[6/20, 7:12 PM] Ummu Amjad: ~_*A HAKA NAKE SON SHI*_~ Daga Alƙalamin _*Sarat Alƙasum ~(Maman Nusaiba)~*_ _🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_ _Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai. Gargadi! Ban yarda wani ko wata su juya min labarina ba ta kowacce fuska, yadda na fara lafiya Ubangiji ka ba ni ikon gamawa lafiya, Allah ya tsaftace mana Alƙalaminmu._ *بسم الله الرحمن الرحيم* Mabuɗi *(1)* Sassanyar iskar yammaci da ke kaɗawa haɗi da sanyin ƙasa suka haɗu suka bada wata kalar ni'imtacciyar iska mai daɗin shaƙa. Daidai kwanar wani layi cikin wata unguwa wata budurwa ce ta yanko layin a guje, gudu take irin na ceton rai tana yi tana waiwayen bayan ta har ta ƙaraso bakin titi. Waiwayawar da za ta yi ta hango wasu garadan maza uku suna nufo ta, cikin tashin hankali ta rasa inda za ta nufa kasancewar wajan shuru sai wata ƙatuwar bola dake gefen hanyar. Can gaba kaɗan da bolar wani kango ne wanda ba a ƙarasa ginin shi ba, hakan yasa ta kwasa a guje ta hanye kan bolar tana huci ji take kamar numfashi zai daina aiki, bakinta a manne yake da gam haka ma hannunta a ɗaure yake, amma a haka take ƙoƙarin tsira da rayuwarta. Wani kalar wari da ke fitowa daga cikin bolar ne ya kawo wa hancinta ziyara, ta taka wata leda mai ɗauke da wani abu mai kama da ruwa ai kuwa ta yi baya luu ta faɗi a cikin bolar, Kafin ta yi wani yunƙuri sai ga su sun iso bakin bolar suna kallon ta, ita kuma ban da kakarin amai babu abin da take ta sallama cewa lalle fa ruwa ya ƙare wa ɗankada, tun da har suka cin mata duk gudun da ta yi ya tashi a banza sun kama ta. "Kai Dagus maza ka saro min kanta yanzu, dan na lura yarinyar nan gudun bala'i ne da ita ta gajiyar da mu sosai. Dan haka yanzu mu sassare mata gaɓoɓin jiki." Ɗaya daga cikin su ya faɗa yana dafa na gefen shi. Ita kuwa ta kasa tashi ballantana ta taimaki kanta sakamakon wani ɗanko mai kama da ƙara ya manne mata kafarta a kan bolar, duk da kuma iskar shaƙa ta yi mata kaɗan hakan bai sa ta daina kiciniyar tashi daga kan balar ba. Duk numfashin da za ta ja sai ta ji kamar ana yankar zuciyarta ne gaf take da rasa ɗan sauran numfashin da take kai-kawo da shi. Wanda aka ce ya je ya saro kanta ne ya nufo kan bolar a fusace, cikin tashin hankali take kallon shi har ya ƙaraso ya zaro wata wuƙa mai baki biyu ya ɗaga cikin rashin imani zai sauke mata ita a ciki aka dakatar da shi. A fusace ya juyo ya dube su, wanda ya ba shi umarnin ya ɗaga masa hannu tare da nuna masa wannan kangon da ke gaba da su, hakan yasa ya gane mai yake nufi ya sunkuya ya ɗauke ta ya nufi cikin kangon. Ihu take kurmawa wanda da shi da babu duk ɗaya, saboda bakinta da yake a manne da gam tana ji tana gani suka shigar da ita kangon har cikin wani guri wanda alamu ya nuna ɗaki ne za ayi a wajan. Jefar da ita ya yi a wajan ta runtse idanu saboda wani kalar azababben zafi da ya ziyarci kunkurinta, Dagus ya sa hannu ya cire mata gam ɗin da suka rufe bakin da shi ya warware mata ɗaurin hannun. Ganin yadda take numfashi ya yi saurin kallon sauran ya ce "Gaye kar fa mu bar yarinyar nan ta wulla kawo wannan abin nata a ba ta dan shaƙa dan mu samu abin da muke so." Ya faɗa yana miƙa wa Gaye hannu ya ba shi wani abu a laulaye cikin wani tsumma. Warwarewa ya yi sai ga magani ya fito a matso kusa da ita ya kafa mata shi a baki, ita kuma cikin rawar jiki ta shaƙi maganin sau uku sannan ta ji ta dawo daidai. Tana riƙewa ya fisge kwalbar maganin ya sa a aljihunsa yana dariya ya ce "Ke har kin isa ki shiga gonar Oga ki zauna lafiya." Ya yi maganar yana kai mata mari mai shiga jiki. Kuka ta fasa a fusace ya ce "Shiii!" Ɗif ta shanye kukan tana haɗe hannu alamar roƙo, gabaɗaya jikinta rawa yake idanunta sai neman rufewa suke saboda tsabar gakabaitar da ta yi, shatin yatsun Dagus ya bayyana akan kyakyawar fuskarta kamar an zana shi, wani kalar numfashi take fitarwa cikin gajiyawa da daddage ta janyo numfashi tare ta rufe idonta cikin tashin hankalin rashin sanin yadda za ta tsira. A sanyaye ta sauke hannayenta daga haɗe sun da ta yi hawaye na zarya kan kuncinta, da ƙyar ta iya haɗiye yawu baki na rawa ta ce "Do..n.. girman Allah ka yi haƙuri kar ku cutar da ni alhalin ban muku komai ba, ka sani idan kuka zalince ni kuma wata rana za a yi wa ɗiyanku ko ƙannanku ko matayenku. Ban san me na muku ba kuka sace ni, don Allah ku faɗa min ko nawa kuke so zan sa Abbana ya ba ku amma karku taɓa min mutumcina, ni ko fita daga gida kuka ce na bari zan bar fita har abada na zama a gida." Ta ƙarashe maganar tana fashewa da kuka mai tsuma zuciya, lalle yau ba mai kwatarta sai Sarki Allah, cikinta da ke kukan yunwa ta kai hannu ta dafe ji take kamar ba a duniya take ba, tsabar yunwar da take ji ko gamin kirki ba ta yi bibbiyu take ganin su Dagus da suke tsaye a kanta. A fusace Gaye ya ce "Ki bamu wannan abin na wajan ki sai mu rabu da ke ki tafi gida." Kwalalo idanu waje ta yi cike da rashin sanin inda maganar su ta dosa, ta ce "Wallahi ni babu wani abu a wajena wanda yake naku, wayata ma ai kun amshe ta ba ni da komai ku rabu da ni." Ta ƙarashe maganar cikin fitar haiyaci, ji take komai ma duniyar ya mata zafi yadda suke gana mata azaba. Jin ta faɗi haka yasa Gaye ya ce "Buɗe hannunki." Kallon shi ta yi cikin tsoro da fargaba taƙi ba shi hannun, sai ma ƙara matse hannayenta ta yi tana gunjin kuka dan magana ma kanta ta kasa yi, shi kansa numfashin da ƙyar take iya janyo shi in da fitar, Dagus ganin ta yi shuru ya daka mata tsawar da ta sanya 'yan hanjinta kaɗawa. "Za ki buɗe ko sai na sare miki hannun!?" Ya faɗa yana mai ƙara kusanto ta. Babu shiri ta buɗe hannun jikinta na rawa tana jin kamar ta zo gangarar mutuwa. Babu komai ya gani sai kawai ya kwashe da dariya, "Hahaha! Yarinya man kaza ai shi mun gama mi shi nashi aikin, yanzu kuma namu ne za mu yi kin gane?" Ya faɗa yana matsowa kusa da ita. Saurin ja da baya ta yi tana girgiza kai tana roƙon su da su rufa mata asiri kar su ɓata mata rayuwa, amma sai suka dinga dariya suna nuna ta. "Ya Allah ka kawo min ɗauki, Ubangiji kar ka bari mutanen nan su ci zarafi na ban musu komai ba Allah ka kawo min ɗaukin gaggawa." Ta faɗa tare da ƙanƙame jikinta tana gunjin kuka. Dagus ya kamo hannunta yana aje wuƙaƙensa biyu ya cire rigarsa yana bin ta da kallon za ki gane ba ki da wayo, ita kuma duk Addu'ar da ta zo bakinta yi take tana rawar jiki gabaɗaya ta sallama wa duniya yau za ta barta.. A gabanta Dagus ya cire riga da dogon wadonsa ya rage daga shi sai na ciki shi ma iya gwiwa, abin da ya ƙara gigita duniyar tunaninta ta cure waje ɗaya tana faɗin "Oh God, help me in my life." Daga can gefen su wani ne sanye da kaya yagaggu yana bacci, jin hayaniyar ta gama hawa kansa sai ya buɗe idanuwansa wanda suka yi jajur saboda bacci. Ganin abin da yake faruwa ya zabura ya juya gefe ya ɗauki wani rabin taɓarya haɗi da wata mulmulalliyar sanda mai kauri da tsayi ya ɗaura wata hula a kansa duk ta yage. Sai da ya zagaye inda ya tashi ya kalli wannan gardawan ya kwarara ihu. "Waiyihuhu! Waye nan ya shigo min gida?" Ya yi maganar yana nufo su. Dukkan su suka ja da baya a kiɗime sai kuma suka ja suka tsaya tare da fito da wuƙaƙen dake ƙugunsu suna nuna wannan mahaukacin da shi. Shi kuwa bai kula su ba wajan ta ya nufa ya yi tsayauwar 'yan dambe yana dariya tare da zagaya ta, leƙa ta ya yi ita kuma ta ƙara mannewa a jikin bango taoro na ƙara lumkuwa a zuciyarta, dariya kuma yi ya soma magana. "Hahaha Anty dama ke ce? Waɗannan babanninki ne da iyayenki da ubanninki?" Ya faɗa yana zama a gaban ta suka yi facing ɗin juna. Da ƙyar ta iya ɗago da kanta ta kalle shi, ganin shigar da ke jikinshi ta ji gabaɗaya ta firgice, hannayensa ta kalla ta ga taɓarya sai kawai ta rufe idanu tana yin duk Addu'ar da ta zo bakinta. Ganin wannan mahaukacin zai ɓata musu lokaci yasa Dagus ya kai masa sara kan kafaɗarsa, ya kuwa ci sa'a ya same shi a daidai. Wani irin ƙara mahaukacin nan ya yi wanda yasa ta ƙara mannewa a jikin bango tana kuka tare da roƙon su. "Don Allah kar ku cutar da shi tun da ba shi ba kuka biyo na roƙe ku." Ta yi magana tana matsowa kusan Mahaukacin wanda jini ya soma ambaliya daga kan kafaɗarsa, sosai ta ƙara ruɗewa har shidewa take tsabar tashin hankali.. Dariya suka dinga mata Dagus ya yi saurin wawurar ƙaramar wuƙarsa bai jira komai ba ya yanki Mahaukacin nan, ya dawo ta gefe ya ɗamko hannunta ya janyo ta kii! Shi ko Mahaukacin nan sosai yankan ya shige shi duk jini ya wanke masa kafaɗar, hakan yasa kansa ya sara nan-da-nan ganin shi ya ɗauke na ɗan lokaci. Sai da ya jima can sannan ya buɗe idanunsa ya ga wayam ba ta gaban shi, a zabure ya ce " Anty!" Tare da miƙewa ya nufi ɗayar ƙofar. Ita kuwa tuni sun yayyaga mata doguwar rigar dake jikinta, kaɗan ya rage su gama cire mata rigar ta ji muryarsa ai kuwa ta daddage ta kwarara ihu da ɗan sauran kuzarin da ya rafe mata. Kafin ta rufe baki Dagus ya faɗo kanta, wani irin nauyi ta ji yayin da Dagus ya rikito bisa kanta ta dinga kiciniyar kwace kanta amma ina ta kasa, wata dabara ta zo mata ta juya da fuskarta ta samu daidai ta ci kuncinsa ta gatsa masa cizo, ihu yasa ba shiri ya kai mata mari ita kuma taki sakin kuncin nasa har sai da ta ji ya kawo jini sannan ta sake masa kunci.. Cikin magagin zafin cizon da ta masa ya tashi daga kan ta ya kai hannu zai damko ta ya ji saukar duka a gadon bayansa. Cikin kiɗima ya juyo dan ya ga waye ya dake shi a cikin abokan aikin nasu, sai dai kuma ya ga saɓanin hakan, dan kuwa Mahaukacin nan ya gani tsaye a bakin ƙofar yana wurga idanunsa ko'ina ya ga inda take. Tana ganin shi ta miƙe da ƙyar ta nufi inda yake, hakan yasa Dagus ya kuma kai hannu da niyar dawo da ita ta yi saurin yin ƙasa da rarrafe ta dawo bayan Mahaukacin. Ganin jini a bakinta yasa ya zazzaro idanu ya kalli Dagus fuskarsa na nuna tsananin ɓacin rai ya ce "Ka daki Anty ko?" Yana gama faɗin haka ya nufe shi da rabin taɓaryar dake hannunsa. Duk da Dagus a tsorace yake amma ya tsaya yana jiran Mahaukacin ya iso gareshi, shi kuma yana zuwa ya wurgo masa rabin taɓaryar dake hannunsa ji kake Tim! Ta same shi a ruwan ciki. Bai tsaya yin komai ba ya hau kansa ya dinga kai masa naushii ta ko'ina, abokan tafiyar Dagus su dama tuni ya sumar da su, dan haka Dagus ya rasa me ceton shi a hannun wannan Mahaukacin. Sai da ya ga baya motsi sannan ya dakata da dukan shi, huci yake yana faɗin " Ka fito mata da jini sai na kashe ka." Ita kuwa tana gefe tana kallon shi zuciyarta cike da mamakin wannan Mahaukaci da ya cece ta a hannun mugaye. Dawowa ya yi wajan ta yana kallon ta bai ce da ita komai ba, sai da ya sauke numfashi sannan ya koma kan Dagus ya ja ƙafarsa ya fitar da shi daga cikin kangon ya dawo ya fitar da sauran wanda a lokacin suka dawo daga sumar da suka yi, yana fito da su suka lallaɓa suka miƙe suna ƙoƙarin gudu. Yana tsaye yana kallon su har sun soma tafiya suna waiwayen shi, shi kuma ganin haka yasa ya koma ciki da sauri ya ɗauko makaminsa ya biyo su a guje.. Ganin mutuwa na tunkaro su yasa suka kwasa a guje sai ga su a bakin hanya, shi ma ya iso yana nuna su da taɓarya ai kuwa suka ƙara wa gudunsu mai tuni suka bar wajan. Kaiwa da komowa ya dinga yi a bakin hanyar kamar mai yin pareti, sai da ya jima a haka sannan ya juya ya koma.. Tana ganin shi ta miƙe tsaye tana kallon shi har ya iso ya zauna a kan wani kwali mai faɗi, wata leda ya buɗe sai ga masa da miya har ta soma tsami sai tashi take. Da sauri ta done hancinta ganin ya sa hannu ya ɗauko guda ɗaya yana murmushi ya kai bakinsa, kakarin amai ta dinga yi shi kuma ya kwashe da dariya ya janyo kwalin ya matso kusa da ita ya tura mata masar yana dariya.. "Anty za ki ci ko?" Ya faɗa yana ɗaukar masar ya nufi bakinta da ita. Da sauri ta janye fuskarta ta ce "A a na koshi ka ci abinka." Dariya ya kuma yi ya ci gaba da ci har ya cinye tas ya suɗe ledar, bayan ya gama ya janyo wata ledar ya bude ya ɗauko ruwa ya sha. Duk tana kallon shi har ya gama sannan ya ce mata "Anty yunwa nake ji." Ya faɗa yana ɓata fuska. Ita abin sai ya ba ta dariya ma dan haka ta yi murmushi abin da yake ba ta mamaki ma da yake ce mata Anty bayan kuma bai taɓa ganin ta ba sai yau, lokaci ɗaya taji zuciyarta ta yi rauni tausayin shi ya tsarga mata zuciya. "Yanzu kila iyayensa suna can suna neman shi, ko kuma sun gaji sun haƙura da nema, ko kuwa dai daga gidan mahaukata ya gudo yake zama a wannan waje mai mugun ƙazanta da wari?" Ta yi magana a sanyaye kafin ta sauke ajiyar zuciya ta dube shi ta ce " Ya sunan ka." Dariya ya mata yana goge sandarsa da wani ɓakin tsumma, sai da ta kuma maimaitawa sannan ya dakata da abin yake ya ce " Ya sunanka?" Ya mayar mata da tambayar da ta masa. Waigawa gefe ta yi ta hango ɗankwalinta da isa wajan ta ɗauko, warware shi ta yi ta kalle shi ganin yadda jini ya ɓata masa jiki sai ta matsa a hankali cike da tsaro ta ce "Kawo na ɗaure ma wajan ciwon." Maƙale kafaɗa ya yi yana turo baki sai kuma ya ce "Ni fa sarki ne a faɗar nan." Sakato ya yi tana kallon shi, ta yi juyin duniyar nan amma fir ya ce shi sarki ne ba za a taɓa masa rawani ba, ita kuma tausayin shi ya cika mata zuciya sai kawai ta rabu da shi ta ce " Zan fita waje dan na koma gida." Ta yi magana tana bin hanyar fita.. Shi ma bayan ta ya bi suka fito a tare har bakin hanya, sai da ta juya ta ga ya biyo ta ta yi fuskar tausayi ta ce "To na gode ka koma." Shi ma fuskar tausayin ya yi ya ce "To na gode ka koma." Murmushi ta kuma yi a karo na biyu. Duk wanda ya zo wucewa sai ya kalle su kallo irin na mamakin yadda ta tsaya a kusan mahaukaci ga shi kuma riƙe da makami amma bai ce mata komai ba, wasu kuma in sun ɗan yi gaba sai su ce mata 'Baiwar Allah wannan mahaukacin zai iya miki illa.' Murmushi kawai take musu ba ta cewa komai tana kuma mamakin yadda in mutane sun zo wucewa sai ya kare ta ya shiga gabanta yana muzurai. Wani Dattijo ne ya zo wucewa ya yi shigar shi ta zuwa Masallaci ta yi saurin tarar shi sai ya tsaya. "Baiwar Allah lafiya?" Ya faɗa yana kallon ta. "Baba ba lafiya ba don Allah ka taimaka min da waya zan kira Mamana su zo su dauke ni." Ta faɗa tana durkusawa, shi ma ganin ta durkusa ya durkusa a gefen ta ya ce "Baba ba lafiya ba don Allah ka taimaka min da waya zan kira Mamana su zo su dauke ni." Dattijon nan ya dubi Mahaukacin ya ce "To amma mai ya haɗa ki da wannan Mahaukacin?" Labari ta ba shi na ceton ta da ya yi ta kuma ce masa sace ta aka yi shi ne ta gudo har ya ceceta, jin haka yasa Dattijo ya cika da mamakin Mahaukacin ya dinga kallon shi ganin yadda ya durƙusa kamar yadda za yi, girgiza kai kawai ya yi fuskarsa na nuna tsananin damuwa ya fito da wayarsa Nokia ya ba ta. Amsa ta yi ta sa wata number ta danna kira, sai da ta kusa yankewa sannan aka ɗauka tare da yin sallama. "Mommy!" Ta faɗa tare da sa kuka wani irin farin ciki na lullube ji na jin muryar mahaifiyarta da ta yi. Daga cikin wayar matar ta dinga salati ta ce "Abir ke ce? Ina kuka shiga muke ta neman ku hankalinmu duk a tashe?" Sai da ta goge hawaye ta ce "Mommy don Allah ki zo ki ɗauke ni Wallahi in suka kama ni kashe ni za su yi." "Su waye za su kashe ki?" Ganin za su ja magana yasa Abir ta ce "Mommy ki bari sai na zo gida, ni dai ku yi sauri tsoro nake ji Mom." "Ok Mamana yanzu a ina kike?" Mommy ta faɗa murya na rawa. Tambayar Dattijon ta yi ya faɗa mata inda take, tana jin mai suke faɗa dan haka ta roƙi tsohon da ya tsaya a wajan ba ta da nisa sosai da wajan za ta iso. Ba dan ya so ba ya ce ya amince.. Kamar an tsikare shi ya buga sanda a ƙasa ya juya ya shiga kewaye su yana dariya, da ido kawai suke bin shi tsoro ya cika musu zuciyoyi kar ya ce zai kai musu duka. Yana gama zagaye su ya wuce ya bar wajan yana faɗin " Anty bari na kawo miki kaya." Suna kallon shi ya tsallake bolar ya shige cikin kangon nan sai ga wata dalleliyar mota ɓaka ta yi packing a gaban su, a razane Abir ta ja da baya ta koma bayan Dattijon nan.. _Littafin nan na kuɗi ne ƴar uwa nomal ~N~ 300, vip ~N~ 500 ne. Ina kuma sanar da ku ga masu buƙatar Littafin ABBA NE complete ayi min magana ta WhatsApp number na 👉🏻🥏+966577675904_ *Kada ku bari a ba ku labarin wannan littafi* _Maman Nusaiba ce🫶🏻_ [6/20, 7:15 PM] Ummu Amjad: ~_*A HAKA NAKE SON SHI*_~ Daga Alƙalamin _*Sarat Alƙasum ~(Maman Nusaiba)~*_ _🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_ Littafin A HAKA NAKE SON SHI na kuɗi ne nomal ~N~ 300 vip ~N~ 500. _🥏 WhatsApp Number +966577675904_ *بسم الله الرحمن الرحيم* Shafi na biyu (2) Da mamaki Dattijo ke kallon Abir ganin yadda nan-da-nan jikinta ya ɗauki rawa, dawo da kallonsa ya yi kan motar yana jiran ya ga waye zai fito wanda kafin ya fito ɗin ma yarinya ta tsorata?. Direba ya fito cikin sauri ya zagayo baya ya buɗe tare da rusunawa ya ce "Oga mun iso wajan." Yana zaune ya hakimce a gidan baya ya kwantar da kansa a jikin kujera idanunsa a lumshe, wanda in ka gan shi a haka sai ka rantse bacci yake shi kuwa yana tsaye. A hankali ya ɗago da hannunsa na hango ya bude idanunsa tare kalon agogon dake hannunsu, sai da ya sha ƙamshi ya shirya dan kasan dan har direba ya kosa da riƙe marfin motar da ya yi sannan ya fito da ƙafarsa ɗaya waje, sai da ya kai sakan arba'in sannan ya fito da ɗayar ƙafar, miƙo kansa ya yi yana wani shan ƙamshi, sai da ya shirya dan kan shi sannan ya fito daga cikin motar. Dogo ne fari sol zubin ƙarfafa kyakyawa ajin farko wanda bai fi shekara 30 ba, fuskarsa sanye da ɓakin glass wanda ya ƙara wa fuskar tashi kyau da ƙwarjini a idanun mai kallon shi, yana da saje wanda ya ƙara ƙawata fuskar. Sanye yake da ƙananan kaya baƙaƙe har hula cap dake kansa wadda a jikin hular aka rubuta *D. S. P*, sake lumshe dara-daran idanunsa ya yi yana yatsina fuska jin iska ta kawo masa wani irin wari marar daɗin shaƙa ya buɗe su tare waro su akan Baba Dattijo, sai da ya gama ƙare wa wajan kallo sannan ya dubi Dattijo ya ce " Hey tsoho ba ka ga wata yarinya a nan ba?" Ya yi maganar yana sauke ajiyar zuciyar ya yi magana mai tsayi, kuma duk da ya ganta amma saboda hali irin nasa yake tambaya. Dattijo ya dube shi ya ce " Kai ɗin waye? Sannan kuma wa kake nema?" Jin muryar wanda ya yi maganar Abir dake bayan Dattijo ta leƙo kanta dan ta tabbatar ko masarrafar jinta daidai ta jiyo mata. Idanuwanta suka sauka a kan shi, sai yanzu ma ta ji ƙamshin turarensa ya kawo mata ziyara cikin wani kalar yanayi ta dan fesar sa numfashi sannan ta fito daga bayan Baba. Wani irin waro idanu ya yi tare da yin taku biyu, ganin haka yasa ta isa gareshi tare da sakin kukan da take dannewa, shi ko saurin cire glass ɗin fuskarsa ya yi yana kallon ta fuska ɗauke da mamakin ganin ta kamar ya ga sabuwar halitta, wani irin yanayi ya shiga na ganin ta cike da al'ajabi ya gyara tsayuwa ya ce "Baby!" Matsowa kusa da shi ta yi kamar za ta faɗa jikinsa ta ruƙo hannunsa cikin muryar kuka ta amsa. "Yaya! Ashe zan sake ganin ku a rayuwata? Don Allah ka yi sauri ka ɗauke ni kar su kuma sace ni." Ta faɗa ta na girgiza hannunsa, farin ciki ya mamaye mata zuciya ganin Yayan nata a wannan lokacin.. Hannu ya sa ya goge mata hawayen duk da a kiɗime yake, amma bai nuna ya shiga ruɗu ba cikin kasalalliyar murya ya ce "My Babyy." Ya ƙarashe maganar yana kallon tufafin dake jikinta, jin warin dake tashi daga jikinta yasa ransa ƙara ɓaci ya buɗe mota tare da kallon ta, ganin haka ya sa ta gane me yake nufi ta nufi ƙofar da ya fito. Har za ta shiga ta juya ta dawo wajan Dattijo ta dube shi ta ce " Baba na gode Allah ya saka da alkhairi zan ɗauki number ka a wajan Mommy, sannan in da hali tun da ka ce kai baya ce ma komai in ka kai masa abinci, ina so ka ba shi magani ko ka wanke masa wajan saboda sun sare shi da girma a wajan. Zan samu lokaci sai na zo in Allah ya ba ni iko , sai an jima Baba Allah ya sada mu da alkhairi." Ta faɗa tana kallon hanyar da ya bi. Murmushi Dattijo ya yi yana jinjina kai, sosai ya ji yarinyar ta birge shi ya ce " Karki damu yarinya ai an jima ma zai fito waje, Allah ya kiyaye gaba ya tsare miki rayuwa." Amin ta ce tana murmushi sannan ta dawo ta shige motar shi ma ya shiga suka bar wajan.. Suna tashin motar sai ga shi ya dawo da sauri Dattijo na shirin wucewa ya ji ƙaran tafiyarsa ya juyo da sauri. Yana muzurai ya dogare sandarsa tare da tsayuwa irin ta fulani yana dariya ya ce "Baba Anty ta kawo abinci?" Girgiza kai kawai Dattijo ya yi ya wuce ya bar shi a bakin hanyar yana ta surutai. Shi kuwa ɗankwalinta da ta yi famar ta ɗaura masa a kafaɗa ya kalla ya ce " Ni ne sarkin wannan rawanin ya zama naki Anty, duk wanda ya zo nan sai ya biya kuɗin mota zai tafi." Haka ya yi ta surutu yana zagaye bakin hanyar, duk wanda ya zo wucewa sai ya ce masa " Kasan Anty?" In ka ce ba ka san ta ba zai ɓata rai ya nufe ka da rabin taɓarya ya ce 'me ya sa ka ce ba ka Anty ba?' In Allah ya taimake ka ka gudu ka tsira, idan kuma ka ce ka san ta sai ya yi ta dariya ya bar ka ka wuce yana bin ka a baya har sai kun yi ƴar tafiya sannan ya dawo.. Tun da suka shiga cikin motar ya dinga kallon ta yana jera mata sannu har suka isa gida. A jikin gidan an rubuta *FAMILY HOME MAITAMA* Babban gida ne yana da ɓangarori hudu haka akwai babbar haraba a gidan inda aka yi wajan aje motoci a gaf da ɓangaran farko, harabar gidan an ƙawatata ce shukoki ko'ina ka kalla kwanan birgewa fulawowi ne a jere isar Magariba na kaɗa su. Suna gama packing direba ya fito ya buɗe musu suka fito, hannunta ya kama suka bi wata ƙofa wadda za ta sada su da cikin gidan. A babban palon gida suka yi sallama in da yake cike da mutanen gidan maza da mata da ƙananan yara, da sauri ta fisge roƙon da ya mata ta nufi wajan wata matashiyar mata hakan yasa ita ma ta tashi da sauri suka haɗe ta faɗa jikinta tana kuka. Kowa na palon fuskarsa ɗauke take da farin ciki sun zagaye ta suna ta taɓa jikinta duk da wari da take bai hana ɗaya bayan ɗaya sun rungume ta ba suna kukan ganin ta. Shi kuma gefe ya samu ya harɗe hannayensa a ƙirji yana kallon su, ganin ba za su gama ba ya sa ya daka wa wasu 'yan mata uku dake rungume ta ita tsawa . "Ku sake ta na ce!" Ya faɗa a fusace, gabaɗaya sun sa kansa ya fara ciwo da wannan hayaniyar ta su, ga wani irin yanayi da yake jinsa da zarar ya kalle ta. Nan-da-nan duk suka sake ta ita kuma ta dunga kallon familyn nata ɗaya bayan ɗaya, can ta hango tsohuwa zaune a kan kujera ta hakimce tana kallon ta, murmushi ta yi ta soma takawa a hankali ta ƙarasa ga tsohuwar da take farin cikin ganin ta ta ce ",Grandma wai ba ki ganni ba ne." Wani irin kallo Grandma ta mata ta sauke ƙafafuwanta daga harɗe su da ta yi ta dubi Abir ta ce " Ke raba ni da wannan 'yan bana bakwai ɗin, so kike na tashi ni ma ina wawurar ki kamar su aje su ɓalla min ƙafa? To ni ba gantalalliya ba ce kamar su yanzu da suka gama ganin ki ba ga shi kin zo har inda nake ba?" Yar dariya Abir ta ɗago kai suka haɗa idanu da shi, langaɓar da kai ta yi kamar za ta sa kuka shi kuma ya kifta mata idanu yana ɗage gira, alama ya mata da ido me ya faru? Cuno baki ta yi gaba ta janye idanunta daga kallon shi ta dawo kan Grandma, zama ta yi a ƙasa kan capet ta yi murmushi ta ce "Grandma kenan wai ko ba ki yi kewa ta ba?" Kauda kai ta yi ta ce "kayya ƴar nan! In da wanda ya fi ni shiga tashin hankali a gidan nan ai sai dai mahaifiyarki, ko baccin kirki bana iya ci saboda damuwar ban san a wani hali kuke ba a mace kuke ko a raye, ina Ibrahim ɗin yake?" Za ta yi magana suka ji an buɗe ƙofa duk suka mayar da hankalinsu kan ƙofar, wani matashin saurayi ne ya shigo yana fito ganin duk mutanen gidan a palon yasa ya yi saurin katse fiton da yake ya soma shafa kansa. Idanuwansa ne suka sauka a kan Abir da ke zaune a kusan Grandma, da sauri ya nufe ta yana faɗin "Wa nake gani kamar Baby? Ita ma dariya ta yi tana kallon shi har ya iso, ƙoƙarin rungumar ya yi ya ji an daka masa tsawa. "In ka taɓa jikinta sai na kakkarya ka a gidan nan!" Ya faɗa rai ɓace yana huci, a zafafe ya nufi wajan ɗaya daga cikin 'yan matan ya ce "Ke Fatima cire hijabinki ki bani." Ba muso Fatima ta cire ta miƙa masa shi kuma ya nufi Abir ya yi saurin saka mata tare da miƙar da ita ya ce " Wuce ki je ki yi wanka ki fitar da kayan nan, duk surar jikinki ana gani shi ne kema har kika wani zauna maza suna kallon ki a haka. Kai kuma Salim ka sake bin ta da kallo za ka sani." Ya faɗa yana nuna shi da hannu.. Dariya Salim ya yi dan bai yi mamakin abin da Yayan nashi ya faɗa ba, ya miƙe tsaye ya dafa kafaɗarsa ya ce " Ni fa daɗi na da kai Yaya Abdul ba ka so a raɓi Baby sai ka ce kai kaɗai ne yayanta, Ammi ki faɗa masa ya daina shiga tsakani na da Baby tun da ni ma ɗan'uwanta ne ba bare ba ne ni a cikin gidan nan." Ya faɗa yana haɗe rai tare da kallon matar dake gefen mahaifiyar Abir.. Ko ci kanku Ammi ba ta ce musu ba sai ma harara da take aika wa Abdul har Salim ɗin, tashi ta yi ta ja tsaki ta wuce daga palon kamar za ta tashi sama. Grandma ta tofar da yawu a inda Ammi ta tashi ta ce "Mai hali dai ba zai basa ba, ni ban taɓa ganin shafaffiya da mai irin Farida ba, mace sai ɓakar zuciya kamar dangin kutare, to Wallahi ba da ni ba kai dai Salmanu ba yi dacen mata ba." Girgiza kai wanda aka kira da Salmanu ya yi ya ce "Ai Mama mu yanzu farin ciki muke da aka samu Abir ta kubuto daga mugun hannun da ta faɗa, ita kuma ki rabu da ita ta je ta yi ɓakin halinta tun da ta saba. Kowa ya tashi ya tafi ɓangaransa Kabir an jima ina son magana da kai." Yana gama faɗin haka ya tashi ya bar wajan. Suma duk suka bar palo ya rage daga Mommy sai Grandma sai Abdul da ya zauna zaman jiran ta fito, da an yi sakan biyu zuwa biyar sai ya kalli ƙofar ɗakinta hakan yasa Grandma ta ce " Uhmm malam ai sai ka tafi ka ba mu waje ko, na ga dai uwarka ba son zaman ka take a nan ba ko da yake ma ai tasan ba ta isa ta hana ka zuwa nan ba saboda uwar ubanka Kabiru tana nan dole ka zo ka zauna a wajena." Murmushi ya yi kawai bai ce da ita komai ba sai ma juyo da kallon shi ya yi ga Mommy da ke zaune tana danna wa, a sannan ya ce " Mommy abinci nake son ci ina jin yunwa ni da Baby." To ta ce masa sannan ta ce " Laraba ki jera abinci a kan denning Babana zai ci abinci." Ɓata fuska ya yi jin sunan wadda ta kira, shi fa abin da ya tsana kenan ya ci abincin ƴar aiki, abinci indai ba na Mommy ba ne duk gani yake ba zai yi daɗi ba, fesar da iskar bakinsa ya yi ya ce "Haba Mom ya za ki ce waccan kucakar ƴar ƙauyen ce za ta haɗa mana abinci kuma wai har da Baby za ta ci girkin ta? Gaskiya Mommy ke muke so ki mana abinci ba mai aiki ba." Ya faɗa yana hura hanci. Murmushi Mommy ta yi ta yunƙura za ta tashi sai ga Laraba ta fito hannayenta dauke da trey tana washe baki ta iso za ta aje. "Ke! Maza bar wajan man." Ba ta san lokacin da kayan hannunta suka kubce ba ji kake tass! Suna fashewa, hankalinta a tashi ta kalli Mommy ta ce "Alkur'anin Allah Hajiya hi ya tsorani har abincin ya zube, aradu tsoron hi nake ji ki faɗa masa ya daina firgita ni Hajiya wannan ai he in hiɗe Goggona ta yi asara ta." Ta yi maganar tana dawowa kusa da Mommy fuskar nan sai maiƙo take saboda man da ta narka wa fuskar... Dariya Mommy ta yi ta ce "Don Allah Abdul ka daina tsorata yarinyar nan haka, kalli ka ga duk kasa jikinta yana rawa." Kwafa ya yi bai ce komai ba, sai da ya gama duba jikinsa ya ga ba ta ɓata masa da ba ya ce "Wallahi ta ci sa'a ba ta ɓata min kayan jikina ba, da sai na kakkarya ta a palon nan." "Ba shakka ɗan marassa tausayi da ka soma yin gadon bakin halin waccan mata uban naka Baraka, Wallahi Abdullahi ka guji cin zarafin ɗan'adam." Cewar Grandma tana kaɗa kai. Cikin shigar doguwar rigar atamfa ta fito daga ɗakinta ta soma takowa a hankali cikin nutsuwa kamar mai tausayin ƙasa, sai yanzu suffarta ta fito. Ɓaka ce ba ta da tsayi har can amma ba za a kira ta da gajerar mace ba, siririya ce ba ta jiki , tana da doguwar fuska mai ɗauke da ɗan ƙaramin bakinta madaidaici, shekarunta ba su fi 18 ba amma ka ganta kamar yar shekara 15 duk da wannan ƙanƙantar amma tana da diri mai ɗaukar hankali, gashin kanta ɓaki sidik wanda ya zubo har gadon bayanta sai sheki yake, hancinta ɗan siriri wanda aka bula shi ta sa masa ƴar barina fara sai ta ƙara ƙawata fuskar. A kusa da Grandma ta zauna ta ce "Mommy ƙafata zafi take min sabo... Ba ta ƙarasa maganar ba sakamakon hayaƙin da ya kawo wa hancinta ziyarar bazata ta shaƙa, nan-da-nan ta soma tari tana riƙe ƙirji, kafin minti ɗaya tuni ta fita haiyacinta.. _My sister Littafin nan na kuɗi ne nomal ~N~ 300 ne vip ~N~ 500 ne , ku hanzarta ku biya naku domin ayi tafiyar nan tare da ku._ _🥏+966577675904_ *Idan kin karanta please ki daure ki min share my sister 🙏* _Hmm mu je zuwa_ _*Maman Nusaiba*_ [6/20, 7:23 PM] Ummu Amjad: ~_*A HAKA NAKE SON SHI*_~ Daga Alƙalamin _*Sarat Alƙasum ~(Maman Nusaiba)~*_ _🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_ _Littafin na kuɗi ne nomal ~N~ 300 ne vip ~N~ 500 ne_ Domin ƙarin bayani ku neme ni a wannan number 👇🏻 🥏+966577675904. *بسم الله الرحمن الرحيم* Shafi na uku (3) Saurin taro ta Abdul ya yi ya kamo hannayenta kafin ta isa ƙasa, ɗaura ta ya yi akan kujera a hargitse yake kallon yadda take jan numfashi, ya kwanto da ita jikinsa ganin Mommy ta nufi ɗakinta. Ƙagara ya yi Mommy ta fito duk daƙiƙa ɗaya in ta ja numfashi ba ta iya janyowa ta shaƙa sai mimmkiwa take a jikinsa, kanta ya shiga shafawa Grandma na tsaye a kansu sai kiran Mom take ta yi sauri. Ita kuwa Mommy maganin take nema a ɗaki, amma kiɗimewar da ta yi yasa ta kasa ganinsa a gaban ta a aje, sai da ta kusan minti goma Allah ya ba ta ikon gani ta ɗauko da sauri ta fito har tana haɗawa da ɗan gudu. Saurin amsa Abdul ya yi ya buɗe maganin ya kai bakinta gabaɗaya ta soma sakin jiki, jin maganin a bakinta ta yi ƙoƙarin shaƙa da ɗan kuzarin da ya rage mata, ƙara ɗago kanta ya yi wannan karon da kanta ta riƙe gwalbar maganin ta ƙara shaƙa numfashinta ya soma kai-kawo. Grandma da ke tsaye ta matso ta ƙara tallabo ta ta zauna ta ɗaura kanta a kan cinyarta, shi ko Abdul ya ƙara shaƙa mata maganin ta kuma shaƙa sai gata ta buɗe idanu. Sannu suka shiga jera mata ta yi lamo a cinyar Grandma tana kallon su dan ta kasa cewa da su komai. Cikinta ta riƙe ta yunƙura ta tashi zaune jin yadda yake mata wani irin kukan yunwa, Abdul ya cire mata ɗankwali yana kallon ta cikin tausayawa ya ma kasa ce mata komai, zuciyarsa sai bugawa take da auari-sauri har sai da ya kai hannu ya dafe saitin zuciyar. Mommy ta sauke numfashi ta ce "Ina ne yake miki ciwo yanzu?" Girgiza kai ta yi kawai abin da Abdul ya tsana kenan a mata magana ta girgiza kai ko ta gyaɗa kai kamar wata ƙadangaruwa, hakan yasa ya koma ya zauna sannan ya ce "Mommy na faɗa miki ki mayar da ƴar aikin nan a kawo miki mai hankali amma kin ƙiya gani kike kamar bana son ta ne, kalli ki ga ta kunna wa mutune turaren wuta a gida bayan kuma saboda Baby ba a yin hayaƙi a gidan nan. Yanzu da gida ba kowa sai dai in kwanan ta ya ƙare ta mutu." Ya faɗa yana jin kamar ya je ya rufe Laraba da duka. Haƙuri kawai Mommy ta ba shi har ta samu Abir ta dawo nomal sannan ta zauna ita ma ta ce "Ka fiya ɗaukan zafi Babana me ye haka? Ni na ce mata take yi mana turaren wuta tun lokacin suka ɓata, zan sanar da ita ta daina yanzu." Tana gama faɗin haka ta miƙe ta shiga kitchen ɗin inda ta samu Laraba na kuka, da sauri ta isa wajan ta ta ce "Laraba lafiya kike kuka?" Ɗago kai ta yi idanunta sun yi jajur ta ce "Hajiya don Allah karki koreni aradu na saba da ku, kuma kin ga yanzu ban san wani gida za a kaini ba in kika koreni, saboda na je wani gida inda 'yan gidan halinsu ɗaya da wannan babban ɗan naki har dukana suke in suka kira ni ban zo da wuri ba. Ki yi haƙuri mai ne na ɗaura shi ne na tafi kai abinci kafin na dawo ya yi zafi sosai, to da na dawo na zuba a wani kwanan sai na zuba wa kwanon ruwa shi ne ya cika kitchen ɗin da hayaƙi har ya je palon." Tana maganar tana ɗaura zane kafin ta kai kalma ɗaya sai ya warware, abin sai ya ba wa Mommy dariya ta murmusa ta ce "Ba komai Laraba ai ke kamar 'yata kike ba zan kore ki ba kin ji, kuma daga yau karki kunna turaren wuta a gidan nan 'yata ba ta da lafiya in ta shaƙi hayaƙi numfashinta ƙoƙarin barin jikinta yake." "Alkur'anin Allah ko da wasa ba zan yi ba Hajiya, na gode Allah ya saka miki kina da kirki." Ta faɗa tana murmushi. Ita ma Mommy murmishin ta yi dan ɗabi'un Laraba na birge ta, kayan abinci ta haɗa da kanta ta dubi Laraba ta ce "Idan na ce ki shirya abinci a kan denning wannan teburin na bakin ƙofa a nan za ki dinga jera abinci idan kin gama, sunan shi haka duk wanda ya ce ki kawo abinci denning to nan za ki kawo." Ita dai Laraba sai to take cewa har Mommy ta gama magana ta fito ta rufe mata ƙofar.. Tarar ta ya yi ya amshi kayan abincin ya aje a gaban Abir ya ɗago ya kalle ta, itama kallon na shi ta yi ganin yadda duk ya kiɗime akan tashin ciwonta, kawar kai fege ya yi ya zauna sannan ya ce "Baby za ki iya cin abincin? " Shagwaɓe fuska ta yi kamar za ta sa kuka ta ce "Yaya na ƙoshi ma da abincin, a ba ni maganin ciwon jiki na sha." Ta faɗa ba wai dan ba ta jin wuyar ba, ciwon jikin nata ne ya rinjayi yunwar shi ya sa ta ji duk ko'ina na jikinta ciwo yake. "A a sai dai na kaiki Asibiti da na gama cin abinci, in kuma mu tafi in na dawo sai na ci to?" Ya faɗa yana zuba mata idanuwansa masu ƙara masa ƙwarjini. Jin wani irin zogi da ƙafarta take yi yasa ta ɓare baki kamar wata yarinya ta saki kuka ta ce "Ni ka tashi ka kaini in mun dawo sai ka ci." Babu muso ya miƙe tare da cewa "Oya tashi muje kar ki kafa min kuka da Magaribar nan." Ganin fita za su yi Mommy ta tsayar da su ta haɗo mata tea ta ce ta sha kafin su tafi, tana turo baki ta amshi tea ɗin ta soma sha tana yatsine fuska kamar tana cin sabulu sai hawaye take ita ala dole an matsa mata sai ta sha. Grandma ta kawar da kai ta ce "Ni Hauwa'u ban taɓa ganin sangartacciya irin wannan mai jiki a bushen ba, tashi ku tafi karki tara mana jama'a." Tashi ta yi tana mitar Grandma tana ce mata mai jiki a bushe, shi kuma ya goya mata baya yana faɗin "Yo Grandma ai irin jikinki ne Baby ta ɗauko, shi ne kike kushe ta." Ya yi maganar yana kama hannun Abir suka wuce daga palon. Grandma ta watsa musu daƙuwa ta shiga zagin Abdul, "koɗaɗɗan mazan koɗaɗɗan wofi, za ka ci butar ubanka tun da har kake haɗa ni da wannan shashashar yarinyar da kuka sangarta ta ta kasa gane ta girma, ni ba ƴar banza ba ce da zan tsaya ina kula ka mu taru mu lalace." Dariya Laraba ta yi tana daga bakin ƙofar kitchen sai cin karas take abin ta ta ce "Inna Wallahi kina da abin dariya wannan ai he ki sa mutum ya yi ciwon ciki, Alkur'an haka Innar Babana take sai masifa." Ta ƙarashe maganar tana ƙarasowa palon.. Sai da ta zauna sannan Grandma ta ce "Ke na ci ƙundun uwaki Laraba, ni kike ce wa ina masifa?" Sunkuyar da kai ta yi ƙasa sai kuma ta yi saurin kama ƙafafuwan Grandma ta soma matsa mata jin tana sauke mata ruwan zagi, ai kuwa Grandma ta yi shuru tana lumshe idanu jin yadda Laraba ke matsa mata ƙafa gwanin daɗi. "Allah ya miki albarka Laraba ta bawa." Washe baki Laraba ta yi jin ana sa mata albarka.. Suna isa Asibiti ana kiran Sallar isha'i, hakan yasa Abdul cewa "Baby muje ciki kafin a gama duba ki na dawo daga Sallah. " Ɓata fuska ta yi ta ɗago za ta masa magana suka haɗa idanu ta yi saurin kawar da kanta, ɗaure fuska ya yi ya ce "To meye na wani haɗe rai bayan Asibitin ba baƙuwar ki ba ce?" Cuno baki gaba ta yi tana matso hawayen dole ta ce "Yaya ni tsoro nake ji don Allah karka tafi ka barni a nan, ka bari in mun je gida sai mu yi kawai. Wancan lokacin ma ai daga kawoni Asibitin da ka yi ba ku sake ganina ba." Ta ƙarashe maganar ta na ƙara matso hawaye suka zuba kan kincinta, ji take ba za ta iya zama ko da na sakan ɗaya ne babu shi a kusa da ita ba. Bai ce da ita komai ba ya fito ya zagayo ya buɗe mata ta fito, ciki suka nifa inda daret suka nufi wata ƙofa, suna isa Abdul ya kwankwasa ƙofar aka ba su izinin shiga suka sa kai ciki. Da Sallama suka shiga inda suka samu Doctor zaune yana duba wasu takardu, ɗago da kai ya yi sai kuma ya riƙe baki cike da mamaki ya ce "A a wa nake gani kamar Mr Abdul Maitama da Ƙanwarsa?" Murmushin gefen baki Abdul ya yi ya ce "Mu ne dai ni da Ƙanwata." Wajan zama ya nuna musu suka zauna ya ba shi hannu suka gaisa sannan ya kuma cewa "Kai amma na yi farin cikin ganin Abir, 'yan kidnapping ɗin da suka sace ta ne suka sako ta ko jami'an tsaro suka kwato ta?" Hade fuska Abdul ya yi jin ya soma jero musu tambaya daga zuwan su ya ce "Kai fa kana da matsala Hashim ya daga zuwan mu za ka tsare mu da tambaya?" Ya faɗa yana hararar shi. Sanin halin Abdul ya sa Doctor Hashim ya canza maganar, ganin zai ɓata musu lokaci yasa Abdul cewa "Ka kira a duba ta ta ji ciwo ne." "Kawai ka bari ni duba ta mana." Wani irin kallo Abdul ya watso masa kamar zai kai masa duka ya rufe shi da masifa "Ko da wasa na kawo Baby Asibiti ka bari wani ƙato ya taɓa koda yatsar hannunta ne sai na karya masa muƙa-muƙi, Ƙanwar tawa za ka ce wai na bari ka duba ta?" Ganin ya harzuƙa yasa Doctor Hashim yin dariya ya ce "Mayar da wuƙaƙen dama tsokanar ka nake." Tsaki ya ja yana harɗe hannayensa bisa ƙirji. Ita kuwa lamso ta yi lakwas a gefen shi tana bin su da kallo har suka gama ba ta ce musu uffan ba. Waya ya ɗauka ya kira wata Nurse ya ce ta zo sannan ya kashe. Ba a fi minti ɗaya ba sai ga ta ta shigo tare da rusunawa ta ce "Sir gani." Nuna mata Abir ya yi ya ce ta je ta duba ta, cikin girmamawa ta amsa sannan ta ce Abir ta tashi su tafi a duba ta. Har sun juya ta fisge hannunta ta dawo wajan shi tana yin raurau da idanu, ganin haka yasa ya kamo ta ya zaunar murya a ƙasa ya ce "What happening my Babyn Yaya?" Hawayen da ta matso su tun a mota ne suka ƙara cika mata idanu, ganin ba za ta yi magana ba sai ya sa hannu ya goge mata hawayen cikin nuna kularsa a kanta ya ce "Baby ba fa komai za a miki ba ki je." Sai a lokacin ta buɗe baki cikin rawar murya ta ce 'Ya... Ya... Ni dai kar ka tafi ka barni." Kumatunta ya shafo ya mikar da ita tsaye ya ce "Salla kawai zan yi." Ya faɗa yana kallon ta cikin idanu.. Ba dan ta so ta bi bayan Nurse ɗin suak nufi ƙofar fita Abdul ya dakatar da su ta hanya kiran sunanta suka waigo a tare, ya ce "Ki kula da ita zan je na yi Sallah minti goma zan dawo." OK ta ce sannan suka wuce, suna fita shi da Doctor Hashim suka fita zuwa Masallaci.. Bayan an gama duba jikinta an tabbatar ba ta samu targaɗe ba ciwo ne kawai waje ke mata, hakan yasa suka rubuta mata wani pharmacy na maganin zafin take shafa wa a wajan.. Minti 20 cif Abdul bai dawo ba hakan yasa Abir ce wa Nurse za ta je mota ta jira shi kawai, ba dan ta so ba ta fita. A hanya suka haɗu da shi suka wuce mota sai gida... Suna tafiya a hanya danger ta tsayar da su, kamar an ce ta kalli gefe ta gan shi tsaye a bakin hanya yana son wucewa, sai ya tafo kamar zai wuce sai kuma ya dawo baya a guje yana dariya. Zuge madubi ta yi ta leƙo da kanta ai kuwa suka haɗa idanu, wata irin faɗuwar gaba ce ta ziyarce ta har sai da ta dafe ƙirji tana ƙura masa idanu, ji ta yi tana son masa magana amma kuma bakinta ya mata nauyi ta kasa furta ko da kalma ɗaya ce ga shi ba ta san sunan shi ba bare ta kira shi. Rufe idanunta ta yi ta buɗe sai ta ga wayam ba kowa a wajan, ƙara leƙowa ta yi ko za ta gan shi amma ba shi ba alamar sa haka ta dawo ta zauna tana mamakin ganin shi a wannan wajan. Danger na ba da hannu suka wuce Abdul ya juyo ya kalle ta ya ce "Baby are you OK?" Kai kawai ta ɗaga masa zuciyarta na ƙara tausayin shi da halin da yake ciki, ba ta san wani irin yanayi take ji ba game da wannan Mahaukacin da ya ceci rayuwarta... Tsaye yake a cikin palo ya juya baya waya kare a kunnen shi sai faɗa yake kamar zai ari baki. "Amma Wallahi Goje ka bani mamaki, yanzu ashe yarinya ƙwaya ɗaya tal ta gagare ku har ta samu hanyar da ta gudu ta kuɓuce daga hannunku? Mun yi da ku cewa yau ne ranar da zan je na aiwatar da aikina a kanta amma sakacin ku yasa ta gudu." Daga cikin wayar aka shiga ba shi haƙuri. "Sorry Oga Wallahi yarinyar nan gudun bala'i ne da ita, duk da hannayenta a ɗaure suke amma ba ka ga yadda ta dinga gudu ba kamar barbela. A labarin da Dagus ya bani ya ce wani Mahaukaci ne ya cece ta daga wajan su." "Dalla yi min shuru suna ƙarti majiya ƙarfin har wani Mahaukaci zai gagare su, to na ba ku nan da sati ɗaya duk inda yarinyar nan ta shiga ku kawo min ita nan." "Dama Oga ai lefin ka ne, kai ka ce mu bar mata wannan maganin da yake wajan ta, sannan ka ce kar mu kunna sigari a inda take dan ba ka so ciwon ta ya tashi kana so ka same ta garau, yanzu ga shi ta fe ce." "To na dai faɗa muku ku nemo mafita in ba haka ba za ku ga mai zan yi a kanku." Yana gama faɗin haka ya cillar da wayar kan kujera ya nufi wata ƙofa..... _*Maman Nusaiba*_ [10/25, 3:35 Yamma] My Addatyna: ~_*A HAKA NAKE SON SHI*_~ Daga Alƙalamin _*Sarat Alƙasum ~(Maman Nusaiba)~*_ _🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_ Littafin na kuɗi ne nomal ~N~ 300 ne vip ~N~ 500. Ga masu buƙatar Littafin ki neme ni ta wannan number. _🥏+966577675904_ *بسم الله الرحمن الرحيم* Shafi na (4) Tallah !! Tallah !! Shahararriyar Marubuciyar nan Ikilima Adam (kyauta daga Allah) wacce ta nishadantar daku a littafin ta mai suna *Kanwata* *kaikajawa kanka , Rai daya janzaki, yau na sake dawowa domin muku Domin tallata muku Littafaina mai Suna *(RUDANI )* Da kuma *Makauniyar Shari'a* littafine mai kunshe da Butulci , cin amana ,zagon Kasa , soyayya irin ta gani kasheni , aminci da saura n su basai n'a cika Ku da surutu ba Hausawa sukace Gani yakori ji. Karku Manta *Makauniyar Shari'a* sabon littafi ne mai bibiyar Ma'anar sunan sa. RUDANI littafine mai cike da Rudani da ban Al'ajabi , duk wacce kika fi buƙata zaki biya kudin sa Naira ɗari biyar kacal. Farashin kowannen su Naira Dari biyar ne 500 kacal Domin Karin bayani Ku tuntubeni a lambata kamar haka (09069080725 ko Kuma + 22953726162 ) wacce Bata shirya Siya ba kada mu batawa juna lokaci. Domin aikawa da kudi kai tsaye . 3115484026 ikilima Adam first bank Turo shaidar biya akan wannan 09069080725 sai najiku. Tun da Abir ta dawo Asibiti shiga ɗakinta babu abin da take sai kuka da hasaso abubuwan da ta gani a wannan ɓakin gida, sosai tsoro da tashin hankali yake kawo wa zuciyarta ziyara yadda suke azabtar da mutane kamar ba su da zuciya a ƙirjinsu. Dan ita a yadda take ganin suna aikata mugun lefin nan tunani take ko an cire musu zuciyoyinsu daga cikin ƙirji ne? , ai ko da wataran ba su ji tausayin mutum in za su cutar da shi ba to fa wata rana za su ji tausayin mutum inda da kawai zuciyar a gangar jikinsu. Ajiyar zuciya ta sauke tare da zama a bakin gado tana dafe kanta jin yadda yake sara mata kamar zai rabe gida biyu, lumshe idanu ta yi zuciyarta na mata zafi in ta tuna alƙawarin da ta ɗauka. Jin ciwon kan na ƙaruwa yasa ta sauke hannayenta daga kan ta kalli ledar maganin da ta yi wulli da ita, tun da dai ta ji sauƙin ciwon jikinta ba ta waiwayi ledar ba har lokacin shan na safe ya wuce ga na yamma ya zo shi ma ba ta sha ba, a hankali ta ɗan muskuta ta janyo ledar maganin ta ɓalli ƙwaya biyu ta zuba a baki, gorar ruwan da ke kusa da ita ta ɗauka sai ta ga ba ruwa a ciki. Miƙewa ta yi ta isa gaban ƴar ƙaramar freezer dake gaba da gadonta ta buɗe ta ɗauko gorar ruwa mai mugun sanyi. Jin yadda ruwan ya yi sanyi har ba ta san lokacin da ta haɗiye yawu ba , dan ita ma'abociyar son ruwan sanyi ce indai ruwa ba sanyi to fa ba za ta sha shi ba duk ƙishirwar da take ji sai dai ta haƙura. Ko Makaranta za ta je sai ta cika wata gora mai girma ta zuba ƙanƙanra mai yawa a cikin ruwan dan kar ma ya huce, kaɗan daga cikin halinta da yake bai wa Abdul takaice, ya yi faɗan har ya gaji ya barta ga kafiya akan abu indai ta ce sai ta yi abu to ba mai hanata yi sai dai a zuba mata ido kawai. Gorar ta kafa a baki ta sha maganin, sai da ta kusa shanye ruwan dake gorar sannan ta janye tana mayar da numfashi jin yadda sanyin ruwan ke ratsa ta. Komawa ta yi kan gadon ta zauna ta laliba kan gadon da zimmar janyo wayarta ta ji wayam, dafe goshi ta yi tunawa da wayar na can a hannun waɗanda suka sace ta, dafe kai ta yi tana mai jin zafin rasa wayarta ta. Kwankwasa ƙofar aka yi ta ɗago da kai tana kallon ƙofar, sai da ta ji an kuma bugawa sannan ta ce "Shigo." Shigowa Mommy ta yi Laraba na biye da ita, a ƙasa ta aje trey abincin tare sosa kai tana buga kan nata alamar ƙwarƙwata ta dame ta da cizo, ganin Abir yasa ta durƙusa har ƙasa tana washe baki ta ce "Madam sannu da hutawa, Alkur'anin Allah kina kama da wata mace da muka gani a TV gidan Sule a ƙauyenmu." Murmushi Abir ta yi jin yadda Laraba ke rattaɓo bayani, ganin kuma ba ta daina susar ƙwarƙwatar ba ya sa ta miƙe ta shige toilet, can sai ga ta ta fito hannunta ɗauke da shampoon kai ta miƙa wa Laraba ta ce "Laraba kike ko?" Da sauri Laraba ta ce " E Madam sunana Laraba amma sunan da aka yanka min rago da shi Shafa'atu ne, Innarmu ce take wani kirana da Laraba wai ni ce mace ta farko a wajan ta shi ya sa take min kara, ni kuma hauhi nake ji kawai dai kar na ce bana son sunan ta ce na mata rahin kunya." Ta ƙarashe maganar tana ɗaure fuska kamar tana gaban Innarta ta. Murmushi ta yi ta dawo bakin gadon ta zauna sannan ta ce "To ki yi haƙuri da hakan, wannan idan kika tashi da safe ki shiga banɗaki ki wanke kanki da shi, haka in dare ya yi ki dinga wanke kan kafin ki kwanta. " Godiya ta dinga jero mata tana washe baki ita ma za ta wanke kai da sabulun 'yan gayu sannan ta fita. Zama suka yi a bakin gadon Mommy ta ce "Abir Grandma fa na jiran ki a waje sun ce za su yi magana da ke akan lamarin nan." Dam ta ji gabanta ya faɗi ta zaro idanu tare da dafe ƙirji tana kallon Mommy, ita da ta yi alƙawarin ba za ta faɗi komai ba ya za ta yi da wannan meeting ɗin da aka shirya saboda maganar? Idan kuma ta faɗa ɗin kenan ta ƙarya alƙawari? Sannan za su iya aiwatar da abin da suka faɗa mata in ta faɗi wani abu game da wannan ɓakin gidan?. Tambayoyi ne suka dinga ziyartar masarrafarta ɗaya bayan ɗaya hakan yasa ta runtse idanu tana neman hanyar da za ta rusa wannan meeting ɗin, buɗe idanuwanta ta yi wanda suke cike da rauni da kuma tsananin tsoron abin da zai biyo baya ta dubi Mommy ta ce "Mommy to me ake so na yi bayan kuma ba na jin daɗin jikina?" Karantar yanayin da ta shiga saboda maganar yasa Mommy ta ji gabanta ya bada ras! Tana tunanin kar dai abin da take tunani game da 'yarta ta tilo ne ya faru da ita? Girgiza kai ta yi tana kawar da wannan mummunan tunanin ta miƙe tsaye ta nufi ƙofar fita tana jaddada mata ta yi ta fito.. shuru ta yi tana juya maganar da ke cikin zuciyarta, dafe kai ta yi gabaɗaya ji take kamar ta fasa ihu dan ba ta son taron nan, a sanyaye ta tashi daga kan gadon ta cire rigar da ke jikinta ta saka riga da sket, kwamtaccan gashinta mai santsi yana sheƙi ya bayayna, warware bakkilar ta yi ta sake ɗaurewa. Sanin halin Yayan nata yasa ta ɗauko hijabi har ƙasa ta saka tana kumbura baki ba dan ta so ba ta fita cikin mutuwar jiki da raunin zuciya hadi da tausayin kanta ta isa palon. Dukkan su sun hallara a palon Abba da Daddy kowanne da matarsa, sai Mommy dake kusa da Grandma Abdul na gefen ta, sauran 'yan gidan duk suna ƙasa kan capet zaune suna jiran fitowar ta. Waje ta samu a kusa da ƙafar Grandma ta zauna kanta a ƙasa ta ce "Abba gani." Gyara zama Abba ya yi cikin nutsuwa ya soma tambayarta. "Mamana su waye suka sace ki? Kuma da suka ɗauke ki me suka miki a can ɗin ke da Ibrahim? Sannan ina shi Ibrahim ɗin yake?" Wani irin raunataccan kuka ne ya kubce mata wanda ta yi iya kar bakin ƙoƙarin ganin ba ta yi kukan ba amma hakan ya custura sai ta ta fashe da kuka mai tsuma zuciya. Kuka take sosai babu wanda ya hana ta kuma babu wanda ya rarrashe ta har sai ta yi mai isarta sannan ta tsagaita kuka tana shashsheka tare da ɗago da kanta, idanuwanta da suka tashi daga farare suka koma jajur ta kai tafukan hannayenta ta rufe fuska ta kuma sakin wani kukan abin da ya tayar wa da su Abba hankali. Cikin kiɗima Abba ya ce "Z... Zo nan Mamana." Da rarrafe ta ƙaraso inda Abba ke zaune ya nuna mata gefen shi, zama ta yi tana ci gaba da kukan tana murza idanu. Hannu yasa ya kwanto da kanta kan ciyarsa ya shiga shafa kanta zuciyarsa na bugawa, kukan da take duk ya tada masa hankali so yake ya ji shin ina ɗan'uwansa yake? Bayan ta lafa kuka ne Mami ta taɓa baki tana turo da ɗaurin ɗankwalinta gaban goshi ta harari Abir, gabaɗaya ta tsani yarinyar daga ita har mahaifiyarta ganin yadda kowa na family su yake so da ƙaunar su. Duk wanda ya zo gidan to a part ɗinta zai sauka komai sai ita , hakan yasa Mami ta tsane ta fiye kima kwata-kwata ba ta so ta ɗaga ido ta gan su a gidan. Tsaki ta ja cikin tsantsar tsana ta ce " Tsuww! Mu kun wani zo kun tara mu kamar wasu masu ɗaukan darasi a aji, ita kuma ta ɓare wa mutane baki tana kuka kamar a kanta aka fara kidnapping, ke kuka baya miki wahala ne?." Ta ƙarashe maganar tana kuma jan wani tsakin.. Jin haka yasa Mommy ta ce "Abir ki faɗa musu abin ya faru da ke, sannan ki faɗa ina Abbanki yake?" Tashi ta yi zaune ta sunkuyar da kanta ƙasa ta soma musu bayanin da ta san in ta yi ba za su aikata mummunan ƙudirin da suka ɗauka a kanta ba. "Abba ni ai na ɗauka Abie ya tafi Niger ne wajan kasuwancinsa, kenan bai dawo ba?" Wata irin zufa ce ta shiga tsastsafo wa Abba, Daddy, Mommy, Grandma, Abdul. Cikin tashin hankali Abba ya ce "Mamana ki faɗa mana duk abin da kika gani dan mu tun da kuka yi tafiyar nan ba mu taɓa jin labarin ku ba, mun yi cigiyar har mun gaji da nema mun fauwala wa Ubangiji." Jinjina kai ta yi ta goge hawayen da ya silalo daga kwarmin idanuwanta sannan ta ce" Ni fa Abba ban san komai ba, kawai zan iya tuna cewa ni da Abie muna mota daga wata ruga da na raka shi ya sayo shanu. To muna cikin tafiya ne mun zo tsakiyar wani jeji wasu maza suka dinga saukowa daga kan bishiya suna nuna mu da bindiga. Suka ce mu ba su kuɗin hannunmu Abie duk ya rikice ya fito da kuɗinsa dake aljihu ya ba su, amma ba su haƙura ba suka ce sai sun bincike motarmu ko akwai wani abu mun ɓoye. A bayan motar Abie suka ɗauko wata jaka mai girma wadda shaƙe take da kuɗin da ya ɗauko daren ranar da za mu yi tafiya daga banki, ya ce min zai sa hannun jari ne a wani company dake nan Yola, shi ne suka ɗauko kuɗin suka buɗe suka ga tabbas kuɗi ne a ciki. Abie ya roƙe su da su bar mu mu tafi tun da sun ɗauki kuɗin, amma suka ce sam ba za mu tafi ba ƙarshe ma wani a cikin su ya harbi Abie a ƙafa ganin haka yasa na kurma ihu neman taimako amma ba mai ji na. Kafin na kuma na biyu ni ma suka buga min wani abu a kaina, tun daga nan ban san komai ba sai shekaranjiya na farka na ganni a ɗaure. Ganin mai gadina yana bacci yasa na yunƙura da ƙyar na tashi tsaye saboda sun ɗaure min hannu ta baya bakina ma sun manna min gam, a hankali na samu na gudu daga gidan ina Addu'ar kar su ganni ashe sun gannin suka biyoni." Nan ta basu labarin yadda Mahaukaci ya ceci rayuwarta a lokacin da suke neman keta mata mutumci, tana dasa aya a maganarta ta fashe da kuka wiwi tare da faɗa wa jikin Abba.. Salati duk suka ɗauka masu kuka na yi masu tagumi na yi, Abba da Daddy su kan su sai da suka zubar da hawaye. Abir ta ɗago ta ce "Abba kenan kuna nufin Abiena bai zo gida ba?" Da ƙyar ya saita kan shi ya ce "Ki yi haƙuri Mamana tabbas bai zo gida ba, sai dai mu yi addu'a Allah ya kubuto shi daga mugun hannun da yake ciki, zan sa Abdul ya sanar da abokan aikinsa dawowar ki gida su ƙara tsananta bincike ko za aci sa'a mu san halin da yake ciki." Hankalin Abir ya ƙara tashi fiye da wanda take ciki, wani irin zafi take jin zuciyarta na mata wanda har yawun dake cikin bakinta ya ƙafe. Da gudu ta tashi ta bar palo ta nufi ɗakinta jiki na rawa, Abdul ya bi bayanta Mami ta raka shi da harara aka yi sa'a Mommy ta ɗago ta ga kallon da Mami ke yi wa Abdul, girgiza kai kawai ta yi ta rafka tagumi. Shin a ina mijinta yake? Yana raye ko yana mace? Tambayar da ba ta da mai ba ta amsa, ta numfasa tana zubar da hawayen tausayin ƴarta da rashin sanin halin da mijinta yake ciki.. Sharce hawaye Grandma ta yi duk jikinta sai rawa yake, da ƙyar ta iya saita kanta ta dube su ta ce "Salmanu ka faɗa wa Abdullahi ya ƙara tsananta bincike su kwato min shi daga hannunsu." Ta yi maganar tana kuma goge hawaye. Abba ya ce kowa ya tashi ya tafi ya rage daga Abba sai Daddy sai Mommy sai Grandma, ya gyara zama ya ce "Inna ki kwantar da hankalinki, in sha Allah Yaya Ibrahim zai fito ya dawo gida lafiya." "Kayya! Kana ji fa wannan bushashiyar ta ce an harbe shi a ƙafa, yanzu ba mu san a wani hali yake ciki ba. Gardama ce irin da Ibrahimu na faɗa masa ya daina fita shi kaɗai batare da masu tsaron lafiyarsa ba, amma fir ya ƙi su bi shi rabon wannan ƙaddarar ne za ta faru da shi, ni dai don Allah ka ƙara jadadda wa Abdullahi su nemo min inda yake." Ta ƙarashe maganar tana face majina. Haka ya shiga kwantar mata da hankali shi da Daddy, ita ma Mommy suna kwantar mata hankali, ita kuma ta ce in sha Allah zai dawo gida. Ta faɗi haka ne dan kar ta nuna damuwarta a fili Grandma ta fita shiga tashin hankali.. Ko da ta shiga ɗaki kan gado ta faɗa tana rera kukan kaddarorin da suka faruwa da ita, yanzu kenan ba a san inda Abie ɗinta yake? Tsagaita kukan ta yi jin an rufo ƙofar, harɗe hannayensa ya yi ya tsaya daga bakin ƙofar yana bin ta da wani irin kallo, tausayinta ya mamaye masa zuciya duk ta bi ta firgice ga ta ita dama ba wani jiki ba duk ƙashin jikinta ya firfito, takowa ya yi a nutse ya iso bakin gadon ya tsaya.. Ɗago kai ta yi ta kalle shi idanunta na tsiyayar da hawaye, hannu ya buɗe mata ta tashi da sauri ta faɗa jikinsa tana shashshekar kuka, juyawa ya yi ya zauna a bakin gadon tana maƙale a jikinsa ya shiga shafa bayanta har yanzu ya kasa ce mata komai. Sai da ya ji ta daina kukan ya ɗago fuskarta da ta yi sharkaf da hawaye ya sa hannu ya shiga goge mata, cikin kasalalliyar murya ya ce "Baby am so sorry kin ji." Lamo ta yi a faffaɗan ƙirjinsa tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da sauri-sauri, dogon numfashi ta ja ta ƙara rungume shi tana saɓa baki. Ƙura mata idanu ya yi yana shafa gashin kanta, ganin tana mutsu-mutsu ya miƙo bakinsa saitin kunnenta ya shiga yi mata ƙira'ar suratul baƙara cikin daddadar muryarsa, lumshe idanu ta yi tana jin yadda sautin muryasa ke ratsa ko'ina na jikinta har bacci ya kwashe ta.. Sai da ya tabbatar baccin ta ya yi nisa sannan ya zame mata hijabin ya kwantar da ita, bargo ya jamyo ya rufe ta tare da ƙara tofe ta da addu'a sannan ya miƙe tsaye, ya jima a tsaye yana kallon yadda take sauke numfashi sannan ya fita.. Daren ranar haka Mommy, , Abba, Daddy, Abdul, Grandma, da sauran su wasu na gidan ba wanda ya runtsa. Ita ka Abir ta samu bace duk da tana yi tana farkawa.. Washegari Abir tana cikin shiryawa Fatima ta shigo ɗakin, cikin sanyin jiki ta ce" Anty Abir wai Yaya Salim ya ce ki je ya kaiki Asibitin." Ba ta juyo ta kalle ta ba ta kuma amsa mata ba har sai da ta gama saka ɗankunne sannan ta juyo ta ce "Ki ce masa ina nan zuwa." Ganin ba ta zauna yasa ba Fatima ta riƙe baki ta ce "Anty juyo na ga kwalliyar mana." Juyowa ta yi tare da aro murmushin yaƙe ta ɗaura bisa fuskarta, ta saka mayafi da takalmi haɗi da jaka duk tana kallon ta sannan ta ce "To tashi mu tafi." Ba muso ta tashi suka jera a tare suka fito zuwa palo, inda suka samu Mommy ita ma na shirin barin palon jikinta sanye da hijabi. "A a! Mommy ina kuma za ki je?" Cewar Abir tana ƙare mata kallo. "Gidan Baba Malam zan je na duba shi da jiki, ba shi da lafiya tun kwana uku da suka wuce kuma na sanar da shi Allah ya kubto da ke." Ta faɗa tana yin gaba. OK kawai Abir ta faɗa ba ta kuma cewa komai ba har Mommy ta fita a palon. Juyowa ta yi za ta yi wa Fatima magana sai ta ga wayam ba kowa, taɓe baki ta yi ta nufi part ɗin Umma wajan Salim. Har ta kusa ficewa a palon ko me ta tuna sai ta dawo ta nufi ɗakin Grandma, tura ƙofar ta yi bakinta ɗauke da sallama. Sallamar tata ce ta maƙale sakamakon ganin Fatima da ta yi a durkushe a gaban drower Grandma ta fito da kayan ciki waje, sosai abin ya mata mamaki. A razane Fatima ta yi saurin kai kallon ta bakin ƙofar nan-da-nan tsoro ya cika mata zuciya ganin kallon da Abir ke mata. Cikin in'ina ta ce " Am dama da... Ɗaga mata hannu ta yi kafin ta yi magana ta tari numfashinta ta ce "Grandma ce ta ce na gyara mata kayanta duk sun hargice, to shi ya sa ma kika ga na bar ki a palo na shigo ɗakin." Ta faɗa tana ƙifƙifta idanu. "Ok to ina Grandma ɗin?" Ta tambaye ta cike da tuhuma dan ita a iya rayuwarta ba ta taɓa ganin Grandma ta sa Fatima aikin ɗakinta ba. "Sun tafi Station ita da Abba da Yaya Abdul ta ce da ita zai je ba za ta bari a barta ba sai an tafi da ita, shi ne Abba ya ce Abdul ya kai su." "Ok." Iya abin da ta iya faɗa ta tsaya tana mata kallon ita fa take jira, ganin haka yasa Fatima durƙusawa cikin hanzari da kuzarinta ta ɗauke kayan da ta fito da su wanda suke a wanke a goge tsaf ta jera a drower. Ganin ta gama Abir ta juya ta fita hakan ya ba wa Fatima damar ɗauko ambulan ɗin da ta ɗauko tun farkon buɗe drower, rigarta ta ɗaga ta soka ta a mara ta yi saurin barin ɗakin tana murmushi.. Salim da ya gaji da jira ya kira Abir ya ce yana harabar gidan ta yi maza ta fito, ta amsa da to ta fita ta same shi a mota suka bar gidan.. Shagon sayar da waya suka fara zuwa suka taya waya ta sa yi iPhone sannan suka isa Asibiti... Suna zuwa Salim ya aje ta ya ce in an gama mata ta kira shi zai je su gaisa da abokin shi ta amsa da to. Ba ta wani ɗauki lokaci ba ta amshi maganin da ta saba amsa duk ƙarshen wata na asma ta fito. Ta daɗe tana jiran Salim bai zo ba ta buɗe sabuwar wayarta ta saka sim ta kira shi ya ce ga shi nan zuwa amma shuru, wayar ta shiga tana dudduba cikin ta sako ya shigo wayar abin da ya ba ta mamaki matuƙa, saboda sim ɗin nata special number ce ba kowa ya san tana da number ba. Buɗe sakon ta yi ta soma karantawa. _"Wato ke mai kunnan ƙashi ce ko? Kin yi alƙawari amma kika karya kin manta sharadin mu da ke?"_ Da sauri ta miƙe tsaye ta nufi hanyar fita daga Asibitin saboda kiɗimewa ba ta san ta fita daga Asibitin gabaɗaya ba sai da ta ji ƙaran motoci na wucewa ta gane ta fito a waje take. Waige-waige ta dinga yi hagu da dama ai kuwa ta ga wasu maza biyu na kallon ta, da gudu ta nufi hanyar komawa cikin Asibitin sai ji ta yi ta yi karo da wani abu ta faɗi Tim!.... Littafin nan dai na kuɗi ne my sister. _Taku har kullum Maman Nusaiba ce_ [6/20, 7:26 PM] Ummu Amjad: [10/25, 3:35 Yamma] My Addatyna: ~_*A HAKA NAKE SON SHI*_~ Daga Alƙalamin _*Sarat Alƙasum ~(Maman Nusaiba)~*_ _🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_ _+966577675904_ *بسم الله الرحمن الرحيم* Shafi na biyar (5) Tallah !! Tallah !! Shahararriyar Marubuciyar nan Ikilima Adam (kyauta daga Allah) wacce ta nishadantar daku a littafin ta mai suna *Kanwata* *kaikajawa kanka , Rai daya janzaki, yau na sake dawowa domin muku Domin tallata muku Littafaina mai Suna *(RUDANI )* Da kuma *Makauniyar Shari'a* littafine mai kunshe da Butulci , cin amana ,zagon Kasa , soyayya irin ta gani kasheni , aminci da saura n su basai n'a cika Ku da surutu ba Hausawa sukace Gani yakori ji. Karku Manta *Makauniyar Shari'a* sabon littafi ne mai bibiyar Ma'anar sunan sa. RUDANI littafine mai cike da Rudani da ban Al'ajabi , duk wacce kika fi buƙata zaki biya kudin sa Naira ɗari biyar kacal. Farashin kowannen su Naira Dari biyar ne 500 kacal Domin Karin bayani Ku tuntubeni a lambata kamar haka (09069080725 ko Kuma + 22953726162 ) wacce Bata shirya Siya ba kada mu batawa juna lokaci. Domin aikawa da kudi kai tsaye . 3115484026 ikilima Adam first bank Turo shaidar biya akan wannan 09069080725 sai najiku. A kiɗime ta yunƙura cikin kuzarin da ba ta san tana da shi ba ta miƙe tsaye, ba ta ma tsaya ganin abin da ta ci karo da shi ba ta nufi ƙofar Asibiti da gudu sai dai kafin ta isa ta ga an sha gaban ta, ware dara-daran idanuwanta ta yi a kan ɓakar ƙafarsa wadda taɓo da ƙura suka mata fenti, saurin kallon shi ta yi gabanta na faɗuwa kamar yadda shi ma ita ɗin yake kallo.. Kamar kullum yau ma sanye yake da gaggayen wandonsa wanda tun farkon haɗuwar su ta gan shi da shi, ƙafarsa ba takalmi haka yake yawo, riga biyar ce a jikinsa ɗaya kan ɗaya kowacce ta yi mugun yin dauɗa. Wani irin sanyi ne ya ziyarci zuciyarta har ba ta san lokacin da ta saki murmushi ba ta gyara tsayuwarta tare da lumshe idanu, buɗe idanuwanta ta yi ta juya bayan ta suka haɗa idanu da mazan nan har yanzu suna inda suke a tsaye sai daddana waya suke lokaci zuwa lokaci suna kallon agogon dake hannunsu.. Ganin ta juya tana kallon su ya yi saurin sunkuyawa ya ɗauki sandarsa ya sakala a kafaɗa tare da yin dariya ya shiga zagaye ta yana cika sadar a ƙasa, sai da ya dawo gaban ta ya ɓata fuska ya ce "Imm Anty tafiya kike yi?" Murmushi ta yi ganin yadda ya harɗe kamar ɗan fulani, ƙura mana idanu ta yi shi kuma ya dinga tambayarta ina za ta je amma ba ta ji mai yake faɗa ba dan ta yi nisa a kallon da take masa, sai da taɓa hannunta sannan ta yi firgigit ta saki murmushi ya kuma tambayar ta ce "A a ina jiran yayana ne." Ta faɗa tana dawowa gefen shi, haka kawai ta ji yau so take ta zauna da shi su yi hira duk da ta san ba ma zai gane inda maganarta za ta dosa ba.. Sauke sandar ya yi yana dariya ya shiga zagaye ta yana faɗin " Anty ta yi tafiya! Anty ta zauna! Anty ta miƙe!" Murmushi Abir ta yi jin yadda yake kiran ta da Anty har da waƙa abin sai ya ba ta nishadi, Jakarta dake riƙe a hannunta gam sakamakon tsoron da ta ji lokacin da za fito a razane ta buɗe ta ɗauko gorar ruwa mai sanyi ta miƙa masa, shi kuwa ya tsare ta da kallo idan ya kalle ta sai kuma ya kalli gorar. "Ga shi maza ka sha ruwa." Ta faɗa tana nuna masa ruwan. Amsa ya yi ya ɗaga gorar yana duddubawa yana faɗin "Allah sarki abokina kai ne haka? Ina kwana? Dama haka kake ban sani ba?" Ya faɗa yana shafa rubutun dake jikin gorar. Ƴar dariya ta yi ƙuncin da ke zuciyarta na yayewa, sosai ta shagala da kallon shi yana nuna mata gorar tare da tambayarta. "Anty ga abokina nan ya ce ki bani kayansa zan kai masa." To kawai ta ce masa ya ci gaba da surutai barkatai wata maganar ita kanta ba ta gane me yake nufi sai dai ta bi shi da to ko a a.. Duk da hankalinta ba a kwance yake ba amma haka take biye masa in ya yi magana ta amsa masa, juyowa ta kuma yi dan ta ga mazan nan ko suna nan sai ta ga wayam ba kowa. Ajiyar zuciya ta sauke ta dube shi ta ce "Ya sunanka wai?" Dariya ya mata ya ce "Ya sunanka zai ci abinci." Ya faɗa yana ɗaga gorar tare shafa bayan. Suna a haka sai ga motar Salim ta iso bakin Asibitin, da sauri ya fito ganin ta tsaye da Mahaukaci riƙe da makami, a ɗan naisa da su ya tsaya ya ce "Baby waye wannan ɗin?" Ya faɗa a tsorace. Murmushi ta yi ta ce "Shi ne wanda nake ba ku labari, kawai na fito ne na haɗu da shi." "Kwalalo idanu waje ya yi ganin yana kallon shi nan-da-nan tsoro ya cika masa zuciya, shi kuma kallon shi kawai yake yana dariya abin da ya ƙara tsoratar da Salim. Baki na rawa ya ce "To..To zo mu tafi gida." Kallon shi ta yi cikin wani irin yanayi, ji take kamar su ɗauki lokaci mai tsayi a haka tana hira da shi, sai da Salim ya sake maimaita maganar sannan ta rausayar da kai kamar za ta yi kuka ta ce" Sai an jima." Ta faɗa tana juyawa ta soma tafiya. Da sauri ya biyo ta ya ce "Anty abinci nan ci." Ya faɗa yana kama mayafinta yana marairaicewa kamar zai sa mata kuka. Ita kuma sai ta ji wani irin abu ya soki zuciyarta ta ji ba za ta iya tafiya ta bar shi ba. Kallon Salim ta ya yi sai ya ce "Baby bari na sayo masa abincin." Girgiza kai ta yi ta ce "Yaya don Allah taimako nake so ka min." Ta faɗa tana narkar da murya. "Indai ba a kan wannan Mahaukacin ba ne zan taimaka, amma in dai akan shi ne ba ma zan iya ba." Ya faɗa yana haɗe rai. Saurin kallon shi ta yi cikin rashin sanin abin yi ta ce "Don girman Allah Yaya mu ɗauke shi a kai shi Asibiti, duba ka ga yadda kayan jikin shi suke fa, ina so na taimake shi kamar yadda ya taimake ni." Ta faɗa tana goge hawayen da ya zubo mata. "Wallahi ba zan ɗauki Mahaukaci a cikin motata ba, so kike ya kashe mu gabaɗaya? Ke wai ma meye damuwarki a kan wannan Mahaukacin wanda bai san kansa ba bare ya san abin da ya dace da shi ba?" Ya yi maganar yana nuna shi da yatsa. Hawaye ne suka cika mata ido murya na rawa ta ce "Don Allah fa Yaya Salim ka taimaka mu ɗauke shi a motar nan, ina so zan kula da shi na kai shi Asibiti ko Allah zai sa a dace ya samu lafiya, ka ga in na yi haka na samu lada kai ma kuma ka samu lada mai yawa na taimako." Ta faɗa tana durƙusawa a gaban shi ta kama ƙafafuwansa tana kuka. Duk wanda ya zo wucewa sai ya tsaya yana kallon su har wani da ya zo wucewa ganin tana kuka ta riƙe masa ƙafa ya tsaya, kallon Salim ya yi cikin nuna tausaya mata ya ce "Haba bawan Allah kai wani irin azzalumi ne? Ta ya yarinya za ta durƙasa a gabanka tana kuka, amma dan rashin sanin darajar mata ka kasa yi mata abin da take buƙata? Ni a gani na ko ba ka son ta bai kamata ka nuna ba ka son ta ba a gaban idanunta, don Allah ku samu waje ku zauna ku fahimci juna." Yana gama faɗin haka ya wucewar shi bai ma tsaya ya ji mai Salim ɗin zai faɗa masa ba. Shi kuwa Salim in ransa ya yi dubu yau Abir ta gama ɓata masa shi, ta zubar masa da mutumci har mutane na tsayawa su ce ya ci zarafin ta bayan ba su san akan Mahaukaci take wannan roƙon ba. A fusace ya ce "Kin san Allah in ba ki tashi ba muka tafi zan bar jin tausayin ba ki da lafiya na lafta miki mari a bakin titin nan, za ki tashi ko sai na miki duka?" Ya faɗa yana ɗaga murya. Idan akwai abin da Abir ke matuƙar tsoron ayi mata ya gigita mata rayuwa to bai wuce a mata tsawa ba, hakan yasa ta miƙe da sauri duk da tsoron da take ji amma ba ta fasa faɗin abin da take son faɗa ba. "Shi kenan kar ka taimaka min Yaya Salim, nasan yau da Yaya Abdul ne na nuna masa wanda ya ceci rayuwata na kuma nemi ya taimaka masa ba zai min wannan wulakancin ba, ni ce fa Ƙanwarka Yaya Salim ko ka manta ne?" Ta faɗa tana fashewa da kuka tare da rufe bakinta dan kar sautin kukan ya fito... Shi kuwa ganin tana kuka ya matso kusan Salim ya durkusa shi ma yana kuka kamar yadda ya ga tana yi, ganin ba ta fasa ba sai shi ya daina ya yi zunbur ya miƙe tsaye ya dubi Salim tare da ɗaga sandar da ke hannunsa ya ce "Kai ne kasa Anty kuka ko?" Ya faɗa yana ɗaga sandar zai sauke masa. Saurin miƙewa Abir ta yi ta shiga tsakanin su tana kallon shi sai ta girgiza masa kai, hakan yasa shi ma ya girgiza mata kai sai kuma ya sauke sandar ya ɓata fuska ya ce "Anty yunwa nake ji, wa ya dakeki Anty? Shi wannan ɗin waye?". Ya jero mata tambayoyi yana yin kamar zai faɗa jikinta. Salim da yake zare idanu ganin za a kassara shi ya ce "Baby mu tafi." Ko kula shi ba ta yi ba ta kalle shi ta ce "Kana jin yunwa ne?" Murmushi ya yi sai kuma ya dafe kafaɗarsa yana yarfa hannu ya ce "Anty ciwo nan yake." Ya faɗa yana narke mata fuska irin na ƙananan yara. Cikin tausayawa ta dinga jero masa sannu shi ma yana maimaita abin da ta faɗa sai kawai ta yi murmushi, Salim kuwa ya cika ya yi fam ganin ma ta manta da zaman sa a wajan sai biya Mahaukaci take suna shashanci, faɗa mata ya yi zai tafi ya bar ta a wajan, ita kuma ta kafe akan lalle dole sai sun tafi da Mahaukacin nan, shi kuma ya ce sam ba zai ɗauke shi ba ya shaƙe shi yana driving, ƙarshe ma ya shige mota ta biyo shi tana roƙon shi yaƙi kallon ta. Ɗago kai ta yi sai ta ga wayam ba kowa a wajan, cike da mamaki da al'ajabi ta ce "To ina ya tafi kuma?" "Tsuwwww! Dalla malama ki zo mu tafi kin tsaya kina ɓata min lokaci a banza saboda wani Mahaukaci. " Ya faɗa yana kunna motar. Ba dan ta so ba ta shiga amma gabaɗaya zuciyarta na can tunanin wajan da ya nufa, Salim kuwa ta gama ɓata masa rai dan haka bai ce mata uffan ba har suka iso gida. Ko packing bai gama yi ba ta ɓalle marfin motar ta fito da sauri ta nufi ciki su Maigadi na mata barka da zuwa amma ba wanda ta amsawa saboda kukan da take ta shige ciki... Grandma na zaune sai ganin ta ta yi ta shigo mayafi a hannu tana kuka, hakan yasa ta kwashi salati. "Muhammadu (S.a.w) ɗan Abdullahi jikan Abdulmuɗallibi ni Hauwa'u! Me zan gani haka ƴar nan?" Zama ta yi tana shashshekar kuka sai ga Salim ya shigo Abdul da Daddy da Abba na biye da shi, suma duk suka dinga tambayarta lafiya take kuka? Goge hawaye ta yi ta ce "Ba Yaya Salim ba ne." Da sauri Abdul ya kalli Salim fuska a haɗe ya ce "Me ka yi mata har ya saka ta kuka?" Tsaki ya ja ya samu waje ya zauna yana hura hanci bai ce komai ba, hakan yasa Abba girgiza kai ya ce "Mamana me ya faru?" "Ba shi ba ne na gan shi ya hana mu ɗauko shi." "Shi wa kenan?" Cewar Abba. Labarin komai ta ba su tana yi tana sharbe hawaye har da majina. Da sauri Abba ya kalli Salim ya ce "Amma Salim ka bani mamaki, madadin ka samu a kama maka shi in ya so ma tun da ba ka son a saka shi a motarka ka samu wata motar ka sako shi a kawo shi, sai kuma ka nuna kai ba za ka yi hakan ba. Duk da kun ce Mahaukaci ne ai za mu iya taimakawa a kai shi Asibiti ko ka manta shi ya ceceta?" Ya ƙarashe maganar cikin fushi. Daddy ya ce "Rabu da shashasha mana, wani lokacin kana abu kamar wanda bai waye ba Salim. Da ta faɗa ma haka ai za ka iya yi wa Abdul waya ya kira yaran shi su zo su ɗauke shi, amma sai ka hau faɗa." Shi ko Abdul bai ce komai ba ganin iyayen nasu sun yi magana, amma tabbas yau ya tabbatar da Salim ba shi da tausayi ya saka ta kuka, wanda yake da yaƙinin sai ta yi ciwon kai ganin yadda idanunta suka yi jajur. Lumshe idanu ya yi yana jin ba daɗi sautin kukanta yake ji har ƙasan zuciyarta, ji yake kamar ya je ya rumgume ta ya rarrashe ta ko ta daina kukan, amma kuma ba zai iya ba tun da su Abba suna wajan.. Ana haka sai ga Mami da Umma sun kawo wa Grandma abincin rana kowacce da mai aikinta dauke da abincin sun sha ado, suklna isowa suka aje abincin suka gaishe su Abba sannan suka fita.. "To me ake tattaunawa ne haka na ga duk ranku a ɓace?" Cewar Umma tana zama kusa da Daddy. Ammi ta taɓe baki ta ce "Kin san dai tatsuniyar gizo ba za ta wuce ta ƙoƙi ba." Jin haka yasa Salim kallon Mami ya shiga faɗa mata abin da ya faru, ta riƙe baki tare da kallon Daddy ta ta yi mitsin-mitsin da idanu cikin masifa ta ce "Ai ban san ba kuna ɓakin ciki da ɗana Salim sai yau, ashe haka kuka tsane shi? Taya zai ɗauko rikakken Mahaukaci a motarsa ya je ya kashe min shi ko ya masa illa? To Allah ko da wasa wani abu ya faru da Salim sai na ɗauki mataki a kanku musamman kai wannan mai suffar kwartayen." Ta faɗa tana nuna Abdul, shi kuma ya yi saurin sunkuyar da kai.. Cikin jin zafin maganar Umma ta zaburo ta ce "Ke Farida kike ko fari? To Wallahi hawauniyarki ta kiyayi ramata! Idan kina cin ƙasa,ki kiyayi ta shuri na faɗa miki. Ko kusa kar ki ƙara alakanta mini ɗa da mummunar kalmar kwarto, kin yi na farko kin yi na ƙarshe Wallahi in kika sake faɗa sai na miki abin da har ki mutu ba za ki manta ba." Ta faɗa tana huci. Kallon banza Mami ta yi wa Umma tana karkada ƙafa ta ce "Òk dukana za ki yi in na sake faɗa? Kamar ke kika haife shi har kike wani hayayyako min ke ga uwarsa ko? To an ce masa mai suffar kwartaye." Ta faɗa tana hararar ta. Umma na shirin yin magana suka ga Maigadi afujajan ya faɗo palon yana zare idanu, a harzuƙe Mami ta ce "To mitsiyaci me ya shigo da kai nan?" Maigadi ya ce..... 🥏 *WhatsApp number* +966577675904 _Taku har kullum Maman Nusaiba ce_ [10/25, 3:35 Yamma] My Addatyna: ~_*A HAKA NAKE SON SHI*_~ Daga Alƙalamin _*Sarat Alƙasum ~(Maman Nusaiba)~*_ _🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_ *بسم الله الرحمن الرحيم* An kusa gama free fage duk mai bukatar ci gaba sai ya min magana ta wannan number. *+966577675904* Shafi na shida (6) Tallah !! Tallah !! Shahararriyar Marubuciyar nan Ikilima Adam (kyauta daga Allah) wacce ta nishadantar daku a littafin ta mai suna *Kanwata* *kaikajawa kanka , Rai daya janzaki, yau na sake dawowa domin muku Domin tallata muku Littafaina mai Suna *(RUDANI )* Da kuma *Makauniyar Shari'a* littafine mai kunshe da Butulci , cin amana ,zagon Kasa , soyayya irin ta gani kasheni , aminci da saura n su basai n'a cika Ku da surutu ba Hausawa sukace Gani yakori ji. Karku Manta *Makauniyar Shari'a* sabon littafi ne mai bibiyar Ma'anar sunan sa. RUDANI littafine mai cike da Rudani da ban Al'ajabi , duk wacce kika fi buƙata zaki biya kudin sa Naira ɗari biyar kacal. Farashin kowannen su Naira Dari biyar ne 500 kacal Domin Karin bayani Ku tuntubeni a lambata kamar haka (09069080725 ko Kuma + 22953726162 ) wacce Bata shirya Siya ba kada mu batawa juna lokaci. Domin aikawa da kudi kai tsaye . 3115484026 ikilima Adam first bank Turo shaidar biya akan wannan 09069080725 sai najiku. Maigadi ya durƙusa a gaban su Abba ya ce "Alhaji wani mutum ne ya zo a ƙofar gida ya ce Uwar masu gida yake son gani." Da sauri Abir ta dafe ƙirji tana kwalalo idanu waje ta ce "Ni kuma Baba Maigadi?" Ta faɗa tana kallon Abba. Kallon Maigadi Daddy ya yi ya ce "Ka je ka masa iso ya zo nan mu ga waye haka yake neman ta?" Kwaɓe fuska ta yi jin abin da Daddy ya faɗa ta ce "Yanzu Daddy ba ka san ko waye ba kuma sai ka ce wai ya shigo mana har ciki? Ni dai ko ya zo ba zan bari ya ganni ba." Ta faɗa tana yin raurau da idanu dama ita indai ta wannan ɓangaren ce to ita ce shugabar ma su kuka a cikin familyn Maitama, hakan yasa wasu daga cikin su indai sun haɗu to fa sai sun saka ta kuka.. Abba ya gyara zama ya ce "Mamana ki bari mu ga waye shi mai neman naki." Gyaɗa kai kawai ta yi ba ta ce komai ba, burin ta kawai ta ga waye haka wanda yake neman ta da gabannin Azuhar ɗin nan? Tuna text ɗin da aka mata yasa ta ji gabanta ya faɗi rass! Ta yi saurin runtse idanu tana karanto Addu'ar neman tsari da waɗannan azzaluman mutanen, wanda suke neman kashe mata rayuwa tun kwananta bai ƙare ba a duniya. Da Sallama Maigadi ya shigo shi kuma yana biye da shi har suka iso cikin palon, Maigadi ya koma bakin aikinsa shi kuma ya tsaya a tsaye tare sa cewa "Assalam alaikum." Saurin kallon shi Abba ya yi ya ce "Wa alaikum salam! Wa nake gani kamar Barrister Huzaifa? To iso ka zauna mana ga guri." Murmushi ya yi tare da ɗago da fuskarsa ya samu waje ya zauna, Ɓaki ne dogo mai matsakaicin jiki wanda shakarunsa ba su wuce 35 ba, yana da kyakyawar ƙirar jiki kana ganin shi ka ga ɗan gayu mai ji da kansa, sanye yake da ɗinkin shadda gizna blue color ta samu ɗinki mai kyau, hakan yasa ta ƙara haskaka shi. Cire glass ɗin da ke manne a idanunsa ya yi tare da cewa "Am Alhaji ya muka ji da wannan ifitila'i da faru?" "Alhamdu Lillah Barrister yanzu haka ma daga office ɗin Ogan su Abdul muke ni da Yaya." Cewar Abba. Girgiza kai Barrister ya yi cike da alhini ya ce "Ni ma yanzu nake ganin ana maganar a TV, shi ne hankalina ya tashi na kasa zama na ce sai na zo naji daga bakinku da gaske Abokina an yi kidnapping ɗin sa? Kasan na kai wata takwas bana ƙasar na tafi ƙaro karatu a ƙasar Turkiyya." Daddy da bai ce komai ba tun zuwa Barrister ya kalle shi ya ce "To ya muka iya da ikon Allah Barrister, gardama ce irin ta Yaya Ibrahim na faɗa masa in zai fita yake tafiya da masu tsaron lafiyarsa, amma gani yake kamar suna takura masa ƙarshe ma ya ce iya aikin su su bi shi office da kuma tsaron cikin gida ,ya fi so ya tafi shi kaɗai ƙarshe duk wasu officer ya mayar da su yin aiki, yanzu ga shi an ma rasa a wani hali yake a yanzu." Mami da tun dazu take jan tsaki ta miƙe ta ce "Sai an jima ni zan je ɓangarena tun da maganar nan dai ba ta shafe ni ba." Sake da baki Abba ke kallon ta har ta fita daga palon, haka ita ma Umma ta miƙe tsam ba ta yi magana ba ta bar palon. Duk ba wanda ya ce wani abu sai da suka bar palon sannan Barrister ya ce "My daughter za ki iya gane mutanen da suka kama ki?" Dam! Ta ji zuciyarta ta buga ta sunkuyar da kai, to ita me ake so kuma ta faɗa bayan wanda ta faɗa? Shi ma ɗin dan ba ta da yadda za ta yi ta haɗa da ƙarya ta faɗa. Ganin taƙi cewa komai yasa Abdul gyara zama ya ba wa Barrister labarin da ta ba su, shi kuwa ya yi shuri yana nazarin maganar ko zai samu amsar da yake son samu, amma sam abin ya kulle masa kai hakan yasa ya kuma cewa "Uwar masu gida, za ki iya tuna kamannin mutanen?" Goge majinar da ta fito daga hancinta ta yi sannan ta ce "Ni fa ban taɓa ganin fuskar ɗayan su ba, duka kullum fuska a rufe suke shigowa ɗakin da suka saka ni." Ajiyar zuciya Barrister ya sauke ya ce "Ok to kukan ya isa haka yi haƙuri, in sha Allah zan ci gaba da bincike akan lamarin, akwai wani abokina D.P.O. ne na masa bayanin ɓatan amma tun da kes ɗin na hannun Abdul zan masa magana na ce an amshi kes ɗin, sannan in sun kira ku sanar da ni Alhaji ni zan koma, amma kafin nan ina son yin magana da Uwar masu gida. "Ya faɗa yana kallon ta. Grandma ta ce "To Huzaifa mun gode kwarai ke kuma tashi ku je waje in kuma mu ba ku waje to?" Da sauri ta ce "A a Grandma mu je bakin motar shi kawai." Ba ta musa mata ba ta tashi ta gyara mayafinta sai kuma ta ga daga gefe wajan da Mahaukaci ya taɓa mata ya yi dauɗa. Ajiyar zuciya ta sauke ta bi bayan Barrister suka fita.. Bayan sun fita Abdul ya ce "Anya kuwa Daddy ba akwai abin da Baby ke ɓoye mana ba?" Murmushi Daddy ya yi ya ce "Haba kai kuwa taya ma za ta ɓoye mana wani abu bayan ta san ba ta wanda za ta faɗa wa damuwarta sai mu iyayenta, ka daina wannan maganar kar ma ka tarbe ta da ita." Ba dan ya yarda ba ya ce da Daddy to kawai dan a bar maganar... Suna fita bakin motar Barrister ya dubi Abir yana ɗan murmushi ya ce "Abir ki yi haƙuri in sha Allah mahaifinki zai kubuta kin ji. Sannan ina so ki faɗa min gaskiyar komai da kika gani bayan an sace ku." Cikin ƙosawa da maganar ta ɗago da idanunta wanda suka yi jajur saboda kukan jda ta ci ta sauke su a kan Barrister, shi ma ƙura mata idanu ya yi sosai yarinyar ke ba shi tausayi ita kuka ba ya mata wahala ballantana wannan mai dalili ne. Shi ya fara ɗauke idanunsa daga kanta tare da ɓala yatsu biyu, da sauri ta sauke nata idanun a kunyace ta ce "Uncle iya abin da na sani shi na faɗa maka ku yarda da ni mana." Ta faɗa tana rufe fuskarta da mayafi.. Wani iri ya ji ba daɗi ya ce "OK zan kira ki idan na samu lokaci je ki ciki." Turo baki gaba ta yi ta tsaya ba ta tafi ba, har ya buɗe marfin motar ya ga tana tsaye sai ya dakata ya dube ta tare da cewa "Ya dai? Ko akwai magana ne?" Ya jero mata tambayoyi. Saɓa baki ta yi cikin Shagwaɓar da ta zame mata jiki ta ce "Uncle ai ba ni da waya sun kwace min ita." Murmushin gefen ba ki ya yi ya ce "that is very good my little, zan sa a bibiyi number in dai wayar a buɗe take tabbas za mu gano inda suke, yanzu ba ni number da kike da ita." Ya faɗa yana miƙa mata wayarta tsadaddiya Ajiyar zuciya ta sauke ta amsa ta sa masa number sannan ta masa sallama ta shige ciki... Ko da ta dawo Abdul ya tsare ta da tambaya. "Baby me ya ce miki?" "Ƙarin bayani ya nema." Abin da ta faɗa kenan ta ɗauki jakarta ta nufi ɗakinta. Kwafa ya yi yana nufar ɗakin Grandma ganin duk sun tashi daga shi sai Grandma da Laraba ke mata tausa, ganin ya nufi ɗakinta ta daddage ta ce "Kai Abdullahi uban me ka aje min a ɗaki da za ka shiga? In ce ba da kuɗin uwarka Sa'ade aka gina min ɗakin ba dai ko? To maza ka yo baya ƙaton banza tuzuru sai warin balaga kake ka zama rikakken namiji ba mata, to ni ba ƴar banza ba ce irin iyayen naka da suka saya ka sai abin da ka ga dama kake yi. Yanzu ba dan ba ma ni zuciyata a tsakake take ina zan yarda ka zauna kusa ma da ni kana warin balaga." Ta ƙarashe maganar tana gutsirar goron da ke hannunta ta ƙara masa da harara. Sai da ya tsaya ta gama sannan ya ba wa iska ajiyar ta ya shige ɗakin. Ganin ya shiga ta kwashi salati "Muhammadu Rasulullahi sallallahu alaihi wa sallama ni Hauwa'u! Wannan wacce irin fitina ce haka? Na ce kar ka shigar min ɗaki amma dan jafa'i sai ka shiga, za ka fito ka sameni a palon nan sai na ma wankin babban bargo." Ita dai Laraba ƙunshe dariyarta take kar ta fito ta yi laifi Grandma ta yi mata tatas kamar yadda ta saba mata... Labari ya karaɗe cikin garin Yola da kewayanta na ɓatan Alhaji Ibrahim Maitama, hatta social media duk inda ka nufa maganar sace shi kawai ake yi, har ma da masu ƙarawa labarin gishiri. Wasu su ce ai abokan kasuwancinsa ne suka haɗa masa tuggu aka sace shi, wasu kuma su ce kawai mahassada ne abin dai kowa da kalar ƙagen da yake faɗa.. Abir duk ta ƙara ramewa ta yi zuru-zuru kamar ba ta cin abinci, tunanin Abie ɗinta take ba dare ba rana ga tunanin yadda za ta ga mahaukacin nan duk ya addabe ta.. Yau ma kamar kullum tana zaune ta lula duniyar tunani can ta tuna number dattijon nan, da sauri ta miƙe ta fito zuwa ɗakin Mommy. Da Sallama ta shiga inda ta samu Mommy ba ta ɗakin, jin ƙaran ruwa a banɗaki yasa ta gane wanka ta shiga, cikin sauri ta ɗauki wayar Mommy ta duba ɓangaren kira ta shiga neman number, sai da ta sha wahala sannan ta samo number ta yi saurin ɗauka ta fita.. Cin karo suka yi da Yasmin ita ma tana sauri, saurin kallon Abir ta yi ganin ita ce yasa cikin ɓacin rai ta ce "Ke wata irin mahaukaciya ce? Ta ya za ki buge ni ko ki bani haƙuri kike ƙoƙarin wucewa?" Ta faɗa a fusace. Ko uffan Abir ba ta ce da ita ba abin da ya ƙara tafasa zuciyar Yasmin ta ɗaga hannu ta zabga mata mari ji kake tass! A ruɗe ta juyo tare da dafe kuncinta saboda wani irin zafi da ya ziyarci dukkan ilahirin jikinta har sai da ganinta ya ɗauke na wucin gadi. "Last warning! Idan kika sake min irin haka sai na kakkarya ki mai ƙirar aljannu jikar mayu, ban san me Yaya Salim ya gani a tare da ke ba har yake wani rawar jiki a kank... Kafin ta ƙarasa ta ji saukar wani gigitaccan mari kan fuskarta, ta juyo a ruɗe dan ganin wanda ya mare ta sai suka haɗa idanu da Abdul nan-da-nan jikinta ya ɗauki rawa, shi kuma tun lokacin da ta mare ta yake tsaye a kofar palon yana kallon ƙarfin hali irin Yasmin, ta bangaje ta kuma ta mare ta ɗan iya shege. Abin da ya ɓata masa rai ya harzuƙa shi da ta haɗa ta da Salim nan-da-nan ya ji zuciyarsa ta ɗauki wani kalar zafi marar iyaka.. Da sauri Abir ta dawo bayan Abdul ta kwanta a bayansa ta saki kuka, ita ba marin ba ne ya ɓata mata rai da take haɗa ta da aljannu shi ya fi taɓa mata zuciya, duk da ta saba jin wannan kalmar a wajan su Mami da sauran yaran gidan. Dawo da ita ya yi gaban shi ya shiga goge mata hawaye yana ba ta haƙuri har ta daina kukan sannan ta zare jikinta daga nasa ta wuce ɗakinta, ita kuma Yasmin ta yi ƙiƙam tana musu kallon ɓakin ciki, sai da ya daka mata tsawa sannan ta fice da gudu.. Shirin Makaranta take ta yi cikin ɗan kuzarin da ya rage mata ta fito inda ta samu Mommy zaune ita da Laraba tana ba ta labarin ƙauyensu, kallon ta Mommy ta yi ta ce "Kin shirya?" "E Mommy zan wuce ayi mana Addu'a." "Allah ya kiyaye ki a dawo lafiya." Murmushi ta yi tare da matsowa ta yi kissing ɗin Mommy sannan ta wuce waje. Direba ta samu yana jiran ta, sai da ta gaisa da su Maigadi sannan ta shiga suka tafi.. Tsaye ya yi a bakin hanya yana goge sandarsa yara na tsokanar shi yana nuna musu sandar, kamar an ce ta waiga ta gan shi cikin sauri ta ce "Direba dakata please." Ta faɗa tana waigen shi Saurin taka birkin ya yi ya tsaya ya juyo ya kalle ta ya ce "Ranki ya daɗe lafiya dai." "E lafiya lau buɗe min na fita akwai abin da nake son yi a nan." "A a gaskiya ki yi haƙuri Maigida ya ce nake kula da ke kar na bari ki tafi wani waje." A fusace ta ce "Za ka buɗe min ko sai zabga maka mari?" Jin abin da ta faɗa ya sa ya buɗe mata ta fito shi ma ya fito, nufar inda yaran suke suka yi sai sauri take kamar za ta tashi sama. Suna isa suka ga yara ne kawai suka yi gungu suna ta wasa, tambayar yaran ta shiga yi. "Ku ba ku ga wani Mahaukaci a nan a tsaye ba?" Wani yaro daga cikin su ne ya ba ta amsa "E amma ai ya yi tafiyar sa yanzu." Da sauri ta riƙe hannun yaron ta ce "Don Allah ina ya nufa?" "Ni ma ban sani ba, na ga dai kawai ba ya nan." Dafe kai ta yi cikin damuwa ta juya ta nufi motar shi ma Direba ya bi bayanta suka koma motar ya tada suka tafi. Wasu irin zafafan hawaye ne suka zubo mata, mutum kamar aljani ta gan shi amma kuma a ce mata ya ɓace wa ganinta kamar walkiya? Lalle dole ta sa a nemo mata shi ko ta nema masa lafiya. Tuna ta ɗauki number Dattijo na ta kira shi ba yasa ta ji ɗan sanyi a ranta tana aiyanawa da ta je gida za ta kira Baba Dattijo... Babban get ne wanda aka buɗe wasu motoci guda biyar suka shige cikin gidan, gida ne na gani na faɗa ya tsaru iya tsaruwa, motar ta tsakiya aka buɗe wani hamshakin mutum ya fito cikin shiga shi ta alfarma ya yi gaba suka bi bayansa. Wani sashe ya shiga na gidan sai ga shi a wani ɗaki mai dubu-dubu wanda babu komai a cikin ɗakin wata kujerar roba a bakin ƙofar ɗakin. Makunnar haske ya laliba ya kunna sai ga ɗakin ya ɗauki haske tauu, wani mutum ne kwance ya takure a waje ɗaya kayan jikinsa duk a yage ga jini a jikin fufafin, ƙara ɓata rai mutumin ya yi ya ce "Babba maza tashe shi." Wanda aka kira da Babba fuska ba annori ya fita waje, bai jima ba ya dawo da ruwa a wata roba yana tururi ya kwamaya wa mutumin nan. A gigice ya tashi yana mayar da numfashi cikin mawuyacin hali ya soma buɗe idanuna, da sauri ya ƙara buɗe su ganin wanda yake tsaye gaban shi, ya ɗaga hannunsa da ƙyar ya ce Jar... Yanzu ma aka fara masoya ku dai kar ku bari ayi tafiyar nan ba da ku ba, ki hanzarta biya kuɗinki domin ayi wannan tafiya mai cike da sarkakkiya tare da ke my sister .. _Taku har kullum Maman Nusaiba ce_ [6/20, 7:34 PM] Ummu Amjad: /25, 3:35 Yamma] My Addatyna: ~_*A HAKA NAKE SON SHI*_~ Daga Alƙalamin _*Sarat Alƙasum ~(Maman Nusaiba)~*_ _🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_ *بسم الله الرحمن الرحيم* Saura fage ɗaya a kammala free fage, duk mai don cigaban littafin A HAKA NAKE SON SHI ya garzayo ya bisa kuɗinsa ta wannan asusun.. Nomal ~N~ 300. Vip ~N~ 500. Account number 0003187186 Name account, khadija Salisu Name Bank, Ja'iz Bank Sai ayi screen short a turo ta wannan number +966577675904. Shafi na bakwai (7) Tallah !! Tallah !! Shahararriyar Marubuciyar nan Ikilima Adam (kyauta daga Allah) wacce ta nishadantar daku a littafin ta mai suna *Kanwata* *kaikajawa kanka , Rai daya janzaki, yau na sake dawowa domin muku Domin tallata muku Littafaina mai Suna *(RUDANI )* Da kuma *Makauniyar Shari'a* littafine mai kunshe da Butulci , cin amana ,zagon Kasa , soyayya irin ta gani kasheni , aminci da saura n su basai n'a cika Ku da surutu ba Hausawa sukace Gani yakori ji. Karku Manta *Makauniyar Shari'a* sabon littafi ne mai bibiyar Ma'anar sunan sa. RUDANI littafine mai cike da Rudani da ban Al'ajabi , duk wacce kika fi buƙata zaki biya kudin sa Naira ɗari biyar kacal. Farashin kowannen su Naira Dari biyar ne 500 kacal Domin Karin bayani Ku tuntubeni a lambata kamar haka (09069080725 ko Kuma + 22953726162 ) wacce Bata shirya Siya ba kada mu batawa juna lokaci. Domin aikawa da kudi kai tsaye . 3115484026 ikilima Adam first bank Turo shaidar biya akan wannan 09069080725 sai najiku. Ya ɗaga hannunsa da ƙyar ya ce "Jarmai! Ka..Kai nake gani ko dai wani ne daban?" Ya faɗa jikinsa na ƙyarma tashin hankalin da ya shiga yanzu ya fi wanda yake ciki, tunani ya shiga yi na zuwan Jarmai wannan mugun waje mai hatsarin gaske. Takowa ya yi har gaban shi wanda suke bayan shi ɗaya daga cikin su ya janyo wannan kujerar robar ya aje masa ita, zama ya yi yana wani irin murmishi wanda shi kaɗai ya bar wa kansa sani, sai da ya done hanci jin yadda wani kalar wari ya kawo wa hancinsa ziyara. "Jarmai ka yi magana mana, ko kaima sato ka aka yi kamar yadda aka mana?" Ya faɗa yana riƙe bayansa da yake masa wani irin zugi na azaba. Gyara zama ya yi sannan ya ce "Manager kenan. Ni ne dai ba wani ba sannan ba wanda ya sato ni da kaina na zo har cikin ɗakin nan." Waro idanu Manager ya yi cike da ta'ajjabin maganar ya ce "K.. ka zo ka fitar da ni ne?" Girgiza kai ya yi tare da miƙewa ya nufi ƙofar fita, sai da ya kusa fita sannan ya juyo ya ce" A tunani irin naka wai gani kake ni masoyinka ne? Ya yi murmishi sannan ya ɗaura "Duk duniya babu wanda na tsana sama da kai Manager, bana son ci gaban da kake samu a rayuwa dan haka yasa na biyo ma ta bayan gida." Wani irin rawa jikin Manager ya ɗauka, kenan dama Jarmai zai iya cin amanarsa? Lalle Jarmai butulu ne, da ɗan sauran kuzarin da rage masa ya miƙe tsaye ƙafarsa na rawa har ya samu ya daidaita tsayuwar, yunwa duk ta lakata shi ga duka da yake sha ba dare ba rana. Bin bango ya dinga yi har ya iso inda Jarmai yake cikin tsananin fushi da takaicin abin da ya masa ya ce "Jarmai ashe kai ɗin bara-gurbi ne a cikin mu? Lalle ka cika ma ci amana Jarmai, kuma kafin ka kasheni ni zan kashe ka." Ya faɗa yana cakumar wuyansa duk da ba wani ƙarfi gare shi ba a halin yanzu, amma zafin abin da Jarmai ya aikata a gare shi yasa ya ji wani irin kuzari ya zo masa har ya samu damar shaƙe masa wuya. Sosai Jarmai ya ji shaƙar da Manager ya masa, shi ya ɗauka kamar ba abin da zai ji dan Manager ya shaƙe shi, sai ga shi ya soma kwalalo idanu waje yana yi wa yaran nuni da su raba su. Bindigar da ke hannun ɗayan su ya buga masa a gadon baya ba shiri Manager ya saki Jarmai, cikin haki Jarmai ya ce "Da na yi niyar na barka da ranka, amma tun da ka nuna min kai mai ƙarfi ne zan nuna maka asalin waye ni, kai ku yi wa jikinsa gunduwa-gunduwa ku jefa wa karnukan gidan nan." Ya faɗa cikin fushi yana wucewa daga ɗakin. Duk da ya kasa motsi amma hakan bai hana shi yin magana ba. "Dan ka kashe ni ai ba jarumta ka yi ba, kuma za ka girbi abin da ka shuka in sha All... Bai ƙarasa maganar ba Jarmai ya juyo ya sakar masa alburushi a kansa nan take jini ya shiga malala a ƙasa ko shurawa bai yi ba ya mutu. "Ni za ka nuna wa taurin kai? Ku kuma kusan yadda za ku yi da shi ina da muhimman aiki a gabana, idan wani abu ya taso ku kira ni." "Ok Oga za mu ji da komai." Suka faɗa a tare kafin wasu suka wuce tare da Jarmai, wasu kuma suka ɗauke gawar Manager. Bayan ta gama lecture ɗinta ta fito harabar Makarantar tana jiran Direba, dafe kai ta yi tana kallon agogon hannunta sai ga Direba ya iso. Ajiyar zuciya ta sauke saboda tsoron da take ciki duk gani take kamar in ta waiga su za ta gani sun zo cutar da ita. Tashi ta yi cikin nutsuwarta ta isa ga Direba tare da kwankwasa glass ɗin motar, zugewa ya yi ganin ita ce yasa shi saurin fitowa yana murmushi ya ce "Ranki ya daɗe barka da rana." Ɗan murmushi ta yi ta ce "Barka dai Habu ya ƙoƙari?" "Alhamdu Lillah." Ya faɗa tare da buɗe mata motar ta shiga suka tafi. Suna isa gida ba ta samu kowa a palo ba hakan yasa ta shige ɗakinta. Tana shiga ta ji cikinta ya murɗa ta yi wurgi da jakar makarantar ta shige toilet da gudu, kafin ma ta tsugunna ta soma sakin zawo a jikinta mai mugun tsami. Sai da ta gama ta cire kayan ta janyo bokati ƙarami ta saka kayan ta kwara musu ruwa sannan ta soma wanka, mamaki ta dinga yi na abin da ya saka ta yin zawo dan yau in ba ruwan shayi ba babu abin da ta sha sai kuma ruwa. Bayan ta fito ta ji ana kiran Sallar Azuhar ta koma ta ɗauro alwala, har ta kabbara iƙama ta ji cikinta ya ba da sautin ƙuuuuu! Sai ta dinga jin kamar ana mata rugugi ba shiri ta cire hijabin ta koma toilet.. Wasa-wasa dai sai ta dinga kabbara Sallar tana bari har sau 5 abin da ya ɗaga mata hankali, tun tana yin zawon tana fitowa da kuzarinta har ya kai ga tana fitowa da duƙe na ƙarshe da rarrafe ma ta fito, Sallar da ba ta yi a tsaye ba sai a zaune ta yi tana jin mlhajijiya na neman kwantar sa ita duk da a zaune take.. Bayan ta gama ta rarrafa ta haye gado da ƙyar take iya ɗaga hannunta saboda zawon ya lakata ta sosai, ƙoƙari ta yi ta fito da wayarta ta lalibo number Dattijo ta danna masa kira.. Lokacin Dattijo ya fito daga Masallaci yana kan hanyarsa ta koma wa gida ya ji wayarsa na ringing, da sauri ya ciro daga aljihun wandonsa sai ya ga sabuwar lamba ce dan haka yaƙi ɗagawa saboda labaran da yaransa ke faɗa masa, cewa ana kiran mutum da sabuwar number da ya ɗaga za a zuke masa jini, wannan dalilin yasa Dattijo ya ƙi ɗauka har ta katse. Bayan ta katse ya girgiza kai ya ce "Kai gara dai na ɗaga yaran nan wani lokacin ƙarya suke faɗa." Yana shirin kiran number ya ga kira ya kuma shigowa ya yi saurin ɗauka tare da karawa a kunne ya ce "Assalam alaikum." Abir da ke kan gado ta yi lufai kamar ba ta da lakka a jiki ta ji saukar muryar Dattijo a majiyarta, wani sanyi ya ziyarce ta ta ce "Wa alaikum salam. Baba barka da rana." "Barka dai yarinya, da wa nake magana?" Ɗan murmushi ta yi ta ce "Ni ce wadda ka taɓa ba ni wayarka watannin baya na kira Mamana." Nan dai ta shiga faɗa masa har lokacin da Abdul ya zo ya ɗauke ta... Baba ya murmusa sannan ya ce "Yarinya ashe ke ce? Ai kullum Zaiyan na tambayar ina Anty, in dai gari ya waye da ya ganni zai ce min "Anty ta kawo min abinci?" Sai na ce masa "Za ta dawo an jima." Ba ta san lokacin da ta tashi zaune ba, wani irin daɗi ta ji ya ziyarce ta tana kuma yin mamakin yadda bai manta da ita ba duk da ba hankali gare shi ba, ƴar dariya ta yi ta ce "Ma sha Allah. Kenan Baba sunansa Zaiyan? Ai na sha tambayar sunan shi amma sai dai ya maimaita min abin da na tambaye shi, sunansa mai daɗi to yanzu ina yake?" Ta ƙarashe maganar tana yin baya ta jingina da jikin gado, ji ta yi kuzarinta ya soma dawowa. Kamar Baba na ganin ta ya riƙe baki cike da mamaki ya ce "Wai dama kuna haɗuwa da shi ne bayan hakan ta faru?" "Kwarai ma kuwa Baba, sau uku na gan shi kuma har ya min magana." Labarin komai ta faɗa masa tana jin ranta wasai, shi kuma Baba ya cika da mamaki marar musaltuwa har ya kasa ɓoye mamakin ya ce "Yarinya to ni dai a iya sanina da Zaiyan bai taɓa barin Unguwar nan ba, tun yana ɗan ƙarami yake a nan kuma ga shi kina maganar har a ƙofar Asibiti kika gan shi." Ita ma riƙe bakin ta yi jin amsar da ya ba ta, to in ba shi ba take gani waye take gani? Ko kuwa dai Baba bai sani ba Zaiyan ke tafiya yawon sa har ya dawo bai san ya je ba? Girgiza kai ta yi ta ce "Baba Wallahi da gaske shi na gani, har fa rannan magana muka yi da shi a bakin Asibiti, yanzu yana nan a Unguwar taku?" Ajiyar zuciya Baba ya sauke ya ce "E yanzu haka ma da zan tafi Sallah sai da na haɗu da shi a ƙofar gidana na kawo masa abinci, na ga ma duk ya rame sosai ko ba shi da lafiya ne ƙila." Da sauri buɗe lumsassun idanuwanta wanda suka yi kama da na masu jin bacci, ƙara gyara zama ta yi sannan ta ce "Baba don Allah wata alfarma nake nema a wajan ka in zan samu." "To ƴar nan ina jin ki." "A a ba yanzu ba zan faɗa ma zan zo Unguwar taku zuwa gobe sai mu yi magana yadda za ka fahimce ni." "To shi kenan sai kin zo ɗin." Godiya ta masa sannan suka yi Sallama. Bayan ta aje wayar ta shiga tunani, gabaɗaya abubuwa sun cunkushe mata duk ta rasa mafita. Numfashi ta fesar tare da sake ɗaukan wayar ta danna wa Abdul kira, sai da ta gama ringing ta katse bai ɗauka ba ta turo baki gaba, ba ta yi fushi ba ta sake kiran shi. Sai da ta kusa katsewa sannan ta yi an ɗauka sai kawai ta ɓare baki ta shiga rera masa kuka.. Shi kuwa dafe kai ya yi yana jinjina rigima irin ta Babyn nasa, ita kuka ba ya mata wahala daga kira sai kuka kuma? Ajiyar zuciya ya sauke tare da yin taku biyu ya zauna akan kujera ya jingina kansa ya lumshe idanunsa, so yake ya rarrashe ta amma bakinsa ya masa nauyi sautin kukan ta na ƙara rikita masa tunani ji yake kamar ana sukar shi in ta tana kukan , buɗe lulu eyes ɗinsa ya yi wanda suke cike da matuƙar gajiya ya ce "My Baby cries enough, faɗa min what happen kike yin rigima?" Ya yi magana yana sa hannu cikin sumar ķansa yana yamutsa ta.. Kamar tana gaban shi ta turo baki tare da kara lafewa akan gadon, cikin Shagwaɓar da ta zame mata jiki ta ce "Yaya wai ba ka dawo daga aikin ba ne? In ce dai ka ce yau hutu kake amma shi ne ka tafi Office." Ta yi maganar tana ƙara narkar da murya. Lumshe idanu ya yi yana sauraron daddadar muryarta har ta kai aya a maganarta, dogon numfashi ya ja tare fesar da iskar cikin bakinsa ya ce "Baby Wallahi kin cika neman rigima, ke ba ki na zauna lafiya sai kin tasa ni a gaba kina min rigima?" Cuno baki gaba ta yi ta janyo ƴar Teddynta ta rungume ba ta ce masa komai, sai da ya gaji da riƙe wayar sannan ya ɗauke hannun jakar computer shi da ke kan kafaɗarsa ya ce "Yanzun nan na dawo gida ko zama ban yi ba lokacin da kika kira ni, amma Kin san me?" Ya tambaye ta. Girgiza kai ta yi tare da buɗe idanunta ta ce "A a Yaya sai ka faɗa." Wani irin kayataccan murmishi ya yi, sannan ya ce "Ki ce Mommy ta haɗa miki abinci sai ki kawo min part ɗina mu ci abincin tare." Ya faɗa yana tashi daga kan kujerar ya soma ɓalle maɓallin rigarsa. Murguɗa baki ta yo ta harari wayar ta ɗago da ƙyar ta runkuya ta miƙe daga kan gadon ta ce "To Yaya bari na kai maka dama ni ɗin ma ba ni lafiya in na zo sai ka sa a kawo min magani." "Subhanallahi! Me ke damun ki Baby?" Ya faɗa a ruɗe. . Sai ta zo kawai ta ce masa ta kashe kiran, cikin kuzarin da ta ji ya zo mata ta nufi freezer ta ɗauko ruwa mai sanyi ta sha sannan ta canja kayan jikinta ta sako riga da wando jins, sosai kayan ya mata kyau ta ɗaura ɗan kwali sannan ta fito daga ɗakin. A ruɗe ta ƙaraso palon ganin Mommy zaune tana share hawaye, cikin damuwa ta ce "Mom me ya faru?" Saurin goge hawayen Mommy ta yi sannan ta kirkiro murmishin yaƙe ta ce "Ba komai Mamana kawai dai kaina ne ke ciwo shi ya sa idanuna suke cika da hawaye." Ta faɗa tana gyara zaman ta. Ba ta gamsu ba da bayanin nata duk da tasan in Mommyn na ciwon kai idanuwanta za su yi ta hawaye, amma ganin yadda yanayin ta yake yasa sam ta kasa kwantar da hankalinta, durƙusawa ta yi ta ce "Mommy ni nasan a kan halin da muke ciki ne kike wannan kukan, ki yi haƙuri in sha Allah Abie zai dawo garemu." Ta ƙarashe maganar ita ma tana kuka. Janyo ta Mommy ta yi ta rungume ta zuciyarta na ƙara bugawa, tausayin ƴarta ta ya cika mata zuciya da gangar jiki, tana son faɗa mata dalilin kukan amma ba ta son hankalinta ya tashi gara ita ta ji da damuwar har komai ya yi daidai. Goge hawaye ta yi ta ce "Mamana tashi ki kira min Yayanki a part ɗinsu. Miƙe wa ta yi daga jikin Mommy ta wuce zuwa part ɗin Umma. Da Sallama ta shiga palon inda ta tarar da Yasmin da Fatima da Khairat da Iman tare da Umma, murmushi ta yi ganin 'yan'uwan nata zaune waje ɗaya gwanin birgewa ta iso inda suke ta durƙusa ta ce "Umma ina yini? Ya gida?" Wani irin kallo Umma ta jefe ta da shi sannan ta ce "Lafiya." A takaice, abin da duk duniya Abir ta tsana ta gaishe ka amma ka amsa mata da lafiya, gani take kamar ma tambayar ta kake ba amsa gaisuwar ba, hakan yasa ta sunkuyar da kai ta ce "Yayana nake nema ko yana ciki." Ta faɗa duk da tasan yana cikin. Yasmin da Fatima da suke bin da kallon tsana suka ja tsaki, Fatima ta ce "To me za ki ba shi da kike neman shi?" Ta faɗa cikin nuna tsanar da take mata ƙarara a kan fuskarta. "Tsuwww! Rabu da uwar nacin jaraba mana, in ban da maita har ɗakin nasa ma sai kin biyo shi kamar wata uwarsa? To baya nan gulmanmiya uwar kissa da kisisina." Yasmin ta faɗa cikin ƙasa da murya dan kar Abdul ya jiyo tashin muryarta. Umma ta saki murmushi ganin hawaye kwance bisa fuskarta Abir abin ya faranta mata rai, ta rasa ma wani kalar asirce yaron Mommy ta yi da ko abinci ta yi baya ci sai na Mommy, hakan yasa ta kuma yin kwafa ta dungure mata kai tare da cewa "Shin ke da uwarki aka haifa wa Abdul ne? Wallahi duk bokon da ya muku aiki a kan yaron nan yake wannan rawar jikin a kanki sai na ga bayan ku gabaɗaya." Ta faɗa a fusace. Iman da ta yi kicin-kicin da fuska kamar ta sa kuka ganin yadda ake wulakanta Abir ta ce "Haba Umma wannan wani irin cin fuska ne haka kuke mata? Sai ka ce ba jininku ɗaya da ita ba? To Wallahi sai na faɗa wa Yaya Abdul ya muku dukan mutuwa mugaye kawai. " Mari Umma ta kai mata ta yi saurin gogewa ta bar kusa da ita ta isa wajan Abir ta ce "Anty Baby tashi ki yi haƙuri da abin da suka miki kin ji, suma so suke ya so ɗaya daga cikin su shi ne suke nuna miki kishin jahilci." Ta faɗa tana miƙar da ita suka yi facing ɗin juna. Murmushi ta yi ta ce "Ba komai Iman ai na saba da hakan, ina Yaya yake?" "Yana ciki bari na kira miki shi." "A a ki bari ma na kira shi Mommy ce ke neman shi dama." Murmushi ta yi ta ce "Ok to ni ma zan je part ɗin Mommy dan na gaishe da Grandma da Mommy. " "Kuturu! Umma ki ji wai za ta je part ɗinsu." Cewar Khairat da tun da aka fara maganar ba ta ce uffan ba. "Yau in kika je sai na miki duka." Cewar Yasmin tana huci kamar wata kasa. Kumbura baki Iman ta yi ta ce "Ke kuma ina ruwan ki? Sai na je ɗin." Kwafa ta yi za ta yi magana sai ga Abdul ya fito cikin ƙananan kaya wandon ya ɗan wuce gwiwa, sosai kayan suka masa kyau Yasmin da Fatima suka saki baki suna kallon shi sai wani murmushi suke, Yasmin ji take kamar ta je ta rungume shi ta masa kiss a kumatu ta haɗa bakinta da nashi, abin da ya fi tsone mata idanu a fuska Abdul lips ɗin da suke sheƙi kamar na mata. Da kallo ya dinga bin su yana wani yatsine fuska ya ce "Ya nake jin hayaniya?" Da sauri Yasmin ta miƙe tana wani irin juya idanu ta ce "My Yaya babu komai fa, kawai Baby ce ta zo shi ne muke tsokanarta muna dariya ko Baby?" Ta faɗa tana juyo da akalar magarta ga Abir da tsananin mamaki ya mamaye ta, bayan sun ci mata mutumci kuma ta ce wai wasa suke? Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "E Yaya na zo kiran ka ne sai muke magana da su." Girgiza kai ya yi dan bai yarda da maganar ba ganin idanunta sun yi jajur, fuska a haɗe ya ce "Waye ya saka ki kuka?" Saurin cewa ta yi "Yaya ba wanda ya saka ni kuka yanzu ne na ga Mom na hawaye shi ne ni ma naji hawayen sun zubo min." Kwafa ya yi yana kallon su Khairat da suka yi shuru suna kallon su, ya ce "Ina abincin to?" "Ban kawo ma ba, Mom ta ce na zo na kira mata kai ka ga sai ka ci bayan kun gama maganar." Umma ta harari Abdul ta ce "Wata magana ce za ku yi?" "Ni ma ban sani ba zan je naji." Daga haka bai ce komai ba ya kama hannunta suka fice a part ɗin.. Yasmin ta miƙe ta ce "Lalle Umma in ba ki tashi tsaye ba sai sun raba ki da Abdul ya koma ɓangaren su da zama gabaɗaya, kalli fa ki ga sai wani rawar jiki yake yi a kan ta, shi ma wannan Yaya Salim ɗin wai son ta yake amma bai faɗa mata ba dan tsoron Abdul yake yi." Iman da ta fito daga ɗakinsu ta wuce da gudu dan kar ma Umma ta hana ta zuwa part ɗin Mommy. Ita kuwa Umma ta yi shuru tana tunanin ta hanyar da za ta bi dan ta raba Abir da Abdul cikin sauƙi ba tare da kowa ya sani na.... *An kusa gama free fage my fans, ku hanzarta ku mallaki naku domin ayi tafiyar nan da ku. Ga duk mai bukata ya min magana ta wannan number 👉🏻+966577675904* _Taku har kullum Maman Nusaiba ce_ [10/25, 3:37 Yamma] My Addatyna: ~_*A HAKA NAKE SON SHI*_~ Daga Alƙalamin _*Sarat Alƙasum ~(Maman Nusaiba)~*_ _🔔📚JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION 📚_ *بسم الله الرحمن الرحيم* Wannan shi ne ƙarshen free fage my sister, ga duk mai son cigaban shi. Nomal ~N~ 300 vip ~N~ 500 Zaku turo kuɗin ku ta wannan asusun👇🏻 Account number 0003187186 Name account, khadija Salisu Name Bank, Ja'iz Bank Sai ayi screen short a turo ta wannan number _+966577675904_ Nomal ~N~ 300 vip ~N~ 500. Shafi na takwas (8) Tallah !! Tallah !! Shahararriyar Marubuciyar nan Ikilima Adam (kyauta daga Allah) wacce ta nishadantar daku a littafin ta mai suna *Kanwata* *kaikajawa kanka , Rai daya janzaki, yau na sake dawowa domin muku Domin tallata muku Littafaina mai Suna *(RUDANI )* Da kuma *Makauniyar Shari'a* littafine mai kunshe da Butulci , cin amana ,zagon Kasa , soyayya irin ta gani kasheni , aminci da saura n su basai n'a cika Ku da surutu ba Hausawa sukace Gani yakori ji. Karku Manta *Makauniyar Shari'a* sabon littafi ne mai bibiyar Ma'anar sunan sa. RUDANI littafine mai cike da Rudani da ban Al'ajabi , duk wacce kika fi buƙata zaki biya kudin sa Naira ɗari biyar kacal. Farashin kowannen su Naira Dari biyar ne 500 kacal Domin Karin bayani Ku tuntubeni a lambata kamar haka (09069080725 ko Kuma + 22953726162 ) wacce Bata shirya Siya ba kada mu batawa juna lokaci. Domin aikawa da kudi kai tsaye . 3115484026 ikilima Adam first bank Turo shaidar biya akan wannan 09069080725 sai najiku. Wani irin wawan birki Salim ya ja yana ƙoƙarin faɗuwa Allah ya taimake shi ya tsaya, sosai ya ji zuciyarsa na tafasa ganin yadda Abdul ya riƙe hannun Abir gam, abubuwa da yawa suka tsaya masa a maƙoshi yana kissima yadda zai tafiyar da lamarin tun kafin ta kwaɓe mana. Saurin maƙalewa ta yi a bayan Abdul tana rawar jiki, yadda ya ba ta iska abin ya tsorata ta matuƙa ta ɗauka ko mafarkin da take yi ne kullum da koyaushe zai tabbata a gaske, sai dai ta ji saɓanin haka dalilin jin muryar Abdul yana magana cikin tsawa da ɗaga murya. "Salim! Ba ka da hankali ne? Wannan wani irin shashanci ne kake kamar wani ƙaramin yaro? Yanzu da ka je ka faɗi ka ji wa kanka ciwo ko ita kasa ta faɗi fa? Ka shiga hankalinka kafin na gyara ma zama." Ya ƙarashe maganar yana nuna shi da yatsa, wani irin kallo yake aika masa mai wuyar fassarawa ganin yadda yake kallon ta, nan-da-nan zuciyarsa ta dinga tafasa ya janyo hannunta da ta sakala a cikinsa ya yi sama da shi ta ɗaura akan ƙirjinsa, ita kuma da duk ta firgice ta ƙara kwantowa kanshi tana lumshe idanu har yanzu gabanta dukan uku-uku yake da sauri-sauri, ba ƙaramin tsoro ta ji ba hakan yasa ta ƙara Ƙanƙame Abdul so take ta yi magana amma ta kasa.. Sosa kai ya yi yana leƙa Abir ya ce "Baby dama so nake ki rakani mu je airport mu ɗauko Uncle Aruf jirgin su ya kusa sauka, sannan kafin mu je za mu isa gidan budurwata ki lallaɓa min ita ko ta kula ni fushi take da ni, ki taimaka Baby kin ji Ƙanwata." Ya faɗa yana marairacewa. Jin abin da ya faɗa nan-da-nan ta nemi tsoron ta rasa sai ga ta ta fito daga bayan Abdul tana washe baki ta ce "Uncle Aruf ne ya sauka a ƙasar ko irin ya sanar da mutane a masa tarba? Gaskiya ni ba zan je ba fushi nake da shi kuma sai na faɗa wa Mom, amma ni ba zan je gidan su budurwarka ba, ka manta ranar da muka je tare take zagina har da cewa sai ta ga bayana? Tun daga lokacin ni ma naji bana son ta." Ta faɗa tana cuno baki tare da kallon Abdul da takaici ya gama cika shi, jin kalmar an zage ta ƙara fusata Abdul, wato kenan ma ɗaukan ta yake suna zuwa inda ake ci mata mutumci a wulaƙantata yana gani ba zai bi mata hakkinta ba? A fusace ya ce "To ba za ta je ba tun da bai ce mata zai dawo ba, ka matsa ka ba mu waje mu wuce ina da aikin yi kafin na zabga maka mari a wajan nan. Kuma Wallahi daga yau na sake ganin ka ɗauke ta kun je wani waje ba tare da izinina ba sai ka raina kanka, kai ga ka uban soyayya shi ne za ka ɗauke ta ka kaita inda ba a son ganinta me ya sa ba za ka iya gyara soyayyarka ba da kanka sai wani ya sa baki a ciki?" Ya faɗa cikin faɗa. Murmushi Salim ya yi ya riƙe baki irin ya yi mamakin nan ya ce "To sannu babanta, wai kai ba damar na ce Baby ta rakani wani waje sai ka hana ta kamar kai ka haife ta? Ina ce dai ni ma Ƙanwata ce ba kai kaɗai ba ne ɗa a gidan nan? Dan haka ka daina min iyaka da Baby tun da ni ma ina da iko a kanta a matsayina na yayanta wanda zai tsaya mata a dukkan lamuran rayuwarta. Kasan dai ba zan bari wani ya cutar da ita ba ina gani da idanuna, Wallahi sai ma na kai magana ta da Baby wajan D.. saurin haɗiye maganar ya yi ganin kallon da Abdul yake masa, shi kuwa Abdul ji ya yi ƙafafuwansa na neman kasa ɗaukar nauyinsa jin maganar da Salim ke ƙoƙarin faɗa, duk da bai ƙarasa maganar ba amma maganar ta girgiza shi, ya rufe shi da masifa kamar zai kai masa duka babu shiri Salim ya kwashe da dariya ya matsa suka wuce yana riƙe da hannunta sai ruwan masifa yake yana gargadin Abir, ko baya nan kar ta kuskura da yarda ta bi Salim in ba shi ya ba ta izini ba, ita kuma ganin yadda yake surfa masifa abin ya ba ta dariya amma sai ta danne ta bi shi da to. Ganin sun dan yi naisa da shi yasa Salim ɗaga murya ya ce "Babban Yaya a huce haka kar ka fashe saboda na ga sai hawa kake kamar fulawar da ta ji yiss, Baby dai Ƙanwata ce." Ya faɗa yana wani irin kayataccan murmushi wanda in ba Babyn tasa ba babu macen da yake yi wa. A fusace ya juyo zai masa magana takaici ya hana shi cewa komai, wani irin zafi yake ji na mamaye masa zuciya har bakinsa na masa ɗaci, har zai juya ya ji dai ba zai iya ba sai ya maganta. "Wallahi kar ka bari mu haɗu Salim." Ya faɗa yana hura hanci tare da zuƙo iska da sauri jin yadda numfahi ke ƙoƙarin barin gangar jikinsa. Juyawa ya yi a fusace ya kama hannunta suka shige part ɗin Mommy... Salim kuwa dariya ya yi yana shafa sajansa ya ce "Mu zuba mu gani, ni da kai shege ka fasa ɗan halak sai yanka." Da guntun faɗansa ya shiga palon har ya zauna bai daina faɗa ba a zafafe, abin ya ba wa Mommy mamaki ta ce "Babana lafiya dai na ga ka shigo kana faɗa?" Hura hancin ya yi yana ƙara buɗe ƙofar hancin, da ƙyar ya sassaita numfashinsa ya ce "Wallahi Mom kar ki bari Salim ya ce zai ɗauki Baby su tafi zuwa wani waje, kin san halin Salim na shaye-shaye zai iya kai ta club in da suke shaye-shayen sigari da shisha." Riƙe baki Mommy ta yi tana jimamin ɗabi'un da Salim ya ɗauka wa kanshi, dan dama ta jima tana zargin ko shaye-shaye yake su ba su sani ba ganin yadda zai zo ya yi ta zuba surutai marar kan gado ashe dai da gaske shaye-shayen yake. Numfasawa ta yi ta ce "To a ina ma ka ga shi Salim ɗin?" Tsaki ya kuma ja kamar jikan tsaka ya ce "Yanzu ya tare mu wai ta raka shi su je ɗauko Uncle Aruf a airport, daga nan ta raka shi wajan budurwarsa dan ya ɗauki mutane marassa hankali." Saƙare Grandma da ta fito ta yi a tsaye, sai ji suka yi ta ce "Amma ko Allah wadaran naka ya lalace! Yanzu shi Arufullah ɗin ne zai zo ƙasar ko ya kira ya ce ga shi nan? Tabbas shi ma ya zama ɗan iska irin ƴar'uwarsa." Abdul ya yi kwafa gabaɗaya ce sun saka masa ciwon kai ya ce "Grandma rabu da shi kawai ki ba wa iska ajiyarsa, Mommy gani Baby ta ce kina nema." Gyara zama ta yi cikin nutsuwa ta ce "Babana Wallahi akwai matsala babba." Ta faɗa idanuwanta na cika da hawaye. Da sauri ya matso kusa da ita cikin tashin hankalin ganin hawayen Mommy da tun da yake bai taɓa ganin hawayen Mommy ba, ko da aka ce an sace Abie da Abir ba ta yi kuka ba illa shuru kawai da ta yi. "Subhanallahi! Mom wacce irin matsala ce haka wadda ta sa kike zubar da hawayenki?" Girgiza kai ta yi ta mayar da hawayen da suke shirin zubowa tana sauke ajiyar zuciya sannan ta ce "Ban san waye yake yi wa rayuwarmu barazana ba, tun kafin su Mamana su ɓata ake min wannan barazanar, lokacin da suka ɓata na ɗauka ni da su sai a kiyama ba zan sake ganin su ba." Kallon ta Abdul ya yi cikin rashin fahimtar inda zancen nata ya dosa ya ce "Mommy ki warware min komai don Allah ko zan samu damar aiwatar da bincike na yadda ya kamata, yanzu haka maganar da nake miki muna bibiyar layin Baby da wayarta ke wajan su, ko sun gane ana bibiyar su ne sai suka kashe wayar gabaɗaya ba mu iya bibiya yanzu." Ajiyar zuciya Grandma ta sauke ta ce "Abdullahi ni fa dan kar ku ce rikicin tsufa ne yasa nake surutai, amma tabbas akwai wanda yasan sirikan ahalin Maitama ciki da waje a cikin su." Jinjina kai Abdul ya yi alamar gamsuwa da maganarta, "Wato Grandma kin faɗi gaskiya, tabbas akwai abin da ba daidai ba a cikin wannan family, kullum kaina ƙara daurewa yake akan lamarin gidan nan. Wani lokacin sai ka ga wasu sun zama salihai gobe kuma ka ji suna abin da ba daidai ba, Mom ki faɗa min abubuwa da ake miki na barazana ƙila na samu wata hanyar da zan samo bakin zaren a cikin labarin da za ki bani." Ƙaran text ne ya shigo wayar Mom ta yi saurin ɗauka ta duba ai kuwa taga sakon da aka saba turo mata ne, a tsorace ta ce "Ka gani ko sun sake turo min sako." Amsar wayar ya yi ya shiga karanta saƙon. _"Idan har kika yi kuskuren faɗa wa Abdul ko da kalma ɗaya ce daga cikin lamarin nan za ki sha mamaki."_ Ƙanƙace idanu Abdul ya yi masifa na cin masa rai, cikin ruwan masifa ya shiga musu reply.. _"In kun fasa ba ta mamaki ubanku ya daki hancin babarsa, ku ƙananan 'yan iska ne in kun isa ku faɗi inda kuke mana na zo ayi ta ta ƙare, banzaye kawai asarar haihuwa."_ Yana huci ya tura musu, har zai ƙara wani rubutun kuma ya daina ya aje wayar yana huci gabaɗaya fuskarsa ta ji jajur saboda ɓacin rai abin ka da farar tafa, ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Mom ki ba wa iska ajiyar 'yan iska ni zan ji da komai in sha Allah, amma dai ki faɗa min ko da kaɗan ne daga cikin al'amurin." "Abdul!" Jin ta kira sunan shi yasa ya gyara zama dan in har Mommy ta kira sunan shi na asali to tabbas maganar da za ta mi shi mai mahimmanci ce." "Na'am Mom, ina jin ki." "Ni dai a iya sanina ba ni da abokin faɗa a rayuwata, haka kawai wata rana aka turo min sako ana min barazana, sosai na shiga mamaki dan ni ba shiga harkar kowa nake ba. Abu kamar wasa ake ce min "Idan ba ki yi abin da muka ce ba za ki rasa kowa naki." Abin ya taɓani sosai amma ba wanda na faɗa wa sai Abban Abir ya ce na share maganar kawai 'yan damfara ne ke haɗa number suna yi wa mutane barazana su ba su kuɗi, hakan yasa na watsar da komai ko sun turo sakon bana bi ta kai har lokacin da aka rasa su Abir. Ba su sake nema na ba sai cikin satin nan wai ina lalata musu aiki komai suka shirya sai na wargaza musu, abin nan ya ɗaure min kai suna tambayata na ba su ma'adanar bayanai alhalin ban san meye ma ma'adanar bayanan ba." Ta ƙarashe maganar tana goge hawaye da mayafinta.. Shuru Abdul ya yi yana tunani kafin ya ɗago ya dubi Mommy da duk jikinta ya yi sanyi, shi kansa lamarin na ƙara kulle masa kai, ga shi kullum matsalar sai ƙara kawo kai take, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce "Mom to wai wani irin shiri ne haka har da suke iƙirarin kina rusa shi? Na ga ke ba wani aiki kike ba kullum kina gida, in bakya gida kina gidan Baba Malam." Ya faɗa cikin takaici. Grandma ta ce "To gane min hanya dai Abdullahi ita ba likita ba, ba ƴar sanda ba, ba Soja ba amma ake maganar wani ana ɓata shiri? Shi shirim ya ci ƙundun ubansa." Ta faɗa cikin faɗa, ita kanta lamarin ya tsoratar da ita... Shuru Abir ta yi tana tunani ita kanta ba ta gane shirin ba duk da ta ga wasu abubuwan, to amma ma'adanar bayanan à ina rltake? Kuma meye a cikin ta da har suka sace su a kan ta? Wani tunani ya faɗo mata ta yi saurin dafe ƙirji tana gyaɗa kai, ta ɗaga baki za ta yi magana sai kuma ta tuna da kashedin su a kanta ta yi saurin yin gum da bakinta hawaye na ta zirya ba tsayawa. Abdul ya ƙura mata idanu ganin yadda bakinta ke motsi ya ce "Baby da alama kina da abin cewa amma kin yi shuru." Girgiza masa kai ta yi hakan ya fusata Abdul ya ce" Idan na sake miki magana kika girgiza min kai sai na kakkarya ki a palon nan." "Ka yi haƙuri babu komai." Tsaki ya ja sannan ya shiga kwantar wa da Mom hankali sannan ya ɗauki numberta ya haɗa da wayarsa ta yadda duk wani sako da zai shigo wayar, to shi ma zai shigo ta shi wayar hakan zai taimaka masa wajan gano abin da yake son ganowa. Abinci Laraba ta kawo masa tare da durƙusawa ta aje ta ce "Ranka ya daɗe aradu har ka bani tsoro." Ta faɗa tana dafe ƙirji ta sha wankan riga doguwa ta atamfa wadda Abir ce ta ba ta. Tsaki ya ja ganin super da ya saya wa Abir a jikin Laraba, shi gabaɗaya yarinyar ba ta kwanta masa a rai ba ga shegen surutu marar kan gado. Ganin ba zai ce komai ba ta wuce abin ta tana waƙar _"A zauna wattaran a saɓa tilas ne, ka sanya a ranka arashi sai ya faru."_ Wani tsakin ya kuma ja ya ce "Mom Wallahi yarinyar nan ta ci kai." Murmushi kawai Mom ta yi ta bar musu palon, Abir ma kaɗan ta ci abincin ta ce ta koshi ta wuce ɗakinta da sauri. Tana shiga ta zauna a bakin gado tana dafe kai cikin damuwa, wandonta da ta cire tun ranar da ta dawo gida ta lalibo shi a ƙasan gado. Aljihun ta laluma nan ta zaro wani farin kyanle ɗan karami a laulaye, murmushi ta yi tare da soma warware abin da yake ciki, har ta kusa warwarewa ta miƙe zumbur ta buɗe wata loka a ƙasan Drowerta ta daga jerun pant ɗinta ta sakala a cikin sannan ta rufe ruf.. Zarya ta shiga yi a ɗakin tana neman mafita, tuna sun yi da Dattijo za ta je Unguwarsu yasa ta fita da sauri palon. Wayam ta gani ba kowa, tana son ta je part ɗin Umma amma tana tsoron cin mutuncin da suke mata ita da Mom ɗinta ga mummunan kalamai, hakan yasa ta haƙura ta koma ɗaki. Dama ita ba ma'abociyar yawo ba ce kuma ba ƙawaye take da su ba sai Iman.. Bayan kwana biyu ta faɗa wa Mom ga abin da take son yi, Mom ba ta hana ta ba ta mata fatan nasara a cikin lamarin. Cikin pink abaya ta shirya tana zuba ƙamshi kai ka ce sabuwar amarya ce, duk da ba wani jiki gare ta ba amma abayar ta yi mata kyau matuƙa, ta fito ta zauna a palo tana jiran Abdul ya sa a kaita.. Zaiyan na tsaye Baba Dattijo ya ce "Zaiyan yau Anty za ta zo." Waro idanu ya yi sai ya fashe da dariya ya ɗaga rabin taɓaryar dake hannunsa ya ce "Hahaha! Anty amma dai za ta kawo min abinci ko?" Ya faɗa yana ɓata fuska. Murmushi Baba Dattijo ya yi yana gyaɗa masa kai, miƙa masa awarar dake cikin leda ya yi ya ce "To ka ci kafin ta zo." Amsa ya yi ya buɗe ledar sai ya lumshe idanu tare da buɗewa ya dubi Baba ya ce "Ni fa Sarki ko?" "Kwarai ma kuwa kai Sarki ne." Baba ya faɗa zuciyarsa na ƙara tausaya masa. Dariya ya yi ya ɗaga awarar sama yana wurga ledar awarar, Baba ya yi saurin ce masa "Ka daina yin haka mana ci za ka yi abinci ne." Soke sandarsa ya yi a ƙasa ya buɗe ya soma ci, ganin haka ya sa Baba ya juya ya nufi gidansa... Kiiii! Ya ji ƙaran mota ya yi saurin juyowa dan shi a tunanin shi hatsari ne aka yi, amma sai kawai ya ga wata ɓakar mota doguwa mai kama da ambulance ta tsaya a kusa da zaiyan, saurin nufo su ya yi sai dai kafin ya iso tuni sun ci zambar Zaiyan sun jefa shi a mota sun ja kiiii sun bar wajan... Ganin shuru-shuru Abdul bai zo ba abin ya ɓata mata rai ta miƙe ta nufi part ɗin Umma. Da Sallama ta shiga amma ba kowa, hakan yasa ta yi saurin wucewa. Fatima da Yasmin suna zaune Umma ta fito tana tambayar wa ta ji yana Sallama? Yasmim ta ce "Wa za ki ji bayan wannan mai kama da aljannu." Kwafa ta yi sai kuma ta saki murmushi ta yi saurin zuwa kitchen dan ta san Abdul tuni ya fita daga gidan. Ganin gawayi a kan wuta yasa ta yi maza ta ɗauko kasko ta ɗaura ta janyo wata ɓakar leda ta buɗe, abin da yake ciki ta kwaso ta afka nan-da-nan hayaƙi ya turnuke kitchen ɗin ta ɗauko da sauri ta kawo palo tana gyaɗa kai kamar wata ƙadangaruwa duk suka yi saurin barin palon.. Abir ta duba ko'ina ba ta ga Abdul ba hakan yasa ta yi fushi ta fito da nufin zuwa wajan Salim shi ya kai ta. Tana shigowa palon kawai ta ji hayaƙi ya mamaye mata idanu da hancinta, cikin tashin hankali ta soma tari tana riƙe ƙirji. Sosai tari ya sarƙe ta nan-da-nan numfashinta ya soma barazanar rabuwa da gangar jikinta, tun tana tari a tsaye har ta kai ga ta durƙushe tana jan numfashi ɗifak-ɗifak haka ta rarrafa tana nufar ƙofar fita. Da ƙyar ta iya kawowa bakin ƙofa tana ci gaba da tari wannan karon da ƙyar take yi, in ta yi tarin sai huhunta da bayanta sun amsa ga wani irin mugun ciwo da azaba suke mata, ji take kamar ana yankan huhun nata sai daga baki take. Salim ta gani tana ɗaga masa hannu amma sam bai gan ta ba hakan yasa ta zube a wajen yim! Ta faɗi ƙasa. Kamar an ce ya kalli gefe ya ganta, a guje ya isa tare da ɗago da ita cikin tashin hankali ya shiga jijjiga ta amma ina tuni ta sheƙa, hankali a tashe ya kira sunanta a ƙarfi. "Babyyyyy!!!! _*Ko ya za ta kaya? Ku _*hanzarta ku sayi naku kar ayi babu ku*_ _Taku har kullum Maman Nusaiba ce_ [6/20, 7:37 PM] Ummu Amjad: :37 Yamma] My Addatyna: _*~A HAKA NAKE SON SHI~*_ *Arewabooks.com: Saratalkasum1897* +966577675904 Shafi na tara (9) A kiɗime yake jijjiga ta yana kiran sunan ta amma ko motsi bai ga ta yi ba, cikin azama ya ɗauke ta da mugun gudu ya nufi part ɗin Mommy da ita yana faɗin "Baby open eyes please." Gabaɗaya hankalin masu aikin gidan ya karkata kan Salim da yake ɗauke da Abir yana magana hankali a tashe. Da ƙafa ya buga ƙofar palon ta buɗe, Mommy da ta fito da cop a hannunta daga kitchen jin an buga ƙofar ba ta san lokacin da ta saki cop ɗin ba ya faɗi ya tarwatse, ganin Abir a hannun Salim yasa ta yi saurin nufar shi tana tambayar shi "Salim lafiya na ga Mamana a haka? Ko accident ta yi?" Ta faɗa tana tallafo ta gabaɗaya suka zauna a ƙasan capet. Huci yake yana kallon kyakyawar fuskarta da ta yi wani irin haske, hannunshi ya ɗauke daga kan wuyanta ya ce "Ni ma ban sani ba Mommy, na zo giftowa ne na waiga saitin part ɗin Umma na gan ta a bakin ƙofar a zube." Kwala wa Laraba kira ta yi ta ce ta kawo ruwa mai sanyi sosai, cikin sauri sai ga ta ta kawo ruwan ganin Abir a mimmike kamar gawa ya sa ta ja ta tsaya a gefe tana dafe ƙirji. Ruwan Mommy ta shafa mata murya na rawa ta ce "Mamana ki buɗe idanunki." Ta faɗa zuciyarta cike da tunanin abin da ya same ta. Da ƙyar ta ja numfashi kaɗan shi ma sai da Mommy ta kara kunne a ƙirjinta sannan ta ji sautin bugun zuciyarta na tafiya a hankali, hakan yasa ta miƙe cikin azama ta nufi ɗakin Abir sai kuma ta kalli jakarta da ke kan kujera, hakan yasa ta yi saurin buɗe jakar ta fito da maganin da take shaƙawa ta buɗe ta shaƙa mata tana zubar da hawayen tausayin ƴarta da ɗaya tilo. A hankali ta ja numfashi hakan ya taimaka mata wajan shaƙo maganin sai ga numfashinta ya dawo daidai ta shiga sauke ajiyar zuciya. Salim ya kamo hannunta cikin tausayin ƙanwar tashi ya zuba mata idanu ganin yadda take sauke ajiyar zuciya tana ɗan motsa hannunta, gyara zama ya yi a tausashe ya ce "My Baby buɗe idanunki." Ya kuma ɗago da kanta dake cinyar Mom tana goge mata fuska, saboda zufar da ta tsastsafo mata. A hankali ta soma buɗe idanunta har ta gama buɗe shiga su a kan fuskar Salim, ta dinga kallon shi kamar ba ta san shi ba, Mommy ta taimaka mata ta tashi zaune suna mata sannu. Salim ya ja numfashi yana hamdala sannan ya ce "Baby me aka miki a part ɗin Umma da har ciwon ki ya tashi? Kuma tashin ma har ya kai matakin ƙarshe?" Ya faɗa yana zuba mata idanu. Maƙoshinta ne ya bushe ta tattaro yawun da ya rage a bakin ta haɗiye shi ko za ta iya magana, sai ta runtse idanu sannan ta buɗe shi tana motsa bakinta amma maganar ba ta fita, hannu ta ɗaga ta dafe cikinta da har yanzu da sauran ciwon ta kalli ruwan da ke hannun Mom hakan yasa ta kafa mata baki ta shanye shi tas, sai bayan ta sha ne ta ji za ta iya magana. "Kawai dai na je neman Yaya ne saboda mun yi da shi zai kaini Unguwa ko ya sa yaransa su kaini, to na ji shuru shi ne na je ɗakinsa dan na gani ko bai fito ba. Nan ta ba su labarin fitowar ta da hayaƙin da ya mamaye ta har hakan ta faru da ita. Fashewa da kuka Mommy ta yi ta ce "Ka gani ko Salim, ni ban san wani abu yarinyar nan ta tsare wa matar nan ba take son ganin sai ta kashe min ita, ai ta san sarai ba ta son hayaƙi shi ne dan ta ga ta shiga part ɗinta ta kunna mata hayaƙin. To Wallahi ta yi na farko ta yi na ƙarshe ba zan yarda ba a kashe min 'ya dan ba a son ta, haƙurina ya ƙare a wannan karon na rantsa da girman Ubangiji yau ɗin nan sai na kira an mana tsakani da ita ta daina cutar min da yarinya, ko ta manta shi Abdul ɗin ɗan'uwanta ne shi gaba da baya? Ba ta isa ta raba Abir da Abdul ba saboda su ɗin ta ko'ina sun haɗa jini dan haka dole ne ayi mana tsakani da ita in ba haka ba sai na yi ƙarar ta naji dalilin da yasa take son salwantar min da ran ɗiya." Ta ƙarashe maganar tana huci hawaye na zarya kan kuncinta, tabbas a wannan karon ta ji ba za ta juri cin kashin da ake mata ba dole a yi wa tufkar hanci kafin su ƙarasa mata ɗiyarta, ba ta san wani abu ta yi wa su Umma ba suke ɗaura mata karan tsana yanzu kuma abin ya tashi daga kan ta ya dawo kan ƴarta.. Kwafa ta yi tana kallon Abir gabaɗaya duk ba ta jin daɗin duniyar, da faɗin ɓakar maganar familyn za ta ji ko da rashin sanin inda mijinta yake? Ko kuma da zama cikin firgici da tsoron da take ciki? Shi kan shi Salim ya jinjina wa haƙurin Mommy yadda Umma da Ammi ke yi mata wasu abubuwan kamar kishiyar su, shi wani lokacin har mamaki yake in ya ji Ammin nasu na faɗin mummunan furuci akan Mom bayan yasan shi a iya sanin shi Mom ba ta shiga harkar kowa. Gyara zama ya yi ya ce "Mommy ba zan hana ki faɗa wa su Abba wannan lamarin ba, saboda kin yi haƙuri na tsayin wannan shekarun ban taɓa gani kin ce komai ba game da abin da suke miki." Shuru ta yi tana goge hawaye ta kira Lanara ta ce ta ƙaro ruwa, da hanzari Laraba ta kawo ruwan Mom da miƙa wa Abir ta ce " Ƙara shan ruwan nan ko kin ji sanyin zuciyarki." A sanyaye ta kalli Mommy ganin yadda take zubar da hawaye, abin da ba ta taɓa gani ba hawayen Mommy sai yau, ita kanta ta gaji da abubuwan Familyn nasu, amsar ruwan ta yi ta shanye tas sannan ta miƙa mata cop ɗin tana fesar da numfashi mai zafi daga bakinta, sannan ta ce "Mommy zan je ki sa a kaini sai mu tafi da Yaya Salim tun da shi ba ya nan, nasan yanzu haka Baba na can yana jira na." Ta faɗa tana yin fuskar tausayi burin ta bai wuce ta je ta yi tozali da shi ba ya yi ta mata tambayar shirme tana ba shi amsa. "Wallahi Baby ba kya jin magana, yanzu ki tashi daga sumar ki kuma ce za ki je Unguwa sai ka ce ba ki san ba ciwon rayuwarki? Sai ki kira shi ki ce masa sai gobe ko jibi za ki je." Salim ya faɗa yana haɗe fuska. Cuno baki ta yi tana tuno da Zaiyan yadda yake mata Shagwaɓa yana kiran sunanta da Anty sai ta saki murmushi, kallon Salim ta yi ta ce "Yaya Salim alƙawari fa na yi yau zan je, ka ga bai kamata na karya ba tun da dai na ji sauƙi." "To ai sai ki tashi ki tafi ko uwar kafiyar tsiya, tun da Yaya Abdul ba ya nan ki bari ya dawo mana sai ku tafi gobe in Allah ya kaimu." Ya faɗa yana hararar ta. Ita ma hararar ta aika masa tana kumbura baki ta ce "To ka manta gobe Monday akwai Makaranta?" Banza ya mata bai ce da ita komai, Mommy ta kira Abba ta ce masa lalle yau tana son ayi zama idan sun dawo daga aiki, cike da mamaki Abba ya ce mata to yana tunanin dalilin da zai sa Mommy ta bukaci ayi zama.. Firr Mommy ta ce Abir ba inda za ta je ta zauna sai Abdul ya dawo, ita kuma ta dinga kukan an hana taje sai faɗi take "Mommy alƙawari fa na yi, kin ga kyan alƙawari cikawa please ki ce Yaya Salim ya kaini." So take kawai ta buɗa idanunta ta yi tozali da shi amma Mom da Salim sun ce sam ba inda za ta je.. Ƙarfe 5:pm daidai na Yamma su Abba suka dawo daga kasuwa, burinsa bai wuce ya ji me Mommy take son faɗa, ya yi sauri ya watsa ruwa ko abinci bai ci ba ya fito daga ɗakin shi inda ya samu Fatima da Yasmin suna rigima, kallon su ya yi ya girgiza kai sannan ya yi gyaran murya suka tsaya kowacce ta runkuyar da kai. "Shashahun banza da girmanku da komai kuke rigima sai ka ce yara ƙanana." Fatima ta ce "Abba wai dole sai ta saka min abayata da takalmi da jaka, dan ɓakin ciki ba za ta sa nata kayan ba sai nawa da suka matse mata jiki." Saurin kai mata duka Yasmin ta yi tana harararta jin abin da ta faɗa ta ce "Wallahi Abba ƙarya take yi ba wani kayanta da na saka, ta nemi tata ta rasa shi ne ta ce wai wannan ce abayarta." Za ta yi magana Abba ya ɗaga hannu hakan yasa ta ja bakinta ta yi shuru. "Ki kira Mamanku ku ce ta same ni a part ɗin matar Yaya har ku gabaɗaya." Yana faɗin haka ya wuce daga palon. Fatima ta shiga ta samu Ammi tana waya sai dariya take ganin Fatima yasa Ammi saurin cewa "Zan kira in an jima." A fusace ta kalli Fatima ta ce "Ke wacce irin shashashar yarinya ce Fatima? Ya za ki shigo min ɗaki ba izini?" Murguɗa baki Fatima ta yi tana harare-harare tare yin ƙasa da murya ta ce "Yo izinin me zan nema in zan shigo? Ai nasan da wa kike wayar." "Me kika ce Fatima?" Ammi ta faɗa a fusace. Saurin girgiza kai ta yi ta ce "Ni babu abin da na ce Abba ya ce mu same shi a part ɗin Mommy." Wani dogon tsaki ta ja "Tsuwwww! Su kullum ayi ta tara mutane kamar wani abin arzƙi za a yi , sai ki juya muje gani nan." Ta faɗa tana faɗa wa toilet, ita kuwa Fatima ta juya ta fita.. 5:30pm kowa ya hallara a palon har Grandma da ba ta fi minti 15 da dawowa daga ganin likita ba ita ma ta hakimce tana kaɗa ƙafa sai bin kowa take da kallon tara saura uku.. Abba ya dubi Mommy ya ce "Matar Yaya me ya faru kika kira taron gaggawa?" Sai da ta yi kwafa tana kallon Umma da ta yi kicin-kicin da fuska ta ce "Kabir ka shiga tsaknina da wannan katafilar matar taka, idan kuma ba haka ba zan aje duk wani ganin girma da ƙimarka da nake na maka ta a kotu a bi min haƙƙina da 'yata." Dafe ƙirji Umma ta yi tana kallon Mommy a masifance ta ce "Kan uban can! Sadiya wai saboda ni aka yi wannan taron? Me na miki da kike son zubar min da girma na a gaban yara?" Ta faɗa kamar za ta kai mata duba. "Kin fi ɗan takon kano sanin hanyar tasha! Ki fita harkar 'yata da ɗan'uwanta tun da dai ai ba ke kika haife shi ba ballantana ki ce in ya sake shiga lamarin ta za ki tsine masa, ke ba ki isa ki raba Abdul da Abir ba dan ba ki da haɗi da shi iyakacinki ke matar Babansa ce ba uwarsa ba." Mommy ita ma ta faɗa a zafafe yau ji take duk abin da aka mata ya zo ƙarshe, kuma ta daina ɗauke kai a lamuran gidan. "Lalle Sadiya kin ci kin sha kin tada kai dole ki faɗa min wannan maganar, yau ni kike yi wa gorin haihuwa Sadiya? Daɗin ta ma ni ma ba juya ba ce na haifi biyu ga su nan a zaune. Sannan da kike maganar Abdul ina ruwana da lamarin shi, kenan ɓakin ciki kike dan ina riƙe shi saboda ni matar uba ce duk abin da ya faru a tsakanin su sai a manna min laifi?" A fusace Mommy ta ce "Duk abin da kika ce haka ne! Na faɗa miki dai ki daina shiga harkarsu tun da ba ke kika ji ciwon kawo ɗaya daga cikin su duniya ba, in kuma akwai wanda kika haifa sai ki mana bayani mu ji. Wallahi haƙura na gaf da ƙarewa a gidan nan, idan da kun ci mutumcina na rabu da ku kuna cin darajar mazajenku to yanzu zan aje ganin girman su nake rama duk abin da kuka min, haba ina dalili ina mafari na gaji!" Ta ƙarashe maganar cikin ɗaga murya gabaɗaya jikinta rawa yake saboda in har ranta ya ɓaci ko'ina na jikinta rawa yake. Kukan ƙarya Umma ta fashe da shi tana sa mayafinta ta rufe fuska "Waiyo Allah! Wai yau ni ake yi wa gorin haihuwa? Laifin ka ne Daddyn Abdul da ba ka bani Abdul na rike ba ai da ba a min gorin ba ni na haife shi ba, sannan ke da kike wani tunkaho ke nawa ɗiyan gareki? Ba ɗaya tal gareki ba kamar rai? Ita ma sunan ɗayar ce dan rabi cuta ta cinye ta, ɗiyar da ba za shiga kitchen ta miki girki mai hayaƙi ba meye amfanin ta?" Ta faɗa tana shafe fuskarta tare da hararar Abir da ta yi kicin-kicin da fuska tana kallon Abdul. Wani irin zafi da raɗaɗi ne suka ziyarci zuciyar Mommy, ta danne hawayen da ke ƙoƙarin zubo mata ta ce "Alhamdu Lillah duk da haka ina gode wa Allah da ya bani mai cutar ma, nasan dai ai ba ita ta ɗaura wa kanta rashin lafiyar ba Allah ne ya jarrabe ta da ciwon, idan ya ga dama lokaci ɗaya zai yaye mata." "Tsuwwww! To yaushe kin taɓa gani mai cutar asma ya warke ya dawo irin na kowanni ɗan'adam?" Cewar Ammi. Kwafa Mommy ta yi ta ce "Ke kuma faɗi ba a tambaye ki ba wa ya kasa da ke da har kika tsoma mana tsantsaman bakinki a cikin magana? Ki bari kema ina nan dawowa kanki Wallahi." Ta faɗa tana gyara zama.. Tun da suka fara cecekucen Abba da Daddy suka zuba musu ido suklna kallon ikon Allah, ganin ba za su ƙyale ba ya sa Abdul cewa "Mom don Allah ki rabu da su a tattauna a shayo kan wannan matsalar, da girmanku da komai kuke sa'insa a gaban yara." "Dama sai ka ce ta rabu da mu mana tun da ga mahaukata ka samu." Banza Abdul ya yi da Ammi bai ce komai ba, dan in ya ce zai kara magana ba zai faɗi kalma mai daɗin ji ba. Abba da ranshi ya gama ɓaci ya ce "Wallahi ban ji daɗin abin da kuka yi ba." Daddy ya ce "Yanzu dai duk ba wannan ba matar Yaya ki faɗa me ke faruwa." "Kabir meye ma bai faru ba, ba wannan karon kaɗai na ne Matarka take son kashe min ɗiya, da zarar ta ga ta je part ɗin ta sai ta kunna hayaƙi alhalin ta san lulurar ta ba ta son shaƙar hayaƙi, amma dan mugunta sai ta yi dan haka wannan ya zama shi ne karo na ƙarshe da za ta kuna wa 'yata hayaƙi dan ta je part ɗin su." Labarin yadda Salim ya kawo Abir ta ba su ita ma Abir ta faɗi farkon shigar ta babu wani hayaƙi a palon da ta fito ne ta ga ya turnike ta.. Sosai ran Daddy ya ɓaci da jin abin da Umma ta aikata ya ce "Amma Wallahi Baraka kin ba ni mamaki." Saurin katse shi Umma ta yi ta ce "Ok haka ma za ka ce?" Cikin fushi ya ce "E haka na ce! Kuma ke ba ki isa ki hana Mamana ta shiga cikin gidana ba kin yi kaɗan, Abdul kuma ba ki da ikon hana shi kiran ta ta zo inda yake a duk lokacin da yake so tun da jininsa ce in ba ki sani ba ma yau ki sani, Mahaifiyar Abdul Ƙanwar matar Yaya ce uwa ɗaya uba ɗaya." Ya faɗa yana nuna Mommy da hannu. "Tsuww! To sai me? Ƙawar ta ce dai ba Ƙanwar ta ba malam gyara maganarka in mantawa ma ka yi." Umma ta faɗa cike da tsanar Mommy. Daddy ya kuma yin magana a kufule "To yau ai sai ki sani Ƙanwarta ce dan haka banu ruwan ki da lamarin Abir da Abdul." Ya faɗa yana nuna ta da yatsa... A masifance Umma ta miƙe tsaye ta ce... *Hmm cakwakiyar familyn Maitama kenan mu je zuwa🤓* Taku ce dai har kullum Maman Nusaiba. [10/25, 3:38 Yamma] My Addatyna: _*~A HAKA NAKE SON SHI~*_ *Arewabooks.com: Saratalkasum1897* _WhatsApp number: +966577675904_ Shafi na goma (10). A masifance ta miƙe nuna Abdul da yatsa ta ce "Lalle Kabir ban san cewa kai munafiki ba ne sai yau, wai kana nufin Abdul ɗin ne ɗan sister Sadiya? To Wallahi ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa, ni za ku rainawa hankali?" Sosai ran Daddy ya ɓaci har ya ɗago da niyar mayar mata da martani suka haɗa idanu da Grandma, hakan yasa ya sunkuyar da kanshi ƙasa yana kissima kalar rashin mutumcin da zai yi wa Umma in sun koma part ɗin su. "Na ga kun wani yi shuru kuna kallo na kamar wasu mujiyoyi kun zuba min idanu?" Ta kuma faɗa tana harare-harare saboda takaici, duk zaman ta da Daddy ba ta taɓa sanin Abdul ɗan sister Mommy ba ne sai yau, hakan yasa ta cika ta yi fam sai huci take kamar wata kasa dan ranta ya yi mugun ɓaci, sai yanzu da take kallon Abdul ta ga yadda kamanninsa da Mommy suka fito tar kamar fuskarta ce aka manne mishi. Wani irin tsaki ta ja tana sauke ajiyar zuciya. Mami jin ta yi jam'i yasa ta kalle ta a wulaƙance ta ce "Duk iskancin ki Wallahi kika ce za ki ja da ni sai na nuna miki bakin rijiya a wajan wasan makaho makaho ne! Ki yi da waɗanda kika raina dai ba da ni ba dan na dama ki na shanye." Ta faɗa tana jan tsaki ta miƙe fuu ta bar palon, ganin haka yasa Fatima ta mara mata baya. Zage-zage Umma ta dinga yi tana cewa Daddy ya ci amanarta da ya ɓoye mata wannan maganar, shi kuma bai ce mata komai ba ta yi ta faɗa har sai da ya gaji ya ce "Baraka naƙi faɗa mikin ki kama ni ki dakeni tun da ke kika haifeni." Ya faɗa a fusace. Ita ma a fusacen ta ce "Kai dai ka ji kunya, lokacin da na dawo daga America za mu yi aure ba ce min ka yi mahaifiyar Abdul ƙawar Sadiya ba ce? Ashe duk ka lumke ni a baibai ban sani ba ka mayar da ni wata sauna irin ka?." Grandma ta kalli Umma ta ce "Ke dai Wallahi Baraka an yi asarar haihuwar ki, yanzu mijin naki ne kike faɗa wa maganar nan? To fita ki bar min gida ki koma naki tun da ba za ki tsaya a miki bayanin komai ba." "Dama Inna ai haka za ki ce, saboda mu ba ƙaunar mu kike ba shi ya sa har da ke aka rufe ni da maganar nan." "To wai dole ne sai an faɗa miki dangantakar Mamana da Mommy ne? In an faɗa mikin ma mai zai amfane ki da hakan?" Abdul ya faɗa yana zaro mata idanu. "Kai dalla matsa ka ba wa mutane waje, ni ba da kai zan yi ba da ubanka nake da kuma wannan munafukar da take wani cewa za ta yi ƙarana." Ta faɗa tana nuna Mommy ta wuce fuu tana sababi. Iman ta tashi ta isa gaban Daddy ta durƙusa fuska dauke da damuwa ta ce "Daddy don Allah ka yi haƙuri ka da ka kula Umma, ni na ga lokacin da ta sa hayaƙi dan ta ga Anty Baby ta shigo gidan, ke ma Mommy ki yi haƙuri kar ki biya Umma kin ji." Ta faɗa a sanyaye. "Ba komai Iman ba zan biya ta ba Allah ya miki albarka." Cewar Mommy. Amin ta amsa tana dawowa kusa da Abdul ta ruƙo hannayensa murya na rawa ta ce "Ya.. Yaya don Allah ka yi haƙuri da abin da Umma take ma, Wallahi ina ciwon yadda take muku mummunan furuci." Ta ƙarashe maganar tana faɗa wa jikinta, sosai take kuka akan halin mahaifiyarta ta.. Rungume ta ya yi yana shafa bayanta, sosai yake jin son ƙanwa tashi na ratsa shi saboda hankali da nutsuwarta. Ɗago da ita ya yi ya share hawayen har yanzu ya kasa ce mata komai, sai da ta ƙara komawa jikinsa tana faɗin "Don Allah Yaya ka yi haƙuri." Sai a lokacin ya mutaa lips ɗinsa saboda mugun takaicin Umma da ya tsaya masa a rai, ya rasa mai ya mata da take bin da da mugun nufi? Lumshe idanunsa ya yi wanda suka yi jajur saboda ɓacin rai ya buɗe su yana kallon Iman da ta yi lamo a jikinsa tana kuka marar sauti.. "My little karki damu kin ji, ki daina damuwa da halin Umma." Ya faɗa yana sauke numfashi a wahalce saboda da yadda ƙirjinsa ke masa wani kalar zafi.. Murmushi ta yi ta goge hawaye ta ce "Love you Yaya." Ta ƙarasa tana manna masa kiss a kumatu. Shi ma kissing ɗin ta ya yi kamar yadda ta masa sannan ta tashi ta dawo kusa da Abir, kumatunta ta kamo tana murmushi ta ce "Anty Baby kin haƙura ko?" Kallon ta ta yi cike da so da ƙauna, tana jin daɗin yadda Iman ke damuwa da damuwar su ita da Abdul, ga kuma duk gidan ita kaɗai ke shiga harkar ta su yi wasa da dariya har take mata kallon ƙawa kuma aminiya mai saka ta farin ciki in ta gan ta a damuwa. Itama kumatunta ta ja tana murmushi ta ce "My little ai ni dama kodayaushe ina cikin yim haƙuri karki damu." Ta faɗa tana shafa gefen fuskarta.. Dariyar jin daɗi ta yi ta gyara zama.. Daddy ya dubi Grandma ya ce "Wallahi Inna kawai alfarmarki Baraka ke ci am.. Daga masa hannu Grandma ta yi ta ce "Kar ka ƙarasa Kabiru na san da hakan ba daɗin zama kake ji da ita ba, ka yi haƙuri komai zai wuce." To kawai ya ce sannan suka ci gaba da tattaunawa.... Motar da ta ɗauki Zaiyan ta dinga sharara gudu a tsakiyar titi, tun suna gararanba a titina har suka fita daga garin suka kama hanya ɗoɗar. Shi kuwa Zaiyan tun da suka jefa shi a mota ya dinga kiciniyar kwatar kan shi yana ƙoƙarin ɗaukan makaminsa amma da yake sarkin yawa ya fi sakin ƙarfi sai suka danne shi, hannu da ƙafa suka ɗaure masa da ƙyar da suɗin goshi shi ma sai da suka shaƙa masa faudar gusar da hankali. Ko minti goma cikakke bai yi ba faudar ta sake shi ya dinga kwarara ihu yana faɗin "Ina za mu je? Za ku kaini wajan Anty ne?" Jin abin da ya faɗa yasa ɗaya daga cikin su ya ce "E can za mu kaika ka ganta ai kana so ko?" Ya faɗa a tsorace saboda kafin su ɗaure shi ya mangare shi a gefen wuya. Dariya ya yi ya ce "Wallahi kun birge ni." Ba su sake kula shi ba ya yi ta surutansa har ya gaji ya yi shuru yana kallon gefen hanya ta glass ɗin motar ai kuwa ya ga bishiyoyi na gilmawa ya zabura ya ce "Kai ku tsaya ga Anty nan tana bin mu da gudu ku tsaya ta hayo." Ya faɗa yana nuna musu bishiyoyin. Su kuma msuka yi banza da shi ya dinga surutu har suka yi tafiya mai nisan gaske, dan sai bayan Magariba suka isa wani gida da ke cikin tsakiyar daji. Hon suka yi aka buɗe musu get suka shiga suka yi packing tare da fitowa suka fito da Zaiyan , wanda tun kafin su iso suka rufe masa idanu, ana fito da shi Maigadin Gidan ya kalle shi cikin tausayawa har aka shige da shi ciki.. Palo ne babban wanda yake shaƙe da kujeru irin na taron wajan dinner aure, suna isowa wata murya daga jikin bango ta shiga yin magana. "Sannun ku da zuwa Jarumai, dama dai ogan ku ya faɗa min cewa za ku yi aiki kamar yadda nake so ku shigo ciki da shi." Jin yadda aka yaba musu kowanne ya shiga hura hanci yana jin kansa shi fitaccacen jarumi ne, suka yi kama-kama biyu suka kama hannuwa biyu suka kama ƙafafuwa suka shige wani ɗaki da shi haske kamar ba Magariba ba. Wani girgegen mutum ne zaune da jajan kaya kansa ɗaure da ɓakin ƙyalle yana ganin su ya kwashe da dariya. "Hahaha! Wannan ya haɗa duk abin da muke buƙata, amma duk da haka sai an kira Alhaji, ku kira min shi ya zo a gaban shi za ayi komai." Mutumin ya faɗa yana tsoma wani gashin doki dake hannunsa a cikin wani ɓakin ruwa ya zazzaga gashin a fuskar Zaiyan, nan-da-nan Zaiyan ya birkice yana kururuwa saboda tsananin azabar da ta shige shi. Dariya suka yi a tare suna sake matso da shi gaban Mutumin.. Ɗaya daga cikin su ya ɗauki waya ya kira Alhaji yana ɗauka ya koro masa jawabi ya ce ai ga shi a bakin ƙofar gidan zai shigo ciki, bayan ya kashe ya sanar da Mutumin Alhaji ya iso sai suka koma gefe suka ƙame kamar wasu mutanen arziki. Cikin dakakkiyar shadda Alhaji ya shigo yana washe baki na ganin an cika masa aiķinsa ya shiga yi wa Mutumin kirari. "Nadumbuza mai abin mamaki, yau dai ga shi an cika aiki ba tare da samun wata tangarda ba." Murmushi Nadumbuza ya yi ya tashi ya ɗauko wannan ruwan ɓaki a cikin ƙwarya ya miƙa wa Alhaji ya ce "Alhaji burinka ya kusa cika ga wannan ka shanye shi tas, sannan ka ƙoƙarta ka ƙarasa ɗayan aikin kafin nan da wani lokaci. Shi kuma wannan za mu yi aiki a kansa yau ɗin nan, amma kafin a kai ga haka sai an yi masa tatar jini an ba wa Uwa Dudu ta sha kafin ta biya mana buƙata." Da sauri Alhaji ya am shi wannan ɓakin ruwan ya shanye tas burinsa bai wuce ya ga an gama komai ba, Nadumbuza ya buɗe wata ƙwarya ya zaro wuƙa mai mugun kaifi ya nufi Zaiyan da ke kwance kamar gawa, saita maƙoshinsa ya yi zai yanka sai ya fasa ya sa aka kunce masa ɗaurin. Kan tsintsiyar hannunsa ya dan yanka sai ya ɗauko wani abu mai tsini ya soka a cikin yankan ya shige cikin hannun Zaiyan har sai da ya hudo ta baya sannan ya cire yana dariya, ƙwarya ya sa ya tari jinin da yake zubowa yana lashe baki tare da yin wasu irin yare yana ɗaga hannu yana shafa wa a jikin Zaiyan. Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ƙwarya ta cika taf da jini amma jinin bai daina zuba ba, sai da ya sa harshe ya suɗe inda duk jinin ya zuba sannan ya koma gefen ƙwaryayyakin dake jere a wajan ya buɗe ɗaya daga ciki ya ɗauko wani magani, buɗewa ya yi ya zuba a ƙofar yankan da ya yi masa nan-da-nan jinin ya tsaya cak kamar ƙafewar ruwan sama . Jinin ya ɗauke ya dinga zagaye tsakiyar ɗakin yana surutai, bayan ya gama suka shiga wani ɗaki da ke cikin ɗakin. Ɗaki ne mai girma sosai yana da duhu sosai ko tafin hannunka ba ka gani, amma suna zuwa tsakiyar ɗakin wani irin ƙara ya dinga kai-kawo cikin kunnuwansu sai ga haske ya baiyana suka yi saurin zube wa a gaban Uwa Dudu suna faɗin "Uwa Dudu mai share mana kuka ke ce gatanmu ga sadaukarwar an kawo miki." Nadumbuza da Alhaji suka faɗa a tare. Cikin wata iriyar murya aka soma magana. "Tabbas yau kun faranta min , kuma kun cika masu biyayya a gare ni dan haka zan yi muku duk abin da kuke so, sai dai ku sani wannan mahaukacin da kuka ɗauko yana ɗauke da wani haɗari wanda ni kaina na kasa ganowa, tun da suka tunkaro gidan nan sandar girman Sarautar gidan nan ta girgiza abin da ba ta taɓa yin haka ba. Hakan yasa na gane cewa lalle fa jinin wannan bil'adaman shi ne jinin da zai ƙara min ƙarfi fiye da tunani, dan haka dole ne duk sati ake kawo min jininsa ina sha." Aka yi shuru sai ga wata halitta mai kama da Mage ta iso ta amshe ƙwaryar jinin ta ɓace, hakan yasa Nadumbuza ya ce "Mai girma Uwa Dudu yanzu to me ya kamata ayi akan wannan yaro?" "Ni zan yi wannan aikin kawai ku tafi, kai ma Nadumbuza na ba ka izini ka je ka ga gida." Ana gama faɗin haka hasken ɗakin ya ɗauke ɗif, hakan yasa suka yi saurin fita... Alhaji ya ɗauko kuɗi ɗauri biyar na rafa ya aje wa Nadumbuza tare da yi masa kirari sannan suka fita shi da yaransa, shi ma Nadumbuza kalaman tsafi ya yi ta yi ya ɗauke Zaiyan ya sa shi cikin ɗaya ɗakin sannan ya fita. Wani rami mai matakala Nadumbuza ya bi daga bayan dakunan ya shige ciki.. BAYAN KWANA Abir na dawowa daga makaranta ta shirya ta matsa wa Abdul sai sun tafi Unguwar *Deboli*, bai musa mata ba suka tafi su uku har da Iman.. Suna fita sai ga Uncle Aruf ya karyo kwana layin, ganin motar Abdul sai ya dinga danna musu oda da ƙarfi yana bin su. Abdul ya ankare da motar da take bin su ya dakata, Uncle Aruf ya fito cikin gayun shi ya ce "Hello my Brother and Baby." Cuno baki Abir ta yi tana jin haushin zuwa Uncle Aruf ganin zai tsayar musu da tafiya, ita kuma gabaɗaya hankalinta ya kasa kwanciya so take ta je ta ɗauko Zaiyan daga wannan ƙazamin wajan, ga kewar shi da ta addabe ta har gizo yake mata in ta zauna. Murmushi Abdul ya yi ganin yadda ta yi kicin-kicin da fuska ya ce "Baby ki yi haƙuri Uncle ya zo yau ba za mu samu damar zuwa ba mu koma." Nan-da-nan idanunta suka cicciko da hawaye ta kifa kanta a cinya ta soma rero kuka, shi kuwa Uncle Aruf ganin Abdul ya soma yin baya-baya da motar sai ya koma tashi suka dunguma cikin gidan. Tana fitowa ta dinga kuka ta shige ciki suka mara mata baya. Da Sallama suka shigo inda suka samu Grandma da Mommy da kuma Laraba na mammatsa wa Grandma ƙafa tana zuba mata surutu.... "Good Afternoon Grandma, i miss you so much." Uncle Aruf ya faɗa yana wani ɗage wa Grandma gira. Ai kuwa kamar jira take ta amshe ƙafarta daga hannun Laraba tare da ƙanƙance idanu ta ce..... _🤓an taɓo mana Grandma ɗin mu🤭_ _*Daku har kullum Maman Nusaiba ce*_ [6/20, 7:40 PM] Ummu Amjad: My Addatyna: _*~A HAKA NAKE SON SHI~*_ *Arewabooks.com: Saratalkasum1897* +966577675904 Shafi na (11) Ƙanƙance idanu ta yi cike da Jin haushin turancin da ya mata ta ce "Kai Arufullahi ka fita idona na rufe kafin na ci kan ubanka mai furfura." Ta faɗa tana hura hanci. Dariya Uncle Aruf ya yi ya tako ya iso gaban ta yana murmushi ya ce "Grandma ke ko irin ɗan missing ɗina ba ki yi ba? Da kika ganni maimakon ki tashi ki tarboni kina min oyoyo sai kuma ki ce haka, yanzu dai ya kike?" Ya faɗa yana kallon Laraba da ta ƙura masa idanu ta saki baki, ita tun da take ba ta taɓa jin wanda turancin shi ya shiga ranta ba irin Uncle Aruf ga ya ɗau wanka irin na gogaggun 'yan boko sai zuba ƙamshi yake, gyaɗa kai ta yi jin kamar an dafa ƙafadarta ta juyo dan ta ga waye haka, ganin shi ta yi yana mata murmushi ya ce "Hello beautiful how are you?" Ai kuwa Laraba ta washe baki cikin jin daɗin ɗan gayu kamar Uncle Aruf ya kula ta , duk da ba ta iya turanci ba amma ta ji daɗi kuma ta san ba zai ce mata ƙazama ƴar ƙauye ba kamar yadda Abdul ke faɗa mata kullum. Baki ta riƙe tana ƴar dariya ta ce "Alkur'anin Allah i love you ɗan gayu, amma dai kai bature ne ko?" Dariya ce ta so subcewa Abir jin bin da Laraba ta faɗa dan ta san dai Laraba ba turanci ta iya ba, amma ta fuskanci tana mugun son koyon turanci. Abdul ya ja tsaki ya dubi Uncle Aruf ya ce "Uncle wannan fa mai aikin Mommy ce har kake wani sakar mata fuska, sannan ba wani sanin turanci ta yi ba I love you ma da ta ce ma ba ta san mai kalmar take nufi ba." Ya faɗa yana hararar Laraba da ta yi lakwas, nan-da-nan nan hawaye ya cika kwarmin idanuwanta ta sa hannu ta goge, a ranta tana aiyanawa dole ma ta koyo turanci ko dan Abdul da yake mata cin zarafi yana kiranta da daƙikiya ƙazama, so take wata rana ta nuna masa ita ba daƙikiya ba ce kamar yadda yake kiran ta da kalmar. Sosai zuciyarta ke mata zafi da ƙuna ta ɗago ta dubi Uncle Aruf da bai ce komai ba sai kallon ta yake ta sa gefen hijabi ta goge hawayen da suka silalo kan kuncinta ta ce "Ni dama ban ce na iya Ingihi ba , dan ban yi makarantar boko ba sai Islamiya ita ma ta shekara ɗaya ce na yi, amma ai nasan kai ɗan gayu ne kuma ba za ka kira ni da daƙikiya ƙazama ba kamar hi?." Ta ƙarashe maganar tana zuba wa Uncle Aruf ido.. Ji ya yi ta ba shi tausayi ya ɗuka kusa da ita ýa ce "Beautiful ki rabu wannan shashashan yaron kin ji, karki sake kuka dan ya ce miki daƙikiya ke mai hankali ce kin fi ƙarfin daƙikiya." Gyaɗa masa kai kawai ta yi sannan ta tashi ta nufi hanyar da za ta sada ta da ɗakin kwananta... Sai da ya ga ta ɓace wa ganinsa sannan ya sauke ajiyar zuciya ya dubi Grandma da ta harɗe hannayenta a ƙirji tana girgirza ƙafa, dawo da kallon shi ya yi a kan Abir ya ga ta yi fuska tausayi ya ce "Baby What happened?" Girgiza masa kai ta yi ba ta ce komai ba dan ita gabaɗaya hankalinta yana can tunanin Zaiyan da son ta gan shi ya yi ta mata surutun nan nashi mai sanya ta nishaɗi, ajiyar zuciya ta sauke ta ƙara kawar da kanta dan kar ma ya kuma mata wata tambayar.. Mommy ta nisa ta ce "Aruf shi ne zuwa ba ko sanarwa? Sannan da ka iso ko ka zo gidan nan sai yau ka shirya ka zo mana?" Gyara zama ya yi ya ce "Am so sorry Mom, Wallahi kin san bana son Khairat ta san na dawo shi yasa na yi zuwan bazata." Murmushi Mommy ta yi ta ce "To barka da zuwa ya mutanen can?" "Suna nan lafiya sun ma ce a gaishe da ku, Grandma na miki odar goro daga can." Jinjina kai kawai Grandma ke yi ta kuma ƙi ɗauke hannayenta daga bisa ƙirji, sai da ta shirya dan kanta ta sauke ta dubi Mommy ta ce "Sa'ade Wallahi suma Tallahi sai na ci mutimcin Abdullahi a gidan nan, akan me zai takurawa yarinyar mutane da ya zo ya ganta sai ya yi ta faɗa mata magana mai zafi? To ni ba ƴar banza ba ce da zan bari ana cin zarafin ɗan'adam ina zaune ina kallo ba zan iya tashi na maka dukan mutuwa a palon nan. Kai wa ya taɓa yi ma gorin ba ka da aure? Dan ka yi wani ɗan iskan bokon ka shi ne har kake wani gadara kai mai ilimi ne? To ka fita idanuna na rufe kafin na zazzabga maka mari irin wanda na taɓa yi wa ubanka Kabiru." Shi dai bai ce komai ba kansa a sunkuye yana ta daddana waya, shi kawai ba ya so ne ya shigo ya gan ta ba kyan tsari duk sai ya ji zuciyarsa na tafasa na barin kanta da ta yi ba gyara, ga bakinta da yake mugun wari in ta yi magana hakan ya tabbatar masa ba ta yin broch sai warin dauɗa da na baki, hakan ne ya sa duk ya ji ya tsane ta ga ƙarin abin haushin ma kayan da ya sayo wa Abir ta kwashe kusan rabi ta ba ta tana saka wa ko kyau ba sa mata saboda rashin gyaran jiki. Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Yi haƙuri Grandma, kawai ni bana son ƙazanta ne shi ya sa nake ce mata ƙazama. " "Na ci butar ubanka Abdullahi, da haƙurin ya mutu sadakar nawa ka bayar? Shashasha kawai tashi ka bar mana palo ka koma na gidanku, da alama dai Baraka ta soma koya ma ɓakin hali." Ta faɗa a fusace kamar za ta kai masa duka. Bai sake cewa komai ba Mommy ta tashi ta kawo wa Uncle Aruf abinci da lemuka masu sanyi sannan ta dawo ta zauna ta ce "Babana ka daina shiga harkar Laraba please, babu ruwanka da ita ta yi duk abin da take so ai ƙuruciya ce za ta fasa duk abin da take da zarar ta yi hankali." To kawai ya ce wa Mommy ya miƙe ya bar palon ya nufi ɗakin Grandma, ai kuwa ta juyo ta ce "Marar mutumci dawo kar ka shigar min ɗaki tun da ita ta gyara min." Ko sauraron ta bai yi ba ya yi wucewar sa yana jin haushin yadda suka taru suna masa magana akan Laraba.. Abir ta dubi Uncle Aruf ta ce "Uncle ina tsaraba na?" Sai da ya haɗiye lomar da ya kai baki sannan ya ce "Oh! Kin ga na manta ta cikin mota, ki bari in na gama zan ɗauko miki ko nasa Maigadi ya fiddo yanzu? Ya ƙarashe maganar yana mai tambayarta. Cikin zumudi da son ganin abin da ya kawo mata ta ce "Yes, Uncle ." Maigadi ya kira a waya ya ce ya zo zai sa shi wani aiki sannan ya kashe, yana aje wayar ya shigo da sallama ya rusuna ya gaishe da su Grandma Mommy ta amsa amma ban da Grandma da ta yi shuru tana bin su da kallo, ya mika masa makullin motar ya faɗa masa abin da zai ɗauko sannan ya fita. Bai ɗauki lokaci ba ya dawo da manyan ledoji baƙaƙe ya aje, godiya ya masa sannan ya ɗauki leda daya ya miƙa wa Grandma ya miƙa Mommy ɗaya ya miƙa wa Abir, ta yi saurin amsa tana kwance ɗaurin sai murmushi take har ta gama kwancewa. Tana buɗewa ta ga dogayen abayu masu kyau 'yan Dubai guda 6 sai riga da wando jins masu kyau sun kai kala goma, ta yi ta ɗaga wa tana dariya tana faɗin "Thank you my Uncle, Allah ya ƙara arziki mai yawa." Ta faɗa tana kara ɗaya daga cikin abayar. Amin ya ce mata yana murmushi, Mommy kuwa Material ne kala biyu sai atamfa kala uku sai mayafan su, haka Grandma ma atamfofi kala shida ya kawo mata har da takalmi da mayafi sai sa masa albarka take kamar ba yanzu ta gama zagin shi ba... Ɗaki ta nufa ta bar su a palon dan tana so taje ta gwada kayan ta ga yadda za su mata, shi kuma ya wanke hannu ya dubi Mommy ya ce "Mom wai ya ake ciki akan lamarin Abie? Sun kira kuwa?" Nan-da-nan annori fuskar Mom ya ɗauke ta girgiza kai ta ce "Ai dama tun da suka sa ce su ba su taɓa kiran ɗaya daga cikin familyn gidan nan ba har Abir ta samu ta kuɓuto daga hannun su." "To amma Mom ita Baby za ta iya gane ko da fuskar mutum ɗaya daga cikin su ne?" Ya faɗa yana jin mugun kewar Abie har idanuwansa sun kaɗa sun yi jajur . "Kayya Aruf! Ba tambayar da ba a mata ba amma ta ce ba ta taɓa ganin ko da fuskar mutum ɗaya ce duk fuskokinsu a rufe suke zuwa inda take." Nan ta ba shi labarin yadda aka yi mahaukaci ya cece ta, sosai Uncle Aruf ya cika da al'ajabi matuƙa wai mahaukaci ne ya ceci ƴar'uwarsa? Gyara zama ya yi ya ce "To ai kuwa ya kamata itama ta yi wani abu game da mahaukacin nan." Ya faɗa yana kallon Mommy. Nisawa ta yi tana murmushi ta ce "To ai yanzu haka maganar da nake ma can ne za su je ka tsayar da su, ta ce tana son ta kai shi Asibiti ko Allah zai sa in an ɗaura shi akan magani ya samu sauƙi." "Yawwa very good." Ya faɗa yana yin jinjina da hannu. A fusace Inna ta ce "Kasan Allah n.. Ba ta ƙarasa ba ya yi saurin tarar numfashinta ya ce "Yes." Sake fusata ta yi ta ɗauki filon da ke kusa da ita ta jefa masa ya cafe yana dariya ta ce "Wallahi sai na zazzage ka in ka sake yi mana wannan yaren muna magana." Dariya ya kuma yi Grandma ta ƙanƙance idanu za ta yi magana suka ji sautin kukan Abir ta iso palon ta faɗa jikin Mommy. "Ke lafiya kike kuka." Mom ta faɗa tana ɗago da ita. Kasa magana ta yi saboda kukan da ya ci ƙarfin ta har da ta tsagaita tukun ta ce "Waiyo Allah! Mommy na shiga uku na lalace ya zan yi da rayuwata? Shi kenan za su kashe bawan Allah bai ji ba bai gani ba ya zan yi da hakkinsa Mommy?" Ta faɗa tana kara fashewa da kuka.. Cikin rashin fahimta Uncle Aruf ya ce "Baby me yake faruwa kike wannan munanan kalaman? Ki sanar da mu mana." Kasa ba shi amsa ta yi tana kuka har da majina, sosai hankalin su ya tashi suka zuba mata idanu har sai da ta yi kuka mai isarta sannan ta ɗago hawaye na zarya kan kuncinta ta ce "Uncle ina Yaya Abdul don Allah ku kira min shi Wallahi zuciyata za ta buga, na ja wa bawan Allah masifa." Ta faɗa ta sake kuma rushewa da kuka wanda ya fi na yanzu tayar da hankali. Ganin haka ya sa Uncle Aruf ya kira Abdul ya ce ya yi maza ya fito akwai matsala, hankalin Abdul ya tashi ya fito daga wanka kenan a ɗakin Grandma ya jiyo sautin kukan ta, ya ɗauka kukan da ya zame mata jiki ne take yi sai da Uncle Aruf ya ce ya zo sannan ya yi saurin fitowa.. Da sauri ya nufo wajan Mommy yana faɗin "Baby me ya faru?" Jin muryarsa yasa ta tashi daga jikin Mommy ta faɗa jikinsa tana sakin kuka ta ce "Yaya na shiga uku sun sace shi." "Wa kenan aka sace?" Ya faɗa a kiɗime. "Zaiyan ɗin mana sun sace shi." Kowa nanata sunan yake dan su ba su san akwai wani mai suna haka a cikin familyn su ba, sai da ya sake tambayar ta sannan ta tsagaita kukan tare da dagowa daga jikinsa ta ce "Yanzu da na shiga ɗaki sai na kira Baba ina son na ce masa yau ba za mu samu damar zuwa ba sai gobe da Yamma sh... Kasa ƙarasa maganar ta yi kuka ya ci ƙarfinta har jikinta rawa yake, ganin hakan yasa Abdul ya kama hannunta suka zauna a kan kujera Uncle Aruf ya miƙa mata ruwan da ke gefensa ta amsa ta shanye duka, haka ta dinga sauke ajiyar zuciya akai-akai har sai da ta ji ta dan samu sauƙi sannan ta soma faɗa musu komai. "Baba ya ce min suna tsaye da Zaiyan yana ce masa gani nan zan zo yana murna sai ya juya ya tafi, ko nisa bai yi ba wata mota ta zo ta ɗauke shi, Yaya don girman Allah ka taimakeni ka samo min shi Wallahi yana cikin halin neman taimako. Dama nasan dole su dawo su neme shi tun da shi ya ceceni a hannunsu dan su rama abin da ya musu, yanzu ga shi sun yi nasarar ɗauke shi wa ya sani ma ko sun kashe shi." Ta ƙarashe maganar tana sake ɓarkewa da sabon kuka har da jan zuciya take kamar za ta shide saboda tsabar tashin hankalin rashin sanin a wani hali a yanzu yake ciki.. Shuru suka yi suna kallon ta tana kuka, Grandma da itama take nata kukan ta face majina ta ce "Amma su ko waɗannan mutane sun cika marassa imani, shi mahaukaci me ya sani da har za su ɗauke shi? Allah dai ya tsine musu cikin kwando.. Ajiyar Abdul ya sauke ya ce "Uncle dole na koma Office na shigar da ƙaran nan, dama alfarma na nema dan na kai Baby can na dawo daga wajan aiki." Jinjina kai Uncle Aruf ya yi ya ce "Haka ne. Tashi mu je a fara bincike sannan a kira shi Baban ya mana bayanin kalar motar da ta ɗauke shi ko za iya gano inda suka kai shi.." Jan majina ta yi ta ce "Un.. Uncle Wallahi ba su da imani mutanen nan, yanzu haka ma sun kashe shi." Ta sake ƙara wa kukan ta volume. Rarrashin ta suka dinga yi har suka samu bacci ya ɗauke ta, Abdul ya kira Abba ya faɗa masa komai sannan suka wuce zuwa station ɗin su Abdul.. Suna cikin tafiya ne wata mota ɓaka ta dinga bin su daga baya duk inda suka nufa sai su ta biyo su a baya, Abdul ne ya nakare da ana bin su ya yi saurin janyo inda yake aje bindigarsa ya fito da ita ya riƙe a hannu ɗaya, Uncle Aruf ya dube shi ya ce "Ya da ɗauko bindiga?" "Ba ka ga ana bin bayanmu ba?" Hannu ya miƙa ya saita madubin gefen motar ga lalle fa motar nan su take bi. Sai da suka kusa isa Police station sannan wannan motar ta fasa bin bayan su... Abu kamar wasa yau tsayin kwana biyu ba labari akan sace Zaiyan, Abdul ya yi binciken har ya gaji amma babu wata alama da zai gano inda yake, hakan yasa yau ya shirya ya tafi Unguwar su Baba dan ya gana da shi. A mutumce ya tarbe shi suka gaisa sannan ya masa bayanin komai, ya kuma bukaci Baba da ya faɗa masa kalar motar da ta zo ta sace Zaiyan.. "Yaro motar nan ɓaka ce, ni kaina na sanar da 'yan sadan da ke kusa da mu amma da na koma washegari ba su saurareni ba ma." Nan dai Abdul ya dinga masa tambaya yana ba shi amsa daga ƙarshe ya masa sallama ya dawo gida.. Kuka da tunani a wannan karon shi ne abokin zaman Abir ta rame ta lalace ko abinci sai Abdul ya mata tsawa take ci, tunanin mahaifinta da Zaiyan kullum take yi ƙarshe rashin lafiya ta kwantar da ita har da karin ruwa leda uku aka mata saboda dama can ita mai yawan culuta ce bare yanzu da damuwa ta yi wa ƴar ƙaramar kwakwalwarta ƙawanya, sai ta rame ta kode da ƙyar take iya takawa... "Hello! Alhaji wannan yaron fa ya sheƙa." Ɗaya daga cikin yaran Alhaji ya faɗa hankalinsa a tashi ya yi tsaye kan Zaiyan da yake cikin jini idanunsa sun kalli sama bakinsa a buɗe.. "What?" Alhaji ya faɗa a matuƙar razane yana miƙewa daga kan kujerar office ɗinsa, nan-da-nan zufa ta tsastsafo masa ya fito da sauri kamar sabon kamu har yana haɗawa da gudu, PA ɗinsa da ta ga yana buga sauri abin ya ba ta mamaki ta biyo shi tana faɗin "Sir! Lafiya dai?" "Ba lafiya ba PA ki kula da komai zan je na dawo." Yana gama faɗin haka ya figi motar ya fita a guje...... _Muje zuwa dai _ _*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_ [10/25, 3:53 Yamma] My Addatyna: _*~A HAKA NAKE SON SHI~*_ _+966577675904_ *Arewabooks.com: Saratalkasum1897* Shafi na (12) Cikin minti 50 sai ga shi ya iso gidan wanda in a da ne sai ya yi awa da rabi yake zuwa in ya tafo daga cikin gari, a kiɗime duk yake hakan yasa ya danna hon da ƙarfi ɗiiii! A guje Maigadi ya fito daga banɗaki wandonsa a hannu ya nufi get ɗin ya leƙa ta ƙaramar kofa ya ga mai gidan ne sannan ya buɗe masa, jiki na rawa ya iso bakin motar ya buɗe yana faɗin "Barka da zuwa Alhaji." A zafafe ya fito daga motar kafin Maigadi ya motsa ya zabga masa mari mai zafin gaske ya wuce fuu! Sake da baki Maigadi yake kallon hanyar da Alhaji ya bi yana jinjina rashin imani irin na Alhaji, so yake wataran ya bar gidan nan saboda zaluntar shi da Alhajin yake amma ko ya yi yunƙurin guduwa sai ya rasa hanya dole ya haƙura ya dawo gidan. Yana shiga ciki ya dinga kiran yaran ɗaya bayan ɗaya suka fitowa jiki a sanyaye suna sadda kai ƙasa, a kufule ya kalle su ya ce "Me kuka ba shi ya ci?" Ɗaya daga cikin su ya ɗago tare da cewa "Babu abin da muka ba shi Alhaji, kai ka ce kar a ba shi komai in ba wannan ruwan da ke cikin ƙwarya ba. Muna zuwa duba shi muka ga baya motsi ƙarshe muka gano mutuwa ya yi ga... Kafin ya ƙara Alhaji ya zabga masa mari yana huci yana nuna su da hannu, takaici ya hana shi yin magana ji yake kamar ya yi hauka saboda sun gama ɓata masa rabin shirin da ya dauki tsayin shekaru yana yi, a tsawa ce ya ce "A ina yake!?" Wanda aka mara bai kuma yin magana ba ya sha kunu yaƙi ba wa Alhaji amsa, sosai ranshi ya sosu ya fice daga palon yana bin wata ƙofa, hakan yasa Alhaji ya ƙara kufula ya ce "Wato yanzu na gano duk laifin Wancan ne da har ya yi zuciya ya tafi, Wallahi in kuka ruguza min wannan aikin gabaɗaya sai na kashe ku har 'yan danginku kun ja musu." Yana gama faɗin haka ya wuce su. A kwance ya same shi ya yi saurin isa ganin yadda idanunsa suke kallon sama sai ya ƙara ruɗewa, ya ɗauko wata laya a cikin aljihunsa ya matse a hannunsa tare da lumshe idanu sannan ya ce "Nadumbuza ina son ganin ka yanzun nan." Yana buɗe idanunsa iska ta mamaye ɗakin mai ƙarfi, a hankali iskar ta wuce sai ga Nadumbuza ya bayyana yana karkada gashin dokin da ke hannunsa ya dubi Alhaji ya ce "Ka yi kuskure Alhaji da ka bari wannan yaron ya mutu." A ruɗe ya ce "Haba Nadumbuza ina da kai ai ba zan sha wahalar samun abin da nake so ba, ka duba min shi kasan dai ai yau ne ranar ɗaukan jinin da za a ba wa Uwa Dudu ko ka manta ne?" "Hahaha! Ban manta ba Alhaji ka yi kuskuren wani abu ne a cikin aikin shi ya sa hakan ta faru, dole yanzu sai ka yi abu ɗaya kafin yaron nan ya tashi." Da sauri Alhaji ya ce "Faɗa min Nadumbuza ko me kake so na yi zan yi komin wahalar shi in dai yaron nan zai tashi." Wata dariyar ya kuma yi yana kewaye Zaiyan yana karkada masa gashin dake hannunsa, sai da ya dawo bayan Alhaji sannan ya ce "Alhaji Uwa Dudu ta ce dole sai ka kwanta da budurwa sabon jini wadda babu namijin da ya taɓa sanin ta a 'ya mace, da jinin da ya fito daga al'aurarta za a ɗauka a haɗa magani a tashi wannan yaro. Ka sani idan har ka rasa yaron nan to kana cikin matsala, in hakan ta faru sai ka maye gurbinsa da ɗan cikinka mai irin shekarunsa ko ƙasa da shi." Ya faɗa yana firfito da jajajan idanunsa ma su firgitarwa. Alhaji ya jinjina kai cike da gamsuwa da maganar Nadumbuza ya ce "Ba ma zan bari na rasa yaron nan ba, maganar budurwa kuma ai ina da safayar 'yan mata dayawa a cikin gidan nan zan sa a kawo ɗaya daga cikin su sai a aiwatar da komai." Ya faɗa yana murmishin jin daɗi. Nadumbuza ya kwarara ihu yana ɗaga hannu sama ya juya ya daɓi kan Alhaji, sai da zagaye shi yana wasu irin kalamai sannan ya ce "Wannan aikin ba fa kai ɗaya za ka yi ba, ni ma sai na yi amfani da yarinyar ta yadda za mu samu isashen jinin da za ayi komai." "An gama ko nawa kake so ka kwanta da su zan kawo ma ballantana ɗaya tal." Dariya Nadumbuza ya kuma yi sannan ya ce aje a kawo yarinyar, Alhaji ya fita daga ɗakin yana kiran yaran gidan. Suna zuwa ya ce "Mutum biyu su biyoni su ɗauko min yarinya ɗaya. " da to suka amsa sannan suka bi bayan shi har suka isa wata ƙofa a dandan ƙasa, sai ka rantse rijiya ce a wajan amma suna buɗewa sai ga hanya mai matakala ta yi cikin ƙasa, Alhaji ya fara shiga kana suka bi bayan shi suka shige ciki.. Ɗakuna ne guda uku da babban palo sai toile dake gefen ɗakunan, ɗaya daga ciki ɗakin ya buɗe ya shiga tare da kunna hasken fitilar ɗakin sai ga haske tau. 'Yan mata ne sun fi ashirin a cikin ɗakin kowacce ta takure a waje ɗaya, Daga jikinsu in ka gansu sai ka rantse babu abin da yake damun su kowacce ta yi frech abin ta, amma da ka kalli fuskokinsu za ka ga damuwa ƙarara ta bayyana. Suna ganin Alhaji a tsaye kowacce ta yi saurin tashi suka zubo masa idanu, da kallo ya dinga bin su har ya hango wata farar yarinya wadda ba za ta wuce shekara 19 ba kayan jikinta duk ya yayyage, tana ɗago kai ta ga ita yake kallo ta zabura tana ɓoyewa a bayan wadda take kusa da ita ta fashe da kuka ta ce "Yaya don Allah kar ki bari ya ɗauke ni ya yanka, ki ɓoyeni Yaya." Ta ƙarashe maganar tana rufe bakinta da hannu.. Wani irin yawu Alhaji ya haɗiye shedan na ƙara ƙawata masa surar jikin yarinyar kasancewar ta fara sol yar duma-duma, duk da halin da suke ciki amma ita har wani sheƙi take sai in ka mata kallon nutsuwa za ka gano matsananciyar damuwa da tashin hankalin da take ciki. Da hannu ya nuna musu ita suka isa wajan ta tana kuka tana kurma ihu suka ɓamɓareta daga jikin ƴar'uwar ta tana faɗin "Yaya ki taimakeni karki bari su tafi da ni Yayaaa! Ta ja sunan da ƙarfi ganin sun fita daga ɗakin. Kuka duk suke yi ba kamar wadda aka ɗauke Ƙanwarta kamar ta yi hauka sai cewa take "Don Allah ku dawo da ita ni na yarda ku kashe ni a madadin ta." Haka suka dinga kuka suna ji aka rufe ƙofar da aka shigo.. Suna tasa ƙeyarta da haka suka fito da ita waje suka buɗe mata ƙofa ta shiga sai ga ta a ɗakin da Zaiyan ke kwance, ganin Zaiyan baki buɗe idanu sun kalli sama yasa ta zaro idanu tana aiyanawa a ranta cewar yau fa ta yi bankwana da duniya. Dariya Nadumbuza ya yi yana lashe baki yana kallon ta ya ce "Yarinya matso nan ki ji." Ƙin zuwa ta yi sai da suka tura ta gaban shi ta runtse idanu jin wani kalar wani na ziyartar ta, Nadumbuza ya ce su ɗauke Zaiyan su fitar da shi daga ɗakin su kai shi ɗayan, shi kuma Alhaji ya tsaya su kuma kar su dawo, to suka ce sannan suka kama Zaiyan suka fitar da shi. Nadumbuza ganin tana kuka ya ɗauki wani ruwa mai kama da farau-farau ya ɗan ɗiba ya yayyafa mata a fuska, ajiyar zuciya ta sauke sannan ta kalle su ta ce "Kar ku cutar da shi ku mayar da ni wajan yayata." Mamaki ne ya kama Nadumbuza jin maganin da ya yayyafa mata bai kama ta ba, ganin za ta ɓata musu lokaci ya sa ya ɗauko wani ɗan ƙyalle ya rufa mata a fuska nan-da-nan ta ji kanta yana juyawa ta durƙusa a wajan tana fitar da wani kalar numfashi na fitar haiyaci. Da ido Nadumbuza ya yi wa Alhaji alama da ya zo ya janye ta, da sauri ya iso dan dama abin da yake son a faɗa masa kenan, cikin saurin ya cire tufafinsa ya janyo ta, kayan jikinta da ƙarasa gayawa sai rawar jiki yake kamar zai kifa kanta.. Hannun ta kamo ya sumbata yana mata wani irin kallo Nadumbuza ya kwashe da dariya ya ce "Alhaji da alama dai..." Sai ya sake fashewa da dariya yana miƙa hannu ya shafo jikinta yana lashe baki,. Alhaji ya ƙara matso da ita ya soma aikata abin da yake son yi. Wani kalar ihun azaba yarinyar take jin abin da ba ta taɓa ji ba a rayuwarta ta shiga ƙoƙarin kwatar kanta amma ina Alhaji ya fi ƙarfin ta, tun tana kiran yayarta da ƙarfi har ta kasa cewa komai ƙarshe ma ta suma. Sai da Alhaji ya ɗauki awa ɗaya cif sannan ya tashi yana huci tare sharce zuba, Nadumbuza da ke gefe yana kallon su sai haɗiye yawu yake yana ganin Alhaji ya tashi shi ma ya ɗaura daga inda ya tsaya. Suna gama komai tuni jini ya shiga malalowa daga jikinta Nadumbuza ya ɗauko ƙwarya ya ɗago ta ya jingina ta da jikin bango ya ɗauko wani ƙyalle ya goge jinin tas ya kara mata wani ƙyallen a gabanta, sai da ya yi tsafinsa ya tsayar da jinin sannan ya juyo ya kalli Alhaji ya ce "Wannan ta gama mana amfani ka san yadda za ka yi da ita." To Alhaji ya ce ya sa aka fitar da ita daga ɗakin shi ma Nadumbuza ya ce ya je zai ƙarasa sauran da kansa. Cikin farin ciki ya fita harabar gidan yana murmushi sai ya tuna marin da ya yi wa Maigadi ya kira shi, da sauri ya iso jiki na rawa yana tsoron kar ya kuma marin sa, sai ya ji muryar Alhaji na cewa "Ka yi fa haƙuri da marin da ba maka ina cikin fusata ne, yanzu ga wannan." Ya faɗa yana ba shi ɗaurin 'yan rafa ya shiga motar ya nufi get. Cike da mugun mamaki Maigadi yake kallon kuɗin ya kasa motsawa daga inda yake har sai da Alhaji ya yi masa hon sannan ya dawo haiyacinsa ya buɗe masa ƙofar, ya dawo ya zauna ya yi shuru yana mamakin kyautar nan saboda a iya zamansa a cikin gidan nan Alhaji bai taɓa masa ko da magana mai daɗi ce ballantana har ya masa kyauta, sai ga shi yau ya ba shi kuɗin da suka kai dubu ɗari cif a hannunsa... Duk familyn Maitama ba wanda bai je ya gano jikin Abir ba amma ban da Umma da Ammi da Yasmin, ko Fatima da take jin kamar ta shaƙe Abir ta mutu da ta ga halin da take ciki ta mugun tausaya mata har taji tsanar ta da ke maƙale a ƙoƙon zuciyarta ta ragu kusan kaso hamsin bisa ɗari, Mommy kuwa babu abin da take in ba addu'a ba magana kan ta wani lokacin gararar ta take yi, ko da ta yi niyar yin magana sai ta ji ƙirjinta ya mata mugun nauyi haka ma harshenta haka za ta haƙura da magana ta yi tagumi tana kukan zuci. Shi kuwa Abdul bincike suke sosai har suka gano motar da aka sace Zaiyan hakan yasa suka shiga neman mai motar ba dare ba rana, yayinda a gefe ɗaya rashin lafiyar Babyn nasa ta ƙara karyar masa da zuciya ko wajan aiki ya fito hankalinsa yana kanta ba zai nutsu ba sai ya dawo gida.. Yau ta samu ta fito daga ɗaki tana bin bango a hankali har ta iso palon, Mommy ta taro ta tare da zaunar da ita hankali tana mata sannu, murmushi ta yi ta ce "Mommy yanzu fa bana jin ciwon komai kawai dai maganina ne ya kusa ƙarewa ina so zan je na amsa." Ta yi maganar tana murmushi." "Haba, ban da abin ki ai sai ki bari Yayanki ya zo sai ya kawo miki da kansa ko kuma Salim ya je ya kawo miki." Ɓata fuska ta yi ta ce "Mom ina so na fita waje na ji iska kwana nawa ina gida ban leƙo ko palo ba?" Ta faɗa tana cuno baki sai ga hawaye sun cika mata idanu. Mommy za ta yi magana sai ga Abdul ya shigo da sallama, wani irin kallo ta jefe shi da shi wanda ya sa Abdul ba shiri ya tsaya cak shi ma yana kallon ta, sosai ta ji wani irin tausayin ta ya ƙara mamaye shi ganin duk ta rame sai hancin da idanu. Ajiyar zuciya ya sauke cikin saita nutsuwarshi ya tako ya ƙaraso ciki. Mommy ta murmusa ta ce "Yawwa Alhamdulillah gara da ka zo Babana." Zama ya yi yana kallon ta cikin tausayawa ya ce "Baby ya jikin naki? Fatan babu inda yake miki ciwo?" Har ta gyaɗa masa kai sai kuma ta yi saurin murmushi sanin halinsa ta ce "I'm ok Yaya." Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce "Lokacin amsar maganinki ya yi za ki iya zuwa ko naje na amso miki?" Saurin cewa ta yi "No Yaya mu je tare so nake na ji iska." To kawai ya ce sannan ya miƙe ya nufi ɗakin Grandma, cire kakinsa ya yi yana jin wata muguwar gajiya haɗi da farin cikin ganin Babyn nasa ta samu sauƙi, zama ya yi a bakin gadon Grandma ya cire safarshi yana lumshe idanu wani irin mugun bacci na fisgar shi. Saurin buɗe idanunsa ya yi yana sauke numfashi ya buɗe drower ya fito da wani ƙananan kaya rigar ɓaka wandon fari ya saka tare da fesa turare kaɗan saboda kar ya yi ƙarfi dayawa ta shaƙa. Cikin haifa da kalama yake takowa zuwa palon yana mamakin rashin ganin Grandma, sai da Mommy ta ba shi ruwa ya sha sannan ya ce "Mom ina Grandma take ne." Yar dariya Mommy ta yi ta ce "Ai kasan hali dai ta ce wai za ta tafi gidan Abban Aruf ta yi musu kwana biyu daga nan za ta je gidan Baba Malam ta basa kuɗi a sauke Alkur'ani mai girma akan lamarin nan." Jinjina kai ya yi ya ce "Gaskiya naji daɗin hakan, ai na dauka ko fushi ta yi da maganar jiya." "Inna kenan Allah ya ƙara mata lafiya." Amin suka faɗa sannan Abir ta ɗauko hijabinta suka tafi Mommy na musu a dawo lafiya suka amsa da amin.. Suna isa Asibitin Abdul ya yi packing kenan sai ga wata Ambulance ta iso jiniyarta ta karaɗe Asibitin, saurin kallon wajan Abir ta yi ta ce "Yaya waye ya mutu?" Shi ma idanunsa akan Ambulance ɗin ya ce "To taya zan sani Baby." Ba ta kuma cewa komai ba suka fito za su shiga sai ganin Nurses suka yi su 6 dauke da gado biyu suka nufi Ambulance ɗin, samun kansu suka yi da son ganin wanda za a fiddo daga ciki suka yi tsaye a gefe motarsu. Miƙo na ciki aka yi suka ɗaura akan gado suka kuma miƙo ɗayan aka ɗaura shi a gadon suka nufi ciki da su da sauri, ana zuwa saitin su Abir ta ji zuciyarta ta buga da ƙarfi ta yi saurin dafe ƙirjinta ta yi baya za ta faɗi ya yi saurin tare ta. Ganin sun wuce su da sauri ta miƙe daga jikin Abdul jiki na rawa ta ce "Ya.. Yaya mu je mu gani." Da mamaki ya kalle ta dan shi ko fuskar waɗanda aka ɗauko bai gani ba, ya ce "Baby!" Fashewa ta yi da kuka tare da faɗawa jikinsa kamar za shige cikinsa jikinta sai rawa yake, hankali a tashe Abdul ya ƙara rungume ta ganin yadda ta ruɗe sai faɗi take su je su ga wanda aka kawo, duk hankalinshi ya tashi ya dawo da ita gefensa ya riƙe ta rabin jikinta a manne da nasa suka nufi Emergency room ɗin da aka nufa da su... Suna isa ana fito da su daga ɗakin da aka saka su za a kai su wani ɗaki, a zabure ta kwace jikinta daga nasa ta nufi Nurses ɗin ta ce "Ku dakata!!! _*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_ [6/20, 7:41 PM] Ummu Amjad: _*~A HAKA NAKE SON SHI~*_ _+966577675904_ *Arewabooks.com: Saratalkasum1897* Shafi na (13) "Ku dakata!" Ta faɗa da ƙarfi tana yowa kan su cikin sauri har tana faɗuwa. Jin yadda ta yi maganar yasa Nurses ɗin da suka janyo gadon suka tsaya suna kallon ta, tana isowa ta soma ƙoƙarin buɗewa hannunta na rawa wani daga cikin nurses ɗin ya ce mata "Ranki ya daɗe kin san waɗannan mutanen nan ne?" Girgiza kai ta yi hawaye na bin kuncinta da ƙyar ta ce" Don Allah ka da ku hanani ganin su." Ta faɗa muryarta na rawa. Abdul ne ya ƙara inda take ya janyo ta ya rungume yana faɗin "Baby wai kina cikin haiyacinki kuwa? Taya daga ganin an fito da mutane daga ambulance ki matsa sai an buɗe miki kin ga fuskarsu?" Ya faɗa tare da duban likitocin ya ce "Am sorry ta ruɗe ne shi ya sa." To kawai suka ce sannan suka ja gadon za su shige ɗakin ta kwace jikinta ta isa gare su da sauri, ta kama gadon tana ƙoƙarin janye rufin da aka yi wa mara lafiyar, Doctor Hashim ne ya hango Abdul sai ya cika da mamaki ya iso sai kuma ya ga Abir ana artabo da ita lalle ilalla sai ta ga waɗannan marassa lafiyar ana riƙe ta. Dakatar da nurses ɗin ya yi yana kallon ta da mamakin ganin yadda ta birkici sai sharbar kuka take bil'haƙƙi, da kan shi ya buɗe mata fuskar, ba Abdul ba hatta shi kan shi Doctor Hashim sai da ya ja da baya in arba da fuskar, ita kuma ta fashe da kuka tana kamo hannun mutumin cikin fitar haiyaci, ta kuma fasa ƙara mai haɗe da kuka ta ce "Abie!" Ba su ba ta damar cewa komai ba suka ja gadon suka shige ciki, kuka ta dinga yi tana nuna hanyar da suka bi ta kasa magana har wasu daga cikin nurses ɗin suka fito daga ɗakin suka shiga ɗayan. Tana ganin sun fito da ɗayan kamar wacce aka tsikara ta miƙe zumbur ta tare su ta ce "Waiyo Allah! Ku buɗe min na gani." Da hannu Doctor Hashim ya musu alama da su buɗe mata ba muso suka buɗe mata fuskar, sake sakin wani kukan ta yi ta waiwaya inda Abdul ya ke tsaye kamar gunki ta ce "Yaya zo ka gani Wallahi Zaiyan ne shi ma ya mutu, La'ilaha illallah Muhammad Rasulullah sallallahu alaihi wa sallam." Ta ƙarasa ta yi baya luuu za ta faɗi. Sauri taro ta Abdul ya yi yana kallon fuskar Zaiyan da aka dinke masa goshinsa da kuma hannunsa, duk da bai taɓa ganin Zaiyan ɗin ba amma ya ji ya ba shi tausayi hakan yasa ya matsa suka wuce ita kuma aka kawo gado suka ɗaura ta aka shigar da ita ɗakin taimako.. Zarya Abdul ya dinga yi a wajan sosai ya shiga tashin hankali, gabaɗaya ya rikice da ganin Abie, wayarsa ya ɗauka ya kira Abba yana ɗauka ya saita muryarsa ya ce "Hello Abba ko mai kuke kai da Daddy da su Mommy ku zo Asibiti ku same mu." Da sauri Abba ya miƙe tsaye ya ce "Waye ba lafiya Abdul?" Girgiza kai ya yi kamar yana gaban shi, wani irin zafi yake jin zuciyarsa na masa maganar ma ta gagare shi, sai da Abba ya sake tambayar shi tukun da ƙyar ya iya haɗiye yawu mai ɗici hana runtse idanu ya ce "Ku dai ku zo Asibitin Doctor Hashim muna nan." Yana gama faɗin haka ya kashe wayar ya dawo zauna a kan ɗaya daga cikin kujerun da ke jere a wajan, tashin hankalin da yake ciki shi ne bai sani ba Abie yana raye ko kuwa dai ya mutu shi ne bai sani ba. Yana zaune Doctor Hashim ya fito daga ɗakin da aka sa Abir ya ce da Abdul ya biyo shi office. Suna isa suka zauna Abdul duk ya ƙagu ya ji me Doctor Hashim zai faɗa masa, sai da ya gama rubuce-rubucensa sannan ya ɗago ya dubi Abdul ya ce "Am so sorry Abokina ba zan ɓoye maka ba Allah ya yi wa Abie rasuwa, dan ba ma yanzu ba ya rasu tun kafin su iso ya rasu, mun yi masa gwaje-gwaje mun gano kansa ne aka buga har jini ya haɗe da kwakwalwarsa hakan yasa kafin su iso ya rasu." Tamkar saukar aradu haka Abdul ya ji furucin Doctor Hashim, da ƙyar ya daure ya ce "Inna lillahi wa inna ilaihin raji'un! Tun daga ina kuka ɗauko shi?" Ya faɗa wasu zafafan hawaye na sauka bisa kuncinsa. Shi kan shi Doctor Hashim sai da idanunsa suka cika da hawaye amma ya yi ƙoƙarin mayar da su dan kar ya ƙara karyar da gwiwar abokin nashi, a sanyaye ya ce "Wata number ce aka kira ake sanar da mu an buge wani mutum da mota amma masu motar sun gudu, shi ne aka tura ambulance inda da taimakon wannan mai kiran suka isa kusan ƙarshen gari a nan suka samu tsohon da ya kira su , inda yake sanar da su ai akwai wani ma gidansa da ya tsince shi da dare bayan ya dawo daga cikin gari ya nuna su shi ne suka ɗauko su gabaɗaya. Tun da suka tafi nake kiran number ka dan ku bi bayansu ku bincika komai to ba ka ɗauka ba har na gaji na aje wayar na kira Uncle Aruf shi kuma wayar ma a kashe take, ashe gawar Abie ce da wannan saurayin wanda na ga Abir ta ƙara shiga ruɗani da ta gan shi, ko ta san shi ne?" Ya ƙarashe maganar yana tambayar Abdul da ya yi ƙiƙam yana sauraron shi. Sai da ya buga tebirin gaban su sannan ya firgita ya dawo haiyacinsa ya yi saurin cewa me kake cewa Hashim?" Sake maimaita masa bayanin ya yi sannan ya ƙara da cewa "Yanzu sauran aikin na damƙa a hannunka." Wani irin zafi zuciyarsa ke masa ya daure ya ce "Shi wannan wani ne wanda ya taimaki Baby shi ɗin ma sace shi aka yi kwanakin baya da suka wuce." Da sauri Doctor Hashim ya ce "To amma ai na ga kwakwalwarsa ta samu taɓuwa, a takaice dai ya haukace." "Na sani." Abdul ya faɗa a takaice yana kai hannu ya goge hawayen da suka zubo amsa. Shi kuwa Doctor Hashim haƙuri ya dinga ba wa Abdul har Abba ya kira shi ya sanar da shi sun zo sannan suka fito tare. Kwatance ya musu na inda suke sai ga su sun nufo su, Mommy da duk ta fi su shiga damuwa a tunaninta Abir ce wani abin ya same ta tun da ta hango Abdul ba ta ganta ba ta yi sauri riga su Abba isa wajan, a ruɗe take tambayarsa "Abdul me ya faru da Abir ɗin?" Girgiza mata kai ya yi Abba ma da ya ƙaraso ya tambaya lafiya? Bai ce da su komai ba sai ganin Abir suka yi ta fito daga ɗakin da aka kwantar da ita tana kuka ganin su Mommy yasa ta ƙara wa kukan ta volume, duk suka dinga tambayar ta me ya same ta amma ta isa ce musu komai, hakan yasa Doctor Hashim ya ce "Abba an tsinci gawar Abie ne yanzu haka yana ɗakin aje gawa." Zaro idanu duk suka yi a kuma tare suka ce "Wani Abie ɗin?" "Abie dai wanda kuka sani. Bayanin komai ya musu har da na Zaiyan ya faɗa musu, Mommy kuwa tun da aka ce Abie ya rasu ta suma a tsaye sai da Abir ta taɓa ta ta ga ta yi baya za ta faɗi ta yi saurin kamo hannunta tana kuka ta ce "Mommy don Allah kema kar ki tafi ki barni." Kan kujera aka aje Mommy Doctor Hashim ya sa aka kawo ruwa mai sanyi suka shafa mata ta sauke kakkarfar ajiyar zuciya sai kuma hawaye suka soma zarya kan kuncinta. Abba ya ce su je a ba su gawar Abie za su masa sutura ya kai su har kan gawar, sai da Daddy ya buɗe gawar ya ga tabbas wannan Abie ne a lokacin ne ya ji wasu hawaye sun silalo masa ya yi saurin gogewa.. Mota biyu suka zo da ita aka saka gawar a motar Abdul Abba da Daddy suka shiga, Mommy da Abir direban da ya kawo Mommy shi ya ɗauke su ɗayar motar suka bar ta nan suka nufi gida.. Tun kafin su je Abie ya kira Daddyn Aruf ya faɗa masa abin da yake faruwa ya ce ga su nan shi da Aruf. Suna packing Abba ya fito ya kamo gawar Abie Daddy na taimaka masa suka fito da ita sai ga motar Daddyn Aruf da kuma ta Salim sun zo a tare, su duka suka shiga part ɗin Mommy da gawar inda suka kai ta ɗakin Mommy. Maigadi da sauran ma'aikatan gidan duk ruɗewa suka yi da ganin an fito da gawa, sai bayan sun shiga Direba ya sa hannu ya goge hawayen da suka zubo masa tuna irin tarin alhairan da Abie ke masa, babu abin da yake yi na gidan Abie ne ya ɗauki nauyin komai nasa kuma duk wata a biya shi albashinsa mai tsoka. Bai san ba san da ya dafa mota yana kuka tare da faɗin "Allahu akbar! Allah sarki Alhaji mutumin kirki mun yi rashi babba a gidan nan, Allah ka haskaka makwancin Alhaji yadda yake haskaka rayuwar bayin Allah kamar ni." Da sauri Maigadi ya matso kusa da shi cikin kiɗima ya ce "Kai wai waye ya rasu?" "Alhaji ne aka tsinci gawar shi." Ya faɗa yana tsayar da kukan. Salati Maigadi ya ɗauka yana dafe kai, tabbas sun yi babban rashi na uban gidan nasu mai kima da daraja a gare su har da danginsu, shi ma goge hawayen ya yi yana girgiza kai ya ce "Allah sarki Alhaji damo sarkin haƙuri, kamar yasan mutuwa zai yi duk ya ba mu albashin shekara-shekara. Ko da na ga kuɗin na sha mamaki saboda bai taɓa mana irin biyan nan ba, ashe dai a ranar ganin ƙarshe muka masa mishi, Allah ya jiƙan bawan Allah nan mai tausayi a taimkon na ƙasa da shi." Amin suka ce duk suka koma inda Maigadi oe zama suka zazzauna cikin jimami, sosai mutuwar ta daki zuciyoyinsu kowa sai girgiza kai yake yana faɗin hidimar da Abie yake yi da shi... Grandma ba wanda ya sanar da ita komai sai da aka kawo ta gida ta ga part ɗin Mommy ya cika da 'yan gidan da kuma makota abin da ya ba ta mamaki, tambayar su take " Kun ji jama'a lafiya dai kuka tare a nan?" Ba wanda ya ce mata komai sai da ta hango Mommy na kuka ta ƙara shiga tashin hankali, Mommyn Aruf ce ta kama hannun Grandma ta ja ta suka shiga har ɗakin Mommy. Wani irin dafe ƙirji Grandma ta yi tana kallon gawa kwance a tsakar ɗaki, su Abba suka kamo ta ta durƙusa a gaban gawar hannu na rawa ta buɗe ta yi arba da fuskar Abie. "Inna lillahi wa inna ilaihin raji'un! Ibrahimu! Ashe ba zan sake ganin ka ba sai dai na ga gawar ka? Allahu akbar kabiran Allah mai kyauta da karɓewa, Allah ya jiƙan ka Ibrahimu." Ta ƙarashe maganar tana goge hawayen da suke ambali a kan kuncinta.. Addu'a ta dinga yi masa su Abba na amsawa da amin har ta gama, da ƙyar Daddy ya fito da ita daga ɗakin ya kawo ta palo ya zaunar da ita a kusan Mommy. "Yi kuka Sa'ade." Ta faɗa tana dafa kafaɗar Mommy da ta yi kim tana kallon 'yan palon masu kuka na yi masu tagumi na yi. Bayan an gama yi wa Abie wanka aka kira ɗaya bayan ɗaya suka dinga masa addu'a, Abir ita ce ƙarshe tana kuka tana kiran sunan Abie da ƙyar aka ɓamɓareta daga ruƙon da ta yi wa gawar Abie aka fito da ita palo, ba ta ƙara rikicewa ba har sai ta ga an ɗauko Abie a makara za a wuce palo ta yi wani irin kukan kura ta kwace ruƙon da aka mata ta nufi mazan da suke shirin barin palo. Da mugun sauri Abdul dake bayan su ya yi saurin tare ta ya ɗauke ta cak ya nufi ɗakinta, ita kuma kuka take tana faɗin "Yaya Abie na Wallahi bai mutu ba ka ce su bari na masa magana zai tashi." Tana gani suka bar palon ta kwalla wani irin ƙara sai ta saki jiki a jikin Abdul, a ruɗe ya kwantar da ita a kan gado ya ɗauko ruwa ya shafa mata a fuska ta ja ajiyar zuciya mai ƙarfi tare da buɗe idanunta. Ganin shi a kusa da ita yasa ya faɗa jikinsa tana kuma sakin wani kukan.. Bai hana ta yin kukan ba har sai da ya ga taƙi bari sannan ya ɗago da ita, sake komawa ta yi cikin jikinsa tana ci gaba da kuka ya kuma ɗago da ita zuciyarsa na masa wani irin azababben zafi, dafa kafaɗunta ya yi cikin wata kalar murya wadda bai san yana da ita ba ya ce "Babyyy." Ya ja sunan idanuwansa sun cika da hawaye suna ƙoƙarin zubowa shi kuma yana ƙoƙarin mayar da su. Cikin kukan ta ce "Ya.. Yaya Abie na." Ta faɗa cikin shashshekar kukan da har ya kai muryarta ta disashe. Kamo hannunta ya yi yana murzawa a hankali bai ce da ita komai ba ita kuma tana kuka ta ƙura masa idanu, sai da ya ji ta yi shuru sannan ya ɗago da idanunsa wanda suka tashi daga farare suka koma jajur kamar an watsa masa barkono ya soma yi mata magana. "Ki yi haƙuri kin ji, kukan ba shi da wani amfani Addu'a Abie yake buƙata ba kuka ba, tashi ki wanke fuskarki ki zo ina jiran ki." Ya faɗa yana miƙar da ita tsaye ya ja ta suka nufi toilet. Ganin ta ki yin komai ya janyo ta ciki ya isa bakin famfo ya wanke mata fuska sannan suka fito. Da ƙyar ya rarrashe ta yana mata nasiha tukun ta yi shuru har ta yarda suka fito palon ya zaunar da ita a kusan Grandma ya fita zuwa maƙabarta... Yana zuwa ana saka gawar Abie a cikin makwanci ya runtse idanu yana karanto Addu'o'in nema wa Abie yafiyar Ubangiji, yana tsaye aka gama aka bar su Abba a kan ƙabarin suna ta Addu'a shi ma ya tsugunna aka yi da shi sannan suka tashi... Bayan an dawo daga maƙabarta aka kafa runfuna a harabar gidan. Tuni labari ya yadu a cikin gari da waje An tsinci gawar Shahararren ɗan kasuwar nan Alhaji Ibrahim Abdullahi Maitama bayan shafe watanni da ya yi ba a san ba inda yake. Kowa na ta tofa albarkacin bakinsa duk inda ka nufa a cikin garin Yola maganar ake ko Social media ka hau da labarin za ka ci karo, wasu na cewa ƙila abokan kasuwancinsa ne suka kashe shi, wasu kuma su ce makiya ne a wani waje da ban kowa na faɗin ra'ayinsa.. Haka aka yi ta karɓar 'yan gaisuwa daga garuruwa daban-daban kama daga kan abokan Abie na kasuwanci da yaran da suke aiki a kamfaninsa da abokansa wasu garuruwa, gidan kullum haka ake wuni ana tabar ɓaki. Mommy kuwa ba ta cewa i ba kuwa ta cewa a a, tana zaune tana kallon kowa da haka aka yi sadakar uku ya rage sai 'yan'uwa na kusa a gidan. Ana yin sadakar bakwai kowa bayan an yi Addu'o'i sauran mutanen da suka rage suka tafi aka bar na gidan. Bayan sati biyu Yanzu Abir ta sadakar da cewa lalle fa Abie ɗinta ya mutu, gabaɗaya ta ƙara koɗewa duk da ita ɓaka ce amma sai ta yi fari saboda kullum da zazzabi take kwana, Abdul na ta kula da ita har Mommy kanta da take cikin takaba haka take wuni da ciwon kai, Grandma kuwa su Abba ke mata jawafi suna zuwa su daɗe a wajan ta sai sun ga ta saki ranta sannan su tafi.. A haukace Alhaji ya dawo daga Germany sakamakon wayar da yaran suka buga masa suna sanar da shi yaron da suka kawo fa sun neme shi sun rasa a gidan, hankalinsa ya tashi matuƙa hakan yasa ya cire ticket ya dawo Nigeria ko gidansa bai isa ba ya wuce gidan da suke. Haka ya dinga faɗa yana yin wurgi da duk abin da yake kusa da shi, Nadumbuza ya dakatar da Alhaji ya ce "Matuƙar kana son ci gaba da komai naka dole sai ka kawo mana jinin ɗanka an yi aiki da jininsa." A gigice Alhaji ya ce "To amma Nadumbuza me zai hana ka yi aikin ka daga nan ba sai na kawo shi ba." " A a bari na tambayo Uwa Dudu naji mai za ta ce a kan hakan." Gyaɗa kai kawai Alhaji ya yi shi kuma Nadumbuza ya tafi wajan Uwa Dudu, bai ɗauki lokaci ba sai ga shi ya dawo yana dariya, ganin haka yasa Alhaji ya ja dogon numfashi sannan ya ce da shi "Ya dai Nadumbuza?." "Uwa Dudu ta ce za ta yi ma alfarma ɗaya tak." Da sauri ya ce "Wacce kenan? Ba na so ne a kawo shi nan ina so ayi komai ta yadda ba za a gane ba." "Ta ce ba sai an kawo shi ba nan, ita za ta ji da komai." Dariyar farin ciki Alhaji ya yi yana cewa "Uwarmu maganin kukanmu." Har ya juya zai fita Nadumbuza ya ce "Alhaji ina buƙatar a kawo min yarinya ɗaya na kashe ƙishina a kanta." Dariya su duka suka ɗauka suna kallon Nadumbuza wanda shi ma dariyar yake, ɗaya daga cikin su ya ce "Nadumbuza mai abin mamaki yo ni na ɗauka irin ku ba sa buƙatar mace." Shafa ƙasumbarsa Nadumbuza ya yi ya ce "Wa ya ce maka? Ai mun ma fiku son hakan." Dariya suka kuma yi Nadumbuza ya ce Alhaji ya zo kafin a kawo masa yarinyar ya ce to suka shige wani ɗaki wanda daga shi sai Nadumbuza suke shiga.. Ɗaki ƙarami daga ciki yana da ƙofa uku, a tsakiyar ɗakin suka tsaya Nadumbuza ya aje sandar shi cikin sauri ya cire hular fatar da ke kansa yana faɗin "Ka yi sauri fa Alhaji kar ka karya aikin ka." Da sauri shi ma Alhaji ya cire kayan jikinshi, Nadumbuza ya ɗauko wata gwalba daga cikin aljihunsa ya lakato wani mai wari, jikin Alhaji ya shafe man yana wasu irin yare. Bayan ya gama yana daga tsayen suka dinga aikata luwaɗi shi da Alhaji, (Allah ya shirya mana al'ummar musulmi). Sai da suka kammala Nadumbuza ya ɗauki wata allura ya soka a jikin Alhaji yana yin yarukan tsafi, jini kaɗan ya fito ya janyo wani ƙyalle fari mai ɗan girma da ke gefen su. Goga jinin ya yi a jikin ƙyalle yana wani irin nishi kamar mara lafiyan da jiki ya yi tsanani, Alhaji ya sunkuya ya ɗauki kayan shi ya mayar ya gyara. "Za ka iya tafiya Alhaji ka ji daɗin ka, ka yi duk abin da kake so a duniyar nan na tsaya maka." Cewar na Nadumbuza yana nannade ƙyallen.. Murmishin jin daɗi Alhaji ya yi ya fito daga ɗakin, sai da ya yi wa yaran gidan kashedi kar su kuma sake yin sakaci su kula 'yan matan da ke gidan duk da yasan babu ta inda za su a wannan gurin da suke su gudu daga gidan. Da to suka amsa ya ciro 'yan rafa ɗaurin dubu ɗari-ɗari ya miƙa wa kowanne, cikin jin daɗin suka masa shi kuma ya yi tafiyar sa yana jin kansa na ƙara girma ya zama fitaccan mai kudi... Doctor Hashim ne ya kira Abdul yake sanar da shi Zaiyan ya farka amma lamarin nasa sai a hankali saboda duka yake kai wa duk wanda ya nufi inda yake, sun samu da ƙyar sun masa allurar bacci ita ma nan da minti kaɗan zai tashi, dan haka ya sa ya yi maza ya zo su san abin yi. Lokacin yana zaune a ɗakin Abir yana nuna mata wasu kadarori na Abie da ke cikin garin Abuja, bayan ya gama wayar ya sanar da ita ta ce masa su je tare, bai musa ba suka fito ya sanar da Mom abin da ke faruwa sannan suka tafi.. Lokacin da suka isa likitoci sun rirrike shi yana ta faɗin "Ku sakeni na tafi wajan Anty." Abin da yake faɗa kenan yana ƙoƙarin kwacewa daga ruƙon da suka masa. Da sauri suka iso cikin ɗakin a daidai lokacin ya masge wani likita tuni ya faɗi warwas, ya yunƙura zai sauko suka kuma riƙe shi ya kwace ya sauko zai fita ta yi saurin damƙar hannunsa.. A zabure ya juyo ya kalle ta, kallon ta yake ba ko ƙiftawa yana ɗaga kai sama zuwa can kuma ya Shagwaɓe fuska tare da juyowa gabaɗaya ya tsaya gaban ta, raurau ya yi da idanu irin na yaro in ya ɗauki tsayin lokaci bai ga mamansa ba. Hanunsa ya ɗaura akan nata sai gani ta yi ya soma kuka yana langaɓar da kai ya ce "Antyyy.!!" _*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_ [10/25, 3:55 Yamma] My Addatyna: _*~A HAKA NAKE SON SHI~*_ *Arewabooks.com: Saratalkasum1897* _+966577675904_ Shafi na (14). "Antyy!" Ya faɗa cikin rawar murya wadda ta sa Abir ta ɗago cikin wani irin yanayi mai wuyar fassarawa ta zuba masa lulu eyes ɗinta farare tas. Duk da gabanta yana dukan uku-uku sai ta ji sunan har ƙasan zuciyarta, lumshe idanu ta yi tana yin hamdala da bai gudu ba suka zo, a hankali ta buɗe idanuwanta ta kalle su ɗaya bayan ɗaya, hannunta da ke cikin nasa ta ɗan ja tana son ya sake mata hannun. Ƙara matse hannun ya yi yana duddubawa kamar mai neman wani abu a jikin hannun nata, numfashi ta sauke zuciya na wani irin bugawa da mugun sauri, da ƙyar ta iya kallon su tana ƙoƙarin saita nutsuwarta cikin ƙasa da murya ta ce "Don Allah za ku iya ba mu guri za mu yi magana da Doctor?" Ba matsala suka ce sannan suka fita daga ɗakin suna mamakin yadda ya yi luf da ya ganta, wani daga cikin su har ya kai bakin ƙofa ya kasa daurewa ya juyo ya ce "Ranki ya daɗe amma dai wannan ɗan'uwan ki ne ko?" Gyaɗa masa kai kawai ta yi ba ta yi magana ba, Abdul da duk jikinsa ya yi sanyi ya iso ya samu waje ya zauna a ɗaya daga cikin gadajen da ke ɗakin, shi ma Doctor Hashim ya zauna a kusa da Abdul. Sai da Doctor Hashim ya ƙare musu kallo sannan ya ce "Ƙanwata zo ku zauna mana." Ya faɗa yana murmishi haɗi da mamakin Zaiyan. Zama ta yi a bakin gadon ganin haka ya sa shi ma ya biyo bayan ta ya zauna a ƙasa kusa da ƙafafuwanta yana sa yatsu biyu a bakinsa, kallon shi ta yi cike da tausayi ta ce "Zaiyan tashi mana ka zauna a nan." Ta nuna masa kusa da ita. Murmushi ya sakar mata har sau da dimple ɗinsa ya lotsa haƙoransa suka bayyana wushiryar da ke tsakanin haƙoran na gaba da na ƙasa ta bayyana, baki ta saki tana kallon shi cike da mamakin ganin dimple a kumatunsa, saboda ita duk haɗuwar da take da shi ba ta taɓa lura yana da dimple ko wushirya ba sai yau ɗin nan. Takalmin ƙafarta ya shafo yana ƴar dariya ya ce "Anty bredi ne kika kawo min?" Ya faɗa yana ƙara shafa takalmin wanda yake irin mai laushin nan ne na yawo a cikin gida. Murmishi ta yi ta ɗago kai ta kalli su Abdul wanda su ma ita suke kallo suna mata dariya, cikin dabara ta saɓule takalmin daga ƙafarta ta janye ƙafar ta sunkuya ta ɗauki takalmin sai shi ma ya yi saurin miƙewa tsaye yana kallon ta, ɗage gira ɗaya ta tana jin wani irin sanyi na ziyartar ta ta ce "Ka ga zauna a nan da na nuna ma." Ta kuma faɗa tana nuna masa gefenta. Ɓata fuska ya yi ya ce "Ni to ki bani bredin na ci." Ya faɗa yana saɓa baki. Dariya Doctor Hashim ya yi ban da Abdul da ya yi shuru yana kallon ikon Allah da jinjina girman Ubangiji, wai kamar wannan sabcecan saurayin ne yake yin Shagwaɓa irin ta yara ƙanana, lalle Allah shi ke tsara wa bawansa rayuwar da yake son ya yi a dauron duniya. Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Hashim, yanzu meye mafita a kan lamarin bawan Allah nan?" "E gaskiya ne meye mafita." Zaiyan ya faɗa yana jujjuya takalmin. Girgiza kai Abdul ya yi yana kallon fuskar Abir da ya hango murmushi bayyana a fuskarta ta, wani sanyi ya ji ganin yau ta saki ranta wanda rabon da ta yi murmushi tun kafin ma a kawo gawar Abie. Tashi ya yi ya ɗauko wata paper wanda take ɗauke da duk abin da ya shafi rashin lafiyar Zaiyan, zama ya yi ya buɗe ya fara yi musu bayani.. "Ku yi haƙuri ranar kwana ukun Abie wani mutum ya zo nan yake sanar da ni wai shi ɗan'uwan Zaiyan ne yana so zai tafi da shi Kano, to ni kuma kawai sai na ji ban yarda ba da shi na ce masa ba zan iya ba shi Zaiyan su tafi ba har sai wanda suka bani amanar shi sun zo sun ce na ba shi zan yarda na ba shi. Mutumin nan ya dage sai na nuna masa ɗakin da aka kwantar da shi ni kuma na ce ban san maganar ba, ƙarshe na so na kira number ka na sanar da kai komai sai na tuna ranar kuna cikin jama'a, shi ne na kira Sajan ɗin Office ɗinku na sanar da shi ga abin da yake faruwa ya ce ga shi nan zuwa. Kafin na gama wayar tuni ya gudu ya bar ni a wajan na yi ta duba shi amma sam ban gan shi ba, hakan ya sa na sa aka ƙara sa idanu a ɗakin da yake ƙarshe ma na kai shi wani ɗaki wanda ba kowa ake kaiwa ciki ba." Da sauri Abdul ya kalli Doctor Hashim yana gyaɗa kai, ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Hasashena ya fara zama gaskiya, tabbas akwai abin da ba daidai a cikin lamarin nan." Ya faɗa yana tuna abubuwan da suka kulle masa kai a baya yanzu a hankali yana samun mafita. "To in kuwa haka ne Yaya mai zai hana mu ɗauke shi mu tafi da shi gidanmu." Abir ta faɗa tana kallon Zaiyan da ya kamo mayafinta yana wasa da shi. Doctor Hashim ya gyara zama ya ci gaba da cewa "Bayanin abin da ya shafi rashin lafiyar sa ya kamata mu ba wa muhimmanci in ya so kai Abdul sai ka ji da sauran." Jinjina kai kawai Abdul ya yi bai ce komai ba ya yi shuru. "To Yaya Hashim yanzu wani magani za ku ɗaura shi a kai wanda zai ci gaba da sha kafin wani lokacin mu ga mai Allah zai yi." Ta faɗa tana janyo mayafinta rabi ta rufe ƙirjinta rabin kuma ya riƙe gam yana naɗawa a hannunsa yana warwarewa. "Kwarai kuwa da gaske ni nasan komai zan saya miki takalmi Anty, na kawo miki bredi ki ci?" Zaiyan ya tari numfashin Doctor Hashim da Ke shirin yin magana.. Ɓata fuska Abir ta yi tana kallon shi cike da tsananin tausayi, kuka take son yi ko za ta ji sassaucin abin da take ji a gangar da ruhinta amma ta yi ƙoƙari ta danne kuka sai sauke ajiyar zuciya take. "Gaskiya ciwon nan nashi ya kai matakin ƙarshe, amma duk da haka ba ta ɓaci ba da izinin Allah sai ki ga an dace ya ji sauƙi. Akwai wani Abokina da can Amerika zan sa ya turo min da wani magani, wanda nake kyautata zaton in sha Allah zai ji sauƙi in kuka saya masa shi yana sha. Wannan raunin na hannunsa da na kunce mi shi ɗaurin sai kawai na ga babu shi babu alamar sa, na yi mamaki matuka saboda wajan an sa wani abu mai tsinin gaske an huda kuma ba wai huda ƙarama ba." Da sauri Abir ta kalli Zaiyan ta ɗago hannun nasa ta ga babu komai, saurin ja da baya ta yi tare da jafe ƙirji ganin ɗayan hannun wasu ƙuraje ƙanana sun cunkuso masa. Baki na rawa ta ce "Yaya ka ga dibi wasu ƙuraje da suke fito masa a hannu." Doctor Hashim ne ya miƙe ya ce "Karku damu da wannan zan rubuta muku wani pharmacy sai ku biya ku saya kuke shafa masa." Ajiyar zuciya ta sauke ta gyara zama ta ce "To yanzu ka nuna masa maganin mu gani ko ya ka ce Yaya?" Ta ƙarasa maganar da tambayar Abdul. "Haka ne Baby, yanzu ya kamata mu ɗauke shi tun kafin wanda ya zo ɗaukan shi ya dawo ya sace shi ba ku sani ba." Ya faɗa yana tashi tsaye. Hararar shi Doctor Hashim ya yi yana faɗin "Haba dai Aboki ya zan yi sake wani ya shigo har Asibitin nan ya sace shi?." Hararar shi ma Abdul ya mayar masa ya ce "Malam kawai ka yi abin da na ce." Ya faɗa yana isa inda suke ya dubi Zaiyan ya ce "Ɗan'uwa tashi mu tafi gida." Maƙale kafaɗa ya yi yana cuno baki gaba ya kalli Abir ya ce "Anty wai ya ce min ɗan'uwa mu tafi gida?" Ya faɗa yana nuna Abdul da hannu irin yadda yara suke in za a ɗauke su daga wajan iyayensu in ba su so. Tashi ta yi tsaye shi ma ya tashi yana riƙe da mayafinta ta kalle shi ta ce "E ɗan'uwanka ne ko ba ka so ka je gida ne?" Saurin kallon Abdul ya yi sai kawai ya yi dariya ya ce "To ina rawanina yake?" A yadda Abdul yake da saurin fusata bai fusatar ba sai ya girgiza kai kawai yana tausayawa Zaiyan, kamo hannunsa ya yi ya ce "Shi ma yana gida muje sai a ba ka." Sake maƙale kafaɗa ya yi ya ƙara komawa bayan Abir kamar wanda ya ga abin tsoro, ganin haka ya sa Doctor Hashim yin ƴar dariya ya ce "Ƙanwata in fa ba ke kika ce masa ku tafi ba, to fa sai dai ku yi ta tsayuwa a nan." Ajiyar zuciya ta sauke ta dube shi ta ce "Zaiyan muje gida ka ji zan ba ka rawanin naka in mun je." Da murna ya fito ya ce "Babba fa nake so wanda zai kai haka." Ya faɗa yana yin faɗi da hannayensa. To kawai ta ce masa suka fita mayafinta rabi a hannunsa Abdul na biye da su a baya har suka fito harabar Asibitin, sai da Doctor Hashim ya ga tafiyar su sannan ya koma ciki.. Suna cikin tafiya a hanya ya dami Abir da yunwa yake ji zai ci abinci, jin haka ya sa Abdul samun wuri ya taka birki a gefen titi ganin wasu masu abinci. Har zai fita kuma sai ya fasa yana tunanin ya wuce ajin ya sayi abincin bakin hanya ana ganin shi da kima da daraja a cikin gari. Kallon shi ta yi ta ce "Yaya lafiya dai ka tsaya?" Girgiza kai ya yi ya ce "Dama shi zan sayo wa abinci sai kuma na ga hakan bai dace da ni ba." Murmushi ta yi ta ce "Yaya ka rabu da shi kawai, indai maganar cewa yunwa yake ji ne abin ya zame masa jiki ko abinci yake ci za ka ji ya ce yunwa yake ji zai ci abinci." Dafe kai ya yi ya ja motar suka wuce... Sai da suka kusa zuwa gida ya tuna bai fa sanar da kowa ba za su kai Zaiyan gidan, hannu ɗaya yasa ya ɗauko waya ya danna wa Abba kira, bayan ya ɗauka suka gaisa nan ya soma masa bayanin komai. "Abba dama mun ɗauko Zaiyan ne za mu kawo shi gida, amma ya kake ganin za ayi da shi? Mu kai shi nan gida ko mu kai shi ɗayan gidan a samo mai kula da shi?" Daga cikin wayar Abba ya nisa yana aje borrow da ke hannunsa ya ce "Yanzu dai ku fara zuwa da shi nan in ya so sai mu yi shawarar abin da ya dace, zan kira Kabir da Jabir sai a zauna ayi maganar da an jima in mun dawo gida." Godiya ya masa sannan suka yi sallama. Suna isa gida ya fito yaran sa suka sara masa ya ɗaga musu hannu, Abir ta fito daga motar ta zagaya ta buɗe masa sai kawai ta ga yana bacci, ta kalli Abdul da ya yi tsaye yana jiran ta ta ce "Yaya bacci fa yake yi." Yaran sa ya yi wa nuni da cikin motar, mutum biyu suka iso bakin motar suka buɗe tare da ɗauko shi suka nufi ciki.. Yasmin da ke tsaye ita da Fatima za su fita suka ga an ɗauko kyakyawan namiji sai suka cika da mamaki, Fatima ta fara cewa "Anty Yasmin ko dai wancan shi ne mahaukacin da aka ce yana Asibiti wanda ya taimaki Baby?" Gyaɗa kai ta yi itama ta ce "Tabbas wannan shi ne mu koma mu faɗa wa Mami kin ga Abba ya kusa dawowa sai muje mu gani da idanunmu." Juyawa suka yi da hanzari cike da zakuwar son ganin kamannin Zaiyan suka faɗo palo, Mami da ke waya ta zabura jin an faɗo palon ba sallama, ganin su Yasmin ne sai ta daka musu tsawa tana zagin su su kuma sai kumbura baki suke. A fusace ta ce "Wallahi Yasmin sai na ci ubanki in Kuka sake shigo min waje ba neman izini." Ta nuna su da hannu kamar za ta kai musu duka. Tana kumbura ta soma magana ƙasa-ƙasa ta ce "Mutum shi ba shi da aikin komai sai yin waya da an zo kuma ya hau mutane da faɗa. " "Magana kike ne?" Saurin cewa ta yi "A a ban ce komai ba." Sake tsare gida Mami ta yi ta ce "Me kuka ji ina faɗa da kuka shigo? Sannan wa ya ce ku dawo bayan kun ce min za ku gidan ƙawar Yasmin?" Ta jero musu tambayoyi. "Mu babu abin da muka ji , kawai dama mun dawo ne dan mu ce miki mun ga an kawo wannan mahaukacin da aka ce yana Asibiti. " Fatima ta faɗa tana kallon Mami. Dafe ƙirji Mami ta yi cikin zare idanu ta ce "What? Mahaukacin ne aka kawo mana cikin gida dan ya kashe mu? To ni kan babu inda zan fita." Dariya Fatima ta yi sanin halin Mami da mugun tsoron mahaukaci ta ce "Ina jin fa har yanzu bai farfado ba daga sumar, dan yanzu ma sai da aka ciccibe shi aka shiga da shi part ɗin su Baby." Ajiyar zuciya Mami ta sauke ta ce su zauna in Abba ya zo za su ji komai a bakin shi... Suna shiga Grandma ta miƙe za ta kwasa a guje Abdul ya yi saurin cewa "Grandma tsaya su IB ne fa." Dafe ƙirji ta yi tana mayar da numfashi ta koma ta zauna ba ta ce komai ba har suka kwantar da shi a kan doguwar kujera suka fita, sai a lokacin ta samu damar sauke hannayenta da ta ɗaura sun da ta yi a ƙirji ta kalli Zaiyan da yake ta bacci, a sanyaya ta ce "Amma kai kuwa Abdul ina gaf da cin ubanka a gidan nan, taya za ka shigo mun palo da gardawan maza sun yi ɗamara?" Ta faɗa tana hura hanci. Murmushi Abir ta yi ta dawo kusa da Grandma ta zauna tana faɗin "Grandma yau dai ga wanda ya taimake ni mun kawo shi har gida." Saurin kallon shi Grandma ta yi ta miƙe ta iso ta tsaya a daf da kujerar ta zuba masa idanu tana kallon shi, ba zato suka ga tana goge hawaye ta zauna a ƙasa, Abdul ya ce "Grandma kukan fa da kike na mene ne?" "Kayya ɗan nan! Bar ni na yi kuka, ji na yi yaron nan ya bani tausayi ya kuma shiga raina, ga mutum har mutum amma babu hankali Allah ya ba ka lafiya ya ma sunanshi?" Ta faɗa tana waiwayen Abir. Muskutawa ta yi sannan ta ce "Sunanshi Zaiyan ne." Jinjina kai ta yi tana faɗin "Allahu akbar." Jin ana kiran Sallar La'asar yasa Abdul ya miƙe ya shiga ɗakin Mommy ya sanar da ita sun zo da Zaiyan zai fita a kula da kyau kar ya gudu, da to ta amsa sannan ya fita.. Tare suka dawo da su Abba har da Daddyn Aruf da Salim suka zarce part ɗin Mommy. Da Sallama suka shigo ciki aka amsa musu suka zauna, Abba ya yi tsaye yana kallon Zaiyan da ke ta bacci fuskarsa ɗauke da murmushi, wata irin faɗuwar gaba ya ji ta ziyarce shi ya yi saurin zama a gefen kujerar da ke kusan tashi yana sauke numfashi. Sai da suka zazzauna sai ga su Mami sun hallara, bayan kowa ya yi shuru Abba ya ce "To yau dai ga wanda ya taimaki Mamana an kawo shi, dan haka muna so mu ga inda ya dace a aje shi a ci gaba da masa magani." Mommy ta nisa ta ce "Allah sarki bawan Allah! Ubangiji ya ba shi lafiya mai ɗaurewa, amma ni a ganina da an gyara wancan ɗaki a saka shi a ciki tun da yana da ƙofa daga waje, inyaso sai a samo wanda zai ke kula da shi kafin mu ga abin da Allah zai yi." Ta faɗa tana kallon shi ganin yana motsawa alamar zai farka. Daddy ya ce "Kuma fa kin kawo shawara matar Yaya, amma mai kaku gani za ayi." Ya faɗa yana kallon Abba da Daddyn Aruf. Abba ya ce "Kawai ayi haka." Jin abin da ya faɗa Daddyn Aruf ya ce shi ma abin da yake son faɗa kenan, kawai yanzu a samo mai kula da shi. Mami ta yi caraf ta ce "Ba shakka! Wato mu saboda ba a ɗauke mu a zaman mutane ba shi ya sa ba a ji ta bakinmu ba ko?" Abba ya zuba mata idanu ta wani masge tana harare-harare Umma ta amshi zancen da cewa "Ato gane mini hanya, makaho ya zo gulma! Yanzu da Mahaukaci kamar wannan sabcecan saurayin za mu zauna gida ɗaya? Mu je muna bacci cikin dare ya lallaɓa ya kashe mu ko ya tsinna mana wuta mu ƙone." Daddyn Aruf da yake ya fi su saurin fusata ya ce "Last warning! In ba a saka ku ba cikin magana kar ku yi wa mutane magana indai ba alkhairi za ku faɗa ba, na ga dai ba a part ɗin ku za a aje shi ba a na mahaifiyarmu ne ko?" Ya faɗa a fusace kamar zai kai musu duka. Murmushi Abba ya yi ya kalli Abdul da shi ma Daddyn Aruf yake kallo yana murmushi ya ce "Ka ga Jabir rabu da su mana, su za su faɗa mana yadda za mu tafiyar lamuran familynmu?" Abdul ya gyara zama ya ce "Abba duk ku bari ni nasan me zan yi a kai." Ya faɗa yana haɗe rai dan kar ma wani ya ce masa me ya sa. Zai sake magana suka ga Zaiyan ya tashi zaune yana mutsitsika idanu, ganin mutane dayawa a palon sai ya waro idanunsa da bacci bai gama sakin su ba, kallon ko'ina yake a palon sai ya yi murmushi, saurin zuro ƙafafuwansa ya yi fuskarsa na nuna alamun tsoro ya ce "Ƙundun uban can! Alkur'an na zo faɗa." Ya yi maganar yana hilla ƙafarsa kana dariya. Kowa shuru ya yi ba wanda ya tanka masa har ita oganninyar ta zuba masa idanu, ganin ba su ce komai ba ya kuma cewa "Nan masarautata ce ko?" Ya shafa kujerar da yake kai yana murmushi. Yasmin ta ce "Wow! Ke Fatima kalli ki ga Wallahi mahaukacin nan da yana da hankali handsome boy za a yi a wajan nan, dubi dimple ɗinsa har ma da wushirya gare shi." Ta ƙarashe maganar tana ƙara yin ƙasa da murya dan kar Abdul ko Abba ya ji su. Fatima ta ce "Ai kuwa dai duk da ba a cikin sutura mai kyau yake ba, amma Wallahi ya haɗu sai dai rashin hankalin dai, maza ɗauko mana video shi kar Yaya Abdul ya gani." Saurin saita wayarta ta yi ta rakube a bayan Yasmin kamar mai chatting ta dinga ɗaukar shi video. Zaiyan ganin ba su ce masa komai ba sai ɓata fuska kamar zai yi kuka ya ce "Anty." Jin abin da ya faɗa sai Grandma ta ce "To wace ce kuma Anty?" Kallon Grandma ya yi sai ya tashi ya nufo ta , saurin maƙalewa ta yi a jikin kujera tana faɗin "In yana duka kar ku bari ya iso inda nake." Abdul ya gumtse dariyarshi yana kallon Grandma har ya ƙaraso kusa da ita ya zauna a ƙasa sai gani suka yi ya saka kuka, dariya Yasmin ta yi Abba ya harare ta sai ta yi saurin rufe baki. "Mama ina Anty?" Ya tambayi Grandma. Abir ta leƙo da kanta daga gefen shi ta ce "Gani nan ba ka ganni ba?" Jin muryarta sai ya yi saurin juyowa inda ya ji muryarta suka haɗa ido, dariya ya yi ya ƙara matsowa kusa da ita ya ce "Anty bredi fa ba ki bani ba." Murmushi ta sakar masa ta ce "Zan kawo ma ai yanzu, Yaya ya kamata fa a taimaka masa da wanka a ba shi wani kayan." Ta faɗa tana kallon Abdul.. To ya ce mata sannan ta sa aka kawo masa shinkafa da miya, haka ya barbaje ya dinga ci yana zubarwa har ya gama ta miƙa masa ruwa ya sha sannan ya shiga jaddada mata bredi da rawaninsa ba ta ba shi ba, so yake ya tafi fada.. Ammi ta gyaɗa kai tana kallon Zaiyan ta ce "Sannu ka ji bawan Allah." Ko kallon ta bai yi ba, gabaɗaya kowa ya tashi ya rage daga Grandma sai Abir.. Bayan ya gama Abdul ya dawo da maza huɗu daga cikin masu tsaron gidan ya ce su ɗauke Zaiyan su tafi da shi, Abir ta so in magana amma ganin fuskar Abdul ba wasa sai ta yi shuru da bakinta aka yi wa Zaiyan wayon cewar bredi za a ba shi suka ɗauke shi... *NIGER* Masarautar Niamey. Hon ake yi Maigadi ya tafi a guje ya buɗe get ɗin, motoci ne farare su takwas a jere suka dinga shigowa ɗaya bayan ɗaya, suna gama paka motocin Dogari ya fito da sauri motar kusa da wadda ya fito ya buɗe ya ɗauko wani jan capet ya shinfida daga bakin ɗaya daga cikin motocin har zuwa wata ƙofa ruwan gold. Saurin dawowa ya yi ya buɗe mota ta biyar yana faɗin "Gyara kimtsi da kyau sauka lafiya Yarima." Sai da aka sauƙi kusan minti uku sannan Yarima ya miƙo kyakyawar farar ƙafarsa waje, sai can ya miƙo ɗayar ya fito gabaɗaya, dogo ne sosai kyakyawa fari kamar Balaraben Saudiya, yana saje wanda ya kwanta luf sai ƙyalli yake haka ma sumar kansa a kwance take luf ga ta yi ɓaki luɓuk. Ƙafarsa sanya take da takalmi mai kama da na fata, jikinshi sanya yake da alkyabba kalar kayan da yake jikin Red color. Wani irin ƙamshi yake zubawa na musamman sai bin harabar gidan yake da kallo yana murmushin gefen baki wanda in ba lura ka yi ba za ka taɓa cewa ya yi ba. Tsadaddan ogogon da ke manne a hannunsa na hagu ya ɗago hannun ya kalla, inda ya nuna masa karfe 2:30pm ya lumshe idanuwansa ya shaƙi iska yana buɗe su akan hannun nasa. Waɗanda suke wajan suka soma masa barka da zuwa yana ɗaga musu hannu. Capet ɗin da aka shinfida ya suma takawa a hankali ana ta masa kirari, duk wanda ya zo wucewa sai ya yi sauri ya zo ya kwashi gaisuwa, ganin sun kusa isa wata ƙofa sai ya ɗaga musu hannu suka ja da baya suka tsaya a bakin ƙofar. Wani tamfatsetsan palo ne na alfarma wanda ya sha kayan ado capet ɗin kansa in kana takawa kamar kana tafiya akan kafita, ya shigo da sallama a nutse cikin takunsa na izza da mulki ya zauna. Ɗaya bayan ɗaya Hadiman sashen suka dinga zuwa suna masa barka da zuwa shi kuma yana ɗaga musu hannu, sai da ta ƙarshe ta zo yatsar dai ta, cikin girmamawa ta durƙusa tana yin ƙasa da kanta saboda tasan halin Yarima sarai baya son ake kallon shi, ajiyar zuciya ya sauke ita har ta ma cire rai da zai ce mata wani abu sai ta ji ya yi gyaran murya. Gyara zama ya yi yana wani ciccin magani kamar an masa lefi fuskar nan babu annori ya ce "Jakadiya Mamma fa?" Ƙara sunkuyar da kai ta yi cikin girmamawa ta ce "Ranka ya daɗe tana ciki yanzu na gama shirya ta." Bai ce komai ba ya mata alama da ta tafi, da hanzari ta tashi ta wuce. Sai na ya ɗauki kusan minti biyar a zaune yana shan ƙamshi sannan ya miƙe ya nufi ɗakin, a hankali ya shiga inda ya hango ta zaune ta ƙurawa waje ɗaya idanu, da ƙyar ya iso ya zauna a gabanta murya na rawa ya ce "Mamma.!!!.. _*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_ [6/20, 7:45 PM] Ummu Amjad: _*~A HAKA NAKE SON SHI~*_ _+966577675904_ *Arewabooks.com: Saratalkasum1897* Shafi na (15) Da ƙyar ya iso ya zauna a gaban ta murya na rawa ya ce "Mamma!!" A hankali ta juyo ta zuba masa idanu tana masa kallon irin ta ga baƙuwar fuska, sai da ta ɗauki lokaci tana kallon shi sannan ta sakar masa murmushi tare da miƙa hannu ta shafa fuskarsa, bakinta na motsawa kamar mai son yin magana. Wani kalar zazzafan numfashi ya fesar ya ɗaura nasa hannun akan nata cikin wani kalar yanayi wanda shi kansa ya kasa gane wani hali yake ciki, a sanyaye ya kuma cewa "Mamma sannu Allah ya ba ki lafiya." Murmushi ta kuma sakar masa hawaye sun cika mata idanu sai kallon ɗan nata take cike da tsabanin so da ƙauna, zare hannunta ta yi ta janyo abincin da aka jera mata da kayan marmari, wanda ko kallon abincin ba ta yi bare ma ta ci, buɗe wata ƙatuwar kula ta soma yi ya yi saurin tashi daga inda yake ya iso gefen ta ya amsa ya buɗe kular. Shinkafa ce fara a ciki ya buɗe ɗayar inda ya ga miyar ta sha isashen nama da kayan haɗi sai zuba ƙamshi take, lumshe idanu ya yi yana ɗan murmushi ya buɗe su akan Mamma ya ce "Za ki ci wannan na zuba mana?" Ya faɗa yana rausayar da kai, ita kuma ta gyaɗa masa kai hakan yasa ya zuba musu ya aje a gaban su. Haka ta dinga ɗauka tana ba shi a baki fuskarta ɗauke murmushi shi ma haka. Bayan sun gama ya janyo ruwan da aka zuba a cikin wani golden ɗin ɗan ƙarami kofi ya tsiyaya cikin wata roba, hannunta ya janyo ya wanke itama ta wanke masa nasa, ya yunƙura zai tashi ya ji ana buga ƙofa. Kallon Mamma ya yi ita ɗin ma ƙofar ta kalla, gyara zama ya yi tukun ya bada izini aka shigo. Jakadiya ta shigo tare da rusunawa ta ce "Ranka ya daɗe Maibartaba ya ce a sanar da kai yana kiran ka a can ɓangarensa." Annorin fuskar Yarima ne ya ɗauke ya kalli Jakadiya ya mata alama da kwashe kayan abinci, sannan ya kama Mamma ya miƙar da ita tsaye suka nufi wata ƙofa.. Taɓe baki Jakadiya ta yi tana jinjina izza da girman kai irin na Yarima, ta kira hadimai suka kwashe kayan wasu suka gyara wajan tare da kunna turaren wuta aka aje a wajan. Suna shiga Yarima ya buɗe wani wuri a ɗakin sai ga Alkyabba kala-kala a jere, ya ɗauki kalar wadda ta zo daidai da kayan jikin Mamma ya sanya mata tare da fesa turare mai daɗin ƙamshi sannan ya zaunar da ita ya fita a ɗakin. Bai jima sosai ba sai ga shi ya buɗe ƙofar ɗakin Mamma, sanya yake da wata blue ɗin jallabiya ƴar Dubai ya ɗaura hula kalar rigar, ga wani fitinannan ƙamshi da yake yi yana taku ɗaiɗai har ya iso cikin ɗakin ya samu Mammi a zaune a inda ya barta. Sunkuyawa ya yi ya kama ƙafarta ya sanya mata wani lallausan takalmi mai kyau, ya ɗago ya ce "Mamma wai ina Auta take ne?" Ya faɗa yana murmishi duk da ya san ba amsa za ta iya ba shi ba. Girgiza maza kai ta yi tana masa nuni da ta tafi makaranta hakan yasa ya sauke ajiyar zuciya sannan suka bar ɗakin. A tsaye suka samu Jakadiya tana jiran fitowar su tana ganin su ta rusuna ta ce "Barka da fitowa Fulani." Gyaɗa mata kai kawai Mamma ta yi suka wuce yana gaba suna biye da shi a baya ita da Jakadiya da wasu Hadimai biyu , suna isa bakin wata ƙofa wani Hadimi ya zo da sauri ya buɗe musu yana faɗin "Barka da sauka Yarima Allah ya ja da kwanan ka, barka da zuwa ranki ya daɗe ." Ya faɗa yana yin murmushi. Shi ma Yarima murmushin ya yi wanda ya sa Hadimi sakin baki, saboda bai taɓa ganin Yarima ya saki fuska ba har ya yi murmushi sai yau. Goya hannayensa baya ya yi ya kalli Hadimin tare miƙa masa hannu ya ce "Halil ya kake?" Sunkuyar da kai ya yi yana ƙara shiga al'ajabin Yarima, sai da Yarima ya yi gyaran murya sannan ya ɗago ya ga ya sake miƙa masa hannu, ya yi saurin amsa yana washe baki tare da cewa "Ina nan lafiya ranka daɗe, fatan an dawo lafiya?" Bai sake ce masa komai ba ya yi gaba ya shige su Mamma na biye da shi. Halil ya ɗan matsa daga bakin ƙofar yana jin daɗi yau ya taɓa hannun Yarima, wani da ke kusa da shi ya ja tsaki ya ce "Uban neman guri har wani wage baki kake yau Yarima ya kula ka." Halil ya ɗage masa gira ɗaya ya ce "To ya son ranka ɗan hassada da bakin ciki? Ai duk wanda Yarima ya kula to shi mai matuƙar sa'a ne a cikin masarautar nan, ni kuma dama masoyin shi ne dan haka ina ƙaunar shi." Yana gama faɗin haka ya wuce abin sa.. Suna shiga babban palon suka samu Maimartaba tare da Kilishi da Sarauniya Bilkisu sun hakimce a gefen Maimartaba kowacce sai zuba izzarta take, Yarima ya ƙara ɗaure fuska ya ruƙo hannun Mamma suka ƙaraso. Murmushi shinfide kan fuskar Maimartaba yana kallon ɗan nashi, hannu ya miƙa wa Mamma ta ɗaura nata a kai ta zauna a daf da shi tsakanin Kilishi da Maimartaba a nan ya mata guri ta zauna, wani kallon banza Kilishi ta yi wa Mamma tana ɗago kai suka haɗa idanu da Yarima da fuskar nan take tamke kamar bai taɓa yin dariya ba, saurin kawar da kai ta yi tana yin kwafa. "Suhal barka da zuwa, ya hanya?" Cewar Maimartaba yana jin son ɗan nasa na ratsa ma'adanar sirrinsa. Matsowa ya yi gaban Maimartaba ya ce " Alhamdu Lillah Papa, ya gidan?" Ya faɗa yana ƙara sunkuyar da kanshi ƙasa kamar zai kwanta a kan cinyar Maimartaba. Hannu ya kai a kan Yarima Suhal shi kuma ya yi saurin ɗauke hular sumarsa ɓaka ta bayyana a kwance luf, shafa kan nasa ya yi ya ce "Allah ya yi maka albarka Suhal, yanzu tun da ka gama karatunka ka samu aiki ai sai ka nemo mata ayi maka aure." Rausayar da kai ya yi cikin nuna so ga mahaifin nasa ya ce "Haba Papa shi kenan dan na samu aiki sai ka ce na nemo mata, 'yan matan nan fa yanzu sai ka duba kafin ka samu mai nutsuwa da hankali." Ya faɗa yana wani yamutsa fuska. Murmushi Maimartaba ya yi ya ce "To shi kenan ai ina dai kallon hanya, idan har ka bari haƙurina ya ƙare zan aura ma duk wadda na ga dama, jiya ma mun yi magana da Sarki Agadez akan ƴar wajansa na ce masa ya bari tukun ka dawo sai na gani ko kai ko Sultan wani sai ya je ya ganta." Kilishi da ta cika da haushin Suhal ko gaishe da su bai yi ba ta muskuta tana yin murmushin yaƙe, cikin kissa ta ce "Suhal ya hanya? An dawo lafiya? Gaskiya har yanzu ba ka canja hali ba yaron nan, ka zo ka same mu ko ka gaishe mu a matsayin mu na iyayenka, anya Suhal?" Ta faɗa tana ƙurawa Maimartaba na mujiya dan ta ji me zai ce.. Sosa kai ya yi yana jinjina lamarin Kilishi, can ciki-ciki ya ce "Ku yi haƙuri na sha'afa ne saboda murnar ganin Papa." Ya faɗa yana sunkuyar da kai. Gyaɗa kai ta yi kamar ƙadangaruwa ta yi wa Sarauniya Bilkisu kallon ya kika ga salon sannan ta dawo da kallon ta kan Maimartaba ta ce "Ranka ya daɗe ai ina ga tun da Sultan ne babba shi ya kamata ace ya auri ƴar Sarkin Agadez, ba wannan solobuyon ba da ko maganar auren aka masa sai yake wani ciccin magani kamar ya ga abin kyama. " Ta faɗa tana hararar shi haɗi da murmushi.. Wani irin sanyi ya ji dan dama shi kwata-kwata ƴar Sarkin Agadez ba ta kwanta masa a rai ba, ta cika wayewa da yawa hakan yasa ya yi hamdala da maganar Kilishi.. Maimartaba ya ce "Kuma fa Kilishi kin kawo shawara mai kyau, yanzu zan sa shi Sultan ɗin ya je ya ganta duk da ya santa, amma wannan zuwan maganar aure ce ba ziyara ba." Taɓe baki Sarauniya Bilkisu ta yi tana kaɗa kai ta saki murmushi cikin tausasa murya ta ce "Allah ya taimake ka ni ai nake gani mai zai hana a haɗa Suhal aure da Fauziya, tun da dama son shi take ta ɓoye dan ita mace ce mai kamun kai da kunya ba za ta taɓa tarbar shi ta sanar da shi ba." Ta faɗa tana wani irin malalacin murmushi tare da kallon Kilishi da ta saki baki tana jin bayanin Sarauniya Bilkisu.. Saurin kallon ta Suhal ya yi ya girgiza kai ya ce "Gaskiya ni Papa bana son ka aura min Fauziya, yarinyar da ba ta jin maganar kowa za a aura min ita?" Maimartaba ya ce "Ai kuwa Fauziya za ta dace da kai, ka ga duk inda za ka je sai ka tafi da matarka." Ƙara ɗaure fuska ya yi yana jin zuciyarsa na masa zafi, in ban da ma Sarauniya Bilkisu da makirci taya ma za ta kawo maganar ya auri Fauziya yarinyar da kullum tana yawo gidan ƙawaye? Kwafa ya yi yana kuma tuna cewa da ace Mahaifiyarsa na magana ai ba za ta taɓa bari a aura masa wadda ba ya so ba, ya tashi tsaye ya ce "Papa zan je na ɗan huta kaina ciwo yake min." Cikin tausayawa Maimartaba ya kalle shi ya ce "To shi kenan ka je zan sa Likita ya shiga a duba ka." "A a Papa ba sai an duba ni ba, tafiyar nan ce tasa kaina ke ciwo." Mamma itama ta miƙe ta yi wa Maimartaba nuni da ita ma za ta wuce sashenta ya ce ta tsaya, ba dan ta so ba ta bar Yarima Suhal ya fita da sauri yana ƙara jin haushin Sarauniya Bilkisu.. "Ku ɗan bamu waje ina so za mu yi magana da Fulani." Bakin ciki ne ya mamaye zuciyar Kilishi ta ce "Wato Maimartaba na lura a matan naka ma son kai kake yi, yanzu dan za ka yi magana da ita sai mun bar palon nan kamar ba ka yarda da mu ba? Indai maganar auren Suhal ce ai muma iyayensa ne mu yakamata ma ace mun zauna da kai an tsara komai, ko sayayyar kayan lefe za ayi mune dai ya kamata ka nema ba wadda ta haife shi ba. Amma tun da ka nuna mana mu ba iyayen shi ba ne ba komai." "Ba ban yarda da ku ba ne, magana zan yi ni da ita kawai abin bai shafe auren Suhal ba." Ya faɗa yana komawar sarkin sa, amma duk da haka Kilishi ta ce ba inda za su je ayi komai a gaban su. Sai da suka gaji da yin shurun ganin fuskar Maimartaba ba wasa yasa suka tashi suka bar palon, sai bayan sun tafi ne Maimartaba ya juyo ga Mamma ya kamo hannayenta cikin kulawa ya soma mata magana.. "Ki yi haƙuri Fulanina, in sha Allah kema wata rana za ki kike magana kamar kowa karki saka wa kanki damuwa." Hawayen da suka cika kwarmin idanuwanta ne suka samu damar zubowa ya sa hannu ya share mata, cikin tausasa lafazi ya shiga kwantar mata da hankali ita kuma ta nuna masa ba ta son Yarima Suhal ya auri Fauziya dan ta ga baya son ta. Bayan sun gama tattaunawa yasa aka kira Jakadiya ta zo ta ɗauke ta suka koma sashenta... *NIGERIA* Cikin shigar ta riga da wando ta fito daga cikin kitchen hannunta ɗauke da glass cup, a nutse ta zauna a kusa da Mom sai kuma ta turo baki gaba ta saurayar kai cikin Shagwaɓar take kallon Mommy. Hararar ta Mommy ta yi ta ce "To me kuma aka yi da kika sakani a gaba kina min kallon ƙurulla?" Turo baki ta yi ta yi raurau da idanu kamar za ta kuka ta ce "Mom ki ce wa Yaya ya faɗa min inda ya kai Zaiyan, so nake ya kaini na gan shi yaushe rabona da shi tun fa ranar da muka zo nan kusan kwana goma kenan." Ta faɗa idanuwanta na cika da hawaye wanda kaɗan ya rage su silalo, wani irin yanayi take ji wanda baki ba zai iya musalta shi ba, sosai kewar shi da son ganin shi suka hana gangar jiki da ruhinta sukoni. In ta yi wa Abdul magana sai ya ce mata ba yanzu ba, hakan ya sa ta daina kula shi ko gaishe da shi ba ta yi in ya zo sai ta ƙi fitowa ta yi zaman ta a ɗaki ta kulle dan kar ma ya shigo mata ba ta sani ba. Mommy da take jan casbaha tana lazumi ta dakata da ja ta dube ta ce "To yanzu ni me kike so na ce masa?" Ai kuwa kamar jira take ta ɓare baki ta shiga rera wa Mom kuka har da shure-shure kamar yarinya ƙarama, ko kallon ta Mommy ba ta yi ba ta dinga rusar kuka har sai Mommy ta ga abin ba mai ƙarewa ba ne ta juyo suka fuskanci juna. "Kukan ya isa haka yi shuru, ba dai so kike ki duba shi ba?" Saurin gyaɗa kai ta yi tana goge hawaye, Mommy ta yi murmushi ta ce "Zan amsa magana sai ya sa a kaiki ki gano shi." Dariya mai haɗe da hawaye ta yi ta rungume Mommy ta ce "Thank you my sweetheart. " Ta faɗa tana sumbatar ta a kumatu sannan ta tashi ta ɗauko wa Mommy wayarta ta tsare gida ta ce sai Mommy ta kira shi yanzu ta faɗa masa, girgiza kai Mom ta yi ta amshi wayar ta lalibo number Abdul tana shiga ya ɗaga, bayan sun gaisa ta sanar masa ya zo ya ķai Abir inda Zaiyan yake ta addabe ta da kuka.. Yana zaune a cikin office ɗinsa ya yi kwafa, wato ma har kai ƙaran shi take dan ya ƙi kaita wajan shi? Zai dawo gidan ai tun da ita in ta kafe akan abu ba ta saduda kamar ɗiyar maguzawa. Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Wallahi Baby ta fiya neman rigima, ni fa na ce da zarar na shirya zan kai ta gan shi." Mommy ta ce "To ni dai kazo ka rabani fa fitinarta bana son wannan kukan nata ƙi ƙarewa har taja wa kanta ciwon kai." To ya ce zai sa a kaita sannan ya katse wayar yana sakin murmushi, Mommy ta ce "Sai ki shirya ai ga shi zai sa a kaiki." Da sauri ta tashi har tana tuntube ta shige ɗakinta, zama ta yi tana murmushi ta buɗe wata leda dake gefen gadonta, kayan sawa ne kala-kala sun kai kala goma har da takalmi ta haɗe su duka a leda ɗaya, buɗe drower ta yi ɗauko chocolate mai yawa ta zuba a ledar. Har ta miƙe sai ta ga wani abu ɗan ƙarami ɓaki mai kama da memory, da mamaki take kallon abin ta sa hannu ta ɗauka tana jijjuyawa. Cike da al'ajabi ta ce "To shi kuma wannan ɗin meye?" Ta faɗa tana ƙara juya abin. Ganin tana ɓata lokaci sai ta bude inda take aje kayan zakinta ta aje abin ta sanya hijabi har ƙasa ta fito. Ko zama ba ta yi ba ɗaya daga cikin masu tsaron gidan ya ce ta fito su tafi, sai ta dawo ta cewa Mom ita kuma ta ce Allah ya tsare ta amsa da amin.. Zaune su Alhaji suke su huɗu a cikin wata rumfa irin ta hamshakan masu, kowannen su ya yi shiga ta alfarma sai dariya suke, Jarmai ya cire glass ɗin fuskarsa ya ce "Gaskiya ina yinka Alhaji, komai yana tafiya cikin tsari." Ya faɗa sana tafawa da Alhaji da ya yi shirmama a zaune da uban tumbi sai jin kansa yake na ƙara girma, gyara zama ya yi ya ce "Yo mu ɗin na wasa ne? Yanzu ba mun yi maganin matsalar mu ba mun huta." Ya faɗa yana murmishi. "Gaskiya ne Alhaji ni in da so samu ne ma, ina so mu san yadda za mu kwashe komai na Alhaji Ibrahim Abdullahi Maitama da Manager." Ɗayan ya faɗa yana sakin murmushi. "Wow kai amma fa kai kanka yana ja PA, yanzu mu tsara komai ta yadda in mun kai sheda ba za ayi wani kokwanto a kai ba, zan kuma je wajan Nadumbuza ya mana aiki mai ƙarfi. Sannan wannan ajiyar da ke hannun ƴarsa lalle a dage a amso ta daga wajan ta, in ta ta yi gardama a aika ta inda muka aika ubanta." Ya faɗa cike da jin haushin Abir yana hura hanci. Jarmai ya shaƙe da dariya ya ce "Ka kwantar da hankalinka Alhaji ai PA zai ji da komai, ko ka manta muna da masu yi mana aiki a cikin gidan nasu?" Sai a lokacin ya saki fuska ya ce "Haka ne fa kuma, to yanzu mu koma kan maganar ɗaya bayan mu gama sai mu ji da wannan yaran masu taurin kai, shi Ɗansandan nan har wani gani-gani yake yi wa mutane dan yana jin kansa shi wani ne, to in na ga dama sai na ce a tsige shi daga aikin kuma a lalata masa takardunsa sai mu ga ta yadda zai yi jin kan." Da Sauri Jarmai ya ce "No Alhaji in muka yi haka ai mun ɓata komai, kai dai mu yi abin da muka tsara ka rabu da yaron nan, abin da nake so mu samu a amso wannan ma'adanar bayanan da take wajan su, idan fa muka tsaya muna gani wankin hula zai kaimu dari.." Da haka dai suka gama tattaunawa kowa na kawo tashi shawarar har suka gama kowa ya nufi inda zai nufa.. Tafiya suka yi mai nisa sosai sun kusa isa wata Unguwar talakawa direba ya tsallaka bakin hanya ya yi packing, da mamaki Abir ta kalle shi ta ce "Ya dai ka tsaya a nan?" Gyara zaman rigarshi ya yi ya ce "Oga ya ce a sauke ki a nan sai mu ƙarasa da ke a ƙafa." Gyaɗa kai ta yi tana sakin murmushi ta buɗe ta fito, suma fitowa suka yi sai da suka wawwaiga ko'ina suka ga ba mai kallon su sannan biyu suka shiga gaba, bayan su ta bi wasu biyun suka bi bayan ta. Kowannen su akwai eapis a kunnensa, suna cikin tafiya lokaci ɗaya duk suka ɗaura hannu a kunne ɗaya daga cikin su ya ce "Hello Oga kana kan layi?" Abdul da ke duba wasu takardu ya gyara zama ya ce "Ku kula da kyau Ali, kar ku bari wani ya ga inda kuke bi." Ali ya gyara kai cikin girmamawa ya ce "Ok Oga za mu kula." "OK thank you guys, good bye." Ya katse kiran sakamakon nocking da ake, izinin shigowa ya ba da aka turo ƙofar. Kyakyawar budurwa ce doguwa fara wadda ba ta wuce 27years ba, sanye take da ɗinkin atamfa riga da siket ɗinkin ya matse ta da ƙyar take juyawa a cikin kayan, glass ɗin da ke manne a idanuwanta ta cire tare da ƙarasowa tana wani yauki da yanga ta yi saƙare da jakar hannunta ta ce " Oga can I be?" Cike da mamaki ya nuna mata kujera ya ce " sit down." Zama ta yi tare da ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana taunar cimgam, nan-da-nan Abdul ya fusata amma ya ɗaure ya danne ɓacin ranta dan ya ji da me ta zo masa, fuska ba annori ya ce "What's going on with you? and who are you?" Sauke ƙafarta ta yi cikin nuna jan hankali ta yi baya da gashin dokin da ke kanta, surar jikinta ta bayyana gabaɗaya ƙirjinta rabi a waje suke, siket ɗin kan shi an masa wata fataha daga kasa har kusan mazaunanta. Ƙara ɗaure fuska ya yi ya maimaita mata maganar, sai a sannan ta ce "Ranka ya daɗe ni na jima ina son ka ba tun yau ba, to na gaji ne da cutar kaina na ce bari na zo na faɗa ma abin da ke cikin zuciyata ko zan samu salama. Don Allah Abdul ka taimaka ka so ni ko da rabin wanda nake ma ne." Ta ƙarashe maganar tana yin fuskar tausayi... Tuni Abdul ya hargitse sakamakon ganin surar jikinta da ya yi, nan-da-nan hankalinsa tashi ainun ya rufe idanunsa yana karanto Addu'o'in neman tsari ga wannan makirar mata, wani irin murɗawa mararshi ta yi ya ƙara runtse idanu yana sauke ajiyar zuciya.. Ita kuwa ganin yanayinsa ya canja ta yi wani shu'umin murmushi ta yi saurin mayar da turaren da ta fesa a ɓoye, gyaran murya ta yi ta ce "Yallabai lafiya dai?" Idanuwansa a lumshe ya ce "Ki tafi zan yi tunani." Wani irin daɗi ne ya ziyarce ta kamar ta kurma ihu dan daɗi ta tashi daga inda take ta dawo kusa da kujerar shi ta tsaya tana ƙara kallon shi, shi kuwa tuni ya ji wannan ƙamshin turaren ya ƙara kusanto shi sai ya yi saurin buɗe idanu ya gan ta a tsaye a kan shi, sake rufe idanunsa ya yi ya ce "Ki tafi please bana son damuwa zan neme ki." Marairaicewa ta yi kamar za ta yi kuka ta durƙusa a gaban shi ta ɗaura hannayenta a kan cinyarsa tana shafawa ta ce "my love, are you okay?" Girgiza mata kai kawai ya yi dan ji ya yi gabaɗaya ba zai iya motsa ko fa yatsarsa ba ce, wani irin fitinannan abu yake ji na fusgar shi zuciyarsa na ba shi umarni amma kwakwalwarsa ta hana hakan, da ƙyar ya iya faɗin " A'o'uzu billahi minan shaɗani rajim! La'ilaha illa antas subhanaka inni kuntu minan zalimin." Sai da ya maimaita sau uku sannan ya ji kuzarinsa na ɗan dawowa, ya buɗe idanu ya ce "Ki fita na ce miki." Ganin ɗan ɓacin rai a kan fuskarsa yasa ta yi saurin miƙewa ta ce "My name is Ayush, ga kuma number wayata nan in ka gama yanke shawara ka kirani." Tana gama faɗin haka ta juya cikin jan hankali ta dinga taku tana kararraya har ta fita a office ɗin. Gabaɗaya Abdul ji ya yi ya kasa yin komai bacci ya rufe masa idanu, cikin wata iriyar kasala ya miƙe ya haɗa kan komai ya bar office ɗin. Yaran sa da mamaki suke kallon shi ganin yau ya tashi ba lokacin da ya saba tashi ba, sannan ko sallamar da yake musu bai yi ba sai kiran direbansa ya yi ya zo ya ɗauke shi... Suna isa bakin wani madaidaicin gida suka buga ƙofar, wani matashin saurayi ya zo ya buɗe musu suka shigo yana musu barka da zuwa. Har cikin palon gidan suka kaita sannan Ali ya ce "Madam mu za mu tafi akwai masu tsaron ki suna waje da kin shirya ki kira na zo na ɗauke ki." Murmushi ta yi ta ce "Ina yake to?" Ali ya bi wata zigaga ta mara masa baya sai ga su a cikin wani palon inda ta ga Baba da matarsa sai Zaiyan da ke zaune ya juya mu su baya, cike da tsananin mamaki ta ce... _*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_ [10/25, 4:05 Yamma] My Addatyna: ~A HAKA NAKE SON SHI~ Arewabooks.com: Saratalkasum1897 WhatsApp number: +966577675904 Shafi na (16) Cike da mamaki ta ce "Baba! Me kuma ya kawo ka nan?" Ta faɗa tana isowa gaban su ta durƙusa. Murmishi Baba ya yi ya ce "Labarin mai tsayi ne ƴar nan, ki zauna a gaisa tukun." Ya faɗa yana nuna mata kan kujera, ita kuma ta yi kim kamar ba za ta zauna ba sai kuma ta zauna tana. Murmushi ta yi ta leƙa Zaiyan ta ga yana ta naɗe hannayensa da ɗankwalinta da ta bar masa. Ajiyar zuciya ta sauke cikin nutsuwa ta ce "Baba ina yinin ku? Ya kwana biyu kuma? Na sha kiran wayarka ba a ɗauka hankalina ya tashi na ce da Yaya ya kaini unguwarku na gani ko wani abu ne ya faru da kai, sai ya ce na bari ba yanzu ba ashe dai kuna nan abin ku." Gyara zama matar Baba ta yi ta ce "Yarinya ai rana ɗaya aka kawo mu da Zaiyan, na yi matuƙar farin ciki da ya kubuto daga hannun mutanen nan." Lumshe idanu ta yi ta kuma buɗe su a kan shi, ganin bai ma san ta zo ba sai ta tashi ta zagayo gaban shi ta tsugunna, hannu ta miƙa ta kama ɗankwalin tana murmushi ta ce "Zain!" Turo baki ya yi bai ɗago ya kalle ta ba, naɗe hannun da yake dai ya dakatar, mamaki ne ya kama ta ganin yaƙi ɗagowa bare ya san ita ce. Baba ya ce "Wannan fa wai fushi ne ya yi da mu, yana tambayar ina kike mun ce za ki zo shi ne ya ga ba ki zo ba ya juya mana baya." Shuru ta yi tana kallon lips ɗinsa da yake saɓa su yana ɗan ciza su kamar mai jin zafi, ƙura mana idanu ta yi inda ta soma ganin baiwar kyan da Allah ya masa. Zararan gashin idanunsa da ya sa musu wani farin abu kamar gari ta ƙura wa idanu, murmushin da yake dimple ɗinsa na bayyana ta lumshe idanu cikin wani kalar yanayi mai wuyar fassarawa a baki ta buɗe su a kan shi ta ga dai bai kula ta ba, hannu ta kuma miƙawa ta ɗan shafo fuskarsa da yi fayau.. Da sauri ya ɗago idanunsa ya faɗa cikin nata, kallan kallo suke ita da shi har ba ta san ba lokacin da Baba da Inna suka ba su waje, har sai ta ta janye nata idanun sannan ta ankara ba sa palon. Shi kuma saƙare ya yi yana kallon ta sai da ta janye idanunta sannan ya yi firgigit ya taɓa fuskarsa. Sake kallon ta ya yi ya ga tana masa murmushi sai ya shagwaɓe fuska yana tattaba 'yan yatsun hannunsa cikin murya irin ta taɓararrun yara ya ce "Umm Antyyy!" Ya ja sunan yana mai juya fararen idanunsa a kanta. Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Na'am Zain." Matsowa ya yi kusa da ita ya kama hannunta ɗaya yana faɗin "To ina abincin?" Ya faɗa yana langaɓar da kai.. Murmushi ta yi ta buɗe ledar da ta kawo ta fito da chocolate babba ta miƙa masa tare da cewa "To ga shi na kawo ma sai ka ci ko." Saurin amshewa ya yi ya sa a baki yana gatsawa bai buɗe ba, hannu ta kai bakinsa ta ce "Ha." Ta buɗe nata bakin, ganin haka yasa shi ma ya yi yadda ta yi ta janyo chocolate ɗin duk ya jiƙa ta da yawun bakinsa, hannu ta sa ta buɗe masa ta zare ta a gidan ta miƙa masa ya amsa ya sa baki... Kallon shi take zuciyarta na ƙara tausaya masa matuƙa, murmushi ta yi tana shirin ɗauke kai ta ji abu a kusan bakinta, da sauri ta kawar da kanta, shi kuwa ganin haka sai ya ɓata fuska ya miƙe tsaye ya ce "Ni ba sarki ba ne Anty sai ki hana na ba ki kema ki ci?" Ya tambaye ta yana aiko mata da sakon harara. Ɗan murmushi ta yi ta miƙe tsaye ta ce "E kai Sarki ne mana Zain, kar ka yi fushi zo ka bani zan ci." Miƙe baki ya yi yana faɗin "Na ma fasa ba ki zan cinye abuna." Ya faɗa yana juyowa ya nuna mata tare da kai wa bakinsa. Saurin amshe wa ta yi tana dariya ta ce "Allah sai ka bani marowaci, ni fa na kawo ma kò ba ka sani ba?" Shi ma da sauri ya miƙa hannu dan ya amsa amma ta yi saurin jefa wa a baki tana dariya, ganin tana masa dariya shi ma sai ya shiga yin dariya yana matsowa kusa da ita, da sauri ta matsa ai kuwa suka dinga zagaya bayan kujeru suna ta dariya. Sai da ta gaji sannan ta soma ƙoƙarin tsayawa shi kuma ya yi saurin ɗamko hannunta yana dariya ya ce "Yawwa na kamo ki." Murmushi ta yi ta zauna a kan kujera hannunta a cikin nasa ya zauna. Haka ya dinga mata shirme tana biye masa, har kayan da ta kawo masa ta kira Baba ya kai shi ɗaki ya canza masa suka fito. Wani irin kyau ta ga ya mata shi kuma sai wani shafa kayan yake yana faɗin "Anty kin ga wannan kayan nawa kuwa?" Ƴar dariya ta yi ta janyo wayarta ta ce "To zo mu yi selfi." Ɓata fuska ya yi yana maƙale kafaɗa Baba ya ce "Haba Zaiyan ita fa ta kawo maka kayan ka je ta ma photo sai ka yi kyau." Jin abin da Baba ya faɗa sai ya isa gareta ya zauna a daf ta ita yana waro idanunsa ganin shi a cikin camera ya ce "Anty wannan abokina ne ya zo?" E kawai ta ce masa dan kar ta tsaya yi masa bayani ya ce ya fasa yi, saita su ta yi ta ɗauka, ganin haka yasa ya kwanto da kanshi kan kafaɗarta yana murmishin da ya baiyanar da haƙoransa ta ɗauke su, abu kamar wasa in ta ɗauka sai ya ce mata. "Yawwa abokina ashe dai ka gane ni." Sai ya nuna photonshi da ta ɗauka. Ita kuwa murmushi kawai take zubawa,yana surutun bai san ba lokacin da ta ɗauke shi video yana turo baki tare da langaɓar da kai gefe yana faɗin shi ma yunwa yake ji, ita kuma tana masa dariya tana cewa ba wata yunwar da yake ji sai ya ɓata fuska kamar zai mata kuka ya ruƙo hannunta ya ce to ta kaishi faɗarsa, dariya kawai take ta ce ma za ta kaishi da sun gama. Sai ya yi dariya ya ce mata "Anty kema kina Uwaye?" E take ce masa har ta gaji ta daina ba shi amsa. Sai kusan Magariba ta shirya tafiya gida ta kira Ali ta ce ya zo ya ɗauke ya, ai kuwa tana tashi ya ce sai ya bi ta aka kama fama da shi har da kuka ya ƙulla kamar wani ƙaramin yaro yana riƙe hijabinta, ji ta yi kamar ta tafi da shi amma ba yadda ta iya tun da magani ake masa, sai da ta masa wayo ta ba shi ledar kayan ta ce ya kai daki ya dawo su tafi ya ce to, yana shiga Baba ya shiga ya rufo su ta yi saurin fita tana goge hawayen suke kwaranya bisa kumatunta, da ƙyar ta iya tsayar da kuka dan kar su tambaye ta ba'asin kukan ta iso bakin motar ta shiga suka tafi gida... *NIGER* Sarauniya Bilkisu tun da Yarima Suhal ya ce ba zai yarda a aura masa Fauziya ba ta kasa zaune ta kasa tsaye, ko da ta dawo ba ta cewa Fauziya komai ba duk da tambayar ta da take yi, sai bayan kwana biyu Fauziya ta kuma samun Sarauniya Bilkisu a palo tana kuka ta zauna tare da dubar ta ta ce "Anty wai ba za ki faɗa min abin da kuka tattauna da Maimartaba ya kira ku ba?" Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon Ƙanwarta ta cikin jin haushin Yarima Suhal ta muskuta, kallon Hadimarta ta yi da ke matsa mata ƙafa ta mata alama da ta basu waje, da sauri ta miƙa ta fita fuskarta ɗauke da damuwa.. "Fauziya ki yi shuru mana, kin san dai bana son ganin kukanki." Saurin tarar numfashinta ta yi ta ce "To in ba kya son ganin kukana ki faɗa min maganar da aka yi mana." Nisawa ta yi tana kallon ta, tabbas sai yau ta ƙara tabbatarwa Fauziya na mutuwar son Yarima, a sanyaye ta ce "Ki yi haƙuri Yarima ya ce ba zai aure ki ba wai ba ki masa a matar aure, shi ya sa nake ce miki ki dinga nuna ke salihar mace ce dan ki samu shiga a wajan shi amma firr ke kin kafe ba za ki nuna hakan ba." Ta faɗa tana jan tsaki. Wani irin zabura ta yi cikin tashin hankali ta dafe ƙirjinta da ke mata wani irin zafin azaba, tuni ta gigice ta kalli Sarauniya Bilkisu ta ce "Na shiga uku! Yanzu Anty ni ce Yarima zai ce wai ban masa ba? Me na rasa na 'ya mace? Duk abin da wani ɗa namiji zai kalle a jikin mace na jan hankali wanne ne bani da shi Anty? "Ta faɗa tare da fashewa da kuka mai tsuma zuciya. A fusace Sarauniya Bilkisu ta ce "Ke kuwa kika rasa tun da ba ki iya takunki ba, a ko'ina sai kin nuna halinki da nuna ke mai izza ce, taya kike tunanin Yarima zai so ki a haka? Yarima ba ya son a wulaƙanta ɗan'adam a gaban shi, baya son mace mai rawar kai, ba ya son rashin kunya, ba ya son duk wanda ba ya ƙaunar mahaifiyarsa da mahaifinsa, ba ya son duk wanda yake cin mutumcin na ƙasa da shi. To ki faɗa min ke a cikin halin nan wanne ne ba kya yi?" Ta faɗa tana ɗaukan apple da ke gaban ta ta kai baki ta gutsira tana jin wani irin ɓakin cikin soyayyar da Ƙanwarta ke nuna wa ɗan kishiyarta, in ban da ma ita shashasha ce taya ma har za ta faɗa soyayya da jinin kishiyar ta? Matar da tafi tsana a duniya take som ganin ranar barin ta masarauta gabaɗaya, amma ga shi Fauziya ta maƙalewa Yarima mai mugun taurin kan tsiya da nuna shi jinin sarauta ne. Allah Allah take kar labarin rashin ɗa'ar da Fauziya ke aikatawa kar ya je kunnen Yarima Suhal.. Shuru Fauziya ta yi ba ta ce komai ba ta miƙe tsaye ta ɗauki wayarta, sai da ta je bakin ƙofa ta ce "Zan je wajan malamina Wallahi ko da tsiya-tsiya Yarima sai ya zama mallakina ni kaɗai, kuma in maganar na masa ladabi ne zan ƙoƙarta yin hakan dan ya ga na canza. Amma Wallahi ko yana so ko baya so sai ya aureni dan ni kaɗai Uwarsa Fulani haifawa ba dan kowacce mace ba." Tana gama faɗin haka ta buɗe ƙofar ta fita tare da bugo ƙofar ji kake garamm! Kwafa Sarauniya Bilkisu ta yi ta ringesa ta ce "Yarinya kenan, ni na fiki sanin ta kan duniya zan nuna miki abin da babba ya hango, yaro ko ya hau kan dutse ba zai hango ba! Da kike maganar Wallahi sai na yi abin da ya fi na baya." Sosai Yarima Suhal ya kasa sukoni saboda Papa ya ce dole sai ya auri Fauziya, sai da ya samu Mamma ya dinga mata kuka yana faɗin "Wallahi Mamma in kika bari aka aura min Fauziya sai na bar muku masarautar nan gabaɗaya kowa ma ya huta, saboda Allah ina ni ina wata Fauziya yarinyar da na sha ganin ta a hotel ita da samarin ta. Ni ina son na auri mace mai hankali da nutsuwa wadda za ta kula min da ke ta so ki kamar yadda take son mahaifiyarta, ita kuwa wannan ballagazar ko gaishe da ke ba ta yi bare ma ta girmama ki." Hankalin Mamma ya tashi ganin hawayen ɗan nata, Ƙanwarsa Ikilima da ke kusa da Mamma ta ja tsaki tana cewa "Wallahi Yaya kar ka yarda a aura maka wannan guzumar matar, duk ai makircin Mama Bilkisu ne ta nace wai sai Papa ya ba ka umarni ka auri Ƙanwarta. Haka fa kwanaki ta shigo har nan ta yi wa Mamma rashin kunya ni kuma na ɗauke ta da mari, shi ne muka dinga faɗa har magana ta je wajan Papa, abin mamaki na ga an ɗaure mata hannu da kai wai na fitar mata sa jini na kuma karya mata hannu. Shi ne Mama Bilkisu ta dinga cewa wai dan ita ba gidan ba ce sai a kashe mata ƙanwa? Ta dinga kukan ƙarya Papa ya min faɗa a gaban su kuma ya ce daga yau ko harara na mata shi zai hukunta ni ya ķuma hana na masa bayanin abin da ya faru har aka yi faɗan." Ta ƙarashe maganar tana goge hawayen takaici kamar yanzu ne aka mata faɗan.. A zabure Yarima ya miƙe cikin wani kalar yanayi har jijiyoyin kansa sun tashi, dama ga shi mafaɗaci tuni zuciya shi ta dinga tafasa ya kalli Ikilima ya ce "Auta! Me ya sa ba ki sanar da ni a waya ba?" Sake goge hawaye ta yi ta ce "To Yaya ta ina zan sanar da kai? Lokacin ɓakin ciki ya hanani yin magana ko École ban je ba washegari." Kamo hannunsa Mamma ta yi ta zaunar, ganin yadda yake huci sai ta kwanto da shi kan cinyarta ta shiga shafa kansa a hankali, wani irin abu ne ya zo ya tsaye mata a saitin ma'adanar sirrinsa, yana son yin magana amma ya kasa. Sai sauke ajiyar zuciya yake, sai can Mamma ta ɗago da shi ta masa alama da ya kwantar da hankalinsa za ta yi wa Maimartaba magana. Rumgume ta ya yi ya ce "Merci beaucoup ma chérie." Kallon Ikilima ta yi ta mata nuni da ta ɗauko mata takarda, da sauri ta tashi ta shiga ɗakin Mamma ta ɗauko mata , amsa ta yi ta soma rubutu. Sai da tafi minti ashirin tana rubutun sannan ta gama ta lumke ta aje, Yarima ya yi murmushi ya tashi ya ce zai je ya ɗan watsa ruwa.. Cikin ɗakinsa ya shiga wanda faɗar tsaruwar sa ma ɓata baki ne, kayan jikinsa ya cire ya ɗaura towel har ya nufi banɗaki sai ya fasa ya koma ya zauna a kan makeken gadonsa. Computer ya janyo ya buɗe tare da saka code ta buɗe tare da buɗe data ai kuwa sakonni suka dinga rige-rigen shigowa. Murmushi ya yi ganin saƙon da yake son ya san dama sai ya tarar da shi, Instagram ya hau ya buɗe sakon wani account da aka sa *Princess A*, saƙonni ya gani sun fi goma ya bi ɗaya bayan ɗaya yana karantawa. "Assalam alaikum Suhal ya kake ya kwana biyu?" Murmushi ya yi ya ƙara yin ƙasa ya ga emoji ɗin kuka ya zaro idanu waje. "Suhal shi ne kaki kulani ko? Ba komai ni ma daga yau na daina kula ka tun da ka manta da Ƙanwarka." Dariya ya yi yana shafa kwantaccan sajansa ya ƙara duba ɗayan. "Da gaske ne ka yada ni ko Suhal? Har sace ni aka yi na samu na tsira da raina amma duk ba ka sani ba, yanzu haka ma Abie na ya rasu yau an yi kwana huɗu ina fatan lafiya ce ta ɓoye ka ba wani abu marar daɗi ba." Dafe kai ya yi cikin damuwa yana mai Allah wadai da halinsa na rashin kulata da ya yi, shi tun da ya aje Computer ma bai sake bi da kanta ba har ya je ya gama karatunsa a ƙasar Turkiyya ya dawo, lumshe idanu ɗinsa ya yi ya kuma buɗe ya janyo wayarsa.. Number ta ya ɗauka ya danna kira sai ya ji a kashe wayar take, fesar da numfashi mai zafi ya yi cikin tsananin son jin muryarta, sai ya ji wata irin kewar ta ta mamaye shi ya nisa tare da gyara zama ya soma rubuta mata saƙon ban haƙuri da uzirin da ya hana shi yi magana. Gaisuwa ya mata sannan ya ce mata number ta ba ta shiga in ta hau ta ba shi wadda zai same ta. Yana gama tura nlmata ya aje Computer ya shige banɗaki... NIGERIA Misalin ƙarfe 10:pm na dare tana zaune ta rafka tagumi hannu bibbiyu ta lula duniyar tunani hawaye na kwaranya kan kuncinta, ringing wayarta ne ya dawo da ita haiyacinta ta zabura ta sauke tagumin da ta yi ta ƙurawa wayar idanu, sabuwar number take gani na yawo kan screen ɗin wayarta ta shiga tunani waye yake kiran ta. Tana katsewa wani kiran na shigowa hakan yasa cikin jin tsoro ta ɗauki wayar hannu na rawa ta yin picking call ɗin, a hankali ta ce "Assalam alaikum." Daga cikin wayar aka amsa mata, "Wa alaikum salam! Baby ya kike ya daren?" Saƙare ta yi da wayar a kunne jin muryar mai magana, sai da ya sake magana sannan ta ce "Lafiya lau nake, Uncle Aruf ba ka rabuwa da canja number? Wallahi har naji tsoro naƙi ɗagawa da farko ashe ma kaine." Ta ƙarashe maganar tana sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi har sai da ya ji. Dariya ya yi jin yadda ta sauke ajiyar zuciya ya ce "Wallahi Baby kin cika tsoro." Turo baki gaba ta yi kamar tana gaban shi ta ce " to ai tsoro halak ne." Dariya ya yi ya ce "Baby gobe za muje company Abie na motoci tare da ke." Waro idanu ta yi cikin Shagwaɓarta ta ce "Ni dai gaskiya Uncle ku je kai da Yaya har da Salim, ka ga ni mace ce." Murmushi ya yi mata kawai ya mata sallama ganin taƙi ba shi damar da zai yi hira da ita mai tsayi ya kashe kiran. Tana zaune sai ta lalibo glass ɗinta a saka ta buɗe computer wadda rabon da ta buɗe tun ranar kwana huɗun Abie da rasuwa, saƙo ta gani ta Instagram hakan yasa ta hau. Cike da mamaki take kallon wanda ya turo saƙon hannu na rawa ta shiga ta soma karantawa. _"My princess am so sorry, Wallahi wata tafiya ce ta taso min na tafi ƙasar Turkiyya, na yi kewar ki sosai da sosai, kuma ban samu na sanar da ke ba tafiyar tawa ina mai ƙara ba ki haƙuri kin ji Ƙanwata. Ya kuma haƙurin rashin Abie? Sannu Allah ya jiƙan shi da rahama yasa kwanciya hutu ce a gare shi, sannan na kira number ki ba ta shiga ki turo min da number da zan same ki ina so na ji daddadar muryar ƙanwata. Miss you so much my princess."_ Wani kalar murmushi ta yi sai kuma ta ɓata fuska kamar tana gaban shi, ba ta ba shi amsa ba sai number kawai da ta tura masa. Kafin ta ɗauke hannu ta ga ya buɗe sai ta riƙe baki ta ce "Ɗan nema ni za ka raina wa hankali?." Kiran ne ya shigo wayarta ta dauka ba ta ce komai ba, tana jiyo yadda yake sauke numfashi daga cikin wayar shi ma ya yi shuru, sai da ta gaji da riƙe wayar ta turo baki ta ce "Ni in mutum ba zai yi ba magana sai na kashe wayata." Dariya ya yi yana jin wani matsanancin farin ciki ya mamaye masa zuciya,kuncin da ya shiga na kwanaki ya sauka jin yadda zazzakar muryarta mai haɗe da shagwaɓa ta ƙarashe majiyarsa, lumshe idanu ya yi dan har ga Allah yana son mace mai shagwaɓa da nuna yarinta da surutu irin na yara, a nutsu ya ce "My princess ɗin yayanta." Ƙara kumbura baki ta yi ta gyara zama ta ce "Ni ai yanzu na goge ka daga layin yayuna ehhe." Ta faɗa tana murguda baki. Waro fararen idanunsa ya yi fuska cike da annori ya ce "Haba dai Ƙanwata sorry mana, ba fa ƙin kula ki na yi ba, da gaske bana ƙasar na yi tafiya ne." Ji ta yi ba za ta iya muso da shi ba ta ce "To ya gajiya ina Mamma da Ikilima?" "Suna nan lafiya lau shekaranjiya ma Auta ke cewa wai ina kike na ce kina nan." Harara ta aika wa wayar ta ce "Hmm wai har da cewa ina nan kamar ya kula da lamarina." Ta faɗa a shagwaɓe. Lumshe idanunsa ya yi yana jin wani yanayi na fisgar shi mai daɗi, a sanyaya ya ce "Princess kin cika neman rigima sai Shagwaɓa, wai ke ba ki san yanzu kin soma girma ba." Ya faɗa yana jin wata iriyar kasala na mamaye shi, iya sautin muryarta in ya ji saka shi yake a wani yanayin shauki na musamman.. Riƙe baki ta yi ta ce "Kai Yaya Suhal a rage mugun hali, yanzu ni ina na wani girma saboda Allah? Am 19years fa, ita ma ban cika ba sai nan da wata biyar. Ai har yanzu ni yarinya ce." Dariya ya yi yana mai jan bargo ya Lulluba sannan ya ce "E kuma fa kina da gaskiya my princess, har yanzu ba ki gama girma ba." Ya faɗa yana dariya. "To sai da safe ma tun da ba ka kawo min tsaraba daga inda ka je ba, wai wata ƙasa ka je?" Ta faɗa tana kwanciya. Da sauri ya ce "No my princess dakata please karki kashe, naje Turkiyya ne na ƙarasa karatuna. Kuma na samu sakamako mai kyau ko tayani murna." Ya ƙarashe maganar yana tashi zaune.. "Allah ni sai da safe bacci nake ji gobe akwai School, congratulations Allah ya taimaka." Amin ya ce mata ba dan ya so ba suka yi sallama ta kashe kiran ta kwanta... Washegari bayan ta dawo daga makaranta ta samu palonsu an yi ɓaki, rabawa ta yi ta zauna a kusa da Grandma ta ce "Uncle sannun ku da zuwa, ya gida? Ina Hafsy?" Ta faɗa tana murmushi.. Alhaji Mustapha ya murmusa yana kallon ta ya ce "My daughter ya aka yi na ga duk kin ƙara ɓaki? Ki yi haƙuri kin ji ki daina saka damuwa a ranki komai zai yi daidai, Hafsy ta ce a gaishe da ke za ta ma zo muku hutu ranar Juma'a." Ya faɗa cikin iya takunsa. Goge hawaye ta yi kanta a ƙasa ta ce "To Uncle in sha Allah zan rage damuwa, da zan fi kowa jin dadi in Hafsy ta zo mana hutu." Murmushi ya yi sannan ya dubi Abba da Daddy da Daddyn Aruf da Mommy da Grandma ya ce "Alhaji Sulaiman na zo ne akan wata magana wadda nake son a sauke nauyinta kar a bar ɗan'uwana cikin masifa." Saurin kallon shi Abba ya yi ya ce "To wannan wani irin nauyi ne haka?" Ƙara gyara zama ya yi ya ce "Ni da Jarmai da Alhaji Tanko ɗan ƙasar Niger mun zuba hannun jari a wani company, to bayan wata biyar kasuwancin ya yi albarka muka samu riba sosai ke Sadiya kin tuna lokacin da muka yi wani meeting a nan palon?" Ya faɗa yana kallon Mommy da ta yi tagumi. Gyaɗa kai ta yi ta ce "Tabbas na tuna kun yi meeting mai tsayi a ranar." Wani irin daɗi ya mamaye shi ya ce "To muna magana ne akan kasuwancin, mun sake zuba kuɗi har naira miliyan ɗari mu huɗu, ni miliyan goma Jarmai miliyan goma Alhaji Tanko miliyan goma, to sauran miliyan saba'in ɗin ta Alhaji Ibrahim ce, mun haɗa mun ba shi kuɗin ya kai da kuɗin wani company da ke nan Niger na atamfofi miliyan talatin ya ce zai kai musu. To bayan kwana biyu ne labarin ɓatan shi ya bazu a gari, ranar kamar na yi hauka hankalina a tashe na dinga gwada kiran wayarsa amma sai ace a rufe take, ga shi mutanen da suke bin mu bashi sun takura mana, ni kuma a lokacin ba ni da kuɗi a ƙasa dan duk na yo oda na kuma zuba hannun jari a kamfanoni har uku. Da ƙyar muka haɗa miliyan goma ni da su Jarmai muka tura musu tare da faɗa musu halin da ake ciki sai suka daina kiranmu. Yanzu kuma sun ga labarin mutuwarsa shi ne suka ce lalle fa mu biya kuɗin nan, to yanzu al'amura duk sun dagule min shi ya sa na zo a samu a ba da miliyan ashirin ɗin nan mu tura musu kayansu... A zabure Abdul ya ce "What?" Ɗaga masa hannu Abba ya yi ya dubi Alhaji Mustapha ya ce "Yanzu idan aka haɗa har nakun nawa kuɗin ya kama?" Alhaji ya goge zufar dake keto masa ganin yadda Abdul ke masa wani irin firgotaccan kallo, baza malum-malum ɗinsa ya yi ya gyara ta sannan ya ce "To kuɗin in aka gama za su zama miliyan sittin ne cif, sannan na sa a tambayi ma'aikatan shi ko akwai wanda yake binsa kuɗi a sauke masa nauyi har ma da waɗanda muke kasuwanci duk na ce musu in suna bin shi bashi su faɗa a biya masa kar ya kwanta da bashi a kabari." A fusace Salim ya juyo ya kafe su Alhaji Mustapha da wani irin kallo, huci yake saukewa yana hura hanci ya miƙe tsaye dan dama shi sam ya tsani taraiyar Abie da su Alhaji Mustapha, cikin ɓacin rai ya ce .... *🤓Magana ake ta biyan bashi mai ya hyaru.* _*Taku har kullum Maman Nusaiba ce*_ [6/20, 7:46 PM] Ummu Amjad: WhatsApp number: +966577675904 Shafi na (17) Cikin tsananin ɓacin rai haɗi da jin haushin Alhaji Mustapha ya ce "Gaskiya Abba ban yarda da maganar nan ba a yi bincike." Ya faɗa yana hura hanci, saboda duk abin da Alhaji Mustapha ya faɗa bai gamsu da shi ba ko ɗaya. Daddyn Aruf ya harare shi yana haɗe fuska ya "Wa ya ce ka sako wa mutane baki? Kenan so kake a bar ɗan'uwan mu da bashi yana cikin kwancinsa?" Sunkuyawa ya yi cikin tsananin fushi ya ɗauki wayoyinsa tare da bin hanyar fita, yana zuwa saitin su Alhaji ya aiko musu da harara sannan ya sa kai shige ɗakin Grandma yana aiyanawa a ransa tabbas sai ya bi diddigin wannan maganar dan gano gaskiya. Abba ya girgiza kai tare da gyara zama shi kan shi ya ji matukar mamakin bashin da ake bin Yayan nasa, saboda in zai yi abu sai ya rubuta ya aje ya kuma kira su ya faɗa musu ga abin da ya yi ko ba ya raye. Alhaji Mustapha yi dinga muzurai yana ƙifƙifta idanu so yake ya ji abin da Abba zai faɗa game da lamarin, Abba ya nisa yana jinjina lamarin a cikin zuciyarsa sannan ya ce "To shi kenan Alhaji in sha Allah za a tura ma kuɗin, kawo account ɗin da za a tura kuɗin, sannan kuma ina takardar shedar yadda komai ya wakana?. " Ya ƙarashe maganar yana kallon shi. Wani irin murmishi Alhaji Mustapha ya yi wanda shi kaɗai yasan na meye ya ɗaga wata ɓakar Jaka ya zaro takardu ya miƙa wa Abba, amsa ya yi ya karanta ya ga lalle rubutun ɗan'uwan sa ne ga kuma sa hannunsa nan ga na Alhaji Mustapha da su Jarmai nan. Daddy ya amsa shi ma ya duba ya ga komai a rubutu sannan ya miƙa wa Mommy ta aje ko dubawa ba ta yi ba. Abba ya bukaci Alhaji ya kawo akawun number ɗinsa a tura kuɗin. Takaici ne ya hana Abdul yin magana, yana zaune duk aka yi maganar komai amma ko ƙala bai ce ba sai binsu yake da idanu ɗaya bayan ɗaya. Alhaji Mustapha kuwa duk a ɗarare suke, sam shurun Abdul firgita shi yake dan yasan halin Abdul sarai in dai ya yi shuru to da abin da zai biyo baya, hakan ya sa ƙara saita nutsuwar shi kar Abdul ya rusa masa wannan gagarumin shirin da suka kwashe shekaru suna yi yau kuma ga shi zai cika. Lumshe idanu ya yi zuciyarshi na tafasa ji yake kamar ya sa kan bindiga ya harbe su Alhaji Mustapha ko zai samu salama, so yake ya ce wani abu amma kamar wanda aka manna masa gam a baki ya kasa cewa komai, ba wai kuma dan babu abin da zai faɗa, yana da tambayoyi masu tarin yawa da yake son yi musu amma sam ya kasa cewa komai sai sauke ajiyar zuciya yake. Kallon Abba ya yi da yake yi wa Mommy magana ƙasa-ƙasa, girgiza kai ya yi yana tattaro yawu da ƙyar ya samu ya haɗiye dan makoshinsa ya bushe, da sun san su waye Alhaji Mustapha da ba su yarda sun bayar da wannan kuɗin ba a take, amma rashin sani aka ce ya fi dare duhu! Tsam ya miƙe daga zaman da ya yi shi ma ya bi bayan Salim zuwa ɗakin Grandma ta bi shi da kallo tana baki. "Kai dai an yi ƙaton banza Abdullahi, yanzu saboda ɓakin hali ana maganar kai da wannan mai ƙirar Yarbawan za ku shige ɗaki kamar wasu mata? To ni ba ƴar banza ba ce da zan tsaya ina faɗa akan ku sai warin balaga kuke, gabaɗaya kun raina mutane ba wanda ya isa ya saka ku abu in ba kun so ba kun zama manyan kanku da kanku kenan?" Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyar Alhaji Mustapha ganin mutanen da suka son ɓata nasa shiri sun bar palon, juyowa ya yi suka kallo juna shi da Jarmai a sace suka saki murmushi, saurin gyara zama ya yi yana wani kamewa ya dubi Grandma ya ce "Inna ai ki rabu da su kawai, kin san yaran nan namu 'yan zamani ne musamman in suka kai mawar aure sai an bi su a hankali sai a zauna lafiya." Ya faɗa yana murmishi. Riƙe baki Grandma ta yi ba ta ce komai ba, Abba ya kuma cewa Alhaji Mustapha ya kawo akawun number ɗinsa. Jiki na rawa Alhaji Mustapha ya ji maganar kuɗi ya janyo wayarsa ya miƙa wa Abba ya ce "Ga sunan akawun ɗin nawa nan sai ka ɗauka." Jinjina kai Abba ya yi ya ɗauka ya miƙa masa wayar, miƙa wa Mommy ya yi ya ce "Matar Yaya ke kika san code ɗin account ɗin ki tura masa adadin kuɗin su." Mommy ta amsa ba tare da ta ce komai ba ta daddana wayarta cikin abin da bai fi minti biyar ba Alhaji Mustapha ya ji ƙarar shigowar su, saurin duba wayar ya yi ya ga alert na miliyan hamsin cif. Wani irin daɗi ne ya mamaye zuciyarsa kamar ya kurma ihun daɗi ganin komai ya tafi daidai, godiya ya musu suka tashi za su tafi ya jadadda wa Abir Hafsat za ta zo mata hutu. Tana murmushi ta ɗaga masa hannu kawai ta matso kusa da Mommy su kuma suka fita har su Abba zuwa harabar gidan.. Kiran Sallar La'asar ne ya farkar da Abdul daga baccin ɓakin cikin da ya yi, buɗe idanuwansa ya yi a hankali ya sauke su a kan Grandma da ke zauna a kan darduma tana yin lazumi, miƙa ya ƙara yi yana jin jikinsa na masa wani irin mugun ciwo ga baccin bai isheshi ba sai hamma yake yi. Hannu ya kai cikin sumar kansa wadda ta ɗan hargitse ya yamutsa ta yana jin kansa ya masa mugun nauyi, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya yaye bargon da ya lullube jiki da shi ya zuro ƙafafuwansa ya zauna a bakin gadon yana kallon Grandma. Tana juyowa ta ga mutum a bayan ta ya tsura mata idanu ta riƙe baki cike da takaici ta ce "Amma kai ko dai Abdullahi an yi futsararren yaro, yanzu ba na hana ka dinga haye min gado ba? To tashi maza sauka ka bar min ɗaki ka koma na uwarka Sa'ade in kuma da kuɗinka a ciki lokacin da za a sayi gadon sai ka faɗa naji dan na biyaka kayan ka." Ta faɗa tana kai masa duka da tasbahar hannunta. Ko ci kanki bai ce mata ba har ta yi faɗan ta ta gaji, lumshe idanu ya yi yana jin sa ba yadda ya saba jin kansa ba, a hankali ya miƙe ya shige banɗakin Grandma duk da faɗa da zagin da take masa kar ya shigar mata ya share ya shiga, bai jima ba ya fito inda ya ga Grandma ta bar ɗakin. A palo ya sami Mommy ta yi tsaye tana danna waya, a nutse ya iso inda take ya tsaya yana kallon yadda take saurin duba contact har ta zo kan tashi ta danna masa kira, hannu ya sa ya zare wayar daga hannunta ta yi saurin juyowa sai ta ga shi ne. Ganin yanayin ta ya sa Abdul saurin kamo hannayenta ya shiga tambayar ta. "Mom me ya faru?" Ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Abdul, Abir ba lafiya yanzu haka jikinta ya yi mugun zafi, shi ne nake son kiran ka ashe ma kana nan." A ruɗe yake kallon Mom wanda in ka kalle shi ba za ka ce ya shiga damuwa ba game da maganar, amma tashin hankalin da ya ziyarce shi har wani dishi-dishi yake gani hakan yasa ya lumshe idanuwansa zuciyarsa na bugawa da sauri-sauri, buɗe idanu ya yi har Mommy ta cire ran zai ce wani abu ya ja numfashi sannan ya ce "Mom bari na dawo daga Masallaci zan kira Hashim ya turo a duba ta." Ya faɗa yana sakin hannun Mom. To kawai Mom ta ce ta nufi ɗakin Abir cike da damuwa, a ƙudundine ta same ta cikin bargo sai ƙyarma jikinta yake, ta yi hanzari isa bakin gadon ta yaye bargon. Waro idanu ta yi ganin yadda numfashinta ke fita da sauri-sauri ta miƙe ta fita zuwa kitchen, ruwa mai sanyi ta zubo a roba ta ɗauko ɗan ƙaramin towel ta dawo ɗakin. Sakawa ta yi a ciki ta matse ta ɗaura mata a goshi tana ɗan dannawa kaɗan-kaɗan, ta dinga ɗauko ruwan mai sanyi sosai tana goge mata fuska har zuwa ƙirjinta. Haka ta dinga yi tana yi tana kallon lokaci.. Da ƙyar ya nutsu ya yi Sallah gabaɗaya hankalinsa na can wajan ta har ya ƙagara a gama Sallar, bayan an salamce ya yi addu'oi sannan ya fito yana sanya hannu a aljihunsa ya fito da wayarsa IPhone sabuwa dal, number Doctor Hashim ya lalibo ya danna mata kira ringing ɗaya ya ɗauka tare da yi masa Allah ya amsa suka gaisa. "Aboki yaya dai? Fatan dai lafiya?" Sai da ya buɗe mota ya shiga ya mata key tukun ya magantu, "Hashim please ka turo a duba min Baby zazzabi ya rufe ta." Ya faɗa yana jin kamar ya sa kuka saboda sanin irin zazzabin da take wanda in ya kwantar da ita kamar ba za ta rayu ba.. "Subhanallahi! To shi kenan zan tura a duba ta yanzu." OK kawai ya ce ya kashe kiran ya ƙaraso gida, cikin sanyin jiki ya buɗe motar ya fito ya shige ciki. Daret ɗakinta inda ya samu Mom ta gama shafe mata jiki tana lullube ta, ƙarasowa ya yi ya zauna a bakin gadon Mommy ta dube shi ta ce "Yawwa zo zauna ni zan je na yi Sallah kafin likitan ya zo." Jinjina mata kai ya yi ta fita, buɗe bargon ya yi ya ƙura mata idanu, sosai ta ƙara haske ta yi wata irin rama kamar ta yi wata a kwance, hannunsa ya ɗaura a gefen wuyanta ya ji har yanzu akwai zafi sosai, ji yake kamar ya mayar da cutar jikinsa saboda tsananin tausaya mata da yake. Wani irin dogon numfashi ya sauke ya shafo cute beauty face ɗin ta, ɗan ƙaramin bakinta da yake sheƙi ya zuba wa idanu yana jin wani lakar yanayi, sake shafo kumatunta ya yi cikin daddadar muryarsa ya shiga tashin ta. "Baby open eyes." Ya faɗa cikin raɗa-raɗa tare da ɗago da ita ya jingina ta da jikin gadon. Turo baki ta yi ta ƙara lafewa cikin bargon tana jin wani mugun sanyi na shigar ta, a hankali ta soma buɗe idanuwanta tana yi yana saɓa baki gaf take da sakin kuka, sai da ta gama buɗe idanunta tarr a kan shi ta dinga kallon shi ba ko ƙiftawa. Iska ya hura mata ta yi saurin rufe idanu ta turo baki sai ga hawaye sun zubo, saurin matso da ita ya yi cikin tsananin kulawa ya sa hannu ya goge mata hawayen. Jin wani kalar azababben ciwo da ķanta yake ta saki kuka tana kallon shi, dama yasan za a rina wai an saci zanin mahaukaciya, a banza ma tana kuka ballantana yau kuma jiki ba lafiya sai ya yi murmushi ya buɗe mata hannu tare da cewa "Oya come here." Saurin faɗawa ta yi jikinsa tana ci gaba da kuka, ji ya yi kamar an raɓa masa wani abu mai mugun zafi ya lumshe idanuwansa yana sauke ajiyar zuciya, ƙara gyara mata kwanciya ya yi bai ce da ita komai ba yana jin yadda kukan ta ke hana shi sukoni. Suna a haka ya ji ƙaran wayarsa, hannu ɗaya ya sa a aljihunsa ya ciro wayar ya ga Doctor Hashim ne ke kira ya ɗauka tare da karawa a kunne, sanar da shi ya yi mai duba ta ta riga ta iso ya ce to ya ce mata ta shigo sannan ya kashe. Suna a haka sai ga Mommy ta shigo tare da Nurse ɗin da ta zo, tana ganin ta ta ƙara ƙanƙame shi tana ƙyarma ta ce "Y.. Ya.. Ya. Kar ka bari ta min allura please." Ta faɗa cikin rawar murya. Shafa kanta ya yi cikin sigar rarrashi ya ɗago da fuskarta ya share mata hawayen ya ce "My Baby ki tsaya a duba ki, ba ki so ki samu lafiya ne?" Ya faɗa yana zaunar da ita a gefen shi. Girgiza kai ta yi ta ma kasa maganar, Mommy ta girgiza kai ta ce "Raguwa kawai, ke kullum in za a miki allura sai ki rikice kamar kin ga wani mugun abu." Tana gama faɗin haka ta fita ta bar musu ɗakin. Nurse ta ƙaraso ta soma duba ta, bayan ta gama ta ɗauko allura tana murmushi ta ce "Sister gyara a miki allura." Saurin ja da baya ta yi ta koma bayan Abdul shi kuma ganin haka yasa ya janyo ta tare matse ta aka tsira mata allura, ai kuwa ta kwalla ƙara tana ƙoƙarin kwace jikinta ya ƙara matse ta yana faɗin "Please tsaya mana kar ki yi mutsi a miki a inda ba daidai ba." Sai da aka mata biyu sannan ta rubuta mata maganguna ta ce "Ranke ya daɗe a sayo mata waɗannan magungunan." Ta miƙa masa paper da ta rubuta maganin ta musu sallama ta tafi.. Zuba mata idanu ya yi ganin yadda ta ɓata masa gaban riga da majina da yawu, girgiza kai ya yi ya ɗago ta ya kama hannun da aka mata allurar ya soma shafa mata wanjan yana faɗin "Sannu my baby." Harara ta aika masa lokaci ɗaya ta tashi daga jikinsa tana kumbura baki, haushin sa ya cika ta sai harara take masa kamar shi ne ya mata allurar, tsakiyar gadon ta isa ta kwanta tana turo baki ta ce "Ni ka bani ruwa na sha." Ta faɗa tana kuka. Dariya ta so ba shi amma da yake shi bai cika yin dariya ba sai kawai ya yi murmushi ya tashi ya kawo mata ruwan, sai da ta banka masa harara kana ta amsa ta dinga sha har da lumshe idanu. Ganin za ta sha ya mata illa ya karbe yana faɗin "Ya isa haka ruwan bari Mommy ta kawo miki ko da tea ne ki sha." Kawar da kai ta yi tana hura hanci dan ita har ga Allah ba ta so ya hana ta shan ruwan ba, Mommy ta kawo mata farfesu shi kuma ya matsa Mommy ta zauna ya ce "Mom zan fita ina so zan koma office akwai wani kes da aka kira ni na wasu mutane." Murmushi Mommy ta yi ta ce "To Allah ya bada nasara Ubangiji ya tsare gaban ka da bayan ka." Cikin jin daɗin addu'ar ya ce "Amin My Mom." Ya sa kai zai bar ɗakin sai kuma ya juyo ya ce "Baby me kike so na dawo miki da shi." "Ni ai fushi nake ma da kai." Ta faɗa tana amsar tea ɗin da Mommy ke miƙa mata. "Kin ga ki aje fushin nan in na dawo sai mu yi magana." "To ka sayo min ice cream. " OK ya ce mata sannan ya tafi.. Alhaji da su Jarmai bayan sun samu wannan makudan kuɗin suka shirya wani ɗan ƙwarya-ƙwaryar party a gidan gonar su shi da tawagar su, sosai suka yi shagali suka ya sa aka ɗauko yan mata uku daga cikin wanda suka ɗauko.. Yan matan da ba za su wuce shekaru 17 ba aka kawo gaban su aka aje musu su, su kuma suna ta kuka Alhaji ya miƙe yana bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya har ya zo kan wata ɓaka yar duma-duma, wani irin lashe lips ya yi yana mata kallon ƙurulla ya kai hannu ya taɓo ƙirjinta yana murmishi ya ce "Sweet girl ta so ki zo nan." Ya faɗa yana nuna mata inda yake tsaye. Jikinta na rawa ta miƙe sai kuka take ta iso gaban shi ta durƙusa ta ce "Don Allah kar ka kasheni Alhaji, duk abin da kake so ka yi da ni amma kar ka kashe ni." Ta ƙarashe maganar tana rufe bakinta gudun sautin kukan ta ya fito.. Wani irin murmishi Alhaji ya yi yana kissima abubuwa kala-kala a zuciyarsa, ɗago da ita ya yi ya rungume ta yana shafa bayanta cikin iya bariki ya ce "In dai na ji yadda nake so za ki zama ajiyata ba zan kashe ki ba." Jin abin da ya ce ta goge hawaye ta ce "Na gode." Tana kuka marar sauti jikinta na rawa jin yadda Alhaji yake yawo da hannunsa a cikin ƙirjinta.. Dariya Jarmai ya yi ya miƙe shi ma ya zabi ɗaya shi ma Alhaji Mustapha ya ɗauki ɗaya suka shige wani ɗaki.. Alhaji ya kamo hannun yarinyar ya bi wani lungu da ita sai ga su a cikin ɗaki ƙarami, ɗakin gado ɗaya ne a ciki mai mugun kyau har da drower a ciki, kwantar da ita ya yi ya shiga cire mata kayan jikinta yana wani lashe baki. Kuka take marar sauti ganin yau ita ce za a keta wa mutumci wanda tun da ta yi wayo take tattalin shi kar ya zube, sai ga shi yau Alhaji zai raba ta da shi. Wani kalar ƙara ta saki na wahala jin gabaɗaya ya danne ta yana mata kiss a duk inda ya ci ķaro na jikinta, shi kuwa Alhaji har wani lumshe yake yana faɗin "Yarinya za aje da ke." Ihu ta dinga yi na azaba tana jin tamkar ba a duniya take ba, wani ƙara da ta kwalla har sai da jijiyar kanta ta fito daga nan ba ta sake motsa ko fa yatsar hannunta ba.. Farkawa ta yi kawai ta ganta an mata wanka an lullube ta da bargo, idanunta da suka yi luhu-luhu ta rufe ta sake bude su hawaye na zirya, rubutu ta gani a cikin ta ta soma dubawa cike da tsoro. Kasa karantawa ta yi dan ba ta gane me aka rubuta ba sai ta fashe da kuka tana faɗin "Waiyo Allah ka ceceni daga cikin wannan mugun gidan, Waiyo Mamana ko a wani hali kike ciki?" Miƙewa ta yi a hankali tana tsoron taka ƙafarta ta lallaɓa ta miƙe tsaye tana jin wani irin zafi ya mamaye mata ko'ina na jikinta, jikinta ta duba ta ga babu kaya ta hangi madubi a jikin drower ta lallaɓa tana ɗigishi ta isa ta tsaya ta soma karanta rubutun da take da tabbacin Alhaji ne ya mata shi. _"Sweet girl gaskiya kin haɗu, ki zauna a wannan ɗakin zan sa ake miki duk abin da kike so, da zarar na zo gidan nan to ke ce abincin da zan fara karyawa."_ Ƙara ta kwalla tana nanata kalmar abinci, sai da ta gaji da tsayuwa sannan ta ga wata ƙofa ta nufi wajan, tana zuwa sai ta ga ƙofar ta buɗe sai ganin ta ta yi a cikin toilet mai mugun kyau kwamin wankan ta ma abin kallo ne,dogon numfashi ta ja ta kunna ruwa mai zafi ta cika kwamin ta shiga ta zauna. Ji take ina ma ace mutuwar ta ta gani da wannan ɓakar ranar da ta riska.. Kwanan ta shida tana fama da zazzabi kafin ta samu sauƙi, duk da a kwance take amma kullum duk dare sai ta kira Baba a waya tana tambayar shi ina Zaiyan ya jikin nashi? Shi kuma Baba zai ce mata lafiya lau yake, kuma yana samun sauƙi game da larurar tashi, hakan na faranta mata rai in ta ji ya faɗa mata haka.. Yau ma kamar kullum misalin karfe 9:00pm na dare, zaune take a gaban mirror tana tsane kanta da ɗan ƙaramin towel tana kallon kanta ta cikin madubi, masharci ta janyo ta jona ta kunna ta shiga taje kan cikin nutsuwa. Bayan ta gama ta ɗauko wani cream fari mai sanyin daɗin ƙamshin amma ƙamshin ba sosai ba ta shafe ko'ina na jikinta da shi, a nutse ta tashi tana jin cikinta na mata kukan yunwa ta shafa cikin da yake a lafa kamar babu yan hanji a cikin. Lumshe idanu ta yi tana jin kamar ta ci abinci babu, saurin buɗe idanunta ta yi ta isa ta buɗe drower ta , kayan baccin ta masu mugun kyau ne jere kala-kala ta miƙa hannu ta janyo wasu riga da wando masu sulɓi haɗi da hula kalar kayan, kayan ta ɗaga ta ga ba su mata ba ta mayar ta shiga dubawa saboda ruwan ido irin nata.. Sai da ta gaji da tsayuwa har idanunta sun cika taf da hawaye tana kumbura baki kamar wani ya mata laifi ta janyo wasu pink ta jefa su kan gado. Sai da ta zauna tana kallon kayan dan ita sam duk cikin kayan ta ji ba wanda ya mata ta saka a jikinta, haka dai ta haƙura ta cire towel ɗin jikinta ta saka kayan ta zauna a bakin gado, so take ta fita ta ci abinci amma saboda lalaci irin nata ta narke a gado tana lumshe idanu ƙarshe ma gadon ta kwanta.. Sai da ta ji yunwa na neman mata illa ta janyo wayarta ta nemo number Mommy ta kira ta, har ta katse ba ta ɗauka ba ta kuma kira a karo na biyu tukun ta ɗauka. A shagwaɓe ta ce "Mom ki ce Laraba ta kawo min abinci yunwa nake ji." Mommy dake shirin shiga ɗaki ta dakata da shiga ɗakin, kwafa Mommy ta yi ta ce "Allah ya shirya ki kawai zan ce, yanzu rabon da ki ci abinci tun da safe kin shige daki kin rufe kamar wata baƙuwar boka." Ta faɗa tana dawowa palo ta kira Laraba. Tana isowa ta ce "Laraba sauran abincin nan da na ce ki ɗauke shi ɗazu, to ki fiddo ki dumama wa Mamana wai yunwa take ji." Sosa kai Laraba ta yi tana mutsitsike idanu saboda baccin da ya mamaye ta, sai da ta ƙara sosa kai sannan ta ce "To Mommy bari na dumama mata." Ta faɗa tana wucewa. Jin abin da Mommy ta faɗa Abir ta gyara kwanciya ta ce "Mom ta yi min shayi ta haɗo da madara mai sanyi a cikin freeze da na ce ta saka a ciki." "Hmmm ba za ki canja ba Mamana, ga shi zan sa ta kawo miki sai da safe." Ta faɗa tana kashe kiran. Tana nan kwance Laraba ta shigo ɗakin ɗauke da trey, a bakin gadon ta aje mata ta shaƙi iska ta ce "Alkur'anin Allah Anty Baby ɗakinki akwai daɗin zama." Ta lumshe idanu tana washe baki. Murmushi Abir ta yi ta sauko daga kan gadon ta zauna a kan capet ɗin dake malale a ƙasan ɗakin, buɗe abincin ta yi ta ga shinkafa ce dafa-duka, ɗagowa ta yi tana ɓata fuska ta kalli Laraba da itama ita ɗin take kallo ta ce "Laraba babu wani abincin sai wannan?" Ta faɗa tana nuna mata abincin da hannu. Ɗaga kai ta yi sama kamar mai tunani sai kuma ta kalli Abir ta ce "Anty Baby ai wannan mugun yayan naki ne ya cinye macaroni mai hegen daɗi da na yi ɗazu." Murmushi kawai ta yi dan ta san Labara da Abdul take, madarar ta zuba a cup sai da ta cika shi taf ta yi sanyi ƙarai, wani irin yawu ta haɗiya ta kai baki ta dinga sha tana lumshe idanu tana buɗe shi a hankali daɗi da gardin madarar na zagaya mata kwanya. Bayan ta gama sha ta ce ta ƙoshi da shayin ta mayar har abincin, riƙe baki Laraba ta yi ta ce "Kai Anty Baby to iya madara fa kika sha." Runtse idanu ta yi dan ba ta son Laraba ta addabe ta da surutu, a hankali ta ce "E na ƙoshi ɗauke sai da safe." To ta ce ta ɗauke kayan tana jin kamar kar ta fita daga ɗakin jin yadda wani irin sanyi ke ratsa ta duk da itama a nata ɗakin akwai AC .. Washegari ta shirya cikin black ɗin Abaya ɗaya daga cikin wadda Uncle Aruf ya kawo mata, jaka da takalmi ta ɗauko ta saka ta yi rolin da mayafin abayar tare da ɗaukan wayarta ta fito.. A zaune ta samu Abdul yana daddana waya ta tako cikin nutsuwarta tana murmushi ta iso gaban shi ta tsaya.. Tun daga kan kyakyawar ƙafarta ya soma kallon ta har zuwa kan fuskarta wadda take ƙyallin, duk da ita ba ma'abociyar kwalliya ba ce amma kwallin da ta saka ta yi ɗigo a tsakanin ƙirar ta ya ƙara mata wani irin kyau na musamman, hannu ya miƙa mata ta kama ya zaunar da ita a gefen shi har yanzu bai daina kallon ta ba, ji yake kamar ya cinye ta saboda tsananin ƙaunar da yake mata. In kuwa ya ga tana yi wa wani murmushi ji yake kamar ana hura masa wuta a cikin zuciyarsa. Hura masa iska ta yi ya yi saurin ɗauke idanunsa ta turo baki ta ce "Yaya wai canja halitta na yi ne da kake kallo na kamar ba ka sanni ba?" Murmushi ya yi ya ce " Baby Wallahi kin yi kyau sosai, sai ina haka ba sanarwa?" Ya faɗa yana kafe ta da dara-daran Idanuwansa masu ƙara masa ƙwarjini.. "Yaya zan je wajan su Baba ne." Ta faɗa tana cuno baki dan kar ma ya ce mata ba yau ba.. Kamar ya karanci me take tunani ya kamo hannayenta ya ce "Baby ba zan hana ki zuwa ba, amma bari na kira Ali ya kaiki." Murmushi ta yi cikin farinciki ta ce "Thank you." Bai kuma ce mata komai ba ya ɗauki waya ya kira Ali tare da sanar da shi ya zo ya kai ta ya amsa da to sannan ya kashe kiran.. Ba su fi minti biyar ba sai ga kiran shi ya shigo wayar Abdul ya sheda masa yana harabar gidan, kallon ta ya yi ya ga yadda take cikin farin ciki sai ya ji wani sanyi na ratsa shi ya ce "Baby ya zo." Miƙewa ta yi ta ce ya sanar da Mommy ta fita duk da ta faɗa mata da safe, shi kuwa ko uffan bai ce mata ba ya bi ta da kallo, yau kawai ji ya yi baya son ta je wajan su Baba, amma ba yadda ya iya idan ya ce zai hana ta zuwa to fa yau duk gidan nan sai kowa yasan halin da ake ciki... Tana fita sai da suka gaisa da Maigadi da sauran ma'aikatan sannan ta shiga suka tafi.. Suna zuwa Ali ya aje ta a ɗan naisa da gidan suka ƙarasa da ƙafa, ita dai mamaki take da an zo kusan gidan sai a aje ta ba za aje har ƙofar gidan ba sai su tsaya a baya. Sai da ya kaita har ƙofar palo sannan ya dawo ita kuma ta sa kai ciki bakinta ɗauke da Sallama.. Yana tsaye a tsakiyar palon ya ji muryarta, saurin juyowa ya yi yana kallon ta. Itama shi take kallo cikin wani kalar yanayi mai wuyar fassara, sosai ta yi missing ɗin shi har ba ta san lokacin da hawaye ya zubo mata ba, kafin ta motsa daga bakin ƙofar sai ji ta yi an rungume ta, kwalalo idanu waye ta yi cikin kiɗima zuciyarta na wani irin bugawa wanda tun da take ba ta taɓa jin wannan yanayi ba sai yau. Wani irin nauyi harshenta ya yi ta kasa furta maganar da take son faɗa, lumshe idanu ta yi cikin kasalalliyar murya ta ce..... Taku har kullum Maman Nusaiba ce. [10/17, 12:52 Safiya] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): Shafi na (18). Cikin kasalalliyar murya ta ce "Zainnn..!" Ta ja sunan jin ya sakar mata nauyinsa, tsoro da firgici suka kawo mata ziyara a tare. ƙin sakin ta ya yi yana fitar da wani irin numfashi, a kiɗime ta soma ƙoƙarin janye shi daga jikinta amma ta kasa. Jin abin na ƙaruwa ta ƙara shiga tashin hankali, ta daddage ta ɗago shi ta soma ƙoƙarin isa kan kujera dan ta zaunar da shi, amma ta kasa kasancewar Zaiyan ya mata nauyi. Da kyar ta iya jan kafa daya tana kiciniyar raba shi da jikinta sai suka zube a kasa warwas, lumshe idanu ta yi tana jin bugun zuciyarta ya ƙara tsananta, haka kawai ta ji kamar ana kiran sunan Zaiyan cikin majiyarta ta yi saurin buɗe idanu ta sauke shi à kan shi. A zabure ta tashi daga faɗuwar da suka yi sakamakon ganin Zaiyan na fitar da wani irin farin kumfa daga bakinsa, ta shiga jijjiga shi a ruɗe tana kiran sunanshi amma sai kakkafewa idanuwansa suka yi a lokacin, hannu ta ɗaura a ka ta tashi zaune ta soma neman su Baba. "Baba!" Ta faɗa da ƙarfi cikin rashin sanin madafa, sai ta fashe da kuka tana surutai irin na wanda ya fita daga haiyaci. "Waiyo Allah! Ka tashi don Allah Zain kar ka tafi ka barni, Baba kuna ina Wai? Inna! Ka tashi ka ji." Ganin ba sarki sai Allah ya sa ta miƙe ta nufi kitchen da sauri har tana haɗawa da gudu, ruwa ta ɗauko a cikin cup tana sharɓe majina ta ƙaraso inda yake. Ruwan ta shafa masa a fuska tana dan bubbuga kumatunsa amma shuru ko gizo bai yi ba, rausayar da kai ta yi tana son tuno wata dabarar da za ta mishi ko ya tashi. Ji ta yi ya damƙi hannunta ta yi saurin kallon shi cikin rawar murya ta ce "Z.. Za.. Zaiyan." Wani irin huci yake fitarwa yana ƙara damke mata hannu ita kuma ta zuba masa idanu tana zubar da hawayen tausayin shi, hannu ta sa ta tallafo kanshi ta ɗaura à kan cinyarta tana shafa kan shi shi kuma sai wani irin gurnani yake yana zabura kamar yaron da damina ta warta. Sun fi minti 20 da haka ta rasa yadda za ta yi da shi, ta kira su Baba ya fia sau a ƙirga amma shuru hakan yasa ta gane cewa ba sa ma gidan, can dabara ta faɗo mata ta janye shi daga kan cinya ta dauƙi cup ɗin da gudu ta koma kitchen ta ɗauko ruwa rabin cup ɗin. Zama ta yi ta dan nutsu ta soma karanto addu'o'i tana tofawa a cikin ruwan tana yi idanunta a kan shi yana ta zabura yana ƙanƙame jiki, bayan ta gama ta yi bismillah ta soma shafa masa ruwan addu'ar. Zafi sosai jikin nasa ya ɗauka duk inda ta shafa masa ruwan addu'ar sai ya ƙara zafi fiye da na da, hakan bai sa ta karaya ba ta ci gaba da shafe masa ruwan sauran da ya rage ta ɗago kansa ta soma zuba masa à kai tana cuɗa sumars wadda take baka siɗik. Karkarwa jikin ya ɗauka idanunsa na ƙaƙƙafewa wani baƙin abu na fita daga bakinsa, kuka take tana ƙara shafa kan nasa ji take kamar ta kurma ihun neman taimako amma to wa zai ma san ta yi ihun ? Gabadaya ta ma manta da ta kira ko da Abdul ne komai ya kunce mata ta tasa shi gaba tana kallo tana kuka..Zafi jikin nasa yake ƙara yi ita kanta zafin ji take kamar tana gaban wuta, saurin gyara masa kwanciya ta yi ta soma karanto masa Suratul yasin cikin ɗan ɗaga murya. Nan-da-nan ya soma Karkarwa yana yin wani irin ƙara baƙin abin nan na fita daga bakin , ganin yana ɓari jikin ta yi saurin janyo shi ta rungume tana kuka tana ci gaba da karantun, tana gama kai karshen surar ta kamo Suratul Iklas zuwa Nas, tana gamawa ya sarƙe da tari yana riƙe wuya tare da buɗe idanunsa yana mayar da su ya rufe. Tashin shi ta yi zaune tana jera masa sannu, juyo da shi ta yi tana shirin yi masa magana sai kawai ya wanke ta da amai, riƙe shi ta yi ya dinga yin aman yana nishi kamar zai amayo da 'yan hanjin cikinsa, bayan ya gama ta yi baya da shi ta kwantar ta tashi cikin dabara ta tattara rigarta da ya amaye ta nufi toilet. Tana shiga ta wanke wajan da ruwa, har za ta juya ta ga omo à gefe ta janyo ta zuba ta wanke tas sannan ta fito. Ta kusa karasowa inda yake ta ji an ɗauke wuta ɗik, da sanɗa ta iso tsakiyar palon tana lalibe har ta ji ta yi tuntuɓe da shi ta sunkuya ta zauna tare da janyo shi tana kiran sunanshi. "Antyyy!" Ta ji sautin muryarshi ta daki dodon kunnenta, da hanzari ta amsa, "Na'am Zaiyan tashi ka zauna." Ta faɗa a sanyaye tana lalibo hannunsa. Doguwar jiyar zuciya ya sauke ya yunƙura ya tashi zaune tana riƙe da hannunsa, jingina shi ta yi da jikinta ta daura kanshi à kafaɗarta.. "Hauwa'u Maijidda..!" Ta yi ji an kiran sunanta Wanda ba kowa ma ya san sunan ta haka ba, a ruɗe ta waiwaya inda ta ji an kira sunan tana zare idanu a cikin dubu. Taku ta ji ana yi ana doso inda take ta ƙanƙame Zaiyan Wanda ya yi laƙwas a jikinta ta rufe idanu gaban ta na faɗuwa.. "Hauwa'u Maijidda." Aka kuma kiran sunan ta ta buɗe idanu jin muryar a gaf da ita, tuni ta soma rawar jiki tana faɗin, " Inna lillahi wa inna laihin raji'un! Allahuma ajurni fi musibati wa akalifili khairan minha. A'uzu billahi minan shedanu rajim." Haka take ta maimaitawa a kiɗime. "budɗe idanuwanki Hauwa'u Maijidda." Ta kuma ji an faɗa a gefen ta, à hankali ta bude idanu tana addu'ar neman kariya daga abin da yake kiran sunan ta, kwalalo idanu waje ta yi cikin tashin hankali sakamakon yin arba da wata doguwar mace fara sol sanye da fararen kaya, zaune take a kan kujera fuskar nan a daure tamau ba alamun rahama, saurin rungume Zaiyan ta yi kamar za ta shige jikinsa ta soma magana "Na haɗa ki da girman Allah karki cutar da mu baiwar Allah." Ta yi maganar tana ɗan kallo kan kujerar sai ta ga wayam ba kowa. Da sauri ta tashi Zaiyan ya riƙe mata hannu ya ce " Anty bani da kowa sai ke." Baki buɗe take kallon shi cike da al'ajabin abin da ya faɗa, gani take kamar wannan macen da ta gani ce ta faɗi maganar, yau wai Zaiyan ne ke cewa ba shi da kowa sai ita? Duk da shi ɗin ba mai hankali ba ne amma kalmar ta daki zuciyarta matuƙa, sosai wani tsananin tausayin shi ya kamaye mata gangar jiki da ruhi ba ta san lokacin da hawaye suka zubo mata ba sai da ta ji yana goge mata ta ankare, ajiyar zuciya ta sauke ta ƙifta idanu tana masa wani irin kallo mai wuyar fassarawa a baki. Tuna abin da ta gani ya sa ta yi saurin waigowa ai kuwa ta ganta zaune da inda ta ganta da farko, wannan karon fuskarta ɗauke da damuwa tana zubar da hawaye abin ya ba wa Abir matuƙar mamaki. Tunani take to ita wannan ɗin mutum ce ko aljana ? "Ka da kiji tsoro Maijidda." Maganar matar ta katse mata tunanin da take, cike da tsoro ta kuma kallon ta ta ce "Baiwar Allah ke wace ce? Kuma me kike nema a gare mu ?" Murmishi ta ga ta yi tasa gefe farin mayafin nata ta goge hawayen da suka zubo mata, hannu ta ɗaga sama kaɗan sai ga wuta ta dawo haske ya gauraye palon. Sosai Abir ta gigice da ganin kyan matar, dafe ƙirji ta yi tana ƙura mata idanuɓ "Babu abin da nake nema a gare ku Maijidda, sanin ni ko wace ce ba yanzu zan sanar da ke ba sai zuwa wani lokacin in na sake haɗuwa da ke." Ta faɗa tana miƙewa tsaye ta juya mata baya.. Sai à lokacin Zaiyan ya ɗago ya kalli matar, baki ya saki yana nuna wa Abir ita da hannu ya ce, "Anty wannan Maman ki ce ?" Jin abin da ya fada sai matar ta juyo tana murmishi, waro idanu ya yi yana rufe baki ya ce "A a ga Maman Anty ta zo." Ya faɗa yana gyara zama. Ita kuwa Abir kallon su kawai take, gani ta yi matar ta matso kusa da su ta dafa kan Zaiyan tana kallon shi ba ta ce masa komai ba. Tsoro ya kuma dabaibaye Abir baki na rawa ta ce "Don Allah karki cutar min da shi amana ce Allah ya bani." "Ba zan taɓa cutar da shi ba, baƙar guba ce a jikinnshi nake fitar masa da ita, yanzu ta fita." Tana gama faɗin haka ta ɓace ɓat daga palon. A mugun tsorace ta dinga waigawa ko'ina à tunanin ta za ta ganta kamar dazu amma ta ga wayam. A hankali ta tashi tsaye shi ma ya tashi ya tsaya à gaban ta, gabadaya ji ta yi ba za ta iya barin shi a gidan nan ba dan zuciyarta ba ta kwanta da ganin wannan macen ba, hannunshi ta kama ta zaunar da shi à kan kujera ta isa bakin ƙofa ta ɗauko handbag ɗinta yana biye da ita. Hannun shi ta kama tana gyara zaman mayafinta gabadaya jikinta sai rawa yake shi kuma sai surutu yake mata, bude kofar ta yi suka fito waje sai buga sauri take Allah-Allah take su fita daga cikin gidan gabadaya. Cin karo ta yi da su Baba ta ja ta tsaya tana kallon su, Baba da Inna suka haɗa baki wajan faɗin " 'Yar nan yaushe kika zo? Kuma ina za ku je ?" Sake ɗamke hannun shi ta yi tana jin ranta na baci na barin shi da suka yi suka tafi shi daya a gidan, ajiyar zuciya ta sauke ta ɗago ta kalle su cikin bacin rai, baki ta buɗe da nufi magana sai kawai ta fashe da kuka. Sake da baki suke kallon ta suna mamaki daga tambayar ta sai kuka, Inna ta matso kusa da ita ta ce "Haba yar nan mène ne kuma na kuka ? Muje ciki kin ji." Kama hannunta Inna ta yi tana ba ta haƙuri ta ja ta suka nufi ciki, Baba ya kama hannun Zaiyan duk da ɗayan nasa hannun a cikin n'a Abir yake. Suna shiga ciki Inna ta shiga ta dauko mata ruwa mai sanyi ta miƙa mata tana faɗin" Sha ruwan. " Ba ta musa ba ta amsa ta sha ruwan tana sauke ajiyar zuciya, ji ta yi zafin zuciyar na sauka sauran ruwan da ta yi ta miƙa masa. Amsa ya yi ya sha ya yi lamo a gefen ta yana wasa da handbag ɗinta, Baba ta gyara zama ya dube ta ya ce "Wai me ya faru yar nan?" Baki ta buɗe da niyar faɗa musu duk abin da ya faru amma sai ta ji ta kasa fada, ƙwalla ce ta cika mata idanu so take ta faɗa ko za ta samu sauki da firgicin da ta shiga, ƙila Baba ya taimaka mata amma bakin ya kasa furtawa sai ajiyar zuciya da take sauke wa. Lum ta ji kan ta ya yi kamar wacce hajijiya ke shirin ɗauka ta dafe kan tare da miƙewa, ji ta yi hankalin ta ya koma gida ta warci handbag ɗinta ta nufi ƙofar fita da sauri. "Anty zan bi ki." Ta ji ya faɗa, saurin buɗe ƙofar ta yi ta fita tana sauri kamar za ta kifa. Zaiyan shi ma ya biyo ta yana kiran sunan ta yana cewa sai ya je tare da ita amma ko kallon shi ba ta yi bare ma ta tsaya ya iso inda take. Sai Yanzu ta tuna wayarta ta zarga jaka ta fito da wayar, kamar jira ake ta fiddo sai ga kiran Ali ya shigo ta ɗaga tare tsayawa da tafiyar da take ta zo gaf da jikin get ɗin gidan ta kama ƙofar ta riƙe tana jin abin da yake faɗa. "Hello Madam kina lafiya?" Sauke ajiyar zuciya ta yi jin ya riƙe mata hannu, sai da ta yi kusan minti biyu tana riƙe da wayar Ali ya ji shuru ya sake yin magana, kana ta daure ta ce "Kana ina Ali? Duk ma inda kake ka zo ka ɗauke ni daga gidan nan." Ta karashe maganar murya na rawa. "Madam gani nan zan shigo maza ki fito." Ya faɗa yana fitowa daga cikin motar ya kama get ɗin ya tura. Da sauri ta ja da baya tana zare idanu, À sukwane Ali ya shigo yana mai ɗane kunamar bindigar shi, dafe eapis ya yi dake kunnensa ya ce "Hello Oga kana kan layi ?" Daga can ɓangaren Abdul da ke ta safa da marwa a harabar Office ɗin su ya ce "Ali ina Baby take? Ina fatan babu abin da ya same ta dai ko ?" Gyada kai ya yi yana kallon Abir da ta yi tsuru-tsuru kamar ka ce mata kaiya ta kwasa a guje, ya ce "E Oga amma dai kamar ba a haiyacin ta take ba, tabbas akwai abin da ya firgita ta." Maza ku fita daga gidan gaf kuke da inda suke, suna nan suna biye da ku ka kula Ali kar wani abu ya samu Baby ko shi Zaiyan ɗin." To Ali ya ce ya dubi Abir ya ce" Madam mu je gida. " Ba ta ce komai ba ta yi gaba Zaiyan na riƙe da hannunta shi kuma ya mara musu baya, a bakin motar police shida ne da motoci biyu bayan wadda ya zo da ita, abin sai ya ba wa Abir mamaki sun zagaye da motocin kowa cikin shirin ko ta kwana, ganin ta ya sa suka bude mata mota suka shige.. Suna shiga motar suka bar wajan da sauri. Suna barin wajan sai wata jar mota ta iso ƙofar get ɗin, buɗe motar aka yi wani sangameman mutu ya fito daga motar sanye da baƙin glas ya nufi get ɗin ya soma ƙoƙarin buɗewa, gam ya ji an rufe ya buga da ƙarfi ya dawo yana hura hanci ya shige motar suka koma ta hanyar da suka fito... Gudu sosai Ali ke yi Abdul na fada musu inda za su bi, sosai suke gudu suka shiga cikin tsakiyar gari. Sai da suka zo wata Unguwa ya ce su rage gudun suka rage, bayan sun kutsa cikin Unguwar ya kira Abir. Dauka ta yi jiki na rawa ta kara à kunne ta ce "Hello Yaya." "Baby are you OK?" Goge hawaye ta yi ta ce "E Yaya amma mun tafo da Zaiyan kar Baba ya ga kamar ba mu girmama shi ba." "Baba kuma Baby? Kin ga gani nan zan zo na ɗauke ki mu tafi gida." To ta ce ta kashe kiran, juyowa ta yi ta ga ya yi bacci kawar da kanta gefe ta yi tana kallon Unguwar... Wani get suka nufa suka yi hon aka buɗe musu suka kutsa ciki, ita dai Abir kamar wata sakare haka ta saki baki tana kallon gidan kamar ba ta taɓa ganin gida irin wannan ba, sai da aka buɗe motar sannan ta nutsu ta fito daga motar. Kallon Ali ta yi ta ce "Ali to ya yi bacci fa." Gyaɗa mata ya yi sannan ya ce "Oga ya ce kar a fito da shi zai iso yanzu." Ba ta kuma cewa komai ba ta ta yi shuru tana mai Kallon gidan, ji ta yi ya birge ta. Motar Abdul ce ta yi hon aka buɗe masa ya shigo, kafin ma à gama packing ya buɗe ya fito yana yin dogon zari irin na zaratan mazaje ya nufo su, tana ganin shi da sauri ta nufe shi suna haɗewa ta faɗa jikinshi ta saki kuka. 'Hmm' Ya ja dogon numfashi yana yin hamdala da ya gan ta cikin ƙoshin lafiya, hannu ya sa ya raba ta da jikinshi ya ɗan rankwafo daidai saitin kunnenta, hucin da ya yi a saitin kunen ya sa ta buɗe ido da sauri tana tsayar da kukan. "My Baby ke ba ki ganin akwai wasu bayan mu? Me ya faru kike kuka?" ya faɗa cikin yin ƙasa da murya in ba a gaf da su kake ba ba za ka ji mai yake faɗa ba. Goge hawayen ta yi ta ce "E ba komai, amma Yaya me ya faru na ga kasa an kawo mu nan?" Ta faɗa tana tsura masa na mujiya. Hannunta ya kama ya ɗago ya kalli su Ali da suka ƙame a wajan, gyara tsayuwar shi ya yi ya ce "Ali ku shigar da shi ciki ku kula da kyau zan je na dawo ?" "OK Sir!" Suka faɗa a tare suna sara masa cikin girmamawa, shi ma sara musu ya yi kana ya juya ya shiga motar direba ya ja suka bar gidan.. Damun shi ta yi da maganar wannan gidan shi kuma ya mata shuru, ganin za ta sa masa ciwon kai ya juyo cikin nutsuwa ya dago habarta da yatsu biyu yana mata wani irin Kallo, itama kallon nashi ta yi tana narke fuska kamar za ta yi kuka,. A hankali ya kai fuskar shi daf da tata numfashinsu ya hade, baki ya kai kan kumatunta ya sumbace ta yana sauke ajiyar zuciya, sai da ya ga ta nutsu sannan ya saki fuskar ya juyo da ita suna kallon juna ya ce "Baby kin takura sai na fada miki abin da ya faru à gidan su Baba ko ?" Saurin gyaɗa masa kai ta yi da sauri, ya ci gaba "Wasu ne suka je gidan shi ne har suka sassari Baba da Inna, yanzu haka ma suna Asibiti à kwance Inna ta fi Baba raunatuwa. To sai bayan Ali ya kaiki ya aje ne muka samu labarin tun jiya da dare wajan karfe uku da rabi aka faɗo gidan, wani makocinsa ne da suka saba zuwa Masallaci tare ya ga bai je Sallah ba ya yi mamaki na rashin ganin shi. Sai da rana ta yi ya je ya ƙwanƙwasa gidan ya ji shuru sai ya tura kofar ya ga ta buɗe ya yi sallama ya ji shuru, hakan yasa ya dan leƙo cikin palon nan ya gansu kwance cikin jini. Hankali a tashe ya fita ya kiran yaranshi maza 2 suka shigo suka duba suka ga suna numfashi sai suka kwashe su zuwa Asibiti amma shi Zaiyan ba su gan shi a gidan ba. To bayan kin tafi shi makocin nasa ya kira ni ya min bayani Baba ne ya farfaɗo ya ba shi number ya kira, shi ya sa kika ji ina ce miki babu abin da ya same ki. " Ya ƙarashe maganar yana kallon ta.. Idanu waje take kallon shi har ya gama ba ta labarin, to in har su Baba suna Asibiti su kuma waɗanda ta gani à gidan su waye ? Ko kuwa suma aljannun ne kamar matar da ta gani? Sai da ya girgiza ta ta yi firgigit nan-da-nan tsoro ya shige ta, cikin kiɗima ta ce.... WhatsApp number : +966577675904 _*Taku har kullum Maman [6/20, 7:48 PM] Ummu Amjad: Shafi na (19) Cikin kidima ta ce "Y.. Yayaaa.." Ta ja sunan tsoro karara ya baiyana kan fuskarta. Dagowa ya yi a nutsu ya dube ta, ganin yadda ta rude sai ya kamo hannayenta ya kai kan fuskarshi yana mai tsare ta da idanu, sai da ya dauki kusan minti biyu a haka kafin ya yi kafin halin janye idanunshi daga cikin nata. Ita kuwa sumar zaune ta yi abubuwan da suka faru sun tsaya mata a rai, yar karama masarrafarta n'a neman kasa daukan wannan abu mai cike al'ajabi. Shin idan har yayan nata gaskiya yake fada mata su Baba suna Asibiti su n'a gida su waye ? Ko kuwa dai sun mutu ne suka mata fatalwa ? Ganin ba ta yi motsa ba Abdul ya girgiza ta ta yi birgigit ta dawo haiyacin ta, doguwar ajiyar zuciya ta sauke ji take kamar ta kurma ihu saboda hargitsewar da yar karamar kwakwalwarta ta yi, dago da kai ta yi cikin wani kalar yanayi ta tsare shi da idanu. Sai da ya gaji ra shurun sannan ya nisa ya ce "Baby ki fada min abin da kike ɓoye min, na ga kamar akwai abin da kike son faɗa." Ya ƙarashe maganar a daidai lokacin da suka ƙaraso gida.. Shuru ta masa gabaɗaya ta rikice, ganin haka ya sa Abdul ya mata nuni da ta fita a lokacin da aka gama yin packing, ba muso ta ɗauki handbag ɗinta jiki a saluɓe ta soma ƙoƙarin fita daga motar. "Baby ki kwantar fa da hankalin ki." Ta ji muryarsa lokacin da ta zuro ƙafafuwanta waje, dakatawa ta yi da fitar ta juyo ta kalle shi. "Yaya ina so ka kaini na ga su Baba a Asibitin, idan kuma ba za ka samu dama ba ka sa a kaini." Ta faɗa tana ɓata rai. Ɗaure fuska ya yi bai ce da ita komai ba ya buɗe motar ya fito, gabaɗaya ya rasa gane kan ta babu abin da ta iya in ba kuka ba nan ta fi kauri, shi kuma baya son saurin kukan nan da take haushi yake ji, shi ya sa wani lokacin yake rabuwa da ita ta yi ta ta yi, har sai in ya ga abin zai zame mata matsala ya rarrashe ta.. Goge hawayen da suka zubo mata ta yi ta fito ta nufi ciki. Da sallama ta shigo kanta a ƙasa kamar wata munafuka, Grandma da ke shafa mai a ƙafa ta ɗago tana amsa mata sallamar. Ganin yadda ta shigo ya sa Grandma ta taɓe baki tana kawar da kai gefe, zama ta yi a kusa da Grandma ta saita nutsuwar ta a sanyaye ta ce "Grandma barka da hutawa." Janye ƙafafuwanta ta yi daga kusa da Abir tana ƙara mulke su da mai, sai da ta sha ƙamshi sannan ta ce "Zan ga dai wanda zai aure ki yar nan, ace kina mace amma ba ki da kuzari irin na yaran da suka balaga kike ɗan kazar-kazar mana, ke duk komai naki a sanyaye yake kamar wata raguwa. Ni kam ban taɓa ganin mutum irin ki ba, ba dan ba kina da sunana da ba zan taimaka miki ba. " Ɗago kai Abir ta yi ta kalli Grandma tana yin murmushin yaƙe, in da sabo ai ta saba da irin wannan maganganun na Grandma, a nutse ta ce" Ke dai Grandma kullum sai kike cewa wai za ki taimaka min, amma har yau ban ga taimakon ba shuru kake ji kamar shaho ya ci shirwa. " Ta faɗa tana tashi ta wuce ɗakinta da ɗan saurin ta dan kar ma ta ji rashin darajar da Grandma za ta mata.. " A ni Hauwa'u." Ta riƙe baki sannan ta ci gaba," Da alama kema yanzu wannan ƙaton banzar ya soma koya miki rashin kunya, in ban da ma ni kin rainani ina matsayin uwar ubanki ki ce min wai kin ji shuru kamar shaho ya ci shirwa? Uwar taki za ta zo ta same ni ina jiran ta har shi fitinannan ɗan'uwan naki duk na ishe ku riga da wando har da ɗankwalin ɗaurawa. " Tana cikin yin sababin sai ga Abdul ya shigo palon, kallon shi ta yi cikin masifa ta ce" Uban me ka zo yi a sashena? " Ta yi micin-micin da idanu tana gyara zama.. Zama ya yi ya riƙe kanshi ya lumshe idanunsa, sosai zuciyarsa ke wani irin lugude sam ya kasa nutsuwa, da sauri ya buɗe idanunshi wanda suka yi jajur ya kalli Grandma. Itama kallon shi take ganin yadda idanuwansa suka yi ja ta sauke ƙafafuwanta ta dube shi ta ce "Abdullahi, me yake faruwa wai? Na ga wannan figaggiyar ta shigo fuskarta da alamun damuwa, ko faɗa kuka yi ne?" Sauke hannayenshi ya yi daga kan ya juyo ga Grandma, ya ɗaga baki zai yi magana ta dakatar da shi ta tashi ta iso inda yake ta kama hannunsa suka nufi ɗakinta.. Suna isa ta zaunar da shi a bakin gado ta ɗauko ruwa mai sanyi ta ba shi tare da cewa "Ka sha ruwan." Bai musa mata ba ya amsa ya shanye duka ya aje cup ɗin, ajiyar ya dinga saukewa idanunsa lumshe, wani irin zafi yake ji ƙirjinsa na masa matuƙa. Grandma ya nisa ta ce "Wai me ke faruwa?" A hankali ya ɗan matso kusa da ita ganin haka ya sa ta kwanto da kanshi kan cinyarta ta soma shafa masa ta soma masa nasiha.. "Abdullahi ko ma mene ne yake damun ka ka yi haƙuri, dukkan tsanani yana tare sauƙi ka kwantar da hankalin ka ka yi aikin ka cikin nutsuwa da adalci." Sai a lokacin ya ji zai iya magana, ya ce "Grandma mutane ba su da amana, mutane mafi yawan su duk azzalumai ne, ban san wani abu Abie ya yi musu ba suka kashe shi. Hakan bai musu ba suke neman rayuwar iyalinsa, Wallahi! Wallahi ! Wallahi! Kin ji na rantse sau uku to sai na binciko duk abin da aka binne duniya ta sani, sai na lalata musu komai na hana su jin daɗin rayuwa kamar yadda suka hana mu ji, hatta gidan nan akwai abin da yake faruwa n cin amana wanda kowa ya kasa fahimtar hakan, ni kuma na yi alƙawari sai na gano wannan maƙarƙashiyar da ake ta shiryawa tsayin lokaci. " Ya ƙarashe maganar yana tashi zaune ya fuskanci grandma.. Shuru Grandma ta yi tana nazarin maganar tana ɗaura ta akan mizani na hankali, tabbas ita kanta ta kasa nutsuwa da wasu daga cikin 'yan gidan. Kallon shi ta yi cikin wani yanayi ta ce "Indai akan gaskiya ne za ka yi aikin nan Abdullahi ina goyan bayan ka ɗari bisa ɗari, ni yanzu ban ma yarda mutanen nan ba sa bin rayuwar mai sunana ba." Ta faɗa tana jan numfashi.. Bai ce da ita komai ba ya tashi ya bar ɗakin.. Ko da ta shiga ɗakin mamaki ne ya hana ta ƙarasawa ciki ganin yadda aka rikito mata kayan cikin drawer ta duk an barbaza su a tsakar ɗakin, da ƙyar ta ƙarasa shigowa ta aje jaka da mafi ta zauna a bakin gado tana mai kallon kayan, ko ba ta faɗa ba wanda ya rikito mata kayan nan akwai abin da yake nema a cikin drower. Tashi ta yi ta soma tattare kayan tana yi tana ɗaɗɗaga kayan tana ƙare musu kallo, bayan ta gama ɗaukewa ta rufe har ta juyo ta ga ƙyallin wani abu a ƙasa, baya ta dawo ta sake baza idanunta tana son sake ganin abin da ta gani. Sai da ta sunkuya ta duddubawa sannan ta hango shi ta kai hannu ta ɗauko, ɗankunne guda ɗaya sai walƙiya yake yi ta koma ta zauna a bakin gado tana juya ɗankunnen ta ji an buɗe ƙofar ta yi saurin ɓoyewa.. Da kallo yake bin ta har ya shigo ya zauna ya kalli hannunta da ta yi baya da shi, hararar ta ya yi ya ce "Meye kika ɓoye Baby?" Ya yi maganar yana kamo hannun nata, ganin haka sai ta kwace hannun ta buɗe ta nuna masa ɗankunnen, ta ce "Yaya akwai wanda ya shigo min ɗakin nan bayan tafiya ta." Labarin yadda ta ga kayan sawarta ta ba shi, shuru ya yi na 'yan wasu daƙiƙu yana kallon ɗankunnen, ya taɓa ganin wannan ɗankunnen amma ya rasa a jikin wace ce ya gani, kallon ta ya yi ya ce "Baby shin kafin hakan ta faru kin taɓa ganin wani abu wanda ba ki san da shi ba a drowerki?" Kai ta ɗan ɗaga sama alamar tunani, can ta kalle ta ce "Akwai wata rana na zo ina gyara kayana na ga wani abu ɗan ƙarami, wanda ni dai da kaina ban san da zaman shi ba a drower, shi ne na samu guri na ɓoye shi." Ɓala yatsu biyu ya yi yana gyaɗa kai, lalle ko ma wace ce wannan mai ɗankunnen to ba tantama ita ce ta saka wannan abin, sake kallon ɗankunnen ya yi sannan ya ce "Tabbas mai ɗankunnen nan ita ta saka miki wannan abin da kika gani, ɗauko min shi na gani." A mamakance ta tashi ta isa bakin drower ta buɗe saitin pant ɗinta ta ɗauko shi daga inda ta ɓoye, mayar komai ta yi ta kawo masa. Kallon abin yake cike da firgici ya ce "Baby bayan kin ga abin nan kin yi wata magana ta sirri a ɗakin nan? Ko kuma kin fito babu kaya a jikinki daga toilet?" Ya yi maganar a ruɗe. Ganin yadda ya shiga damuwa sai abin kuma ba ta mamaki, tunawa ta yi da Mom ta shigo har ɗakin nan ta ba ta wasu takardu da kuma wanda wajan ta, wani irin zufa ce ya soma tsatsafo mata duk da ba ta san mai abin ya ƙunsa ba, sai da ya sake maimaita mata maganar sannan ta soma faɗa masa abubuwan da ta yi bayan ta ga abin.. "Na ga abin da wasu kwanaki mun yi waya da Yaya Suhal ya ce min yana nan zuwa Nigeria wani aiki zai kawo shi Yola, sannan satin da ya wuce Mommy ta kawo mun wasu takardu ta ce na aje mata su kar na bari kowa ya san da su. Kuma sau tari ina fitowa daga toilet ba kaya, amma Yaya mene ne shi wannan ɗin abin? " Ta ƙarashe maganar tana tsare shi da kallo.. " oh my god!" Ya faɗa yana riƙe kai, numfashi ya fesar sannan ya soma magana, " Wannan da kike gani ana amfani da ita ne wajan gano wani abu a inda aka aje ta, kuma tana dauka video ko da kuwa kin lulluɓe ta indai tana wajan za ta take daukan sautin muruarki, maza bani computer ki." Ya ƙarashe maganar yana gyara zama.. Tashi ta yi jiki na rawa ta ɗauko masa computer ta zauna, buɗewa ta yi ta miƙa masa, amsa ya yi ya ɗaura abin a kan computer ya daddana ya yi wani rubutu mai tsayi, sai da ta gama wurgawa sannan ta nuno duk abin da yake cikin ta.. Ɗaya bayan ɗaya ya soma buɗe recoding din, muryar Abir ya dinga ji inda take kuka tana yi wa Abie dinta addu'a. Na ƙarshen ne wanda ya ji muryar Mom na faɗin, - _"Mamana ga wannan takardun ki aje su a inda ba wanda zai gani, na babanki ne ya bani su ajiya lokacin da kuka kusa wannan tafiyar, shi ne na kawo ki aje su a wajan ki idan ba za ki adana ba in Yayanki ya zo ki ba shi ya aje su."_ Muryar Abir ya ji tana cewa za ta ɓoye su. Video ya dannawa deleting wanda ta fito daga wanka ne ba ta suturta jikinta ta ba, sai da ya tabbatar ya goge duk wani abu da camarar ta ɗauka sannan ya kashe computer ya dauke camera. Miƙewa ya yi ya bar ɗakin bai ce da ita komai ba ta bi shi da kallo, ajiyar zuciya ta sauke tana yi wa Allah godiya da Abdul ya gano wannan mugun abun da ake son aikata mata... Tunanin Zaiyan ne ya faɗo mata ta ɗan ba ta rai ta ce "Bawan Allah, Allah ya ba ka lafiya Zain." Tashi ta yi ta shige banɗaki ta watsa ruwa, bayan ta fito ta zauna tana ta tunanin abin al'ajabin da ta gani yau.. Abdul ko da ya koma part ɗin su ya ga Umma tana safa da marwa, da har zai wuce sai kuma ya tsaya ya dube ta ya ce " Umma lafiya kike ta zarya?" Kallon banza ta watsa masa ta yi tsaki ta nuna shi da yatsa ya soma masifa. "Me ya shafe ka da ni? Idan ka sake kirana da Umma sai na ci mutumcin ka marar kunya kawai, matsa ka bani guri kafin na bangaje ka." Bai ce mata uffan ba yawu ɗakinsa. Washegari Abdul ya ƙona wannan manaɗar bayanan, shi kuma ɗankunnen ya samu waje ya ɓoye shi. Sai da su Baba suka cika sati cif a Asibiti kana shi ya samu sauƙi aka ba shi sallama, Inna ce dai da saura ciwukan da ke jikinta ba su warke ba. A ranar Abdul da ya gaji da ganin kukan Abir akan sai ya kaita ta gansu ya kai ta, sosai ta sha kuka ganin halin da Inna take ciki nan ta ƙara tsorata da mutanen da ta gani masu kama da su Baba. Kullum cikin tunanin matar nan take ba dare ba rana, so take ta sake ganin ta dan ta faɗa mata ita ɗin wace ce? Sannan me ya sa take ɓacewa? Cikin satin ta ƙara ramewa ga Mom itama ba ta samu zama kasancewar za ayi aure a gidan Baba Malam zai aurar da ɗiyarsa ita ce mai sayo kayan ɗaki, hakan yasa ba ta tsaya ta kula da ita ba ballantana ta tambaye ta me yake damun ta har ta rame.. Yau ne ranar da Suhal ya mata alƙawarin zai zo, dan haka ta kira Hafsat a waya ta ce ta zo ita da Iman su taya ta tarbar shi. Hafsat ta ci wanka ta zo gidan su Abir sai murna take wai yau ita ce Abir ta kula, wanda rabon da ta yarda su gaisa ma a waya tun kafin ayi kidnapping din su. Cikin shigar ta ta riga da wando jis ta shigo ta maƙale mayafi a kafaɗa tana zuba ƙamshi, da murna Abir ta tare ta suk rungume juna suna murnar ganin juna, Iman ma ta sha wanka cikin shigar riga da sket na atamfa. Ita kuwa oganniyar shigar abaya ƴar Dubai ta yi ta yi rolin da mayafin abayar.. Ƙarfe biyu uku daidai suka ji hon, da sauri Iman ta leƙa ta ga wata jar mota sabuwa dal ta shigo harabar gidan ta yi packing, da sauri ta juyo ta kalle su ta ce "Anty Baby ya zo ga shi nan.". Murmushi Abir ta yi ta ji gaban ta na faɗuwa, sai da ta ji saƙo ya shigo wayar ta ta yi saurin dubawa. _"My princess yau dai Allah ya yi zan ganki a zahiri, gani a harabar gidan ku."_ Murmushi ta yi ba ta ba shi amsa ba.. Su Iman ta aika ta ce suje su shigo da shi ɗakin baƙi, ita kuma ta nufi ɗakin Mommy dan ta faɗa mata zuwan shi. Suna fita Iman da ta zaƙu ta ga wannan Yaya Suhal ɗin da kullum Abir ke maganar shi ta kwankwasa masa glas ɗin motar. A hankali ya buɗe motar ya zuro ƙafar shi waje, kallon su ƙasa ya yi inda ya yi arba da ƙafafuwan su, sai da nuna izzar ta shi ya sha ƙamshi son ran shi har ran Hafsat ya so ɓaci sannan ta ga ya miƙo ɗayar ƙafar, fitowa ya yi yana zuba wani irin fitinannan ƙamshi su kan su su Iman sai da ƙamshin ya tafi da su.. "Assalam alaikum 'yan mata." Suka ji zazzaƙar muryarsa ta daki dodon kunnuwansu. Iman ta kalle shi da kyau tana masa kallon a inda ta san wannan mai fuskar, sai kuma ta basar ta saki murmushi ta ce "Wa alaikum salam, barka da zuwa." Gyaɗa mata kai ya yi bai kuma cewa komai ba, iso suka masa har ɗakin baƙi wanda yake tashin ƙamshin turaren wuta mai daɗi. Zama ya yi ya su kuma suka fita suka kawo masa abinci na musamman da lemuka masu daɗi, sannan suka koma suka sanar da Abir sun gama komai ta tashi da nufi ɗakin cikin daukin son ganin Suhal.. Da sallama ta shiga ya amsa mata bai ɗago ba yana danna waya, sai da ya ji kamar ana kallon shi ya dakata da danna wayar ya saki ƙayataccan murmushi ya ce "My princess manya." Ya faɗa yana ɗago da kanshi ya zuba mata daradaran idanuwansa farare masu ɗaukan hankalin wanda aka kalla. Kanta a ƙasa ta isa ta zauna a dan naisa da shi tana murmushi. "A kuma fuskar taki ma rowar ta za ki min bayan na yi tattaki na zo dan na kalli kyakyawar fuskar ƙanwata?" Ya faɗa yana murmushi wanda ba kowa yake yi wa irin sa ba.. A nutse ta ɗago da kanta ta daura idanunta a kan fuskarsa, a zabure ta miƙe tana nuna shi, mamaki, al'ajabi, tsoro suka kawo mata ziyara ta iso gaban shi da sauri baki na rawa ta ce" Zainn... _Taku har kullum Maman Nusaiba ce_ [10/20, 11:43 Yamma] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): ~A HAKA NAKE SON SHI~ Shafi na (20) +966577675904. Baki na rawa ta ce "Zainnn.. Ta durƙusawa ƙasa, wani irin bugu zuciyarta ke yi fat! Fat! Fat! Da sauri-sauri, shin idanuwanta ne suke gano mata ba daidai ba? Ko dai da gaske shi ne take gani a gaban ta tsaye? In kuwa shi ne to me ya sa ya mayar da kan shi Mahaukaci bayan yana da hankali? Runtse idanu ta yi tana girgiza kai cikin ruɗewa ta sake ɗago kai ta kalle shi, shi ɗin dai take gani ba wani ba, miƙewa ta yi tana dafe ƙirji ta ce "Zain, shin kai nake gani ko kuwa dai tsananin son ganin ka ne ya sa nake kallon kowanni namiji da fuskarka?" Ta ja fasali sannan ta ɗaura, "Ka yi magana mana dama kai ba mahaukaci ba ne kake shiga irin ta mahaukata?" Sake da baki Suhal yake kallon Abir da ta soma fita daga haiyacinta, sunan da ya ji tana kiran sa da shi ya ba shi mamaki matuƙa, sai tambayar kansa yake waye kuma wani Zain? Ko kuwa gamo ta yi ne kafin ta shigo? Wayarsa da ta saɓule daga hannunsa ya ɗauka, numfashi ya fesar ya tsura mata idanu, tabbas ita ɗin kyakkyawa ce sosai, fuskarta da ta sha kwalliya yake kallo ba ko ƙiftawa, wani irin yanayi yake jin na fisgar shi game da ita. Ajiyar ya sauke tare janye idanunsa daga kallon da suke wa juna ita da shi, shi yana mata kallon ƙurulla ta masa kyau fiye ma da yadda ya gan ta photo, yayin da ita kuma take masa kallon ya ba ta amsar tambayar da ta masa amma ya yi shuru ya zuba mata na mujiya.. Gyara zama ya yi ya ce "My princess, wai waye Zain? Naji kina kira na da sunan shi dan gidan waye shi da har yake miki gizo?" Ya faɗa yana ɗan haɗe fuska, wani irin zafi ya ji da ta ce wai tana tsananin tunanin wani can da ban bayan shi ga shi a gaban ta da ya yo tattaki tun daga wata ƙasar ya zo dan ya gan ta eyes to eyes, dafe kai ya yi ya sake kallon ta.. Shuru ta yi tana kallon shi yana maganar, ta kasa yarda ba Zaiyan ba ne saboda shi ma Suhal yana da wushirya irin ta Zaiyan har sajan duk iri ɗaya ne. Ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ta sauke tana ɗan lumshe idanu, can dai ta buɗe su a kan shi nan dai ta ga bambancin da ke tsakanin shi da Zaiyan, shi yafi Zaiyan fari, sannan girarshi ta haɗe da ƴar'uwar ta saɓanin Zaiyan da tashi ba ta haɗe ba. Ji ta yi ta ɗan samu sassauci na ruɗewar da ta yi ta koma inda ta zauna a farko ta zauna, sai ta dafe kai ta saki ta kalle shi cikin wani irin yanayi ta soma magana. "Am so sorry Yaya Suhal, Wallahi na ruɗe ne dayawa." Saurin tarar numfashin ta ya yi, "Kin ruɗe kamar yaya My Princess? Ki faɗa min waye Zain?" Ya yi maganar yana ɓata fuska.. Ajiyar zuciya ta sauke ganin yadda ya ɓata rai sai ta ji ba daɗi, yana murna ya zo dan ya ganta ta ganshi sai tana kiran shi da wani sunan ai dole ma ranshi ya ba ci, a hankali ta ce "Zain wani majinyaci ne wanda muke kula da shi, kana matuƙar kama da shi sosai sai dai kai ka fishi fari shi kuma farin nasa na duhu ne, ka yi haƙuri ka ji Yayana, amma dai sai na ga kamar a photo ba ka yi kama da shi ba, a photon ka fi haka girma." Ta faɗa tana yi masa ƙayataccan murmushi mai sanyaya zuciya. Shi ma murmushin ya yi ya kuma cika da mamakin wai yana kama da wajinyacin su, ai kuwa zai so ya ga wannan majinyaci dan ya ga yadda suke kama wanda har ya sa ta ruɗe da ta gan shi. Cikin nuna zallar farin ciki ya ce "Ƙanwata sarkin kuka da rigima, yo ai wancan ba ni ba ne Yayana ne, amma zan so na ga wannan bawan Allah mai kama da ni." Riƙe baki ta yi tana tunano photonshi kwaya ɗaya tal wanda sai da ta yi masa fushi sati kana ya turo mata, ashe ma ba shi ba ne yayansa ne, harara ta aika masa ta ce " Amma ko kai kuwa Ya Suhal ka zama ɗan basaja, yanzu da yayan naka ka zo ai shi zan kalla ba kai ba." Ta karashe maganar tana murguɗa masa baki.. Kyakkyawan murmushi ya mata, ya ce "Ai dama na ce zan miki bazata, to wannan ita ce." Murmushi ta yi ta miƙe ta isa gaban kayan abincin ta zuba masa lemo mai sanyi, a nutse ta miƙa masa tare da cewa "Yanzu dai bismillah ka sha wannan ka ci abinci, in yaso daga baya ma yi maganar." Amsa ya yi ya yi bismillah ya sha lemon. Abincin ta zuba masa farar shinkafa da wake da miya ta sha nama sai zuba ƙamshi take, ɗayar kular ta buɗe nan kuma dambu kuskus ne ya ji kayan kamshi shi ma yana tururi ta ɗago ta kalle shi tana ƴar dariya ganin yadda ya yi mata ƙuri da idanu ta ce "Ya Suhal wai wannan kallon fa? Ko ba haka ka yi tsammanin gani na ba? Ka ganni ƴar figigiya ko?" Ta ƙarashe maganar tana dariya.. murmishi mai sauti ya yi ya amshi cokalin da take miƙa masa ya ce "Tabbas ƙanwata na so na gan ki babba ki fini jiki ma." Waro idanu ta yi tana rufe baki ta ce "Tamɗijam! Wai ni ɗin ce ka so ka ganni irin ƙatuwar nan?" Gyaɗa mata kai ya yi dan ya fara cin abincin, turo baki ta yi tana hararar shi ba ta ce komai ba ganin ya soma cin abincin. Satar kallon shi take idan ya sunkuya kai zai ɗauki shinkafar in ya ɗago sai ta yi saurin janye idanuwanta kamar ba ita ba, shi kuwa yana kallon ta duk abin da take yi sai ya ji ta ƙara shiga ranshi yadda take turo bakin sai ya ji wani abu na fisgar shi ya lumshe idanu yana zaune tsokar naman da ya saka a baki, in ka kalle shi sai ka ɗauka daɗin abincin ne yake kai masa har kwanya yake lumshe idanu, shi ko ba wani daɗin girkin ba ne ya sa shi hakan yanayin da ya shiga ne ya sa ya lumshe idanu. Bayan ya gama ta ƙara zuba masa lemo tana sakin murmushi ta ce "Ya Suhal manya." Hararar wasa ya mata yana goge bakinsa, gira ya ɗage mata ya ce "To Princess ya gida ya su Mommy? Ina wajan Yaya Abdul?" Rufe fuska ta yi tana ƴar dariya, ita fa daɗi take ji in yana ce mata princess, sauke hannun ta yi ta ce "Yaya yana nan lafiya an jima ma za ka ganshi dan ya kusa dawowa daga wajan aiki, kuma na ce masa in ka zo ya zo ku gaisa ya ce zai dawo da wuri, Mom kuma tana ciki." Ya ɗaga baki zai yi magana Iman da Hafsat suka shigo bakinsu ɗauke da sallama, amsa musu suka yi Suhal ya kame yana wani shan ƙamshi ganin yadda Hafsat ta ƙura masa idanu, zama suka yi Iman ta ce "Yaya Suhal barka da zuwa, ya gidan?" Ta faɗa cikin nutsuwa. Ɗan sakin fuska ya yi ya amsa mata gaisuwar, itama Hafsat ta gaishe shi tana sakar masa murmishi ya amsa ba yabo ba fallasa.. Sun jima suna jan shi da hira shi kuma yana bin su da E ko a a, kallon Abir ya yi da ta gama amsa waya ya ce "Princess ki min iso wajan su Mom mu gaisa ina son na tafi zan bi jirgin ƙarfe tara da rabi na tare." Ya yi maganar yana rufe hasken wayarshi.. Ɓata fuska ta yi ta ce "To Yaya ya ce ga shi nan zan shigo ya dawo, ka bari mana sai gobe ka tafi." Girgiza mata kai ya yi bai ce da ita komai ba, suna haka sai ga Abdul da Salim sun yi Sallama a palon suka amsa musu.. "To uwayen surutu kun zo kun sa baƙo a gaba kuna zuba masa zance, sai ku tashi ai ku fita." Salim ne ke maganar yana miƙa wa Suhal hannu suka yi musabaha. Iman ta yi masa kallon to sannu ubanmu ta kawar da kai, ita kuwa Hafsat Abdul ta kafe da idanu yana gaisawa da Suhal har sai da ya ɗago suka haɗa idanu ta yi saurin ƙasa da nata cikin jin kunyar ya kama ta tana kallon shi, ɗan ƙaramin tsaki ya ja wanda ba kowa ya ji ba sai Abir da ke zaune kujera ɗaya da shi, gyaɗa kai ta yi tana danne dariyar ta dan ta san da wa yake... Shuru Abdul ya yi yana tunanin inda ya san wannan fuskar, sai can Zaiyan ya faɗo masa ya ɗago ya kalli Suhal da shi ma yanzu ya fahimci yana masa kallo irin wanda Abir ta masa, gane hakan ya sa ya yi murmushin gefen baki ya ce "Yaya Abdul Princess ta ce Wai ina matuƙar kama da wani majinyacin ku?" Ya faɗa dan ya ƙara tabbatar da abin da yake son sani.. Salim ya kalle shi yana ɗaga kai sama, can ya dube shi ya ce "Gaskiya dai bro kana kama da wata fuska da na taɓa gani, amma ban san a ina ba ne na kalli mai kama da kai." Itama Iman haka ta faɗa Suhal ya ƙara cika da mamaki, ko dai mafarkin shi ne yake son tabbata? Girgiza kai ya yi ya ce "Zan so na ga wannan mutumin." Sai da Abdul ya gama jin maganganun su sannan ya ce "E tabbas kana kama Zaiyan majinyacin mu wanda yake fama da matsalar ƙwaƙwalwa, da ba dan ka fishi haske ba da sai na ce kaine Zaiyan." Ya faɗa yana jinjina tsananin kamar da suke.. Suhal ya gyaɗa kai ya ce "Don Allah zan iya ganin ko da photon shi ne?" Abir Abdul ya kalla ta buɗe wayarta ta, gallary ɗin wayar ta shiga ta nemo wanda suka yi a tare ta miƙa masa ya amsa. Hasken wayar ya ƙara ya kalli photon, dam! Ya ji gaban shi ya faɗi sakamakon yin arba da photon Zaiyan, tabbas in wani ya gan shi zai ce shi ne jikin wannan photon ya yi shigar mahaukata, na gaba ya janyo inda suka yi dariya shi da Abir, bai san ba lokacin da ya ce "Ikon Allah.! Hannu ya kai ya shafa fuskarsa yana kallon photon, ya jima yana kallon photunan sannan ya ci karo da video su, saurin buɗewa ya yi ya ga yana bin Abir ita kuma tana guduwa yana ce mata yunwa yake ji, ita kuma tana ce masa ba za ta ba shi ba.. Bayan ya gama gani ya miƙa mata wayar zuciyar shi cike da son ganin wannan mahaukaci mai kama da shi, a nutse ya ce "Don Allah zan iya ganin shi?" Girgiza masa kai Abdul ya yi yana miƙewa ya ce "Gaskiya da wahala dan yau aka kai shi Asibiti sai zuwa gobe za a dawo da shi, in za ka kai gobe to zan iya kaika ka gan shi." Numfashi ya ja ya ce "OK to ba damuwa zan kai goben in sha Allah dan na gan shi, yanzu ayi min iso na gaishe da su Mom." Iman da Hafsat suka fita dan sanar da Mom zai shigo, bayan Iman ta dawo ta ce zai iya shiga suka miƙe su duka suka nufi palon su Grandma.. A sallama suka shiga Mom da grandma suka amsa musu, durƙusawa ya yi cikin ladabi ya soma gaishe da su, suka amsa masa cikin sakin fuska. Abir ta yi murmushi ganin Mom na kallon shi ta ce "Mom yana kama da Zaiyan ko?" "Kwarai ma kuwa sosai suke kama?." Cewar Mom tana kallon shi. Murmishi kawai ya yi wato dai in ya fahimta kowa kallon nasa da yake na kamannin shi da Zaiyan ne, tashi ya yi ya musu Sallama ya ce zai koma masaukin shi. Grandma ta riƙe baki ta ce "Haba dai ɗan nan, ka taso tun daga wata ƙasa ka zo wajan jikata kuma ka ce wai a hotel za ka kwana? Ai ka zauna a gidan nan za ka kwana ba in da za ka je." Ta gutsiri goron da ta kunce a leda ta ci gaba da magana "Ni ce nan Uwar ubanta ba ka ga muna kama da ita ba?" Murmushi Suhal ya yi ya ji grandma ta birge shi, amma ba zai iya kwana ba a gidan su dan haka ya dubi Grandma ya ce "Allah sarki Kaka, ai da yau ma zan tafi zuwa dare, to na fasa ne saboda ban sani ba ko zan haɗu da wanda za mu yi meeting da shi ƙarfe huɗu da rabi, in ban samu mun haɗu ba dole na kwana." Gyaɗa kai ta yi tana miƙe ƙafarta ta ce "To kai ko yaro daga wani gari kake a ƙasar Niger ? Sannan su waye iyayenka?" Saurin kallon ta Abdul ya yi jin maganar da ta yi, ya daga zuwan baƙo sai tambayar su waye iyayenshi ? Murmushi ya kuma yi zai yi magana suka ji sallama su Abba, amsa musu suka yi suka ƙaraso ciki suka zauna. Suhal cikin ladabi ya juya gefen su Abba ta soma gaishe da su, cikin fara'a suke amsa mishi suna masa barka da zuwa yana sunkuyar da kai. Grandma ta sake maimaita maganar da ta yi yanzu ganin za a manta, har Abba zai yi magana sai kuma ya fasa, Suhal ya ƙara sunkuyar da kai ƙasa ya soma musu bayanin asalin shi a takaice.. "Suna na Yarima Suhal Abdulwahid, mahaifina shi ne sarkin garin Niamey a yanzu ni ne ɗan shi na biyu, mahifiyata mu biyu ta haifa ni fa ƙanwata Ilikima, sauran kuma yaran abokiyar zaman Mamana ne." Ya ɗago ya kalle su jin sun yi tsit kamar ba kowa a palon, kowa ya ga shi yake kallo sake da baki fuskokin su na nuna tsananin mamaki, murmushi ya yi dan ya san dama za a rina dole su yi mamakin hakan, ci gaba ya yi da magana.. "Dama ƙarfin zuwa na Nigeria dan na zo gidan su Princess na ganta a zahiri itama ta ganni na kuma gabatar da kaina a gare ku." Da wani irin sauri Abdul ya ɗago ya kalle shi, Salim ya riƙe baki ya ce "Ka gabatar da kanka kuma? Ka mana yadda za mu gane." Numfashi ya ja sannan ya ci gaba "E kamar yadda na ce zan gabatar da kaina ga iyayenta." Ya ɗago ya kalli Abba da shima shi yake kallo ya ce "Abba ina neman izinin auren princess." A zabure ta kalle shi ya juyo shi ma ya zuba mata idanu, wani irin bugu ƙirjin ta yake yi saboda ruɗewa, kenan dama Suhal dan sarki ne bai taɓa faɗa mata ba? Abdul kuwa kasa cewa komai ya yi, da ya yi niyar magana amma kalmar neman auren da Suhal ya faɗa ita ta tokare masa maƙoshi nan da nan ya bushe, wani irin tafasa zuciyarsa ke yi haɗi da wani kalar azababben zafi wanda yake jin shi har tafin ƙafarsa.. Grandma ta gyaɗa kai ta nisa ta ce "To amma kai kuwa yaro dama ka taɓa haɗuwa da ita ne? Ko kuwa sai yau ka ganta?" Girgiza kai ya yi ya ce "Inna ai princess ba ta taɓa ganina ba sai a photo shima ɗaya ne wanda ya jima da yi, ƙanwata Ilikima kawai ta sani dan har gaisawa suna yi sosai, ta sha nacin na turo mata photona amma sai na ce mata ai ni bana photo da kyar na turo mata ɗaya shi ma na yayana ne na turo mata. Ta sha tambaya na ƙara turo mata Photona sai na ce ban samu na yi ba, da haka nake mantar da ita zancan, na kuma ce kar Ikilima ta tura mata in ta nema a wajan ta tun tana mita har ta gaji ta daina tambaya, ni kuma ina da photonta a wajena hakan yasa ba ta taɓa ganin fuskata ba ina daidai wannan shekarun, sai yau da ta ganni har take cewa muna kama da wani majinyacin su. Abba in har ka bani izini in na koma gida zan sanar da Babana ya turo ku yi magana." Shuru Abba da Daddy suka yi suna nazarin maganar shi, sai can Abba ya yi ƙarfin halin cewa, "Suhal ita Maman nawa ta san kana son ta?" Girgiza kai ya yi hakan ya ba wa Abba damar ci gaba. "To ka nemi soyayyar ta in har ta amince tana sonka mu ba mu da matsala, amma ka sani ƴarmu tana da lalura za ka iya auran ta a haka?". Saurin ɗaga kai Suhal ya yi cikin wani irin farin ciki ganin ya soma samun ƙwarin gwiwa ya ce "Abba ai Princess ko guguwa ce zan aure ta kuma na kula da ita na daraja ta, ta faɗa min cutar asma gare ta ba ta son hayaƙi da duk wani abin da zai sa ciwon nata ya tashi." Lumshe idanu Abdul ya yi sai yanzu ya ji ya ɗan samu sassauci a zuciyarshi, ko ba komai Suhal na son Abir da gasken gaske. Daddy ya yi murmushi ya ce "Mu yanzu abin da zamu ce kawai Allah ya tabbatar mana da alkhairi, ka je ku daidai kanku kai da ita in ta amince sai mu mu shigo lamari." Ɗadi sosai ya mamaye zuciyar Suhal, a nutse ya ce "Na gode sosai Baba." Abba ya dubi Abir ya ce "Mamana shin kina son shi?" Shuru ta yi ba ta ce komai ba, ita yanzu me za ta ce akan hakan saboda ba ta taɓa masa kallon so ba, sai da Abba ya sake maimaitawa ta ɗago ta kalle su ta ga duk ita suke kallo amma ban da Abdul, tashi ta yi da sauri ta bar palon ta nufi ɗakinta.. Da kallo suka bi ta Daddy ya ce kawai ya nemi soyayyar ta in ya samu su ba su da matsala za su yi bincike a kan shi, cikin jin daɗi ya musu sallama zai koma Abdul da Salim suka fito da shi dan su masa rakiya. A bakin mota ya juyo ya kallo Abdul da ya ɗaure fuska kamar haɗarin da ya so zubo ruwa, ɗan murmushi ya yi ya ce "Yaya Abdul don Allah ka shayo min kan princess Wallahi in ta ce ba ta sona zan iya rasa raina." Saurin kallon shi Abdul ya yi cike da mamaki, kenan in mace ta ce ba ta sonka sai ka mutu kamar wata ɗiyar roba? Wani haushi ya ji ya ba shi ji yake kamar ya shaƙe shi saboda ya ce wai son Baby yake amma ya danne bacin ran ya ƙirƙiro murmushin yaƙe wanda ya fi kuka ciwo. Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Karka damu Suhal, ai indai Baby ce za ta ma soka in sha Allah." Godiya ya musu suka yi musahaba ya shiga mota ya tafi.. A fusace Abdul ya dawo ciki inda ya samu palon sai Iman da Hafsat suna hira, tsaki ya ja ganin yadda Hafsat ta tashi tana masa wani irin kallo ta ce "Yaya Abdul ba ko magana ma?" Bai kula ta ba ya juya ya nufi part din su yana tafiya yana jan tsaki kamar jikan tsaka. Iman ta dawo part din su Umma da tun da aka ce mata wani ne ya zo wajan Abir ta kasa zaune ta kasa tsaye ganin dalleliyar motar da ya zo da ita, ba ta ƙara ruɗewa ba ma sai da Iman ta ba ta labarin daga a har z tana yi tana murna Abir za ta auri dan sarki. A fusace Umma ta ce "Kut! Yaranmu suna nan duk sun fita komai amma ya ce sai ita yake so? To Wallahi ba zai yiyuba." Fuuu ta wuce ɗaki Iman ta bi ta kallo tana girgiza kai, ita ta ɗauka faɗa matan da ta yi za ta yi murna ne tun da kullum cewa take ba ta son ganin ta a gidan yanzu za ta bar gidan ai sai ta yi murna ba ta fusata ba. Sunkuyawa ta yi ta ɗauke parantin da Umma ta jero abinci ta kai kitchen ta dawo ta wuce ɗakinsu.. Daret masaukin shi ya nufa cike da zallar farin ciki. Yana isa wanka ya yi ya gabatar da Sallar La'asar wadda tun a hanya ya ji ana kiran Sallah, abinci ya yi magana aka kawo masa mai rai da lafiya ya ci ya ƙoshi sannan ya ɗauki computer shi ya soma duba saƙonni, sai da lokacin da zai fita su hadu da wanda za su haɗu ya yi ya rufe computer. Wanka ya sake ya saka ƙananan kaya farare da baƙar cap ya feshe jikin shi da turare masu ƙamshi ya fita.. Sai kusan karfe 11 ya dawo hotel ɗin a gajiye dan sun sha meeting sosai, abinci ya sa aka kawo masa ya ci ya koma kan gado ya janyo computer shi ya soma rubutu a wata number.. Bai fi minti uku da tura saƙon ba wata number ta turo masa saƙo. _"Oga yau dai na gano maka komai game da wannan kes din namu, ga bayanan nan na turo ma."_ Cikin zallar farin ciki ya jumƙe hananyensa duka biyun ya ce "Yess." Rufe computer ya yi Taku har kullum Mom Nusy. [6/20, 7:50 PM] Ummu Amjad: ~A HAKA NAKE SON SHI~ +966577675904 Shafi na (21) Rufe computer ya yi yana jin zallar farin ciki, can kuma sai ya ɗaga kai sama ya lula duniyar duniya. Riging wayarsa ne ya dawo da shi daga tunani, janye hannun da ya yi tagumi ya yi ya janyo wayar dan ya ga waye da daren nan yake kiran shi, ganin mai kiran ya sa ya shi jan tsaki ya aje wayar yana jin ɓacin rai na ziyatar shi. Sake kira aka yi wannan karon ya ƙara fusata ya yanyo wayar ya amsa kiran bai ce komai ba. Sai da ta sauke ajiyar zuciya yana jin ta daga cikin wayar, jin ta yi shuru ya ƙara fusata ya tashi daga inda yake zaune ya koma kan kujera ya zauna, sai da ya shaƙi ƙamshi son ran shi, so yake ya nuna mata in ta wannan ɓangaren ne ya dame ta ya shanye. Sai da ta ji dai ba zai ce komai ta yi gyaran murya yana jiyo wata murya ƙasa-ƙasa wadda ba tata ba, tsaki ya ja yana hura hanci shi fa in ba dan ba yana bin umarnin Maimartaba ta tuni ya kakkarya yarinyar nan da ba ta aiki sai yawon gidan ƙawaye, kuma wai a haka ake cewa a aura masa ita mace ba kamun kai ba tarbiya. Har ya yi niyar kashe wayar amma ya fasa kashewa jin muryar namiji yana magana. _"Haba Fauza me ya sa kika maƙale wa wannan yaron da ba ƙaunar ki yake ba? Mene ne ni bana miki a rayuwa? Duk abin da kike so ina miki ina biya miki buƙatarki da nema ina saya miki duk kayan shaye-shayen da kike so me kike nema a wajan shi? Ko ni na miki kaɗan ne bayan kin san ni din jarumi ne?"_ Riƙe baki Suhal ya yi yana nanata kalmar biyan buƙata da jarumta, kenan dai duk abin da ake faɗa akan wannan yarinyar gaskiya ne? Tsaki ya ja ya kashe wayar ya soma safa da marwa, lalle ya zama dole ma ya samu hanyar za a daina maganar auren shi da ita, in ba haka ba yana zaune lafiya za a kwaso cuta a yaɓa masa, a rayuwar Suhal ya tsani ya ga mace ba ta kamun kai ko kuma mai hulɗa da maza, sai ga shi wai shi ake son laƙabawa mai halayen da ya fi ƙyama a duniya. Numfashi ya fesar ranshi n ƙara ɓaci ya koma ya zauna gabaɗaya jikinshi ya yi sharkat da zufa, tuna abar ƙaunar shi da ya yi sai ya ji ɓacin ran na sauka ya ɗago wayar ya lalibo number ya danna mata kira. Sai da ta gama ringing ba ta ɗauka ba bai haƙura ba ya sake kira, wannan karon sai da kusa tsinkewa kafin ta ji an ɗaga kiran. Cikin magagin bacci ta ce "Hello Ya Suhal.." Ta faɗa tana ɗauke hannunta a kan wayar ta bar ta akan kunnen. Sai da ya ja dogon numfashi jin yadda muryarta ta ƙara masa daɗin sauraro, ji ya yi kamar kar ta fasa magana ta ci gaba da yi yana sauraro har sai bacci ya ɗauke shi, wani ƙayataccan murmushi ya saki sannan ya soma magana cikin nutsuwa da kamewa. "My Princess am so sorry na tashe ki a bacci ko?" Ya yi maganar yana matse pilon da ke gaban shi ya lumshe idanu. Itama ƙara shigewa ta yi cikin bargon ta tana jin bacci na fusgar ta, da ƙyar ta iya tattaro kalaman da za ta faɗa masa, ta ce "Yaya Suhal bacci." Ƴar dariya ya yi yana gyara kwanciya, sai da ya soma jin saukar numfashin ta ya gane da gaske fa baccin take ji ba wasa take masa ba, hakan ya sa ya kira sunanta ya ji ta amsa sama-sama ya ce "Princess don Allah za ki aure ni?" Shuru ya ji babu amsa ya yi murmushi ya kashe wayar ya yi addu'o'i sannan ya kwanta... A ɓangaren Abir kuwa tana jin shi da niya ta kyale ya kasa ce masa komai, wani irin bawai take jin in ta tuna maganar neman auren ta da ya yi, ba ta jima ba bacci ya kwashe.. Washegari ta shirya ta tafi makaranta, kasancewar yau tana da jarabawa dan haka duk take sauri ko abinci ba ta ci ba ta fito harabar gidan. Kiciɓus suka yi da Abdul yana son shiga part ɗin su, ɗan ja da baya ta yi ta zuba masa idanu, dam ta ji gaban ta ya faɗi ganin yadda idanuwansa suka yi jajur sai lumshe su yake yana buɗewa, a nutse ta matso kusa da shi ta ce "Good morning Yaya." Shuru ya yi bai ce mata komai ya lumshe idanu, so take ta wuce amma tana tsoron masifar shi ya ce ta raina shi, a sanyaye ta kuma cewa "Yaya ba ka da lafiya ne wai?" Ta Yi maganar murya na rawa dan ta ƙagara ta wuce school.. Sai a lokacin ta iya buɗe idanu ya zuba masa su yana jan numfashi, gabaɗaya ji yake wani irin zazzaɓi na son rufe shi har ya fara jin sanyi, fesar da zazzafar iska ya yi daga cikin shi sannan ya ce da ita, "Muje na sauke ki." Ya faɗa yana yin gaba sosai yake jin gaɓaɓɓan jikinsa na yin sanyi. Ganin ya yi gaba ta turo baki tana wani langaɓar da kai gefe kamar yana gaban ta sannan ta bi bayan shi zuwa mota, tana turo baki ta shiga gaba bsi jiira komai ba ya danna hon Maigadi ya zo da sauri ya buɗe masa suka bar gidan.. Sai da suka yi nisa da gida sannan ta ga ya gangara bakin hanya ya tsaya, da sauri ta ɗago da idanunta karaf idanunsu ya sarƙe cikin na juna, wani irin bugawa zuciyarta ke yi hango wani irin abu cikin kwayar idanuwansa. Ita ta fara janye nata idanun ta sunkuyar da kai sai ga hawaye sun soma zarya, yau gabaɗaya ta kasa gane kan Yayan nata mai faranta mata rai kullum da koyaushe, hannu ta sa ta goge ta sake ɗagowa ta dube shi, wannan karon yana kallon gefe sai ajiyar zuciya yake saukewa ita kanta ta tsorata ta gani yadda y sauke numfashi kamar mai irin cutar ta ta asma in ta tashi. A hankali ta ɗaura hannunta kan nashi ta soma shafawa kamar wanda wani abu ya cije shi, dogon numfashi ya sauke ya lumshe idanu, wani irin yanayi yake ji mai wuya fassarawa a baki. Murya na rawa ta kuma cewa "Yaya are you OK?". Wani irin rawa ya ji jikinshi ya ɗauka bai san lokacin da ya janyo ta ya rungume ta ba, sosai ya shigar da ita jikinsa yana sauke numfashi da sauri-sauri.. Waro idanu ta yi jin yadda yake matse ta kamar ya samu ɗiyar roba, mutsu-mutsu ta soma yi jin yana shafa mata baya tsoro ya shige ta ta ce "Y...Ya..Yaya.." Ta ja sunan cikin wani kalar firgici.. Ƙara matse ta ya yi ya ɗaura kan shi a kan kafaɗarta ya lumshe idanunsa, hawaye ne suka cika masa idanu suna shirin zubewa ya soma ƙoƙarin mayar da su amma ina tuni har sun ɗigo a gadon bayan ta. Da ƙyar ya saita nutsuwar shi jin yadda take kuka tana kiran sunan shi, a hankali ya ɗago kanshi ya sa hannu ya tallabo fuskarta ya ƙura mata idanu, wani irin zaro idanu Abir ta yi ganin sawun ruwan hawaye a kan kumtunsa ta kai hannu ta taɓo dan tabbatarwa, da gaske dai hawaye ne a fuskar Yayan nata cikin tashin hankali ta soma tambayar shi. "Yaya wai me ke faruwa ne? Hawaye fa na gani da kan kuncinka Yaya, shin wani abin ya faru marar kyau?" Ta jeru masa tambayoyi tana kafe shi da idanu, gabaɗaya ji ta yi zuwa makarantar ma ya fitar mata a rai sakamakon ganin hawayen Yayan nata mafi soyuwa a rayuwarta.. Wani yawu mai ɗaci ya haɗiya sannan ya ce "Ba komai Baby, kawai dai kaina ne min wani azababben ciwo, kuma kin san dai in ina ciwon kai haka idanuna ke fitar da ruwa." Dogon Numfashi ta ja ta yi fuskar tausayi ya ce "Amma dai har da zazzaɓi ko?" Ta yi maganar a sanyaye. Gyaɗa mata kai ya yi bai kuma bari ta masa wata tambayar ba ya daure ya kunna motar suka ci gaba tafiya. Suna ƙarasawa School ta fito ta rataya handbag ɗinta ta sunkuyo suka haɗa idanu ta ce "Yaya please ka je Asibiti a duba min lafiyar ka kafin ka isa office." Gyaɗa mata kai kawai ya yi ya zuge glas ɗin ya wuce.. Ji ya yi kamar kar ya je aiki yau, amma ba yadda ya iya saboda yana da aiyuka masu tarin yawa a office dole ya je ya samu ya ɗan rarrage ko ba yawa ne. Zaune suke a babban wani palo su uku palo ya kacame da hayaniya. Alhaji Mustapha ya miƙe tsaye ya ce "To billahillazi ba zai yiyuba, taya a matsayin ka na babba da mu a wannan harkar ace kai ne za ka fara taka dokokin wannan lamarin? To b zai yiyuba ka yi abin da Nadumbuza ya ce in har kana son zaman lafiya. Ka samo inda aka ɓoye yaron nan tun da jinin ɗanka ba shi da ƙarfi kamar wancan mahaukacin, in kuma ba haka ba duk za ka jaza mana masifa." Ya ƙarashe maganar cikin tsananin fushi kamar zai kai wa Alhaji duka.. Alhaji ya yi shuru yana nazari can ya ɗago ya kalli Alhaji Mustapha ya ce "Hmm wato duk ƙoƙarin da nake ba ku gani ko? Ni yanzu ba wannan ba ne ba ma abin damuwa ta nasan za a samo min inda wannan taƙadarin yaron ya ɓoye shi, duk wani motsi in na yi yana biye da ni so yake ya samu kafa ɗaya da zai kama ni da lefi amma bai san cewa wanda ya riga ka bacci dole ya riga ka tashi, na kusa kawo ƙarshen rashin kunyar shi very soon. Jarmai ya kaɗa kai yana jin tsananin tsanar Abdul, a fusace ya ce "Oga ka faɗa mana me yake faruwa bayan neman yaron da muke?" Gyara zama ya yi yana yin kwafa ya ce "Abu mafi girgiza hankali shi ne Damisa ya diro Nigeria, kuma zuwan da ya yi ba wai irin na baya ba ne, wannan karon da zafin sa ya dawo jiyar nan ya sauka amma ya gano sirrikan mu dayawa, kuma gaf yake da gano inda muke ban san ta wata hanya za mu ɓullowa lamarin ba. Matsala ta gaba kuma wannan shegiyar yarinyar da duk wata kadara ta Ibrahim ke hannunta wani yaro daga Niger y zo neman auren ta, kuma an amince masa a gidan ita kawai suke jira. Idan har muka bari ta bar ƙasar nan da takardun nan to tabbas wata rana za ta buɗe su har ma'adanan sirrin da duk wata ɓarnar da muke Ibrahim ya naɗi komai, in fa ba mu tashi tsaye ba akwai matsala." Ya ƙarashe maganar zufa na tsatsafo masa y yi sharkaf kamar ruwan sama ya dake shi.. Dukkan su ba wanda bai shiga tashin hankali ba musamman jin labarin Damisa ya dawo Nigeria, Jarmai ya tashi tsaye ya ya buga tebirin da ke gaban su shi kan shi ya ji mugun tsoro na shigowar Damisa gari, kallon su ya yi ya ce "To abin da za ayi kawai, mu sa a kashe shi kada mu bari wannan karon ya sake guduwa ba tare da mun aika shi can ba. Itama ya kamata wannan karon mu kwato komai daga gare ta mu kashe su daga ita har ɗan'uwan nata, kai har uwarta ma mu kashe dan ita uwar ta fi yar sanin komai game da mu. Shi kuma yaron nan mu san yadda za mu sato shi. " Murmushi Alhaji ya yi ya ce "Jarmai kenan, har yau ka kasa gane waye Damisa mutumin da ko fuskarsa mun kasa gane wata kala ce. Ko kai ka taɓa ganin fuskar Damisa babu takunkumi?" Shuru Jarmai ya yi Alhaji Mustapha ya ce "Dole fa mu samo wata hanyar, amma Oga tun da muna da mana aiki ita mace ce mai zai hana mu nemi wani abu daga wajan Barru? kasan fa wani lokacin kan ta kawo wuta?" Gyaɗa kai Alhaji ya yi tare da cewa, "Hakan ya yi sosai zan same ta mu tattauna abin da ya biyo baya sai na sanar da ku, shi kuma Abdul na gano tarkon da zan ɗana masa ya faɗa tun da mun tura masa Juju babu abin da ya faru da shi. Tabbas wannan karon ba zai kuɓuta daga tarko na ba, har ita yarinyar duk na samu masa mafita ita ma zan sa Barru ta yi wani abu game da ita, kun ga kenan abin da ya rage masa guda biyu ne. " Kowa jinjina kai yake cike da gamsuwa da maganar Alhaji, Alhaji Mustapha ya ce" To amma wani irin tarko ne za ka yi wa Abdul? " Dariya Alhaji ya yi yana zagaye su ya dawo ta gefen Jarmai sannan ya ce" Ba ina da 'ya ba? " "Kwarai haka ne." Suka faɗa a tare, ya ɗaura "To ita ce makami na, Hafsat tana tsananin son Abdul amma tsoron shi da take ne ya sa ta ɓoye, dalilin shishige masa da take yi ne ya ce kar ta ƙara zuwa gidansu ya yanke ƙawancan su da Abir, yanzu kuma ita da kanta Abir ɗin ta nemi Hafsat dan haka wannan dama ce babba a gare mu dan samun abin da muke so." "Gaskiya wannan shawara ta yi." Cewar Jarmai yana yi wa Alhaji jinjina. Dariya duk suka sa Alhaji ya kalle su ya kaikaice hular shi ya kai ta gidan tara ya ce "Ni fa gaskiya ina son ganin ƴar shila ta a kusa da ni, dan haka yanzu zan sa a kawo min ita nan na more." Dariya suka kuma sawa suna tafawa, Jarmai ya ce "Gaskiya ko ni ma ina da buƙatar hakan." Alhaji ya ce musu duk zai sa a kawo musu mata uku, ya kira waya ya ce kawo musu. Suna nan zaune suna hira sai 'yan mata guda uku duk an rufe musu idanu da wani kyalle, ciki Alhaji ya nuna musu suka kai kowacce ɗaki ɗaya sannan suka fito suka tafi.. Dukkan su tashi suka yi kowa ya nufi ɗakin da yake mallakinsa ne in sun zo gidan, Alhaji yana shiga ya samu yarinyar zauna ganin shi ya sa ta miƙe tsaye tana kallon shi, shafa ƙasumbarsa ya yi yana ƴar dariya ya ɗauko wani turare a aljihunsa ya fesa mata a jiki. Kanta ne ya dinga juyawa ta lumshe idanu ya tafo ya rungume ta yana lumshe idanu, gani ya yi ta ƙara girma ta yi wani irin haske ko'ina na jikinta ya ciko ga zafin jikinta, a hankali ya ce "Sweet girl ba ki da lafiya ne?" Buɗe idanuwanta ta yi ta sauke a kan shi, duk da ba a haiyacin ta take ba amma ba ta kasa ba shi amsar tambayar shi ba.. "Ba ni da lafiya ciki ne da ni." Da sauri ya kalle ta yana nanata kalmar ciki, kamo hananyenta y yi ya ce "Karki damu mu huta zan sa a zubar da cikin daga nan ma ake baki ƙwayoyin hana ɗaukan ciki." ƙura masa idanu ta yi ta kasa cewa komai sai kawai ta yi baya ta zube a kan gadon, dariyar 'yan duniya ya yi ya bi ta kan gadon. Tana jin sa yana bidirin shi amma ta kasa ko da motsa yatsar ta ne, so take ta kwace jikinta amma sam ta kasa sai kukan zuci da take.. Bayan y gama ya ɗauke ta ya kaita toilet da kan shi ya mata wanka shi ma ya yi suka fito. Wasu kaya ya ɗauko mata riga da wanda zuwa lokacin ta fara dawowa haiyacin ta ya ce ta sa, ba muso ta saka tana layi kamar ƴar maye sai lumshe idanu take. Waya ya yi ya sanar da likitansa ya zo ya same shi a gidan gonar shi sannan ya kashe, suna nan zaune ya ji kira ya shigo wayar shi ya ɗauka nan yake sheda masa ya zo. Hannunta ya kama suka fito haraba gidan inda suka same shi zaune a kan kujera cikin rufar da suka saba zama, kasancewar ya masa bayanin komai ya buɗe jakar da ya zo da ita ya zaro allura ba ɓata lokaci ya mata, sannan ya ba ta magani tare da miƙa mata ruwan da ya tarar a kan tebirin yana kallon ta ta shanye tas tana zubar da hawaye. Bayan ta sha ya mayar da ita ɗaki ya ce in ta ga jini ya soma zuba ta shiga toilet zai zo ya taimaka mata, ita kuwa da idanu kawai take bin shi har ya gama mata jawabi ya tafi.. Bayan kamar minti 40 ta soma jin cikinta yana murɗawa ta runtse idanu tana yarfa hannu, ta rarrafa ta shiga toilet nan jini ya ɓalle mata kamar ruwa haka yake zuba, tun tana sanin a inda take har ta fita daga haiyacin ta jini ya ci gaba da zuba. Alhaji ya leƙo ya ganta kamar gawa ya koma da sauri ya kira Likita suka zo a tare, tattaɓa ta ya yi ya ji ba ta numfashi ya kalli Alhaji ya ce "Da alama fa yarinyar nan ta mutu, dan ni ban ji tana numfashi ba." A ruɗe Alhaji ya kalli Likita ya cakumi wuyan rigarsa ya ce "Kar ka bari na rasa ta dan tana da mahimmanci a wajena." Ya sake shi yana huci ya dawo kanta ya jijjiga ta yana faɗin "Sweet girl ki tashi mana kar ki min haka, in kika mutu a ina zan ke samun jin dadin da nake samu a gare ki?" Girgiza kai Likita ya yi yana kallon Alhaji, wai yau Alhaji ne yake damuwa da yarinyar da ya sa a zubar mata da ciki? "Sai dai ka nemi wata dan wannan ba lalle tana da rai ba, yanzu bari na ɗauke ta mu tafi Asibiti in ta mutu kuma kawai mu san yadda za ayi a rufe komai." Ba dan Alhaji ya so ba ya bari Likita ya sunkuce ta suka fita ya saka ta a mota suka bar gidan.. Ƙarfe uku Suhal ya kira Abdul ya faɗa masa yaushe zai kai shi ya ga Zaiyan? Lokacin ya taso daga office ya faɗa masa su haɗu a makarantar su Abir zai je ya ɗauko ta itama ta gan shi ya masa kwatance sannan ya kashe. A tare suka iso School din lokacin itama ta fito tana leƙo waje sai ta ga Abdul, da sauri ta fito ta shige motar shi tana masa barka da zuwa ya gyaɗa mata kai, ta kuma tambayar jikinshi nan ma kai ya gyaɗa mata sai ta ja bakin ta ta yi shuru. Suhal ya fito daga motar da ya hayo ya biya mai motar ya nufo su, sai a lokacin ta lura da shi ta ɗaure fuska tana turo baki, kallon ta Abdul ya yi bai ce komai ba hr Suhal ya buɗe baya ya shiga tare da yi musu Sallama. Sai a lokacin Abdul ya amsa masa ita kuma ta yi kamar ba ta ji shi ba, murmushi ya yi ya ce "Princess how are you today?" Da kyar ta ce "fine." Jan motar ya yi suka nufi Asibitin da aka kai Zaiyan, suna isa suka fito suka nufi ɓangaren da yake. A kwance suka same shi yana bacci, Suhal da yake danna waya ya ɗago ya kalli Zaiyan, a razane ya ja da baya yana nuna shi ya yi saurin isowa gaban gadon y shafa fuskar Zaiyan, wani irin faɗuwa gaban shi ke yi ya ƙura masa idanu. Abir ta yi murmushi ta ce "Ka gani ko Ya Suhal? Ai na ce ma dama abu kaɗan ne ya bambanta ku." Gyaɗa kai ya yi yana janye idanuwansa daga kan fuskar Zaiyan ya ce "Tabbas na gani Princess, Allah mai halitta sai ya yo mai kamar ka sak sai dai hali ko wani abu ya ɗan bambanta ku." Ya faɗa yana komawa bakin ƙofa y ci gaba da kallon shi. Zai sake yin magana suka ji an buɗe ƙofar an shigo, da sauri Suhal ya juya dan ya ga waye ya shigo. A daddafe ta rufo ƙofar tana haki, Suhal y dube ta ya ce " Baiwar Allah lafiya kika shigo nan? Ko dai kin manta ɗakin jinyar ki ne?" Jin surutu a bakin ƙofar ta ƙaraso kusa da Suhal ta soma magana tana rarrabewa, "D.. Dan Al.. Allah.. K.. Kar ku ce ina nan, za su kashe ni." Tana ƙarasa maganar ta yi baya luu ta zuba a ƙasa. A ruɗe suka yo kan ta, Abir ta janye gashin gashin da ya rufe mata fuska, a razane Suhal ya kalle ta cikin kiɗima ya ce "Sajida... Taku har kullum Maman Nusy. [10/23, 10:20 Yamma] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): ~A HAKA NAKE SON SHI~ +966577675904. Shafi na (22) Kallon shi Abir ta yi jin abin da ya faɗa, ɗago da ita ta yi ta dubi Suhal da ya ƙame a tsaye kamar soja ta ce "Ya Suhal ka san ta ne?" Girgiza kai ya yi ya ƙaraso kusa da ita ya sa hannu ya amshe ta daga hannun Abir, hawaye masu ɗumi ne suka silalo daga kwarmin idanuwansa ya ɗiga kan fuskarta, huci yake yana ƙara rungume ta kamar wani zai kwace ta daga gare shi ya ɗago ya kalli Abir da Abdul da suka yi ƙiƙam suka kallon ikon Allah ya ce "Princess na san ta ita ɗin matata ce tun shekaru biyar da suka wuce." Ya faɗa yana shafa bayan ta, jin ya taɓo danshi a gefen cikinta ya yi saurin kallon hannun, jini ya gani ya waro idanu ya sake kallon gefen cikin sai lokacin ya ga jini duk ya jiƙa mata doguwar rigar Asibitin da ke jikinta, a ruɗe ya ce "Sajida waye ya miki haka." Dogon numfashi ta ja tana juya kan ta cikin tsananin ciwo ta soma buɗe idanu, ganin fuskar wanda yake riƙe ta ita ya sa ta ƙara buɗe idanun tana yatsina fuska, ɗago da ita ya yi dan ta kalle shi da kyau yana goge hawaye ya jingina ta da gefen kafaɗarsa. A sanyaye ta ce "Suhal." Gyaɗa mata kai ya yi ya ce "E nine, Sajida ashe kina raye ?" Fashewa ta yi da kuka ta faɗa jikinshi ya yi saurin ɗago ta yana girgiza mata kai ya ce "Tell me Sajida duk tsayin shakarun nan a ina kike? Kuma waye ya kawo ki Asibiti?" Su dai su Abir sun zama 'yan kallo dan haka ta ƙaraso gadon da Zaiyan yake kwance ta zauna a gefe ta rafka tagumi tana kallon Sajida da jini ya ɓata mata riga, gabaɗaya ji ta yi ta ba ta tausayi ta goge hawayen da suka zubo mata tana sauke ajiyar zuciya. Ganin taƙi yin magana Abdul ya zaro wayarsa daga aljihu ya kira Likita, bayan ya ɗaga ya sheda masa ya zo ɗakin da Zaiyan ke ciki sun zo ya amsa da to sannan ya kashe kiran.. Bai fi minti ɗaya ba sai ga shi ya buɗe ƙofar ya shigo bakinshi ɗauke da sallama suka amsa, zabura Sajida ta yi Suhal ya shigar da ita jikinsa ganin yadda ta firgice ya ce "Likita ne fa." Kallon ta Likita yake yi cike da mamaki har ya kasa ɓoyewa ya ce "Wannan ba majinyaciyar mu ba ce mai matsalar ƙwaƙwalwa? Me ya kawo ta nan ɗakin?" Ƙara riƙe Suhal ta yi tana gunjin kuka ta ce "Wallahi ni ba bahaukaciya ba ce da hankali na aka mayar da ni mai taɓin hankali." Wani irin kallo Suhal yake yi wa likitan wanda ya sa 'yan hanjin Likita kaɗawa, shafa kanta ya yi ya ce "Ai ko ma waye ya mayar da ke mahaukaciya sai na gano shi na ɗauki mummunan mataki a kan shi, ashe duk tsayin lokacin nan kina raye muke neman ki har mun gaji mun miki sadaka mun ɗauka kin mutu ashe kina nan a raye? Kai kuma na dawo kanka." Ya nuna likita cikin zallar ɓacin rai ya ci gaba "Yau sai ka faɗa min wanda ya kawo muku ita a zaman mahaukaciya." Ya faɗa a zafafe yana nuna shi da yatsa.. Ganin abin zai tada cecekuce Abdul ya ce "Ka kwantar da hankalin ka mana Suhal, ka bari yanzu tukun ya duba lafiyarta in yaso sai ayi maganar." "Ba dai a Asibitin nan ba za a duba ta? Ni zan duba ta da kaina." Da mamaki Abdul ya kalle shi ya ce "To kai likita ne dama?" "Yes I'm doctor." Ya faɗa yana huci ya sake cewa "Zan iya tafiya da ita masauki na akwai kayan aikina a cikin kayana zan mata komai." Ya faɗa yana tashi tsaye ya miƙar da ita ta ƙwalla ƙara tana dafe mararta tana juya kai cikin azaba. Da sauri Abir ta sauko ta iso wajan su ta kamo hannun Sajida ta dubi Suhal da ya riƙe ta ta ce " Ya Suhal ka bari please a duba ta a nan, ka ga fa jini a jikinta bai fasa zuba ba in ka ce sai ka je masaukin ka to za ka iya rasa ta gabaɗaya." Ajiyar zuciya ya sauke ya raba ta da jikinsa Abir ta kama ta ta dubi Likita ta ce "Likita muje ka kaimu inda za a duba ta." Jiki a sanyaye Likita ya ce "Ok muje to." Har zai bi bayan su Abdul ya hana shi ya bi bayan su, shi kan shi so yake ya san wace ce Sajidar nan da Suhal ya ƙidime da ganin ta kuma ya ce wai matarsa ce da haka dai ya iso bakin ƙofar ɗakin da aka saka ta Abir ma na tsaye a wajan tana safa da marwa, kusan minti 30 ba su fito ba Abdul ya ce ta koma ta kawo Suhal su za su tsaya da shi ita kuma ta zauna a wajan Zaiyan, to ta ce ta koma ɗakin ta same shi yana kaiwa da komowa ganin ta ya sa ya soma tambayar ta. "Princess ya jikin nata." Sauke hannayenta ta yi daga ƙirji ta ce "Tukunna dai, Yaya ya ce na kaika ku tsaya a can ni na zauna a nan.". Da sauri ya ce "To.. TO mu je ki kaini." Jagora ta masa har bakin ƙofar ta nufo ɗakin za ta koma suka yi kiciɓus da Hafsat, riƙe baki Hafsat ta yi tana ƴar dariya ta ce "Su Baby manyan gari, wa kika kawo Asibiti?" Murmushi ta yi tana ɗan yarfa hannu ta ce "Babu kowa kawai dai mun zo duba wani friend ɗin Yaya ne." Jin abin da ta faɗa ya sa Hafsat kallon bayan Abir, ganin ba ta ga Abdul ɗin ba sai ta harare ta ta ce "Kai ƙawata ban san ki da ƙarya ba, ina Yaya Abdul ɗin yake?" Ganin tana ɓata mata lokaci ya sa ta ce "Ya tafi wajan mara lafiyar ni kin ga sai an jima tafi abin ki zan neme ki a waya in na koma gida." Tana faɗin haka ta wuce ta bar Hafsat tsaye a wajan cikin son ganin Abdul, amma ba yadda ta iya dole ta tafi.. Tana isa ta samu ya soma buɗe idanunsa, da sauri ta matso jikin gadon tana murmushi. Yana buɗe idanu da ita ya fara yin arba ya mayar ya lumshe ya sake buɗe su a kan ta, ƙoƙarin tashi ya soma yi ta taimaka masa ya tashi ta kara masa pilo a bayan shi ya jingina da gadon, a hankali ya ɗago ya kalle ta ya sakar mata da kyakkyawa murmushi yana miƙa mata hannunsa. Kama hannun ta yi tana mayar masa da martanin murmushin ta ce "Sannu Zaiyan ya jikin naka? " Murmushi mai sauti ya sake yi a karo na biyu, sai da ya haɗiyi yawu sannan ya soma magana da muryarsa mai mata daɗi in tana sauraron shi a duk lokacin da yake magana. "Anty a gidana kike?" Ya faɗa yana tattaɓa fuskarta. Ƴar dariya ta yi cike da jin daɗin ya tashi ta sauke hannunsa daga kan fuskarta ta kai hannu za ta gyara masa rigarshi da ta dan saɓule daga wuya farar fatarshi ta bayyana, tana ɗaura hannunta a kan shi ta ji wani chok ya kama ta ta yi saurin ɗauke hannun tana sauke numfashi, a hankali ta dube shi ta ga ita yake kallo ta sakar masa murmushi ta ce "Ka yi kewa ta ko?" Gyaɗa mata kai ya yi yana yin dariya, za ta sake magana ta ga ya zare allurar ƙarin da ake masa ya zauna a tsakiyar gadon ya ci gaba da kallon ta. Cike da mamaki take kallon shi, ta ce "Me ya sa ka cire ƙarin ruwan?" "Ba ya buƙatar hakan dan cutar da shi ake ba wai ruwan ba ne ake sa masa guba ce." A ruɗe Abir ta ɗago jin wata murya a gefen Zaiyan, matar da ta gani ranar nan ta gani ta bayyana cikin shigar ta ta fararen kaya. Wannan karon Abir ba ta ji tsoro ba ganin an ɗauke wutar ɗakin, ajiyar zuciya ta sauke ta lalibo Zaiyan ta kama hannunsa ta riƙe gam, hasken jikin matar shi ne ya haske ɗakin kamar an haska fitila. A ɗarare Abir ta ce "Baiwar Allah wai ke ɗin wace ce?" Gaban ta ta dawo ta kalli Zaiyan ta ce "Ki daina gaggawa Hauwa'u Maijidda zan sanar da ke komai, har ma abin da ya shige miki duhu duk zan sanar da ke game da wannan bawan Allah." Ta nuna Zaiyan ta ci gaba "Tabbas na san zuciyarki tana raya miki abubuwa da dama a kaina, za ki ɗauka ko dan na cutar da ku nake tare da ku, ni kuma ina tare da ku ne dan na taimaka muku." "Ta yaya za ki taimaka mana bayan ban san ke wace ce ba? Kuma kin ga wannan ba shi da lafiya yana cikin halin taɓin hankali don Allah kar ki cutar min da shi." Murmushi ta yi ta harɗe hannunta a kan ƙirji ta ce "Maijidda, ina da tarin maganganun da zan sanar da ke, amma hakan ba zai yiyuba kasancewar ba ni da lokaci zan bari sai wani lokacin na sanar da ke komai, amma zan dinga bibiyar rayuwarki dan na taimaka miki ke da shi. Idan Yayan ki ya zo ki ce masa ya sa a sallame ku ku tafi gida maganin Asibiti ba zai taɓa warkar da shi ba, ku koma gida ba yanzu zai samu lafiya ba sai nan da wani lokacin hakan kuma ba zai yiyuba har sai kuna tare a waje ɗaya, idan har kika bar shi kika tafi wani wajan da zama to tabbas samun lafiyarsa ba lalle ya samu ba ballantana ki san shi ɗin ɗan waye? Daga ina ya fito? A wani gari yake? Ki yi nazari Hauwa'u Maijidda. " Tana gama faɗin haka ta ɓace ɓat a wajan sai ga wutar ɗakin ta kawo.. Dafe ƙirji ta yi tana juya maganar a cikin zuciyarlrta, gwauron numfashi ta sauke tana ɓata fuskar kamar za ta saki kuka ta ce "Babu wanda yake ba wa wani lafiya in ba Allah ba, idan har da sharri kike bibiyar rayuwarmu Allah ya yi mana tsakani da ke, in sha Allahu kuma zai warke ras ya yi rayuwa irin na kowa na kaishi gun ahalinsa ni da Yayana da yarda Allah." Ta ƙarashe maganar tana hura hanci, gabaɗaya ma ji ta yi matar nan ta ba ta haushi, ta zauna shi kuma ya matso kusa da ita ya ɗaura kan shi a kan kafaɗarta, ganin haka ya sa ta ɗago shi tana shagwaɓewa ta ce "Kai indai ina kusa da kai ba ka da wajan zama sai jikina kamar wata mamanka?" Ta ƙarashe maganar tana cuno baki. Hannu ya kai ya taɓo bakin nata ya yi dariya ya ce "Mamata ce ke Anty?" Dariya ta saki ba shiri, bayan Antyn da yake ce mata yau kuma ta koma Mama? Taɓe baki ta yi ta ce "Tab ƙato da kai zan haife ka? Ni ai Anty nake ba mama ba ka ji ko!" Ta faɗa tana zaro masa idanu irin ga Uwarsa tana masa kashedi.. Gira ya ɗage mata ya ce "Tab ƙato da kai zan haife ka? Ni ai Anty nake ba mama ba ka ji ko!" Dafe kai ta yi jin ya maimaita abin da ta faɗa ta kafe shi da idanu tare da yin tagumi, shi ma kamar yadda take kallon shi ta yi tagumi haka ya yi, sauke hannun ta yi tana ɓata rai ta ce "Idan na yi magana kar ka sake kwaikwayo na, idan ka sake zan dai kula ka." Kamar jira yake ta dasa aya ya maimaita yana wasa da zoben hannunsa fara sol wadda aka rubuta sunan *Abir* a jiki, da mamaki ta kalli hannun nasa ganin wata zoben bayan wadda ta sa masa mai sunan ta, ita wannan ruwan gold ce sai sheƙi take yi, kamo hannun ta yi tana duba zoben ta ce "Zaiyan waye ya saka maka wannan zoben?" Kallon hannunsa ya yi yana ɓata fuska ya ce "Zaiyan waye ya saka maka wannan zoben." Dafe kai ta yi tana rufe idanu, gabaɗaya ita ba ta so in ta yi magana a kwaiwaye ta sai ga shi shi kuma Zaiyan da Allah ya jarabce shi da hakan sai ya kwaikwaye ta, ta ɗago za ta masa magana ta ji an turo ƙofar ta juyo ta ga su Suhal ne.. Kallon shi Suhal ya yi ganin yadda yake shige wa Abir sai abin ya tsaya masa a wuya, tunawa da shi ɗin ba mai hankali ba ne sai ya sauke ajiyar zuciya ya ƙaraso kusa da su ya tsaya yana kallon Zaiyan, so yake ya ɗago fuskar shi su haɗa idanu hakan ya sa ya yi gyaran murya ya soma magana. "My Princess an jima zan koma Niger tare da Sajida." Da sauri ta kalle shi sai yanzu ta tuna da kalmar da ya faɗa na matarsa ce Sajida, wani iri ta ji ta kalle shi cike da kunyar maganar da za ta fito daga bakinta, ƙasa ta yi da kai ta ce "Sorry to say Ya Suhal." "OK tell me." Ya faɗa yana kafe ta da na mujiya. "Ya Suhal na ji ka ce wannan baiwar Allah matarka ce." Gyaɗa mata kai ya yi duk da ba kallon shi take ba, sai ta ci gaba. "Kenan in kuka tafi ka janye maganar auren nawa?".Wani irin ƙayataccan murmushi ya yi ya shafa sajansa, kenan Princess ɗin tasa tana son shi take ɓoye masa? Wani irin daɗi ya ji ya gyara tsayuwar shi cikin nutsuwa kamar ba shi ba ne yanzu ya ruɗe da ganin Sajida ya ce "Princess kenan, to dan kawai na ga matata sai na janye maganar auren ki? Ai ni da ke miji da mata ne in sha Allah zan kuma tabbatar miki da hakan idan na koma Niger nan da sati ɗaya Maimartaba zai turo a nema min auren ki, kuma bana son a sa lokaci mai tsayi. Sannan maganar Sajida ki aje a gefe Allah ya ba ni damar auren mata ɗai-ɗai har guda huɗu, kin ga kuwa dan ina da Sajida ba zan ƙi auren ki ba my Princess ɗina.." Ya ƙarashe maganar yana murmushi, ya ji daɗi da ta nuna masa hakan ko ba komai yanzu zai daina kokwanto akan soyayyar shi da ita.. Ajiyar zuciya ta sauke, ita fa ba wai dan kishi ta masa hakan ba, so take ta san taya suka haɗu har aka musu aure? sannan kuma taya aka neme ta aka rasa tsayin shekaru 5 cif? Kallon shi ta yi ta ce "Ina son naji shin taya aka sace Sajida?" Murmushi ya yi ya ce "Zan faɗa miki yanzu dai an sa mata ruwa da allurori ya ma kusa ƙarewa, minti kaɗan za a sallame mu sai mu zauna mu ji komai daga bakin ta ni ma na faɗa miki yadda muka yi soyayyar mu da ita." Ɓata fuska ta yi ta harare shi ya yi dariya, Zaiyan ya kalli Suhal bai ce komai ba yana zaune a gefen ta kamar ba ya ɗakin, sai da Suhal ya ce "Zaiyan ya kake?" Saurin ɗagowa ya yi ya kalle shi ya maimaita abin da ya faɗa masa yana dariya. Idanu ya zuba masa ganin yadda komai nasa irin nashi ne, ji ya yi kamar an zare masa kuzari ya ja ƙafar shi ya isa gare su ya kamo hannun shi ya sauko da shi daga kan gadon, tsayar da shi ya yi a gefen shi ya kalli Abir wadda ita ma su take kallo ya ce "Ya kika gani Princess?" Yatsarta manuniya da ta gefe ta haɗe ta miƙe uku tare da yin murmushi ta ce "Kamar 'yan biyu ma sha Allah." Ganin yadda ta yi sai Zaiyan shi ma ya yi yana dariya maimaita abin da ta faɗa, sai kuma ya matsa daga jikin Suhal yana nuna shi da hannu ya matso kusa da Abir ya ce "Anty kin ga wannan babban yana taɓa min hannu." Ya faɗa yana daddaga hannunsa akan goshin Suhal ya dawo inda take ya tsaya tare da saka yatsu biyu a baki ya ci gaba da kallon Abir.. Ƴar dariya Suhal ya yi ya ce "Allah ƙadiran wa muridan! Wai har shan yatsu yake kamar wani ɗan goye?" Dariya ta yi ta ce "Wallahi fa wani lokacin yana yin haka idan wani ya taɓa shi." Gyaɗa kai Suhal ya yi ya ce mata zai koma ya dauko Sajida sai su tafi ta amsa da to ya fita... Ba su jima sosai ba sai ga su sun shigo Sajida na haƙaƙarin Suhal yana jera mata sannu, ganin haka ya sa Abir ta wurga masa harara ta ce "To kawo ta nan sarkin marassa kunya." Sosa kai ya yi ya janye jikinshi daga nata Abir ta tallafo ta ta kai ta bakin gadon ta zaunar, kallon Abdul ta yi da ya gama waya akan shigar da kes ɗin Sajida ya kalle ta, haɗe rai ta yi ta ce "Yaya ka sa a sallami Zaiyan mu tafi gidan su Inna.". Da mamaki ya kalle ta ya ce "Baby me ya kawo kuma maganar a sallame shi bayan bai gama shan magani ba?" Ƙara murtuke fuska ta yi irin ba wasa ɗin nan ta ce "Ni dai na faɗa ma ba na son zaman shi a Asibitin nan kwata-kwata mu koma gida." "To idan naƙi fa?" "Ba ma za ka ƙin ba ai, ka ce a ba shi sallama ko kawai mu tafi ba sai an ba shi sallamar ba, ni fa gabaɗaya ma Asibitin nan bana ƙaunar ta ko kaɗan mu tafi gidan su Baba. In kuma ba za ka iya faɗa wa Doctor ɗin ba ni sai na je na masa bayani da kaina." Sake da baki suke kallon ta, ganin ta ci gaba da faɗa ya sa Abdul cewa su tafi kawai, hannun Sajida ta riƙe shi kuma Suhal ya kama Zaiyan da nufi ya riƙe shi ya ce sam ba zai yarda wani ya riƙe shi ba bayan Antynsa, dole ta haƙura da riƙe Sajida ta kama hannunsa Suhal tuni dama ya yo gaba ya bar su, Abdul ya ce shi su isa motar ita kuma ta zo su suje ya sanar da likita ya ba su takardar sallama.. Suna fitowa ya yi saurin ɗauko wani kyalle ya rufe fuskarsa ita ma ɗankwalin da ke kanta ya janyo ya rufe mata fuska suka yo wajan motar. Kiciɓus suka yi da Alhaji har yana gogar Sajida, a fusace Suhal ya juyo ya cikin kakkausar murya wadda bai san yana da ita ba ya ce "Malam ya kana tafiya kana kaɗar mutane ba ka gani ne? Ko makaho ne kai?" Ɗago kai Alhaji ya yi yana kallon Suhal da yake shafa mata inda ya goge ta sai huci yake, zaro idanu Alhaji ya yi ganin Sajida jiki na rawa ya ce "Sweet Girl! Ina kika shiga tun ɗazu nake neman ki hankalina ya tashi?" Ya yi maganar yana son taɓa ta. A zabure Suhal ya make masa hannu ya ce "Are you mad? Matar tawa za ka taɓa har kake cewa wai sweet girl?" Saurin janye hannunsa ya yi yana ƙifƙifta idanu, ko dai idanuwansa ba daidai suke gano masa ba? Kamar ita yake gani fa ga kayan nan irin nata, Numfashi ya sauke ya ce "Am sorry yaro, na ɗauka 'yata ce da na kawo Asibiti ta fito ashe ba ita ba ce kayan ne iri ɗaya." Wani irin dogon tsaki ya ja ya wuce ya saka ta a mota shi ma ya shiga ya rufo glas ɗin motar ya cire kyallan yana mayar da numfashi.. Ƙiƙam Alhaji ya yi yana bin motar da kallo wadda yake mata ganin kamar ta Abdul ce, dafe kai ya yi jin kira na shigowa wayarsa ya ja tsaki ya tsaya kamar wani yake jira.. Abdul da Abir suna isa Office ɗin babban likitan suka yi nocking ya ba su izinin shigowa, a nutse Abdul ya murɗa ƙofar suka sayo kai ciki bakunansu ɗauke da sallama. Ɗago da kai ya yi yana duban su, ganin Abdul ne ya sa shi sakin fuska yana musu barka da zuwa suka amsa tare da zama. Yadda ya riƙe mata hannu sai ta ji ba za ta iya zama ba sai ta tsaya a tsaye ganin Doctor ɗin yana kallon Zaiyan, haɗe rai ta yi tana turo baki gaba ta kalli Abdul ta ce "Yaya ka faɗa masa ni so nake mu tafi." Ta Yi maganar kamar za ta sa kuka saboda mugun haushin kallon da yake yi wa Zaiyan ɗin take ji. Kallon ta ya yi yana yin murmushin gefen bakin, dawo da kallon shi ya yi ga Doctor dan kar ta tada masa rigima ya kasa rarrashin ta, ya san halin ta sarai na kafiya akan abin da take son yi ko za a mata dan haka ya nisa tare da sake ɗaure fuska kamar ba shi ba ne yanzu ya yi murmushi ya yi gyaran murya ya ce "Doctor ina so ka rubuta mana sallama, Baby ta ce ba ta son zaman shi a Asibitin." Ya ƙarashe maganar yana satar kallon ta ta gefen idanu.. Da mamaki Doctor ya kalli Abdul sai kuma ya aje biron da ke hannunsa ya ce "To amma na ga ai bai gama shan maganin da na rubuta masa? Ya kamata ka rabu da maganar ta ka bar shi aci gana da kula da shi har a dace." Ya faɗa yana kallon Abir da ta yi kicin-kicin da fuska ba alamar fara'a a game da ita. A fusace ta kalle shi cikin faɗa ta ce "Malam kawai ka ba mu sallama mu tafi gida, ina ce dai ni ce na amince a kawo shi? To na fasa yanzu zan yi ta masa addu'a ba zai sake zama a Asibitin nan ba." Tana gama faɗa ta kama hannun Zaiyan da ke riƙe da handbag ɗin ta yana jujjuya ta ta nufi hanyar fita. " Babyyy!" Ya kira sunan ta a fusace, gabaɗaya yau duk ya ga ta canza masa kamar ba ita ba,. Tsayawa ta yi ba ta dawo ba ganin hakan Abdul ya soma ba wa Doctor haƙuri, "Am sorry Doctor." Ce masa ya yi babu komai ya ɗauki takarda ya rubuta musu sallama, amsa Abdul ya yi ya masa sallama suka bar office ɗin, ai yanawa a ransa kamar ya zane ta.. Suna fitowa sun nufi motar suka haɗu da Alhaji Mustapha yana ƙoƙarin shiga, da sauri ya kalle su yana washe baki ya ce "A a, 'yata kune a Asibiti? Waye ba lafiya?" Ya faɗa idanuwansa a kan Zaiyan da yake riƙe da hannun Abir, wani irin daɗi ya ji ya lulluɓe shi ganin Zaiyan, ya ji duk komai zai zo masa cikin sauki ya gyara tsayuwar sa yana son jin abin da za su faɗa masa. "Daddy mune ɗazu ma na haɗu da Hafsy, mun zo ganin mara lafiyan mu ne shi ne ma aka sallame shi za mu tafi gida." Da sauri ya ce "Ayya, wannan ashe shi ne majinyacin da Hafsat ke faɗa min? To Allah ya ba shi lafiya ni ma Hafsat ɗin ce ta kawo mai aikin gidan ta kwana tana ciwon ciki, shi ne na ce bari na zo na duba ta ni ma ɗa na kowa ne." Ya ƙarashe maganar yana kallon Abdul ganin yadda ya yi kamar bai san da shi ba, ya ce "Abdul ya aikin?" Kawar da kai ya yi bai ce komai ba ya yi gaba ya ja hannun Abir da ba ta ji daɗin abin da ya yi wa Alhaji ba. Suna shiga motar suka samu Suhal yana ta aikin rarrashin Sajida na ta kuka tana ƙanƙame shi, ita ma a baya ta zauna ganin ya manne mata yaƙi yarda ya zauna ba tare da ita ba, suna shiga Abdul ya ja motar suka bar Asibitin.. Daret gidan da su Baba suke Abdul ya nufa, suna isa ya yi hon aka bude masa get ya shigo. Baba na habar gidan yana jiran zuwan su saboda Abdul ya kira Baba kafin su iso ya sanar da shi za su zo.. Suhal sai da ya ja cap ɗin shi ta rufe masa idanu sannan ya tashi Sajida cikin lallami ya fito da ita, Baba ya musu jagora zuwa cikin gidan yana musu sannu da zuwa suka amsa Baba sai kiran Zaiyan yake amma fir ya ƙi ko kallon shi yana maƙale da Abir kamar wani yaron goge.. A palo suka samu Inna duk suka zauna, sai a lokacin Suhal ya janye cap ɗin dan ya gaishe da su Baba, ya ɗago ya kalle su cikin nutsuwa ya ce "ina yinin ku Baba.?" A ruɗe Baba ya zaro idanu ya nuna shi da yatsa ya ce.... _*Taku har kullum Maman Nusy ce*_ [6/20, 7:51 PM] Ummu Amjad: ~A HAKA NAKE SON SHI~ +966577675904 Shafi na 23 "Kai wane ne? Daga ina kake? Ya aka yi na ga kun kama da Zaiyan?" Ya jero masa tambayoyi a lokaci ɗaya yana dafe ƙirji, sosai ya shiga firgici ganin sak kamar copy ɗin fuskar Zaiyan ne aka yi aka daura a fuskar Suhal.. Murmushi Suhal ya yi ya cire cap ɗinsa ya sa hannu ya barbaza sumar kanshi da take a kwance luf-luf kamar gashin mace macen ma irin mai yalwar gashi, kallon Baba ya yi da har yanzu ya kasa zama in ya kalle shi sai ya juyo ya kalli Zaiyan da yake ta yi wa Abir ƙorafin ba ta masa wanka ba. Sajida da sai yanzu ta soma jin ciwon ya lafa ta kalli Suhal ta soma tambayar shi. "Suhal waye wancan ɗin?" Ta nuna Zaiyan da ya ɗago da kai a daidai lokacin da ta nuna shi, zaro idanu ta yi tana dafe ƙirji cikin kiɗima ta kuma yin magana, "Suhal ko dai da gaske ne na samu taɓin hankali?" Ganin ta ruɗe ya ruƙo hannunta ɗaya ya ce "Ki nutse Sajida ba taɓin hankali kika samu ba, wannan wani mai kama da ni ne ba shi da lafiya na." Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tana kallon Zaiyan, sosai take jinjina lamarin Ubangiji buwayi gagara misali, ko a hanya ta ga Zaiyan tsaf za ta ce Suhal ɗin ta ne shi dan Abu kaɗan ne ya bambanta su.. Zama Baba ya yi yana jin sanyi a zuciyarshi, tabbas wannan lamarin ya saka masa kokwanto a zuciya, gyara zama ya yi ya dubi Abir ya ce "Ƴar nan waye wannan ɗin?" Sunkuyar da kai ta yi tana murmushi sai kuma ta haɗe fuska tuna cewa Sajida matar Suhal ce, Abdul ya riƙe baki yana jinjina kai, ashe dai su Baby an soma girma da shirme. "Baba wannan sunan shi Suhal ɗan ƙasar Niger ne shi, kuma ɗa ga masarautar Niamey, ya zo neman auren Baby ne." Faɗaɗa fara'a Baba ya yi yana kallon Abir da ta yi kicin-kicin da fuska ya ce "A ma sha Allah to Allah ya sanya alkhairi, yaro na tayaka murna dan wannan yarinya mutum ce har mutum, tana da hankali da nutsuwa ga girmama manya ga tausayi." Murmushi Suhal ya yi yana kallon Abir ya juyo ya kalli Sajida da ta saki baki tana kallon shi, kenan aure zai yi? Kuma wannan ita ce wadda zai aura? Wani irin kishi ne ta ji ya taso mata kanta ya sara ta yi saurin runtse idanu, hannu ta kai ta riƙe kan tana faɗin "Wash kaina zafi." Inna ta miƙe tana cewa "Muje na ba ki magani, tare kuka zo da shi wannan yaron? Ke ƙanwarsa ce ?" Ji ta yi maganar da Inna take mata kamar tana ƙara mata zafin zuciya ne, baya ta yi ta kwanta kanta a jikin kujerar ta ce "Ai Mama ba sai kin ba ni magani ba, an ba ni a Asibiti zan sha an jima." Jin haka ya sa Inna ta koma ta zauna tana kallon ta, Abir da ta cika ta yi fam ta ce "Inna wannan ɗin fa matar Ya Suhal ce." Da sauri Inna ta kalle ta tana dafe goshi, sai yanzu ta gane inda maganar Sajida ta nufa na cewa kanta na ciwo kishi ne ya taso mata, kallon Suhal ta yi da yake danna waya ta ce "Kai ja'irin yaron nan me ya sa ka tafo da matarka wajan wata? Sai ta ga kamar ka yi haka ne dan ka ci zarafin ta." Girgiza kai ya yi bai ce komai ba, shi kan shi ba zai so ya mata irin haka ba amma ya zai yi? Ya ganta ne a bazata a lokacin da ya cire rai da ganin ta na har abada, sai ga shi Allah ya sa zai su ga juna, a nutse ya ce "Inna ba da ita na zo nan ba, ban taɓa tunanin ma zan sake saɗuwa da mai kama da ita ma, dan ta ɓata shekaru biyar cif mu a tunaninmu ma ta mutu ashe tana raye." Kallon ban fahimta ba Inna ta yi wa Suhal, sai kuma ta riƙe baki ta ce "Ku ma dama a Niger ɗin ana yin kidnaping?" Girgiza mata kai ya yi ya ɗan muskuta sannan ya ce "Mu gaskiya irin wannan lamarin na sace-sace a Niger ba a yisa, ko kuma na ce a Jaharmu ba a yi, itama a nan Nigeria aka sace ta." Abin da Abir dama take jiran ji ta ɗago ta kalli Suhal karaf suka haɗa idanu da Sajida ta yi saurin kawar da nata, fuskarta a gefe ta soma magana. "To amma Ya Suhal ku da kuke Niger me ya kawo Sajida Nigeria har aka sace ta?" Nisawa ya yi sannan ya ce "Princess ƙaddara ce ta kawo ta da bin shawarar ƙawa." Ya faɗa yana tunano abin da ya faru a baya ransa na ɓaci kamar yanzu ne abin da Sajida ta aikata masa yake gani.. Nan da nan idanuwan Sajida suka cika taf da hawaye, na nadama da da-na-sanin ƙawar ta ta mamaye ta wanda a kullum take tun cikin yi da ta faɗa iftila'in nan. Goge hawaye ta yi ta kalli Abir ta ce "Ni zan faɗa miki duk abin da ya faru, da kuma soyayya ta da Suhal har ya kai ga an daura mana aure.". Gyara zama Abir ta yi cike da zaƙuwa ta ƙagara ta ji labarin Sajida. "Ni sunana Sajida haifaffiyar garin Niamey, Babana ɗan Niamey ne Mamana ƴar Kano. Mu biyu ne a wajan iyayenmu ni ce babba sai ƙanwata Halima. Tun da na taso nake da son tara ƙawaye a ganina in kana yin ƙawaye to kai wayayye ne kuma me class, hakan ce ta sa tun ina yar shekaru 17 na tsunduma harkar social media Wanda a nan ne na haɗu da wata a Facebook ana ce mata Bishira, cikin ƙanƙanin lokaci muka ƙulla kawance da Bishira ganin yadda take nuna min kulawa na saki jiki da ita. Wata rana na hau online na ga ta yi post ta je Abuja ita da 'yan gidansu har ta yi tagging dina a sahar, sosai suka birge ni na bi ta prvt na ce mata "Ƙawata kin yi matuƙar kyau fa." Ina tura mata ta dawo min da amsa tare da emoji ɗin da ke nuna ta ji daɗi, nan muka dinga hira inda a nan take faɗa min cewa wasa take min da ta ce ita a Kaduna take ita ƴar Kano ce cikin gari, na ɓata rai sosai dan ni a rayuwata na tsani ƙarya, na ce mata kar ta sake min ƙarya akan abin da ya shafe ta na dauke ta ƴar'uwata take faɗa min gaskiya akan komai nata. Ganin na fusata ya sa ta ba ni haƙuri ta ce ba za ta sake ba na haƙura muka ci gaba da magana. Ko a gari kawayena sun fi shida, kuma kowacce muna tare da ita muna chat sosai,. Mun kai shekara da haɗuwa da Bishira sai take ce min ai ita yanzu ta koma Istagram ni ma na buɗe yanzu ba sosai za take hawa Facebook ba, a lokacin jiki na rawa na je na rubuta sunan shi a play store na sauke a waya na buɗe. Buɗe Istagram ɗina da wata ɗaya na haɗu da Suhal, ganin yana yawan rufe fuskarsa in zai ɗaura photonshi sai abin ya birge ni na dinga bibiyar duk wani post ɗin sa, naji ya shiga raina ban ankara ba na kamu da matsanancin son shi na kasa sukoni. Wasa-wasa abin ya soma saka ni tunani ga shi ni a matsayina na mace wadda aka san ta da kunya da kawaici bai kamata a ce na tunkari Suhal da maganar so ba, haka na kasance abin duniya ya isheni har sai da Mamana ta same ni wata rana a ɗaki ina ta zubar da hawaye na ciwon so, mamaki sosai ta yi da ganin ina kuka ta zauna a kusa da ni ta dafa kafaɗata na zabura sai na ga ita ce, a sanyaye ta ce da ni, "Sajida wai lafiya na ga kwana biyun nan kin koma wata iri? Me ke damun ki wai? Ki faɗa min." Rasa me za faɗa mata na yi na faɗa jikinta na saki kuka tamkar marayan da aka hana abinci, hankalin ta ya tashi ta dinga tambaya ta amma na kasa magana, ganin ta shiga tashin hankali sai na sassauta kukan nawa na soma tattaro ƙaryar da zan shirga mata. "Mama Wallahi wasu irin mafarkai nake marar kyau, da na kwanta sai na yi shi y asa duk na damu." Ajiyar zuciya Mama ta sauke ta dube ni tsaf, ta so ta ƙaryata maganar tawa amma ta ƙi yarda mu haɗa idanu, a sanyaye ta ce "Kuma shi ne duk kika tashi hankalinki? Mafarki fa ba gaskiya ba ne Sajida, amma ki dinga yin addu'a in za ki kwanta, ko kuma zan koya miki wasu addu'o'in in za ki kwanta sai na shigo na koya miki." Da to na bi ta har ta fita daga ɗakin. Ina so na yi wa Suhal magana amma ina tsoron ya min wulaƙanci, a ganina shi ɗin ɗan masu kuɗi ne duk da a lokacin ban san ya kamannin shi yake ba, wata ranar Lahadi na ɗauri aniyar yi masa magana ta dm ɗin sa ko da ba zai kula ni ba, haka kuwa aka yi karfe goma na dare na hau online na shiga dm ɗin sa na masa Sallama tare da sheda masa ina ɗaya daga cikin friend ɗinsa. Abin mamaki ina turawa aka buɗe amma ba amsa, ban yi zuciya ba washegari ma haka na tura masa saƙon barka da safiya, nan ma ya buɗe amma ba amsa sai abin ya ƙular da ni matuƙa na ja tsaki na aje wayar.. Ina so na manta da shi amma zuciyata ta kasa na kwana ban yi ba bacci, kullum da photonsa nake kwana a ƙirjina wanda na ɗauka a Instagram ɗinsa na kai aka wanke min shi, bana son kowa ya gani shi ya sa na ɓoye shi sai zan kwanta dauko kasancewar ɗakina daban na ƙanwata daban.. Da dare na hau online na shiga Instagram ina addu'a ko zan ga saƙon Suhal, kamar a mafarki na ga saƙon shi ya shigo min, hannuna na rawa na shiga zuciyata na wani irin zillo na son ganin abin da ya fada min. _"Wa alaikum salam. Ma sha Allah da fatan kina lafiya, lokacin da kika turo saƙon duk ba ni na buɗe ba ƙanwata ce wayar na hannunta."_ Wani irin daɗi naji a lokacin a raina ina cewa 'Ashe ma ba shi da girman kai irin na ɗiyan masu kuɗi.' Da sauri na mayar masa da amsa. "Ayya Allah sarki! Ai na ɗauka ko kaima wulaƙanta mutane gare ka, ashe ba haka ba ne." Emoji ɗin murmushi ya turo min tare da sake turo emoji wanda ake haɗe hannu alamar afuwa, dariya na yi mai sauti muka gaisa ya ce min zai sauka babansa na kiran shi, ba dan na so ba na masa sallama ya sauka. Da dare na sake taɓo shi na ci sa'a yana kai muka gaisa ina tambayar shi ina ƙawar tasa ya ce ta yi bacci, mun yi hira ba lefi tukun muka yi sallama.. Wasa-wasa muka zama abokai har muka dawo whatsapp da yin chat, kuma har lokacin ban yi gangancin furta masa kalmar so ba, illa kawai ina nuna masa ita a aikace, ina ba shi lokacina da zarar y min magana, ina damuwa da duk abin da ya dame shi, ko ciwon kai yake sai na wuni ranar ina kiran shi a waya amma sai taƙi shiga, haka nake ta dakon son shi har muka yi kusan shekara a matsayin abokai.. Wata rana kamar a mafarki na tashi daga bacci na ga saƙon shi wanda ya sa na kurma ihu daɗi ban sani ba.. _Sajida a gaskiya na yaba da hankalinki, hakan ya sa na ji kin kwanta min à rai dan haka na ji ya kamata na gabatar miki da kaima kafin na cuci kaina, da fatan ban miki yaro ba shekara ta 26,da fatan ba wanda ya shiga gabana?"_ Saƙon da ya turo min kenan wanda ya sa na yi ta murna ina jin kamar na fi kowa sa'a a duniya, dan haka na mayar masa da amsa. _"Yayana kenan, ai babu macen da za ka ce kana so taƙi ka sai dai in ba ta san kai ba ne, amma zan yi shawara duk abin da na yanke zan sanar da kai."_ Bayan ya ɗaga ya ce kar a dauki lokaci kwana ɗaya tak ya ba ni, ni kuma ina jin daɗi na ce masa to. Washegari na tabbatar masa da na amince da soyayyar shi a gareni, ya yi murna sosai ya kuma ce min shi fa ba da wasa ya zo ba da aure yake sona. Ban ji wani ɗar ba na ce masa ai ni ɗin ma lokacin aurena ya yi. Haka muka dinga ba wa junanmu kulawa har ya haɗa ni da ƙawar shi Ikilima muka saba da ita, sai da ya ga mun shaƙu sosai ya sanar min da ko shi waye, ranar kasa bacci na yi jin shi ɗan gidan sarauta ne, na shiga fargaba sosai a tunanina ba za a bari ya aure ni ba.. Kwatsam sai ga shi an turo gidanmu daga masarauta ana nemawa Yarima aurena, ranar naji farin ciki sosai amma fargaba ta hana farin cikin ya bayyana, ita kanta Mama sanyi ta yi saboda zaman gidan sarauta yana cike da ƙalubale marar iyaka rashin daɗin sa ya fi jin daɗin yawa.. Wata ɗaya aka saka dan an ce Suhal zai yi tafiya zuwa ƙasar Turkiyya in an yi biki sai mu wuce tare, naji daɗi sosai dan dama ni ina son na ga naje ƙasashen waye... Saura sati biyu bikinmu sai Maman Bishira ta ce a kawo ni Nigeria tana so za ta min gyara na musamman, da farko Mama taƙi yarda ta ce ai indai maganar gyara ne a nan Niamey ba za a nuna musu ba ta bari ayi min à nan, amma sai Bishira ta kafe har da kuka wai ita fa ta nemo mai yin gyara tun daga Maiduguri kar na watsa mata ƙasa a ido, jin haka ya sa na ce Mama ta bari naje in ya so ana saura sati biki sai mu tafi har Bishira. Ba dan Mama ta so ba ta amince amma ta ce na bari Baba ya dawo aji mai zai faɗa, yana zuwa na sanar da shi shi ma da farko yaƙi maganar na yi ta kuka ina roƙon shi da ya bari naje kwana biyar kawai zan yi, da kyar ya bari ya ce Halima ta rakani duk da garin kakanni na ne na saba zuwa. Da dare na samu Suhal na faɗa masa ya ce bai yarda na fita ko kofar gida ba, raina ya mugun ɓaci amma haka na haƙura ina ta lallaɓa shi amma fir ya nuna bai amince ba.. Da na faɗa wa Bishira yadda muka yi da Suhal sai ta hau sababi tana cewa ai shi ba ubana ba ne yanzu ba ya da ikoa kaina tun da ba a ɗaura mana aure ba, haka ta yi ta zuge ni tun bana ɗauka har na ɗauka na zo ina ta yi masa mita ya hana ni tafiya ga shi lokaci tafiya yake yi. Ganin na takura masa har na yi fushi bana daukan kiran sa ya ce indai har ina so na tafi to fa lalle sai dai a ɗaura mana aure in yaso da na dawo shagali kawai za ayi a kaini gidansa, na ce na amince na kashe wayar dan lokacin haushi nake ji na jan mini rai da yake na aje wayar, Mama na faɗawa komai ba ta ce komai ba sai da Baba ya zo ta sanar da shi, nan shi ma yake sanar da ita sun yi waya da Maimartaba ya sanar da shi kuma ya amince da hakan.. Haka kuwa aka yi washegari da safe aka ɗaura aurena da Suhal a Masallacin Unguwar mu akan sadaki jika hamsin saifa, da yamma na shirya ya cire min ticket na ce Halima ba za ta bi ni ba ni kaɗai zan tafi. Dama tun da dare Halima ta sheda mini ba za ta bini ba, haka ya kaini filin girgi wanda zai dauke ni zuwa Kano ta dabo dimbin giwa. A ranar sai ya yi ta kallo na kamar ya ga sabuwar halitta, abin ya dameni na ce masa "Ma shéri wai lafiya kake kallo na haka?" Buɗar bakinsa sai cewa ya yi "Ma famme kawai bana son tafiyar nan taki, sai naji kamar karki tafi mu tafi gida daga nan mu yi zaman mu ba sai an yi wani taron biki ba." Murmushi na masa kawai dan yadda na ci buri akan bikin nan nawa taya ma zan yarda a yi min haka? Muna tattaunawa girji ya sauka aka soma kiran fasinjoji muka tashi ni da shi muka nufi jirgin, yana tsaye na shiga girjin yana ɗaga min hannu, da na zo bakin ƙofa na juyo na ɗaga masa hannu sannan na shige. Ana gama shiga jirgi ya tashi ina ta murna yau zan haɗu da Bishira ƙawata wadda kullum take min ƙorafin yaushe zan zo musu visit... Jirgin mu na sauka ɗan kanwar Mama ya zo ya ɗauke ni muka tafi gidan kakanni na, bayan mun isa na yi wanka na huta muka gaisa da 'yan gidan na sanar da kakata dalilin zuwan nawa duk da Mama ta fada musu.. Ƙarfe 8:30 ina kan darduma na gama Sallar isha'i sai ga kiran Bishira ya shigo wayata, dauka na yi ko gaisawa ba mu yi ba ta hau yin masifa wai me ya sa na sauka a gidan kakanni na bayan zuwan da na yi dan ita na zo? Ni dai haƙuri na ba ta dan Bishira irin masifaffun mutanen nan ne masu saurin fusata, nan ta sheda min ga ta a ƙofar gidan kakanni na na fito mu tafi mai gyaran jiki tun da safe ta zo tana jiran zuwana. To na ce na kashe kiran ina son na tambaye ta wa ya mata kwatancen Unguwar Kakanni na amma ina tsoron ta rufe ni da masifa, haka na saka hijabi na dauki jakata ƴar goye na goya na bar wasu kayan a ɗakin kakata na fito na sheda mata Bishira ta zo, fatan alkhairi ta min na amsa da amin na wuce da sauri ganin kiran Bishira ya sake shigowa a karo na biyu... Ina fita na ganta a wata dalleliyar mota fara sol sai sheƙin sabuntaka take, na isa cike da farin cikin ganin ta na kwankwasa glas ɗin motar kasancewar shi baƙi bana ganin ta ina daga waje. Fitowa ta yi cikin shigar ta ta alfarmar kamar yadda nake ganin ta a waya ta washe baki ta rungume ni kamar ba ita ba ce ta rufe ni da masifa ɗazu. Murna muka yi da ganin juna sannan ta amshi jakata ta sa a baya na zagaya na shiga gaba kujerar mai zaman banza ta ja muka tafi.. Sai da muka yi tafiya ta awa daya sannan muka zo wani tantsameman gida a Nassarawa J R. A, Ina ta santin gidan yadda ya tsaru tun kafin ma na shiga ciki, hon ta yi aka bude mata get ta ja muka shiga ciki ta yi packing a inda aka tanada dan aje mota... Dam! Naji gabana ya faɗi ganin wani hamshaƙin mutum ya fito cikin shiga ta alfarma ya nufo motar da muke, da kan shi ya bude min ƙofa na fito cikin girmamawa na rusuna dan da ganin sa na aiyana a raina mahaifin Bishira ne, a nutse na ce masa "Daddy barka da gida, mun same ku lafiya?" Washe baki ya yi tare da cewa "Haba dai 'yata tashi maza kar ki sa ƙura a kayanki muje ciki." Murmushi na yi in jin daɗin tarbar da na samu a wajan mahaifin Bishira, ta zagayo da jakata ta kama min hannu har da shi na biye da mu muka bi wata hanya,. A wani babban palo muka tsinci kanmu sosai na nuna kauyenci duk da ba yau na saba ganin palo irin wannan ba dan ko na gidan da Suhal ya min ya fi shi ado da komai, amma dai sai na ga wannan ɗin ya fi nawa tsaruwa. Zama muka yi aka kira wata hamshaƙiyar mata ta iso ta sha ado ta min barka da zuwa na amsa ina sunkuyar da kai, Bishira ta ja ni ta kaini wani ɗaki mai kyau da komai a ciki na bukata ta ce min tana zuwa na yi wanka.. Bayan na fito daga wanka na ci abinci Bishira ta fito da ni harabar gidan tare iyayenta kamar ba dare ba ne dan ko'ina tar haske ne ya mamaye, haka muka zauna har na soma jin bacci sannan ya ce mu je mu kwanta.. Washegari mai gyaran jiki ta soma ta dinga gyara ni ta ko'ina, duk inda na wuce sai na bar kamshi hatta kayan sakawata ƙamshin ya zauna a jiki. Ranar kwana na uku ne na Bishira ta ce na ba ta wayata tana son yin waya da saurayinta ba ta caji a wayarta, ban mata muso ba na ba ta dan ni ma a lokacin mun gama hira ni da masoyina.. Wasa-wasa har dare ban sake jin ɗuriyar Bishira ba sai na fito palon gidan inda a nan na ga Iyayen Bishira suna hira na iso ina sunkuyar da kai ga ƙamshi na tashi a jikina, baban Bishira ya tashi da kan shi ya nuna min inda ya zauna ya ce na zauna a gefen shi, kunya na ji sai ya yi dariya ya ce ai shi kamar uba yake a gareni jin hakan ya sa ina ɗari-ɗari na zauna a kusa da shi, sai da na gaishe su na ce "Daddy dama Bishira ce ta ari wayata tun safe ban sake ganin ta ba, ko ina ta tafi haka?" Ƴar dariya na ga ya yi ya kamo hannayena ya ce "My Daughter kwantar da hankalinki ai ta tafi wajan party sai gobe za ki gan ta." Baki na saki ina kallon shi ina nanata kalmar party a raina, ban sake cewa komai ba na tashi na koma ɗakin da aka sauke ni. Haka kawai naji hanalina bai kwanta da gidan nan ba, amma na haƙura in Bishira ta dawo gobe zan koma gidan kakata daga can sai na koma Niger. Washegari na tashi ban ga Bishira ma nan hankalina ya tashi, da na fito sai na ga wasu 'yan mata su biyar waɗanda ba za su fini à shekaru ba, dan a lokacin shekaruna 20 cif, Maman Bishira ta ce na zo mu zauna na iso na yi wa sauran barka da zuwa, daga kayan jikin su za ka gane yaran ɗiyar masu ƙaramin ƙarfi ne.. Haka ranar na wuni ina saƙa da warwara na rasa a inda zan samu waya na kira Bishira na mata tatas dan ta kaini bango, shuru kamar an aiki bawan garin uwarsa ba ta dawo ba. Da dare ina kwance ina bacci na ji ana zuge min zip ɗin riga, kasancewar ina da nauyin bacci ban damu ba sai na gyara kwanciyata na ci gaba da bacci, kamar wasa na ji ana min yawo a jiki har ana neman cire min rigar tawa na farka a firgice in zare idanu, wa zan gani? Baban Bishira na gani zaune kan gadon da nake daga shi sai gajeran wando yana ƙoƙarin damƙo ni, a zabure na matsa ina zaro idanu cikin tashin hankali na ce "Daddy lafiya?" Bai ba ni ba amsa illa ƙoƙarin riƙe ni da yake na ja da baya ya biyo ni, na fasa ihu amma bai daina bi na ba, ganin haka ya sa na dinga kiran sunan Bishira ta zo ta ceceni duk da ba ni da tabbacin ta dawo gidan.. Dariya na ga ya yi yana shafa gemun shi ya ce "Ki daina ɓata bakinki ma, ke da ganin Bishira har abada dan ta bar gidan nan kenan, dama dan ta bamu guri ne ta tafi. Sannan ki daina kira na da Daddy dan ni ba ubanta ba ne nan gidan babu iyayen Bishira." Faɗin irin tashin hankalin da na shiga ɓata baki ne, tuni jikina ya ɗauki rawa na rasa yadda zan yi da rayuwata, ganin haka sai na ga ya miƙa hannu ya dauko waya a gefen gadon wanda nake kyautata zaton tashi ce ya zo da ita, daddanawa ya yi ya kara a kunne can kuma ya bani tare da cewa "Ga Bishira nan." Saurin amsa na yi na fashe da kuka ita kuma ta fashe da dariya ta ce "Ke dalla malama ki yi wa mutane shuru, dama ba ki sani ba tarko ne na haɗa miki, tun da Alhaji ya gan ki ya takura sai na kawo ki Kano yana son ki da harka kin masa. Ya ba ni maƙudan kuɗaɗe har da na gyaran jikin da aka yi miki duk shi ya biya dan ya samu abin da yake so, dan haka sai an jima ni na gama aikina. " Tana gama faɗin haka ta kashe kiran. Ƙara na fasa ina yin wulli da wayar na diro daga kan gadon na zo ina ƙoƙarin bude ƙofa na ga a kulle take, juyowa na yi na ga ya taso ya biyo bayana, nan muka dinga zagaye ɗakin ina kuka ina rokon shi kar ya taɓa ni amma sam yaƙi daina bina ni kuma ban fasa guje masa ba, na yi nadamar sanin Bishira a rayuwata, ashe dama kawalcina ta yi ban sani ba? Shi ya sa ta dage sai na zo ta yi iyayen ƙarya duk dan ta cika burin ta a kaina ? Wani irin marayan kuka na saki na durkushe a bakin ƙofa na haɗe hannayena biyu ina ta rokon shi ya rabu da ni, in kuɗi yake so zan sa Mijina ya tura masa ya bar ni tafi gida amma ya yi ta min dariya, a taƙaice a wannan dare wannan azzalumin ya keta min mutumcina ya ci zarafina ya wulaƙantani.." Kuka ne ya ci ƙarfin ta ta dinga yi har da majina idanunwanta suka yi jajur, shi kan shi Suhal wani irin ɗaci yake ji na ketawa matarsa ta sunna mutumcj da aka yi, numfashi ya fesar yana janyo ta ya rungume ta bai ji kunyar kowa ba suma ba su damu ba dan kowa tausaya wa Sajida yake, Abir mai ruwan ido a kusa ta yi sharkaf sai sharce hawaye take tana tuna abin da ya faru da ita lokacin da take hannun masu garkuwa da mutane. Sai da Sajida ta tsagaita da kukan sannan ta ci gaba.. "Washegari aka kira likita ta duba ni har da dinki ta min ta sa min ruwa, na fi sati a kwance ban san inda kaina yake ba abin da kawai yake aiki a jikina idanu da zuciya, bayan su babu abin da nake iya motsawa da na yi yunƙurin tashi sai na ji azababben zafi ya mamaye min ko'ina na jikina dole na koma na kwanta, kwana na 20 cif kafin na samu lafiya Alhaji na ta zirya a kaina a lokacin ina jin ina ma na samu damar kashe shi a rage iri, ranar da aka sallame ni da dare ina bacci na ji an shaƙa min wani abu a hanci, daga nan ban kuma sanin inda kaina yake ba sai da rana ta fito na tashi na ga Alhaji a gefena yana bacci hannayensa a kan ƙirjina na kwalla ƙara ya zabura ya tashi. Kuka na dinga yi ina faɗin "Waiyo Mamana Bishira ta sayar da ni an mayar da ni karuwa, da na bi umarnin Suhal da hakan ba za ta faru da ni ba, amma sharri ƙawa ya ja min ga shi yau wai ni ce ake aikata zina da ni waiyo rayuwata, Allah ka ɗauki raina na huta da ganin wannan ɓakin gidan. " Yana jina har na gama ya ja tsaki ya tashi ya zo saitina ya dauke ni ina kurma ihu ina yagon shi amma bai aje ni ba sai da ya kaini banɗaki ya min wanka ya fito da ni.. Haka kullum sai ya yi zina da ni ko da rana ya zo gidan sai ya zo ya kwanta da ni, dan kar na masa gardama da ya zo yake fesa wani turare a ɗakin daga nan ba na sanin ina kaina yake har sai ya gama biyan buƙatar shi ya tafi na tashi na yi ta kuka ina tsine wa Bishira. Na rame na ƙanjame bana cin abinci ko an kawo min, hakan ya sa Alhaji sai ya zo ya zazzare min idanu sai na ci. Shekara ta ɗaya a gidan kwatsam na samu ciki. " Da sauri Suhal ya kalle ta ta girgiza masa kai alamar kar ya katse ta gama ba su labari ya kawar da kai gefen, ita kuma ta ci gaba. "Rashin lafiya ta same ni inda aka sheda wa Alhaji ina da cikin wata uku a gun ya ce a zubar da shi, lokacin na dinga kuka dan ba ni da bakin magana tsoron Alhaji nake ji kamar rai da ajali, haka aka min allura aka ba ni magani ya tsare ni ya ce sai na sha jiki na rawa na shanye maganin. Ban daɗe da hakan ba cikina ya dinga murɗawa, karshe dai cikin ya zube suka kuma min allura ta bacci, sai da na yi kwana biyu na farfaɗo ya mayar da ni wani ɗaki. Haka na dinga rayuwa kamar wata karuwa a gidan, a cikin shekaru huɗu sai da na samu ciki sau huɗu yana sawa ana zubar min, a shekara ta biyar ne ya ce za mu tafo Yola tare, zuwa lokacin na sallama komai na rayuwata ga tsoron shi da nake ji, na yi yunƙurin guduwa amma da na fito sai na ga gabana ruwa ne kamar kogi dole na koma na zauna, haka muka biyo jirgi daga Kano muka zo Yola a nan ne ya kaini gidan shi ya ce wa matarsa ni ƴar aiki ce ya kawo mata, kuma ta riƙe ni da amana kamar ƴar da ta haifa ta amsa da to ta tarbeni da fara'a. Ni kuwa a lokacin naji ɗan sanyi ina ƙissima wata rana zan gudu a gidan.. Ashe ba haka abin ya ke ba, lulluɓin biri ne akuya da fatar kura. A wajan matarsa nuna wa yake kamar ƴar da ya haifa, amma da dare ya yi zai je ya far mini na yi kukana na gani, dan kar ma matarsa ta ji a ƙasa ya sa aka bani ɗaki su kuma suna sama in dare ya yi yake zuwar min ɗaki, ko na kulle na kwanta sai dai na ji shi a bayana. Haka na ɗauki wata 11 a gidan kullum burina wata rana na fita daga gidan nan kar na mutu a cikinsa, kwatsam yau da sati ɗaya na dinga rashin lafiya matarsa a lokacin ta tafi London ba kowa daga ni sai shi a gidan dan yaransa ban taɓa ganin su ba matarsa ta ce suna Ameria karatu suke. Ganin ba yadda nake ya kira aka duba ni nan suka ce masa ciki ne da ni na wata hudu hayin na biyar, kallo na ya dinga yi ya ce me ya sa ban faɗa masa ba tun cikin yana wata ɗaya? Ni kuma naki ce masa komai na koma na kwanta, washegari ya dauke ni ya kaini Asibiti ya ce a zubar a cikin. Nan Likitan yake sheda masa matsawar aka ce za a zubar da cikin jikina mafaita ba za ta sake daukan ciki ba, kuma ba lalle na rayu ba. Jin haka sai ya ce indai zan daina daukan ciki a zubar babu abin da zai faru, ni kuma a lokacin kamar kurma haka na zama a gaban su ina ji ina aka kaini wani ɗaki ya ce sai gobe da safe za a min aikin. Washegari da Ƙarfe 11:am na rana yau kenan aka min allura, ban ji ciwo ba har sai bayan bayan Sallar Azuhur ciwo ya hana ni zama na dinga murƙususu a ɗakin ni kadai. Da ciwon ya kwanta ne na lallaɓa na iso bakin ƙofa na murɗa naji ta bude sai kawai na rike ɗankwalina a hannu na fito ina sauri, har zan bar Asibitin sai na yanke shawarar na samu wani wajan na laɓe in suka gaji da nemana ya tafi sai na fito na gudu, shi ne na faɗo ɗakin da kuke har Allah ya sa na ga mijina." Ta sharce majina ta ɗago kai ta kalle su kamar yadda suma ita suke kallo ta ce "Wannan shi ne abin da ya faru bayan na baro Niger, yanzu ban sani ba iyayena suna da rai ko sun mutu ban sani ba." Tashi Abir ta yi jikinta na rawa kamar mazari, ta soma takowa ta yo wajan Sajida sai ta yi baya luu ta zube a ƙasa.... Hmm. Yanzu ma aka fara 🙃 *Taku har kullum Maman Nusy.* [10/27, 6:31 Yamma] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): ~A HAKA NAKE SON SHI~ Na: Maman Nusaiba *BONUS FAGE💃🏼💃🏼* Albishir ku masoya littafin *A HAKA NAKE SON SHI* ganin mutane na ta maganar kud'in da na sa wato N500 ya yi yawa, hakan ta sa zan yi promo yau din za ku iya biya N300 a maimakon N500. Daga yau ranar Juma'a zuwa wata Juma'ar mai zuwa, kwana 7 cif idan kika wuce sati daya ba ki biya ba to zai dawo kudin sa n da N500. Za ku iya tura kudin ku ta wannan account din👇🏻 Account number 0003187186 Name account, Khadija Salisu Name bank, Ja'iz bank WhatsApp number +966577675904 Shafi na 24 Da wani irin mugun saurin Suhal da Abdul suka iso gaban ta kowa so yake ya taɓa ta, saurin ɗago da ita Abdul ya yi ganin Suhal na ƙoƙarin taɓa ta ya ɗaure fuska ya miƙe da ita cak ya dawo inda yake ya zauna. Ganin an ɗauko ta Zaiyan shi ma ya miƙe ya isa gaban Abdul yana kuka wiwi kamar ƙaramin yaro ya ce "Anty waye ya dake ki na rama miki? Ki tashi ki rakani mu tafi gidana sai mu yi zaman mu a can tun da su wanɗannan dukan ki suke, kuma in na yi kuɗi ba zan taimaka musu ba sai na kama su da kaina na kulle su a ɗaki." Zaman dirshan ya yi ya kamo hannunta da yake reto ya kalli zoben da ke yatsar ta tsakiya, baki ya riƙe yana juya hannun ya ce " lalala! Me ya sa kika sa wannan abin? Ki ga fa ya ɗaure miki yatsa bari na fitar miki da shi. " Idanu Abdul ya zuba masa yana kallon shi cikin taussayawa, ganin yana ƙoƙarin zare mata zoben ya kai hannu ya riƙe nasa ya ce "kana son Anty ta daina kula ka?" Da sauri ya ɗago yana girgiza kai ya ce "Ka ba ta haƙuri Baba ba zan sake yi mata lefi ba, ka tashe ta na ce ta yi haƙuri." Ya rufe fuska yana kuka kamar an masa wani abin. Ajiyar zuciya ya sauke yana jin wani iri, Inna ce ta ƙaraso da ruwa da ta tafi ɗaukowa daga kitchen ta miƙa masa, amsa ya yi ya kurɓa ya fesa mata a fuska. Da sauri Zaiyan ya kalli Abdul ya sake fashewa da kuka yana faɗin "Baba me ya sa ka kashe Anty? Sai na rama mata abin da ka mata da ta farko daga mutuwa za mu tafi mu bar ku tun da ka kashe ta." Hawaye ne ya cika wa Baba idanu bai san lokacin da ya gangaro ba sai da ji ɗumin su a kuncinsa, hannu ya sa ya goge yana jin tsananin tausayin Zaiyan na ratsa masa kowacce kafa ta jikinshi. Numfashi ta ja da ƙarfi ta soma buɗe idanu wanda tun kafin ma ta buɗe hawaye ke ta silalowa, tana gama buɗewa ta sauke kallon ta a kan Zaiyan da hawaye suka wanke masa fuska yana ta murtsa yatsunsa, da sauri ta tashi daga jikin Abdul ta sauka ƙasa ta zauna a kusa da shi duk bai san ta tashi ba. "Zaiyan." Jin ta kira sunan shi ya ɗago da sauri ya ga ita ce, ɗan waro idanu ya yi ganin ta a kusa da shi ya ce "Allah sarki Anty ashe kema dukan ki suke kamar ni, wannan mai min allurar har da nuna min irin wannan abar irin tawa da kika sayo min.Tun da ma haka ne tashi na kaiki gidana kin ga babu wanda yake son mu sai Inna, idan na kaiki sai ki goya ni muna zuwa yawo ko?" Sake da baki take kallon shi, wato yanzu kamar an buɗe masa baki a yau ɗin nan sai surutu yake zuba mata ba kamar baya ba da in 'yan maganar ba su zo ba sai ya kwana bai ce komai ba, dogon numfashi ta ja tana gyaɗa kai ta ɗago ta kalle su wanda suma ita suke kallo. Girgiza kai ta yi ta ce "Ka gani ko Yaya? Na faɗa maka babu wani magani da suke yi masa sai ma cutar da shi da suke, yanzu a yanayinsa babu abin da ya ragu sai ma ƙaruwa da ya yi. Dama can dan ba ka nemi shawara ta da ba zan bari ka kaishi wannan Asibitin ba. Zaiyan kawo hannunka na gani. " Maƙale kafaɗa ya yi yana turo baki ya ce "Dan ki yi min wayo ne ki gudu ko? To ba zan yarda ba ki soka min wannan abin mai tsini." Sake rushewa ya yi da kuka ya ƙara matsowa kusa da ita abin da ya ƙara tayar mata da hankali, Zaiyan bai fiya yin kuka ba ko da kuwa ta ce ta daina kula shi sai dai ya ba ta haƙuri saɓanin yau da tun da suka dawo ta ga ya canja sosai daga surutu sai kuka. Hannu ta kai ta goge masa hawayen tana girgiza masa kai cikin wani kalar yanayi ta ce "Babu abin da zan yi maka ka ji, mu ga hannunka sai na sayo maka kaya masu kyau irin na 'yan gayu." Ta Yi maganar tare da goge hawayen da suka zubo mata. Miƙe ƙafa ya yi yana haɗe hannayensa ya miƙa mata duka tare da cewa "Imm Anty dayawa fa nake so kayan." To ta ce masa ta kama hannun tana zubawa, ɗago kai ta yi ta kalli Suhal ta ce "Ya Suhal tabbas mafarkina ya zama gaskiya, wannan Asibitin ba magani suke yi wa Zaiyan ba jinin jikinsa suke ɗauka suna yin wani abin da shi, kalli nan ka ga inda suke daukan jinin." Ta faɗa tana nuna masa tsintsiyar hannunsa, ta ƙara da cewa "Tabbas akwai abin da yake faruwa da Zaiyan a ɓoye ba tare da kowa ya sani ba, ko ma meye wannan likitan da ke duba shi yasan komai game da ɗaukan jinin. Wata rana na taɓa ganin ƙuraje a daidai inda wannan ɗan ƙurjin yake, in ka tuna Yaya a Asibitin Yaya Hashim na nuna muku ya ce ba wata matsala ba ce babba za a iya sa masa magani ya warke, daga haka ban sake bi ta kan ƙurajen ba ganin sun yi baƙi alamar sun warke." Kanta ne ta ji ya sara mata ta dafe kan tana runtse idanu kamar daga sama ta ji ana mata magana a cikin kunnuwanta. _Maijidda lalle ya zame miki dole ki sa idanu akan shi, in ba haka ba wata rana sai dai ku samu gawar Zaiyan an gama shanye masa jini, ki yi abin da ya dace kafin ki shiga gagarumar matsala wadda zai miki wahalar fita."_ Ɗaga kai ta yi sama ta buɗe idanunta sai ta ji kan ya daina mata ciwo, ajiyar zuciya ta sauke ta kalle su tana gyaɗa kai tabbas zargin da take zai iya zamowa gaskiya, kamar dai yadda ta ji an sanar da ita mafi rinjaye na zuciyarta ya karkata a kan maganar da ta ji ta zo mata kamar wadda aka yi wa wahayi. Suhal ya ce "Princess ba za mu iya tabbatarwa da maganar ki ba har sai na bincika na gani, sannan yana da kyau kai Abdul da za ka kai shi Asibitin nan ka yi bincike akan ta sosai, tabbas a cikin Asibitin nan akwai maciya amanar Asibitin kamar dai ɗaya daga cikin su da ya zubar wa da Sajida ciki. Ya kamata ka bincika wannan likitan. " Gyaɗa kai Abdul yake yana nazarin maganganun su, tabbas ya yi gangancin yanke hukuncin kai Zaiyan Asibitin nan, wanda bai nemi shawarar kowa ba sai ta abokin shi wanda a take yake sanar da shi sam kar ya kai Zaiyan wannan Asibitin ya bari in ya gama shan magani in ba a ga alamar sauki ba sai su fitar da shi waje, amma saboda gardama irin ta Abdul ya ƙi jin shawarar da ya ba shi ya ɗauke shi ya kai, yanzu ga shi matsala ta soma biyowa baya. Dogon numfashi ya sauke ya miƙe tsaye ya yi taku biyu tare goya hanayensa baya yana ta nazari, sai zuwa can ya juyo ya kalli Suhal da ya kafe shi da idanu yana jiran jin me za faɗa, cikin nutsatsiyar murya irin ta cikakkun maza ya soma magana. "Dole zan koma Asibitin nan dan na nemi wannan likitan na masa tambayoyi, amma kafin nan ka duba mana shi mu gani ya jininsa yake." Shi ma tashi ya yi ya kalli Sajida sannan ya dawo da kallon shi ga Abdul ya ce "Sai na koma masauki na kayan aikin suna can, minti ashirin zan dawo ko kuma a bari ma zuwa gobe sai na zo da safe na duba shi, in ma da buƙatar wasu abubuwan za ka iya yi wa abokin ka waya ya kawo mana sai mu yi aikin." Gyaɗa masa kai ya yi ya dawo kusan Sajida ya ce "Ke kuma tashi muje yau nake son na kaiki Kano gidan su Mama su ganki, idan na shirya zan koma sai mu tafi tare. Amma kafin nan zan sake duba lafiyarki sai na kaiki." Ya faɗa yana miƙar da ita. Tana cije lips ta miƙe har yanzu ciwo mararta take sosai dauriya kawai take dan kar ta tayar wa da Suhal hankali, numfashi ta dinga saukewa zufa ta dinga yanko mata. Kallon ta ya yi da kyau yana jera mata sannu, da kyar take taka ƙafar ya musu sallama suka nufi kofar fita sai jin murya Zaiyan suka yi yana yi wa Suhal magana. "Abokina kaima Baba ne ya haife ka? Za ka zama Abokina?" Juyowa ya yi yana murmushi ya kalli Zaiyan da yake ci gaba da jaddada masa ya yarda su zama abokai, gyara tsayuwa ya yi ya ce "E na yarda mu zama abokai." Miƙewa ta yi zumbur ya isa gaban Suhal ya zagaye su yana dariya, sai da ya zagaya su sau uku sannan ya dakata yana dariya ya miƙa masa hannu ya ce. "A ƙulla abokai zan ke zuwa gidanka." Murmushi Suhal ya yi ya miƙa masa hannu suka ƙulla sannan ya kalli Sajida da ya ga tana kallon shi kamar wadda take masa harara, riƙe haɓa ya yi tare da taɓe baki ya ce "Dalla can malama ke kuma meye kike wani harara ta? Haushi kike ji dan ban ƙulla abuta da ke ba? To ni sarki ne wannan shi ne Abokina ba ke ba ƴar ƙarama." Tsoro ne ya kama Sajida ganin yadda yake hura hanci, ta maƙale hannun Suhal ta ce "Don Allah mu tafi Suhal tsaro nake ji kar ya bigeni." Ganin ta ruɗe ya sa Suhal sake yi musu sallama suka fita Zaiyan na ce masa ya dawo fa an jima yana dariya ya amsa da to zai dawo sannan ya rufo ƙofar.. Dawowa ya yi ya zauna a kusa da Abir ya shafa cikinsa yana kwaɓe fuska ya ce "Anty yunwa nake ji." Ya faɗa yana kafe ta da idanu. Inna ce ta tashi ta kawo masa tuwo da miyar kuɓewa, ai kuwa ya dinga ci yana zuba miyar a jikin rigarsa, bayan ya gama cinyewa ya yi gyatsa yana sa hannunsa mai miyar ya goge bakinsa da shi, gabaɗaya miyar ta ɓata masa fuska har kusan kunnuwansa miyar ce, ya kalli Abdul ya ce "Baba yunwa nake ji." Kitchen Abir ta koma ta ƙaro masa abincin nan ma ya cinye, duk jikin kayansa ya ɓaci da miya Baba ya tashi ya kama shi tare da Abdul suka ce ya zo ayi masa wanka, ai kuwa ya kwace yana hararar su ya ce "Anty wai za su yi min wanka.". Runtse idanu Abir ta yi har sai da ya sake maimaita mata ta dube shi ta ce "Ka je ayi ma wanka, in kuma ba haka ba zan yi tafiya ta ba zan sake dawowa ba, kuma daga yau na hana kake ce min Anty." Da sauri ya miƙe yana kallon ta sai kuma ya dawo gaban ta ya ce "zan je ba za ki tafi ba ko?" Gyaɗa masa kai ta yi ya miƙe ya isa wajan Baba ya kama shi suka nufi banɗaki, yana tafiya yana waiwayowa yana ce mata "Anty ba za ki tafi kina nan?" E take ce masa har suka shige banɗaki, Inna ta tashi ta je ta dauko masa wani kayan ta ɗan buɗa toilet ɗin ta miƙa wa Baba ya amsa.. Sallama suka yi wa Inna Abdul ya ce za su dawo gobe ta musu godiya tana saka musu albarka suka bar gidan.. Tsaye yake yana zarya a babban palon, gabaɗaya jikinsa ya yi sharkaf da zufa sai goge ta fuska yake yana fesar da iska. Wayarsa ce ta soma ringing ya yi saurin dubawa, ganin number babu suna sai ya yi tunanin ko ɗaya daga cikin su ne ya canja taku ya daga tare da karawa a kunne ya ce "Hello." Muryar da ta amsa masa ce ta sa shi zabura har wayar ta suɓuce masa ta faɗi, hannu na rawa ya sunkuya ya ɗauka ya duba ya ga har yanzu mai kiran yana nan. Ya daɗe a haka ba a yi magana ba ai kuwa ya fusata ya ce "Kai yaro in kana cin ƙasa ka kiyayi ta shuri! Hawainiyarka ta kiyayi rama ta Wallahi! Kai gani kake tsoron ka ne ya sa muke ɓuya ko me? Ka yi kuskure Damisa da har ka sake dirowa Nigeria, tabbas wannan karon sai dai uwarka ta haifi wani ba dai kai ba, idan kuma ta gama haihuwa sai ta ci gaba da jimami in ka mutu." Ya ƙarashe maganar yana huci ga zufa da take ta yanko masa, duk sanyin AC da yake sanyaya palon ji yake kamar a gaban tukubar gashin tsire yake.. Dariya Damisa ya yi daga cikin wayar sannan ya ce "Alhajin Allah kenan, ai daga yau ka soma lissafa kwanakin ka Damisa ya dawo, ai ja da baya ba tsoro ba ne ga rago shirin faɗa ne! Matuƙar ina doran duniya ba zan taɓa barin ku a raye ba, na girma ne da muradin daukan fansa dan haka ban ga wanda zai ceceku daga hannuna ba. Wannan yarinyar da ka yi wa faɗe har ta yi ciki ka sa aka zubar karshe ta mutu kuka jefar da ita, to ina so ka sani tana nan a raye kuma ni nan zan tsaya mata wajan ganin an kwata mata haƙƙin ta da kika ɗauka. Mugaye kawai azzalumai masu suffar hawainiya." Tun da ya fara maganar Alhaji ya yi sumar tsaye, tunani ya dinga yi waye ya sanar da Damisa wannan rufaffan sirrin nasu? Girgiza kai ya yi yana ƙarfafa wa kanshi gwiwa ya yi dariya wadda shi kan sa ya san ta yaƙe ce, zama ya yi ya ce "Kai ɗin banza! Waɗanda suka fika zarra ma sun zo sun kara da mu ba su ji dadi ba sun bar duniyar bare kai ɗan ƙaramin kwaro, ina mai tabbatar maka da kaina zan fasa kaika da bindiga." Dariyar basawa Damisa ya yi ya ce "To mu zuba mu gani shege ka fasa ɗan halak sai yanka, bar ganin ƙanƙantar allura itama ƙarfe ce!" Ƙit ya kashe kiran, Muzurai Alhaji yake yana sauke wayar ya yi saurin shiga app ɗin kira ya ga number da ya kira shi da ita, wata number ya kira ya ci sa'a an ɗauka, da sauri ya soma magana. "Hello maza ga number nan zan zano maka ka duba min daga ina mai kiran yake." Cike da girmamawa ya ce "OK Sir." Zano masa number Damisa ya yi shi kuma yana sawa a kan computer da ke gaban shi, Alhaji na gama ba shi ya katse kiran ya zauna a kan kujera yaraf yana sauke numfashi, bai taɓa tunanin Damisa zai taɓa dawowa ba a yadda suka yi masa kisan gilla, sai ga shi ya rayu ya dawo da zafin sa fiye da yadda suka san shi a baya. Kira ne ya shigo wayar tashi ya wawuro wayar da ya yi jifa da ita gefe, ganin Alhaji Mustapha ne ke kira ya yi saurin dagawa yana huci, kafin ma ya ce wani abu Alhaji Mustapha ya soma magana a ruɗe. "Hello kana jina? Wallahi in ba mu tashi tsaye ba wannan ɗan iskan yaron sai ya goge masa hadda, wai ni zai kira yake faɗa min maganar banza to Wallahi wannan karon sai na sa an daddatsa min naman jikinsa na ba wa kare ya cinye." Yana dasa aya Alhaji ya kaɗa kai yana jin muguwar tsanar Damisa a zuciyarsa, kwafa ya yi ya ce "Hmmm. Yo ai ni ma yanzu ya kira ni yake min maganar banza, in dai muka sake sai wanki hula ya kaimu dare muna ji muna gani, ya kamata ka yi abin da ya dace, daga ɓangaren ka ni ma zan yi wani abu tun da Uwa Dudu ta ce ba ta iya ganin suffar Damisa kodayaushe kamar yadda muke ganin fuskarsa a rufe itama haka take gani. Amma ya kake gani ko za mu iya samun wani gagarumin malami ko boka wanda zai kashe mana Damisa cikin ruwan sanyi? " Alhaji Mustapha ya nisa yana tunani, can ya yi murmushi ya ce "Wannan yarinyar da take mana aiki ta ce min tana da wani riƙaƙƙen boka amma inda yake akwai nisa, ta ce yana can kan dutse aikinsa kamar yankan wuƙa." Murmushi Alhaji ya yi ya ce "Yawwa har naji sauƙi yanzu ka nemo mana ita sai ta mana kwatance kawai, amma kuma duk da haka muke sa ido a kan shi kafin aikin ya hau kansa." Haka suka ci gaba da tattaunawa suna tsara yadda za su bi wajan kashe Damisa, har Alhaji zai kashe Alhaji Mustapha ya yi saurin cewa "Sir abu ma fi sauƙi mu haɗa har wannan shegun yaran da uwarsu, ka ga sai mu yi yadda muke so." Dariya suka sa sannan ya kashe, bai fi minti uku ba sakon wanda yake bincikar masa number Damisa ya shigo. Inda yake sanar masa wanda ya kira layi yana kashe kiran ya daina aiki da sim ɗin, sosai Alhaji ya ji mugun haushi amma da ya tuna abin da suka tsara sai ya yi dariya ya tashi ya fita... Washegari Suhal ya dawo da kayan aiki dan ya duba Zaiyan, bai daɗe da zuwa ba sai ga Abdul tare da abokin shi da Abir sun yo sallama. Yana ganin ta ya kawar da kai gefe, murmushi Doctor Hashim ya yi dan shi Zaiyan na birge shi, ita kuwa kallon shi take ganin yadda ya yi mata sihirtaccan kyau na musamman ta yo inda yake cikin nutsuwarta. Tana isowa ya kalle ta ya haɗe girar sama da ƙasa ya ce "Mun yi baram-baram." Riƙe baki ta yi tana mamakin kalmar da ya faɗa ta ce "Zaiyan da ni ɗin ce aka yi baram-baram? Ni ce fa Antyn ka ko ka manta?" Hararar Abdul ya yi yana hura hanci ya ce "Ba ke ba Anty da Baba ne muka yi baram-baram, shi ne ya sace ki ya gudu gidansu nake ta neman ki, Anty wai ina ne gidanku nake zuwa muna magana? Kin wannan abokin nawa." Ya nuna mata Suhal, ya ci gaba da magana. "Yau shekarar shi ashirin a gidanmu bai je ko'ina ba muna tare da shi har London muka je, amma shi Baba ko tsoron Allah ba ya yi ya sace ki dan kar aje London da ke yanzu ga shi har mun dawo abin mu. Kin ga da kina nan da na sayo miki kayan wasa ba sai kin je aron na wasu ba.." Dariya Doctor Hashim ya yi yana zama ya ce "Wai yaushe Zaiyan ya zama mai surutu ban sani ba? " Murmushi Abir ta yi ta ce "Ga dai zahiri ka gani Yaya Hashim tun jiya yake ta zuba mana surutu." Ta faɗa tana kallon shi. Baba ya yi murmushi ya ce "Ai ko bacci da kyar ya yi, jiya da dare ya yi ta kuka yana cewa an sace masa Antynsa da abokinsa naje na kwato masa su, sai da muka dinga masa addu'a kafin ya samu ya yi bacci asuba na yi ya tasheni wai mu tafi Masallaci shi ma zai yi Sallah. Da kyar na masa dubara na ce ya yi a gida zan je na dawo sai mu tafi." "Allah sarki bawan Allah." Cewar Doctor Hashim yana goge hawayen tausayin Zaiyan, shi kuwa Suhal tun da ya zo yake kallon Zaiyan ya rafka tagumi, ɗagowar da Zaiyan zai yi ya ga Suhal ya kafe shi da kallo, ai kuwa ya miƙe ya isa gaban shi ya tsaya. Kallon shi shi ma yake yana ɗan waro idanu kamar wanda ya ga wani abu a jikinshi, ganin yana kallon ƙafarsa shi ma sai ya kalli ta Suhal ya ga babu takalmi ya sunkuya ya fidda nashi takalmin ya miƙa masa yana yin fuskar tausayi ya ce "Ashe kaima abokina Babanka ba ya tsoron Allah shi ya sa yaƙi saya ma takalmi, to in dan wannan ne da kake ta kallo ga shi nan na ba ka kyautar shi har abada." Ya faɗa yana daura masa takalmin a cinyarsa.. Ɗaukan takalmin Suhal ya yi bai ce komai ba ya sake ɗagowa ya kalli kayan jikinsa, nan ma Zaiyan ya daure fuska kamar wanda zai dake shi ya ce "Dalla can meye kake kalle min abuna?" Sake kallon kanshi ya yi ya kuma kallon Suhal sai ya ga yana zubar da hawaye, sai ya saki fuska ya kama rigarshi ya cire yana fadin "Ka ga indai dan wannan kayan ne kake yiwa kuka ga shi nan na ba ka su kyauta, bari na ba ka har wandon ma dan na ga a gidanku babu masu tsoron Allah bare su ji tausayin ka tun da Mamanka ta mutu su saya maka kaya da takalmi." Yana maganar yana cire wandon ya haɗa da t-shirt ya rage sai shi sai single da wandon ciki iya gwiwa ya tsugunna ya aje masa a kusa da ƙafuwansa ya ci gaba da magana. "Yanzu da ban ba ka nawa ba sai dai ka yi ta kuka dan ba ka da uwa? To yi shuru duk zan raba kayana na ba ka rabi sai kake sawa, amma fa karka bai wa Babanka tun da shi ba ya tsoron Allah irin na Babana da ya sace min Anty ya gudu." Tsit suka yi suna kallon shi su Abir masu ruwan ido a kusa tuni ta jima da yin sharkaf da hawaye, ganin kirar jikin Zaiyan ta ji ƙirjin ta ya buga ta runtse idanu tana sauke numfashi, ita in ba jikin Yayanta ba ba ta taɓa ganin jikin namiji haka ba.. Abdul ya girgiza kai ya ce "Zaiyan ɗauki kayanka ka sa ba ka ga shi ma yana da nashi ba?" Hannu ya kai zai ɗauki kayan sai kuma ya yi saurin ɗauke hannun yana zare ido ya ce "Ka ga abokina ka yi haƙuri Wallahi ni ba bawaro ba ne aron kayan zan yi, amma tun da ba ka ba ni ba ga shi nan na aje ma kayan ka." kasa magana Suhal ya yi idanuwansa sun yi jajur hawayen ma sun kasa zubowa, wani irin zafi yake ji a zuciyarsa da zarar ya kalli halin da Zaiyan yake ciki. Abdul ya kuma cewa "Ka ɗauka ba sata ba ce ka yi." Kallon Suhal ya yi ya ce "Shin za ka ara min kayan naka? Wai ka ji Baba ya ce na ɗauka ni kuma na san in na ɗauka ba ka ban ba ai sata ce na yi ko?" Murmushi Suhal ya yi hawaye suka zubo masa ya ɗauki kayan ya miƙa masa ya ce "Ai kai abokina ne tun da Babanka ya ce ka ɗauka ga shi na ba ka kyauta." Dariya ya yi ya ƙi amsar kayan ya dawo wajan Abdul ya kai hannu ya taɓa gemunsa, waro idanu ya yi ya kuma taɓa gemun ya ce "Baba kaima irin na abokina gareka?" Gyaɗa masa kai Abdul ya yi yana murmushi ya ce "Je ka amso kayan ka sa." Rausayar da kai ya yi ya ce "To amma dai Baba ka ji tsoron Allah ka daina sace mutane." To kawai Abdul ya ce zai daina sannan ya isa ya amso kayan nashi ya mayar ya dawo kusan ƙafar Abir ya zauna, murmushi ta yi ta yi wa Suhal nuni da ya zo ya soma aikinsa ya taso ya iso, hannun Zaiyan ya kama cikin lallami ya ce " Abokina ka tsaya na duba ka in kana so mu tafi London ɗin." Da har ya kwace hannunsa yana kumbura baki jin abin da ya faɗa sai ya yi dariya ya miƙa masa hannun.. Gwaji ya dinga masa Doctor Hashim shi ma ya iso yana taya shi, ya auna jininsa ya ga ya yi ƙasa soaai, sai da suka gama sannan Suhal ya ce "Gaskiya jinin jikinsa ya yi ƙasa, in da hali za a iya sa masa leda biyu ta jini dan yana buƙatar shi yau ɗin nan." Doctor Hashim ya ce "To ai kuwa bari na hanzarta na faɗa wa nurses ɗin mu akwai jini irin nasa leda ɗaya, in ya so sai a samo ɗayar ko zuwa an jima ne." Mamaki ne ya rufe Abdul har ya kasa ɓoyewa ya riƙe baki ya ce. "Hashim ba ka ce min idan mutum ba shi da jini yana jin zafi a jikinsa ba, idan zai fita daga haiyacinsa har sai an sa masa jinin zai dawo daidai?". . "Kwarai kuwa haka ne Abdul, ni kaina na yi mamakin ganin ba shi da jini isasshe amma bai nuna alamun da za a gane hakan ba, alama ɗaya kawai na gani ita ce ya yi fari sosai ya koɗe fiye da baya, amma bayan haka ban ga komai ba abin nan ya ba ni al'ajabi fa." Duk shuru suka yi Abir ma shuru ta yi tana danganta hakan da wannan Aljanar da take bibiyar su, ko dai ita ce take zuƙe wa Zaiyan jini? Dam! Zuciyarta ta buga ta sauke numfashi ba ta ce komai illa kallon Zaiyan da take yana ta yi wa Suhal maganar tafiyar su zuwa London shi kuma ya ce masa za su je sai an jima.. Hashim ya kira ya tambayi nurse ɗaya daga cikin su ina jinin yake, ta faɗa masa ai yanzu suka saka wa wata mata, dafe kai ya yi ya aje wayar yana kallon su ya ce "Wai babu jinin yanzu mu tafi da shi Asibiti mu ga ko za a samu na sayarwa a wajan wani abokin aiki na, mu a Asibitin mu wahalar samu yake." Suhal ya yi murmushi ya ce "Kar ku wani damu zan ba shi nawa ko leda uku kuke so ku ɗiba a jikina, jininsa irin nawa ne mai wuyar samu in kwanan mutum ya zo ƙarshe kafin a samu mai irin jininsa asa masa sai ka ga ya mutu." Wani sanyi Abir ta ji ya ratsa ta, ita kuwa da me za ta sakawa Suhal da wannan karamci da yanuna mata akan amanarta? Lumshe idanu ta yi tana yi wa Suhal addu'a.. Abdul da Suhal da Doctor Hashim ne suka tafi Asibitin ita kuma Abir Abdul ya sa aka mayar da ita gida ba dan ta so ba.. BAYAN SATI BIYU. Yau su Alhaji Mustapha suka shirya tsaf suka nufi gidan Boka na kan Dutse. Jirgi ya ɗauke su daga Yola zuwa Legos, daga nan suka kutsa cikin dajin oready dama tuni sun sa wani yaron su dake Legos ya tanadar musu mota suka shiga suka tafi.. Sai da suka wuni liƙis suka tafi gaf da faɗuwar rana suka iso gindin dutsen, haka suka dinga hawa suna bin wata matakala da ke jikin dutsen har suka hau can sama tsololokuwa. Wata hanya suka gani wajan kamar ɗaki wanda aka yi shi da dutse, kamar yadda Zee ta musu bayani Alhaji Mustapha ya ce "Boka dan gidan Iyami jikan Jahun, waye ya ce da kai ba kai ɗan butar uwa?" Wata irin girgiza dutsen ya ɗauka suka maƙale juna cike da tsoro, Alhaji Mustapha ne ma wanda ya dan fi su dakewa ya tsaya ƙam yana muzurai, wani gajeran mutum ne ya fito baƙi wuluk da manyan idanu jajaye. Sanye yake da ganye a ƙugunsa ya masa kamar baza, wuyansa wasu layu ne kala-kala haka ma damtsensa kambu ne mai haɗe da laya har zuwa tsintsiyar hannunsa, hannunsa riƙe da wani gashi fari kamar na tinkiya. Hannu ya daga sama ya kwarara ihu ya yi wa kansa kirari sannan ya nuna musu inda ya fito ya ce "Kun zo inda za a share muku kukan ku iyalan sheɗan, ku shiga muje ciki." Da ɗari-ɗari suka shiga sai ga su a wani babban ɗaki wanda aka masa ado da fatocin namukan dadi kala-kala, samar wasu kawuna ne a jere sun kai goma kamar na mutune.. Jiki na rawa suka zauna Jarmai zai yi bayanin abin da ya kawo su Boka ya daka musu tsawa ya ce.... _*Taku har kullum Maman Nusaiba*_ [6/20, 7:53 PM] Ummu Amjad: ~A HAKA NAKE SON SHI~ +966577675904. Shafi na (25) Boka ya daka musu tsawa ya ce "Ba a yi mana bayani in ba mu muka ba da dama ba, duk an faɗa mana abin da yake tafe da ku iyayen sheɗan, kuma buƙatarku za ta biya matuƙar kuka yi abin da na sa ku." Jiki na rawa Alhaji Mustapha ya ƙara duƙar da kanshi ƙasa kamar zai yi wa Boka sujjada ya ce " Ai duk dokokin da ka shinfiɗa mana za mu bi boka matuƙar buƙatar mu za ta biya, kai ko mutum kake so mu kawo maka da rai za mu nemo a kawo ma ko nawa kake so za mu iya, mu dai kawai burin mu ayi mana aiki yadda ya kamata." Zaro jajayan idanunsa Boka ya yi ya tashi tsaye yana zagaye su yana wasu irin yarika, sai da ya gama zagaye su son ransa sannan ya dawo ya zauna yana kallon su, hannu ya saka a cikin wata buta da ke gefen shi ya fito da wasu layu guda biyu ya aje a gaban su ya ce "Kun ga wannan layun? " A tare suka gyaɗa masa kai sun amsawa da "E Boka mun gani." Dariya ya yi ya ɗauke layar ya jimƙe su a hannu yana ta surkunlan shi, bayan ya gama ya sake aje musu wannan karon kuma layar sai ta zama uku ya soma magana yana muzurai. "Me kuke so ayi musu su duka." Da sauri Jarmai ya ce "Abu na farko da muke so Boka, muna son a kashe Damisa, na biyu muna son a sa wannan yarinyar ta tattaro duk wata kadara da mahaifinta ya bari ta kawo mana har inda muka cikin sirri bare da kowa ya sani ba, na uku kuma bayan ta gama kawo mana muna so a kashe yarinyar da uwar, shi kuma ɗan'uwan ta ya zama kamar karen mu duk wani abu da muke so a hukumance da mun ba sa umarni ya bi babu gargada. Sannan in mun tsunduma harkar siyasa mu yi nasara, muna so kowa da ke wannan Jaha tamu ta Yola ya ƙaunace mu ya zaɓe mu in lokacin zaɓe ya yi.." "Hahaha! Sallamammu za ku samu biyan buƙata, amma fa aikin nan da za mu yi muku mai matuƙar wahala ne, dan haka dole abin daki-daki yadda komai zai tafi daidai. Abu ma fi sauƙi shi ne in kuka tsunduma harkar siyasa za ku yi nasara sosai mutane za su so ku fiye da tunaninku, na biyu kuma ba za a iya kashe Damisa ba saboda tun kafin ku zo wata yarinya ta taɓa kawo sunan shi a kashe shi, da na tura masa baƙaƙen aljannu babu wanda ya dawo a rayé duk ya kashe su, shi kan sa aljanin kan sa ne mugun hatsabibi ne. Maganar wannan yarinyar da mahaifiyarta shi ma ba za a iya kashe ta ba yanzu, saboda ƙaddararta mu mai yawa ce a rayuwarta. Yanzu haka maganar da nake muku wata gagarumar jarabawa na tunkaro ta ta zo kaf da faɗawa ciki, ba ku kaɗai ba ne kuke bibiyar rayuwar wannan yarinyar akwai masu son ganin bayan ta bayan ku ɗin nan, dan haka aikin ta mai wahala ne amma zan gwada na gani. Ɗan sanda shi nashi mai sauƙi ne da zarar ka aura masa ƴarka za ka kake samun duk wani lagon shi. " Katse shi Alhaji Mustapha ya yi cikin jin daɗin bayanin Boka ya ce "Boka dama ina so na ma maganar ita ƴar wajan nawa da zan sa dole ya aure ta, ina so a cusa masa tsananin ƙaunar ta, ta yadda duk abin da ta ce masa ba zai mata gardama ba." Dariya Boka ya yi ya girgiza kai ya ce "Wannan duk mai sauƙi ne, da zarar kun koma za kuke ganin aiki yana ci ɗaya bayan ɗaya, dokokin da sharaɗin wannan aikin wannan layar za ku samu gawa wadda ta kwana kafin a binne za a sa a bakin gawar a ɗinke bakin da zare da allura, wannan ɗayar layar ita kuma za ku samu maƙabarta ku je kan ƙabarin ƙaramin yaro wanda ba zai wuce shekaru 15 ba ku tona ƙabarin har sai kun tardo gawar sai ku saka layar a gefen shi ku mayar ku binne. Wannan ɗayar layar za ku samu rijiya tsohuwa wadda aka daina shan ruwan ta ku jefa ciki, idan har kuka yi haka a daidai to buƙata za ta biya. " Ji suka yi kamar su kurma ihu dan dadi, dan wannan sharaɗin ai mai sauƙi ne a wajan su, Alhaji Mustapha da ya fi kowa jin daɗin wannan lamari musamman da zai aurar da ƴarsa wadda ta gagare shi marar jin maganar manya, ga shi idan har ta haihu zuwa shekara lokacin za su kashe Abdul sai dukiyarshi ta zama ta Hafsat, shi kenan komai ya zama mallakin su. Tsawa Boka ya daka musu ya ce "Ku tashi ku tafi." Jarmai ya sa hannu a aljihu ya fito da ɗaurin 'yan rafa guda biyar kowani dauki dubu 100k, aje wa ya yi a gaban Boka jiki na rawa ya ce "Boka gagara badau ga kafin alƙalami, idan aiki ya ci duk abin da kake so za ayi ma." Ɓata rai Boka ya yi ya ce "Mu ba ma amsar kuɗi sai dai mu biya buƙata da mutum ko mace ce ko namiji ne, dan haka kowa ya shiga can na biya buƙata ta da shi." Kallan kallo suka dinga yi, Alhaji ya ce "Kun ga na gane abin da yake nufi, dan haka indai muna son mu cimma burinmu to fa sai boka ya yi amfani da mu dan ya samu ƙwarin gwiwar yi mana aiki yadda muke so, abin da mun saba yi ko so kuke sai na muku gwari-gwari?" Jin abin da ya faɗa sai suka fahimta dan haka Jarmai ya tashi dan tuni Boka ya shiga ciki wata ƙofa yana jiran ɗaya daga cikin su ya zo, da ɗari-ɗari ya shiga ɗakin.. Sun fi awa kafin ya fito yana sharce zufa ya yi sharkaf kayan shi a hannu daga shi sai gajeren wando ya fito ko single ɗin ya cire ta, Dariya Alhaji Mustapha ya yi yana kallon Jarmai da ya dawo wajan sa ya zauna yana sakin numfashi. Tashi Alhaji ya yi ya ya cire babbar rigarshi ya shige ɗakin, shi kuwa sai da ya fi awa ɗaya sannan ya fito yana ɗaure zariyar wandon shaddarshi, murmushi ya yi ya kalli Alhaji Mustapha ya ce "Malam tashi ka je ko mun koma Legos." Tashi ya yi shi ma ya shige, shi ma kamar na Alhaji ya fi awa kafin ya fito rigarshi saɓe kan kafaɗarsa, Boka ya fito yana wani tanɗe baki ya zauna a wajan zamansa ya kwashe da dariya, suma dariya suka yi ya nuna su da hannu ya ce " Ku tashi ku tafi in kun ga wani abu ba daidai ku dawo, ku fita da baya-baya." Haka suka tashi suka fita boka na musu rakiya da ruwan ashar har suka fita. Da sauri suka dinga sauka lokacin har dare ya yi dan a lokacin ƙarfe 10:pm na dare, da haske wayar su suka haska suka fita suka dinga tafiya har suka zo inda suka faka motarsu suak shiga suka bar wajan.. Suna isowa Legos ƙarfe 12 ta buga suka samu hôtel suka kwana washe gari suka Legos zuwa Yola.. Yau Suhal ya shirya shi da Sajida za su koma gida ba dan ya so tafiya ba sai dan kiran da Maimartaba yake masa da kuma Ikilima suna tambayar ko lafiya bai dawo ba, haka dai ya tattara ya nufi gidan su Baba dan ya musu sallama. Suna isa suka samu Zaiyan a harabar gidan ya ɗane kan bishiya mangwaro dake ɗan gefe da inda suka paka mota yana lilo. Sai ya kama rishe ya zuro kanshi ƙasa ya maƙale ƙafafun a jikin rishe ya dinga lilo yana ta dariya, jin ƙarar mota a gefen shi sai ya daina lilon ya tsaya cak shi bai sauko ba kuma bai koma ya zauna akan rishen ba kansa yana reto yake kallon motar har Sajida ta fito Suhal ya fito, ganin wanda ya fito sai ya sheƙe da dariya ya ce "Shege abokina ashe shi ma yana da jirgin sama." Da mamaki Suhal yake kallon Zaiyan ganin yadda ya ɗane sama ya zuro kai, ƙarasowa ya yi ya kalle shi ya yi murmushi ya ce "A a abokina me ya sa ka hau sama?" Lumshe idanu ya yi ya ce "Sabuwar masarautata ce nake son yin gini mai kyau, shi ne fa ka ga na zo ina koyon yadda ake ginin dan bana so Baba ya ce ba ta yi kyau ba." Dariya Suhal y yi har ita Sajida, kallon shi ya yi ganin yana masa dariya sai ya koma samar rishen yana Ɓata fuska ya ce "Ni fa na faɗa ma ka daina kula wannan Maman taka tun da haushi take ji dan ban ƙulla abota da ita ba, amma dai zan ke kallon ta tun da ita Mamanka ce." Sajida ta gumtse dariyar ta ta kalli Suhal ta ce "Allah ya ba ka haƙuri Zaiyan, ni ai bana jin haushi dan ba ka ƙulla abota da ni ba." Tim! Suka ji a bayan su suka waiga da sauri sai suka ga shi ne ya faɗo daga sama, tashi ya yi yana karkaɗe jikinsa ya ce "Ke dai Maman abokina bakya tsoron Allah, ki faɗi gaskiya kawai in ba wannan hular tawa kike so zan ba ki ita sai kike sakawa, ni fa da kike ganina na iya komai." Kamo hannunsa Suhal ya yi ya ce "Ka ga abokina rabu da ita muje ciki mu gaisa da su Inna za mu tafi Niger." Turus ya tsaya yana kallon Suhal, sai can kuma ya yi dariya ya ce "To amma abokina in ka tafi wa zai zuwa gidan mu yana sayo min wannan alewar mai zaƙi da kayan wasa?" Shafa kai Suhal ya yi yana yi murmushi ya ce "Ai a can ake yi shi ya sa zan je na kwaso ma mai yawa wadda za ka daɗe kana sha, kai har ma da kayan wasan zan sayo ma masu kyau." Tsalle ya yi ya rungume Suhal yana tare ya ce "Ashe kana tsoron Allah abokina?" Duk da Suhal ba ma'abocin dariya ba ne wannan karon sai da ya yi dariya jin abin da Suhal ya faɗa, ɗago shi ya yi ya ce "E ina tsoron Allah mana." Kama hannunshi Zaiyan ya yi suka nufi ciki yana kwara wa Inna kira. "Inna! Inna!". Da sauri Inna ta fito daga ɗaki a firgice dan ba ƙaramin tsoro ta ji ba da kiran da yake mata, ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Au ashe kune yake ta kira na? To sannun ku da zuwa." Suhal ya ce "E Inna mun zo yi muku Sallama ne daga nan za mu tafi Kano sai mu wuce gida daga can." "Allah sarki yaron nan Allah ya maka albarka, mun gode da taimakon da ka yi wa Zaiyan Allah y saka da alkhairi." Ta faɗa tana share hawaye. Murmushi ya yi da ya zame masa jiki ya ce "Haba dai Inna meye kuma na kuka ai a kowani lokaci za ku iya ganina na dawo nan garin, ina Baba yake?" "Malam bai ya nan, ya fita zuwa can unguwar da muka taso an yi wa maƙocin sa haihu ne ya je wajan bikin." Sallama ya mata tare da aje mata ɗaurin kudi ya juya zai tafi ya ji Zaiyan na magana. "Abokina kake jin tsoron Allah zan ke zuwa gidan ku gobe da jibi." To Suhal ya ce ya fita harabar gidan inda a nan suka hadu da Abdul da Abir sun iso gidan. Gaisawa suka yi sannan Suhal ya ce Sajida ta shiga mota, sai da ta iso kusan Abir ta ce "Abokiyar zama za mu wuce gida sai Allah ya kawo mana ke Niamey, na gode kwarai da kulawa Allah ya bar zumunci." Murmushi ta yi ta dafa Sajida ta ce "Kar ki wani damu ƴar'uwata ko gaishe da gida." To ta ce tana shiga mota. Suhal da Abdul suka koma gefe suka yi magana wadda ba wanda ya san me suka faɗa, bayan sun gama ya ce wa Abdul yana so zai yi magana da Abir ya ce masa ba komai ya shige mota yana jiran ta. Kallon ta ya yi ya ce " My Princess zan tafi ƙi kula min da kanki, ku kuma yi tunani na sosai kafin na isa gida na kira ki a waya." Gyaɗa masa kai ta yo saboda wata irin kunyarsa take ji ta mamaye ta, sai da ya sake magana sannan ta ce "To Ya Suhal a sauka lafiya Allah ya kiyaye hanya Mom da Grandma sun ce na gaishe da kai suna ma fatan alkhairi. Na gode sosai da karamci Ya Suhal?" Murmushi ya yi ya ce "Ba komai ni ma ki ce ina gaishe su sosai, mu za mu wuce ki kula da Zaiyan da kyau." Daga haka suka wuce, sai da suka ga tafiyar su kana suma suka tashi motar su, har Abdul ya ce su shiga Abir ta hana dole ya fasa suka tafi gida... Sai da suka zo kofar gida ya yi ya kalle ta da wani kalar yanayi ya ce "Ki je gida tun da kin ce yau ba ki da school." Raurau ta yi da idanu ganin yanayin sa, gabaɗaya ta kasa gane kan Yayan nata sai wasu irin halaye yake tsiro mata wanda ta kasa gane su, ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Yaya wai wani lefi na yi maka kake min irin wannan hukuncin? Why Yaya?" Shuru y yi bai ce mata komai ba zuciyarsa sai tafasa take, wato ma b ta san b abin da ta mi shi? Kawar kai ya yi yana jiran ta fita, ganin ta ɗago za ta sake masa magana ya janyo ta ya rungume yana bubbuga bayan ta, so yake ya ja da baya da ita ko zai samu sassauci in auren ta ya zo, amma ita kullum sai kuka tana ce masa me ta masa ya daina kula da ita.. Sai da ya ji ta daina kukan ya sake ta ya haɗiye wani kakkauran yawu mai daci, ya sanyaye ya ce "Ki je gida in na dawo daga office zan same ƙi mu yi magana." Jin haka ya sa ta tashi ta dauki Jakarta ta wuce, sai da ya ga ta shige sannan ya karya kan motarsa ya nufi Office.. Da dare ta yi ta jiran zuwan shi amma shuru, hakan ya sa ta kusan kwana tana kuka da tunani har sai da ta ji kanta n neman rabewa gida biyu ta haƙura ta kwanta.. Washegari ma haka ta yi dakon zuwan sa amma bai zo ba ta yi ta damuwa har Mom ta tambaye ta me ke damun ta ta ce ba komai... Kwankwasa kofar ake ba ƙaƙƙautawa Grandma da k zaune ta kwala wa Laraba kira ta fito a guje, kofar ta nuna mata ta buɗe sai ta ga Abdul ne jikin shi duk jin, ai da sauri ta ja da baya tana dafe ƙirji ta ce "Yaya Abdul me ye a jikin kayanka?" Duk da ba shiri suke ba amma yau sai ya ji ba zai iya hantarar ta ba, dogon numfashi ya ja sannan ya ce "Baby tana nan?" "E ba su jima da dawowa daga makaranta ba ita da su Hafsat.". Bai sake cewa komai ba ya iso ga grandma da ke riƙe da baki tana bin shi da kallo har ya durƙusa ƙas, a ruɗe ta ce "Abdullahi me ya faru da kai na ga jini a jikin ka?" "Riƙe kai ya yi da kyar ya ce "Grandma Mom ce mota ta buge ta, yanzu haka tana Asibiti b ta san wa yake kanta ba." Ya karashe maganar wasu zazzafan hawaye na zubo masa.. "Inna lillahi wa inna laihin raji'un!" Suka ji an furta daga bayan su, da sauri suka juyo suka ga Abir ta daura hannu a ka da Hafsat da Iman. Saurin isowa suka yi tana kuka ta ce "Yaya don Allah ka kai ni na ga Mommyna." Miƙewa y yi ya kama hannunta Grandma ta tashi ta yafa mayafinta suka ɗunguma zuwa harabar gidan, Laraba ma ta wato hijabinta ta sa ta bi bayan su tana kuka.. Sun zoza su shiga sai ga Ammi ta fito cikin shirin fita, ganin su ya sa ta dakata da shiga motar ta yo wajan ta ce "Inna lafiya dai na gan ku wasu na kuka?". "kayya ! Ina fa lafiya Farida wai Sa'ade ce mota ta bige ta yanzu hka ba ta san wa yake kan ta ba." Dikira Ammi ta dauka ta ce "Ai kuwa bari na fasa fitar nan muje Asibitin, ke Hafsat da Iman ku zo motata." Motar suka shiga cikin azama suka nufi Asibiti... _Taku har kullum Maman Nusaiba ce_ [10/30, 1:27 Safiya] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): ~A HAKA NAKE SON SHI~ +966577675904 Shafi na (26) Gudu sosai Abdul yake hankalinshi a matuƙar tashe, yadda ya bar Mommy yake ta tunawa sai zufa yake sharcewa yana fesar da zazzafar iska daga bakinsa. Abir kuwa ciwon ta ne ya tashi saboda hayaƙin da ta shaƙa da danger ta tsayar da su ta leƙo kai da kai dan ta ji iska wani mai mashine ya baɗe wajan da hayaƙi, hakan ya sa ta mayar da kanta da saurin gudun kar ta shaƙa, amma Inna har ta shaƙa nan-da-nan ta dinga tari tana laliben jakarta ta tuna ko wayarta ba ta dauƙo ba saboda kiɗimewa da ta yi.. Jin tarin nata ya yi yawa ne Abdul ya ɗan juyo ya ga tana dafe ƙirji, da sauri ya kalli Grandma ya ce "Grandma ɗaga nan please ki ɗauko wa Baby maganin ta ciwon ya tashi." Ya faɗa yana nuna mata lokar da ke gefen hannunta. Da sauri Grandma ta buɗe hannu na rawa ta fito da shi, zuwa lokacin har ta soma fita daga haiycinta ta juyo ta janyo hannunta ta kafa mata maganin a baki, sai da ta danna ta shaƙa sau uku kafin ta ji ta dawo daidai.. Suna isowa duk suka fito suka nufi ciki da sauri yana riƙe da hannun Abir, emergency room suka nufa gaf da wani ɗaki wanda in har aka shiga da mutum to fa lalle hatsarin da ya yi ko cutar da ke damunsa ta mugun tsananta. Kuka ta dinga yi tana addu'ar Allah ya fito mata da Mommynta, ganin tsayuwar ta yi yawa ne suka koma kan kujerun da ke gefe suka zauna suna jiran fitowar likitocin.. Sun fi awa biyu suka suna zaune har Ammi ta fara ƙosawa saboda kiran da ake mata a waya sai aka buɗe ƙofar, da sauri duk suka tashi suka yi kan doctor suna tambayar shi ya jikin Mom? Buɗe baki Abdul ya yi zai yi magana ya ga an turo gadon da aka ɗauki Mom da shi, dam! Gaban shi ya faɗi ya ƙura wa gadon idanu, ganin za su wuce Abir ta kalli Doctor Hashim cikin kuka ta ce "Yaya Hashim ina Mom ɗi na?" Girgiza mata kai ya yi sannan ya ce "Gaskiya jikin nata ya tsanan ta amma ta ce tana son ganin Abdul da ke." Da sauri ta damƙi hannun Abdul tana kuka ta ja shi suka nufi ciki, a kwance suka gan ta an sa mata ƙarin jini ɗayan hannun kuma ruwa ne aka jona mata, na'urar da ke nuna yadda numfashinta ke tafiya Abdul ya kalla ya ga tana tafiya ahankali-ahankali. Lumshe idanu ya yi yana jin gaban shi na ƙara tsananta bugawa, hannu ta miƙa musu ganin haka ya sa Abir ta rushe da kuka ta isa kusa da ita ta kwanta kanta a cikin Mom tana rera kuka mai tsuma zuciya. Da ƙyar Mom ta ɗaura hannunta a kan Abir cikin wata kalar murya mai karyar da zuciyar mai karatu ta ɗago da idanuwanta ta kalli Abdul ta ce "Yarona zo nan." Zama ya yi a ɗayar kujerar ya kama hannunta wanda ta ɗaura akan Abir ya janye ya riƙe cike da rauni yake kallon Mom, ba zai kwatanta tashin hankalin da yake ciki ba na ganin wadda ta kasance Yayar uwa a gareshi kuma gurbin uwar da ta haife shi a wannan halin, lumshe idanu Mom ta yi ta sauke ajiyar zuciya tana fitar da numfashi a hankali ta soma magana.. "Abdul ga ƙanwar ka nan ka kula da ita, ka maye mata gurbin uwa, uba ɗan'uwa, ka zame mata bango abin jingina da za ta raɓa ta ji daɗi. Abdul ka da ka bari Abir ta zubar da hawayen maraicin uwa da uba, ka kula min da ita ka ɗaura ta akan hanya mai kyau kar ka bari ta tara ƙawayen banza wanda za su ɓata mata tarbiya." Hawaye ne ke bin kuncin Abdul duk dauriyar shi ji ya yi ya kasa, kai ya jinjina wa Mom ya ce "Mom ki daina irin wannan maganar in sha Allah za ki tashi, kuma dama Baby ai tawa ce ko kina raye nine zan kula da komai na rayuwarta har ƙarshen tawa rayuwar.." Murmushi mai ciwo Mom ta yi ta nisa ta ce "A kullum kana tambaya ta shin ina dangina suke? To yau zan sanar da kai asalin mu ni da ƴar'uwata marigayiya, har da tarihin Maitama family duk zan sanar da kai in Allah ya ba ni damar faɗa ma duka." Gyaɗa kai ya yi yana goge hawaye, ya ɗauki shekaru sama a ashirin yana tambayar Mom ina ahalinta suke? A wata ƙasa suke? Ko daga ita sai mahaifiyarsa kawai ba su da kowa? Har Baba Malam ya je ya tambaya amma ya ce bai san komai ba, kallon Mom ya yi ya ce "Mom ina jin ki ko na ce muna jin ki." "Iyayenmu 'yan ƙasar Niger ne amma ba nan suke da zama ba a nan Nigeria suke rayuwar su, mahafinmu ya kasance Jakadan yan Niger ne a nan Nigeria. Tun da aka yi wa Babanmu aure ya kwaso matarsa mai suna Aisha wadda a garin su ake kiran ta da Shatu suka dawo Kano da zama, auren su da shekara biyu ta haifi 'yan biyu mata wato ni da 'yar'uwata, ni ce Hassana ita ce Usaina. Shakara biyu da haihuwar mu ta sake haifo mace wadda ita ce mahifiyarka,. Mun taso cikin so da ƙaunar juna kanmu a haɗe yake. Haka muka yi ta girma muna karatu har muka kai mun gama secondary school, mu na shirin shiga jami'a ne wata ranar Juma'a Baba ya je Sallar Juma'a bai dawo da ƙafarsa ba sai gawar shi aka kawo gida, mun yi kuka kamar za mu shiɗe musamman Mama har suma ta yi, haka muna ji muna gani aka masa wanda aka kai shi gidansa na gaskiya, bayan an dawo aka ci gaba da karɓar gaisuwa har na tsayin kwana bakwai sannan aka bar mu daga mu sai Mama, sai wasu 'yan' uwanta mace da namiji su biyu da suka zo daga garin su Mama Maradi, sai kuma dangin Baba Kawu Sule da Ladidi,, .. Bayan kwana biyu suma suka shirya suka ce Mama ta haɗa komai nata mu tafi, amma sai Baba Malam da yake maƙocin mu ya ce sam kar su tafi da mu su bar mu mu gama karatu zai kula da rayuwar mu in sha Allah. Ai kuwa Kawu Sule ya ce da mu zai tafi mu Maradi tun da zama ba wani zuwa muke ba sai ana wata sabgar kasancewar 'yan'uwan Baba ba son Mama suke ba, Yayan Mama ya fusata ya ce babu wanda ya isa ya raba mu da mahaifiyarmu tun da ba son mu suke ba ba za mu bi su ba su dinga azabtar da mu, da kyar Baba Malam ya raba su suna shirin yin dambe. Haka Kawu Sule ya zazzagi Mama tatas ya ce dama ita ce ta yi sanadin mutuwar shi, ba ta kula shi ba ya ce sai an raba gadon su an ba su tun da gidan nan mallakin Baba ne, haka Yayan Mama ya zuciya ya ce Baba Malam y raba gadon su ya ba su.. Haka aka raba gado dama Baba gida biyu gare shi wanda ake haya a ciki, da aka raba mu muka ci gidan da muke ciki, suma aka ba su na su inda suka ci gida daya. Sai da suka sayar da gidan aka ba su kudin su sannan suka bar Kano. Washegari Yayan Mama suka shirya da ƙyar suka yarda suka bar mu a nan Mama na kuka ta rabu da 'yan'uwanta suka tafi gida, haka muka shiga Jami'a muna ta karatu ba ma kula kowa saboda kashedin da Mama ta yi mana, mun shiga aji na biyu a nan ne na haɗu da wani mai suna Ibrahim in da kai tsaye ya ce yana sona, amma na ce masa ya yi hakuri an hanani kula samari, amma yaƙi ji yake ta bibiya ta har sai da Hajara ta ce na haƙura na kula shi, ba dan na so ba nake kula shi... Muna gama jami'a ya zo gidanmu inda Mama ta haɗa shi da Baba Malam ya ce aurena yake son yi, a lokacin shekarun mu 18 Hajara 16. Baba Malam ya sanar da shi mu marayu ne Babanmu ya rasu in ya san yaudara ta ya zo yi kamar yadda wasu ɗiyan masu ke yi wa ɗiyan talakawa ya tafi, sai da ya rantse ya ce shi ba haka yake ba sona yake tsakani da Allah Baba Malam ya tambayi sunan iyayen shi, inda yake sanar masa sunan mahaifinsa Abdullahi Maitama. Jin sunan babban mutum Baba Malam ya cika da mamaki amma ya kawar ya ce ya turo magabatan sa ayi maganar gemu da gemu, cikin jin daɗi ya tafi gida ya sanar da mahaifinsa komai. Baban Ibrahim mutum ne mai karamci da sanin darajar talaka haka ma matarsa wato mahaifiyar Ibrahim, bayan sati da maganar suka zo gidanmu inda suka yi maganar komai Baba Malam da ya zame mana uba ya yi bacike akan Ibrahim, inda bai samu wata matsala daga ɗabi'u ko halayensa ba hakan ya sa ya amince ya ba shi aurena aka sa bikin wata ɗaya tak.. Mama ta tura wa dangin baba da danginta maganar an sa ranar bikina, ai kuwa takanas Kawu Sule ya zo har Kano ya ci mutumcin Mama ya ce bai aminci da auren nan ba ɗansa shi ne mijin da zan aura ba wani bare ba, na yi ta kuka saboda za a rabani da Ibrahim wanda nake tsananin so, Haka ya yi ta masifa ya ce kuma da mu zai tafi dama ai ya kyale mu ne mu gama jami'a aure zai mana a can garin su Baba da ɗiyan 'yan'uwan shi, muna ta kuka ya ce sai mun haɗa kayan mu mun bi sa ai kuwa Mama ta shaƙa ta nuna masa matsayin ta na uwa, ta ce masa bai isa ba ya tafi da mu tun da ba shi da mutumci, tun da Baban mu ya rasu ba su taba cewa bari su zo su ganmu ko su taimaka mana ba, ko mun shirya za mu sai ya ce kar mu zo sai ya ce mu zo, sai da ta masa tas sannan ta mayar da mu ɗaki ta ce ba inda za mu je. Sosai Kawu Sule ya ji zafin maganar da Mama ta faɗa masa haka ya tafi ya ce ranar biki sai sun zo, Mama ta ce in sun ga dama kar Allah ya sa su zo haka dai ranar muka wuni ba daɗi.. Lokacin biki na yi Kawu Sule da tawagar su suka zo har dangin Mama, an sha biki aka kai ni J. R. A inda dangin Baba ke zuzuta kyan gidan da Ibrahim ya gina min, bayan biki da kwana biyu Ƙanen mijina mai suna Kabir ya ga Hajara ya ce shi fa lalle a aura masa Hajara cikin satin nan, lokacin su Kawu Sule ba su tafi ba Daddyn su ya zo ya nemi auren Hajara a wajan Kawu Sule, ganin kuɗin da aka kawo na na gani ina so da sadaki Kawu Sule ya ruɗe ya ce ya bai wa Kabir Hajara yana son nan da kwana biyu a ɗaura aure sai su wuce maradi. Sosai Kabir ya yi murna bayan kwana biyu aka ɗaura auren su, washegari aka yi walima aka kai Hajara gidan Kabir, sosai Usaina ke kuka ganin sai ita kaɗai haka muka dinga rarrashin ta muna faɗa mata itama nata mijin na hanya.. Zaman auren mu a gidajenmu ba wata matsala, sai dai matsalar dangin miji yan uwan Daddyn su Ibrahim. Family Maitama ahali ne masu yawa suna da matasa da samari ba lefi, Grandma yaran ta biyar Ibrahim, Kabir, Sulaiman, Nabila, Yasira. Nabila da Yasira duk an musu aure da yaran su, Yasira na Madina da mijinta, Nabila na Gemerny da mijinta. So asalin Fulanin Yola ne, kasuwanci ya dawo da mahaifin Ibrahim Kano inda duk ya daura su kan kasuwancin, duk cikin su Ibrahim ya fi kwazo dan haka ya tara duniya sosai yana da kamfanin motoci a nan Kano, yana da shaguna a kwari na sayar ta atamfofi da duk wani nau'in kayan sakawa a jiki, yana hulɗa da manyan 'yan kasuwa na ƙasashen Africa. Sulaiman shi ke kula da shagunan da ke kantin kwari, shi kuma Kabir ma'aikacin banki ne.. Ƙannen mazajenmu basa nuna mana tsangwama ko kaɗan hasali ma so da kauna suke nuna mana kamar yan uwansu na jini haka muke wasa da dariya, a ɓangaren dangin Daddy kuwa ba mai son mu yan'uwansa mata biyu da namiji ɗaya, matan su ke nuna basa son mu saboda sun so su haɗa yaransu aure da su Ibrahim su kuma sun ce basa so, namiji ne mai suna Alhaji Ishaq bai taba nuna mana rashin so ba sai matar shi da ɗiyan ta ke nuna mana tsani da kyara.. Shekarar mu ɗaya da aure na samu ciki, zo ku ga murna wajan Kabir har walima ya haɗa mana a gidan, haka na dinga samun kulawa ta ko'ina daga wajan mijina har Inna har cikina ya kai mawar haihuwa na ce zan tafi zaman haihuwa, ai kuwa Inna ta ce ba inda zan je ita za ta kula da ni. Ganin wannan karamci na Inna sai Mama ta haƙura ta bar ni a gidana, cikina na isa haihuwa na haifo yaro na namiji kyakkyawa fari tas mai kama da baban shi, ranar an sha murna da yamma aka taso ni muka dawo gida aka ci gaba da kulawa da ni, ranar suna yaro ya ci sunan Daddy aka sha hidima. Bayan suna Mama ta ce za ta ɗauke ni na yi wanka a gida amma Inna ta ce a bar ni a gidanta ita za kula da ni, sosai Mama ta ji daɗi ganin yadda surukar mu ke matukar son mu. Yarona na cika wata da haihuwa wata ranar Lahadi jikin shi ya ɗau zafi muka nufi Asibiti, ko da muka je ana ɗaura shi a gado ya rasu, na sha kuka kamar ba gobe saboda na kwallafa rai a kan yaron. Sai da na cika arba'in sannan aka dawo da ni gidana muka ci gaba da rayuwa.. Bayan wata biyu na samu wani cikin muna ta murna har ya kai wata biyar aka yi taro a familyn Maitama muka tafi wajan taron Ibrahim na lallaba ni. Ƙanwar Daddy na gani na ta dinga sababi wai an zo musu taron family da bare, ni kuma na yi shuru ina kawar da kaina gefe saboda bana son na mata rashin kunya a gaban mijina ya ji ba daɗi, Inna ce ta mata tatas ta ce kuma ko da wasa ta sake zagina sai ta rama min tun da abin nata ya wuce gona da iri. Bayan an gama taro na na ɗan zaga harabar gidan ina shan iska sai ji na yi an bangaje ni na yi saurin direwa Allah ya taimake ni ban fadi ba, juyowar da zan yi na ga Hajiya tana jijjiga jiki ta ce "Maiya mai farar ƙafa Wallahi mu dai Hauwa'u ta cuce mu da ta bari jinin mu ya auri dangin tsiya, kuma Wallahi ba ki isa ba ki haihu a wannan gidan kin yi kaɗan matuƙar ina raye, ba za mu haɗa jini da masu farar ƙafa ba dangin matsiyata." Shuru na yi ina kallon ta har ta gama sannan na ce mata "Hajiya kenan, ai ke ba ki isa ki hanani haihuwa ba tun da ba ke kike ba da haihuwar ba Allah ke badawa, kuma ina ganin girman ki sosai saboda kina kanwar mahifin mijina, amma ba dan haka ba tsaf zan cire miki ɗankwali Wallahi ki kama girman ki na suruka ta." Zagina ta dinga yi tana faɗa min baƙaƙen maganganu, ni kuma da na gaji da ji na koma ciki tare da ɓoye damuwata dan kar Inna ta gani ta tambaye ni dalili. Bayan mun koma gida cikin dare ciwon ciki mai tsanani ya mamaye ni, haka muka nufi Asibiti aka shigar da ni dakin taimakon gaggawa, gari na wayewa cikin jikina ya ɓare.. Bayan wata biyu da hakan labari mai daɗi ya zo mana, Usaina ta samu mijin aure itama a nan Kano yake, amma ba ɗan garin ba ne amma a nan aka haife shi kamar mu, sai da Baba Malam ya kira Kawu Sale ya sanar da shi Usaina an zo neman auren ta ko ya tura su can Maradin? Kawu Sale ya ce kawai Baba Malam ya sa rana in dai ya yi bincike akan yaron, haka kuwa aka yi suna zuwa bayan kwana biyu aka sa biki nan da wata biyu Usaina murna take sosai, a lokacin kuma Mama na fama da ciwon zuciya yanayin kuzarin ta ya ragu amma dan kar ta tayar mana da hankali ta daure. Lokacin biki na yi aka yi shagali su Kawu Sule sun zo wannan karon sai nan-nan yake da mu har aka gama biki suka koma maradi. Usaina shekarar ta daya da aure ta samu ciki muka shiga murna da farin ciki marar musaltuwa, kwatsam cikin Usaina na cika wata tara wata ranar Asabar wadda ta zame mana baƙar rana, gidan su Usaina ya kama da wuta ƙurmus komai ya ƙone na gidan har su gabadaya babu wanda aka iya ceto kasancewar gobarar dare ce, ranar kamar na yi hauka saboda wannan tashin hankali sai da muka kwana a asibiti daga ni har Hajara da Mama,. Bayan mun farfado aka musu zaman makoki na kwana bakwai aka musu addu'a, sosai na shiga damuwa na rashin Usainata mun shaƙu fiye da Hajara hakan ya sa na fi Hajara shi ga damuwa. Watan su biyu da mutuwa na kuma samun ciki wannan karon tare muka samu da Hajara, ban yi wata murna ba na dinga addu'a cikin na yin wata uku shi ma ya zube, Hajara kuwa lokacin haihuwa na yi ta haifo ɗanta namiji fari tas mai kama da ita wato kai. " Ta ɗan nisa ta ci gaba, "Ranar suna aka mayar da sunan yarona na farko, haka na dinga kula da kai sai bacci yake rabani da kai, kana yin wata biyu na samu wani cikin ina ta tunani ban kuma kwallafa rai ba akan cikin ganin duk wanda na samu zubewa yake, har cikin ya kai watan haihuwa kullum fargaba nake, ranar Litinin ina jin naƙuda kaɗan-kaɗan cikin dare na yi wani mugun mafarki ina farkawa jini ya ɓalle min, kafin ma muje Asibiti na haifi yaro namiji bai zo da rai ba. Haka aka gyara ni Hajara take kula da ni dan yanzu Mama na fama da rashin lafiya sosai, ana tsaka da haka cikin dare Mama ta ce ga garin ku nan ta mutu ta bar mu. Mun sha kuka kamar ba gobe da kyar muka dawo kaiyacin mu ni da Hajara, Kawu Sule na kira amma bai dauka ba bai zo ba wajan mutuwar, har su dangin Mama babu wanda ya zo muka yi ta mamaki. Su Hajiya da suka zo gaisuwa suka dinga faɗa mana baƙaƙen maganganu Surukar mu ta musu cin mutumci ta kore su, bayan mutuwar Mama komai ya mana zafi duk da ba ci ko sha ko sutura muka rasa ba, kawai in muka tuna mu marayu ne gaba da baya babu wanda za mu yi shawara da shi duk da akwai surukar mu da take iya bakin ƙoƙarin ta wajan ɗebe mana kewar iyayenmu.. Watan ka uku da haihuwa Hajara ta kamu da cancer nono sai madara ake ba ka, ganin ban daɗe da haihuwa ba sai na yi wa mijina magana akan a kawo min kai na soma shayar da kai ganin yadda ka soma ramewa, bai musa ba ya nemi Daddyn ka a waya ya faɗa masa ganin ba ya gida amma bai same shi ba, sai kawai ya je a ɗauko min kai kana ta tsala kuka kaƙi ka sha madara, haka na wanke nonona na yi kunun alkama da duk abin da zai kawo ruwan nono dan ka samu ka sha. kwana uku da kawo ka ruwan nono ya zo na dinga shayar da kai, shi kuma mahaifin ka da ya neme ka sai Hajara ta ce ai kana wajena na dauke ka dan itama ban ce mata shayar da kai zan yi ba iya mijina da Inna na faɗawa.. Haka ka yi ta girma har na yaye ka, zuwa lokacin Hajara ta warke tas sai tafiya ta sami Kabir suka bar min kai suka yi tafiyar su Dubai, sai da suka cika shekara hudu ciwon ƙafa ya kama Hajara dole suka dawo Nigeria, ganin ta a wannan halin hankalina ya tashi na shiga nema mata magani ni da Kabir duk inda muka ji mai magani sai mun je. Sai da ta kusa shekara a cikin wannan yanayin da yamma daga shiga toilet sai fiddo gawar ta aka yi, na yi kuka na rasa yadda zan yi na dawo ni kaɗai ina ji ina gani aka yi mata wanka aka kai ta makwancinta, na ci gaba da kulawa da kai Kabir kuma ya shiga damuwa na rashin matarsa, Hajara na cika wata biyar da mutuwa Hajiya ta zo gidan ta ce lalle sai Kabir ya yi aure ba zai zauna ba mata ba tun da ƙanen shi Sulaiman zai auri ƴar ɗan'uwansu shi za ta aura masa Baraka yar wajan ta, Sam ya nuna ba ya son Bakara saboda ta mugun raina shi dan a lokacin ma tana ƙasar waje tana karatu, amma Hajiya ta je ta ƙulla makircin ta har da kukan wai na asirce Kabir so nake na je Maradi na kawo wata a dangina na aura masa. Haka ta dage sai da ta shayo kan baban su Kabir ya ce ya auri Baraka aka sa bikin lokaci ɗaya da na Sulaiman, haka aka yi ta hidima ranar biki aka gama ni dai ina cikin jima min rashin ƙanwata ban wani yi walwala ba, hakan ya sa dangin su Daddy ke zagina wai kishi nake taya gawa, raina ya ɓaci zuciyata ta sosu na yi ta kuka na dawo gida.. Bayan bikin su gabaɗaya muka tashi daga Kano muka koma babban gidan Maitama Family wanda Daddy ya gina amma ya ce ba zai bar Kano ba tun da part uku ne mu mu zauna kawai, haka muka haɗa komai namu muka dawo Yola da zama na sha kuka da nake gidan Baba Malam zan masa Sallama. Bayan mun koma na zama saniyar ware su Farida ba sa ganina da mutumci kullum rashin kunya suke min, amma haka nake dannewa na rabu da su na ci gaba da kula da kai dan a lokacin na fidda rai da haihuwa. Sai da Farida ta haifi yara biyu Salim da Yasmin, Baraka ta haifi Khairat sannan na samu wani cikin, a lokacin kana da shekara tara ka dinga murna kaima za ka samu kanwa. Cikina na kai wa watan haihuwa na haifi yata mace wato ta ci sunan Inna *Hauwa'u Maijidda* wa ke Abir, wadda na cire rai za ta taka ƙasa, tun da aka haife ta ta tashi da farin jini Kabir har Office yake zuwa da ita, shi kuma Sulaiman sai ya ga ta yi bacci ko tana kuka yake kawo min ita, komai suka samu mai sunan Innar su za su kai wa. Wannan abu na kona wa Farida da Baraka rai suka ɗauki karan tsana suka ɗaura mata, ko wajan su Salim ta je yin wasa koro ta suke su mata duka ta sha kukan ta ta more, in kuma kana nan za ka goya ta ku yi ta wasa. Shekarar ta shida wata rana tana fita zuwa wajan su Salim ta faɗi a ƙasa sai kawai ta dinga yin abu kamar mai farfaɗiya, hankali a tashe muka nufi Asibiti aka soma ba ta taimakon gaggawa..... _Taku har kullum Maman Nusaiba._ [6/20, 7:55 PM] Ummu Amjad: ~A HAKA NAKE SON SHI~ Littafin A HAKA NAKE SON SHI na kuɗi ne, idan har kin gan shi a waje to na sata ne kika karanta. Ga du mai buƙatar shi sai ya neme ni ta whatsapp number na 👇🏻 +966577675904 Shafi na (27) Muna tsaye a bakin ƙofar ɗakin da aka shigar da ita ni da Abban ta duk hankalin mu a tashe, sai da suka kwashe minti talatin kafin aka buɗe ƙofar, da sauri muka nufi likita muna tambayar shi jikin Abir wanda ya kasance uba ne ga Doctor Hashim. Cewa ya yi mu bi shi office ɗin shi, Kamar na shiga ɗakin amma haka na haƙura muka rankaya zuwa office ɗin sa. Bayan ya gama rubuce-rubuce ya soma mana bayanin abin da ke damun ta. "Alhaji gaskiyar magana yarinyar ku ta kamu da cutar asma, yanzu ma abin da ya tayar mata da cutar hayaƙi ta shaƙa shi ne musabbabin ganin ta a haka. Amma ku kwantar da hankalin ku in sha Allah za ta samu lafiya zan ɗaura ta a kan wani magani wanda in ciwon ya taso mata za ta shaƙa shi, sannan zan ba ku ƙwayoyi ta yadda zai dinga kawar da cutar a hankali har ta warke." Tashin hankalin da muka shiga ba shi da iyaka na yi ta kuka saboda ita kaɗai na haifa da zan kalla na ji sanyi irin yadda kowacce mace ke ji in ta kalli ɗanta. Bayan ba mu shawarwari da magunguna ya ce za mu iya ganin ta ƙila ma ta farfaɗo, ni ce a gaba na riga shi shiga inda na hango ta zaune a kan gadon tana ta kallon ɗakin, ganina ya sa ta dinga kiran sunana tana cewa "Mom nan ɗin ina ne?" Rungume ta na yi ina kuka Likita ya zo ya cire mata allurar ƙarin ruwan da ya sa mata ta ƙare, ya rubuta mana sallama muka dawo gida.. Tun daga ranar na ƙara sa idanu akan ta bana bari ta je inda ake tashin ƙura ko ta yi gudu, hakan ya sa har ta yi shekara ciwon bai taɓa tashi ba hakan ya yi min daɗi. Ba wanda ya san tana da ciwon a lokacin har kai kanka sai wata rana Abban Abir ke sanar da Kabir da Sulaiman, ban san ya aka yi ba su Farida suka ji maganar ba washegari kamar haɗin baki Hajiyar Baraka ta zo ita da babban ɗanta wanda sai a watan da ya gabata na san shi ne Daddyn Aruf, wanda shi bai yo halin Hajiyar su ba mutum ne mai kirki. Bayan mun gaisa yake sanar da ni matarsa na gaishe ni na ce ina masawa na tambayi Aruf ya ce yana nan lafiya sannan ya min sallama ya tafi. Sai da suka ga ya tafi Hajiya na ta soma zazzagina, ban ce da ita komai har ta zauna naje kitchen na kawo mata lemo mai sanyi da ruwa na aje a gaban ta ina kawar da ɓacin raina na ce "Hajiya sannu da zuwa ga ruwa ki jiƙa maƙoshinki kafin na ƙarasa girki." Kallon banza ta mini tana yatsina fuska ta buɗe mayafinta tana kaɗa ƙafa ta ce "Kin ga alama yunwa a tare da ni? Ko an faɗa miki ni dangin matsiyata ce da har zan so na ci abincinki wanda ki ka gama barbaɗe shi da guba na ci? To ki kama kanki ƴar matsiyata kawai, kuma Wallahi sai na sa Ibrahim ya sake ki ya auri ƙanwar sa Ilham dan mun gaji da zaman ki a gidan nan bakya haihuwa, sai dai ki ci ki sha ki yi kashi amma ba a iya haihuwa na. Tun da kika haifi wannan ƴar taki mai suffar mayu ba ki sake haihuwa ba, ko da yake ita ɗin ma sunan tana raye ne tun da farfaɗiya take, kin ga kuwa ko ta girma babu wanda zai auri mai cutar hauka da sunan matarsa, dan haka dole ma ki bar gidan nan ko kina so ko bakya so sai kin koma inda kika fito kin mallake mana ɗa sai yadda ki ka yi da shi, har su iyayen nasa kin mallake su to ni da yake a tsaye nake a kan ƙafafuna na gagare ki, shi ya sa duk abin da na ce wa Yaya a kanki ba ya yarda sai ya ce na cika ƙorafi, Allah dai ya raba mu da dangin jaraba 'yan anace." Hawayen da suka cika idanu ne suka zubo na yi saurin miƙewa ina kawar da kaina gefe dan kar su gani, sai dai ina Baraka ta gani ai kuwa ta sheƙe da dariya tana cewa "Wallahi kuwa Mama ai sai dai mutum zuciyarsa ta buga ya mutu saboda kishi, amma ƙanwata sai ta shigo gidan nan a matsayin matar Yaya Ibrahim. In kuma ƙawar ki za ki nemo ta aure shi kamar yadda kika aurawa Kabir wannan mummunar to sai ki soma kira ta ki faɗa mata. " Tana gama faɗin haka ta wuce dan dama Hajiyar tun da ta faɗa min baƙaƙen maganganu ta bar palon. Damƙo ta na yi ta yo baya ina huci na zabga mata mari mai shiga jiki na nuna da yatsa na ce "Ai da Ibrahim ya auri ƴar tasha gara na aura masa ƙawar tawa, tun da ita mutuniyar kirki ce ba irin ku ba masu bin bokaye da aikata saɓon Allah, kuma maganar na aurawa Kabir ƙawata waye ya ce miki ƙawata ce ita?" Cikin jin zafin marin ta ce. "Ban sani ba yar wahala, ƙawar ki ce mana Kabir ya faɗa min ke ki ka ce ya auri ƙawar ki ba wani son ta yake ba kawai rabon Abdul ne." Sake ɗaga hannu na yi zan ƙara mata wani marin naji an riƙe hannunna na juyo a fusace dan a lokacin ina jin komai ba zan iya yi saboda na kai maƙura, kallo na ya yi yana sauke hannuna ƙasa ya ce "Haba Sadiya me ya yi zafi haka ke da kike da mutumcin ki za ki biya marar sa daraja kuke faɗa?." Ajiyar na sauke na sunkuyar da kaina na fashe da kuka ita kuma Baraka ta tafi riƙe da kunci tana zagina, ruwa mai sanyi ya ba ni na sha sannan naji sanyi a zuciyata, nan ya tambaye ni abin da ya haɗa mu na faɗa masa komai. Tashi ya yi tsaye dan dama shi mutum ne mai fusata kamar kai, ban san me ya faru fa ba dai sai kiran Inna na gani na dauka ta dinga ba ni hakuri akan abin da Hajiya ta mini na ce ba komai... Haka muka ci gaba da rayuwa ina ta addu'a Allah ya ba ni ciki ko dan gorin da suke min, amma ban samu ba..." Katse Mom Abdul ya yi ya ce "To amma Mom ya aka yi har tsayin lokacin nan Umma ba ta san Mamana sister ɗin ki ba ce ? , kuma na ga a baya da kika yi rayuwar ki ba a kiran ki da Sadiya ko me ya sa?" Numfashi ta sauke tana murmushi ta ce "Abin da ya sa ba a kira na da Sadiya saboda sunan Mahaifiyar Baba ne, shi ne Mama ke kira na da Hassana sunan tagwaitaka ta, ita kuma Baraka Kabir ne ya ce mata mamanka ƙawata ce saboda ta tsaneni dan ita ba girman nan ba ce a wajan Yasira ta girma ba ta shiga mutane sai girman kai, shi y sa ko wani abu aka yi a familyn ku ba ta sani kuma ko daga baya ta ji b ta damuwa, hakan ya sa wai dan ta ƙuntata min ta dage sai an ba ta kai ta riƙe ka wai kar na goga maka baƙin jini irin nawa. Da farko ya ce mata sam ba zai iya tunkara ta ba ya ce na ba shi kai zai bai wa matarsa ta ci gaba da ruƙon ka, amma fir ta tashi masifa kullum sai ta zo a part ɗi na ta min tatas ta uwa ta uba, wani lokacin ma sai ta kama sunan iyayena yake zagi amma na rabu da ita ta zageni ta gaji ta koma gidanta. Ni kuma ganin hakan na tattara ka na kai mata na ce ga ka nan amana, idan ta yi da kyau za ta gani ta faɗa min baƙar magana na kyale ta na wucewa ta. Wata rana kwatsam da Asuba Inna ta kira Kabir ta sanar da shi Daddy ya rasu, haka muka tattara muka tafi Kano wajan mutuwa. Muna zuwa na sulale na tafi gidan Baba Malam in da na same shi ba yadda yake, sana'ar da yake jarin ya ƙare ko fita waje ba ya yi da kyar suke samu suna ci, na yi kuka ina cewa Baba Malam "Baba kenan yanzu ba ka dauke ni a matsayin ƴar da ka haifa ba? Me ya sa ba ka sanar da ni ba halin da kake ciki Baba?" Haƙuri ya ba ni ya ce baya so ya tayar min da hankali ne shi ya sa, haka na wuni a gidan na sa aka sayo buhun shinkafa da duk abin da za su buƙata aka kawo musu gidan dan a lokacin ina busyness ɗin sayar da kayan kitchen.. Bayan an yi sadakar bakwai su Kabir suka tattara Inna suka ce ta dawo kusa da su, da farko ta ƙi yarda ta ce rugar su za ta koma wajan 'yan'uwanta suka ƙi amincewa dole ta haƙura muka tafi Yola da ita. Bayan mun je na samu Abban Abir na sanar da shi halin da Baba Malam yake ciki, inda ya nuna bai ji daɗi ba da ban faɗa masa ba tun muna Kano, na ba shi haƙuri ya ce zai gani zai yi wani abu na masa godiya dan duk Nigeria ba ni da wanda ya kai Baba Malam.. Bayan kwana biyu da maganar sai ya ce na shirya zai kai ni wani waje na shirya ni da kai da Abir in za ka iya tunawa lokacin da muka je wani gida a nan muka samu Baba Malam da iyalansa. " Gyaɗa kai Abdul ya yi yana ƙara riƙe hannun Mom, tari ta dinga yi suna mata sannu har ya tsaya sannan ta ci gaba.. "Ranar na yi farin ciki marar musaltuwa na yi ta yi wa Abban Abir godiya har da kuka ganin yadda ya inganta rayuwar yaran Baba Malam, ya saka su a makaranta boko da Islamiya ya saya musu gida ɗan madaidaici, har shi kan sa Baba Malam ɗin ya ba si jari ya dinga sayar da kayan abinci irin su shinkafa, taliya, kayan miya, da dai sauran su.. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya har Allah ya yi wa Abokin Abban Abir Alhaji Mustapha dawowa daga America, nan fa suka ɓarke da zuminci har ni da matarsa muna ziyartar juna. Samun ta a daidai wannan lokaci ya min daɗi saboda Hajiya Nafisa mace ce mai wayewa da girmama mutum, sosai muke zuminci har muka zama Aminan juna inda da an yi hutu za ta buƙaci na kai mata Abir na sa a kai ta da ƴarta Hafsat su yi ta wasa, hakan ya sa naji kamar Hajara ce ko Usaina a tare da ni babu abin da nake boye mata na rayuwata itama ba ta boye min komai nata.. Matsalar daya Abir ba ta son zuwa gidan su tun da ta kai shekaru 10 ta daina zuwa, ko Hafsat ta zo gidanmu sai ta yi ta share ta ita kuma ba ta zuciya da an sake hutu sai ta dawo.. Tun da kowa ya san Abir na da wannan ciwon ba damar ta fita cikin su Yasmin wasa sai su ja ta cikin gidan su, Farida ko Baraka da sun gan ta za su sa turaren wuta ya yi hayaƙi sosai sai su rufe kitchen ɗin su ce mata ta zo ta dauko musu ruwa ko cup, da ta shiga numfashinta zai sarƙe ta yi ta fama in sun ga tana neman mutuwa sai su dauko ta su kawo ta bakin kofa su koma da gudu, an yi haka ya fi sau biyar na gaji na je har part ɗin su na ci mutumcin su na kuma faɗa wa mazajensu komai, ranar sai da kowacce ta kwana a gidan su dan sun ce ba za su yarda suke wulaƙanta musu ɗiyar ɗan'uwa ba itama mutum ce mai gata fiye da kowa na gidan, hakan ya tada fitina suka kore su har sai da suka yi kwana biyu sannan aka dawo da su.. Tun daga ranar suka ƙara tsanar ta ni ma da na san da haka na hana ta zuwa inda suke, a lokacin kai kuma kana can wajan ƙanwar su Kabir Yasira da ke Gemerny. Sosai Allah ya buɗa wa Abban Abir dan kaf family Maitama babu wanda ya kama ƙafarsa a kuɗi har wanda suke ƙasar waje duk ba su kai shi kuɗi ba, hakan ya sa Hajiya ke ta shiga da fita wajan ganin ƴarta ta aure shi, shi kuma ya ce mata ba ya buƙatar wani aure ni kadai na ishe shi a rayuwa, ai kuwa ta dinga kukan markici ta ce na asirce shi dole ya ce ba zai min kishiya ba ya yi ruwan rogo da ita har ta gama sababin ta ta tafi.. Kwatsam wata rana aka turo min saƙo wai na faɗi inda mijina yake aje kuɗi ko a kashe shi da Abir, na tsorata da ganin wannan saƙon na kasa zaune na kasa tsaye har sai da ya dawo na ba shi ya karanta ya ce na share 'yan damfara ne, ban yi masa muso ba na share maganar amma kullum ina cikin zullumi a zuciyata. Haka aka ci gaba da turo min saƙon safe da yamma wani lokacin ma har da dare ake turo min, duk na tattara na watsar ko an turo bana bi ta kai karshe dai na kai number wajan ɗan gidan Baba Malam saboda ya karanci computer na ce ya min bincike a kan layi ana yawan kira na da shi, a take ya dauko kayan aikin shi ya shiga bincike inda ya ce min ai mai kiran nawa yana cikin daji ne. Hankali na ya tashi ina ta tsoro ko yan bindiga ne haka dai na dawo gida na sanar da Abban Abir komai ya ce kar na damu babu abin da zai same ni sai alkhairi.. Kwana biyu na ga Abban Abir na yawan tunani ba tambaye shi ko lafiya? Sai ya ce min ba komai wasu kaya yake tuna lissafin su, ranar kai ka tafi aiki ita kuma Abir tana gida Abban ta ya ce ta raka shi zai je sayan shanu rugar su Inna, tana murna ta raka dauko mayafi suka tafi, wannan rana ita ce ganina na karshe da shi sai gawar shi da aka kawo bayan sun kashe shi. Kuma har yau mai yi min barazanar nan bai daina bibiyata ba sai tambaya ta yake abin da ban sani, amma ni dai na san Abban Abir ya ba ni wasu takardu da kuma wata yar akwati ƙarama yar madaidaiciya ya ce na aje a wajena kar na bari kowa ya gani, tabbs in har hasashe na ya zama gaskiya akwai abin da yake cikin wannan akwatin wanda shi ne mai min barazanar nan yake son na ba shi, ban kawo shi ba ne sai da na tuna da ya ce kar na bari kowa ya sani..." Dogon numfashi Abdul ya sauke yana murza hannun Mom ganin yadda bakin ta ya bushe ƙamas, cikin muryar da ke nuna tsananin damuwar da yake ciki ya ce "Mom yanzu ina wannan akwati da takardun suke?" Fisgar numfashi ta yi ta runtse idanu tana juya kai irin na wanda yake cikin tsananin azaba, sai da ta ɗan jima sannan ta ce "Idan ka shiga ɗakina ka buɗe inda nake saka kayana can ƙarshe ka laliba za ka ji wata leda, in ka ɗauko to ita ce akwatin takardun kuma na bai wa Abir ta aje a wajan ta dan ta ce min Abban ta ya ba ta wata takarda ba ta ma duba ba ta ɓoye ta, kuma na ga...." Tari ne ya sarƙe ta ta dinga aman jini, hankali a tashe Abdul ya fita suka yi kiciɓus da Doctor Hashim a bakin ƙofa, da sauri su Grandma suka shigo ita da Hafsat da Iman Ammi kuwa tuni ta gaji da jira ta yi tafiyar ta. Duba ta ya soma yi bakinta na mutsawa jikinta na ƙyarma ta ɗamko hannun Abdul ta ɗaura a na Abir tana kallon su hawaye na gangarowa kan kuncinta zuwa cikin kunnenta, kuka sosai Abir ke yi tana faɗin "Mom don Allah ki tashi kar ki min haka, ki tashi Mom kar na zama marainiya gaba da baya." Jikin ta ne ya saki idanuwanta suka rufe ruf kamar mai bacci, Doctor Hashim ya cire mata garin jini da ruwan da ake mata ya fidda mata robar da aka sa mata a hanci ya janyo zanin ya rufe mata fuska. A kiɗime Abdul ya kalli Doctor Hashim ya ce "Ba... Ban gane ba na ga ka rufe mata fuska?" Zagayowa ya yi ya dafe kafaɗarsa ya ce "Am so sorry Abokina Mom ta amsa kiran Mahalicci." Wata irin zabura Abir ta yi ta fasa kuka ɗif kukan ya ɗauke sakamakon numfashinta da ya dauke, da sauri Abdul ya dauke ta suka nufi waje shi da Doctor Hashim yana kiran nurses.. Inna da su Iman kuka suke har wata nurse ta zo ta ce su fito waje, a bakin kofa suka tsaya Abdul ya fito daga ɗakin da aka kwantar da Abir ya rasa me zai yi kuka zai yi ko kawai ya yi ta buga kamshi da jikin bango ko zai ji sauki? Hannun Grandma ya kama ya zaunar da ita ya ce zai kira su Abba a waya ya sanar da su, Inna ta riƙe kai ta ce "Bar ni in yi kuka Abdullahi, Allah sarki Sadiya baiwar Allah." Kiran Abba ya yi yana ɗagawa ya ji kuka ya zo masa ya danne murya na rawa ya ce "Ab.. Abba please ku zo Asibitin Hashim Mom ce.." Kasa ƙarasawa ya yi saboda kukan da ya hana shi yin maganar har karshe. Zabura Abba ya yi ya tashi daga kan kujerar da zaman sa kenan ya dawo daga office, a ruɗe yake magana. "Abdul me ya faru da matar Yaya?". Da ƙyar ya daure ya iya faɗa masa mutuwa ta yi, nan Abba ya dinga maimaita Inna lillahi wa inna laihin raji'un! Ya ce ga su nan zuwa. Aje wayar ya yi ya jingina a jikin bangon Asibiti yana zubar da wahaye na rashin Mom. Suna nan sai ga Abba da Salim da Daddyn Aruf sun iso hankali tashe, dakin ya nuna musu aka fito da gawar Mom suka wuce da ita gida, Abir kuma Iman da Hafsat suka tsaya a wajan ta kafin ta farfado daga suma da ta yi.. Haka aka yi wa Mom wanka aka kai ta gidan ta na gaskiya, sai a lokacin Abdul ya ji wani irin kewar Mom ta rufe shi ya shiga ɗaki ya rufe kan shi ya dinga kuka mai tsuma zuciya.." Taku har kullum Maman Nusaiba [11/1, 10:19 Yamma] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): ~A HAKA NAKE SON SHI~ 🥏+966577675904 Shafi na (28) Ji ya yi an dafa shi, cak ya tsayar da kukan bai juyo ya kalli wanda ya dafa masa kafaɗa ba ya yi shuru. Bubbuga kafaɗarsa take yana ji amma ya yi ƙiƙam kamar wani gunki, sai da ya shirya dan kansa ya juyo. Cikin tsananin mamaki yake kallon ta hawaye na bin kuncinta tana girgiza masa kai ko alamar tsoro babu a tare da ita, wanda in a da ne iya kallo zai mata jikinta ya ɗauki rawa. Sunkuyar da kai ta yi, jin bai ce komai ba sai ta kamo hannayensa ta nufi bakin gado da shi. Kamar raƙumi da akala haka ya bi ta ta zaunar da shi a bakin gadon ita kuma ta zauna a kan carpet da ke mamale a ƙasa, sai da ta goge hawaye zuciyarta na dukan uku-uku ta ɗago ta zuba masa idanuwanta da suka yi ja saboda tsabar kukan da ta ci. Shi kuwa kawai kallon ta yake yana ta tunani, ashe Laraba za ta iya zama a gaban shi ba tare da tsoron komai ba? Gyaran muryar da ta yi ya sa shi ƙifta idanu yana mai ƙare mata kallo, ita kuwa ji ta yi duk kunya ta rufe ta amma ta daure ta kawar da duk wani tsoron da yake a zuciyarta dan ta sanyaya masa zuciya. Cikin dakiya ta soma masa magana a nutse kamar ba ita ba ce ta dinga kuka mai sauti har sai da Grandma ta rungume ta ta hana ta ƙuga kuka.. "Yaya Abdul ka yi haƙuri kullu nafsin za'iƙatul maut, duk wani mai rai da ka gani a duniya ko mutum ko aljan ko damba ko ƙwari to zai amsa kiran Allah babu wanda in kwanan sa ya ƙare a duniya za a ƙara masa na wani dole ya tafi inda ba a dawowa. Ka daure ka cije nasan raɗaɗi da ciwon da kake ji a zuciyarka, amma ka yi haƙuri Mom Addu'ar mu take buƙata ba wai kuka ba, tun da yau ta yi ban ga ka ci komai ba ka fita aiki har wannan lamarin ya afku. Don Allah Yaya Abdul. " Ta kamo hannayensa cikin rawar murya gaf take da fashewa da kuka, ta ja numfashi ta ci gaba. "Ka daure ga tea nan na kawo ma ka sha ko ka ji kuzari a jikinka, ka da ka yi rauni sosai hakan zai sa in Anty Baby ta farfaɗo ka kasa ba ta ƙwarin gwiwar dangana." Saƙare Abdul ya yi yana kallon ta cike da tsananin al'ajabi, ashe Laraba tana da hankali har haka? Ashe ta iya maganar kwantar da hankali in mutum na cikin tsananin damuwa? Nisawa ya yi tare lumshe idanu yana sauke ajiyar zuciya bai ce da ita komai ba, ita kuwa Laraba har ta cire ran zai ce da ita komai dan har ta soma ƙoƙarin tashi ta ji ya ruƙo hannunta tare da buɗe idanuwansa a kan ta. Sosai ta tsorata da ganin yadda idanuwansa suka yi jajur kamar an watsa masa barkono, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce "Laraba na gode da shawarar da kika ba ni, ban taɓa tunanin kina da hangen nisa har haka ba." Ya faɗa yana sauke numfashi. Murmushi ta yi mai haɗe da hawaye ta ɗago da kanta suka haɗa idanu, a nutse ta ce "Yaya Abdul kenan, in ban nutsu ba yanzu to sai yaushe? Shekara ta fa 23 kuma tun da na taso nake ganin ƙaddarori kala-kala a rayuwata. A gabana a kan cinyata ƴar da na haifa ta rasu, a gabana ƙanwata ta amsa kiran Allah, a gabana Babana ya gama min wasiyya ya rasu, a gabana mijina ya rasu. Yanzu wanda ya ga wannan abin da idanunsa in bai nutsu ba to sai yaushe zai nutsu?" Ta faɗa tana goge hawaye a karo na barkatai.. Tsura mata idanu ya yi cike da tsananin tausayin ta, hannu ya sa ya goge mata hawaye da suka kasa tsayuwa da ta goge za su zubo, girgiza mata kai ya yi ya ce "Kenan kina nufin ba ki da kowa sai mahaifiyarki?" Girgiza kai ta yi ta ce "Ai Mamana ta rasu tun lokacin da ta haifi ƙanwata ta biyu, ba ni da kowa duk sun mutu sai ƙanwata ɗaya itama ban san inda take ba. Na sha zuwa har gidan redio na bayar da cigiyar ta amma har yanzu shuru babu ita babu dalilin ta, daga fita School ban sake saka ta a idanuna ba har yau. " Ta ƙarashe maganar tana fashewa da kuka tuna tilo ɗin gudan jinin ta ƙanwarta.. Tausayin ta ne ya ƙara mamaye Abdul ya ce "Ki yi haƙuri kin ji, tashi ki je bayan komai ya lafa zan neme ki mu yi magana.." Kai ta jinjina masa ta tashi ta fita daga ɗakin, shi kuma ya rafka tagumi yana tunanin Mom. Sai da ya ji kansa zai rabe biyu saboda tsananin ciwon da yake masa sannan ya ɗauki tea ɗin da ya soma hucewa ya masa shan ruwa... Haka aka yi ta karɓar gaisuwa har aka yi kwana ukun Mom Abir ba ta farfaɗo ba, sosai hankalin su Abba ya tashi sai zirya suke Asibiti suna duba ta. Bayan an yi sadakar sati Grandma ta koma Asibitin ta ce Hafsat ta dawo gida itama ta huta, ba dan ta so ba ta dawo gida cikin damuwar ganin Aminiyarta a wannan yanayi na doguwar suma.. Sai da Mom ta cika kwana goma cif sannan Doctor Bashir ya ce su zo ƙarfe 10:am na safe za ta farka. Gabaɗaya duk suka hallara har Mommy Hafsat da matar Daddyn Aruf, ba su jima da zuwa ba aka ce ta farka amma suka hana kowa shiga suka ce za su fito da ita wajan su, saboda akwai wasu majinyatan a ɗakin wanda ba a son buɗe sauti a inda suke.. Wata nurse ta kama ta ta taimaka mata suka fito daga ɗakin, ganin su duk a bakin kofar ta ji wani irin kuka ya zo mata kece da shi tana nufar Mommyn Hafsat da itama ta taro ta ta faɗa jikinta ta fashe da kuka. Kuka take tana faɗin "Ummi da gaske wai Mommyna ta tafi ta bar ni ni kaɗai? Waiyo Allah ni Hauwa'u! shi kenan na zama marainiya gaba da baya babu uwa babu uba? Don Allah ku ce min Mom ta farfaɗo tana gida a zaune." Rarrashin ta Ummin Hafsat ke yi tana ba ta haƙuri har ta tsagaita kukan, ɗago da ita ta yi ta share mata hawaye ta kama hannunta suka ƙaraso wajan su Abdul da duk ta gama karyar musu da zuciya wasu har sun soma kuka. Sallama aka ba su suka tafi gida kowa sai jimami yake, mutuwar Mom ta dawo musu sabuwa saboda sambatun da take har suka isa gida.. A harabar gidan suka samu Baba da Inna tare da Zaiyan suna tsaye Maigadi na faɗa masa su Abba sun tafi Asibiti sai ga su, sai da suka gama fitowa daga motar Abdul ya nufo su yana goge hawayen da suka zube masa, rusunawa y yi ya ce "Baba ku ne tafe?" "Mu ne ɗan nan ina ita Hauwa'u take?" Ya ɗaga baki zai yi magana ya ji Abir ta kuma fashewa da kuka ta nufo inda suke, Inna ta kamo hannunta cikin kwantar da murya ta soma mata nasiha. "Ki yi haƙuri kin ji ƴar nan, babu abin da mahaifiyarki ke buƙata sai addu'ar ki a gare ta." Tsagaita kukan ta yi ta ɗago ta kalli Baba ta ce "Baba Mommyna ta tafi ta bar ni dama ita ta rage min." Cikin jimami Baba ya ce "Ki yi haƙuri kin ji Allah ya jiƙan ta da rahama?" Sai a lokacin Zaiyan ya ɗago ya ga Abir na ta kuka, saurin isowa ya yi kusan ta ya kama hannunta ya fashe kuka shi ma yana kallon ta ya ce "Anty waye ya dake ki? Baba ne ko abokina na rama miki?" Cak ta tsayar da kukan ta shiga sauke ajiyar zuciya, ta ce "Zain Mommyna ta tafi ta bar ni." Shuru ya yi yana kallon ta kamar mai karantar wani abu a maganar da ta yi, hannu ya sa ya goge mata hawayen ya kamo hannayenta ya ce "Anty kema Babanninki sun mutu?" Gyada masa kai ta yi ya kalli Abdul ya ce "Baba ka dinga jin tsoron Allah ka daina sace Anty, yanzu ka ga saboda haka babannninta sun mutu." Girgiza kai Abdul ya yi ya kamo hannunsa suka nufi ciki, suma sauran suka biyo bayan su. Yasmin ta riƙe baki tana dariya ta ce "Lalle ma ki ji fa Fatima, wai Yaya ne Baba." Itama dariyar suka duk nufi part ɗin su dan dama tuni su Umma sun wucewar su tun lokacin da Abir take cewa Baba ta rasa Mom. A palo suka zauna suna ta ƙoƙarin ganin sun kwantar mata da hankali, Laraba ce ta iso ta rungume Abir suka fashe da kuka sai faɗi take "Laraba yanzu shi kenan Mom ta tafi ta bar ni?" Haƙuri ta dinga ba ta har ta samu ta yi shuru, miƙar da ita ta yi suka wuce ɗakinta tana kara mata nasiha akan Haƙuri da juriya yayin da ka rasa wani abu mai mahimmanci a rayuwa, da haka ta mata dubara ta kawo mata tea tana kawar da kai ta lallaɓa ta har ta shanye, ta shiga toilet ta hada mata ruwan wanka ya dawo ta ce ta je ta yi wanka. Ƙin tashi ta yi sai picture ɗin Mom take kallo wanda yake maƙale a jikin bangon ɗakin, da ƙyar ta tashi Laraba ta raka ta ta tsaya a bakin ƙofar har sai da ta ga ta cire komai daga ita sai pant da karamar rigar ciki ta fito ta bar ɗakin... Haka Abir ta dawo kamar kurma abinci sai Abdul ya zo ya saka ta a gaba take ci, idan kuwa ya dage sai ta ci dayawa sai ta sa masa kuka dole ya rabu da ita. Shi kan shi Abdul ɗin dauriya ce yake a matsayinsa na namiji kuma babban ɗa gidan, kullum sai ya yi kukan rashin Mom musamman idan ya shirya zai fita aiki da ya shiga part ɗin su, sai ya ga kamar zai ga ta fito daga kitchen dauki da breakfast ɗin sa ta ce ya zo ya karya kafin ya fita. Tun da ya koma bakin aiki ba ya samun abincin kari saboda Umma ta ce sai dai yake zuwa ƙabarin Mom tana ba shi abincin tun da dama can ba nata yake ci ba, dan haka yanzun ma ba zai ci ba duk da Mom mutuwa ce ta yi ba wani gari ta tafi ba. Idan ta faɗa masa haka sai dai ya girgiza kai ya wuce part ɗin su in ya samu Laraba ta gama sai ya ci, in kuma ba ta gama ba haƙura yake ya tafi haka bai karya ba.. A ɓangaren Abir kuwa sam ba ta iya bacci rashin Mom a tare da ita in ta tuna yana gigita duniyar ta, gabaɗaya ta ƙara ramewa ta ƙanjame kamar wadda ta yi shekara tana jinya abin ka da mai ƙaramin jiki, ba ta da aiki sai kuka sai kallon photon Mom. Abin da take son sani shin ina dangin Mom suke? Ko suma sun mutu kamar yadda Mom ɗin ta mutu? In kuwa suna rayé me ya sa ba su nemi Mom ba har tsayin wannan shekarun? Wannan tunanin kadai yana hanata sukoni in ta tuna ita dai ba ta kowa a dangin uwa da ta sani face Abdul, Shi kaɗai ne gudan jinin ta da za ta bugi kirji ta ce ga dangin mahaifiyarta... Suhal yau ya sauka Nigeria shi da Ikilima sun zo gaisuwa, sosai Abir ta ji haushin rashin zuwan sa lokacin da aka yi mutuwar duk da kuwa ya faɗa mata uzirin shi ba ya ƙasar ya tafi Ghana ne wajan wani taro da Maimartaba ya tura shi ya wakilce shi. Suna sauka a airport Abdul da Salim suka je ɗaukan su, bayan sun isa sai da ya kira Suhal ya masa kwatancan inda suke tsaye suna jiran su.. Tun daga naisa Ikilima ta hango Abdul da ba ta gani ta kyale ta daddaɓi Suhal ta ce "Yaya kalli wani haɗaɗɗan gaye." Murmushi kawai ya yi yana kallon Abdul har suka ƙaraso, hannu ya miƙa masa suka gaisa Ikilima ta ce "Sannun ku." Da fara'a suka amsa da yawwa sannan suka nufi motar suka shiga sai gida.. Suna isowa gidan Ikilima ta kalli Suhal ta ce "Yaya ina Anty Princess ɗin take ne?" Dafe kai ya yi yana hararar ta ya ce "Ke wai me ya sa kin fiya surutu ne?" Cuno baki gaba ta yi ta fito suka nufi ciki. A palo suka samu Grandma tana jan tasbaha ta manne farin glass a idanunta sai kallon su take, zama suka yi Suhal ya ce "Grandma ina yini? Mun same ku lafiya?" "Alhamdu Lillah ɗan nan ya iyayen naka suke? Wannan fa ko ƙanwar ka ce?" Ta faɗa tana kallon Ikilima da take yaba kyau da tsaruwar gidan. Murmushi ya yi ya ce "E Autar mu ce ai." Jinjina kai ta yi sai kuma ta yi murmushi ta ce "Allah sarki har ka tuna min da tawa Autar, itama yau za su sauka Nigeria wajan dare ƙila, amma ta ce idan ba su zo ba yau ko gobe to gaskiya ba za su samu zuwa ba, ba su zo wajan mutuwar nan ba mijin nata sunƙi ba shi hutu har ita kanta su zo ganin gida." Ta faɗa tana goge idanu. Suhal ya tankwashe ƙafafunsa ya ce "Grandma ya kuma muka ji da rashin Mom? Wallahi mutuwar nan ta taɓa ni sosai, lokacin bana gida ina Ghana sai yau ɗin nan na dawo da safe na ce ba zan bari sai na huta ba gara na zo na yi gaisuwar nan tun da an zama ɗaya." Ya ƙarashe maganar yana sauke numfashi. Tashi Abdul ya yi ya nufi ɗakin Abir dan ya sanar da ita zuwan Suhal. Ko da ya shiga cikin bargo ya same ta ya tako har bakin gadon ya zauna tare da sa hannu ya yaye bargon, ƙura mata idanu ya yi ganin yadda take bacci amma sai zabura take tana jan numfashi, hakan ya tabbatar masa ba ta jin daɗin baccin yi kawai take. Addu'a ya dinga tofa mata har ta fasa zaburar, a nutsu ya yi Bismillah ya kai hannu ya shafo fuskarta cikin wani irin yanayi na tausayin halin da take ciki ya ce "Baby! Baby tashi mana Suhal ya zo suna palo ke ake jira?" A hankali ta shiga buɗe idanuwanta tana mayar da su tana rufe wa har ta gama buɗe su a kan fuskarsa, turo baki gaba ta yi kamar za ta sa kuka ya yi saurin ɗago ta ya zuro da ƙafafunta bakin gadon, kallon ta ya yi ganin yadda take yatsine fuska ya ce "Kin ga yi hakuri ki tashi ki wanke fuskar ki ki kimtsa ki fito ya zo shi da ƙanwar sa." Waro idanu ta yi alamar mamaki sai kuma ta mike ta zari ɗankwalinta da ɗan kuzarin ta ta nufi toilet. Yana nan zaune har ta fito ta ɗan shafa mai sai ya fita ya ba ta waje ta canja kaya sannan ta nufi palo. Tun daga naisa yake kallon ta ganin yadda ta rame sosai, wani irin abu ne ya kawo masa ziyara ya lumshe idanunsa yana mai ƙara jin tsananin ƙaunar ta a cikin zuciyarsa. Zaunar da ita ya yi suka tashi har grandma suka ba su waje, Ikilima ta ƙura wa Abir idanu tana ƙare mata kallo, matsowa ta yi kusa da ita ta kamo hanayenta cikin tausayawa ta ce "Anty Princess sannu kin ji, Allah ya jiƙan Mom da rahama ubangiji ya haskaka makwancin ta." Goge hawayen da suka zubo mata ta yi murya na rawa ta ce "Amin Auta na gode sosai. Ya Suhal barka da zuwa ya su Mamma Kun zo lafiya?" Numfashi ya ja yana jin kamar ya rungume ta ya yi ta rarrashin ta har sai ya ga ta yi dariya, sosai yake jin zafin kukan da take ya ɗan jumƙe hannunsa na dama ya buɗe sannan ya ce "Alhamdu Lillah Princess, Allah ya jiƙan Mom ya haskaka kabarin ta, Mamma ta ce ayi miki gaisuwa kuma ta ce ki rage damu ki daina kukan nan addu'a kawai Mom ke buƙata.." Jinjina kai kawai ta yi sai ga Iman da Laraba sun shigo da sallama dauke a kayan abinci, sannu da zuwa suka masa sannan suka ja Ikilima har Abir aka bar Suhal ya ci abinci. Abdul ne ya shigo palon shi da Salim suka dauki kayan abincin suka nufi ɗakin baƙi ya biyo su a baya. Daret wajan cin abinci suka wuce inda sun gma jera abinci, sun zauna kenan sai ga Umma ta shigo ganin Ikilima ya sa ta yin fara'a tana fadin "A a mutanen Niger ne har an iso?" Murmushi Ikilima ta yi ta durƙusa ta gaishe da Umma ita kuma ta amsa tana washe baki, sabuwar mai aikin ta ce ta iso da ƙatuwar kula guda biyu ta kalli Iman ta ce "Ke Iman tashi ki kaiwa surikin namu abinci ki zuba masa ya ci ya ƙoshi, ki ce masa kar ya yi kara ya ɗauka nan kamar gidan su ne." Ta faɗa tana miƙa mata kular, miƙewa Iman ta yi cike jin daɗin Umma ta mutumta su Ikilima ta am shi kular ta nufi ɗakin baƙi. Da sallama ta shiga ta sami Abdul da Salim da Suhal na shirin cin abinci, kallon ta Abdul ya yi ya ce "Ya dai Iman?" Aje abincin ta yi tana murmushin jin daɗi ta ce "Yaya Umma ce ta ba da abinci ta ce a kawo wa Yaya Suhal ya ci kuma kar ya bar saura ya cinye duka abincin da ta zubo." Ta faɗa tana buɗe kular, ƙamshin haɗaɗɗiyar shinkafa da kaza ya daki hancin Suhal nan da nan ya ji yawunsa ya tsinke, kallon kular ya yi yana murmushi ya ce "Ai kuwa naji daɗi kuma ki ce wa Umma na gode sosai da wannan karamcin zan shigo na gaishe ta, zubo min na ci ki gani kar ki ce wa Umma ban ciba." Dariya ta yi ta dauki filet ta zuba masa haɗi da cokali ta miƙa masa, amsa ya yi ya soma ci sannan ta fita. Kamar haɗin baki tana fita sai ga Yasmin itama ta shigo ɗauke da abinci, murmushi Salim ya yi ya kalli Suhal ya ce "Iyye wato yau dai kai ɗan gatan su Umma ne, ga Ammi ma ta kawo maka nata girkin." Murmushi kawai ya yi Yasmin ta aje ta gaishe da Suhal ya amsa ba yabo ba fallasa ya ci gaba da cin abinci, sai da ta ɗan jima sannan ta ce "Ammi ta ce a kawo wa surikin ta girki ne ta yi na musamman dan shi." Ta faɗa tana hararar kular Umma haushi ne ya turniƙe ta ganin yana cin abincin Umma ta haɗe rai ba ta ma saurari mai za su ce ba ta wuce fuu.. Da kallo suka bi ta Salim ya yi dariya ya ce "Ja'ira kawai." Bayan kowa ya gama cin abincin Suhal ya nemi Abdul da Salim su yi masa iso wajan Umma da Ammi su gaisa kafin su Abba su zo, Abdul ya shiga part ɗin Ammi da sallama ya samu duk suna zaune a palo kamar ba su jiran shi. Murmushi Ammi ta yi tana kallon Abdul ta ce "A a Abdul, ina surikin namu yake? ." Kawar kai ya yi sai kuma ya daure fuska ya kalli Fatima ya ce "Ke matso nan." Da sauri ta matso ta sunkuyar da kai, kallon ta ya yi sama da ƙasa ganin shigar da ta yi, riga ce da wando kayan sun ɗame ta sosai duk wani abu mai jan hankali a jikin mace sai da ya bayyana ga kanta babu ɗankwali. Tsaki ya ja ya ƙara daure fuska ya ce "Maza ki canza kayan nan ki sa na kirki kafin na canja miki kama a gurin nan." Da sauri ta wuce ɗaki tana kumbura baki, Kallon Ammi ya yi ya ce "Zai shigo ya gaishe ki ya ce a masa iso wajan ki." Washe baki Ammi ta yi ta ce "To ka ce masa ya shigo." Juyawa ya yi ya bar part ɗin ya nufi na Umma. Ammi ta raka shi da harara ta ce "Shi ya rasa ma wa zai aura sai wannan sauran cutar? To zan ga ta yadda za ta auru har ta je gidan sarauta, muna nan da ita a gidan nan har tsufan ta ba ta isa ba ta yi aure ɗiyan mu na zaune ba su yi ba." Yana isa Part ɗin Umma ya sanar da ita ganin Khairat ta yi shigar mutumci bai ce komai ba ya wuce. Jan shi suka yi ya fara zuwa part ɗin Ammi. Da murna ta tare shi suka gaisa ta gyara zama cikin kissa da iya bariki ta ce "Yawwa Yarima, dama ina son na maka wata tambaya in ba za ka damu ba." Jinjina mata kai ya yi ta ci gaba, "Ka ce da ka je gida za ka yi wa Maimartaba magana azo ayi maganar auren Abir, to amma mun ji shuru har wannan lamari ya faru uwar yarinya ta rasu, ni dai ina so ka riƙe ta da amana ka ga dai marainiya ce ita ba uwa ba uba mu ne komai nata. Kar ka aure ta ka kaita Kasar ku ake wulaƙanta mana ɗiya a gidan sarauta, dan naji an ce in dai kai ba jinin sarauta ba ne ka auri ɗan sarauta sai ka zama abin tausayi mu kuma ba za mu so a wulaƙanta mana ɗiya ba marainiyar Allah. In har kasan ba za ka jajirce a kan ta ba to gaskiya kar ma magana ta yi nisa. " Ta faɗa irin ita ga ta ƙanwar Abie, har wani hade rai take tana girgiza kai.. Ƙara sunkuyar da kai Suhal ya yi ya ce "In sha Allahu Ammi ba zan ba ku kunya ba, kuma na muku alƙawarin ba zan taɓa bari Princess ta yi kukan maraicin iyaye ba ko na dangi, ni da Mamana da ƙanwata za mu kula da ita yadda ya kamata." Ya ƙarashe maganar yana miƙewa tsaye dan ya gaji da tsugunnawar da ya yi.. Washe baki Umma ta yi ta ce "To shi kenan Yarima, Allah ya maka albarka naji daɗin wannan bayanin naka." Amin ya ce ya mata sallama tare da ɗauko kuɗi ɗauri biyu na rafa ya aje a kusan ƙafarta suka bar palon. Wani irin shu'umin murmushi ta yi ta ɗauke kuɗin ta kalli Fatima ta ce "Ku kalla a samarin ku wa ya taɓa ba ku ko da ɗauri ɗaya na irin wannan?" Girgiza kai suka yi suka ƙara jin tsanar Abir ganin yadda ta samu mai kuɗi kuma ɗan gidan mulki za ta aura su kuma ga su nan har yau ba wanda ya ce zai turo sai tara samarin kawai.. A part ɗin Umma ma bayan sun gaisa sai da ya aje mata dauri biyu na kuɗi kamar yadda ya aje wa Ammi ta masa godiya sannan suka tafi. Tana ganin sun tafi ta yi ta dariya tana juya kudin ta shige ɗaki, Khairat ta bi bayan ta... Sai da su ABBA suka zo ya musu gaisuwa sannan ya ba su hakuri akan jin sa shuru da suka yi uziri ne y taso masa, ba komai suka ce nan ya sheda musu nan da wata uku zai turo zuwa lokacin Abir ta warware ta rage damuwa, ba su ja ba suka amince ya musu sallama suka nufi masauki... Washegari ya so zuwa gidan su Baba amma ya fasa suka koma ƙasar su. Haka kullum yake kiran ta yana kwantar mata da hankali ya yi ta mata hira yana ba ta labarin wani abu da ya gani a kasashen waje, tun ba ta yin magana har ta dangana ta hakura take ɗan sakin jikin ta tana yarda su yi hira. Da haka dai kwanci tashi har wata uku ya cika inda dangin Suhal suka zo aka yi maganar gemu da gemu suka fahimci juna aka sa biki wata ɗaya, sun so bikin ya wuce wata ɗaya amma suka roƙi alfarma akan cewar Maimartaba ne ya ce asa haka. Sosai suka ya ba da kirkin su Abba bayan an gama komai suka tafi gida cike da jin daɗin yadda aka karrama su.... _Maman Nusaiba ce_ [6/20, 8:03 PM] Ummu Amjad: ~A HAKA NAKE SON SHI~ +966577675904 Shafi na (29) Da gudu Iman ta shigo palon tana faɗin "Anty Baby! Anty Baby ki na ina wai?" Riƙe baki Grandma ta yi tana gyada kai kamar ƙadangaruwa, sai da Iman ta ƙaraso inda take ta gyara zama ta ce "Ke kuma sangadan ware daga ina?" Ta Yi maganar tana hararar ta. Dariya ta yi ba ta bai wa Grandma amsa ba ta nufi ɗakin Abir tana kwaɗa mata kira. A bakin gado ta same ta tana ƙoƙarin ɗaura ɗankwali, hakan ya sa ta ƙaraso da sauri tana murmushi ta dafa ta. Hawaye ta gani akan fuskarta nan da nan fara'ar da ke kan fuskar Iman ta dauke, a ruɗe take tambayar ta. "Anty Baby me ya faru kike kuka kuma?" Goge hawayen ta yi ta ɗago ta kalli Iman ta ce "Ba na son na tafi na bar gidan nan Iman." Ta fashe da kuka tana daura kanta a kan kafaɗar Iman. Murmushi Iman ta yi tana bubbuga bayan ta cikin rarrashi ta ce "Haba Anty Baby, ke fa mace ce ya zame miki dole ki bar gidan iyayenki matsawar kin kai lokacin da za a aurar da ke, ki daina kuka ai za mu ke zuwa muna ganin ki kuma muna waya da ke har ma vidéo call za muke yi. Na tabbata Yaya Suhal zai riƙe ki da amana kamar yadda ya faɗa wa su Abba, yana da hankali da nutsuwa ga sanin darajar so. " Tashi ta yi daga zaunan ta ɗan yi taku biyu zuwa uku ta kalli Iman tana girgiza kai ta ce "Iman yanzu idan na tafi wa zai ke kula min da Zaiyan? Kuma kin ga ban gama karatuna ba za a min aure." Ta dawo ta zauna tare da rafka tagumi hannu bibiyu. Tsaki Iman ta ja jin abin da ta faɗa, dafa kafaɗarta ta yi tare da ɗaure fuska irin ga uwar ta ɗin nan za ta ja mata kunne har da su gyaran murya, kallon ta Abir ta yi ba ta ce komai ba ta kuma goge hawayen da suka sake zubo mata. "Malama ki na ba ni mamaki wani lokacin, yanzu duk wannan fafutukar da Yaya Abdul yake akan Zaiyan ba ki gani ba? Duk wani abu da ya shafe shi shi yake yin komai sai dai in ya gama ya zo ya faɗa miki amma duk da haka wai har kike tunanin wa zai kula da shi dan kin yi aure? Wallahi kin ban mamaki Anty Baby, bai ma kamata ki yi irin wannan maganar ba sam. " Ganin yadda ran Iman ya ɓaci sai ta ɗan yi murmushi ta ruƙo hannayenta cikin sanyin murya ta ce "Allah ya ba ki haƙuri Iman, ba wai ina nufin Yaya ba ya yin wani abu a kan Zaiyan ba ne, ina tunanin in na tafi zai ke ta tambaya ta sannan shi ma Yaya da ya yi aure zai rage zuwa inda suke, saboda abubuwa za su masa yawa shi ya sa kika ji na ce haka." Ta Yi maganar tana dan rausayar da kai kamar tana gaban Abdul.. Murmushi Iman ta yi ta ce "OK to tashi mu tafi palo ki zauna an jima su Abba za su shigo, dama na zo ne na kawo miki albishir bikin naku nan da wata ɗaya ne wai Maimartaba ya ce a sa wata ɗaya." Wata irin faɗuwar gaba ce ta mata dirar mikiya har sai da ta dafe ƙirji tana zaro idanu, baki na rawa ta ce "W.. Wa. Wata ɗaya fa kika ce Iman?" Ta faɗa alamar tsoro ƙarara ya baiyana a kan fuskarta. Gyaɗa mata kai kawai ta yi ta yi gaba ta bar ta dafe da ƙirji tana bin ta da kallo har ta ɓace wa ganin ta.. Wani irin kuka ne ya subce mata ta juya ta faɗa kan gado ta dinga rera kuka kamar yanzu ne aka ce mata Mom ta rasu. Washegari ta shirya tsaf misalin karfe 10 na safe ta sa aka kaita gidan su Baba. Motarsu na yin packing ta hango Zaiyan a zaune yana kasa itace kamar wanda zai sayar sai surutu yake ta yi yana karkasawa, murmushi ta yi ta fito tare da nufo inda yake wani irin sanyi na mamaye mata zuciya.. Tana isowa ta tsugunna a gaban itacen tana ƴar dariya wadda rabon da ta yi ta ma manta ranar, a hankali cikin sanɗa ta janyo itacen da ke gefen shi tana kunshe dariyar da ta zo mata sanin halin shi. Da sauri ya juyo ganin ana jan masa itace, karaf suka hada idanu ai kuwa ya zabura kamar an tsikare shi ya miƙe tsaye ya soma dariya yana faɗin "Shege Baba ashe gaskiya ya faɗa min shekarar da ta gabata, dama ya ce ba zai ƙara sace ki ba kina kuka sai ga shi kin zo gidana, me kike so Anty?" Ya faɗa yana zama a daf da ita ya yi tagumi hannu bibiyu ya kafe ta da idanu. Ajiyar zuciya ta sauke sai kuma ta sakar masa sanyayyan murmushi tana kallon shi, kallon kallo suke a tsakanin su ba wanda ya yi ƙoƙarin janye idanunshi daga kan na ɗan'uwan sa. A ɓangaren Abir ita tana masa wani kalar kallo ne wanda ita kanta ta kasa fassara shi, ga tsananin tausayin shi da ya mamaye mata gangar jiki da ruhi sosai take jin zafi mai haɗe da ciwo a cikin zuciyarta in ta tuna nan da kwanaki kaɗan za ta bar shi. Shi kuwa Zaiyan kallon da yake mata na sauraron amsar da za ta ba shi, amma ganin ta kafe shi da na mujiya sai shi ma ya ci gaba da kallon ta yana murmushi a tunanin sa wasa ne suke. Ita ta fara janye idanuwanta ta lumshe su cikin yanayi irin na musu rashin lafiya har wani jiri-jiri take ji saboda yadda zuciyarta ke bugawa da sauri-sauri, bude idanu ta yi a kan shi ta ga ya ɓata rai kamar zai yi kuka sai ta sakar masa murmushi ta ce "Zaiyan wa ya ce maka Baba saceni ya yi?" Dariya ya yi yana tashi tsaye, miƙa mata hannunsa da ya yi ƙura ya yi ya ce "Za ki sha mangwaro Anty?" Ya faɗa yana nuna mata bishiyar mangwaron da ke gefen su ta yi ɗiya sosai amma ba su kai ga nuna ba. Tashi ta yi ta kalli bishiyar ta ce "To ai bai nuna ba ka bari nan da sati sai na sha." Ta faɗa tana sauke numfashi. Murmushi ya mata ya damƙi hannunta yana cewa "To zo muje Inna ta siya miki abinci ki ci, kin ga abokina tun da ya tafi bai dawo ba, kuma ya ce wai na yi ƙawance da mamansa yanzu Anty sai in yarda kawai dan yake cewa na amshe masa Mamansa?" Dariya ta yi daidai lokacin suka iso palon sai ta yi sallama, amsa mata Inna ta yi tana mata sannu da zuwa ita kuma tana amsawa. Bayan sun gaisa nan ta sanar da Inna an sa mata rana nan da wata daya mai zuwa, sosai Inna ta taya ta murna ta kuma sa mata albarka tana amsawa da amin. Suna a haka Baba ya zo suka gaisa Inna ta faɗa masa sa ranar auren Abir, ya ji daɗi sosai ya ce ai Abdul ya faɗa masa a waya.. Sai da Yamma lis ta musu sallama ai kuwa Zaiyan ya manne mata ya ce shi fa babu inda za ta tafi ta bar shi dama dan Baba yana sace ta ne yake hakura amma yanzu tun da ya dawo da ita to zai bi ta, dariya sosai Abir ta yi in ta ji ya ce wa Abdul Baba ta kama hannunshi suka nufo harabar gidan tana yi masa wayo dan ya bar ta ta tafi. "Zaiyan ka koma ciki zan je na sayo maka kayan daɗi ne a kasuwa har da kaya duk zan sayo ma." Maƙale kafaɗa ya yi yana turo baki ya ce "Ni dai Anty zan bi ki." Dafe kai ta yi ta juyo ta ga Baba ya nufi bayan ɗakunansu ita kuma Inna ta koma ciki ta sauke ajiyar zuciya ta ma rasa wata kalma za ta yi amfani da ita wajan ganin ya koma ciki, iska ta firzar ta kalle shi cikin idanu ta ce "Zaiyan ka yi hakuri ka koma zan dawo." Ta faɗa tana dan haɗe fuska. Nan ma maƙale kafaɗa ya yi ya ce "Tab Alƙur'an in na yarda shege nake, salon ki tafi Baba ya sace ki." Dariya maganar ta ba ta sai ta yi murmushi ta zarga handbag ɗinta da ke maƙale a kafaɗarta ta zaro 'yan dubu-dubu sun kai ashirin ta miƙa masa tare da cewa "To amshi wannan ka kai wa Inna sai ka dawo mu tafi." Waro idanu ya yi yana kallon kudin ya ce "Kai kai kai! Duk wannan kudin zan kai mata?" Gyaɗa masa kai ta yi ta ɗaga baki za ta yi magana ya warci kuɗin ya kwasa a guje yana ɗaga murya ya ce "Ki tsaya yanzu zan kai mata na dawo." Da hanzari ta fito da wayar ta jin yltana ringing sai ta ga Ali ne ta yi hamdala tare da dagawa ta ce "Hello Ali ka iso ne? Can kuma ta ce "OK yanzu zan fito kafin ya dawo." Da sauri ta fita daidai lokacin Baba ya dawo ganin yadda ta fita ya yi murmushi, ko ba a faɗa masa ba ya san abin da take yi wa sauri.. Tana fitowa yana isowa ta shiga ya ja suka bar gidan.. Zaune take a gaban wani ƙaton mutum ya sha rawani kamar Limani da ɗan gemunsa kamar na tsatso, gaban shi wani faranti ne cike da ƙasa yana ta zane a kai, can ya ɗago yana cewa "Hajiya gaskiya akwai matsala gagaruma." Dafe ƙirji ta yi tana fadin "Na shiga uku! to yanzu Malam me ye abin yi? Dan ni Wallahi na tsani na daga idanu na ga yarinyar nan a cikin farin ciki, na tsane ta tsana mai tsanani tun da har za ta samu mijin aure ɗiyanmu suna nan ko mashinshini babu ba zai yiyuba, ina so ka sa mata baƙin jini ta yadda kowa zai tsane ta ya ji ba ya son ganin ta har familyn ta bana son kowa ya Ƙaunace ta so nake duk duniya kowa ma ya tsane ta kamar yadda na tsane ta. Kuma ina so auren nan duk ta yadda za ayi a ruguza shi Malam. " Ta faɗa tana hura hanci sama. Murmushi Malam ya yi yana shafa gemunsa ya kuma share zanan da ya yi ya soma zana wani, ɗago da kai ya yi ya ce "A cikin 'ya'yanki wace ce Khairat?" Baki ta washe ta ce "Babbar 'yata ce Malam wani abu ya faru ne? " Girgiza kai ya yi yana cigaba da zanan can dai ya Goge gabaɗaya ya ɗauki Casbi ya ja sai ya aje a gaban ta ya ce "zaɓi ɗaya." Zaɓa ta yi ta miƙa masa ya amsa ya ci gaba da ja har da wani lumshe idanu yake kamar bai yin hadda, sai da ya ɗauki lokaci kana ya aje ya sake zana ƙasar ya goge sannan ya ce "Hajiya wannan aikin da kika zo da shi ya sha bamban da duk aiyukan da nake miki a baya, tabbas ganin bayan wannan yarinyar abu ne mai wahala saboda tana da tsari sosai a jikinta ba ta wasa azkar ɗin safiya da maraice, sannan akwai wani haske da nake gani a tare da ita na kasa gane shi wanan haske mene ne shi? Tabbas dole ne sai an tashi tsaye indai har kina son wannan aikin naki ya ci, amma ko da kin yi ba lalle kowa ya tsane ta ba dole sai an samu mai son ta ko da ba cikin garin nan yake ba. Maganar a lalata aure wannan mai sauƙi ne za ayi ya dawo da shi kan ƴarki Khairat ita ce za ta zama matar Yarima Suhal, da fatan ya ci wannan magani da na ce a zuba masa a abinci? " Wani irin daɗi Umma ta ji jin za a raba wannan aure, baki na rawa ta ce "Tabbas ya ci dan Iman ta tabbatar min sai da ya ci kana ta baro ɗakin, ni dai burina ta yi baƙin jini yadda bana son mahaifiyarta itama bana son ta dan haka a yi ko ma mene ne wanda zai ƙunsa mata baƙin ciki har mutuwar ta." Jinjina kai Malam ya yi ya ce "Haka ne Hajiya, ki je gida za ki ga abin da zai biyo baya, auren ai kin ce saura sati biyu ko?" Saurin gyaɗa kai ta yi tana jin wani farin ciki na mamaye ta, dole ne ma ta je ta soma gyara Khairat kafin satin nan ya cika, dan so take ko da Khairat ta je masarautar Niamey à gan ta Kamar ƴar gidan mulki. Har ta runƙuya za ta tashi sai kuma ta yi saurin dawowa ta ce "Malam ina son a kama mana Yarima a hannu ya haukace akan Khairat, so nake sai ranar ɗaurin aure ya ce ya fasa son Abir Khairat yake so zai aura, ina so taji baƙin ciki marar yankewa a wannan rana." "Ba ki da matsala Hajiya ai yanzu haka tun jiya na soma aiki a kan shi kuma za ki ga mai zai faru ranar bikin." Godiya ta masa ta tafi tana ta dariyar ƙeta har Allah-Allah take ranar nan ta zo dan ta ga wata kalar suma Abir za ta yi... Alhaji tun da Doctor ya ɗauki Sweet girl ɗin shi ya kasa samun nutsuwa da an jima sai ya kira ya tambaya ko ta farfaɗo, doctor ya ce masa da sauran lokaci dai, hakan na ƙona masa rai dan haka ya shirya ya je asibitin da kan shi har ɗakin da aka kwantar da ita, tun daga bakin ƙofa yake kallon ta har ya iso bakin gadon ya zauna tare da kama hannayen ta yana ɗago da ita ya rungume ta yana sauke ajiyar zuciya. Shi dai Doctor mamaki ne fal ransa akan lamarin Alhaji yana son ya tambaye shi amma mugun tsoron Alhaji ya hana ya yi tambayar dan haka ya bar maganar a ransa, sai da ya yi gyara murya ganin Alhaji na ƙoƙarin raba ta da rigar Asibitin da aka sa mata. Yi ya yi kamar bai san da shi ba ya sumbace ta a goshi ya juyo ya kalli Doctor ya ce "Likita yanzu yaushe za ta tashi wai? Bana son a samu matsala fa akan sweet girl ɗi na, in kuwa hakan ta faru Wallahi zan iya kashe kowa a kan ta saboda ina matuƙar son ta fiye da tunaninka." Jinjina kai ya yi dan yanzu ya kawar da mamakin sa akan Alhaji, ajiyar zuciya ya sauke ya ce " Alhaji ayi hakuri ai zuwa dare ko gobe da safe za ta farka, ta yi doguwar suma ne shi ya sa da ace wasu likitocin ne da tuni sun ce ma ta rasu saboda yadda numfashinta ya ɗauki, sai ka auna kafin da kyar kake ganin bugun zuciyarta shi ma ba daidai yake bugawa ba. Da zai yiyu Alhaji zan ba ka shawara in za ka bi." Ya faɗa yana kallon Alhaji. "Maza ka faɗa min indai akan samun lafiyarta ne zan kashe kuɗi ko yafi miliyan goma ne." Jinjina kai Doctor ke yi tabbas Alhaji yana ji da yarinyar nan sosai, gyara tsayuwa ya yi ya ce "Me zai hana ka fitar da ita waje in da halin yin hakan?" Ya faɗa yana mai ɗan rusunawa kamar zai gaishe da shi. "To shi kenan yanzu abin da za ayi zan bari goben ta farka sai ka mana komai na tafiya, dama ina so zan je kasar Istanbul ka ga sai muje can a duba min ita." Ya faɗa yana shafa fuskarta da ta yi wani irin fari bakinta ya bushe har fari lips ɗinta suka yi kamar an sa musu gasarar koko.. Juyawa ya yi ya bar shi ya koma bakin aikin shi, shi kuwa Alhaji ya tsura mata idanu har sai da yaji ringing wayarsa sannan ya ɗan janye ta daga jikinsa ya ciro wayar. Ganin Jarmai ne ke kira sai ya yi saurin ɗagawa tare da karawa a kunne ya ce "Jarmai ya ake ciki? Ina fatan dai jiya duk ka yi sauran aikin nan da boka ya ba mu?" Daga can ɓangaren Jarmai ya yi dariya ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya ya ce "Alhaji albishirin ka." Da sauri Alhaji ya ce "Fari tas Jarmai maza ka faɗa min nasan ko ma meye yana daya daga cikin samun nasarar mu.", Tashi ya yi tsaye ya goya hannu baya ya ce "Wannan yaron da muke nema Dagus ya ce sun ga hanyar da wannan yarinyar take yawan bi, hakan ya sa suka dinga bibiyar ta har suka ga wani gida ne take zuwa inda suka tabbatar min wannan yaron yana ciki. Yanzu aiki na gama saura ita yarinyar da ɗan'uwanta, suma nan ba da jimawa ba za su kawo mana kan su. " Ya yi dariyar 'yan duniya sannan ya ci gaba da magana. "Ina faɗa maka Damisa mun bar jin labarin sa da alama sun kashe shi, amma dai zan tambayi Dagus naji ya ake ciki." Dariya Alhaji ya yi yana kallon fuskar sweet girl ɗin sa, wani daɗi ne ya mamaye shi ya ce "Ka rabu da wannan yaron Jarmai mu yi aiki mai mahimmanci wanda yake gaban mu, tun da dai mun samu jinin da ya yi daidai da nasa kawai ka bu rabu da rayuwar shi tun da dama mahaukaci ne, abin da ya dace kai ka sake komawa wajan Boka a rikita mana Abir ta kasa nutsuwa har sai ta kawo mana dukkan kadarorin mahifinta sannan ta ji nutsuwa. Shi kuma Abdul ai mun gama kama shi kawai so nake na ga kiran Alhaji Mustapha. " Shuru Jarmai ya yi can dai ya ce "To shi kenan mu aje maganar mahaukaci a gefe, ka ga yanzu nan da shekara mai zuwa za a fara zaɓe dan haka mu tsiro da wata gidauniyar tallafi wadda za ta sa al'ummar Yobe in mun nemi takara su kaɗa mana ƙuri'a. Ba ka ce min nan da sati biyu ba ne daurin auren Abir?" "E nan da sati biyu ne." "E jibi ne kuma duk za mu je mu yi bake-bake akan komai mu nuna mata tsananin ƙauna a wajan taron nan, kuma a matsayin ku na abokan mahifinta ku nuna mata ƙauna a ranar dan ni ka ga uba nake a gare ta." Ya fada yana shafa tumbinsa. Dariya Jarmai ya yi ya ce "Alhaji ba ka da mutumci Wallahi." Shi ma dariyar ya yi suka kashe. Yana kashe kiran sai ga kiran Alhaji Mustapha ya shigo suka gaisa, bayan sun ɗan yi hira nan yake sanar da shi yanzu su Abba suka zo neman auren Hafsat kuma ya amince a hada da na Abir, sosai Alhaji ya yi farin ciki ganin nasarori na tunkaro su gadan-gadan sannan suka yi sallama... An kawo lefi akwati sat shida kowacce ka buɗe cike take taf da kaya na alfarma har da su alƙabba kala-kala, su Umma su ne akan gaba sai jin dadin take tana yi wa Abir kallon za ki gani.. Ɗiyan Inna da ke kasashen waje suka dura Nigeria ranar an sha kuka a part din su Abir, Yasira na rungume da Abir cike da tausayin ta sai rarrashin ta take tana kula da ita, da kan ta ta nemo mai gyaran jiki tun daga Maiduguri ta ce a gyara Abir ciki da waje ta fito ta yi kyau sosai, har da maganin ƙiba ake ba ta dan ta dan yi kumari kafin a kaita gidan ta... Hafsat da Daddyn ta ya faɗa mata ya sa auren ta da Abdul sai da ta buga tsalle ta rungume shi tana kukan farin ciki, dan tun da take babu namijin da take da burin mallaka sama da Abdul, ranar kasa bacci ta yi sai kiran ƙawayen ta take tana sanar da su bikin ta nan da kwana sati biyu duk tana gaiyatar su. Washegari sai ga kiran Abdul abin da ba ta taɓa tunanin zai faru ba Abdul ya kira ta a waya, nan yake sheda mata ta fitar da nako ta mata lis din komai zai turo mata kudin, ai kuwa ta yi ta masa shagwaɓa tana faɗa masa yadda take son shi a zuciyarta da matsayin sa shi ma ya sanar da ita duk matan duniya babu kamar ita, kamar ta yi hauka dan daɗi ta kira Abir suka fitar da anko kala hudu... Yau kofar gidan su Abir cike take a Mutane tun daga farko Layin har karshe mutane ne, kama daga kan yan Niger manya da kuma abokan Suhal da shi kansa Suhal ɗin ya sha shadda gizna sai sheƙi yake irin na angwaye, sai dai kana kallon fuskarsa za ka san ba shi da nutsuwa sai dafe kai yake yana kallon wayarsa lokaci zuwa lokaci.. Bayan an gama daura aure su Abba suka shigo gida inda suka buƙaci a kira duka kowa na familyn yana son ganin su, Umma na jin haka ta rangaɗa guɗa ta zari mayafi ta nufi part ɗin Inna.. Sai da kowa ya hallara har da Hajiya mahaifiyar su Umma itama ta zo, bayan ya buɗe taro da addu'a ya kalli Abir ya ce "Mamana kin yi imani da Allah da mala'ikinsa da kitattafansa da duk manzannin da ya aiko da ƙaddara mai kyau ko akasin haka da ranar karshe?" Jikinta ne dauki rawa ta gyaɗa kai tana ƙara mannewa a jikin Mom Yasira. Ajiyar zuciya ya yi ya ce "An ɗaura auren Abdul da Hafsat, sannan an ɗaura auren Yarima Suhal da Iman.." Wata irin zabura Iman da Abir suka yi a tare suka furta Kalmar "Me ka ce ABBA?" Suka faɗa ta mugun kiɗimewa kowacce sai kallon ƴar'uwar ta take. Fashewa da wani irin kuka mai taba zuciya Abir ta yi tana jan numfashi ta nufi Abba, so ta yi magana amma kukan da ya ci ƙarfin ta ya hana ta yin maganar, kafin ta ƙarasa ta zube a ƙasa sumammiya. Hankali a tashe Iman da ke kusa da inda ta faɗi ta shiga jijjiga ta tana faɗin "Ƴar'uwata don Allah kar ki min haka, Wallahi ko me za ayi ba zan taɓa yarda na auri Yaya Suhal ba, ki tashi Anty Baby...!" _Taku har kullum Maman Nusaiba_ [11/6, 10:53 Yamma] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): ~A HAKA NAKE SON SHI~ +966577675904 Shafi na (30) Gabaɗaya suka yo kan ta cikin tashin hankali amma Iman ta hana kowa ya taɓa ta har Abdul, duk wanda ya yi ƙoƙarin taɓa ta sai ta kurma ihu tana nuna shi da tsaya alamar kashedi. Abba da Daddy da Daddyn Aruf suna zaune ba su tashi ba sai kallon ikon Allah suke ganin Iman ta yi bake-bake ta hana kowa zuwa wajan Abir da ta ke kwance kamar Gawa, a hankali Daddyn Aruf ya tashi ya isa tare da tsugunnawa ya kalli Iman da take gunjin kuka fuskarta ta ci kaca-kaca da majina da hawaye sai kiran sunan Abir take, numfashi ya ja cikin nuna alhini ya ce "Iman ban san ki da wannan halin ba, taya za ta suma amma ki ce ba za a taɓa ta ba?" Ƙara ta kwalla har sai da Daddyn Aruf ya runtse idanuwansa har cikin kwanyarsa yake jin ƙaran, a haukace ta ɗago idanuwanta sun yi jajur ta ɗaura su akan na Daddyn Aruf ta saki kuka ta ce "Matuƙar kuna so na bari ku taɓa Anty Baby sai kun janye auren da kuka ɗaura min da Yaya Suhal kun ɗaura da ita, wannan wani irin tashin hankali ne nake gani ni Iman? Don Allah Uncle ka rufa min asiri ka cewa Abba ya janye kalamansa Wallahi ina son Anty Baby ba zan yarda na zama katangar da za ta raba tsakanin ta da Yaya Suhal ba." Ta ƙarashe maganar tana kama hannun Daddyn Aruf da ya kafe ta da na mujiya. Kafin ma ya yi magana ta ɗago da Abir tana bubbuga kumatunta cikin tsananin fargaba ta ce "Anty Baby ki rufa min asiri ki tashi, Wallahi ko mutuwa kika yi ba zan yarda na auri Yaya Suhal ba, duka nawa nake? Ƙarama da ni za a ce wai an min aure?" Juyowa ta yi ta kalli Abdul da hankalinsa yana kan su ta goge hawaye ta ce "Yaya idan har ka bari aka raba Anty Baby da farin cikinta to tabbas Mommy za ta yi kukan cin amanar da ta ba ka, kai ka mata alƙawarin za ka kula da ita duk abin da take so za ka mata amma kana gani za su aura min wanda take so Yaya why ba ka faɗa min ba kafin a ɗaura? Why Yaya?" Ta faɗa tana sake ɓarkewa da sabon kuka.. Kowa ita ya zubawa idanu sosai ta ba su tausayi, Umma kuwa wani irin kiɗimewa ta yi jin ba Khairat ba ce aka aura wa Suhal Iman ce, duk da hakan dai wani sashe na zuciyarta cike yake fal da farin ciki tun da dai an fasa auren da Abir, tashi ta yi ta iso gaban Iman tana matso hawaye ta ce "Auta ki yi hakuri kin ji, ba wai su Abbanki sun yi hakan ba ne dan su sa rashin jituwa tsakanin ki da Abir ba, sun yi haka ne dan kar mutumcin su ya zube a idanun mutanen Unguwa da ma masarautar Niamey, ki ɗauki ƙaddara kar ki bijire wa iyayenki kin ji. Yanzu kawo ta a yayyafa mata ruwa ko ta farfaɗo sai asan abin yi. " Goge hawaye ta yi cikin tsananin jin zafi ta ce "Wallahi Umma ni ba na son Yaya Suhal, kuma kin ga ko su Anty Khairat ba a musu aure ba amma ace ni ƙarama da ni za ku aurar shi ma auren na dole? Don Allah Umma ki ce su Daddy su ba wa Anty Baby Yaya Suhal shi ne zaɓin ta a kullum." Ta ƙarashe maganar tana sakin Abir Umma ta tallafo ta ta rungume.. Umma ji ta yi kamar ta rufe Iman da duka saboda cewar da ta yi ba ta son Suhal, abin da take ta mafarkin 'ya'yanta su samu aure a gidan masu kuɗi amma ita ta samu daga sama sai ta ce ba ta so ai ba ta isa ba ma. Hararar ta Umma ta yi ta ƙasan idanu za ta yi magana Mom Yasira ta iso da ruwa mai sanyi sosai ta gumtsa ta fesa mata a fuska.. Dogon numfashi ta ja ta soma motsawa duk suka zuba mata idanu, a hankali take buɗe idanuwanta har ta gama buɗe su akan fuskar Mom Yasira da ke gaban ta a durƙushe. Yunƙurawa ta yi ta tashi zaune Umma na taimaka mata ta goge hawayen da suka zubo mata ta ɗago kai ta kalli Iman, a sauri Iman ta matso ta kama hannayenta tana sakin sabon kuka ta ce "Wallahi Anty Baby ko kin mutu ba zan yarda na auri Suhal ba bare kina da rai da lafiya, ki faɗa musu ni ba zan yarda da wannan haɗin ba ba na son su haɗani gaba da ƴar'uwata." Ta faɗa tana ci gaba da kuka.. Sunkuyar da kai ta yi tana jin yadda zuciyarta ke mata wani irin azabtaccan ciwo mai mugun zafi, ji take dama mutuwa ta yi da wannan baƙar ranar da ta riska wai Suhal ɗin ta ne aka aurawa ƙanwarta Iman? Girgiza kai ta yi ta ɗago ta kalli Iman tare da kai hannu ta goge mata hawaye tana yin murmushin yaƙe wanda Hausawa ke cewa ya fi kuka ciwo! Da kyar ta iya saita nutsuwarta ta ɗago da haɓar Iman cikin wata kalar murya mai ban tausayi ta soma yi mata magana. "Ƴar'uwata ki amshi zaɓin da su Abba suka miki dan shi ne ma fi alkhairi a gareki, ni na yi imani da Allah ne ya rubuto ba zan taɓa auran Suhal ba ke ce matarsa shi ya sa hakan ta faru damu. Kar na kuma jin kin ce ba kya son wanda yake son Antyn ki kin ji. " Ta karahe maganar wasu hawaye masu ɗumi suka silalo kan kuncinta, duk wanda ya ji maganar Abir ya san ƙarfin hali ne kawai take saboda yadda muryarta take rawa. Nisawa ta yi sannan ta ci gaba.. "Kaf familyn mu ke kaɗai ce a mata nake jin zan ba da raina fansa na fanshi naki, indai har da gaske kin ɗaukeni a matsayin ƴar'uwa ta jini kuma wadda kike tsananin so da ƙauna, to ki karɓi Suhal a matsayin mijinki kar ki nuna ba ki son shi saboda yana matuƙar son yayarki. Nasan dole ki ji ba daɗi Iman, amma ki daure ki yi biyayya za ki ga ribar hakan a nan gaba kaɗan, ni ma Allah zai kawo min nawa mijin in sha Allah tashi kin ji amaryar Yaya Suhal muje na faɗa miki yadda za ki zauna da shi kanwata. " Ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa jiri na son ɗaukar ta.. Saurin dawo da ita Iman ta yi ta ce "Anty Baby k.." Ɗaure fuska ta yi ta gyara zama ta ce "Kar ki ce komai Iman in dai har na isa na faɗa ki ɗauka." Shuru ta yi ta haɗiye sauran maganar tana zubar da hawaye... Wani irin tausayin ta ne ya mamaye Abba, shi kan shi bai so hakan ta faru fa amma ya zai yi da ikon Allah? Kallon ta ya yi ya ce "Mamana zo nan." Tashi ta yi tsaye tana jin kanta na sara mata kamar zai rabe gida biyu ta daure ta taka ta isa gaban Abba ta zauna a kusan ƙafafuwansa, kanta ya shafa yana jinjina ƙarfin hali irin nasa, itama Iman kiran ta ya yi ta zo ta zauna a kusa a Abir ta ɗaura kanta a kafaɗarta tana jin ciwon wannan lamari.. Gyara zama ya yi ya dubi Grandma da tun da ta zo gurin ba ta ce komai ba sai tagumi da ta yi, a sanyaye ya ce "Inna ina me ba ki haƙuri akan wannan lamarin, nasan za ki ce mun yi gaban kan mu ba mu neme ki ba ki gafarce mu." Sauke tagumin ta yi ta nisa sannan ta ce "To Sulaimanu ya za mu yi da lamarin Ubangiji? Amma ya aka yi hakan ta faru shi nake son ji?" Ta faɗa cikin alhini.. Kallon Daddy ABBA ya yi hakan ya sa ya soma yi musu bayani.. "Inna mu kan mu abin ya ɗaure mana kai, an zo ɗaurin aure sai muka fara ɗaura na Abdul mun zo ɗaura na Mamana har ana ƙoƙarin addu'a sai ɗaya daga cikin dogaran da suka zo ɗaurin aure ya kira ni gefe, hakan ya sa na ce su ɗan dakata muka fita gefe sai ga Suhal ya zo. Ganin yadda yake a hargitse sai abin ya ba ni mamaki nake tambayar su lafiya suka nemi su keɓe da ni? Nan Suhal ke ce min Wallahi shi kwata-kwata ba ya son a aura masa mamana ayi masa musaya, abin ya girgiza ni matuƙa na nemi naji dalilin da ya sa ya ce ba zai aure ta ba sai dai ayi masa musaya, ya ce min shi kawai dai ba ya son auran ta ne a ba shi wata a cikin 'yan matan gidan. Ganin haka ya sa na tsayar da su a nan na taso su Yaya muka zo har da wakilan shi muka shiga tambayar shi ya ce shi sam ba zai aure ta ba, ganin ana jan lokaci sai Yaya ya ce masa to ya zaba wacce yake so? Ya ce mana Iman yake so ita zai aura, mun girgiza sosai da jin hakan ganin Iman ƴar ƙarama ce duk da a addinance ta isa aure amma mun so ya ce ko Yasmin yake so tun da ita ce babba, mun so mu faɗa miki amma abin ya gagara dole muka koma aka ɗaura auren da Iman inda mutanen wajan suka sha mamakin wannan juyin, saboda duk garin nan ba wanda bai ga invitation ɗin auren Mamana ba a social media. " Mom Yasira ta fusata ta ce "Wallahi Yaya ban ji daɗin wannan lamarin ba Allah ya gani na so mai sunan Inna ta auri Yarima saboda nutsuwar shi ga yana son ta, amma lokaci ɗaya ya ce ba ya son anya Yaya?" Ta faɗa tana hura hanci.. Kallon banza Umma ta mata tana jin kamar ta zabga mata mari mai zafi. Nasiha sosai su ABBA suka yi wa Iman suna ƙara gargadin ta ko da wasa kar ta nuna masa ƙiyayya, ita kuma Abir suka yi ta ba ta haƙuri tare da kwantar mata da hankali suna nuna mata muhimmacin haƙuri akan abin da ka rasa, ta ce musu ai tuni ta haƙura ta bar wa Iman da haka dai Abba ya ce kowa ya tashi ya koma a ci gaba da hidima a gyara amarya an jima za su wuce Niger.. Hannun Iman Abir ta kama suka fita Abba ya bi su da kallon tausayi, yana jinjina irin ƙaunar da ke tsakanin su. Da sauri Umma ta biyo su Iman ganin za su shiga ɗakin Abir ta kira su suka waiwayo, ƙarasowa ta yi ta kalle su a fuska ta yi kamar za ta sa kuka, amma zuciyarta cike take fal da farin ciki marar musaltuwa. "Abir don Allah kar ki sa damuwa a ranki kin ji, ki yi haƙuri dama can Suhal ba shi ba ne mijinki, naki mijin yana can a wani waje a gaba Allah zai haɗa ku, kuma kar ki ɗauki gaba da Iman duk da nasan ƙaunar da ke tsakanin ku ba ma za ki yi haka ba amma an ce zuciya ba ta ƙashi." Ta faɗa tana dafa ta.. Murmushi Abir ta yi ta ce " Ai Umma ko raina zan ba da akan Iman ballantana wani ɗa namiji, in sha Allah ba zan taɓa ganin baƙin Iman ba dan ta auri wanda nake so. " Jinjina kai Umma ta yi ta ce "Haka ne 'yata, to kawo ita Iman ɗin a shirya ta kin ji Abban ku ya ce an jima za a wuce da ita." Kallon Iman ta yi tana ƴar dariya ta ce "Amarya ki je ayi miki wanka yau za mu kora ki gidanki." Dukan wasa Iman ta kai mata tana ƙara jin son ƴar'uwatar tata ta bi Umma suka wuce part ɗin su... Daret ɗaki ta nufa Mom Yasira ta bi bayan ta ita da Mom Nabila. A tsaye suka same ta ta cire ɗankwali da hijab tana tsaye ƙiƙam kamar wadda aka dasa, ganin su ya sa ta kawar da duk wata damuwa ta ƙirƙiro murmushi tana kallon su. Rarrashin ta sosai suka dinga yi tana kuka mai tsuma zuciya har ta yi shuru, sai da suka tabbas ta daina kuka sannan Mom Nabila ta fita ta kawo mata tea ta sha ta miƙa mata maganin ciwon kai ta sha sannan ta zauna a bakin gado, sosai suka kula da ita suna ƙara yi mata nasiha ta kuma ce ta yi imani da ƙaddara kar su damu da ita ma za aje kai Iman... Suna fita ta rafka tagumi tana tuna irin yadda Suhal ke nuna mata tsananin so da Ƙauna, yana ba ta lokaci a kullum dan su ƙara samun kusanci da juna ashe dai ba rabon sun rayu a matsayin miji da mata. Ajiyar zuciya ta sauke jin an dafa ta, juyo wa ta yi ta ga Abdul ne ba ta san ba lokacin da wani irin kuka ya zo mata ta faɗa jikinsa ta fashe da kukan... Bubbuga bayan ta yake yana jin wani iri kukan ta na taɓa masa zuciya, da yana da iko da ya hana wannan auren abar mata masoyinta. Ɗago da ita ya yi yana share mata hawaye cikin wani kalar yanayi ya ma kasa magana, da sauri ta koma jikinsa cikin kuka ta ce "Yaya me na yi wa Suhal haka da zafi har ya zaɓi ya kasheni kwanana bai ƙare ba? Ko wani abin aka ce masa ina yi marar kyau da har zai bar ni ya koma kan wata?" Kanta ya shafa yana jin ciwon abin da aka mata amma ya zai yi da ikon Allah? Dole ne ya sa ta ta haƙura da Suhal tun da Allah bai ƙaddara shi ne mijin da za ta aura ba. Sake ɗago da ita ya yi ya yi gyaran murya tare da ruko hanayenta ya ce "Baby ke fa musulma ce me ya sa kike irin wannan kalaman? Ki yi haƙuri nasan dole za ki ji zafin abin, amma ki yi wa Suhal uziri kar ki ƙullace shi ko da na ɗaya rana ne, kar ki tuhume shi da cin amanarki ki yafe masa abin da ya aikata a gareki, ki gode wa Allah ma Iman ya ce yana so jininki ƴar'uwarki wadda duk family kowa ya sheda kun fi kusanci da juna. Ina so ki manta da Suhal a matsayin masoyi ki goge wannan a babin rayuwarki ki ci gaba da harkokin ki kamar yadda kika saba, ban da abin ki meye na tayar da hankali? kin fa san da cewa matar mutum kabarinsa wani ba zai taɓa auran matar wani ba dole kowa tashi zai aura, ki ƙaddara cewa ke naki mijin ne bai zo ba yana nan tafe. Tashi ki zauna nasa Laraba za ta kawo miki abinci ki ci ki nuna kamar ba ki ji ciwon abin da ya faru ba ki saki ranki ko da kuwa a zuciyarki ba hakan ba ne, idan har ki na kuka za ki ba wa maƙiyan ki damar yi miki dariya tun da dama ba son auren ki suke ba da shi. " Shuru ta yi tana sauraron shi har ya gama yi mata jawabi, a hankali ta kai hannu ta goge hawayen murya a shaƙe ta soma magana. "In sha Allah Yaya zan daure na rasa Mom ma na dangana bare wani Suhal, zan yi duk abin da ka ce Yaya in sha Allah ko na fita ba zan yi kuka ba." Ta faɗa tana kirkiro murmushi yaƙe. "Yawwa my Baby dama nasan ai ke Jaruma ce." Murmushi ta kuma yi suka ji an buɗe ƙofar an shigo, Labara ta iso ta aje farantin tana hura hanci ta zauna tare da kallon su. Abdul ya yi murmushi ya ce "To ke kuma fa wa ya taɓo ki?" Kwafa ta yi sannan ta ce "Su Maman Yasmin ne wai dan naje kiran wannan tsohuwar shi ne har Yasmin ta mareni ban mata komai ba." Ta faɗa tana goge hawayen da suka zubo mata.. Waro idanu suka yi a tare Abir ta ce "Me kika mata har ta sa hannu ta mare ki?" Tsaki ta ja ta ce "Wai dan sun ganni suke cewa dama ai Suhal ba da ke ya dace ba da ɗaya daga cikin su ya dace, to shi ne fa ina isa ni kuma ban ce komai ba na ce ana kiran Hajiya shi kenan na yi lefi tsohuwar nan ta dinga zagar min iyaye tana cewa ko Mom da ta ja da su sun kai ta ƙasa bare ni ƴar aikin ta, ni ma in munafurci ya kawo ni rahoto zan dauka na kawo muku sai su min abin da zai sa ko sunan familyn gidan nan aka ambata sai na suma. Shi ne na ce ta daina zagina ni ai ba ƴar familynsu ba ce kawai fa daga haka Yasmin ta mare ni za ta sake min Iman ta fito daga ɗaki ta kareni ta ce na tafi ba su da mutumci. " Jinjina kai Abdul ya yi ransa na ƙara ɓaci, ya zama dole ya saita wa Yasmin hanya a gidan nan, Abir itama ji ta yi wannan karon ba za ta yi haƙuri ba dole ta ɗauki mataki, idan har ita suna mata tana kyale su a matsayin su na 'yan'uwanta to ba fa za ta kyale suke cin zarafin ƴar aikin su ba kuma amanar da Mom ta bar musu. Tashi ta yi tsaye tana huci ta kalli Laraba ta ce "Laraba tashi muje yau sai na ga uban wa yake daure musu gindi suke wulaƙanta ki." Sake da baki suke kallon ta jin abin da ta faɗa, shi kan shi Abdul ya yi mamakin kalamanta saboda bai taɓa gani tana zagi irin haka ba bare yin rigima. Ɗagowa ya yi da niyar mata magana ya ga wayam, da sauri ya miƙe ya nufi palo... Suna zaune ana tattaunawa akan wanda za su raka amarya gidanta, tana isowa ta duba su da kyau ta hango Yasmin a gefen Hajiya tana mata kallon ya haƙuri, kwafa ta yi ta ƙaraso har inda suke ta tsaya a kan Yasmin cikin fusata ta ce "Uban wa ya ba ki umarnin ki mari Laraba? Ƙanwar Ammi ce ko ta Daddy? Kun haɗa jini da ita ne da kika mare ta?" Gabaɗaya palon dauki wuta suka yi ganin yadda Abir ke masifa ba ji ba gani, Hajiya ta riƙe baki ta ce "Yo mu ai tun da aka hada mu da irin masifa ai mun shiga uku, yarinya kin haifu kin dauki gadon mai dattin ɗankwali duk wani baƙaƙen halayenta ga su nan kin soma fito da su za ki daura daga inda ta tsaya n...." Ba ta ƙarasa ba Abir ta katse ta tare da cewa "Hajiya ya ishe ki haka!" Ta faɗa a fusace sannan ta daura "Shin wai me Mom ta tsare muku ne da kuka tsane ta har haka? Lefin ta ne ɗan ta zama matar Abie? Ko wani yana auran matar wani ne? To Wallahi daga yau na daina jin karar kowa a familyn nan ko min tsufan mutum ya ƙara zagar min uwa ko ya ci mutumcin ta a gabana kotu ce za ta rabani da shi, haba wannan wacce irin rayuwa ce wai?" Ta faɗa tana yin numfashi fat! Fat! Kamar wacce tsananin zazzabi ya rufe ta... Tsoro ne ya kama Hajiya ganin yau wai Abir ce take faɗa mata magana son ranta, Mom Yasira kuwa murmushi ta yi ita kan ta abin na damun ta akan tsanar da su Hajiya suka yi wa Mom, Abdul kuwa sumar tsaye ya yi a bakin kofar ɗakinta, mamaki ya hana shi takowa bare ya zo ya janye ta daga gaban su. Ita kan ta Ammi ta girgiza da jin kalaman Abir tana tunanin yaushe ta zama marar kunya? Yasmin ta miƙe ta daga hannu za ta mare ta ta yi saurin damƙe hannun, cikin tsananin ɓacin rai Abir ta ce "Kar ki kuskura ki aika babban kuskuren da zai sa har ki mutu kina da na sanin shi marar amfani." A kufule Yasmin ta ce "In an mare ki wani abin za ki.. Kafin ta ƙarasa ta ji saukar mata tass! Tass!.. A kiɗime ta ɗago ta ga Abir na nuna ta da tsaya ta ce "Ki riƙe girman kafin na sa ƙafa na take na murje shi a ƙasa." Tana gama fadin haka ta sake mata hannu ta dawo gefen Mom Yasira ta kwanta akan cinyarta, sosai zuciyarta ke tafasa ta lumshe idanu tana jin ruwan ashar ɗin da Yasmin ke mata ana rike ta sai ta zo ta dake ce.. Mom Yasira ta ɗago ta ta miƙar da ita suka wuce dakin Grandma. Hajiya ta kalli Gradma ta ce "Lalle Hauwa'u, ki na gani wannan yarinyar ta mari Yasmin amma kika yi shuru?" Kawar da kai Gradma ta yi ta ce "To me kike so na ce? Kun ga ku tashi ku tafi ku shirya amarya dangin Ango suna son a wuce bana son damuwa ni." Ta faɗa tana kaɗa ƙafa. Kwafa Hajiya ta yi ta tashi ta kama hannun Yasmin da take jin takaicin marin da Abir ta mata duk suka wuce... Bayan an gama shirya amarya aka fito da ita harabar gidan za a saka ta a mota amma fir ta ce ba za ta shiga ba sai ta ga Abir, dole Mom Nabila ta kama hannunta suka zo ɗakin Gradma suka gan ta a zaune tana shan tea, ganin Iman ya sa ta miƙe tana murmushi ta ce "To ƴar'uwata Allah ya ba da zaman lafiya sai mun yi waya." Idanuwan Iman ne ya cika taf da hawaye Abir ta kamo ta suka rungume juna ta saki kukan da take danne wa, rarrashin ta Abir ta yi tana faɗa mata ai za su yi waya da sun je za ta kira Mom Yasira su gaisa, da kyar Mom Nabila ta ɓamɓare ta daga jikin Abir tana kuka tana waiwayen ta har suka bar ɗakin .. Umma ta rungume Iman tana murmushi ita kuma tana ta kuka tana cewa ba za ta tafi ba, da kyar ta lallami ta shigar da ita mota suka tafi.. Daret airport suka tafi nan suka haɗu da dangin Ango nata jiran su, ba su daɗe ba jirgi ya sauka suka shiga ya ɗaga su zuwa kasar Niger.... Yasmin kuwa ta ci alwashin sai ta yi wa Abir abin da za ta zama abin kwatance da zarar sun dawo daga kai Iman, itama Ammi haka ta ƙudurta za ta saita wa Abir zama... _Maman Nusaiba ce_ [6/20, 8:43 PM] Ummu Amjad: ~A HAKA NAKE SON SHI~ +966577675904 Shafi na (31) Cikin dare zazzaɓi mai tsanani ya rufe Abir sai rawar sanyi take tana ƙara ƙudundunewa a cikin bargo, da kyar ta ɗaga idanuwanta ta kalli gaban ta ko za ta ga wayarta amma ba ta gani ba. Wani irin murɗawa cikinta ya yi ta runtse idanu tana fitar da wani irin numfashi mai zafin gaske, juyi ta dinga yi tana salati ji take kamar ana yankan 'yan hanjinta in cikin ya murɗa. Zuwa can ya lafa ta shiga sauka numfashi sai zufa ta dinga karyo mata kamar an mata feshin ruwa, dogon numfashi ta ja tana jin kanta ya mata mugun nauyi ga wani irin zafi da ya ɗauka daga ciki ji take kamar an kara mata kan a gaban tukubar gashin tsire. Ciwon cikin ne ya ƙara taso mata gadan-gadan wannan karon ko addu'ar ta gagare ta sai miƙa take tana lauyewa kamar maciji, wani irin abu mai nauyi ta ji an sakar mata shi akan ƙirjinta wanda ya yi barazanar ɗaukewar numfashinta in ta fesar da iska ba ta iya shaƙowa, nan da nan ta fita haiyacin ta ta dinga shure-shure kamar wacce take kan gaɓar mutuwa sai kumfa da ke fita daga bakinta idanuwanta sun kalli sama.. Ta jima a cikin wannan yanayin kafin daga bisani idanuwanta suka dawo daidai amma nauyin da take ji yana nan kamar ƙara mata ma shi aka yi, wani haske ta gani ya baiyana a gefen ta ya haske mata fuska aka dauke wutar ɗakin.. Cikin shiga ta kamala ta baiyana fuska ɗauke da murmushi, kallon ta Abir take har ta iso kan gadon ta zauna ta kai hannu ta shafa mata ƙirjin, ɗayan hannun ta ɗaura a kanta tana kallon ta cikin idanu. Kamar cirar ƙaya haka Abir ta ji zazzaɓin ya sauka har ciwon kan da nauyin ƙirjin duk babu su ras take jin ta, a hankali ta yaye bargon da ta lulluɓa ta tashi zaune ta fuskance ta tana kallon ta ba ko kiftawa. A hankali ta kama hannun Abir hakan ya sa Abir jan numfashi jin wani sanyi ya ratsa mata jiki, murmushi ta kuma yi ta ce "Hauwa'u duk na ga abin da ya faru da ke, amma ki yi haƙuri kamar yadda masoyanki ke faɗa miki, rashin auren Suhal shi ne alkhairi a gareki dan da Allah ya sa kuna da rabon aure to tabbas maƙiyan ki za su iya mayar da ke abin tausayi a idanun duniya. Yanzu haka ma baƙaƙen aljannu ne aka turo miki waɗanda za suke firgitar da ke in tsakiyar dare ta yi, so suke lalle dole sai kin bar duniya sun danne duniyarki da mahaifinki ya bar miki. Yanzu dai mafita ɗaya ta rage miki matuƙar ki na son ki samu salama a rayuwarki. " Ta faɗa tana kafe ta da kallo. Sosai tsoro ya mamaye Abir tana jinjina lamarin, shin ita kaɗai ce me wannan baƙin jinin ko akwai wanda aka tsana irin ta a duniya? Me ta yi da ake son ganin lalle sai ta mutu? Girgiza kai ta yi cikin tsoro ta ce "Mama yanzu ni ba ni da damar da zan yi farin ciki a duniya? Me na musu da har ba a so a ɗaga ido a ga ina cikin walwala? Don Allah ki faɗa min su waye maƙiya na bayan 'yan'uwana?" Tashi ta yi daga kan gadon ta koma jikin bango ta maƙale ta zauna kamar tana ƙasa, waro idanu Abir ta yi tana kallon ta cike da tsoro, ita kuwa ƴar dariya ta yi cikin ƴar siririyar murya ta soma magana. " Hauwa'u kenan, ke dai ki dage da addu'a saboda maƙiyan ki sun fi masoyanki yawa a rayuwarki, ba kuma zan faɗa miki wannan mafitar ba za ki gani da idanuwanki kuma ki bi hanyar, sannan ba zan faɗa miki maƙiyan ki na waje ba har sai lokaci ya yi zan sanar da ke komai da kike tambaya ta. " Rausayar da kai ta yi cikin rashin sanin madafa, to ita taya za ta bsamu sassaucin wannan rayuwa da take ciki? Nisawa ta yi ta dube ta ta ce "To amma Mama me ya sa ba za ki sanar da ni wani abu da ya shafi Zaiyan ba? Kin ga yanzu ni nake kula da shi ya kamata ki faɗa min komai nashi ta yadda in ya samu lafiya na sada shi da ahalinsa." Ta faɗa tana zubar da hawaye. "Ki daina arhar hawayen ki a inda ba a san darajar su ba, ka da ki ce a gaban kowa za ki zubar da hawaye, in kuwa ki ka ci gaba da haka tabbas maƙiyan ki za su ci gaba da samun nasara a kan ki, lokaci ya yi da za ki shiga hankalinki ki nutse ki daina kuka a inda ba a san ke mutum ba ce. Zaiyan shi ne mafitar ki a daidai wannan gaɓar, ki jira lokaci zai nuna miki Zaiyan ne mafitar matsalar da kike ciki. " Tana gama faɗin hakan ta ɓace ɓat kamar ba ta taɓa wanzuwa a ɗakin ba.. Dafe kai Abir ta yi tana jin komai ya cinkushe mata, Zaiyan da bai san ba kanshi taya zai zama maganin matsalar da take ciki? Buɗe idanu ta yi ta juya gefen ta ta lalibo wayarta ta ga har karfe biyu da rabi ta yi na dare, da sauri ta sauko ta nufi toilet ta dauro alwala ta zo ta tayar da Sallar nafila. Bayan ta gama ta ɗaga hannu ta na kwararo addu'o'in Allah ya kare ta ya mata tsari da duk wani abin cutarwa, ta yi wa Mom addu'a da Iman da Abdul da dukkan musulmai bakiɗaya sannan ta shafa. Sai da ta kwanta sannan ta janyo waya ta leƙa Tiktok dan ta ga me ke faruwa, da maganar auren ta ta fara cin karo a commet section mutane dayawa sun jajanta mata wasu har zagin Suhal suke suna ce masa mayaudari, runtse idanu ta yi ganin commet ɗin wata fans ɗin ta da ta jero ruwan ashariya tafi kala goma ta yi wa Suhal har da su tsinuwa. Gaba ta yi nan ma magana ake akan auren wasu har video daurin auren suka ɗaura, mutane da dama ba su ji daɗin abin da ya faru da ita ba, wani sanyi taji ganin kowa na alhinin abin da ya faru da ita ta yi gaba. Posting ɗin wani gaye ta gani mai suna da manyan marufa *BIG BOY* Ya yi posting ɗin video daurin auren ta tare da yin rubutu wanda yake nuna bacin ransa akan lamari. _"Gaskiya Yarima Suhal ka zama cikakken mayaudari, na rantse da Assamadu da ace a Nigeria kake saboda da friend ɗi ta Abir in ban sassoka maka wuƙa ba shege nake, kai alƙur'an duk ranar da na gamu da kai sai na sare ma kafaɗa."_ Riƙe baki Abir ta yi tana ganin yan comment na goya masa baya, gyaɗa kai kawai take tana kallon ikon Allah masoyanta kowa sai da ya sa abin da ya faru da ita a fagen ɗin sa yana mai nuna alhini. Sai da ta ji bacci na fusgar ta ta aje wayar ta tashi zaune, ayatul kursuyu ta karanta ƙafa bakwai ta soma duk ƙafa ɗaya a kowacce kusurwa gabas, yamma, arewa, kudu, sama, ƙasa, ta karshen ta shafe a jikinta sannan ta karanta ƙulhuwa, falaƙi da saani tukun ta kwanta... Hafsat ko ƙawayenta ba ta bari ba sun zauna an sayi baki ba ta zaro kuɗi daurin dubu ɗari ta ba su, da mamaki duk suke kallon ta wata yar ajinsu ta ce "Hafsy wannan fa?" Murmushi ta yi ta yaye mayafin da aka rufe mata fuska ta sauko daga kan gadon, kallon raini ta musu ta ce "My Husband ne ya ce ba ya son surutu dan haka ya ba ni kudin sayan baki da kun kawoni na ba ku ba sai kun jira shi ba." Ta faɗa tana cire ɗankwali ta yi jifa da shi.. Wata daga cikin su ta ɗaka wa Hafsat duka a mazaunai ta ce "ƴar iska marar mutumci, to ki bi dai a hankali Wallahi in dai wannan ɗan zafin kan ne sai ya gasa miki aya a hannunki, mu za ki nunawa kin yi aure? Kai ku zo mu tafi gobe ma rana ce ai." Ta faɗa tana yin gaba. Dariya Hafsat ta yi tana maƙale kafaɗa irin ko a jikinta, sauran sallama suka mata suna jinjina tsaurin idanu irin na Hafsat. Ko lokacin da aka ɗaura aure Mom ɗin ta ta ce sai washegari za a kaita, ai kuwa ta yi tsalle ta dire ta ce Wallahi yau za a kai ta gidanta ba za ta sake kwana a gida ba. Saboda mamaki Mom ɗinta kasa magana ta yi ba ta taɓa tunanin rashin kunyar Hafsat ya kai har haka ba, ganin abin ya yi yawa aka kira Daddynta ya zo ta sake maimaita maganar a gaban shi ya kuwa ce kawai a kaita kar su ga lefin ta so ne. Sai da Mom ɗinta ta kira ta dan ayi mata nasiha ta kafe ta ce ita fa ta san yadda ake zaman aure haƙuri da biyayya ne dan haka ba sai an mata wata nasiha ba. Mommy ba ta tsinke da lamarin Hafsat ba sai da ta ga Hafsat ta shiga ta yi wanka tana cewa kwalliyar ma in ba za a mata ba sai ta yi da kanta, haka dai aka shirya ta suka tarkata ta aka kawo ta gidanta.. Zama ta yi ta kira kira Abdul yana ɗauka ta sa kuka, a ruɗe Abdul ya miƙe tsaye yana faɗin "My love lafiya kike kuka?" Turo baki ta yi ta ce "To ba kai ba ne kaƙi zuwa sai jiran ka nake, ni fa so nake na gan ka kusa da ni." Ta faɗa tana yin baya ta kwanta tare lumshe idanu.. Da sauri ya ce "Am so sorry my love gani nan zuwa yanzu, please ki daina kuka." Ya faɗa yana katse kiran, kallon shi Hashim ya yi cike da mamaki ganin yadda ya ruɗe ya ce "Malam ba za ka tsaya su zo ba mu raka ka?" Ko ci kanka Abdul bai ce mishi ba ya dauki wayoyinsa y yi gaba, baki sake Hashim ke kallon Abdul har ya fita.. Yana packing ta leƙo daga window tana kallon shi, wani irin so da ƙaunar sa na ratsa ta ta yi saurin komawa kan gadon ta kwanta ta soma kukan ƙarya. Tun daga palo yake jin sautin kukan ya yi saurin shiga ɗakin duk ya riɗe kamar ba Abdul ba, da sauri ya hayo kan gadon ya ɗago da ita ya ce "My love yi shuru gani na zo." Hannu ta sa tana murza idanu ta faɗa jikinsa ta dinga masa shagwaɓar wai ta gaji shi zai mata wanka, babu muso ya dauke ta cak ya nufi toilet da ita yana rarrashin ita kuma tana ƙara narke masa. Bayan sun gama wanka ko Sallah ba ta bari su yi ba ta manne masa da ya motsa za ta ce bayan ta ciwo, shi kuwa duk abin da ta ce masa biye mata yake yana shafa bayanta yana jero mata sannu ya ja musu bargo suka.. _NIGER_ Suna isa Niger cikin garin Niamey motoci daga gidan sarauta suka zo ɗaukan amaryar Yarima Suhal, wata irin faduwar gaba Iman ta ji ta kawo mata ziyara ta dafe ƙirji tana tunanin yadda dangin Suhal za su karɓe ta a matsayin suruka, sai da Mom Nabila ta dafa ta tare da cewa "Ka da ki sare Iman ki zama mai ƙarfafawa kanki gwiwa ba mai sakar da ita ba, ki yi Bismillah mu fita ga masu jiran mu nan a tsaye." Jinjina kai ta yi ta tuna maganganun Abir nan-da-nan ta ji kwarin gwiwa ya zo mata ta tashi Mom Nabila ta riƙo hannunta suka fito.. A hankali take taka matakalar jirgin har suka sauko dukkan su, da sauri masu hidimar gidan sarauta suka shinfiɗa wani jan carpet mai tsayi har bakin motar da amarya za ta shiga, a kan carpet ɗin an sanya sunan *YARIMA SUHAL* da manyan harufa. Haka Mom Nabila ta saki hannun Iman ta ce ta nutsu ta bi kan carpet ɗin ta dinga tafiya tana yin addu'a har ta shiga motar, da to ta amsa ta soma takawa a hankali da ta zo kusa da hidimai sai sun dan rusuna sun ce "Barka da sauka Gimbiya." Ita kuwa sai ta ji wani bambarakai wai namiji da suna Hajara! Haka ta dinga takawa cikin nutsuwa inda wasu ke cewa ai amaryar nan ƴar Gayu ce sosai ga izza da haka dai har ta shige Motar.. Saida aka dauke carpet ɗin sannan Mom Nabila ta iso bakin motar ta kalli Iman ta ce "Sun ce wannan motar ke da Ango ne dan haka mu za mu shiga sauran, ki nutse kin ji." Ta faɗa a hankali ta yadda ba mai jin abin da take fada. Jinjina kai ta yi ita kuma duk suka nufi sauran motocin suka shiga aka nufi Masarauta.. Sai da suka yi nisa sosai daga airport ɗin ta ji an tsaya, ba ta ɗago ta ga ko a ina suke ba ta ƙara lulluɓe fuska tana jin wani sanyi na mamaye mata kamar mai jin zazzaɓi, motar aka buɗe masa cikin shigar sa irin kalar kayan jikinta ya shigo aka rufe sannan suka ja motar.. Wani kalar ƙamshi Iman ta shaƙa wanda tun da take jin ƙamshin turaruka ba ta taɓa jin ƙamshi mai daɗin wannan turaren da ta ji ba, a hankali ta ɗago kai dan ta ji ƙamshi sai ƙara mamaye motar yake. Waro idanu ta yi ganin Suhal zaune a daf da ita ya sha kyau kamar ba gobe, wani irin fitinannan kyau ta ga ya ƙara yi mata akan wanda ta san yana da shi ta lumshe idanunwanta ganin ba ma ita yake kallo ba hankalinshi a can yana kallon gefe, tunani ta dinga yi dama ya riga su zuwa ne? Girgiza kai ta yi ta soma wasa da yan yatsunta dan taji daɗi da bai mata magana ba.. "My Iman." Ta ji ya kira sunan ta murya can ƙasa, ɗago kai ta yi ta kalle shi sai ta ga ya juyo sun haɗa idanu ta yi saurin sunkuyar da kai, sai da ya sake kiran ta sannan ta ɗan turo baki gaba ta ce "Ka ga Malam karka sake kiraye min suna." Ta faɗa tana murguɗa baki. Murmushin gefen baki ya yi ya matso sosai daf da ita ya miƙa hannu ya janyo ta jikinsa ya rungume ta, zazzaro idanu Iman ta yi ta soma mutsu-mutsun kwacewa sai kuma ta ga hakan bai dace ba tun da akwai direba ga kuma dogari, ba dan ta so ba ta kwantar da kanta a ƙirjinsa tana sauke ajiyar zuciya. Kumatunta ya shafa yana jin kamar ya mayar da ita cikinsa saboda yadda yake jin son ta na ratsa shi, a hankali ya sunkuyo ya manne mata kiss à kunci ya ce "Wannan bakin rashin kunyar taki sai na murɗe shi." Ya faɗa da wani kalar salo. Ji ta yi haushi ya kama ta kai da ba a son ka meye na wani zaƙewa? Turo baki ta kuma yi ba ta ce masa komai ba har suka iso masarautar.. A harabar masarautar suka samu su Mom Yasira tsaye suna jiran zuwan su, a hankali ya ɗago da ita kamar wanda ya ɗauki kwai,, ita kuwa duk haushi ya cika mata ciki ganin yadda yake mata ta yi kwafa tana aiko masa harara, duk kuma yana ganin abin da take ya share ya buɗe motar dogarai suka kewaye shi suna fadin "Gyara kimtsi da kyau! Allah ya taimaki Yarima ango." Fuskar nan a haɗe ya fito daga motar ya sunkuya ya kamo hannun Iman ya fito da ita ya tsayar da ita a gefen shi tare da jingina ta da jikinsa ya saƙalo hannunsa a ƙugunta. Guɗa matan suka ɗauka ana faɗin amaryar Yarima ta sauka lafiya, sai da aka kuma shinfiɗa musu carpet green color suka soma takawa, a hankali suke tafiya sai ya saki fuskar shi amma bai yi murmushi ba haka suka taka har zuwa babban palon Maimartaba suka zauna, a nan suka tarar da Mamma da Sarauniya Bilkisu da kuma Kilishi sun kakimce a kan kujera kowaccen su ta sha ado na ban mamaki kamar za su je gasar kyau, kasancewar su farare sai suka ƙara haska wajan duk da Kilishi baƙa ce amma ita ɗin ma ta yi kyau sosai.. Mom Yasira ta kama Iman ta zaunar da ita a gaban su Kilishi su kuma suka samu waje suka zauna.. A wulaƙance Sarauniya Bilkisu ta ce "Sannu da zuwa." Amsawa suka yi da yawwa itama Kilishi ta musu sannu da zuwa inda Mamma kuma ke yi musu murmushi, Ammi ta riƙe baki ganin Mamma ba ta ce komai ba sai ma gani ta yi ta ɗago da Iman ta rungume ta tana ci gaba da murmushi. Iman da yake ta san labarin Mamma a wajan Abir sai ta ƙara shigewa jikinta, a hankali ta ɗago daga jikinta tana murmushi ta ce "Mamma." Jinjina mata kai ta yi idanunwanta suka cika da hawaye ta yi saurin hana su zubowa, zama ta yi itama Iman ta zauna ta gaishe da su Kilishi suna mata wani irin kallo suka amsa.. Bayan sun gama aka ce duk su fita Maimartaba zai shigo a bar mace ɗaya a tare da Iman sai matan Sarki da Ango, Mom Yasira ta ce ita za ta tsaya su su tafi masauki, da farko Ammi ta so ta tsaya amma dan kar ta bayar da su ta haƙura suka fita... Marmartaba na shigowa ya yi musu nasiha sosai ya ja hankalin su game da zamantakewar aure, sosai duk jikin su ya yi sanyi ita da Suhal sai zubar da hawaye take har ya gama musu nasiha. Bayan Maimartaba ya yi tasa su Kilishi suma suka dinga yi wa amarya da ango nasiha, mamaki fal ran Suhal amma ya yi ta murmushi jin wai Kilishi ce take cewa ya ji tsoron Allah ya riƙe amana kar ya zalunci ƴar mutane, sai da suka gama Maimartaba ya ce ya sallame su kowa ya tashi Mamma ta yi wa Mom Yasira alama da su biyo ta suka bi bayan ta. Sai da suka fito za su shiga sashen Mamma Iman ta ga an tsaya a gaban ta, tsayawa suka yi ganin hamshaƙiyar matashiyar budurwa tsaye a gaban su tana yi musu murmushi. Dam! Iman ta ji gaban ta ya faɗi ganin kallon da take mata amma ta dake ta ƙara jan alƙabba ta rufe fuskarta. "Amarya ayi min afuwa ban zo da wuri ba ga shi har za ku shiga sashen Mamma, ina fatan za a riƙe min Yayana da amana." Ta faɗa tana sakin murmushin da ita kaɗai ta bar wa kanta sani. Jinjina kai kawai Iman ta yi Jakadiya ta ɗan rusuna ta ce. "Ranki ya daɗe muna so za mu kai Gimbiya ta samu ta huta ga Angonta can yana kallon mu kar mu yi lefi." Ta faɗa cikin jin tsoron Fauziya dan kar ta mata tijara a gaban su Mom Yasira.. Gyaɗa kai ta yi zuciyarta na tafasa ganin wannan wannan ƴar kwailar ce matar Suhal, kwafa ta yi ta yadda ba za su gane ba ta ba su izinin wucewa suka yi gaba.. Daret gaban wajan Suhal ta nufa da yake gefe shi da wata hadimarsa wacce ba za ta wuce shekarun Abir ba suna magana, tana isowa ta yi gyaran murya ya yi banza da ita ya dubi hadimar ya ce "Ina Fatan kin gane bayanin duk da na miki ko?" Rusunawa ta yi cikin girmamawa ta ce "Na fahimta ranka ya daɗe kuma ango." Murmushin gefen baki ya yi abin da duk hadiman gidan ba sa samu sai ita kaɗai yake iya sakin wa fuska ya mata magana, wannan abu na ƙonawa sauran hadiman gidan rai ganin yadda komai nasa in ya tashi ita zai kira. Ganin zai zubar mata da girma a gaban ƙaramar yarinya ta dan nisa ta ce "Yaya Suhal Ango wajan ka fa na zo." Wani irin kallo ya mata wanda ya sa ta sha jinin jikinta, sallamar hadimar ya yi ta tafi ya dubi Fauziya murmushi ya mata wanda ya sa ta shagalta da kallon shi, tsaki ya ja sannan ya ce "Ba ni da lokaci sai na matata, idan kina da wata magana sai ki bari nan da wata uku sai ki yi maganar." Ya faɗa yana yin part ɗin Mamma.. Wani irin turiri zuciyar Fauziya ke yi ganin yadda ya gasa mata magana, kwafa ta yi ta nufi part ɗin Sarauniya Bilkisu tana jin kamar ta fasa ihu ko ta ji sassaucin kishin da ke cin mata zuciya... _Maman Nusaiba ce_ [11/9, 11:01 Yamma] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): ~A HAKA NAKE SON SHI~ +966577675904 Shafi na (32) Suna shiga part ɗin Mamma aka shigar da su masaukin su in da shi ma ne part babba wanda ya kasance na Iman ne, sosai suka yaba da tsarin palon komai na musamman ne a ciki Ammi sai gyaɗa kai take tana jin haushin da ba Fatima ko Yasmin ba ce ta samu wannan daular, ɗakin da ke kallon kitchen ta nufa ta murɗa ta shiga ciki. Waro idanu ta yi ganin wani makeken gado an masa shinfiɗa ta alfarma sai ƙamshi ɗakin yake, da kyar ta isa bakin gadon tana riƙe baki cike da jinjina lamarin gidan sarauta. Ko'ina na ɗakin sai da ta duba har wardrobe ta buɗe ta ga kayan Yarima Suhal ne kala-kala iri daban-daban ga su nan a goge wasu an rataye su ko buɗa su ma ba a yi ba, gyaɗa kai kawai Ammi take ta sake buɗe ɗayan gefen inda kuma ta ga set ɗin kayan mace ne wanda take kyautata zaton na Iman ne cike da wajan a jere tsaf sai ƙamshi suke, wata riga da wando ta gani 'yan kanti masu azabar kyau duk cikin kayan sun fi jan hankalinta, a hankali ta ta janyo ta buɗe tana riƙe baki mamaki ya ƙara kama ta ganin kuɗin kayan ya fi dubu 50k a naira. Cukuikuyawa ta yi ta cusa dan ta kasa linke su kamar yadda ta gani, dafe ƙirji ta yi tana zama a kan gadon ta ji wani irin laushi ta kasa jurewa sai da ta ce "Tabɗijam! Lalle yarinya kin samu tsuntsu daga sama gasasshe, yanzu wannan daular duk ke kaɗai za ki zauna a cikin ta? Lalle Abban Salim mugun munafiki ne da yaƙi aura wa Yarima Yasmin ya aura masa wannan shashashar da halin su ɗaya da Abir." Tashi ta yi tana ta nazari sai zagaya ɗakin take carpet ɗin da ke mamale a ƙasan ɗakin kan shi abin kallo ne, wani kalar laushi gareshi ko a iya kan shi za ka iya kwanciya ka yi bacci. Jin ana faɗin ina take ta yi saurin ɗaukan mayafinta da ta aje a bakin gadon ta yo palo. Da kallo Mom Yasira ta bi ta tana jinjina tsaurin ido irin na Ammi ganin daga inda ta fito, ganin kallon da Mom Yasira take mata sai ta waske tana wani kawar da kai ta saki murmushi tare da cewa "Ɗakin amarya na gani ba ko'ina na je ba." Yasmin da ke tsaye tana kallon palon ta kalli Ammi ta ce "Ammi yana da kyau ko? Amma kuma ya aka yi ba ku mata jere ba na ga komai na ciki sabo ne?" Kwafa Ammi ta yi tana wayancewa ta ce "To ai dama tun da aka sa auren Abir da Yarima ya ce ba ya son su Abbanku su kawo ta komai ita kaɗai yake so, a matsayin ta na marainiya kuma wadda yake da burin zama da ita zai mata komai dan faranta mata rai, ashe ma ba ita ba ce matar tasa." Ta faɗa tana yin murmushi dan ta ga me su Mom Yasira za su ce. Banza suka mata sai matar Daddyn Aruf ce ta rausayar da kai ta ce " Allah sarki mai sunan Inna ko a wani hali take yanzu? " Sallama suka ji an yi suka amsa tare da kallon kofar, Ikilima ce ta shigo cikin shigar ta ta alfarma da ka gan ta sak Suhal sai dai shi ya fi ta fari. Fuska ba yabo ba fallasa ta iso tare da dan rusunawa ta ce "Sannun ku da zuwa baƙi, ina wadda ta yi wa Anty Princess kwacen Yayana?" Ta faɗa tana murmushi. Dam! Ƙirjin Iman ya buga ta runtse idanu tana karanto addu'ar samun nutsuwa, abin da take gudu kenan ta san dama ba lalle dangin Suhal su ƙaunace ta ba kamar yadda suke son Abir, saboda ita Abir in dai ka yi mu'amala da ita to tabbas dole ne ka ji ta shiga ranka saboda sanyin halin ta ga tausayi da girmama mutane. Tun da ta ga yadda su Kilishi ke mata kallon daga ina ta tsure ta shiga damuwa, ko ba a faɗa mata ba tasan ba za su taɓa zama lafiya da kishiyoyin surukar ta ba. Dogon numfashi ta ja tana ɗan ɗago kai ta kalli Ikilima ba ta ce komai ba. Murmushi Ikilima ta sakar mata tare da isa inda take ta kama hannunta, buɗe mayafin nata ta yi tare da cewa "Ki tashi muje Yaya ne yake son ganin ki, ya ce da kaina zan kaiki inda yake." Zazzaro idanu ta yi tana jin kamar ta kurma ihu ta tashi aljannun ƙarya dan kar ta je, amma ganin yadda Mom Nabila ke hararar ta ya sa ta saki fuska ta miƙe tsaye tare da gyara lulluɓin ta ta kalli Ikilima ta ce "To muje." Su dai su Ammi kallon su suke ba wanda ya ce musu ƙala har suka shige ɗakin da Ammi ta shiga. Da mamaki Ammi ke kallon inda suka shiga ta dafe ƙirji tana tunanin dama Yarima yana cikin ɗakin ta shiga? Ras ! Ta ji gabanta ya faɗi tuna kalmar da ta faɗa a ɗakin ta yi ƙasa da kai jin Jakadiya ta shigo tana nuna musu inda aka tanadar musu abinci na musamman.. Suna shiga ɗakin Iman ta yi ta mamakin ganin komai na ɗakin kalar na ɗakin Abir ne, kenan ta faɗa masa kalar yadda take so ɗakinta ya zama? Hawaye ta ji sun cika mata kwarmin idanu ta yi saurin mayar da su tana sauke numfashi. Wani waje Ikilima ta buɗe wanda a iya ganin mutum zai ce wardrobe ne, ƙofa ce a ciki ta kunna hasken wajan ko'ina ya gauraye da haske, ita dai Iman wani mugun tsoro ne ta ji ya sake shigar ta tana tunanin anya kuwa Suhal ba ɗan shan jini ba ne? Jiki na rawa Ikilima ta riƙe hannunta suka soma taka matakalar tana cewa "Ya sunan Antyn nawa." Baki na rawa ta ce "I.. Iman suna na." Riƙe baki Ikilima ta yi tana ta mamaki dama wannan ita ce Iman ɗin da suka taɓa gaisawa a wayar Abir? Ba Ta ce mata komai ba suk ci gaba da tafiya sai ga su a wani makeken palo mai ɗauke da dakuna uku har da kitchen, baki Iman ta saki tana kallon ko'ina har ba ta san ba lokacin da Ikilima ta yi wucewar ta ta bar ta tsaye a tsakiyar palon. Photon Suhal ne manne a jikin bangon palon ya sha ƙananan kaya ya hakimce a kan kujera fuskarsa ɗauke da murmushi abin da ya dauke mata hankali kenan ta shagala. A hankali ya iso cikin sanɗa ya biyo ta baya ya rufe mata idanu, a firgice ta soma ƙoƙarin kwacewa amma yaƙi ba ta damar hakan sai kawai ta fashe da kuka tare da cewa "Waiyo Allah Anty Baby ashe nan gidan masu shan jini ne aka kawoni?" Dariya ce ta so subce masa ganin yadda jikinta ke kyarma, a nutse ya sa ɗayan hannun ya ƙaraso da ita ya manne ta da jikinsa. Ajiyar zuciya ta sauke jin ɗumin jikinsa haɗi da ƙamshin turare wanda ta shaƙa lokacin da suka dira Kasar, kanshi ya kwanto a kafaɗarta yana shaƙar ƙamshin jikinta. Shuru ta yi tana jin zuciyarta na narkewa saboda yadda ta tsinci kanta a sabon yanayin da ba ta taɓa ji ba, sakin ta ya yi yana jan mumfashi ya juyo da ita suka yi facing ɗin juna tare da ɗago da fuskarta ya ƙura mata na mujiya.. Turo baki ta yi ganin yadda ya tsare ta da kallo, harara ta aika masa duk da tsoron da take ji ta kwace fuskarta tana riƙe ƙugu ta ce "Kai ni fa ƴar iska ba ce da kake wani shafe min jiki, anya ma kai ba ɗan mafiya ba ne?" Ta faɗa tana kaɗa ƙugu irin ba ta san rainin nan.. Murmushi ya yi yana kallon yadda ta turo baki ya lumshe idanu a kasale, matsalar auren kwaila kenan ba ta aje komai ba sai rashin kunya da son girma. Buɗe idanuwansa ya yi ya ɗan gyara tsayuwarsa ya ce "Ƴar kwailata." Haushi ne ya kama ta jin ya ce mata ƴar kwaila ta sake aiko masa harara, kwafa ta yi ta ce "Ni ce ma kwailar?" Ta faɗa tana nuna kanta.. Gira ɗaya ya ɗage mata alamar tabbatarwa, hanci ta shiga hurawa tana tsaye a gaban shi sai murmushi yake mata, sai da ta gaji da tsayuwar ta ɗan ɓata fuska ta ce "Kamar ba a san darajar baƙo ba an bar ni a tsaye, salon man ƙwafrina ya ƙame." Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Ai kin fi ƙarfin baƙuwa Imani nan duk naki ne ki shiga duk inda kike so babu wanda zai miki shamaki." Ya faɗa yana kama hannunta suka nufi ɗaya daga cikin ɗakunan. Tana saka ƙafa ta shaƙi wani ni'imtaccan ƙamshi mai kwantar da hankali ta ja numfashi tare da lumshe idanu, sosai ƙamshin ɗakin ya tafi da imaninta har ba ta san sun ƙaraso bakin gadon ba sai da ta ji ya zaunar da ita, saurin buɗe idanu ta yi tana murguɗa masa baki ta ce "Wa ya ce ka zaunar da ni?" Ta faɗa tana kafe shi da idanu. Bai kula ta ba ya wuce daga ɗakin, bai jima ba ya dawo da abinci mai rai da lafiya sai ƙamshi yake tashi, tsohuwar yunwar da take ji tun safe ta taso mata ganin abincin. Zama ya yi a kan carpet ɗin ɗakin ya dube ta tare da cewa "Sauko ki ci abinci." Ba ta musa ba ta sauko ta zauna a ɗan nesa da shi dan kar ma ya ce zai taɓa mata jiki ita kuma tsoro take ji, girgiza kai kawai ya yi sai ya tura mata abincin ya miƙe tsaye ya nufi can jikin gadon. Da wutsiyar ido take kallon shi dan ta ga me zai yi, da sauri ta mayar da kanta kasa tana gwalalo idanu waje ganin ya cire kayan jikinsa daga shi sai ƙaramin wando iya gwiwa, hannu ta kai ta dafe ƙirji tana jinjina rashin kunya irin ta Suhal wai yau a gaban ta yake cire kaya ko irin ya shiga toilet sai ya fidda a can.. Duk abin da take yana kallon ta ya yi murmushin sa wanda yake ƙara masa kyau ya shige toilet.. Da sauri ta shiga cin abinci dan ba ta so ya iso ya same ta tana ci, sai da ta gama tas ta janyo ruwan da ke cikin roba ƴar madaidaiciya wadda aka haɗo da abincin ta wanke hannu a ciki. Tana dauke hannu ya fito sanye da towel ɗan ƙarami a kan kafaɗarsa yana tsane ruwan jikinsa, ƙara tsorata ta yi har jikinta ya soma rawa amma ta daure ta ci gaba da zama. Sai da ya saka single da Gajeran wando sannan ya isa gaban mirrow ɗin da yake shaƙe da mayuka kala-kala kamar ɗakin mata, wani cream fari ya buɗe ya shiga shafe jikinsa da shi yana kare mata kallo ta madubi. Bayan ya gama ya iso inda take bai ce mata komai ba ya dauke kayan abincin ya fita, sai da ta soma jin tsoro ganin yaƙi dawowa sannan ta ji takun tafiyarsa, kamar wata soja haka ta ƙame tana son ya shigo ta ce ya mayar da ita wajan su Mom Yasira. Tun daga kan yatsun ƙafafuwansa ta soma kallon shi har zuwa kan fuskarsa da take ba yabo ba fallasa, kawar da kai ta yi ya yi murmushi ya ce "Tashi muje na miki wanka." Kwalalo idanu waje ta yi dariya ta kama shi amma ya basar yana ƙara cewa "OK to na gane tashi ki je ki yi da kanki." Ya faɗa yana nuna mata hanyar toilet. Harara ta aiko masa, in ban da ma ya raina ta ita zai kalla ya ce zai yi wa wanka? Salon ya kalle mata jiki dan ba shi da kunya, kwafa ta yi tana hura hanci ta shige toilet ɗin shi kuma ya zo bakin gado ya zauna... Wayarsa ya buɗe sai ka sakonnin Abir suna ta shigowa har da kira, dafe kai ya yi yana jin zuciyarsa na masa ƙuna da raɗaɗi irin na rabuwa da masoyi, da kyar ya buɗe saƙon nata inda ta masa dogon rubutu ya soma dubawa gaban shi na dukan uku-uku, ba ya so Abir ta kalle shi a matsayin ma ci amana alhali shi daga gareshi ba hakan ba ne.. _"Assalam alaikum, Yaya Suhal ina fatan kana lafiya dai ko? To Alhamdu Lillah. Yaya Suhal na ga abin da ya faru kuma na yi imani da Allah cewar kai ɗin ba ba ne mijina, ina so mu ɗauki haka a matsayin ƙaddara daga Allah, sannan don girman Allah Yaya Suhal ka riƙe min ƴar'uwata da amana, idan har ka cutar da ita to tamkar ni ce ka cutar hakan kuma zai azabtar da zuciya da gangar jikina, ga amanar Iman nan ka yi haƙuri da duk abin da za ta yi ma saboda abin ne ya mata girma, da farko ta tubure amma daga ƙarshe ta yi haƙuri ta rungumi kaddara. Ina muku fatan alkhairi Allah ya ba da zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba baɗi muje bikin suna bissalam."_ Lumshe idanu ya yi yana jin kamar ya ce ya fasa auren Iman, amma in ya yi wani tunani sai ya ga gara ya rungumi ƙaddara domin yi wa wadda ke son shi da gaskiya halacci, gabadaya ji yake komai ya masa zafi dauriya kawai yake ba ƙaramin azabtuwa yake da wannan gagarumin aikin da ya daukar wa kansa akan masoyiyarsa.. Tashi ya yi ya dauko mata kayan bacci masu kyau green color masu ya aje mata bakin gadon sannan ya fita. Leƙowa ta yi ta ga ba ta gan shi ba ta fito daure da towel fari sol, da mamaki ta kalli kayan da ya aje mata tana tunanin to ita yaushe aka zo har aka kawo mata tufafi? Jinjina kai ta yi tuna maganar su Ammi zuciyarta ta karye tuna Abir hawaye suka zubo mata ta sa hannu ta goge, kayan ta dauka tana juyawa ganin riga da wando ce wandon iya gwiwa ne rigar kuma ko cibiya ba za ta kai mata ba. Zama ta yi tana jan tsaki ita zai raina wa hankali ya ba ta kayan 'yan iska irin wanda ya gani a Turai? Ganin dai babu sarki sai Allah ya sa ta miƙe ta isa gaban mirrow ɗin ta dauki man da ya shafa itama ta shafe jikinta da shi sannan ta sa kayan. Bakin gado ta dawo ta rafka tagumi tana jiran ya dawo ta tafi burin ta ya mayar da ita wajan su Mom Nabila amma kamar an aiki bawa garinsu, da haka dai bacci ya dauke ta sai asuba ta farka.. Washegari misalin karfe 8:am ya zo ya tayar da ita taƙi tashi ai kuwa ya sunkuce ta ya kai ta toilet, ba ta ankare ba ta ji ta a ruwan ɗumi ta buɗe idanu da sauri tana waiga ko'ina sai ganin ta ta yi a toilet. Zaro idanu ta yi tana kare jikinta ya yi murmushi shi dariya kawai take ba shi in ta yi wani abin, bai jira komai ba ya saɓe ta da soso da sabulu ita kuma ta kulle idanuwanta tana kuka wiwi kamar wadda ake zanewa. Bayan ya gama mata da kan shi ya dauko ta suka fito ya canja mata kaya ya shirya ta cikin riga da sket dinkin shadda, cewa ya yi ta yi Sallah ta ce masa ai akan kunnenta aka kira Sallah tana maganar tana murguɗa baki har ta kai karshe. Girgiza kai ya yi ya janyo hannunta suka fito palo inda suka tarar an gama shirya musu kayan kari masu rai da lafiya, da kyar ta ci kaɗan tana cewa ya kaita wajan 'yan'uwanta. Suna gamawa ya fito da ita zuwa wajan su Ammi suka gaisa ya fita ya bar ta.. Sai wajan karfe goma aka shirya gagarumar walima a wani babban ɗakin taro da ke cikin masarautar, su Mom sun ga manyan mata hamshaƙai masu ji da izzar sarauta da kuɗi kowacce in ka gan ta sai ka rantse gasar kyau za ta je.. Bayan an tashi suka mata nasiha saboda gida za su dawo ai kuwa ta yi tsalle ta dire ta ce tare za su koma, da kyar da lallami aka samu ta kyale amma ta ce tafiya ba fashi babu wanda zai bar ta a wannan babbar masarautar da babu wanda ta sani, abin ya ishi su Mom Nabila ta kira Umma ta ba ta wayar ta rarrashe ta amma ta ce ita fa Wallahi ko ana muzuru ana shaho sai ta koma Nigeria ba mai barin ta a nan. Ƙarshe dai su Abba suka yi ta mata nasiha amma taƙi ji sai kuka take kamar ranta zai fita, dubara ta faɗo wa Umma ta sa aka kira Abir ta ce ta je ta mata magana ta ce sai ta dawo da su Ammi. Abir da sauri ta koma part ɗin su ta kira Mom Nabila ta ce a ba ta Iman, tana amsa ta fashe da kuka ta ce "Ni gaskiya Anty Baby ba zan zauna a nan ba zan bi su mu koma Nigeria, Wallahi ban san kowa ba ni dai ki ce wa Abba ya sa Yaya Suhal ya sakeni mu koma gida." Dafe kai Abir ta yi saboda itama ba ta daɗe da gama kukan rashin masoyinta ba kanta ya mata nauyi sai sara mata yake, ajiyar zuciya ta sauke ta ce "Ashe bakya sona Iman? Na dauka duk gidanmu ke ce wacce kika fi kowa so na ashe ba haka ba ne?" Saurin tsayar da kukan Iman ta yi ta miƙe tsaye ta ce "Wallahi Anty ina son ki mana." "To in dai har da gaske ki na so na me ya sa ba za ki Ƙaunaci wanda yake so na ba? Ki yi hakuri ki zauna da kin yi wata biyar ko shida zai kawo ki ganin gida. " Fashewa da kuka ta yi har da dira ƙafa ta ce "Wata shida kuma Anty Baby? Ina lefin sati ɗaya ma." Ta faɗa tana zama kan kujera. Dariyar yaƙe ta yi ta ce "Sati fa? To shi kenan zan masa magana da kin cika sati ya kawo ki ganin gida." Ta faɗa tana jinjina shirme irin na Iman. Wani sanyi Iman ta ji sai ta kyalkyace da dariya tana rufe fuska ta ce "To na yarda zan zauna." Itama dariyar ganin ta shayo kan ta ta yi, nan suka yi sallama tana ƙara jadadda wa Abir daga sati fa ba za ta sake kwana a Niamey ba ta ce mata to sannan ta kashe wayar.. Riƙe baki Mom Yasira ta yi ta ce " 'Yan'uwa jini da hanta to mu za mu wuce." Rufe fuska ta yi tana dariya tana ɗaga musu hannu har suka fita daga palon, da sauri ta biyo su inda ta samu suna yi wa Mamma sallama suka wuce ita kuma ta shiga gaishe da Mamma, alama ta mata da ta zo ta zauna ba muso ta zauna a gefen Mamma suka kama hira ita da Ikilima... _NIGERIA_ Tana aje wayar magani ta ɓalla ta sha ta fito palo ta zauna zaman jiran zuwan su Mom Yasira.. Sai La'asar sakaliya suka iso gida aka hau ba da labarin Iman da yadda ta birkice Abir nata murmushi, ko ba komai ta ji daɗi tun da Iman ta yarda ta zauna.... Bayan an yi biki da sati biyu Abir ta shirya ta tafi gidan Baba dan ganin Zaiyan. Kamar kullum a zaune ta same shi yana ta yin gidan ƙasa ya kwaɓa taɓo yana yaɓe ɗakunan da ya yi, ganin ita ce sai ya tsuke fuska ya ce "Na daina miki magana." Lumshe idanu ta yi tana jin zafin zuciyarta na sauka, a hankali ta isa gaban ɗakunan ƙasar da ya yi ta aje handbag ɗinta ta ce "Ni ma zan yi wasan." Ta faɗa a shagaɓe tana turo baki kamar yadda ya yi.. Hannu ya kai ya yaɓa mata taɓon da ya gama kwaɓawa a kumatunta yana dariya, ɗayan kuncin ya kuma sa mata taɓon yana dariya tare da cewa "Wannan faudar za ta miki kyau Anty, cire ɗankwalin na miki wankin kai." Kafin ta yi magana tuni ya cire mata hular da ke kanta ya kwaso taɓon hannu bibiyu ya zuba mata a cikin lallausan gashinta da ya sha gyara baƙi siɗik sai sheƙi yake yi, sai da ya gama daddaɓa mata taɓon duk tana kallon shi kuma ta kasa tsayar da shi, miƙewa ya yi ya buɗe rigar shi zariyar wandonsa ya kunce ya zare zariyar ya ɗaura mata a kan yana murmushi. Ita dai Abir kamar an dasa ta haka ta yi kawai ji ta yi ba za ta iya ce masa komai ba, zama ya yi yana sake kwaɓa wani taɓon mai yawa, bayan ya kwaɓa ya dube ta da ta kafe shi da idanu sai ya ɓata rai ya ce "Kallon ki irin na Maman abokina ne sai na daure mata hannu ma in tana kallo na." Murmushi kawai ta yi ya janyo kwanon da ya kwaɓa taɓon ya ce "Kawo ayi miki lalle irin na Inna ki yi kyau." Ya faɗa yana miƙa mata hannu tare da nuna mata ƙafarta. Dariya ta yi kamar wacce aka yi wa wahayi ta miƙa masa ƙafarta da ta sha kunshi ja da baki na amarci, kama ƙafar ya yi har da gyara zama ya soma yi wa ƙafar wankan taɓo kamar yadda tsofaffi ke yi ya shirɓine mata ƙafar har ƙwafrin duk ya yayyaɓe su, ƙafar ɗaya ya kama ya mata irin na ɗayar har da huci yake irin na wanda ya daɗe a tsaye yana aiki. Bayan ya gama sai gani ta yi ya warci hannunta ya yaɓe shi duka, tashi ya yi zaune ya ɗaga kwanon taɓon ya ƙarasa kwarara mata a kai har da sa hannu ya goga a inda bai samu ba... Kallon yadda ta yi wani iri kamar wata mai ciwon daji sai kawai ta fashe da dariya, shi ma dariyar ya yi yana zama a gaban ta ya ce "Anty ina son ki." A wani kalar zabure ta kalle shi, duk da ta san ba wani abin mamaki ba ne jin Kalmar saboda ya saba faɗa mata, amma a wannan karon ji ta yi ta bambanta da sauran lokutan da yake sanar da ita yana son ta... Baba da Inna ne suka fito suka gan su a haka ta kafe shi da kallo, dariya Inna ta yi ganin yadda aka mata wankan taɓo, shi ma kan shi Baba dariya ya yi hakan ya sa ta yi saurin kallon su, dariyar da suke mata ta sa ta ji kuka ya zo mata kawai ta ɓare baki ta fashe da kuka wiwi. A rude Zaiyan ya kalle ta yana ta cewa "Anty waye ya dake ki?" Ganin taki ba shi amsa sai kawai shi ma ya zauna ya yi tashe-tashe ya shiga rero kuka, ai kuwa me su Baba za su yi in ba dariya ba Inna har da riƙe ciki.... _Maman Nusaiba ce_ [6/20, 8:43 PM] Ummu Amjad: ~A HAKA NAKE SON SHI~ *No editing* Shafi na (33) Tsayar da dariyar Inna ta yi ta nufo su ganin yadda suke kallon juna kowa sai kuka yake kamar wasu yaran goye, tana isowa Zaiyan ya kalle ta yana goge hawaye y ce "Inna kin gani ko Anty tana kuka, ko Baba ne ya ce zai sace ta irin na jiya?" Ya faɗa yana kallon Inna da take ƙoƙarin gumtse dariyarta. Baba ne ya iso ya dubi Abir da zuwa yanzu ta daina kukan sai kallon su da take ya ce "Hauwa'u me ya faru kike kuka wai?" Kallon jikinta ta yi ta dawo da kallon ta kan Zaiyan sai kawai ta sake rushewa da kuka jikinta ya yi sharkaf da zufa ga taɓon da ya yaɓe mata duk ta ji jikinta ya yi wani kalar, dariya Inna ta kuma yi tana cewa "Ke yanzu kuka ba ya miki wahala Abir? Yanzu Zaiyan ɗin n kike yi wa kuka sai ka ce kin samu wani nutsastse? To tashi ki je ki wanke jikin naki kar kayan jikin ki su lalace." Ta faɗa tana nuna mata famfon da ke can gefen su. Girgiza kai Baba ya yi ya ce. "Ɓata jiki kuma na nawa? Ba ki ga har kanta ya wanke mata da taɓon ba? " Sai lokacin Inna ta kalli kan da kyau ta ga shi ma an masa wankan, riƙe baki ta yi ta maka hannun Abir ta miƙar da ita tsaye, ita kuwa kallon Zaiyan ta yi da ya mike kamar an tsikare shi suka hada idanu ta harare shi tare da cewa "Mun ɓata da kai." Tana faɗin haka ta yi gaba zuwa bakin fomfon. Turo baki ya yi yana kifkifta idanu irin na yaron da ya yi lefi ya bi bayan su, Baba ya koma ciki dan dama leƙo Zaiyan n suka yi su ga ko yana inda yake. Sai da ta fara wanke hannuwanta da ƙafafu sannan ta sunkuya Inna ta janyo maisar da ake ba wa shukokin wajan ruwa ta jona ta dinga duba mata ruwan ita kuma tana wankewa, sosai ta jigata saboda ƙasar ta daddaɓe a can ƙasar kanta sai da Inna ta dinga tayata sannan ya wanko. Ta jiƙa kayanta sai hararar Zaiyan take da matso kusa da ita hannunsa duk taɓo ne haka ma kayan jikinsa sabbi ne kar amma ya lalata su da taɓo, gashin ta kama ta matse ruwan yana zubewa ta ɗago ta kalle shi yana ta juye-juye kamar mai yin training. Inna ta ce "To yanzu ki shiga ciki ki yi wanka dan wannan kayan naki sai dai ki fidda sun jiƙe." Ta faɗa tare da wucewa ciki ta bar su a nan tsaye ita da shi. "Anty ni ma ki wanke min irin naki." Ya faɗa yana nuna mata jikinsa. Lumshe idanu ta yi jin yadda sanyi ke shigar ta kaɗan-kaɗan, bude idanu ta yi ta sauke su a kan shi ya tsayar kamar yadda yaro ke tsayawa a gaban mamansa in yana son wani abu, girgiza kai ta yi ta ce "Ba kai ka ɓata min jiki ba naki na wanke ma ɗin." Ta faɗa tana hade fuska. Baki ya riƙe yana daga kai sama zuwa can dai ya ce "Zan saya miki wani kayan fa." Maisar ta dauko ta nuna masa ya tsugunna ta wanke masa, bi musa ba ya tsugunna ta wanke masa kai da ƙafafu sannan ta ce y tashi su shiga ciki ya yi wanka, da sauri ya tashi ya kama hannunta suka shige ciki. A palo suka samu Inna ta yi wa Zaiyan dubara ta shige toilet shi ma Baba ya lallaba shi ya shigar da shi toilet, bayan ta gama wankan Inna ta dauko mata zani ta yi ɗaurin kirji ta fito da shi sai a lokacin ta yi tunanin wani kaya za ta saka? Dafe kai ta yi ta zauna a bakin gadon Inna sai ga ta Inna ta shigo da kaya a hannunta, miƙa mata ta yi tare da cewa "Ungu ki sa wannan na ga ku 'yan zamani ne kayan maza ma sakawa kuke, wannan na Zaiyan ne a cikin wanda kika sayo masa ne na ga ya yi kama da na mata na ce bari na kawo miki ki sa." Murmushi ta yi tana amsar kayan ta daga su tana gani, riga da wando ne rigar mai haɗe da hula ce wando kuma dogo hakan ya mata, tashi tsaye ta yi ta ce "To Inna na gode bari na to." Fita Inna ta yi ita kuma ta saka kayan ta ga wadon ya mata tsaye rigar ma ta mata yawa kasancewar ya fita tsawo sosai, murmushi kawai take in ta kalli kayan da ranar da ta kawo masa su a ranar ya sa su yana murna. Bayan ta sa ta fito palo inda ta samu Zaiyan ya tubure yana ta cewa ina Antynsa take? Ƴar dariya ta yi ta ƙaraso tare da cewa "Gani fa babu inda na tafi." Murmushi ta ga ya yi ya iso inda take tsaye ya kama hannunta yana jan ta y ce "Zo muje na ciro miki mangwaro Anty." Bin sa ta yi suka fito harabar, bishiyar mangwaro ya hau ya tsinko mata guda uku manta nunannu sannan ya sauko ya zauna a gindin bishiyar ya ce "Anty zo ki sha." Ya faɗa yana kai wa bakinsa. Da sauri ta amshe tana faɗin "Bari na wanke sai ka sha." Ta wanke su yana tsaye a gefen ta ta miƙa masa ɗaya suka dawo suka zauna yana sha yana ta zuba mata shirme, ta wuni a gidan ita da Zaiyan suna harabar gidan suna ta wasanni sai yamma ta tafi gida.. Umma ta dawo wajan Malam ta ta zayyano masa yadda komai na auren Abir ya kasance har ya dawo kan Iman ta ɗora da cewa "Amma Malam ai ba haka muka yi da kai ba ko? 'yata babbar ita zai aura amma na ga saɓanin haka, ko dai wani abu na yi wanda ya saɓawa dokar aikin?" Ta faɗa tana mai rausayar da kai. Zane Malam ya yi a kan ƙasar da take gabansa, bayan ya gama ya ɗago ya gyara zama yana kallon Umma ya ce "Hajiya ai ni aikina yana ci sosai, ina tunanin dai da sunan karamar ne aka yi aikin shi y sa hakan ta faru." Nisawa ta yi ta zarga handbag ɗinta ta dauki daurin 'yan rafa ta dire masa a gaban shi, jinjina kai take tana murmushi ta ce "To duk ba matsala Malam hakan ma dai ya yi daidai tun da itama wadda ya aurar ɗiyata ce, yanzu ga wannan ina son a kashe ta kawai kowa ma ya huta." Da hanzari Malam ya dauke kuɗin ya zuba su a lajihun babbar rigarsa ya gyara rawanin kansa ya ce "Na faɗa miki tun zuwan ki shekarun baya ba zai yiyuba a kashe ta, amma yanzu za a iya haukatar da ita ko a sa kowa ya ƙyamace ta da haka baƙin ciki ya kashe ta." Ya faɗa miƙa hannu gefensa ya dauko wata leda ya miƙa mata, amsa ta yi ya ce "Wannan duk ta yadda za ayi ki turara mata shi ta shaki hayaƙin." Kwalalo idanu waje Umma ta yi tana juya ganin ta ce. "To ai Malam cutar asma gare ta in ta shaki hayaƙi ciwon zai iy tashi, ni kuma bana son kowa ya gano abin da nake so nake komai ya tafi cikin tsari ba tare da kowa ya nakara ba." Shuri Malam y yi sai kum ya saki murmushi ya ce. "To shi kenan ki bari za mu yi aikin da kan mu, sannan ina ƙara jaddada miki kar ki bari a gano wannan ajiyar tamu." Jinjina kai ta yi ya amshe maganin ya b ta wani ya ce "Ki zuba mata a cikin abinci in ta ci za ki ga abin da zai faru." Da murna Umma ta amsa ta tafi.. Haka kullum Abir ke tafiya gidan su Baba su wuni suna ta shawayi a harabar gidan, hakan na ƙara mantar da ita duk wata damuwa da take ciki. A cikin watanni 5 ta ƙara shaƙuwa da Zaiyan fiye da misali ba ta iya wuni sai ta gan shi, wani abu dake samun ta rashin samun kulawar Yayan nata da har da Grandma duk kowa ya ja baya da ita ba mai cewa ya ta tashi ko mai ta ci, haka kullum za ta yi ta kiran Abdul a waya amma yaƙi dauka in ta kira Hafsat ta tambaye ta ko ina yake dai ta ce mata ai yana nan, wannan abu ba ƙaramin ƙona mata rai yake ba ga shi ta rasa wa za ta faɗawa ta ji sanyi a zuciyarta. Yau dai ta shirya cikin shigar ta ta abaya Arabian gown ta ɗan sa kwalli ta fito tana danna wa Ali kira, yana dauka ta ce masa ya zo ya kai ta gidan Abdul ya ce ga shi nan zuwa. Umma ce ta kutso kan motarta harabar gidan Abir ta bi ta da kallo, tana fitowa Abir ta saki ranta tana murmushi ta ce "Umma sannu ko biki ake ne?" Dariyar Allah sarki ta mata tana wayamcewa ta iso inda take, kallon ta take sama da ƙasa abin da ya bai wa Abir mamaki har za ta yi magana sai ta tsinkayo muryar Umma na cewa "Abir anya kuwa kina lafiya? Yau an fi sati ina zuwa part ɗin ku dan na kira ki Iman sai damuna take kin ƙi ɗaukan kiran ta in ta kira ki, ina fatan dai ba gama kike yi wa ƴar kanwar taki ba." Ta faɗa tana yin shu'umin murmushi tare da dafa ta tana shafa kafaɗarta. Nisawa Abir ta yi cikin tsananin damuwa ta ɗago ta kalli Umma idanuwanta har sun cika da kwalla, murmushi Umma ta kuma yi tana mata wani irin kallo wanda ita kadai ta bar wa kanta sani. Sunkuyar da kai ta yi sannan ta ce "Umma Wallahi ba gaba nake da Iman ba, abin da ya sa na daina ɗaukan kiran ta in ta kira sai dai ta tasa ni gaba tana min kuka wai sai na sa Yarima ya kawo ta Nigeria, hakan ya sa na daina ɗaukan kiran ta dan na yi ta ba ta hakuri ta daina maganar zuwa Nigeria tun da mijinta ba ya son kawo ta yanzu, amma fir ta kafe har kwana hudu ta yi a ɗaki ta rufe kanta ba ta fitowa waje za ta kashe kanta dan ya ce ta bari ba yanzu ba." Zaro idanu Umma ta yi cike da ganin wautar Iman ta ce "Wai Iman ɗin ce ta yi haka? Wallahi sai na ci mutumcin ta tun da mu take so ta mayar ƙananan mutane, ba ta gidan sarauta komai na gulma da tsugudidi ba ne? Ke rabu da ita sai na ci ubanta tabbas, yanzu yaushe ne ta yi hakan za ta kashe kanta?" Ta faɗa tana jin da Iman a kusa da ita take to tabbas babu abin da zai hana ta zane ta, saboda yadda take son ruguza mata burin da ta ci akan ta.. Ajiyar zuciya ta sauke ganin yadda Umma ke sababi ta ɗan tausayar da kai ta ce "Wallahi Umma Iman sai dai ki mata addu'a ta kafe akan ita lalle ba ta son Yarima tun da auren cin amana ne aka mata, na nuna mata babu wata cin amana ta kwantar da hankalinta amma taƙi, yau Ikilima ta kirani take sanar da ni Iman ba lafiya ana mata karin ruwa duk ta rama saboda ko abinci ba ta ci ta rufe kan ta a ɗaki, hankalina ya tashi da naji haka na ce yaushe hakan ta faru? Ta ce min yau ne ta je sai Yarima ke sanar da ita halin da suke ciki ita da shi a gidan, to da kyar dai ta sidin Goshi ta yarda ta bude mata kofa inda tana budewa ta suma a bakin kofar. Amma don Allah Umma kar ki mata faɗa dayawa ki bata mata rai kuma ta yi abin da ya fi haka ma, ki mata nasiha kawai da addu'a kin ga yarinya ce har yanzu 16 gareta ba za ta yi wani dogon tunani ba in za ta aikata wani abin." Ta karashe maganar tana gyara zama Jakarta bisa kafaɗa.. Gyada kai kawai Umma ke yi, wato ma ita Iman za ta kunyata ta je garin shirme ya sako mata ita duk wani alwashin da ta ci ya tashi a banza? Kwafa ta yi ta ce "OK Abir ba komai zan mata nasihar, yanzu ke ina za ki fita da ranar nan?" Murmushi ta yi ta ce "Gidan Yaya zan je ga ma Ali nan y iso." OK kawai Umma ta ce ta yi gaba tana sauri kamar za ta tashi sama. Da kallo ta bi bayan Umma har ta shige part ɗinta, fuska dauke da jimami ta nufi mota ta shiga saboda tana tsoron kar Umma ta yi wa Iman tas kuma ta ɓata mata shirin da take yi.. Tun kafin su je gidan take kiran Abdul dan ta sanar da shi za ta je gidansa amma yaki ɗaukan kiran, hawayen da suka cika mata kwarmin idanu suka zubo, wannan wani irin wulakanci ne kamar ita yau Abdul yake sharewa kamar bai ma san ta ba a rayuwarsa. Hannu ta kai ta goge hawayen a daidai lokacin da Ali ya yi hon aka bude msa get, yana gama packing ta masa godiya ta nufi ciki. Nocking ta yi inda ta ji muryar Hafsat tana cewa "Waye?" Sai da ta yi magana Hafsat ta ji muryarta sannan ta bude kofar suka rungume juna cike da farin cikin ganin juna, Hafsat ta bata rai ta ce "Besty Wallahi na yi fushi da ke, ace aurena 5 month's amma ki kasa zuwa gidana kamar na yi miki wani mugun abu?" Murmushi Abir ta yi ta gyara zama tana kallon palon yadda ya tsaru ga photon Hafsat da Abdul nan sun hada goshi tare lumshe idanu aka dauke su, dariya ta yi ta ce "Oh ni Hauwa'u! Hafsy ku ne love wannan style na photo haka kamar a turai?" Ta faɗa tana kallon kofar da ake ƙoƙarin budewa. Farr Hafsat ta yi da idanu sai kuma ta ɗan yi fuskar jimami ta ce "Allah sarki ƙawata, yanzu kema fa da ki na can a gidan sarauta." Ta faɗa itama tana kallon Abdul da ya yi tsaye a bakin kofa yana kare musu kallo. Kawar da kai Abir ta yi tana jin zafi da raɗaɗin ciwon son Suhal ya motsa mata ga kuma Abdul da ya yasar da ita kamar ba shi ba ne Mom ta kama hannunta ta damka a nasa ta ce ya kula da ita. Saurin saita kan ta yi jin Hafsat na yi wa Abdul Welcome back, ba ta CE masa ko uffan ba kamar yadda shi ma da kallo kawai yake bin ta kamar ya ga wata sabuwar halitta, kwafa ta yi ta kalli Hafsat da ta maƙale a jikinsa tana ce masa wanka zai yi ko abinci zai ci shi kuma ya wani girgiza kai ya ce takardu ya zo ɗauka an jima zai dawo. Dawowa wajan Abir ta yi tana ba ta hakuri ta bar ta ko ruwa ba ta kawo mata ba, murmushi ta yi kawai ba ta ce komai ba, sosai ranta ya sosu ganin Abdul da gaske ya wuce bai ko kalle ta ba duk da Hafsat ta ce ma Abir ta zo amma ya share maganar. A sanyaye ta dauki ruwan da Hafsat ta kawo mata ta sha kaɗan sannan ta mike tsaye tare da ɗaukan handbag ɗin ta ta ce "To ni zan tafi dan dama ba zama na zo yi zan koma gida ina so na yi bacci kafin ayi Azuhar." Sake da baki Hafsat ke kallon ta sai kuma ta haɗe rai ta ce "Haba Besty kamar ana korar ki daga zuwa ki ce za ki tafi? Ki bari mana sai yamma kin ga yayanki zai koma office sai ni kadai a gidan. Amma jira ni ina zuwa minti biyu." Ta faɗa tana yin bedroom ɗin ta da sauri. Tana shiga suka yi kiciɓus da Abdul zai fito, harara ta aika masa ta ce "My love wai kai da Besty me ke faruwa a tsakanin ku? Me ta yi maka haka da zafi da har ka gan ta ka yi kamar ba ka san da mutum a palo ba? Gaskiya I'm not happy with that mood, wannan dai ba halinka ba ne yin haka. Sam ban ji daɗin ganin hakan ba a tare da kai, kai ne fa uban ta kuma dangin mahaifiyarta a ma cire dangin uba, ya kake so ta yi da damuwar da ke damun ta ko da yadda ka mayar da ita shara?" Sai da ta gama maganar ya wani hade girar sama da ƙasa ya gyara tsayawa kamar yana filin daga, sai da ya shafa kwantaccan sajansa sannan ya ce "Oh my sweet ki rabu da Baby tun da haka ta zaɓar wa kanta rayuwa, ko irin ta kirani ba ta yi yanzu wata nawa da auren mu amma taƙi zuwa gidana sai yau ta ga dama ta zo? In kin gama matsa ki ba ni waje zan wuce ina makara." Ya faɗa yana son raɓa ta zai wuce ta sha gaban shi tana haɗe fuska.. Abir da ke tsaye palo tana jiyo tashin muryar Hafsat dan haka komai a kan kunnenta suka faɗa, wasu hawaye masu ɗumi ne suka silalo kan kuncinta ta sa hannu ta goge ta ɗaga ƙafa za ta yi gaba ta yi mutum a kusa da ita, da sauri ta matsa tare da ɗagowa ta kalle shi. Kama hnnunta ya yi fuskar nan ba alamar annuri ya ce "Wa ya ba ki izinin zuwar mini gida? Saboda kin rainani shi ya sa kike abin da ki ka ga dama ko?, To muje na sauke ki a gida shashasha kawai." Ya faɗa yana jan hannunta Hafsat na masa magana amma bai ji ba ya wuce da ita. Kuka Abir ta sa tana jin duniyar ta mata zafi, wai yau ita Abdul ke kora daga gidansa? A mota ya saka ta bai ko kalle ta ba ya ja suka bai gidan, sai da suka isa gida ya juyo ya yana kallon ta a fusace ya ce "Za ki yi shuru ko sai na kifa miki mari?" Saurin rufe bakinta da hannu ta yi tana zubar da hawaye, so take ta fita amma ya sa lock dole ta hakura ta na sauraron fadan da yake mata na ba gaira ba dalili, sai da ya gama yi mata rashin mutumci sannan ya buɗe mata ta fita tana goge kwalla ta shige ciki shi kuma a zafafe y bar gidan yana ji kamar ya mata duba... _NIGER_ Bayan Sallar isha'i Yarima Suhal ya shigo ɗakin Iman ya samu ba ta nan, zama ya yi a bakin gadon yana mamakin inda ta je tun da bai gan ta a wajan su Mamma ba, wayarta da ke ringing ya hanga a tsakiyar gadon ya kai hannu ya dauka. Ganin an saka Umma a number sai ya yi picking up call ɗin tare da karawa a kunne, kafin ma y yi magana ya ji Umma ta soma masifa.. "Iman ni za ki tonawa asiri a family Maitama? Wallahi zan saɓa miki yadda bakya tunani in na sake ji ko gani kin takurawa Abir sai ta yi wa mijinki magana ya kawo ki gida, uban me za ki yi a gidan in kin zo? Ki fita idanuna kafin na hada ki da Daddynku in ya dawo. In ban da ke sakarya ce a aura miki miji nagartacce mai hankali ga mulki amma kike cewa ke wai an miki auren cin amana uban wa kika ci amanar? Ki ci gaba da shashancin kika sake ki ka fusata mijinki ya koro ki to ki nemi wata uwar b dai ni ba dan banki. Ina magana kin yi shuru kin kyale ni wato ga mahaukaciya na yi ta haukana ni kadai ko? " Murmushi Suhal ya yi yana kaɗa kai ya ce "Umma barka da dare, ba fa Iman ba ce ta dan fita ta bar wayar ne a ɗaki, sannan ki daina damuwa da duk abin da take za ta daina in ta yi hankali." Kwalalo waje Umma ta yi tana dafe ƙirji, hamdala ta yi da duk maganar da ta faɗa babu mai aibu a ciki, hakan ya sa ta ɗan yi murmushi ta ce "Haba Yarima yanzu kamar kai ta tasa ka gaba tana ma rashin kunya ai wannan ba tarbiyar da muka ba ta ba ce." "Ihum Umma kenan, ai kar ki wani damu da lamarin Iman za ta fasa soon in sha Allah, sai da safe." Ya faɗa yana katse kiran; ƙin aje wayar ya yi ya shiga whatsapp inda ya shiga number Abir ya ga yadda take danne voice tana kuka take cewa ta yi masa magana ita a mayar da ita gida, murmushi ya yi ya kunna voice ɗin Abir inda take ta ba ta haƙuri tana nuna mata ta bi umarnin mijinta. Wani abu ne ya tsaya masa a zuciya jin muryar Abir ciwon so ya motsa mishi a hankali ya buɗe na Iman, nan ya ji tana faɗin ita fa a daina haɗa ta da Yarima Suhal ita wannan auren cin amanar ba za ta lamunta ba dole ya sake ta ya auri Abir, emoji ɗin dariya da dafe goshi ya ga Abir ta turo mata.. Fita ya yi daga whatsapp ɗin jin ana ƙoƙarin buɗe ƙofar banɗaki. Kanta a ƙasa ta ƙaraso bakin wardrobe ɗin ta buɗe ta soma tsaɓar kayan da za ta saka, kusan duk wani ɗabi'u nata irin na Abir ne musamman wajan saka kaya in sun fito daga wanka su dinga ruwan idon wani kalar kaya za su saka, harɗe hannu Suhal ya yi yana kallon ta yana murmushi in ta yi wani abin sai ya ga kamar yana tare da princess ɗin sa.. Haka ta yi ta birkito kayan tana jan tsaki har da kama ƙugu, sai can ta zaɓi wata riga iya gwiwa mai laushi da hular ta, murmushi ta yi ganin kalar kayan da Abir ɗin ne ke so ta cire towel ɗin kan ta cire na jiki dan ta sa kayan ko mai ba ta shafa fa, kamar an ce ta kalli madubin da ke manne jikin wardrobe ɗin ta ga mutum ya kafe ta da idanu ba ko ƙiftawa, ƙara ta kwalla tana zubewa a ƙasa. A zabure ya sauko daga kan gadon ya yo inda take durkushe tana kurma ihun kuma jikinta na rawa ta ma kasa ɗaukan towel ɗin ta ɗaura duk ta kiɗime, sunkuyawa ya yi a ruɗe yana faɗin "Iman lafiya? Ko wani abu ya same ki?" Zabura ta yi ta yi baya jikinta ya dauki rawa ta yi baya za ta buga kanta da jikin gado ya yi saurin taro ta, kuka ta sa tana faɗin "M.... Maman Nusaiba ce🤏🏻😎 [11/13, 11:34 Yamma] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): ~A HAKA NAKE SON SHI~ Shafi na (34) "Me ya kawo ka ɗakina?" Ta faɗa tana runtse idanu da ƙarfi tare sake sakin kuka ta cigaba da cewa "Ni ka tafi ka ba ni guri ko kunya ba ka ji kake kalle min jiki." Nannauyar ajiyar ya sauke ganin ba rauni ko buga jikinta da wani wajan ta yi ba kawai dan ta gan shi take wannan ihun, zama ya yi a kan gado ya miƙa hannu ya ɗago ta tana zillewa tare da kai masa duka a duk inda hannunta ya kai, shi ko dariya yake mata ƙasa-ƙasa dan kar ta ji ya ƙara yin lefi, a nutse ya ɗago da fuskarta ya kai bakinsa ya sumbace ta a goshi ai kuwa ta kwalla ƙara tana fadin "Ni fa ba ƴar iska ba ce irin ka, Wallahi zan faɗawa Anty Baby kana nuna min iskanci." Ta faɗa tana turo baki. Hannu ya sa ya matse bakin nata ta shiga mutsu-mutsun kwacewa jin wani zafi ya kawo mata ziyara amma ta kasa saboda ta ko'ina ya riƙe ta gam, daina motsi ta yi ta bude idanuwanta a kan shi suka hada idanu, harara kawai take aika masa duk da ya matse mata baki amma ko ɗar ba ta ji ba idanuwanta cike suke da masifa har wani ja ya soma saboda faɗa na cin mata rai kuma babu bakin faɗa. "In ki ka sake turo min wannan bakin naki kamar gidan tsutsa sai na cire shi, me ya sa ke kin cika neman rigima ne My Iman? Ko bakya so ki shiga aljanna?" Ya faɗa yana sakar mata bakin ganin hawaye sun cika mata idanu. Tana samu ya sakar mata bakin ai kuwa ta ɓarke da kuka har da ɗaura hannu a ka kamar wacce aka zane, girgiza kai ya yi ya tashi ya isa inda ta watsar kayan ta, a hankali ya tsuguna a gaban kayan ya kai hannu ya dauka tare daga su yana dubawa tare ta yin murmushin gefen baki ganin kayan sosai suka masa kyau, dan shi ya sayo su da hannunsa a Amerika da ya je wani taro wanda Abir ta zaɓa da kan ta tana zuzuta kyau kayan, lumshe idanu ya yi yana jin wani irin zafi marar iyaka a zuciyarsa sai ji ya yi an warce kayan. Da sauri ya ɗago suka hada idanu ta yi saurin kawar da kanta tana hura hanci, murmushi ya yi ya miƙe tsaye shi rashin kunyar da take masa birge shi yake a maimakon ya ji haushin ce mata ɗan iska da take. A hankali ya kai hannu ya riko nata hannun ai kuwa ta fasa ƙara ta tattaro dukkan ƙarfinta ta turo shi baya jikinta na rawa, da sauri ta gyara zaman towel ɗin da ta dauka ta ɗaura ta nufi gefen ɗaya tana kuka ai kuwa ta buga gwiwarta a jikin wani show glass da ke kusa da gadon ta fasa kuka tana yarfa hannu. Jin kukan nata ya bambanta da wanda take ya sa shi saurin ɗago da fararen idanuwansa da suka soma ja ya kalli inda take tsaye, waro idanu ya yi ganin jini na bin ƙafarta kamar kiftawa da bismillah sai ga shi a gaban ta a rikice yana tamabauar ta. "Subhanallahi! Garin yaya kika ji wa kanki ciwo Iman?" Ya faɗa yana janye towel ɗin zuwa kan gwiwarta inda ya ga rauni ta samu a gwiwa. Kuka take tana yarfa hannu ya rasa yadda zai mata ga taƙi ya canja mata kaya sai harara take aiko masa tana kuka, ganin za ta ja masa lokaci ya dauke ta cak ya aje a gaban miro ya ɗauki mai da hanzari ya ɗago da ita ya zaunar akan cinyarsa yana jera mata sannu, ai kuwa ta kafe ta ce bai isa ya taɓa mata jiki ba ya ba ta kayan za ta saka ya yi banza da ita. Ganin za ta sa masa ciwon kai da ihun da take ya matse ta ya sanya mata kayan tana ce masa mugu ya ce ya ji ɗin, yana gama sa mata ya ɗago fuskarta da ta yi sharkaf da ruwan hawaye da majina ya sa hannu ya goge mata fuskar yana jin ba daɗi, numfashi ya fesar ya kura mata idanu yana kare mata kallo ta turo baki. Murmushi ya saka mata ya yi gyaran murya ya ce "Wai me ya sa kike jin tsoro na?" Kara cuno baki ta yi tana dafe gwiwar da ta ji ciwo ba ta ce masa komai ba, shi ma bai wani damu ba ya sauke ta tare da cewa "Oya muje Momma na jiran mu za mu ci abinci." Ya faɗa yana kama hannunta suka nufi kofar fita daga dakin, sosai ta ji gwiwar na mata zugi dan haka ta dinga ɗigisawa tana yarfa hannu tare matse hawaye dan ta ƙagu su isa wajan Mamma.. Jakadiya ta fara ganin su ta dafe ƙirji tana bin Iman da kallo ganin jini ya biyo jikinta, kallon ta Ikilima ta yi ganin yadda ta rikice ta ce "Ya dai Jakadiya?" Saurin yin ƙasa da kai ta yi tana kallon Mamma cikin yin ƙasa da murya ta ce "Ranki ya daɗe da alama fa Gimbiya babu lafiya a tattare da ita." Ta faɗa tana zare idanu kamar maye ya ci ɗa a kasuwa. Kallon hanyar ɗakin Suhal Mamma ta yi ai kuwa ta yi arba da su Iman sai yarfa hannu take tana kwaɓe fuska shi kuma yana lallaɓa ta suna ci gaba da tafiya, gaban Mamma ne ya faɗi amma ta dake tana jiran su iso dan ta tabbatar da abin da idanuwanta suka gane mata.. Suna gaf da isowa ta sa kuka tana kwace jikinta daga rukon da ya mata ta nufo kan Mamma ta faɗa jikinta ta ƙara wa kukan ta volume, da sauri Mamma ta rungume ta tana bubbuga bayan ta alamar rarrashi, Jakadiya da ta kasa hakuri ta ɗan matso ta ce "Gimbiya wai me yake faruwa kike kuka?" Ɗagowa ta yi daga jikin Mamma ta kalli sashen da yake suka hada idanu ya yi wani kicin-kicin da fuska sai ta kuma sakin wani kukan har da shashsheka, ita dai Mamma shafa bayanta take ita ba bakin magana gareta ba ballantana ta rarrashe ta da kalamai masu daɗi. Sai da ta yi me isar ta sannan ta kalli Jakadiya tana goge hawaye ta ce "Ba shi ba ne ya ... Kasa ƙarasawa ta yi saboda kukan da take ya hana ta yin maganar, Jakadiya da son gulma ta kama hannunta ta ce "Haba Iman to meye na kuka kuma? Ai kowa haka yake fara rayuwar aure ki yi haƙuri." Ta faɗa tana gyaɗa kai. "To amma Jakadiya ai sh.. "Jakadiya tashi ki b mu waje za mu ci abinci." Suhal ya faɗa fuska ba annori, nan da nan ya dawo mata Yarima Suhal ɗin da ta sani ta yi saurin tashi jikinta na rawa ta fita.. Kallon shi Mamma ke yi ta tambaye shi da maganar kurame me ya yi wa Iman ɗin haka? Nisawa ya yi ya ce "Ni fa babu abin da na mata buge gwiwa ne ta yi a ɗaki, shi ne taƙi na gani sai rigima take yi wa mutane." Ya faɗa yana rausayar da kai ganin Mamma ta tsare shi da kallo.. Ikilima ta dannawa likitan su kira ta ce ya zo ya duba Matar Yarima ta samu rauni, to ya ce mata ga shi nan zuwa sannan ta kashe. Shi dai kallon su yake ganin yadda suka mayar da shi gefe sai rarrashin Iman suke ta lafe a jikin Mamma tana hararar shi da zarar sun haɗa idanu, kwafa ya yi yana kaɗa kai sai ga doctor mace an yi mata iso ta shigo. Rauni ta wanke mata aka sa mata magani a wajan, ko abinci ba ta ci ba bacci ya yi gaba da ita. Sai da Mamma za ta tafi wajan Maimartaba ya amshe ta suka nufi ɗakin su, itama Ikilima ta wuce nata ɗakin tana yi wa Suhal dariya jin ya ce wai Iman ta yi nauyi sosai.. Kwantar da ita ya yi ya lallaɓa shi ma ya kwanta tare da dauko ta ya mata masauki a jikinsa ta ci gaba da bacci, shi kuwa kasa bacci ya yi yana ta saƙa da warwara da kyar bacci ya yi gaba da shi.. Jakadiya na fita part ɗin Kilishi ta nufa inda Hadiman part ɗin ke gaishe da ita, cikin gadara take amsawa kamar ita ce matar sarkin har ta iso babban palon Kilishi wanda yake shuru ba kowa a palon sai ƙaran AC da ke tashi, mamaki ne ya kama ta ganin rigar Kilishi a palon haka dai ta danne ta nufi ɗakin. Kwalalo idanu ta yi lokacin da ta shiga ɗakin ganin mutum a kwance a gadon Kilishi ita kuma ba ta ma ɗakin, jiki na rawa ta yo baya sai ta ji ƙaran bude kofar bandaki sai ta yi gyaran murya tare da cewa "Ranki ya daɗe Jakadiya ce ina son yin magana da ke mai muhimmanci." A zabure Kilishi ta yi tana zare idanu, da sauri ta isa bakin gadon baki na rawa ta ce "Maza ka tashi uwar gulmar gidan nan ta zo ga ta nan a palo, ka bi ta kofar baya." Ta faɗa tana janyo doguwar rigarta ta zura da sauri ta zari mayafin rigar ta sa. Da hanzari ya tashi ya bi kofar baya kaya jikinsa a hannu, gyara gadon ta yi da sauri ta cire zanin gadon ta ja bargon ta lullube ko'ina sannan ta nufi wajan mayukan shafawar ta. Sai da ta shafa mai ta saka turare mai ƙamshi sannan ta nufo palon rai a matuƙar bace. Tana isowa ta hade rai cikin masifa ta ce "Ke wacce irin dabba ce Jakadiya? Ba ki ga na sallami masu min hidima a wannan palon ba zan kwanta ke kuma kika kwaso kafafu kika shigo min har kusa da ɗakin bacci na? To meye ma ya kawo ki da daren nan?" Ta faɗa tana zama a kan kujera. Rausayar da kai ta yi cike da jin haushin ta ce mata dabba, kasa daurewa ta yi ta ce "Ranki ya daɗe ki yi hakuri aikin da kika saka na yi miki ne yake neman lalacewa, shi ne na shigo na leƙa dakin sai na ga Yarima yana bacci a gadonki sai na dawo nan." Dam! Gaban Kilishi ya faɗi ta yi saurin kallon Jakadiya da ta yi ƙasa da kai, ganin ba ta kallon ta sai ta kawar da tsoron da ta shiga ta ɗaure fuska ta ce "E Yarima ne yake bacci wai ya dawo ya gaji sosai muna magana ya yi bacci, amma ina me jan kunnenki Jakadiya kar ki sake leƙa min ɗaki, ke ko nan palon ban ba ki izini ki shigo min ba ko ma meye ki bari na fito palo na biyu ko na uku sai mu yi magana, ki kula bana son shigigi da shiga inda ban bayar da damar hakan ba. " Ta faɗa tana hamdala da Jakadiya ba ta gane komai ba. " Tuba nake ranki ya daɗe zan kiyaye. " "Me ya kawo ki ?" Ta faɗa tana yatsina fuska. Gyara zama ta yi ta ce "Ranki aikin da muka yi duk ya tashi a banza, yau dai Yarima ya yi aika-aika ba ki ga ba yadda ya mata, ni ina tunanin ma sai an yi mata dinki." Ta faɗa tana dagowa ta kalli Kilishi da ta dafe kirji tana jin wannan gagarumin labari. Kasa cewa komai Kilishi ta yi ta yi kamar mai sumar zaune sai da Jakadiya ta kira ta sannan ta dawo haiyacinta. "Ki je Jakadiya zan neme ki ko zuwa jibi ne ni na san mai za ayi, wato Fulani so take ta cusa mana baƙin ciki ni kuma ba zan yarda wata can ta zo ake fifita ta biye da ni ƴar gidan sarauta." Jakadiya ba ta ce komai ba ta tashi ta tafi tana son komawa part ɗin Mamma amma in ta tuna yadda Suhal ya mata tsawa sai ta ji tsoro, haka dai ta nufi sashensu.. _NIGERIA_ Dukkan su Abba ya tattare 'yan gidan a palo gabaɗaya, bayan kowa ya zauna Abba ya ce "Wai Yaya Kabir ina Inna take ne? Na fa ce mata za mu tattauna." Girgiza kai Daddy ya yi ya ce "Inna fa ta bar gidan ma wai ana biki a can rugar su sun tafi ita da Laraba sai nan da sati ko kwana goma za ta dawo, ni na dauka da Mamana za ta tafi amma ta ce sam ba za ta tafi da ita ba ta shaki hayaƙin ruga ta sa ta uku ba." Sunkuyar da kai Abir ta yi ita dai ba ta ce komai ba, Abdul ya yi sallama ya shigo tare da Salim aka amsa musu, daure fuska ya yi ganin su Fatima zaune har da su Umma, cike da ba da umarni ya kalle su ba alamar wasa ya ce " Ku kuma wa ya ce ku zo taron manya? Ko har da ku za a tattauna ni da Salim mu koma inda muka fito?" Ya faɗa yana hura hanci ganin Abir ya ƙara ɓata masa rai ya daka mata tsawa ya ce "Tashi ki ba wa mutane waje duk kun wani zauna munafukai." Ya faɗa yana kallon Yasmin. Tashi suka yi sim-sim suka wuce, Abir ma mikewa ta yi za ta tafi Abba ya ce "Dawo Mamana wannan taron dan ku ukun nan aka kira shi." Dam! Ta ji gaban ta ya faɗi ta lallaba ta dawo ta zauna, gabadaya yau ji take kamar ta yi ta kurma ihu ko ta ji sanyi saboda yadda jikinta yake mata wani kalar yanayi wanda ta kasa gane na meye, ga kanta da yake juya mata da ta yi tafiya mai ɗan tazara dole sai ta tsaya ta huta.. Gyaran murya Abba ya yi ya ce "Mamana dalilin kiran taron nan na kira shi ne dan ku ukun nan kamar yadda na faɗa, muna son haɗa ku aure ke da ɗan'uwanki Abdul ko kuma Salim, amma dai ni na ga Abdul ɗin ya fi dacewa da ke ba Salim ba." A matuƙar razane suka ɗago suna kallon Abba dukkan su, shi Salim abin da dama yake so ya ji su ba shi Abir wadda yake tsananin so da ƙaunar ta fiye da misali, shi kuwa Abdul da Abir sun san da cewa babu a tsakanin su, Abir tana jin ko da ace akwai aure a tsakanin ta da Yayan nata to fa tabbas za ta dauki Salim ta bar shi, saboda yadda ya tsane ta yanzu ko ganin ta ya yi sai ya ci mata zarafi ya ga hawayenta sannan hankalin shi yake kwanciya, a yayinda shi ma Abdul ɗin yake jin ko da akwai aure tsakanin shi da Abir ba zai aure ta ba dan shi Hafsar shi ta isheshi.. "Kun yi shuru kun kyale, Mamana ke wa kike so a cikin su?" Wani irin zafi ta ji kanta ya dauka ta runtse idanu, da kyar ta iya cewa "Ni Abba ban son ko ɗaya daga cikin su, Salim Ammi ta tsaneni ba ta sona har su Fatima, shi kuma Yaya gabaɗaya ma ba ya so ya daga idanu ya kalle ni ba zan iya auren wanda ba ya ƙauna ta ba, ballantana ma babu aure a tsakanina da Yaya har abada ina da wanda nake so yake so na." Baki sake duk suke kallon ta Ammi ta yi murmushi ta ji daɗi da Abir ta ce ba ta son Salim dan ko da ta amince sai ta hana auren, ita kuwa Umma turo ɗankwalinta gaba ta yi tana kallon su tana gyada kai irin an faranta mata rai ɗin nan. Abba ya ce "To me ya sa kika ce babu aure a tsakanin ki da Abdul Mamana?" Kai tsaye ta ce "Saboda Mom ce ta shayar da shi har ya kai mawar yaye." Salati Umma ta dauka kamar da gaske ta riƙe baki tana jinjina kai, kallon Abir ta yi ta ce "Wai kina nufin nono ɗaya kuka sha ke da Abdul?" Gyaɗa mata kai Abir ta yi tana sauke numfashi, tambayar Abdul Abba ya yi ya ƙara tabbatar musu babu aure a tsakanin shi da Abir sai dai Salim shi kuwa ta ce ba ta so. "To in ba ki son Salim waye wanda kika fitar a matsayin miji? Kin ga su Yasmin sun samu mazajen aure ita da Khairat sauran Fatima ya rage." Shuru ta yi tana wasa da yatsu hannunta hakan ya ɓata wa Abdul rai ya saka mata tsawa ya ce ta faɗi waye. Ji ta yi ta gaji da wannan ƙuncin na gidansu kai tsaye ta ce " Abba ni ku aura min Zaiyan sai na ci gaba da kulawa da shi. " Kwalalo idanu waye suka yi suka hada baki wajan fadin "Zaiyan..." _Maman Nusaiba ce_ [6/20, 8:43 PM] Ummu Amjad: ~A HAKA NAKE SON SHI~ Shafi na (35) Ji ta yi sun ma ɓata mata rai da suka hada baki wajan kiran sunan Zaiyan, hura hanci ta yi tana jin gara ta ɗauki wannan kasadar da ta ci gaba da zama a gidan nan suna ƙunsa mata baƙin ciki. Ɗago kai ta yi kan ta tsaye ta dubi Abba ta ce "E shi fa Abba, ina son shi sosai kuma zan zauna da shi har karshen rayuwata, ko ba komai zan samu ladan kula da shi kuma in sha Allah ina sa ran nan gaba zai samu lafiya. Ina so zan nema masa magani ko da ba a ƙasar nan ba ne zan tafi kowacce ƙasa wajan ganin ya samu lafiya kamar kowa." Ta faɗa idanuwanta na zubar da hawaye ; ji take in dai ba a aura mata Zaiyan ba to tabbas za ta iya mutuwa. Ƴar dariya Umma ta yi tana tafa hannu wannan abu yana yi mata suga wai Mahaukaci take so? Daure fuska ta yi ta ce "Haba Abir yanzu ki rasa wa za ki ce ki na so sai mahaukaci wanda bai ma san rayuwar duniya ba? Anya kuwa ki na cikin haiyacinki Abir?" Ta faɗa tana riƙe haɓa alamar mamaki. Ammi da ta yi shuru tana jinjina lamarin sai kawai ta rafka tagumi, can dai ta nisa ta ce "Abir ke yanzu in aka ce ki auri Zaiyan sai ki aure shi dan kema ki na mahaukaciya irin shi? Ya za ayi mu yarda jininmu ta auri mahaukaci ki dai sake magana ba dai wannan ba, idan kin ce ba ki son Salim ba wani abu ba ne mu ba za mu bari ayi miki auren dole ba, sai ki kawo wani. " Ran Abir ne ya ƙara ɓaci taya ma tana ce musu ga wanda take so amma a ce mata wai ba shi ba, a fusace ta ɗago ta kalli Ammi cikin tabbatar mata da maganar ta ce " E shi ɗin dai *A HAKA NAKE SON SHI* a haka zan zauna da shi, ina ce dai ni zan zauna ba wani ba ko? To ku aura min shi na bar muku gidan gabaɗaya tun da dama ai ba son gani na kuke ba." Ta faɗa tana huci gabaɗaya ma gani take so suke su hana su Abba yin magana.. Abba ya nisa ya ce "Mamana ki bar maganar Zaiyan kin ga ba shi da hankali, ki haƙura ki auri Salim ɗan'uwanki zai kula da ke." Daddy da ya fusata ya ce. "Sulaiman ka daina ma rarrashin ta, ko ta ɗauka mu ma ba mu da hankalin ne irin ta za mu yarda a aura mata mahaukaci? To Wallahi ki ma canja zaɓi in ba haka ba ni da kaina zan ɗaura miki aure da Aruf ya dawo ayi bikin ku ya dauke ki ku tafi can ku ƙarata." Ya faɗa yana nuna ta hannu. A zabure Abir ta ɗago tana nanata maganar Daddy, Uncle Aruf za a haɗa ta da shi bayan ta ce ga zaɓin ta? Tab ai kuwa ba zai yiyuba dole ne ta tsaya ƙyam akan ƙafafunta wajan ganin an ba ta wanda take so. Goge hawaye ta yi cikin tashin hankali ta ce. "Wallahi ni dai Abba ba na son Uncle Aruf ya fiya kula 'yan mata duk wadda ya gani sai ya ce yana son ta, Kuma ma ai ni ga wanda nake so in karya nake ku kira shi nan ku tambaye shi zai ce muku yana so na." Ta faɗa tana fashewa da kuka.. Abdul da ya kawo wuya ya zaburo ya zabga mata mari ji kake tas!Tas! Yana huci ya kama kunnenta cikin tsananin ɓacin rai ya ce "Su Abban ne suna faɗa ki na faɗa saboda ba ki da kunya? Wallahi na sake jin bakinki a wajan nan har a gama sai na kakkarya ki fitinanniya kawai, an ce ba za ki aure shi ba ƙanen banki ne shi?" Ya faɗa yana sake kai mata wani dukan Salim ya yi saurin riƙe hannunsa ganin yadda shatin yatsunsa suka baiyana ruɗu-ruɗu a kumatunta. Rai ɓace Salim ya kalli su Abba da suka zuba musu idanu ya ce "Yanzu Abba kuna gani yake dukan ta kamar wata jaka ba za ku hana shi ba? Wannan wani irin zalinci ne? Ban taɓa tunanin irin wannan ranar za ta zo ba Yaya Abdul ya sa hannu ya daki Baby, ina ruwan ka da zaɓinta tun da kai dama yanzu ka tsane ta? Wallahi in ka sake dukan ta sai na rama mata baiwar gidanka ce ita da za kake dukan ta?" Ya faɗa kamar zai kai wa Abdul duka; nan da nan ran maza ya ɓaci sai huci yake yana kallon Abdul da shi ma a samar yake, bai taɓa tunanin akwai ranar da Abdul zai yi wa Abir haka ba saboda tsananin so da ƙaunar da ke tsakanin su.. Ganin abin ya kacame Umma ta miƙe tsaye tana murmushi tare da takowa ta iso gaban Abir ta miƙar da ita tsaye, share mata hawayen ta yi ta kalli su Daddy tana ɗan hade rai ta ce "Ku aura mata wanda take so mana meye a ciki? Ba dai yana da iyaye ba sai su yi zaman su, ni a matsayina ba ƙanwar mahaifinta kuma uwa a gareta ba zan taɓa bari ku aura mata wanda ba Zaiyan ba. Ba dai aure kuka so ta yi ba? To tun da ta kawo wanda take so ai sai ku bar ta ta aure shi in ba neman tashin hankali kuke yi ba a gidan nan, kun takura mata dayawa marainiyar Allah dan kun ga ba ta uwa ba ta da uba sai ita kaɗai, wanda take sa ran zai zame mata dangin uwa shi ma yanzu dukan ta yake ya kuke so ta yi ne? " Ta faɗa irin ga uwar tar nan na magana cike da gadara.. "Haba Baraka ya za ki ce mu bari ta auri mahaukaci? Anya kema ki na haiyacinki kuwa?" Abba ne ya faɗa cikin jimamin wannan lamari.. Ƙanƙance idanu Umma ta yi tana kada kai ta ce. "To uban iyayi ba fa zan bari ka aura mata wanda ba ta so ba, yadda kake tunƙaho Abir jininka ce ni ma jinjina ce, kun yi munafuncin ku kun raba ta da wanda take so kuka aura wa ƴar'uwarta, ba dan ba ma tana son Iman me kuke tunanin zai faru tsakanin su?" Ta faɗa tana hararar Ammi da ta saki baki da hanci tana kallon ta. "Ihumm iko sai Lillahi ni Farida, au Allah ko Baraka ? To ke ki aura mata shi mu gani ƴar iya uwar shisshigi, ai duk kusancin ki da Abir su sun fi dan haka ki iya bakinki mu shayo kan matsalar nan." Ta faɗa tana kawar da kai. Daddy ya dubi Abir ya ce "Shi dai kike so ko? Kuma za ki zauna da shi a matsayin miji?" Gyada kai ta yi ta ce "Ni A HAKA NAKE SON SHI." "To wa zai ciyar da ke yake tufatar da ke? Wa zai ba ku gida ku zauna?" Turo baki ta yi ta ce "Ni zan saya mana gida sai nake kasuwanci." Ta faɗa tana hararar Abdul.. Ganin wannan magana ba mai ƙarewa ba ce Abba ya ce su tashi su tafi zai neme su gobe in kowa ya dawo daga aiki, haka kowa ya fita yana ta jinjina maganar Abir.. Abdul kuwa da mugun ɓacin rai ya bar gidan saboda maganganun da Salim ya yaɓa masa ya ji ya ƙara tsanar Abir, shi kuwa Salim wani irin tausayin Abir ne ya mamaye shi yana tunanin ta ya marar hankali zai auri mai hankali kamar gari ba manya? Haka dai ya shiga motarsa ya mata key ya wuce. Ita kuwa Ammi kasa zama ta yi sam ba ta so Abba ya ce Salim zai aura wa Abir, dan ita ba ta son a haɗa yaronta da jinin matsiyata su Mom gara ta zaɓo masa a ɗiyan Aminanta yaran masu kudi su aura.. Su kuwa su Abba fita suka yi da nufin yin shawara. Ita ko Abir tana shiga ɗaki kan gado ta faɗa ta fashe da kuka, wannan wacce irin jarrabawa ce haka? Kowa yanzu bai damu da ita ba, tashi ta yi zaune tana share hawaye ta soma magana cikin kuka. "Ya Allah ka fitar da ni daga wannan halin da nake ciki, kowa ba ya so na dan an ga mahaifiyata ta rasu Abie na ma ya rasu ba wanda ke min kallon so, da suna raye nasan ko da kowa ya gujeni su za su ƙaunace ni." Kai da gwiwa ta haɗe ta ci gaba da rero kuka, kamar daga sama ta ji saukar wani abu a gefen ta ta buɗe idanuwanta da sauri. Duhu ne ya mamaye ɗakin sai kawai ta ji wani sanyi ya ziyarci zuciyarta, a hankali ta sake duban gefen ta yi arba da shi ya yi tsaye yana kallon ta. Da sauri ta zabura ta miƙe tsaye baki na rawa ta ce "Z. Za.. Zaiyan." Ta faɗa a ruɗe. Zama ya yi a bakin gadon yana sakar mata murmushi sai kawai ta ga ya soma canja halitta zuwa matar nan, dogon numfashi ta ja ganin ba shi ɗin ba ne. "Maijidda kukan ya isa haka." Ta faɗa tana dafa kafaɗarta. Sabon kuka Abir ta sa cikin rashin sanin inda za ta sa ranta ta ji sanyi, cikin raunanniyar ta ce "Mama to ya zan yi?" Shafa bayanta ta yi ta ce "Kar ki ce komai ki kwanta ki yi bacci, komai zai wuce amma auren ki da Zaiyan ba fashi ko me za su yi." Tana maganar tana shafa kan ta kwantar da ita tare da ja mata bargo. Nan da nan bacci ya yi awon gaba da ita, murmushi ta yi ta ɓace a ɗakin.. A fusace Alhaji ya kira Alhaji Mustapha sai safa da marwa yake, ganin ya daga ya soma sababi. "Wai Mustapha me ka dauke mu ne? Ya za mu ji shuru kuma an yi aure watanni fiye da shida amma ba labarin wani abu da muka samu." Daga can ɓangaren Alhaji Mustapha ya gyara zama ya ce "Kai fa daɗi na da kai Alhaji gaggawa, yanzu haka na kira Abdul akan cewa muna neman shi a gidana za mu tattauna akan wasu batutuwa kuma ya ce ko yanzu nake son ganin sa zai zo, ka kwantar da hankalinka ni ai nasan me nake yi." Ya faɗa yana kaɗa ƙafa. Ajiyar zuciya Alhaji ya sauke ya ce "Ni yanzu ba wannan ba ma, wai yarinyar nan ta rasa wa za ta ce tana so sai mahaukacin nan da muka taɓa kamawa? Amma kai ya kake gani mu bari auren ya yiyu ko kuma mu sanar da Boka na kan dutse ya yi mana maganin ƴar banza?" Ƴar dariya Alhaji Mustapha ya yi ya ce "Kai fa Alhaji wani lokacin ƙwaƙwalwarka manta lissafi take, ta ya ma za mu yarda a ƙi yin wannan auren? Ai wata dama ce ta zo mana in aka yi auren, da zarar an gama komai muna gano inda aka kai ta zance ya gama." Ya faɗa yana dariya. Shi ma dariyar Alhaji ya yi yana dukan kansa da hannu ya ce "Ka yi gaskiya Mustapha dan haka mu yi yadda za mu yi ayi a gama.." Da haka dai suka gama tattaunawa kowa na kawo tashi shawarar.. Sai bayan kwana biyu aka sake yin taro inda dukkan su ba wanda ya sake muso akan zabin Abir, sosai ta yi mamaki ganin duk sun goya mata baya har da shi kan shi Abdul da yake dukan ta akan maganar, haka suka sa Abdul ya kira Baba a waya ya zo gidan da Yamma.. ABBA ya dubi Baba ya ce "Mamana ta ce ita Zaiyan take son aura." A ruɗe Baba ya kalli Abir da ta yi kicin-kicin da fuska dan kar ma wani ya mata magana, Baba ji kawai ya yi wannan haɗin ya masa dan haka ya ce "Kwarai kuwa ai zan fi kowa farin ciki in hakan ta faru, in ma yanzu kuke son a ɗaura na zo da sadaki." Daɗi ne ya mamaye zuciyar Abir ta saki murmushi, Abdul ya ce "To Baba kawo ai ko iya mu mun isa mu ɗaura mata aure kawai ta bika ku tafi ba sai an tsaya ana wani tara mutane ba." Shi dai Baba komai aka ce to kawai yake faɗa ya ciro kuɗi a aljihunsa ya lissafa su dubu 30k ne ya miƙa wa Abba ya ce "Ga sadakin Hauwa'u ina nema wa Zaiyan auren ta." Murmushi Abba ya yi ya amsa ya miƙa wa Daddy ya ce "Mun amsa kuma mun ba ka Mamana." Baba gani yake kamar wasa kowa ya sheda sadaki a palon suka yi addu'a suka ɗaura wa Abir da Zaiyan aure lokacin ita kuma ta gudu ta shige ɗaki tana jin kanta kamar sabuwar halitta... Bayan sun gama Salim ya yi jugum yana kallon ikon Allah, wai Abir ce aka ɗaura wa aure a palo ba tare da an tara mutane dayawa ba? Tashi ya yi ya nufi ɗakin ta jin Abba ya ce ya je ya sanar da ita ta haɗa komai nata su tafi, kwafa ya yi ya nufi ɗakinta.. A gaban wardrobe ɗin ta ya same ta janyo ƙatuwar akwatunta tana zuba kaya, riƙe baki ya yi ya ce "Baby yanzu wai da gaske har kin zama matar aure.?" Kallon banza ta watsa masa ta ce "Ga zahiri ka gani malam." Gyaɗa kai ya yi kamar wani ƙadangare, yana tsaye ta kwashe kayanta bakiɗaya duk wani abin da tasan tana so sai da ta kwashe abin ta har da zannuwan gadonta duk ta kwashe, ganin ba za ta gama ba ya ce mata Baba na jiran ta ta ce to ya je tana zuwa ya fita.. Takardun da Mom ta ba ta ta dauko ta janyo ɗayar akwatin ta sa su a ƙasa duk wani abu da tasan mai amfani ne ta dauke kayanta ta cusa a akwati, ATM card ɗin ta ta saka a handbag ta kwashe kuɗaɗanta da ke cikin loka wani kuɗin ma tun Abie na da rai yake ba ta in za ta yo shopping duk take Tara su.. Bayan ta gama ta janyo akwatuna uku ta fito ta sa key ya kulle dakin ta nufo palo inda iya Baba kawai ta samu ta kalle shi tana murmushi ta ce "Baba muje." Shi dai Baba jinjina lamarin nan yake na auren su, tashi ya yi ya amsar mata akwati ɗaya suka fito zuwa harabar gidan inda ta bude motarta ta saka kayan, Baba ya shiga itama ta shiga za ta mata key sai ga Umma da sauri tana gyara zaman hijabi ta tsayar da ita.. "Abir ya za ki tafi ke ɗaya ba za ki bari mu raka ki ba ne?". Ɓata rai Abir ta yi ta ce "A'a Umma ai ba sai kun rakani ba da Baba za mu wuce." Ta faɗa tana kunna motar. Dariya Umma ta yi tana tafa hannu wannan lamari ya mata daidai, ja baya ta yi ta ce "To matar Mahaukaci a gaishe da gida." Ta faɗa tana kuma yin wata dariyar. Hannu kawai Abir ta daga mata Allah-Allah take ta bar gidan, hon ta yi Maigadi da ya cika da mamaki ya buɗe musu get yana bin Abir da kallo, kasa haƙura ya yi ya ce "Oh ikon Allah! Aure da mahaukaci mai babban suna? To Allah ya ba da zaman lafiya." Cikin hauƙi take taƙi hankali kwance kamar bawan da ya samu 'yanci. Suna isa ta yi packing a harabar gidan ta kalli Baba ta ce "Baba kaima ba ka son auren nan namu ko?" Ta faɗa tana yin fuskar tausayi. Saurin girgiza kai Baba ya yi ya ce. "Ina Hauwa'u, ai na ma fi kowa farin ciki da wannan aure naku, Allah ya biyaki da gidan aljanna akan abin da kike mana na alkhairi." Amin ta ce suka fita daga motar ta buɗe ta ɗauko akwatunan suka ja ita da Baba suka nufi ciki. A hargitse suka samu palon an yi ɗaiɗai da kujerun palon hatta dining table ɗin palon an kakkarya kujerun, gefe ɗaya kuma an farfasa kayan wani show glass babba da ke gefen kujerun palon an amsa raga-raga. Kwalalo idanu Baba ya yi jikinsa ya ɗauki rawa nan-da-nan zufa ta shiga yanko masa ta ko'ina, kallon ko'ina na palon Abir take ganin ba kowa, kamar daga sama suka ji ƙaran fashewar wani abu a kitchen ta saki akwatin hannunta suka nufi kitchen ita da Baba. A hankali suke takawa har suka isa bakin kofar, a ruɗe ta kalli Zaiyan da ya dauko wani cup ya ɗaga zai dankwaza shi da ƙasa ta taƙarƙare ta ce "A'a Zaiyann..!!" Cak ya dakata da fasa cup ɗin ya ɗago kai ya kalli bakin kofar, ganin ita ce ya nufo ta da saurin yana sakin kuka ya faɗa jikinta tare da cewa "Antyy....!" _Maman Nusaiba ce_ [11/15, 10:59 Yamma] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): ~A HAKA NAKE SON SHI~ Shafi na (36) Da sauri ta sa hannu ta rungumo shi ganin yadda jikinsa yake rawa kamar mazari, nan-da-nan hankalin Baba ya tashi ganin idanuwan Zaiyan sun soma juyewa baƙin na yin sama. Ɗago da shi ta da kyar saboda nauyin da ya mata ta ga idanuwansa suna farfari ta juyo ta kalli Baba a ruɗe, hannu Baba ya sa ya amshi Zaiyan suka taka a hankali suka fito daga kitchen ɗin ko'ina ya zubar da kaya ya kashe. A hankali suka dinga jan shi ƙafafuwansa na jan ƙasa saboda ya musu nauyi, suka bi ta gefen da ba komai suka nufi ɗakinsa da shi. Ruwa Baba ya dauko da sauri ya dinga tofa addu'o'i a cikin sannan ya dinga shafa masa a fuska, miƙa ya dinga yi yana ƙara riƙe Abir da ta soma zubar da hawaye tana shafa kansa bakinta dauke da Addu'a. Zafi rau jikinsa ya ɗauka hakan ya sa Baba ya ɗauko bargo daga kan gadonsa ya lulluɓa masa yana fadin "Allah ya ba ka lafiya, bari naje na kira Ɗanladi mu kwashe kayan palon ke ki zauna a nan karki fito." Ya faɗa cikin jimami tare wucewa ya rufe musu ɗakin.. Shuru ta yi tana sauke ajiyar zuciya tana kallon fuskarsa, kyakkyawar girarsa da ta kwanta baƙa ta kai hannu ta taɓa ya ɗan motsa, saurin da ɗauke hannu ta yi sai kuma ta ga ya ƙara shigewa jikinta yana jan numfashi. Buɗe idanu ya fara yi hakan ya sa ta soma kiran sunan shi, "Zaiyan buɗe idanuwanka ka ganni." Hannu ya sa yana mitsitsika idanu jin muryarta ya buɗe idanu a kan kyakkyawar fuskarta tana sakar masa murmushi, saurin tashi ya yi daga jikinta yana zaro idanu ya daga baki zai yi magana sai kuma ya fasa ya zura mata na mujiya. Murmushi ta yi tana gyara zama ta buɗe masa hanayenta ta ce "Zo nan ka kwanta ka ga ba ka da lafiya." Ta faɗa tana nuna masa cinyarta. Ɓata fuska ya yi yana riƙe kansa ya matso ya kwanta a cinyarta tare da zagaye ƙugunta da hannu ya lumshe idanu, ta goge hawayen da suka soma silalo mata tana shafa kansa a hankali tana ƙissima abubuwa daban-daban.. Baba na fita ya kira Ɗanladi suka kwashe komai na palon, har kitchen suka kwashe wanda ya farfasa Ɗanladi ya share ko'ina tas suka dauke carpet ɗin palon suka fitar da shi waje suka zazzage tas tare da sharewa, dawo da shi suka yi suka shinfida ya yi wa Ɗanladi godiya sannan ya fita shi kuma ya nufi ɗakinsu dan ya watsa ruwa.. Ana kiran Sallar magariba Inna ta dawo daga wajan bikin da ta je, ko da ta shigo palon ta ga wayam babu kujeru sai akwatuna 3 da ta gani a palon, sosai ta cika da mamaki ta wuce ɗaki. A bakin ƙofa suka ci karo da Baba yana shirin tafiya Masallaci, ɗan murmushi ya yi ya ce "har kin dawo? To sannu da zuwa." Ya faɗa yana tsayawa a gaban ta. Itama murmushin ta mayar masa tana cire hijabin jikinta ta ce. "E na dawo Malam, amma ya na ga an dauke kujerun palon nan ko sabo za ka canja mana ne? Na ga kuma har da akwatuna." Ta faɗa tana kallon Baba. Girgiza mata kai ya yi ya ce "Ki bari in na dawo zan sanar da ke komai, ɗiyarki na nan tana ɗakin Zaiyan ki shigar mata da akwatunanta cikin ɗakin in dawo zan miki bayani." Ya faɗa yana wucewa. Cike mamaki Inna ke nanata Kalmar akwatuna, ganin dai ba mai ba ta amsa ta isa ta aje Jakarta ta shige bandaki.. Abir jin an kira Sallar magariba sai ta lallaɓa ta daga kan Zaiyan da nufin ta kwantar da shi, a hankali ta janye cinyarta ta kwantar da shi a kar carpet ta yunƙura za ta tashi ta ji an ruko ta, waro idanu ta yi ganin ya buɗe idanuwansa a kanta ya turo baki ya ce "Anty kar ki tafi ki bar ni." Ya faɗa yana tashi shi ma ya riƙe hannunta. Ba yadda ta iya haka ta buɗe wardrobe ɗin sa ta dauko masa wasu kayan yana rike da rigarta ta nufi toilet, a bakin ƙofar ta tsaya tare da kama hannunsa wanda ya riƙe mata gefen riga ta ce "To ka tsaya a nan na yo alwala sai na canja ma kayan." Ta faɗa tana zare hannunsa. Maƙale kafaɗa ya yi ya dawo bayanta ya kwanto kansa bisa kafaɗarta yana fadin "Dan ki gudu ne." Dafe Goshi ta yi ta masa dubara amma sam ya ce mata ba zai yarda ta shiga ta bar shi a bakin ƙofa ba sai dai su shiga tare, ba yadda ta iya haka suka shiga banɗakin duk jikinta rawa yake, haka ta juyar da shi gefen da ake alwala ta nuna masa madubin wajan ta ce masa ai abokinsa ne ya masa magana, shi kuwa murmushi ya yi ya miƙa hannu yana shafa jikin madubin da haka ta yi saurin tsugunnawa ta yi tsarki ta miƙe tana mayar da numfashi. Rigar jikinsa ta cire masa ta goge masa zufa shi kuma yana tsaye ƙiƙam yana kallon ta sai inda ta juya shi, ganin dai duk jikinsa ya yi baƙi ta janyo hannunsa suka iso wajan wanka ta kalle shi ganin ya ƙi yin gaba ta ce. "Ka tsaya mana jikinka zan wanke ma." Ta faɗa tana ƙarasa janyo shi ya tsaya a saitin da ruwa ke zuba ta kunna. Zabura ta yi lokacin da ruwan ya zubo ta yi saurin riƙe hannunsa tana ce masa ya tsaya, haka ta dinga fama da shi da ta dauko sabulu za ta goga masa sai ya ce shi fa ba ya so, da kyar da siɗin goshi ya yarda ta masa wankan da wandonsa bakin gwiwa haka ta masa wanka da shi a jikinsa. Ita kanta ta yi jigib da ruwa kayanta sun jiƙe haka dai ta janyo wani towel da ta gani a toilet din ta goge masa jiki sannan ta yi alwala shi ma ta masa suka fito. Sai da ta zo za ta canja kaya ta tuna ba ta ma shigo da kayan ba ta nufi palo cikin sanɗa, akwatunan ta janyo za ta shige ɗaki ta ji muryar Inna ta daki dodon kunnunta ta juyo da sauri. Cike da mamaki Inna ta iso tana kallon ta ganin yadda ta jiƙe da ruwa ta ce. "Hauwa'u waɗannan kayan duk naki ne?" Gyaɗa kai kawai Abir ta yi ta juya ta shige ɗakin cikin saurin, riƙe baki Inna ta yi tana cewa "Iko sai Allah! To bari dai mu gani malam ya dawo." Juyawa ta yi ta nufi kitchen tana ta mamakin yadda ta ga kitchen ɗin ba haka ta fita ta bar shi ba.. Abir na shiga ɗakin ta zarge akwati mai kayanta ta fito da wata doguwar riga da mayafinta shi ma Zaiyan ta ɗauki nasa kayan da ta dauko masa ta ce ya zo ta sa masa, bai musa mata ba ya iso gabanta ta dauki jallabiyarsa baƙa ta sa masa a haka ta fidda masa na jikin ta nuna masa yadda zai sa ta ba shi ya saka yana dariya, jallabiyar ta cire ta sa masa rigar sannan ita ma ta koma jikin wardrobe ta buɗe kamar mai ɗaukan kaya ta kare da murfin ta yi saurin canja kaya. Salla ta tayar shi ma ya yi kamar yadda ya ga tana yi, duk abin da ta yi sai ya yi har suka gama Sallar ta juyo ta kalle shi tana murmushi. Matsowa ya yi kusan ta ya ce. "Kai kai kai! Anty." Dariya ce ta so subce mata ta danne jin ana kwankwasa musu kofa, tashi ta yi yana biye da ita a baya ta buɗe ƙofar ta ga Inna ce tsaye. Murmushi ta yi ta ce "Inna Baba ya dawo ne?" "E ya dawo shi ma ya ce a kira ki." Ta faɗa tana juyawa ta fice ;ita kuma ta juya ta dauko mayafin rigar da wayarta suka yo palo. Tun da suka fito Baba ke kallon su yana jinjina lamarin da ya faru, suna isowa ta zauna ƙasa Zaiyan ya kwanta kansa a bayanta yana riƙe da hannunta sai kallon su Baba yake, riƙe baki Baba ya yi ya ce "Zaiyan yau kuma mu ka nuna kamar ba ka san mu ba?" Ƙara komawa bayan Abir ya yi bai ce komai ba hakan ya sa Baba ya yi murmushi, Inna ta nisa ta ce "Malam wai me ke faruwa ne? Na ga Hauwa'u ta dauko kayan har akwati uku, sannan palon nan an kwashe kujeru sai wannan dayar aka bari a gidan ko dan itama a lungu take shi ya sa ba ku gan ta ba?" Ta faɗa tana kallon Baba. Gyara zama Baba ya yi ya faɗa mata yadda suka tarar da palon har zuwa lokacin da suka kwashe komai na palon suka fitar, ya dan muskuta ya kalli Abir yana girgiza kai ya ce "Maganar Hauwa'u kuwa da yammar nan aka ɗaura auren ta da Zaiyan, shi ya sa kika ga ta zo da akwatuna." A zabure Inna ta kalli Baba baki na rawa ta ce "Ba...Ban gane me kake nufi ba Malam? Wai Zaiyan da Hauwa'u ne aka ɗaura wa aure?" Ta faɗa tana dafe ƙirji. Jinjina mata kai ya yi alamar tabbatarwa ta rafka tagumi tana kallon Abir da ta nuna ko a jikinta sai ma danna waya da take, tafa hannu Inna ta shiga yi ta ce "Hauwa'u anya kina haiyacinki kuwa? Zaiyan ɗin ne aka aura miki matsayin miji? Anya dangin nan naki suna ƙaunar ki kuwa Hauwa'u." Ta faɗa cike da ta'ajjibin wannan lamari na Abir. Aje wayar ta yi da ɗago ta kalli Inna kafin ta yi magana idanuwanta suka cika da hawaye sai ga su sun zubo shar, da kyar ta saita kanta ta ce " Inna kenan, ki bar maganar dangina ba ta ni suke ba kowa ta kan shi yake da 'ya'yansa, ni kuma da ba ni da wanda zai kula da ni sai Allah wanda a kullum da shi na dogara shi ya sa ma na saɓi na bar musu gidan su daina ganina." Hawayen da suka sake zubo mata da goge Inna ta ruko hannunta ta ce "Ke fa daɗina da ke arhar ruwan ido kuka ba ya miki wahala." Kamar jira take ta fashe da kuka tana rufe fuskarta da tafin hannu, sai da ta yi kuka sosai Inna na rarrashin ta sannan ta tsagaita ta shiga ba wa su Baba labarin abin da yake faruwa a gidansu da sauyawar da kowa na gidan ya mata, har labarin abubuwan da Abdul yake mata duk ta sanar da su tana yi tana sharce hawaye har da majina. Salati Inna da Baba suka ɗauka cike da tausayin ta, ba su taɓa tunanin Abdul zai yi wa Abir tsana har haka ba, Inna ta jinjina kai ta ce "Ki yi haƙuri Hauwa'u in sha Allah wata rana za ki yi farin ciki marar yankewa, amma hukuncin da kika yanke na wannan auren sam bai yi ba taya ma da hankalinki za ki auri mai allurar hauka? Gaskiya ɗabi'unki sun canja Hauwa'u ban san ki da taurin kai ba." Ta faɗa tana sauke numfashi.. Murmushi mai ciwo Abir ta yi ta ɗan motsa ta ji ya riƙe ta gam ga duk ya sakar mata nauyinsa, hannunsa ta taɓa tana kiran sunansa ta ji shuru sai da Baba ya leƙa ya ga ya yi bacci. Jin ana kiran Sallar Isha'i Baba ya ce su kai shi ɗaki kafin ya tafi masallaci, yunƙurin tashi ta yi a hankali sai gani suka yi shi ma ya miƙe tsaye yana ƙara riƙe Abir, ganin hakan sai ta ce Baba ya je ita za ta shigar da shi ɗakin ya amsa da to.. Inna ta nufi kitchen ta ɗaura abinci, ita kuma ta lallaɓa ta ja shi suka nufi ɗakinsu. A kan gado ta zauna shi ma ya zauna ya kwanta a kafaɗarta yana lumshe idanu, nuna masa ta yi ya kwanta amma sam yaƙi ya kwanta yana manne da ita ta dafe kai tana kallon shi, haka ta haƙura ta haye tsakiyar gadon shi ma ya hau ta kwanta tana kallon shi, ganin ta kwanta ya matso bayanta ya kwanta tare da zagaye cikinta da hannunsa yana sauke mata numfashi a kanta saboda ya fita tsayi sosai. Lumshe idanu ta yi tana jin gaban ta na faɗuwa, shi kuwa ya yi luf sai jan numfashi yake da ta motsa zai buɗe idanu hakan ya sa ta haƙura ta yi kamar tana bacci. Sai da karfe 9:30pm ta ga Inna ta shigo da kayan abinci ta aje ta fita ba ta ce musu komai ba, kunya ce ta mamaye Abir saboda yadda Inna ta gan su manne da ita da shi ta tashi zaune za ta sauko ta ji shi ma ya tashi zaunen. Haka ta janyo abincin ta dinga ba shi a baki yana ci yana mata surutu ita kuma tana bin shi da e ko a'a har ya koshi, bayan ya gama ya ce itama ta ɗaga bakinta zai ba ta, tana murmushi ta ɗaga baki ya dinga cusa mata kafin ta cinye wani ya sa mata wani, da kyar ta janye tana ce masa ta koshi shi kuwa sai ya ɓata fuska ya ce ta cinye duka dan ta zama ƙatuwa kamar abokinsa Suhal. Bayan sun gama suka nufi toilet ta wanke masa hannu itama ta wanke ta ɗauro alwala ta masa suka fito. Sallar Isha'i ta gabatar haɗi da shafa'i da wutiri duk abin da ta yi shi ma Zaiyan sai ya yi har ta shafa addu'a, tashi ta yi ta hau gadon shi ma ya yau ta yi musu addu'a suka kwanta. Kasa bacci ta yi sai juyi take gabaɗaya jin ta take a takure saboda ba ta saba kwana da kowa ba, waya ta dauka ta ga sakon Iman ya shigo ta share ta ci gaba da tunanin da ya zame mata jiki... Karfe 11:00pm na dare Alhaji Mustapha ya kira Abdul ya zo ya same shi a gida ya ce ga shi nan zuwa.. Yana zuwa ya tarar da Alhaji Mustapha da Jarmai suna zaman jiransa, guri ya samu ya zauna tare da gaishe su suka amsa fuska sake suna ƴar ido. Zuwa can Abdul ya ce. "Dad gani ka ce na zo za mu yi wata magana mai muhimmanci, ina so mu yi mu gama na baro Hafsat a gida ta ce min kar na wuce awa ban dawo ba ni kuma ba na son na ɓata mata rai ta yi fushi." Ya faɗa yana ɗan ɗaure fuska.. Dariya Alhaji Mustapha ya yi ya ce "Ƴar jakar uba har wani umarni take ba ka dan ta samu waje? Ka rabu da ita ni zan mata bayani ko da ka wuce awa ɗaya ballantana ma minti talatin ya wadatar mu gama maganar. " Ya faɗa yana kallon Jarmai da yake wani hawa kamar fulawa shi ga suriki. Gyada kai ya yi hakan ya sa Alhaji Mustapha ya ce "Dama mu abin da muke so ba wani dogon turanci za mu tsaya yi ba, ina son ka amso mana ma'adanar bayanai a hannun ƙanwarka Abir, sannan da wata takarda wanda sun jima a tare da ita, so muke duk ka amso mana su saboda namu ne ba na mahaifinta ba." Ya faɗa yana daure fuska irin ba wasa din nan.. Sauke ƙafa Abdul ya yi da ɗaura ɗaya kan ɗaya ya nisa ya ce "Lalle sai na kakkaya Baby kat, me ya kai ta ɗaukar muku kaya? Ko dai sata ta fara ne ban sani ba?" Ya faɗa yana ƙara jin tsanar ta na ƙara ruruwa a zuciyarsa, ji yake zai iya ɗaura bindiga a kanta ya ɗana mata kunama ya harbe ta.. Alamar jinjina Jarmai ya yi wa Alhaji Mustapha a ɓoye, ɗan jim ya yi sannan ya ce "Ka bari kawai Abdul karambanin yarinyar nan ne ya sa ta buɗe kayan mahaifinta ta ɗauka duk da ta san ba na babanta ba ne amma ta dauke shi." Kwafa Abdul ya yi ya miƙe tsaye ya ce. "Ka yi haƙuri Dad zan dawo maka da kayanka gobe ko jibi zan je gidan nata ta ba ni na kawo ma." Ya faɗa yana wucewa bai ma tsaya ya saurari mai zai faɗa masa ba.. Dariya suka sa suna tafawa shi da Jarmai, sai da ya jima da fita sannan Jarmai ya ce "Amma ai ba mu tambaye shi takardun ba." "kwantar da hankali Jarmai ai a hankali za muke amso komai har mu gama mu aika shegu lahira." Dariya suka kuma sawa suna tafawa... _NIGER_ zaune suke a harabar gidan daga can gefen part ɗin Mamma, Ikilima ce da Iman sai masu Hidima suna ta musu fifita su kuma suna hira. Ikilima ta miƙe ta ce tana zuwa za ta dauko wani abu ta wuce. Kamar daga sama ta ga an tsaya a gaban su, ɗago kai Iman ta yi ta kalle ta tun daga kan ƙafafu har zuwa fuskarta da take a daure, sosai ta ji gaban ta ya faɗi amma ta dake ta ce "Malama ba ki iya Sallama ba ne?" Wani irin Abu Fauziya ta ji ya zo mata wuya, ita wannan ƴar ficikar yarinyar za take ce mata ba ta iya sallama ba? A fusace ta ce "Ai na ga nan ɗin gidan Ubanki ne." Wani irin ɓacin rai ne ya ziyarci zuciyar Iman jin an zagar mata uba, kallon banza ta watsa mata ba ta ce mata komai ta kawar da kai, hakan da ta yi ba ƙaramin fusata Fauziya ya yi ba ta ƙunduma mata ashar ta kori hadiman duk suka bar wajan daga ita sai ita. Miƙewa tsam Iman ta yi ta sa takalmi tana ƙoƙarin wucewa ta ji an damƙo ta, da sauri ta kalle ta ta sa hannu ta kwace tana huci gaban ta sai dukan uku-uku yake na tsoron Fauziya amma a fili ta dake ta nuna babu wannan tsoron. Ɗagowa ta yi da nufin yin magana ta ji saukar mari tas! Tas! Tas! A kumatunta, a firgice ta ɗago ta kuma ƙara mata wani, ƙara Iman ta kwalla ƙara jin zafin marin ya gama mata jiki.. Suhal da ke ƙoƙarin isowa wajan ya ji ƙaran Iman hakan ya sa ya tako da hanzari dan ya ga meke faruwa da ita, a kan idanuwansa Fauziya ta yi wa Iman mari na hudu kamar wani zaki sai ga shi a gaban su yana huci. Da sauri Fauziya ta saki Iman tana zaro idanu tuni jikinta ya hau rawa tun kafin ma ya ce mata komai, Iman da ta gigice ta yi baya za ta faɗi ya yi saurin taro ta ta faɗo kan shi. Jin ƙamshin turaren sa ya sa ta saki kuka tana ƙanƙame shi ya ƙara shigar da ita yana cewa "Yi shuru gani na zo yau sai na ga wanda ya daure mata gindi har ta sa hannu ta dakar min ke.." Da sauri Fauziya ta juya za ta gudu ya daka tsawa tare da sa ƙafa ya taɗe ta faɗi tim, Ikilima da ta dawo ta ga abin da yake faruwa sai ta amshe Iman daga hannunsa tana cewa "Wallahi Yaya in ba ka rama wa Iman abin da ta mata ba ba ka cika mijin kwarai ba." Tana faɗin haka ta ja Iman suka koma gefe. Kan ta ya yi gadan-gadan yana zare bal ɗin jikinsa cikin tsananin ɓacin rai.... 😂Iyar Haidar, Mom Islam ku zo ku raba faɗa 🙃 _Maman Nusaiba ce_ [6/20, 8:43 PM] Ummu Amjad: ~A HAKA NAKE SON SHI~ Shafi na (37) Yana isa bai tsaya yin komai ba ya dinga zabga mata bal ɗin ba ji ba gani, ihu take tana faɗin "Waiyo don Allah ka yi haƙuri Yaya Suhal ba zan sake shiga harkar ta ba." A mugun fusace ya yi bol da ita ta saki wani irin ƙara na azaba saboda da yadda ya daki kadon bayanta da ƙafa, damkar ta ya yi yana daka mata tsawa sai ga ta ta tsaya ƙyam akan ƙafafunta sai rawar jiki take. Wani irin kallo yake bin ta da shi mai cike da tsantsar tsana yana huci kamar namijin zaki, jefar da bal ɗin ya yi ya nuna ta hannu ya ce "Wallahi ko da wasa na sake ji ko gani kin harari matata sai na canja miki suffar jiki, ke yanzu ko cewa aka yi ki ɗaga wannan banzan hannun naki ki mari matata sai ki yi?" Kwafa ya yi ya juyo ya kalli su Iman da har yanzu kuka take tana rakuɓe a jikin Ikilima, tsaki ya ja ya ce "Yadda kika daga hannu kika dake ta sai ta rama." Ya faɗa yana nufar Ikilima ya kamo ta ya tsayar da ita a gaban Fauziya. Idanu Iman ta daga ganin Fauziya ya sa ta kwalla ƙara ta yi saurin faɗawa jikin Suhal tana ci gaba da kuka ta ce. "Yaya ni ka ɗaukeni mu tafi wajan Mamma wannan muguwa ce." Ta faɗa tana ƙanƙame shi. Ɗago da fuskarta ya yi ya sa ɗayan hannun ya raba ta da jikinsa, cikin ba da umarni ya ce "My Iman ɗago ki kalle ni da kyau, yadda ta mareki kema ki rama yanzun nan." Saurin komawa jikinsa ta yi tana girgiza kai ta ce "A'a ni dai mu tafi tun da ka rama min." Ta faɗa tana dira ƙafa. Kallon banza ya watsa mata ta sunkuyar da kai tana rawar jiki, wutar tsanar Iman na ƙara ruruwa a zuciyarta ta kuma ci alwashin rama duk abin da Suhal ya mata a kan ta.. "Maza ki wuce an jima ki saurari abin zai biyo baya shashasha jaka aladiya wadda kanta babu komai sai tarin iskaci da wulaƙanci." Sim-sim ta wuce tana dafe bayanta da yake mata azabar ciwo, ganin ta tafi ya ɗauke ta cak ya nufi ciki da ita yana jin haushin abin da aka mata.. Duk abin da ya faru akan idanun Jakadiya har sai da ta ga sun tafi sannan itama ta tafi da sauri har tana haɗawa da tuntuɓe. Ko da suka shiga daret ɗakinsu ya nufa da ita yana jera mata sannu har suka isa ciki, aje ta ya yi ya shiga toilet ya haɗa mata ruwan zafi sannan ya fito ya same ta kwance kan capet, da sauri ya iso ya tsugunna ya kai hannu ya shafo fuskarta da satin yatsun Fauziya suka kwanta a kan kyakkyawar kumatunta.. Lumshe idanu ta yi tana jin yana kiran sunan ta amma ta yi shuru kamar mai bacci. Ganin haka Suhal ya tankwashe ƙafafu ya ɗago da ita ya kwantar da ita a kan cinyarsa tare da sunkuyo da kansa ya soma hura mata iskar bakinsa. Turo baki ta yi tana buɗe idanuwanta akan kyakywar fuskarsa da take a dame duk ya shiga yanayi, shagala ta yi da kallon shi tana yin raurau da idanu ya riƙe hannunta cikin sanyin murya ya ce "Am so sorry my Beauty in sha Allah ta yi na farko ta yi na karshe kin ji." Ya faɗa yana murza hannunta cikin tausayawa. Kwaɓe fuska ta yi ta kai hannu ta zagaye bayansa jin wani sanyi na shigar ta, dankwalin kanta ya saɓule ya shiga shafa lallausan gashinta baƙi siɗik, lumshe idanu ta yi tana ƙara yin luf jin wani ɗumi mai daɗi na shigarta.. Hannu ya kai ya taɓa wuyanta ya ji shi rau ya yi saurin ɗaukewa yana ɗago da ita ya ce. "My Iman ba ki da lafiya ne? " Ya faɗa yana tallafo fuskarta ya tsare ta da kallo. Hawaye ne suka silalo mata ta buɗe idanu cikin rawar sanyi ta ce "Ya.. Yaya ka rufeni sanyi nake ji har kaina ciwo yake." Ta faɗa tana kwantar da kanta a ƙirjinsa ganin yaƙi sakar mata fuska ballantana ta koma ta kwanta. Nisawa ya yi yana bubbuga bayanta ganin ta soma mutsu-mutsu, juyin da take ne ya ƙaru hakan ya sa ya ce "My Iman bayan zazzaɓi da ciwon kan ina yake miki ciwo? Sannan tun yaushe kike jin zazzaɓi ba ki sanar da ni ba?" Ya faɗa a ruɗe. Kuka ta sa masa tana yarfa hannu jin ciwon na ƙaruwa ta tashi zaune ba shiri ta dafe cikinta, juyar da kai ta yi suka haɗa idanu ta ce "Yayaaa." Ta ja sunan tana mayar da numfashi. Amsawa ya yi yana riƙe ta sai tambayar ta yake ina ne ke mata ciwo, sai da ta yunƙura za ta tashi ta ji cikinta ya murɗa ta kwashi salati tana yarfa hannu cikin azabar ciwo ta ce "Yaya cikina ciwo, waiyo zan mutu Yaya ka kaini wajan Umma na ni dai." Ta faɗa a gigice. Da hanzari ya tashi ya dauke ta ya nufi gidan ƙasa, stap bibiyu yake tsallakewa sai ga shi a palon ya zarce ɗaki ya kwantar da ita, inda kayan aikinsa suke ya nufa ya dauko abin gwaji ya soma gwada ta. Da farko taƙi ya taɓa ta ganin yana son cire mata rigar jikinta har sai da ya lallaɓata ta yarda ya zarge zip ɗin rigar. Bayan ya gama ya dauko allura ya ja ruwa ai kuwa tana ga allura ta zabura za ta gudu ya damƙo ta ya matse, kuka take tana ƙoƙarin kwacewa amma ta kasa saboda da yadda ya riƙe ta bai mata da wasa ba, ya tsira mata allurar ta ƙanƙame shi tana fadin "Mugu azzalumi." Sai da ya gama mata ya yi murmushi ya ce "Raguwa kawai, ke ba ki da lafiyar ma ba za ki daina rashin kunya ba?" Murguda masa baki ya yi tana kai masa duka ya kauce yana murmushi, tana cikin yi masa mita ta ji amai ya tafo mata ta yi saurin tashi daga jikinsa ta soma ƙoƙarin sauka a gadon, da sauri ya kamo ta a zaton shi gudu ne za ta yi. Raurau ta yi tana dafe kirji ta rufe bakin amma yaƙi sakin ta kawai ta miko kanta bakin gadon ta shiga kwara amai kamar za ta amayar da kayan cikinta. Sai da ta gama yana riƙe da ita sannan ya dauke ta ya yi toilet da ita, wanka ya mata tana kuka tana ce masa ba shi da kunya shi kuma ya ce ya ji ɗin da haka suka fito. Shiryata ya yi a cikin wasu riga da wando masu kauri pink color kayan sun yi matuƙar dacewa da farar fatarta, mai ya shafa mata duk tana lafe a jikinsa tana masa mita yana rarrashin ta da haka ya shafe ta da mai ya dauke ta ya bi ta gefen da babu aman ya kwantar da ita tare da lulluɓe ta a wani tattausan blanket. Wajan ya shiga gyarawa wayarsa da ke gefen Iman ta soma ringing, bai bi takan wayar ba ya ci gaba da abin da yake amma hankalinsa na kan ta duk motsin da ta yi akan idanuwansa. Sai da ya gama gyara ko'ina sannan ya hayo gadon ya dauki wayar, ganin Mai martaba ne ke kira sai ya kalli Iman yasan dalilin kiran ba zai wuce na abin da ya yi wa Fauziya ba, dogon tsaki ya ja baya son ya tashe ta ganin ta fara bacci amma ba yadda ya iya ya yaye blanket ɗin ya dauki hijab ya sanya mata ya dauke ta suka fito.. A tsaye ya ga Jakadiya tare da Ikilima ya dire Iman, sai a lokacin ta buɗe idanuwanta ta ganta a palon Mamma ta ɗan gyara tsayuwa tana kallon Ikilima da ta haɗe girar sama da ƙasa. "Ranka ya daɗe Mai martaba yana son ganin ka a ɓangarensa." Kallon Iman ya yi da take lumshe idanu ya ƙara daure fuska ya dawo da kallon shi kan Jakadiya hakan ya sa ta yi gaba da sauri, a baya suka bi ta zuwa kiran Mai martaba yana riƙe da ita suna tafiya a hankali har suka isa ɓangaren Mai martaba.. _NIGERIA_ Tun safe Abir da Zaiyan suke harabar gidan suna ta wasa, ƙasa ya kwaba ta biye masa suka yi gida duk sun ɓata jikinsu. Sai da suka gama komai ya kama ƙugu sai kuma ya zauna a gaban gidan ya ce. "Anty wannan shi ne dakinmu." Ya faɗa yana nuna mata ɗaki da toilet da shi da kansa ya yi, murmushi ta yi ya nuna dakin na gaba ya ce. "Wannan kuma na Baba da Inna ne, ɗayan kuma in na sayo ɗiya mai kyau irin ta kallo-kallon palon Inna zan aje ta a wannan ɗakin." Ya faɗa yana karkaɗe hannunsa a jikin rigarsa.. Ƴar dariya ta yi tana kallon inda ya ce na ɗiyar da zai samu musu ne, ganin ta yi shuru ya zagayo ta bayan ta ya rungume ta yana sauke numfashi ya ce "Anty zan ci abinci." Lumshe idanu ta yi tana jin saukar numfashinsa na sauka a dokin wuyanta, ajiyar zuciya ta sauke da kyar ta ce. "To tashi a jikina muje ciki sai na zuba ma abincin." Ta faɗa tana miƙa hannu ta tabo fuskarsa. Dagata ya yi ya tsaya yana jiran ta tashi, mikewa ta yi tsaye ta ji ƙaran hon sai ta cika da mamakin waye yake musu hon? Maigadi ya buɗe masa get ya shigo ciki tare da paka motar, shuru Abir ta yi tana kallon motar gaban ta na dukan uku-uku ganin wanda ya shigo, shin me ya zo yi a gidan nan? Ko dai cin mutumcin da sama yi mata ne ya biyo ta har gidanta zai mata? Sunkuyar da kai ta yi ganin ya fito ya nufo inda suke. Wani kallon banza yake watsa mata ya tsaya a gaban ta tare da jan tsaki ya ce. "Ke!" A firgice ta ɗago ta kalle shi fuskar nan babu alamar rahama a tattare da shi, nusunawa ta yi cikin ɗauri-ɗauri ta ce "Yaya barka da zuwa." Bai amsa mata ba sai tambayar da ya jefo mata, "Baby ina ma'adanar bayanan da kika dauka a kayan Abie? Sannan ina takardar da ke wajan ki?" Ya faɗa cikin tsawa-tsawa. Cikin rashin fahimta ta ɗago kai ta kalle shi ta ce "Yaya wacce takarda da ma'adanar bayanai kake magana?" A tsawace ya ce "Ok tambaya ta ma kike saboda ba ki da kunya?" Nan-da-nan idanunta ya cika da kwalla ta rausayar da kai ta ce "Wallahi ni Yaya ban san akan wata takarda kake magana ba." Iya fusata Abdul ya fusata jikinsa har tsuma yake ya daka mata tsawa ta ja da baya a ruɗe, biyo ta ya yi ya sabga mata mari cikin ƙaraji ya ce. "Ina takardar da kika dauka? Za ki fito min da su ko sai na miki dukan tsiya?" Dafe kunci ta yi a gigice ta yi baya za ta faɗi ta ji an tare ta ta faɗa kan wani abu..... _Maman Nusaiba_ [11/18, 9:28 Yamma] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): ~A HAKA NAKE SON SHI~ *Bonus fage* Shafi na (38) Runtse idanu ta yi sai ta ji ya ɗago da ita yana huci, a hankali ta buɗe idanu ta sauke shi akan shi yana kallon Abdul da ya yi tsaye a gaban su yana hura hanci. A fusace Abdul ya tako ya iso gaban su cikin ba da umarni ya miƙa hannu tare da cewa "Maza bani kafin na kakkarya ki." Matsawa Zaiyan ya yi ya koma gefe ya yi shuru yana kallon su, ganin ya saki hannunta ta ja da baya tana girgiza wa Abdul kai ganin yana ƙara kusanto ta, hakan da ta yi ya ƙara tafasa masa zuciya iso ya damƙo ta ya tura ta can ta yi baya ta faɗi akan hannunta. Ƙara ta ƙwalla tana birkitowa ta juya cikin tsananin azaba, ganin ya sake yowa kanta ta dinga ja da baya tana fashewa da kuka, ganin shi take tamkar zaki sai rawa jikinta yake, hannu ya miƙa mata ya ce "Idan na ƙyirga uku ba ki ba ni takardar nan ba sai na kashe ki na kashe banza a wajan nan." Ya faɗa yana sake kai mata duka ya ji an yi carab da hannun nasa. Da mamaki yake kallon Zaiyan da jijiyoyin kansa suka tashi idanuwansa suka yi jajur kamar an ɗiga masa jini, wani kalar huci yake fitarwa yana ƙara matse hannun Abdul ya sa ɗayan hannun ya kai masa naushi a baki, nan take bakin ya fashe sai jini ya dinga biyowa ta gefen bakinsa. Idanu rufe ya ƙara murda hannun Abdul sai huci yake ya tsare Abdul da idanu, Abdul jin azaba ta mamaye shi ya ɗaga hannunsa ɗayan ya kai wa Zaiyan naushi nan ya yi caraf da hannun, baya-baya ya dinga tura Abdul har sai da suka isa bishiryar mangwaro ya jingine shi yana fadin "Me ta maka kake dukan ta? Yau sai na maka duka tun da ka daki Anty." Ya faɗa yana kai masa duka ta ko'ina. Duk yadda Abdul ya kai ga ƙoƙarin kwacewa amma sam ya kasa saboda yadda Zaiyan ya yi masa matsar da duk ƙarfin da yake ji da shi ya kasa kwatar kansa a wajan shi. Da kyar ta miƙe tana yarfa hannu ta ɗingisa ta nufe su ganin yadda yake dukan Yayan nata, tana isa ta miƙa hannu za ta taɓa Zaiyan sai kuma ta fasa zuciyarta na ba ta umarnin ta bari ya masa dukan sakwara, ganin dai zai yi kisan kai ta miƙa hannu da kyar ta ce "Zain please ka rabu da shi Yaya ne fa." Ta faɗa tana kama damtsen hannunsa. Cak ya tsaya da dukan nasa zuwa lokacin Abdul ya yi laga-laga sai fitar numfashi yake a wahalce, amma duk da hakan bakinsa bai mutu ba sai cewa yake "Wallahi Baby in ba ki bani takardun da na buƙata a wajan ki ba sai na kashe ki." Ba ta kula shi ba ta lallaɓa Zaiyan ya matsa daga gefen shi, goge hawaye ta yi zuciyarta na mata zafi wai yau ita ce Abdul ke furta mata kalmar zai kashe ta, durƙusawa ta yi a gaban shi ganin ya yi ƙasa ya zauna ba shiri. Kamo hannunsa ta yi Zaiyan da ke bayan ta ya buge hannun yana turo baki ya soma jan ta, turjewa ta yi ta sa masa kuka tana girgiza kai, hura hanci ya yi sai kuma ya sake ta shi ma ya rushe da kuka ya zauna a gefenta yana kallon Abdul kamar yadda itama take kallon sa. Hannun Abdul ta riƙe cikin raunanniyar murya baki na rawa ta ce "Ya.. Yaya don Allah ka yafe min in lefi na maka wanda har ka tsaneni haka, ban san akan wasu takardu kake magana ba ni babu komai a wajena. Ko a mafarki aka ce min irin wannan ranar za ta riskeni zan ƙaryata, sai ga shi wai yau Yaya ni kake duka kamar ka kama mai lefi why Yaya? Ashe ba za ka riƙeni amana ba kamar yadda Mom ta bar ma? Anya kana cikin haiyacinka kuwa Yaya?" Ta ƙarashe maganar tana ci gaba da kuka.. Wani irin nauyi ya ji zuciyarsa ta masa, har ya miƙa hannu zai taɓa nata ya ji wani abu ya danne wannan yanayin da ya taso masa nan da nan ya janye hannun, tashi ya yi da kyar yana jan ƙafa ya isa bakin motarsa ta yi saurin tashi duk da tana jin ciwo ta daure ta runtse idanu ta take ƙafar ta nufi motar, ganin haka shi ma Zaiyan ya bi bayan ta ko ajikinsa sai ma saurin isa gefenta ya yi ya riƙe hannunsa. Yana ƙoƙarin tashin motar ta iso tana share hawaye ta ce "Don Allah Yaya kar ka ce za ka yi driving da kanka ka bari na kira ma Ali ya zo ya kaika." Wani irin kallo ya watsa wanda ya sa ba shiri ta ja da baya tana sakin kuka, me yake damun Yayan nata? Ko dai shi ɗin ma ya samu tabin hankali ne? Tsayar da kukan ta yi ba shiri ganin yadda Zaiyan ke tayata kamar wasu yaran goye. Shi kuwa Abdul cikin zafin rai da na zuciya ya ja motar ya nufi Get ɗin gidan duk da rawar da ƙafarsa take, amma wutar ƙiyayyar ta da ke ruruwa a zuciyarta ta mantar da shi an dake shi, da sauri Maigadi ya matsa ganin zai buge shi, shi kan shi cike yake da tsananin mamaki da al'ajabin abin da ya faru a gaban idanuwansa, dan a iya saninsa yasan Abir dai ƙanwar Abdul ce wadda ba ya son ɓacin ranta duk abin da take so shi yake mata, sai ga shi yau shi ne har da dukan ta.. A wajan ta durƙushe ta kalli Zaiyan da yi tsaye yana turo baki, tashi ta yi ta faɗa jikinsa ta ci gaba da kuka tana faɗin "Rashin uwa babban ciwo ne a rayuwa, ya Allah ka dawo min da hankalin Yayana ya daina tsana ta abin na taɓa min zuciya, Waiyo Abie na nasan da kana raye ko da duk duniyar nan za su taro su tsaneni kai ba za ka tsaneni ba, ya Allah ka dubi marainiyarka ka kawo mata mafita. " Shi kuwa ƙara rungume ta ya yi ya ci gaba da nasa kukan, sai da ya ji ta tsayar da kukan shi ma ya tsayar da nasa ta ɗago daga jikinsa tana share hawaye. Fuskarta ya ɗago ya sa hannu yana share mata hawayen itama ta shiga share masa nasa, sosai zuciyarta ke ƙara karaya da lamarin Yayan nata ta sake komawa jikinsa ta sa sabon kuka.. Wannan karon Zaiyan bai yi kuka ba sai ma ƙoƙarin raba ta da jikinsa da yake yana fadin "Anty Baba mugu ne sai na kashe shi tun da ya dakeki." Sai da ta yi mai isar ta har Maigadi ya ga abin ba na ƙarewa ba ne ya iso wajan su, runsunawa ya yi ya ce. "Ranki da daɗe wai lafiya Oga ya miki wannan ɗanyan aikin?" Girgiza kai kawai ta yi zuciyarta na zafi ta kama hannun Zaiyan suka nufi ciki, riƙe baki Maigadi ya yi yana ƙara jinjina girman abin da har zai sa Abdul ya daketa, haka dai ya juya ya koma bakin aikinsa yana jiran dawowar su Baba.. Suna shiga dakinsu daret toilet suka nufa dan zuwa lokacin ta daina kunyar cire kaya a gaban Zaiyan tun da ba wani hankali yake da shi ba da zai gane daidai da rashin daidai, cire masa nasa kayan ta yi ta tara musu ruwa mai ɗumi ta dauko sabulu ta kama hannunsa suka shige cikin bahon wankan. Lumshe idanu ta yi gabadaya kanta ya yi nauyi ƙwaƙwalwarta ta cunkushe, ajiyar zuciya ta sauke tana yin hamdala da wannan lamari ya faru su Baba ba sa gidan.. Sai da suka yi ta wasa da kumfa ita da shi sannan ta cuɗa shi shi ma ganin yadda ta masa ya dauki sabulun ya cuɗa ta, bayan sun gama ta sa masa towel sai dariya yake ya iso bakin madubi sai ya waro idanu yana dariya ya kama hannun Abir ya janyo ta iso kusa da shi ya nuna mata da hannu ya ce "Anty kalli shi ma Abokina ya sa irin wannan abin da kika sa mini." Sake kallon madubin ya yi sai ya ga Abir ai kuwa ya ɗaga hannu zai kurma ihu ta yi saurin rufe masa baki ya kwashe yana nuna mata ya ce "Shege Abokina ashe shi ma har yana da mama ga ta nan irin Anty." Ganin abin nashi ba na karewa ba ne ta kama shi suka fito, mai ta shafa masa ta miƙa masa kayansa ya yi tsaye yana bin kayan da kallo yana taɓe baki, girgiza kai ta yi ta shirya shi da kanta saboda tasan hali indai yaƙi amsa to ba zai sa ba sai dai ita ta shirya shi. Fuska ta hɗe alamar ta yi fushi da shi, ganin ta yi fushi sai ya sa iso gaban gadon ya zauna a ƙasa irin na ɗa da uwa. Kallon shi ta yi ganin yadda ya rausayar da kai sai ta ji ya ba ta tausayi sosai, hannu ta miƙa masa ya yi saurin tashi ya hayo gadon ya yi zaune yana kallon ta, murmushi ta yi ta ja da baya ta jingina da jikin gadon ta buɗe masa hannu ya yi saurin zuwa ya lafe a jikinta yana sauke ajiyar zuciya. Kamar wani yaro ta shiga bubbuga bayansa cikin ɗan lokaci sai jin saukar numfashinsa ta yi alamar ya yi bacci, a hankali ta lallaɓa ta kwantar da shi ya motsa ya ƙara riƙe ta sai ta kwanta har sai da bacci ya kama shi gadan-gadan ta raba shi da jikinta ta sauka a gadon ta rufe shi da bargo ta fita. Wajan Maigadi ta isa ta ce masa kar ya sake ko da su Baba sun dawo ya sanar da su zuwan Abdul da abin da ya faru a tsakanin su, to ya ce mata ba dan ya so ba sai dan ganin yadda ta marairaice sai ta ba shi tausayi. Godiya ta masa ta dawo ciki ta dinga safa da marwa a palon ta rasa ta inda za ta ɓullowa lamarin familyn nata, ganin dai lokaci na tafiya ta shiga kitchen ta ɗaura musu shinkafa da wake da miya, bayan ta gama ta gyara ko'ina ta rufe abincin ta dawo ɗaki ta samu har zuwa lokacin Zaiyan bacci yake hakan ya mata daɗi. Kayan jikinta ta canja ta ɗauro alwala jin ana kiran Sallar Azuhar, bayan ta gama Sallah ta ji sallamar Inna da Baba hakan ya sa ta cire hijab ta nufo palon. Murmushi ta yi tana isa ta amshi ledar hannun Baba ta ce "Baba sannun ku da zuwa ya hanya?" Murmushi ya yi ya ce "Alhamdu Lillah Hauwa'u ya gidan? Ina shi mutumin yake?" Tashi ta yi tsaye tana ce musu ai bacci yake ta wucewa kitchen, ruwa ta kawo musu mai sanyi suka sha. Bayan Baba ya dawo daga Masallaci ta gabatar musu da abinci, har sun fara ci sai ga Zaiyan ya fito yana sosa kai ya iso inda take ya zauna,riƙe baki Inna ta yi ta ce "Zaiyan ko ka mana sannu da zuwa ma?" Turo baki ya yi ya ce "Inna Baba ya zo ya daki Anty ni kuma na rama mata." Ya faɗa yana jumƙar shinkafar ya kai baki. Aje cokali Baba da Inna suka yi suna kallon Abir da ta tauna abinci ta kasa haɗiyewa sakamakon maganar Zaiyan, Baba ya ce "Hauwa'u shin da gaske ne abin da Zaiyan ya faɗa?" Murmushin yaƙe ta yi wanda ya fi kuka ciwo tana danne kukan da ke shirin kwace mata, hadiye abincin ta yi da kyar ta ƙara sunkuyar da kai tana boye hannunta da zuwa lokacin ya kumbura sai azabar ciwo yake mata daurewa kawai take, a hankali ta ce "A'a Baba ba haka ba ne, a ina ma ya ga Yaya a gidan nan." Ta faɗa cikin ƙarfin hali ta ci gaba da cusa abincin ba dan yana mata daɗi ba. Kallon juna Inna da Baba suka yi kowanne yana juya maganar a ransa, idanuwan Inna ne ya kai kan hannun Abir na hagu da ya kumbura sai ɓoyewa take, da sauri Inna ta kama hannun wanda sanadin hakan ya sa Abir ta zabure tana salati sakamakon ciwon da ya ziyarce ta, Inna ta ruɗe ta sakar mata hannun tana mai kare mata kallo cike da tuhuma ta ce. "Tabbas Hauwa'u akwai abin da ya faru bayan mun fita, kuma da akwai ƙamshin gaskiya a maganar Zaiyan." Ta faɗa tana aje cokalin da ke hannunta ta janye abincin daga gaban ta. Kallon Zaiyan Baba ya yi da yake ta cin abinci duk ya zubar da abincin, girgiza kai ya yi ya nisa ya ce "Lalle da gaske ne Abdullahi ya zo gidan nan, me kika masa haka har ya cutar da ke haka?" Fashewa ta yi da kuka tana tashi daga inda take ta koma gefen Inna ta kwanta a kan cinyarta, hakan ya ƙara saka su a damuwa ta shiga bubbuga bayan ta tana rarrashin ta har ta tsagaita kukan, Inna ta sake tambayar ya aka yi ta ji wannan ciwon? Sai a lokacin ta ji za ta iya magana ta tashi zaune tana runtse idanu saboda ciwon da hannunta ke mata kamar ana sassoka mata allura haka take ji, a raunane ta ce "Inna babu wanda fa ya zo gidan nan, kawai faɗuwa ce na yi a toilet shi ne na faɗi akan hannun shi ya sa ya kumbura yana min zugi, na bari ne mu gama cin abinci sai na nuna muku a kira mai gyara ya gyara min." Ya faɗa tana hararar Zaiyan da ya saki baki yana kallon ta. Har Zaiyan ya ɗaga baki zai yi magana ta yi saurin tashi ta isa gareshi tana masa murmushi ta amshe cokalin da ke hannunsa ta dinga ɗibar abincin tana ba shi a baki duk dan kar ya kuma fadin wani abu game da yayan nata, tsam su Inna sun gane ba ta son Zaiyan ya sake magana ne ta yi haka sai suka ci gaba da cin abincin. Bayan sun gama Baba ya fita ya kira mai gyara, sai da Inna ta rirrike ta aka mata soma mata gyara tana ta kukan azabam Ganin hakan da Zaiyan ya yi ya fusata ya buge hannun mai gyaran ya ce "Ka daina dukan ta ashe kaima ba ka tsoron Allah? To zan maka duka in ka sake saka Anty kuka, in ma kayana kake so ai sai ka faɗa na dauko ma na ba ka ba sai ka daki Anty ba zan ba ka." Yana fadin haka ya wuce dakin su. Mai gyara da ya gama tsorata ganin tsarkacecen matashi yana zare masa idanu sai ya saki hannun Abir, Baba ya yi murmushi ya ce "Malam Salihu ka rabu da wannan yaron ka ƙarasa gyara mata kafin ya fito, shi indai an taɓa ta to zai ce dukan ta ake." Gyaɗa kai Malam Salihu ya yi cike da mamaki, ci gaba ta yi mata gyara mata Inna ta rufe mata baki tana ce mata "Yi hakuri a ƙarasa kar ta yi ihu Zaiyan ya yi ya fito ya hana a gyara mata, dan dole ta yi gum da bakinta ta shiga juya kai sai zufa take haɗawa. Wani irin ja Malam Salihu ya yi wa hannun ai kuwa ba shiri ta kwace bakinta ta sa ƙara tana kiran sunan Mom, sakin hannun ya yi ta dinga fitar da numfashin wahala za ta tashi ya ce sai an shafa mata magani ai ƙashin gwiwar hannunta je ya goce shi ya sa aka jima ba a gyara mata ba. Lumshe idanu ta yi hawaye masu ɗumi suka silalo mata a daidai lokacin kuma Zaiyan ya fito hannunsa dauke da leda babba ɗayan leda ce babba hannun kuma takalma ne kala uku, da kallo suka bi shi har ya iso ya aje a gaban Malam Salihu ya yi raurau da idanu ya ce "Ga shi nan na kwaso ma kayan ka tafi da su duka amma karka sake dukan Anty ta yi kuka, ba ka ga yau da Baba ya zo gidan nan ba ya dake ta kawai ni kuma na rama mata. Yanzu kai za ki ji daɗi in aka daki Antynka?" Ya faɗa yana matso ƙwalla suka zubo kaɗan.. Sake da baki Malam Salihu ke kallon ikon Allah dan shi a iya sanin shi da Baba bai san akwai mai larura a gidansa ba, ganin bai ce komai ba Zaiyan ya matso kusa da shi yana hawaye ya ce " Baƙo ka dinga jin tsoron Allah ka daina dukan Anty, tun da kayan nan kake so ga shi nan na kawo ma ka dauka ka tafi ka bar mana gida." Ya yi maganar yana rushewa da kuka kamar wanda aka daka.. Mamaki da al'ajabi ne suka ƙara mamaye Malam Salihu, nisawa ya yi ya ce "To shi kenan na daina amma ka aje kayan ka yanzu zan tafi daga gidan naku." Girgiza kai ya yi ya isa gaban ta ta zuba masa idanu so take ta yi dariya amma zugin da hannunta yake ya hana ta yin hakan, hannun mai ciwo ya ɗan taɓa yana tsayar da kukan ya ce. "Anty a nan ne ya dake ki ko?." Kyale shi ta yi sai da ya sake maimaita maganar ta daure ta ce "Kwashe kayan wannan ka mayar da shi ɗaki indai ba ka so na daina ma magana." Da sauri ya kalli kayan sai kuma ya ce "Kayan baƙo ne kin ga ai ba zan daukar masa ba." Sai da aka yi da gaske sannan ya kwashe kayan yana cewa Malam Salihu ya ba shi kayan ya kai dakinsu ya ce masa e tukun ya shige dakin. Sallama ya musu ya miƙa musu maganin da za take shafawa a hannun ya tafi, itama ta tashi ta nufi ɗakin inda ta samu ya yi ɗaiɗai da kayan sawar shi, ganin ta shigo ya janyo ledar ya dinga cusawa yana ce mata ga shi yana mayar da kayan ta girgiza kai ta hau gado ta kwanta. Sai da ya gama duk shiriritar shi sannan shi ma ya iso gadon ya kwanta yana mata surutu ta yi kamar ta yi bacci har ya gaji da yin maganar bacci ya kwashe shi.... Abdul da kyar ya iya barin Layin Unguwar sai kyarma jikinsa yake dole ta sa ya tsayar da motar y kira Ali ya zo ya dauke shi. Asibiti suka nufa Doctor Hashim ya duba shi yana tambayar shi me ya same shi haka amma ya yi banza ya kyalle shi har ya gama masa bai ce da shi komai ba, shi ma sanin halin abokin nasa sai kawai ya share shi bayan ya masa allura ya yi masa sallama ya nufo gida. Tunani yake wata kalar azaba zai gana wa Abir da ta sanadin ta aka masa haka? Sosai zuciyarsa ke tafasa sai kwafa yake da haka iso gida. Ko da ya zo gidan tambayar duniyar nan Hafsat ta yi amma ko ci kanki bai ce mata ba har da kuka ta yi dan ya faɗa mata dalilin jin ciwuka a jikinsa amma ya yi kunnen uwar shegu da ita, karshe ma tashi ya yi ya shige ɗaki ya bar ta a palon. Haka ya wuni a ɗaki har dare yana ta saka da warwara ya rasa wani hukunci zai yi mata dan ya wuce, yanke shawara ya yi kawai ya kashe ta bayan ta ba shi abin da ya buƙata kawai kowa ma ya huta, dan haka y ɗauki wayarwa wajan karfe goma na dare ya yi mata dogon rubutu ya tura mata.... Kamar daga sama tana zaune bayan ta yi ruwan ɗumi ta gasa hannunta ta ga sakon shi ya shigo wayarta, hannu na rawa ta dauka a zaton ta ko hakuri zai ba ta akan abin da ya mata amma sai ta ga saɓanin haka.. _"Baby tabbas zan iya kasheki akan wannan abin, idan har ba ki ba ni ta ruwan sanyi ba to za ki ga me zai biyo baya k.._ Saurin fita ta yi tana dafe kirji cikin tashin hankali, tashi ta yi tsaye ta dinga kaiwa da komowa tana tunanin abin da za ta yi. Can dai ta janyo akwatunanta ta zuzzuba kayanta da na Zaiyan da duk abin da tasan nasu ne, bayan ta gama ta zarge ta bubbuga Zaiyan ya tashi zaune ta janyo hannunsa ya sauko. Gabadaya jikinta rawa yake ta nuna masa ya riƙe wannan duka za su tafi wani waje, murna ya dinga yi ya soma mata surutu ta yi saurin ce masa in ya yi magana ba za ta tafi da shi ba sai ya yi shuru. Hijab ta saka ta cire wayarta a caji ta dauki cazar ta suka fito a hankali hannunta ɗaya sarƙafe a jikin wuyanta ɗayan kuma ta ruko akwati tana ja a hankali har suka fito harabar gidan, ta ce ya tsaya kar ya matsa ya ce mata to ta koma cikin sanɗa ta shiga dakinta buɗe loka ta janyo takarda da biro ta soma rubutu tana zubar da hawaye har ta gama, akwatin ta janyo ta fito palo ta aje da takardar tana share hawaye ta fita.. A hankali ta buɗe get ɗin ta fitar da Zaiyan ta ba shi kayan yana fito da su waje itama ta fito ta janyo kofar a hankali suka ja akwatunan suka hau hanya suna ta tafiya... Sai da suka yi tafiya mai nisa sannan suka samu motar haya ta faɗa masa inda zai kaisu, suna tafiya tana sharar hawaye har suka iso wani hotel ya paka ta biya shi kudinsa ya fito musu da kayan ta ce zaiyan ya janyo su tafi ta janyo ɗaya suka nufo ciki. Ɗaki ta kama musu na kwana ɗaya aka kai su ta yi musu godiya, alwala ta ɗauro ta dinga sallar shi kuma Zaiyan ya zauna yana ta kallon ta karshe ma bacci ya kwashe shi. Yadda karen dawa bai runtsa ba haka Abir ba ta yi bacci ba tana zaune ta jingina da bakin gadon.. Washegari karfe tara ta yi wanka ta masa ta shirya su ta kira aka kawo musu pizza da tea suka yi breakfast, bayan sun gama suka fito da kayan su ta biya kuɗin suka tafi, sai da ta saka niƙaf. Mota ta tara suka shiga mai mota ya ce ina za a kaita, ta yi shuru ta rasa ma ina za ta faɗa masa can dai ta ce masa "Za ka iya kaimu Kano?" Girgiza mata kai ya yi ya ce "Gaskiya Hajiya ba zan iya ba amma zan kaiki tasha sai na haɗa ki da wani abokina yana zuwa Kano." Godiya ta masa suka isa tasha ya kai ta wajan abokinsa lokacin yana lodin Kano, bayani ya masa ya amshi kayan nata ya sa a bayan mota ta juyo ga wanda ya kawo ta ta ce " Na gode sosai bawan Allah ga wannan. " Ta miƙa masa dubu goma ai kuwa ya dinga mata godiya yana jaddada wa abokina ya kai ta har inda take so ya ce kar ya yi wasa wani abu nasu ya ɓata ya amsa da to, shiga motar suka yi daman ta cika mai motar ya ja suka hau hanyar Kano..... Ga duk mai son cigaban labarin nan ya nemeni ta wannan number. *+966577675904* _Maman Nusaiba [6/20, 8:43 PM] Ummu Amjad: *A HAKA NAKE SON SHI* Shafi na (39) Tun da suka shiga mota Abir kuka take tana kallon gefen hanya, kukan rabuwa da ahalinta da kuma rashin sanin inda za ta je in an sauke ta a garin Kano take. Sai da suka kusa isa Kano cikin wani daji motar tasu ta yi wani kalar ƙara ta yi gaba ta yi baya kafin ta tsaya, hankalin waɗanda suke cikin motar ya tashi ci kuwa har da Abir dan ta ma fi su firgicewa ganin inda suke tsaye, ƙanƙame Zaiyan ta yi da ya rungume ta ya kwanto da kansa bisa kafaɗarta tana mayar da numfashi. Mai motar da yaron mota suka fita dan ganin abin da ya samu motar, duddubawa suka dinga yi inda suka ga tayar motar ce ta fashe yaron motar ya dawo wajan masijojin nasu yana fadin "Ba wanda ya samu rauni duk kuna lafiya?" Ya faɗa yana shiga cikin motar tare da dudduba su. Wata mata da ke zaune a gefen su Abir ta kalli yaron motar tana haki ta ce "Wallahi sai da na suma na wucin gadi, wagga wacce irin mota ta haka? Shin dama motarku na da matsala ba ku hwada ba?" Haƙuri ya dinga ba ta tana sababi ita da mijinta har ya samu suka hakura, Abir ta yi tagumi tana jin matsananciyar faduwar gaba. Rana har ta soma sanyi anan suka yi La'asar ƙarshe ma duk fitowa suka yi kowa ya samu waje ya zauna, su kuma suna ta ƙoƙarin kunce ganin sun canja tayar ko sun tafi daga cikin dajin, ana haka sai ji suka yi ana dirowa daga kan bishiyoyin da ke zagaye, kowa ya ruɗe ganin gardawa sun fi goma tsaye gaban su fuskokinsu a lulluɓe, haka ma hannayensu riƙe yake da bindugu manya-manya sai zare idanu suke. Tsawa suka daka musu suka ce duk su zauna a waje ɗaya, wasu da rarrafe ma suka iso inda aka nuna musu, Ta Sakkwato da mijinta har sun fi kowa shiga ruɗu, Direba suka damƙo cikin rashin imani suka yi boll da shi ya wuntsila ya faɗi a kan Zaiyan da ke jikin Abir har lokacin bacci yake wanda bacci nasa ya ba wa Abir mamaki ganin hayaniyar da ake ba ta sa ya tashi ba. Ɗaya bayan ɗaya suka ce kowa ya zo ya fito da abin da yake jikinsa ko ya yi ta ransa, haka maza suka fara zuwa ana lalibe su har takalman su ake cewa su cire ko sun maƙala kuɗi a nan, bayan an gama aka kira mata wanda dukan su su shida ne, kowacce ta zo sai suce ta cire dankwali ta fito da komai na jikinta har su warwaraye da sarƙa duk sai an amshe. Ganin hakan ya sa Abir ta laliba sarƙarta wadda ta kasance ta gold ce da Abie ya saya mata a matsayin kyauta lokacin da ta yi candy, sai da Kowa ya je ita ce ƙarshe ta tashi a hankali ta kwantar da Zaiyan a dandan ƙasa ta mike ta isa wajan mai amsar kaya, ɗankunne ta ba su da sarƙarta har zoben da Abdul ya saya mata da jimawa aka ce sai ta fitar da ita, haka ta cire tana zubar da hawaye suka ce ta cire ɗankwali ko akwai abin da ta ɓoye ta cire suka ga ko kitso kan babu tukun suka ba ta umarnin tafiya. Har ta kai gwiwowinta ƙasa za ta zauna ta ji ɗaya daga cikin su ya daka mata tsawa ya ce "Shi wannan na kwancen uban wa ya ce yaƙi tashi mu lalibe shi?" Jikinta ne ya ɗauki rawa da kalle shi ta kuma kalli Zaiyan da ita kan ta baccin nasa ya dame ta, baki na rawa ta ce "Wallahi babu komai a jikinsa hasali ma ba shi da lafiya shi ya sa ka gan shi haka." Ta yi maganar tana riƙe hannun Zaiyan. Dariyar basawa babban su ya yi cikin taku irin na rikakkun gardawa ya tako ya iso gaban Abir ya tsaya tare da ɗaura bindiga a gadon bayan Zaiyan ya ce "Idan har kina so mu rabu da shi to sai dai ki zaɓi ɗaya a cikin biyun nan da zan faɗa miki, ko ki ba ni kanki mu zagaya ta can baya ko kuma na kashe shi sai ki zaɓa." Ya faɗa yana taune lips ɗin sa na ƙasa. A mugun firgice Abir ta ɗago ta kalle shi ta haɗe hannaye biyu ta ce " Don Allah ku min rai karku wannan zaraɗin ya min tsauri dayawa, idan har kuɗi kuke so zan ba ku ina da shi a jakata sai na ba ku, amma ka da ku kashe min miji Wallahi ba shi da la... Marin da ya zabga mata ne ya sa ta yin shurun dole, yana huci ya ce "Na ma fasa ba ki zaɓin dole ki amshi buƙata ta, kai gabaɗaya matan nan sai mun zagaya su dan na ga alama har bakin magana kuka samu, kai Bangis ɗauke ta ka kai min ita in na gama sai ku zo ɗaya bayan ɗaya." Yana gama fadin haka ya ja da baya ya harɗe hannu yana bin ta da wani irin kallo. Daƙas-daƙas Bangis ya nufo Abir fuskarsa kan ta abin tsoro ce, ganin dai da gaske ɗaukan ta za su yi ta kama hannun Zaiyan ta fashe da kuka tana fadin "Zain don Allah ka tashi ka ceceni a hannun waɗannan marassa imanin za su keta min haddi." Jijjiga shi take amma sam ko motsawa bai yi ba sai ma wani irin gurnani da yake kamar mai ciwon farfaɗiya in ciwon ya tashi, Bangis ya kama hannun Abir yana daka mata tsawa ya dinga janta a ƙasa tana kurma ihun kiran Zaiyan amma shuru, Ta Sakkwato ta koma bayan mijinta ta ruɗe sosai har ba ta san lokacin da ta saki fitsari ba ta soma surutai, "Waiyo Allah ka kawo mana dauki, kun ce ku na biɗar kuɗi mun ba ku yanzu kuma ku ce kowatta sai kun mata hwaɗe, wagga zalunci har ina?" Sai da Bangis ya kai Abir inda Ogan nasu ya umurce shi ya kai ta na daure ta sannan ya dawo, kuka da kururuwar kiran mijinta kawai take saboda an daure mata hannu a jikin bishiyar, wajan ta ya isa yana fadin "Yarinya idan za ki tsaya na yi abin da nake so ki tsaya, idan kuma gardama za ki min zan bi ki ta karfi da yaji sannan na kashe mijin naki har ke karan kanki zan alburushe ki." Shuru ta yi tana girgiza masa kai ya kwashe da dariya yana kai hannu ya dafa kafaɗarta da nufin ya mata kiss, ƙara ƙwalla wanda har dajin kansa ya amsa kowar muryarta ta kira sunan Zaiyan da ƙarfi a lokacin da ya zabga mata mari, a kuma daidai lokacin ne Zaiyan ya daina wannan gurnanin da yake ya buɗe idanuwansa ya tashi tsaye da sauri yana murza idanuwansa, kiran sunan shi da ta ƙara yi ne ya sa shi saurin janye hannayen daga fuskarsa ya ɗago kai ya kalli yan fashin. A zabure Bangis ya yi baya ya ɗaga murya ya ce "Oga! Oga! Damisa! Damisa!" Haka ya dinga maimaitawa yana nufar inda Ogan nasu yake. Ya kai hannu zai yaga rigar da ke jikinta cak ya tsaya jin abin da Bangis ya faɗa, afujajan ya iso yana haki ya nuna masa da hannu ya ce "Oga Wallahi Damisa na gani." Tashi ya yi tsaye yana hura hanci ya ce "Kai fa mahaukaci ne a ina kasan fuskar Damisa da har ka gane yana cikin wadannan mutanen?" Ya faɗa kamar zai kai masa duka saboda ya ci alwashin yin abin da yake so da Abir. Ganin sun shiga yin gardama a tsakanin su Abir ta saɓule ɗaurin da aka mata ta kwasa a guje ai kuwa suka mara mata baya, tana isa ta faɗa jikin Zaiyan da ya yi tsaye kamar gunki yana kallon su fuskar nan tashi a haɗe. Turus Bangis ya yi jikinsa ya dauki rawa ya ce. "Oga billazil Azim wannan Damisa ne, ba na taɓa ce ma na taɓa ganin fuskar Damisa ba shekarun baya? Kuma wannan dai shi ne Damisa." Ya faɗa yana yin baya. Wani irin kallo yake bin su da shi ya sa hannu ya ɗago da Abir ya ce "Anty waye ya sa ki kuka?" Ya faɗa yana goge mata hawayen. Da hannu ta nuna masa su Bangis ta ce "Su ne za su keta min haddi." Shuru ya yi ita kuma ta ci gaba da kuka, Ta Sakkwato da mijinta da sauran mutane duk bayan Zaiyan suka dawo kowa sai rawar jiki ya yi, kallon su ya yi cikin wata kalar murya wadda Abir ba ta taɓa jinsa da ita ma ya ce "Wa ye a cikin ku ya taɓa ta." Ya faɗa yana raba Abir da jikinsa ya nufo su. Durƙusawa suka yi Bangis ya ce "Shi kenan yau kwanan mu ya kare, tabbas wannan muryar Damisa ce." Dukan su ya dinga yi suna ba shi haƙuri suka ce za su mayar wa da kowa kuɗinsa da suka amsa, sai da Abir ta isa ta kama shi tukun ya daina dukan su ya juyo ya kama hannunta yana huci bai ce mata komai ba, ita dai da mugun mamaki take kallon shi gani take kamar ba Zaiyan ɗin ta da ta sani ba da in an taɓa ta yake birkicewa fiye da haka. Haka suka mayar wa da kowa abin da suka amsa, suna tsaye mai mota ya ƙarasa kulla ƙusa kowa ya shiga suka tayar da motar a guje suka bar dajin. Su kuwa su Bangis jikin su a sanyaye suka kutsa kai cikin dajin suna ta mamakin yadda aka yi Damisa ya shiga motar haya.. Tun da suka kama hanya ba wanda ya yi magana sai Ta Sakkwato da ke yi wa Zaiyan godiya, shi kuma tuni wani baccin ya sake yin gaba da shi. Sai tara na dare suka iso Kano, sai a lokacin Abir ta sauke nannauyar ajiyar zuciya ganin ta a cikin gari. Sauke su aka yi Direba sai da ya ga Abir ta sauko ya ja su gefe ya ce "Hajiya yanzu daga nan ina za ki je in haɗa ki da wanda suka san gari?" Sunkuyar da kai ta yi tana riƙe hannun Zaiyan ta ce "Ban san ina za mu je ba ni ma, amma dai ina neman gidan haya." Ta Sakkwato da ta iso wajan ta ji abin da take faɗa ta ce "Indai gidan haya kike so to ki biyo mu akwai ɗaki da palo da toilet wanda ba a kama ba." Shuru Abir ta yi tana tunanin wai yau ita ce za ta zauna a gidan haya, gidan ma wai ɗaki ɗaya da palo, ganin dai ba ta da wata dabara ta amince za ta bi Ta Sakkwato da mijinta su tafi, godiya ta masa ta ba shi kuɗin motarsa ya fito musu da kayan su suka tafi.. Wata motar suka dauka ta kai su har unguwar Rijiyar zaki kofar wani gida, tun da suka fito suke jin tashin kiɗa a ciki haka suka biya mai mota suka nufi ciki shi kuma Mijin Ta Sakkwato ya wuce bai shiga gidan ba.. Mata ne jere sun fi ashirin suna cashewa wasu kuma na zaune suna sha'anin gaban su sun cika gidan, wata daga cikin matan ce ta hango Ta Sakkwato da ta washe baki tana fadin "Ga Ta Sakkwato! Ga Ta Sakkwato! Maman Amal Ta Sakkwato ta dawo." Ta faɗa tana isowa gaban su. Saurin buya Zaiyan ya yi a bayan Abir ya kwanta a bayanta, murmushi kawai ta yi ta fuskanci matar ganin suna gaisawa da Ta Sakkwato. "A a, Ta Sakkwato baƙuwa kika tafo mana da ita ba?" Ta faɗa tana kallon Abir da itama ita take kallo fuska dauke da murmushi. Dariya Ta Sakkwato ta yi ta dafa kafaɗar Abir ta ce "Wallahi fa Maman Amina baƙuwa ta nai za ta kama haya a wancan ɗakin da ya rage." Dariya Maman Amina ta yi tana yi wa Abir sannu da zuwa ta amsa tana murmushi, Ta Sakkwato ta ja Abir da kayan su suka nufi wani ɗaki da ke kusan na karshe a dakunan ta ja birki ta tsaya. Kashe Dijan suka yi wani mai shigar jallabiya milk color ya ɗane hannu yana rataya jaka da kafaɗa ya tattare rigarsa daga kasa ya riƙe ya yo wajan su Abir, ya sha fauda da janbaki sau wani yauƙi yake yana taku ɗaiɗai.. Baki Abir ta saki tana kallon ikon Allah ganin namiji da kwalliya yana taunar cingam sai murguɗa mazaunai yake ga ba wani jiki gareshi ba. Yana isowa ya kalli Abir yana wani waƙine baki ya zagaya su tukun ya dawo gaban su ya riƙe ƙugu, tafi ya yi yana buga cinya ya ce "Chass Wallahi, Ta Sakkwato wannan ƴar shawalwalar tarwaɗar fa? Gaskiya ta yi kalar madara a ina kika samo ta?" Ya faɗa yana ƙara yin dariya ya juyo ya kalli matan ya kuma cewa "Jama'a taro ya tashi aci abinci a tafi gida ga Ta Sakkwato ta iso, kun ga kuwa ai in mai guri ya zo dole ne mai tabarma ya naɗe ko ba ya so." Ya kuma sa hewa suka tafa da wani saurayi da ya iso wajan.. Ta Sakkwato ta ƙara jin kanta a sama ta kalle shi tana wani ciccin magani ta ce "Ladidi minana aka yi a gidan ga da daren nan an kunna kiɗa?" "Hehehe sawa, wai kin manta da Samira ɗiyar Maman Samira jiya aka kai ta dakin mijinta?" Riƙe baki Ta Sakkwato ta yi tana gyada kai ta ce "E kuma fa haka ne, ina Tabadawa?" Sai da suka yi shewa sannan suka sanar da ita ta je wajan biki itama, ba ta sake ce musu komai ba ta shiga dakin su Abir suka bi bayan ta, sosai Abir take mamakin wannan saurayi mai suna Ladidi.. Komai ta nuna mata ta buɗe ɗakinta ta fito da wata ƙaramar katifa yar madaidaiciya ta kawo ɗakin, komawa ta yi ta kuma dauko tabarma babba ta kawo tana murmushi ta ce "Ki shinhiɗa wagga Katifa da tabarma ku kwanta kafin ki sayo, dakin a gyare yake." Murmushi Abir ta yi tana jin daɗin karamcin Ta Sakkwato, a nutse ta ce "Hajiya na gode matuƙa da wannan karamcin, idan Allah ya kai mu ki kaini kasuwa na sayo kayan amfani, amma yanzu a ina zan samu abinci mu saya yunwa muke ji ni da Mijina." Murmushi ta yi ta kalli Zaiyan da yake wasa da gashin kan Abir, kasa daurewa dai ta yi ta ce " Wai ki na nuhin wagga mijinki na?" Gyaɗa mata kai ta yi tana murmushi ta ce "E mijina ne shi ba shi da lafiya ne." Tashi tsaye ta yi ta leƙo ta kira Ladidi ya iso ɗakin da sauri yana dafe kirji wannan karon ya ɗaura zani a samar kayan, wani kalar maƙale hannu ya yi yana rausayar da kai ya ce "Haba Hajiya wannan kira haka ai sai ki yi wa masoyina asara, tsakani da Allah muna can muna zuba soyayya sai ki kwalla min wannan kira kamar Maigadin gidanki?" Tsaki Ta Sakkwato ta yi tana hararar Ladidi ta ce "Dalla can gafara! Ni ba wani ɗumi na ce ka yi min ba ka amshi kuɗi ka sayo wa baƙuwa abinci dan nasan ba lalle yau kun yi ba." Ta faɗa tana kallon Abir ta miƙa mata hannu ta ce "Minana sunanki yarinyar ga?" Jim ta yi tana tunanin wani suna za ta ce, can dai ta kalle ta ta ce "Sunana Jiddo." "Ahayye ayiriri nanaye Allah na dawo in ji ɗan yawon duniya caɓas! Wallahi ana yi ina jin sugar ke ban mu tafa Jiddo wannan suna naki yi ya zau kamar Maggi Onga a miyar kuka Chass ni Ladidi." Ya ƙarashe maganar yana miƙa wa Abir hannu. A kufule Ta Sakkwato ta ce "Ni Ladidi daɗi na da ke shisshigi, meye na wani cewa ta ba ki hannu?" Baki ya riƙe yana fadin "To fa ikon Allah na kwance ya tashi! Hajiya daga harkar arziki sai cibi ya zama ƙari, ƙari ya zama ƙababa? To kin ga Jiddo ba ni kuɗi na sayo muku abinci kar Hajiya ta yi min ƙazafi." Murmushi Abir ta yi dan ita a iya rayuwarta ba ta taɓa ganin ɗan Daudu ba eyes to eyes sai yau, kuɗin ta ba shi dubu biyar ta ce ya sayo mata har da karton ruwa na gora mai sanyi, juyi Ladidi ya yi ya dauko shoki ya dire tare da cewa "Wannan kuɗin na abicin ne ki kawo na ruwan." Dubu biyar ta ƙara masa ta ce ya sayo mata komai kuma ya yi sauri mijinta kar ya yi bacci, shewa ya yi sannan ya fita. Kama baki Abir ta yi tana bin kofar da kallo, tashi ta yi ta shinfiɗa katifar ita kuma tabarmar ta shinfiɗa a gaban katifar. Tashi ta yi yana biye da ita suka shiga bandaki, wani irin wani ne ya bigi hancinta ta yi saurin matsewa tana yowa baya, sai da ta jima sannan ta ja shi ta shiga tana done hanci kamar za ta yi amai haka dai ta daure ta yi alwala shi ma ta masa suka fito. Kayan su ta buɗe ta canja wani ta sa hibaji sai ta kasa bambance ina ne ƙibila, leƙowa ta yi ta ga Ta Sakkwato na ta sababi ta tambaye ta ina ne ƙibila ta nuna mata tukun ta koma ciki.. Bayan ta gama sallolin ta tana zaune sai ga Ladidi da kaya, sannu ta masa ya amsa ya miƙa mata abinci da ruwan tare da ba ta sauran canji, godiya ta masa ya tafi.. Abincin ta aje musu amma fir Zaiyan yaƙi cin abicin sai ya kwanta a cinyarta, sosai abin ya dame ta ganin yau ba su ci komai ba tun safe sai yanzu amma ya ce yaƙi ci, haka dai ta ci kaɗan ta rufe. Wayarta ta dauko ta buɗe nan da nan kiran da aka mata wayar na kashe ya dinga nuna mata, Baba ya mata kira ya fi goma, Hafsat ta mata kira 6, Iman 4 sai Suhal da ya mata biyu. Duddubawa take ko za ta ga na Abdul amma ba ta gani ba sai sabon text message da ya turo mata wanda tana shiga ta ga yadda aiko mata munannan kalamai wanda wasu ƙwaƙwalwarta ta kasa ɗaukan su sai share hawaye take, na ƙarshe har da barazanar zai ce ta yi kisan kai. Ta zaro idanu tana fita a number. Ba wanda ta yi gangancin kira ko yi masa reply ta kashe wayar ta tashi Zaiyan daga kan cinyarta suka nufi ɗaki, haka ta dinga juyi tana kuka bacci ya kaurace wa idanuwamta.... _Maman Nusaiba ce_ [11/20, 10:13 Yamma] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): *A HAKA NAKE SON SHI* Shafi na (40) Kiran Sallar assalatu ne ya tayar da Abir daga baccin da ya shure ta, a hankali ta buɗe idanuwanta ta yunƙura za ta tashi ta ji ya kanannaɗe ta, idanu ta zuba masa tana kallon kyakkyawar fuskarsa mai kewaye da baƙin saje, hannu ta kai ta shafa fuskar tana ɗan bubbugawa ko zai tashi. Juyi ya yi a kanta ya gyara kwanciya yana ƙara matse ta kamar ya samu pilo, runtse idanu ta yi jin zafi ta sa hannu ta soma ƙoƙarin ɓamɓare shi daga jikinta amma ta kasa, mintsinin shi ta yi a wuya ya buɗe idanunsa tar a kanta, turo baki ta yi tana faɗin "Ka tashi mana mu yi Sallah an fa kira." Shi ma turo nasa bakin ya yi kamar yadda ta yi ya tashi daga kanta ya koma gefen ta ya kwanta yana taɓa gashin kanta, harara ta aika masa ya yi saurin janye hannun ya tashi zaune yana shafa inda ta mintsile shi kamar zai yi kuka, itama ta tashi ta zaune ta kama hannunsa ganin yadda ya yi kicin-kicin da fuska ta sakar masa murmushi ta ce "To yi haƙuri ba zan kuma yi ma ba." Shi ma murmushin ya mata ta tashi riƙe da hannunsa yana biye da ita suka shiga toilet, wanka ta yi niyar yi sai ta tuna ko soso ba ta da shi bare sabulu, dafe kai ta yi suka yo alwala suka fito.. Bayan sun gabatar da raka'atainun fajur suka zauna ta ɗaga hannu tana ta kwararo musu addu'a shi ma yana maimaita abin da take faɗa, sai da ta ji ana tayar da iƙama sannan ta shafa ta tashi suka yi Sallar. Bayan sun gama Zaiyan ya saka ta a gaba yana kallo, gaban ta ne ya faɗi sosai ganin yadda yake kallon ta kamar mai nazartar wani abu, can dai ya matso kusa da ita ya zauna har suna jiyo numfashin juna ya marairace ya ce "Anty yunwa nake ji." Ya faɗa yana riƙe ciki. Abicin su na jiya ta janyo ya yi sanyi sosai kasancewar sanyi ya fara shigowa ta tura masa, da sauri ya sa hannu ya jimƙa zai kai baki ta yi saurin riƙe hannun ta ce "Ka ce bismillah." Dariya ya yi ya faɗi sannan ta sakar masa hannun ya soma cin abincin, tagumi ta yi tana kallon shi yadda yake cin abincin sai ya birge ta, dan haka ta janyo wayarta ta kunna ta dinga masa vidéo bai sani ba, sai da ya gama cin abincin ya haɗe hannayensa ya musu kamar shafa mai, maimakon ta ji haushin abin da ya yi sai kawai ta yi murmushi tana girgiza kai ta aje wayar, kafin ma ta yunkura tuni ya goge hannun nasa a jikin rigarsa, dafe kai ta yi ta kalle shi ganin yadda ya ɓata rigar, ba ta rabu da jimamin abin da ya yi ba sai gani ta yi ya sake mayar da hannu ya kwashe sauran abincin da ya bari ya cinye, wannan karon kuma a fuskarta ya goge hannunsa yana dariya. Takaici da ya mata yawa kawai sai ta fashe da kuka tana kallon shi, da sauri ya matso kusa da ita ya ce. "Anty wa ya sake ki." Buge masa hannu ta yi tana tsayar da kukan jin hayaniya a tsakar gidan, tashi ta yi ta kama shi suka shiga banɗaki ta wanke masa hannu ya wanke bakin itama da wanke fuskarta sannan suka fito. Kwashe kayan ta yi ta zuba a ledar da aka sayo mata abincin ta aje gefe ta janyo gorar ruwa ta buɗe ta miƙa masa, amsa ya yi ya shanye tas har da lumshe idanu yake sai ta ji ya mugun ba ta tausayi, rabon da ya sha ruwa tun jiya da safe a hôtel, tuna abin da ya faru jiya ya sa ta yi tagumi tana hasaso komai da ya wakana a yammacin jiya. Kenan da Allah ya ba wa 'yan fashin nan rana da tuni sun yi mata faɗe ko ma ta mutu in kwanan ta ya ƙare? To amma ya aka yi suke kiran Zaiyan da Damisa? Shin ko dai dama can sun san shi ne? Tambayoyin da take juya su tana kallon shi yadda ya yi wata kalar murya a jiya shi ya fi matuƙar saka ta kokwanto da kuma al'ajabi, nisawa ta yi ta gyara kwanciyarta shi kuma yana zaune a kan dabarmar yana surutu shi kadai. Tashi shi ma ya yi ya kwanta a gaban ta yana matsa ta can baya ta kai masa duka a gadon baya, daina tura ta ya yi ya juyo suka yi facing ɗin juna ya ƙura mata idanu, saurin rufe idanu ta yi shi ma ganin haka ya rufe nashi... Karfe 11:Pm na rana suka farka sakamakon kwankwasa ƙofar da ake yi, ɗankwalinta ta zara ta ɗaura ta bude ƙofar , Ta Sakkwato ta gani tsaye bakin ƙofar tana gyara zaman mayafi ganin ta ya sa ta saki murmushi ta ce "Haba Jiddo kwanan ai ya isa haka ki shirya muje na kaiki ki sayo abin da kike so, ko kuma Ladidi ya miki rakiya?" Ta faɗa tana kallon Ladidi da ya iso shi da ƙawar shi cikin shirin fita. Girgiza kai ta yi tana ɗan murmushi ta ce. "A'a Hajiya mu tafi da ke kin ga shi fa namiji ne ni kuma matar aure ce bai kamata ya rakani ba." Riƙe baki Ladidi ya yi yana kallon Abir ya ce. "To sabon salo lalle a mazaunai, ni 'yasu ! Yanzu ke saboda rashin girmama ɗiya mace haka za ki dinga dangantani da namiji gatsal haka? Gaskiya Ta Sakkwato ki faɗa mata in tana so a gidan nan mu shirya da ita ta daina ce min namiji ehe, dan Wallahi ba ƙaramin aikina ba ne in yi ɗamara mu ba hamata iska." Ya faɗa yana turo ɗankwalli gaba.. Murmushi Abir ta yi ta ce "Allah ya ba ki haƙuri Ladidi." Farr ya yi da idanu ya gyara zaman handbag ɗinsa ya ce "Ba komai ai ke kin shigo da ƙafar dama." Komawa ta yi ciki ta canja kaya ta canja wa Zaiyan suka fito tana riƙe da hannunsa, matan gidan duk suka bi da kallo ta kawar da kai tana kallon Ta Sakkwato da take fitowa daga ɗaki, Maman Amal ta kalli Maman Samira ta ce "Ke anya kuwa wannan sabuwar matar da aka kawo mana ba mai girman kai ba ce? Kalli fa yadda take wani daure fuska ko gaishe mu ba ta yi ba." "Hmm na ga alama gaskiya Maman Amal amma dai kar mu yanke hukunci." Ƙarasowa ta yi wajan su duk suna kallon ta ta ɗan nusuna ta ce. " kun tashi lafiya ya yara?" Washe baki suka yi duk suka amsa da lafiya ta juya tana riƙe da hannunsa, wannan karon bai kwaikwaye ta gaisuwa ba sai ma shuru da ya yi yana kallon su. Maman Samira ta kalli bayan su ta ce. "Kut! Lalle Allah mai halitta, ke Maman Amal kin ga wani santalelan matashi mai jini a jika, anya ma wannan ba balarabe ba ne?" Itama Maman Amal shi take kallo har suka bar gidan... Mai adaidaita suka tare suka shiga ta ce ya kai su Kwari, suna tafiya Ladidi na ta ba su labarin wata yarinya a Layin Unguwar tasu wai ta yi ciki, ita dai Abir na jin su suna ta hira Ladidi na shewa har suka iso Kwari.. Suna isa suka suka fara sayayya inda Abir ta sayo duk wani abu da tasan za su buƙata har da ƴar madaidaiciyar freezer ta sayo musu da babbar katifa. Bayan sun gama suka sa a mota suka yo gida. Suna isowa lokacin karfe 12: daidai na rana, zama ta yi tana tunanin yadda za ta dafa abinci ga shi Zaiyan nata korafin zai ci abici, jin haka sai Ta Sakkwato ta zubo masa tuwon shinkafa da miyar taushe amma sam ya ƙi kallo bare ma ya ci, riƙe baki ta yi tana cewa "Ikon Allah! To ba yanzu kake damun mutane da ɗumi ba yunwa kake ji shi ne na kawo ma abincin ka ce ba ka ci? To Wallahi sai ka ci." Ta faɗa tana aje masa abincin a gaban shi. Harɗe hannaye ya yi yana hararar abincin ya ɗago ya kalli Ta Sakkwato fuska daure, saurin tafiya ta yi ganin kalar kallon da ya mata abin ya ba ta tsoro dan ta yi tunanin zai tashi ya dake ta ne. Tana so ta yi girki amma tana tsoron ciwon nata ya tashi, ganin ba yadda ta iya sai ta ɗauki mayafin abaya ta nade hancinta da shi ta janyo rishow ɗin da ta sayo ta buɗe shi a kwallinsa ta fito da shi, mai ta zuba Ladidi yana gefe ta ce ya ba ta ashana ya shiga ɗakinsu ya kawo mata, wutar ta kunna tana ɗaura girkin.. Sai da ta kusa gama girkin ta ji babu abin da ta ji hakan ya sa ta buɗe hancinta, buɗe tukunyar ta yi tana kawar da kai ta ga ta tafu ta sauke. Ladidi ya taso yana wata kalar tafiya ya iso bakin rishow ɗin ya ce "Sannu da aiki." Gyaɗa masa kai kawai ta yi ta shige ɗaki, ba ta jima ba ta fito da babbar kula ta zuba musu abincin ta zuba wani ta miƙa wa su Ta Sakkwato tana murmushi ta ce "Hajiya ga abinci, don Allah kuma kar ki ce ba za ki ci ba." Murmushi ta yi ta amsa ta mata godiya ta miƙe ta miƙa wa Ladidi ya amsa yana shewa tare fadin "Allah dai ya biya ƴar madara ai dole mu ci girkin da kika yi." Girgiza kai ta yi ta koma ta sake dauko wata kular ta zuba ta nufi su Maman Amal, tun kafin ta isa hayaƙin da yake tashi a inda Maman Samira ke girki ya kawo mata ziyara, amma haka ta daure ta toshe hanci ta isa ta sunkuya ta aje musu kular, magana take son yi amma ta kasa saboda ta shaƙi hayaƙi ta yi baya tana riƙe ƙirji tana tari. Da kallo su Maman Amal suka bi ta ganin yadda ta done hanci, Maman Amal ta ce "Wannan yarinyar ƴar rainin hankali ce, diba ki ga yadda take done hanci dan ta zo inda muke." Maman Samira za ta yi magana suka ga ta durƙushe tana tari, da sauri duk suka yo kanta suna tambayar ta lafiya, kasa magana ta yi sai nuna musu ɗakinta take da hannu Ta Sakkwato da ta rikice ta ce "Ku taimaka mu kai ta ɗaka." Kama ta suka yi suka shigar da ita ɗakin zuwa lokacin da kyar take jan numfashi tari kawai take, handbag ɗinta take nuna musu da hannu hakan ya sa Maman Amal ta janyo jakar ta zarge ta zazzage ta, maganin shaƙa na cutar asma ta gani hakan ya sa ta gane shi take so a ba ta, da sauri ta kai bakinta ta ta fesa ta shaƙa ta ƙara mata sai ta saki jiki. Baya suka yi da ita suka zaunar da ita akan gatifar tare da jingina ta da bango suna jera mata sannu sai ajiyar zuciya take saukewa ɗaya bayan ɗaya tana lumshe idanu, da sauri Zaiyan ya shigo ɗakin ganin ta a zaune sun saka ta gaba sai ya iso kan katifar ya zauna yana kallon ta tare da zaro fararen idanuwansa, wuyanta ya taɓa sai kawai suka ga ya soma kuka yana tattaɓa ta yana fadin "Anty me suka ba ki?" Maman Amal ta miƙe da sauri baki buɗe tana kallon Zaiyan sai ya ga Ladidi ya leƙo daga bakin ƙofa, ganin Zaiyan na kuka sai ya sheƙe da dariya ya ce "Oh ni Ladidi! Wasu dai sun rako maza duniya, kai yanzu saboda lalacewa kuka ne kake?". Ya faɗa yana nuna Zaiyan. Kallon shi ya yi ya tsayar da kuka ya ce "Ba su ba ne suka mata wani abu." "Ahaiye caɓas, billahillazi ka ba da maza ɗan matashi, yo kai wani kalar soloɓuyon namiji ne Allah ya yi? Hmm ikon Allah to ba da ni ba rakiyar fatalwa na yi nan." Ya faɗa yana sake yin dariya ya wuce. Turo baki ya yi ya taɓa fuskarta ta buɗe idanu ta kalle shi, nisawa ta yi ta kalli su Maman Amal ta ce "Na gode muku Allah ya saka da alkhairi, kai kuma daina kukan ka fita ka ci abinci kafin na yi wanka." Ta faɗa tana janye hannunsa daga kan kuncinta.. Maman Amal dai ta yi tsaye kamar gunki riƙe da baki, sai da ta ji godiyar da take musu sannan ta sauke hannun ta gyaɗa kai kamar ƙadangaruwa ta ce "Shin ni kuwa Jiddo wannan ƙanenki ne?" Murmushi ta yi ta ce. "No, he is my husband." Shuru Maman Amal ta yi kawai abin da ta gane a kalaman Abir Husband tasan dai miji ake nufi, kallon Zaiyan ta yi ta ce "Wato dai in na fahimta mijinki ne?" Gyaɗa mata kai ta yi hakan ya sa ta ƙara cika da mamaki, tashi suka yi suka bar mata ɗakin suna mata Allah ya kiyaye amma suna ta jinjina maganar wai Zaiyan mijinta ne. Ganin sun fita ta kwashe kayan handbag ɗin ta tashi ta zuba wa tukunyar ruwa ta dauke abincin har na Zaiyan ta kawo masa ɗaki ta ce ya zauna ya ci, bai musa ba ya zauna ya ci gaba da ci ita kuma ta kwanta jin wani zazzabi na shirin rufe ta babu jimawa bacci ya kwashe ta.. Tun da Grandma ta dawo ba ta ga Abir ba sai ta yi tunanin ko a gidan Abdul take, sai da Abba ya shigo tana palo Laraba na matsa mata ƙafa ta ka dubi Abba ta ce. "Wai ni kuwa Sulaimanu ina wannan shashashar yarinyar take? Na ga tun da muka dawo ban gan ta ba ko ta koma gidan Abdullahi da zama ne?" Wani ɓacin rai ne ya ziyarce zuciyar Abba jin kalaman Grandma dan shi ya ma manta da babin Abir, da kyar dai ya ce "Ai ta yi auri wannan mahaukacin da take kula da shi." Maimakon Grandma ta yi mamaki ko ta shiga ruɗu sai kawai ta ja tsaki ta ce "To ai shi kenan." Ba ta sake cewa komai ba daga haka suka daure hira, hankalin Laraba ya yi mugun tashi ganin yadda duk suka yi kamar ba su damu da Abir ba, da sauri ta miƙe ta kalli Grandma ta ce "Inna zan je na kira Mamata mu gaisa tun da muka dawo ban kira ta ba." To Grandma ta ce ita kuma ta wuce da sauri ta nufi ɗakinta har tana tuntuɓe, tana isa ɗaki ta soma zarya tana huci sai haɗa zufa take, tsayawa ta yi ta harɗe hannaye ta lula duniyar tunani. Ta fi minti biyar a haka tukun ta saki murmushi ta soma magana. "Tabbas lokaci ya yi da za ku san wace ce Laraba, lokaci ya yi da zan kawo karshen duk mai sa hannu akan wannan mutanen, lokacin yaƙi ya yi kuma ba makawa sai an yi." Ta ƙarashe maganar tana janyo gana mostgo ɗin kayanta ta soma binciko kayan tana watsi da su. Computer ta zaro daga can ƙasan gana mostgo ɗin ta kulle kofar ɗakin ta dawo ta zauna, kunnawa ta yi ta sa code ta buɗe ta shiga wani waje ta dauko wata number, sake sa hannu ta yi ta fito da waya iPhone 12 ruwan fauda ta kunna ta buɗe ta sa wannan number ta danna kira. Sai da ta yi ringing ta gama ba a dauka ba sai ta aje ta dawo kan computer ta soma yin rubutu cikin sauri, tana tsaka da yin rubutun sai ga number an kira ta ta yi saurin dauka ta kara a kunne. "Hello Sir Jk ce ke magana, lokacin zuwan ka Nigeria ya yi dan sun aikata maka babban zunubi..." _Maman Nusaiba ce_ [6/20, 8:43 PM] Ummu Amjad: *A HAKA NAKE SON SHI* Shafi na (41) Shuru ta yi tana sauraron shi sai gyaɗa kai, zuwa can ta tashi tsaye tana goya hannayenta baya ta soma magana. "Haka ne Oga ina ganin yau ɗin nan aikina akan wannan ahali ya kammala, amma ni abin da nake son samu kafin na bar ƙasar, ina son na gano wani hali ƙanwata take ciki a hannun wadannan azzaluman? A ƙara min ko da weekend biyu ne na binciko inda take zama." Daga cikin wayar Damisa ya ja numfashi sannan ya ce "Jk ka da ki karaya komai ya kusa zuwa karshe, ni nasan inda kawarki take a halin yanzu, sai dai rayuwar da take a wannan waje ta ƙazartar dan haka nake ta shiye-shiryen dawowa na kawo karshen wasan. Tabbas sun aikata babban zunubi mafi muni a rayuwarsu kuma zan tabbatar musu da hakan da yardar Allah, amma su na gidan kike lura da duk wani shige da ficen su ki gano mana me suke shirin ƙullawa akan ta. " Jikin Laraba ne ya ɗauki rawa ta dafe ƙirji ta yi ƙasa da murya ta ce "Oga da gaske kake ƙanwata tana raye har ka gano inda take?" Ta faɗa hawaye na zubo mata. "Hmm Jk ki nutsu ka da jin na ce nasan inda take ki kasa haƙuri mu gama aikin nan, da zarar na sauka zan amso ta." Jinjina kai ta yi kamar yana kallon ta, sai da shuru ya ratsa su na 'yan sakanni tukun ta nisa ta ce. "Babu damuwa Oga ba zan karaya ba, zuwa an jima zan tura maka da bayanai na jiya kuma yanzu zan turo su." OK ya ce mata sannan suka yi sallama ta aje wayar, dawowa ta yi kan computer ta ƙarasa rubutun da ta soma ta tura masa sannan ta kashe, kwashe su ta yi ta mayar da su muhallin su ta janyo ƙaramar wayarta ta gyara zama. Numbers Abir ta dannawa kira amma ta ji ta a kashe hakan ya sa ta dafe kai ta aje wayar, toilet ta shige ta wanke fuska ta fito da hanzari ta fita zuwa kitshen ɗaura girki.. Yau sammako Umma ta yi ta isa zuwa gidan malamin nata fuskarta ɗauke da farin ciki, tarba ta samu daga malam ta musamman har da abinci ya kawo mata ta ce ta ƙoshi, gyara zama ta yi ta soma mi shi bayanin komai. "Gaskiya Malam aiki ya yi kyau sosai, yanzu haka maganar da nake maka kaf family Maitama kowa ya tsane ta kuma ya manta da babin rayuwarta a cikin family, ƙarshe ma dai ko gidan ba ta zuwa tun da aka ɗaura auren. Yanzu kuma abin da nake so ina son a cikin samarin gidan Sarautar Niamey a samu ɗaya a cusa masa son Khairat ya aure ta. " Ta faɗa ɗukar da kai kamar za ta masa sujjada. Murmushi ya yi ya soma rubutu a cikin ƙasa bai ce mata komai ba, sai da ya gama ya ɗago yana murmushi ya ce "Hajiya to ai ita yarinyar da mijin nata sun bar garin kusan sati ɗaya kenan, kuma ba wani abu ba ne ya sa ta barin ganin sai dan tsira da ranta da na mijinta." Kwalalo idanu waje Umma ta yi tana dafe ƙirji ta ce "Ni fa yanzu Malam ba na so a kashe ta, ina so a bar ta a haka ta wulaƙanta a duniya, amma waye ya mata barazanar mutuwa?" Ta faɗa tana kallon Malam. Gyara zama Malam ya yi ya saki murmushi ganin yadda Umma ta ruɗe ya ce "Ya na ga hankalinki ya tashi da jin labarin nan? Ke da kike cewa a kashe ta ya da haka?" Sauke hannu daga ƙirji ta yi ta ce "A'a Malam, ni fa ba tausayin mayyar yarinyar nan naji ba, kawai dai bana so wani ya min katsalandan ya ɓata min aikin da nake a kanta tun kafin ta zo duniya, na tsane ta fiye da kima wanda ya mata hakan nake son jin shi ko waye shi." Jinjina kai Malam ya yi ya ce "Yayanta ne shi ya mata barazanar zai kashe ta ta bi dare ta gudu, yanzu haka tana garin Kano amma ban gano takamaiman inda take zaune ba." Dariya ta yi ta kaɗa kai tana kallon Malam ta ce "Ina son inda ta je ɗin ma su tsane ta kowa a garin ya hana ta muhalli, ba tana tunƙaho da dukiyar mahaifinta ba? To yanzu tun da ta bar komai na uban nata so nake ta yi rayuwa mai mugun matsatsi wadda babu talakan da ya taɓa yin irin wannan rayuwar a fadin duniya. " Ta faɗa tana huci. "Na riga da na faɗa miki Hajiya yarinyar nan fa ba ke kaɗai ba ce kike bibiyar rayuwarta akwai maƙiyan babanta." Ɓata rai ta yi ta ce "Haka kake faɗi, kuma na yi ta fama ka faɗi min su waye su amma sai ka ce wai sun fi ni rashin imani." Murmushi Malam ya yi ya soma jan Carbi idanuwansa a rufe, bayan kusan kamar minti biyar ya aje ya ce ta zaɓi ɗaya ta dauka ta miƙa masa, sai da suka yi haka sau uku sannan ya ce mata ta je zai yi aiki a satin nan komai zai kammala. Tana isowa gida ta yi packing ta fito cikin takun ta na izza da taƙama ta nufo part ɗin ta. Kiciɓus suka yi da Laraba kula riƙe a hannunta za ta fito daga part ɗin, kallon banza ta watsa mata ita kuma Laraba wani kalar shu'umin murmushi ta yi wa Umma ta jinjina kai tana kawar da kai gefe. "Iyye! Ke uban wa ya ba ki izinin shigar min part ba tare da ni na sani ba?" Ta faɗa kamar za ta kai mata duka. Wani irin duhu ne ya mamaye zuciyar Laraba jin zagin da ta mata, ji ta yi da ba dan tana tuna kar ta ɓata musu aiki ba da ta shaƙi Umma ta zabga mata mari, saboda yawan zagin ta da take kamar wata uwarta, matsawa ta yi ta ce. "Haba don Allah, kuma yanzu sai kin zageni dan kawai kin ganni part ɗin ki? To Allah ya ba ki haƙuri kar ki sauke gajiyar yawon ki a kaina." Tana faɗin haka ta yi saurin wucewa fuu saboda matuƙar kufula da ta yi, idan har ta ce za ta sake daƙiƙa a wajan babu abin da zai hana ta fito mata a asalin ita ko wace ce, ita kuma ba za ta so hakan ba.. Da zagi Umma ta raka ta ta shige part ɗin ta.. _NIGER_ Iman na zaune ta rafka tagumi gabaɗaya lamarin masarautar ya fitar mata a kai, ga ta kira Abir ta faɗa mata damuwarta amma sam wayar ba ta shiga a kashe, hakan ya sa ta kira Umma yau take tambayar ta ina Abir take in ta kira ba ta shiga, a nan ta sanar mata auren da ta yi, hankalinta ya yi mugun tashi da jin wannan labarin hakan ya sa ta kulle kan ta a ɗaki ta dinga rusar kuka tana tuhumar su Abba da Suhal ne silar komai da yake faruwa da ƴar'uwarta, da Suhal bai ce ya fasa auren ta ba suma su Abba ba su goya masa baya ba yanzu da tana cikin farin ciki a gidan mijinta. Dafata ta ji an yi ta yi saurin juyowa, sanye yake da shigar kayan gado wato tufafin gidan sarauta black colour ya daura hula yellow kalar zaren da aka yi wa rigar ado da shi, ƙafafuwansa cikin wasu tsadaddun takalma na fata suma launin kayan, murmushi ne shinfiɗe samar fuskarsa ya miƙa mata hannunsa alamar ta zo.. Maƙale kafaɗa ta yi tana turo baki, indai ta gan shi da wannan shiga to tabbas tasan garin zai bari, ita kuma tsoron kowa na masarautar take Ikilima da Mamma kaɗai ta yarda da su, lumshe idanu ya yi yana buɗe su a kanta kamar mai jin bacci, takowa ya yi ya iso gaban ta ya durƙusa ya ɗaura hannayensa a kan cinyarta, ɗayan hannun ya sa ya ɗago fuskarta yana girgiza mata kai. Kwacewa ta yi tana ja da baya ta koma ƙuryar kujera ta haɗe kai da gwiwa ta shiga rera masa kuka kamar marainiya, dafe kai ya yi yana kallon agogo ganin lokaci na tafiya, ba yadda ya iya ya cire takalmansa ya zauna a gefen ta ya zuba mata ido. Ɗagowa ta yi jin shuru bai mata magana karaf suka haɗa idanu sai ta kuma fashewa da kuka ta ce "Ni ka tafi ka ba ni guri tun da dama ba tausayina kake ba." Dariya ta ba shi sai ya yi murmushi ya dauke ta cak daga kan kujerar ya nufi ɗaki da ita, duka ta dinga kai masa tana faɗin ya sauke ta har ya dire ta a kan gado, cire rigar ta sama ya yi ya cire hular ya hayo gadon ya dauko ta ya rungume. Shuru ta yi tana sauke ajiyar zuciya har sai da ya ji ta ɗan samu sauki ya ɗago da ita ya zaunar, goge mata hawayen ya yi ya ce "My Iman waye ya taɓa min ke a gidan nan?" Jin abin da ya faɗa ta turo baki ta kawar da kai gefe ta ce "Anty Baby ce." Ta faɗa tana sake sakin wani kukan. Runtse idanu ya yi ya ce. "Me ta yi ita Princess ɗin?" Daina kukan ta yi ta ba shi labarin auren da ta yi, alamar mamaki shi ma ya nuna ya ce "Ni ma fa na kira ba ta dauka Allah ya sa dai lafiya." Rigima ta sa masa tana kuka har da tirje-tirje take ta ce ba zai tafi ba sai ya kira mata ita sun yi magana, babu yadda ya iya ya ciro wayarsa ya lalibo number ta ya danna mata kira, har ta katse ba a dauka ba ta ce ya sake kira, sake kira ya yi ya miƙa mata wayar ta zaƙu ta ji an dauka, sai da ta kusa katsewa sannan ta ji an daga tare da yin sallama. Muryar da ta ji an yi sallamar ce ta ba ta mamaki ta ce "Hello ina me wayar take.? Daga can ɓangaren aka ce yanzu za a kai mata, Iman tana jin Abir na cewa "Hajiya waye ya kirani?" Ta Sakkwato ta miƙa mata wayar tana ce mata in ta amsa sai ta ga ko waye, amsa ta yi ganin sunan Suhal ɓaro-ɓaro akan screen ɗin wayar ta riƙe kai tunawa da Iman. "Assalam alaikum, Ango mijin Bloodyna ya kwana biyu." Kukan Iman ne ya iso majiyarta ta miƙe tsaye ta shige ɗaki, zama ta yi a gefen Zaiyan da yake bacci ta ce "Haba Iman ke wai sai shegen sakalci kika sa a gaba, me ya faru?" Goge hawaye Iman ta yi ta kalli Suhal da shi ma ita yake kallo ta ce "Haba Anty Baby wannan wacce irin rayuwa ce haka kika daukar wa kanki? Ki yi aure ba tare da kowa ya rakaki gidan miji ba saboda zubar wa da kai daraja, kuma ki rasa ma wa zaki aura sai mai larurar ƙwaƙwalwa? An ce ma wai kin bar garin ke da shi Anty Baby in za ki je da kika bar asalinki inda danginki suke kika koma cikin mutanen da ba su san ki ba?" Haɗiye kukan da ya zo mata ta yi tana huci zuciyarta na mata wani kalar azabbaben ciwo wanda ba zai musaltu a baki ba, nisawa ta yi ta ce "Ƴar'uwata ki daina zubar da hawaye akan abin da na aikata, nasan Allah na tare da ni, bakin da ya yi kuka wata rana shi zai yi dariya, ba zan sare ba kuma ban yi nadamar auren da na yi ba dan shi kaɗai ne samun kwanciyar hankali a gareni, duk abubuwan da suka dinga min ba su faɗa miki ba sai auren da na yi ne suka sanar da ke dan ki ga lefin abin da na aikata? Tabbas ban san yaushe na kafe sai na aure shi ba sai yanzu na gane shi ɗin a zaman mijina yake. Yanzu so kike na rabu da shi ya shiga duniya ya faɗa mugun hannu ni kuma na koma gida su ci gaba da ƙunsa min baƙin ciki har ya yi ajalina? To ba zan taɓa komawa Yobe ba zan ci gaba da zama a duk inda Allah ya kaini na kuma zauna da Zaiyan a matsayin mijina na har abada, ke ko da a haka a Zaiyan zai zauna bai warke ba ba zan taɓa barin sa ba saboda tun farkon haɗuwa da shi na kamu san shi. A HAKA NAKE SON SHI a matsayin mijina, A HAKA NAKE SON SHI ko da kuwa mutanen duniya za su nuna rashin dacewar hakan, A HAKA NAKE SON SHI duk rantsi duk wahala ba zan taɓa gudun shi ba, A HAKA NAKE SON SHI ko da tsirara yake yawo, A HAKA NAKE SON SHI zan faɗa ko a gaban waye. Ya kike so na yi da rayuwata Iman? Yaya Abdul yana min barazanar zai kashe ni har ma da Zaiyan? Yana tambaya ta abin da ban san da shi ba shi ya sa na yanke shawarar barin musu garin na koma wani yankin, na san dai kari da yawa maye ba zai ci kansa ba, kuma idan su sun ƙini wanda na tarar a nan suna so na muna zaune lafiya, in sha Allah kamar yadda na ƙudurta zan ci gaba da nema masa magani ko da kuwa kuɗin account ɗina za su ƙare. "Ta ƙarashe maganar tana share hawayen da suke ta sunturi kan kuncinta. Sai da ta gama bayanin ta kaf daga Iman har Suhal ba wanda ya katse ta, Iman ta ƙara jin tausayi ƴar'uwarta ta, gyara zama ta yi tare da nisawa ta ce "Ki yi haƙuri Anty Baby in sha Allah komai zai zo daidai." "Yaushe? Sai yaushe zan yi farin ciki Iman? Kin san kuwa tsananin raɗaɗi da ciwon da nake ji a gangar jiki da ruhina?" Saurin katse ta Iman ta yi ta ce "Haba Anty Baby ke fa musulma ce ka da ki yi saɓo mana, ai duk tsanani yana tare da sauƙi, ki ci gaba da addu'a ni ma ina tayaki da Yaya Suhal Allah ya ba wa Zaiyan lafiya, amma ki faɗa min abin da Yaya Abdul ɗin ya miki." Murmushi mai ciwon ta yi ta gyara zama tana yamutsa sumar kan Zaiyan zuciyarta na ƙara karaya na hali da suke ciki, nisawa ta yi ta ba ta labarin komai da ya faru har tafowar su Kano da yan fashin da suka so yi mata faɗe da yadda Ta Sakkwato ke yi mata kirki a gidan nasu na haya.. Kuka sosai Iman ke yi jin halin da ƴar'uwarta ta take ciki, wai yau Abir ce a gidan haka wanda ko a mafarki ba ta yi tsammanin haka ba? Ƴar'uwarta ƴar ƙwalisa ƴar wanka marar hayaniya ga Sanyin hali da tausayin al'umma ga kuɗi duk Nigeria ana sa Abie a jerin masu kuɗin ƙasar amma ita ke rayuwa a gidan haya? Goge hawaye ta yi ta ce "In da za ki yarda zan nemi alfarma a wajan Yaya Suhal ki dawo nan ƙasar da zama, kin ga za mu zauna a gari ɗaya." Girgiza kai Abir ta yi ta ce. "Karki damu Iman ba sai na je Niger ba anan ma ina jin daɗin zama da mutanen gidan, kawai ki tayani da addu'a Allah ya ba ni ikon cinye jarabawar da ya mini, ina Yaya Suhal ɗin yake?" Wayar ta miƙa masa ya ƙara a kunne cike da tausayin abar Ƙaunar tashi dan duk abin da suke faɗa ya ji, a sanyaye y ce "My Princess barka da warhaka." Murmushi ta yi ta ce "Ka ga malam ka fa daina ce min princess ɗin nan dan ni ba ɗiyar masu rawani ba ce, ni yanzu Antynka ce." Ta faɗa tana ƴar dariyar yaƙe. Shi kan shi yasan ba dan jin nishaɗi ta yi dariyar ba, ta yi kawai dan ta kawar da hirar tasu. Gaisawa suka yi tana tambayar su Mamma ya ce suna lafiya, tukun ya ce " Tsaya-tsaya Princess karki kashe ba ni abokina mu gaisa." Murmushi ta yi tana kallon Zaiyan da tun tana yi wa Iman jawabi ya tashi ya tsare ta da idanu, miƙa masa wayar ta yi ta ce. "Ka mlamsa ku gaisa da abokinka da zai kaika London." Maƙale kafada ya yi ya murza idanuwansa ya ce "Ni na daina kula shi ba ya tsoron Allah ya min karya." Ya faɗa yana rufe idanu irin ya yi baccin nan. Ƴar dariya ta yi ta ce "To ka dai ji bai manta maganar ku ba, idan ya huce kun gaisa wataran." Jinjina kai ya yi ya dinga tambayarta a wacce unguwa take in wani abu ya kawo shi Nigeria ya kai mata Iman, amma fir ta ce masa kar ya damu za ta faɗa masa ba yau ba sai wani lokacin, ganin ma za su takura mata ta kashe wayar gabaɗaya... _Maman Nusaiba ce_ [11/23, 9:35 Yamma] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): *A HAKA NAKE SON SHI* Shafi na (42) Sororo ya yi da wayar jin ƙit ta kashe, Iman da ta yi zaman dirshan a tsakiyar gadon ta kafe shi da kallon ya mata ƙarin bayani, aje wayar ya yi a gefe yana furzar da askar cikin bakinsa ya ce "My Iman zan tafi wani taro wanda aka gayyaceni ni da 'yan'uwana, so kar ki fita ko'ina dan su Mamma ba sa nan sun ɗan fita su sha iska amma a cikin masarautar nan wajan yake, idan ki na so zan kaiki sai na wuce." Tun da ya fara maganar ta kafe shi da idanu har ya dasa aya, matsowa ta yi kusa da shi a sanyaye ta ce "Yaya Suhal please ka taimaka ka mayar da ni ƙasarmu, ka ga danginka ba sa so na saboda ni ba jinin sarauta ba ce, gaskiya ni ba zan iya zama ana wulaƙantani ba, ka mayar da ni wajan iyayena kawai." Ta faɗa tana riƙe hannunsa hawaye na zarya kan kuncinta. Shuru ya yi yana jinjina ƙarfin hali irin na Iman, haka za ta tasa shi a gaba ta yi ta kuka kamar an yi mata wahayin sa ta ce ita fa ba ta son shi ya sake ta kawai ta koma gida, lallaɓa ta yake ya mata wayo har ta daina kukan ya hana maganar, cikin satin nan kuma abin ya yi yawa kullum sai ta ce ya sake ya mayar da ita wajan iyayenta ai dama ita ba ta ce tana son shi ba. Kuka ta sa mana tana kai masa duka sai faɗi take "Wallahi ba ka isa ba sai ka sakeni ka mayar da ni wajan dangina, ni ba zan ci amanar ƴar'uwata ba." Haka ta dinga faɗa tana tura shi baya amma ko gizo bai yi ba, ba ya jin daɗin Kalmar sakin nan da take ambata, amma ita ko a jikinta abin ma ya zame mata jiki. Ruƙo hannunta ya yi ya saita nutsuwarsa irin ba wasa ɗin nan, da kyar ya ce "Iman me ya sa ke har yanzu kin kasa gane daidai da rashin daidai wajan furta wa mijinki kalamai? Babu kyau mace ta dinga ambatar Kalmar saki wannan ba ɗabi'ar mace ta gari ba ce, ki daure mu rungumi ƙaddararmu sai ki ga Allah ya sanya mana soyayyar juna duk da ni na jima da son ki a zuciyata, ke ce dai gabaɗaya kin kasa yarda da ƙaddarar Ubangiji. Don Allah Iman ki yi haƙuri mu tabbatar da zamar a mata da miji mu gode wa Allah akan abin da ya tsara a kanmu, ki sani ba wai dan bana son Princess ba ne na ce ke zan aura, ina da nawa dalilin akan hakan kuma na sadaukar da soyayyata ne dan na ceto rayuwar princess, dan haka Ko da wasa ba zan taɓa sakin ki ba ni da ke mutu ka raba, idan ki na son zuwa Nigeria zan kaiki amma ba yanzu ba." Kallon ka raina min hankali ta masa tare da yin kwafa tana hararar shi cike da takaicin ya sharara mata ƙarya da ya ce wai dan Anty Babynta ya yi hakan, hanci ta hura tana huci sai hawa take kamar fulawar da taji yiss. Dariya ta so ba shi amma ya gumtse dan ya nuna mata kuskuren ta, zaunar da ita ya yi a kan cinyarsa ya ɗago da fuskarta, buɗe idanu ta yi cike da masifa ta sauke su akan nasa idanuwan, ba shiri ta kawar da kai duk faɗan da take jin za ta yi masa gabaɗaya ta ji ta saduda ta sunkuyar da kai, gyara zama ya yi ya yana lumshe idanu gabaɗaya ta hana shi sukoni kallon da take masa ya sa shi shiga yanayi. Jin bai ce komai ba ta fusata ta ce "Malam ka ga kar ka wani yi min daɗin baki, in da gaske kake dan ka ceto rayuwar Anty Baby ne me ya sa ba ka aure ta ba a lokacin da ta fi kowa buƙatar ka? Saki dai dole ka sakeni naje na auri wanda nake so ehe, sai ka wani zaunar da ni kana wani tsara min magana kai ga ka sarkin iya magana ko? To ba zan yarda ba. " Ta faɗa tana murguɗa masa baki. Girgiza kai ya yi yana jin gabaɗaya ta caza masa kai har wani ciwo kan yake masa, shigar da ita ya yi jikinsa yana fitar da wani kalar numfashi wanda ya yi sanadiyar tsoratar da Iman ta soma kiciniyar kwacewa, ƙin ba ta damar hakan ya yi dan dole ta yi lamo a jikinsa tana sauraron ta ji wata maganar zai tsara mata. Sun fi minti biyar a haka shi bai ce uffan ba itama haka dan so take ya sake ce mata wani abu ta masa tatas kuma ta takura masa dole ya sallame ta ta koma gidansu, can ta tuna da Sajida ai kuwa ta tattara duk ƙarfinta ta yakice shi daga jikinta ta diro daga kan gadon, ita sai yanzu ma ta tuno ashe fa yana da wata matar bayan ita ga shi har yau ba ta gan ta ba a gidan. Kama ƙugu ta yi tana jijjiga sai hura hanci take ta ce "Ni fa ko mai za ka faɗa ba zan taɓa yarda ba ehe, haka kawai ka wani tsare ni da surutu to ina matarka take ma wadda Anty Baby ta ba mu labarin ta? Saboda rashin adalci ba ka taɓa haɗa mu mun gaisa da juna ba ko ka kaini part ɗin ta, saboda ita ɗiyar gwal ce shi ya sa ko fitowa part ɗin Mamma ba ta yi ita ƙasatacciya ko? To Wallahi ni Iman na fi karfin kishiya ta min gani-gani dan ba zan dauki raini ba ehe, kuma in dai har kana son na tabbatar da kana da adalci to ka kira ta ta zo nan palonka mu ga juna, in ba haka ba da kaina zan gudu na koma garinmu. " Ta faɗa tana turo ɗankwali gaba.. Tun da ta fara maganar yake kallon ta cike da birgewa, indai tana yin masifa wani irin kyau take masa na musamman, shi ya sa ko tana masa rashin kunya yake rabuwa da ita ta yi ta gaji dan kanta ta bari, wani ƙayataccan murmushi ya yi ya miƙa hannu zai janyo ta ta matsa da sauri tana hararar shi. "Alƙur'an ka taɓani sai na tara ma mutane a gidan nan." Ta ƙara matsawa. Shammatar ta ya yi ya damƙo hannunta ya janyo sai ga ta a kanshi, ɗaure fuska ta yi irin ba wasa ɗin nan ta ce. "Malam cikani wanka ma zan yi." Zaunar da ita ya yi a gefen shi ya rasa da wani yare zai fahimtar da ita ta gane, zuro ƙafafuwansa ya yi bakin gadon ya soma yi mata magana. "Iman bana so ki sake furta kalmar sakin nan, nasan kin je islamiya kuma an koyar da ke komai ciki kuwa har da macen da za take cewa mijinta ya sake ta salin alin ba lefin tsaye ba na zaune, Ubangiji shi ya halitta saki a tsakanin ma'aurata amma ba ya son ayi shi, duk lokacin da aka yi saki al'arshin Ubangiji sai ya girgiza, ni kuma a tsarina ba zan taɓa rabuwa da ke har abada. Kar na kuma jin kin ce na sakeki babu kyau wannan kalmar ta fito daga bakinki a matsayinki na musulma wadda ta yi imani da Allah da ƙaddara a kowanni lokaci ta riske ki ki amsa hannu bibiyu ki gode wa Lillahi wahidulƙahar, sai ki ga ya miki sakamako da aljana mfificiya ranar gobe ƙiyama... " Jikinta ne ya yi sanyi zuciyarta ta raunana sai yanzu take tuna irin kuskure da ta dinga tafkawa, ɗago da kai ta yi ta ce " Am so sorry Yaya Suhal, ba zan sake cewa ka sakeni ba in sha Allah, amma ka faɗa min ina Sajida take?" Wani sanyi ya ji ya ratsa zuciyarsa ya yi ajiyar zuciya ya ce "Sajida ai ta rasu tun lokacin da muka dawo gida da sati biyu, kawai dai naƙi faɗa wa Princess ne ganin hali da take ciki." Da sauri ta ɗago ta kalle shi baki na rawa ta ce "Wa.. Wai Sajidar ce ta rasu? Inna lillahi wa inna laihin raji'un! Allah ya jiƙan ta da rahama." Amin ya ce ya kalli Agogo ya yi fuskar tausayi ya ce "Yanzu haka saura minti 20 a fara taron nan ga shi kin tsare ni da rigimar nan taki, muje na miki wanka ko na tafi." Turo baki ta yi sai kuma ta yi saurin faɗin "Amma me ya sa ka ce min ka aureni ne dan ka tseratar da rayuwar Anty Baby? Don Allah ka bar ni a duhu ka sanar da ni dalili ko zuciyata za ta samu salama." Ta faɗa tana marairaicewa kamar za ta sa masa kuka. Ce mata ya yi ba yanzu ba amma wani lokacin zai sanar da ita komai da ya shafi rashin auren Yayarta ta, ba dan ta so ba ta haƙira suka shige toilet ya mata wanka sai mita take wai ba shi da kunya, murmushi kawai yake dan ya lura ita rashin kunya da kauɗin bakin nan a jininta yake. Bayan ya gama shirya ta ya kama hannunta suka nufi can wani ɓangare daga masarautar ya sada ta da su Mamma, da sauri ta iso suka rungume juna ita da Ikilima suna murna ta durƙusa ta gaishe da su Mai martaba, fuska cike da annuri yake amsa mata ta kalli su Kilishi har za ta share su sai kuma ta tuna a gaban wa take ta gaishe su, sai da Kilishi ta mata kallon tsaf sannan ta amsa, Saraunjya Bilkisu kuwa ko kallon ta ba ta yi suka ci gaba da hira... _NIGERIA_ Tun lokacin da ta kashe waya ta dinga kuka tana tunanin rayuwarta ita da mijin nata, ji ta yi ana goge mata hawaye ta ja dogon numfashi jin ɗumin hannunsa akan kumatunta, kasa juyowa ta yi ta kalle shi saboda ba ta son kallon da yake mata yana saka ta a wani kalar yanayi, shi kuwa bai ma san dawan garin ba wai amarya ta yi kashi a moɗa! Jin yana taɓa mata wuya ta yi saurin kai nata hannun ta ɗaura akan nasa amma ta kasa janyewa ta yi shuru idanuwanta a lumshe, kallon ta yake kamar mai nazarin wani abu daga gareta, sai da suka kai minti biyu a haka sannan ya matso kusa da ita ba zato ba tsammani ta ji ya rungume ta tsam a jikinsa. Kwalalo idanu waje ta yi zuciyarta na bugawa da sauri, duk da ba wani sabon abu ba ne ya rungume tan amma yau dai ta ji ya bambanta da sauran, a hankali ta buɗe fararen idanuwanta wanda tsoro ya cika su ta sauke su a kan shi, wani kalar kwarjini na musamman ta ga ya mata, ga gemunsa da kullum take gyara masa ya ƙara wa fuskar tasa kyau, lips ɗinsa da yake saɓa su ta ƙurawa idanu tana jin ƙarfin bugun zuciyarta na ƙaruwa, kwayar idanuwansa ta kalla wanda shi ɗin ma ita ya tsare da kallo suka dinga kallo juna, dam! Ta ji gabanta ya wani kalar faɗi har sai da ta yi saurin kai hannu ta dafe ƙirjinta da yake harba mata. Sake buɗe idanu ta yi ta kuma kafe shi da kallo, sak Suhal take gani a gaban ta, komai nasa irin na Suhal kawai launin fata ne ya bambanta su, ajiyar zuciya ta sauke babu abin da yake matuƙar birge ta a fuskarsa irin gemunsa mai haɗe da kwantaccan saja sun luf-luf, ga idanuwansa farare tas duk kyan nata sai ta ga nashin ya fi nata haske. Baki ta daga da niyar yi masa magana ta ji an dauke wutar ɗakin,. Tunani ta yi ko 'yan nepa ne suka dauke wutar sai dai ta ga saɓanin haka jin ɗakin ya ɗauki girgiza kamar zai kifa cikin ƙasa, ƙara riƙe hannun Zaiyan ta yi da ya zama kamar gunki ɗan hasken da ke shigo musu ta ƙofa shi ma ya ɗauke, lumshe idanu ya yi suka ji kamar ana taɓa wani abu kamar leda. Tagumi Abir ta yi dan ita a yanzu dai babu wani abin da zai firgita ta, haske ne ya bayyana a jikin bango ya dinga matsowa kusa da, kallon wajan duk suka yi suna son ganin abin da zai bayyana. Cikin shigarta ta kamala ta bayyanan musu suffarta fuska ɗauke da damuwa, zabura Zaiyan ya yi yana nuna ta ya ja baya ya koma bayan Abir yana kyarma, karshe ma ya yi kamar ya suma hakan ya tayar da hankalin Abir ta dubi matar ta ce "Haba Mama ya za ki firgitar min da shi?" Ta faɗa kamar za ta fasa kuka.. Murmushi ta yi ta zauna a inda Zaiyan ya tashi ta kama hannun Abir, kallon ta Abir ta yi sai sannan ta ce. "Na zo ne in miki godiya akan kulawa da Zaiyan da kike, sannan ina matuƙar farin ciki da ke ce kika kasance matarsa duk da lokacin da ki ka yi hakan ba kya cikin haiyacinki, na zo na muku bankwana ne zan yi wata tafiya ban sani ba ko zan daɗe ban dawo ba, amma kuna zuciyata duk inda zan je." Tsagaitawa ta yi sannan ta ɗaura "In na dawo in sha Allah zan sanar da ke komai game da Zaiyan, da inda ya fito da yadda aka yi ya samu ciwon haukan nan har ma da iyayensa duk zan miki bayani a kan su." Da sauri Abir ta ce "Mama please ki faɗa min shin iyayen Zaiyan suna raye ko sun mutu? In suna raye a wani yanki suke ko a wani gari suke? Sannan me ya sa in dai har suna da rai suka kasa neman jininsu? Ki faɗa min iya wannan kafin ki tafi please Mama." Ta faɗa tana zubar da hawaye. Girgiza mata kai ta yi sannan ta ce "Ki yi haƙuri ba yau na yi niyar faɗa miki labarinsa ba, yanzu lokaci ya tafi zan tafi sai mun sake haɗuwa, kuma karki damu duk komai zai zama daidai." Tana gama faɗin haka ta miƙe, da hanzari Abir ta miƙe itama cikin raunanniyar murya ta ce "please Mama me ya faru da ni har aka aura min Zaiyan? Ko ciwon hauka ni ma na yi ban sani ba?" Juyowa ta yi ta kalle ta tare da yin murmushi ta ce "Abin da kaɗai zan iya ce miki shi ne, asiri aka miki amma hakan ma ya min tun da ba su cutar da ke ba." Tana faɗin haka ta ɓace ɓat a ɗakin.. Dafe kai Abir ta yi sai kuma ta sunkuya ta ɗago Zaiyan da ta miƙe ya faɗi ruf da ciki ta gyara mana kwanciyar, zama ta yi ta yi tagumi ta lula duniyar tunani.. A ɓangaren Abdul kuwa yanzu ya zama wani sha ka tafi, duk wani abu da ake a office ɗinsu na 'yan sanda sai ya sanar su Alhaji Mustapha. Ita kanta Hafsat wani lokacin har mamaki take in ya ce mata meeting zai yi da Daddynta abin na tsaya mata a rai, abin da ya fi damun ta ma da ta masa maganar Abir sai ya ce mata bai san ina take ba, haka za ta haƙura ta koma gefe tana kallon shi... Baba da Inna tun washegarin Abir ta gudu suka ga takardar da ta aje musu, hankalin su ya tashi ganin abin da ta rubuta ya yi mugun tayar musu da hankali. Baba ya rasa me zai yi ya dinga danna mata kira amma wayar a kashe dole suka haƙura suka zuba wa sauratar Allah ido.... _BAYAN WATA BIYU_ Yau ta ji za ta leƙa Istagram dan haka ta janyo Computer ta ta buɗe , saƙo ya yi ta zuwa amma ta kasa budewa, wani saƙo ne ya ja hankalinta na friend ɗinta na Tiktok *Big Boy*, a hankali ta buɗe saƙon nashi. _"Hello my dear friend, how are you? So naji duk abin da ya faru da ke kuma nasa an yi min bincike an tabbatar min da e lalle abin da ake faɗa a Tiktok ba ƙarya ba ne gaske ne, abin da nake son isar miki ni dama na jima ina tsananin son ki, to amma da na ga kin sa Invitation ɗin aurenki sai na haƙura na koma gefen ina ba wa zuciyata haƙuri. A takaice dai ina son ki sosai kuma a shirye nake ko nawa ne zan kashe dan na aure ki, Dad ɗina zai yi min duk abin da nake so dan haka in kin ga saƙona ki ba ni amsa, amma karki kuskura ki furta min kala ɗaya wadda indai ina son abu na tsani a faɗa min ita, karki ce ki na da wani saurayin dan zan iya kashe mutum a kanki, I love you Habibty na. "_ Kwalalo idanu waje Abir ta yi tana sake nanata Kalmar so, gabaɗaya hankalinta ya yi mugun tashi da ya ce zai iya kisan kai a kan ta. Ƙarfafa zuciyarta ta yi ta masa reply. _"Am so sorry bawan Allah ni ai tun tuni na yi aure da jimawa, dan haka karka sake turo min wani sako wanda ya shafi so ni ɗin matar aure ce, please and please ka da ka sake yi min magana."_ Kamar jira yake ta tura masa ta ga ya ɗaga, kafin ta motsa ta ga ɗan gajeran saƙo. _" Kut! Kin yi me kika ce? To ba aure ba ko ke ce limamin da yake ɗaura aure sai kin kashe wannan auren kin aureni, ban taɓa cewa ina son abu ba kuma na rasa dole kema ki rabu da wanda kika aura ki zo gareni, idan har ba haka ba zan sa a nemo min inda kike a duk faɗin jahar Yola Wallahi. "_ Tsaki ta yi ta tura masa nata saƙon. _"Kuma ai sai ka yi, kai ɗin banza ka isa ka sa na kashe aurena na aure ka ban san kai ko a wacce duniya kake ba, to Wallahi ka yi kaɗan kuma ka jima ba ka binciko inda nake ba a Yola, aikin banza kawai."_ Emoji ɗin love ya turo mata ta yi saurin fita ta sauka a online ɗin ta kashe computer tana me da na sanin buɗe ta, tashi ta yi ta janyo pilow ta ɗaga kan Zaiyan ta ɗaura sannan ta fita ɗan yi musu girki... Tana fitowa ta ji ana ta zage-zage a wajan su Maman Samira, suna ganin ta Maman Amal ta ce "Yawwa zo ba mu kuɗin da kika satar wa Maman Samira." Sororo ta yi tana kallon ikon Allah, kuɗi kuma? To waye ya ce musu ita ta saci kuɗin? Abin da tafi tsana a duniya sata, dan haka ta ji ranta ya yi mugun ɓaci ta kalli Maman Amal ta ce "Ban gane me kike nufi ba? Wai ni kike zargin na satar miki kuɗi?" "Chass kuwa, billahillazi sai kin fito mana da kuɗin nan ko mu nakaɗa miki ɗan banzan duka a gidan nan, ai me ɗaure miki gindin ba ta nan bare ta shigar miki, mu za a nuna wa bariki da iya shege." Cewar friend ɗin Ladidi mai suna Gamboliya... Kasa ce musu komai ta yi jikinta sai rawa yake ganin yadda suka kewaye ta, ba ta ankara ba ta ji saukar mari tas! A zabure ta ɗago ta ga Maman Amal tsaye gaban ta tana huci, hannu ta ɗaga za ta sake kai mata mari ta ji an daka mata wata gigitacciyar tsawa. "Idan har kika sake ɗaura hannunki akan fuskarta za ki ga abin da zai biyo baya!............" _Maman Nusaiba ce_ [6/20, 8:43 PM] Ummu Amjad: *A HAKA NAKE SON SHI* Shafi na (43) Saurin waigowa Maman Amal ta yi idanunwanta suka sauka akan mai gidan da suke haya, a wuƙance ta sake kallon shi ta matsa daga kusa da Abir tana nuna ta da yatsa ta ce. "Ki fito min da kuɗina ko kuma na kai ƙaran ki wajan 'yan sanda." Ƙarasowa ya yi yana baza babbar rigarsa tare da gyara zaman hula ya turo ta gaban goshi irin ba mutumcin nan. Kallon Abir ya yi da idanuwanta suka ƙafe saboda da tashin hankali, cike da tausayawa ya tsaya a gaban ta ya yi gyaran murya ta ɗan kalle shi, waro idanu waje ta yi baki na rawa ta ce. "Bawan Allah kamar na taɓa ganin ka." Shi ma kallon sani yake mata can ya gyaɗa kai yana murmushi ya ce "Tabbas mun taɓa haɗuwa motata mai ya ƙare min a hanya kika ba ni galam a cike tab, ashe ma a nan garin kike kuma a gidana ki na haya, amma dai duk da haka ba ki jima da zuwa nan gidan ba ko?" Ɗan murmushi ta yi ta kai hannu ta shafa kuncinta da yake mata raɗaɗin zafin marin da aka mata, sunkuyar da kai ta yi ta ce "E ban jima da zuwa ba gaskiya." Kallon Maman Amal ya yi yana haɗe rai ya ce. "Ke kuma baiwar Allah me ya haɗaki da ita kika daga hannu ki ka kifa mata mari kamar Allah ta aiko ki? Haka ake rayuwa? Bai kamata kuke faɗa ba kuna gida ɗaya." Haushi ne ya rufe Maman Samira ta matso tana hura hanci ta ce. "Alhaji wannan da kake gani ɓarauniya ce, kuɗi ta sace min har dubu ashirin da biyar." Ta faɗa kamar za ta kai mata duka. Girgiza kai Alhaji ya yi ya ce "Gaskiya ban yarda wannan nutsatsiyar yarinyar za ta ɗaukan miki kuɗi ba da sunan sata, ke da gani ma ai kin san tafi ƙarfin wata dubu ashirin da biyar, kin ga ta miki kala da mabuƙata?" Ya faɗa a fusace yana nuna mata Abir.. Kafin Maman Samira ta yi magana sai ga Ta Sakkwato ta shigo gidan ita da Ladidi suna tafa hannu ko Sallama ba su yi ba, riƙe baki Ladidi ya yi yana maƙale ɗayan hannun ya ce "Ni 'yasu! Me zan gani haka a gidan nan kun kewaye ta?" Da sauri Abir ta ɗago ganin Ta Sakkwato sai ta ji kamar ta ga mahaifiyarta ne ta yo wajan ta da sauri ta faɗa jikinta ta fashe da kuka, sallallami Ta Sakkwato ta dauka tana rungume Abir bakinta har kumfa yake saboda masifa. "Wace ta ta dakeki? Tashi ki hwaɗa min wacce shafaffiya da mai ce ta saka ki kuka?" Ta faɗa tana ɗago da ita. Kasa ce mata komai ta yi dan sai yanzu take jin mugun zafin ƙazafin satar da aka manna mata, Alhaji ya dubi Ta Sakkwato ya ce. "Wai ta ce kuɗi ta sace musu dubu ashirin da biyar, ni kuma ban yarda ta dauka ba." "kan balastin can! Wallahi kin tabo masifa da bala'i a gidan ga, mi ankayi da wata banzar dubu 25? Wace ta ta taɓa ki hwaɗa min kar ki ji tsoron kowa?" Ta faɗa tana hura hanci sama sai jijjiga jiki take. Tsayar da kukan Abir ta yi ganin yadda ake ta cacar baki tsakanin su Maman Amal da su Ta Sakkwato, Alhaji da ya ga abin ba na ƙarewa ba ne ya ce "Wallahi yanzun nan zan kira mazajenku su zo, wannan wacce irin rayuwa ce? Ni zan biya kuɗin kar na kuma gani ko da kallon banza kun mata, dan Wallahi daga yau ma ta daina biyan haya kyauta na bar mata daƙin ta yi zaman ta har lokacin da ta ga za ta bar shi." Ta Sakkwato ta girgiza kai ta ce." Wallahi ina iya waca ma mari Gamboliya, da kai anka haɗe baki anka ƙulla mata sharrin masu sharri?" Wani farr ya yi da idanu ya kalle ta, gyara zaman jakarsa ya yi ya ba su labarin komai da ya faru har marin da Maman Amal ta yi wa Abir, wata zabura Ta Sakkwato ta yi ta wanka wa Maman Amal mari ta kuma ƙara mata, tana huci ta nuna ta da yatsa ya ce "Wallahi ina iya sumar da ke a gidan ga, ta taɓa zuwa ɗakinki kun yi ɗumi da ita ko amsar wani abu? To ki fita idona in rufe in ba haka ba kotu ce za ta raba mu da ke. Yarinyar ga tun da ta zo nan gidan ga ba ta taɓa ɓata muku rai ba, amma saboda rashin adalci ku ce ta satar muku kuɗi?" Sosai Maman Amal ta ji zafin marin da Ta Sakkwato ta mata, idan ta ce za ta tanka tasan halin Ta Sakkwato yanzu nan sai ta hau kanta da duka, hakan ya sa ta yi shuru amma haushin Abir ya cika mata zuciya.. Hayaniyar su ce ta tayar da Zaiyan ya fito yana mutsitsika idanu, hango ta ya yi tana goge hawaye kafin ka ce me sai ga shi a gaban ta, a ruɗe ya kama hannunta yana kallon ta ya ce. "Anty waye ya sa ki kuka?" Sabon kuka ta kece da shi ta ruko nasa hannun ta ja shi suka koma gaban ƙofar daƙinsu, hannu ya sa yana share mata hawayen sai tambayarta yake wa ya sa ta kuka? Amma ta kasa ce masa komai. Da wata kalar murya wadda ya yi magana da ita a dajin nan ya ce "Waye ya sa ki kuka Anty." Da sauri ta kalle shi taga yadda yake tsuke fuska, ba ta san lokacin da ta nuna masa Maman Amal ba cikin kuka ta ce. "Wai ta ce na satan mata kuɗi." Saurin sakin hannun ta ya yi ya yi dogon zari uku sai ga shi a gaban su, tamkar wani zaki haka ya dinga huci ya nuna Maman Amal da hannu ya ce. "Ke!" A firgice duk suka kalle shi, Maman Amal kuwa ji ta yi kamar ma ta saki fitsari saboda tsoro, huci ya yi ya ce. "Anty ba ta ɗaukan abin da ba nata ba, me ya sa kika saka ta kuka?" Ya faɗa yana ƙoƙarin damƙo ta. Da sauri Ta Sakkwato ta shiga tsakanin su tana girgiza masa kai ta ce. "Yi hakuri ka ji ɗana, ai na rama mata duk abin da ta mata kar ka ce mata komai mun bi mata haƙƙinta." Ta faɗa tana sa hannu daga baya ta tura Maman Amal baya da ta sanƙare jin muryar Zaiyan kamar wani Soja. Janye hannunsa ya yi yana huci sai kuma ya yi baya ya koma bai ce komai ba ya dawo inda take, kowa sake da baki yake kallon shi Abir da ta ƙame a jikin bango ta ji ya taɓa fuskarta. Firgigit ta kalle shi sai ta ga yana ɓata rai kamar zai yi mata kuka, dafe kai ta yi gabadaya ta ma rasa a wani bangare za ta jingina mijin nata, a mai hankali ko mahaukacin da ta sani tun farko? Ko kuma mai ɗan tabin hankali kaɗan? Hannunsa ta ja suka shige ɗaki, ruwa mai sanyi ta ba shi ya sha yana jan numfashi ya kwanta kawai sai bacci. Tagumi ta rafka tana kallon shi cikin wani yanayi na alhini da al'ajabin abin da yake yi wani lokacin, tashi ta yi ta fito waje ta ga duk sun watse ta Sakkwato na ƙofar dakinta sai faɗa take tana gyara kayan miya, murmushi Abir ta yi ganin yadda Ta Sakkwato ta damu da ita kamar ita ta haife ta, ta juya ta dauko wake mai cakuɗe da fari da ja ta iso ta zauna a kusa da Ta Sakkwato suka soma hira... Bayan ta gama girki ta je ta tashi Zaiyan amma yaƙi tashi ko ta ɗago shi sai ya saki jiki ya yi baya, haƙuri ta yi ta shiga wanka kafin ya tashi su ci. Har karfe shabiyu da rabi bai tashi ba ita kuma yunwa take ji hakan ya sa ta zubo ta fito zuwa ƙofar Ta Sakkwato, samu ta yi mijinta ya zo sai ta yi baya za ta koma ya ce ta zo shi zai shiga daga ciki... Karfe 2:30 mijin Maman Amal da mijin Maman Samira suka zo, sai da suka ci abinci suka fita daga gidan sai ga yaro ya yi sallama yana tambayar ina Maman Samira, da sauri ta ce. "Gani nan yaro yo nan wajan." Ta faɗa tana hararar Abir da ta ɗago. Yana zuwa ya miƙa mata wata baƙar leda ya ce "Wai in ji Sabitu ya ce kuɗinki ne dubu ashirin da biyar da ya dauka ba ki sani ba, ya ce in ya dawo zai miki bayani." Yaron na faɗin haka ya wuce abin sa.. Saroro ta yi tana kallon ledar da kuɗin yake ciki, ɗagowa ta yi suka haɗa ido da Abir ta yi saurin kawar da kai ta fito da kuɗin ta lissafa ta ga har da ƙarin dubu 5 akai, jikinta ne ya yi sanyi ta kalli Maman Amal murya kasa ta ce. "Ashe Sabitu ya dauka har na ce waccan ta dauka." Kafin ta ba ta amsa ta ga Gamboliya a gaban ta ya miƙa mata hannu yana wani zaro ido ya ce. "Miƙo mana kuɗin da Alhaji ya biya ki tun da kin samu nakin." Jiki a sanyaye ta miƙa masa kuɗin tana bin shi da kallo. "Tsuww an ji kunya dai, Wallahi ke dai Maman Samira kin yi faɗuwar sokana, yanzu don Allah ina mutumcin haka zuwa Makkah da kare? Kin liƙa wa ƴar mutane har da dukan ta ashe ma ƙasurgumin ɓarawon yana ɗakinki, a dinga bincike in za ayi abu." Yana gama faɗin haka ya warci kuɗin fuu ya wucewar shi ya dawo wajan su Abir.. Miƙa wa Abir kuɗin ya yi ya ce " Ƴar shawalwala ingo ki sa a aljihunki, kuma Wallahi in kika yafe wa su Maman Amal sai mun ɓata da ke, wannan cin zarafin da suka miki ai kotu ce kawai za ta rabamu da su. In ban da sun raina ki ina abin ma yake wai mayya ya ci jariri! Ai kowa ya gan ki ya san kin fi karfin dubu 25 Wallahi, dan ba ma gidan har suka samu kwarin gwiwar isa inda kike ma." Zama ya yi yana ci gaba da sababi Abir ta murmusa, ita dai in su Ladidi suna magana kawai kallon su take yadda suke maƙale hannu suna tafi abin na ba ta dariya, kuɗin ta dauka ta miƙa wa Ta Sakkwato ta ce "Hajiya ki amsa ki aje masa in ya dawo sai a ba shi, sannan ki miƙa min godiya ta a gare shi na karramawar da ya min." Ta Sakkwato ta kalli gefen su Maman Amal ta wurga musu harara ta amshe kuɗin ta kalmashe ta soka a gefen cikinta. Sai da ta kusa cinye abincin da ta zubo ɗagowar da za ta yi ta ga mutum a tsaye a gaban ta, turo baki ya yi sanye yake da wando iya gwiwa da singlet, da sauri ta haɗiye abincin da ta kai baki ganin faffadan ƙirjinsa mai cike yalwataccan gashi baƙi, kallon su Ta Sakkwato ta yi ta ga suma shi suke kallo sai ta wayance ta dawo da kallon ta kan shi ta ce "Muje ciki ka yi wanka sai ka ci abinci." Zama ya yi a gaban ta ya sa hannu ya dauko abincin ya nufi bakinta da shi, ba dan ta so ba ta daga baki ya sa mata, ganin zai kuma daukowa ta riƙe hannun nasa ta ce "Tashi muje ciki na ce ma." jimƙe wanda ya dauko ya yi ya nufi bakinta ta kauce ai kuwa ya yaɓa mata a kunci, zaro ido ta yi ya kuma kai mata ta kauce ya yaɓa mata a haɓa.. "Chass Wallahi, ƴar shawalwala tashi ku shiga daga ciki wannan mijin naki ɗan rigima ne." Cewar Ladidi. Gabaɗaya kunya ta rufe ta ta dauke plate ɗin ta kama hannunsa, har sun kusa isa Ta Sakkwato ta ce "Jiddo in kin gama ina son ganin ki." Jinjina mata kai kawai Abir ta yi suka shige ɗaki.. A ɓangaren su Alhaji Mustapha liyafa ta ci gaba, saboda yanzu lokacin zaɓe ya yi sun kuma je sun cike form na 'yan takarar Gwamna, Alhaji Mustapha shi suka sa a matsayin wanda zai yi takarar gwamna in ya haye kuma su yi mulki su uku.. Yau ma sun haɗa taro na yan mata da da samari masu yi musu campaign suna ta tsara yadda komai zai tafi, Alhaji Mustapha ya mike ya kira zugar yan sara-suka suka tsaya a gaban shi suna fadin "Sai ka yi mai dubun nairori kai ne gwanan Yola ko suna so ko ba su so dan uban mutum sai ka ɗare kujera." Daɗi sosai Alhaji Mustapha ya ji ya fito da ɗaurin 'yan rafa guda biyar ɗaurin dubu ɗari-ɗari ya ba su, saurin amsa shugaban nasu ya yi Alhaji Mustapha ya ce "Ku je ku ji daɗinku da wannan kuɗin, indai kuka min abin da nake so zan ba wa kowannen ku mota da kuɗi masu tsoka." Ihu suka kwasa suna faɗin "Allah dai ya biya muna godiya." Da haka ya sallame suka tafi ya dawo kan matan, suma kuɗi ya ba su kamar yadda ya ba wa mazan, gyara tsayuwa ya yi ya kalli wata matashiyar mata wadda za ta kai shekaru 35 ya ce "Bisho ku sha ruwa da wannan indai na ɗare kan kujera za ku ga yadda zan muku duk abin da kika nema a wajena, ku ne za ku tafi ƙauyuka zan sa a baku atamfofi da taliya da sauran abubuwa wanda za a raba wa duk wanda suke goyon bayan mu." Rusunawa Bisho ta yi ta ce "An gama ranka ya daɗe godiya muke." Har ya juya zai koma wajan zamansa ya hango wata tsaleliyar budurwa fara sol ta ci kwalliya, sanye take da doguwar rigar atamfa ta rufe jikinta da mayafi, sake kiran Bisho ya yi ya nuna mata yarinyar wadda ko kanta ba ta ɗago ta kalle su ba bare ta san da ita suke ba. Isa ta yi ta kira ta tare da mata rada a kunne ta jinjina kai, sai bayan taro ya tashi sai ga ta ta dawo Alhaji Mustapha na tsaye yana jiran ta, tana isowa ta rusuna ta ce "Ranka ya daɗe gani." Wani kallon ya bi ta da shi yana shafa gemu ya ce "Wato yarinya kawai na ga kin mini ne, ina gayyatarki nan da kwana uku zuwa wani waje mu fahimci juna, dan gaskiya na gani na ƙyasa." Hade rai ta yi ta ce "To yanzu sauri nake ranka ya daɗe ka ba ni adress ɗin inda za mu hadu." Wani ƙayataccan murmushi ya yi ya ce "Ba ni number ki." Ƙaramar wayarta ta ciro ta bashi number, ganin wayar ya ce mata tana babbar yarinya bai kamata ta kasa riƙe iPhone ba, ta ce masa ba da kuɗin sayan iPhone ɗin ai sai ya ce da sun hadu zai saya mata, haka ta mai sallama ta fita a gidan... Tana fita ta warware mayafinta ta ƙara yafawa, sai da ta yi tafiya mai nisa sannan ta buɗe Jakarta ta dauko wayarta ta daddana ta danna kira, bayan sun gaisa ta yi murmushi ta ce "Oga yanzu na dawo daga gidan wadmɗancan marassa mutumcin, sannan akwai ƙarin wata cakwakiyar kuma abin ya matuƙar girgiza ni sosai." Daga can ɓangaren Damisa ya ce "Ai za ki ga abin da ya fi ma haka ma Jk au na manta Laraba." Dariya ta yi ta ce. "Haba Oga kaima Laraba za ka ce kamar a gidan aikin nawa?" Tashi ya yi zaune ya goya hannunsa baya ya ce "Yanzu meye abu na gaba, saura sati ɗaya na duro ƙasar?" Daɗi sosai ya kama Laraba dan ta ƙagara ta hadu da ƴar'uwata, haka ta dinga faɗa masa duk wani abu da su Alhaji Mustapha suke ƙullawa, ƙarshe suka yi Sallama ta wuce da sauri ta samu mota ta shigo sai gida... Abir sai bayan kwana uku ta tuna Ta Sakkwato ta ce tana son magana da ita, hakan ya sa ta yi jiran dawowar ta gida. Bayan ta dawo ta shiga ɗakinta ta bar Zaiyan zaune yana kallo a computer ta, zama suka yi Ta Sakkwato ta ce. "Ya dai mi ya ka hwaruwa ?" Murmushi ta yi ta ce "Kin ce ki na son magana da ni, to na manta sai yau na tuna na zo." Gyara zama Ta Sakkwato ta yi dan dama abin ya daɗe yana damun ta tun haduwar ta da Abir, nisawa ta yi ta ce "Wai shin ina iyayenki suke? Kuma ya anka yi ki na cikin nutsuwar ki kika yarda aka aura miki mahaukaci wanda ba zai amfane ki da komai ba?" Ta faɗa a tausashe. Sunkuyar da kai ta yi idanuwanta sun cika da ruwa, a hankali ta ce "Ni marainiya ce ba uwa ba uba ba dangin uwa, dangin uba kuma sun tsaneni ba sa son zamana a cikin su shi ya sa na yi wa kain hisabi, shi ma mijina ba shi da kowa a duniya sai ni sai waɗanda suka riƙe shi suna taimaka mana lokacin da muna kai shi Asibiti." Labarinta ta faɗa mata babu abin da ta boye mata har auren ta da Suhal duk ta sanar da ita, jin Ta Sakkwato take tamkar mahaifiyarta shi ya sa ta sanar da ita ko ta samu sassauci a zuciyar ta.. " Inna lillahi wa inna laihin raji'un! Sannu kin ji Jiddo Ubangiji ya ba wa mijinki lafiya, ki daina kuka kin ji yata na miki alƙawarin zan zame miki uwa duk abin da kike so ki tambayeni zan miki shi ko min tsadar shi, sannan ki adana duk abin da kika san yana da mahimmanci karki yi sake da shi. " Sosai zuciyar Abir ta sanyaya ta rungume Ta Sakkwato tana mata godiya, haka suka ci gaba da hira tana ƙara kwantar mata da hankali.. Zaiyan ganin Abir ba ta ɗakin sai ya tashi ya fito waje, bai ga kowa ba sai Maman Samira da take wanki, juyawa ya yi zai koma ɗaki sai kuma ya nufi kofar fita daga gidan. Maman Samira na ganin shi amma tsoron shi ya sa ta kasa cewa komai ha ya fice a gidan, ganin haka ta yi saurin komawa dakinta dan kar ma ya dawo ya same ta a waje.. Abir ta fito daga dakin Ta Sakkwato ta shige dakinta ta ga wayam, bandaki ta leka ta ga nan ma baya nan, hankali a tashe ta fito tsakar gidan ta kwadawa Ta Sakkwato kira ta fito da sauri har tana tuntuɓe. "Minana ya hwaru kike kira hakan ga?" Fashewa ta yi da kuka ta ce. "Zaiyan ba ya ɗaki kila da bai ganni ba ya fita waje, bari na leka kofar gida ko zan gan shi." Kafin Ta Sakkwato ta ba ta amsa ta janyo Hijabinta da ke kan igiyar shanya ta nufi waje da gudu, Ta Sakkwato ta ce "Bari mu gani kila ta samu shi a kofar gida." Tana fita ta leka ba ta gan shi ta ƙara shiga tashin hankali, Layin nasu ta dinga bi tana tambayar duk wanda ta gani bai ga Zaiyan ba? Wasu su ce ba su ma san waye wani Zaiyan ba, ta kusa shan kwana hannunta a ka tana rusa kuka ta ji ƙaran mota a bayan ta, saurin matsawa ta yi ta ji an yi sama da ita cak a tsilla ta cikin motar. Ihu take tana bige-bige karshe ma suka shaƙa mata fauda ta yi shuru suka ja motar a guje suka bar Layin..... _Maman Nusaiba ce_ [11/26, 12:55 Safiya] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): *A HAKA NAKE SON SHI* Shafi na (44) Kusan minti ashirin da fitar Abir Ta Sakkwato ta ga ba ta dawo ba, saurin janyo mayafinta ta yi ta nufi waje ta gani ko lafiya ba ta dawo ba. Wayam ta gani babu ita babu alamar ta, hankali a tashi ta nufi ƙofar gidan maƙotan su tana tafa hannu sai sallallami take. Da sallama ta shiga gidan inda ta samu matar gidan na shirin fita, kallon ta matar ta yi cike da mamaki ganin yadda ta shigo, matsowa kusa da ita ta yi ta ce "Ta Sakkwato lafiya?" A ruɗe ta ce. "Ina fa lafiya Aisha, yarinyar ga da take haya a gidanmu ce ta fito neman mijin ƙofar gida, to ganin shuru ba ta dawo ba shi ne na bi bayan ta na ga ba kowa, na shigo nan ne ko ta zo neman mijinta." Riƙe baki Aisha ta yi sai kuma ta dafe ƙirji tana salati, "Subhanallahi! To ina ta shiga haka? Amma kin san dai ai magidanci ba zai shigo min gida ba ina matar aure ko? Ina tunanin dai ko ya fita kasuwa ne." Dafe kai Ta Sakkwato ta yi, a sanyaye ta ce "Ai mijin nata yana da taɓin hankali kaɗan, bari na tafi tun da ba wanda ya shigo a cikin su." Tana faɗin haka ta yi saurin wucewa tana surutai.. Sake da baki Aisha ke bin bayan Ta Sakkwato da kallo, sai nanata kalamar ba shi da hankali take cike da al'ajabi, dan ita a yanda ta ji kawai dai an ce mata wata matashiyar mace ta kama haya a gidan da mijinta kamar Balarabe. Jinjina kai ta yi ta fito ta yi inda za ta je.. Ta Sakkwato na fitowa ta hango Zaiyan tsaye da shi da ɗayan maƙocin su ya ruƙo hannunsa yana jan shi, da hanzari ta iso garesu tana huci ta kalli Zaiyan ta ce "Ina Jiddo ɗin?" Ta faɗa tana kama hannunsa za ta wuce da shi ta ma manta ta tambayi maƙocin nasu. "Ta Sakkwato wannan ɗin daga ina yake? Ko kin san shi ne?" Juyowa ta yi ta dawo ta ce " Malam Iro ba ka gan shi tare da wata yar baƙar yarinya ba?" Girgiza kai Malam Iro ya yi cike da son ƙarin bayani dan shi bai san su a Unguwar ba, nisawa ya yi ya ce "Baƙi ne kika yi daga garinku? Ni ban gan shi da kowa ba, hasali ba yarona Umar ne ya tare yana ce masa wai ina Anty? To sai ya kirani lokacin na shigo gida ko zama ban yi ba naji kiran shi yana daga ƙofar gida, to da na zo na gansu nake tambayar shi ina yake nema? Sai ya ce min shi Anty yake nema. Umar ya ce min ai yana zaune a ƙofar gida ya gan shi ya fito daga gidanku shi ne na zo na kawo shi, dan na lura kamar ba shi lafiya." Ya faɗa yana kallon Zaiyan da yaje ta murza idanu. "E ba shi da lafiya, matarsa ta fito nemansa yanzu ni ban san ina take ba." Tana gama faɗin haka ta ja hannunsa ganin ya fara kuka suka wuce gida.. Su Maman Amal sun yi cirko-cirko suna jiran dawowar su sai ganin su suka yi su biyu sun shigo, Gamboliya ya ce "Ta Sakkwato yo ina ƴar shawalwalar take.?" Zaunar da Zaiyan ta yi tana rarrashinsa har ya daina kukan amma bai daina faɗin "Ina Anty take? Baba ne ya zo ya sace ta ko?" Haka yake ta faɗa duk suka zuba masa ido, ganin ba zai kyale ba Ta Sakkwato ta dauko masa abinci ta sa masa a gaban shi, ƙin kallon abincin ya yi ya lafe a jikin bango ya yi shuru yana kallon gefe ɗaya. Ganin ya kyale Ta Sakkwato ta shiga ɗaki ta kira mijinta ta sanar da shi halin da ake ciki, shi ma salati ya dinga yi ya ce ta kai maganar wajan yan sanda ko an dace su samo ta, ba ta musa ba ta ce Ladidi su tsare Zaiyan kar su kuskura su bari ya fita suka amsa da to sannan ta fita... Tun da suka ɗauke ta suke ta sharara gudu ba ji ba gani, sai da suka yi tafiyar awa ɗaya da rabi suka yi hon a wani babban get ruwan gold, wangale musu ƙofa aka yi suka sa kai ciki da sauri. Suna gama packing daidai lokacin ta buɗe idanuwanta ta gan ta a cikin mota, firgita ta yi za ta fito ta ji ƙafarta a ɗaure, kallon ƙafar ta yi sai ta ga an buɗe ƙofar, wani rikakken namiji ne ya kunce mata ɗaurin ya mata alama da hannu ta fito daga ciki. Ba muso ta fito tana rarraba ido ganin ta a wani tanfatsetsan gida, murya ta ji daga gefen ta, "Madam muje." Duk inda suka nuna mata nan take bi hankali a tashe ita ba kanta take tausayawa ba mijinta wanda ba kowa zai iya zama da shi ba sai ita da ta zame masa dolen sa shi abin da ya fi damun ta. Wata ƙofa suka bi kamar za su zaga bayan gidan sai ga su a bakin wata kofar ƴar madaidaiciya, dam! Gaban ta ya faɗi nan da nan jikinta ya dauki rawa tuno da abin da ya faru da ita a baya, sai da aka ce ta shiga sannan ta ɗaga ƙafa da kyar ta sa kai ciki. Ganin su ta yi a wani babban palo wanda yake Kusan cike da 'yan mata da samari, gabadaya sun shagala da jin kiɗan wata waƙar turanci wadda in ba shigowa palon ka yi ba ba za ka taɓa cewa an kunna music ba, kallon su take cike da tsoro tana ƙara ƙanƙame jikinta.. Wani matashi ne fari yake nufo inda take tsaye, sanye yake da T-shirt da wandonta iya gwiwa black color, fuskar nan a daure amma duk da haka in ka kalle shi za ka gane ba lefi yana da kyau daidai misali, gefen wuyansa zanen tatu ne an rubuta *Big boy*, haka ma hannuwansa duk an yi rubutu da zanen tatu ɗin, abin ka da farar fata sai zanen ya fito raɗau a jikinsa. Tafiya yake cike da kasaita har ya iso gaban Abir ba ta sani ba tana can ta lula duniyar tunani, yatsunsa biyu ya ɓala mata a kusan fuska ta yi saurin kallon shi, ja da baya ta yi tana nuna shi da hannu baki na rawa ta ce "K.. Kaine?" Saboda ta gane fuskarsa tana ganin shi a Tiktok. Wani ƙayataccan murmushi ya yi bai ce da ita komai ba, sai da ya ga za ta sake masa magana ya nuna mata hanya. Nunawa ta yi ba ta ma san me yake nufi ba, tsare ta ya yi da ido yana kada kai, da wata ce ta masa haka babu abin da zai hana ya kifa mata mari, amma saboda da yadda yake matuƙar so da kaunar ta ya sa bai ji komai ba sai ma birge shi da ta yi. "Idan ba ki tafi da ƙafarki ba ni zan dauke ki na kaiki." Da sauri ta kalle shi ta ga da gaske ɗaukan na ta zai ganin yadda yake janye hannun rigarsa, da sauri ta bi hanyar da ya nuna mata, 'yan matan wajan suka bi ta da kallo cike da mamakin Big boy ganin ta masa gardama bai mata hukunci ba. Wani ɗaki ya nuna mata yana ɗaure fuska, jiki na rawa ta shiga ta tsaye a tsakiyar ɗakin cike da tsoro take kallon ɗakin. Kujera ya nuna mata cike da izza cikin kakkausar murya ya ce "Baby zauna a kan kujera." Ya faɗa yana nuna mata da hannu. Durkushewa ta yi ta fashe da kuka jikinta na rawa, zama ya yi akan kujerar ya kafe ta da ido yana ciza lip ɗin sa na ƙasa shausƙin son ta na jan shi, tashi ya yi ya iso gaban ta ya tsugunna tare da kai hannu da nufin ya goge mata hawaye. A zabure ta yi baya tana girgiza masa kai cikin karaji ta ce. "Kai waye? Me na tsare maka da kake son takura wa rayuwata? Don girman Allah ka rabu da ni na koma wajan mijina yanzu ban san a wani hali yake ba." Ta faɗa tana haɗe hannayenta duka biyun. Dunƙule hannu ya yi ya naushi iska yana dafe kai, wani irin tafasa zuciyarsa take da ta ambaci sunan wani a matsayin miji ba shi ba, ɗago da idanuwansa ya yi da suka yi jajur saboda ɓacin rai ya ce "Ba ki da wani miji wanda ya fini Baby, tun da kika tako ƙafarki gidan nan kin zo kenan har abada, dan haka gobe zan sa a rubuta miki takardar sakin wancan mijin naki sai a ɗaura mana aure. Ina matuƙar son ki Baby kuma duk abin da kike so a gidan nan zan miki, kowacce ƙasa kike so a duniya zan kaiki ki shaƙata ki ga duniya, me za ki da wancan mijin naki da alama ma ko abincin kirki baya baki, kalli yadda kika rame kika ƙara baƙi kamar ba ke ba, zan samar miki da duk wani jin daɗin rayuwa ki share wancan mijin naki. " Ya ƙarashe magana zai kamo ta. Ƙara ta ƙwalla ba shiri ya janye hannun yana faɗin "OK na daina, yanzu faɗa min me kike so a kawo miki? Kina shan giya?" Kwalalo idanu waje ta yi ta sake rushewa da kuka cikin tashin hankali, yau ji take mutuwar ta ce ta zo wai ita ce a gidan masu shan giya har ana tambayar ta ko tana sha? Girgiza kai ta yi ta tsayar da kukan cikin rawar baki ta soma magana. "Kai musulmi ne ko kirista?" Kan shi tsaye ya ce. "Musulmi ne ni." "Inna lillahi wa inna laihin raji'un! Allahuma ajurni fi musibati wa akalifili kharan minha! Wannan wacce irin masifa ce nake gani ni Hauwa'u? Ya Allah ka ceci rayuwarmu ni da mijina daga sharrin bayinka." Saƙare ya yi yana kallon ta, shi bai ga wani abin tayar da hankali ba a maganarsa, ganin ita yake kallo ta daure ta aro jarumta ta gyara zama ta ce "Bawan Allah a ina ka taɓa ganin an yi aure kan aure? Na ce ma ina da miji ko ba ka san haramun ba ne ka ce kana son macen da take da aure? Da ka je Islamiya ba a sanar da kai bambancin haram da halal ba?" Sake kashe shi ta yi da mamaki, can ya maƙale kafaɗa ya ce "Ni ban san komai ba ita kanta Islamiyar ban san ta ba." Waro idanu ta yi tana bin shi da kallo, kamar shi matashi ace bai ma san ya bambance haram da halal ba ai abin mamaki ne, sake haɗe hannu ta yi ta ce "Don Allah bawan Allah ka mayar da ni inda ka daukoni indai har da gaske so na kake." Kallon ta ya yi yadda take zubar da hawaye sai ta ba shi tausayi, miƙewa tsaye ya yi ya ce "Zan sa a mayar da ke, amma ki sa mijin nan naki ya sake ki mu yi aure." Bai mata damar yin magana ba ya nuna mata hanyar fita, da sauri ta bi hanyar tana addu'ar Allah ya taimake ta kar ya canja ra'ayi ya ce ya fasa mayar da ita. Shi kuwa sai da ya tsiyaya giya a wani babban glass cup Sannan ya bi bayan ta, a palo ya gan ta tsaye wanda suke palon duk basa nan, gaba ya yi ta bi bayan shi har harabar gidan. Suna ganin shi maza uku suka taso ya tsilla wa ɗaya key ɗin mota cikin ba da umarni ya ce "Ku mayar da ita inda kuka dauko ta, ban da gudu ku tafi a hankali kar wani ya yi gangancin yin gudu mai yawa har a jijjiga mata jiki, in hakan ta faru kuma kun san gabar ba sai na ƙarasa ba. Sannan idan kuka kuskura wani a cikin ku ya mata ko da kallon second 5 ne zai ya am shi hukunci, kar wanda ya mata magana dan ita ɗin mallakina ce dole ku daraja ta ku ba ta girma kamar Sarauniya. "Ya faɗa yana ja da baya ya shiga shan giyarsa da ya fito da ita... Cike da girmamawa suka ce za su kiyaye, ita dai Abir sakin baki da hanci ta yi tana kallon ikon Allah, da auren ta amma ace dole sai ta so wani dan nuna iko. Motar ta shiga suka ba ta wani baƙin kyale mai kauri suka ce ta daure idanunta ganin Ogan nasu a tsaye suna tsoron taɓa ta, ba muso ta amsa da ɗaura amma ya ce su matsa ya iso bakin motar ya ɗaga hannu a kusan fuskarta ya ce. "Baby ki na gani na?" Girgiza kai ta yi, hakan ya sa ya yi baya ya ba su hannu suka rufe motar. A kan idanuwansa suka bar gidan sannan ya juya ya koma ciki.... Can naisa da Layin su suka sauke ta ta fito ta kunce ɗaurin, doguwar ajiyar zuciya ta sauke hango gidansu da ta yi, amshe kyallen suka yi suka yi saurin barin wajan ita kuma ta yi gaba.. Tafiya take da sauri cike da zullumi ganin wasu samari a bakin hanya duk sun zubo mata idanu, a tsorace ta bi gaban su ta wuce wani ya biyo ta yana faɗin " 'Yan mata ba ki ji ba." A fusace ta juyo ta ce "Malam ni matar aure ce." Tana fadin haka ta wuce fuu sai buga sauri take. Shi ko saurayin a sanyaye ya dawo ya sanar da su wai aure gareta, amma suka ce karya take kawai dai ta ga ta wuce ajinsa ne... So take ta yi gudu amma ba ta son ciwon ta ya tashi, hakan ya sa ta rage sauri jin ta soma huci da sauri, sai da ta tsaya ta ɗan huta tana addu'ar ta isa lafiya kar ta faɗi a waje, miƙewa ta yi ta iso kofar gidan daidai lokacin ana kiran Sallar magariba.. Da Sallama ta shiga gidan babu wanda ya ji ta duk sun taru suna ta rarrashin Zaiyan, shi kadai ya ji muryarta ta kawo wa majiyarsa ziyara ya zabura da sauri ya miƙe ya kalli kofar gida, da sauri ya nufo ta itama ta nufo shi da sauri suka haɗe a tsakar gidan tare da rungume juna suka sa kuka su duka mai tsuma zuciya..... _Maman Nusaiba ce_ [6/20, 8:43 PM] Ummu Amjad: *A HAKA NAKE SON SHI* Shafi na (45) Gabaɗaya da kallo suke bin su cike da tausayawa, ɗago kansa ta yi tana tsayar da nata kukan, shi ma daina kukan ya yi ya sake rungume ta yana ƙanƙame ta tamkar yaron da ya shekara bai ga mahaifiyarsa ba. Lumshe idanu ta yi tana shafa bayansa cikin wani kalar yanayi marar musaltuwa, sake ɗago shi ta yi jin yadda yake matse ta, a hankali ta raba jikinta da nashi ta kamo hannunsa suka ƙaraso wajan su Ta Sakkwato. Gamboliya ya cire mayafinsa cike da alhini ya ce "Ƴar shawalwala wai ina kika tafi tun da rana? Kin tayar mana da hankali matuƙa." Dogon numfashi ta ja ta yi baya ta zauna akan tabarmar da Zaiyan ya tashi da ya ganta, suma duk suka zauna kowa ya zuba mata ido yana son jin abin da za ta faɗa. Ta Sakkwato ta dauko mata ruwa mai sanyi ta ba ta, amsa ta yi ta sha kaɗan saboda muguwa yunwar take ji tafi gaban misali har cikinta ya ƙulle, kallon shi ta yi ganin ya kwanto a kafaɗarta ta girgiza kai, sai da Gamboliya ya sake tambayar ta sannan ta faɗa musu cewar sace ta aka yi. Waro idanu waje duk suka yi Ladidi ya dafe ƙirji yana faɗin "Na shiga uku an fasa aurena! Amma kin tsallake rijiya da baya da har kika kuɓuta daga hannunsu ba su miki komai ba." Sannu suka dinga jero mata tamkar mara lafiyar da kan gadon Asibiti, ita kuwa ta yi shuru tana sauke numfashi, karshe ma ta tashi ta kama hannun mijinta suka nufi ɗaki jiki a matuƙar sanyaye. Towel ta dauko daga cikin kayanta ta dube shi ganin duk inda ta nufa yana biye da ita, dogon numfashi ta ja cike da gajiyawa da kyar ta iya buɗe bakinta, "Ka zauna zan yi wanka ka ji, kuma kar ka fita waje har sai na fito." Maƙale kafaɗa ya yi ya amshe towel ɗin ya daga shi yana duddubawa, ganin hakan ya sa ta ja shi suka shige bandakin, ko a ciki ma haka suka yi wanka yana rike da hannunta ɗaya, ita kuwa duk ta gaji ga takaicin riƙe mata hannu da ya yi ta yi ta magana ya sake mata hannu amma yaƙi ji, bayan ta gama shi ma ta taya shi ya yi wanka sannan suka fito. Sallolin da suke kan ta ta gabatar ɗaya bayan ɗaya tana yi yana biye da ita duk abin da ta yi sai ya yi, bayan ta shafa fatiha ne ta soma tunanin abin da za ta dafa musu ga shi kuma kuɗin hannun nata ya yi ƙasa sosai, dubu goma kacal ya rage mata a cikin dubu ɗari da hamsin da ta zo da su garin kash a hannu, sai dollars guda biyu gareta wanda kyauta ce da Abdul ya mata ranar zayayowar haihuwar ta. Nisawa ta yi tana dafe jikin jin yadda ake mata rugugin da ya haifar da rage kuzarinta, lumshe idanu ta yi sai kuma ta tashi tsaye ta nufi wajan kayan abincin su, taliya leda biyar gare su sai sauran shinkafar su da ta yi ƙasa sosai a cikin buhun, leda ɗaya ta dauko ta haɗo kan kayan miya ta fito waje ta zauna a kusa da rishow ɗin ta. Ladidi da yake ƙoƙarin fidda abincin su na sayarwa ya dakata da fitar, kallon ƙarfin hali ya mata ya iso inda take zaune tana ƙoƙarin tayar da wuta, tsayawa ya yi a gefe yana tafa hannu kamar wanda ya ga abin da ya shallake tunaninsa, ya ce. "Haba ƴar shawalwala, yanzu kuma girkin meye za ki ɗaura?" A matuƙar gajiye ta ɗago ta kalle shi, ita kan ta tasan ƙarfin hali ne take makaho da shiga rijiya, daina ɗaura abincin ta yi hango manyan kulolin kayan abincin su da zai fitar, ta ce "Ladidi tun da ka dafa abincin ka zuba mana wanda za mu ci ni da Zaiyan sai ka faɗa min nawa zan bayar." Ta faɗa tana sauke tukunyar da ta ɗaura. Ladidi bai ce mata komai ba ya nufi ɗakinsu da hanzari, wata yar madaidaiciyar kula ya dauko ya iso wajan abincin, sai da ya cika ta taf da shinka dafa-duka da naman ta ya kawo mata, ta amsa ta miƙe tare da cewa "To tsaya na dauko kuɗin nawa ne?" Gyara zaman mafinsa ya yi tare da karkace kai ya ce "Kin ga ban ce ki ba ni ko sisin kwabo ba, ki je ku ci dan shi ma kan shi mijin naki tun da kika fita har kawo yanzu bai ci komai ba yana ambaton sunanki." Yana gama faɗin haka ya wuce ya dauke abincin ya wuce.. Murmushi ta yi tana bin bayan shi da kallo, tana kuma jinjina kirki irin na Ladidi matsalar shi ɗaya kawai Daudu, wanda ta ce masa ya dawo yadda yake ranar sai da ya wuni bai shiga sabgar ta ba yana fushi. Ɗakin ta shiga ta aje abincin ganin Zaiyan kwance yana rawar sanyi, da hanzari ta iso ta aje abincin tare da kamo shi ta ɗago da shi tana bin shi da kallo, wuyansa ta taɓa ta ji zafi rau ta shafea kansa kamar za ta fashe da kuka ta ce "Ka gani ko? Ban so ka yi wankan nan na Magariba ba ga shi yanzu zazzabi ya rufe ka, tashi ka ci abinci sai na sa a sayo ma magani ka sha." Ta gyara masa zama yadda zai ji daɗin cin abinci, budewa ta yi ta sa masa a gaba ya yi saurin kai hannu zai ci ta riƙe, da kallo ya bi hannun nasu sai kuma ya ƙura mata ido bai ce komai ba, ta harare shi ta ce "Ka ce Bismillah." Ɓata fuska ya yi yana turo baki ya yi bismillah sannan ta sakar masa hannun ya soma ci. Zuba masa na mujiya ta yi tare da rafka tagumi tana ƙara jin tsananin so da kaunar sa na ratsa kowanni ɓargo da jijiya na jikinta, sauke hannun ta yi ta kalli kular abincin ta ga ya cinye bai fi loma uku ba ya bari yana karkaɗe wanda ya zubar masa a jiki, mamaki sosai ta yi ganin yawan abincin ta miƙa hannu ta dauke da nufi ta cinye amma ta ga ya warce, hawaye suka cika mata idanu saboda yadda cikinta ke neman agaji gaggawa har wani zagawa kanta yake. Haƙura ta yi ta miƙa masa ya amsa ya dauko sai ta ga ya kai bakinta, da sauri ta amsa tamkar marayan da ya kwana bai ci ba, yana gama ba ta ta ga ya tashi ya nufi banɗaki , bin shi ta yi da kallo cike da ta'ajjibin abin da ya yi ta miƙe ta bi bayan sa.. Wanke hannu ta ga ya yi ya kurkure baki ya juyo ya kalle ta, mayar da kansa ya yi ya ci gaba da goge bakin ita kuma ta yi ƙiƙam kamar an dasa ta, tana wata duniyar ta ji ya yanyo hannunta yana wankewa, bayan sun gama suka fito... Sai bayan Sallar Isha'i ta fito lokacin Ta Sakkwato ta fito waje tana waya sai sababi take, sai da ta gama ta ɗan rusuna ta ce "Mama barka da dare, don Allah akwai maganin zazzabi a wajan ki?" Sauke wayar ta yi ta kama hannunta suka zauna ta kalle ta da kyau, sannan ta ce "Jiddo amma dai ba ki ci abinci ba ko?" Murmushi kawai ta yi, hakan ya ba ta damar ci gaba, "Wai ni tsaya ma shin ba kin ce min ki na da cutar asmah ba?" Gyada mata kai ta yi ta ɗaura, "Kuma jiya na ga kin yi girki da gawayi amma ciwon naki bai tashi ba, shi ne nake ta mamaki saboda an ce masu irin cutar basa son hayaƙi ko su yi gudu hakan zai tasar da ciwon nasu, ke kuma jiya kin tari hayaƙi ba ki yi komai ba." Murmushi ta yi ta ce. "Mama ni ma kaina na yi matuƙar mamakin hakan, saboda gas ɗi na ya ƙare na amshi gawayi a wajan Gamboliya ina jin tsoro haka na ɗaura, sai ga shi dai Alhamdu Lillah har na gama ban ji komai ba, gara ma ɗazu da ina sauri ina haɗawa da ɗan gudu naji kamar ciwon zai tashi amma yanzu Alhamdu Lillah bai tashi ba. Kila ko Ubangiji ne ya amshi Addu'ar da nake ba dare ba rana akan wannan ciwon nawa, saboda yadda na tsinci kaina a cikin jarrabawar rayuwa sosai hankalina ke tashi in zan yi girki, ina addu'a Allah ya sa karshen wahala ta ta zo akan wannan ciwo da nake fama da shi tun ina karama." Ta faɗa tana goge hawayen da suka zubo mata. Dafata Ta Sakkwato ta yi tana girgiza mata kai, sannan ta ce "Jiddo ya kamata ace kin fara sana'ar da za ta riƙe ku da sauran kuɗin da ya rage hannunki, kin ga in kina biɗar wani abu ba sai kin wahala sosai ba tun da kina da abin yi, ina kuma fatan Allah ya sa hanyar warkewa ce Allah ya kawo miki a daidai lokacin da kike tsananin buƙatar hakan. Amma waye ya sace ki? Ki hwaɗa min komai kinjiya karki boye min wani abu dan ke kamar ɗiyata ta ce. " Share wahaye ta yi ta ce " Mama na gode da irin yadda kike nuna damuwar ki a kanmu ni da mijina Allah ya biya ki, in sha Allah zan soma sana'a saboda kuɗin da ke hannuna sun kusa ƙarewa saura kaɗan, amma zan kai dollars a bani naira sai na ga me zan ke sayarwa. Wani mutum ne ya sa aka sato masa ni wai so na yake zai aure ni. " Kwalalo Idanu Ta Sakkwato ta yi ta ce "Auren ki zai yi? To ba ki ce masa ke tun tuni an miki aure ba?" Nisawa ta yi ta ce "Na sanar da shi Wallahi..Nan dai ta kwashe komai ta sanar mata." Dafe ƙirji kawai ta Sakkwato ta yi tana zaro idanu, sai da ta jima tana juya lamarin a ranta sannan ta ce "In sha Allah babu abin da zai miki, kuma ba zai sake dauke ki ba, shi mahaukacin ina ne da zai ce yana son matar aure? Anya ma wagga yaro ya yi karatun addini kuwa? Ni yanzu ba wannan ba, kin iya irin sana'o'i na hannu?" Gyada mata kai ta yi ta ce "Na iya kitso da ƙunshi, ina yi wa Iman wani lokacin har Laraba ina yi wa, ƙunshi kuma musamman aji na shiga aka koya min a lokacin na shiga da zummar nake yi wa kaina ba sai naje na biya kuɗi ba an yi mini, tun ban iya ba har na kware amma ba wanda nake wa sai ƙanwata Iman, dan duk gidanmu ita kaɗai ce take hulɗa da ni. " Gyara zama Ta Sakkwato ta yi ta ce "Ma sha Allah, to ai kuwa zan samo miki customer sosai dan duk Layin nan mace ɗaya ce take kitso, mai lallen kuwa sun tashi. In sha Allah zan sayo miki kayan lallen da kuma kayan kitson ki fara yi min har lalle sai na nunawa kawayena." Wani sanyi ta ji ya ziyarci masarrafarta sosai ta ji daɗin wannan bayani, haka suka cigaba da hira.... Gari na wayewa Ta Sakkwato ta tsife kitson kanta ta zauna Abir ta yarfa mata kitso na gani na faɗa, su Maman Amal suka dinga yaba kitson yadda ta yi mai kyau sosai kowa sai yabawa yake, hakan ya sa Ta Sakkwato ta dube su fuska a ɗan daure ta ce "Kun ga idan har idanuwanku sun ga abin da zuciyarku ta yaba to yana da kyau ku ce ma sha Allah ko da ba a fili ba ne, ku daina hwaɗin magana kai tsaye ba tare da kun ce ma sha Allah ba." Maman Samira ta rausayar da kai ta ce "Yi hakuri Ta Sakkwato in sha Allah ba za mu kuma zuzuta abin da ya birge mu ba tare da min ce ma sha Allah ba." Hanci ta hura tana cewa "To ni dai na hwaɗa muku gaskiya ku gyara." To suka ce mata Abir na ta murmushi duk suka zauna a gaban ta Maman Amal ta ce "Don Allah Jiddo za ki yi min irin kitson da kika yi wa Ta Sakkwato? Kuma nawa zan ba da? Dan gaskiya ya yi min matuƙa kin ga mijina gobe da dare zai dawo ki min har da lalle tun da Ta Sakkwato ta ce har shi ma kin iya, sai ki min lissafi naji nawa ne." Sunkuyar da kai ta yi ta ce "Ai ku yan gida ne ba sai kun biya ba." Ta Sakkwato da ta fito daga ɗaki ta yi caraf ta ce "Babu maccen da za ki yi wa kitso a sadaka, dan kowacce mijinta yana ba ta kuɗi in za ta yi, in kina so a miki wannan kitson irin na manyan Hajiyoyi da lalle dubu biyu za ki ba da." Waro idanu Maman Amal ta yi ta ce "Haba Ta Sakkwato dubu biyu kuma? Gaskiya a rage min ni fa ƴar gida ce, duka ma kuɗin da aka bani dubu ɗaya ne na kashe ɗari uku a ciki sai ɗari bakwai ya rage." Ta Sakkwato ta kada kai ta ce. "To kin ga Kuwa dole ayi miki na daidai kuɗinki ba irin nawa ba, ko ni biya zan yi dubu uku ma ni zan ba ta cif." Ita dai Abir ba ta ce ba komai sai murmushi take da an jima ta leka Zaiyan da yake ta bacci tun na dare bai tashi ba.. Bayan ta gama yi mata lalle suka dinga yabawa Ta Sakkwato na sababi ta ce dole su ce ma sha Allah kar bakinsu ya faɗa ƴar mutane, suka ce to.. Washegari da rana ta yi wa Maman Amal kitso da ƙunshi, sosai lallen ya birge Maman Amal ta dauko waya ta ce ayi mata photo ta turawa Baban Amal ya gani kafin ma ya iso, ganin wayar ba za ta fito da kyan ƙunshin ba Abir ta ce "Jira bari na dauko wayata na miki da ita za ta fi haskawa." Ɗaki ta shiga ta dauko iPhone ɗin ta suka dinga bin wayar da kallo, sai yanzu suka sake tabbatar da cewa lalle fa duk inda Abir ta fito ɗiyar masu hannu da shuni ce. Photo ta yi har da ɗan short video ta yi wa kitson ƙunshin ta yi iya photo, Ta Sakkwato ta ce ta dauki nata ƙunshi da kitson ta buɗe account take tallata sana'arta, ta amsa da to.. Bayan ta gama mata da yamma ta shiga Tiktok ɗin ta ta goge sunan da aka san ta ta sanya *Zaijiddatu* ta canja email da komai nata wanda aka sani, karshe ma ta goge duk wani post da ta yi a Tiktok wanda aka san ta da sunanta *Princess Abir* ya dawo *ZaiJiddatu*, ta poster ƙunshi da kitson ta kuma yi rubutun cewa tana ƙunshi da kitso ga duk mai so ya mata DM sannan ta sauka. Haka ta koma Istagram ta canja suna kamar yadda ta sa a Tiktok ta canja komai, WhatsApp ɗin ta da aka san ta da number ta canja ta sa special number ta wadda iya mutum hudu ne yake da ita Suhal, Abdul, Mommy, Iman, number Abdul ta shiga ta yi blocking ɗin shi ta goge number shi. Number Mommy ta shiga inda ta ga last message ɗin da ta mata wanda a ranar ta rasu, hannu ta kai ta shafa rubutu tana goge hawaye cikin tsananin kewa ta ce "Allah ya jiƙan ki da rahama Mom, nasan da kina raye rayuwata ba za ta zama haka ba duk da nasan idan Allah ya dauro wa bawansa ƙaddara a rayuwa babu wanda zai yaye ma sai shi, amma duk da haka nasan da ace kina duniyar ko da magana mai daɗi ce za ki min dan naji sanyi a raina. " Kwanciya ta yi tana kuka marar sauti.... _NIGER_ Suhal na shirin fita fada Iman ta tsare shi da rigimar sai ya sanar da ita dalilin zaɓar ta ya bar yayarta. Zama ya yi yana ɗaura agogo cike da gajiyawa da wannan tambayar, yau dai ya ƙudurta a ransa zai sanar da ita dan ya huta da tambaya, turo baki ta yi ta matso kusa da shi ta ce "Ni Wallahi sai ka faɗa min dalilinka in ba haka ba na gudu." Murmushi gefen baki ya yi ya kamo ta ya zaunar tare da zuba mata idanu, tsumkon shi ta yi a wuya ya runtse idanu yana jinjina ƙeta irin ta Iman, a nutse ya buɗe idanuwansa ya sauke su a kan ta ya kama hannayenta ya ce "Kin shirya jin dalilina? Sannan idan na faɗa miki ba za ki shiga ɗumuwa ba?" Saurin gyaɗa masa kai ta yi tana gyara zama, kawar da kai ya yi yana tuna abubuwa da dama da suka shuɗe amma ya kasa manta su, idanuwansa ne suka ciko da kwalla amma ya yi saurin shanye su ya juyo da kansa gareta, ta tsorata da ganin yadda idanuwansa suka yi jajur, amma saboda ta matsu ta ji me zai ce mata ta marairaice ta ce "Ya Suhalll.." Ta ja sunan hakan ya sa ya saki murmushin da bai shirya wa zuwan sa ba, nisawa ya yi ya ce "Iman a yanzu babu wanda ya fiki kusanci da ni, gado ɗaya muke kwana mu ci abinci a tare duk wani ɗabi'una kaɗan ne ba ki sani ba, wannan maganar ma tana daya daga cikin ɗabi'una da ba ki taɓa jin su ba. Ba na son hankalinki ya tashi da jin wannan maganar amma babu yadda na iya tun da kin takura sai kin ji zan sanar da ke yanzu. " Ya tsagaita yana kallon ta, ita kuma ta kafe shi da kallo, hannunta da ke cikin nasa ya murza a hankali yana lumshe idanu sannan ya ci gaba "Na sadaukar da soyayyata ne dan na ceci rayuwar Princes a sakamakon mugun ƙullin da aka ɗauri niyar yi mata dan a raba mu, an yi niyar cutar da ita dan tun farko kasheta aka ce ayi amma abin ya gagare su." Kwalalo idanu waje Iman ta yi tana kallon shi, baki na rawa ta ce "M.. Me ta tsare musu a rayuwa ne?" Girgiza kai ya yi ya ci gaba "Tsanar da aka yi wa mahaifiyarta ne ya shafe ta, ganin ta taso kowa na familynku na son ta, ki yi haƙuri da jin abin da zan faɗa Iman, ba kowa ba ne ya mata wannan cutarwar sai Umma." A mugun zabure ta miƙe tsaye baki na rawa, kamo ta ya yi ya zaunar da ita jikinta sai rawa yake, gabaɗaya hankalinta ya bala'in tashi ƙarshe ma ta fashe da kuka ta soma magana cikin fitar haiyaci, "Wallahi da ana canja uwa ni dai da na canja tawa uwar, ashe tsanar da Umma ta yi Anty Baby har ta kai ta hana ta yin aure? Ya Allah ka kare min Anty Baby a duk inda take, Wallahi ni dai ban yi sa'ar uwa ba n... Saurin rufe mata baki ya yi jin za ta yi saɓo, rungume ta ya yi yana bubbuga bayan ta cikin kwantar da hankali ya ce "Ki daina kuka kawai ki yi wa Umma addu'ar shiriya, labarin yadda Umma ta je gidan Malam ya sanar da ita shi kuma da yake bibiyar duk wani motsi nata hankalina ya tashi, ya ƙara da cewa "Ni kuma na ga Khairat ba ta cikin tsarin matan da nake so da aka zo ɗaurin aure na ce ke nake so duk dan na kubutar da Princess daga sharrin Umma." Tsayar da kukan ta yi ta ce "Amma kai ya aka yi to asirin bai kama ka ba?" Murmushi kawai ya mata bai ce komai ba ya mayar da ita jikinsa ya ci gaba da rarrashin ta, sai da ya ga ta saki ranta sannan ya ce kar ta kuskura ta nuna wa Umma ta san wani abu game da abin da take ƙullawa a gidan, to ta ce masa ta kuma ƙudurta a ransa duk daren Allah za ta tashi tsaye ta yi ta nafila tana nema wa ƴar'uwarta kariya daga sharrin mahaifiyarta.... Sai da ya ga ta yi bacci sannan ya wuce ya bar ɗakin, bayan ya gaishe da Mamma ya nufi ƙofar fita ya buɗe zai fita, wani abu baƙi ya gani kamar gawayi an barbaɗe ƙofar da shi sai wani irin wari yake, girgiza kai ya yi yana murmushi ya ce "Hmmm rai dai." Wata Hadima ya gani za ta wuce ya kira ta, jiki na ɓari ta iso ta durƙusa tana gaishe shi ya amsa ba yabo ba fallasa, nuna mata wajan ya yi ya ce yanzu ta share ta goge tas ta amsa da to. Dawowa palo ya yi ta share komai ta goge sannan ta ɗan leƙo da kai ta sanar da shi ta gama, da hannu ya mata nuni da ya gode sannan ta wuce tana ta mamakin abin da ta share. Sai da ya karanta ayatul kursuyi da falaƙi da naasi sannan ya yi bismillah ya fito, gabaɗaya masarautar ta isheshi da duk abin da ke cikin ta, ba dan yana tuna Mamma da Ikilima ba da babu abin da zai dawo da shi Niger zai yi zamansa a Germany ya amshi tayin aikin da suka masa na likitanci, yana ta saƙa da warwara har ya isa fada.... Duk abin da aka yi a kan idanun Jakadiya ta yi kwafa ta wuce fuu.. _NIGERIA_ abubuwa sun kankama na siyasa su Alhaji Mustapha babu zama ba su da lokaci, duk inda suka ji wani gidan marayu sai sun je sun kai taimako tare da yan jarida su dauki video suna yaɗawa a kafafen sadarwa, suna nuna irin taimakon da Alhaji Mustapha yake yiwa mabuƙata, hakan kuwa ya ƙara kankaro masa mutumci da ƙima a idanun al'umma duk inda ka yi a Jahar Yola maganar shi ake, hakan na faranta ran Alhaji Mustapha da abokan nasa matuƙa. Kacokan suka dauki nauyin gidan talabijin na jaridar *zo ka sha kallo* wannan gidan radio ya yi hura a jahar Yola dan haka duk abin da aka yi suka watsa a media sai ya bazu gari, su kan su masu aiki a gidan redio suna ta yabon Alhaji Mustapha saboda yadda yake musu ɓarin kuɗi in ya zo aka tattauna da shi... Yau ma sun tashi daga wani taro sai ga kiran Abdul ya shigo wayarsa, saurin ɗauka ya yi ya koma can gefe inda ba hayaniya ya yi picking call ɗin. A hanzarce ya ce "Hello Abdul ya aka yi ne.?" Daga can ɓangaren Abdul ya ce "Dad lamari yana neman ya ɓaci fa." Zaro idanu ya yi ya ce "Kamar yaya kenan?" "Dad an kama wasu kaya da aka dauko su daga Legos zuwa nan Yola, kuma nasan kayanka ne haka suma direbobin suka ce kayan ka ne amma abinci ne da za ka rabawa talakawa, bana so Ogan mu ya samu labarin an kama kayan saboda ya soma zargin wani abu a game da kai. Yanzu duk inda kake ka zo a samu ka amshi kayan nan kafin ya ji labari. " Zufa ce ta shiga karyo masa ta ko'ina ya sa gefen malum-malum ya sharce kamar mayen da ya ci ɗa a kasuwa ya juya ya ga kowa hulɗar gaban shi yake, marar gaskiya ko ruwa sai ya yi zuba! Ya sake matsawa ya ma rasa me zai ce saboda kaso biyu bisa uku na dukiyarsa ya zuba ya yo safarar wannan kayan tun daga ƙasar Japan, ja baya ya yi ya nisa sannan ya ce "Ga..Gani nan zuwa." Yana sauke wayar ya ji ƙaran shigowa text message bai duba ba ya mayar da wayar a aljihu ya juyo zai tafi suka yi kiciɓus da Jarmai, kallon shi ya yi ganin shi ma a ruɗen yake ya ce "Jarmai ya dai?" Nuna masa text ɗin da aka yo masa ya yi yana huci, kafin Alhaji Mustapha ya karanta kira ya shigo wayar, ganin sabuwar number ce sai yaƙi dauka yana kallon Alhaji Mustapha. Sake kira aka yi hakan ya sa a fusace Jarmai ya ɗaga kiran ya buɗe sauti dan Alhaji Mustapha ya ji, a kufule Jarmai ya ce "Wai uban waye kai?" Dariya ya yi wadda ta sa su zabura suna kallo juna, sai ya yi gyaran murya ya ce "Ku har kun isa ku ci banza? To wasan ya kusa zuwa karshe wannan karon sai kun bambance tsakanin aya da tsakuwa." Ƙara fusata Alhaji Mustapha ya yi, gabaɗaya ya rasa abin da yake masa daɗi ya ce "To kai waye?" Sake yin wata dariyar ya yi sannan ya ce "Damisa bisa kanku..." _Maman Nusaiba ce_ [11/30, 1:59 Safiya] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): *A HAKA NAKE SON SHI* Shafi na (46) A mugun firgice suka kalli juna suna zare na mujiya, jikin Jarmai ne ya ɗauki rawa ya saki baki ya bi wayar da kallo kamar ya ga wata sabuwar halitta, Alhaji Mustapha ya ja numfashi gabaɗaya ya gama jiƙewa da zuba sai zaro idanu yake, Jarmai ya mayar da wayar aljihunsa tare yin ƙasa da kai kamar bafade a gaban sarki, ya ce "Damisa nan yana shigar mana hanci da ƙudundune fa, shin ba Boka na kan dutse ya faɗa mana cewa ba zai sake waiwayar Nigeria ba? Ko kuwa dai akwai abin da muka yi ba daidai ba a cikin sharruɗan da Boka ya gindaya mana?" Ya faɗa yana ɗago da kai ya kalle shi cikin idanu. Alhaji Mustapha bai ce komai ba, duk lissafinsa ya karkata ne kan kayansa da ke hannun 'yan sanda, ba ya so su buɗe su ga abin da yake cikin kayan duk da kuwa yasan abu ne mai wahala su iya buɗe kayan har su gani, amma hakan bai hana shi shiga ruɗu da tashin hankali ba dan duk wani ƙarfinsa ya ta'alƙa ne a kan kayan, dawowar Damisa ba ta girgiza shi ba kamar ta kayan dan haka ya harɗe hannaye a ƙirji tare ta kallon Jarmai. Ganin ba zai tanka masa ba ya matsa ya juya zai tafi dan ransa ya sosu da hakan, kama hannunsa ya yi tare da cewa "Sorry Jarmai ina cikin yanayi ne, idan muka yi sake fa ɗan zaki zai girma." A fusace Jarmai ya juyo ya ce "Girma kuma na yaushe? Ai tuni ɗan zaki ya gama girma har ma ya fito farauta." Ya faɗa yana hura hanci sama. "OK yanzu ka je Office ɗin su Abdul ayo belin kayan nan, ni kuma zan samu Alhaji mu tsara yadda Damisa zai faɗa tarkonmu, wannan karon na sha alwashi sai mun masa kisan gilla." Bai ce komai ba ya wuce yana gyara zaman babbar rigarsa, shi ma tafiyar ya yi suka ƙarasa sallamar mutanen da suka zo sannan suka bar wajan.. Gana mostgo ɗinta ta cicciɓo tana nishi saboda kayan da ke ciki masu nauyi, palo ta iso ta aje tana haki ta kalli Grandma da su Abba duk sun hallara a palon har da Daddyn Aruf, da kallo duk suka bi ta ta yi kwafa a ɓoye tana sunkuyar da kai ta ce "Inna ni zan wuce ƙauyenmu sai kuma na ce Allah ya sada mu da alkhairi." Kallon ta Grandma ta yi tana rike haɓa ta ce "Yau gani ga ja'irar yarinya, me ya yi zafi shi ba wuta ba? Ki mayar da kayan nan kin ji ƴar albarka." Kukan karya ta sa tana durƙusawa a gaban ta ta ce "Babu abin da aka min Inna, kawai dai zan koma wajan mahaifiyata ne na ci gaba da kulawa da ita." Su Abba suka yi ta fama ta haƙura ta ƙara ko da wata 6 ne in ya so sai ta tafi amma ta nuna musu ita fa ta gaji ta aikatau ɗin nan hutawa take son yi, babu yadda suka iya haka suka haƙura suka rabu da ita ta mike ta dauki kayan, har Abba ya ce ta tsaya a kai ta har garin nasu amma ta ce za ta biya gidan da kawarta take aiki direban gidan zai kai su, haka dai Abba ya dauki kuɗinta na wata biyar da ba a ba ta ba ya miƙa mata tare da cewa "To ga haƙƙinki ko." Sunkuyar da kai ta yi ta ce "Ni ai tun kafin Abir ta yi aure ta biyani kuɗin shekara, dan haka ba sai kun ba ni kuɗi ba an biyani tun kafin ma na yi watannin." Wani irin nauyi ne ya danne musu zuciya gabadayan su jin ta ambaci sunan Abir, har Abba zai yi magana amma ya kasa saboda bakinsa ya masa nauyi, yana so ya tambaye ta a ina Abir ɗin take amma nauyin da ya danne masa zuciya ya hana shi furta hakan, ita kuwa duk tana kallon fuskokinsu ganin yadda lokaci ɗaya suka canja ta jinjina kai ta musu Sallama ta wuce suka bi ta kallo ba wanda ya ce mata a sauka lafiya, itama ba ta damu da hakan ba dan tsare ta da tambaya da suka yi sun kusa ɓata mata lokaci. A harabar gidan ta ci karo da Adul ya fito daga cikin motarsa, da kallo ya bi ta cike da mamaki ganin ta dauko kaya ta nufi get, da hanzari ya kira sunanta ta waiwayo ya mata alama da ta zo, ba muso ta iso gaban shi tana sauke jakar ta rusuna tare da cewa "Yaya Abdul barka da rana, ya wajan Anty Hafsat?" "Barka dai Laraba ina zuwa haka na ga kin kinkimo gana mostgo kamar ƴar yawon cirani?" Kallon ba ka da aikin yi ta masa dan mugun haushinsa take ji in ta tuna irin dukan da ya yi wa Abir, ta wani sashen kuma ya ba ta tausayi ganin yadda ya fige ya rame duk ya yi baƙi ya zama kamar wani dolo, kamar waina a tanda sai juya shi ake son rai. " Gida zan koma Yaya Abdul." Da mamaki ya kuma kallon ta sai ya basar ya zaro kuɗi ya miƙa mata tare da cewa "Ga wannan duk da ban san ba a nawa Mom ta dauko ki duk wata." Kallon hadarin kaji ta masa ta mike tsaye ta ɗaura gana mostgo ɗinta a ka ta kalli kuɗin, wani maƙoƙo ne ya tokare mata maƙoshi ta nisa ta ce "Ka aje kuɗinka an biya ni haƙƙina sai an jima." Ba Ta ma tsaya ta ji mai ce mata ba ta wuce da sauri ganin time na tafiya ta buɗe get ta wuce abin ta mai gadi na mata Allah kiyaye tana amsawa da amin har ta bar gidan.. Tafiya take da sauri kamar za ta kifa, sai da ta isa bakin babban titi ta tari mota ta ce ya kai ta airport, nan ya sanar da ita dubu uku za ta ba shi tun da ita ɗaya ce ta ce ba matsala. Tun da suka kama hanya ta ciro iPhone ɗinta nan ta ga saƙon shi ya ce mata karfe 11 na rana zai sauka, agogon wayar ta duba ta ga 10:40am ta sauke ajiyar zuciya tana murmushi. Suna isa ta biya shi kuɗin sannan ta nufi filin jirgin ta samu waje ta zauna, tana nan zaune jirgin su ya sauka aka buɗe mutane suka dinga fitowa ɗaya bayan ɗaya, cikin shigar shi ta ƙananan kaya masu yi masa matuƙar kyau ta hango shi yana taka matakalar jirgin yana saukowa, sosai ya mata kyau ya sha baƙin glass sai wani shan ƙamshi yake cike da izza da nuna shi ɗin mai aji ne yake saukowa, yana fitowa ya zaro wayarsa a aljihu ya danna mata kira, tana murmushi idanuwanta a kan shi ta daga kiran. "Hello Jk kin iso ne?" Ɗagowar da zai yi suka haɗa idanu ta mike tsaye tana ƴar dariya, yadda Ogan nata yake ɗaukar wanka abin na ba ta citta, har ya iso ba ta sani ba sai da ya ɓala yatsunsa ta firgita tana sa ƴar ƙaramar dariya ta ce "Welcome to Nigeria again sir." Murmushi ya yi mata tare da cewa "Thank you." Kayan nata ya amsa ya ɗaura akan akwatinsa ya dube ta yana yin gaba ya ce "Jk duk meye a cikin jakar nan ta yi nauyi?" Gefen shi ta dawo suka jera ta ce "Computer guda biyu ce a ciki sai tufafina wanda Abir ce ta ba ni su masu kyau." Jinjina kai ya yi bai sake cewa komai ba ta ga sun nufi wata baka mota mai kyau, shiga suka yi direban ya ja suka wuce. Sai da suka bar Airport din direba ya ce "Welcome back Oga, Ni ai na dauka kai da Nigera da sunan aiki ka gama sai dai ka zo dan hutawa, ko da ma za ka zo ɗin ba dai Yola ba sai dai ko Abuja ko Kano." Gyara zama Damisa ya yi ya ce "In sha Allah wannan karon shi ne zuwana na karshe da sunan aiki, kuma har Kano zan je ina da wasu abokan aiki a can." "To Allah ya taimaka Oga, Jk ke ma kin ɓata rabona da ganin ki tun zuwan ki na farko ƙasar nan." Ƴar dariya ta yi ta ce "Muhammad kenan, yo ai ni ina ƙasar babu inda naje." Sani halin Damisa baya son a dinga doguwar magana sai kawai ya ce ta ji daɗi. Wani dan madaidaicin gida suka yi hon aka bude musu get suka kutsa ciki, suna gama packing suka fito Maigadi na musu barka da zuwa ya amsa sannan suka wuce ciki.. Wanka suka yi Laraba ta canja kaya ta sanyo abaya ta fito ta ɗaura musu girki mai rai da lafiya, a cikin kalolin girkin da Mom ta koya mata ta musu haɗaɗɗan girki. Bayan sun gama cin abinci suka dawo palo kowa ya fito da computer shi suka hau aikin da yake gaban su.. Yau kawayen Ta Sakkwato suka zo kitso wajan Abir tun karfe 10:30am na safe, manyan mata ne irin 'yan kwalisar nan matan masu hannu da shuni, Abir ta yi ta mamakin inda ta Sakkwato ta samu irin wannan ƙawaye haka, jin ana kiran ta ta ɗago da kan Zaiyan da zazzabi mai ƙarfin ya rufe shi ta kwantar. Bude idanuwansa ya yi ya sauke su akan ta ta sakar masa murmushi ta ce "Ka kwanta ka ji in sha Allah zuwa gobe zan kaika asibiti in kuɗi suka taru, yanzu na yi baƙi kar ka fito waje an jima zan shigo na ba ka magani." Ta faɗa tana taɓa gefen wuyansa ta ji har yanzu zafi rau zazzabin na nan bai ragu ba, cike da damuwa ta janyo ɗan madaidicin bargonsu ta lulluɓa masa ta fita. Da kallo ya bi ta har ta rufe masa kofar ya tashi ya zauna, kansa da ke mugun sara masa ya riƙe yana jin yadda ake masa dakan tsakwara a cikin kan, wani kalar numfashi ya dinga fitarwa ya yi baya ya faɗa kan katifar, nan da nan jikinsa ya dauki rawa ya ƙanƙame jiki yana fitar da numfashi da sauri-sauri tamkar wanda ya zo gangarar mutuwa. Wani farin kumfa ya dinga fita daga bakinsa idanuwansa suka ƙaƙƙafe ya dinga fisgar numfashi da ƙarfi yana durje-durje irin na wanda rai ke ƙoƙarin fita daga gangar jikinsa, can kuma kamar an tsikara masa allura idanuwansa suka dawo daidai ya tashi zaune yana rarraba idanu, wani kalar murɗawa cikinsa ya yi ya cije lip ɗinsa na ƙasa yana juya kai, tamkar macen da ke kan nakuda ciwo ya tashi ba zama ba tsayuwa haka Zaiyan ya dinga birgima yana juyi. Ya daɗe a haka cikin ya sake murɗawa sai amai ya biyo baya kamar an bude famfo, sai da ya amayar da abin da ya ci tas amma bai daina kakarin aman ba sai nishi yake, ya dauki lokaci a haka tukun ya daina kakarin ya zube a gefen da ya yi aman sai bacci... Abir kuwa na can a ƙofar Ta Sakkwato tana yi wa ƙawayenta kitso, amma gabaɗaya hankalinta sam ba ya ga hirar da suke yana kan mijinta, abubuwan da ya tsuro a cikin satin nan duk ya dame ta, ya daina magana ba ya iya cin abinci sosai da ya soma ci zai turo, wanda a in a baya ne zai ci abincin mutum uku ƙwarara ya kuma ce mata bai ƙoshi ba sai dai ta rabu da shi dan kar ya ƙwari cikinsa, ya dawo kamar kurma komai za ta yi masa sai dai ya kalle ta da ido kawai ba ya cewa e ko a'a. Nisawa ta yi jin ɗayar matar na cewa "Jiddo ni irin na ta Sakkwato za ki yi min." Murmushin yaƙe ta yi tana ƙarasa wa wadda take wa ta ce "To Hajiya in sha Allah." Kallon ta matar take sai kuma ta ce "Jiddo kamar fa na taɓa ganin fuskarki a Tiktok, ba ke ba ce aka ce za ki auri ɗan sarkin Niamey sai ranar ɗaurin aure ya ce ba ya son ki ƙanwarki zai aura?ko ba ke ba ce tabbas kuna kama gaskya, sai dai kamar ita wacce ɗiyar masu kuɗi ce a garin Yola ko ya ma sunan Familyn nasu?"Ta faɗa tana sake kallon Abir. Tun da ta fara magana gaban Abir yake bugawa cikin tashin hankali, gyara zama ta yi ta kalli matar tana murmushi ta ce" Ayya Allah sarki Hajiya, ni ma wannan matashiyar ƴar tiktok ɗin naji ana maganar ta sosai, an ce tana kama da ni amma ni ban ma san ta ba gaskiya, matso a kama miki mijina ba shi da lafiya yana ɗaki a kwance. " Ta nisa ta dubi Ta Sakkwato ta ce "Mama don Allah ki yi wa Baba waya in zai dawo ya zo min da maganin maleria." Ta Sakkwato da ta yi saƙare tana kallon ƙawata ta ɗauke kanta daga kallon ta ta dawo kan Abir, ganin yadda duk ta yi kicin-kicin da fuska sai ta ji ta ba ta tausayi, tasan rayuwarta ta baya ta tuna. Tashi ta yi ta shiga ɗaki ta dauko waya ta kira mijinta ta sanar da shi ya tafo wa da Abir maganin maleria ya amsa da to sannan ta kashe kiran, tana fitowa ta sanar ta ita ya ce zai kawo mata ta mata godiya.. Komai cikin sauri take yi dan ta ƙagara ta gama musu su tafi ko ta koma wajan mijinta, tana gaf da gamawa ta biyun sai ga wasu yara biyu, dayar ba ta fi 14 ba dayar kuma ba ta fi ƴar shekara 10 ba sun yo wajan su da sallama, amsa musu suka yi babbar ta kalli Ta Sakkwato ta ce "Ta Sakkwato Mamanmu ta ce mu zo wajan ki ki sa Jiddo ta mana kitso da lalle za mu tafi wajan biki Kaduna gobe." Murmushi ta yi sai kuma ta ce "Ku zo na ga kuɗin hannunku in bai kai yadda ake yi sai ku koma ta ƙaro muku." Kuɗin suka miƙa mata ɗari biyar ce, riƙe baki Ta Sakkwato ta yi ta ce "Wallahi Aisha muguwar ƴar rainin hankali ta, yo wannan ai kuɗin babbar ne ta bayar." Wayarta ta dauka ta kira Aisha ta rufe ta da masifa tana fadin wai babbar za ayi wa kitso da ƙunshi dayar kuma sai ta ƙara biya, da kyar da siɗin goshi Aisha ta shayo kan Ta Sakkwato ta ce za ta shigo ɗaukan su sai ta ƙaro ɗari uku ayi musu su duka, duk da haka sai da Ta Sakkwato ta mata tas sannan ta kashe wayar. Duk da Abir na cikin damuwa sai da ta yi murmushi ganin yadda Ta Sakkwato take masifa har kumfan baki take, sake kallon ta ta yi ta ce "Allah Mama ki rage faɗa, kin ga su yan gida ne ana mutumci sai ake rage musu ai ba komai." Hararar ta Ta Sakkwato ta yi ta ce "Wagga yarinya ba ki san rashin daraja irin ta matan Layin nan ba, indai kika nuna za ki musu Kyauta to fa sai sun kai ki maƙura, dan duk wacce ta kunce kitso za ta zo ki mata ta ba ki naira ɗari biyu ta yi gaba dan ba su san zafin sana'a ba, dan haka ki ma daina yi musu sako-sako kar su kashe ki daga tsaye. " Ita dai murmushi take ƙawayen ta Sakkwato suka biya ta kuɗi mai tsoka tare da mata godiya suka tafi. Har ta yi wa babbar rabin kison ta ji ana kiran Sallah ta saki ta ce za ta yi Sallah, suma cewa suka yi za su yi Sallar Ta Sakkwato ta ja su ɗakinta... Buɗe ɗakin ta yi ta shiga sai ta gan shi kwance kan tabarma, isowa ta yi sai ta ga amai felas a gaban shi ta waro idanu tana birkito shi, tashi ta yi ta dauko ɗan ƙaramin towel ɗinta na ka ta jiƙo da ruwa ta dawo kan shi, fuskar ta goge masa ta tare da ɗago da kansa ta tura shi da kyar ta ɗaura masa kan akan katifa, rigar jikinsa ta cire ta rufa masa bargo ta dawo tsakar ɗakin ta goge aman tana zubar da hawaye ciki da tausayawa, sai da ta goge tas ta gyara wajan ta dauko turare har za ta fesa sai ta tuna in fa ta fesa ta shaƙa akwai matsala, banɗaki ta koma ta tsiyayo chappo da suke wanka ta zuba ruwa ta dauko ta goge tsakar da shi. Sai a lokacin ta ji ƙarnin aman ya ragu sosai ta wuce toilet ta ɗauro alwala, tana fitowa ta gabatar da Sallah ta daga hannu sama tana ta kwararo musu addu'a ta samun sassauci na halin da suke ciki ta shafa. Fitowa ta yi ta ƙarasa musu bai ma bushe ba yaran suna murna suka tafi gida ganin uwar tasu ba ta zo ba da ta ce za ta shigo, ita kuma ta ɗaura musu girkin taliya fara da man ja, ko da ta gama kasa ci ta yi saboda jikin nasa ya yi zafi sosai, ga shi duk ta haɗa kan kuɗin da ke wajan ta ta sayo musu kayan abinci iya kuɗin kitso da kunshin yau gare ta ballantana ta kai shi Asibiti, hakan ya sa duk ta damu ta kasa fitowa daga ɗaki ta tasa shi gaba kamar ta samu tv lokaci zuwa lokaci tana share hawaye... Bayan mijin Ta Sakkwato ya dawo ya kawo mata maganin ta jika ta ba shi da kyar yana kaucewa rabi ya sha rabi ya zube, sai lokacin taji sanyi da ta ba shi maganin ta fito wajan matan gidan tare da fito da silitif ɗin ƙunshi ana hira tana yankawa dan kar azo nema babu. Can cikin dare suna bacci ta ji wani abu mai nauyi ya danne ta, da kyar ta buɗe idanu ta sauke su a kan shi ya kwanta a ruwan cikin ta, gyara masa kwanciya ta yi duk da nauyin da take ji ta koma bacci, kamar wasa ta ji yana taɓa ko'ina na jikinta ta zabura ta yunƙura za ta ture shi amma ta kasa. Duk yadda take tunanin Zaiyan yau ya shallake tunanin ta, abin da ba ta taɓa tsammani ko zato daga gare shi ba yau shi take ji da gani, a iya rayuwarta in aka ce mata Zaiyan zai aika mata haka za ta musa, jin abin yana neman wuce gona da iri ta daddage ta ƙarfin tsiya ta hankaɗa shi can gefe ta fashe da kuka mai sauti sai kuma ta yi saurin toshe bakinta tana tashi zaune, Kallon shi take duk da ɗakin da duhu amma ɗan hasken fitilar da ta kunna ya sa ta hango shi yana ta juyi. Ta jima tana kallon shi tun yana juyi har ya daina bacci ya dauke shi, gabaɗaya wani mugun tsoron shi ta ji ya mata dirar mikiya, wai yau Zaiyan ne ke ƙoƙarin raba ta da tufafin jikinta abin da ko a mafarki ba ta yi tsammani ba, dan ita a tunaninta ba zai taɓa neman ya yi wani abu na auratayya da ita ba, tashi ta yi da sauri ta shige toilet tana goge kawaye, ganin jinin al'ada ne ya zo mata duk da haka ta ɗaura alwala ta zo ta zauna ta dinga lazumi tana kallon shi, karshe bacci ya kwashe ta a kan abin Sallar cike da mafarkai kala-kala.... _Maman Nusaiba ce_ [6/20, 8:43 PM] Ummu Amjad: *A HAKA NAKE SON SHI* Shafi na (47) Kiran Sallah Asuba ne ya tayar da ita daga nannauyan baccin wahalar da ya dauke ta, a hankali soma ta buɗe idaunwanta da suka yi mata nauyi saboda kukan da ta ci ga baccin da ya rufe idanu, da kyar ta iya tashi zaune tana yarfa hannu ba shiri ta koma ta kwanta, wani azababben zafi mai fitar mutum daga haiyaci ya ziyarce ta, a gabaice ta sake yunƙurawa tana cije lip ɗinta na ƙasa cikin wani kalar yanayi marar musaltu, da kyar ta zauna tana runtse idanu mararta ta mugun ɗaure mata ga zafi sosai da take ji, kallon ƙafafuwanta ta yi ta ga har sun fara kumbura kamar na mace mai tsohon ciki ta ja numfashi da kyar tana juya kai, jin tana neman sheƙawa ba shiri ta sunkuya ta rarrafa ta isa bakin katifar tana haki kamar wacce ta yi gasar tsare. Juyowa ta yi ta ga ta ɓata daddumar, waro idanu ta yi ta rasa ya ma za ta yi kawai ta fashe da kuka, sautin kukan ta ne ya tayar da shi daga bacci ya buɗe idanuwansa ya sauke su a kan ya, da sauri ya tashi zaune ya matso kusa da ita ya ce "Me ya faru." Sororo ta yi ta saki baki da hanci tana kallon shi jin yadda ya mata magana, amma da yake tana cikin yanayin da ba za ta iya wani dogon tunani ba sai ta nisa ta ce "Don Allah ka kaini banɗaki please." Tashi ya yi ya ɗauke ta cak ya nufi banɗaki da ita sai kuka yake tana faɗin bayanta zai karya, aje ta ya yi har zai fita ya ga kamar wani abu a hannunsa ya yi sauran kai duban shi gare ta, fahimtar hakan ya sa ta kuma ɓarkewa da sabon kuka tana jin kamar ƙasa ta tsaye ta shige, ruwa ya sa ya wanke tas ita kuma duk ta yi zuru-zuru kamar ɓarawon da dubansa ta cika, yana gamawa ya fito ya bar ta a ciki ya rufe mata kofar. Daddumar da ta ɓata ya ɗauke ya aje a gefe har zai juyo ya ga wata babbar kula irin ta gidan bikin nan, isa ya yi gaban kular ya buɗe ya ga ruwan zafi ne a ciki sai tururi yake , dube-dube ya soma yi can ya gano roba irin ta wanka sabuwa dal ya ɗauko ya zuba ruwan zafin rabin roba ya nufi banɗaki. A inda ya barta a nan ya dawo ya same ta sai ganin shi ta yi da ruwa yana tashin tururi ya aje mata bai ce da ita komai ba ya fita, ganin haka ya sa ta tashi a daddafe ta cire kayan jikinta da suka ɓaci ta shiga ruwan, da kyar ta daure ta zauna taba yarfa hannu har taji ruwan ya mata daidai ta jingina kanta da jikin bangon banɗakin tare da lumshe idanu, sai da ta ji ana kabbara Sallah ta tashi ta ƙarasa yin wanka sai lokacin ta tuna babu abin da za ta sa ta fita, ta tsaya tana karanta wasiƙar jaki. Ji ta yi an buɗe ƙofar an shigo ta yi saurin kallon ƙofar ta ga shi ne. Saurin kare jikinta ta yi tana rawar sanyi kamar mai jin zazzabi, shi kuma bai kalle ta ba ya iso inda take ya sa towel ɗin da ya shigo da shi ya naɗo ta ya ɗauke cak suka yo waje, idanu ta rufe ƙirjinta na mugun bugawa da sauri-sauri har ya aje ta akan katifar, komawa ya yi ciki ita kuma ganin haka ta yi saurin dauko duk abin da za ta yi amfani ta shiga sawa da sauri tana kallon ƙofar , har ta gama bai fito ba ta sulale ta kwanta tare lulluɓe jikinta da bargo ta yi mataƙau tana baza na Zomo kamar ɓarawon da ke shirin yin sata. Fitowa ya yi ya janyo dayar daddumar ya tada kabbara, a hankali ta ɗan buɗe ta ƙyalla idanu tana kallon shi cike da tarin tambayoyi a cikin zuciyarta, gabaɗaya lamarin Zaiyan yana son girman ƴar karamar masarrafarta, shin Zaiyan ɗin ne dai take gani a gaban ta yana Sallah kamar kowanni mai hankali da nutsuwa ko kuwa dai aljannun jikinsa ne suka sa shi yin hakan? Lumshe idanu ta yi ta sake buɗe su ta rasa wa za ta tara ta amayar wa da abin da yake cikinta ko za ta samu solution a zuciyarta, abin da ya mata jiya da dare shi yafi tsaya mata a rai ta ƙara jin tsoron shi ya kuma mamaye kowacce kafa ta jikinta, indai har kintacanta da daidai yake kintato mata samun lafiya ta bayyana a tattare da rijalun nata, yana yi mata wasu abubuwan irin na masu hankali ga shi yau har ruwan zafi ya kai mata banɗaki ya kuma dauko ta da ta gama, lalle in ba ƙarya idanuwanta suke gano mata ba Sallah cikakkiya take ganin Zaiyan yana gabatarwa kamar kowa.. Nisawa ta yi tunanukan da take gabaɗaya sun haddasa mata wani ciwon kai mai tsanani, tana jin shi ya gama ya zame a wajan ya kwanta ta yaye bargon ta tsura wa bayan sa idanu, yadda ya kwanta a takure sai ta ji ba daɗi ganin ita tana kan katifa shi kuma a ƙasa, a hankali ta tashi ta buɗe ledar da ta yo musu cefane ta ɗauko madarar ruwa ta buɗe hannu na rawa saboda yunwar da take ji ta kafa kai, sai da ta kwankwaɗe tas sannan ta isa wajan tukunyar abincin da ta dafa da dare ta sa cokali za ta ci a haka, tuna ba kyau yin hakan kar ta ɓata abincin sai ta miƙa hannu ta ɗauko wani plate ɗan madaidaici ta zuba taliyar da ta sandare ta yi sanyi ƙarara kamar ta kwana a freezer. Haka ta dinga turawa tana ci tana hawaye har taji ta ɗan rage yunwar ta janye ta tashi daga wajan, banɗaki ta shiga ta wanko bakinta ta ta dawo ta tsaya a kan shi tana ƙare wa kyakyawar surar jikinsa kallo. Yadda yake fitar da numfashi abin sai ya birge ta har ba ta san san da ta saki murmushi ba, bargon ta ɗauko ta rufa masa ita kuma ta yaye zanin gadon ta rufe jiki da shi da haka bacci ya dauke ta... Sai wuraren karfe 11:00am ta farka duk jikinta a mace, banɗaki ta shiga ta gyara jikinta ta fito jin matan gidan suna ta hira, kallon inda ya kwanta ta yi ta ga ba kowa, da sauri ta kalli katifar sai ta gan shi a can karshen bango yana ta bacci, doguwar ajiyar zuciya ta sauke ta saka hijabi ta fito waje. Maman Amal ta riƙe baki ta ce "Ke Jiddo wai lafiya kike kuwa? Kin san karfe nawa yanzu?" Janyo kujare ta yi ta zauna a gefen Aisha maƙociyarsu tana murmushi ta ce "Wallahi bacci yau na sha sosai, kun tashi lafiya? Ina Mama take ne ban gan ta a nan ba?" Maman Samira ta ce "Ai Ta Sakkwato ɗazu ta gama wanke mu tas ta fita daga gidan, yau ko inda za ta je ba ta sanar da mu ba ta fita tana sababi." Yar dariya ta yi ta ce "Mamana ba dai faɗa ba." Hira suka ci gaba da yi ana ta shewa sai ga wata mata ta zo a mata lalle, nan Abir ta shiga ta ɗauko kayan ƙunshi ta shiga yi mata. Yau gabaɗaya sun hallara ana ta tattaunawa kamar dai kullum su uku, Alhaji ya gyara zama ya ce "Yanzu dai abin da ya fi mu koma gidan boka, kun ga yanzu ana gaf da fara zaɓe kar mu bari Damisa ya ɓata mana shiri, sannan na ga kwana biyu Abdul ba ya kawo mana labarin komai game da wajan aikinsu shi ma mu sa a ƙara kama mana shi a hannu kar ya kuɓuce. " Alhaji Mustapha ya yi kwafa dan shi gani yake ma ya fi kowa tsanar Damisa, a kufule ya juyo cikin faɗa-faɗa ya ce "Ni fa da za ku bi shawarata kawai daga can ma mu sa a kashe shi cikin ruwan sanyi, yanzu kuna ga mun bari an yi auren wannan sheɗaniyar yarinyar dan mu cika burinmu amma mun ƙasa cikawa, mun sa a bincika mana ita a kowacce Jaha amma shuru ba wanda ya ce mana ya gan ta, sanin kanku ne duk wani sirri namu Ibrahim ya tattara ya miƙa mata, idan har ta ga wannan sirrin me kuke tunani zai faru? Duk da shi wanda zai mata ja gabar mun shanye shi sai abin da muka ce zai yi, ya kamata mu tashi daga baccin asarar da muke mu nemo ta duk inda ta shiga a faɗin Nigeria. Ba na so wani abu ya kawo mana cikas a harkar siyasar nan tamu. " Dukkan su sai gyaɗa kai suke kamar wasu ƙadangaru suna sauraron shi har ya gama jawabi, Jarmai ya buɗe baki zai yi magana ya ji ƙaran wayarsa da ke gefen shi, hannu ya sa ya ɗauka sai ya ga ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan jaridar da suka dauka ne ya kira shi. Karawa ya yi a kunne kafin ma ya yi magana na cikin wayar murya na rawa ya ce "Hello ranka ya daɗe idan kuna kusa da tv ku kunna tashar Albarka tv akwai abin da yake faruwa." Hannu na rawa Jarmai ya sauke wayar ya janyo remote ya kunna tv da ke palon, kai tsaye ya kawo tashar da aka ce ya kawo, shuru suka yi dan lokacin a tashar sun tafi hutun taƙaitaccan lokaci, bayan sun dawo ne aka ɗaura daga inda aka tsaya inda mai gabatar da shirin ya soma faɗin, _"A yau ne aka gano wasu lefuka masu muni wanda su Alhaji Mustapha dan takarar gwamna shi da abokan shi suke aikatawa, suna safarar mata daga nan Nigeria zuwa ƙasashen Turai ana mayar da su karuwai, wanda wani matashi mai suna Damisa ne ya tabbatar mana da hakan ya kuma sanar da mu gidansu na shaƙatawa a can suke kai yaran su aje kafin a fita da su ƙasar waje."_ Saurin kashe TV Jarmai ya yi yana zaro idanu waje, dukkan su ba wanda bai girgiza ba da jin wannan labari, nan take Alhaji Mustapha ya kira wata number ana ɗauka ya soma faɗin "Duk inda wannan ɗan jaridar yake ku nemo min shi ku masa barazana ta yadda da kansa zai ƙaryata wannan labarin da ya yaɗa, sannan ku tabbatar kun gano min a wani hotel Damisa yake a faɗin garin nan." Yana gama faɗin haka ya kashe wayar sai huci yake, sai da ya jima a haka sannan ya ce "Yau ba sai gobe ba za mu tafi gidan boka kuma yanzu nake so mu tafi ba sai kowa ya je gida ya shiryo ba. Idan har muka zauna a haka Damisa zai mamaye mu gabaɗaya." Ba wanda ya yi muso da maganar tasa suka sa aka samar musu da tickets na zuwa Legos, ba su daɗe ba aka ce masu komai is ready suka yo Airport, ba jimawa jirgin yan kasuwa ya sauka suka hau sai Legos.. Laraba ta shirya tsaf cikin shirin ta na shigar abaya ƴar Dubai ta yi rolin da mayafin a kanta, baƙin glas ta saka ta fito palon tana riƙe handbag ɗinta a hannu cike da aji ta tsaya, kallon ta Damisa ya yi ya yi ƴar dariya ya ce "Wannan kyau haka sai ka ce matar Gwamna, wannan sai ki sa a dinga kallon ki duk inda kika nufa." Dariya ta yi tana cire glas ɗin ta ce "Haba dai Oga ni da zan fita aikin Allah ai sai na nuna wa waɗanda zan je wajan su ni ba kanwar lasa ba ce, dan haka kai dai ka haɗo ni da bodyguard ɗinka mu wuce Kar mu shiga time ɗin aiki na gaba." Jinjina ya mata yana murmushi ya ciro bandir goma cif ɗaurin yan rafa ya miƙa mata, baki ta saki tana kallon shi cike da mamaki ta ce "Oga ya za ka miƙo min kuɗi har miliyan ɗaya na kai wa ƙaton banza ya ci? Ni fa da za ka bi shawarata da kawai mun yi yadda na tsara, idan har ya ga ba haza zai yi mana abin da muke so." Murmushi ya sakar mata ya koma ya zauna yana faɗin "Nasan fa me nake yi Jk, ai da wannan aka ruɗe shi har ya yi abin da aka sa shi, to muma da shi za mu ruɗe shi ya mana abin da muke so, kin san fa ta hanyar da aka hau ta nan ake sauka! So wannan ba komai ba ne matuƙar buƙata za ta biya, idan har yaƙi bamu haɗin kai ne za mu fahimtar da shi a yaren da zai gane. " Dariya Laraba ta yi tana gyara zaman Jakarta ta ce "Wani lokacin fa kai mugu ne Oga." Shi ma murmushi ya yi ya ce "Ke dai je ki kawai." Sallama ta masa ta kwashe kuɗin ta sa a jaka ta fita zuwa harabar gidan, direba ya buɗe mata mota ta shiga suka bar gidan.. Umma na zaune gaban malam tana koro masa bayanin sabon aikin da zai mata, sai da ta gama masa bayani tas ya ɗago ya kalle ta yana murmushi ya ce "An yi an gama dan yanzu haka na gama aikin, amma ba fa zai ɗauki lokacin bai yawa ba asirin zai karye, saboda yana samun kariya daga wata aljana mai mugun haɗari, abin da ya sa ma har na samu na cika aikin a yanzu ba ta a tare da shi ta yi tafiya, kuma tana gaf da dawowa." Wani kalar shu'umin murmushi Umma ta saki tana jin daɗi ya mamaye ta, sake kaɗa baki ta yi ta ce "Ka tura masa masu ƙarfin gaske wanda zai mata faɗe ta yadda za ta kamu da yoyon fitsari ta ruɓe ta lalace, dan nasan yanzu dai ba ta kuɗin da za ta biya ayi mata magani in ya mata faɗen, sannan asa mijin da ya mata haka ya shiga duniya kar su sake haɗuwa ita kanta ina so ta dauwama a inda take rayuwa yanzu. Sannan ina so 'yata ta mallake mijinta sai abin da ta ce masa. " Ƴar dariya ya yi yana kallon Umma ya girgiza kai ya ce" wato Hajiya ke a layin marasa imanin ma ke number one ce, ki yi komai ba komai Hajiya aljanna ta mai rabo ce. " Dariya ta yi tana jin kanta ya ƙara girma ita ga ta ba mai ja da ita ya kwana lafiya, tashi ta yi ta ce masa ayi a gama mata komai kafin ita wannan aljana ta dawo, dan so take a farraƙa su ko a hanya kar su haɗu da juna. An ga Malam ya ce mata sannan ta tafi.. Tana fita kamar da minti goma ya ji ana neman izinin shigowa, izini ya bada ta shigo tana shan ƙamshi ta zauna tare da gaishe shi, ganin santaleliyar budurwa a gaban shi sai ya washe baki yana faɗin "Sannu da zuwa Hajiya." Hararar shi ta yi ta cikin glas ɗin ta gyara zama sannan ta amsa, yana washe baki ya ce "Hajiya me ke tafe da ke?" Yatsina fuska ta yi ta ciro kuɗin da aka ba ta ta dire masa shi a gaban shi, Malam ganin tsallar madarar kuɗi maƙudai a gaban shi sai ya ruɗe yana shafa gemu ya ce "Ma sha Allah, to wani kalar aiki kike so ayi miki Hajjaju?" Ji ta yi kamar ta kai masa naushi a baki jin ya ce ma sha Allah kamar wani mutumin arziƙi, Nisawa ta yi ta ce "Waccan matar da ta tafi nake son ka warware duk wani aiki da kasan ka yi mata, ni kuma zan kawo maka talumkar wannan kuɗin da kake gani a gaban ka." Kwalalo idanu waje Malam ya yi yana kallon ta sai kuma ya kalli kuɗi, ga kuɗi amma kuma in ya tun irin amanar da ke tsakanin shi da Umma sai ya ji ba zai iya warware mata aiki ba, shi kansa bai san iya adadin aikin da ya mata ba wanda ta sa ya yi aikin a kan su wasu sun mutu wasu kuma bai san ma a wata duniya suke ba, ya girgiza kai ya ce "Hajiya gaskiya ni da matar nan akwai amana, shekara da shekaru ina mata aiki babu ta yadda za ayi rana tsaka na zo na warware mata aiki ba, wani aikin ma na manta yadda na yi shi bare na warware." Ran Laraba ne yayi mugun ɓaci ta zare glas ɗin da manne a fuskarta tana masa kallon za ka yi bayani, gyara zama ta yi ta ce "Malam ko na ce Boka ka yi abin da na faɗa ko kuma ka ga abin da zan yi maka." Ta faɗa tana zaro bindiga daga cikin Jakarta ta saita satin goshinsa tana hura hanci ta ce "Za ka warware ko kuma ba za ka warware ba.?" Jikin Malam ne ya dauki rawa karr karr karr ganin bindiga a zahiri, baki na rawa ya ce "Hajiya sauke bindigar mu yi magana kin ji." Saukewa ta yi ya kalle ta a tsorace ya ce "Wanne da wanne kike so na warware miki?" Ƙara daure fuska ta yi ta ce " Faɗa min irin aikin da ka yi mata ko na fasa kanka yanzu." A ruɗe ya soma faɗin "Gaskiya in na ce zan faɗa miki adadin aikin da na yi wa Hajiya to na yi karya, saboda matar nan tun kafin ta yi aure take zuwa wajena na yi mata aiki, hasali ma nine na fara sanin ta a 'ya mace kafin ma ta kai ga yin aure, aikin da na mata wanda daga shi nake mata manyan aiki shi ne ta sa na sawa matar Yayan mijin da za ta aura sihirin kar ta ga jininta a duniya, duk cikin da za ta samu sai ya zube.." Ya ɗago ya kalli Laraba da ta nutsu tana jin bayanin shi, jin ya tsaya ta ce " Ci gaba mana ina jin ka. " "Wata rana ta sake zuwa ta ce min na yi mata aikin da zai yi ajalin matar wanda take so dan ita ta tsani kishiya musamman ma wadda za ta tarar, haka na mata aiki ta tafi tare da aje min kuɗi, bayan wasu kwanankin ta dawo ta ce min ai buƙata ta biya matar ta rasu har ma an yi sati biyu da mutuwar, nan ta ce na sa a takurawa shi mijin matar ace sai ya yi aure kuma ita zai aura tun da ɗan'uwanta ne shi, haka na mata aiki babu jimawa aka yi auren su ita da shi, tun daga lokacin da kalar aikin da da ta zo da shi, ta zo na yi wa mijinta aiki akan duk wani nema nasa ya zamana yana tafin hannunta. Haka take zuwa na buƙatata da ita nake biya mata tata buƙatar har ta haifi ƴarta ta farko, a lokacin ta zo min da cewa matar da aka yi wa aiki kar ta haihu tana nan yau ta haihu na yi wani abu a kai, na buga ƙasa amma na kasa yi mata komai a lokacin na ce ta bari har sai yarinyar ya ɗan girma tukun sai ta zo ayi komai. To bayan wasu shekaru ta dawo na mata aiki aka daurawa yarinyar cutar asmah, tare da baƙaƙen aljannu wanda za suke tsotse mata jini tana ramewa kar ta girma ballantana kyanta ya ƙara bayyana ta riga yaran su a aure, babu muso na mata aiki ta aje min kuɗi masu yawa ta tafi, wata rana ta dawo ta ce na yi mata aiki akan Yayan mijinta ya yi wa wannan Mamar yarinyar kishiya ya auri ƙawarta, na buga amma na kasa saboda kullum cikin tsarin Ubangiji mijin yake, a lokacin ita kan ta matar ta dukufa da neman kariya shi ya sa na ƙasa musu komai dole ta haƙura . To can baya ta zo ta ce na sa yarinyar da ɗan kishiyarta su dinga lalata har su samu ciki ba wanda ya ankara har sai cikin ya fito, na ce to ta tafi amma na kasa yin wannan aikin har wani abokina na sa ya tayani amma shi ma ya kasa, ganin haka ya sa ta ce a mayar da yaron ya zama kamar mace ya kasa amfanuwa ta fannin auratayya, nan ma bai yiyuba. Watanni kaɗan da suka wuce ta zo ta ce min uwar yarinyar ta rasu amma kafin ta rasu an soma maganar auren ƴar. Nan y asanar da ita yadda suka yi har aka fasa auren Abir da Suhal ya dawo kan Iman.. " Laraba da hawaye ke bin kuncinta ta fusata ainun ta tashi ta zabga masa mari, nuna shi da yatsa ta yi ta ce " Mugu azzalumi ci gaba ina jin ka wanda ya dauke kayansa daga gaban rahamar Ubangiji. " Sosai ya ji marin ya shige shi, ya dafe kunci ya ci gaba da cewa "Aikin da na mata na kusa-kusar nan shi ne na yi wa duka Familyn nasu aiki suka tsani yarinyar, babu wanda yake damuwa da ita har shi wannan Yayan nata, nan ma dai bayan lokaci ta zo ta ce a yi mata aiki yarinyar ta tubure ta ce wani mahaukaci da take jinya shi take so a aura mata, haka kuwa aka yi nan da nan sai ga aiki ya kama yarinyar ta tubure a satin aka ɗaura musu aure, karshe ma ta kuma cewa a kaɗa su su bi duniya daga ita har mijin su wahala har su mutu. Na yi aiki cikin dare inda aikin nawa ya zo aka gaɓa ranar Yayanta ya je ya mata duka, na raba mata hankali ta rasa sukoni ta tattara kayansu ta bar gidan, na sa duk familyn nasu suka manta da shafin rayuwarta babu wanda yake son ayi masa maganar ta indai dan family su ne, yanzu kuma ta zo ne ta ce min tun da na gano inda suke nasa mijin ya mata faɗe na fitar haiyaci, wanda za ta kamu da cutar yoyon fitsari ta ruɓe. Yanzu haka maganar da nake miki tuni na gama yin aikin akan mijin kuma take ya isa gare shi." Ta faɗa yana zare idanu.. Laraba ta yi saƙare tana jin kalar rashin imani irin na wannan malam bokan, dauke kuɗin ta yi ta ce "Maza ka warware aikin da ka yi wa mijin nata yanzu." Rausayar da kai ya yi ya ce "Hajiya ai ko da zai warwaru to fa sai nan da kwana uku." "To naji warware in kwana ukun ya yi sai sihirin ya bar jikinsa, sannan ka warware na Family da mijinta, cutar da ka saka wa baiwar Allah ka warware mata kafin na fasa kanka da bindiga, su kuma sauran bayin Allah da ka cuta sun mutu za ka je gaban Allah ku haɗu a can." Tana zaune sai da warware na Family tas da Daddy na Abir duk ta sa ya warware su duka, ta kuma mishi barazanar cewa duk ina ya gudu dan ya tsere musu suna da mutane a kowacce Jaha, duk inda ya shiga a faɗin Nigeria za su kamo shi su kashe, kuma ya kuskura ya sanar da Umma ya warware aikin da yake mata zai ga abin da zai same shi, to ya dinga faɗi yana Allah-Allah ta bar gidan dan wani zawo yaji ya tafo masa , tana fita ya runtuma a guje banɗaki sai karan zawo kake ji... Tana fitowa ta goge hawayen da suka zubo mata ta shiga motar suka bar wajan, yau ta ji abin da ya girgiza mata masarrafa sai share hawaye take tsananin tausayin Abir na ratsa mata zuciya... _Maman Nusaiba ce_ [11/30, 2:03 Safiya] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): *A HAKA NAKE SON SHI* Shafi na (48) Yau tun bayan Sallar Asubahi Gandma ta fito palo tana shige da fice ko za ta ga kiftawar Abir amma shuru har ƙarfe tara ta buga ba ta fito ba, mamaki sosai ya kama ta ta zauna kan kujera tana kallon ƙofar ɗakin, ganin dai lokaci na tafiya ta nufi ƙofar ɗakin ta soma kwankwasawa tana faɗin "Ke kasa uwar bacci ki tashi ki fito rana ta take kina shema bacci, maza ki fito so nake ki rakani Ruga yau." Shuru ta ji ba a amsa mata ba sai ta murɗa ƙofar taji a kulle ɗakin, kwafa ta yi tana cewa "Ƴar banza mai zubin taliya ƴar murji, mutum ya neme ki da abin arziƙi ma sai kin nuna masa isa da izza kamar jinin sarauta, yo ko ke ce Suhal ai sai haka busasshiyar banza jiki duk ƙashi, daga yau ma kin daina rakani in zan je Rugar sai na ga ta inda za ki ga kayan tarihi iri da namu na Fulani. " Tas ta gama sababin ta amma shuru ko motsi ba ta ji ba na alamar za a buɗe mata kofar, ta dawo ta zauna tana kaɗa kai sai ga Abba ya iso palon shi da Daddy Fatima na riƙe da hannun Abba, zama duk suka yi tare da gaishe ta tana kaɗa ƙafa ta amsa sai hura hanci take, Abba da ya gane hakan sai ya rausayar da kai ya ce "Inna ke da wa da farar safiyar nan?" Tsaki ta ja ta ce "Ni da Hauwa'u mana, ina ta kiran ta ta yi mursisi taƙi fitowa daga ɗaki." Kafin Abba ya ba ta amsa Fatima ta yi caraf tana dariya ta ce "Kai Grandma da alama rikicin tsufa ya soma kawo miki ziyara, Baby da ta jima da yin aure me kuma zai kawo ta ta zauna a gida ga gidan mijinta?" Duk kallon ta suka yi baki sake, Inna ta zaburo ta watso mata daƙuwa ta ce "Ingo nan dan cucun uwaki Faɗima, Hauwa'un ce ta yi aure ba tare da mun sani ba? To uban wa ma ta aura in har da gaske kike? Sannan wa ya ɗaura mata aure? Nasan dai su Sulaimanu ba za su mata aure ba su shawarceni ba." Abba ya yi shuru yana son tuno yaushe suka mata aure amma ya kasa, hankalinsa ya tashi jin yadda Fatima ke rantsuwa da zatin Allah Abba da Daddy da Abdul da Salim da Daddyn Aruf ne suka ɗaura wa Abir aure, kuma a ranar suka ce ta bar gidan ta tafi gidanta. Kuka Grandma ta sa tana tafa hannu tana kallon su, su kansu sun rasa me ya shiga kan su har suka mata wannan cin zarafin a matsayinta na ɗiyar yayansu kuma amana a gare su, Abba ya miƙe tsaye yana zarya dan duk cikinsu ya fi su shiga tashin hankali idan ya tuna yadda ɗan'uwansa ke jaddada masa ko ya riga shi mutuwa a riƙe masa Abir amana. Number ta ya lalibo ta kira ya danna mata kira, sai aka ce masa an yanke layin, zama ya yi yana kallon Daddy da shi ma ɗin shi yake kallo ya nisa ya ce "Ko kana da ɗayar number ta?" Girgiza kai Daddy ya yi dan ya ma kasa yin magana, Abba ya ce Fatima ta ba shi dayar number Abir ta ce ita ai ba ta ma da numbobin ta ko ɗaya, tashi duk suka yi suka ce wa Grandma za su nemo duk inda Abir take. Kuka sosai Grandma ta dinga yi tana faɗin "Kai jama'a! Kenan dai da gaske sun aurar da yarinyar nan? To ni kuma ina wani waje har aka yi hakan ban sani ba?" Tunawa da Laraba ya sa ta tashi ta nufi ɗakin Laraba tana kwaɗa mata kira, murɗa ƙofar ta yi ta ga babu kowa a ɗaki sai gado da drower, haka ta juyo tana sallami ta dawo ta zauna duk ta rikice, can dai ta tuna Laraba ta tafi wajan ahalinta sannan ta ji sauki ta koma kan labarin jikartata.. Ko da Abba ya fita sai ya koma part ɗinsu ya samu Ammi zaune tana chatting, ganin sun dawo ne ya sa ta ɗago kai ta kalle su cike da mamaki ta ce "Abbansu lafiya kuka dawo?" Zama suka yi Fatima ta turo baki ta kalli Ammi ta ce "Ammi wai Grandma ce take tambayar su Abba ina Baby take? Shi ne fa na ce an mata aure duk suka nuna ba su san maganar ba, ni kuma tsaf nasan an yi mata aure kema kuma kin san da hakan, amma dai ga ki ga Abba ki faɗa masa ko zai yarda da gaske ne sun aurar da ita wa mahaukaci. " A zabure Abba ya ɗago yana zaro idanu ya kalli Fatima cike da tsananin tashin hankali jin kalamanta na karshe, baki na rawa ya ce "Ba.. Ban gane me kike nufi ba Fatima? Mun aura mata mahaukaci kuma? Ba na son shirme fa." Turo baki ta yi tana kallon Ammi da ta kalli Abba da mamaki, aje wayar ta yi ta gyara zama ta ce "Lalle Abbansu! Kai da kanka ka ba da aurenta wa mahaukaci wanda take jinyar shi ita da Abdul, amma tun farko ma kun nuna ba ku so.. Nan ta shiga faɗa masa yadda aka sha artabo da Abir akan aure ta kafe ta ce sai shi take so ta aura.." Salati Abba yake bai san ba lokacin da ya mike tsaye ya fice bai ce da su komai ba, duk ya kiɗime jikinsa ya dauki rawa da kyar ya iya buɗe ƙofar palon ya fita, Ammi ta riƙe baki ta ce " Ke ni ma fa har yau mamaki nake na auren Abir, kuma tabbas akwai abin da aka yi wa 'yan gidan nan har suka yi wannan aika-aikar ba tare da sun lura ba.." Fatima ta matso kusa da Ammi ta ce "Haka ne Ammi, ni ma haka nake ji har yau, ko ba komai ai Baby jininmu ce ya kamata asan wa za ta aura saboda rayuwarta abin tausayi ce, ranar fa naje gidan Yaya Abdul muna hira da Hafsat take faɗa min irin rashin darajar da Abdul yake yi wa Baby, ni kaina na sha mamaki ganin yadda suke amma yake mata cin mutumci, lalle fa Ammi akwai abin da ake ƙullawa a gidan nan wanda ya haddasa faruwar duk lamarin nan. " Ta ja numfashi ta kalli Ammi sai kuma ta ɗaura da cewa, "Anya kuwa Ammi ba ke ba ce kika ƙulla wani abu dan a manta da Baby? Saboda kin ce mana kin tsane ta dan ta fimu kyau da farin jinin jama'a ga Abie ya fi su Abba dukiya, mu ma kike saka mu muna tsangwamar ta in ta zo inda muke." A razana Ammi ta kalli Fatima cikin tashin hankali, tashi ta yi daga inda take ta matso kusa da Fatima ta ruƙo hannunta murya na rawa ta ce"Ha.. Haba Fatima, yanzu da hankalina zan sa ɗiyar ɗan'uwana a wannan halin? Ko kin manta shi Yaya Ibrahim ɗin iyayenmu uwa ɗaya uba ɗaya suke? Ai duk tsanar da na yi wa Abir ba zan taɓa yi mata irin zalincin nan ba, ni fa dama ƙiyayyar tawa ganin ana fifita ta ne akan ku komai Abbanku ya samo sai ya ce mai Mamana, in daga Office ya zo sai ya sa a kawo masa ita nan ku kuma ya share ku hakan ne ya sa naji na tsane ta, amma in ba haka ba Wallahi ba zan iya yin wani abu da zai cutar da ita har haka ba, wata irin cuta ta kai a aura ma mahaukaci wanda ba ka san ranar warkewar shi ba?" Shuru Fatima ta yi tana wani ya tsine fuska dan ita sam ba ta yarda da maganar Ammi ba, karshe ma tashi ta yi ta nufi part ɗin Umma tana yan wake-waken ta. Ko da ta isa tana daga tsaye ta gaishe da Umma tana done hanci jin wani ƙauri-ƙauri na tashi, Umma ta harare ta tana dauke kaskon turaren wutar da ta kunna tana baɗe gidan da shi ta kai kitcken, dawowa ta yi ta zauna tana kaɗa ƙafa ya ce "Ke kuma lafiya kika shigo min gida kika tsaya min a ka kamar na ci miki bashi?" Kallon hadarin kaji Fatima ta yi wa Umma sai kuma ta kama ƙugu cikin tsiwa da rashin kunya ta ce "Wato na ƙara tabbatar da duk wani abu da kuke ƙullawa a gidan nan ke da Ammi, ku ne kuka shiga ku ka fita har kuka sa su Abba suka aura wa Baby mahaukaci ba su sani ba ko? To billahil lazi sai na sanar da Grandma cewa ku ne mugayen da ku ka yi makirci kuka haɗa komai da ya faru ke da Ammi. " Ta faɗa tana murguɗa baki cike da rashin kunya.. Ras! Ras! Ras! Haka gaban Umma ke bugawa ba ƙaƙƙautawa ta ruɗe sosai da jin maganar Fatima, sai kuma ta masge ta kirkiro murmushi ta yi wa fuskarta kwalliya da shi ta ce "Haba Autar Ammi, ke fa daɗina da ke rashin kunya wani lokacin, yanzu ban da ma sakarci irin naki taya za mu sa Abir ta auri mahaukaci bayan ba mu ba ne za mu ɗaura mata aure? Kuma ma ne ya kawo wannan maganar bayan kin san da kanta ta ce a haka take son shi? " Kallon uku saura kwata ta aika mata sai kuma ta zauna akan kujera ta zayyano mata duk abin da aka yi a part ɗin Grandma da kuma nasu, zufa ce ta dinga karyo wa Umma ta haɗiye yawu ba shiri, ganin ba za ta yi magana ba Fatima ta ja tsaki ta mike tana faɗin "Ai nasan dama kune mugaye azzalumai, Wallahi tsaf sai na sanar da su Abba kai har su Yaya Abdul sai na sanar da su kune ummal aba'isar lalacewar komai na gidan nan." Ta ƙarashe maganar tana banko kofar palon da ƙarfi ta wuce abin ta ta koma part ɗinsu.. Umma ta rikice sosai sai zarya take a palon, ganin in ta zauna wankin hula zai kaita dare ne ya sa ta figi mayafinta ta dauki jaka da makullin mota ta fita a harzarce... ABBA na fita ya nemi Abdul a waya, bayan sun gaisa yake tambayar Abdul ina ne gidan su Baba? Jim Abdul ya yi dan shi ma sai ɗazu yake tunanin in ya tashi daga aiki zai je, kwatance ya masa sannan suka yi sallama ya karya kan motarsa ya nufi Unguwar su Baba. Yana isa ya yi hon Maigadi ya zo ya buɗe masa ƙofa ya kutsa kan motarsa ciki, yana gama packing ya fito suka gaisa da Maigadi sannan yake tambayar sa ko masu gidan suna nan? E ya ce mata ya nemi ya yi masa izini da masu gidan, ya amsa da to ya nufi ciki. A zaune ya samu Baba da Inna tana yanka masa lemon zaƙi ya sanar da su wani hamshaƙi mai kuɗi ya zo ya ce yana so a masa izini, cike da mamaki Baba ya ce "To fa! Waye kuma haka? Amma dai je ka ce masa ya shigo." To ya faɗa ya fita ya sanar da Abba abin da suka ce, godiya ya masa ya nufi ciki yana addu'ar da ya shiga ya fara cin karo da fuskar Abir, Sallama ya yi suka amsa masa Baba ya mike tsaye yana murmushi ya ce "A a sannu da zuwa Alhaji yau kai ne a gidan namu?" Murmushi Abba ya yi yana wurga na mujiya ko zai ga ta inda za ta ɓullo, ruwa Inna ta kawo masa ya ɗan sha kaɗan dan kar Baba ya ce yaƙi cin abincin gidansu, bayan sun gaisa ne Abba ya yi shuru ya ma rasa ta ina zai fara yi wa Abba bayani, Baba da ya gane akwai abin da Abba ke son faɗa masa sai ya gyara zama tare da cewa "Alhaji lafiya dai ko?" Girgiza kai Abba ya yi da kyar ya iya cewa "Baba ina Mamana? Na ga ba ta fito ba ko ba ta ji muryata ba ne." Kallon rashin fahimta suka masa Inna ta ce "Wace ce kuma mai suna haka Alhaji?" Ɗago kai ya yi ya ce "Abir nake magana." Shuru duk suka yi ba su ce masa komai ba, Abba ya ƙara shiga tashin hankali ganin fuskokinsu sun bayyana damuwa, a sanyaye ya ce "Malam ba ku ce komai ba ina take?" Labarin guduwar ta cikin dare ya sanar masa, ya tashi ya dauko masa wasiƙar da ta rubuta musu da za ta bar gidan, Abba ya dafe kai yana faɗin "Inna lillahi wa inna laihin raji'un!" Daga haka bai iya cewa komai ba ya tashi ya tafi ko sallama bai musu, da kallo suka bi shi cike da mamakin wannan lamari na Abba Inna ta nisa ta ce "Gaskiya Malam akai abin da yake faruwa a gidan su Hauwa'u." Baba ya yi shuru yana tunanin abubuwan da suka wuce, shi kansa tun da aka yi auren nan lamarin ke damun shi har ila yau da Abban ya zo neman ta, duk tsayin watannin nan ba su zo sun neme ta ba sai yanzu da su kan su ba su san a wata duniya suke ba? Girgiza kai ya yi ya tashi tare da yi wa Inna sallama ya ce ko ma meye za su sani. Yau tun da wuri ta gama yi wa masu zuwa kitso wajan ta, wanka ta yi ganin ta samu tsarki ta gabatar da Sallar La'asar, fitowa ta yi ta zauna ana ta hira amma duk hankalinta baya kan hirar, tun safe take jin muguwar faduwar gaba haka ta daure dai ta yi wa wanda suka zo kitso cikin ƙarfin hali. Sai gaf da Magariba ta nufi ɗaki dan ta dauko kayan girki, turus ta tsaya ganin shi zaune dafe da kai ya jingina da bango, ƙarasowa ta yi ta iso gaban shi a ɗarare ta kai hannu ta taɓa kafaɗarsa, ɗagowa ya yi suka haɗe idanu ta yi saurin janye nata saboda da yadda ya mata kwarjini a idanun gani, a sanyaye ta ce "Zazzabin ne dai bai sake ka ba?". Lumshe idanu ya yi bai ce mata komai ba, itama ba ta damu da sai ya ba ta amsa ba ta kai hannu gefen wuyansa ta ji shi rau ta yi raurau da idanu suka cika da hawaye, zazzabin nan ya takura masa kullum da shi yake wuni har kusan karfe goma, sai can dare zai sake shi daga gari ya waye kuma ya dawo masa sabo dal, abin na damun ta matuƙa har ta gaji da ba shi magani dan har Asibiti suka je jiya aka rubuto masa magani ta sayo masa. Tashi ta yi ta dauki roba mai ɗan girma ta shige banɗaki, ba ta jima ba sai ga ta ta fito da ruwa a ciki ta aje a gefen shi, towel ta dauko ta tsugunna ta kamo hannunsa ya kalle ta, turo baki ta yi ta ce "Tashi ka koma kan katifa zan danna ma jikin ko zai sauka." Shi dai kawai da ido yake bin ta duk abin da ta faɗa, tashi ya yi suka iso kan katifar ta zaunar da shi ta soma ƙoƙarin cire masa rigar, ya saki jiki sai inda ta juya shi yana bin ta da kallo har ta cire rigar, towel ɗin ta jiƙa ta soma danna masa a jiki.. Sai da taji zafin jikin ya ragu ta aje ta nufi yin girki, shinkafa ta dauko ta haɗo da komai na buƙata ta fito waje ta soma ƙoƙarin ɗaura girki ganin rana ta tafi da faɗawa. Ana kiran Sallar Magaria ta zuba shinkafar ta rufe ta ci gaba da fifita wutar dan yau ma da gawayi take girki, tuni dama ta koma yin girki da gawayi ganin gas ya yi tsada sosai ga shi ita ba ta da wani ƙarfin da za ta ce dole lalle sai da shi za ta musu girki, sayan abinci da cefane ma kaɗai ya ishe ta ballantana sayan wani gas, dan dole ta haƙura ta sayo buhun gawayi take lamarin ta da shi. Abin da ya fi saka ta jin daɗi ma ganin ko ta tari hayaƙi babu wani abu da take ji, yanzu ko maganin ulcer ta daina sha saboda ba ta jin ciwon kamai ga shi ta soma murjewa ta yi fresh duk da damuwar da take ciki, hakan ya sa Maman Amal da ba ta gani ta kyalle yau rana da ta ga ta yi kwalliya ta fito ta dinga kallon ta tana murmushi. Abir da ta gaji da kallon ta ɓata fuska ta ce "Ni fa Wallahi Maman Amal sanin halina ne ba ki yi ba na tsani kallo ya yi yawa, in wani abu kike son faɗa ai sai ki faɗi ba wai kike ruƙo mun na mujiya ba, wannan ai sai ki sa na kasa sakin jikina." Dariya Maman Amal ta yi tana zama kusa da Abir ta ce "Mayar da wuƙaƙen Jiddo ni fa kawai mamaki ne nake?" Kallon mamakin me ta mata ita Kuma ta kuma sa dariya, ta muskuta kamar mai tsoron kar aji me za ta faɗa ta yi ƙasa da murya ta ce "Ke wai har yanzu ba ki gane me nake gani a jikinki ba?" Abir da ta ƙagu taji me ta gane ta girgiza kai, murmushi ta kuma yi ta ce "Ke alƙur'an ciki ne gareki, ke kamar wata ƴar fari ba ki gano kina da ciki ba? Ba ki ga canjin da kika samu ba?" Ta faɗa tana ƴar dariya.. Kwalalo idanu waje Abir ta yi sai kuma itama ta yi dariya ba ta ce komai ba, dan tasan ita dai babu wani ciki da take da shi, Maman Amal kuwa ta yi ta tsokanar ta har Maman biyu ta sa mata ita kuma tana ta murmushi ganin matan gidan sun kama maganar Maman Amal da gaske... Bayan ta gama Sallah ta zo ta ga abincin ya gama dafuwa ta sauke gefe, zama ta yi tana mamakin ganin Ta Sakkwato yau shuru ba ta dawo gidan ba, bayan an yi Sallar Isha'i ta janyo wayarta jin saƙonni na shigowa ta bude, customers ɗin ta daga Tiktok mutum uku suka yi mata DM suna son lalle, kowanne ya nuna mata kalar wanda za ta masa ta sanar da su ga kuɗin shi suka ce ba matsala sannan ta kwatanta musu Unguwarsu suka ce gobe bayan Asuhar za su zo, murmushi ta yi ta amsa da to sannan ta sauka. Har za ta sauka ta ci karo da labarin da ake yaɗawa na su Alhaji Mustapha, kwafa ta yi tana faɗin "Azzalumai in sha Allah dubunku ta kusa cika, Allah ya yi wa wannan bawan Allah albarka Damisa da ya binciko cutar da al'umma da kuke a karkashin ƙasa." Shuru ta yi can maganar 'yan ta'addan nan ta faɗo mata, jinjina kai ta yi tana fita daga Tiktok ɗin ta ce "Tabbas zan so na ga wannan mutumin mai suna Damisa da har ake danganta mijina da shi." Saƙon Iman ta gani tana sanar da ita in ta ga saƙon ta kira ta akwai bayani, murmushi ta yi ta danna mata kira, ringing ɗaya ta dauka ko gaisawa ba su yi ba Iman ta soma faɗin "Anty Baby kin san kuwa yau me ya faru a family?" Girgiza mata kai ta yi kamar tana ganin ta ita kuma ta ɗaura da cewa "Wai yau Abba ya kirani yana ce min wai na ba shi number ki wannan." Abir ta zaro idanu ta ce "To me zai yi da number ta kuma?" "Hmm ke dai bari, ai yau na sha mamaki Abba ya tirke ni a waya yana ce min shi fa bai san yaushe suka miki aure ba, ni kuma abin ya ƙular da ni amma na danne na ce masa ai kuwa dai sun miki aure tun da jimawa, nan ya dinga ta mamaki da alhini ya ce na ba shi number ki na ce masa ni ma kaina neman ki nake dan an ce kin bi dare kin gudu daga ke har mijin naki an rasa inda kuke, shi ne fa naji duk ya rude ya ce min sai an jima Wallahi ya ba ni tausayi ba ki ga yadda ya shiga tashin hankali ba saboda video call muka yi da shi. " Murmushi mai ciwo Abir ta yi tana tuna yadda Abba ke nuna masa so kamar zai mayar da ita cikinsa, goge hawayen da suka zubo mata ta yi ta ce "Kar ki ba su number ta dan bana son kowa ya san inda nake, zan ci gaba da rayuwa a nan ni da mijina cikin farin ciki da kwanciyar hankali dan da alama ma Zaiyan ya soma samun lafiya." Dirkowa Iman ta yi daga kan gado tana washe baki kamar gonar auduga Ikilima da ke gefen ta ta kwashe da dariya, ta gyara wayar ta ce "Kai amma kuwa in har Zaiyan ya soma samu lafiya ina tayaki murna, amma to Anty Baby idan ya samu lafiya ya nuna bai san ki ba fa?Kuma kin ga ba ki san shi waye ba daga ina ya fito? Duk fa ba ki sani ba kila ma yana da mata har da yara, amma dai duk da haka gara ya samu lafiyar zai fi da zaman ci da kai da kike. " Gaban ta ne ya faɗi rass! Ta dafe ƙirji ta ce" Kin ga in sha Allah ba shi da mata, kuma ina ji a jikina Zaiyan zai warke mu yi rayuwa kamar kowa. " Jin ta yi maganar a fusace sai Iman ta fashe da dariya tana faɗin "Jinjinar ban girma zuwa gareki Anty Baby wannan fusata haka? Kila fa na ce ba tabbatarwa na yi ba, yanzu dai ba wannan ba Ikilima ta ce za ku yi magana ga ta nan za ta kwace wayar." Sauke ajiyar zuciya ta yi ta a ba ta suka gaisa, Ikilima ke cewa ta yi kewar Abir matuƙa itama ta ce ta yi kewarta, sun jima suna hira sannan suka yi sallama.. Zubo musu abinci ta yi ta tashi Zaiyan ta dinga ba shi da kanta yana ci har ya koshi ta taimaka masa ya tashi ta raka shi banɗaki, ita kuma ta kasa cin abincin maganganun Iman sun tsaya mata a rai, janye kwanon abincin ta yi ta fito waje ta rafka tagumi hannu bibiyu... Cikin dare wajan karfe uku na dare Zaiyan ya kasa kwanciya ya dinga juyi yana murƙususu kamar mai nakuɗa, can dai ciwon ya lafa ya kwanta yana huci.. Abir za ta juya ta ji ta gam an riƙe ta, da sauri ta buɗe idanu ta ga yadda jikinsa yake rawa har haƙoransa suna karo da juna, a ruɗe ta soma ƙoƙarin tashi dan ta rufe shi amma sam ta kasa samun damar haka. Waro idanu ta yi ganin abin da yake shirin aikata mata, tana son yin ihu amma ba ta so aji ta ta dinga zaro idanu numfashinta na ƙoƙarin barin gangar jikinta, jin wani baƙon al'amari da ba ta taɓa jin shi ba tun da ta zo duniya ya sa bude baki da kyar tana fisgo numfashi ta ce "M.. Me.. Meye haka Zaiyan ka cikani ma..." Ba ta samu damar ƙarasa maganar ba sakamakon wani azabbaben zafi da ya ziyarce ta, haka ta dinga kai duka tana fisge-fisge kamar sabuwar kamu amma a banza... Kiran Sallah akan kunnenta aka yi ta yunƙura za tashi ta kasa, juya kai take tana kiran sunan shi amma sam bai motsa ba kamar matacce, kuka ta sa wanda sautin muryarta ba ya fita sosai tana miƙa hannu tana tabo nashi hannun, gajiya ta yi ta yi lamo tana nishi kamar mai nakuda in ta rufe idanuwanta sai taji kanta na mugun sara mata, idan ta buɗe kuma tsoron ganin Zaiyan ya sa taji jikinta ya dauki rawa, ta ci kukan ta marar sauti har ta gaji jin kanta na neman rabewa gida biyu ta haƙura... Har ta fidda rai da zai tashi taji yana numfarfashi karshe ma tari ya sarke shi, tun yana yi a kwance har ya tashi zaune idanuwansa a rufe ya dafe ƙirji, daga karshe ya dinga attishawa ba ƙaƙƙautawa har ita kan ta abin ya tsorata ta, can da ta lafa ya ja dogon numfashi sai ji ta yi yana faɗin "La'ilaha illallahu Muhammad Rasulullah sallallahu alai wa sallam." Daga haka bai kuma cewa komai ba, ta maƙure tana kallon ikon Allah jin ya yi kalmar shahada, bude idanu ya yi a hankali ya sauke shi akan ta ya zabura yana ja da baya baki na rawa ya ce "W..Wace ce ke?" Gaban ta ya faɗi ya kalli kansa ya ga ba shi ta komai ya yi sauri janyo kayan shi ya sa yana a'uziya sai ƙara tambayarta yake ita wace ce? Da ta gaji da tambayar ta tabbatar dai lalle fa ya samu lafiya ta nisa ta ce "Matarka mana." Sororo yake kallon ta irin ya ga abin al'ajabin nan, sai da ya kuma kallon nan ya gane abin da ya faru ya yi baya ya dafe kai, sai nanata Kalmar mata yake yi to yaushe ya yi aure bai sani ba? Kuma shi da bai ma isa aure ba ya aka yi har Mamansa ta bari ya yi aure? 😂😂😂Cakwakiya Iyar Haidar tamu ta gargajiya ki zo ki yi wa Zaiyan bayani... _Maman Nusaiba_ [6/20, 8:43 PM] Ummu Amjad: A HAKA NAKE SON SHI* Shafi na (49) Ganin ba shi da wanda zai ba shi amsa sai wannan yarinyar da ya gani a kwance cikin yanayi ya nufi ƙofar da yake kyautata zaton bandaki ne, ita kuwa da kallo ta bi shi tana sharar hawaye cike da tausayin kanta, wai yau ita ce Zaiyan ke cewa wace ce ita? To amma ai ba lefin shi ba ne dole dama ya yi wannan tambayar, da kyar ta daure ta juya ta lalibo dogon hijabinta har kasa ta sa ta rufe jiki da shi. Tana nan kwance sai ga shi ya fito ɗaure da towel idanuwansa a kan ta dan gani yake kamar mafarki yake, yunƙurawa ta yi ta duƙa za ta rarrafa ta ji ya ce "Dakata!" Cak ta tsaya tana kallon shi cike da takaicin dakatar da ita da ya yi, ga ya sanyo towel ɗin da take son in ta yi wankan tun da a cikin banɗakin yake ta sanyo, a fusace ta ce "To ka kaini banɗaki. " Da mamaki ya kalle ta sai kuma ya basar ya soma dube-dube, ganin bai samu abin da yake nema ba ya juyo da kallon shi gareta ya ce "Kayana fa." Maimakon ta ba shi amsa sai ta sa masa kuka, ba yadda ya iya ya sunkuya ya dauke ta ya kai ta banɗaki, kasancewar ba ta rabuwa da ruwa mai zafi ta ce ya kawo mata ruwa da ta aje, yana son ya tambaye ta a cikin me amma ba ya son ta kuma fusata ya fita. Sai da ya jima kafin ya gano ruwan a inda take zubawa ya kinkima ya kai mata, ba ta ko kalle shi ba ya fita zuciyarsa cike da tarin tambayoyi, wayar da ya gani a gefen katifar ya ɗauka ya danna ya ga har ma an fito a Masallaci, har zai aje ya kuma kallon kan screen ɗin wayar inda ya yi arba da photonsu shi da ita sun haɗa kai waje ɗaya suna murmushi ita da shi, tsananin mamaki ya kuma rufe shi ya soma yarda da cewar da ta masa ita matarsa ce, ganin lokaci na tafiya ya yi saurin yaye abin shinfiɗar ya sa wani sannan ya zo ya tada iƙama.. Ita kuwa sai da taji ruwan zafin ya huce sannan ta tashi tana daddafa bango har ta miƙe tsaye, alwala ta ɗaura ta gwada tafiya ta ji ba ta jin ciwo mai tsanani dan haka ta daure ta fito ba komai a jikinta tana kumbura baki, ganin ya kai goshinsa ƙasa ta ɗaure ta cije lips ta janyo towel ɗin da ya cire ta sanya duk da ya jiƙe, ta tsaya a tsaye kamar soja ta zuba masa idanu ganin yadda yake Sallah a nutse. Zama ta yi a kan katifar tana runtse idanu sai kuma ta yi saurin tashi ta kalli katifar ta ga an cire abin shinfiɗa an sa wani, dogon numfashi ta sauke ta rarrafa ta kwanta tana jiran ya gama itama ta gabatar da Sallah, shi kuwa duk abin da take yana jin motsin ta, bayan ya gama ya shafa Fatiha sannan ya juyo ya kallo inda take, ƙura mata idanu ya yi gaban shi na faɗuwa tarin tambayoyi sun cika masa ciki ya ma rasa da wacce tambaya zai fara yi mata, tashi ya yi ya dawo kusa da ita ganin idanuwanta a rufe ya dan bubbuga gefen ta ta yi saurin zabura ta tashi, da kallon mamaki ya bi ta ganin yadda ta firgita ya girgiza kai tare da nuna mata dadduma.. Turo baki ta yi ta tashi tsaye ta nufi wajan kayansu ta buɗe, wani babban Hijabi ta dauko wanda sau ɗaya ta taɓa saka shi dan har jan ƙasa yake, zura shi ta yi tana ɗan ɗingisawa ta iso ta tayar da iƙama cikin dauriya. Da kyar ta gama Sallah a tsaye tana yi tana zubar da hawaye, ƙarshe ma da ta je sujjadar karshe ta fashe da kuka tana rokon Allah ya kawo mata ɗauki a halin da take ciki, hankalinta a mugun tashe yake da ta tuna tambayar da Zaiyan ya mata wai ita wace ce? Maganar na firgitar da ita da haka ta gama Sallar ta zauna akan daddumar ta sunkuyar da kai dan kar ma su haɗa idanu. Shi kuwa shuru ya yi yana jin abin da take faɗa sai ya ji ta mugun ba shi tausayi, hakan kuma ya tabbatar masa lalle akwai abin da yake damunta matuƙa, kusa da ita ya matso ya sa hannu ya ɗago fuskarta ita kuma taƙi su haɗa idanu sai ta runtse idon, iskar bakinsa ya fesar yana jan numfashi ya saita nutsuwarsa sannan ya ce "Ya sunanki? Kuma nan ɗin a ina muke? Ina mamana take? Yaushe na aureki?" Saurin buɗe idanuwanta ta yi tana rawar jiki gabaɗaya tsoro ya dabaibaye ta, yanzu kenan ta zama ba ta kowa a kusa da ita? Shi wanda take gani ta ji sanyi yau ga shi Allah ya nufe shi da samun lafiya ya nuna bai san ita ko wace ce ba, hawayen da suka cika mata kwarmin idanu ne suka zubo ta kai hannu za ta goge sai ta ji ya sa lallausan hannunsa yana share mata, sai da ya sake tambayar ta a karo na biyu sannan ta tsagaita kukan ta ce. "Sunana Hauwa'u Maijidda amma an fi sanina da Abir, nan kuma muna a gidan haya ne su kuma da Jiddo suke kirana, sannan ni ban san ina mamanka take ba dan ba tare da ita ba na ganka." Saurin sakin fuskarta ya yi yana kallon ta, to in ba ta san mamansa ba waye to ya shige masa gaba har aka yi masa auren? Girgiza kai ya yi cikin wani kalar yanayi har idanuwansa sun soma canja launi ya ce "To waye ya nema min aurenki indai ba ki ga mamana ba?" Tashi ta yi ta isa ta zauna a bakin katifar ta janyo computer ta ta daddanna, ɗago kai ta yi ta dube shi ta masa alama da ya zo ya tashi jiki ba ƙwari ya isa gareta ya zauna a gefen ta, photunan su shi da ita ne suka bayyana ga su nan bila'adadin har da video ta miƙa masa, jan majina ta yi ta ce "Ka duba ka gani.." Ɗaya bayan ɗaya yake ganin photunan wani suna rungume da juna, wani kuma ya kwanta kansa a cinyarta ta ɗan ranƙwafo ta dauke su selfi, wani kuma suna harabar gidan duk sun ɓata jikinsu da ƙasa ta musu photon, ya kuma yin ƙasa inda ya dauko video da suke tsare da shi tana dauka yana bin ta, sake ɗauko wani ya yi ya ga yadda ya yayyaga kayan jikinsa sabbin fil ita kuma tana gefe ta kama kunnensa, sake yin ƙasa ya yi sai ya ga video da yake kiran ta da Anty, al'ajabi, mamaki, tsoro, firgici, duk suka kawo masa ziyara a lokaci ɗaya.. Ɗago kai ya yi ya kalle ta cikin wani kalar yanayi ya ce "Anty." Jinjina masa kai ta yi tare da matsowa daf da shi ta ce "Sunan da kake faɗa mini kenan tun farkon haɗuwa ta da kai ka taimakeni." Mayar da kansa ya yi ya ci gaba da kallon photunan, ganin haka ta miƙa hannu ta dubo photon Baba da Inna wanda ta musu su huɗu ta nuna masa tare da cewa "Waɗannan sune a matsayin iyayenka, kuma su ne suka nema ma aurena." Shuru ya yi yana kallon su Baba yana ƙara zuƙo fuskar Baba, sai can ya nisa ya ce "Wannan bawan Allah kamar dai na san shi can shekarun baya, mun taɓa zuwa gidan wani mai kama da shi ni da Mamana." Ya ɗago ya kalle ta sannan ya ɗaura, "To yanzu ina su waɗannan bayin Allah suke?" Ajiyar zuciya ta sauke ta rausayar da kai ta ce "Suna Yola mu kuma muna Kano." Da mamaki ya ce "Kano kuma? To me ya kawo mu Kano bayan kin ce su suna can a Yola?" Ganin dai suna jan maganar ta soma faɗa masa duk abin da ya faru da su tun daga farkon haɗuwar su har auren da aka musu da yadda su Baba suka riƙe shi kamar su suka haife shi, ta kuma sanar da shi tarihin rayuwarta da yadda kowa ya tsane ta har da Yayanta Abdul har izuwa gudowa da suka yi daga Yola suka dawo nan Kano da gwagwarmayar da take wajan ganin ta ciyar da su ta tufatar da su.... "Inna lillahi wa inna laihin raji'un! Wai kina nufin ki ce min duk tsayin shekarun nan ciwon hauka nake fama da shi?" Kamar wata ƙadangaruwa ta gyada masa kai, ta nemo photon Family ta ta nuna masa ɗaya bayan ɗaya, amma ba ta sanar da shi labarin Suhal ba dan tana so wata rana ta masa bazata. Shi kuwa duk tausayin ta ya cika masa zuciya, ya kuma ƙudurta a ransa ko ba ya son ta zai zauna da ita saboda haliccin da ta masa a rayuwar da suka yi, a hankali ya miƙa hannu ya janyo ta jikinsa ya rungume yana shafa bayanta, ita kuwa jin ta a jikinsa sai ta yi lamo tana sauke numfashi.. Sun dauki lokaci a haka ta ji ya ɗago ta tare da ɗago fuskarta ya manna mata kiss a kumatu ya kuma mata a goshi, duk da tsoron sa da take ji hakan bai sa ta ja da baya ba sai ma lumshe idanu ta yi tana jin yadda yanayin ta yake canjawa. Janye jikinta ta yi ta janyo wayarta ta duba lokaci ta ga karfe 10:a.m har ta yi, da hanzari ta yunƙura za ta tashi ya yi saurin kamo hannunta ta dawo ba shiri ta zauna, ƙara ta sa tana yarfa hannu ya kalle ta yana jero mata sannu ta kwace hannun ta kuma miƙewa tana hararar shi. "Ina za ki tafi?" Haushi ya rufe ta ta sunkuya ta ɗauki abincin su na jiya ta fita ba ta ce masa uffan ba, ganin ta fusata sai ya koma kan katifar ya kwanta yana lumshe idanu, tambayoyi yake son mata amma ya ga gabaɗaya ma tsoron shi take ji, tuna abin da ya faru tsakanin su ya ƙara jin tausayin ta sai kuma ya tashi zaune, so yake ya ƙara ganin yadda ya koma dan sosai ya yi mamakin ganin girman shi a photo, Janyo computer ya yi sai ya ga akwai code ba zai iya amfani da ita ba, sunanta ya sa amma aka nuna masa error ne ya saka, sai ya sa sunansa da ta faɗa masa ya ga ta buɗe abin ya ba shi mamaki yana kuma jinjina zallar tsagwaron son da take masa, photunan ya kuma bi yana kallo ganin yadda ya tara gemu ga saje, ya riƙe baki yana yi wa Allah godiya da ya ba shi lafiya... Haka ta daddaure ta dumama musu abincin, bayan ta gama ta kuma tafasa wani ruwan zafin sai ta zuba ɗan kaɗan a coup ta koma ɗakin. Yana ta daddanna computer ta same shi kawai ta share shi ta isa ta haɗa shayinta mai kauri ta ɗauki wayarta ta fito da cup ɗin a hannunta tana hura hanci, wato ma shi ko a jikinsa ta kuma yin kwafa ta zauna a waje tana kallon su Amal da suke wasa ita da ƙannanta biyu. Sai da ta shanye shayin tas sannan ta dawo ɗakin ta tsaya masa a ka ƙerere, kallon ta ya yi da alamar tambaya sai ta turo baki ta ce "Ka ɗauko min ruwa a waje na dafa." Bai ce da ita komai ba ya janye computer ya fita ya ga babu kowa sai wasu yara biyu, ya kalli gidan ya ga dai lalle fa a gidan haya suke, dauko ruwan ya yi ya kawo mata zai aje ta ce ya zuba mata irin na asuba, ya zuba mata sannan ya fito. Kayan wanka ta dauka ta shige abin ta ya bi bayanta da kallo, mamaki sosai yake yadda ta jure rayuwar irin ta talaka saboda shi, ta baro ahalinta gidan da ko maigadin gidan ya fi ƙarfin ya zauna a irin wannan gidan ballantana ɗiyar masu gidan, komawa ya yi ya kwanta jin yadda kuzarinsa ke yin ƙasa, wata irin kasala ce ta rufe shi sai miƙa yake karshe sanyi ya kama shi ya janyo abin rufa ya rufa ya ƙudundune. . Umma hankali a tashe isa gidan Malam, koda ta isa ta soma zaiyano wa Malam shiri fa na neman wargajewa, sai da ta gama yi masa jawabi bai ce da ita komai ya yi tsumu-tsumu kamar ɗan tsakon da ya faɗa ruwa. Kallon shi Umma ta yi cike da mamaki ta ce "Malam ya ka yi shuru ba ka ce komai ba?" Gyara zama ya yi yana muzurai ya janyo farantin gabaɗaya komai a sanyaye yake aiwatarwa, bayan ya gama duddubawa ya ɗago ya kalle ta ya ce "Ba komai duk za a gyara da alama dai ke ce kika ɓata aikin." Dafe kirji ta yi tana zaro idanu jin abin da Malam ya faɗa, a ruɗe ta ce "Malam ni dai don Allah a taimaka min kar aikin nan nawa ya samu matsala, yanzu fa gabaɗaya family Maitama ya hargitse sai neman wannan yarinyar suke." Kwantar mata da hankali ya dinga yi ya sanar da ita zai gyara komai sannan ta tafi. Karfe 1:30pm daidai shi ya riga ta tashi ya shige banɗaki ya yo wanka ya fito, yana goge jikinsa ne ya ga tana motsawa sai ya juya mata baya dan kar taƙi tashi. A hankali ta soma buɗe idanuwanta har ta gama buɗe su a kan shi, saurin tashi ta yi ta zari hijabi ta wuce banɗaki kanta a ƙasa, da kallo ya bi bayanta cikin yanayi mai nuna zallar tausayin ta, girgiza kai ya yi ya sanya kaya ya shinfiɗa musu dadduma ya zauna zaman jiranta ta fito. Jim kaɗan sai ga ta ta fito ta nufi wajan kayan su, sai da ta juya ta ga ba ita yake kallo ba sannan ta yi saurin sa kaya cikin rawar jiki. Duk abin da take yana kallon ta ta gefen ido, ganin yadda take sauri sai abin ya ba shi dariya wai duk dan kar ya ga jikinta ne take wannan abu kamar mazari, tana gamawa ba ta ce masa komai ba ta iso kan daddumar, shi kuma ganin haka ya tada iƙama. Bayan sun gama ne ya juyo tare da gyara zama cikin nutsuwa ya sa hannu ya matso da ita kusa da shi ganin tana takurewa a waje ɗaya , ba dan ta so ba dai ta zauna. A hankali ya ɗago da fuskarta ya tsura mata idanu, itama tun tana ƙin kallon sa har ta saki jiki ta ɗago ta kalle shi. Sun jima a haka sannan ita ta fara janye nata idanun sai a lokacin ya motsa lips ɗinsa cikin sayayyar murya ya ce "Jiddo." Da sauri ta kalle shi ta yi sauri sunkuyar da kai, murmushi ya yi sannan ya ɗaura da cewa, "Kin san asalin sunana kuwa?" Tana daga haka ta girgiza masa kai sai kuma ta ɗago tana kumbura baki, murmushi ya kuma sakar mata ya sa hannu ya bubbuga kumatunta, saurin ɓoye fuskarta ta yi a jikinsa ya ɓamɓaro ta tare da cewa "Kin ga tashi mu yi magana mai mahimmanci, ina so na sanar da ke ni ko waye." Lumshe idanu ta yi wani sanyi ya ziyarce ta har kasan zuciyarta, dama abin da take son tambayar shi yau ɗin nan tun da ta ga yanzu duk wani abu na rayuwarsa zai tuna a cikin kwana biyun da ya yi na samun lafiya, zama ta yi akan cinyarsa ya tallafo ta ta baya ta kalle shi tuna wani da ya yi mata kawai sai ta sa dariya tana rufe fuska, shi ma murmushi ya yi yana mamakin abin da ya sa ta yin dariya, sai da ta tsagaita ya ce "Me kike yi wa dariya?" ƙunshe baki ta yi tana son ta daina dariyar dan ta sanar da shi, sai da ta tsayar da dariyar ta sauka akan cinyarsa ta zauna a gefen shi ta ce "Na tuna wani lokaci ne da ka min wankan taɓo har da cewa nan wajan bai samu ba. Nan dai ta shiga faɗa masa abin da ya faru ranar da ta same shi yana ɗakin ƙasa har kuka ta yi dan takaicin abin da ya mata." Ƴar dariya ya yi dan yanzu ya daina mamaki in ta ce masa ya yi wani abu a baya, agogon da za sayo masa ya janyo ya kalli lokaci ya ga ai har karfe biyu ta gota, kallon shi ta yi yana shirin ta yi ya ce "Bari na fita ko ma dako ne na yi na nemo mana abinci, har yau ina ƙara jinjina miki akan yadda kike ɗawainiya da ni na tsayin lokaci." jinjina masa kai ta yi dan ta so ya sanar da ita asalinshi, amma kuma ta hakura sai ya dawo ta masa Allah ya kiyaye har zai fita sai ta dauki waya ta miƙa masa, kallon ta ya yi ganin waya kuma ba tata ba ce, amsa ya yi yana juya wayar tare da mata kallon ta yi masa ƙarin bayani. Sunkuyar da kai ta yi ta ce "Jiya na ga Ladidi zai sayar da wayarsa shi ne na saya maka kafin ka samu ka yi sabuwa, na sa ma har layi da number na a ciki da ta Mama da ta mijinta." Ta faɗa tana tashi tsaye. Rasa me zai ce mata ya yi kawai ya janyo ta ya rungume, murya can ƙasa ya ce "Jiddo ke matar rufin asiri ce, ke mace ce wadda kowanni namiji zai so samu Allah ya miki albarka, Ubangiji ya ba ni ikon kyautata miki fiye da yadda kika min." Murmushi ta yi ta ɗago daga jikinsa ta ce "Amin mijina Allah ya tsare ka a dawo lafiya." Fitowa suka yi a tare tana riƙe da hannunsa, Tasakkawato da ke shirin fita ta tsaya tana kallon su cike da burgewa, murmushi Abir ta yi ta ƙaraso kusa da ita ta ce "Mama ina zuwa? Jiya fa da dare kika dawo ko hira ba mu yi da ke ba, shi ne yanzu za ki kuma tafiya ba ko gaisuwa?" Zaiyan ya matso tare da ɗan rusunawa ya ce "Mama ina yini?" Baki buɗe take kallon Zaiyan da ya sha wanka sai kuma ta ce "Jiddo shin wanga mijinki na ko kuwa dai ba shi na ba?" Ƴar dariya ta yi ta ce "Shi ne fa Mama yanzu dai bari na raka shi zai fita sai na dawo mu yi magana." Da kallo kawai ta bi bayan su har suka fita, sai da Abir ta dawo suka nufi ɗakin Tasakkawato suka zauna, ƙasa hakuri ta yi ta ce "Jiddo ki yi min bayani mana kin bar ni a duhu." A kunyace ta faɗa mata abin da ya faru daga lokacin ya samu lafiya, tana gamawa ta kuma rufe fuskarta ji take kamar a gaban Mommy take ta sanar da ita abin da ya faru. Hannu Tasakkawato ta daga sama ta ce "Alhamdu Lillah, na tayaki murna Jiddo da mijinki ya samu lafiya ma sha Allah." Ita dai daga haka kasa cewa ta yi komai kanta a ƙasa, sai da ta gaji da surutu ta ga dai ba ce mata komai za ta yi ba ta tashi suka fita inda take faɗa mata ɗiyar ɗaya daga cikin ƙawayen ta ake yi wa aure, Allah kiyaye Abir ta ce ta wuce... Bayan La'asar ta samu wasu yara biyu sun zo kitso, sai da ta duba kibiyar kitson ta rasa hakan ya sa ta sa hijabi ta nufi gidan Aisha ta aro. Ko kofar gidan ba ta ƙarasa ta ji an yi sama da ita ta faɗa cikin wani abu, ihu take son yi ta ji an rufe baki ruf.... *Maman Nusaiba ce [12/8, 12:48 Safiya] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): *A HAKA NAKE SON SHI* Shafi na 50 Shuru-shuru suka ji ba ta dawo ba Maman Amal da ta fito daga ɗaki riƙe da hannun Amal ta tsaya tare da riƙe baki, ganin yaran zaune dan tana shirin shiga ɗaki ta ɗan kwanta Abir ta fita, ƙarasowa ta yi ta ce "Wai Jiddo ɗin ba ta dawo ba ne? Ɗaya daga cikin su ta mike tsaye cikin nuna damuwa ta ce" Wallahi fa har yanzu ba ta dawo ba, kuma ni ina da zuwa wajan birthday ɗin ƙawata da dare, ga shi ba ta ma gama min kitso ba ballantana ayi maganar ƙunshi gara na tafi kawai dan kar na ɗauki lokaci Mamana ta ga kamar ko wani wajan na biya." Tana gama faɗin haka ta wuce abin ta, ganin haka ya sa itama ɗayar ta bi bayan ta suka wuce suna mita... Zama Maman Amal ta yi sai ga Tasakkawato ta dawo da kaya niƙi-niƙi a cikin ledoji, da kallo ta bi ta har ta aje kayan a bakin kofar ɗakinta tana sauke numfashi, juyowa ta yi ta kalli ƙofar ɗakin Abir ta ce "Jiddo fito kar ki yi girki na kawo muku abinci har da marar dafawa ma." Maman Amal ganin Tasakkawato ba ta kula ta ba sai ta ɗan matso kusa da ita ta ce "Tasakkawato Jiddo fa tun ba yanzu ba ta fita amsar kibiya a wajan Aisha amma shuru ba ta dawo ba." Saurin kallon ta Tasakkawato ta yi tare da dafe ƙirji ta ce "Subhanallahi! To me ya hwaru da ita? Kin ga bari na shiga gidan Aisha naji." Ba ta tsaya jin komai ba ta wuce da sauri ta sururutai. Ko da ta je gidan Aisha ta samu ba ta ma gidan babu kowa, haka ta juyo ta dawo tana sallallami. Abu kamar wasa har bayan isha'i ba ita ba labarin ta, duk sun zauna sun yi jugum-jugum musamman Tasakkawato sai suka ji karar waya a ɗakinta, tashi Maman Amal ta yi ta shige ɗakin. Wayar ta gani a gefen katifarsu ta ɗauka tana bin sunan da ke kan screen ɗin wayar da kallo, ganin an rubuta *Abzai*, miƙa wa Tasakkawato ta yi cikin sauri ta ɗaga babu jinkiri tare da cewa "Hello wane na?" Muryar Zaiyan ta ji yana fadin "Am so sorry Jiddo gani nan zuwa gida ina kan hanya." Tasakkawato ta ƙara faɗin "Kai ba ita ta ba, ka yi maza ka dawo akwai matsala." Tana faɗin haka ta katse kiran,. Suna nan zaune sai ga shi ya shigo gidan da Sallama, amsa masa suka yi Maman Amal ta saki baki tana kallon shi jin ya yi magana, ganin a halin da ake ciki sai ta haɗiye tambayarta ta kalle su, tsayawa ya yi a gaban Tasakkawato fuskar nan tasa ba alamar annuri ya ce "Mama ina ta ce muku za ta je?" "Wai gidan Aisha za ta amso kibiya ta rasa tata, to shi ne fa har yau ba ta dawo ba." Shuru ya yi yana kallon gefen suka zuba masa idanu, sai da ya ɗauki lokaci a haka sannan ya ɗan yi taku biyu zuwa uku ya juyo, furzar da iska bakinsa ya yi cike da tsananin jin zafin da zuciyarsa ke masa, har zai yi magana kuma ya fasa ya ciro wayarsa ya daddanna wasu numbobi ya kara a kunne. Ringing ɗaya a na biyu aka dauka, shuru ya yi alamar yana sauraron abin da ake sanar da shi, sai zuwa can ya nisa ya ce "OK thank you." Daga haka ya katse kiran ya nufi ɗaki yana faɗin "Ku kwantar da hankalinku in sha Allah zan nemo ta da kaina." Tasakkawato ta biyo bayan shi tana fadin "Kayya! To kai da ba gari ka sani ba taya za ka iya nemo ta? Ba ma wannan ba ba ka san a wani waje take ba, kawai dai lalibe ne za ka yi a cikin duhu." Bai ce mata komai ba ya shige ɗaki ya bar su a tsaye suna maida yanda aka yi.. Jar mota sabuwa dal ce ta yi packing a wani gida, wanda kafin ma ka shiga za kake juyo kiɗa na tashi. Fito da ita suka yi idanuwanta a rufe suka nufi ciki da ita, sosai 'yan mata da samarin ke cashewa a cikin wannan gida, Wasu na shan giya, wasu na rungume da samarinsu, wasu kuma sun rungume mata 'yan'uwan su suna kissing ɗin juna, Wasu kuma suna gefe suna kallon masu rawa ana musu liƙi. Wani keɓantaccan ɗaki aka kai ta suka cire mata kyallen da suka rufe mata ido, da sauri ta bude idanuwanta tana kallon inda take, gane abin da ya faru da ita sai kawai ta fashe da kuka tana bin wanda suk kawo ta da kallo, su kuma suka juya suka bar ɗakin.. Tana nan zaune sai ga wata budurwa tashigo ɗakin tare da zama a kusan da ita, saurin matsawa Abin ta yi ta bin da kallo ganin yadda take mata wani kalar kallo. Dariya budurwar ta yi ta sake matsowa tare da dafa kafaɗarta cikin salo irin nasu na 'yan bariki ta soma faɗin "Welcome back my girl, bari ni na samu kasona kafin Oga ya samu isowa kar ya dauke ki ban samu abin da nake so ba." Ta faɗa tana jan Hijabin da ke jikin ta ta cire shi, saurin yin baya ta yi ta kuma biyo ta baki na rawa ta ce "K.. Ke me za ki yi min?" Dariya kawai ta yi ta damki hannuwanta ta kama rigar ta ja da ƙarfi har sai da kan dinkin ya yake kaɗan, a zabure ta mike tana nuna ta da hannu rai a matuƙar ɓace ta ce "Wallahi kin yi kaɗan ki ga jikina, banza shashasha." Itama mikewa ta yi cikin zafin nama ta nufe ta da nufin ta kama ta, ai kuwa ta kwasa a guje za ta fita a ɗakin ta yi saurin tare kofar ta rufe, ganin haka sai ta koma can ɗaya gefen tana haki tare da cewa "Ki fita ki ba ni waje kafin na illata ki." Kallon ba ki da aikin yi ta mata tana nufo ta, ganin haka ya sa Abir ta tsaye tare da dakewa jin wani ƙarfin gwiwa ya zo mata, tana isowa ta nemi ta kama ta ita kuma ta goce suka kama kunce. Sun ɗauki lokaci a haka Allah ya ba ta rana ta ɗago ta yi saurin kai hannunta ta damki wuyan, nan da nan ta zazzaro maganai waje saboda ta mata ruko ba na wasa ba, sai da ta ga ta soma sakin jiki ta sake ta sai ga ta can ta zube a ƙasa tana haki, nuna ta ta yi da hannu ta ce "Ni za ki nuna wa ke cikakkiyar ƴar iska ce? To kin yi kuskur... Ba Ta ƙarasa yin maganar ba sakamakon jin an bude kofar, saurin juyowa ta yi suka yi ido hudu da shi cikin shigar shi da yaran Turai. Tsaki ta ja tana riƙe ƙugu ganin wanda ya sato ta a karo na biyu, wani kalar kallo da take masa wanda shi kansa har abin ya ba shi mamaki ya zauna a kujerar da ke gefen su, kwafa ta yi ta ce "Wai kai wani kalar jahili ne? Ka taɓa ganin an yi so dole? Ko ana aure kan aure ne?" Murmushi ya yi yana kallon ta, ya gyara zama ya ce "My love ai duk wanda ya aure ki ya yi banza, yanzu haka ma da madaura aure na zo za a ɗaura mana aure sannan mu yi party mu tare a gidanmu, ke kin san kalar son da nake miki kuwa?" Banza ta mishi ta matsa ta ɗauki hijabinta da sauri ta saka, za ta zauna ta ga wasu mutane sanye da manyan kaya su huɗu sun shigo ɗakin sai washe baki suke, wajan zama ya nuna musu suka zauna ya nuna musu Abir tare da cewa. " Ita ce amaryar tawa. " Washe baki suka yi kowa na fadin "Gaskya ranka ya daɗe ka yi dacen mata wannan zuƙeƙiyar balarabiyar." Saurin katse su ya yi ta hanyar ɗaga musu hannu, waya ya dauka ya kira sai ga mata biyu sun shigo ya nuna musu budurwar nan suka yi waje da ita. Zama suk yi mutum biyu suka ce sune iyayen Abir, biyu kuma na Big boy suka fiddo sadaki suka ba da su kuma suka masa, ɗaga hannu suka yi a tare suka ce "An ɗaura auren big boy da amaryarsa princess Abir mun sheda Aure ya ɗauru." Tashi big boy ya yi ya kwarara ihu tare da yin juyi ya kama kansa irin daɗi ya kai masa, ya ciro kuɗi daurin yan rafa ɗauri biyu ya ba su suka fita a ɗakin, kallon ta ya yi yana faɗin " Kin ga yanzu kin zama matata bari naje na shigo miki da lefenki ciki." Fita ya yi da sauri yana bude murya tare da sanar da yan palon ya yi aure, ai kuwa suka kwashi ihu aka sa sabon kiɗa tare da ƙure volume.. Ganin ya fita ta yi saurin rufo kofar ta murɗa mata key tare da yin ƙasa ta sulala ta fashe da kuka. Yana zuwa ya ga ta rufe kofar ya yi ta bugun duniyar nan taƙi budewa, ya sa key ɗin da ke wajan shi amma yaƙi shiga saboda akwai wani a jiki, ita kuma tana jin yadda suka taru suna fadin "Amarya bude wa ango kofa zai shigo." Da sun ce haka sai ta kara wa kukan ta ƙarfi, gabaɗaya hankalinta yana kan mijinta. Da suka gaji da magana sai suka koma suka ci gaba da shagalin bikin auren big boy.. Abu kamar wasa Abir ta yi kwana biyu a cikin wannan ɗakin yunwa duk ta lakata ta, cikin kwana biyun da ta yi ta mugun ramewa saboda da ba da aikin yi sai kuka Sallah kawai take tsayar da ita daga kukan da take, ita kanta Sallar ta sanadin agogon da ke manne jikin ɗakin ne take amfani da lokacin da yake nunawa ta yi Sallah. A ɓangaren Big boy Kuwa yana nan bai tafi ba kullum sai ya kawo abinci ya aje mata a bakin kofar, wanda in zai sa a zubo sai ya barbaɗe shi da maganin bacci dan in ta ci burinsa ya cika. Sai dai in ya dawo sai ya tarar da abincin kamar yadda ya bar shi, hakan na baƙanta masa rai dan tsananin son da yake mata ya sa sai ya yi ta lallamin ta ta fito ba zai mata komai ba amma sai dai ya ji sautin kukan ta tana faɗin ba za ta bude masa ba. Wannan abu ya tsaya wa Big boy a rai ba ya so ta kamu da ciwon yunwa, haka dai yake zama a gidan idan ya ji shuru sai ya fita can baya akwai ruwan wanka irin nasu na yaran girman Turai... Zaiyan gabaɗaya ya shiga damuwa duk yadda ya yi tunanin abin ba haka yake ba, kullum sai ya fita neman matarsa har gidan redio yake zuwa yana bayar da cigiyarta amma shuru kake ji wai shaho ya ci shirwa. Ita kuwa Tasakkawato har mamaki take in ya ce mata yaje waje kaza ya ba da cigiyar Abir, sai ta yi ta tambayarsa da ya je bai ɓata ba? Kullum haka take faɗa idan ya dawo, da ya gaji da tambayar sai ya yi murmushi ya ce "Mama kenan, to ai ni à cikin garin nan babu Unguwar da zan je na ɓata kuma ba zan tambayi kowa ba da kaina zan je, saboda a cikin garin na taso na girma da hankalina muka bar garin." Baki bude take kallon shi har ba ta san lokacin da ya shige ɗaki ba, sai da ta ji ƙaran rufowar sannan ta ankare da ba ya nan. Ɗaki ta nufa zuciyarta ba daɗi ta yi sabo da Abir ba kaɗan ba, haka dai ta yi ta juyayi ta tura wa ƙawayenta photon Abir ta sanar da su an sace ta su taimaka mata su sa a nemo musu ita. Su kan su ƙawayen nata sun girgiza da jin wannan mummunan labarin, nan take suka mata Alƙawarin sa wa a binciko musu duk inda take ta musu godiya sosai ta sha kuka ta more sannan ta yi bacci.. Shi kuwa Zaiyan ba ya iya bacci, yau ma ya zauna yana ta tunanin yadda take ba shi kulawa tana tattalinsa kamar kwai, duk da ba ta san shi ko waye ba amma hakan bai sa da ya dawo cikin hankalinsa ta rage wani abu daga cikin kulawar da take ba shi, ko da lamarin nan ya faru a tsakanin su ba ta ji haushinsa ba iya fushinta na kwana ɗaya ne ta huce. Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon samar ɗakin abin duniya ya masa yawa, ya rasa ta ina zai fara, da neman mamansa zai fara? Ko da neman matarsa? Tashi ya yi tsaye sai kuma ya yi saurin dawowa ya zauna, computer Abir ya janyo ya nude code ya shiga Google, wasu abubuwa ya duba sai can sai ga photon wani ya bayyana sanye da ƙananan kaya fuskarsa rufe da wani kyalle, ƙura masa idanu ya yi da ɗan wasu daƙiƙu, murmushi ya saki ya fita ya shiga Facebook.. Wani suna ya rubuta *Bashow* sai ga account ɗin y fito masa ya shiga, number shi ya dauka ya fita daga Facebook ɗin ya danna masa kira. Sai da ta yi ringing ta gama bai ɗauka ba ya kuma kira, ta kusa katsewa ya ɗauka ya yo shuru bai ce komai ba, sai da wancan ya gaji da shurun ya ce "Hello." Murmushi Zaiyan ya yi tare da faɗin "Bashowwwwww." Ya ja sunan yana sakin murmushi mai sauti duk da na yaƙe ne yake. Daga cikin wayar Bashow ya kurma ihu murna yana faɗin "Abokina dama ka na nan a raye? Don Allah a ina kake?" Gyara zama ya yi ya ce. "Ina Kano." Bashow ya ce. "Da gaske? Yaushe za mu haɗu?" Numfashi ya ja ya ce "Ka ga yanzu dai idan har kana da lokaci za mu iya haduwa yanzu tun da dare bai yi ba sosai karfe 10:00pm ce, wani abu ne ya taso shi ya sa na nemo ka dan ka kira sauran ka sanar da su dawowa ta cikin da'ira." Ya nisa sannan ya ɗaura da ba shi ɓatan Abir amma bai ce mata matarsa ba ce su taya shi neman ta.. Bashow ya jajan ta masa nan ya yi masa alƙawarin gobe su haɗu da safe sannan suka yi sallama... Washe gari suka haɗu inda suka rungume juna cike da kewar juna, nan suka samu waje suka zauna suka tattauna sosai, bayan sun gama ya dawo gida ya harhaɗa kayansa ya zuba a cikin akwati ɗaya ya ɗauki computer Abir ya fito. Kofar ɗakin Tasakkawato ya iso ya kira ta ta fito, ganin si da akwati ta dafe ƙirji ta ce "Ina za ka je Zaiyan?" Sunkuyar da kai ya yi ya ce "Mama zan tafi wajan Abokina, inda a can za mu ci gaba da binciken inda Jiddo take har Allah ya sa mu gano ta, ga wanne key ɗin akwai kayanta a ciki in na sake dawowa zan amsa." Daga haka ya wuce da hanzari bai ma tsaya ta samu damar yi masa wata tambayar ba.. Da kallo kawai Tasakkawato ta bi bayan shi har ya fita, ɗaki ta koma ta dauko Hijabi da handbag ta fito ta wuce.. A ɓangaren su Abba kuwa har sun gaji da laliban inda za su ga Abir sun zuba wa sarautar Allah idanu, gabaɗaya familyn duk sun shiga damuwa na rashin sanin inda take, Grandma har kwanciya a Asibiti ta yi saboda wannan hali da suka shiga,.. Abdul kuwa tun da ya dawo haiyacinsa bacci ya kaurace wa idanuwansa sakamakon abubuwan da suka tsaya masa a rai. Na farko dai ya ga Hafsat a matsayin matarsa ta sunnah ranar ji ya yi kamar ya shaƙe ta ta mutu, amma ya danne zuciyarsa ganin yadda take kuka da ya daka mata tsawa ya ce ta tafi gidansu zai rabu da ita, sosai ta ba shi tausayi dan shi kansa ya san Hafsat na son shi sosai kawai dai ba ya son haɗa jini ne da Alhaji Mustapha, sai dai kuma babu yadda ya iya ya hakura. Abu na biyu kuma ganin babu ƴar amanarsa a tare da shi, wannan abin shi ya fi tayar masa da hankali in ya tuna Wai ma Zaiyan ta aura kuma sun gudu, haka yake kwana yana salla a yana kuka tare da rukon Allah ya baiyana masa ƙanwarsa cikin gaggawa ya nemi yafiyar abin da ya mata.. Abu na uku kuma, bayan ya dawo haiyacinsa ya shiga wayarsa ya ga yadda ya dinga fadar sirrin duk wani abu da ya danganci aikinsa, a lokacin sai da na saki ƙara na takaicin duk abubuwan da ya tura wa su Alhaji Mustapha, abin karin takaicin wai har ma group gare su su huɗu ya shiga tashin hankali ganin irin abubuwan da ya faru, haka zai zauna ya yi ta Istigifari yana neman yafiyar Ubangiji kan cin amanar ƙasar shi da ya yi... Su Alhaji Mustapha kuwa komai ya ci gaba dan yanzu an soma zaɓe sai zarya suke wajan duk wani malamin tsubbu da bokan da suka ji labarin aikin su na ci a lokacin, da zarar sun samu labari za su kai masa ziyara. Hakan ya sa duk suka rufe bakin mutane aka manta da maganar da Damisa ya yi, hakan ya sa hankalinsu ya kwanta har suke tunanin Damisa ya sheƙa jin shuru.... Ranar zaɓe suka je shi da tawagarsa suka kaɗa ƙuri'a ana ta ɗaukan vidéo ana saka wa a social media. Bayan an gama zaɓe aka tabbatar wa da Alhaji Mustapha shi ne ya ci Gwamnan Jahar ba ki ɗaya, ranar kusan kwana suka yi suna yin party inda aka kawo musu 'yan mata ƙanana sabuwar balaga dan dukkan su yara ne, a cikin su babu wadda ta kai shekaru 20 daga mai 19 sai mai 18 sai mai 17. Yaran nan na kuka haka suka sa aka musu allurar bugar da hankali suka aikata abin da suke so da su. Haka bayan kwanaki aka rantsar da Alhaji Mustapha ya ɗare kan kujerar Gwamna... Damisa kuwa ya ji baƙin ciki da Alhaji Mustapha ya samu kujerar nan, abin da ya ƙara fusata shi da aka yi watsi da abin da ya faɗa, hakan ya sa ya bi ta ƙarƙashin ƙasa.. Yau Abir watan ta ɗaya cif da rabi a cikin wannan gida, duk yadda Big boy ya yi tsammanin abin zai zo masa da sauki ya wuce tunaninsa, yana tsaka da haka Daddynsa ya kira shi ya ce ya je ya dauko shi daga airport, ba dan ransa ya so ba ya fita tsabar sauri ko kofar palon bai kulle ba ya wuce... Abir na ganin shi ta taga har ya fita, ta lallaɓa ta buɗe ɗakin ta fita waje, cikin sanɗa ta dinga tafiya ta leƙo ta ga Maigadi ba ya bakin kofa, cikin azama ta nufi kofar ta bude a hankali ta fita ta mayar ta rufe, tana ganin ta fito waje ta kwasa a guje ta karya kwanar layin.. Sai da ta ci gudu sosai sannan ta iso bakin hanya ta tsayar da wata mota ta shiga, sai da ya fara tafiya sannan ya tambaye ta ina zai kai ta? Ta sanar da shi suka ci gaba da tafiya. Allah-Allah take ta gan ta a gida sai waiwayen bayan su take, gabaɗaya ta galabaita da kyar take numfashi har suka iso gida.. Ta maza ta yi ta fito daga ciki da kyar ta ce "Ɗan tsaya na kawo ma kuɗin." To ya ce mata ta daddaure ta nufi cikin gidan, da kyar da iya yin sallama tana tafiya jiki a mace, Tasakkawato da ta fito daga ɗaki ta hange ta ai da sauri ta nufo ta. Kafin ta iso ta yanke jiki ta faɗi sumammiya. Ƙwalla kiran su Maman Amal ta yi suka fito duk suka yo kan ta hankali a tashe.... _Maman Nusaiba ce_ [6/20, 8:43 PM] Ummu Amjad: : *A HAKA NAKE SON SHI* Shafi na 51 Ɗaukan ta suka yi su uku suka nufo ɗakin Tasakkawato, hankalin Tasakkawato a tashe take kiran sunanta tana kuka, Maman Amal ta ɗauko ruwan sanyi aka shafa mata a fuska. Ajiyar zuciya ta sauke tana motsa idanuwanta amma a rufe suke, sannu suka dinga jero mata tare da kiran sunanta ta kasa motsawa, sai zuwa can ta soma buɗe idanuwanta har ta buɗe su tar a kan su. Taimaka mata suka yi ta tashi zaune suka jingina ta da jikin kujera sai bin su take da kallo, Tasakkawato ta rungume ta tana faɗin "Alhamdu Lillah Allah mun gode maka, sannu Jiddo ina yake miki ciwo yanzu?" Girgiza mata kai ta yi da kyar ta iya cewa "Mama ruwa." Da hanzari Tasakkawato ta kawo mata gorar ruwa mai sanyi ta kai mata baki, da sauri ta soma sha har da lumshe idanu suka zuba mata ido cike da alhini, sai da ta shanye tas sannan ta janye gorar tana sauke numfashi. Abinci Maman Samira ta kawo mata tuwon Masara fara da miyar taushe, sosai ta ci tuwon dan taushen ya mata daɗi sosai, bayan ta gama ta kawo mata ruwa ta wanke baki da hannu, sai a lokacin ta yi gyatsa ta kalli Tasakkawato ta ce "Mama ina Zaiyan yake?" Zama ta yi a kusa da ita tare da dafa kafaɗarta, hakan ya sa ta ɗago ta kalle ta ita kuma ta nisa ta ce "Ki huta tukun sai na sanar da ke komai, yanzu ba surutu ya kamata ki yi ba ki kwanta ki huta zuwa an jima zan miki bayanin komai." Gabanta ne ya faɗi ta yi raurau da idanu sai ga hawaye sun zubo sharr ta turo baki ta ce "Please ki sanar da ni yanzu." Rarrashin ta da dinga ita kuma ta ci gaba da kuka tana faɗin ina Zaiyan yake, ƙarshe ma ta sarƙe da tari ta yunƙura za ta tashi Tasakkawato ta yi saurin ruko ta, tambayar ta take ina za ta je? Dafe ƙirjinta ta yi da yake mata zafi da daure ta ce "Mama amai nake ji." Jin haka ya sa Tasakkawato ta nufi toilet da ita, sai da ta amayar da abin ta ci sannan ta samu salama zuwa lokacin ta galabaita matuƙa. Bayan sun fito ta kwanta a kan kujera tana rawar sanyi Tasakkawato ta dauki bargo ta rufe ta da shi, nan da nan zazzaɓi mai zafi ya rufe ta ta ƙudundune a bargo. Haka suka saka ta a gaba Maman Amal ta dubi Tasakkawato ta ce. "Ni kuwa wai har yau Zaiyan bai sake dawowa ba?" Girgiza mata kai Tasakkawato ta yi tare da cewa "Bai sake dawowa ba tun ranar da ya bar gidan nan,ni yanzu tsoro na ɗaya kar Jiddo ta shiga damuwa na rashin ganin sa in ta farka." Haka suka ci gaba da tattauna maganar kowa jiki a sanyaye.. Tun da Zaiyan ya koma gidan su Abokinsa ya kasa nutsuwa, duk da abubuwan da suke gaban shi amma tunanin rashin matarsa ya fi komai tayar masa da hankali, idan abokinsa ya tambaye shi me yake yi wa zurfin tunani sai ya sanar da shi cewa kawai dai ba ya jin daɗin garin ne.. Yau ma kamar kullum da misalin ƙarfe 11:00pm na dare shi da Bashow suna zaune gaban computer, ɗago kai Bashow ya yi fuskarsa dauke da damuwa ya ce. "Aboki Wallahi ka ga na kasa kwato maka da account ɗinka, yanzu haka maganar da nake ma wanda ya yi maka hacking ɗin account ɗin ya yi posting." Saurin janyo computer ya yi yana jin ranshi na ƙara ɓaci, rubutu ya ga gani an yi sak kamar shi ya yi, photon kan dp ya danna sai ya ga an canja wanda yake kai tun lokacin da yake cikin hankalinsa, ƙara zuƙo photon ya yi ya ga dai sak yadda yake dressing haka mai hacking ɗin ya yi nasa ya ɗaura. Ya cika da zallar mamaki ganin ikon Allah, sai da ya jima a haka sannan ya dauke idanuwansa daga kan photon, lumshe idanu ya yi yana jin yadda kansa ke mugun sara masa babu abin da yake gani in ya rufe idanu sai Abir da take masa gizo, ya ƙara kwantar da kansa a jikin kujerar yana tuna bakar ranar da ta raba shi da matarsa, gabaɗaya ya kasa nutsuwa tuna halin da take ta tashi ba lafiya sosai ga shi kuma an sace masa ita. Saurin buɗe idanu ya yi tare da janyo computer ya shiga Facebook, wani numbobi ya danna tare da yin ɗan rubutu ya tura, haka ya dinga wurgawa na Kusan minti biyar ya kafe computer da kallo sai gani ya yi ta nuna masa OK, saurin danna Ok ya yi sai ga shi ya kwato account ɗin sa. Hannu ya ɗaga sama ya ce "Alhamdu Lillah na kwato shi Bashow." Murna suka yi sannan ya shiga Istagram nan ma ya kwato kayanshi har Tiktok sai da ya shiga ya kwato sannan ya janye computer yana fesar da numfashi, sai lokacin kuma ya dauki wayarsa ya lalibo number Abir ya danna kira, nan take aka ce masa wayar a kashe take.. Bashow da ya gaji da ganin yadda Abokin nasa ya zama sai ya matso kusa da shi yana daure fuska ya ce "Zaiyan!" Kallon shi ya yi sai kuma ya kawar da kai yana jin idanuwansa sun cika da kwalla, hannu ya sa ya juyo da fuskarsa yana hura hanci ya ce "Yanzu Zaiyan ban kai matsayin da za ka faɗa min abin da yake damunka ba? Ko ka manta yadda muke tun muna yara? Ka sanar da ni duk abin da yake faruwa sai mu ga ta ina za mu ɓullo wa lamarin." Hawayen da yake riƙewa ne suka samu damar zubowa, Bashow ya rude ganin hawayen abokin nasa ya shiga tambayar shi, "Don Allah ka sanar da ni abin da yake damunka Zaiyan? Ba ka dauki ni yadda na dauke ka ba kenan? Ai damuwarka damuwata ce ka faɗa min me ke faruwa?" Ajiyar zuciya ya sauke yana jin yadda zuciyarsa ke masa zafi, bai taɓa sanin tsananin son da yake yi wa Abir har ya kai haka ba, Bashow ya takura sai ya sanar da shi hakan ya sa ya ɗago ya kalle shi yana goge hawaye ya ce "Bashow an sace matata." "What? " Ya faɗa yana zaro idanu sannan ya ɗaura, "Wai kana nufin har aure ka yi amma ba ka taɓa sanar da ni ba? Haba Zaiyan me ya sa ka boye min auren da ka yi? Kuma ma ina ka baro Mama ka dawo Kano da zama?" Ganin yadda ransa ya ɓaci Zaiyan ya ce "Bayan mun bar Kano na kamu da lalurar kwakwalwa." Saurin kallon shi ya yi ya ɗaga baki zai yi magana ya dakatar da shi, labarin komai ya sanar da shi har auren da kuma yadda suka dawo Kano. Kallon shi kawai Bashow ke yi yana sauraron wannan labari mai ban tausayi da takaici, nisawa ya yi ya ce "Yanzu haka ban san wani hali take ciki ba, ga shi ba ta da lafiya na bincika amma shuru." Dafashi ya yi cikin tausayawa ya ce "In sha Allah za a gan ta, amma sai nake ganin ya kamata ka kuma koma wa gidan da kuke zama ko sun samu wani labari akan hakan. Tabbas na san Princess Abir a Tiktok ga ta da saukin kai, idan ka yi mata comment sai ta ma reply Wallahi na yi mamaki da ka ce ita ce ka aura ɗiyar mashahurin mai kuɗin nan Alhaji Ibrahim Maitama, zan so na gan ta a fili saboda saukin kan ta. " Jinjina kai ya yi ya ce "Wallahi ni sam na manta da haka saboda duk na ɗimauce." Haka dai suka ci gaba da tattaunawa inda Zaiyan ya yanke shawara bayan kwana biyu za su je su gani... Bayan kwana biyun suka shirya shi da Bashow suka nufi gidan gaban Zaiyan na faduwa.. Tun da ta dawo ba ta ce musu ga abin da ya faru da ita ba sai kuka kawai take, zazzabi kuma ba ya barin jikinta ba ta iya komai sai kwanciya in ta farka ta dasa kuka tana kiran sunan Zaiyan kamar wata yarinyar goye. Wannan abu ba ƙaramin tsayar wa da Tasakkawato hankali ya yi ba, hakan ya sa ta dauke ta ta kaita wajan Limamin da ke kusan gidansu ta ce ya yi mata addu'a ko ta dawo haiyacinta, haka aka mata Addu'ar suka dawo cikin ikon Allah ta rage yin kukan sai dai ta yi tagumi tana kallon matan gidan. Sai da Tasakkawato ta lallaɓa ta tukun ta sanar da ita Big Boy ne ya kuma sace ta, ta sanar ita komai da ya faru. Salati ta dinga yi ta ce dole ne su kai ƙaran shi wajan 'yan sanda ayi musu tsakani, washe gari ta shirya ta dauke ta suka tafi office ɗin' yan sanda suka shigar da ƙara. Bayan sun gama shigar da ƙaran aka ce su faɗi gidan waye dan a kira shi ayi musu tsakani? Abir ta ce ba ta sunan shi na asali ba ko iyayensa amma dai ana ce masa Big boy, nan wani ɗan sanda ya riƙe baki ya ce tabbas ya san shi su tafi zai sa a kira shi su musu tsakani. Sai bayan sun tafi wannan ɗan sandan ya ce su jaga takardar da aka shigar ƙaran dan za su iya rasa aikin su saboda wannan kes ɗin, sanin waye mahaifin Big boy ya sa suka yaga takardar suka ci gaba da lamarin su.. Zazzaɓi dai yaƙi rabuwa da ita kullum tana kwance sai ƙara ramewa take, hakan ya sa takanas Tasakkawato ta leka gidan maƙociyarsu kasancewar ta likita ta ce ta zo ta duba Abir ɗin.. Bayan ta zo ta mata gwaje-gwaje ta gama, tambayoyi da dinga mata tana ba ta amsa sannan ta mata allura, bayan ta gama mata ta yi rubutu a takarda ta miƙa mata tana murmushi ta ce "Congratulations Allah ya raba lafiya." Baki sake Abir take kallon Doctor Tasakkawato ta rungume ta tana faɗin "Kai Alhamdu Lillah zan yi jika Jiddo ta samu juna biyu." Dak! Dak! Dak! Haka zuciyarta ke bugawa da sauri-sauri, sai ta rasa abin da za ta yi kawai ta fashe da kuka tana ƙanƙame Tasakkawato, shafa kanta take ta ƙara riƙe ta aka mata allura wanda hakan ya ƙara wa kukan ta mai. Suna cikin haka suka ji maganar mijin Tasakkawato yana kiran ta, sakin Abir ta yi ta fito tana shirin yin magana ta haɗa idanu da Zaiyan da ke bayan mijinta, waro idanu ta yi sai kuma ta yi dariya ta koma ɗakin da sauri ta kama hannun Abir da ta tsayar da kukan ta ce "Ke tashi mijinki ya dawo." Kafin ma ta taimaka mata ta tashi ta yi saurin mikewa ta yo waje kanta ko ɗankwali babu, tana fitowa da shi ta fara yin arba ya harɗe hannayensa a ƙirji yana sakar mata da ƙayataccan murmushi irin na masoyan da suka daɗe ba su ga juna ba. Da sauri ta isa gare shi ba ta ji kunyar kowa ba ta faɗa jikinsa tana sakin sabon kuka, shi ma ba kunya ya ƙara rungume abar shi yana shafa bayanta.. Sumar wucin gadi Bashow ya yi ganin Abir a zahiri, sosai ya shagala da kallon su. Murmushi ya kuma yi ya ɗago da ita daga jikinsa ya sa hannu ya shiga share mata hawayen yana faɗin "Yi hakuri Baby ba gani na dawo ba." Turo baki ta yi tana kallon gefen shi, da alamar tambaya ta dawo da kallon ta kan Zaiyan sai kuma ta ji ashe fa ba ta da ko ɗankwali, da sauri ta matsa za ta koma ɗaki Tasakkawato ta miƙo mata Hijabi, amsa ta yi ta saka tana sunkuyar da kai. Dariya Maman Amal ta yi ta ce "Ikon Allah sai yanzu kika ji kunyar mu Jiddo?" Rufe fuska ta yi tana komawa gefen Zaiyan ta tsaya, Tasakkawato ta ba su key ɗin ɗakinsu Zaiyan ya ce " Mama barka da rana." Murmushi ta yi ta ce "Kwan lahiyarka ɗan nan? Na shiga damuwa da ba ka zo ba har Jiddo ta dawo rashin lafiya ta rufe ta, yanzu dai ku zo muje daga ciki." Murmushi ya yi yana ƙara jin son Tasakkawato da ta zame musu uwa shi da matarsa, bin bayanta suka yi suka shige ciki, ruwa ta dauko musu suka sha. Takardar ta miƙa masa ta ce" Kalli ka ga. " Amsa ya yi yana duba takardar inda ya ga an sa Jiddonsa na dauke da ciki har na wata biyu cif, da sauri ɗago yana kallon su baki na rawa ya ce "M.. Ma.. Ma shin da gaske ne Jiddo tana dauke da cikina a jikinta?" Gyaɗa masa kai ta yi sai gani ta yi ya sauka daga kan kujera ya yi Sujjada yana faɗin "Alhamdu Lillah ya Allah." Bayan ya dawo ya kalli Abir ji yake kamar ya rungumi abar shi amma ba zai iya ba a gaban Tasakkwato, ganin kallon da suke wa juna Bashow ya miƙe ya ce yana zuwa, Tasakkawato ta cikin ɗakinta tana murmushi, ganin haka ya sa shi miƙar da ita suka fito hannayensu cikin na juna ya bude ɗakin suka shiga.. Janyo ta ya yi ya manna mata kiss a Kuma cikin wani kalar salo ya ce "Miss you Baby." Narke masa ta yi ya ja ta suka faɗa kan katifa, buɗe cikin ta ya yi ya ƙara kunne akai yana murmushi, ta ture shi tana faɗin "Ya za ka kwanta min a ruwan ciki?" Ta faɗa tana murguda masa baki. Dariya ya yi ya dawo gefen ta ya haɗa goshinsa na ta ta maƙale masa, lumshe idanu ya yi ya ce "Baby ya kamata mu koma Yola fa." Saurin tashi ta yi a jikinsa ya sa hannu ya dawo da ita, gyaran murya ya yi suna kallon juna cikin ido ya ce "Akwai abin da nake son yi a can, kuma na ga saƙon ƙanwarki tana cewa hankalin Family a tashe yake na rashin sanin inda kike, so ya kamata mu koma can zai fi dan ni kaina ina son sanin inda Mamana take." Hannunsa ta riƙe tana tuna familynta sai ta ji ta kwaɗaitu da son ganin su musamman Yayanta, nisawa ta yi sannan ta ce "Ni ma ina son naje gida." Kwanciya ta yi suka ci gaba da hira.. Tun da aka ce tana da ciki Zaiyan ke tattalin ta, da zarar ya fita zai yi ta kiran ta yana tambayarta me take so ta ci ya zo mata da shi? Idan 'yan rigimar suka zo sai ta samu wani abu mai wiyar samu ta ce shi take so, shi kuma haka zai yi ta nema da kyar ya samu ya kawo mata. Soyayya suke zubawa ta gaban kwatance idan ya dawo yana tare da matarsa ko hirar daren da suke yi da yanzu ya hana ta yana maƙale da abarsa suna shan soyayya, ita kuwa dama abin da take so kenan a ba ta kulawa ta musamman a dinga ririta ta, hakan ya ƙara narkar da zuciya a cikin kogin kaunar mijin nata... Sai da suka dauki sati sannan suka shirya suka ce za su koma inda suka fito, ranar Tasakkawato ta sha kuka da kyar suka rabu da juna ita da Abir, Abir ta ce mata ta dauki duk kayan amfanin ta da zarar ta samu lokaci za ta zo kuma za suke waya kullum, da haka dai suka tafi har kofar gida suka yo musu rakiya suna ɗaga musu hannu.... Gidan su Bashow suka je inda Maman Bashow ke ta nan-nan da Abir, Zaiyan ya sanar da ita ai Abir na da ciki, ta taya su murna tana murmushi ta ce "Ya kamata ka yi wa abokinka faɗa ko zai samu ya yi auren shi ma." Jinjina kai ya yi suka mata sallama suka fito, key ɗin mota Bashow ya ba shi suka shiga ta ɗaura niƙaf yana kallon ta da mamaki, murmushi kawai ta masa Bashow ya ɗaga musu hannu har suka bar harabar gidan... Sai bayan La'asar suka isa Yola Abir na ta sha bacci abin ta, gidan su Abir ya nufa har sai da ya kusa isa ya tashi ta ta gan ta kusan Unguwarsu, wasu zafafan hawaye suka zubo mata ta yi saurin gogewa. Hon ya yi Maigadi ya leƙo sai kuma ya koma ya bude musu get suka shigo. Da mamaki Maigadi ke kallon motar har Zaiyan ya fito cikin shigar ta shadda fara ƙal, saurin isowa Maigadi ya yi ya rusuna ya ce "A'a, ranka ya daɗe barka da zuwa saukar yaushe?" Da mamaki ya kalli Maigadi sai kuma ya basar ya yi murmushi ya ce "Lafiya lau mutanen gidan suna nan kuwa?" Jinjina masa kai ya yi tare da tabbatar masa duk suna nan, gefen da take ya je ya bude mata ta fito suka nufi part ɗinsu. Hayaniya ce ke tashi a palon Abir ta kalli Zaiyan sai suka ɗan tsaya, sautin muryar Abba suka ji yana faɗin, "Wallahi Baraka Kin cuce mu duniya da lahira, ban taɓa tunanin za ki iya aikata wannan mugun abin ba, yanzu sai ki faɗa mana inda ƴarmu take muje mu nemo ta, marainiyar Allah babu abin da ta tsare miki amma kika mata wannan cutarwar za ki ga sakamako.." Kasa jurar maganganunsu suka yi Abir ta cire niƙaf ɗin ta buɗe ƙofar palon bakinta dauke da sallama. Gabaɗaya ƙofar suka kallo, wani ihun murna Fatima ta yi ta nufi Abir tana faɗin "Abba ga Baby ta dawo." Murmushi mai haɗe da hawaye take ganin wai yau ita ce Fatima ta rungume tana murnar ganin ta, janyo hannunta ta yi ita kuwa sai kallon su take dan so take ta yi tozali da Abdul. Shi kuwa bai ma san ta shigo ba saboda eapis ya saka saboda faɗan da suke, kalaman Fatima ne na karshe ya sa shi saurin ɗagowa ai kuwa ya yi arba da ita, da wani irin sauri ya mike tsaye itama tana gano shi ta kwance hannunta ta nufe shi tare da sakin kuka, saurin taro ta ya yi ta faɗa jikinsa tana faɗin "Yayaaa." Maman Nusaiba ce [12/10, 11:36 Yamma] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): *A HAKA NAKE SON SHI* Shafi na 52 Kuka take sosai tana faɗin "Yaya ashe akwai ranar da za ka iya shafe babina a rayuwarka? Ashe akwai ranar da za ka furta min kalmar tsana? Don Allah Yaya ka gafarceni in na yi maka wani lefi, wanda har ya sa ka yanke min wannan mummunan hukuncin." Ɗago da ita ya yi yana share mata hawaye itama tana share masa, murya na rawa ya ce "Bab..Baby Wallahi babu abin da kika mini, hasalima ni ne zan nemi yafiyar abin da na aikata a gareki, ban san na aikata wannan abubuwan ba sai daga baya, ga muguwar da ta shiga tsakaninmu da ke nan azzaluma." Ya faɗa yana nuna mata Umma da ta yi baƙi wasu ƙuraje sun feso mata a jiki sai susa take tana kallon kowa na palon.. Ɗaya bayan ɗaya haka ta bi ta rungume su kowa na palon kuka yake, sai da ta zo kan Ammi sai ta tsaya tana kallon ta, tsoron isa gare ta take dan ba ta san ya za ta karɓe ta ba, gane hakan ya sa Ammi fashe wa da kuka ta miƙa wa Abir hannu tare da cewa "Zo nan 'yata Wallahi na yi nadamar abubuwan da nake miki, zo ki ji tsumin jikin mamanki." Isa ta yi suka rungume juna suna kuka gwanin ban tausayi.. Bayan komai ya lafa ne Abdul ya ɗago ya kalli Abir ya ce "Baby ina Zaiyan ɗin yake? Ko kin baro shi a gidan su Baba?" Saurin tashi ta yi tsaye dan sai yanzu ma ta tuna da shi, ganin ahalinta ya mantar da ita komai, da hannu ta nuna musu shi tana narke fuska ta nufe shi. Dukkan su baki suka saki suna kallon wanda ta nuna musu a matsayin Zaiyan ɗin, kowa gani yake kamar Suhal ne a tsaye. Grandma ta face majina ta ce "Ke Hauwa'u ba ma son shiririta fa, yanzu wannan ɗin ne Zaiyanu? Wannan ai Suhal ne mijin Iman dan kin dauke mu makafi sai ki nuna mana shi ki ce shi ne Zaiyanu?" Ƴar dariya Abir ta yi tana isa gare shi ta kamo hannunsa ba tare da ta ce matsa komai ba, amma da ido take masa alamar ya yi haƙuri, shi kuma ya yi shuru yana jin zafin rungumar ta da Abdul da Salim da suka yi. Zaunar da shi ta yi a gefen Abdul ta zauna a kusa da shi tana ƴar dariya, Abdul ya shafa kan Zaiyan ya ce "A'a, mutumin yau ba ko gaisuwa? Ko ka manta da Baba ne da ka masa dukan sakwara?" Ya faɗa yana tariyo dukan da ya ci a hannunsa. Sunkuyar da kai ya yi ya tuna da Abir ta sanar da shi Abdul ne yake kira da Baba, ɗago kai ya yi fuskarsa dauke da murmushi ya ce "Abba Dad sannun ku da gida, mun same ku lafiya? Kai kuma yanzu ai ba Babana ba ne sai dai na ce maka Yaya kamar yadda Baby ke kiran ka." Sumar zaune Abdul ya yi sauran 'yan palon suka dinga kallon shi, Ammi ta kasa daurewa ta ce "Uwar masu gida ko dai mijin naki ya fara samun sauki ne?" Kallon shi ta yi ta juyo da kallon ta ga Ammi ta ce "Ai ya jima da samu lafiya, yanzu yana cikin hankalinsa ras yake kamar kowa?" Ta faɗa cikin jin daɗi. Baki suka haɗa wajan faɗin "Kai ma sha Allah! Mun taya ki murna har shi ma Zaiyan ɗin." Bayan an gama murnar samun lafiyar Zaiyan, Abba ya yi gyaran murya ya kalli kowa na palo sannan ya ce "Mamana ga dama maganar ki ce ake yi sai ga ki Allah ya kawo ki." Ya tsagaita sannan ya ɗaura "Ita ce silar duk wani abu da ya faru da wannan ahalin, har mahaifiyarki ita ta sa mota ta bige ta karshe ta rasa rayuwarta, ta cutar da ke cuta mai yawa." Ya ƙarashe maganar yana goge hawayen da suka gangaro daga kwarmin idanuwansa. Kallon Umma kawai Abir ke yi tana girgiza kai sai ta fashe da kuka tare da cewa "Kin cutar da ni Umma dayawa ba zan taɓa yafe miki ba ko wani irin hali za ki shiga, ke ce silar zamana marainiya gaba da baya me na miki Umma? Kin kashe min Uwa kin kashe min uba duk dan Abie ɗina yaƙi amincewa da buƙatarki? Wallahi na yi Allah wadai da kasancewar ki ɗaya daga cikin ahalina. " Kuka ne ya ci ƙarfinta har da shiɗewa take, saboda yau ɗin nan an fama mata ciwon da ke daskare a cikin zuciyarta.. Hannu ya sa ya kwanto da ita jikinsa yana bubbuga mata baya tare yi mata magana a saitin kunnenta ta yadda ba me jin abin da yake faɗa. "My Wife please stop crying, kin Ga ba ki da cikakkiyar lafiya idan kina kukan nan zai haddasa miki ciwon kai, ƙarshe ki zo ki yi ta mai har ya kwantar da ke. Ba na son kukan nan kar Baby ya wahalar min da ke." Tsayar da kukan ta yi ta janye jikinta daga nashi, sai da ta dauki lokaci cikin shuru duk suka zuba mata idanu. "Na tsaneki daga ke har uwarki da ƴar'uwarta shi ya sa na sa aka kashe su, ke ma na so na aika ku daga ke har Abdul amma aka kasa yi min maganin ku, shi ya sa na bi wannan hanyar." Umma ce ke faɗa tana kallon Abir, sautin muryar Umma ya razana ta ta maƙale a jikin mijinta. Daddy ya nuna ta da hannu ya ce "Wallahi kin taɓe duniya da lahira Baraka." Ya kalli Abir sannan ya ɗaura da cewa "Mamana kin ba mu magana a dunƙule, ki warware mana zare da abawa dama tana da sa hannu a lamarin Yaya Ibrahim?" Dogon numfashi ta ja sannan ta ce "Duk abubuwan da na sanar da ku lokacin da na kuɓuta daga wajan wanda suka sace ni ƙarya na faɗa muku, hakan kuma ya samo asali ne sakamakon barazana da suke min da cewar idan har na nuna na san wani daga cikin su za su kashe kowa na familyn nan. To ni kuma tsoro ya shige ni shi ya sa na faɗi cewa wasu ne suka tare mu a hanya. " Tagumi Abba ya yi ya ce "Muna jin ki ki sanar da mu komai da ya faru, kar ki ji tsoron kowa a cikin wanda suka miki barazana." Jinjina kai ta yi sannan ta soma fadin "Ranar wata Sunday da safe naje zan gaishe da Abie sai na ji sautin muryarsa yana cewa, "Wallahi Baraka idan ba ki fita a harkata ba zan miki rashin mutumci, kuma yau ɗin nan ba gobe ba zan sanar da mijinki duk abin da kika min na rashin ɗa'a." Jin ya ambaci sunan Umma sai na yi ta mamaki, amma haka na ja ƙafa na shiga ɗakin na same shi tsaye yana safa da marwa, jin sautin murna Umma na yi ta cikin wayar tana cewa "Matuƙar ba ka amince da buƙatata ba za ka ga matakin da zan ɗauka a kan ka, kuma dole ma ka samar mana gidan da za muke haduwa muna kasancewa da juna, idan ba haka ba Billahil Azim zan nuna maka wace ce Baraka, na fi ka shu'umanci. Tun ina ƙarama nake dakon soyayyarka amma ka tashi ka je ka auro wata bare dangin matsiyata wadda asalinta ma ba a sani ba. " Tana fadin haka ta kashe kiran. Zama Abie ya yi cike da damuwa na iso na zauna kusa da shi, kallona ya yi na ce masa, "Abie wace ce wannan matar da take ce ma ka nema muku gida?" Gyara zama ya yi ya dube ni sannan ya ce "Mamana duk da ƙananan shekarunki amma kin san ba na ɓoye miki komai ko?" Na gyaɗa masa kai kamar wata ƙadangaruwa, ya ɗaura da cewa, "Wannan da kika ji a waya Baraka ce matar Daddynki." Waro idanu na yi na rufe baki sannan ya daura, "Ban san me ya shiga kan Baraka ba ta takura min, yanzu kamar ni za ta nema da aikin fasadi? Ko ba komai ai ni yanzu Yayan mijinta ne bai kamata take nema mu aikata saɓon Allah ba, wai ni yau take kallon tsabar idona ta ce tana so na muke keɓewa muna cin amanar ɗan'uwa dan ta mayar da ni ɗan iska." Ya faɗa yana huci. Sosai maganar Abie ta girgiza ni sai ga Mom ta shigo ta zauna a ɗayan gefen Abie ta ce "Ai Abban Abir ka ba wa iska ajiyarta kawai, yo hauka ake yi ba ta san nasan duk tsiyar da take shukawa ba." Kallon Mom na yi duk jikina ya yi La'asar gabaɗaya maganganunsu sun saka ni cikin kalar wani yanayi na jimami da al'ajabi, da kyar na iya cewa, "Mom dama Umma bayan cin mutumcin da take miki a gidan nan ashe akwai wani mugun abin da take aikatawa? Gaskiya Umma ta yi nisa ba ta jin kira." Cike da takaicin Umma Mom ta nisa ta ce "Zan sanar da ke wannan maganar saboda halin rayuwa, sannan kar ki kuskura ki sanar da kowa har sai lokacin faɗar maganar ya yi." Gyara zama na yi cike da zabuwa na baza na zomo ina kallon Mom. "Khairat da kike gani ba jinin wannan gida ba ce, ɗiyar wani bokanta ce wanda yake mata aiki akan duk abin da take son aikatawa." Saboda tsananin tashin hankali ban san lokacin da na miƙe tsaye dafe da ƙirji ba, baki na rawa na ce "Mo.. Mom da gaske kike Anty Khairat ba ɗiyar Daddy ba ce? To a ina shi uban nata yake? Amma dai Iman ɗiyar Daddy CE Ko? Don Allah kar ki ce min itama Iman ba jinin gidan nan ba ce." Na faɗa hawaye na ambaliya kan kumatuna. Kamo hannuna Abie ya yi ya zaunar yana bi na da kallo ya ce "Ai duk yadda kike tunanin Baraka da wuce haka ita da ɗan'uwanta Sadisu." Jinjina kai Mom ta yi ta ce "Tabbas haka ne ba ƴar gidan nan ba ce, ni da kaina na kama su dumu-dumu suna aikata zina ita da malaminta lokacin ba a fi wata biyar da auren su ba, sannan kuma daɗin-daɗawa Kabir ba shi da lafiya a lokacin, ni da Abie ɗin ki muka kai shi Asibiti lokacin yana cikin tsananin kewar ƴar'uwata. Dalilin kai shi Asibiti kuwa shi ne, hatsari ya yi na mota wanda har ya samu rauni a mararsa ba wani mai girma ba, hakan ya sa kawai aka sa masa magani sannan suka sanar da mu ba matsala in sha Allah, bayan sati sai abin ya zo da wani irin yanayi ko fitsari Kabir zai yi sai ya sha azaba. Ganin haka ya sa Abie ɗinki ya kira family Doctor ɗin su ya zo ya duba shi ƙarshe ya ce mana gaskiya sai an je asibiti ya masa gwaje-gwaje dan akwai abin da ya kasa ganewa, muka shirya muka tafi da shi aka masa komai washe gari muka koma amsar result, bayan mun je nan yake sanar da mu Kabir ba zai sake haihuwa ba a halin yanzu saboda jijiyar da ke haɗe da kwayoyin halittar haihuwarsa ta taɓo sosai, amma ya ce zai ɗaura shi akan magani na wata takwas idan har bai ji sauyi ba to sai dai ya tura shi ƙasar waje wajan wanda suka fi shi kwarewa. Hankalinmu a tashe muka dawo gida sai shi Kabir ɗin ne ma yake kwantar mana da hankali, na dauki waya zan kira Mama na sanar da ita abin da yake faruwa su dakatar da aura masa Baraka amma fir Kabir ya ce kar na faɗa musu halin da yake ciki hankalinsu zai tashi fiye da namu, da farko na ce masa sam sai na faɗi amma ya yi ta haɗa ni da girman Allah dole muka ja bakinmu muka yi shuru, shi kuma ya ci gaba da shan maganin da aka ɗaura shi dan lokacin saura sati biyu a ɗaura aurensu da Baraka. Tun da aka yi auren ba ya kwana a ɗakinta itama kuma ba ta damu da hakan ba, haka zai gudo part ɗinmu ya shiga ɗakin da yake nasa ne kafin ya yi aure ya kwanta, wani lokacin ma ba ma sanin ya zo har sai mun fito muna karyawa sai mu ka ya fito.. Auren su da wata uku ranar Baraka ta kama rashin lafiya muka nufi Asibiti da ita, gwajin farko aka sanar da mu cewa tana dauke da ciki na tsayin wata biyu da sati ɗaya, na girgiza sosai da jin wannan batu da farko sai na yi tunanin ko dai ya samu lafiya ne? Hankalina ya kasa kwanciya na ce ya rakani Asibiti dan kar ma yaƙi zuwa ban ce shi za a duba ba, shi kuma sai murna yake wai zai ƙara zama Daddy. Bayan mun je aka nuna masa waje aka ce ya kwanta, kallona ya yi ya ga ba wasa a fuskata sai ya nufi inda suka nuna masa, bayan an gama gwaji aka tabbatar min da har yanzu ba a samu wani solution ba game da rashin lafiya tasa, sai dai a bari ya gama shan maganin a gani. Ranar da muka dawo ya daina kwana a part ɗin mu ya koma nasu, ranar da zan yi mugun gani ta zo part ɗina ta ce min na yi mata ɗanwake tana so, sai na ce to na tashi na mata na aje ina jiran ta zo ta amsa amma shuru, hakan ya sa na tashi na nufi part ɗinsu ina ta kwaɗa sallama amma shuru.. Har zan juya na ji surutu a ɗakinta hakan ya sa na nufi ɗakin dan a lokacin Kabir ya fita aiki zuwa Abuja, ɓude ƙofar da zan yi na gan su haihuwar iyayensu ita da wani gardi na kwashe salati. Sun tsorata da ganina ta kama kukan ƙarya tana ce min na rufa mata asiri ba za ta sake ba, haushi ya sa na daka mata tsawa na ce ta sanar da ni gaskiya tun yaushe take cin amanar mijinta? Ta ce ai tun kafin ta yi aure suke aikata iskancin su, hakan ya sa naji tashin hankalin da nake ciki ya ƙaru na kuma ce mata ta faɗa min shi ne wanda ya mata cikin ko kuma na Kabir ne? A lokacin ta kuma sa kuka ta ce "Wallahi ba na Kabir ba ne nasa ne, tun da na shigo gidan nan ban taɓa haɗa shinfida da Kabir ba, dama can ni ba shi nake so ba mijinki shi nake so." Na dinga nanata Kalmar Inna lillahi wa inna laihin raji'un! Na mata faɗa sosai sannan na fita na bar su a ɗakin. Ko da na dawo ka rasa taya zan sanar da Kabir dan shi a lokacin ta gama shanye shi ba ya jin maganar kowa sai maganarta, ashe wai Malaminta ne da yake mata aikin akan duk wanda take son hawa kansa, na ji hakan ne bayan ta zo part ɗina ko kunya babu take cewa Kabir wai ita ya kaita England a can za ta haifa masa Baby, shi kuma sai murna yake na bi shi da kallon tausayi. To bayan ya tafi ne sai na shige ɗaki zan dauko wani abu ina fitowa naji wayar da take da shi, inda take sanar da shi wai aiki ya ci ban tona musu asiri ba kuma Kabir ya amshi cikin a matsayin nasa. Ban nuna naji komai ba... Da haka har ta haifi ƴarta mace wadda aka sa mata suna Khairat, yarinyar kana kallon ta sak ubanta ce kamar ya yi kaki ya tofar... Sai da aka daɗe da yaye Khairat a lokacin ne kuma ta Kabir ya samu lafiya, bayan wani lokaci aka haifi Iman. Iman tabbas ɗiyar Kabir ce dan har gwajin jini sai da na kai ta aka yi mata ita da Kabir, a lokacin in da za ki tuna mun je amsar maganinki. " Ta ƙarashe maganar tana jan dogon numfashi.. Kamar an yi ruwan ƙanƙara a jikina haka na dinga rawar sanyi, sai da Abie ya taɓa ni sannan na ɗan ji sauki na goge hawayen tausayin Khairat. Tun daga ranar da na kalle ta sai naji idanunwa sun cika taf da kwallar tausayinta ina tuna ranar da za ta san ko ita wace ce a gidan nan... " Kuka ne ya ci ƙarfinta ta faɗa jikin Zaiyan, Tun da aka fara labarin jikin kowa ya yi sanyi, Khairat kuwa kuka take bil'haƙƙi tana kallon Umma da ta yi tsuru-tsuru sai muzurai take babu alamar nadama a tattare da ita.. Sai da ya rarrashe ta sannan ta daina kukan ta kalle su ɗaura da cewa "Bayan sun ba ni labarin nan sai Abie ya dauko wani ɗan ƙaramin abu kamar memorie ya ba ni ya ce na adana shi kar na bari kowa ya san da shi, ya kuma tattara takardunsa na filaye da duk wata kadara tashi ya ba ni su ita kuma Mom ya ba ta wata takarda ya ce ta aje masa. Bayan mun gama karyawa ya ce na zo na raka shi gidan gonarsa ina murna na janyo Hijabi muka wuce.. Muna isa ya zazzagaya da ni inda ake kiwon kaji, har mun juya za mu dawo sai ga Umma ta shigo ita da Daddyn Aruf da abokansa Daddyn Hafsat da Jarmai da Manager Abie. Da mamaki ya kalle su ya ce "Yaya Ku ne a gidan gonar tawa ba ko sanar wa?" Dariya suka yi masa sai abin ya ba shi mamaki, Daddyn Aruf ya ce da Abie, "Kai Ibrahim miƙo mana wannan memorie." Murmushi ya yi ya ce "Ai Wallahi ko me za ku yi ba zan ba ku ba, ashe ku ne azzaluman da suke safarar 'yan mata ƙanana? Wallahi Yaya Sadisu ka ba ni matuƙar mamaki, ban taɓa tunanin zaman da kake a England safarar Mata kake yi ba,in sha Allah sai na kai wannan bayanin wajan babban kwamishinan 'yan sanda. Ke kuma marar kunya futsararriya fasiƙa ki fita idona na rufe, zan sanar da Kabir duk rashin darajar da kike min." Dariya duk suka saka Manager ya dawo gefen Abie ya ce"Ni ma bana goya bayan su kuma in sha Allah da ni za ka je kai wannan ɓannar da suke yi, Wallahi Alhaji Mustapha kun ba ni mamaki matuƙa." Ganin Manager ya dawo wajan Abie sai suka shiga ba wa Abie hakura shi kuma ya nuna sam ba zai ba su abin da suke so ba, haka suka fita suka bar wajan.. Sai da Yamma mun dauko hanyar dawowa muna cikin tafiya kawai sai ga wasu ƙarti sun tare mana hanya, a lokacin hanyar banki muka nufa saboda Abie zai kai kuɗinsa. Haka suka zagaye motarmu wasu suka fito da Abie wasu kuma suka fito da ni suka sa mu a cikin motocinsu tare da rufe mana idanuwa, muna ji ana ta tafiya da mu sai dare sosai muka ji an tsaya a wani waje, haka suka sauko mu suka dinga jan mu muna bin su idanu a rufe. Suna ɓude mana fuska nan muka yi arba da su Daddyn Aruf, zabura na yi na maƙale a jikin Abie na sa kuka Umma ta dauke ni da mari tana huci ta ce "Idan har ubanki yana son ki to ki ce masa ya yi mana abin da muke so." Kallon Abie na yi tare da ce masa, "Abie don Allah ka ba su kar su taɓa lafiyarka mu koma gida." Girgiza min kai ya yi ya ce "Sam ba zan yarda na ba su ba ki rabu da su." Jin haka ya sa suka dinga dukan mu har sai da muka daina motsi sannan suka rabu da mu, muna ɓude ido muka gan mu a wani ɗaki inda Umma ta ce Abie ya aminta da ita za ta yi wa Daddyn Aruf dabara ya sake mu, shi kuma ya ce ya gambace ya mutu da ya aikata zina, ni ma na ce da Abie da ya amince mata gara su kashe mu gabaɗaya... Ban san iya adadin Kwanakin da muka yi ba a wannan baƙin gida, da niya suke zuwa su sa yaransu su dinga dukan Abie ni kuma su kaini gaban masu shan shisha idan sun zuko hayaƙi su fesa mini a fuska, haka ciwona zai tashi na yi ta tari ina riƙe ƙirji sai sun ga na suma sannan su zuba min ruwa na farfado tukun su shaƙa min magani na dawo daidai.. Kullum haka ake mana suka yi ta gana mana azaba amma Abie ya ce ba zai ba su komai ba, ana haka wata rana suka yo copy takardun kadarorinsa suka ce sai ya sa hannu, ya ce ba zai sa ba Daddyn Hafsat ya fusata ya buga masa kai da bango kan fashe yana da jini, na kwashi kuka suka hana na yi haka na rufe bakina ina kallon Abie kwance kamar gawa. Washe gari suka dawo yana jin jiki ga sun hana mu abinci suka ce ya sa hannu ya ce ba zai sa ba ai dukiyarsa ce ba ta wani ba, akan me za su nemi kwace masa duniya? Sosai suka fusata sai suka hana ake bamu abici sai dai a zuba gishiri a cikin ruwa a ba mu mu sha. Ranar kwana na uku mun galabaita suka manta ba su rufe kofar ba Abie ya lallaɓa ya ga ba kowa duk sun sha giya bacci ya kwashe su, ya ce mu fita.. Ɗaya daga cikin su ya motsa ya tashi zaune har mun je baƙin kofar fita Abie na ganin haka ya yi saurin turani waje ya ce na yi maza na samu na bar wajan na boye, haka ina ji ina gani na tafi na bar Abie a cikin wannan yanayi na tsakanin mutuwa da rayuwa. Har na ɗan yi nisa naji muryoyinsu na shige gefen hanya jikin wata bishiya na rakube ina sauke numfashi na azaba, sai da naji sun koma na fito na ci gaba da tafiya da ɗan kuzarin da ya rage min sai jiri nake ji.. Ina tafiya ina kuka har na iso bakin hanya na kasa samun mota saboda lokacin ko tsuntsu ba ya motsi talatainin dare ne, na ci gaba da bin gefen hanyar ina tafiya har gari ya waje ban yi rabin isa kusa gari ba ma ballantana na ce na tsira, ina tafiya ina hango gari amma na kasa isa tun safe har rana ta take, wata Ruga na gani na isa ina haki na ce su taimaka min da ruwa, ganin yadda jikina yake sai suka ban ruwa suna yin baya-baya da ni suna ce min lafiya? Na ce musu sace ni aka yi shi ne na gudo, ruwan na sha kaɗan naji cikina ya ƙulle na isa inuwar da ke gidan nasu na zube anan ina mayar da numfashi. Mai gidan ya sa aka yo Kunu mai ɗumi suka tashe ni na sha shi ma ba me yawa ba saboda yunwa ta riga ga da ta dira min ciki, na kwanta suka sani a gaba suna min sannu har bacci ya kwashe ni na walaha, ban farka ba sai La'asar suka nuna min banɗaki da ƙyar na yi Sallah a zaune, bayan na gama na ce zan tafi na musu godiya suka ce na tsaya na samu lafiya za su kaini da kan su, amma na ce musu na gode dan ba na son su biyo ta kan gidan su same har na jaza musu, haka na juya na hau hanya lokacin da ɗan kuzarina na dinga tafiya dan na rasa motar da za ta dauke ni duk wanda na tsayar ba ya tsayawa. Sai da na shigo gari ina ta son tare mota kawai naji ana cewa "Ga ta can ku bi ta." Na kwasa a guje ban taɓa yin gudun da na yi ranar ba, na karyo wata kwana na shigo wata Unguwa na rasa ina zan nufa sai na bi wajan wata bola zan tsallama na faɗa wani kango dan na buya sai na kasa, suka tarar da ni a wajan saboda na taka wani danƙo. Da suka kaini wannan kango suka shaƙa min maganina ganin ciwona ya tashi saboda gudun da na yi, sun so su min faɗe sai Allah ya dube ni da idanun rahama ashe a lokacin Zaiyan yana nan a kwance cikin wannan kangon sautin kukana ya tashe shi a bacci, inda ya musu duka har suka sare shi a lokacin.." Ta ƙarashe maganar tana kallon Zaiyan da shi ma ita yake kallo.. Kowa ya yi tsit in ban da kukan Grandma da su Fatima babu abin da kake ji, har Abdul ya yunƙuro zai yi magana ta ɗaga masa hannu tare da cewa "Bayan na dawo gida Umma da Daddyn Aruf suke ta yi min barazana akan in na sanar da wani abin da na gani za su kashe Mom, haka zan sha kuka na gode Allah karshe ma video suke yi wa Abie suna azabtar da shi su turo min, shi kuma Abie zai yi ta cewa kar na kuskura na yarda dan na ga wannan vidéo da suke masa suna turo min na miƙa wuya na ba su abin da suke so, karshen da suka ga naki ba su abin da suka nema suka kashe Abie suka jifo gawarsa bakin hanya, wanda aka same su a tare da Zaiyan. Shi kan shi Zaiyan a lokacin su ne suka sace shi suka masa wani abin.. " Kuka ta fashe da shi ta kalli Umma ta ce "Yanzu sai ki zuba ruwa a ƙasa ki sha kun kashe min iyaye.." Babu abin da kake ji sai muryar Grandma da take jero wa Umma tsinuwa, Ammi ta miƙe tsaye ta isa gaban Umma ta zabga mata mari tana kuka ta ce "Wallahi kun yi asara a rayuwar ki, dama ke kika zugani nake tsangwamar Abir ashe da abin da kike aikatawa bayan haka? To ki jira Wallahi za ki ga ƙarshenki yadda zai kasance fasiƙa azzaluma." Daddy ya ce ya saki Umma saki ɗaiɗai har uku kuma bai yafe mata cin amanarsa da ta yi na kawo masa ƙato kan gadon aurensu na sunnah suka aikata zina, ihu Umma ta kurma ta yi kukan kura ta damko Abir ta kai mata duka a ruwan ciki. Wani kalar azababben ƙara Abir ta ƙwalla wanda har sai da jijiyoyin kanta suka fito ta ƙanƙame hannun Zaiyan, Abdul ya zo ya damƙi Umma ya kifa mata mari ya hankaɗa ta ta yo baya ta faɗi, kafin ta motsa ya yi saurin ciro ankwa ya goya hannunta ta baya ya ɗaura masa.. "Ki ka tona min asiri sai na kashe ki ɗiyar mayya." Umma ke faɗa Abdul ya tura ta waje ya saka ta a mota ya ce da Ali su kaita su kulle a ɗaki wanda ake tsananin horo sannan ya dawo ciki. Zaiyan duk ya rikice ya ɗago da ita sai yarfa hannu take tana faɗin "Waiyo Yaya zan mutu ciki, Waiyo Allah.." Kafin Ammi ta ɗago da ita sai ganin jini suka yi ya soma malalauwa daga jikinta, hankalinsu a mugun tashe Zaiyan ya amshe ta daga hannun Ammi ya fita da ita da gudu Abdul da Ammi suka biyo su baya. Mota duk suka shiga Abdul ya ja a guje suka nufi Asibiti........ _Maman Nusaiba ce_ [6/20, 8:43 PM] Ummu Amjad: *A HAKA NAKE SON SHI* Shafi na 53 Kafin su isa Asibiti sai da ta suma sau uku tana darfafaɗowa, hankalin Zaiyan ya yi mugun tashi ga jinin da yake zuba kamar an ƙara masa gudu. Suna isa Asibiti aka fito da gadon ɗaukan marassa lafiya a daura ta, amma Zaiyan ya ƙi su taɓa ta ya dauke ta da sauri suka nufi ciki norses ɗin na biye da shi har ɗakin emergency, ƙin fitowa ya yi suka yi ta fama amma ba ce ba fa zai fita ya bar matarsa ba, sai da Abdul ya shigo ya janyo shi yana ba shi baki tukun ya fito. Kasa zama ya yi sai safa da marwa yake yana jinjina kai, shi kansa Abdul ya bala'in shiga damuwa ganin ƙawar tasa kuma amanarsa a wannan yanayin, Ammi ta yi tagumi ta zuba wa ƙofar ɗakin idanu... Suna nan zaune sai ga su Fatima duk sun iso, Khairat kuwa har yanzu ba ta daina kuka ba sai jero wa Umma Allah ya isa take tana nanata kalmar ita ba ɗiyar gidan ba ce. Ko nan da can ba wanda ya motsa ya je duk sun zauna ba e ba a'a, sai da suka ɗauki kusan minti 45 sannan aka buɗe ƙofar, duk suka yi saurin tashi suna rige-rigen tambayar Doctor Hashim. Kallon su ya yi sai kuma ya dubi Abdul ya ce "Aboki ina mijin nata? Ko da yake shi ba zai ma gane ake nufi ba kai zo muje." Ya faɗa yana yin gaba sai ya ji an damƙo shi ta baya, da sauri ya juyo suka haɗa idanu da Zaiyan wanda idanuwansa suka yi jajur saboda tashin hankalin da yake ciki, sai da Doctor Hashim ya ji tsoro ganin yadda yake kallon shi ya dauka duka zai kai masa, amma ya ji ya sake masa riga ya nisa ya ce "Ni ne mijinta muje tare da Yaya Abdul sai ka mana bayanin, wa ma ya ce maka ba zan gane bayanin da za ka yi min ba?" Ya faɗa yana ɗaure fuska tare da hararar shi. Saurin yin gaba Doctor Hashim ya yi yana jin gabansa na faɗuwa yadda Zaiyan ɗin ke masa magana, su Ammi suka zauna a nan su kuma suka mara masa baya zuwa office ɗinsa. Bayan sun zauna ya gama rubuta komai ya ɗago ya dube su, a nutse ya fara faɗin "To Alhamdu Lillah mun yi nasarar ceto rayuwarta.." Saurin katse shi Zaiyan ya yi ya ce "Doctor cikin da ke jikinta fa?" Saurin kallon shi Abdul ya yi baki buɗe har zai yi magana sai kuma ya fasa, Hashim ya yi murmushi ya ce "Ka kwantar da hankalinka cikin yana nan bai fita ba, amma dai kaɗan ya rage ya salwanta saboda an daki cikin nata ne, dan kune ma ya sa na yi shuru ban sanar da 'yan sanda ba saboda na ga kuna da babban ɗan sanda a gida, yanzu dai nan da kwana uku za a iya sallamar ku, ga wannan ku amsa a sayo magani shi za a ba ta gobe da jibi dan ta warware. " Ya miƙa musu takardar Abdul ya amsa ya miƙa wa Zaiyan tare da ciro kuɗi ya ba shi, kallon kuɗin ya yi Abdul ya girgiza kai ya ce "Ka amsa ka sayo maganin." Miƙewa ya yi ba tare da ya amshi kuɗin ba ya juya ya wuce, har ya je bakin kofa ya juye ya ce "Ka yi hakuri ba sai na amshi kuɗinka ba, ina da kuɗi a jikina zan je na sayo da shi." Yana gama faɗin haka ya buɗe ƙofar ya fita. Da kallo suka bi shi sai da suka ji ya rufe ƙofar sannan Doctor Hashim ya yi gyaran murya ya ce "Wai wannan ba Zaiyan ba ne? Sannan kuma ba shi ba ne ka ce min an aura wa Baby?" Jinjina kai Abdul ya yi yana murmushi ya ce "Shi ne fa ai ya warke ras dan yau ma suka diro garin ɗazun nan." Murna ya taya su yana faɗin "Ikon Allah! Ga shi kuma har da tsarabar Baby ta zo muku da shi dan ma ku ƙara tabbatar da cewa ya samu lafiya." Hira suka ɗan taɓa sannan Abdul ya fito, a hanya suka haɗu da Zaiyan yana miƙa wa norse maganin da ya sayo yana tambayarta zai iya ganin matar tasa kuwa? Nan take sanar da shi za su iya shiga amma ban da hayaniya sosai. A tare suka wuce inda suka sanar da su Ammi ai ciki ne a jikin Abir Allah ya sa bai ɓare ba, sosai suka yi murna da jin wannan daddaɗan labarin suka shiga ɗaya bayan ɗaya suna duba ta, ita kuma tana kwance tana baccin wahala... Sai Yamma lis duk suka koma gida Ammi ta ce za ta tsaya ta kula da ita, amma Zaiyan ya ce kar su damu zai kula da ita su tafi da safe sai su zo, ganin ya nace sai Ammi ta hakura tana faɗin "Kai jama'a yaran zamani gabaɗaya ba ku kunya." Murmushi ya yi yana shafa kwantaccan sajansa wanda ya ƙara ƙawata fuskar, su kuma suka tafi amma Abdul duk ya kasa nutsuwa gani yake kamar da sun tafi za su kuma guduwa, ganin hakan ya sa Zaiyan yin wani kalar murmushi ya shige ɗakin... Misalin karfe 1:am na dare yana akan dadduma ya kai sujjada yana ta kwararo wa matarsa Addu'ar samun lafiya da addu'ar Allah ya haɗa shi da mamansa, sai da ya gama sannan ya shafa fatiha ya ɗago ya kallo gefen gadon da take kwance. Idanu ya zuba mata ganin tana ƙoƙarin farkawa, ya tashi da hanzari ya isa bakin ya hau ya ɗago da ita ya rungume tare da shafa bayanta yana jero mata sannu, a hankali ta buɗe idanuwanta ta gan ta a Asibiti nan abin da ya faru ya dawo mata tiryan-tiryan, hannu ta sa ta goge hawaye da suka zubo mata ta ɗago daga jikinsa suka zuba wa juna idanu.. Hannu ya kai ya goge mata hawayen yana girgiza mata kai ya ce "Baby ki yi shuru kin ji Allah ya ba ki lafiya, in sha Allah sai na bi miki haƙƙinki." Ya faɗa yana shafa gashinta mai santsi. Hannu ta ɗaura akan cikin ta sa masa kuka marar sauti ya yi saurin kwato da ita jikinsa yana rarrashin ta, da kyar ya shayo kanta ta daina kukan tana daga jikinsa ta ce "Nury yanzu shi kenan Umma ta yi sanadin zubewar cikina? Na kwallafa rai akan cikin nan me ya sa Umma ta tsane ni har haka?" "Babynmu yana nan maƙale a mararki bai fita ba, in sha Allah kuma sai kin haifa min shi mu ga girmansa." Saurin kallon shi ta yi ya jinjina mata kai alamar tabbatarwa, hamdala ta yi ta raba jikinta da nasa ta koma ta kwanta tare da masa nuni da ya kwanta, babu muso ya kwanta ya janyo ta jikinsa kamar wata uwa da ɗanta ta dinga shafa kansa tana faɗin "Ka yi bacci nasan duk ka gaji." Murmushi ya sakar mata ya ɗago ya manna mata kiss a kumatu sannan ya koma ya kwanta, ta jima tana kallon shi kafin bacci ya yi awon gaba da shi, ajiyar zuciya ta sauke tana bin shi da kallo har ya ɗan rame daga fuska.. Ɗan hasken ɗakin ne ya dauke ta yi shuru tana ƙara rungume Zaiyan, tuna matar nan sai ta kamu da tsananin farin ciki tana jiran ta bayyana. Bayan kamar minti biyar sai ga ta ta bayyana fuskarta dauke da murmushi tare da cewa "Assalam alaikum Hauwa'u." Itama murmushin ta yi ta ce "Wa alaikum salam Mama, sannu da zuwa." Matsowa ta yi kusa da gadon ta dubi Zaiyan ta ce "Alhamdu Lillah yarona ya warke, kuma abin daɗin ma ya kusa zama Baba." Sunkuyar da kai Abir ta yi tana wasa da yan yatsunta, sai da ta jima a haka sannan ta kalli Abir ta ce "Yau na zo na cika miki alkawarin da na ɗaukar miki tun farkon haduwar mu, yau za ki san waye Zaiyan, su waye iyayensa, duk zan sanar da ke." Cike da zaƙuwa Abir ta ce "Mama na jima ina jiran wannan ranar ki sanar da ni." Jinjina kai ta yi sannan ta ce "Dama na sanar da ke ni ba mutum ba ce kamar ke, wannan suffar da kike gani ina baiyanan miki da ita ta wadda ta raini Zaiyan ce." Saurin katse ta Abir ta yi ta ce "To Mama ina ita wadda ta raine shi take ? Kuma su waye asalin iyayensa?" "Duk za ki ji su ke dai ki nutsu da kyau." Jinjina kai Abir ta yi ita kuma ta ɗan yi shuru na sakanni sannan ta soma ba ya labarin. "Asabe ta kasance ƴar aiki ce a gidan wani attajirin mai kuɗi mai suna Alhaji Abdu matarsa kuma Hajiya Husna, tun Husna na amarya Asabe da mijinta wanda yake musu gadi suke zaune a wannan gida suna musu aiki, mijinta Maigadi ita kuma tana musu aikin gida da girki har Allah ya azurta Husna da samun ciki. Haka suka yi ta tattalinsa wannan cikin Alhaji Abdu yana ƙara shagwaɓa Husna duk abin da ta ce tana so shi zai yi mata. Alhaji Abdu ɗan kasuwa ne wanda yake zaune a J. R. A. Unguwar masu kuɗi a Kano, haka suke zaman su lafiya lau dan Husna ta ɗauki Asabe tamkar uwar da ta haife ta. Cikin Husna ya girma dan har ya shiga watan haihuwa Alhaji Abdu ya shirya musu komai na tafiya ƙasar waje ya ce a can za ta haihu, ana ya gobe za su tafi suka fiddo kayan tafiya aka aje a palo duk abin da za su buƙata sun fito da shi, nan kowa ya tafi ya kwanta.. Misalin karfe 2:30pm na dare Alhaji Abdu ya fito palo cikin sauri ya ɗaga wata ƙofa tare da duba agogon da ke tsintsiyar hannun sa ya ga dai lokaci daidai nuna masa biyu da rabi ce ta dare. ƙarar da ya ji ne ya sa shi saurin yin baya yana zaro idanu fuskarsa na nuna tsoron davke cikin zuciyarsa, cikin sanɗa ya koma ta ƙofar da ya fito. Bai tsaya yin komai ba ya nufi kan gadon tare da faɗin, "Husna! Husna!" A razane Husna ta buɗe idanuwanta jin yadda kiran ya karaɗe majiyarta, ƙaton cikin da ke jikinta ya kasa ba ta damar yin motsi mai kwari. Kamo hannunta ya yi cikin azama ya zaunar da ita yana kallon ƙofar shigowa, ita ɗin ma ƙofar take kallo kuma daidai lokacin jaririn da ke cikinta ya yi wani irin juyawa. "Inna lillahi! Maigida zan mutu." Ta yi maganar tana ciza lips ɗinta na ƙasa. Sakin ta ya yi ya kunna hasken ɗakin nan-da-nan haske ya gauraye ɗakin ya dawo kusa da ita tare da ɗago fuskar ta, Kama ta ya yi ya saukar da ita cikin rawar baki ya ce "Hu..Husna akwai matsala fa." "Wacce irin matsala Maigida?" Ta yi saurin tarar numfahinsa da tambaya. "Maza tashi 'yan fashi ne suka shigo mana gida ki bi ƙofar baya ki gudu, kuma komin runtsi ki daure ki tseratar da rayuwarki da abin da yake cikinki ni zan tsaya." Ya faɗa yana saka mata hijabi tare da damƙa mata wata ƙaramar akwati. Baki ta buɗe da niyar yin kuka ya yi saurin rufe mata bakin cikin azama tare da girgiza mata kai. "Kada ki ɗaga murya Husna ina son ki bar gidan nan yanzun nan, zan ba su duk abin da suke so, idan na rayu zan neme ki ga wayata da taki nan a cikin jakar nan karki damu muje." Ya faɗa tare da kama hannunta ya ja ta suka fito zuwa palo, hakan ya sa suka ji karar buga get ɗin gidan Husna ta yi saurin ƙanƙame mijinta sakamakon ciwon naƙudar da ya taso mata. Ganin haka ya sa ya dauke ta ya bi ta kitchen ya fitar da ita , saurin sakin ta ya yi murya a raunace ya ce "Don girman Allah Husna ki tafi da na rasaki gara ace nine na mutu, idan kuma kuɗi suke so zan ba su duk abin da na mallaka gabaɗaya indai ba za su cutar da mu ba." Fashe wa da kuka ta yi ta ƙara riƙe hannunsa ta ce "A a gaskiya ka zo mu gudu tare ba zan iya tafiya na barka ba, ko ka kira 'yan sanda." Ta yi maganar tana jan hannunsa. Shi kan shi sai yanzu wannan dabarar ta zo kansa, tashin hankalin da yake cikin ya mantar da shi duk wata dabara, dan haka ya ja hannunta suka zagayo ta ƙofar get inda suka tarar da maigadi kwance cikin jini. Tsoro da firgici ya sa Husna ja da baya ya yi saurin janyo ta ya riƙe ta gam, cikin sanɗa suak nufi fita daga gidan sai Aisha ta tsaya jikinta na rawa ta ce "Maigida Inna Asabe na nan fa tun da sun shiga ciki ka yi sauri ka taso ta mu gudu." A hanzarce ya nufi ɗakin maigadi inda ya samu Asabe ta maƙale a jikin gado, jin shigowa ya sa ta ɗauke numfashi cikin tashin hankali. Da sauri ya matso wajan gadon ya ce "Maza taso mu tafi Inna." Ya faɗa yana kallon ta da dan hasken fitilar da ke ɗakin.. Jin mai maganar yasa Asabe fitowa ta bi bayan shi suka fito, ganin mijinta cikin jini ya sa ta ɗaura hannu a ka za ta kurma ihu Husna ta yi saurin rufe mata baki "Karki kuskura ki yi kuka mai sauti za su ji mu su fito." Ba yadda ta iya ta hadiye kukan ta, tana kallon mijinta haka ta juya ta ƙaraso bakin ƙofar da nufin ta buɗe ƙofar suka ji an daka musu tsawa. "Kai Alhaji!" Hankali a tashe Alhaji ya yi saurin ɗamka hannun Husna a na Asabe ya ce "Maza ku fita kafin su iso." Ya faɗa tare ɗan tura su suka fita ya yi saurin juyowa ya danne ƙofar. Manyan garada su shida dauke da bindigu a hannayensu, dukkan su sun rufe fuskoki ba a ganin komai a fuskar sai iya idanu. Zagaye shi suka yi wani ya ɗaura wa Alhaji bindiga a ka ya ce "Kai ga ka mai wayo ko? Duk wayonka mun fika sanin kan tsiya Wallahi." Alhaji dai bai ce da su komai ba ya yi shuru yana muzurai, ɗaya daga cikin su ya ce "Ina matar taka take?" Sai a sannan Alhaji ya iya magantuwa, "Ai ta yi tafiya ne?" Ya faɗa yana sunkuyar da kansa ƙasa cikin rashin sanin mafita.. "Mu za ka raina wa hankali? Muje ka fito mana da duk abin da yake cikin gidan nan." Wanda ya ɗaura masa bindigar ya faɗa a fusace kamar zai kai masa duka. Jiki na rawa ya miƙe suka saka shi a gaba har cikin ɗakinsa da yake aje duk wani abu da yake da muhimmanci, su kuma da kan su suka shiga birkice ɗakin inda suka fito da jikar kuɗi rafar 'yan dubu-dubu. Yana gani suka kwashe komai sannan suka ɗauko wani takardu suka ce sai ya sa hannu a ciki, shi kuma bai musu muso ba ya sa hannu da duka takardun. Bayan ya sa hannu suka dage lalle sai ya taso matarsa ta fito, ya ce da su ba ta dawo ba daga wajan biki, dalilin haka yabsa wani ya bugi kafadarsa da gindin bindiga. "Ka fito da ita ko kuma mu da kan mu mu fito da ita." Wanda ya dake shi ya faɗa yana huci. Bai sake ce musu komai ba sai wani daga cikin ya zaburo tare da cewa, "Lokacin da muka nufo shi na ga kamar ya buɗe ƙofa, kai tabbas ita ya buɗe wa ƙofa ta gudu Oga." A tare suka ce tabbas haka ne nan take suka yi masa harbi uku ko shurawa bai yi ba ya mutu a wajan, su kuma suka kasu biyu. Mutane uku suka fita nemo su Husna, uku suka shiga bincike gidan suna ɗauke duk wani abu da suka san yana da daraja... Husna da Asabe suna gudu inda suka bar layin gidan jini ya soma zuba a jikin Husna, Asabe ta rasa yadda za ta yi da ganin wannan tashin hankali suka samu gefen hanya suka tsaya. Ba ka jin komai sai kukan karnuka da kwari Asabe ta cire ɗankwalinta ta ɗaura wa Husna a a ƙasan marar tana faɗin, "ɗaure hajiya mu ɗan ƙarasa barin unguwar kar su zo su same mu a nan." Runtse idanu Husna ta yi tana juya kanta saboda azabar ciwon da take ji, can kuma ciwon ya lafa suka ci gaba da tafiya inda Aisha ta daure ta yi ƙarfin hali ta soma gudun ceton rai jin ciwon ya lafa sosai.. Sun kusa fita daga Unguwar suka ji ƙarar tafiya ana bin bayan su, kafin su ankara har sun kusa cin musu sai sautin muryoyinsu suke ji suna faɗin, "Ga sawonsu nan ." Hankalin Asabe ya tashi a daidai lokacin ciwon naƙuda gadan-gadan ya zo wa Husna ta durkushe Asabe ta yi saurin shiga kafadarta tana mata sannu cikin rada, ta lallaɓa suka bi gefen hanya jikin wata bishiya suka tsaya a nan. Cikin abin da bai fi minti shabiyar ba Husna ta fara nishi sai jin kukan jariri Asabe ta yi, hankalinta ya kuma tashi ta cire wa Husna hijabin dake jikinta ta rasa ya za ta yi da jaririn da ba ta san me aka haifo ba. Daukan jariri ta yi ta lulluɓe da hijabin har uwar dan ba ta da abin da za ta yanke cibiya ta rungume hawayen tausayin kansu na bin kuncinta.. Cikin jini Husna ta ɗaure ta miƙe tsaye suka ci gaba da tafiya duk da jiri na ɗaukan ta amma Asabe ta riƙe hannunta ɗaya gam tare da haɗa ta da jikinta. 'Yan fashin dake bin su suka ci gaba da haska sawon su har suka zo wajan da ta haihu, hakan yasa suka kuma bin sawon wanda jinin dake zuba jikin Husna ne yasa suke ganin inda suka nufi. Cikin 'yan mintuna suka cin musu tare da zagaye su. Kuka suke suna roƙon su su rabu da su amma suka nuna sam ba su san hakan ba, Husna ta ce ita har abada ba za ta sake dawowa garin ba su bar su su tafi cikin duniya. Ɗaya daga cikin su ya ce "Ba za ki ɓata mana aiki ba yadda aka ce mu kashe ku gabaɗaya to sai mun kashe ku, musamman ma ke." Ya nuna ta. Kafin su yi wani yunkuri suka buga musu dinkin bindiga a tsakiyar kai take dukkan su suka zube, yayin da Asabe ke ƙanƙame da jajriri dake cikin hijabi a rade a haka ta musu. Waya suka kira ana ɗagawa ɗaya ya ce "Oga mun kamo su har mun aika su amma kuma matar nan ta haihu." Daga cikin wayar aka soma magana cikin tsawa da ba da umarni. "Kar ku yi min kuskure a aikin nan Indai abin da ta haifa da rai ku ɗauke shi ku kai cikin daji ku jefar, sannan ku ɗauko gawar matar tasa da ta maigadin ku kawo su gidan sai ku ƙarasa aikin." Yana gama faɗin haka suka ji an yanke kiran.. Ɗaukan Husna suka yi suka wuce, ita kuma Asabe suka taɓa suka ji ba ta motsi sai suka shiga duba gefen da suka dauke Husna ko za su ga jaririn amma ba su ga komai ba sai jakar da ta dauki, ganin ba su samu ba ɗaya daga cikin su ya ce "Kai yaron nan fa ya mutu sun jefar shi kawai mu wuce ita wannan mu bar ta a nan kawai." Sai da alfijir ya keto sannan Asabe ta farfado daga sumar da da yi, saurin bude jaririn ta yi ta ga kamar ya rasu hankali a tashe ta lallaɓa ta tashi ta jakar Husna ta dinga tafiya. Sai da gari ya waye tantawarai Asabe na tafiya ta rasa in za ta shiga da jaririn nan, can gaba ta hango Asibiti ai kuwa ta nufi Asibiti da sauri har tana haɗawa sa gudu.. Ko da ta isa miƙa musu jaririn ta yi suka amshe shi aka shiga da shi ɗakin taimako, sun jima sannan suka fito suka ce bukaci ta faɗa musu jaririn waye? Har za ta sanar da su abin da ya faru sai kawai ta ce " 'yata ce ta haife shi kuma ta rasu, to ba ni da kowa daga ni sai Yayanta shi ya zauna tare da ita ni kuma na garzayo na kawo muku jaririn ku duba min shi ko shi ma ya mutu." Kasa yarda suka yi da maganarta nurses ɗin sai faɗa mata suke ta sato jariri ne za ta ce musu jikanta ne? Ana Haka sai ga Doctor ya iso ya nemi jin ba'asin taron da suka yi suka sanar da shi ta sato ɗan mutane, kallon Asabe ya yi sai kuma ya ce duk su tafi suak wuce, ya kalli Asabe ya ja ta zuwa ɗakin da aka kwantar jaririn ya gan shi sun sa masa na'urar ƙarin numfashi. Sai da ya tambaye ta ina ta samo shi, ganin likitan na da nutsuwa ta sanar da shi abin da ya faru tana kuka, sosai hankalinsa ya yi mugun tashi ya ce zai sanar da 'yan sanda ta zauna ta kula jaririn. Godiya ta masa shi kuma ya tafi bakin aikinsa da nufin in ya gama zai shigar da rahoto, kwanan su biyar a Asibiti aka Sallame ta wannan Likita shi ya dauke ya ya kai shi gidansa y ci gaba da kula da shi, shi da kansa ya sa wa yaron suna Zaiyan saboda sunan da yake so in Allah ya ba su haihuwa su saka amma ba su samu ba kusan shekaru 10 da aure. Haka Zaiyan ya taso cikin kyakkyawar kulawa har ya kai shekaru shida suka saka shi a makaranta, Zaiyan ya taso yaro mai surutu ga shiga rai duk wanda ya zauna da shi to fa zai ji kamar ya yi ta zama da shi, haka ya dinga karatunsa cikin kwanciyar hankali. Shekarar Zaiyan 12 Doctor ya samu takardar ƙarin karatu, ya sanar da Asabe ta sa masa albarka ya ce zai saya musu gida su koma dan nasun ya musu girma, haka ta yi ta sa musu albarka suka sanar da Zaiyan tafiyar ya dinga rusa kuka sai ya bi su, da kyar aka rarrashe shi ya yi shuru matar Doctor na kuka ta saki hannun Zaiyan suka bar gidan. Doctor daret Unguwar Talakawa ya samu ya saya musu gida ɗan matsakaici, ya ba su kuɗi mai yawa sannan ya ce mata duk wani abu na karatun Zaiyan ya biya ya dage da karatu, yana kuka ya ce "Abba zan bi ka." Girgiza masa kai ya yi ya ce masa zai dawo tukun ya yarda ya tafi... Haka suka ce gaba da rayuwa yayinda Asabe ke boye wannan jaka ta Husna dan kar Zaiyan ya gani ya tambaye ta, shi kuma ya mayar da hankali yana ta karatu.. Shekara biyu da tafiyar Doctor amma ba su taɓa jin duriyar su ba, Asabe ta kira amma ba ta samun su saboda a kashe ma ake ce mata, haka ta zuba wa sarautar Allah idanu.. Zaiyan na gama karatu ya ce shi fa aikin ɗan sandan farin kaya yake so (C. V. N), Asabe ta goya masa baya har ya shiga aikin kuma aka dauke shi, haka yake kula da Asabe lokaci zuwa lokaci yakan ce mata wai ina babansa yake? Kuma ina dangin su? In ya faɗi haka sai ta ce masa ai babansa ya rasu tun kafin ya zo duniya, su kuma dangi ba su da shia gidan marayu suka taso ita da babansa, idan ta faɗa masa haka sai ya ji tausayi ya kama shi na uwar tasa ya ce mata in sha Allah zai tara kuɗi ya saya musu gida ya inganta rayuwarta.. Abin da yake damun Asabe yadda Zaiyan yake tambayarta wannan jakar meye a ciki? Sai ta ce masa kawai kayan tarihi ne sai ya yi shuru yans kaon jakar, hakan na tsoratar da ita dan ba so ya ga abin da yake ciki. Bai dauki lokaci ba yana aiki ya samu ƙarin matsayi, Asabe ta taya shi murna ta sa masa albarka, shi da kansa ya saka wa kansa suna Damisa a office ɗinsu da haka ake kiran shi... " Da sauri Abir ta kalle ta baki na rawa ta ce "Ma.. Mama k.. Kina nufin ki ce min Zaiyan shi ne Damisa?" Jinjina mata kai ta yi sannan ta ɗaura da cewa "Kwarai kuwa Zaiyan shi ne Damisa, ƙwarewarsa a wajan aiki ya sa wannan suna ya bi shi, sosai yake zaƙulo masu lefi in ba 'yan office ɗin su ba ba wanda ya san shi ne Damisa, saboda a gida da Zaiyan yake amsawa. Sannan shi masanin computer ne dan in ya shirya binciken mutum yakan iya yi masa hacking ɗin account na social media, har sim card yana rufe wa mutum shahararre ne a wannan fannin, hakan ya sa ko barayi za su binciko inda suke shi ake nema ya bi diddigin su har ya gano inda suke.. Lokacin da ya cika shekaru 25 aka canja masa wajan aiki zuwa Yola, haka suka haɗa kayansu suka dawo Yola da zama. Tun da ya dawo yake ta zaƙulo masu lefi har ya je kan wasu shu'uman mutane wato Alhaji Mustapha da Alhaji Sadisu, tun da suka gane yana son binciko gidan gonarsu da suke sato yara ƙanana su yi safarar su zuwa ƙasar waje hankalinsu ya tashi, ranar da ya gano komai ya kai bayanan office din Ogansu ya nufo gida.. A hanyar dawowarsa wata babbar mota ta bigi motarsa ta watsar da shi can, haka aka dauke shi aka kai shi Asibiti abokan aikin sa nufi suka gidan su dan sanar da Asabe suka tarar da mummunan labari, inda suka samu ta yanke jiki ta faɗi ko shurawa ba ta yi ta tafi kenan. Sai da Zaiyan ya yi kwana goma a Asibitin sannan ya farka amma me? Gabaɗaya ya manta komai na rayuwarsa hankalin abokan aikinsa ya tashi suka nufi gidansu da shi, ba kowa a gidan suka rasa wa za su bari wanda zai kula da shi, wani maƙocin su Zaiyan mai suna Malam Amadu shi ne ya ce su kawo shi gidansa zai kula da shi. Haka suka dinga kula da shi komai sai sun kowa ya masa, ya kai shekara a haka kamar ya samu sauki saboda ya iya magana komai ya iya kawai dai memorie ne bai dawo ba, abu kamar wasa ya soma fita yana yawo a Unguwa ashe abin ya ƙara ta'azzara ciwon hauka tuburan yake. Suka mayar da shi Asibiti amma an yi gwajin duniyar nan ba a ga komai ba a kwakwalwarsa, Malam Amadu da matarsa suka shiga damuwa haka suka ci gaba da riƙe shi, wani lokacin ma a kan bola yake kwana sai ya ga dama ko in yana jin yunwa ya shigo ya ce su ba shi abinci.. Karshe ma ya koma wani kango da kwana haka zai yi ta tare mutane a bakin hanya ya tsare su da surutu kuma ba dama ka motsa in bai ba ka izini ba, yana tsaka da ciwon ne Allah ya jefo masa ke cikin rayuwarsa.. " Kuka marar sauti Abir ke yi tana shafa kan Zaiyan, ta ɗago idanuwanta da suka yi jajur ta ce "Mama to yanzu ina wannan jakar ta mahaifyar Nury? Sannan su iyayen nasa da aka sa musu wutar mutuwa suka yi ko kuwa sun farfado kafin wutar ta kona su suka tsira?". "Wannan Jakar tana wajan Malam Amadu, kafin Asabe ta rasu shi ta ba wa ta ce ya ajiye mata kar Zaiyan ya gani, wannan kuma ba zan ce miki komai ba game da iyayesa, iya abin da zan iya sanar da ke shi ne, ke ce za ki sada Zaiyan da ahlinsa shi ɗin ɗan'uwan mijin kanwarki ne Iman, iyayensa suna nan a raye ki sada shi da su Hauwa'u. " Ta faɗa tana zubar da hawaye.. Baki buɗe Abir ke kallon ta sai kuma ta jinjina kai ta ce "Tabbas jini ba ƙarya ba ne Mama, dan tsananin kamar da suke ta ɓaci amma ban san ta ya zan musu bayani su fahimta yaron su." Dafa ta ta yi tare da cewa "Wannan Jakar ita ce babbar shedar da za ki nuna musu, duk da suna kama da makahaifinsa sosai amma dole sai da shedar nuna cewa shi ɗansu ne." Gyaɗa kai ta yi ta daga baki za ta yi magana ta ɗaga mata hannu dole ta gumtse maganar da take son faɗa, sauka ta yi ƙasa ta tsaya akan kafafuwanta tana kallon Zaiyan. Miƙa ya yi ya kai hannu yana laliban fuskar Abir sai kuma ya buɗe idanuwansa, da sauri ya diro daga kan gadon ba ki na rawa ya ce. "Ma... Ma yaushe kika zo da daren nan? Ashe zan sake ganin ki Mama?" Murmushi ta yi sannan ta ce "Ba ita ba ce." Saurin kallon ta ya yi ta jinjina masa kai, gyara tsayuwa ta yi ta sanar da shi komai da y faru bayan ya yi accident, hawaye suka dinga bin kuncinsa yana jin wani kalar zafi, ta wani gefen ya ji sanyi jin an ce iyayensa suna raye har ma Abir ta san ɗan'uwansa. Sai da suka jima a haka sannan ta ɓace daga ɗakin.. Rufe idanu ya yi yana ta tariyo irin yadda Inna Asabe ki ririta shi, iska ya fesar ya dawo kan gadon ya kwanta yana goge hawayen da suka zubo mishi, ganin haka ya sa ta janyo shi ta rungume tana masa nasiha... Bayan Kwana uku aka sallami Abir suka dawo gida inda Zaiyan ya tafi gidan su Baba, ya sha kuka sosai ya kuma gode musu da irin ɗawainiyar da suka yi da shi, amma bai ce musu Suhal ɗan'uwa ba ne dan shi har yanzu ya ma kasa yarda yana da iyaye bare ɗan'uwa. Jakar Baba ya ba shi inda ya ga wayoyi biyu da suke ciki ya buɗe ya ga akwai memory a ciki ya zare shi, ya sa a tasa wayar amma suka nuna basa yi sun lalace, ya ji takaici sosai ya zazzage duka kayan da yake ciki nan ya ga irin ƴar karamar walit ɗin nan ta maza, ɗauka ya yi buɗe ya ga irin ɗan ƙaramin photon nan da ake sakawa a jikin walit ɗin guda biyu na mace da na namiji. Sai a sannan ya ƙara tabbatar da cewa ba fa Inna Asabe ta haife shi ba, ya dauke photo ya adana ya mayar kayan ciki ya samu waje ya aje.. Bayan sati Iman da mijinta suka duro Nigeria, Zaiyan ya ƙagara ya ga wannan mai kama da shi ɗin da Abir ke cewa kamar tasu ta ɓaci. Abdul ya dauko su daga airport suka nufo gida, ɗakin baƙi aka kai Suhal ita kuma Iman ta yo part ɗin su Abir, sun sha kukan yaushe gamo sannan suka fito palo aka soam hira. Abdul da Salim suka shigo suka gaisa da Suhal sannan suka fita dan su ba shi waje ya ci abinci, ji ya yi a buɗe kofar an shigo, bai ɗago ba dan shi a tunaninsa Iman ce ta zo sai da ya ji sallama ya yi saurin ɗagowa dan ya ga, waye. Haɗa idanu suka yi da Zaiyan wanda ya sha wanka cikin shigar ƙanana kaya sai zuba ƙamshi yake, murmushi Zaiyan ya yi ya ce "Barka da zuwa abokina sai yau ka dawo daga London ɗin?" Dariya mai hade da mamaki Suhal ya yi sai kuma ya miƙa masa hannu suka gaisa, zama suka yi Suhal ya dube shi yana murmushi ya ce "Welcome back Damisa." Da sauri Zaiyan ya kalle shi baki na rawa ya ce... Maman Nusaiba ce*_ [12/14, 9:49 Yamma] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): *A HAKA NAKE SON SHI* Shafi na 54 "A ina kasan wannan sunan?" Ya faɗa cike da zallar mamaki tare da zama gefen hannunsa na hagu. Aje cup da ya dauko ya yi ya tashi ya iso kusa da shi, hannunsa ya kama ya ƙura masa na mujiya fuskarsa ɗauke da murmushi idanuwansa sun ciko taf da ƙwalla. Hannu ya kai ya shafa fuskar Zaiyan a yayin da hawayen suka samu damar gangarowa kan kuncinsa, shi kuwa Zaiyan cike da mamakin zubar hawayen nasa ya ɗan gyara zama ya ce "Aboki me ya sa kake kuka?" Kamar jira yake kawai ya rungume shi ya sa kuka mai sauti har da shashsheka, wannan abu ba ƙaramin tayar wa da Zaiyan hankali ya yi ba, yana bubbuga bayansa ya ce "Wai ko dai wani abin Iman ta ce na yi wa Baby ne? Don Allah ka sanar da ni me ya sa kake kuka?" Ɗago da kansa ya yi cikin wani kalar yanayi ya kamo hannunsa, sumbata ya yi jikinsa duk ya dauki rawa da kyar ya iya cewa "Alhamdu Lillah Allah na gode maka da ka nuna min wannan rana da na ga wannan baya naka, Allah na gode maka da ganin wannan rana." Shi dai baki sake yake kallon shi har ya gama maganar sannan ya gyara zama tare da goge hawaye, murmushi mai sauti ya yi ya ce "Tun ranar farko da na fara ganin ka naji a jikina kai ɗin jinina ne, hankalina kasa kwanciya ya yi har sai da na gan ka tare da princess, kai ɗin Yayana ne jinina uwa ɗaya uba ɗaya suka haifemu ni da kai, Yaya Zaiyan don Allah ka biyo ni mu tafi ka ga alhalinka. " Ya faɗa yana ƙara rungume shi... Tsabar mamaki Zaiyan ka sa motsawa ya yi sai bin shi yake da kallo, ɗago shi ya yi zai yi magana sai ga Abdul da Salim sun shigo Abir da Iman na take musu baya. Turus suka ja suka tsaya ganin su rungume da juna fuskakinsu na bayyanar da tsananin mamakin ganin su a haka, Abir da ta san komai murmushi ta yi ta nufo inda suke ta tsaya a kan su, haɗe fuska ta yi ta ce "Kai ɗaga min miji kar ka jinyata masa kafaɗa, ƙato da kai ka wani maƙale masa kamar Babyn goye." Ta faɗa tana zama a kusa da mininta. Baki Salim ya riƙe yana kallon Abir jin abin da take faɗa, kada kai ya yi ya ce "Lalle su Baby an zama futsararrun duniya, yanzu a gaban namu kike cewa mijinki?" Dariya ta yi tana rufe fuska ganin Abdul na kallon ta yana murmushi, sakin juna suka yi Suhal ya goge hawaye yana fante fuskarsa da murmushi, Iman ta zauna a kusa da shi tana kallon shi ta ce "Ya Suhal me ya sa ka yin kuka daga zuwan mu?" Girgiza mata kai ya yi bai ce da ita komai ba, Abdul ya samu waje shi da Salim suka zauna sannan ya ce "Suhal wai me ke faruwa ne muka gan ku kuna kuka?" Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Zaiyan Yayana ne shi." Saurin kallon shi suka yi Salim ya ce "To amma taya ya zama Yayanka? Shi fa ba ɗan Niger ba ne a Nigeria yake." "Tabbas ɗan uwanka ne Suhal, kuma in sha Allah za mu tafi dan na sada shi da iyayensa kamar yadda na yi wa Mama alƙawari zan cika in sha Allah." Abir ta faɗa tana murmushi. "Sai magana kuke a dunƙule, ki warware mana ta yadda za mu fahimce ku." Cewar Abdul. "Kamar yadda ka ji na faɗa shi ɗin Yayana ne ciki ɗaya muka fito, idan za ka tuna kwanakin baya da ka duba account ɗinka na Facebook da Instagram ba ka ga an yi ma hacking ba? Kuma da ka dawo ka kwato kayanka?" Jinjina kai Zaiyan ya yi tare da cewa "Kwarai kuwa dan da kyar ma na amso abuna." "To ni na kwance shi lokacin da ka kamu da rashin lafiya na ci gaba daga inda ka tsaya." Saurin kallon shi Zaiyan ya yi baki na rawa ya ce "Am.. Amma saboda me ka yi hakan?" "labarin yana da ɗan tsayi zan sanar da ku komai in kun shirya." Suka baza na zomo hakan ya ba shi damar ci gaba da magana. "A yadda Wazirin kakana ya sanar da ni ni ma zan sanar da ku dan ku tabbatar da Zaiyan ɗan'uwana ne. Babana asalin sunanshi shi ne Abdulwahid, shi ne ɗa na farko ga sarki Zaidu. Sarki Zaidu yana da mata biyu mahaifiyar Abdulwahid mai suna Sarauniya Zuwairiya ita ce ta farko, wadda ta kasance ita ba jinin Sarauta ba ce, hakan ya sa take fuskantar ƙalubale iri-iri a cikin masarautar. Tun da ta haifi Abdulwahid ba ta sake haihuwa ba sai abokiyar zamanta mai suna Fulani Abida ita ta dinga haihuwa, yaranta biyar hudu mata ɗaya namiji mai suna Haris wanda yake ɗa na biyu a wajan Fulani. Haka suka girma in da kullum cikin gori da faɗa wa Sauraniya bakaken maganganu take, duk abin da ake yi Saurniya Zuwairiya ba ta taɓa ce musu uffan ba dan har uwar mijinsu sai da suka kulla makirci ta tsane ta, babu mai son ta sai mijinta haka ta daure ta ci gaba da rayuwa.. Abdulwahid na zama cikakken Saurayi ya gama karatunsa wanda ya karkata kan kasuwanci, Sarki Zaidu bai so hakan ba dan shi abin da yake so Abdulwahid da ya gama karatu ya fito da mata ayi masa aure zuwa wani lokacin ya sauka ya ba shi kujerar, amma ba yadda ya iya haka ya rabu da shi ya bar shi ya soma kasuwanci. Sosai hakan ya yi wa fulani Abida daɗi dan ba ta so ace ya nuna yana son mulki, dan haka ta dinga zuga ɗanta Haris akan kar ya bari ace za a ba wa Abdulwahid Saurata, idan har aka ba shi shi kuma ya zama fanko. Hakan ya yi tasiri a zuciyarta Haris ya ƙulla gaba da Abdulwahid wanda bai ma san yana yi ba dan shi ta ksuwancinsa yake, kasashe daban-daban yake zuwa yana sayo kaya kama daga kan atamfofi kala-kala, kayan maza Jallabiya da ƙananan kaya, takalma kala-kala na maza da mata. In takaice muku dai babban campany ya buɗe in da ya zuba masu kula da komai, Sauraniya sai ta ji daɗi da ɗan nata bai ƙwallafa rai a kan wannan sarauta ba, hakan ya sa take ƙara ƙarfafa masa gwiwa wajan ganin kasuwanci sa ya haɓɓaka a ko'ina a faɗin Niger da ma kasashen da ke maƙotaka da su suvsan wannan campany na Abdulwahid.. Ganin ya zama cikakken matashin mai kuɗi sai abin ya hana Fulani Abida sukoni, ta dinga bin malamai da bokaye tana son a lalata wannan sana'a tasa ya daina samun customer, amma duk ina taje ba ta samun nasara sai su ce mata ai Abdulwahid na tare da tsari, sannan akwai wata Aljana da ke tare da shi tun da ya zo duniya take jikinsa ba ta bari a cutar da shi, idan kuwa mutum ya dage sai ya cutar da shi to fa takan yi fata-fata da mutum. Hankalin Fulani Abida ya tashi amma saboda sheɗan ya mata futsari a kai ba ta daina bin bokaye ba, har Allah ya ara mata rana ta aika Jakadiya can yankin Mali wajan wani ƙasurgumin boka, bayan ta masa bayani ya ce ai aljanar ya san ta zai saka ta a gwalba kuma aiki kamar an yi an gama ta faɗi me take so. Jakadiya ta ce a sa Abdulwahid ya bi duniya ya lalace kar ya sake waiwayar ahalinsa, ya ce an gama ta aje masa maƙudan kudade ta dawo wa da Fulani albishir mai daɗi, ranar sai da ta mata kyauta mai tsoka tace in aiki ya ci za ta ba ta sarƙar daham mai kimanin kuɗi naira miliyan biyar. Cikin dare Abdulwahid ya tashi ya haɗa kan kayansa kamar mai zuwa inda ya saba kasuwanci ya bi ta kofar da babu masu tsaro ya bar gidan, gari na wayewa aka nemi shi aka rasa aka yi ta neman sa amma ba a gan shi ba. Abu kamar wasa ya ɓata fat Sauraniya ta yi ta kuka ta ci gaba da addu'ar Allah ya bayyana mata yaronta, ita kuwa Fulani Abida dan murna ji ta yi kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha, haka aka shafe shekara ba ya nan karshe ma aka wayi gari companynsa ya ƙone ƙirmus babu abin da aka fitar, wannan abu ya ƙara tayar wa da Sarauniya hankali har ta kwanta ciwo karshe ya yi ajalinta. Gida ya dawo na Fulani Abida ta dinga zuba mulkinta son rai, karshe ma ta nemo wa Yarima Haris mata biyu ɗaya ɗiyar sarkin Maradi ce ɗaya kuma ɗiyar sarkin Dosso ce, aka yi biki aka kai su gidajensu. Rashin lafiya ta kama Mai martaba dole ya sauka ya ɗaura Haris akan karagar mulki, burin Fulani Abida ya cika ɗanta ya zama sarki sai abin da ta ce a tsartar a masarautar ake yi. Sarki na kwance sai an kwantar sai an tayar ba wanda yake kula da shi saboda gabaɗaya an sa kowa ya manta ma da shi, wazirinsa ne kaɗai ya garara mantawa da shi shi ke zuwa ɗakin da aka kai shi yake kula da komai, ganin haka ya sa Fulani ta sa Haris ya cire shi a matsayin Wazirinsa, shi kuma ya yi hamdala saboda dama ba ɗaukan shawararsa Haris ke yi ba... Haka rayuwata ta ci gaba da tafiya da daɗi ba daɗi, sai da Abdulwahid ya shafe shekaru goma sha biyu cif kwatsam wata rana sai ga Abdulwahid ya bayyana tare da matarsa. Bayan an zauna aka sha zuwa ganinsa kowa na murna ya dawo, bayan an tashi ya tambayi ina mamansa? Fulani da yake makira ce ta fashe da kuka ta ce ai ɓacewar shi ce ta sa ta kamu da ciwo karshe ta rasu, ya sha kuka sosai tukun ya gabatar musu da matarsa Husna.. Bayan ya dawo sai ga Mai marbata ya miƙe tsam akan ƙafafuwansa, sosai Abdulwahid ya ji daɗi matuƙa ya ci gaba da kula da shi, Fulani na bin su ta ƙarƙashin ƙasa har sai da ta tabbatar ta kulle bakin Sarki dan kar ya ce zai sauke ɗanta ya maye gurbinsa da Abdulwahid, shi kuma a lokacin ta babansa yake bai damu da wata sarauta ba, amma hakan bai gamsar da ita ba sai ta kira shi suka zauna da Sarki da shi, nan take sanar da shi ai tun da ya dawo kuma shi ne babba ya amshi mulki daga hannun ƙanensa. Hankalinsa ya tashi ya ce shi fa ba zai taɓa hawa kan kujerar mulki ba ya bar wa Haris girman ya ci gaba da mulki, hakan ya mata daɗi amma a fili ta ce masa me ya sa bai dauke ta a matsayin uwa ba har zai bijire wa umarninta? Haƙuri ya yi ta ba ta ƙarshe ta ce ta haƙura tukun suka tashi, haka ta dinga sa Husna a jiki tana bugun cikin akan rayuwar da suka yi, inda ita kuma a ganin ta ai ta zame musu uwa ta faɗa mata komai da ya faru da su, in da ta ce mata bayan an sa musu wuta hayaƙi ya rufe su, ita ta fara farfaɗowa daga suma ta nufi mijinta da yake kwance cikin jini yana numfashi sama-sama. Ƙarshe dai ya tashi suka samu suka fita ta ƙofar baya, in da suka yi tafiya mai nisa duk da suna cikin jigata, sun galabaita matuƙa gara ma ita akan Abdulwahid da fita jigata, suna zuwa tafiya a hankali ba su san inda kan su yake ba har suka faɗa gefen hanya suka nufi daji, suna zuwa saitin wata bishiya suka kasa tafiya nan suka zube zuwa lokacin ba su da ƙarfin da za su iya taka kafafuwansu... Sai da gari ya waye suka tashi in da suka gan su cikin wata Bukka ta Fulani, sosai Husna ta yi mamaki shi Abdulwahid sun sa masa magani a inda aka harbe shi sun daure wajan. Sai da suka yi sati sannan Husna ta warware shi kuma Abdulwahid bai ƙarasa warkewa ba ana ci gaba da masa magani, haka suka ci gaba da zama da fulanin nan da ke bayan gari har ya warke tas. Sai a lokacin ɗan Fulani ya zauna ya sanar da su cewar sun tafo su dayawa za su dawo gida daga cikin gari nan suka gan su jikin wata bisjiya, da farko sun ki ɗaukan su dan tsoro suka ji ko sun mutu sai daga baya suka duba suka ga baccin wahala ne suke, sai suka ɗauke su suka tafo da su Ruga suka yi musu magani. Godiya sosai su Husna suka yi musu inda Abdulwahid ya nemi da su musu alfarma su ci gaba da zama da su, suka ce ba matsala. Haka suke rayuwa a cikin Ruga har sai da suka yi shekara sannan hankalin Abdulwahid ya karkata kan gida, haka suka shirya suka bar Rugar in da suka dawo gari suka yo shigar Fulani Baffa ya kai su tasha suka shiga mota suka bar Nigeria. Bayan sun sha tafiya ta kwana hudu suka iso Niamey inda daret suka yo gidan Sarauta. Ko da Husna ta zo nan a labarin Fulani Abida ta sa kukan ƙarya tana cewa ai yanzu komai ya wuce. Kin ji ta yadda aka yi suka dawo Niamey. " Ya faɗa yana sauke numfashi tare da kallon Abir da ta yi tagumi. Jin sun yi shuru ya sai ya ci gaba da cewa "Rayuwa na tafiya in da Abdulwahid ya koma kan kasuwancinsa ya kuma samu albarka, mahaifinsa ya ba shi kudade masu yawa ya ce ya ja jari, wannan abu ya ƙona zuciyar Fulani sai ta sa a ƙara durkusar da shi amma sam abin ya garara, dan ko da Jakadiya ta je wajan bokan da ya mata magani ta tarar ya mutu har ya kumbura ya soma tsami, haka ta dawo hankali tashe ta sanar da Fulani. Tun da ta samu labarin mutuwar boka sai ta bi ta wata hanyar, da makirci irin nasu na mata da nuna tana son Abdulwahid da matarsa ta sa Mai martaba ya umarci Abdulwahid ya ƙaro mata biyu tun da shi ne babba a gidan, da farko bai Mai martaba bai amince ba haka ta dinga bi ta hanyoyi da dama har ta samu ta shayo kan shi, washegari ya kira Abdulwahid ya sanar da shi abin da yake so in da shi kuma bai yi muso ba ya yi biyayya ya auri ɗiyan abokan mahaifinsa. Bayan an yi auren ta ƙara samun dama tana jan kishiyoyin Husna a jiki duk dan ta kuntata mata, ita kuma ta nuna ba ta san tana yi ba. Ta samu labarin wani boka nan da nan ta tura Jakadiya ta amso mata magani dan a saka wa Husna ta ci ta kamu da ciwo wanda ba za ta mutu kai tsaye ba sai ta yi azabtuwa, ana kawo mata maganin ta shirya musu cin abinci a part ɗinta ta sa wannan magani a cikin abincin da ta ware wa Husna. Zumuɗin da take ya sa ta manta abincin da ta zuba wa magani shi ne ta ci, da dare ta dinga kurma ihu saboda mugun zafin da take ji a cikin naman jikinta. Tun daga lokacin duk wani sihiri da ta yi ya dinga karyewa, ƙarshe fatar jikinta ta yi baƙi da ta yi wajan mutane sai ayi ta gudu, abin ya tayar mata da hankali ta shiga neman magani amma duk in da ta je sai a ce ba za a iya magani ba ƙaiƙayi ne ya koma kan masheƙiya, ganin rayuwa ta juya mata baya ta dawo ta tona wa kanta asiri ta sanar da su komai. Sarki ya fusata sosai ya ce ya sake ta babu shi babu ita, ganin haka ya sa Haris ya ce shi ba zai iya mulki ba dama Fulani ce ta cusa masa son yin mulki ya bar wa ɗan'uwansa zai koma England ya ci gaba da karatunsa tare da matan sa. Haka ya haɗa kayansa ranar da zai tafi Fulani ta dinga kurma ihu tana sururutai tana cirar gashin kanta, hankali a tashe aka rufo ta a ɗaki kafin a kawo malami ta rasu. A lokacin kuma Husna ta samu ciki shi kuma Haris bayan an yi wata da mutuwar Fulani ya yi tafiyar sa, dole Abdulwahid ya amshi mulki.. Auren Abdulwahid da ɗiyan abokan Mai martaba wata hudu Husna ta yi ɓari, ta sha kuka sosai dan ta ƙwallafa rai akan cikin dama tana kukan rabuwa da jaririnta, ɓarin nan sai ya fama mata wannan ciwon da ke danƙare cikin zuciyarta. Daga nan ba ta sake samun ciki ba sai da Kilishi ta haifi ɗanta namiji aka sa masa Sultan, har sai da ya kai shekara biyu sannan itama Allah ya ba ta ciki ta haifi ɗanta namiji wato ni kenan, sai da na yi shekara goma da haihuwa sannan aka haifi ƙanwata Ikilima yayin da Kilishi ta sake haifo ɗanta namiji mai suna Arma. Zaman Mamma da su Kilishi kamar zaman Kakarmu ne da kishiyarta Fulani Abida, dan duk wani rashin mutumci in suka kwaso ita suke zubawa, sukan ce mata ɗiyar matsiyata da ko danginta ba a sani ba, wannan kalma na ƙona zuciyar Mamma haka take kauda kai ba dan ba ta da abin faɗa ba sai dan kawai ta nuna biyayyarta ga mijinta da ya ce kar ta kula su ko me za su ce a kanta. Kwatsam wata rana Mamma ta tashi da ciwon wuya aka kira likita ya duba ta ya ce babu matsala ya rubuta magani aka sayo mata, abu kamar wasa sautin muryar Mamma ya dauke tun ina ɗan yaro dan lokacin shekaruna 13 ne a duniya, haka ta kasance ta dawo kurma tana jin komai amma ita ba za ta iya bude baki ta yi magana ba. A daidai wannan lokacin ne kuma Mai martaba ya amsa kiran mahaccinmu ya rasu. Allah buwayi gagara misali yanzu haka Mamma ta samu lafiya tana magana kamar kowa, sannan ta kan ce mana za ta dawo Nigeria ta yi cigiyar danginta, wanda tun kafin ta samu lafiya ni na gano dangin nata." Ya fesar da iska daga bakinsa. Sauke tagumi Abir ta yi cike da al'ajabi ta ce "To Amma Ya Suhal taya aka yi ka gano dangin nata?" Murmushi ya yi ya ɗago ya kalli Zaiyan ya ce "Ta dalilin ɗan'uwana na gano su." Abdul ya haɗe hannayensa waje ɗaya ya ce. "Kamar yaya kenan?" "Ni yanzu abin da nake son sani a wajan ka shi ne, ya aka yi kasan cewa nine Damisa? Wanda in ba abokan aikina ba babu wanda ya san wannan sunan." Murmushi ya yi ya girgiza kai ya ce kun san ya aka yi na san kaine Damisa ?" Girgiza kai suka yi a tare, hakan ya ba shi damar ci gaba da cewa "Wata rana na zo Nigeria cikin garin nan kwatsam zan shiga wata Asibiti sai na ci karo da Zaiyan lokacin yana tsakar yin hauka, na yi ta kallon shi ganin yadda muke kama har ya iso kusa da ni ban sani ba sai ji na yi ya warci gorar ruwan da ke hannuna ya wuce fuu, da kallo na bi shi har ya tsallaka bakin hanya ya wuce. Tun daga ranar na kasa sukoni na tuna da labarin da Waziri ya ba ni na cewar su Mamma sun yi zama a Nigeria kuma har sun haifi yaro yanzu ba su san yana raye ko ya mutu ba, hakan ya sa naƙi komawa England wajan karatu na kuma dawowa Nigeria. Da zarar na zo bakin asibitin nan zan gan shi, wata rana na juyo zan dawo sai na haɗu da wata mata ta tsare ni ta ce "Bawan Allah ka taimaki ɗan'uwanka." Da mamaki na ɗago kai sai na nemi matar nan na rasa, hakan ya sa da na dawo masaukina na dinga tunanin taya zan taimaki wannan mahaukaci da nake gani? Da yake ina da abokai wanda muka yi karatu da su a England na sa suka nemo min Zaiyan a lokacin dan na kai shi Asibiti, muna zuwa ko taɓa shi ba ayi ba ya gudu daga asibitin aka neme shi aka rasa, na damu sosai haka na dinga bin diddigi ko zan samu labarinsa har Allah ya sa na haɗu da wani abokin aikinsa, inda ya sanar da ni tarihin rayuwarsa har sunan da ake kiransa da shi Damisa, ya kuma ce min yanzu ba shi da kowa a wani kango yake kwana.. Na kaɗu da jin labarinsa hakan ya sa na tattara na nufi Kano naje har office ɗin da ya yi aiki, da farko sun ɗauka shi ne sai da na sanar da su ba shi ba ne ɗan'uwansa ne, sun sha mamaki dan su a iya sanin su da Zaiyan ba su taɓa ji ko gani ya ce ga ɗan'uwansa, su suka haɗa ni da abokinsa Bashow.. " Waro idanu Zaiyan ya yi yana jinjina lamarin, Suhal ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ci gaba. "A wajan Bashow na ƙara samun duk wani abu na Zaiyan, har aikin da ya fara akan su Alhaji Mustapha in da shi Bashow ya yi ta ƙoƙarin ya ɗauko Zaiyan daga Yola ya dawo da shi Kano amma abin ya gagara, saboda da an yi niyar zuwa ɗaukan shi sai a neme shi a rasa gabaɗaya. Bayan na koma Niger na samu wata friend ɗina wadda ta dalilin ta ne na gano Zaiyan ɗan'uwana ne, na aminta da ita na sanar da ita abin da nake son yi dan itama ma'aikaciya ce kamar Zaiyan. Ita ta binciko min har da photon Inna Asabe ta samo, bayan na iso Nigeria daret Kano ma sauka dan na tattauna da friend dina Jk, har masaukin da nake ta zo muka zauna nan take sanar da ni ai tasan matar nan ƙawar mahaifiyarta ce a da tana aiki a gidan wani attajiri mai suna Alhaji Abdu, jin haka ya sa na tambaye ta sunan matar in da ta sanar da ni sunan ta Husna. A take naji jikina ya ƙara yin sanyi, na ce mata shi mahaukacin ɗanta ne? Ta ce da ni "A'a, ai Inna Asabe ba ta taɓa haihuwa ba wata rana ta zo gidanmu Mamana ke tambayar ta ya aka yi ta rayu bayan an ce gidan gabaɗaya ya ƙone kurmus? Sai ta sanar da ita duk abin ya faru da ita da yaron da ke wajan ta a lokacin Zaiyan ya girma, haka suka sha kuka Mamana ta nemi da ta rufe wannan sirrin kar ta kuskura ta sanar da kowa ta riƙe shi a zaman ita ta haife shi. To ba su san ba ina jin abin da suka faɗa hakan ya sa na ce zan bi ta na wuni a gidanta, da murna ta ce mu tafi. Bayan naje na ga Zaiyan zuciyata ta cika da tausayin shi. Ban taɓa sanin ya samun ciwon hauka ba sai yau, tun da suka bar garin ba mu sake ganin Inna Asabe ba har itama Mamana ta rasu." Ko da ta kawo nan a maganarta ta fashe da kuka, ni kaina jarumta na nuna ina mai ƙara jin tausayin Zaiyan, ƙarshe muka haɗa rukuni na sayi gida a Kano da kuma Yola na sa duk wasu matakan tsaro akan su Alhaji Mustapha, a nan ne na gano su suka sa wannan babbar motar ta kaɗe ka, to da suka samu labarin kana raye shi ne suka sa aka haukatar da kai ta yadda ba mai cewa sihiri aka yi ma.. Hakan ya sa na ci gaba da aikin da ka tsaya, duk zuwan da zan yi sai sun sa a kasheni amma ba sa sanin inda na sauka bare su cimma burinsu, wani zuwa da na yi ne na samu labarin an sace kanwar Jk na shiga bincike har na gano su Alhaji Mustapha ne ke sawa a sato musu 'yan mata a Jahohin Nigeria, Ƙarshe su fitar da su kasashen waje a mayar da su kasuwai, abin ya tayar da hankalin JK matuƙa na yi ta kwantar mata da hankali tare da mata alƙawarin nemo mata ƙanwarta, haka muka ci gaba da yin aiki a sirrince tare da amincewar Ogan su Zaiyan. Tun daga lokacin na daina ganin Zaiyan ko na zo Asibiti ba na samun shi, har sai da Allah ya haɗa ni da Princess muka ƙulla abokata daga ƙarshe na gabatar mata da soyayyata, ranar da na zo gidansu ta kira ni da suna Zaiyan abin sai ya ba ni mamaki, da na tuna ina neman mai wannan suna sai na matsa da sai kun nuna min shi. Ko da na shigo gaishe da su Mommy na kaɗu sosai da ganin ta sak mahaifiyata, hakan ya sa a sace nake kallon ta har na baro gidan, da kuka haɗa ni da Zaiyan na tabbatar shi ne sai naji sanyi da na ga ana kula da shi. Bayan na koma gida na samu Mai maibarta ina tambayarsa wai Mamma ba ta 'yan'uwa ne? Sai ya ce min tana da su hasali ma ita Mamma yan biyu ce akwai Hassanarta da kuma kanwarsu, nan ya sanar da ni Sunayen su. Sai na ce masa mai zai hana mu nemo "yan'uwan Mamma dan su san tana raye ba ta mutu ba, nan ya nuna min ɓacin ransa ya ce shi da Nigeria har abada ba ya ma so na sake yi masa maganar Nigeria ya dinga faɗa karshe ma ya ce kar na sake zuwa Nigeria in ba ta kama dole ba. Ganin haka sai na ba shi haƙuri na dawo na ci gaba da bincike har na tabbatar da Mommy ita ce Twins sister ɗin Mamma, sosai na yi farin ciki na kuma yi baƙin cikin mutuwar ƙanwarsu, dan na ƙara sa ido akan rayuwar Mom da su Abdul ya sa na turo musu Jk ta zauna a gidan duk wani abu da yake wakana tana sanar da ni, ita ta gano irin cutarwar da Umma ke yi wa Mom na ce ta sa ido a kan ta sosai, ko lokacin da ta kai sunana wajan malaminta akan a sa na fasa auren Princess na auri Khairat Jk ce ta lalata shirin, maganin da aka ba ta ta yi amfani da shi dan na ci abincin ta yi nasarar canja abicin da aka kawo min. Bayan na gama muka haɗu ta sanar da ni komai ta ba ni shawara da na fasa auren Princess na auri Iman na yi kamar asiri ya kamani amma na ce Iman nake so, haka ba dan na so ba na hakura da Princess dan na tseratar da ita daga cutar da za ayi mata na auri Iman, duk da haka ba ta bar Princess ba ta sa aka yi mata asirin da kowa ya tsane ta karshe kuma ta ce Zaiyan za ta aura ko an ƙi ko an so duk dan ta ga ta wulaƙanta, lokacin na yi tafiya wayar Jk ta samu matsala ba na samun wani labari game da gidan nan, sai bayan auren na san komai har guduwar da suka yi. Ƙarasa ba su labarin yadda suka sa aka karya sihirin ya yi, da yadda suka samu nasarar kwato ƙanwar Jk.." Saboda tsananin farin ciki Abir sai da ta yi sumar wucin gadi har sai da Zaiyan ya dan shafe ta sannan ta dawo haiyacinta, ta ɗaga baki za ta yi magana suka ji an yo sallama. Kowa kofar ya zuba wa ido in da suka hango Laraba tsaye ta sha ado cikin shigar doguwar rigar atamfa ta mayafi haɗi da jaka, saurin tashi Abir ta yi ta iso gaban ta baki na rawa ta ce "La..Laraba ke ce nake gani haka ko mai kama da ke ce?" Murmushi Laraba ta yi ta kamo hannun Abir suka iso ta zauna tana kallon Suhal, shi ma murmushi ya yi mata tare da cewa "Barka da zuwa Jk ƴar amana, yau dai mun kammala aikinmu." Ƴar dariya ta yi ta ce "Kuma fa haka ne, mai guri ya zo mai tabarma sai ya naɗe mun gaishe da Damisa." Ta faɗa tana kallon Zaiyan.. Abdul ya share hawayen da ya zubo masa ya dubi Abir ya ce "Baby ashe dai mu ma da rabon za mu ga dangin uwayenmu? Alhamdu Lillah dama ni tun da na haɗu da Zaiyan nake jin shi har raina ashe jinjina ne shi." Salim da ya yi shuru yana kallon su ya nisa ya ce "Wai dama Yarima Larabar ce Jk?" Gyada masa kai ya yi ya ce "Tabbas Laraba ita ce Jk wadda na turo gidan nan a matsayin ƴar aikin Mom." Gabaɗaya suka kamu da farin ciki matuƙa amma Zaiyan bai ce komai ba, sai da Abir ta taɓa shi ya ɗago ya kalle ta yana haɗe rai ya ce "Ni fa har yanzu ina kokwanto a maganar ka, amma bari na nuna ma photon nawa iyayen ka gani." Ya faɗa yana fito da photon da ya dauka a cikin walit ɗin da ya gani a jakar nan, nuna masa ya yi Abdul ya yi saurin amsa yana kallon photon ya ƙara tabbatar da cewa su ɗin yan'uwa ne, Suhal ya ce "Tabbas wannan su ne iyayena kuma kaima naka, idan kana son tabbatarwa za mu iya tafiya har Niger su da kan su za su yarda kai ɗansu ne." Haka suka ci gaba da tattaunawa sosai Abir ta kamu da murnar za ta ga Twins sister ɗin Mom, suna tashi Abdul ya kira su Abba ya sanar da su komai, sun yi farin cikin jin Hussainar Mom na raye kuma Suhal da Zaiyan yaranta ne.. Ko da Grandma ta samu labari ta sha kukan farin ciki dan ta san yadda Mom ke yawan maganar ƴar'uwarta, ranar Abir da Abdul da Zaiyan ba wanda ya runtsa saboda tsabar farin ciki... Kwanan su biyu suka tattara zuwa Niger in da jirgin su ya yi tashin safe karfe 7:30am. Ko da suka sauka Suhal ya yi wa Zaiyan rawani irin na buzaye ya rufe masa fuska yana ta murmushi yau zai yi wa iyayensa bazata, haka aka zo ɗaukan su suka nufi masarauta. Suna sauka a part ɗin Mamma suka yada zango in da Suhal ya bukaci Mai martaba da su Kilishi duk su zo part ɗin Mamma, sun sha mamakin wannan kira na Suhal haka dai suka tafo dan ba dama su ce ba su zo part Mamma ba.. Sai da kowa ya zauna Mamma ta fito daga ɗaki ta sha ado tana zuba murmushi ta nufo su, zabura Abir ta yi tana kallon Mamma sak Mom take gani tana nufo in da take, Abdul ya yi saurin riƙe hannunta tare da girgiza mata kai. Sai da Mamma ta zauna ta dube su ta ce "Sannun ku da zuwa." Salim ne kadai ya yi karfin halin amsa mata dan shi ma ya ruɗe, Suhal ya warware rawanin Zaiyan ya ce "Mamma da Papa shin kun san wannan fuskar?" A tare suka kalle shi idanu waje Mamma ta ƙura masa idanu, kasa daurewa ta yi ta ce "Subhanallah! Wannan bawan Allah ina kallon shi na ji ya shiga raina, Yarima a ina ka samo mai kama da kai?" Jakar ya janyo daga bayan Zaiyan ya aje a gaban su ya fito da wayoyin su har da photonsu, Mamma ta ruɗe sosai baki na rawa ta ce "A.. A. Ina ka samo wannan jakar da kuma photunan?" Bai ba ta masa ba sai photon Inna Asabe ya ciro a aljihunsa ya nuna musu ya ce "Nasan ke da Papa Kun san wannan matar." A tare suka amsa da "E.. E mun san ta." "To wannan da kuke gani shi ne ɗan da kuka haifa." Da wani irin saurin Mamma ta zabura sai ga ta gaban Zaiyan, kallon juna suka yi ta fashe da kuka tana rungume shi..... Maman Nusaiba ce [6/20, 8:43 PM] Ummu Amjad: *A HAKA NAKE SON SHI* Shafi na 55 Shafa bayansa take tana faɗin "Ashe da rabon zan sake saka ka a idanuna yarona? Idan mafarki nake don Allah ka da ku tayar da ni ina so na ci gaba da ganin sanyin idaniyata." Shi ma Zaiyan kukan yake yana ƙara ƙanƙame mahaifiyarsa cikin tsananin so da ƙauna, a hankali ya ɗago daga jikinta suka kalli juna ya juyo ya kalli Abir da take kuka wiwi, janyo ta ya yi ta matso kusa da shi ya damƙa hannunta a na Mamma yana murmushi mai haɗe da hawaye, Mamma ta kalli Abir gabanta ya faɗi ta rufe idanuwanta ta sake buɗe su a kan ta. Ajiyar zuciya ta sauke ta kai hannu ta taɓa fuskar Abir tana kallon Suhal ta ce "Yarima wannan kamar ita ce ka taɓa nuna min wadda za ka aura Allah bai yi ba?" Jinjina mata kai ya yi idanuwansa sun cika taf da hawaye ya gyara zama yana murmushi, Mamma idanuwanta akan Abir sosai ta ga kamannin Mom a fuskarta, Suhal ya kalli su Mai martaba ya ce "Papa wannan ita ce matar Zaiyan, ita ce wadda na so aura Allah bai nufa ba ashe ma za ta zama matar Yayana." Waro idanu Mamma da Mai martaba suka yi har da su Kilishi da suka zama 'yan kallo, Mai martaba ya kalli Zaiyan yana tariyo rayuwarsu ta baya, yadda suka ci burin zuwan shi duniya a lokacin, hannu ya miƙo wa Zaiyan shi kuma ya rarrafa kamar wani yaro ya iso gaban Mai martaba. Rungume shi ya yi yana jin ƙaunar yaron nasa na ratsa jikinsa, alama ya yi wa Abir da hannu ta zo, ta ƙaraso ya haɗa su ya rungume yana sanya musu albarka. Sai da suka gama kukan farin ciki Abir ta kasa daurewa ta matso gaban Mamma ta fashe kuka, hankalin Mamma ya tashi ta ruƙo ta tana tambayar ta ko wani abu aka yi mata? Jan majina ta yi tana shashshekar kuka ta juya ta janyo handbag ɗinta ta buɗe jikinta sai rawa yake, wani babban photo ta ɗauko ta miƙa wa Mamma. Da wani irin sauri Mamma ta kalli Abir baki na rawa ta ce "W. W. Wannan ai photon 'yan'uwana ne sa ni a ina kika same shi ƴar nan?" Faɗa wa ta yi jikinta cikin kuka ta ce "Mamma muma ɗiyanki ne ni da Yayana, ni ɗiyar Hassanarki ce yayana kuma ɗan kanwarki Hajara." Rasa me Mamma za ta yi a wannan lokacin ta yi, wai yau ɗiyan yan'uwanta ne a gaban ta tare da nata yaran? Ɗagowa Abir ta yi ta nuna Abdul tana murmushi ta ce "Ba mafarki kike ko gizo ba Mamma zahiri ne, mu ɗin jininki ne." Tsabar farin ciki Mamma sai furta Alhamdu Lillah kawai take tana shafa fuskar Abir ta dawo ta taɓa hannun Abdul da Zaiyan, sun dauki lokaci a haka sannan Mamma ta gyara zama ta ce "To amma me ya sa ba ku zo da su Hassanata ba? Ko dai suna baya a gaba za su zo, kai ma ina Inna Asabe take?" Sunkuyar da kai Abir ta yi tana kuka ta ce "Mamma sai haƙuri ƙanwarki ba a daɗe da yi muku wannan wutar ba ta rasu, ita kuma Mom ba ta fi shekara biyu da rasuwa ba, wannan gaisuwar da Suhal ya je to ita ce ta rasu har ita Inna Asaben duk sun riga mu gidan gaskiya." Tsabar kiɗimewa da Mamma ta yi sai gani suka yi ta yi baya ta zube a kan Mai martaba a sume, da sauri Ikilima ta tashi tana kuka ta ɗauko ruwa tana yayyafa mata tare da cewa "Mamma don Allah ki tashi ka da ke barmu, kin ga ke kadai kika rage musu a rayuwa." Ta durƙusa tana jijjiga ta. Numfashi ta ja tana buɗe idanu ta tashi da sauri za ta miƙe Mai martaba ya yi saurin janyo hannunta ta dawo ta zauna, shi kansa jarumta yake nunawa idanuwansa sun yi jajur sai kallon Zaiyan yake, ji yake kamar ya maida shi ciki. "Inna lillahi wa inna laihin raji'un! Hassanata da ƙanwata da Inna Asabe duk sun rasu? To yanzu ina mahaifiyata? Ko itama ta rasu?" Ta faɗa tana sauke ajiyar zuciya. "Bayan an haifi Yaya Abdul ta rasu." Sosai Mamma ta sha kuka har idanuwanta suka kumbura, ta so ace ta ga 'yan'uwanta da kuma Inna Asabe amma mutuwa ta musu yankan ƙauna , Kilishi ta girgiza da ganin Zaiyan a matsayin babban ɗa ga mijinta, ita kanta Sarauniya Bilkisu mamaki ya hana ta cewa komai sai bin shi take da kallo. Mamma ta tashi taje ta wanke fuska ta dawo ta kira Abdul da Abir suka zauna kowanne a gefe ɗaya, hannu ta sa ta zagaye su Abir ta yi murmushi tana jin wani sanyi na ratsa zuciyata ga ta ka twins sister ɗin Mom Kuma mahaifiyar mijinta, shi kansa Abdul wata nutsuwa yake ji gani yake kamar a jikin Mom yake. Abinci ta sa aka jera musu suka zauna aka fara ci, Kilishi ta kasa daurewa tana kallon Abir ta ce "Fulani ko dai mun samu ƙaruwa za ayi mana jika a gidan nan?" Saurin sunkuyar da kai Abir ta yi tana jin kamar ta nutse ƙasa dan kunyar su Mamma, murmushi Mamma ta yi tana aje cokalin da take cin abinci ta kalli Abir tare da cewa " 'Yata wai haka ne?" Girgiza kai ta yi tana yatsine fuska jin cikinta yana hautsina mata, da sauri ta miƙe ta wuce sai ta rasa ina za ta bi ga amai ya tafo. Tashi Mamma ta yi ta bi bayanta ta same ta tana tofar da yawu sai yunƙurin amai take, da hanzari Mamma ta kama hannunta ta nufi ɗakinta da ita ta kai ta toilet. Sai da ta amayar da abin da ta ci yau sannan ta samu sa'ida, wanke bakinta ta yi tana mayar da numfashi gabaɗaya jikinta ya dauki rawar sanyi ta lallaɓa ta fito. Mamma na jikin ƙofar tana jira ta fito ganin ta ta ƙanƙame jiki ya sa ta janyo ta ta kaita kan gado ta kwantar, jikinta ta taɓa ta ji zafi rau ta zauna a bakin gadon tana jero mata sannu. Sai da ta lullube ta ta wani lallausan bargo mu kauri sannan ta fito wajan cin abincin, Zaiyan duk ya kasa nutsuwa sai juya cokalin yake a cikin abincin.. Suhal ya yi murmushi ganin yadda ya yi kicin-kicin da fuska, dafa shi ya yi murya ƙasa-ƙasa ya ce "Yaya tashi ka bi matarka ba sai ka dinga mana cin magani ba." Hararar shi Zaiyan ya yi yana hura hanci, murmushi ya yi ya juyo ya ga itama Iman taƙi cin abincin sai kumbura baki take, gira ɗaya ya ɗage mata ya ce "Ke kuma fa? Me kike so?" Sunkuyar da kai ta yi ta ce "Ni zan je wajan Anty Baby." Da hannu ya mata alama da ta tashi ta je, da hanzari ta tashi sum-sum ta wuce har tana tuntuɓe.. Kallon su Mamma ta yi ta girgiza kai suka ci gaba da cin abinci har suka gama suka dawo palo, Mamma ta sa Suhal ya duba Abir ai kuwa Zaiyan ya ce bai isa ya gan masa mata ba sai dai su je tare, dariya duk suka yi Abdul ya ce "Iyye sannu masu kishi." Banza ya masa suka jera shi da Suhal suna tafi gwanin birge wa kamar 'yan biyu. Duba ta ya yi ya rubuta maganin da za a sayo sai Zaiyan ya ce masa ai akwai maganinta da take sha kullum, ya bukaci a kawo masa ya gani. Jakar Abir Iman ta ɗauko ta duba maganin ta miƙa masa, sai da ya dudduba su da kyau ya ga suna da kyau sannan aje ya, kamo hannun Iman ya yi yana dariya ya ce "Kin ga My Imani zo mu bar musu ɗakin mu tafi namu kar Yaya Zaiyan ya cinye ba ko gishiri." Dariya Iman ta yi suka wuce tare da rufo musu kofa.. Gadon ya hau ya yaye bargon ya zuba mata idanu, yadda take bacci numfashinta na fita a hankali sai ya ji ta birge shi, hannu ya kai ya shafo fuskarta ta soma motsi. Buɗe idanu ta yi tana kallon samar ɗakin sai ta ji mutum a gefen ta, juyowa ta yi suka haɗa idanu ta sakar masa murmushi, shi ma ya mayar mata da martanin murmushi cikin wani kalar yanayi ya ce "Baby sannu kin ji, yanzu ya kike jin jikin naki?" Yawu ta haɗiya saboda maƙoshinta ya bushe ta ce "Da sauki Nury." Janyo ya yi ya ja bargon ya rufe ta yana shafa kanta har bacci ya yi awon gaba da ita. Ya jima yana kallon ta sannan ya tashi ya fita ɗakin ya koma wajan su Mamma da suke ta hira Abdul na ba ta labarin family Maitama har abin da Umma da Daddyn Aruf suka yi wa 'yan'uwanta. Wani Sabon kukan Mamma take tana cewa ba za ta bar rayu kan 'yan'uwanta su tafi a banza ba, yadda Umma ta yi sanadin barin su lahira itama sai ta tsaya kai da fata an hukunta ta, Iman na bayan Suhal ta sunkuyar da kai sai zubar da hawayen baƙin halin Umma take. Washe gari Mai martaba ya sa aka zaga ko'ina da su Zaiyan ana nuna shi a matsayin babban ɗansa, sosai kowa ke mamaki sai kwasar gaisuwa ake duk in da ya yi sai a zube ana gaishe da su, suna gamawa Suhal ya sa aka shirya musu fita shan iska. Sosai suka ji daɗin garin Abir sai sambatun kyan rastaurant ɗin da suka je take wai sun iya abinci mai daɗi ta ci masa da miya.. Kilishi ta zubar da makaman yaƙinta ganin Mamma ta mata nisa, amma kuma tana tsoron shiga cikin su in ta tuna yadda ta musguna wa Mamma a baya, ita kuwa Sarauniya Bilkisu sabon shiri ta yi ta kasa samun kwanciyar hankali na bayyanar Zaiyan, ga shi ita ba ta taɓa haihuwa ba bare ta ce ta ƙarfi da yaji ɗanta zai gaji sarauta. Sai da suka yi sati sannan ne Abdul ya ce su fa za su koma Nigeria su shigar da ƙara kotu, Mamma ta ce ba za a bar ta ba dole ta je ta tsaya a bi mata haƙƙinta na sanadin mutuwar 'yan'uwanta. Mai martaba ya ce suje in an fara zama zai zo shi da su Suhal, Zaiyan ba dan ya so ba ya zauna dan shi cewa ya yi ya fi jin daɗin zamansa a Nigeria, sannan shi ma yana da kes da su Alhaji Mustapha amma Mai martaba ya ce ya bari Abdul zai shigar da ƙara su kuma za su biyo su daga baya. Haka Mamma da Ikilima da Abdul da Abir tare da Salim suka tafi Nigeria Zaiyan ya yi kamar ya ce a bar masa matarsa amma kunyar Mamma ta hana shi cewa komai, yana kallo jirginsu ya ɗaga zuwa Nigeria.. A Abuja aka sauke su daga nan wani jirgin ya ɗauko su ya kawo su Yola, Ali ne ya zo ɗaukan su a babbar mota. Hannun Abir sakale da na Mamma suka sauko daga cikin jirgin suna murmushi, Mamma ta lumshe idanu jin ta a ƙasar da ta taso, Ali da ya hango su daga naisa kwalalo idanu waje ya yi yana kallon Mamma gani yake kamar Mom ce ta yi fatalwa ta riƙe hannun Abir, har suka iso inda yake bai sani ba sai da Abdul ya girgiza shi sannan ya yi saurin ƙamewa yana sara mata tare da cewa "welcome back Sir." Ya sake kallon Mamma ya ce "Sir wai ni kadai ne nake ganin Mom na min gizo ko kuwa kuma kuna ganin ta?" Dariya Abir ta yi ta ruko hannun Mamma ta ce "Ba gizo ba ne kuma ba ita ba ce, ƴar'uwarta ce." Ajiyar zuciya ya sauke yana murmushi ya gaishe da ita ta amsa tukun ya buɗe musu suka shiga ya ja suka bar wajan.. Suna zuwa gida su Abba duk sun tsaya a harabar gidan suna jiran zuwan su, fitowa Ali ya yi ya buɗe musu kofa suka fito ita da Abir. Fatima ta waro idanu tana faɗin "Wow Abba Wallahi ba dan kun ce min Mom twins ce da za iya rantsewa wannan Mom ce." Murmushi kawai Abba ya yi yana yi wa Mamma barka da zuwa ta amsa cikin fara'a, kallon Daddy ta yi ta ce "Kabir kaine haka ka girma?" Ƴar dariya Daddy ya yi yana riƙe da hannun Khairat ya ce "Haba dai Usainar matar Yaya shekaru ai sun ja, ke kanki ai ba haka kike ba." Part ɗin su Abir suka nufa suka yada zango a nan, Grandma ta yi kuka na ganin Mamma saboda da tuna Mom. Sabon kuka aka yi Gradma na tambayar mijinta ta ce suna nan zuwa ai, sai da komai ya lafa sannan suka ci abinci aka dawo palo aka ci gaba da hira. Suna tsaka da hira sai ga Hafsat ta faɗo palon a firgice, kallon ta duk suka yi ta zube a gaban Abir ta fashe da kuka, Abir ta ɗago da ita tana faɗin "Friend lafiya kike kuwa? Me ya faru kika shigo haka a firgice?" "Don Allah Baby ki taimake ni ki rufa min asiri, Wallahi in na bar gidan Yaya Abdul mutuwa zan yi, ki ba shi haƙuri ya maida ni ɗakina ai ba ni na masa lefin ba, kuma ban taɓa sanin Daddy mutumin banza ba ne sai yau. Don Allah ki sa baki ya mayar da ni Wallahi ina son shi, ko ba dan ni ba ɗan cikinsa da ke jikina ya yi haƙuri ya zauna da ni na haife shi a gidan ubansa, nasan Daddy Mai lefi NE a gare ku amma ni ban yi muku komai ba Wallahi da zuciya ɗaya nake son ku daga ke har shi." Hafsat ke faɗa tana gunjin kuka gwanin ban tausayi.. Mamma ta kalli Abdul tana haɗe rai ta ce "Me ya sa ka yi wannan ɗanyan aikin Abdul? Ka sanar da iyayenka da za ka sake ta?" Sunkuyar da kai Abdul ya yi yana hararar Hafsat da take kallon shi tana kuka, sai da ta sake magana sannan ya ce "To Mamma ai na ga da mahaifinta aka kashe Abie da Mom, ni ban ga ba amfanin zamana da ita saboda wataran za ta iya cutar da ni, ni ko auren ta da na yi ban san yaushe na ce ita zan aura ba duk cikin tuggun babanta ne, ta wannan hanyar ya yi amfani na dinga yin abubuwan da sai da na tsani kaina bayan na dawo haiyacina, kin ga kuwa ai ba matar zama ba ce tun da ubanta ƙanen Fir'auna ne. " Dakuwa Mamma ta yi wa Abdul ta ce "Na ci gidanku Abdul, ka taɓa gani lefin wani ya shafi wani? Kai za ka ji daɗi idan Suhal ya sako Iman?" Daure fuska ya yi ya ce "Allah Mamma ba wani rashin jin daɗin da zan yi dan Suhal ya sako Iman ai uwarta ta ja mata." Faɗa sosai Mamma ta yi masa ta ce ya je ya dawo da matarsa tun kafin ta saba masa, ita ba ta da lefin komai babanta ne mai lefi dan haka kar ya ɗaura wannan lefi akan ta ba ta san hawa ba bare sauka. Sosai Hafsat ta ji daɗi matuƙa ta dinga yi wa Mamma godiya sai cewa take kamar kara aka tsaga ita Mom, murmushi Mamma ta yi ta lallaba Hafsat ta ce ta je gida Abdul zai je ya dawo da ita, cikin farin ciki ta tashi ta tafi.... Su Alhaji Mustapha suna tsaka da cin karansu ba babbaka ciwo ya rufe su su ukun duka, tsutsotsi ne ke fita daga duburarsu abin ya tayar musu da hankali suka garzaya asibiti. Likita ya ɗaura su akan magani ta nan ne ma abin ya zo musu da sauki, suka ci gaba da sharholiyarsu ta siyasa. A zaman watannin da Alhaji Mustapha ya yi a kan kujerar mulki ya saci kuɗi masu mugun yawa, duk abin da aka ba shi ya raba wa 'yan Jaharsa sai ya raba a kashi goma ya dauki kashi ɗaya ya ba su sauran kuma ya danne shi. Kwatsam sai ga shi yau an aiko musu tsammaci daga kotu Abba yana karansu akan kashe masa ɗan'uwa da suka yi, Abdul yana karansu akan kashe masa yayar mahaifiya da suka yi, Zaiyan yana karansu akan cutarwar da suka mishi har ya zama mahaukaci. Zufa ce ta dinga karyo musu duk sanyin AC da ke palon amma jikin su ya yi sharkaf, Hausawa na cewa marar gaskiya ko a ruwa gumi yake! Hankali a tashi Daddyn Aruf ya wuce gida yana susa duk jikinsu ƙaiƙayi yake musu... Yau su Zaiyan suka iso kuma yau ne zaman farko na kotu, suna sauka suka ɗan huta tukun suka ɗunguma su duka gidan suka tafi kotu. Suna isa kowa ya zauna sai ga su Alhaji Mustapha sun iso su da maƙarrabansu suka je in ake tsayawa duk suka tsaya sai wani cin magani suke. Jarmai ya ce "Kar ku kuskura ku ba da hanyar da za ta nuna duk abin da muka faɗa ƙarya muka yi." Ya faɗa ƙasa-ƙasar, ɗagowar da zai yi suka haɗa idanu da Mai martaba ya zaro idanu yana daddaɓa kafaɗar Daddyn Aruf ya ƙara Sunkuyar da kai ya ce "Kamar Alhaji Abdu nake gani da kayan sarauta." Kallon in da yake Daddyn Aruf ya yi ai kuwa ya gan shi, gabaɗaya tsoro ya kama su suka Sunkuyar da kai suna addu'ar Allah ya sa ba shi ba ne fatalwarsa ce.... Maman Nusaiba ce.... [12/22, 11:09 Yamma] Anty Sarat (Mom Nusy 🌹): *A HAKA NAKE SON SHI* END. Shafi na 56 Alƙali na isowa bayan ya zauna ya yi a rubuce-rubuce Magatakarda ya tashi tsaye ya soma bayani, "A yau ranar Talata ashirin ga watan Yuni Alhaji Sulaiman yake ƙaran ɗan'uwansa Alhaji Sadisu tare da abokansa Alhaji Mustapha Gwamnan mai ci a yanzu da kuma Jarmai, D. S. P Abdul Kabir shi ma yana ƙaran su a bisa zargin kashe masa yayar mahaifiya.." Haka dai ya gabatar duk ƙaran da aka shigar ya miƙa wa Alƙali takardar ya koma ya zauna. Alƙali ya yi rubuce-rubuce sannan ya ɗago yana gyara zaman glas ɗinsa ya ce "Ko lauyan mai ƙara yana kusa?" Miƙewa Barrister ya yi ya gyara zaman rigarsa ya tsaya da kyau sannan ya ce "Sunana Barrister Huzaifa Alaramma, ni ne lauyan wanda yake ƙara." Ya koma ya zauna. Jinjina kai Alƙali ya yi ya kuma cewa, "Ko Lauyan wanɗanda ake ƙara yana kusa?". Tashi ya yi tare da rusunawa ya ce "Sunana Barrister Shamsuddin ƙaribullah ni ne lauyan wanɗanda ake ƙara." Ya koma ya zauna. Alƙali ya ba da dama lauyan wanda ya yi ƙara ya fara tambayoyinsa, tashi Barrister Huzaifa ya yi ya isa gaban su Alhaji Mustapha yana murmushi ya dube su sannan ya ce "Shin ko za ku iya bayyana wa kotu sunanyenku?" Wani mugun takaici ne ya kama Dadyn Aruf ji yake kamar ya shaƙe Barrister Huzaifa, shi ya fara gabatar da kan shi sannan su Alhaji Mustapha. Gyara tsayuwa ya yi ya kalli Daddyn Aruf ya ce "Alhaji Sadisu shin ko za ka iya faɗa mana alaƙarka da Alhaji Ibrahim Maitama?" Yana wani ciccin magani ya fara magana, "Ibrahim ɗan'uwana ne shi da mahaifiyata da mahaifinsa uwa ɗaya uba ɗaya suke, kuma abokin kasuwanci na ne shi." Ya faɗa yana hura hanci. Girgiza kai Barrister ya yi ya ce "OK to amma me ya haɗa ka da shi har kuka sace shi daga ƙarshe kuka kashe shi." "Ubjection my lord! Ya kamata barrister ya daina ƙoƙarin rikita wanda yake tambaya." Cewar Barrister Shamsuddin. "Ƙorafi ya karbu Barrister ka gyara kalamanka." Ɗan rusunawa Barrister ya yi sannan ya kalli Alƙali ya ce "Ya mai girma mai shari'a ina son kotu ta ba ni dama na gabatar da shaida ta ta farko, ina son kotu ta kira min Baraka." Mai kira ya ƙara sanarwa in Baraka tana nan ta fito, aka buɗe ƙofar kotun sai ga Umma tare da 'yan sanda duk ta yi baƙi ta rame ga wasu kuraje da suka ɓata mata fatar jiki, ta iso ta tsaya a gefen su tana sunkuyar da kai ganin Iman na kallon ta. "Baraka muna so ki sanar da kotu gaskiyar abin da ya faru tsakanin ku da Alhaji Ibrahim har aka tsinci gawarsa.. Hawaye suka gangaro kan kuncinta ta jinjina kai tana jin damasa marar iyaka na shiga jikinta, a hankali ta buɗe baki murya na rawa ta ce "Na yi alƙawari zan sanar da kotu gaskiyar abin da ta tambaye ni in dai har na sani." Jinjina kai Barrister ya yi ya ce "Muna sauranron ki mana bayani yadda ku huɗun nan kuka ci amanar Alhaji Ibrahim." "Ubjection my lord! Ya kamata Barrister Huzaifa ya daina sa mata magana a baki."Cewar Barrister Shamsuddin.. "Ƙorafi bai karbu ba, Barrister za ka iya ci gaba da tambayarka. " Murmushi ya yi ya dubi Umma ya ce "Malama Baraka ki taimaka ki sanar da kotu gaskiya kar ki wahalar da shari'a." Jinjina kai ta yi ta ce "Yaya Ibrahim ɗan'uwana ne, tun da na taso na mallaki hankalin kaina nake tsananin son shi shi ya sa ko a makaranta ba ni da aiki sai maganar sa duk da bai san ma ina yi ba, kwatsam rana ɗaya naji labarin an sa bikinsa da wata ba ni ba, a lokacin ina ƙasar waje ina karatu duk na kasa zama ina jiran lokacin biki ya yi na zo na ga wadda ta yi min Kwacan masoyi. Duk da haka ban haƙura ba na samu ƙawata da maganar ta ce na bari za ta je wajan wani malamin ta zai yi aiki a kan wadda zai aura. Lokacin biki na zo na ga matar Yaya Ibrahim kyakkyawar gaske ga shi duk dangi son ta suke, abin ya ƙona min rai na dinga bin malamai dan a fasa auren amma ina sai da aka yi, bayan aure naje wajan wani boka na sa a juye mata mahaifa kar ta haihu har abada ta nan ne Yaya Ibrahim zai ji ba zai zauna da juya ba ya sake ta sai a aura masa ni, da farko kamar na yi nasara sai ga shi suna cika shekara da aure ta samu ciki na tashi hankalin ƙawata muka koma wajan boka na ce masa asa duk cikin da za ta samu ya dinga zubewa. Wannan karon aiki ya ci dan duk cikin da ta samu zubewa yake amma duk da haka Yaya Ibrahim bai ji ya daina son ta ba sai ma ƙara kulawa da ita yake, ganin da gaske na rasa shi sai na dawo kan Kabir wanda shi kuma yake auren ƙanwata. A lokacin ba na shiga harkar kowa dan sai ayi abu a cikin family ban sani ba, saboda na haɗu da ƙawaye masu aji kamar ni sai na watsar da kowa na riƙe ƙawayena ko Hajiyata ba ta kula danginta iya mahaifin su Ibrahim kawai take iya zuwa gidansa in ana wani abin, shi ma a sosai ba dan ko auren Yaya Kabir ta ce min ba ta je, hakan ya sa da na tambayi Yaya Kabir Hajiya ta ce min matarsa ko ƙawar matar Yaya Ibrahim ce ko kanwarta ce, saboda ban tsaya naji maganar Hajiya da kyau ba na katse wayata. Shi kuwa Yaya Kabir sai ce min ya yi ƙawarta ce ba ƙanwata ba, hakan ya sa na ƙara jin tsanar Sadiya tun da cusa wa Kabir ƙawarta. Haka zan zo na musu cin mutumci na zage su amma Sadiya da Hajara ba sa ramawa sai su barni na yi ta faɗa ni kadai, da Inna ta samu labari ta sa Yaya Kabir ya min iyaka da gidan hakan ya ƙara sa min tsanar su na tattara na koma England na ci gaba da karatu. Ina daga can nake sawa ayi min aiki a kan su har na ci nasarar kashe Hajara, ita kuma Sadiya a lokacin asirin da na mata ya karye ta ta haifi ɗiya mace, ban yi ƙasa a gwiwa ba na sa aka yi wa ƴar turan baƙaƙen aljanu ƙarshe aka sa mata cutar asma. Shi kan shi auren Yaya Kabir sai da haɗa da bin malamai tukun na shayo kansa ya yarda da aurena. Bayan auren na ci gaba da bibiyar Yaya Ibrahim ina neman shi da mu keɓe ba tare da mijina ya sani ba, ya min tas ya ci mutumcina abin ya ƙara fusata ni, naje gida muna hira da Yaya Sadisu sai yake ta faɗa yana cewa shi fa Yaya Ibrahim ya sa masa ido ba dama ya ɗauki wani abu sai ya tambayi dalili in da zai samu dama shi fa zai kawar da shi ma bakiɗaya ya amshe matsayinsa na MD ɗin companynsa na motoci. Bayan ya gama min bayani sai na ce masa me zai hana mu yi masa barazana mu ɗauke ƴarsa mu ce za mu kashe ta in bai yi abin da muka ce ba, hakan ya yi wa Yaya Sadisu daɗi ya tafi gidansa ni ma na tafi nawa, na dinga neman ta hanyar da za mu sace Abir duk in da na bi sai na ga hanyar ba mai ɓullewa ba ce sai na fasa, ana haka sai Yaya Sadisu ya ya je wajan wani boka ya masa aiki a kan Inna, washe gari ya je har cikin ɗakinta ya kanannaɗe ta da daɗin baki ya ce ta sa Yaya Ibrahim ya ba shi kuɗi masu yawa zai ƙulla kasuwanci da wani company a can England zai koma can da zama shi da matarsa, ya jeru mata ƙarairayi har sai da ta kira Yaya Ibrahim ta ba shi umarnin ya ba shi kuɗi masu kauri, duk da ba ya so haka ya ɗauko million 30 ya ba shi amma ya ce shi wannan ba zai ishe shi yin abin da yake so ba shi da zai yi kasuwanci da turawa, hakan ya sa Inna ta ƙara tursasa shi ya ƙara masa wata milion 20 ya haɗa ya yi hamsin.. Yana ta kasuwanci na a can England ashe sun haɗe baki da aminin Yaya Ibrahim suka nemo wasu matasa biyu da suke musu leƙen asiri a company Yaya Ibrahim, duk abin da yake wakana a company sai sun sani suna ta ƙoƙarin ganin sun durƙusar da cigaban da Yaya Ibrahim yake samu. Kwatsam wata rana suna tattaunawa a kan yadda za su amshi tayin wata ƙungiya da suke son a ke yo musu safarar ƙananan 'yan mata zuwa ƙasashe daban-daban, in da Yaya Sadisu ya ce zai sa a haɗa da Abir har ma mahaifiyarta in ta kama sai sun yi safarar ta ashe wani ɗan jarida na ɗaukan su, ba su ankare da shi ba har sai da suka gama magana za su fito Jarmai ya ga kamar gilmawar wani abu sai suka fito waje, ɗan jarida na ganin sun gan shi sai ya dinga gudu suka sa aka biyo shi amma sai ya samu ya tsere musu ya ɓuya. Wannan ɗan jarida ya yi ta zuwa Office ɗin Yaya Ibrahim amma masu tsoron wajan suka hana shi shiga, da kyar suka bari ya shiga yana ta musu magiya ya samu aka bar shi ya ga Yaya Ibrahim sai ya ba shi wannan ɗauka da ya yi ya kuma masa bayani cewar suna da gida a bayan gari wanda a gidan akwai gidan ƙasa a nan suke zuba yaran da suka sa aka dauko musu. Sosai Yaya Ibrahim ya girgiza da jin abin da ya faɗa ya masa godiya tare da yi masa kyauta mai tsoka ya adana wannan ɗauka, su Alhaji Mustapha suna neman wannan ɗan jarida amma sun kasa gane kamanninsa hakan ya sa suka tsorata kar ya je ya tona musu asiri, suna haka sai ɗaya daga cikin masu musu leƙen asiri a companyn Yaya Ibrahim ya faɗa musu ai ya zo ya ba da wannan ɗauka, nan da nan suka sa aka nemo shi aka kaishi wani ɗaki a gidan da suke kai mata ake gana masa azaba ƙarshe suka kashe shi. Ranar da muka ci nasara a kan Yaya Ibrahim shi ma da taimakon wani direbansa ya sanar da mu ya tafi gidan gonarsa in da ake kiwon kaji, a nan muka same shi.. Nan ta sanar da su duk abin da suka yi wa Abie har suka kashe shi tare da Maganer shi.." Ta ɗago fuskarta ta yi faca-faca da hawaye da majina ta ɗora da cewa "Su Alhaji Mustapha sun je har gida sun sharara wa su Yaya Sulaiman ƙaryar ana bin Yaya Ibrahim kuɗi har naira milion 50 aka ɗauka aka ba su. Suka kuma samun wata hanya da suke karɓar kuɗi daga hannun matasa 20 da ya buɗe wa shaguna a kasuwa na sayar da atamfofi, ya zuba musu kaya suke sayarwa ya ce musu shi iya uwar kuɗi yake so riba in sun samu su kula da rayuwarsu, sai suka zagaye suka ce ai shi ya ce riba ake raba ta gida uku su su ɗauki ɗaya su kawo kaso biyu, ba su musa ba dan a lokacin ganin Yaya Ibrahim wahala yake musu kuma sun san abokansa ne.. Yanzu haka maganar da nake muku sun tara yara sun fi talatin a wannan gida, wasu su suke lalata da su wasu kuma su fitar da su kasashen waje. Sai ku ji ana ta cewa an sace yara mata masu akasarin su su suke sace su duk suna nan a wajan su, wasu ma sun mutu saboda faɗen da suke musu su rasu, wasu kuma sun kai su ƙasar waje an juyar musu da tunani babu abin da suke sai yin zina da turawa suna biyan su maƙudan kuɗaɗe duk wata kuɗin yaran sai ya shigo account ɗin Yaya Sadisu daga ƙasar waje. Wannan yaron ma mai suna Damisa su suka sa mota ta kaɗe shi dan ya gano sirrin su, da suka ga bai mutu ba shi ne suka sa aka haukatar da shi, su yanzu haka ba su taɓa sanin kamannin Damisa ba duk abin da aka aiwatar ta ɓangaren Damisa ta hannuna ya biyo, na ga fuskar Damisa sau ɗaya shi ma sai da na sha wahala kafin na samu ganin shi lokacin an sallamo shi daga asibiti. Tun ganin farko da na yi wa Zaiyan lokacin da Abir ta kawo shi gidanmu na gane shi ne Damisa, amma kuma ganin a haukace yake sai na rabu da shi na ci gaba da harkokina, ko lokacin da suka ce Damisa ya yo musu saƙo na ce ba Damisa ba ne har yau a haukace yake amma suka ƙi yarda da maganata, ƙarshe ma nasa ita Abir ɗin ta aure shi suka bar garin.." Ta kalli barrister Huzaifa tana share hawaye ta ce "Wannan shi ne abin da ya faru wanda na sani ban rage ko ɗaya daga cikin abin da na sani da wanda na aikata da hannuna ba.." Ta fashe da kuka tana faɗin "Ina rokon Abir da ta yafe min lefin da na aikata a gare ta da duk wanda na zalinta." Kus-kus kowa yake da na kusa da shi suna tsine wa Umma, wasu kuma suna ƙara jinjina son zuciya irin na su Umma, Inna da su Abir suna ta kuka Inna sai faɗi take "Amma ku dai Allah ya tsine muku dau dubu, yanzu Baraka ke da Sadisu aka haɗa baki baki da ku aka kashe min yaro saboda wani kuɗi dauɗar duniya kuka kashe ɗan'uwanku da matarsa? Rashin imanin naku ya kai har kuke ɗauke ɗiyan al'umma kuna kaisu ayi zina da su a ba ku kuɗi? Kaicon ku da wannan bakar zuciya irin taku.." Rarrashin ta Mamma ke yi ita kan ta idanuwanta sun yi jajur saboda kuka, ta ƙara tabbatar da lalle mutanen nan ba su da imani gabaɗaya a rayuwarsu. Sai da aka lafa sannan Barrister ya matso kusa da Alhaji Mustapha ya ce "Kun ji abin da abokiyar aikinku ta faɗa? Gaskiya ne ko akwai in da ta faɗa ba daidai ba?" Alhaji Mustapha ya wani ɗaure fuska ya ce "Duk abin da ta faɗa ƙarya take abu biyu ne zan ce gaskiya, shi ne amsar kuɗi da muke a hannun matasan da ya taimakawa sai wanda muka je ya gida muka amsa bayan mutuwar sa." Jarmai da yake zubar da hawaye ya yi saurin cewa "Wallahi babu ƙarya a maganarta duk abin da ta faɗa mun aikata shi." Wani irin kallo Alhaji Mustapha ya masa shi kuma ya sunkuyar da kai, Barrister ya ce "Idan har ita ƙarya take shi ma Jarmai ɗin ƙarya yake?" Ganin fa ba sarki sai Allah ya sa suka amsa lefin su, Jarmai ya kalli Barrister ya ce "Kuma Alhaji Mustapha ne ya sa 'yan daba suka je gidan Alhaji Abdu suka banka musu wuta bayan sun ɗauke duk wata kadara tashi, sai ga shi ba su mutu ba da ran su." Ya faɗa yana nuna Mai martaba.. Kallon in da yake nunawa Barrister ya yi suka haɗa ido da Mai martaba, dawo da kallon shi kan Jarmai ya yi ya ce "To saboda me ya masa wannan aika-aikar?" "Saboda ya ga kasuwancinsa ya soma fin nasa bunƙasa, cikin ƙanƙanin lokaci Alhaji Abdu ya buɗe katafaren shago a kantin kwari, wannan abin ne ya ƙona masa rai hassada ta mamaye masa zuciya, shi ne cikin dare ya sa aka sa musu wuta babu abin da ya haɗa su kawai dan ya fi shi samu ne. " Barrister ya kalle shi irin kallon sannu mugu, nisawa ya yi ya ce "To dama shi Alhaji Mustapha a Kano yake? Ko kuwa yana daga nan Yola ne ya sa aka yo abin?" Goge hawaye Jarmai ya yi ya ce "Da ya zauna a Kano, dawowar abokinsa Alhaji Ibrahim Yola ne ya sa ya shi ma ya baro Kano amma asalin shi ɗan Fulanin Yola ne." Kotu ta buƙaci Mai martaba ya zo ana neman shi, dogarai suka zagaye shi ya tashi ya zo ya tsaya Alƙali ya dube shi ya ce "Abin da ya faɗa gaskiya ne.?". Jinjina kai ya yi tare da cewa "Da farko kirana ya yi yana barazana ya ce sai na saki matata ya aure ta in har ina son zaman lafiya, ni kuma na ce sam ba zan yi hakan ba shi ne sai yaji haushi ya kashe wayar, da dare suka sa mana wuta Allah ya sa na fitar da matata ita da aikin gidan Maigadi kuma suka kashe shi, amma sai da suka bi bayansu suka dawo da Matata. Nan ya ba su labarin yadda suka Kuɓuta suka yi jinya sannan suka koma ƙasarsu ya amshi mulkin gadon gidansu. Ya nisa tare da sakin murmushi ya ce "Shi Damisan da suke son kashewa ɗana ne ni na haife shi, shi ne jaririn da ana haihuwar shi suka ɗauko mahaifiyar suka dawo da ita suka sa mana wuta, ba su san cewa duk Zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana buzuru ana shaho sai ya yi." Jinjina kai Alƙali ya yi ya ce ya je ya zauna sannan ya koma mazauninsa, Alƙali ya yi Rubuce-rubuce ya sannan ya ce "Alhaji Mustapha da Alhaji Sadisu da Jarmai shin ko za ku iya sanar da mu dalilin da ya duk kuka aikata wannan ta'asar?" Alhaji Mustapha da jikinsu ya ɗauki ɓari sai yanzu shi da Daddyn Aruf suka san da cewar lalle fa ruwa ya ƙare wa ɗankada, Daddyn ya fashe da kuka ya ce "Wallahi babu abin da suka mana kawai ni baƙin ciki da hassada ce ganin Ibrahim ya zama mai kuɗin da duk Nigeria da ma Africa ta san da shi ta fannin kasuwanci, ni kuma ba wanda ya sanni duk abin da na taɓa sai na ga ba ya min albarka irin na Ibrahim." Suma sauran haka suka faɗa, Alƙali ya yi rubuce-rubuce ya ɗago tare da cewa "Sakamakon samun ƙwararan hujjoji masu laifi sun amsa laifin su kotu ta yanke wa Baraka hukuncin kisa ta hanyar jifa, ta aikata zina da auren a kanta, hakazalika kotu ta yanke wa su Alhaji Sadisu hukuncin kisa ta hanyar rataya, nan da sati ɗaya za ta aiwatar da hukuncin za su dawo da dukiyar marigayi Alhaji Ibrahim Abdullahi Maitama. " Ya buga guduma ya miƙe duk kowa ya mike. Masu kuka na yi ma su Allah wadai na yi har kowa ya fito waje. Suna kallo aka nufi cikin mota da su Alhaji Mustapha Inna na jero musu Allah ya isa tana goge hawaye da gefen zaninta, har za a saka su sai ga 'yan jarida sun yo ca a kan su sai tambayar su ake amma suka ƙi cewa komai aka tura su cikin mota suka bar filin. Suma su Inna gida suka tafi kowa jiki a sanyaye Iman da Khairat sun yi kuka kamar ran su zai fita, sosai suke kokawa da halin mahaifiyarsu... Bayan sun je gida aka zauna ana ta maida yanda aka yi ranar ba wanda ya iya cin abincin dare, washe gari Hajiyar su Umma ta zo tana kuka ta dinga ba wa su Abba haƙuri tana neman gafarar su ta ce ba ta san duk abin da suke shukawa ba, Abba ya ce sun yafe mata ba komai sai ta nemi a ba ta Khairat da Iman su tafi gidanta in za su koma sai ta dawo da Iman ita kuma Khairat ta zauna a wajan ta. Ai kuwa Iman ta yi tsalle ta dire ta ce ba ta zuwa ita tana gidansu cikin yan'uwanta, itama Khairat ta ce ba in da za ta je tana wajan Inna, dole ta haƙura ta tafi tana kukan nadamar abubuwan da ɗiyanta suka aikata. Bayan kwana biyar da gama shari'a aka ɗauki 'yan sanda aka tafi tare da su Alhaji Mustapha zuwa gidan da suke aje yara mata ƙanana, sun isa aka dinga bi lungu-lungu ana fito da su har da masu ciki, aka ɗura su a mota sannan 'yan sanda suka banka wa gidan wuta ya ƙone ƙurmus, sai da suka tabbatar komai na gidan ya ƙone sannan suka zagaye wajen da wata irin waya sannan suka tafi.. Sai da aka gama zartar da hukunci sannan su Mamma suka soma shirin tafiya Niger, a lokacin Hafsat ta ji labarin za su tafi a wajan Abir hankalinta ya tashi ta tafo gidan ta samu Mamma tana kuka ta ce ta ƙara ba wa Abdul haƙuri ya dawo da ita ɗakinta, Mamma ta ji Hafsat ta ba ta tausayi ta kwantar mata da hankali tukun ta tafi. Ta Kira Abdul ta mi shi nasiha mai ratsa jiki tukun ya ce ya dawo da ita su je su kawo ta. Da yamma ta je ita da Ammi da su Abir suka dawo da ita, ranar Hafsat ta sha kukan farin ciki da Abdul ya ce mata zai zauna da ita har karshen rayuwarsa yana son ta. Washe gari suka haɗa komai nasu na tafiya sai a lokacin Khairat ta fashe musu da kuka tana sambatu dama ana canja uwa da ta canja Umma ta zaɓi Mamma, sosai ta ba su tausayi Mamma ta sa Suhal da Abdul da Zaiyan har Salim suka ɗauke ta suka kai ta gidan mahaifinta Malamin Umma. Ita da Abir suka tafi gidan Baba Malam daga can su isa gidan su Baba su musu sallama. A zaune suka same shi duk ya rame ya ƙanjame suka nuna masa Khairat suka ce ita ce ƴar da suka haifa shi da Umma, ya sha kuka yana ruƙon ta gafara ta ce ta yafe mishi suka rungume juna suna kuka gwanin ban tausayi, da kyar suka rabu ta amshi number wayarsa suka dawo gida. Kafin su tafi Abba ya kira Baba Malam aka raba gado kowa aka ba shi nasa, Abir na kuka ta ce Abba ya gina mata makarantar Islamiya da gidan marayu, companyn motoci da ta ci gadonsa ta ce Abdul da Salim su kula da komai ita ba ta buƙatar komai yanzu. Bayan Sallar La'asar suka shirya aka fito da kayan su harabar gidan Khairat ta rikice ta ce sai ta bi Mamma Niger, Daddy ya ce su tafi ko ta rage damuwar da take ciki, hakan ya yi wa Mamama daɗi dan ba ƙaramin tausayi Khairat ke ba ta ba. Duk yan gidan suka musu Rakiya har Airport suna tsaye har jirgin su ya tashi tukun suka dawo gida.. Rayuwa ta yi wa su Abir daɗi matuƙa in da Mamma ke kula da su sosai. Cikin Abir sai ƙara girma yake zama da kyar tashi da kyar, ba ta yin komai sai dai ta wanke goma ta sa biyar komai sai an yi mata motsa jiki kaɗai take yi safe da yamma. Zaiyan ya soma fafutukar neman aiki irin nasa aka je aka masa takardar ɗan ƙasa, bai sha wahala sosai ba kasancewar sa jinin sarauta, ya samu takardunsa na makaranta a wajan abokinsa Bashow ya nuna suka tabbatar da ingancin ilimin da ya samu sannan suka ba shi aiki. Mamma ta hana shi amsar aikin amma Mai martaba ya ce ta rabu da shi in lokaci ya yi zai aje aikin, ba dan ta so ba ta rabu da shi. Zaiyan ya ɗauko Abir suka zo Nigeria ziyara, dama kafin ya zo ya yi magana da Abdul yana son gida mai kyau zai saya suna isa daret gidan su Baba suka aje, gaisawa kawai suka yi ya ɗauke su da komai nasu suka nufi sabon gida, ya ɗauko musu maigadi da masu aikin cikin gida, sun sha murna sosai ya ba wa Baba kuɗi har ma da Inna. Kwana biyu suka yi a Yola suka nufi Kano in da suka fara dira gidan su na haya, Tasakkawato kamar ta goya Abir sai kiran matan gidan take tana faɗin "Ku zo ku ga Jiddo." Duk fitowa suka yi kowa sai murnar yake na ganin Abir, ta gaisa da su tana kallon kofar ɗakin su Ladidi ta ce "Wai Mama ina Gamboliya da Ladidi?" Riƙe baki Tasakkawato ta yi ta ce "Waɗannan ai kwarakwatar tsiya na Jiddo, sun je sun tabo wata karuwa ta sa an zo har gida an kama su, yanzu haka suna can wajan police." Cike da jimami ta sa aka kai ta Police station ɗin ta yo belin su ta yi ta musu faɗa karshe ta dawo yi musu nasiha, duk jikinsu ya yi sanyi suka ce mata sun tuba sun daina shigar mata za su dawo asalin su na maza, Abir ta ji daɗi sosai ta ba su kuɗi masu kauri ta ce su ja jari su koma gaban iyayensu. Ta sha addu'a sosai har kuka suka yi. Abir tasa Bashow ya nemo mata gida mai kyau ta saya wa Tasakkawato da mijinta, ranar Tasakkawato ta sha kukan murna tana jero musu addu'a zaman lafiya suna amsawa da Amin. Kwanan su biyu a Kano suka wuce Niger... Wata ranar Asabar cikin dare Abir ta kama nakuɗa suka nufi asibiti ta ita, cikin ikon Allah ta haifo yara biyu duka mata. Ranar ko nurses ɗin asibitin sun san an haifi jikokin sarki Abdulwahid,sun sha kyautar kuɗi, haka aka gyara ta da yamma suka dawo gida.. Haka aka dinga sanar da 'yan'uwa da abokan arziki kowa na taya murna, ana ya gobe suna 'yan Nigeria kwainsu da ƙwarkwatarsu suka yo Niamey. Da dare Zaiyan ya lalleɓi Abir ta ɗauko masa yaran ita da Ikilima suka kawo masa ɗakinsa, Ikilima ta tafi ta bar su tana cewa Abir kar ta jima Mamma ta neme ta ta amsa da to. Kallon yaran yake masu kama da shi yana shafa su, janyo ta itama ya yi ya rungume cikin zallar ƙaunar ta ya ce "Baby kin gama min komai a rayuwa, ban san da me zan saka miki ba da wannan yara da kika haifo min su kyawawa, hakan ya sa ni ma zan miki wata bazata." Ya faɗa yana murmushi. Ɗago kai ta yi ta kalle shi cikin wani kalar yanayi na shaukin son mijin nata ta ce "Nima ka gama min komai a rayuwa Nury, Allah ya ƙara mana zaman lafiya da kwanciyar hankali, amma wata kyauta ce za ka ba ni?" Murmushi ya yi mai kayatarwa ya kama kumatunta ta ce "Na samo dangin su Mamma yanzu haka da su za ayi bikin sunan nan." Da wani irin sauri ta kalle shi ya jinjina mata kai, saurin tashi ta yi a jikinsa tana dariyar farin ciki ta gyara hijabinta ta ce "Ina zuwa Nury bari na kira Mamma ba zan ji wannan abin farin cikin ba ni kaɗai." Ba ta tsaya ta ji me za ce mata ba ta wuce da sauri, bin bayanta ya yi da kallo yana lumshe idanu.. Ba ta fi minti uku da tafiya ba sai ga su sun dawo tare da Mamma da Suhal har Ikilima, Mamma ta dinga tambayar ya faɗa mata in da suke ta je ta gan su." Ganin duk Mamma ta ruɗe sai ya ɗauki yaran ya gyara gadon ya kwantar da su ya musu addu'a duk suna tsaye sannan ya ce su je, ya yi gaba suka bi shi baya har zuwa wani sashe na ɓangarensu ya buɗe wata kofa ya shiga suka mara masa baya. A zaune suka samu Kawu Sale da wasu mata uku. Mamma da su Kawu Sale sun sha kuka Sosai ƴar'uwar mahaifiyar su Mamma ta goge hawaye ta ce "Naje Kano sau uku yan unguwar suka ce min ƴar'uwata ta rasu ku kuma ba su san a ina kuke ba, na nemi Baba Malam shi ma aka ce mijin Hassana ya zo ya dauke shi, ku yi haƙuri ku yafe mu Usaina babu kalar neman da ba mu yi muku ba a Kano amma ko labarin ku ba mu samu ba har muka gaji ni da Sale muka dawo Maradi.. " Mamma ta ce "Ba komai Mama ba ku yi mana komai ba, Kawu ina wannan ƙanwar taku?" Ta faɗa tana kallon Kawu Sale. Da hannu ya nuna mata matar da ke gefen shi, suka rungume juna suna ta kuka, Mamma ta ɗago ta sanar da su duk wani abu da ya faru da su tana yi tana kuka. Sun sha hira sosai Zaiyan ya koma ya ɗauko musu jariran suka sa musu albarka, sai da suka kusan kwana suna hira Mamma na kusan Kanwar mahaifiyarsu.... Washe gari aka yi suna lafiya, Hassana ta ci sunan Mom Husaina ta ci sunan Inna Asabe Ba dariya, an sha taro an tashi lafiya kowa sai yaba kyan yaran yake. Washe garin suna su Grandma suka haɗa kaya suka ce kuma sai in Iman ta haihu itama cikin ya soma girma, Abir ta ce in Hafsat ta haihu za ta zo suna haka dai suka rabu.. Haka aka ci gaba da kula da 'yan biyu kyautar Allah su da Mamansu har suka yi arba'in ya yi daidai da kwana biyar da haihuwar Hafsat, Abir ta shiga zaga dangi ta fara zuwa maradi ta ga dangin su masu yawa suka mata tara da arziki ta dawo, washe gari ta wuce Nigeria. Har Ruga ta je suka zaga dangi suka je gidan su Baba Inna na ta murnar ganin su, ta wuce gidan Baba Malam suka gaisa sannan ta dawo gida. Ana gama suna da kwana uku Zaiyan ya zo ya ɗauke a barsa suka koma gida.. Sai da 'yan biyu suka yi wata hudu Iman ta haifi ɗanta namiji, an sha murna sosai aka dinga kula da su ranar suna aka sa wa yaro sunan Abie Abir na jin an faɗi sunan yaron ta yi ta kukan farin ciki ta je ta rungume Iman tana mata godiya, murmushi Iman ta yi ta ce "To meye na yin godiya na ga dai Abie ni ma Daddyna ne ko?". Dariya Abir ta yi suka ci gaba da hira. Sarauniya Bilkisu ta ga dai in ta sake za ta yi abin da zai sa sarki ya sake ta sai ta watsar da komai ta je nemi yafiyar mijinta da Mamma, suka ce sun yafe mata itama Kilishi ta nemi yafiyar su suka yafe mata, sosai Mamma ta ji daɗi na canjawar kishiyoyin nata.. Sultan ya dage shi Khairat yake so aje a tambayo masa auren ta, Mai martaba ya sa aka je nemo masa auren Khairat su Daddy suka ce su ba su da matsala a sanar da mahaifinta, Malam da suka je wajan shi da magana ya ce shi babu abin da zai ce duk abin da suka yanke daidai ne, nan ya ƙara neman yafiyar Daddy ya ce bai masa komai ba ya yafe masa. Salim na ganin haka ya ce to shi yana son Ikilima, abin ya musu daɗi aka haɗa ranar auren gabaɗaya... Lokacin aure na yi aka shiga hidimar biki, Abir ita da Iman ba sa zama hidima ta yi yawa, bayan an gama biki aka kai amare gidanjensu lafiya.. *BAYAN SHEKARA BIYAR* A tsakanin wannan shekarun Abir ta sake haihuwar wasu yan biyun maza, sosai Zaiyan ya yi murna. An yi wa Fatima da Yasmin aure suma, Khairat da Ikilima duk sun haihu.. Cikin nutsuwa ya ke tafiya fadawa na take masa baya har ƙofar ɓangarensa, hannu ya ɗaga musu suka tsaya ya shige su kuma suka koma. A palo ya samu yaran sun ciccira pilows ɗin kujerun palon, Badariya da Sadiya suna gefe Hassan da Husain ne ke ta watsi da komai na palon, suna ganin shi duk suka yo wajan suna faɗin "Abba sannu da zuwa." Murmushi ya yi ya ce "Yawwa yaran kirki ina Mamanku?" Sadiya da ke gefen shi ta ce "Ta shige ɗaki ta ce mun dame ta." Murmushi ya yi ya miƙe suka nufi ɗakin. Akan gado suka same ta kwance tana kallo a waya, ganin su ya sa ta daure fuska ta ce "Duk ku fita nan ɗin ma sai kun shigo kun lalata da ba ku jin magana?. Rakuɓewa suka yi a bayan Zaiyan suna miƙo kansu suna kallon ta. Dubara ya musu ya ce su tafi waje zai rarrashe Mama suka fita da sauri. Kayan jikinsa manyan ya cire ya bar na ciki ya hayo gadon, kwanciya ya yi ya janyo ta yana ƴar dariya ya ce "Anty yunwa nake ji." Dariya ta yi tuna baya ya ja musu bargo yana faɗin "Mu yi bacci kafin su Abie su dawo ɗakin nan." Murmushi ta yi ta ƙara shegewa jikinsa ta lumshe idanu.... Tammat bi hamdu Lillah anan na kawo karshen wannan littafi mai suna A HAKA NAKE SON SHI, kuskuren da ke cikin sa Allah ya yafe min, abin da na rubuta daidai Allah ya ba ni ladan da ni da ku maru karatu waɗanda suka dauki darasin ciki suk, yi amfani da shi. Mu haɗu da ku a littafina mai suna *ANDIZO* Ku da jin sunan ma kun san akwai nishadi a cikin labarin, mu tara da ku a sabuwar shekara in sha Allah bissalam my lovely fans Ina yinku.. _Maman Nusaiba ce_