanunsa na tsawon sakanni sannan ya buɗesu lokacin da suka chanja colour. Abin da baya so kenan shi yasa be so dawowa Nigeria ba. Wannan wane kalan takurawa ne, a ce duk inda mutum ze je se da wasu a bayansa kamar wani ɗan fashi? Be taɓa tunanin idan ya dawo nan ɗin ze soma da wannan ƙalubalen ba. Amma a yau ɗin ze gama da wannan chapter, ya shiga next chapter. Idan kuma hakan taƙi toh dole se dai ya sake bar musu ƙasar. .. Tunda Abba yayi parking sum_sum ta fice daga cikin motar, jin har lokacin bece da ita komai ba. Hakan ba ƙaramin sake sakawa jikinta yayi sanyi bane. Ammi da Didi na parlour suna kallan Sunnah TV. Ta shigo a sanyaye. Kowa ya ganta ya san akwai wani abun, dan da babu komai, tana shigowa zaka san ta shigo da maganarta. Se dai yau ɗin babu wanda ya jiyo muryarta, babu wanda ta nufa dan runguma, se ƙarasawa da tayi kan kujerar da Ammi ke kai ta ɗora kanta a kafaɗarta sannan tace "Amminmu!" Murmushi Ammi tayi tana jin daɗin dawowar Lulun fiye da zato tace "Na'am 'yan matan Ammi.." "Kai Ammi" Lulu ta faɗa tana murmushin itama. Ɗan satar kallan Didi Lulu tayi, yanda take wani cika tana batsewa tana ɗaɗɗama rai ne ya sanya ta sake tuna abin da ya dawo da ita gida. Se kawai ta sake yin shiru tana kuma jiran shigowar Abban, dan ta san a yadda ta gan shi yau ɗin nan kam se ta sha faɗa. Se dai ga mamakinta har bayan wajen mituna 20 da shigowarta Abba be shigo ba, tun tana jin tsoro har tazo ta dena. Se kawai ta miƙe da sauri ta shige ɗakinsu. Didi na tsaye bakin wardrobe tana gyara kayanta. Lulun ta ƙarasa ta rungumeta tana faɗin "Na yi missing na ki fa Didina.." "Ni sakeni Malama." Didi ta faɗa tana mazewa. Maƙe kafaɗa Lulu tayi lokaci ɗaya tana faɗin "A'ah, naƙi ɗin.." "Toh jikinki ne?" "Ehh mana, ai dai na Didina ne." Lulu ta faɗa tana murmushi. Jin Didin ba tace komai ba ya sanyata faɗin "Abba ne fa ya ɗakkoni. Kuma ya min faɗa na dena abin da nake yi In Sha Allah.." "Ke ɗin?" Didi ta faɗa tana juyowa ta kalleta. Se ta jinjina kai tana sake marairaice fuska kamar wata marainiya. Yadda tayi ɗin ne ya tilastawa Didi yin dariya. Se kawai ta rungume Twinnynta ta cikin matuƙar kewar junansu. Tun daga lokacin ma duk se suka sake suka manta ma da abin da Lulun tayi. Shi kansa Abba tun dawowarsu gidan basu sake ganinsa ba, kamar ma baya cikin gidan kwata_kwata. Hakan ne ya ƙara sawa Lulu karsashi wajen sakin jikinta ta cigaba da harkokinta. Har zuwa washegari kuma Abban be yi mata magana ba, hakan ne ya sanya ta soma tunanin ko ya manta, ko kuma ya bar maganar. Ita idan haka ɗin ne ma tafi kowa farin ciki, dan haka ta sake sakin jikinta, ta dinga kakkaucewa duk wata hanya da zata haɗata da Abban, duk da yadda daga jiyan zuwa yau be samu zama a gida sosai ba. ... Ammi ce kaɗai cikin parlourn tana kallan tashar Arewa 24 inda suke nuna shirin Akushi da rufi. Da yake Ammin tana son shirin ya sanyata zama tana kalla, duk da ita ɗin ba ma'abociyar kallo bace. Babu daɗewa se ta miƙe zuwa wajen fridge ɗinsu da ke cikin ɗakin dan ɗaukar ruwa. Sallamar da taji cikin parlourn ita ce ta sanyata juyawa. Se tayi murmushi ganin me shigowar tace "A'ah... Sadiya! Sannu da zuwa." Ammi ta faɗa tana ƙarasowa cikin ɗakin cike da mamakin ganin Mamin, tunda dai ta ga jiya Lulu ta dawo, ba dai tana nufin ta zo ta sake tafiya da ita ba ne? Idan kuwa haka ne gaskiya a wannan karon dole ne ta magantu. Zama Ammi tayi tana ajje ruwa da lemon da ta ɗauko cikin fridge. Yayin da Mami ma ta ƙaraso ta zauna kan kujerar kusa da Ammin tana murmushi tace "Se kuma kika ganni?" Itama Ammin murmushi tayi kafin tace "Uhmm. Kina lafiya? Ina Jadwa?" "Alhamdulillah. Ina 'ya'yana?" Mami ta faɗa tana ɗan duba bayanta. "Suna ciki.. Ina ga ko bacci suke" "Toh madallah. Yayan na nan ne?" Mami ta faɗa tana miƙewa. "A'ah ya fita dai." "Toh bari na je kafin ya dawo" Inji Mami. "Toh." Ammi ta faɗa tana binta da kallo sanda take dab da shiga ɗakinsu Lulun. Kamar kuma wadda aka tambaya se ta juyo tace "Kin san na zo ne na sake bawa Yaya haƙuri, sannan na yiwa ɗiyartawa faɗa." Jinjina kai Ammi tayi tana ɗan murmushi tace "Uhmmm." Daga haka ba ta sake cewa komai ba har Mamin ta shige ɗakin. Suna zaune kan gado, Didi da Little ke kwance a jikinta na karanta musu wani English novel da aka basu a school Mamin ta shigo. Da gudu Lulu dake sanye cikin doguwar riga kanta babu ɗan kwali ta miƙe ta rungume Mamin tana faɗin "Oyoyo." Hugging nata back Mami tayi tana murmushi lokaci ɗaya tana faɗin "Wannan kannaki daughter.." ta faɗa tana riƙe baƙin gashin Lulun. Er ƙara ta saki tana saka hannu ta riƙo hannun Mamin. Se a lokacin ta saki sannan suka ƙarasa cikin ɗakin. Ajiye littafin hannunta Didi tayi, tana kwantar da Little da yayi bacci a kan gadonsu. Sannan ta juyo tace a nutse "Sannu da zuwa Mami." "Yawwah Afrah. Ya karatun?" "Alhamdulillah.." "Toh madallah." "Daughter ina fata dai Abba be sake miki faɗa ba?" Mami ta faɗa tana kallan Lulu da ke zaune kusa da ita. Se da ta ɗan turo baki sannan tace "Ehh fa. Ai be ma yi ba fa, inaga se yau.." ta ƙarashe maganar a narke. Shafa kanta Mami tayi kana tace "Shi kenan, shinkenan. Didi.." ta kai ƙarshen maganar tana kallan Didi. "Uhmm" Didi ta faɗa cikin sanyin nan nata. "Ɗan bamu waje zan sake yi mata faɗa.." kusan a tare Lulu da Didi suka kalli junansu, sannan Didi ta maida duban nata kan Mami, kamar za tace wani abu se kuma ta fasa, kawai ta miƙe ba tare da tace komai ba. Riƙo hannunta Lulu tayi da sauri tana faɗin "Didi ki zauna.." Lulu ta faɗa har lokacin fuskarta a narke. Hannu Mami ta kai ta zare hannun Lulu daga cikin na Didi tace "Barta ta je, ina son na yi miki faɗa ne sosai. Idan tana nan zata dinga rarrashinki, idan kuwa bata nan fa? Didi je ki abinki.." tun kafin Mamin ma ta gama maganar Didi ta fice daga ɗakin. Lulu ta bita da kallo har ta fice ɗin. Sannan ta dawo da dubanta kan Mami da itama ta bi Didi da kallo har ta fice. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta saka hannunta a cikin jakarta ta ɗauko waya, kana ta ɗago tana kallan Lulu ta soma faɗin "Kina ji na?" Tayi maganar tana juya wayar hannunta.. *♡☆A JINI TAKE☆♡* *(IZZATA)* By _*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_ *CHAPTER ONE* Page_10 __"Ehh Mami." Ta faɗa tana kallan wayar. Se da Mamin ta gyara zama sannan tace "Riƙeta ki ji." Tayi maganar tana miƙa mata wayar. Babu musu ta saka hannu ta karɓa tana kallan Mamin, dan ta ƙagu ta ji abin da zata faɗa matan. "Ki ajjeta a wajenki, za a kiraki zuwa anjima. Kada kice ba zaki ɗaga ba dan na san halinki, kin ji koh?" Baki ta tura gaba tana ajje wayar kamar wadda ta ga wani abun tsoro, ta kuma soma yamutsa fuska. Harara Mami ta jefa mata sannan tace "Bana son iya shege Lulu.." "Ni wallahi a'ah Mami, bana so. Ni nace miki ina son waya?" Iska Mami ta furzar tana tunanin yanda zata yi ta shawo kan Lulun. "Tsaya ki ji, ki ajje wayar nace a wajenki koh? Na ji ba za a kiraki yau ba, se gobe uhmm?" "Wai ke ce zaki kira?" Ta tambaya cike da sakarcinta. "Wayyo Allahna Lulu.." Mami ta faɗa tana dafe kanta gami da sauke ajiyar zuciya. "Bani wayar" tayi maganar tana ɗaukarta daga inda Lulun ta ajjeta. Kasheta tayi gaba ɗayanta sannan ta miƙe ta ƙarasa zuwa wajen wardrobe ɗinsu, ta buɗe ta Lulu ta sakata a ƙasan kayanta sannan ta dawo ta zauna tace "Na san Yaya da kuma Amminku ba za su barki yanzun ki fara kula samari ba. Toh wata gagarumar dama ce ta samemu Lulu, saboda haka wannan wayar ki kunnata zuwa gobe zan kiraki. Sannan kuma ko da an kiraki ki ɗaga, wani ne ya ganki yace yana so. Ki ba shi haɗin kai kinji? Idan komai ya daidaita ni da kaina zan sami Yayan da maganar. Me ye dan kin fara soyayya a S.S 1?" Ita tun ɗazu da ta fara magana sam bata fahimci abin da take so ta faɗa ba, se yanzu da ta ambaci soyayya. Dan haka cikin sauri ta soma ƙoƙarin miƙewa tana faɗin "Kaii!!" Tayi maganar tana fiddo da idanunta waje. Hannunta Mami ta janyo, tana tunanin yanda zata ɓillowa Lulun kada ta ɓarar musu da wannan gwagwgwaɓar damar. Se dai ta riga ta san halin Lulun wani lokacin a botsare take. Dan haka cikin rarrashi tace tana murmushi "Dawo ki zauna daughter." "Ni wallahi ki sakar min hannu Mami. Hmm uhmm jam!" Ta faɗa ainahin ƙuruciyarta na bayyana, wanda hakan har se da ya sa Mamin ta sake murmusawa. "Ke da wasa fa nake. Dawo ki yi zamanki, ni ce na siyo miki wayar saboda na ga kina sonta.." Se a lokacin sannan Lulu ta tsaya tana kallan Mamin. "Don Allah?" "Ehh mana, ko ba kya so?" Se tayi murmushi tana komawa ta zauna cike da jin daɗi. Se kuma ta ɓata fuska tace "Toh ta yaya zan yi amfani da ita? Idan kuma Abba ko Ammi suka gani fa?" "Ba ma zasu gani ba, se dai idan ke ce kika yi niyya." Mami tayi saurin bata amsa. Ta buɗe baki za tayi magana Ammi tayi sallama cikin ɗakin. Se ta fasa cewa komai. Ammi ta ɗan kallesu sannan ta ƙaraso ta nemi waje ta zauna. "Uhmm bari ki ga na zo na tafi.. dama unguwa fa zan wuce daga nan ɗin." Mami ta faɗa tana miƙewa. Kallanta Ammi tayi da ɗan mamaki, se dai kawai ta basar tace "Haba dai, har kuma zaki tafi?" Yaƙe tayi tana faɗin "Wallahi kuwa, gwara na tafi.." ta faɗa tana yafa mayafinta. Lulu da Ammi suka miƙe, suka fito parlourn tare. Da sauri Didi da ke zaune a ɗakin ta kulle idanunta kamar me bacci, dan ita dai haka kawai yau ɗin take jin haushin Mamin. "A'ah Afrah bacci take kenan?" Mami tayi tambayar ba dan tana buƙatar amsa ba. Har compound suka rakata, suka yi sallama. Har kuma suka koma Ammi bata basu damar keɓewa sun yi magana ba, wanda hakan ba ƙaramin sosa zuciyar Mami yayi ba, dan dai kada a fahimci wani abun ne ya sanyata mazewa. .. Sanye cikin ƙananan kaya kamar yanda kuka san Bad Man ɗin ma'abocinsu ne yake, kansa ya ɗora masa wata haɗaɗɗiyar facing cap da ya juyar da ita ta baya. Hannunsa ɗaya na cikin aljihun wandonsa yayin da shegiyar hamshaƙiyar wayarsa ke ɗayan hannun nasa kafe a kunnensa yana amsa waya. A haka ya cigaba da takawa har zuwa wajen motarsa. Kai tsaye ya shige, bayan ya katse kiran ya tasheta. A bakin tanƙamemen gate ɗin gidan nasu ya tsaya yayi horn, da yake yana idar da Sallahr isha'i ya fito, se ya kasance yawanci duk suna cikin masallaci, se ɗaiɗaiku saboda ba a barin wajen haka babu kowa. Be haƙura ba ya sake danna horn fuskarsa a matuƙar haɗe yana kallan wanda ke tsaye a wajen. Daga gefe yaji an yi knocking glass ɗin gefensa. Kamar ba ze juya ba, se kuma ya juya a hankali ya watsawa wanda ke tsaye a wajen idanun nan nasa bayan ya sauke glass ɗin kaɗan. Cikin lokaci ƙanƙani ya ɗan daburce, da ƙyar ya iya soma faɗin "Yallaɓae sun ce kada a buɗe gate ɗin. Wai kada kowa ya fita. Kayi haƙuri yallaɓae." Ya ƙarasa maganar cike da girmamawa. "Kai! Ni sa'anka ne?" Ya ƙare ransa a ɓace, yana jin yanda zuciyarsa ke tafasa. "Will u just open the gate for me ko kuma.." Tun kafin ya ƙarasa Idi yayi gaba da sauri ya ƙarasa jikinsa na rawa ya buɗe gate ɗin. Me gadin da ke zaune a wajen yana kallansa. Se dai bece komai ba har Bad ɗin ya fice daga gidan. Se a lokacin ya kalle shi yace "Shi ne ka buɗe masa kofar koh? Idan suka fito me zaka ce musu?" Cikin fushi Idi yace "Me yasa da na buɗe a gabansa ba ka zo ka rufe ka ce ba ze fita ba? Se yanzu zaka wani zo kana faɗa min magana." "Ni dai wallahi idan suka zo babu ruwana, ban ma san kayi hakan ba." Tsaki Idi ya ja duk da yadda shi ma yake a tsorace, amma tsoron Bad Man ɗin yafi tsoron mutanen. Dan kuwa ya san idan da be buɗe masa ƙofar ba ko me nene ya biyo baya shi ya jawa kansa. Wani ƙaramin joint se dai haɗaɗɗe Bad Man ya wuce. Ya sauka ya soma takawa zuwa ciki, gefen swimming pool inda mutanen da ke zaune a wajen basu da yawa, se dai kowa da abin da yake yi. "Heyy Bad!" Na ji an faɗa cikin er ɗaga murya. A nutse ya ɗaga lumsassun idanunsa ya kalli Hero da ya kira sunansa. Ya ɗan yi murmushin da ke ƙawata kyakkyawar fuskarsa. Cikin sauri Hero ya ƙaraso ya rungume shi yana faɗin "Wai dama da gaske kake?" Be ce komai ba se "Uhmm" kawai da yace. "Let's go Friend.." Hero ya faɗa yana jan hannunsa suka ƙarasa suka nemi waje suka zauna. Ɗan kishingiɗa Bad Man yayi yana sauke ajiyar zuciya ganin tarin drinks a wajen kala_kala se wanda ya zaɓa. "Kana nan kana sharholiyarka koh?" Yayi maganar a hankali kamar wanda aka ma dole. Ɗan shafa kansa Hero yayi yace "Ba zaka gane ba ne Friend.. dole se ana yi ana ɗan ehh yaaa..nee." Hannu Bad Man ya saka ya janyo wata hamshaƙiyar kwalba wadda da alama ma ko taɓata ba a yi ba. Ya ja ƙaramin tambulan ya tsiyaya a ciki sannan ya janyo ruwa shi ma ya ɗan tsiyaya a kai kana ya ɗauka. Duk abin da yake Hero kallansa kawai yake yi. Se da ya ga yana shirin kaiwa baki sannan yace "Wait Friend.. Me nake gani? Kana nufin.." "Yeap!" Bad ya katse shi da faɗin haka. Wani ihu Hero ya saki hadda miƙewa tsaye. Se kuma ya koma ya zauna yana dariya yace "Shege Bad Man.." shi dai be bi ta kansa ba ya soma kai cup ɗin bakinsa ya shanye abin da ke ciki tass. Be jira ba ya sake ƙara wata cikin cup ya sake kaiwa bakinsa, shi kuma Hero se zuga shi yake yi cike da farin ciki. Ana cikin haka, zuwa lokacin ya ɗan soma jin kansa na ɗaure masa, dan be tsaya tunanin komai ba ya fara afata a cikinsa. Se dai sam tsadarta ba ta kai wadda yake amfani da ita ba, shi yasa ma ya ji ta kamar wani sabon abu. Wayarsa da ke ajje ta soma ringing. Da idanunsa da ke a lumshe ya ɗan buɗe ya kalli wayar, shi sam be saba jin irin yanayin nan dan ya sha wani abun ba, ya dai buɗe idanun nasa yana gyara zamansa. Ɗaukar wayar Hero yayi yana faɗin "Noo Bad. Ba zaka iya answering call ba a wannan yanayin.." Ɗan tsuke face yayi yana watsa masa idanunsa duk da har lokacin kansa sake yi masa nauyi yake. Yace bayan ya ɗan janyo iska daga huhunsa "Give..me.." yayi maganar a ɗan rarrabe yana miƙa masa hannu. Babu musu ya miƙa masa wayar, ba tare da ya kalli me kiran ba ya ɗaga. Daga can ɓangaren Aunty (ƙanwar Mom) tace "My son.." sarai ya gane muryar wace duk kuwa da yanda yake jinsa kamar ba shi ba. Cikin ƙarfin hali yace "Yes Aunt.." "Ya na ji muryarka haka? Ko har yanzu baccin gajiya ka ke?" Auntyn ta tambaya "Uhmm" kawai ya faɗa har lokacin idanunsa a lumshe. Fahimtar bacci yake yi ne ya sanyata faɗin "Olright i will call u later.. Sleep well.." Daga haka ta yanke kiran ba dan ta so ba, dan ta so ne su ɗan gaisa sosai saboda yadda wata muhimmiyar tafiya ta kamata a ranar da ya dawo daga California. .. A nutse ya saka kansa cikin ɗakin bakinsa ɗauke da sallama. Ummeey ta amsa sallamar tana kallansa. Se ya ƙaraso ya nemi waje ya zauna kusa da Ummeeyn. Sanye yake cikin wani tattausan yadi me kyau wanda ya matuƙar yi masa kyau, kansa babu hula, se kwantacciyar baƙa ƙirin ɗin sumar kansa kamar ta larabawa. Yau ne karon farko da na soma ganin kansa a buɗe, ni se na ga ma kamar yafi kyau a hakan. A nutse ya kalli kan gadon da Abeey ke kai a kwance yace "Ummeey bana son fita. Ki bari na soma kai shi asibiti tukunna." Kallansa Ummeey tayi yanda ta ga damuwa ƙarara a kan kyakkyawar fuskarsa. Se ta maida dubanta kan Abeey tace "Ka bari ya kai ka a dubaka mana." Girgiza kai Abeey yayi yana ɗan murmushin ƙarfin hali kafin ya buɗe baki yace "Haba.. haba.. ciwo ne fa kamar na ko da yaushe. Duk kun bi kun damu kanku kamar yau na fara irin wannan ciwon? Kai Affan.." ya dakata yana kallan Gwani "Na'am Abeey." "Tashi ka tafi makaranta. Ka bar ɗalibai na jiranka." "Abeey!" Gwani ya faɗa yana kallan Abeeyn da kana kallansa ka san baya jin daɗi. "Affan! Ni nace maka ka je koh?" Abeey ya faɗa yana kallansa. Se ya jinjina kai a nutse kafin ya miƙe jikinsa a sanyaye. Duk da be so hakan ba, amma tunda Abeeyn yace ya tafi gwara ya tafi ɗin. Dan haka ya juya ya kalli Ummeey yace "Ummee bari na je.. Abeey Allah ya ƙara maka lafiya." "Ameen_Ameen ɗan albarka. Allah ya tsare." Abeey da Ummeey suka kusan haɗa baki wajen faɗar hakan. "Ameen." Ya amsa a nutse, kafin ya fice daga ɗakin. Kai tsaye ɗakinsa ya koma ya sake shiryawa kamar yanda ya saba fita, ya naɗe kansa sannan ya fice zuwa makarantar. .... "Wato Afaaf baki da kirki koh? Ni zaki zubarwa da mutunci a idon duniya?" Da sauri ta ɗaga kanta cike da mamakin jin furucin Abban. Se dai ta riga ta san halin Abban, idan yana faɗa baya so a ce komai. Hakan ne ya sanyata yin shiru, ta maida kanta ƙasa, kamar mutuniyar kirki ta gaske. "Tunda har suka kirani suka faɗa min laifinki, hakan ya nuna ba tun yau kika soma ba. Wato kin daɗe kina nuna musu rashin daraja, se da kika kaisu bango sannan suka faɗa min. Ni ba ma su burgeni ba da basu zane min ke ba, sannan kuma ki dawo ni nan na ƙara miki da wani sabon, shashashar yarinya." Sosai Abba ya cigaba da mata faɗa, wanda a yadda na ga yanayinta kamar ya shigeta. Se daga ƙarshe Abba ya ƙare da faɗin "Ina so ki buɗe kunnenki da kyau ki ji, ka da ki bari, ka da ki sake a sake kawo min ƙararki daga makarantarku, ko bokon ko islamiyyar. Idan ba haka ba wallahi zan saɓa miki Afaaf, zan saɓa miki kin ji na faɗa miki." A hankali ta ɗaga kai alamar "Ehh" sannan ta buɗe baki a hankali tace "Ka yi haƙuri Abba." "Ka da ki sake." Ya faɗa kawai yana soma takawa dan ficewa daga ɗakin. "Cewa en uwanki su fito mu tafi, yau da kaina zan kai ku." Bata kawo komai a ranta ba, ta miƙe ta koma cikin ɗakinsu, inda Didi ke zaune duk da ba jin faɗan take ba, amma duk a dame take kamar ita aka yiwa faɗan. Da sauri ta kalli Lulun, se dai yanda ta ga fuskarta ne babu yabo ba fallasa ya sanyata ɗan jin sanyi tace "Lulu!" "Uhmm! Abba yace ku fito ze kaimu." Tun kafin ta ƙarasa faɗa Little har ya miƙe ya fice daga ɗakin a guje. Didi ta miƙe cikin sanyin nan nata ta riƙo hannun Lulu tace "Sorry." Ta faɗa fuskarta a ɗan narke. Ɗauke kai Lulu tayi sannan tace "A'ah. Ai dama haka kike so." Waro manyan idanunta Didi tayi sannan tace "Nii! A'ah fa.. Ni kawai so nake ki chanja daga wannan Lulun kin ji?" "Tohm" Lulu ta faɗa. "Dat's my baby gurl." Didi ta faɗa a ranta tana fatan Allah ya sa daga yanzun Lulun ta chanja gaba ɗaya. Kai tsaye compound ɗin gidan suka nufa. Abba na cikin motar har ya tayar da ita ma. Babu ɓata lokaci suka shige bayan motar dan Little ya shekara a gaba. Se da suka shiga sannan Abba ya tayar da motar suka bar gidan. Kai ba zaka ce Abban ne yanzu ya gama faɗa ba, yanda ya saki jiki yana jan 'ya'yan nasa da hira. Hakan ba ƙaramin kwantar da hankalin Lulu yayi ba, ko babu komai ta san ya sakko. A ƙofar makarantar Abba yayi parking motarsa. Se dai ga mamakinsu su duka, se ya sauka daga motar shi ma. Kallan juna Didi da Lulu suka yi, Lulu ta ɗan karkatar da kanta alamar tana tambayar Didin ko ta san dalilin Abban na yin haka? Girgiza kai Didi tayi. Ganin babu wanda ze amsa musu tambayar ya sanya su saukowa daga cikin motar. "Abba a dawo lafiya." Suka haɗa baki wajen faɗa. "Allah ya sa. Mu je ciki, ina son ganin malaminku." Haka kawai dukkansu suka ji jikinsu yayi sanyi, amma se suka basar suka bi bayan Abban dake riƙe da hannun Little zuwa cikin makarantar. "Afrah kama hannun Little ku shige. Zamu ga Malam Affan." Abba ya faɗa yana miƙawa Didi hannun Little. Karɓar hannun nasa tayi tana faɗin "Toh Abba." Se ta kalli Lulu da ke tsaye kamar wadda aka dasa. Dan tunda Abba yayi maganar ta kasa cewa komai. Ɗan lumshe mata idanu Didi tayi tana jinjina mata kai dan ta bata ƙwarin gwuiwa. Se itama ta lumshe idanun tana ɗan sauke ajiyar zuciya. Haka nan kawai se ta ji a ranta ba se ta tambayi Abban dalilin tsayawarsu ba, dan ta san zuwa yayi kawai ya gaisa da Gwanin. Malam Ahmad ne ya ƙaraso wajen Abban, ya miƙa masa hannu suka gaisa sannan Abba yace "Malam Affan be shigo ba ne?" Jinjina kai Malam Ahmad yayi kana yace "Wallahi kuwa. Amma na tabbatar wani babban uzuri ne ya riƙe shi. Zaka iya jiransa idan ba sauri kake ba." "Ehh toh.. da yake dai akwai inda zan je ne, ina ga zan tafi, se na dawo." Wani irin sanyi Lulu taji yana ratsata jin furucin Abban. Sosai hakan ya mata daɗi dan dama bata so a ce Abban da kansa su gaisa da Gwanin. Se dai tun kafin Malam Ahmad ya kai ga cewa komai Gwani ya shigo cikin makarantar cike da takun nan nasa na nutsuwa. "Aff, ka gan shi ma ya zo." Malam Ahmad ya faɗa yana murmushi. Cikin jin daɗin ganinsa Abba yace "Toh madallah." Suka sake gaisawa sannan Malam Ahmad ya bar wajen. Se da suka gaisa da Gwani ya faɗa masa Abba wajensa ya zo sannan ya wuce. Wani irin takaici ya zo ya cika Lulu, ta ji kamar tayi kuka dan haushi, ta faki idanun Abba ta watsa masa harara sannan tayi saurin ɗauke idanunta kada ko shi ko Abban wani ya ganta. Sallama yayi sanda ya ƙaraso wajen Abban. Abba ya amsa sallamar yana miƙa masa hannu suka gaisa cike da girmama juna. "Amm Malam Affan, idan babu damuwa ga Afaaf nan na dawo da ita. Ina kuma sake baka haƙuri don Allah kayi haƙuri, In Sha Allah hakan ba zata sake faruwa ba." Nauyin maganar da ke fitowa daga bakin Abban ya sanya Gwani ɗago kai yana girgiza kai sanda wani ɗan murmushi ya suɓuce a kan fuskarsa yace "Ka dena bani haƙuri don Allah.." Shi ma murmushin Abba yayi kafin yace "Toh shi kenan. Amma ga ta nan na kawota ta baka haƙuri!" Da wani irin sauri ta ɗaga kai ta kalli Abba tana so ta tabbatar da gasken abin da taji a kunnenta, hakan Abba ya furta? Kallan gargaɗin da taga Abba ya jefeta da shi ne ya sanyata shan jinin jikinta. Shi kuwa Gwani se a lokacin ma ya san da wanzuwarta a wajen. "Babu komai, kaje kawai, zuwanka ma ya wadatar." Gwani ya faɗa. Girgiza kai Abba yayi be ce komai ba se sake kallan Lulu da yayi kafin yace komai ta fahimci abin da yake nufi. Dan haka ta ɗan lumshe idanunta tana jin yadda bugun zuciyarta ke cigaba da ƙaruwa. Narkakkun idanunta sun cika taff da ƙwallar baƙin ciki ta soma takowa zuwa inda suke. Da ƙyar ta iya tausar zuciyarta ta tattaro kalmar haƙuri, se dai bata kai ga furtata ba ta jiyo muryar Abba na faɗin "Tsuguna ki ba shi haƙuri." Yayi maganar fuskarsa a haɗe, dan kuwa shi kansa ya soma fuskantar take_taken Lulun, shi kuma ba ze yi sake ba wajen kula da tarbiyyarta. Dan haka idan ma tana tunanin tafi ƙarfin kowa ciki kuwa hadda malaminsu, toh yau ɗin zata gane malamin nasu ya fita matsayi. Sosai taji kanta ya wani irin juya mata, idanunta a rufe na tsawon sakanni, ƙafarta na wani irin rawa, tana jin maganar da Abba ya faɗa ɗin kamar wata wuƙa aka saka aka yanketa. Ita a wajenta ma har gwara a yanketa ɗin da a ce ta tsugunawa Gwani wai ta bashi haƙuri. Kallanta Abba yayi a ransa yana fata kada a ce Lulun ta sake nuna halinta tun ba a je ko ina ba, dan idan hakan ta faru toh babu shakka yau me raba shi da ita se Allah. Cikin rashin sanin mafita ta zube a kan gwuiwoyinta, zuwa lokacin tuni hawayen da suka cika mata idanu sun gama zuba a kan fuskarta. Wani irin sanyi na kaɗa ilahirin jikinta. Ba dan taso ba, ba dan kada ta wulaƙanta Abbanta a gaban mutane ba, da babu abin da ze sanyata tsugunawa ta bawa Gwanin haƙuri, ko da kuwa korarta za a yi daga makarantar. Duk yadda zuciyarta ke mata ƙuna, tana hanata aikata abin da mahaifin nata ya umarceta da yi, haka ta take, ta cije, ta buɗe baki da ƙyar tace "Ka yi haƙuri.." ta faɗa wasu sabbin hawaye masu ɗumi na kwaranyowa a kan fuskarta, lokaci ɗaya tana ji har abada mutuncinta da kuma ajinta ya gama tsiyayewa a bainar nasi.. *♡☆A JINI TAKE☆♡* *(IZZATA)* By _*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_ *CHAPTER ONE* Page_11 ___"Allah ya kiyaye gaba." Shi ne abin da Gwani ya faɗa yana maida dubansa kan Abba da ya soma faɗin "Toh Malam Affan, na gode." Ɗan murmushi ne ya wanzu a kan fuskar Gwanin ba tare da yace komai ba, se miƙa masa hannu da ya yi suka sake gaisawa. Daga haka Gwani ya yi hanyar ajinsa cikin nutsuwa. Kallan Lulu Abba ya yi da har yanzun take tsugune a wajen, ta kasa ko da motsa wa ne ballantana ta miƙe. Har kuma lokacin idanunta a rufe suke, ta kasa buɗe wa dan ji take yi kamae tana buɗe wa ɗin za ta ga idanun kowanne ɗalibi a kanta wanda hakan ze tabbatar mata da cewa kowa ya ga wannan dizgin da ya faru da ita. "Afaaf.." Abba ya faɗa yana kallanta, ganin har lokacin ba ta tashi ba. Se a lokacin ta buɗe idanun nata, se dai har lokacin ba ta tashin ba, saboda yanda take jin ƙafafunta har lokacin na rawa. "Kee!!" Abba ya sake faɗa. Se a lokacin ta yi saurin tattaro duk wani kuzari da ya rage mata, ta soma miƙewa a hankali, har ta miƙe a kan ƙafafunta. "Na'am Abba.." ta yi ƙarfin halin faɗar hakan. Duk da ya lura da yadda idanunta suka yi ja, hakan be sanya shi tambayarta dalili ba, dan ya san dalilin. Dan haka se cewa ya yi "Maza ki wuce aji. A yi karatu lafiya, Allah ya ba da sa'a." "Ameen." Nan ma ta yi ƙarfin halin faɗa. Se da ya ga ta soma takawa zuwa hanyar da za ta kaita ajinsu sannan Abban ya fice daga makarantar. A hankali ta cigaba da taka wa, tana ɗan lumshe idanunta ko za ta samu ƙwallar da ta rage cikin idanunta ta koma. A haka har ta ƙarasa ajin nasu. Ba tare da ta kalli inda yake zaune ba ta shige cikin ajin lokaci ɗaya ɓacin ranta na ƙaruwa, tana jin wata irin tsanarsa na ratsata. Kai tsaye waje ta samu ta zauna, ba tare da ta lura ma da inda ta zauna ɗin ba. Tunda ta shigo Didi ke kallanta, ta ɗauka yanzun da ta shigo za ta ga canji daga gareta, se dai ba ta gani ba. Ta ɗan lumshe idanunta tana fatan a ce za ta ga ranar da Lulun za ta shiryu. Wani murmushi Abida ta saki lokacin da Lulu ta zauna a kusa da ita. Se ta saka hannu ta riƙota tana faɗin "Subhanallahi, masoyiyarta me ya faru?" Ta yi maganar tana kallanta. Hannu Lulu ta saka ta janye hannun Abidar sannan ta ɗauke kai tana jin kamar ana ƙara mata ɓacin rai ne. Ba ta haƙura ba ta sake kai hannunta za ta riƙo na Lulun. Da sauri Lulu ta juya ta watsa mata wani kallan gargaɗi ranta a matuƙar ɓace tace a hankali "Malama ki bari mana.." ta faɗa muryarta a cunkushe. Jinjina kai Abida ta yi, ashe kenan duk yanda take tunanin Lulun ta wuce haka? Lallae kam akwai aiki babba a wajenta. Ita tunda ta zauna a cikin ajin ba ta san me yake magana a kai ba, saboda takaicin yanda muryarsa ke ratsa cikin ajin cike da nutsuwa, kamar me tantance kowacce kalma. Hakan ne ya sanya gaba ɗaya en ajin suka nutsu, kowanne na saurarar bayaninsa. Kasancewar yau ɗin ba ranar hadda bace ya sanya littafai suka dinga yi babu sanya. ... "Wai me ya faru ne?" Didi ta faɗa tana zama a kusa da Lulu. Girgiza kai Lulu ta yi sannan tace "Babu komai fa Didi, kawai dai kaina ke ciwo.." Da sauri Didi ta miƙe tun kafin ta ƙarasa maganar "Kuma na sha magani." Shi ne abin da Lulu ta ƙarasa faɗa kafin Didi ta fita daga ɗakin. Dawowa Didi ta yi tana ɓata fuska, se da ta zauna sannan tace "Kin tabbatar kin sha?" Da sauri Lulu ta jinjina kai lokaci ɗaya tana faɗin "Ehh fa.." "Me ƙarya.?" "Ɗan aljanna.." in ji Lulu. Se suka yi dariya dukansu, kafin Didi ta miƙe tace "Se na faɗawa Ammi kuwa.." da sauri Lulu ta riƙo hannun Didi tana narkar da fuska tace "Ni fa da wasa nake. Kawai dai.." ta faɗa tana cigaba da yamutsa fuska. "Kawai dai me..?" Didi ta tambaya "Abin da ya faru a makaranta ne.." "Oh my goodness.. Lulu me yasa kike son ɗorawa kanki damuwa ne babu gaira babu dalili? Me Gwani ya miki? Me ya tsare miki? Shi fa mutum ne me kirki da sanin ya kamata, me ze sa ya miki wani abun da ba za ki ji daɗi ba? Ya fa san me yake yi, wallahi idan dai har kika bi abin da yake so shi kenan zaku koma zaman lafiya. Mutumin kirki ne.." ta ƙarasa faɗa a gajiye, dan bata san kuma me za ta cewa Lulun bayan haka ba. Dan kuwa ba yau ce ranar farko da ta zauna tana fahimtar da ita kirkin Gwani ba, ba kuma ta san sanda za ta gane hakan ba. "Tohm Didi na ji.." ta faɗa cike da ƙosawa. "Gwani mutumin kirki ne" ita har ta gaji da jin wannan maganar. Kowa haka yake faɗa a lokuta da dama, se dai ita har yanzun ba ta gani ba. Ita a wajen ta ma ba ta taɓa ganin mutum mara kirki, me girman kai irinsa ba. Kuma abin da ke sake ƙona mata rai da shi, yanda yake taƙama da wata izza bayan shi ba ɗan kowa ba ne. Harara Didi ta jefawa Lulu ba tare da tace komai ba, ta sauka daga kan gadon ta wuce zuwa inda wardrobe ɗinsu take. Kai tsaye wardrobe ɗinta ta buɗe ta soma dubawa da alama wani abun take nema. Zuwa can anjima ta rufe tata. Se ta koma kan ta Lulu ta soma dubawa, duk abin da take Lulu na kallanta, har ta zo za ta ɗauke kai se kuma ta maida kanta wajen Didin da sauri. Babu ɓata lokaci ta diro daga kan gadon ta ƙaraso wajen Didin tana faɗin "Wai me kike nema ne? Je ki zauna zan duba miki.." ta faɗa tana tuna wayar da Mami ta ajje mata a ƙasan kayanta. Da mamaki Didi ta kalleta, ta riga ta san halin Lulun da kan son jiki, amma yau ita ce ke cewa ta je ta zauna ta bincika mata abu? Lallae. Se ta jinjina kai tana sauke ajiyar zuciya tace "Anya kuwa Lulu? Yau waye ne ya miki faɗa haka?" "Abba mana." Ta faɗa cikin basarwa tana ƙaƙalo wani murmushi ta yi. Dan ta san idan har ta yi murmushin yaƙe toh Didin kan iya ganota cikin lokaci ƙanƙani. "Tohm.." Didi ta faɗa tana harɗe hannunta a ƙirji ta koma ta zauna tana kallan Lulun. .. Da sauri Mommah ta miƙe tana kallan Bad Man ɗin da ya shigo cikin ɗakin. Murmushi ya suɓuce a kan fuskarta. Se ta ƙarasa tana faɗin "Areef..!" "Mommah.." ya faɗa da wannan kakkaurar muryar tasa me daɗin sauraro. Babu ɓata lokaci ya cigaba da takawa zuwa cikin ƙaton parlourn har zuwa sanda ya ƙarasa inda jerin kujerun suke, ya nemi waje ya zauna ya ɗora ƙafarsa ɗaya a kan ɗaya. Neman waje itama Mommah ta yi ta zauna, duk da yanda ta ji daɗin ganinsa amma ba ta son abin da ze janyo tashin hankali tsakaninta da Mom. Dan ta san daga wannan ɗan zuwan da ya yi idan har ta sani za ta iya tayar mata da hankali. "Areef.. Mom ta san za ka zo nan ɗin?" Da mamaki ya kalli Mommahn jin tambayar da ta fito daga bakinta. Se ya ɗauke kai kawai ba tare da ya amsa mata tambayar ba yace cikin er basarwa "Gud evening.." Ta riga ta san halinsa. Ta san sarai ya ji ta, amsar ce dai ba ze bayar ba. Hakan ne ya sanyata yin murmushi sannan tace "Ka na lafiya? Ya hutu?" Ɗan murmushin gefen baki ya yi kafin ya ɗan taɓe bakinsa yace "Uhmm.. Cool.." Murmushi Mommah ta sake yi lokaci ɗaya tana miƙewa ta wuce ƙatuwar freezer da ke can wani ɓangare a cikin ɗakin ta buɗe. Kafin ta kai ga ɗauko komai ta jiyo muryarsa yana faɗin "I don't need anything Mommah.." ya faɗa yana miƙewa lokaci ɗaya yana gyara zaman hular kansa. "Haba Areef, ka tsaya ko ruwa mana ka sha.." Mommah ta faɗa sanda take kallansa. Se ya girgiza kai yace "Not dis tym gaskiya." "Ohk se yaushe?" Mommah ta faɗa. Kamar me tunani ya ɗan tsaya se kuma yace "Ahmm bye.." ya yi maganar yana soma takawa ya fice daga ɗakin. Se ta bi shi da kallo, duk da be ci komai ba, amma ta ji daɗin zuwansa sosai. Kai tsaye bayan fitarsa daga ɗakin part ɗin Daddy ya wuce, dan ba tun yanzu ya ke kiransa a kan yana nemansa ba. Zaune kan kujera yana kallo a Al_jazeera, kan kujerar da ke gabansa kayan marmari ne reras waɗanda suka sha haɗaɗɗen yanka me ɗaukar idanu. Se kuma juice shi ma da ke ajje, wanda har ya tsiyaya shi a cikin tambulan yana ɗan sipping lokaci zuwa lokaci. Kai tsaye shigewa yayi kawai ya nemi waje ya zauna yana kallan T.Vn shi ma, daidai kuma lokacin da suka gama labaran. Ɗaukar remote Daddy ya yi ya kashe T.Vn sannan ya juya ya kalli Bad Man yace "Haka ya kamata ɗan musulmi ya shigo ɗaki?" Daddy ta faɗa yana kallansa. Ɗan yamutse fuska ya yi sannan ya zamo daga kan kujerar da yake kai yace "Sorry Dad.. Assalamu alaik.." sosai muryarsa ta yi daɗi sanda ya furta sallamar kamar wani balarabe. Daddy ya yi murmushi yana faɗin "Ko kai fa..Wa alaika assalam." Gaisawa suka yi sannan Daddy yace "Yaushe za ka fara aiki? Ko se ka huta?" "Yes Dad.." ya faɗa kamar me jiran tambayar Daddyn da ma. "Ba lokaci me tsayi dai za ka ɗauka ba.." Daddy ya faɗa. "But.. zan ɗan soma ziyatar en uwa da abokan arziƙi, idan na gama se na fara aikin.." Kallansa Abba ya yi jin abin da ya faɗa ɗin. Se da ya girgiza kai yana murmushi kafin yace "Kamar gaske.. kai ɗin..?" Shi ma murmushin ya yi kamar ba shi ba amma be ce komai ba har zuwa sanda Daddy ya sake faɗin "So abin da nake so da kai.. ka zauna a gida ka yi hutunka. Ban son fice_ficen nan.." "Ohk.." Sallamar Mom cikin ɗakin ita ce ta sanya Daddy kallanta, ya amsa sallamar sanda take cigaba da takowa cikin ɗakin. Kai tsaye kusa da ɗanta ta je ta zauna tana murmushi. Se da ta saka hannu ta kamo hannunsa sannan ta kalli Daddy tace "Barka da wannan lokaci Yallaɓai.." ta kira shi da sunan da Mommah ke kiransa da shi a lokuta da dama. Hakan ne ya sanya shi murmushi, kafin shi ma ya amsa mata da sunan da ya saba kiran Mommahn da shi a duk lokacin da ta kira shi da 'Yallaɓae' "Barkanki dai Ranki ya daɗe.." "My boy.." "Mom.." ya faɗa tana kallanta can ƙasa. Maida dubansa Bad Man ya yi kan Abba yace "Abba ka faɗa wa Mom, ta de na kirana da Boy, look at me fa.." ya yi maganar yana kallan kansa. Murmushi Abba ya yi shi ma se ya kalli Bad Man ɗin, duk da ba wasu shekaru na azo a gani ke gare shi ba amma da ke ƙaƙarfa ne shi, me murɗaɗɗen jiki da kallo ɗaya za ka masa ka gane ya horu da ɗaga ƙarfe ya sa ba za ka iya ƙiyasta shekarunsa a yanayin jikinsa ba. "Gaskiya dai.. ki dena kiransa da Boy.." "Oh my gosh.." Mom ta faɗa tana girgiza kai, fitinar Areef ɗin yawa gareta. Amma dai ta san idan har ba denawar ta yi ba ba ze dena mata mita a kan hakan ba. Dan haka tace "Noted Sir.." ta faɗa tana kallan Daddy da murmushi kan fuskarta. Shi ma murmushin ya yi. Daga haka se suka ɗan cigaba da hira, Bad Man na gefensu yana danna waya, dan shi sam be saba da wata hira ba, yanzun nan za ta ginshesa. Dan ma ya ga suna buƙatarsa cikin ɗakin ne, hakan ne ya sanya shi zama ɗin se dai gaba ɗaya hankalinsa na kan wayarsa ne. ... A karo na barkatai ta sake kiran layin da ta ɗora shi a kan wayar da ta bawa Lulun, se dai kamar ko yaushe yanzun ma faɗa mata suke yi a kashe layin yake. Ta yi tsaki babu adadi, ta shiga zagaye ɗakin tana jin ɓacin rai na taso mata. Jadwa da tun ɗazu take ankare da ita tace "Mami wai har yanzun?" Kamar jira take dama, se kuwa ta soma faɗin "Ki bar min ja'irar yarin mana. Ina ganin jiki zan saɓa na sake zuwa can gidan ko zan samu Kaseem ya ƙyaleni na huta." Mami ta faɗa tana komawa ta zauna a kan kujera. Tana zama kuwa se ga kiran Kaseem ya sake shigowa wayarta. Kamar ba za ta ɗaga ba, se kuma ta ɗaga ɗin ta kara a kunnenta. Daga can ɓangaren yace "Amm Madam dama cewa na yi, why not ba za ki ba ni address na gidansu ba? Idan ya so kai tsaye se na je wajenta. Ko ma na fara zuwa wajen mahaifinta saboda wallahi da gaske na ke aurenta zan yi." Ajiyar zuciya Mami ta sauke kafin ta soma faɗin "Kaseem ka yi haƙuri, ka san fa yarinyar nan dududu a S.S 1 ta ke.. Abbanta kuma na so ta yi karatu. Ko ma ba haka ba bana jin ze aurar da ita ba ta gama secondary ba, shi ya sa na ke nema maka wata hanyar da zaku samu dai kuna gaisawa." Kamar yana gabanta ya shiga girgiza kai sannan yace "Ki yi haƙuri, don Allah ki ba ni address ɗin. Idan na je wajen mahaifin nata ina so ne kawai a san da zamana ko da ba yanzu ze aurar da ita ba. Amma na fi so ko me zan yi na yi shi ne da sanin mahaifin nata." Shiru Mami ta yi se kawai ta amsa da "Toh shi kenan.." Daga haka ta katse kiran. Duk abin da dama suke cewa Jadwa na ji, se da Mamin ta katse kiran sannan ta soma faɗin "Mtswww, wai shi a lallai dole mutumin kirki.. duk ƙoƙarin da kike yi be gani ba shi uban iya. Aikin banza" ta ƙare maganar tana maida kanta kan wayar da take dannawa. Ita dai Mami ba tace komai ba duk da dai ta yadda da abin da Jadwan ta faɗa. .. "Abeey wallahi ba ka da lafiya.. ka bari na kira mota mu kaika asibiti.." Murmushin ƙarfin hali Abeey ya yi yana kallan Gwani kafin yace cikin ƙarfin hali "Na sani.." ya ƙare maganar yana ɗan sauke numfashi kamin ya ɗora da "Idan ma asibitin kuka kaini wani abun za su ƙaƙalo su ce a yi aiki kamar wancan karon.. toh ina kuɗin su ke? Ina za a nemo kuɗin?" Ɗan lumshe manyan fararen idanunsa Gwani ya yi sannan ya buɗe yace "Allah ze kawo Abeey. In Sha Allah ma ba wata babbar damuwa ba ce.." "In Allah ya yadda.." Ummeey ta faɗa cike da tausayin Abeeyn da ke sauke taggwan ajiyar zuciya kamar wanda ya yi aikin wahala.. https://chat.whatsapp.com/BClMNPwWybg2n3oRvtemv8 *♡☆A JINI TAKE☆♡* *(IZZATA)* By _*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_ *CHAPTER ONE* Page_12 ___Cikin mamaki Didi ke kallan Abida da ke cigaba da shigowa cikin parlourn. Abida ta saki murmushi sanda ta ida shigowa cikin ɗakin. Har ta ƙaraso ɗin Didi ba ta dena binta da kallan mamaki ba. "Me ya kawota gidan?" Ita ce tambayar da ke ta lugude cikin zuciyarta. "Wannan daga gani Didinmu ce.." Abida ta faɗa tana murmushi. Ɗan lumshe idanu Didi ta yi tana ɗauke kai sannan ta dawo da shi kan Abidar tace "Lafiya dai koh?" "Eh fa. Kawai dai na zo ne mu gaisa da Umma. Ina Afaaf?" Ta yi maganar duka a haɗe. Sauke ajiyar zuciya Didi ta yi, se ta shiga lalube cikin zuciyarta ko da za ta iya hasaso dalilin Abidar na zuwa gidansu, bayan ba su da wani haɗi da ita, daga ita har Lulu?. Kawai dai se ta fice daga ɗakin zuwa na su ɗakin inda Ammi da Lulu ke zaune. "Ammi kin yi baƙuwa." Didi ta faɗa tana neman waje ta zauna. Da mamaki Ammi tace "Baƙuwa kuma?" "Ehh ƙawar Lulu ce." Da sauri Lulu ta kalli Didi jin ta ambaci sunanta. "Ƙawa kuma? Ni ɗin?" Ta tambaya cike da mamaki "Fatima?" In ji Ammi. Girgiza kai Didi ta yi sannan tace "A'ah wannan wata sabuwa ce.." ta faɗa tana ɗaukar littafinta da ta ke karantawa. Babu shiri Lulu ta sakko daga kan gadon tana faɗin "Am eager na ga wace friend ɗin ta wa.." ta faɗa da iya gaskiyarta. Dan da gasken ta ƙagu ta ga wacce me ƙarfin halin ce har da biyota gidansu? Dan ita dai ta san ba ta da wata ƙawa bayan Masoyiya. "Ke ce?" Ta faɗa cike da maɗaukakin mamaki a kan fuskarta. Gyara zama Abida ta yi tana ji kamar ta tashi ta rungume Lulun, se dai ta basar tace tana murmushi "Wallahi kuwa.." taɓe baki Lulu ta yi lokaci ɗaya tana jinjina kai. "Ikon Allah.." ta faɗa tana ƙarasowa ta zauna kan kujerar da ke kusa da wadda Abidar ke kai. Tana zama se ga Ammi ta fito. Cikin sauri Abida ta sauko daga kan kujerar da take kai ta tsuguna har ƙasa, tun kafin Ammin ta gama ƙarasowa cikin ɗakin tace "Ina wuni Umma? An yini lafiya?" Ta tambaya lokaci ɗaya. "Lafiya ƙalau Alhamdulillah.." Ammi ta faɗa tana neman waje ta zauna. Se Abidar ta cigaba da zama a ƙasan tana ɗan murmushi jefi_jefi, wai ita a lallai dole me hankali. "Ki koma kan kujerar mana." Ammi ta faɗa tana murmushi. Da sauri ta girgiza kai tace "A'ah Umma nan ɗin ma ya yi.." miƙewa Ammi ta yi tace tana kallan Lulu da tun shigowar Ammin ba ta sake cewa komai ba "Ki kawo mata ruwa mana?" "Toh" ta amsa da hakan, yayin da Ammi ta shige ɗaki. Tashi tsaye Abida ta yi tana faɗin "Ki bar shi ma kawai wallahi, gida zan tafi. Ai mun gaisa da Umman. Bari na wuce.." "Toh ki gaida gida.." Lulu ta faɗa. "Gida ze ji.." Abida ta faɗa tana ficewa daga ɗakin. Lulu ta bi ta da kallo har ta fice, kafin ta ɗaga kafaɗa tana taɓe baki ta wuce ɗaki. ... Jikinsa a matuƙar sanyaye ya fito daga cikin office ɗin. Se ya ɗan dakata a gefe, ya jingina jikinsa da jikin bango idanunsa a ɗan lumshe. Gaba ɗaya tunaninsa ya tafi ne wajen yadda ze dinga samun kuɗin da za a dinga yi wa Abeeyn wankin ƙoda duk bayan sati 2. Bugun zuciyarsa har wani ƙaruwa ya yi, sanda ya ke wannan tunanin. Sam be lura da tsayuwar wani a kusa da shi ba, se lokacin da ya ji magana kamar daga sama "A'ah Malam Affan.. Lafiya dai koh?" Abba da tun ɗazu ya hango shi ya faɗa bayan ya ƙaraso dab da shi. Se a lokacin ya buɗe idanunsa da sauri ya sauke su a kan Abban. Shaida fuskar da ya yi ne ya sanya shi ƙaƙalo murmushin yaƙe yace "Lafiya ƙalau.." ya yi maganar yana miƙa masa hannu suka gaisa. Girgiza kai Abba ya yi yace "Anya kuwa?" Ƙarya ba halinsa ba ce, hakan ne ya sanya shi gyara tsayuwarsa sannan yace "Ehh toh.. Abeey ne babu lafiya..Amma In Sha Allah babu wata damuwa, dan yanzu haka ma fita zan yi, daga zarar na dawo za mu koma gida ne.." "Ikon Allah.. Toh Allah ya ba da lafiya me ɗorewa." "Ameen Ameen.." "Mu je na gaishe shi koh?" Abba ya tambaya yana kallan Gwanin. "Eyyah da yake ya samu bacci yanzun.." jinjina kai Abba ya yi cike da gamsuwa da maganar Gwanin, tun kafin ya ƙarasa yace "Toh shi kenan, Allah ya ƙara afuwa." "Ameen na gode." Gwani ya faɗa da ɗan murmushi kan fuskarsa, dan sosai ya ji daɗin yadda Abban ya nuna kulawarsa a kan Abeeyn. Dama tun sanda ya zo wajensa ya fahimci mutumin arziƙi ne, se dai yanzun ma se mutuncinsa ya ƙaru sosai a cikin idanunsa. Sallama suka yi, Abba ya yi inda ze je, yayin da shi kuma Gwani ya tafi wajen Ummeey da ya tabbatar tana can tana jiransa ne. Aikuwa tun kafin ya ƙaraso ta miƙe cike da zumuɗin jin abin da ze faɗa ɗin. A nutse ya ƙaraso wajen yana kallan Ummeeyn da duk damuwa ta gama bayyana a kan fuskarta yace "Ummeey.. ki kwantar da hankalinki. In Sha Allah babu damuwa me yawa. Zan fita yanzun, zan yi ƙoƙari na samu na haɗa kuɗin da za a yi masa wankin ƙoda ko na wannan satin ne.." ya ƙare yana ɗan ajje numfashi gami da lumshe idanunsa. "Wankin ƙoda kuma Affan?" Umma ta faɗa tana buɗe ido sosai. Cikin kwantar da murya yace "Ki kwantar da hankalinki Ummeey.." ya yi maganar yana kallanta. Girgiza kai Ummeey ta yi ba tare da tace komai ba, se komawa da ta yi ta zauna a kujerar da ta tashi daga kanta tana ji kamar ta yi kuka. A yanzu dai a yanayin da suke ciki samun kuɗin da za a dinga yiwa Abeeyn wankin ƙoda se dai idan Allah ne ze kawo musu wata hanyar. "Hasbunallahu wa ni'imal wakeel." Ummeey ta faɗa sanda ta ke kai hannunta kan fuskarta cike da tausayin kansu. Kusa da ita Gwani ya zauna, ya sake ƙasa da murya cikin rarrashi yace "Ummeey ka da ki ɗaga hankalinki. In Sha Allah kuɗin nan za su samu." "Allah ya yadda." Ummeeyn ta faɗa ba dan tana da tabbacin za su samu ɗin ba, se dan sunan Allah da ya ambata. .. Bin ta da kallo Ammi ta yi sanda take ƙoƙarin ɗaura niqab cike da ƙarfin hali. Cikin tausayawa Ammi tace "Afrah ajje niqab ɗin nan, da lafiya ake yin komai. Saboda haka ki bari idan kika warke se ki je.." Ammin ta faɗa saboda yadda ta lura da Didin kawai ƙarfin hali take yi amma ba ta da lafiya. Duk da haka kuma ba ta haƙura ba take shirin tafiya. Se da Lulu ta tura baki gaba, dan ta san idan da ita ce cewa za a yi ta tafi ta warke a can, dan kowa ya san halinta, abu kaɗan ne ze sanya tace ba za ta je makarantar ba, ko da kuwa lafiyarta ƙalau. Saɓanin Didin da koda yaushe cikin son zuwa makaranta take ko da kuwa ba ta jin daɗi. "Didi fa baki da lafiya.. kawai ki bari se gobe idan Allah ya kai mu." Itama Lulu ta faɗa tana kallan Didin da har ta koma ta zauna. Se kawai ta koma ta kwanta a kan gadon tana jin wani irin sanyi na ratsa ƙasusuwanta. Ɗaukar katon blanket Lulu ta yi ta ɗora mata a kai sannan ta kalli Ammi tace "Ammi mun tafi." "Toh Allah ya kiyaye." "Ammi mun tafi." Little ma ya faɗa yana yin gaba. Shi ma da addu'ar ta bi shi da ita tana murmushi. Ko da suka je makarantar yau Gwani be zo ba, dan haka wani malamin ne ya shigar musu ajin. Hakan ne ya sa yau ɗin da wuri aka tashe su. Dan haka ana tashin nasu Lulu ta kama hannun Little suka fito daga makarantar tare da Masoyiya. "Aou Fatima da tafiya za ki yi ki bar ni?" Abida ta faɗa sanda ta ƙaraso inda suke. "Eyyah a'ah fa. Kin ga mun tafin ne?" Fatima ta faɗa. "Toh don Allah idan ba zaku samu damuwa ba ku ɗan raka ni wani gida mana?" "Gida kuma?" Fatima ta tambaya. "Ehh pls ka da ku ce a'ah.." "Masoyiya ni fa tafiya zan yi, kin san Didi ba lafiya.." Lulu ta faɗa tana kallan Fatiman. "Wani gida fa kawai za ku raka ni.." Fatiman ta sake faɗa se dai yanzun Lulu take kalla. "Pls mu rakata ɗin.." Fatima ta faɗa tana kallan Lulu. Da sauri Lulu ta girgiza kai sannan tace "A'ah ku yi haƙuri pls.." "Pls mana." Fatima ta faɗa tana riƙo hannun Lulu. Se da ta jefa mata harara sannan tace "Mu yi sauri don Allah.." Wani irin murmushi ne ya suɓuce wa Abidar. Se ta soma takawa tana tunanin yanda za ta yi su rabu da Fatima a yanzun. Cigaba da tafiya suka yi jefi_jefi suna ɗan taɓa hira kaɗan. Little kuma na ƙarawa tafiyar tasu armashi ta hanyar surutansa wasu na hankali, wasu na shirme. Dakatawa Fatima ta yi tana ɗan yamutse fuska sannan tace "Ina ganin fa baƙon watana ne wallahi.." ta yi maganar tana ɗan riƙe cikinta. Kallanta dukansu suka yi. Lulu tace "Toh mu koma gida kenan?" "A'ah mu ƙarasa gidan mana, ae za a samu pad." Abida ta yi ƙundunbalan faɗin hakan, cike da fatan ka da Fatiman tace "Toh" Aikuwa addu'arta ta karɓu dan kuwa buɗar bakin Fatima se cewa ta yi "A'ah Abida. Kin ganni fa a gida, gwara na tafi gobe ma haɗe, ki yi haƙuri.." "Babu komai ai, tunda ga Afaaf za ta raka ni." "Waye Afaaf?" Lulu ta faɗa tana kallan Abidar. "Ke mana, ko ba za ki raka ni ba dan Masoyiyarki ta tafi? Don Allah Fatima ki ce ka da ta ƙi raka ni. Ni kaɗai zan je kamar wata mayya." Ta ƙare kamar me neman taimako. Cikin rarrashi Fatima ta kalli Lulu tace "Pls ki rakata mana." Ba dan ta so ba, se dan kawai dai ka da Abidar tace ta wulaƙanta ta ne ya sanyata faɗin "Na ji.." ta faɗa tana sake kama hannun Little suka cigaba da tafiya. Dan farin ciki Abida ji ta yi kamar ta tsaya ta taka rawa. A haka suka cigaba da tafiya, har suka ɓillo wani bakin titi. Cike da ƙosawa da tafiyar, dama kuma abinka da ba ta yi niyya ba, Lulu tace "Ni fa gaskiya am tired. Har yanzu ba a zo ba?" Murmushi Abida ta yi kana tace "Mu na tsallaka titi gidan ya ke.." "Ah toh.." Lulu ta faɗa. Daidai lokacin da suka tsallaka titin ya yi daidai da lokacin da Gwani ya ke saukowa daga cikin Napep tare da wani ɗalibin Abeey. Shi ya soma sauka sannan Gwani ya sauka, ya miƙawa me Napep ɗin kuɗinsa. Yayin da ɗalibin Abeey ɗin me suna 'Abbati' ya ɗan miƙe hannunsa kamar wanda suka yi tafiyar awanni ya gaji. Daidai sanda ya ɗan juya yayi daidai da lokacin da su Lulu suke ƙoƙarin shiga gidan hannunta riƙe da Little. A haka sam ba zaka gane ma gida ba ne, saboda yanda wajen ya ke kamar ba ƙofar gida ba, sannan kuma shaguna da yawa sun yi ƙoƙari wajen kare gidan, dan idan dai har baka san da zaman gidan a wajen ba, toh ba za ka gane akwai gida a wajen ba. A kan Lulun kuwa idanunsa suka sauka sanda ta ida shigewa cikin gidan. Tsaki Abbati ya ja yana girgiza kai, cike da takaicin wannan abu da ke faruwa. Ya kasa shiru har se da ya kalli Gwani da ke ƙoƙarin sake tare musu wani Napep ɗin saboda wannan ɗin tayarsa ce ta samu matsala. "Wallahi ya kamata a saka ido a kan gidan nan sosai. Iyaye ma kuma yana da kyau su sake saka idanunsu a kan 'ya'yansu. Wallahi Malam yanzu ba ka ga wata yarinya da na gani ba dududu a shekaru ba zata wuce a ƙirga su ba, amma ta shiga gidan nan. Ban san me yasa kamar hukuma na tsoron gidan nan ba ne." Girgiza kai kawai Gwani ya yi sannan yace a nutse "Allah ya kyauta, ya kuma shirya.." ya yi maganar sanda ya ke hawa cikin Napep ɗin da ya tare musu. A ɗan mamakance Lulu ta dinga bin gidan da kallo, dan gaba ɗaya ta rasa a wane muhalli za ta aje gidan. Ta kasa gane me ake yi a gidan, suna ake yi ko biki ake yi? Duk ta kasa ganewa. "Wai biki a ke?" Little ya faɗa yana bin wani waje da a ke kiɗa da kallo. "Ehh" ta faɗa, dan itama a yanzun ta gane bikin a ke yi, saboda yanda ta ga taron mata ne a ko ina, se jefi_jefin maza kaɗan kaɗan. "Kar ki damu Afaaf, ai mun zo." Abida ta faɗa tana jin ita kam yau burinta ya gama cika, tunda har ta iya ɗauko Lulun ta kawota gidan nan, ai komai ya ƙare kuma. Har cikin wani parlour suka isa, ita dai Lulu ta gama ƙuluwa, ta gama fusata dan har ta riga ta ƙudura a ranta cewar, ko me Abidan za ta yi ba za ta sake rakata wani wajen ba, se dai ta ji haushi ta dena kulata. Ita kaɗai ce a cikin ɗakin sanye cikin wasu riga da wando waɗanɗa suka bi lafiyar jikinta suka zauna sosai. Siririya ce se dai ba can ba, amma da ke tana da diri ya sanya a kallo ɗaya ba zaka kirata da siririya ba. Kanta babu ɗan kwali se tulin attach ɗin da ke zaune a kanta kamar ba ɗorawa a ka yi ba, saboda yanda suka zauna sosai. "Yallaɓiya saukar alkhairi.." Abida ta faɗa tana murmushi gami da ƙarasawa kusa da matar. Da sauri Ladi ta juyo tana kallan Abida kafin ta maida kanta kan Lulu da har lokacin take tsaye a bakin ƙofar, ta daɗe da ƙaguwa a kan Abidar ta fito su tafi. Lumshe idanunta Ladi ta yi kafin ta koma kan kujera ta zauna yaɓar har lokacin idanunta a kan Lulu. Se ta nuna wa Lulu kujera tana faɗin "Ki zauna mana Baby.." Ladin ta faɗa tana wani maƙe muryarta da tafi kama da ta wani ƙaton gardin. Ita sam Lulu ba ta kawo komai ba, dan ba ma ta ji sunan da Ladin ta kirata da shi ba. Haka zalika shigar jikinta ma bata damu da ita ba, dan tafi tunanin me aure ce, kuma yamma ta yi shi ya sa ta yi wa mijinta kwalliya. Se ta ɗan zauna kaɗan tana sake riƙe hannun Little fuskarta a haɗe saboda yanda ta riga ta ƙulu da Abida. "Duk yanda ki ke kwatanta min ita ai ta ninka hakan sau 10 Abida. Wannan aba haka kamar ita ta yi kanta? Kalleta fa don Allah? Ke na ninka miki kuɗinki sau 3, dan na tabbatar yau ɗin nan akwai ƙurewa daɗi maleji.." Ladi ta faɗa tana sakin wani shu'umin murmushi har lokacin idanunta na kan Lulu tana binta da wani irin kallo kamar tsohuwar mayya.. https://chat.whatsapp.com/BClMNPwWybg2n3oRvtemv8 *♡☆A JINI TAKE☆♡* *(IZZATA)* By _*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_ *CHAPTER ONE* Page_13 ___Cikin er rashin fahimta Lulu ta ɗaga kai ta kalli matar da a lokacin ta miƙe daga inda ta ke zaune ta soma takowa zuwa wajen Lulu, lokaci ɗaya tana furta "Karɓi yaron ki ajje mata shi.. Me ya sa ma ku ka taho da shi?" Ta yi maganar sanda ta ƙaraso dab da Little. Ta saka hannu ta riƙo hannunsa. Da sauri ya fuzge hannunsa yana ɓata fuska gami da shigewa jikin Lulu. Tashi ta yi daga kan kujerar tana sake riƙe hannun Little da ke kuma ƙanƙame hannunta. Se dai ga mamakinta se ta ji matar na faɗin bayan ta kalli Abida "Ɗauke shi ki fita da shi, ze hanamu rawar gaban hantsi.." Ba ta ƙarasa maganar ba se kuwa Abida ta ƙaraso ta kai hannunta wajen Little dan ɗaukarsa. Iya ƙarfinsa ya saka ya fashe da kuka daidai lokacin da Lulu ta gama fusata da su gaba ɗayansu. Cikin fushi tace "Wai meye haka ne? Ina za ki kai Little ɗin? Ina ruwanki da shi? Idan za ki gama abin da ya kawoki gidan nan ki zo mu tafi toh. Idan kuma ba za ki tafi ba ki faɗa min na kama hanya.." Da mamaki Ladi ta kalli Abida cikin ƙasa da murya tace "Ki na nufin ba ta san abin da ya kawota gidan nan ba?" Se da ta ɗan yamutse fuska sannan tace "Da ta sani da ba ki ganta cikin gidan nan ba.." "Ohhh.. na gane.." Ladi ta faɗa tana jinjina kai daidai lokacin da ta maida dubanta kan Lulu. Ɗan lumshe idanunta Lulu ta yi saboda yadda ta ga Abidar da matar na neman maidata er iska, ta yi magana ma sun juya suna wasu maganganun. Hakan ne ya sanya ta saɓi Little da ke matse ƙwalla a kafaɗarta sannan ta yi hanyar fita. Da sauri Ladi ta yi maza ta tare hanyar tana faɗin "Na shiga ukuna, ina kuma za ki je?" Cikin rashin fahimtar dai Lulu tace "Ban gane ba? Nan ɗin gidanmu ne da in zan fita za a tambayeni inda zan je?" Ta tambaya tana watsa mata wani kallo. Ajiyar zuciya Ladi ta sauke tana tunanin ta yadda za ta ɓullowa Lulun, dan daga yadda ta ke magana kaɗai ta fahimci ita ɗin ba irin matan da ake kawo mata ba ne. Dole se ta yi da gaske, idan ba haka ba tana ganin wannan ganimar haka za ta tafi ba tare da ta ƙaru da komai ba. Cikin rarrashi ta soma faɗin "Kin ga ki kwantar da hankalinki, ba wani abun tashin hankali ba ne. Kawai fa harka ce ta jin daɗi da za ki samu kuɗi bayan jin daɗin.. Ke Abida zo ki buɗa mata bayani yanda za ta fi fahimta.." ta ƙare maganar tana kallan Abida. Kamar wata doluwa Lulu ta bi Abidan da kallo tana jin yadda jikinta ya yi wani mahaukacin sanyi, har wani rawa ya soma yi, dan kuwa hatta hannunta da ke ɗauke da Little se da ya ka sa riƙe shi, ta ɗan sassauta riƙon sanda shi kuma ya ke sake riƙeta kamar ze shige cikinta. "Kin ga Afaaf, ki kwantar da hankalinki, ka da ki tashe shi. Ba fa wani abu ne me wahala ba, kawai dai za ku ɗan shafe mintuna ne fa da Jakadiya ku ɗan jiyarwa kanku daɗin jikinku.." Runtse idanunta Lulu ta yi sanda bugun zuciyarta ya ƙaru, yanayin yanda jikinta ke rawa ma ya ƙaru. Ta kai wajen second 20 idanun na ta a lumshe, wanda farin ciki har ya soma cika zuciyar Ladi da ke ganin Lulun za ta amince da buƙatarsu. Se dai me? Cikin sakannin da basu wuce 3 ba Lulu ta buɗe idanunta a kan Ladi da kuma Abida da ke kusa da juna, muryarta har rawa take yi sanda ta soma faɗin "Ashe Abida ke ɗin mutuniyar banza ce? Ashe mutuniyar wofi ce ke mara tsoron Allah? Ashe shi ya sa tun kallan farko da na miki na ji ba ki min ba? Na kasa sakin jiki da ke duk saboda yanda zuciyata taƙi aminta da ke? Amma ki ka yi yadda za ki yi, ki ka yi amfani da muguwar zuciyarki da muguwar manufarki ki ka sakani na soma kulaki, har na iya ɗakko jiki na rakoki wani wajen? Tirr da irin wannan rayuwar taku. Tirr da wannan ƙazamar rayuwar taku da ba kwa jin kunyar idanun mutane ballantana ku ji tsoron Allah. Wa'iyazubillahi, Allah ya kiyasheni da aikata aikin danasani da nadama.. Matsamin na wuce.." Ta yi maganar sanda ta sake rungume Little. "Babu inda za ki je. Ai kin shigo kenan.. ta yaya ma zan bari ki shigo gidan nan sannan na barki ki fita ba tare da na ji kalarki ba? Tun da Abida ta ke kwatanta min ke na ji na ƙawatu da son ganinki. Daga kuma lokacin da na yi ido biyu da ke na ji duk wani burina na son ganinki ya ruguje, abin da kawai na ke buƙata shi ne kasancewa da ke.." Ladi ta faɗa tana matsowa kusa da Lulu. Wani irin hawaye me zafi ne ya zubo daga idanun Lulu na dama na tsantsar takaici da kuma sake yin tirr da halin Abidar da Ladin. Ganin yanda ta ke matsowa kusa da ita ne ya sanyata saurin matsawa gefe tana faɗin "Ka da ƙazamin jikinki ya soma gangancin taɓani.. ki matsamin na fita idan ba haka ba wallahi zan miki abin da ba za ki taɓa mantawa da Afaaf a rayuwarki ba.." Lulu ta faɗa duk da yanda take jin ƙirjinta na wani irin bugawa cike da tsoro. "Bana son taurin kai Malama Afaaf.. kawai ki yi biyayya, salin alin za ki fice daga gidan nan da kuma damin kuɗi a hannunki.." In ji Ladi tana sake matsawa kusa da Lulu "Ke ce matsiyaciya ba ni ba, ke kuɗi suka dama.." Kafin Lulu ta ƙarasa faɗa ta yi gefe saboda yadda Ladi itama ta yi gefe dan so take kawai ta ƙwace Little daga hannun Lulu sannan ta san yanda kuma za ta yi da Lulun. Hakan ne ya janyo Lulu ta taka ƙafarta se ta yi baya kamar za ta faɗi, ta yi saurin dafe Little tana ƙoƙarin miƙewa a kan ƙafarta Ladi ta riƙota. Kuka Little ya sake fashewa da shi saboda yanda ya tsorata, ga wannan matar da ta gama tsorata shi. Se kuwa ya shiga rera kukan shi. Abin da ya sake ƙular da Lulu kenan, ta saka hannunta bayan tattaro duk wani ƙarfinta ta tunkuɗa Ladi gefe. Se kuwa ta yi baya ta zube a wajen. Da sauri Lulu ta yi amfani da wannan damar ta tura ƙofar ɗakin ta fice da wani irin saurin da ba ta san tana da shi ba, a ranta tana karanto duk addu'ar da ta zo bakinta. Yunƙuri Abida ta yi dan bin bayan Lulu, Ladi da ke zaune a ƙasa zaman daɓaro ta yi saurin dakatar da ita ta hanyar faɗin "Ka da ki bi ta. Batta na san yanda zan yi da ita.. Na ganta koh? Kuma ta min. An kawo min ita ta gudu.. Za ki ga abinda zan mata.." Ta ƙare maganar tana sakin wani murmushin takaici, musamman idan ta tuna wannan samu da rashin. Ga Lulun har gida amma ta tafi ba tare da ta aiwatar da abin da ta ke da niyyar aikatawa ba. Sosai ƙirjin Abida ke bugawa, ita ba rashin samun damar da Ladi ba ta yi bane yafi tsaya mata a rai ba. Gaba ɗaya tunanin ta ya tafi ne ka da Lulu ta je ta faɗi abin da ya faru, ta kuma tona mata asiri a cikin unguwa bayan babu wanda ya santa da wannan hali. Lura da yadda Abidar ta shiga damuwa ne ya sanya Ladi faɗin "Ka da fa ki sakawa kanki damuwa. Ni ce fa Jakadiya Ladi.." ta ƙare tana tuna surar Lulu da ta iya gani daga cikin hijab, uwa uba kyau da kuma yarintar da ke tattare da ita, suna cikin abubuwan da suka ɗauki hankalinta na son kasancewa da ita. ... A hankali ya saka hannunsa ya tura ƙofar ɗakin da Abeeyn ke kwance da sallama a bakinsa. Duka suka amsa masa sallamar. Ya ƙaraso ciki, se dai da mamaki kan fuskarsa ya ke kallan Abba. Cike da mamakin dai ya furta "A'ah Yallaɓae...!" "Uhmm Malam Affan sannu da dawowa." Ɗan lumshe kyawawan idanunsa ya yi kaɗan kamin ya nemi waje ya zauna saboda gajiyar da ya yi kana yace a nutse "Yawwah.. Ashe ba ka tafi ba. An gode Allah ya bar zumunci.." "Aou ka san abin da ya yi kenan?" Ummeey da shigowarta kenan ta faɗa tana murmushi. Se ya kalli Ummeeyn da ɗan mamaki a kan fuskarsa, dan be fahimci a kan abin da take magana ba, ya girgiza kai yana faɗin "Ummeey.." Daga inda Abeey ke kwance yace shi ma yana murmushin "Ka godewa Allah ka godewa wannan bawan Allahn Affan. Ya hutasheka wahala dan kuwa ya biya kuɗin wankin ƙodar.." Da sauri Gwani ya kalli Abba cikin mamakin jin abin da ke fitowa daga bakin Abeeyn. "Ya biya kuɗin?" Ya tambayi kansa. Ya riga ya san Abban ba ze masa wasa a irin wannan abin ba. Hakan ne ya sanya shi sake kallan Abban yace "Yallaɓae..?" Murmushi Abba ya saki kafin ya miƙe yana faɗin "Dama jiranka na ke yi Malam Affan.. tunda ka dawo bari na tashi na tafi.. Allah ya ƙara afuwa ya sa kaffara.." "Ameen_Ameen." Abeey da Ummeey suka amsa addu'ar, se dai shi Gwani ya kasa cewa komai saboda mamakin Abban na biyan kuɗin bayan a haka dai za a iya cewa ba su da wani haɗi. Se da ya ga da gasken Abban fita ze yi sannan ya soma takawa cikin nutsuwa, kyakkyawar fuskarsa na ƙawatuwa da murmushin da ya matuƙar karɓar fuskarsa yace "Muna godiya sosai. Allah ya bar zumunci, ya saka da alkhairinsa.." ya faɗa dan tabbas ya ji daɗin yadda Abban ya nuna kulawarsa a kan Abban tun da farko. Ya riga ya san babu kyau maida hannun kyauta baya, ba dan haka ba da se ya faɗawa Abban ya bar kuɗin tunda ga su ya samesu. Se dai ko babu komai idan har ya bar shi Abban ze ji daɗi, ya kuma san yana yin wasu abubuwan ne duk dan ya sake wanke kansa a kan laifin da ba shi ya aikata ba. "Allah ya ƙara afuwa." Abba ya sake faɗa yana ficewa daga ɗakin. Ɗan sake lumshe idanunsa Gwani ya yi bayan fitar Abban, a nutse ya taka ya nemi waje kusa da Ummeey ya zauna yana sauke ajiyar zuciya. "Affan a ina ka samo wannan mutumin?" Abeey da har lokacin be koma bacci ba ya faɗa. Se a lokacin ya ɗan buɗe idanunsa. Se ya jefa idanunsa gefe a ransa yana tunanin abin da ya kamata ma yace. Ƙarya ba halinsa ba ce dan haka buɗar bakinsa se cewa ya yi "Mahaifin ɗalibaina ne!" "Ɗalibai kuma?" Ummeey ta faɗa cike da mamaki. Se ya jinjina kai dan tabbatar da abin da ya faɗa sannan ya ɗora da "Ehh Ummeey.." "Ikon Allah.. Allah ya saka masa da alkhairi.." Abeey ya faɗa yana sake jinjina kirki irin na Abba. .. Tafiya ta ke yi cike da sassarfa, fararen idanunta sun cika taff da ƙwalla wadda ƙiris ta ke jira ta zubo. Jefa ƙafarta kawai ta ke yi ba tare da sanin inda za ta saka ƙafarta ta ba. Babu abin da ta ke hangowa ta ke kuma sake tunawa se maganganun Ladi da Abida masu muni marasa kuma daɗin ji. "Ba za su biyomu ba koh?" Little da ya gama firgecewa tun ɗazun ya faɗa a tsorace. Ba ta iya amsa masa ba, se cigaba da tafiya da ta yi har lokacin jikinta be dena rawa ba. Daidai sanda suka kusa isa gida ta sake jiyo muryar Little na faɗin "Lulu ba za su biyomu ba koh?" Se a lokacin ta tuna daga ina suke, ina suke shirin zuwa yanzu, waye kuma a hannunta. Take ƙirjinta ya wani irin buga. Se ta sanya hannu ta sauke shi daga kafaɗarta zuwa kan wani dandamalin ƙofar wani gida. Da sauri ya sake riƙota yana faɗin "A'ah kar ki tafi ki barni kin ji?" Ya faɗa yana kallan gefe da gefensa. A take ta ji duk wani tunanin gidan nan ya soma yin nasa wajen. Tsoro da fargabar tunkarar gida ya mamayeta. Ta manta sam ba ita kaɗai ba ce, ballantana idan ta koma gida ta haɗa ƙarya ta faɗa. Ita da Little ne, a yadda kuma ya tsoratan nan babu abin da ze hana shi bayar da labarin abin da ya faru. A tambayeta ina ta je tace mene ne? Wane gida ne? Me ta je yi gidan? Tuna abubuwan nan da ta yi ne ya sanya ta riƙo Little ɗin, daidai lokacin da wata sabuwar ƙwalla ta taru a cikin idanunta. Se kawai ta koma ta zauna a kan dandamalin cikin rashin sanin abin yi... A yi manage da wannan pls. Gobe idan Allah ya kai mu za mu haɗe. https://chat.whatsapp.com/BClMNPwWybg2n3oRvtemv8 *♡☆A JINI TAKE☆♡* *(IZZATA)* By _*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_ *CHAPTER ONE* Page_14 ___Ta shafe fiye da minti 10 zaune a wajen ba tare da ta sake niyyar ko da miƙewa ba ne. Se da ta jiyo muryar Little na taɓata yana faɗin "Wai anan za mu zauna?" Se a lokacin ta sauke ajiyar zuciya lokaci ɗaya tana ɗan lumshe idanunta sannan ta miƙe a hankali ta kamo hannun Little ɗin. Karon farko tun fitowarsu daga gidan nan ta buɗe baki tace "Gida za mu tafi.. ka da ka faɗawa kowa inda muka je ka ji?" Ta faɗa tana kallansa. "Kaiii!!" Ya yi maganar kamar wani babba yana jinjina kai gami da waro idanunsa masu kama da na Twins sakk. Se da ta ja doguwar ajiyar zuciya sannan cikin rarrashi ta soma faɗin "Zan siya maka sweet idan ba ka faɗawa kowa ba. Ai babu inda muka je daga makaranta koh.?" "Ehh" ya faɗa yana ɓata fuska, se kuma ya ɗora da "Amma babba.." murmushin da ya tsaya a iya bakinta ta yi, saboda har lokacin ba ta gama komawa daidai ba. "Yeap.. babba sosai ma." "Yes!" Ya faɗa kamar wani babba yana murmushi. Se ta saka hannunta ta sauko da shi ta kama shi suka soma tafiya zuwa gida, har lokacin tafiyarta ta dai babu wani kuzari. Suna zuwa ƙofar gida ta kalli Little tace "Ina ma muka je?" "Makaranta." Ya amsa mata da sauri yana murmushi. Kamar wata mara laka haka ta cigaba da takawa zuwa cikin gidan. A hankali ta yi sallama a ƙofar parlourn cike da fatan babu kowa a ciki. Aikuwa babu kowa ɗin a ciki se ta yi saurin shigewa cikin ɗakinsu. Anan ta samu Didi da Ammi suna sallah. Se kawai ta saki hannun Little da sauri ta shige toilet. Se a lokacin ta sauke ajiyar zuciya gami da jingina kanta jikin bangon toilet ɗin tana lumshe idanunta. Wasu irin hawaye masu ɗumi suka zubo a kan kuncinta. Sam ba ta da saurin kuka, ko kuma zuciyarta ta karye da wuri, se ga shi yau ɗin cikin ƙanƙanin lokaci zuciyarta ta karye, ta ka sa mantawa da abin da ya faru a yau ɗin. Daidai lokacin da ta ji ƙarar buɗe ƙofar ɗakin alamar an fita ta fashe da kuka kawai, kukan da ba ta san dalilinsa ba tunda dai Allah ya kuɓutar da ita. Se da ta gama kukan sannan ta ɗauro alwala ta fito bayan ta wanke fuskarta sosai. A ɗakin ta tarar da Little zaune kan gadonsu yana cin abinci, yayin da Didi ke kwance a kan gadon saboda zazzaɓin da har lokacin be gama sauka a jikinta ba. A hankali ta ƙaraso ta ɗauki dadduma ta shimfiɗa, tana gyara zaman hijab ɗin jikinta ta jiyo muryar Didi na faɗin "Har kin gama kukan?" Se ta dakata da sauri tana kallan Didin da ke lulluɓe da blanket. Kallan Little ta yi da ke cin abincinsa hankali kwance. Ta san idan ya ji maganar Didin ze iya tuna abin da ya faru, hakan ne ya sanyata kallansa tace "Little.. je ka ci abincin a parlour ka ji?" Babu musu ya miƙe riƙe da ƙaramin plate ɗin da abincin ke ciki ya fice da sauri. Se a lokacin ta kalli Didi a hankali tace bayan ta ɗan yamutse fuska "Ni fa ba kuka nake yi ba.." "Uhmm, ya miki kyau.. ban san lokacin da muka fara ɓoyewa juna wani abun ba. Amma ki cigaba." Didi ta faɗa tana gyara kwanciyarta. Shiru ta yi dan ita kanta ta san abin da ta ke ƙoƙarin yi ɗin ba daidai ba ne, kasancewar ba sa taɓa ɓoyewa junansu wani abun. Dan haka gudun ka da ta ja lokaci ya sanyata tayar da Sallah. Se da ta idar sannan ta miƙe ta koma kan gadon, a hankali tace "Didi.." juyawa Didi ta yi daga ɓangaren da ta ke, ciki ciki tace "Ka da ki ce min komai malama.." "Am sorry.." ta yi maganar a narke. "Ke yanzu fa ba zan ji ba. Duk sanda kika yi niyyar faɗa min kya faɗa min, ae dama na ga take_takenki kwana biyun nan" girgiza kai Lulu ta yi tana faɗin "Haba mana Didina.." "Kya ji da shi dai.." Didin ta faɗa tana ture hannunta. Murmushi kawai Lulu ta yi, dama yanzun kwata kwata ba ta son yin zancen nan, dan haka gwara ta bari idan Didin ta sakko se ta ba ta labarin, zuwa lokacin itama ta nutsu. .. "Ba za ki gane ba ne Jakadiyarmu.. Tsorona Allah tsorona ka da yarinyar nan ta ɗauka maganar nan ta je ta yaɗani a wajen mutane." Tsaki Ladi ta yi tana girgiza kai cike da fusata da zancen Abidar da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa. "Ke ki dakata da min maganar nan na faɗa miki. Ita ɗin banza ta faɗawa wani? Ni nan ni ce fa na faɗa miki ba za ta sanarwa da kowa ba. Ko ba ki yadda da ni ba ne? Idan ba ki yadda ba ki cigaba da damun kanki. Kuma ma dan an sani se mene ne? Kina tunanin duk zuwan da ki ke gidan nan dama babu wanda ya taɓa ganinki? Kin ga kawai ki yi sha'aninki hajjajuna.." Ladi ta faɗa tana gyara zamanta. "Toh." Abida ta faɗa tana karkatar da kanta lokaci ɗaya tana ɗan taɓe baki kawai. "Maganar Afaaf?" Kamar wadda Lulun ke gabanta ta saki murmushi hadda lumshe idanunta kafin ta soma faɗin "Zan ba ta dama ɗaya ne a yanzu haka.. ki sake gwada sa'arki wajen janyo min hankalinta zuwa wajena. Idan kuma taƙi se na chanja wani salon, kin san ance idan dama taƙi se a koma hagu. Naga kan yarinyar na rawa saboda haka zan taka mata birki. Zan saka a wulaƙanta min abin da take taƙama da shi sannan daga ƙarshe dole ta dawo ƙarƙashina a lokacin da rayuwarta za ta koma mara amfani a wajen kowa. Ni kuma a sannan ne zan ci karena babu babbaka. Kin ga ta yi biyu babu kenan.." ta ƙare tana murmushi tana kuma hasaso yanda komai ze tafi. Jinjina kai Abida ta shiga yi bayan gama sauraron maganar Ladin. Tabbas Ladin ta fusata, kuma ba komai ne ya sake ingizata ba se ganin Lulun da ta yi, kuma ba ta sameta ba. Ta riga ta san abin da take faɗa ɗin da gasken za ta aikata, za ma ta iya aikata abin da yafi haka. Dan haka za ta yi ƙoƙari wajen sake janyo ra'ayin Lulun ko dan ka da Ladi ta saka a ɓata mata rayuwa. "Shi kenan. Zan sake zuwa na lallaɓata. Ki saka a ranki kin gama samun Afaaf." Abida ta faɗa tana murmushi dan ta kwantar da hankalin Ladin. Aikuwa se ta yi murmushi tana faɗin "Allah ko Abida?" "Ƙwarai kuwa.." Abida ta faɗa tana sake yin wani murmushin kai ka ce ta ma kawo mata Lulun ne. .. Baƙuwar motar da ya gani ce a ƙofar gidan ya sanya shi dakatawa. Cike da mamaki ya ke kallan motar ganin da gasken a ƙofar gidan ta tsaya. "Ɗan uwa zan kiraka zuwa anjima.. pls ka da ka ƙi amsawa.." Kaseem ya faɗa sanda ya hangi Abba. Daga can ɓangaren shiru ne ya ɗan wanzu kamar ba waya ya ke ba, se kuma a hankali na ji an ce "Oh..k.." daga haka tun kafin Kaseem ɗin ya katse wayar aka datse kiran. Girgiza kai Kaseem ya yi a hankali yana furta "Wannan baudaɗɗen Areef ɗin halinsa se shi.." Da sauri ya sauka daga motar ya ƙarasa inda Abba yake bayan ya jefa wayarsa a aljihu. Cike da girmamawa ya tsuguna yana faɗin "Barka da wannan lokaci.." "Barka dai.." Abba ya faɗa yana riƙe hannun Kaseem suka gaisa sannan ya ɗora da "Tashi mana" murmushi Kaseem ya yi kana ya miƙe ɗin. Se kuma ya ɗan yi shiru har se da Abba yace "Se dai kuma ban shaida fuskar ba.." "Ehh wato dama dai ba ka sanni ba.. amma dai na zo ne a kan Afaaf" ya faɗi sunan kamar yanda Mami ta faɗa masa. "Toh.. Allah ya sa dai ba laifi ta yi ba" Abba ya faɗa dan har ya fara tunanin ko malaminsu ne ya kawo ƙararta kuma. Da sauri Kaseem ya shiga girgiza kai har lokacin kansa na ƙasa "A'ah a'ah wallahi, babu abin da ta yi. Kawai dai wata maganar ce daban." Se a lokacin Abba ya ji daɗi dan har se da ya sauke ajiyar zuciya sannan yace "Toh mu je daga ciki mana.." Cikin jin daɗi Kaseem ɗin ya bi bayan Abba zuwa cikin gidan. A compound ɗin gidan suka zauna kan wasu kujeru masu kyau. Shiru Abba ya yi sanda ya gama saurarar maganar Kaseem ɗin. Se ya sauke ajiyar zuciya sannan yace "Gaskiya ka zo da magana me kyau. Kuma zuwa wajena da ka fara yi ya sake tabbatar min da ingancinka. Se dai kuma wani hanzari ba gudu ba.." da sauri Kaseem ya ɗaga kai ya kalli Abba, cike da tsoron abin da ze fito daga bakin nasa. "Ita dai yarinyar nan yanzu haka a S.S 1 take, yanzu ne suke ƙoƙarin shiga S.S. 2. Saboda haka ko da zan aurar da ita na fi ƙaunar ta gama secondary school, idan ya so se ta cigaba a gidan mijinta. Idan hakan ya yi maka toh babu damuwa se na soma ba ka dama wajen ita yarinyar. Idan har kun daidaita toh se mu san abin yi kuma." Ajiyar zuciya Kaseem ya sauke yana murmushi kamar wanda aka ce an ɗauki Lulun ne ma an ba shi gaba ɗaya. "Na gode sosai Yallaɓae, Allah ya saka da alkhairi ya ƙara girma. Hakan da ka yi ya yi daidai, kuma nima ya min. Bani da damuwa da gama secondary ɗinta idan dai har ta amince da ni.." ya ƙare maganar ƙasa_ƙasa cikin er jin kunya. Murmushi Abba ya yi dan hankalin yaron ya burge shi yace "Toh babu damuwa. Allah ya ba da sa'a." A zuciyarsa ya amsa da Ameen ɗin daidai sanda Abba ya miƙe. Ba dan ya so ba shima ɗin ya miƙe yana ta kokawa da zuciyarsa a kan kada ta rinjaye shi ya furta yana son ganin Lulu. "Zauna.. bari na turo maka ita." Wani irin sanyi ne ya ji ya ratsa shi, har se da ya lumshe idanunsa yana komawa ya zauna kan kujerar. Se kuma ya tuna be cewa Abban komai ba, hakan ne ya sanya shi ɗaga murya wajen faɗin "Toh Allah ya saka da alkhairi" A parlour Abba ya sami Ammi, Didi da kuma Lulu zaune suna kallo. Ya kalli Didi da ke kwance yace "Afrah ya jikin?" "Da sauƙi Abba" "Toh Masha Allah, Allah ya ƙara afuwa." "Ameen Ameen" suka haɗa baki wajen faɗar hakan. "Sannu da zuwa Abbansu." Ammi ta faɗa. "Yawwah.. Ke Afaaf.." Abba ya yi maganar lokaci ɗaya. "Na'am Abba.." "Tashi ki je waje, kin yi baƙo.." gaba ɗayansu suka ɗaga ido suka kalli Abban cike da mamakin furucinsa. "Baƙo kuma?" Ammi ta tambaya tana kallan Abban. Se da ya nemi waje ya zauna sannan yace "Yanzu dai ta fara zuwa ka da a bar ɗan mutane da jira. Ke kuma zauna na faɗa miki yanda a ka yi.." Kallan Abba kawai Lulu har ma da Didi suke yi, jikin kowaccensu a sanyaye, musamman ma Lulu da har jikinta ya soma rawa, idanunta sun tara ruwan hawaye, jin wai ita ce ke da baƙo kamar a film. Toh me aka zo yi wajenta kenan? Me aka zo a ce mata? Ko dai ɗan makarantarsu ne? Kai ta ma fi tunanin hakan, tunda da dai ita a shekarunta yanzun dai ba soyayya take yi ba. "Daɗina da ke Afaaf shininniƙi. Afrah maza shirya ki rakata. Ba wani abun ba ne ba.." jin abin da Abban ya faɗa ne ya sanya duka suka ji ɗan sauƙi. Duk da har lokacin jikin Didi be gama komawa normal ba, haka ta miƙe dan ba za ta iya barin Lulun ta fita ita kaɗai ba, duk da Abban yace musu babu komai, shi ya sa itama ta gama kawowa ranta ɗan ajinsu ne. Babban hijab kowaccensu ta saka, a haka suka fito daga ɗakinsu, kowaccensu dai har lokacin jikinta a sanyaye kamar waɗanda aka yiwa mutuwa. Bin su da kallo Ammi ta yi se dai ta gaza furta komai. So take kawai su fita ta ji bayani daga bakin Abban. A hankali suke takawa cikin compound ɗin, se baza idanu suke yi, ko da za su ga wani wanda suka sani zaune. Se dai har suka kusa ƙarasowa ba su ga alama ba. Hakan ne ya sanya Didi dakatawa tace "Kin ga dai wajenki a ka zo, ni dai wallahi komawa zan yi." Kamar za ta yi kuka Lulu tace "Don Allah Didi ka da ki tafi. Don Allah ka da ki koma kin ji? Wallahi a tsorace na ke, matuƙa tsoro nake ji. Ban san ko ɗan ajinsu waye ba. Ko kuma yayan wata ne a cikin en ajinmu." "Ehh kuma haka ne" Didi ta faɗa, se kuma ta ɗora da "Kin ga bari na zauna anan ina hango ku. Zan ƙaraso daga baya." "Don Allah da gaske?" Lulu ta faɗa "Ehh wallahi.." Se a lokacin sannan Lulu ta sauke ajiyar zuciya kana ta soma takawa zuwa inda Kaseem ke zaune. Se ta nemi kan kujerar ta zauna tana faɗin "Ga ni!" Wani murmushi ne ya suɓuce masa sanda ya ɗora idanunsa a kan Lulu. Wani farin ciki na mamaye ilahirin jikinsa. So daga ƙarshe dai ya yi tozali da wannan kyakkyawar fuskar bayan tsawon lokacin da ya ɗauka yana begenta. Ya ɗan lumshe idanunsa kaɗan sannan ya buɗe yace "Barkanki da fitowa gimbiya." Cikin rashin fahimta ta juya tana kallansa, ba ta san sanda tace "Gimbiya kuma?" Murmushi ya sake yi kamin yace "Ƙwarai kuwa.. Na san za ki yi mamakin zuwana, se dai wannan ɗin sam ba abin mamaki ba ne idan muka yi duba da kwanakin da na shafe ina nemanki." Ita duk wannan maganganun nasa ba ganesu take yi ba, ta fi so ta ji ya fito kawai ya faɗa mata shi yayan wance ne ta aiko shi wajenta. "Wato tun ranar da na soma ganinki za ki shiga islamiyya ke da ɗan uwanki. Allah ya ɗora min ƙaunarki. Na kasa haƙuri har se da na bi ki gidan da ki ka je, ashe gidan Aunt ɗinki ne. In taƙaice miki labari dai ta hanyarta na bi na sameki yau ɗin nan.." ya ƙare yana murmushi, yana sake kallan fuskarta cike da so da ƙauna. "Da yaro ka ganni a hannuna?" Ta tambaya bayan ta juyo gaba ɗayanta. "Ehh" ya faɗa da murmushin dai. "Kuma a dawowa se ka ga na shiga gidan Aunty Sadiya.." "Exactly.." ya faɗa yana nunata, irin kin gano ɗin nan. Se kawai ta saki murmushi a karo na farko tun bayan fitowarta wajen. Se ya shagala da kallanta yanda ta yi wani shahararren kyau da ta yi murmushin "Kenan idan haka ne Didina ka gani?" "Ban.. gane.. ba!" Ya faɗa a ɗan rarrabe yana kallan Lulu. Murmushin dai Lulu ta sake yi ko kunya ba ta ji, bayan da farko ko murmushi ta ƙi yi. "Twin sister ɗina ce.." Waro idanu Kaseem ya yi cike da mamaki da kuma al'ajabin abin da ke fitowa daga bakin Lulun. "Twin sister na ki kuma?" Ya tambaya a mamakance, wanda tsananin mamakin se da ya bayyana a kan fuskarsa. "Ƙwarai kuwa.." Cikin matuƙar mamakin dai ya shiga jinjina kai kafin ya sauke ajiyar zuciya yace "So ki na nufin ki ce min duk wannan neman da na ke ba ke na ke nema ba? Twin sister ɗinki ce?" "Ehh.." in ji Lulu. "Ikon Allah.. ya sunanta?" "Afrah.." jinjina kai Kaseem ya yi, se kuma ya saki murmushi kafin ya soma faɗin "Ko daga sunan ma namu ya fi daɗi.." dariyar da ba ta shirya yi ba Lulu ta yi na jin maganar Kaseem ɗin. Mutumin da ko wadda ya ke ƙauna ɗin ya kasa ganewa, wai shi ne me faɗin suna ya fi daɗi. "Ko ba ka faɗa ba, sunan Didina ya fi daɗi dama ai." "Uhm humm. Pls kira min ita, wallahi na ƙagu na yi tozali da kyakkyawar fuskar da ta hanani bacci kwana da kwanaki. Tsananin kamannin da kuke yi ne ya sanya na kasa banbance ku." Se ta miƙe kawai lokaci ɗaya tana jinjina kai, kenan me Abbansu ya ke nufi? Aurar da su ze yi a waɗannan shekarun nasu ko kuwa dai me? "Zo ki ji Didi.." Lulu ta faɗa sanda ta ƙarasa inda take zaune. Miƙewa Didi ta yi dan dama ta gaji da zaman "Alhamdulillah, mu tafi. Wallahi dama kaina se sara min yake yi." "Toh Didi wajenki fa ya zo, ya ɗauka ni ce ke.." "Ni kuma?" Didi ta faɗa tana buɗe ido. "Ehh fa.." "Toh waye shi?" Didi ta katseta da faɗin hakan. "Nima ban sani ba. Amma ki je se ki ji koh?" "Ni ba inda zan je." Didi ta faɗa tana juyawa dan komawa cikin gida. Da sauri Lulu ta yi maza ta koma gabanta tana faɗin "A'ah Didi ka da ki yi haka. Kin ga har wajen Abba ya je plss.." "Toh me zan masa?" Ta yi maganar tana tura ɗan ƙaramin bakinta gaba. "Toh ki je ki jiyo mana." Ba dan taso ba haka ta soma takawa cike da takun nan nata na nutsuwa zuwa wajen bayan Lulu ta ɗan rakota. Cikin siririyar muryarta ta yi sallama tana neman waje ta zauna. Tunda ta tunkaro shi ya zuba mata idanu. So yake ya gano shin akwai banbanci tsakaninta da wadda ta tafi yanzun ko kuwa da gasken tsananin kamarsu ce ta ruɗa shi har ya kasa tantance wadda ta ruɗa masa tunani, ta hana shi nutsatstsen bacci, kullum se tunaninta, da hango kyakkyawar fuskarta. "Lallai Allah me halitta." Ya faɗa sanda Didi ta ƙaraso wajen, lokacin kuma da ya gama fahimtar lallai da gasken dole ne ya ruɗe, ya kasa bambance wadda ya fara gani har ta tafi da shi. Wani irin sabon sonta ya tsirga masa tun daga kansa har ƙafa. Ya ɗan lumshe idanunsa kafin ya buɗe yana amsa sallamarta ta kana ya ɗora da "Amincin Allah ya tabbata a gareki ya ke wannan kyakkyawar ma'abociyar kwarjini." "Ameen kaima haka." Didi ta faɗa tana ji kamar ta tashi daga wajen ta ruga zuwa cikin gida, musamman saboda yadda kanta ke ciwo, da kuma yanda take jin wani banbarakwai, tana kuma ji kamar saɓo take aikatawa zaman nata da wani namiji a irin shekarunsu. "Kin wahalar min da zuciya Kyakkyawatah." Ya faɗa a narke kamar wani ƙaramin yaro, har se da hakan ya sanyata saurin ɗaga ido ta kalle shi. Ya sakar mata wani murmushi yana sake langaɓar da kai gefe kamar yaron goye lokaci ɗaya yana furta "Da gaske na ke fa. Na san da yau ta wuce ban yi ido huɗu da fuskarki ba za a iya ganina a gadon asibiti, saboda yanda ko da yaushe zuciyata ke harbawa saboda ƙaunarki.." yanzun ma dai ƙare maganar ya yi a shagwaɓe. Daidai lokacin da wayarsa ta soma ringing kenan. Se ya kalleta a nutse yace bayan ya sakar mata murmushi "1mint pls.." ya yi maganar yana miƙewa. Itama miƙewar ta yi ta soma takawa zuwa inda Lulu take. Haushi da takaici kamar su karta. "Didi me ya faru?" Lulu ta tambaya tana kallan yanda Didin ta haɗe rai kamar wadda aka daka. "Ɗan iska ne!.." Da sauri Lulu ta buɗe ido sosai tace cikin rashin fahimta "Ɗan iska kuma?" Ta yi maganar manyan kyawawan idanunta a waje. "Ehh mana.. Ni ze yi wa shagwaɓa." Didi ta faɗa tana harara kamar Kaseem ɗin na gabanta.. https://chat.whatsapp.com/BClMNPwWybg2n3oRvtemv8 *♡☆A JINI TAKE☆♡* *(IZZATA)* By _*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_ *CHAPTER ONE* Page_15 ___Dariya Lulu ta sheƙe da ita har da sunkuyawa. Se da ta yi me isarta sannan ta ɗago tana kallan Didi tace "Shagwaɓa kuma Didi? Ƙato da shi?" Taɓe baki Didi ta yi sannan tace "Ehh fa, ba kyan gani.." ta ɗan dakata daga nan se kuma ta ɗora da "Ke mu tafi gida, ni jikina ma rawa yake yi tun ɗazu.." "Allah nima haka" Lulu ta faɗa tana riƙe hannun Didin dan komawa gida. Se kuma Didi ta dakata a hankali tace "Amma kamar ba mu kyauta ba koh?" Cikin mamaki Lulu tace "Me muka yi?" "Da zamu tafi mana ba sallama" Shiru Lulu ta ɗan yi na sakanni, se kuma can tace "Toh mu je mu ce masa se da safe." Duk se suka juya suka soma komawa zuwa inda Kaseem ɗin yake, aikuwa daidai lokacin da shima ya gama wayar da yake yi. Se da ya sakar musu murmushi sannan yace yana kallansu su duka "Tabarakallah Masha Allah.." ya faɗa sanda ya sake tabbatar da lallai kamannin nasu sakk da sakk ne wanda shi dai be ga wani banbanci ba. Ba dan hijab ɗin jikinsu kala daban daban ba ne da babu yanda za a yi ya gane Didin tasa. "Lafiya dai koh Gimbiyata?" Ya yi maganar yana kallan Didi. Sosai dariya ta ciyo Lulu se dai ta maza ta yi ta a cikin ranta, a kan laɓɓanta ta furta "Wai gimbiya.." yayin da Didi kuwa waɗannan sunayen da yake ta kiranta da su ita haushi ma suke bata. Daga ganin mutum kawai se ya dinga ce mata Gimbiya. Gashi kuma dama tun ɗazu a tsorace take saboda wannan sabon al'amarin na keɓewa da namiji su yi magana. "Tafiya zamu yi." Ta faɗa cikin sanyin nan nata. Lumshe idanunsa Kaseem ya yi yana jin muryarta ta har cikin zuciyarsa, sannan ya yi murmushi yace "Kin gaji ne?" Da sauri ta jinjina kai. Se ya sake yin murmushin kafin yace "Tohm shi kenan. Bari na tafi amma fa zan dawo. Ki kula min da kanki. Allah kuma ya tsare min ke a ko ina.." Wata irin kunya ce ta lulluɓe Didin, ita har ga Allah kunya yake ta bata, babba da shi ya dinga irin waɗannan maganganun. Se dai kuma haka kawai ta tsinci kanta da yin murmushi da kuma dena jin haushinsa da ta ji a farko. Ita kam Lulu se ta juya kamar ta fashe da dariya a wajen. "Toh" shi ne kaɗai abin da Didi ta iya furtawa. "Good nyt Twinnynmu" ya yi maganar yana kallan Lulu. "Uhmm" Lulu ta faɗa bayan ta juyo tana ƙaƙalo murmushin yaƙe. Daga haka suka juya a tare zuwa cikin gidan. Se ya yi murmushi yana jin yanda zuciyarsa ta yi wani irin sanyi, yau ɗin se yake jinsa kamar yafi kowa dace tunda ya yi tozali da kyakkyawarsa. Kai tsaye ficewa ya yi daga gidan ya hau motarsa ya soma driving cike da farin ciki. Ba ya jin ze iya sake yin ko da kwana 1 ne be sanyata a idanunsa ko ya ji muryarta ba. "Oh my god.." ya faɗa sanda ya tuna be karɓi contact ɗinta ba. "Ya aka yi haka ne? Me ya mantar dani?" Ya yi tambayar kamar akwai wani a gefensa da ze ba shi amsar. Jin shiru ne ya sanya shi lalubo amsar da kansa, ya san tabbas ganinta da ya yi ne ya mantar da shi ma wata number. Aikuwa ya yi babbar mantuwa wanda dole ne ya koma ko dan nemo abin da ze sanya shi dinga jin muryarta ko da yaushe. A compound ɗin gidan ya ajje motarsa kasancewar babu wanda be san shi cikin gidan ba, shi yasa be samu tsaiko ba a lokacin da ze shigo. Dan haka yana gama parking se ya sakko daga motar har lokacin murmushi yaƙi barin fuskarsa ya wuce parlourn Daddy bayan sun yi waya da shi. Da sallama ya shiga cikin parlourn, Daddy na zaune a kan wasu haɗaɗɗun kujeru da ke zaune a can wani gefe cikin ɗakin, waɗanɗa da alama an yi su ne dan hutawa ko kuma karatu. Daddyn na zaune kan kujera yana karanta jarida idanunsa sanye cikin wani glass da ya matuƙar amsar kyakkyawar fuskarsa me kama da ta Bad Man. "Barka da wannan lokaci Daddy" Kaseem ya faɗa sanda ya nemi waje a ƙasan kujerar Daddy ya zauna. Murmushi Daddy ya yi yana ajje jaridar hannunsa sannan ya saka hannu ya sauke glass ɗin fuskarsa kana yace "Barka dai Kaseem. Ka shigo?" "Ehh Daddy.." "Toh barka da zuwa.. Ina ɗan uwan naka?" "Na ɗauka ma zan same shi a nan ɗin ai Daddy. Buh let me call him." Ya yi maganar yana fito da wayarsa dake cikin aljihu. "Nop! let me call him my self." Daddy ya faɗa yana ɗaukar rantststsiyar wayarsa dake a gefensa ya ɗakko number Bad Man ɗin ya kira. Ringing 1_2 ya ɗaga. "Kana ina?" Daddy ya tambaya. Daga can ɓangaren ya ɗora wata hula me kyau a kansa sannan yace "Ina ɗakina." "Amma ka manta maganar da muka yi?" "Ohhh sorry Dad.. Bari na zo." Ya faɗa yana takawa zuwa kan gado ya zauna ya shiga gyara zaman takalminsa. Be daɗe cikin parlourn ba ya fito zuwa sashen Daddyn se zuba ƙamshin daɗɗaɗan turarensa yake yi, tafiyarsa kaɗai abin kallo ce, haka zalika kayan dake jikinsa ma na tashin kai ne. A haka har ya ƙarasa parlourn Daddyn. "Sannu da hutawa.." Bad Man ya faɗa bayan ya zauna a kan kujerar gefen Daddy ya ɗauki ƙafa ɗaya ya ɗorata a kan ɗaya. Wani kallo Daddyn ya watsa masa ba tare da yace komai ba. Se ya ɗan buɗe baki sannan ya saka hannunsa ya sauke hular dake kansa kana yace "Sorry Sir.." ya faɗa yana saukar da ƙafar da ya ɗora a kan ɗayar. Se a lokacin sannan Daddy ya kalli Kaseem yace "Koma kan kujerar." Ya san halin Daddyn ba ƙaunar musu yake yi ba musamman kasancewarsa mutum me zafi dan haka kawai se ya hau kan kujerar kusa da Bad Man ya zauna. Se a lokacin suka gaisa, duk da basu daɗe da yin magana a waya ba. Bayan wajen minti 2 Daddy yace "Amm kai Areef.. ga ɗan uwanka nan In Sha Allah zuwa nan da sati 2 nake so ku soma kasuwancinku na ƙashin kanku. Ba na so kowa ya zauna ƙarƙashina, hakan ba abin tutiya bane. Na fi so dukanku ku ci gashin kanku." Jinjina kai Kaseem ya yi sannan yace "Muna godiya sosai Daddy. Allah ya ƙara girma da arziƙi me amfani." "Ameen ya rabb" Daddy ya yi maganar yana maida dubansa kan Bad da ke danna wayarsa. Duk da ya ji abin da Daddyn ya faɗa se dai shi gaba ɗaya hankalinsa ma na kan Hero da suke magana, yanzu kuma ya ji Daddyn na maganar kasuwanci, hakan na nufin ko da yaushe ze iya fita daga gida ba tare da wani takunkumi ba. "Heyy!" Daddy ya faɗa yana kallan nasa. Kamar kuwa ya san da shi ake, daidai lokacin da ya ajje wayar ya ɗaga kai ya kalli Daddyn kana yace "Hakan ya yi. Duk da dai na so na ɗan ƙara hutawa amma babu damuwa." Ya faɗa cikin er basarwa yana cizon lips ɗinsa na ƙasa lokaci ɗaya wani ƙawataccen murmushi na tashi a kan kyakkyawar fuskarsa. Jinjina kai Daddy ya yi sannan yace "Tohm shi kenan, Allah ya taimaka. Yanzu se ku faɗa min duk wani abu da kuke buƙata, ina so ne a yau na sallameku zan shiga wasu sabgogin ne." .. A ɓangarensu Lulu kuwa lokacin da suka koma cikin ɗakin su Abba basa nan, hakan ne ya sanyasu wucewa nasu ɗakin kawai. Ajiyar zuciya Didi ta sauke sanda ta zauna a gefen gadonsu tana faɗin "Na shiga ukuna." Ta yi maganar tana dafe ƙirji. Da sauri Lulu ta ƙaraso tana faɗin "Me ya faru Didi?" Se kuma ta girgiza kai tace bayan ta ɓata fuska "Ba komai fa. Amma kuma me yasa Abba yace mu je wai? Na ga dai idan mutum ya fara zance ai aure ake masa koh?" Didi ta faɗa tana kallan Lulu. Ɗan ɗage idanu Lulu ta yi kafin tace cike da tsokana "Umm ƙila aurar da Didina ze yi." Duka Didi ta kaiwa Lulun, se ta yi saurin tashi daga wajen tana dariya lokaci ɗaya tana faɗin "Sorry my luv. Da wasa fa nake wallahi." Ta faɗa dan ta ga alamar Didin ta ɗauka da gaske take. "Ni dai zuwa zan yi na maimaita karatu, gobe islamiyya.." Didi ta faɗa tana ƙarasawa wajen jakarta ta ɗauka. Wani irin bugawa zuciyar Lulu ta yi sanda ta tuna da abin da ya faru, ita sam ta manta se yanzu da Didin ta yi maganar islamiyya sannan ta tuna. Se ta nemi waje kawai ta zauna tana lumshe idanunta. Bata ankara ba se ji ta yi Didi ta dafa kafaɗarta a hankali, cikin rarrashi tace "Lulu me ya faru ne wai?" Da sauri ta riƙo hannun Didin sosai sanda farar fuskarta ta ɗan yi ja ta soma faɗin "Didi mutane abin tsoro ne, na tsorata matuƙa. Na rasa yanda zan yi na faɗa miki ko ke ko Ammi. Amma ina tsoron na yi shiru ta je ta cigaba da jan mutane." Cikin rashin fahimta Didi tace "Wai a kan me ki ke magana ne? Wace ce?" "Abida.." Lulu ta faɗa. Daga haka ta shiga labartawa Didi abin da ya faru tun daga farko har ƙarshe. Gaba ɗaya Didin se ta ruɗe, ilahirin jikinta ya ɗauki rawa. Se ta ja Lulun jikinta tana faɗin muryarta na rawa, har idanunta sun kawo ƙwalla "Babu abin da suka miki koh? Ba su miki komai ba koh?" Jinjina kai Lulu ta yi kafin tace "Ehh fa Didi." "Tashi mu je mu faɗawa Ammi." Didi ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa. Da sauri Lulu ta riƙota tana girgiza kai tace "Kin san dai halin Ammi, yanzun nan za ta ɗaga hankalinta har abin ya zo ya dinga damunta. Ki yi shiru kawai tunda dai Allah ya kuɓutar dani.." girgiza kai Didi ta yi tace "A'ah gwara kawai a faɗa mata ɗin." "A'ah Didi, mu bar shi kawai a tsakaninmu se kuma a islamiyya da zan tona mata asiri." Buɗe ido Didi ta yi tace bayan ta girgiza kai "Kin san mene tonon asiri kuwa Lulu? Ai ta riga ta san kin santa, ba za ta nuna halinta a makarantar nan ba. Se dai kawai a yi mata barazana saboda tsaro. Ke idan ma tana tsoron ka da asirinta ya tonu za ki ga ta ja baya da zuwa makarantar, mu kuma daga yau za mu dinga saka mata ido, idan hakan ya yi toh shi kenan, idan kuma be yi ba se mu sanar da wani malamin." "Amma Didi.." lumshe idanunta Didi ta yi tana jinjinawa Lulun kai. Ba dan ta so ba tace "Toh Allah ya ƙara tsarewa." "Ameen." Didi ta faɗa tana tuna yanda tun farko ta kasa aminta da yarinyar, ashe mutuniyar banza ce, shi ne hadda ɗauko ƙazaman ƙafafuwanta ta zo gidansu. Se ta girgiza kai kawai, daidai lokacin da Ammi ta shigo ɗakin "Me ya faru?" Ta tambaya sanda ta gansu kamar masu zaman makoki. Da sauri dukansu suka wanzar da murmushi kan fuskarsu kafin suka ce "Babu komai Ammi." Duk da bata yarda ba, amma se ta bar shi ɗin kawai, a tunaninta may be magana ce a tsakaninsu da basa so ta sani, dan ta san idan da suna so ta sani ɗin su da kansu zasu zo su faɗa mata. ... Kiran wayar Ladi da ya shigo cikin ƙatuwar wayarta Abida ta kalla. ta ja doguwar ajiyar zuciya tana tunanin yanda za ta ɓillowa Ladi, tun farko ta sani ba ta kai mata zancen Lulu ba, da yanzu ita da kanta za ta dinga fakar Lulun tunda itama tana sonta. Se dai kuma tunda Ladin ta ƙyalla ido a kanta ya zama dole ita ta haƙura da ita. A karo na barkatai kiran Ladin ya sake shigowa cikin wayarta, se ta jefar da wayar gefe tana faɗin "Na shiga ukuna.." ta yi maganar tana dafe kanta, ita kam yau ta ga ta kanta. Ba za ta iya ɗaga kiran Ladin ba, dan ko ta ɗaga ma ba ta san me za tace mata ba, saboda ta tabbatar maganar Lulu za ta mata. Se dai kuma ta san shi kansa rashin ɗaga kiran matsala ne, hakan ne ya sanyata janyo wayar ta kasheta gaba ɗaya. Tun ɗazu take kwance a gida ta kasa fita ko nan da can ne, ballantana kuma a yi zancen islamiyya, dan ita dai har yanzu tsoron zuwa take bare ta haɗu da Lulu, dan ita kanta za ta iya zama sheda a kan Lulun ba ta da kirki. Ta riga ta tsara yau ba za ta je makarantar ba, duk yadda ake ciki dai se gobe za ta je, kafin lokacin ta gama tsarawa kanta yadda za ta ɓillowa Lulun har ta yadda da ita ta sake kaita wajen Ladi. Hakan ne ya sanyata gyara kwanciyarta ta soma saƙawa da warwarewa duk a kan Lulun. ___"Duk wanda ba shi da littafin ya fita.." Gwani ya yi maganar lokacin da yake buɗe nasa littafin. Kallan Lulu Didi ta yi ganin tana shirin miƙewa, dama ita haka take so, dan ba ƙauna ma take ya dinga shigo musu aji ba. "Wai dama ba ki zo da shi ba?" Didi ta tambaya ƙasa_ƙasa. Jinjina kai ta yi tana ɓata fuska "Allah kuwa se na faɗawa Ammi wannan rashin kirkin da kike yi." Didi ta faɗa tana ɗauke kai ta maida kanta kan littafin hannunta. Ita dai Lulu burinta kawai ta fice daga ajin. Se kuwa ta saɓi jiki tana wani ciccin magani ita a lallai dole kar ya rainata. Ko kallan sharar da ta kwasota be yi ba, kai ba ma za ka ce ya san ta fita ba. Se dai tana ficewar ya yi gyaran murya sannan ya yi sallama cikin muryar nan tasa da duk lokacin da yake larabci ba za ka yi tunanin idan ka yi masa hausa ze ji ba. Cike da farin ciki Lulu kuwa ta nemi wani aji da babu kowa a ciki ta zauna, dama tana sane taƙi zuwa da littafin dan ya koreta. Se kuwa ta zauna abinta inda ta san har ya gama ba za ta jiyo muryarsa ba. Kafin a tashi Gwani ya bar makarantar zuwa asibiti, dan haka se Malam Ahmad ya shigo ya karɓi ajin. Se a lokacin sannan Lulu ta shigo ajin, tana ƙoƙarin ƙarasawa kusa da Didi ta jiyo muryar Malam Ahmad ɗin na faɗin "Afaaf Muhammad Aji.." se ta dakata sannan ta ɗaga kanta ta kalle shi kana ta amsa da "Na'am.." "Daga ina?" Ya tambaya yana kallanta. Dan tsabar shaƙiyanci da rashin kirki irin na Lulu, se ta ɗan yi shiru a ranta tana tuna sunan da ya kamata ta yi amfani da shi ba tare da ta ambaci sunan Gwani ba, dan se take ji kamar ta manta sunan nasa ma, hakan ne ya sanyata faɗin "Littafi ne ba ni da shi, shi ne ya koreni.." "Waye..?" Ya sake tambaya. Ji ta yi kamar kawai ta yi wucewarta ba tare da ta amsa masa tambayar ba, se dai ba ta yi hakan ba. Amma kenan yana nufin dole dai se ta faɗi sunan kuma ta fara faɗar wata kalmar girmamawar kafin sunan shi. Duk da baya kusa amma ai mutane suna ji. "Amma ya aka yi ke Afrah ki ke da shi?" Malam Ahmad ya katseta da faɗin hakan yana kallan Didi. Se da Didi ta sauke ajiyar zuciya sannan cikin niƙab ɗinta ta furta "Ya mu'allim manta guda ɗaya muka yi a gida." Ɗan numfashi kaɗan ya sauke sannan yace "Shi kenan, je ki zauna." A hankali ta ƙarasa cikin ajin ta nemi waje ta zauna. Didi ko kallanta ba ta yi ba, dan yau ɗin da gaske ta ji haushin abin da Lulun ke yi sosae. "Idan Allah ya kai mu anjima, za a je dubiyar mahaifin Malam Affan kamar yanda muka sanar jiya. Waɗanda za su je se su jirani a harabar makaranta." Malam Ahmad ya faɗa. daga nan be wani daɗe ba ya fita daga ajin. Gaba ɗaya en ajin a harabar makarantar suka haɗu, dan kowannensu na son zuwa gaishe da mahaifin Gwanin ko dan kirkinsa a garesu. Se dai ita kam Lulu kallan Didi da har lokacin ba ta kalleta ba ta yi tace "Bari na je na ɗauki Little mu tafi. Se kun dawo.." da sauri Didi ta kalleta cike da mamakin jin furucinta. "Wai me ke damun Lulun? Anya kuwa kanta ɗaya? Me ye haka take yi kamar wani maƙiyinta ne Gwani? Me yasa ta ɗauki abin da yake mata a matsayin tsana, bayan kullum ita ke janyowa kanta? Fuskarta a haɗe duk da tana cikin niƙab amma Lulu ta fuskanci hakan. Ta kuma sake tabbatar da fushin ne sanda ta soma faɗin "Wai Lulu me ye haka ne? Abin da kike yi kina ganin daidai ne? Mene ne aibu dan kin je kin duba mahaifinsa ko kuwa za a gutsiri naman jikinki ne?" Ta ƙare tana kallan Lulun. "Ba za a gutsiri naman jikina ba. Amma kawai na ɗauki ƙafa na je na duba babansu bayan wulaƙantanin da ya yi ɗazu? Ko ba ma wannan ba, duk tarin wulaƙancin da yake min a cikin makarantar nan ni kuma kamar wadda ba ta da zuciya a ƙirjinta se kawai na je duba wani na shi. Me ye haɗina da shi? Wallahi Allah ya kiyaye. Ni fa Didi in fito miki a mutum wallahi saboda Abba da Ammi nake zaune a makarantar nan, ba dan haka ba da ina da dama da tuni na chanjawa kaina makaranta kuma duk a dalilin wannan mutumin" Ta ƙare maganar tana yamutsa fuskarta da itama take a haɗe alamar zancen da take faɗa tun daga ƙasan zuciyarta suke fitowa kuma tana jin zafinsu. Kallanta kawai Didi take yi tunda ta soma maganar har ta kai ƙarshe cike da mamakin Lulun.. https://chat.whatsapp.com/BClMNPwWybg2n3oRvtemv8 *♡☆A JINI TAKE☆♡* *(IZZATA)* By _*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_ *CHAPTER ONE* Page_16 ___"Ohk good.." Didi ta faɗa tana jinjina kai lokaci ɗaya tana juyawa ta bar Lulun a tsaye. Binta Lulu ta yi da kallo har ta koma inda en ajin nasu suke. Babu daɗewa suka fice daga makarantar da jagorancin malamansu mata da maza. Se a lokacin ta sauke ajiyar zuciya sannan ta kama hannun Little suka fara tafiya. "Masoyiya don Allah ki taho mu je." Fatima Kabeer ta faɗa tana kallan Lulun. Kallanta itama Lulun ta yi kana tace bayan ta ɗauke kai "Aou ai na ɗauka ke ma kin bisu ne." Girgiza kai Fatima ta yi sannan tace "A'ah fa, ke na zo kira." Da sauri tace "Kin ga idan za ki tafi kawai ki tafi, wallahi ba zan je ba." "Shi kenan.. mu tafi kawai." Se suka cigaba da tafiya. Ba su yi nisa ba Lulu ta kalli Fatiman tace "Ke wai kin fasa zuwa ne?" "Ban sani ba!" Ta faɗa tana galla mata harara. Dariya Lulu ta yi kamin tace "Sorry Masoyiya." "Kya ji da shi." Fatima ta faɗa tana sake ɗauke kai. "Wai ina Didi?" Little ya faɗa tana ɗaga kansa ya kalli Lulu. Cikin er basarwa tace "Sun je gaisuwa." Shi Little ɗin ma be fahimci abin da take nufi ba, se Fatima da ta buɗe baki tace tana kallanta "Kee Masoyiya ba fa mutuwa ya yi ba." "Aou toh.." ta faɗa tana buɗe idanu itama kamar da gasken ba ta san ba mutuwa ya yi ba. Se ta ɗora da "Ai da na ga an tarkata kawunanku ne na yi tunanin mutuwa ya yi. Lallae!" Ta ƙare tana ɗan taɓe baki. "Er rainin hankali, da ban san halinki ba da kin gama dani." Se kuma suka yi dariya gaba ɗayansu. Har gida se da Fatima ta kai Lulu sunata hira. A parlour suka taradda Ammi tana karatun Qur'an. Jin sallamarsu ya sanyata kai ƙarshen ayar da take sannan ta rufe, ta ajje shi a gefe, kana ta amsa sallamarta su. "A'ah Fatima!" Ammi ta faɗa tana murmushi. "Na'am Ammi, ina yini?" Fatima ta faɗa sanda ta ke zama. "Lafiya ƙalau, ya karatu?" "Ammi kin san ina Didi ta ke?" Little ya faɗa yana buɗe idanunsa, bayan ya haye kan kujerar da Ammin ke kai. Girgiza kai Ammi ta yi tana ɗan murmushi dan ta san shirmensa ne kawai "Gaisuwa.." ya faɗa yana jinjina kai. Se kuma ta maida dubanta kan su Lulu da ke zaune tace "Gaisuwa kuma? Waye ya rasu?" "A'ah fa Ammi, babu wanda ya rasu. Babansu Gwani Affan ne ba lafiya shi ne aka je duba shi." Ajiyar zuciya Ammi ta sauke sannan tace "Toh Allah ya ƙara afuwa." "Ameen." Fatiman dai ta amsa. Kallan Little Lulu ta yi tace "Little kai min jakar nan ɗaki." Kafin ya kai ga cewa komai Ammi tace "Toh me yasa ku ba ku je ba?" Da sauri Lulu ta yi caraf tace "Ammi kaina ke ciwo sosai. Shi yasa ma Ya mu'allim yace a rakoni gida." "Toh Subhanallahi Allah ya sawwaƙe. Sannu Fatima an gode." Murmushi kawai Fatima ta yi tana ɗan satar kallan Lulu ta maka mata harara. Ita kuwa ta ɗauke kai kamar ba ta san da ita take ba. .. Se dab da maghrib Didi ta shigo gidan. Ammi da Lulu na parlourn a zaune. Lulu na koyawa Little home_work. Ƙarasawa ta yi ta zauna a kan kujera tana faɗin "Ammi na gaji." "Sannunki, ai kin yi ƙoƙari, Allah ya ba da lada. Ita waccan malalaciyar da ciwon kai ya hana zuwa yanzu ai kin ga tana nan zaune ke kin samu lada." "Ciwon kai kuma?" Didi ta faɗa tana kallan Lulu. Da sauri Lulu ta soma kaɗa mata kai tana sake maida fuskarta kalar tausayi a kan ta tausaya mata ka da ta faɗawa Ammi gaskiya. Se kuwa ta ɗauke kai daidai lokacin da Ammi ke faɗin "Ba ki ganta tana wani mashau_mashau ba kamar wadda Asibitin ke kanta gaba ɗaya." "Kai Ammi!." Lulu ta faɗa tana tura baki. "Tashi maza ki yi sallah, ki zo ki sha magani. Idan ba haka ba ranki ya ɓaci. Bana son irin ciwon Didi na ƙin shan magani." Ammi ta faɗa. Se da Didi ta saci kallan Lulu sannan ta soma faɗin "Ammi wallahi ba wani ciwon kai." Ta faɗa dan yau ɗin kamar yanda ta yi alƙawari se ta faɗawa Ammin abin da ta sake yi tunda ba ta jin magana. "Ban gane ba?" Ammi ta faɗa tana kallan Didi. "Cewa ta yi wai ba za ta je ta duba shi ba, tunda ba su da haɗi. Wai dan ɗazun ya koreta daga aji saboda ba ta da littafi, kuma bayan tana sane taƙi tafiya da littafin." Ajiyar zuciya Ammi ta sauke tana maida dubanta kan Lulu da ta yi saurin ɗauke kai tun bayan da didi ta fara magana. "Anya kuwa ba wasu ƙawayen ke hure mata kunne ba?" Ammi ta faɗa tana kallan Didi. "Ammi ba wasu ƙawaye. Fatima ce fa kaɗai ƙawarta ta." "Toh ita Fatiman me ya hanata zuwa?" "Ita fa Fatiman har ta taho za mu tafi, da ta ga Lulun ba za ta je ba, shi ne ta fasa zuwa saboda Lulun ta nuna ta ji haushi." "Shirmen banza kenan.." Ammi ta faɗa ranta a ɓace. Se ta maida dubanta kan Lulu tace "Zo nan!" Ammi ta faɗa har lokacin tana kallanta. Se a lokacin ta ɗaga kanta ta kalli Ammin, duk rashin gaskiya ya gama bayyana a kan fuskarta. A hankali ta taso ta soma takawa zuwa inda Ammin take, a sukwane ta zame ta zauna a ƙasan ƙafar Ammin kanta a ƙasa bayan ta faki idon Ammin ta jefawa Didi harara, itama ta maida mata tana ɗauke kai. Hannu Ammi ta kai ta kamo kunnen Lulu ta ja shi, har se da Lulun ta ɗan saki ƙara tana kai hannunta kan hannun Ammin. "Wato ba kya jin magana koh? Duk irin faɗan da Abbanku ya yi miki ba ki ji ba? Dan kin ga ban saka baki ba a lokacin, wallahi da kin bari na saka baki dukanki zan yi ko kuma na kaiki wajen malamin ya zane min ke da kanshi. Wai me kike taƙama da shi ne Lulu? Me kike ƙoƙarin ɗauka ki azawa kanki? Ke babu wanda ya isa ya sarrafaki kenan bayan iyayenki ko me kike nufi? Shi ba malaminki bane? Be isa ya sakaki ko ya hanaki ba? Kin yi laifi ya hukuntaki ta fatar baki kawai amma a wajenki laifi ya yi. So kike kenan duk abin da kika yi ya zuba miki ido kawai, saboda ke ce malamin shi kuma ɗalibin? Ashe ma tsoronki yake ji. Toh ki buɗe kunnenki da kyau, wallahi daga yau aka sake ce min kin yi wa wani rashin daraja, ba ma shi kaɗai ba zamu gauraya da ke. Kin ji dai na faɗa miki." Ammi ta ƙare maganar tana sakin kunnen nata. Se ta kai hannu ta riƙo kunnen da har ya soma mata zafi, haka kuma ya yi ja kamar wanda aka yi wa wani abun. Se ta ɗaga kai a hankali tace "Ki yi haƙuri Ammi." Ɗauke kai Ammi ta yi kamar ba ta ji ba. Ta san halin Ammi ba kamar Abba take ba, ba ta iya fushi ba, idan tace za ta yi fushi da ke har se kin wahala, dan haka gwara tun wuri ta nemi sulhu, hakan ne ya sanyata tashi gaba ɗayanta ta hau kan kujerar, sannan ta ɗora kanta a kan cinyar Ammin tace "Don Allah Ammi ki yi haƙuri, ba zan ƙara ba." Ta ƙare maganar hawaye na zuba a kan fuskarta. Se da Ammi ta ji saukar zubar hawayen Lulun a jikinta sannan ta dafa kanta tace a hankali "Ka da ki ƙara." Da sauri ta jinjina kai tana ɗagowa sanda farar fuskarta ta gama yin ja sosai. .. Har suka koma ɗaki ba wadda tace da er uwarta ko uffan, kowacce se wani ɗauke kai take ita a lallai dole ita aka yi wa laifi. Se dai duk so suke a cikin nasu ɗaya ta soma yi wa ɗaya magana se a shirya. A haka dai har suka yi magribh ba su kula junansu ba, kowacce na cigaba da basarwa. ... "Amm idan ba damuwa kafin ka tafi ko za ka mun magana da Abba mana." Kaseem ya faɗa yana kallan drivernsu Lulu wanda wani lokacin shi ke kai Abba ya kuma ɗauko shi daga duk inda ya je. "Eyyah, ai ba ya cikin gidan ma gaskiya. Be dawo ba tukunna." "Toh godiya nake. Bari na jira shi." Kaseem ya faɗa yana gyara tsayuwarsa a jikin motarsa. Se da drivern ya zo ze wuce se kuma ya sake katse shi da faɗin "Yi haƙuri don Allah, ko za ka ɗan sanar wa da gidan Kaseem ne, da yake na zo mun yi magana da Abbansu so yau ɗin kuma dai zuwan na Afrah ne.." Murmushi Ado driver ya yi fahimtar abin da Kaseem ke nufi da ya yi. "Toh babu damuwa.. bari na sanar da su." Daga haka ya juya ya koma cikin gidan. A bakin parlourn ya tsaya ya yi sallama. Ammi da ke zaune ta amsa tana faɗin "A'ah ashe ba ka tafi ba." "Wallahi kuwa Hajiya. Na zo tafiya ne se kuma na haɗu da baƙon da kuka yi. Yace min dai sunansa Kaseem kuma ya zo wajen Abban En biyu ne. Toh da na faɗa masa baya nan shi ne yace min ko zan kira masa Afrah.." "Afrah kuma? Ikon Allah." Ammi ta faɗa, dan ita gaba ɗaya tama manta da maganar, ko tuntuɓar su ma ba ta yi ba bayan dawowarsu, dan ta yi tunanin ma za su mata maganar da kansu, se dai tunda su basu mata ba, gwara ita ta yi musu. "Toh shigar da shi ɗakin baƙi.." "Toh Hajiya." Ado driver ya faɗa yana wucewa. Miƙewa Ammi ta yi ta wuce ɗakin Twins. A kan gado ta samesu dukansu suna karatun wani english novel ba wadda ke kallan wani. A nutse ta ƙarasa cikin ɗakin ta nemi waje ta zauna a kan gadon tana kallan en biyun nata. Se ta yi murmushi kawai dan ta gane zaman nasu ba lafiya ba, kowacce haushin er uwarta take ji. "Wajen wa Kaseem ya zo ne?" Duk tare suka ɗaga ido suka kalli Ammin kafin suka kalli junansu. Jin sun yi shiru ne ya sanyata sake faɗin "Tambayarku fa nake." "Ammi wajen Didi fa ya zo." Lulu ta faɗa tana tura baki, ita a lallai dole ba ta so faɗar sunan Didin ba. "Allah ya shirya min ku. Duk ku zo nan." Ammi ta yi maganar duka a tare. Se suka sakko gaba ɗayansu zuwa ƙasa. Kusan a tare suka ɗora kansu a kan cinyar Ammin. Se ta ɗauki duka hannayenta ta ɗora a kan kowacce sannan ta soma faɗin "Shi ne ba ku faɗa min ba? Ba dan na tambaya ba wato shiru za ku min koh?" Se suka girgiza kai a tare. Lulu tace "Ammi ya ɗauka ni ya gani a ranar, shi ne na faɗa masa Didi ce, dan lokacin da ya ganta ma ni ina gidan Mami." "Toh Masha Allah. Tashi ki ɗauko Little ya miki rakiya zuwa ɗakin baƙi ku gaisa." "Ni dai Ammi Allah.." "Allah me..? Je ki idan kin dawo se ki faɗa min idan ya yi miki toh shi kenan. Idan kuma be miki ba se mu bashi haƙuri." Ammi ta faɗa tana murmushi. Dariya Lulu ta yi tana ɗaga kai ta kalli Didi daidai lokacin da ta kulle fuskarta tana faɗin "Ammiiiii.." ta ja ƙarshen sunan tana murmushi itama. "Tashi maza." Ammi ma ta faɗa tana murmushin. Se ta miƙe a hankali ta ƙarasa wardrobe ɗinta ta ɗauko gogaggen hijab ɗinta jalbab ta saka sannan ta kalli Lulu bayan ta marairaice fuska tace "Ki zo ki rakani kin ji?" "Naƙi ɗin." Lulu ta faɗa tana murguɗa baki gani da ɗauke kai. "Pls mana.." "Kin ga, ɗauki Little ya rakaki, idan kin dawo har faɗan naku ma zan shirya.." Ammi ta faɗa tana kallan Didin da ko er shafa powder ma a kan fuskarta be dameta ba. Hakan kuma ba shi da wani muhimmanci dan kuwa ko a yanzun da bata shafa komai a kan fuskarta ba ta fito ta yi kyau abinta. Parlour ta fito ta kalli Little da ke kallan Mbc 3 hankalinsa kwance. Tace sanda ta ƙarasa kusa da shi "Little zo ka rakani." Da sauri ya sakko daga kan kujerar da yake kai yana murmushi yake faɗin "Toh mu tafi.." ya faɗa yana miƙa mata hannunsa. Se kuwa ta riƙe shi ɗin suka fita daga ɗakin zuwa ɗakin baƙin. Cikin sanyayyiyar muryarta ta yi sallama cikin ɗakin. Kaseem ya ɗaga kansa da sauri yana kallanta, be san sanda ya sauke ajiyar zuciya ba a daidai lokacin da ya yi arba da kyakkyawar fuskarta. "Kai!! Dama ba unguwa zamu ba." Little ya faɗa a shagwaɓe. Murmushi Kaseem ya yi yana kallan Little ɗin da ko ba a faɗa ba kamarsa ta gama fallasa cewa ƙaninsu ne. Se ya miƙe ya ƙaraso inda suke ɗin ya riƙo hannun Little yana faɗin "Unguwa zamu je mana." Sakar masa hannu Didi ta yi, se suka koma cikin ɗakin yayin da ita kuma ta rufa musu baya. "Barka da fitowa gimbiya.." "Ina yini?" Ta faɗa dai a nutsen kuma cikin sanyi. "Lafiya ƙalau Alhamdulillah. Kin fito lafiya?" Ya sake tambaya yana kafeta da idanu. "Alhamdulillah.." ta faɗa tana ɗan satar kallan Little da be ce komai ba har lokacin. Se kuma can ta jiyo muryarsa yana faɗin "Ina wuni?" "Lafiya ƙalau Little.. me ye sunanka?" Ya tambaya yana kallansa "Ai ka faɗa." Little ya faɗa yana buɗe ido. "Me fa?" Kaseem ya tambaya dan be gane abin da Little ɗin ke faɗa ba. "Little sunana." "Ohhh! Haka ake kiranka da shi? Nyc name. Me ye sunanka na gaskiya?" "Areef." "Woww.. suna me daɗi..Sunan brother ɗina" Kaseem ya faɗa yana murmushi. "Kai fa?" Little ya tambaya shi ma yana murmushi "Kaseem!" Yamutse fuska Little ya yi kafin yace "Nawa ya fi daɗi.." dariya Kaseem ya yi yana ji yaron na sake burge shi. Se ya saka hannu ya ɗora shi a gefensa sannan yace "Zauna nan mu yi magana da gimbiyata." Ya ƙare yana kallan Didi da ta zauna lokaci ɗaya yana miƙawa Little wayarsa. Se kuwa ya karɓa cikin ƙanƙanin lokaci ya kamo game ya fara yi. "Na san za ki yi mamakin sake ganina yau. Se dai ni a wajena idan kullum za ki amince na dinga zuwa gidan nan se na fi kowa farin ciki. Toh amma na san ko masauki ba a min ba ko da kuwa raɓani ne a yi a wani ɓangaren." Ya ƙare maganar kamar me neman taimako. Se ta ɗaga kai ta kalle shi. Ganin ita yake kalla ya sanyata saurin ɗauke kai. Jin ba tace komai ba ya sanya shi ɗorawa da "Wata babbar mantuwa na yi a gidan nan. Na tafi ba tare da na karɓi abin da ze dinga sakawa kodayaushe na dinga jinki ba. Na tafi ba tare da na karɓi abin da ze sanyani na haƙura da zuwa gidan nan kullum, na samu ko da a sati ne na dinga zuwa sau 3 a lalace kenan." Yanda ya yi maganar ne ya tilasta mata yin ƙaramar dariya. Hakan da ta yi se ya ga tamkar ƙara mata kyau aka yi. Se ya gyara zama yana cigaba da kallanta. "Allah kuwa a lalace mana." "Sau ukun?" Ta faɗa tana buɗe ido. "Tohm shi kenan zan rage. Amma dai yanzu ki bani number ka da Abba ya zo ya sameni yace na fiya naci har na dawo." "Ba ni da waya." "Da gaske?" Ya tambaya still dai yana kallanta. Se ta jinjina kai kawai. Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace "Shi kenan, zan samu mu yi magana da Abba idan ya amince na kawo miki waya se na dinga jin muryarki ta nan, har kuma na samu na ƙarasa isar da saƙon zuciyata." Ya ƙare maganar yana murmushi. Da sauri ta girgiza kai kafin a hankali tace "A'ah Abba ba ze bari ba.." Sosai hakan da tace ya sake birge shi, dan kuwa yanda yake gani emmatan yanzun masu irin shekarunta nawa ne ke riƙe da waya ba tare da hakan ya damesu ba ko ya dami iyayensu ba. "Na san me yasa Abba ze hana.. toh amma kuma yanzu idan kin tuna ai da ni kaɗai za ki dinga waya. Ni kaina ba zan bari ki dinga waya da kowa ba, kuma ba za ki dinga amfani da wayar ba saboda karantunki.. saka miki ido zan yi.." se ta yi murmushi kawai ba tace komai ba. "Didi bacci.." Little ya faɗa yana hamma. Se ta kalle shi sannan ta kalli Kaseem ɗin tace "Bari mu tafi.." "Kai haba tun yanzu?" "Didi bacci.." Little ya sake faɗa yana riƙo hannun Didin, bayan ya sakko daga kan kujerar da Kaseem ke kai. Se ta miƙe kawai tana riƙo hannun shi. Ba dan ya so ba, se dai shi ma baya so ya zaƙe, hakan ne ya sanya shi miƙewa yace "Tohm shi kenan.. Allah ya tashemu lafiya. A gaida min da Twinnynmu.." "Tohm." Didi ta faɗa, se kuma a hankali tace "Ka gaida gida." Lumshe idanunsa ya yi yana jin daɗin abin da ta faɗa ɗin. "Gida ze ji kyakkyawata." Daga haka ta fice daga ɗakin, shi kuma ya bita da kallo har ta fice. Se ya koma ya zauna a kan kujerar yana lumshe idanunsa. Anya kuwa ze iya bari har se Didin ta gama secondary kafin a aura masa ita? Ba dan ba dan ba da yace Abban ya aura masa ita har secondary ɗin ta ƙarasa a cikin gidansa, se dai dan kawai ka da a ce ya zaƙe ne. Tana komawa gidan kai tsaye hayewa kan gado ta yi ta kwanta dan ba ta so kowa ya mata maganar dan wallahi kunya take ji. Ko Lulu sanda ta shigo cikin ɗakin tana toilet, dan haka da ta fito ma se ta ga Didin kwance kan gado kamar me bacci. Ita kuwa Ammi ta fahimci dalilin Didin na yin hakan, dan haka kawai se ta yi murmushi tana ƙyaleta zuwa gobe sa yi maganar har Abba. ... Tun ɗazu ta ke attempting na yi wa Lulu magana, se dai kuma yanda ta ga ta wani haɗe rai, haka zalika ta nuna ma kamar ba ta san da zamanta a wajen ba, ya sa ta maaze. Har dai zuwa sanda aka fita sallah. A daidai sanda Lulun ta ke ƙoƙarin shiga aji saboda mantuwa da ta yi Abida ta tareta da faɗin "Afaaf!" Se ta ɗaga kai ta kalleta da mamakin yanda rashin kunyar ta ya iya barinta ta mata magana. Ɗauke kai ta yi da niyyar barin wajen, se ta sake matsowa da sauri tace "Haba ke kuwa don Allah ki tsaya ki ji abinda zan faɗa miki." Jin abin da ta faɗa ne ya sanya Lulun dakatawa, dan ta ɗauka ko za ta bata haƙuri ne ko kuma ta sanar da ita ta yi nadama. "Lafiya? Ki yi maza ki faɗi abin da za ki faɗa ina da abin yi.." Lulu ta faɗa bayan ta tsaya a wajen. "Amm don Allah ki taimakamin Afaaf, ki taimakawa rayuwata, ki taimakawa shugabarmu da ke matuƙar buƙatarki ki zo na kaiki wajenta ko da zuwa ɗaya ne don girman Allah.." "Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un." Lulu ta maimaita tana kallan Abida cike da maɗaukakin mamakinta. Bata taɓa tunanin maganar da za ta sake mata ba kenan, ashe da gasken ba ta da kunya? Ashe ba ta tsoron Allah da gaske? "Ki kama kanki, ki fita a hanyata. Na ga wa'azi ba ya shiga jikin irinku, saboda haka wallahi zan tona miki asiri kowa ya san wace ce ke. Kin san kuma idan har en makaranta suka sani shi kenan se kowa ya ji a cikin unguwar nan. Shi kenan kuma ta ɓare da ke." "Toh se me? Kin daɗe ba ki tona min asiri ba. Idan ki ka je ki ka faɗa ai za su tambayeki yanda aka yi ki ka sani, ko me za ki faɗa ba yadda za su yi da ke ba. Saboda haka yanzu ma ba se gobe ba ki je ki tona min asirin." "Haka ki ka ce?" Lulu ta faɗa tana murmushi, dan ita sam wannan maganar da Abidar ke faɗa ta san kawai faɗa take yi saboda rasa abin faɗa. Ban da haka a irin wannan abun har se ta tsaya ma tunanin idan ta je faɗa za ta ɓare da ita? "Haka na ce!" Abida ta faɗa itama tana kallan Lulun. "Ohk.. ki tsaya ki yi kallo.." Lulu ta faɗa tana juyawa a fusace, tana tuna yadda Didi ta hanata tona mata asiri tun ranar farko, da ta barta tun a ranar ta sanarwa wani daga cikin malaman ta san da tuni yanzu an daɗe da korar Abidar daga makarantar.. Me son yin payment yanzu kafin mu gama Free pages, ze tura ₦300 ne ta 8124818273, Zahra'u Yusuf Ishaq, Opay. Shedar biya ta 08124818273. https://chat.whatsapp.com/BClMNPwWybg2n3oRvtemv8 *♡☆A JINI TAKE☆♡* *(IZZATA)* By _*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_ *CHAPTER ONE* Page_17 ___Ganin da gasken juyawa Lulun ta yi ya sanya Abida saurin riƙota tana faɗin "Afaaf! Wai kin ɗauka da gaske nake? Wallahi da wasa nake miki. Kawai ina so ne na ga za ki iya abin da ki ka faɗa ɗin? Se kuma na ga ashe za ki iya ɗin?" "Cikani malama. Ashe har yanzu ba ki san wace ce ni ba, ni za ki yi wa gatse?" Lulu ta faɗa fuskarta a haɗe tana kallan hijab ɗinta da Abida ta riƙe. Jin ta ƙi sakinta ne ya sanyata saka hannunta ta fincike hijab ɗinta sannan tace "Dallah can cikanii!!" Daga haka ta juya. Cikin wani irin sauri Abida ta zo har gaban Lulun tace lokacin da fuskarta ta koma kalar tausayi "Don girman Allah ki yi haƙuri, wallahi na tuba fa ba zan ƙara ba, kuma ki saka min ido." "Matsa min hanya." Lulu ta faɗa ba tare da ta kalleta ba. Ganin dai da gasken so take yau ɗin ta tona mata asiri a bainar nasi ya sanyata zubewa a kan gwuiwoyinta sannan tace sanda idanunta suka cika da ƙwallar da ba ta tsoro ba ce, face ta zallar takaicin tsugunawa Lulun, lallai ko me Ladi za ta saka a yi wa Lulu ita me amincewa ce komai muninsa kuwa. Se a lokacin sannan Lulu ta dakata tana huci dan wallahi a yau ɗin ta yi niyyar zuwa wajen wani malamin ne ta sanar da shi abin da ya faru, se dai Abidar kuma ta bata tausayi dan haka ta fasa tafiyar. Kafin tace komai ta sake tsinto muryar Abidar na faɗin "Nima ba dan komai ba ne ya sanya na dage a kan wannan maganar ba, se dan na san ba a yi wa Jakadiyarmu musu, babu wanda ke ƙaunar ja da abin da tace. Toh amma tunda ke kin ƙi yadda, kin kuma nuna ba ki da tsoro, ba ni da damuwa zan je na sanar da ita yanda muka yi da ke, kuma daga yau ba za ki sake jina na zo miki da wannan maganar ba. Ba ma ke kaɗai ba na riga na tuba nima. Ina kuma me sake baki haƙuri.." "Ita ɗin banza! Wace ce ita? Ku dukanku ma su waye ku? Who the hell do u think u are da har kuke ganin ba za a iya muku musu ba?" "Ai na ce ki yi haƙuri.." Abida ta sake faɗa kamar da gasken ta yi nadama. Tsaki Lulu ta ja kawai ta shige daga wajen ta barta a durƙushe. Se a lokacin sannan Abida ta bi Lulu da kallo, haushinta da kuma tattaurar zuciya gami da taurin kai irin nata na ƙara fusatata. "Ki jira haɗuwarku da Ladi.." ta faɗa tana fidda wani huci cike da ɓacin rai. Daga haka ta cigaba da tsugunon tsawon mintuna kamar ba za ta bar wajen ba, se kuma can dai itama ta miƙe ta fita Sallahr rai a ɓace. .. Gaba ɗaya kwanakin yana busy sosai saboda yanda Daddy ya sakasu a gaba a kan fara kasuwancin da za su soma. Sanye cikin gajeren wando da kuma wata hamshaƙiyar farar riga mara hannu, wadda ta gama bayyana halittar ƙaƙƙarfan damtsen farin hannunsa da baƙar suma ke kwance luff luff kamar ba jiki ba, saboda yanda ta ke jere kuma a kintse kamar wadda ya ke saka hannu da kansa ya ke jerata. Numfashi kaɗan ya ke ɗan saukewa kasancewar ya daɗe yana motsa jikin. Baƙar sumar kansa da gashi ke nan ajje tuli kamar ba ya askewa ta ɗan hargitse ta kuma jiƙe da gumin da za ka iya cewa ruwa ya watsa a kan. Se dai da ya ke shi ɗin ba gwanin gumi ba ne a jiki ko a fuska ya sanya jikin nasa gumin kaɗan ne babu yawa kamar wanda ma be yi wani motsa jiki ba. A hankali ya kai hannunsa ya ɗauki wani farin towel da ke ajje wanda yafi kama da sabo gall, ya ɗan buɗa shi sannan ya kai kansa ya shiga tsane gumin da ke cikin kan nasa. A hankali kuma ya koma ya zauna dan ya ɗan sake jin daidai kafin ya faɗa toilet dan yin wanka. Ɗan fesar da iska ya yi daga bakinsa sanda ya tuna nan ba da jimawa ba Daddy kan iya kiransa su ƙarasa magana. Lokaci ɗaya kuma ya tuna da Hero da ke ta kiransa tun ɗazu be ɗaga ba. A hankali ya kai hannunsa inda wayarsa ke ajje, ya jawota yana ɗan lumshe idanunsa, takurar Daddy ta yi yawa, har ya soma ƙosawa da ita. Tun yanzu kuma haƙurinsa na neman ƙarewa a kan rashin samu ya sha ishashshiyar giya. Dan tun lokacin da ya je joint ɗin nan ya sha ta hannun Hero be sake sha ba, couz he thought gaba ɗaya ta ƙasar nan haka take babu daɗi, ga kuma bugarwa da sakawa a dinga yiwa mutum kallan ɗan ƙwaya. Shi ya sa ya dakata se ya samarwa kansa irin wadda ya saba sha sannan ya yi kodimo son ransa. Se dai a dalilin wannan kasunwancin da za su fara ya sa komai ya dakata masa, ga shi kuma yanzu gaba ɗaya gangar jikinsa ta ƙi aminta da kwana biyun da be sha ba, hatta shi kansa jinsa ya ke yi wani daban. Number Hero ya kamo ya danna masa kira kafin ya saka a kunnensa. Tana shiga kuwa Hero ya ɗaga dan dama a ƙage yake da son ganin kiran Bad Man ɗin. "Bad..!!" "Hero." Ya faɗa har lokacin idanunsa a lumshe. "Inata kiranka ba amsa.. Akwai daddaɗan labari.." "Labari?" Bad Man ya faɗa. Dariya Hero ya yi kafin yace "Yeap. maganar harkar nan da na ga ba ta maka daɗi ba, na samo maka the most expensive one, am sure u will enjoy it.." "Really?" Ya faɗa yana ɗan ɗage girarsa gami da buɗe idanunsa. "Offcourse yes!" "Ohk nawa ne price nata?" Bad Man ya faɗa dan sake tabbatar da da gasken me tsadar ce ko kuma dai kawai zuzutawar Hero ɗin ne "Na yi dropping maka message. Check ur DM pls.." "Alright.. Thanks.." "Haba haba, ka da ka sa na ji wani iri mana, da girmanka? Ai ko me na maka girmanka ne my Man.." Murmushin gefen baki Bad Man ya yi wanda ya matuƙar ƙawata fuskarsa kafin ya kai hannu ya ɗan shafa kwantacciyar sumar da ke zaune luff a kan fuskarsa wadda kallo ɗaya za ka mata ka san mamallakinta na kula da ita, dan kuwa ba ta da yawa irin wadda ake askewa ce a kai a kai, hakan ne ya sanya kodayaushe ta ke cikin nutsuwa babu hayaniya. ... "My son!!" Aunt Makiyy ta faɗa tana ƙarasowa cikin ɗakin ta yi hugging nasa cike da kewar ɗan yayarta ta. Ɗan murmushi ya yi kafin ya yi hugging nata back. "Ba dai daga bacci ka tashi ba?" Ɗan yamutse fuska ya yi sannan yace "Nop, na ɗan motsa jiki ne." "Dole ko da yaushe jikinka ya ƙara murɗewa. Kana kallan yanda fatarka take sake yin kyau da sheƙi, gami da sake murjewa kuwa?" Ta yi maganar tana kallan yanda ya yi kyau cikin wasu tsadaddadun ƙananan kaya. "Aunt.." se ta yi murmushi kafin tace "Da gaske fa.." Daidai lokacin da Mom ta shigo ɗakin kenan. Da murmushi kan fuskarta ta ƙaraso tana faɗin "Se yaushe za ku fito ne?" "Yanzu ma kuwa.." Aunt Makiyy ta ƙare maganar tana kallan Bad Man, sannan ta ɗora da "Yau da kaina na shirya maka abinci me daɗi. Hope dai ba fita za ka yi ba?" Hannu ya kai ya ɗan murza goshinsa sannan yace "Eyyah akwai inda zan je buh idan na dawo zan ɓullo.." "Ai kaa ji kuma." Aunt Makiyy ta faɗa tana ɓata fuska. Komawa ya yi ya zauna a kan ƙaton haɗaɗɗen gadonsa sannan ya soma saka takalminsa. Se da ya gama kafin ya miƙe yana gyara zaman hular kansa da ta mugun karɓarsa kafin ya kalli Mom da Aunt Makiyy yace "Zan tafi.." Matsawa kusa da shi Mom ta yi ta gyara masa zaman hular kansa kafin tace "A haka ka fi kyau My boy.." ɗan murmushi kawai ya yi dan ya ga alama Mom ɗin ba dena faɗar sunan nan za ta yi ba, saboda yanda ya gama zama a bakinta. "Wai batun aiki ne?" Mom ta sake tambaya. Ɗaga kafaɗarsa ya yi lokacin da hannunsa ɗaya ke cikin aljihun wandonsa. "A'ah.. zan ɗan ga gari ne.." Murmushi Mom ta yi kafin tace "Ni wannan fice_ficen duk ba sonsu nake yi ba. Ba dan bana so ka sake yin nisa da ni ba, da nace Daddynka ya sama maka aiki a wata ƙasar, saboda nan ɗin akwai 'ya'yan talakawa sosai da za ka dinga hulɗa dasu.." "Gaskiya kam, nima ina bayanki Mom. Amma dai mu yi haƙuri da nan ɗin. Abin da za a kiyaye kawai shi ne haɗa shi da 'ya'yan talakawa, wannan kuma aikinki ne tunda mijinki ne.." Aunt Makiyy ta faɗa tana kallan Mom. Jinjina kai Mom ta shiga yi cike da gamsuwa da zancen Aunt Makiyy ɗin, se can ta kalli Bad Man da ba za ka taɓa cewa ya ji abin da suka faɗa ba. "Ga key nan, idan kun gama hirar se ku kulle min." Ya yi maganar yana nuna key ɗin part ɗin nasa. Daga haka ya soma takawa ze fice "A'ah Son mu je. Me za mu yi anan ɗin ba ka nan?" Aunt Makiyy ta faɗa tana soma takawa, se Mom ma ta biyo bayanta suka fice daga part ɗin. A compound suka yi sallama sannan ya soma takawa zuwa parking space. Daidai yana ƙoƙarin buɗe motarsa dan shi ba ya buƙatar taimakon kowa, Mommah ma ta ƙaraso wajen sanye cikin wata atamfa me shegen kyau da babban mayafi da ya dace da atamfar. Murmushi ta yi tana jin daɗin ganinsa dan ta daɗe ba ta sanya shi a ido ba. Daddy da ke gefenta sanye cikin wata shadda jamfa da wando ya kalli Bad Man da ya ƙaraso wajensu. "Barka da wannan lokaci.." "Barka dai Areef.." suka haɗa baki wajen faɗa, kafin Mommah ta ɗora da "Ina za ka je ne haka?" Se da ya ɗan saci kallan Daddy kafin cikin basarwa yace "Ina za ki je? Lem me drop u.." "A'ah haba, je ka inda za ka ke, ba se ka wahalar da kanka ba driver ze kai ni.." Mommah ta faɗa tana murmushi. Ɗan yamutse fuska ya yi yace bayan ya kai hannunsa ya ɗan shafi gefen kansa "Babu wani takura fa.. Daddy bari na ajjeta.." "Kinga Sa'adatu je ki ya kaiki. Ai hakan ya fi.." Murmushi ta sake yi kafin tace "Tohm shi kenan.. Daddyn Areef bari na je se na dawo.." "Allah ya tsare.." Daddy ya faɗa, kafin ya maida dubansa kan Bad Man yace "Pls daga nan ka da ka wuce ko ina.." Murmushin da be shiryawa zuwansa ba shi ne ya ƙwace masa kafin yace "Ohk.." Daga haka ya shige motar, yayin da Mommah ta shiga wajen me zaman banza kafin ya tada motar. Se a lokacin sannan Daddy ya soma takawa dan komawa ciki cike da nutsuwa gami da kamala a cikin tafiyar tasa. ..."Zo ku zauna nan, tun a ranar ban samu mun yi magana ba se yau.." Abba ya faɗa yana kallan Twins. Babu musu suka nemi waje suka zauna dan ba su san a kan me ma Abban ke magana ba. "Mun yi magana da shi wancan yaron Kaseem. So ban dai gane takamaimai ma a kan wadda yake magana ba. Afrah ce ko kuma Afaaf?" Abba ya faɗa yana kallansu. Da sauri Didi ta yi ƙasa da kanta cike da kunyar Abban, dan ba ta taɓa tsammanin maganar da ze yi ba kenan. "Abba wajen Didi fa ya zo.." Lulu ta faɗa tana satar kallan Didi tana ɗan ƙunshe dariyarta. Ammi da ke lura da Didin itama ta yi murmushi tana ɗauke kai. "Toh ikon Allah.. ke Didi matso nan kusa da ni.." Abba ya faɗa yana yin alama da hannunsa. Cike da kunyar dai ta matso tana sake yin ƙasa da kanta. "Ki nutsu ki faɗa min kin ji? Yaron da ya zo wajenki da gaske yake aure ze yi, saboda haka za ki faɗa min idan ya yi miki zan san yanda za a yi a tsaida magana, idan ya so kuna gama secondary ɗin nan se a saka rana a ɗaura aure. Saboda haka faɗa min kina son shi?" Kunyar da tafi ta ɗazu ce duk ta sake rufe Didi, se kace wadda ke gaban alƙali ƙirjinta har wani harbawa yake yi. "Abba.." shi ne abin da ta faɗa kawai har lokacin kanta a ƙasa. "Assalamu alaikum.." Mami ta yi sallama cikin ɗakin. Dukkansu suka amsa sallamarta ta suna kallan ƙofar. Da gudu Lulu ta miƙe ta faɗa jikinta tana faɗin "Oyoyo Mamina.." Murmushi Mamin ta yi sannan tace "Yawwah daughter. Na same ku lafiya?" "Ehh.." Lulu ta faɗa. Se suka ƙaraso cikin ɗakin, Mami ta nemi waje ta zauna suka gaisa da Abba da kuma Ammi sannan suka ɗan shiga hira kaɗan_kaɗan. Zuwa can Abba ya miƙe saboda lokacin sallah da ya gabato, ya musu sallama ya fice daga ɗakin. Cike da jin daɗi Didi ta miƙe ta tafi ɗakinsu dan dama wannan titsiyen da Abban ya mata gaba ɗaya ta kasa sukuni. Se a lokacin suka ɗan cigaba da hira jefi_jefi da Ammi. Zuwa can wayar Ammi ta shiga ruri, se ta kalli Mamin tace "Bari na amsa kira.." "Toh babu damuwa.." Mami ta faɗa tana murmushi. Se ta miƙe da wayar a hannunta ta shiga ɗaki. Se a lokacin Mami ta kalli Lulu da ke kusa da ita ta maka mata harara sannan tace "Ina wayar da na ba ki?" Buɗe ido Lulu ta yi gami da buɗe baki tana tuna wayar da Mamin ta bata, dan wallahi tun ranar da ta bata ta manta da babinta. Toh aba ce dama da ba ta gabanta. "Wallahi na manta da ita.." ta faɗa tana tura baki. "Shashashar yarinya.." Mami ta faɗa tana ɗan dafe kanta. Se kuma can ta ɗaga kai ta kalli Lulun tace "Kenan ba ku taɓa waya da Kaseem ɗin ba?" Se a lokacin sannan Lulu ta yi murmushi kafin tace "Albishirinki.." cike da farin ciki Mami tace "Goro fari tass. Maza faɗa min kuna ta waya koh?" "Toh ba ni ya gani ba, ashe Didi ya gani ya ɗauka ni ce. Kuma ma ya zo wajen Abba ya kuma zo wajen Didin ma sau biyu.." "Didi kuma?" Mami ta faɗa cike da mamaki. "Ehh.." Lulu ta faɗa da murmushin dai. Zuwa can Mami ta sauke ajiyar zuciya tana jinjina kai kafin tace "Lallai" ta faɗa a kan laɓɓanta tana jinjina kai, kafin ta saki murmushi tana soma tsara yanda komai ze tafi. .... "So nake na yi mata wani abun da har ta mutu ba za ta taɓa mantawa da shi ba, ba kuma tare da ta san ni ce na aikata mata ba. Dan idan dai har ta sani na san ba za ta dawo wajena neman taimako ba. Dan haka zan yi amfani da dabarata na sakata ta ji dole a wajena ne za ta zo ta samu mafita.." Dariya Abida ta kwashe da ita bayan gama sauraron abin da Ladi ta faɗa kafin tace "Ina yinki Jakadiyarmu, Allah ya ƙara miki lafiya da kwanya. Kamar me za a yi mata?" Ɗan murmushi Ladi ta yi tana wani jujjuya kai irin ita shegiyar nan ana fasa mata kai kana tace "Auruwa ne ba na so ta yi, dan idan dai har ta yi aure na san ba za ta taɓa amincewa da buƙatata ba, shi ya sa nake so in yi mata wani abun da za ta kasa auruwa, wanda daga ƙarshe idan ta rasa mafita dole ta dawo wajena" Cike da amincewa da zancen nata Abida ta shiga jinjina kai, dan itama ta daɗe da ƙuluwa da al'amarin Lulu, gwara a yi mata abin da ze tarwatsa wannan ji ji da kan nata da kuma taurin kan da take fama da shi. "Ta ina za a fara kenan?" Abida ta faɗa tana murmushin jin daɗin yanda a wannan karon Ladin ke zama tana shawara da ita, se dai ta san hakan na da nasaba da kasancewar ita ta kawo Lulun. Amma dai koma menene ita hakan ma ya yi mata daɗi. Shiru na tsawon mintuna Ladi ba tace komai ba, se ƙurawa waje ɗaya idanu da ta yi kamar me nazari. Bayan shafewar wasu mintuna ukun Ladi ta saki wani murmushi tana sauke ajiyar zuciya gami da murza hannunta irin komai ya yi ɗin nan, kafin a fili ta furta "Hero!!!" Ta faɗa tana sake jinjina kai gami da sakin wani murmushi.. Me son yin payment yanzu kafin mu gama Free pages, ze tura ₦300 ne ta 8124818273, Zahra'u Yusuf Ishaq, Opay. Shedar biya ta 08124818273. https://chat.whatsapp.com/BClMNPwWybg2n3oRvtemv8 *♡☆A JINI TAKE☆♡* *(IZZATA)* By _*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_ *CHAPTER ONE* Page_18 __"Hero!" Abida ta maimaita sunan tana jinjina kai. Ba ta taɓa jin sunan a bakin Ladi ba, ba kuma ta taɓa ganinsa a cikin gidan nan ba. Dan haka maimaita sunan da ta yi tana jira ne ta ji Ladin ta mata ƙarin bayani a kan Hero ɗin. Kamar kuwa Ladin ta gane abin da take so, se ta yi murmushi kafin ta fara faɗin "Cikin lokaci ƙanƙani kwanyata ta samo min mafita. Ba na buƙatar jigari_jigarin mutum, duk da ko cikin gidan nan ina da yaran da zan iya sakawa su min aiki a kan yarinyar nan. Se dai Hero tantiri ne kuma riƙaƙƙen ɗan duniya na bugawa a jarida. Shi ya dace na saka ya min wannan aikin, na san ze min yadda ya kamata har ma ya ƙara wani abun a kai.." Ladi ta ƙarasa maganar tana miƙewa. Cikin jin daɗi Abida tace "Gaskiya ne, dama irinsa ya kamata a haɗa wannan shegiyar yarinyar me shegen taurin kai da shi, na san ze gyara mata zama.." "Me kyan ma kuwa.." in ji Ladi. ... Tana zaune a gaban Kurfoti da ƙaramar tukunya ke kai tana yin miya, ƙamshi me daɗi gaba ɗaya ya cika gidan, dan kuwa Ummeeyn gwana ce wajen iya sarrafa abinci. "Sannu da aiki.." Abeey da ke kishingiɗe kan dadduma ya faɗa yana murmushi. Itama murmushin ta yi sannan tace "Yawwah.." "Ni dai da ina da hali da na samo miki er aiki ta dinga rage miki wasu ayyukan.." Abeeyn ya sake faɗa. "Uhmm, wacce er aiki kuma? Dukka ayyukan gidan ma nawa suke? Ni da yaron nan ze taimaka ya yi aure ai ka ga na samu er tayin hira nima.." Ummeey ta ƙare maganar tana juyo da kujerar da take kai ta koma tana kallansu Abeey. Kallan Gwani da ke zaune gefensa yana karatun wani littafin addini Abeey ya yi yace "Toh kai ka ji.." Se a lokacin ya ɗaga kansa ya kalli Abeeyn, ya ɗan yi yaƙe sannan yace "Abeey wai ni?" "Ja'iri.. da wa nake nufi idan ba kai ba?" Ummeey ta faɗa tana kallansa. "Ummeey idan aiki ya miki yawa ni me taimaka miki ne fa.." ya faɗa yana kallan Ummeeyn. "Ni babu wani aiki da ya min yawa. Kawai dai ina buƙatar er tayin hira ne.." "Tohm.." ya faɗa kawai. Murmushi Ummeeyn ta yi tana maida dubanta kan Abeey tace "Ya jikin?" "Jiki ya warware Alhamdulillah.. Anjima ma ina so na leƙa wajen ɗaliban can, saboda na kwana biyu ban yi musu karatu ba. Affan kuma kin ga akwai inda yake zuwa, ba ze yiwu ace kodayaushe kuma ba shi da lokacin hutu ba.." "Abeey lokacin hutu kuma? Babu damuwa fa Abeey, ka cigaba da zamanka har zuwa lokacin da za ka warware gaba ɗaya se ka koma karatun." Ya ɗan dakata sannan ya ɗora da "Zan je na musu karatun.." "Allah ya yi maka albarka Affan. Allah ya albarkaci gaba ɗaya rayuwarka. Ya nuna min wata rana da ni da Ummeeynka muka daɗe muna jiranta kafin na bar duniyar nan. Idan hakan ta faru shi kenan ni kuma burina ya cika." Ya riga ya san maganar da Abeeyn ke yi a kan aure ce, dan ba yau ne karo na farko da ya saba yin makamanciyar wannan maganar ba. Se dai da yake shi ɗin ba ma'abocin magana bane ya sa be taɓa tambayar Abeeyn ba, se shi da kansa da ya fahimci aure Abeeyn ke nufi. "Ameen Ameen.." Ummeey ta amsa itama tana murmushi. ... "Mami lafiya kuwa na ga kina ta murmushi?" Jadwa da fitowarta kenan daga cikin ɗaki ta faɗa tana kallan Mamin. "Ke zo ki zauna ki ji min abin da ya faru." Mami ta faɗa tana riƙo hannun Jadwa suka zauna a kan kujera. Dariya Jadwa ta yi kafin tace "Ke dai Mami duk sanda ki ka je gidan Abba se kin dawo da labari.." "Ke dallah can ƙaruwarki ce yanzun ba tawa ba.." "Ƙaruwata kuma Mami? Me ya faru?" Jadwa ta faɗa tana gyara zama. "Ashe Kaseem ba Lulu yake so ba." "Kamar yaya Mami? Toh wa yake so?" "Afrah.." "What? Didi kuma? Ta ya ya?" Ajiyar zuciya Mami ta yi kamin tace "Ke ba wannan ba. Na haƙura ne dama saboda Lulu yake so, amma tunda na san Didi yake so ba zan haƙura ba, zan yi yanda zan yi na sama miki shi. Ke ki ka fi buƙatar shi ba wannan yarinyar me baƙin hali irin na uwarta ba.." "Mami.." Jadwa ta faɗa tana buɗe idanunta. "Ke ban son iya shege. Ba kya son Kaseem ɗin ne?" "A'ah idan zan samu ina so mana.." Jadwan ta faɗa tana tura baki. "Ja'ira.. Ahh toh.." Mami ta faɗa tana murmushi. ... Driving yake yi, babu abin da ke tashi cikin motar se sautin kiɗa me ɗan karen daɗi. Yana driving ɗin yana bin sautin waƙar cike da ƙwarewa. Hero da ke ɓangaren me zaman banza ma yana taya shi bin waƙar, se dai shi lokaci zuwa lokaci ya kan tsaya ya kalli wayarsa. Zuwa can wayarta sa ta shiga ruri daidai lokacin da Bad Man yace "Wannan jahilin ringtone ɗin fa?" Ya faɗa yana yamutse fuska lokaci ɗaya kuma yana jijjiga kansa saboda bin sautin da ke tashi da yake yi. "Kawai dai be yi maka. Right?" "Ƙwarai.." Bad Man ya bashi amsa yana cigaba da driving ɗin. "Hero!!" Shi ne abin da Ladi ta faɗa bayan Hero ɗin ya ɗaga wayar. "Jakadiyar Mata.." Hero ya faɗa yana dariya. "Shegen kaya, da alama yanzu haka kana wani hamshaƙin club ɗin ne koh?" Ta faɗa saboda yanda ta jiyo kiɗa na tashi sosai kamar a club. Se da ya yi dariya sannan yace "Ko kaɗan fa.." "Ah toh ai na san hali ne.." Dariyar ya sake yi sannan yace "Yanzu dai ya ake ciki? Dan na san tunda na ga kiran nan na ki akwai wani abu.." Ajiyar zuciya Ladi ta sauke kafin tace "Don Allah idan ba za ka damu ba ina son ganinka.." "Toh fa. Ganina kuma?" Ya tambaya. Se da ta jinjina kai kamar yana gabanta sannan tace "Ƙwarai kuwa don Allah. Taimakamin za ka yi ne a kan wata matsala da na san za ka iya magance min ita cikin ƙanƙanin lokaci.." "Kina ina?" "Ina gida." Ladi ta faɗa cikin farin ciki. Be ce komai ba ya katse wayar ya juya ya kalli Bad Man yace "Pls Bad ajiye ni anan mana.." Kamar be ji shi ba ya cigaba da bin waƙarsa hankali kwance. Se kuma da aka ɗan wula sannan ya yi parking motarta sa. Hero ya sauka yana faɗin "Zamu yi waya plss." "Ohk.." ya amsa yana jan motar. ... "Na ji daɗin zuwanka Hero. Wannan na ɗaya daga cikin alfarma masu muhimmanci da aka taɓa yi min a rayuwata.." Ladi da ke sanye cikin ƙananan kaya babu ɗan kwali a kanta se tulin gashin doki da ke a kan nata ta faɗa tana kallan Hero. Murmushi ya yi yana gyara zamansa sannan yace "Just tell me me ya faru? Kiran me ki ke min? Kin san dai ban fiye son harkar da babu ƙaruwa a cikinta ba.." ya faɗa yana gyara zaman hular kansa. Ajiyar zuciya Ladi ta sauke kafin tace "Ka da ka damu mutumina. Wannan harka ce ta ƙaruwa irin sosai ɗin nan. Aiki nake so ka min a kan wata yarinya, na san wannan ɗin ba baƙon abu ba ne a wajenka musamman idan za a biyaka." "Uhmm Ladi kenan. Ka da kice min aiki kawai zan yi miki babu wata ƙaruwa a ciki? Manta da batun biyana kuɗi, idan dai har zan ƙaru a tafiyar toh ba na buƙatar ko sisinki. Ke dai kawai ki saka a ranki komai ki ke buƙata kin gama samu.." "Shi ya sa na yi yanda zan yi na nemoka Hero.." "Akwai wata yarinya, ina sonta. Se dai ina so ne na ɗan saita mata zama dan ta nuna min ita ɗin mutuniyar kirki ce. Toh wannan batun na mutuniyar kirki nake so ya fita a kanta. A idanun kowa ta tashi daga me wannan sunan. Ni kuma daga nan ka gama aikinka zan ƙarasa sauran.." wata dariya Hero ya fashe da ita kafin ya soma faɗin "Idan dai har na fahimci abin da ki ke nufi.. so ki ke a lalata rayuwarta, ta kuma zo ta rasa mijin aure, ta rasa kallan mutuncin da mutane ke mata, ta yadda za ta rasa mafita se kawo kanta gare ki?" "Dalilin da ya sa nake ƙaunar aiki da kai kenan mutumina. Akwai ka da kwanya." Ta faɗa tana nuna saitin kanta fuskarta ɗauke da murmushi. Ajiyar zuciya Hero ya sauke sannan yace "Ka da ki damu, har ma abin da ba ki ce ba za a yi miki, tunda dai nima ƙaruwata ce.." "Hero kai ɗin na musamman ne. Allah ya ƙara maka kwanya.." "An daɗe ana faɗa min hakan. Ke dai kawai faɗa min sunanta. Er gidan waye? Ya ya kamanninta su ke? Idan ze samu ma a samar min hotonta. Kwatancen gidansu kuwa ba wahala ze min ba idan dai har na san sunan ubanta.." A yi manage da wannan pls, ba na jin daɗi ne. Da bama zan yi ba, kawai dae dan kar na barku a gantale ne shi ya sa na yi wannan ɗin. https://chat.whatsapp.com/BClMNPwWybg2n3oRvtemv8 *♡☆A JINI TAKE☆♡* *(IZZATA)* By _*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_ *CHAPTER ONE* Page_19 ___"Yanzu abin da za a yi zan haɗaka da yarinyar da ta santa sosai. Ta san gidansu, ta san sunan uban yarinyar, za ta kuma iya samo mana hotonta.." Jinjina kai Hero ya yi kamin yace "Hakan ma ya yi.." ... Sake buɗe idanunta dai ta yi sosai dan sake tabbatar da da gasken Areef ɗin ne ya sauke Mommah a motarsa. Juyawa ta yi da sauri tana faɗin "Mom... Mom kina ina ne wai?" Ta yi maganar ranta a ɓace. "Gani nan. Wannan uban kira haka irin na tashin hankali.." "Toh ai wannan ya fi tashin hankali, kin san abin da na gani yanzu kuwa?" Ta faɗa tana neman waje ta zauna har lokacin fuskarta a haɗe. "A'ah se kin faɗa. Me ki ka gani?" Mom ta yi saurin faɗa tana neman waje ta zauna. "Areef na gani fa ya sauke waccan matar a motarsa.." Cikin rashin fahimta Mom tace "Wace matar kenan?" "Wacce mata ce a cikin gidan nan bayan Sa'a..?" Aunt Makiyy ta faɗa tana kallan Mom ɗin. "Bari mana Makiyy, ki bari mana don Allah.." "Ke wallahi ba wasa nake ba. Ni abin ne ya ɗaure min kai wallahi, kina ina har haka ke faruwa cikin gidan nan? Wace irin sakewa ki ka yi har hakan ke faruwa? Drivernta ya zama ko kuwa me ne?" Jinjina kai Mom ta shiga yi cike da ɓacin rai. Shi Areef ɗin ne ba ɗan goyo ba, ba abun tace za ta masa faɗa ba yanzun nan ya tubure mata ya yi fushi da ita, abin da ba ta so kenan. Se dai koma dai mene ne dole ne ta masa magana tun kafin Mommah ɗin ta sake zaƙewa, duk da dai shi ke biye mata. "Zan san abin yi.." Mom ta faɗa tana soma tafiya. Da sauri Aunt Makiyy ta miƙe tana faɗin "Wane za ki san abin yi? Ai yanzu nake so mu je mu ɗauki mataki, babu wani za a san abin yi.." Komawa Mom ta yi ta zauna ta yi murmushin yaƙe kafin tace "Ke daɗina da ke gaggawa. Halin Areef ne ba ki sani ba? Yanzu muna cewa za mu masa faɗa ko kuma mu ci mata mutunci fushin kanmu ze koma. Saboda haka ki bari kamar yanda na faɗa ɗin zan san abin yi.." "Shi kenan ai. Koma dai me ya faru ki fara tuhumar kanki.." Aunt ɗin ta faɗa tana miƙewa dan ita kam ta fusata ba ƙarya. ... Cikin wata doguwar riga me kyau ta shirya, rigar da ta matuƙar amsarta. Ta ɗauki ƙaramin mayafin rigar ta yi rolling, kasancewar rigar me ɗan faɗi ce ya sanya ta saketa sosai, ta kuma matuƙar yi mata kyau. "Ka ga fa en matan Ammi.." Lulu ta faɗa tana dariya ƙasa_ƙasa. "Allah kuwa ba na so.." Didi ta faɗa tana jefawa Lulun harara. Wata dariyar Lulu ta sake sheƙewa da ita sannan tace "En mata ce mana tunda ki ka fara zance. Dan ma ban ce en matan Kaseem ba.." Juyawa Didi ta yi tana neman abin da za ta iya jifar Didin da shi. Lura da hakan da Lulu ta yi ya sanyata miƙewa da gudu ta fice daga ɗakin tana dariya. Biyota Didin ta yi tana ta ciccin magani, ita kuwa Lulu tana zuwa ta faɗa jikin Ammi tana cigaba da dariya "Tsokanar ce koh?" Ammi ta faɗa tana girgiza kai. "Ammi dukanta ta yi koh?" Little da ke gefen Ammi ya faɗa yana kallan Lulu, se ta juya ta jefa masa harara daidai lokacin da Didi ta fito daga cikin ɗakin "Awwwn Masha Allah.. ka ga en matana" Ammi ta faɗa tana murmushi. Dariya Lulu ta fashe da ita yanzun har da ƙyaƙyatawa, tana cigaba da dariyar kuma tace "Ammi nima fa abin da nace mata kenan take jin haushina. Toh ai gashi nan Ammin ta faɗa miki da kanta.." ta ƙare maganar tana kallan Didi. Tura baki Didi ta yi tana neman waje ta zauna. "Ammi ki ma Lulu magana Allah.." "Ai dama na san tsokanarta ki ke yi ja'ira. Yoh ni ko yau Allah ya kawo miki miji ai aurar da ke zan yi na huta.." "Chaaɓɓ.." Lulu ta faɗa tana jinjina kai lokaci ɗaya tana dena dariyar. Se a lokacin sannan Didi ta yi dariya har da yi mata gwalo. "Tashi ki je Afrah an bar ɗan mutane na jira. Ki tsaya ki nutsu Afrah.. kin san dai Abbanki na dab da yanke hukunci, dan ina me tabbatar miki da cewar idan dai har ki ka amince toh a cikin satin nan za a iya bashi damar turo magabatansa." Ɗan numfashi Didi ta ja ba tare da tace komai ba se miƙewa da ta yi ta ja hannun Little suka fice daga ɗakin jikinta a sanyaye. Sallamar da aka yi a bakin ƙofa ne ya sanya su amsawa dukansu. Da sauri Lulu ta miƙe tana faɗin "Oyoyo Masoyiya.." ta faɗa tana rungumeta. "Yawwah.." Fatima ta faɗa tana ƙarasowa cikin parlourn. Gaisawa suka yi da Ammi. Da yake akwai sabo a tsakaninsu ya sa suka ɗan taɓa hira, daga baya Ammin ta miƙe. Da sauri Fatima tace "Ammi wajenki na zo.." komawa Ammi ta yi ta zauna tana faɗin "Toh ina jin ki.." "Dama gobe Umma ce za ta aike ni, shi ne tace in miki magana se Afaaf ta raka ni.." "Gobe..?" Ammi ta tambaya. "Ehh Ammi.." Ajiyar zuciya Ammi ta sauke kafin tace "Amma gobe ai akwai makaranta, me ze hana ku bari se Alhamis ko Juma'a?" "Ammi ai saƙo ne za a karɓo shi ya sa." Shiru Ammi ta yi na tsawon sakanni sannan tace "Toh shi kenan Allah ya nuna mana.." "Ameen Ammi an gode.." "Kun sanarwa da Ya Sayyadin naku?" Kafin Fatima tace komai Lulu ta yi caraf tace "Ehh Ammi fa mun faɗa masa.." "Toh shi kenan, babu damuwa.." "Mun gode Ammi.." daga haka Ammin ta miƙe ta bar parlourn. Neman waje Lulu ta yi ta zauna, Fatima ta jefa mata harara tace "Ta ya ya ma za ki ce mun faɗa masa? Bayan na yi na yi da ke mu je mu faɗa masa kin ƙi? Da kin bari nace ba mu faɗa ba ai na san Ammi za ta tura Didi ta faɗa masa.." Tsaki Lulu ta ja kafin tace "Ke rabu da shi dallah. Sanin kanki ne dai ba ya karɓar uzuri idan ba daga wajen me yin uzurin ba. Da ki ka je faɗa masa ba har da ni ki ka ce ba? Amma me yace? Wai in zo da kaina. Toh ni a faɗan da Ammi da Abba suka min cewa kawai suka yi na dena rashin ji. Ah toh. Ban faɗa ba idan na dawo ya yankani.." "Amma ba kya tsoron ya sanarwa da Abba?" Fatima ta faɗa tana kallan Lulu. "Ke ba ze faɗa ba dallah. Kema me ye na damun kanki ne wai?" "Masoyiya ka da fa ya dake ki.." "Duka kuma? Aou dama yana duka ne?" Girgiza kai Fatima ta shiga yi kamin tace "A'ah ba ya yi amma dai kar ya sake miki abin da ya saba yi ki ce ya dizga ki.." "Masoyiya wai me ye haɗinku da wannan mutumin ne na ga kina ta wani kare shi? A'ah kin ga faɗa min wallahi ba wanda zan faɗawa.." Lulu ta ƙarashe maganar a hankali tana kuma gyara zama. Duka Fatima ta kai mata a fusace tana faɗin "Ban sani ba.." Dariya Lulu ta yi tana faɗin "Ah toh.. ai yanzu dai kya ƙyale ni na sarara.." "Allah ya shirya min ke Masoyiya.." "Ameen in da gaske ki ke.." Lulu ta faɗa tana yamutse fuska. "Wai kin san mene ne?" Fatima ta faɗa tana gyara zamanta. "A'ah se kin faɗa.." "Abida ce ta zo gidanmu ɗazun.." "Abida kuma?" Lulu ta tambaya da sauri tana kallan Fatiman. Se ta jinjina kai, kafin ta kai ga sake cewa komai Lulu ta sake faɗin "Karki faɗa min da gaske ne? Me ta zo tace miki? Yi maza ki faɗa min plss." Taɓe baki Fatima ta yi kafin tace "Ke ba fa komai. Ba abin da tace min, kawai dai gaisawa muka yi, ban da nan ba komai.." "Ohk toh idan ta kuma zuwa ki faɗa min plss.." "Tsaya.. wai me ya faru ne haka na ga duk kin tsorata? Wani abu?" Girgiza kai Lulu ta yi tana faɗin "Nop babu wani abu fa.." Daga haka suka cigaba da hira. Zuwa can Fatiman ta tafi bayan ta je ta yiwa Ammi sallama. Ba ta daɗe da fita ba Didi ta shigo cikin ɗakin hannun Little ɗauke da wata babbar leda da kaya cike a ciki. Da sauri Lulu ta miƙe tana faɗin "Zo mu gani, me aka baka?" Baya ya yi da ita da sauri yana faɗin "A'ah na wa ne fa.." Tsaki Lulu ta ja kafin tace "Kai ba ci maka zan yi ba, kawai gani zan yi.." Se a lokacin sannan ya miƙa mata ta kama hannunsa suka nemi waje suka zauna. Didi ma neman waje ta yi ta zauna kawai. Buɗe ledar Lulu ta yi ta shiga fito da abubuwan da ke cikinta. Tarin chocolates ne kala kala kamar za su yi magana masu daɗi, aji da kuma tsada. "Awwwn Didina ta girma wallahi. Duk wannan namu ne?" Ta yi maganar tana kallan Didi. Murmushi kawai Didi ta yi tana maida dubanta kan Little da ke faɗin "Hmm Uhmm Jamm! Allah kuwa na wa ne.." Kumatunsa Lulu ta kama ta ja tana faɗin "Duka wannan za ka shanye wai?" "Ehh mana. Ai Yah Kaseem ɗin ne yace na wa ne duka tunda Didi ba ta so.." "Iyee!! Yah Kaseem! Wa ya ɗora maka sunan a bakinka haka raɗau?" Lulu ta faɗa tana riƙe haɓa. "Didi ce.." ya faɗa yana karɓar ledar daga hannun Lulu. Se ta maida dubanta kan Didi daidai lokacin da ya nufi ɗakin Ammi hannunsa ɗauke da ledar. "Didi.." "Kee.." Didi ta faɗa tana murguɗa baki. "Ba shakka.. kin san me? Faɗa min gaskiya Didina.." Lulu ta ƙare maganar tana dawowa kusa da Didi, sannan ta ɗora da faɗin "Ki na sonshi koh?" Shiru Didi ta yi tana ɗan wani juya kai kafin can tace "Na ji ina son hira da shi. Da ze tafi ma na ji ba daɗi.." Tsalle Lulu ta yi kafin ta koma ta zauna a kan kujerar tana faɗin "In faɗawa Ammi kin amince koh? Don Allah don Allah kar ki ce a'ah.." Lulu ta faɗa cikin zaƙuwa. "Tohm.." shi ne abin da Didi ta faɗa tana murmushi. Kawai se Lulu ta rungumeta cikin matuƙar farin ciki. .. "Kema fa kanki kamar na Hero ne yana ja wallahi.." Ladi ta faɗa tana kallan Abida. Murmushi Abida ta yi kafin tace "Wallahi kam irin aikin nan akwai wahala. Amma idan buri ze cika ai babu matsala." "Bayan kin tura hotunan kin goge amma?" Ladi ta tambaya. Shiru ta yi na en wasu sakanni se kuma can ta shiga girgiza kai sannan tace "Gaskiya dai ban goge ba. Amma ai babu damuwa, za ta yi tunanin kawai hoton ne ya birge ni shi ya sa na tura. Kuma ma shi ne dalilin da yasa ban tura wanda ita Afaaf ɗin take ita kaɗai ba. Se na tura wanda suke tare ita da masoyiyarta ta. Kin ga ko da ta gani ba na tunanin wani abun ze zo kanta.." "Hakane kuma" Ladi ta faɗa tana jinjina kai. "Bayan nan kuma na samo mana wani information ɗin.." Abida ta faɗa tana neman waje ta zauna. Da sauri Ladi tace "Yi maza ki sanar min me ya faru?" "Na ji tace gobe akwai inda za su je. Se dai duk abuna ban ji inda za su je ɗin ba." "Aiki me kyau Abida. Maza miƙo min wayata.." ta yi maganar tana nuna mata wayarta da ke ajje a kusa da Abidan. Babu musu ta miƙa mata ta shiga nemo number Hero ta kira shi. "Albishirinka!!" Ladi ta faɗa tana murmushi. "Goro.." shi ma ya maida mata yana murmushi. "Idan kana da lokaci ka ɓillo dan an samu cigaba. Idan kuma ba ka da shi faɗa min kana ina yanzun nan ka ganni a wajen.." "Shegiyar mata.. ba se kin zo ba, ki jira ni zan ƙaraso.." Hero ya faɗa "Toh godiya nake.." .. Kowaccensu cikin hijab ta shirya me kyau. Sun fito a Malaman Addini sun yi kyau abinsu. Se da ta gama ɗaura niƙab ɗinta sannan ta kalli Ammi tace "Ammi mun gama.." "Toh.. gashi nan. Idan ki ka kai se ki taho ki zo ki wuce makaranta tunda dai ke ba ki sanar da ba za ki je ba. Dan haka se ki barsu su su je aiken Umman Fatiman. Allah ya tsare.." Ammi ta faɗa lokaci ɗaya tana miƙawa Didin ledar hannunta. "Ameen ya rabbi Ammi.." suka amsa a tare, sannan suka fito zuwa compound. Drivernsu Lulu ne ya ɗauke su kai tsaye zuwa gidan da Ammi ta aikesu. Babu laifi sun ɗauki mintuna masu ɗan dama a gidan, saboda da farko ma da suka je matar bata nan, se da suka jirata ta dawo suka bata saƙon, sannan suka yi mata sallama suka fito. "Didi toh ki zo kawai mu tafi tare mana. Gobe se mu je makarantar duka.." girgiza kai Didi ta yi tace "A'ah ni kam. Na san Gwani ze shigo yau ɗin nan, kuma ban faɗa masa ba.." Taɓe baki Lulu ta yi sannan tace "Ai shi kenan.." "Toh se kun dawo. Amma fa kar ku saki jiki magribh ta yi muku a waje.." "In Sha Allah Didi.." suka amsa a tare. Har ta fara tafiya se kuma ta juyo tace "Toh Baban na jiranku, ko me za ku jira anan?" "Ahh haba Didi ki hau ya maidaki gida mana. Ta baya zamu ɓilla ne, akwai hanya me sauƙi, anan za mu samu mota ta kaimu unguwar.." "A'ah ni dai na samu abin hawa kawai.." Didi ta faɗa. "Ba komai fa Didi.." "Shi kenan toh. Allah ya tsare.. Se kun dawo" "Ameen.." nan ma suka amsa a tare. Motar Didi ta shige yayin da su kuma suka yi baya kamar yanda suka faɗawa Didin. Tafiya kaɗan ce kuwa ta kaisu titin. Babu daɗewa kuwa suka sami abin hawa suka hau. Da yake gidan na en uwansu Fatima ne ya sanya babu laifi sun ɗan jimawa matar. Se dai kafin gabatowar magribh suka suka soma shirin tafiya. Babu yanda ba ta yi da su a kan su zauna ba su ka ce an ce ka da su kai magribh. Babu yadda ta iya haka suka mata sallama suka tafi. Suna tafiya suna hira abinsu har zuwa sanda suka ƙaraso titi. "Laaa pls Masoyiya zo mu je yau dai na siyi wannan popcorn ɗin. An daɗe ana tallarsa amma ban taɓa ɗanɗana irinsa ba duk sona da popcorn." Lulu ta faɗa tana kallan wani haɗaɗɗen wajen saida gugguru wanda ke kusa da wani hamshaƙin restaurant. "Ai kin ji kuma kwaɗayi. Ni wallahi ma yunwa nake ji. Ki bari kawai mu tafi gida.." "Amma er uwakkun nan tace ki zauna ki ci ki ka ƙi ci?" Taɓe baki Fatima ta yi kafin tace "Abincin na su ne be min ba." Dariya Lulu ta sheƙe da ita tace "Wallahi na bar abin ne kawai a raina saboda er uwakku ce. Ashe ke ma da kanki haka za ki ce. Kai jama'a!" Ta ƙare tana saka hannu a baki ta kare tana cigaba da dariyarta. "Kya ji dai da shi.." Fatima ta faɗa tana yin gaba. "Aou wai nufinki ba za a siya ba?" Lulu ta faɗa tana riƙo hannunta. "Masoyiya wallahi na gaji. Don Allah ki taho mu tafi.." "Kin ga ki ce dai yunwa kawai ki ke ji. Ga restaurant nan ki zo mu shiga na san za a samu wainar shinkafa, ki yi kodimonki da ita kin ga kowa an yi abin da yake so kenan.." Se da ta ambaci wainar shinkafar kuma sannan ta yi murmushi, dan kasancewarta me son wainar shinkafa sosai. Se suka taka zuwa wajen saida popcorn ɗin. Se da ta siya sannan suka shiga restaurant ɗin da ya gaji da haɗuwa. Abin da ya kawo su kawai shi suka yi. Aikuwa cikin sa'a suka samu wainar shinkafar. Ita dai Lulu da yake ba yunwa take ji ba, kuma wainar shinkafa ba ta wani daɗata da ƙasa ba ya sanya ba ta ci komai ba, se kawai ta jira Fatiman ta ci abincin. "Masoyiya wallahi ko ba yunwa nake ji ba na ga abincin nan se na ci.. Chaaɓɓ kin ji daɗi kuwa?" Ta faɗa tana cigaba da cin abincinta. "Ke mu dai ki yi sauri wallahi. Nima na gaji.." "Ehh tunda kin samu abin da ki ke so ba?" Ta faɗa tana watsa mata harara. "Oho dai.. Ai kema kin samu.." Se da ta ci yanda take so sannan ta kora da lemo, kana suka miƙe a tare dan barin wajen. A daidai sanda suka gama fitowa daga inda ya kasance nan ne mutane ke zaune suna cin abinci da sauransu, a daidai lokacin da Lulu ke kallan Fatima suna magana, se kawai ji ta yi kamar ta bugi wani abu, kafin ta gama tantance mene ne se ji ta yi an zagayeta da hannaye guda biyu. A daidai kuma wannan lokacin ne sautin ɗaukar hoto ya daki dodon kunnena "Ƙyaras.." daga haka Hero ya saki Lulu ba tare da ya bari ta kalli fuskarsa ko shi ya kalleta ba ya yi ciki da saurin da cikin sakannin da ba su wuce a ƙirgasu ba ya ɓacewa ganina. Cikin tsananin ɓacin rai, haushi, takaici gami da baƙin ciki ta ɗaga hannunta da niyyar tunkuɗe wanda ta ke tunanin rashin hankali ne ya saka ya zo wucewa ze mata irin wannan bangazar, se dai cikin sakanni ta ji an riƙeta alamar ba da gangan aka yi hakan ba. Kafin kuma ta ɗauki wani mataki se ji ta yi an saketa. Gaba ɗaya jikinta rawa yake yi kamar gangar da ake kaɗawa. Fararan manyan idanunta sun cika fall da ƙwallar baƙin ciki, se dai har wani huci take fitarwa saboda ɓacin rai. A fusace ta juya dan ɗaukar matakin da ya dace tun kafin ma hankalin wasu ya dawo kansu, ballantana a san abin da wani dabban ya yi mata ba. Daidai lokacin da Bad Man da ke sanye cikin wasu tsadaddadun kaya en ubansu ya kalli Hero sanda ya wuce da gudu kamar wanda aka kaɗo, ganin be fahimci dalilinsa na yin hakan ba, ya sanya shi juyawa fuskarsa kamar ko yaushe babu walwala dan dubawa ko wani abin ne ya faru? Se dai yana juyawar ita kuma fusatattun idanunta da ke cike da fushi suka sauka a kansa, kasancewar shi kaɗai ne ta gani a wajen wanda ya ke kusa da su, se waɗanda ke nesa da su. Ta kuma riga ta san wanda ya mata wannan haukan be ci a ce sun samu tazara da yawa ba, dan haka ganin Bad Man kusa da su ya sanyata sake tabbatar da cewa lallai shi ne ɗan iskan da ke ƙoƙarin yi mata akuyanci. Cikin sakannin da basu wuce 3 ba ta ɗaga hannunta ta sauke masa lafiyayyuyan yatsun hannunta guda biyar reras a kan farar hamshaƙiyar fuskarsa.. https://chat.whatsapp.com/BClMNPwWybg2n3oRvtemv8 *♡☆A JINI TAKE☆♡* *(IZZATA)* By _*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_ *CHAPTER ONE* Page_20 ___"Ɗan iska kawai.." ta faɗa fuskarta ɗauke da zallar ɓacin rai, har kuma lokacin ƙwallar da ta taru a idanunta na nan. Kyawawan ianunsa da basu da yalwar girma ya sake ƙanƙancewa yana kallanta cikin yanayin da na kasa fahimtar wane iri ne. Cikin lokaci ƙanƙani ya ɗaga hannunsa a nutse ya shafa kyakkyawar fuskarsa. Kafin ya kai ga yin wani yunƙuri saboda yanda man kansa ya tsotse da wannan al'amarin, so yake ma ya gama tabbatar da da gasken abin da ya faru ya faru. Wace ce ita? Fatima ta yi saurin riƙo Lulu tana faɗin "Zo mu tafi ke.." kafin Lulun tace komai Fatima ta saka hannu ta jata da ƙarfi suka wuce. Daidai lokacin da Hero ya ƙaraso dab da Bad Man yace a hankali "Ka da ka yi wani yunƙuri. Za ka jan yo hankalin mutane.." Hannunsa ya saka ya tunkuɗe Hero, idanunsa sun kaɗa sun yi jajur, har wani huci yake fitarwa, angry face ɗinsa ta sake haɗewa waje ɗaya. Saboda yadda ya tura Hero ɗin da ƙarfin gaske ya sanya shi yin gefe kamar ze kifa, dan Bad Man ɗin ba daga nan ba wajen ƙaƙƙarfan jiki. Da wani irin sauri ya sake yin gaba yana faɗin "Plss Bad. Ka da ka yi haka. Babu wanda ya gani, idan ka yi wani yunƙuri kowa ze san abin da ya faru.." "Heyy leave me. I said leave me.. Me ye ka ke faɗa ne? Waye kai da kake tunanin za ka faɗa min magana na ji? Na ce who are you?" "Ni ba kowa bane Bad. But abin da kake ƙoƙarin yi ne nake ganin kamar be kyautu ba, ace kamar Areef Matawalle da kansa ya tsaya yana sa'insa da er gidan talakawa.." "Er gidan talakawa.. Er gidan ko uban waye ba damuwata bane.." "Don Allah ka zo mu je mu zauna mu yi magana. Ba dan halina ba don Allah.." Hero ya faɗa kamar mutumin arziƙi. Da ƙyar ya samu Bad Man ɗin ya yadda suka koma suka zauna bayan ya tabbatar masa da cewa ko ɓurɓushin en matan be gani ba. "Ka santa ne?" Bad ya tambaya har lokacin a kufule. "Noo ban santa ba. But abin da ta maka ze sanya ni nemota in ɗauki fansa.." "Fansa? Har na yi wannan lalacewar?" Bad ya katse shi da faɗin hakan. Kafin ya ɗora da "Ka nemo min wace ce ita. Ina ne gidan ubanta.. ban san dalilinta na marina ba but zan nuna mata true colour ɗina.." "Amma Bad har yanzu na kasa gane dalilinta na marinka fa? Anya kuwa lafiyarta ƙalau?" Ɗan runtse idanunsa Bad ya yi yana jin kamar lokacin ne en yatsunta suka sauka a kan fuskarsa. Da sauri ya buɗe idanunsa ya saukesu a kan Hero ɗin daidai lokacin da yake shafa fuskarsa yana kuma hasaso irin wulaƙantaccen marin da ze yi wa yarinyar da tafi kama da mara hankali. Jin be ce komai ba ya sanya Hero sake faɗin "Anya kuwa lafiyarta ƙalau? Ko kuma tana ɗaya daga cikin maƙiyanka, shi ya sa ta zaɓi tozartaka a cikin jama'a. Da ka biye mata kuma ka ga kai ta janyowa zubewar mutunci ba kowa ba.." "Hero!!" Ya faɗa a zafafe yana watsa matsa rikitattun idanunsa. Babu shiri ya yi shiru yana sauke ajiyar zuciya "Sorry Bad.. Yanzu dai me kake so a yi?" "Just ka binciko min gidan ubanta.. Wallahi ko waye ubanta ba ze hana ni shiga har cikin gidan, kai har cikin ɗaki zan shiga na bata wulaƙantaccen mari da kuma tarin gargaɗi. Haters??" Ya ƙare a mamakance. Shi har yanzu abin mamaki yake bashi. Ajiyar zuciya Hero ya sauke yana jinjinawa rashin ji irin na Bad Man. Ya riga ya san tunda ya faɗa hakan ze cika ne, ko me kuwa za a yi se ya cika abin da ya faɗa. Lallai yarinyar ta janyowa kanta ruwan dafa kanta. Daga tarkon Ladi ta janyowa kanta na Bad Man. "Shi kenan.. ka bani kwana ɗaya zan bincika maka.." ya faɗa a ransa yana saƙa yanda ze jewa da Ladi maganar nan. Shi har ya ma gama tsara yanda komai ze tafi, tabbas shigowar Bad Man cikin wannan tafiyar shi yafi komai daɗi, shigowarsa ciki za ta ƙarawa abubuwan armashi. Koma yace shigowarsa ce ma za ta gyara komai. ... "Wallahi Allah ya isana.." Lulu ta faɗa tana share ƙwallar da ta ƙi tsayawa a kan fuskarta. "Masoyiya ni fa kina bani tsoro wallahi. Yanzu duk girman mutumin nan, kwarjini da sauran abubuwa ki ka kasa jin kunyar marinsa cikin jama'a? Ba kuma ya rama fa?" Da sauri Lulu ta juya ta kalli Fatima. "Shi be ji kunyar taɓa jikina ba, se ni zan ji kunyar marinsa? Ɗan iskan banza kawai, mugu, azzalumi.." ta sake faɗa tana kuma ɗauke ƙwallar idanunta. "Haka ne kuma.." Fatima ta faɗa. Har suka isa gida Lulu bata dena mita ba, tun Fatima na bata haƙuri har ta gaji ta yi shiru. Se da suka kusa shiga gida sannan Fatiman ta kalleta tace "Amma dai ya kamata ki tsaya ki saita kanki in case kar Ammi ko Didi su fahimci wani abun.." Shiru ta yi kamar ba zata amsa ba. Se kuma can tace "Na ji.." "Yawwah ko kefa.." da ƙyar dai ta tsaya ta nutsu ɗin sannan suka shige cikin gidan. A parlour suka tarar da Little da Didi da dawowarsu kenan daga islamiyya. "Sannunku da dawowa." Didi ta faɗa tana murmushi. "Yawwah Didi.." Fatima ta faɗa, yayin da Lulu ta nemi waje ta zauna a kan kujera. Didi ta kalleta tace "Ke kuma lafiya?" "Ƙishirwa nake ji.." ta faɗa tana turo baki. Jinjina kai Didi ta shiga yi tace "Lallai Lulu kullum taɓararki ƙara gaba take yi, wai ƙishirwa kike ji.." Fatima ba ta daɗe ba ta yi wa Ammi sallama sannan ta wuce gidansu bayan ta yi wa Lulu sallama. ... Cikin takun ƙasaita ta shigo ɗakin, tana tafiya tana yauƙi kamar wata budurwa, hannunta ɗauke da tire da ke ɗauke da wani glass jug da cups ɗinsa a gefe. A hankali ta ƙaraso ta aje a gaban Daddyn sannan ta koma ta zauna tace bayan ta ɗan yi fari "Barka da hutawa Yallaɓai.." Murmushi ya yi yace "Barka dai.. Kina lafiya?" "Lafiya ƙalau nake.." "Toh madallah.." "Bari na zuba maka.." ta yi maganar tana miƙewa ta tsiyaya juice ɗin cikin glass cup ɗin sannan ta miƙa masa. Babu musu ya karɓa daidai lokacin da Mommah ke faɗin "Barka da wannan lokaci.." kamar ba za ta amsa ba, se kuma can tace "Barka.. Yawwah Yallaɓai dama magana ce na zo mu yi a kan ɗana.." Se da Daddy ya ɗan kurɓi juice ɗin sannan yace "Toh ina jin ki.." Kallan Mommah Mom tayi sannan ta maida shi kan Daddy tace "Ai na ga akwai baƙuwar fuska ne.." "Baƙuwar fuska kuma? A ina?" Daddy ya faɗa yana kallan cikin ɗakin. Yamutse fuska Mom ta yi kafin tace "Dole nace baƙuwar fuska mana Yallaɓai, tunda dai magana ce da ta shafi tsakanin iyaye biyu a kan ɗansu.." Se a lokacin ya fuskanci abin da take nufi, se ya girgiza kai cike da takaicin halinta yace "Amma dai kin san ɗa na kowa ne koh?" Se ta girgiza kai da sauri tana faɗin "In ji hausawa ba? Amma ɗa ai na me shi ne.." "Ranka ya daɗe, a huta lafiya.." Mommah ta faɗa tana murmushin yaƙe. Amsa mata Daddy ya yi yana binta da kallo cike da tausayawa har ta fice. Se a lokacin ya dawo da dubansa kan Mom yace "Ki dena wannan abin da kike, ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba na sha yi miki faɗa a kan irin wannan halin, amma kin ƙi dainawa. Se yaushe ne za ki dena?" Ya yi maganar yana kallanta. "Tom.." ta faɗa dan so take kawai a bar maganar, kafin ran Daddyn ya sake ɓaci, yanzun nan ya chanja mata fuska bayan magana take so su yi. "Dama magana ce a kan Areef.." ta faɗa a tausashe. "Ina jinki.." Daddyn ya bata amsa a taƙaice. Se da ta sauke ajiyar zuciya sannan tace "Dama so nake na roƙi alfalmar ko za a samar masa aiki a wata ƙasar na ga yafi sabawa da can ɗin.." Kallanta Daddy ya yi kamar me nazarin wani abu daga fuskarta. Ba tace komai ba ta yi shiru tana jiran ta ji amsar da za ta fito daga bakinsa. Murmushi Daddy ya yi yana girgiza kai yace "Aiki a wata ƙasar, ke ba ma a wata ƙasar ba matsala ce a wajen Areef. Dama ya lafiyar kura bare ta yi zawo? Idan dai har aiki na samar masa, toh ya zame masa dole ya dinga zuwa kodayaushe. Idan kuwa kasuwanci ne babu ruwansa, ze iya ɗora wani a kan wani abun idan ya yi niyya. Ko kuwa kin fi so ya dogara ne da gwamnatin nan tamu? Idan hakan ki ke so shi kenan. Amma dai ki tabbatar kin fara tuntuɓar ɗan naki, dan idan dai har na yanke hukunci ba zan chanja ba.." Numfashi Mom ta ajje kana tace "Ai Yallaɓai ba ina nufin aiki gama gari ba.." "Duk wani aiki sunansa aiki ne.." Daddy ya katseta da faɗin hakan. "Shi kenan.. Zan tuntuɓe shi na ji daga bakinsa.." "Hakan ma ya yi.." Daddy ya faɗa yana kai juice ɗin hannunsa baki ya kurɓa. ... Tare suka fito daga asibitin shi da Abbati kamar ko yaushe, da yake shi ɗin amintaccen Abeey ne ya sa se ya zama kamar shi ne mataimakin Gwani a duk wasu al'amuran da suka shafi rashin lafiyar Abeey ɗin. Abbatin ke ɗauke da ledar maganungunan Abeey haka suka fito titi. Gwani yana cikin favourite shigar nan tasa da ke matuƙar yi masa kyau, wadda kodayaushe ba a iya ganin sumar kansa da ke a rufe, se zahirin kyakkyawar fuskarsa da ke a buɗe, shigar da a lokuta da dama idan mutane suka kalle shi kafin ya yi magana kai tsaye suke kiransa da balarabe, saboda babu wani abu da ya banbanta shi da su. Fari, kyau, shiga da komai da komai irin nasu ne. Kai Gwani fa na daban ne a komai. "A'ah Malam Affan, yau ma dai mun sake haɗuwa.." Abba ya faɗa yana murmushi. Shi ma murmushin ya maida masa yana miƙa masa hannu suka gaisa. Suka gaisa ma da Abbati, sannan Abba yace "Ya me jikin?" "Alhamdulillah.." Gwani ya faɗa cikin nutsuwa. "Madallah.. Allah ya ƙara afuwa.." Abba ya faɗa "Ameen" Gwani da Abbati suka haɗa baki wajen faɗar hakan. "Dama ina so na sake ganin jikin nasa. Se dai yanzu ina sauri ne, akwai inda zan je.. Ka saka min numberka, idan na shirya zan zo na duba jikin Malam.." Abba ya faɗa yana miƙawa Gwani wayarsa. Karɓa ya yi a nutse ya shigar da numbersa sannan ya miƙawa Abban. Daga nan Abba ya yi musu sallama ya shige inda ya zo. "Malam wannan mutumin na da kirki wallahi.." Jinjina kai Gwani ya yi kamin yace "Tabbas.." "Allah ya saka masa da alkhairi, ya ƙara zumunci... ko shi ma dai ɗalibin Malam ne?" Girgiza kai Gwani ya yi daidai sanda suka tare adaidaita yace "A'ah.." ... Allah Allah take kawai ya gama abin da ze yi ya fita ba tare da ya tashi waɗanda suka yi fashi ba. Babu daɗewa ya gama littafin, sannan ya rufe shi. Se kowa ya shiga mayar da littafan cikin jaka ana jiran ya yi addu'a a tashi. Se dai me? Abin da dai ba ta son ji shi ne abin da ya faɗa wato "Wanda duk ya yi fashi ba tare da ya sanar min ba, ya fito.." Kamar kar ta tashi, se kuma ta tuna irin wannan abin da take yi ma fa yana janyo raini. Cikin ikon Allah yau se ya kasance su biyu ne suka yi fashin. Kallanta Didi ta yi sanda ta miƙe a mamakance. Ƙasa_ƙasa tace da Fatima "Dama ba ku faɗa ba?" Girgiza kai Fatima ta yi kunya na kamata se kawai ta yi shiru tana kallan Lulu da ta fita zuwa wajensa. Da ɗayar er ajin tasu ya fara, fuskarsa a tamke, dan shi ba ya son raini, idan yace ba ya son abu kawai ba ya so. Babu daɗewa suka gama da ita, ashe mamansu da kanta ta zo ta sanarwa da Malam Ahmad a kan rashin zuwan nata, saboda Gwani da bata samu ba. Dan haka se ya sallameta, sannan ya maida dubansa kan Lulu yace "Me ya hanaki zuwa?" Shiru ta yi a ranta tana tunanin abin da ya kamata ta faɗa. Se kawai ta yi shiru tana ɗan motsa jikinta. A karo na biyu ya sake maimaita tambayar tasa. Se a wannan karon sannan ta ɗan soma motsa baki fuskarta a haɗe kamar me faɗar wani abun. "Babu dalili kenan?" Ya faɗa ransa a ɗan ɓace. "Toh Ya Sayyadi ƙarya zan yi?" Ta fada tana ɗan yamutse fuska a kuma gajiye. "Hafsa! Karɓo min bulala.." ya faɗa yana kallan Hafsa Abba da ta kasance Monitor. Da mamaki gaba ɗaya en ajin ke kallan Gwanin jin abin da ya faɗa, dan a iya saninsu, tun zuwansa makarantar ba ya taɓa shiga aji da bulala, a gaba ɗaya makaranta ma babu wanda ya taɓa ganin sanda ya yi duka. "Toh Ya mu'allim.." ta faɗa tana miƙewa ta fice daga ajin. Tunda ta ɗaga kai ta kalli Hafsa Abban dan tabbatar da da gasken bulala ya aika a karɓo masa ta kasa saukewa. Dukanta ze yi bayan an tabbatar da cewar ba ya duka? Kenan ita yake so ya wulaƙanta a cikin ajinsu? Shi ya sa ze daketa? Wayyo Allah, me ya sa ta bari hakan ke shirin faruwa? Daga lokacin da ya daketa da bulala kuma ai shi kenan ita kuma tata ta ƙare. Duk wani mutuncinta da en ajin ke gani ta san tsiyayewa ze yi tass ya bi rariya. Kallan banza da yake mata shi kuma se dai ya ƙaru tunda dai har ya daketa. Se ta yi ƙasa da kanta tana jin wata ƙwalla na taho mata, anya kuwa ba za ta bi zugar da take ji zuciyarta na mata ba? Anya kuwa za ta jure zama ya daketa kamar jaka? Ba kuwa za ta bi abin da zuciya ke saƙa mata ba, idan ya so ko hakan ne ze zama sanadiyyar korarta daga makarantar, a koreta ɗin. Ta san dai Abba da Ammi za su mata faɗa, idan ya kama ma su daketa, amma dai ta san ba za su karyata ko su kasheta ba, kuma dai koma mene ne daga ƙarshe dai ta tsira da mutuncinta a wajen Gwanin. ... "Haba Hero. Ya mun gama magana da kai kuma za kace min ka fasa ka samo wata zazzafar hanyar? Ni dai tunda ka fita kuma ban san me za ka ce min ba, dan wallahi jikina ya yi sanyi.." Ladi ta faɗa cikin rashin jin daɗi. "Kin ga zauna anan ki ji.." ya yi maganar yana riƙo hannunta ya zaunar da ita gefensa. "Ki tsaya ki saurare ni. Na gama aikina na farko ba tare da an samu wata matsala ba. Ina shirin gabatar da na biyun na ga wata hanya da idan muka bi ta za ta ɓillar da mu hanya ɗoɗar. Kin san Areef Matawalle? The only son of Alhaji Matawalle..? "Ni kuwa na san shi. Duk da dai ban san shi a gaske ba, amma na san shi a hoto.." "Gud.. Toh abokina ne.." "Abokin ka kuma? How?" Ladi ta tambaya cike da mamaki. Ɗaga kafaɗa ya yi yana taɓe baki kafin yace "Manta da wannan.. Ke dai ba kin gane a kan wanda nake magana ba?" "Ehh na gane.." "Toh garin aikina na farko, akasi ya saka yarinyar ta ɗauka shi ya rungumeta, tsausayi ya sakata sharara masa mari.. Toh tsausayi mana, dan kuwa Bad Man ba ya yafiya, wannan kamar a rubuce yake.." "Kai ka bari Hero. Na shiga uku. Mari kuma? Lallai na sake tabbatar da rashin kunyar yarinyar nan. Amma dai me ze yi mata?" Dariya Hero ya sheƙe da ita kafin yace "Ke ai mu aiki ya zo mana cikin sauƙi.. Ni ɗin nan ba ɗan gidan uban kowa bane." Ya yi maganar yana nuna kansa. Dariya Ladi ta yi tace "Kuma a haka fa se a ɗauka kai ɗin ɗan gidan wani shegen ne.." "Ah toh ya za a yi?" Ya faɗa yana sakin dariyar gefen baki. Se ya ɗora da faɗin "Sunan mahaifin yarinyar can Alhaji Muhammad Aji. Duk da dai ba wani shahararren me kuɗi bane amma dai yana da rufin asirin da ze iya kai ƙara.Ke kin san ko ba shi da hali ma ze ɗauki mataki ne, kin san talakawa da buri. Idan dai har na aikatawa ɗiyarsa wani abun na san ze ɗauki mataki a kaina ni ɗin da ba ni da kowa.." ya ƙare cike da izgili yana wani rausayar da kai. Har se da hakan ya sanya Ladi sheƙewa da dariya. Se dai kafin tace komai ya ɗora da faɗin "Shi kuwa Bad Man ɗan gidan Alhaji Matawalle ne, kina tunanin akwai wanda ze iya shari'a da shi bayan wannan shegen kuɗin da yake da su? Bar shi ma a wani me taurin kan ze iya, amma kina tunanin duk wanda ze yi shari'a da Matawalle ze yi nasara a kansa ne?" Ɗan shiru Ladi ta yi tana nazarin maganar Hero ɗin. Can dai tace "Fito min a mutum. Me ka ke so ka ce?" Gyara zama ya yi sannan ya soma faɗin "Yace ze je har gidansu a kan mari kawai.. ya ki ke gani idan al'amarin da nake ƙoƙarin aikatawa ya koma kansa? Komai ze zo da sauƙi dan na riga na san Bad Man ba ze yi zaman kurkuru ba. Kin ga ba a saka ni a matsala ba ke kuma kin samu cikar burinki.." Murmushi Ladi ta shiga yi cike da gamsuwa da maganar Hero ɗin. Se kuma can tace "Amma kuma idan aka samu matsala aka riƙe abokin naka a gidan yari fa?" Ɗan taɓe baki Hero ya yi sannan yace "Ehh toh.. duk can za ta ƙare musu. Ke dai ba kin samu abin da kike so ba?" Dariya Ladi ta yi sosai, jin yadda Hero ɗin ya zame kansa daga wannan al'amarin cikin ƙanƙanin lokaci. "Lallai Hero ban san da abin da zan biyaka ba. Kai ɗin na daban ne Hero. Duk wanda ya samu kwanya irin taka ya godewa Allah, dan wallahi ba duk kai ba.." Dariya ya yi jin yanda take ta fasa masa kai. "Amma tsaya? Kamar na san halin Alhaji Matawalle fa a kan ra'ayin riƙau, da son gaskiya, har ma da kula da tarbiyyar wasu bare nasa. Kana nufin kace min duk waɗannan halayen nasa da suka janyo masa baƙin jini a wajen wasu mutanen ɗansa guda ɗayan nan yana neman mata?" Shiru Hero ya yi na tsawon sakanni, kafin can yace "Gaskiya dai a'ah.. Amma a wannan karon ze fara..!!" https://chat.whatsapp.com/BClMNPwWybg2n3oRvtemv8 *♡☆A JINI TAKE☆♡* *(IZZATA)* By _*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_ *CHAPTER ONE* Page_21~22 ... Babu daɗewa Hafsa Abba ta shigo ajin hannunta ɗauke da bulalar. Da sauri Lulu ta kalleta ganin da gasken karɓowa ta yi. Babu ɓata lokaci ta ƙarasa ta miƙawa Gwani. Karɓa ya yi, ita kuma ta koma wajenta ta zauna. A hankali ta ɗan kalli Gwanin se ta ga yana ƙoƙarin miƙewa. Cikin rawar murya tace "Ya Sayyadi Fatima fa ta faɗa maka.." ta faɗa dan ganin mafita ta ƙwace mata. Ɗan shiru Gwani ya yi a ransa yana saƙa abin da ya kamata ya yi wa Lulun. Dan kuwa shi kansa ya san ba dukan ze yi ba, saboda ba ya jin har abada ze iya kai hannunsa jikin mace, gani yake kamar wani saɓo ne ze aikata. Be fasa miƙewar ba hannunsa ɗauke da bulalar da tun shigowarsa makarantar be taɓa riƙewa ba yace bayan ya kalleta fuskarsa a ɗaure "Ka da ki sake zuwa makarantar nan, se bayan kwana biyu.." Ya faɗa, daga haka ya fice daga ajin. Duka en ajin bin Lulu suka yi da kallo, masu mata kallan mara tarbiyya na cigaba da yi. Masu mata kallan wadda ba ta jin magana na cigaba da yi. A hankali kuma se kowa ya fara zamewa daga cikin ajin, har kuma lokacin Lulu na tsugune kamar wadda aka dasa. "Ki tashi mu tafi.." Fatima ta faɗa tana riƙota. Se a lokacin ta miƙe jikinta a matuƙar sanyaye se dai fuskarta kamar wadda aka yi wa mutuwa. Ta sauke numfashi tana hararar iska sannan ta kalli cikin ajin. Didi na tsaye tana jiransu su wuce, se dai ba ta ko kalli inda Lulu take ba. Ganin da tayi ta miƙe ne ya sanyata ficewa daga cikin ajin, se suma suka bi bayanta. "Aikin kawai. Ka daɗe ba ka ba ni suspension ɗin ba mana.." Lulu ta faɗa sanda suka fito. Kallanta Fatima ta yi tace "A'ah Masoyiya.. Idan kika je gida me za ki cewa Ammi?" "Uhmm me basirata take yi? Cewa zan yi ba ni da lafiya. Ai ni wallahi ma ya ba ni lasisin da zan ji daɗin rayuwata na kwana biyu ba tare da na gan shi ba" "Hmmm.." Fatima ta faɗa. Bayan shuɗewar wasu sakanni tace "Amma dai Masoyiya ya kamata ki dinga sassautawa. Wannan abin ya yi yawa wallahi. Kuma su Abba za ki janyowa, don Allah ki bari.." "Toh.." Lulu ta faɗa kawai. Har suka je gida Didi ba tace da Lulu komai ba, ta barta ta yi abin da ta ga dama, tunda ba ta jin magana. Itama kuma Lulun se ta share Didin, dan ka da ta mata magana ma ta tuna abin da ya faru, ballantana ma har ta faɗawa Ammi ko Abba. Dan haka se ta mata shiru, idan kwana biyun suka wuce se ta kulata. ... "Ki tashi ki fito mu ci abinci koh?" Ammi ta faɗa tana kallan Lulu da ke cikin blanket ita a lallai dole mara lafiya. "Ammi na ƙoshi. Wallahi bacci nake ji.." Ƙarasowa Ammi ta yi cikin ɗakin zuwa kan gadon ta nemi waje ta zauna. Yaye blanket ɗin ta yi sannan tace "Lafiya kike kuwa? Me ke damunki?" "Ammi zazzaɓi ne a jikina.." ta faɗa tana runtse idanu. "Zazzaɓi a jikinki kuma shi ne ba za ki faɗa min ba? Wannan ai shashanci ne. Tun yaushe kike jinsa?" Ammi ta faɗa tana taɓa goshin Lulun. Jin sanyi ƙalau ya sanyata faɗin "Ikon Allah! Kuma babu zafi jikinki.." "A cikin jikina nake jinsa.." Lulu ta faɗa tana rungumo bargo. Miƙewa Ammi ta yi tace "Kin ga tashi maza ki shirya mu wuce asibiti.." Waro idanu Lulu ta yi tana jin yadda hantar cikinta ta kaɗa. Da sauri tace "Ammi ba se mun je ba don Allah. Zan warke ne wallahi.." Ɓata rai Ammi ta yi tana kallanta tace "Ki tashi nace koh?" "Don Allah Ammi, don Allah kar mu je.." "A wane dalilin zamu ƙi zuwa wai? Za ki tashi mu wuce koh se na zo na saɓa miki duk da baki da lafiya?" Ammi ta faɗa tana yaye blanket ɗin gaba ɗaya. Se a lokacin Lulu ta miƙe lokacin da ƙwalla ta cika idanunta taff. Haka ta miƙe ta buɗe wardrobe ta fito da hijab ta zura. Haka tana ji tana gani Ammi ta sakata a gaba suka fito parlour. "Didi idan Little ya tashi ya ci abinci plss. Zan kai Lulu asibiti ba ta jin daɗi.." Kallan Lulu Didi ta yi, ta galla mata harara tana ɗauke kai. Ita kuwa Lulu se ta langaɓar da kanta kamar da gaske. "Toh Ammi. Allah ya tsare.." Didi ta faɗa tana jinjina kai, hadda ƙwafa, dan so take ƙaryar Lulun ta ƙare a yau ɗin. Bata daɗe zaune a wajen ba bayan fitar su Ammin Abba ya shigo. "Sannu da zuwa Abba.." ta faɗa tana kallan Abban. "Yawwah.. Afrah. Ina Ammin taku?" "Ta fita kai Lulu asibiti." "Toh Subhanallahi.. Me ke damunta?" "Wai zazzaɓi.." "Aou wai ne ma Didi?" Abba ya faɗa yana kallanta. Se ta tura baki tace "Toh Abba haka na ji tace.." "Kenan ba haka ba ne?" Shiru ta yi tana tunanin anya kuwa ta faɗawa Abban? Se dai tana so ne Lulun ta koma kamar kowacce ɗiya dake son janyowa iyayenta yabo, ba kamar yadda take a yanzun ba, da take janyowa iyayensu zagi. "Abba suspension aka bata fa." "Suspension kuma?" Abba ya faɗa cike da mamaki. Jinjina kai ta yi kafin tace "Ehh fa Abba. Laifi ta yi wa Gwani Affan shi ne ya bata. Amma Abba ka yi haƙuri, na faɗa ne ba dan komai ba, se dan ko za a yi haƙuri kawai a cire Lulu daga makarantar nan Abba. Wallahi bata so ne kawai, kuma Abba ka da ta janyo a zageku.." Numfashi Abba ya sauke yana ɗan jujjuya kai. "Wannan yarinya, wannan yarinya.. Kai!!" Abba ya faɗa. Se kuma ya miƙe yace yana kallan Didi "Bari na je na dawo kafin su dawo.." "A dawo lafiya Abba.." ta faɗa tana bin Abban da kallo. A ranta tana fatan Allah ya sa ya yadda ya cire Lulun daga wannan makarantar. Kai tsaye Abba wayarsa ya ɗauka ya kira Gwani, se da ya tabbatar masa yana gida sannan ya katse wayar, bayan ya ji kwatancen gidan. "Ya ya me jikin?" Abba ya faɗa yana kallan Gwani. "Alhamdulillah.." Gwani ya faɗa da murmushi kan fuskarsa, dan ba kaɗan ya ji daɗin zuwan Abban ba. "Fita za ka yi ne?" "Wallahi kuwa.. Amma Abeeyn na ciki.." Gwani ya faɗa. "Toh babu damuwa. Dama zuwa biyu ne ya kawo ni. Na farko na duba jikin Malam, na biyu kuma na ba da haƙuri a kan abin da ya faru.." Kallan Abba Gwani ya yi dan be fahimci abin da yake magana a kai ba. Dan haka da mamaki yace "Haƙuri kuma?" "Ƙwarai kuwa. Wato Malam ka san yaran yanzu ka haifesu ne amma ba ka haifi halinsu ba. Na ji duk abin da yarinyar nan ta yi, shi ya sa na ɗauko jiki na zo na ba ka haƙuri don Allah ka yi haƙuri ka yi haƙuri kamar dai kodayaushe.." Girgiza kai Gwani ya yi yace bayan ya ɗan yi murmushi "Ban so ma ka shiga cikin maganar nan ba. Babu komai In Sha Allah. Allah ya shirya.." "Ameen ya rabbi. Na gode.." "Haba babu komai." "A ƙara haƙuri dai don Allah.." Murmushi kawai Gwani ya ƙara yi, mutuncin Abban na ƙaruwa a cikin idanunsa. Ba Abba ne ya bar gidan ba se da ya shiga ya gaishe da Abeey sannan ya baro gidan. Sosai Abeeyn ma ya ji daɗin zuwan nasa, da ze tafi kuwa ya masa godiya dan lokacin ma ya ji sauƙi Alhamdulillah. .. A kwance yake kan gadon idanunsa a lumshe, kansa a kan hannayensa, yana ɗan bubbuga ƙafarsa dake sauke a ƙasan gado. Ya kasa sukuni tun jiyan, gaba ɗaya hankalinsa na kan Hero ne, yana jira ya zo masa da labari a kan yarinyar nan. Kamar daga sama ya ji wayarsa na ringing. Da ɗan sauri ya buɗe idanunsa da suka ɗan kaɗa saboda ɓacin rai. Ya miƙe zaune sannan ya ɗaga wayar. "Ya?" Ya faɗa tun kafin Hero ɗin yace wani abu. "Komai ya kammalu.." "Kana ina?" Bad ya faɗa bayan ya miƙe tsaye. "Tun yau za ka je ne?" Iska ya ɗan fesar yana lumshe idanunsa da ɗan ɓacin rai yace "Just tell me kana ina?" "Ohk..." Be ajje wayar ba se da Hero ɗin ya sanar da shi inda yake, sannan ya jefata cikin aljihunsa kana ya ɗauki shegiyar hularsa me kyau ya ɗorata a kan kwantacciyar sumar kansa ya fice daga ɗakin. Cikin sa'a Daddy baya nan, hakan ne ya sa be samu tsaiko ba ya fice daga gidan bayan ya kartawa masu tsaron rashin kirki. Dan kuwa idan dai Daddyn na nan shi ne kawai suke aikinsu, dan ma dai shi ɗin idan Daddy na nan be cika fita sosai ba. Idan kuwa Daddyn baya nan, daga ya yi musu magana a kan ze fita za su ƙyale shi ya fice jiki na rawa, ba tare da lura da amanar da Daddyn ya basu ba. "Tafiyar za ta ɗauke mu minute nawa?" Ya faɗa sanda yake kallan Hero. "30 minute.." "Ohk let's go.." ya faɗa yana shirin miƙewa. "But Bad. I think ya kamata ka ɗan sha wani abun, ina me tabbatar maka da rashin kirkin da za ka yi se yafi wanda ka shirya masa.." Wani wulaƙantaccen kallo ya bi cup ɗin da Hero ya miƙo masa da shi sannan yace bayan ya ɗan ja ƙaramin tsaki "Ba na buƙatar komai dan zan yi rashin kirki.. Idan za ka je ka miƙe mu tafi.. Idan kuma ba za ka je ba just give me the address.." "Toh juice fa?" Ya faɗa yana kallansa. Jin be ce komai ba ya sanya shi sake faɗin "Sorry my man. Mu je.." ya faɗa yana miƙewa. Se kuma ya cigaba da faɗin "Ina fatan za ka koyawa yarinyar hankali, yanda ko da wani ne ya sake sakata aiki a kan kowanne game gari ne ba za ta karɓa ba ballantana a kanka.. Mari fa..?" "Heeyy!!!" Bad ya faɗa cikin ɗaga murya yana kamo Hero kamar ze dake shi. "Na bar maganar.." Hero ya faɗa. Komawa Bad ya yi ya zauna jin kansa ya ɗan sara masa. Se ya saka hannu ya ɗauki sassanyan Juice ɗin da Hero ya zuba masa ya kai bakinsa ya shanye tass sannan ya ajje yana ɗan sauke numfashi idanunsa a lumshe. Wajen sakanni talatin sannan ya buɗe idanun nasa, ya kalli Hero yace "Let's go.." ya faɗa yana miƙewa. Babu musu a wannan karon Hero ya yi gaba yana faɗin "Ohk Sir.." Ko da suka isa wajen motar Bad Man, Hero har da saka hannu ya buɗe masa ƙofa, ya shiga ya zauna har lokacin fuskarsa babu fara'a saboda ɓacin ran da ya kwana da shi. Zagayawa Hero ya yi ya tayar da motar kai tsaye suka wuce gidan na Muhammad Aji. ... Se da ya ɗaga kai ya kalli motar lokacin da ta shiga cikin layin. Be kawo komai ba suka cigaba da ciniki da me saida ɗatar. Har ƙofar gidan Hero ya yi parking na motarsa, ya kalli Bad Man yace "Ga gidan nan.." Hero ya faɗa yana nuna gidansu Lulu. Bin gidan ya yi da kallo kamar me nazari, se kuma ya ɗan yi murmushi yace "Well done. Za ka iya tafiya.." Babu musu yace "Allah ya bada sa'a.." ya faɗa yana murmushi. Daga haka ya sauka daga motar, shi ma Bad ɗin ya sauka. Shi Hero se ya fice daga layin yayin da Bad Man ya yi cikin gidan. Hannunsa ya saka ya tura ƙofar gidan. Da wani banzan kallo yake bin gidan da shi. Be dakata ba har se da ya durfafi inda ɗakunan gidan suke. Ƙofar ɗakin a buɗe take, hakan ne ya sanya shi shigewa ciki kawai. A nutse ya soma jefa idanunsa cikin ɗakin ko ze hango fuskarta. Ko ma ba tata ba ya hango ta wata, se dai be hango kowa ba. Hakanne ya sanya shi ɗan soma takawa zuwa cikin ɗakin. Motsin da ya ɗan ji a ɗakin da yake shirin gettawa ne ya dakatar da shi. Se ya dawo da baya ya saka hannunsa ya tura ƙofar ɗakin. Daidai lokacin da ta fito daga toilet. Se ta ɗauki hijab ta saka, dan ta riga da ta saba, ko da tana gida ne ta zauna da hijab. Kamar a mafarki ta ji an turo ƙofar ɗakin. Se ta ɗaga kai da sauri, ta ma ɗauka za ta ga ki Little ne, se dai me? Cikin lokaci ƙanƙani idanunta suka sauka a kan Bad Man dake tsaye bakin ƙofar hannayensa saye cikin aljihu, fuskarsa a ɗinke kamar wanda be taɓa dariya ba. Ba ta san lokacin da ta saki ƙara ba jikinta na ɗaukar rawa. Se ta yi hanyar banɗaki cikin matuƙar tsoro, firgici da rikicewa. Se dai me? Se ta ji toilet ɗin a rufe, ta manta ita da kanta ta cire key ɗin ta ajje shi kan drawer. Kallan wajen ta yi kamar za ta ɗauko, se dai Bad ɗin ya soma matsowa. Se kawai ta fashe da kuka tana kallansa. "Tsoro kuma kike ji yanzu? Wace ce ke? Waye ya aikoki?" Ya yi tambayar duka a lokaci ɗaya kyakykyawar fuskarsa kuma har lokacin a haɗe. "Wace ce ni kuma?" Ta tambayi kanta cikin mamaki. Se dai ba ta san tambayar ta fito fili ba. "Tambayata ki ke? Ina iyayenki suke? So nake na mareki a gabansu na ga abin da za su iya yi.. Ba so kike ki zubar min da mutunci ba? A banza.." ya ƙare yana murmushin takaici. Ita ba ma saurararsa take ba, kawai ta yi shiru ne kamar tana jinsa amma tana kallan gefensa ne tana tsara yanda za ta yi tsalle ta fice daga ɗakin. Se dai har kuma lokacin "Waye shi?" ta ƙi barin ƙwaƙwalwarta. Jin da ya yi ta yi shiru ne ya sanya shi sake kufula, se kawai ya cigaba da takawa, daidai lokacin da ta yi iya ƙoƙarinta wajen yowa gaba dan ficewa daga ɗakin. A fusace ya kai hannunsa kan lallausar fuskarta ya shimfiɗa mata wani gigitaccen mari. Se dai aka samu akasi be sameta ba, saboda yanda ta kauce, hakan ne kuma ya yi sanadiyar faɗuwarta gefe, tsausayi ya sanyata buguwa da gefen drawer. Nan take ta zube a wajen. Ɗan runtse idanunsa ya yi da ƙarfin gaske bayan hannunsa ya taɓa fuskarta. Cikin sakannin da basu wuce 10 ba ya ji gaba ɗaya kansa ya wani irin juyawa, gangar jikinsa ta soma rawa, jiri ya kwashe shi. Kansa ya yi masa wani dumm kamar an ɗora masa wani ƙaton gini a kan nasa. Gaba ɗaya gidan ya shiga juya masa, ya soma ganin sama na komawa ƙasa, se ya riƙo kan nasa da sauri. Se dai duk da haka da wani jiri ya kwashe shi se gashi zube a tsakar ɗakin har kuma lokacin jikinsa be dena wata muguwar karkarwa ba. Daidai lokacin da Habu Driver ya shigo cikin ɗakin. Da sauri ya yi watsi da ledar hannunsa, ya ƙarasa yana kallan Didi da kuma saurayin dake kwance shi ma a tsakar ɗakin. Tsoro duka suka cika shi a lokaci ƙanƙani. Se dai ya riga ya san daga lokacin da ya ga motar ta shigo layin be ci ace har ya aikatawa Didin wani abu ba. Ta yiwu dai wani abun suka shaƙa ya sumar dasu dukansu. Gaba ɗaya saboda tsabar rikicewa se ya rasa ma abin da ze yi. Ya dinga musu fifita zuciyarsa na bugawa. Se daga baya da ya ga Bad bayan en sakanni ya kan ɗan jijjiga da jikinsa sannan ya miƙe ya fita daga ɗakin a guje. Se kuma ya tsaya, tunawa da ya yi idan har ya kira wani daga cikin en unguwar za su iya zargar wani abu. Hakan ne ya sanya shi komawa ciki. Da taimakon Allah ya yi ƙoƙari ya fito dasu ya sakasu cikin mota sannan ya hau ya tasheta ya fice daga gidan. Kai tsaye asibiti ya wuce da gudu, yana addu'ar Allah ya sa basu mutu ba. Yana kuwa zuwa aka karɓesu hannu bibbiyu. Da yake akwai mutane da dama da suka san Bad har sun fara ƙus ƙus cikin asibitin suna faɗawa junansu suma suna munafunci. Shi dai Habu Driver yana tabbatar da an shigar dasu babu ɓata lokaci ya ɗauki waya ya kira Abba. .. Babu daɗewa se ga Abba cikin asibitin hankali tashe. A lokacin ne kuma likita ya nemi ganin wanda ya kawo Bad Man ɗin da kuma Didi. Abba da kansa ya je, dan lokacin ma be fahimci abin da Habu Drivern ke faɗa masa ba. Dan haka ya nemi waje yana jiran cewar doctor. "Wato ita yarinyar buguwa ta yi da wani abu a gefen kanta. Wanda hakan ya janyo mata suma saboda yanda ta bugu ɗin. Shi kuma Yaron bisa rashin sani, ko kuma da saninsa ya sha wasu ƙwayoyi ne da suka yi wa ƙwaƙwalwarsa girma sakamakon rashin saninsu da ta yi. Se ta kasa karɓarsu saboda ba ta saba da su ba. Hakan ne ya janyo masa fita daga hayyacinsa. Se dai cikin ikon Allah ita yarinyar ta riga da ta farfaɗo. Shi kuma yaron gaskiya dai har yanzu be farfaɗo ba, se dai muna saka ran nan da dare ya farka ɗin In Sha Allah.." Ajiyar zuciya Abba ya sauke kafin yace "Na gode.." "Amma yana da kyau ku kira mahaifin yaron.." "Mahaifin yaron kuma? Ka san shi ne?" Abba ya faɗa yana kallan Doctor ɗin. "Yeap. Ɗan gidan Alhaji Matawalle namu ne fa.." "Alhaji Matawalle?" Abba ya faɗa cike da mamaki. "Ƙwarai kuwa.." Likitan ya faɗa cike da tabbarwa. Miƙewa Abba ya yi ya miƙawa Doctorn hannu suka yi musabaha sannan yace "Thank u.." daga haka ya fice daga Office ɗin. ... Har ya isa ƙofar gidan mamaki be bar kansa ba. Ya rasa gane me ya kawo ɗan gidan Alhaji Matawalle gidansa? Me Didi ta masa da yazo wajenta? Mene ne ya sumar dasu gaba ɗayansu kuma lokaci ɗaya? Duk da likitan ya yi masa bayanin dalili amma yana buƙatar wani gamsheshshen bayanin, musamman a kan zuwan Bad ɗin cikin gidansa. Dan kuwa Habu Driver ya faɗa masa yanda komai ya faru, kamar yadda kuma ya zo ya gansu a sume hakan ya faɗawa Abba. Yanzu kuma shi ne ya ba shi shawarar zuwa ya sanarwa da Alhaji Matawallen abin da ya faru, sannan ya masa magana a kan ya jawa ɗansa kunne a kan zuwan da ya masa cikin gida. "Yace ka jira shi a ɗakin can.." Wani ya faɗa yana kallan Abban. Kallansa Abba ya yi da ɗan mamaki, dan be taɓa tunanin a zuwan farko Alhaji Matawallen ze yadda ya gan shi ba, bayan yadda wasu ke faɗar shi yana da jin kai. Se dai tun a karon farko maganganun mutanen na ƙoƙarin tashi a matsayin ƙarya da baƙar hassada. Har ɗakin aka raka shi. Ya nemi waje ya zauna har kuma lokacin hankalinsa gaba ɗaya na kan Didi da aka tabbatar masa da babu abin da ya sameta. Cikin nutsuwa ya yi sallama cikin ɗakin. Abba ya amsa yana kallansa. "Tabbas da gaske shi ɗin ne" Abba ya faɗa a ransa yana sake kallan Alhaji Matawallen. Se dai shi yau ɗin da ya gan shi a fili ma se ya ga kamar yafi kyau a kan yadda yake ganinsa a hoto. "Barka da wannan lokacin.." "Barka dai.." Daddy ya faɗa. Se da suka gaisa dai sannan Abba ya gyara zama yace "Na san za ka yi tunanin ko me ya kawo ni gidanka? Toh dama dai magana ce a kan ɗanka.." Da sauri Daddy ya ɗaga kai ya kalli Abba cike da mamaki yace "Ɗana kuma? Me ya faru da shi?" Ya faɗa hankali a tashe. Babu ɓata lokaci Abba ya shiga zayyana masa abin da ya faru daga farko har ƙarshe. Yana shirin zayyane masa dalilin zuwansa se ya ga ya miƙe yana faɗin "Ya Subhanallahi.. Ya Salam.. Babu dai abin da ya sami ɗiyar taka koh?" Daddy ya tambaya cike da kulawa. "Ehh.." Abba ya faɗa. Komawa Daddy ya yi ya zauna yana mamakin abin da Abban ya faɗa, kenan me ya kai Areef gidansa? Me ya sanya shi ya sha wani abu bayan be taɓa sha ba? Ko dai wasu ne suka ba shi ya sha ba tare da ya sani ba? Yana da tabbaci a kan ɗan nasa, dan kodayaushe cikin masa addu'a yake. Ya kuma san ba ya neman mata, ballantana yace kai tsaye ya je wajen yarinyar ne dan ya haiƙe mata. Toh amma me ya faru kenan? "Mu je asibitin.." Daddy ya faɗa yana sake miƙewa. Miƙewa Abba ya yi yana kallan Daddyn cike da tausayawa. Haka kawai ya ji ya ba shi tausayi a kan yanda mutane ke kallansa. Ashe haka yake da sauƙin kai?. Duk yanda masu kula da Daddyn suka taho dan yin aikinsu, haka Daddyn ya dakatar dasu. Ya hau motar da kansa, sannan Abba ya hau ɓangaren me zaman banza, Daddy ya tashi motar. Tunda suka shiga asibitin se idanu suka koma kan Alhaji Matawalle. Magulmata suka ƙaru, aka cigaba daga inda aka tsaya. Ko bi ta kansu Daddy be yi ba ya sauka daga motar zuwa cikin asibitin. Kai tsaye ɗakin da aka kwantar da Didi ya fara zuwa ya dubata. Tana kwance tana baccinta hankalinta kwance. Daddy ya sauke ajiyar zuciya sannan ya nufi ɗakin da aka kwantar da Bad Man. A hankali ya ƙarasa yana kallan kyakykyawar fuskarsa da ta yi fayau kamar mara lafiya. Cikin tausayawa ya kai hannunsa ya ɗan shafa goshinsa. Wayar Bad ɗin da ya gani ajje ya ɗauka ya ɗan soma dannawa. Kai tsaye message ya fara dubawa, ganin babu wani abun da ze gani ya sanya shi shiga call logs. Number Hero ce ƙarshen wadda aka kira. Hakan ne ya sanya shi kiran layin ya sakata a hands free yana kallan Abba da ya shigo cikin ɗakin. Kira 1 Hero ya ɗaga wayar cike da mamaki. "Bad ba dai har ka dawo gida ba? Ina yarinyar take? Marin nata kawai ka yi kamar yadda kace ko kuwa dai wani abun ya faru? Ka na nufin kace min babu wani abu da ka mata? Ka bani labari don Allah.." Hero ya faɗa hankali a ɗan tashe. Dan ya san in dai har ƙwayar nan ta yi aiki a jikin Bad Man, toh ba ze samu damar da har ze iya kiransa a waya ba, dan ya san yanzu haka ma yana can a wata duniyar in dai ta yi masa aiki. "Ƙitt!!" Daddy ya katse wayar. Se ya nemi waje ya zauna a cikin ɗakin ya kifa kansa a kan hannunsa. Ɗa ne Allah ya ba shi mara jin magana, ba dan haka ba ya daɗe da raba shi da irin waɗannan abokan. Yanzu ga shi suna neman tura shi ga halaka be sani ba, da tsausayi ya faru se dai su janyo masa azabar Allah da kuma kunyar duniya, da ɓacin suna. Yayin da suke gefe babu abin da ya damesu. Ko me ye ribarsu idan sun tunkuɗa wanda ba shi da ra'ayin aikata abu? Ko me za su ji a kan hakan? "Ya ilahy.." Daddy ya faɗa. Neman waje Abba ma ya yi ya zauna. A hankali yace "Lafiya kuwa?" Se a lokacin Daddy ya ɗago idanunsa ya kalli Abba. Ya gyara zamansa sannan ya soma faɗin "Abokai ke neman ɓata masa suna. Se dai ban san dalilin da ya sanya suke so ya aikatawa ɗiyarka abin da suke so ya yi ba. Alfarma nake son nema a wajenka.. Don Allah ina so kafin mu bar cikin asibitin nan ka ba ni erka na aurawa yaron nan nawa.." Da sauri Abba ya kalli Alhaji Matawalle yana ji kamar ya yi wani saɓo ne. Cikin mamaki yace "Aure kuma?". "Ƙwarai kuwa aure. Tunda muka shigo cikin asibitin nan idan ka lura za ka ga idanun mutane a kanmu yake. Zan yi amfani da wannan damar ne wajen maidawa da munafukai fatan tsiyar da suke mana. Ko da an ɗaura auren ba za a fitar a yau ɗin ba. Se idan wani abun ne ya taso sannan za mu fito mu sanarwa da duniya dama can mata da miji ne. Idan dai har ka sanni ka san yanda nake da maƙiya a cikin garin nan waɗanda ban san dalilinsu na ƙina ba. Su nake tsoro, ɓacin sunan yarinyarka da yarona har ma da namu gaba ɗaya nake tsoro. Dan haka ka yadda a ɗaura auren nan a yau ba se gobe ba.." Har Daddy ya gama wannan bayanin Abba be ce komai ba, dan gaba ɗaya kansa ya kulle. Jin da Daddy ya yi Abba ya yi shiru ne ya sanya shi sake faɗin "Na san ɗana yana da rashin ji. Se dai na isa da shi.. na kuma yadda ko da ba ɗana ba ne zan iya bawa 'yata aurensa ba wai kuma dan ka yadda ba. A'ah na shaidi ɗana.. Amma na faɗa maka aibunsa, kuma ina fatan idan ya yi aure matar ta chanja min shi. Tun kuma da na ganka na ji hankalina ya kwanta da kai.. Ina kuma da tabbacin kwatankwacin yanda kake haka ɗiyarka ma za ta kasance.." ya ɗan dakata anan sannan ya sake faɗin "Ka yi duba i zuwa wannan abin alkhairin da muke ƙoƙarin aikatawa. Na farko za mu watsawa maƙiya ƙasa a ido. Na biyu muna ƙoƙarin haɗa aure ne sunnah babba. Sannan na uku daga mu har 'ya'yanmu za mu tsira daga zargin nutane.." Se a lokacin Abba ya sauke ajiyar zuciya sannan yace bayan ya ɗan runtse idanunsa "Allah ya tabbatar da alkhairi. Idan babu alkhairi ya kawo sanadiyyar wargajewar al'amarin kafin lokacin da za a ɗaura auren.." "Ameen.." Daddy ya faɗa cikin jin daɗi. "Se dai wani hanzari ba gudu ba. Ina so a ba ni aron awa ɗaya na je na dawo.." "Awa ɗaya?" Daddy ya tambaya. Kafin kuma Abban ya amsa yace "Shi kenan.. Allah ya dawo da kai lafiya.." "Ameen Ameen.." Abba ya faɗa yana miƙewa ya fice daga ɗakin. Daddy ya ɗan maida dubansa kan Bad cike da tausayawa. ... "Toh na san za ka yi mamakin zuwana bayan na zo ɗazu. Se dai wata muhimmiyar magana ce ta saka ni dawowa, amma ban san yanda za ka ɗauketa ba." Murmushi Abeey ya yi kafin yace "Babu damuwa, kar ka ji komai ka sanar da ni. Na riga na fahimci maganar na da muhimmanci, dan haka kawai ka sanar da ni." Se da Abba ya sauke ajiyar zuciya sannan yace "Mun riga mun san cewa iyayen ɗa namiji su ke zuwa neman aure wajen iyayen 'ya mace. Se dai a wannan karon abin ya chanja, duk da mun san hakan ba laifi bane. Ni da kai na na zo neman iri, neman alfarma, neman haɗa iri da kai Malam. Ina neman alfarmar 'yata ta auri ɗanka Affan.." "Ikon Allah.." Abeey ya faɗa yana jinjina kai. Se kuma ya yi murmushi sannan ya soma faɗin "In dai har mahaifin yarinya ze nemawa 'yarsa auran wani ɗa, toh lallai tabbas wannan ɗa ya cika ɗa, tunda har uba da kansa ya ga dacewar haɗa ɗiyarsa da shi. Dan haka ina me sake godewa Allah da wannan ni'imar da ya min, wannan ma kaɗai ya isa ya nuna min hankalin Affan ko kuma wasu abubuwan nasa ne suka birgeka har ka ji kana sha'awar haɗa alaƙa da shi. Saboda haka ka kwantar da hankalinka, In Sha Allah wannan ɗin duk ba me wuya bane. Ya ya sunan yarinyar taka?" Cikin matuƙar jin daɗi Abba yace "Afaaf.. Ɗalibar shi Malam Affan ce.." "Ikon Allah. Masha Allah, Masha Allah.. gaskiya na ji daɗin wannan al'amari.. Hakan kuma yana nuni da komai ze zo mana cikin sauƙi. Allah ya tabbatar mana da alkhairinsa.." "Ameen Ameen. Na gode sosai Malam, Allah ya saka da alkhairi.. Se dai kuma na zo da wata magana ne Malam.." "Toh ina jinka.." Gyara zama Abba ya yi yana tunanin ta inda ze fara wannan maganar. Se dai kawai ya daure ya soma faɗin "Wato Malam ina me roƙo da neman alfarmar ɗaura auran a yau ɗin nan idan babu damuwa. Da yake ita yarinyar tana da er uwar tagwaitaka, se auranta ya tashi itama a yau ɗin saboda wani dalili. Hakan ne ya sanya ni tunanin na nemawa er uwarta alfarmar auran Malam Affan saboda ba tun yau ba hankalin yaron ke burge ni Malam. Dan haka nace bari na zo da ƙoƙon barata ko za ka amince ka yadda yau ɗin a haɗa auransu gaba ɗaya.." Shiru Abeey ya yi na tsawon sakanni yana nazarin maganar da Abban ya faɗa. Se can ya sauke Numfashi kafin yace "A yau yau ɗin za a ɗaura auran ita er uwarta ta?" "Ehh Malam. Nan da anjima kaɗan.." "Shi kenan.. Amma bari na fara sanarwa da shi yaron.." "Toh.." Abba ya faɗa a sanyaye dan yana tunanin idan har Gwani ya ji wadda Abeeyn ze aura masa ba lallai ne ya amince ba. Dan babu wanda ze so aurarwa 'ya'yansa uwa wadda ba ta gari ba. Se dai ya yi hakan ne da zuciya me kyau, yana fatan idan har Gwani ya auri Lulu ya chanjata da ikon Allah. Ya kuma yadda ze aurawa ɗan gidan Matawalle Didi ne saboda itama ta chanja shi, duk da be san yana shan wani abu ba, kamar yadda Daddy ma da kansa be san yana sha ba. Se dai ya fahimci wasu daga cikin halayen nasa. Ya kuma yadda da Didin ɗari bisa ɗari, ya san da yaddar Allah za ta chanja yaron shi ma. "Ka da fa ka damu. Affan ba ze taɓa cewa a'ah ba. Kawai dai dan na fita haƙƙinsa ne, da kuma na mahaifiyarsa.." Abeey ya faɗa yana kallan Abba da jikinsa ya yi sanyi. "Toh godiya nake.." Kai tsaye Abeey shigewa ya yi zuwa cikin gidan. Ummeey da ke zaune a ɗaki ya kalla bayan ta amsa sallamar da ya yi. "A'ah Malam sannu da dawowa.." "Yawwah.." Abeey ya faɗa yana neman waje ya zauna. Miƙewa Ummeey ta yi da nufin kawo masa ruwa, ya yi saurin katseta da faɗin "Dawo ki zauna. Magana zamu yi.." "Toh.." ta faɗa tana komawa ta zauna. Wayarsa Abeey ya ɗakko daga aljihu, ya kamo number Gwani ya kira. Babu jimawa kuwa ya ɗaga. Da ɗan murmushin da idan ka ga ya yi za ka iya tunanin na yaƙe ne, se dai ba na yaƙen bane, haka yake a halittarsa, dan shi ɗin ba shi da wata fara'a a halitta. Se dai wannan murmushin ba ƙaramin kyau yake masa ba. Yace "Abeeyn Affan.." ya faɗa kamar yanda ya saba faɗa wani lokacin. Murmushi Abeey ya yi kafin yace "Na'am Affan. Ka na ina ne?" "Ina wani masallacin ne Abeey. Musabaƙa ake yi, yanzu ma haka an samu er matsala ne, kafin mu koma na ga kiranka.." ya faɗa. "Toh madallah. Kana dai ji na koh?" "Ehh Abeey.." "Na samar maka mata" Abeey ya faɗa. Se ya ɗan yi murmushi, dan ya ɗauka ko zalayar Abeeyn ce da ya saba lokaci zuwa lokaci. "Tohm Abeey.." "A wannan karon da gaske nake Affan. Na sama maka mata.." "Toh na gode. Allah ya ƙara girma.." Gwani ya faɗa a nutse. "Ameen Ameen. Idan kuma har ka amince toh ina so ne na ɗaura muku aure a yau ɗin nan ba se gobe ba.." Ɗan tsayawa ya yi kamar be ji abin da Abeeyn ya faɗa ba. Dan se ya ji kamar wani wasa. Jin shiru ne ya sanya Abeey faɗin "Ka na tare da ni Affan?" "Ehh Abeey.." "Toh ka amince? Ko kuwa akwai damuwa? Ba a ina nufin damuwar gida da sauran kayayyaki ba a'ah ina magana ne a kan zaɓin da na maka. In dai har ya maka toh kar ka damu.." "Toh Abeey. Allah ya sa albarka.." Ya faɗa da nutsuwar nan tasa. "Allah ya yi albarka.. Se ka dawo.." Abeey ya faɗa. Tunda ya fara maganar Ummeey ke kallansa. Ya yi murmushi yana kallanta sannan yace "Ina fatan kin ji abin da nace koh?" "Wai kuma Malam kana nufin abin da ka faɗa ɗin?" Se da ya jinjina kai sannan yace "Ƙwarai kuwa.. yanzu haka ma zan fita na samu uban yarinyar za mu je a ɗaura auren. Kar ki damu kin ji?" "Ai dole ne na damu Malam.." Ummeey ta faɗa tana girgiza kai. "Toh ai yanzu so nake ma na ji kema kin ce kin amince.." "Anya kuwa?" Ummeey ta faɗa. "Sosai ma kuwa.. Babu damuwa In Sha Allah alkhairi ne kin ji?" "Toh Allah ya sa.." Ummeey ta faɗa bayan ta sauke ajiyar zuciya. Se a lokacin sannan ya fita daga ɗakin zuwa inda ya bar Abba. Babu ɓata lokaci suka ɗauki hanya zuwa asibitin. Fita suka yi daga asibitin zuwa wani masallaci dake nesa da asibitin bayan sun bar masu kula da marasa lafiyar. Cikin ƙanƙanin lokaci aka tara mutane. Daddy ya bayar da sadakin Didi, yayin da Abeey ma be yi ƙasa a gwuiwa ba wajen fito da kuɗi daidai shi, kuɗaɗen da be daɗe da samun su ba, ya bayar dasu a matsayin sadakin Lulu. Babu ɓata lokaci aka shiga shirye shiryen ɗaurin aure. Cikin lokaci ƙanƙani kuwa aka ɗaura auren AREEF ABUBAKAR MATAWALLE da amayarsa AFRAH MUHAMMAD AJI. Se kuma AFFAN ABUBAKAR AHMAD da amaryarsa AFAAF MUHAMMAD AJI.. (Ƙaƙaƙaraƙaƙa🤭🤐) ... Tunda suka shigo gidan Ammi ke ta duba ɗaki ba ta ji motsin Didi ba. "Wai ina yarinyar nan ta shiga ne?" Ta faɗa sanda ta buɗe ƙofar toilet. Ganin nan ma babu ita ne ya sanyata sake fitowa parlour inda Lulu ke zaune. Tana shirin yin magana Abba ya yi sallama cikin ɗakin shi da Didi. Ajiyar zuciya Ammi ta sauke tana faɗin "Yallaɓai na shiga tashin hankali fa. Na kira wayarka ba ka ɗauka ba, na yi duban duniya ban ga yarinyar nan ba. Ashe fita kuka yi ." Ta ƙare tana kallan Didi. A hankali Didi ta nemi kusa da inda Ammi ta tashi ta zauna a sanyaye. Abba ma neman waje ya yi ya zauna daidai lokacin da Ammi ta sake faɗin "Lafiya kuwa?" "Nemi waje ki zauna.." Abba ya faɗa yana nuna mata kusa da shi. Babu musu ta zauna, se dai haka kawai ta ji jikinta ya ɗan yi sanyi. Kallan Lulu da ke kwance kan kujera ya yi fuskarsa a haɗe yace "Afaaf tashi ki zauna.." A hankali ta ɗan fara ƙoƙarin tashi irin da gasken bata da lafiya. Abba be ce mata komai ba har ta sauko ta nemi kusa da inda Didi ta zauna a ƙasa tun zaman su Abba a kan kujera. Bayan shuɗewar wasu sakanni ba tare da kowa yace komai ba Abba ya soma faɗin "Ashe suspension aka baki?" Ya yi maganar ba tare da ya ambaci suna ba. Da sauri Lulu ta ɗaga kai ta kalli Abba ƙirjinta na bugawa. Ganin shi ma itan yake kalla ya sanyata yin ƙasa da kai sannan ta soma haɗo maganganu tana inda inda. "Suspension kuma?" Ammi ta faɗa cike da mamaki. Jinjina kai Abba ya yi kafin yace "Ƙwarai kuwa,. Ta sake fusata malamin da rashin ɗa'a irin nata, shi ya sa ya bata hutun kwanaki, se dai be sani ba a shashanci irin na yarinyar nan daɗin hakan za ta ji.. Se dai wannan ɗin ba abin damuwa bane, dan kuwa ba ma bada kwanaki da aka yi ba, dama ko ba a yi hakan ba, daga yau kowaccensu ta gama zuwa makaranta se da izinin mijinta.." Ammi, Lulu, Didi gaba ɗaya kallan Abba suka yi jin wani saɓo da ya yi. Cike da mamakin furucinsa duka suke kallansa, se suke ganin kamar Abban be san abin da ya faɗa ba. Ganin kallan da suke binsa da shi ne ya sanya shi kallan Ammi da mamakinta yafi na kowa bayyana yace "Ƙwarai kuwa a yau ɗin nan na aurar da Afaaf da kuma Afrah.." Cikin matuƙar tashin hankali Ammi tace ƙirjinta na bugawa "Aure kuma? Aure na gaske kake nufi ko kuwa wanne Abbansu?" Ta tambaya fuskarta ɗauke da zallar mamaki da tashin hankali. Ajiyar zuciya Abba ya sauke dan ya ga alamar Ammin ta gama rikicewa, yace "Aure dai kamar yadda muka yi ni dake.." Numfashi Ammi ta sauke da ƙarfi tana ɗauke kai a kan laɓɓanta ta furta "Ya ilahy!" Se kuma ta kalli Abban a nutse tace "Wa ka aurawa su Abba?" Ammi ta faɗa bugun zuciyarta na ƙaruwa. Kallan Twins Abba ya yi waɗanda kowaccensu su take kalla, jin abin suke kamar a mafarki, bama su yadda da gaske Abban yake ba. Kawai sun ɗauki hakan a matsayin wasa ne yau Abban yake musu. Wasan da idan dai har ba a yi saurin ƙarƙare shi ba zuciyoyi biyu na dab da bugawa. "Na aurar dasu ne ga waɗanda suka dace, don kuwa ina fatan ko kuma nace idan Allah ya yadda ta silar auren nan wasu ɓangaren za su taimaki wasu ɓangaren, har su yi amfani da damar da Allah ya ba su wajen gyara abokanan zamansu, wanda kai tsaye zan iya kiran hakan da jihadi. Ki bari zan miki bayanin komai, kada ki tayar da hankalinki, dan kin riga da kin san uba ba ze taɓa zaɓarwa 'ya'yansa abin da ze cutar dasu ba. Dan haka ki kwantar da hankalinki.." Ita gaba ɗaya ma wasu maganganun na Abban ba fahimtar su take ba, dan haka ta ɗan girgiza kanta sannan tace "Zan kwantar da hankalina Abbansu, amma bayan ka faɗa min wanda ka aura musu. Sannan kuma ka tabbatar min ni da 'ya'yana da gaske abin da kake faɗa gaskiya ne?" "Ki dena tantama da wannan maganar, ba wasa bace. Da gaske na aurar da yaran nan a yau ɗin nan.." ya ƙare maganar yana kallan Twins da ke zaune kamar wasu shashashu ko waɗanda ba sa hayyacinsu. Gyara zama Abba ya yi sannan ya kalli Lulu ya ɗan yi murmushi kafin ya soma faɗin "Shi dai wannan malamin naki da kika ɗauke shi ba a matsayin malaminki ba. Ki ke masa kallan wanda kike taimakawa kina zuwa makaranta bayan shi yake koyar dake. Ki ke masa kallan wulaƙantacce dan yana Malamin Addini. Ki ka yi watsi da tarbiyyar da muka baki ki ke rashin daraja gare shi. A yau ɗin kuma cikin ikon Allah na ba shi auranki... Ma'ana dai na aura masa ke, yanzu haka kin koma ƙarƙashinsa ne, dan kuwa ya zama mijinki.." Ɗan runtse idanunta Lulu ta yi sanda gaba ɗaya kanta ya buga. A hankali kuma ta ji wani jiri jiri na kwasarta duk da a zaune take, se ta ɗan yi gefe sannan ta kai hannunta ta riƙo kanta, daidai lokacin da take sake tuno maganganun da Abban ya faɗa, dan sake tabbatar da abin da kunnuwanta suka ji. "Malam Affan!" Abba ya bawa Ammi da ta masa magana amsa. Wata ƙara Lulu ta saki sanda ta gama fahimtar inda zancen Abban ya dosa, gaba ɗaya idanunta suka makance a lokacin, kunnuwanta suka yi wani dumm, gangar jikinta ta kasa riƙeta, ƙirjinta ya cigaba da bugawa da gudun da ya mugun wuce na ƙa'ida. Saboda yanda ta ji kanta ya ɗaure tamau kamar wadda aka ɗorawa wani ƙaton abu akai, ya sanyata riƙo kan lokaci ɗaya tana faɗin "Na shiga uku..." Tun kafin ta ida faɗar hakan ta yi wani baya kamar wadda aka ja, se kawai ta zube a wajen sumammiya. Abba, Ammi har ma da Didi duka kanta suka yi. Ammi na kiran sunanta cikin tsananin tashin hankali. Da ƙyar Didi ta iya ƙarasawa inda Lulun take, se dai ta kasa aikata komai, dan gaba ɗaya jikinta wani irin rawa yake kamar mazari. Haka zalika idanunta sun cika fall da ƙwalla, ita kaɗai kuma ta san yanda take jinta a cikin tashin hankali, har taso ta ɗan dena fahimtar wasu abubuwan saboda yanda ƙwaƙwalwarta ta toshe a lokacin. Tunda Abba ya ambaci sunan Gwani Affan a matsayin wanda ya aurawa Lulu, jikinta ya ɗauki zafi, ba ta taɓa zata ba, ba ta taɓa tsammani ba. Ga kuma er uwa rabin jiki a kwance kamar matacciya. Wannan tashin hankalin shi ne ya sanya ƙwalla zubowa daga cikin idanunta, se kuma wanda yafi kowanne, wato jiran jin sunan wanda Abba ze faɗa a matsayin wanda ya aura mata itama... ALHAMDULILLAH! Anan na kawo ƙarshen A JINI TAKE Chapter one. Me son cigaba da karanta littafin A JINI TAKE Chapter two, ze tura ₦300 ne ta 8124818273, Zahra'u Yusuf Ishaq, Opay. Shedar biya ta 08124818273. Don neman ƙarin bayani za a iya tuntuɓata ta 08124818273.