*_Bossladieswriters_* *Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jin Ƙai* Dukkan godiya da yabo sun tabbata ga Allah (SWT), Mai kowa, Mai komai, wanda Ya bani ikon fara wannan sabon littafi nawa mai suna “A Cikin Rayuwa.” Ina roƙon Allah Ya sa littafin nan ya amfane ni da ku gaba ɗaya, Ya Ubangiji, Ka bani ƙwarin gwiwa da nutsuwa; yadda muka fara lafiya, Ka sa mu kammala a cikin ƙoshin lafiya. Allah Ka kiyaye ni daga rubuta abin da zai cutar da ni ko da al’umma baki ɗaya. Ameen. *BAYANI NA MUSAMMAN (Disclaimer)* Labarin nan ƙirƙirarren labari ne, ba na gaske ba. Duk wani suna, wuri, ko yanayi da ya yi kama da na ainihi, hakan ya faru ne bisa bazata, ba da niyya ba. Na rubuta wannan littafi ne da nufin isar da saƙo game da rayuwa, soyayya, ƙaddara, da darasin da ke tattare da su, ba don nuna wani mutum ko abin da ya faru a zahiri ba. Idan wani ya karanta littafin ya ga wani abu da ya yi kama da shi ko da rayuwarsa, to hakan ba wai na nufin shi ba ne, domin ni ɗan’adam ce, ba ni da ikon sanin yadda rayuwar wani ke gudana sai dai abin da Allah Ya bani damar hasashe a kai. Manufar littafin ita ce bayyana darasi, motsa tunani, da kawo haske cikin tafiyar rayuwa, ba don cin zarafi ko kushe kowa ba. *Godiya ta Musamman* Jinjina ta musamman ga ƴan ƙungiyata, Boss Bature, QueenMarh, da Hafsat Amjad. Nagode da goyon baya da kalaman ƙarfafa gwiwa a koda yaushe. May Allah continue to unite our hearts and raise *BossLadiesWriters* higher. Ameen. Wannan littafi tukuici ne gare ki, *Mommy Kubrah*. Allah Ya ƙara miki lafiya da nisan kwana mai albarka, Ya bar mana zumunci har Aljanna. _Beloved sis, Hafsat Bature, your support means everything to me._ _There are no words enough to express my gratitude, all I can say is, may Allah bless and strengthen you always._ Ya Rabb! Bless and have mercy on all mothers, especially my mother. 🤲❤️ _My P.A, Munarh Bature, a ɗaura damarar komawa fagen daga, let’s go again!_ *_✨A CIKIN RAYUWA✨_* _By Zainab Bature (Zeelaluh)_ CHAPTER ONE Farkon Tafiya _A cikin rayuwa, wasu abubuwa ba su faruwa a bisa kuskure, sai don a koya mana darasi._ _Bata san cewa ƙaddararta za ta haɗa ta da wani da duniya ke kallon sa a talabijin ba._ _Amma kafin soyayya ta zamo haske a gare ta, dole ne ta ratsa cikin duhun da rayuwa ta tanadar mata, duhun da ke ɗauke da sirri, hawaye, da ƙaddarar da za ta canza mata rayuwa har abada....._ Kaduna State, Saturday, 10:00am Babbar harabar makarantar cike take da mutane, kasantuwar yau ne suke yin bikin yaye ɗalibai da bada kyaututtuka ga waɗanda suka yi ƙwazo (speech and prize giving day). Mahalarta taron sun haɗa da iyaye da ƴan'uwan yaran da suka gama karatu a matakin primary da kuma secondary, saura sun haɗa da manyan baƙi da aka gayyata ciki har da masu manyan muƙamai a gwamnati. Duk da makarantar bata gwamnati bace mai zaman kanta ce (private school) amman kana gani kasan babbar makaranta ce, tana da tsarin gini mai matuƙar kyau da kuma bangarorin karatu ukku, (Nursery, Primary, Secondary). Gaba ɗaya mahalartan suna zaune a cikin manyan rumfuna da aka kafa a bangarorin babban filin makarantar, bangaren da iyaye tare da ƴan'uwa da abokan arziki suke daban, haka manyan baƙi suna a bangare na musamman an tanadar masu da abubuwan ci da sha a saman teburan dake gaban manyan kujerun da suke zaune, daga cikin manyan baƙin akwai matar kwamishinan ilimi na jahar Kaduna mai suna Hajiya Aisha, da wasu daga ma'aikatar ilimi ta jahar. Iyaye da ƴan'uwan ɗaliban da ke karatu a makarantar kowa ya yi shiga ta alfarma wadda kallo daya zai bayyana maka kowa yana da hali daidai da nasa, kasantuwar karatu a makarantar na da kuɗi ba laifi, amman kuma makarantar na bada ilimi sosai. Suma ɗaliban makarantar suna a cikin rumfa daban, gaba ɗayansu suna sanye da kayan makarantar, yayin da ɗaliban da ake yayewa suke zaune daga gaba kowanne na sanye da uniform na makarantar daga sama sun daura rigar da ke nuni da sune suka kammala karatu (graduation gown and cap). Kowa ya natsu yana kallo da saurar diramar turanci da wasu daga cikin ɗaliban suke gabatarwa kan muhimmancin ilimi, a diramar gidan wani magidanci ne dake da mata ɗaya da kuma yara mata guda biyu Fa'iza da Maryam, sai dai ba uwa ɗaya ta haife su ba su duka, matar gidan ta kasance tana gatanta wadda itace ɗiyarta da ta haifa wato Fa'iza, komi yarinyar take so tana yi mata, yayin da ɗayar da ba a so mai suna Maryam mahaifiyarta ta rasu a wurin haihuwarta take fuskantar tsangwama da ƙyara, sai mahaifinta na gida ne take samun ɗan sassauci don shi yana matuƙar son ta da tausaya mata, duk da shima ba wani katabus gare shi ba a gidan. Haka ake ɗaura ma wadda ba a so talla safe da yamma duk da ta kasance tana matuƙar son yin ilimi amman an hana ta zuwa makaranta, saboda aminiyar matar babanta da ke ruƙonta ta bata shawarar kada ta sake ta bari yarinyar ta yi karatu, a cewar ƙawar tata yadda take tubarkalla kyakkyawa idan ta yi karatu ta goge to ƙarshe ba ƙaramin mutum ne zai aure ta ba. Duk wasu aikace-aikacen gidan ita ce take yin su, idan ka ganta ba wata suturar kirki haka wurin kwanciyarta a ƙasa ta ke kwana saman wani ɗan mataccen zani, duk da cikin gadon kayan mahaifiyarta da ta samu har da katifa amman an hana ta kwanciya a kai. Saboda son karatun da take yi ne yasa duk idan aka ɗaura mata talla da safe ta kai wata makaranta, sai ta je bakin tagar wani aji tana sauraren abubuwan da ake koya masu, wani lokacin idan aka yi tambaya ma ita ce take bada amsa daga waje, wannan dalilin ya sa wani malamin turanci ya rinƙa siye abun da take sayarwa ya raba ma ɗalibai ita kuma sai ya saka ta shiga cikin ajin ta zauna don ta faɗa masa halin da take ciki a gidansu da hana ta karatun da aka yi, daga baya ganin irin ƙoƙarin ta ya sa malamin ya tunkari shugaban makarantar da lamarinta. Da taimakon shugaban makarantar da malamin suka sa ta fara yin karatu kyauta. Saboda ƙwazonta bayan gama karatun ta na primary ta samu tallafin karatu (scholarship) daga gwamnati har zuwa jami'i zata yi karatu kyauta. A ƙarshe ta yi nasarar zama ƙwararriyar likita, yayin da ƴar'uwarta Fa'iza ta saka shiririta da yawon bin maza har ta yi cikin shege wanda mahaifiyarta da ƙawarta suka yi ƙoƙarin zubar da shi kamar yadda suka saba yi mata amman ya ƙi zubewa, ƙarshe ta haɗu da lalura bayan ta haife cikin ba rai, yar'uwarta Maryam da ta zama likita ita ta yi mata aiki har ta samu lafiya, ita ta gina masu gida take kuma tallafa ma rayuwar su. A ƙarshe suka ƙare da yin kukan dana sani. Bayan gama yin diramar mutane suka shiga tafa ma ɗaliban kan irin ƙoƙarin da suka yi diramar ta tafi daidai ta yi ma'ana sosai, da kuma musamman yadda suka rinƙa yin magana da turanci cikin gwanancewa ba tare da wata tangarɗa ba, ɗalibar da ta fito a matsayin Maryam wato wadda ba a so mai suna SALMA BASHIR, ta fi samun yabo a wurin mutane ganin duk da ƙananun shekarunta don bata wuce shekara sha biyu ba amman ta nuna ƙwazo sosai a diramar. Bayan gama diramar an ci gaba da yin programs daban-daban na ilimi kuma kowanne akwai dalibar nan mai suna Salma Bashir wadda ta kasance kwakkyawar gaske, kanta na sanye da hular rigar kammala karatun jikinta, tana da gashi mai tsawo sosai don kitson da aka yi mata na gaba ya sauko har zuwa ƙirjinta. Abu na ƙarshe da aka yi shine bada kyaututtuka ga ɗalibai masu ƙwazo, Salma Bashir ta samu kyaututtuka da dama ciki akwai ta ɗalibar da ta fi ƙwazo a matakin primary, akwai ta bajinta da ta yi a diramar da aka yi kan ilimi, sannan a bangaren english club ɗin makarantar an bata kyauta cikin daliban primary masu ƙwazo a bangaren debate da quiz, haka a bangaren wasanni wato sport nan ma ta samu kyauta. Kyauta ta ƙarshe da za a bata aka bayyana matar kwamishinan ilimi hajiya Aisha a matsayin wadda zata bata kyautar, bayan Salma ta je gabanta, hajiya Aisha tana murmushi ta fara miƙa mata hannunta da ya sha gold suka yi musabaha ta ce, "Congratulations, Salmat. Keep working hard and stay focused, the sky is your limit." Jinjina mata kai Salma ta yi da faffaɗan murmushi akan fuskarta ta ce, "In sha Allah. Thank you maa." Jinjina mata kai Hajiya Aisha ta yi da murmushi akan fuskarta, bayan ta bata kyautar ta dakatar da ita, ta juya tare da miƙa ma ƙawarta da suka zo tare suke zaune a wuri guda hannu, buɗe jaka matar ta yi ta fiddo rafar kudi yan dubu guda biyu wato dubu ɗari biyu ta miƙa mata, hajiya Aisha ta ɗaura ma Salma a saman kyautar ta ce mata itama ga tata kyautar nan, gaba ɗaya wurin aka saka tafi masu ɗaukar hotuna da vedio suna ta ɗaukar su, godiya Salma ta yi mata ta juya ta koma wurin zaman ta, bayan hajiya Aisha ta koma ta zauna ƙawarta hajiya Zulaihat tana murmushi ta ce, "Yarinyar ta burge ni sosai, ga kyau ga ƙwaƙwalwa. Da ta zo gaban ki sai na ji inama a ce ɗiyar ki ce don har ɗan yanayi na ga kun yi." Murmushi hajiya Aisha ta yi don ta san dalilin yin maganar tata, bai wuce sanin cewa Allah bai bata ɗiya mace ba sai maza, sai dai itama a cikin ranta ba ƙaramin burgeta yarinyar ta yi ba har ta ji sha'awar inama a ce Allah Ya bata ɗiya mace kamar ta. Bayan kammala taron mahaifiyar Salma wadda ta kasance farar mace sannan tana da ɗan jiki amma ba sosai ba, yanayin ta bata da tsawo amman kuma ba gajera bace, tana sanye da wani haɗaɗɗan lace, tun daga wuyanta zuwa hannunta zinari ne, kana ganin ta ka ga wayayyar mace ƴar boko, ta rungume Salma jikinta cike da farin ciki tana yaba mata kan ƙwazon da ta nuna a wurin, muryarta da tsananim farin ciki take faɗin, "I am really proud of you my baby. Allah Ya raya min ke ya ci gaba da albarkantar rayuwar ki. In sha Allahu sai kin zamo abun alfahari ga kowa, ina jin hakan a raina." Ɗagowa Salma ta yi da murmushinta mai burgewa ta ce, "Thank you my aunty Kubra, nima ina alfahari da ke." Ƙara rungume ta ta yi tana jin ƙaunar yarinyar na ƙara ninkuwa a cikin ranta, ƙawar aunty Kubra da suka zo tare mai suna Naja'atu itama ta kamo Salma jikinta ta taya ta murna tare da bata kyautar da ta kawo mata, ta yi mata addu'oin fatan allkhairi a rayuwarta. "Aunty, daddy bai zo ba? Ban gan shi ba." Salma ta tambaya tana kallon Aunty Kubra da farin cikin dake kan fuskarta ya ɗan canza jin tambayar da Salma ta yi, ganin Salma ta kafe ta da ido alamar amsar ta take jira ta yi ɗan murmushi tare da dafa kafaɗarta ta ce, "Wani uzuri ne ya taso masa bai samu zuwa ba, na san idan muka koma gida zai taya ki murna." Kai Salma ta jinjina tana murmushi, kallon juna suka yi ita da Naja'atu, ganin fuskar Kubra ta nuna alamun damuwa ta ɗan girgiza mata kai alamar kada ta yi hakan. Bayan gama komai suka nufi wurin da aunty Kubra ta faka motarta, a seat ɗin baya aka saka kyaututtukan Salma, aunty Kubra ta shiga mazaunin driver, Naja'atu ta zauna a kujerar gaba yayin da Salma ta zauna baya. Bayan sun hau hanya, akai akai Salma take kallon kyaututtukanta farin ciki ya bayyana a kan fuskarta, ta cikin madubin motar aunty Kubra ke ta kallonta yayin da a daidai wannan ga6ar ita kaɗai ta san abun da ke kai kawo a cikin zuciyarta. "Da alama kin ji daɗin kyaututtukan da kika samu ko baby?" Da sauri Salma ta kalli Aunty Naja'atu da ta juyo ta yi mata maganar, kai ta ɗaga mata tana yin ƴar dariya, aunty Naja'atu ta ce mata haka nasara take kawo ma mutum alkhairai don haka ta ci gaba da bada himma kan karatunta, Salma ta amsa mata da in sha Allah. Ba gida kai tsaye suka wuce ba, wani babban shopping mall aunty Kubra ta kai Salma ta ce ta zabi duk abun da take so, itama ta zabar mata wasu abubuwan, aunty Naja'atu ma ta ƙara siya mata wasu kyaututtukan, daga nan wani eatery mai kyau suka wuce suka ci abinci aunty Kubra ta yi ma Salma takeaway ɗin small chops da su ice cream kafin suka wuce gida. Misalin ƙarfe tara na dare Aunty Kubra ta turo kofa ta shigo cikin ɗakin, tana sanye da doguwar rigar bacci kanta ta saka hula, idonta akan Salma dake kwance a saman gado tana sanye da kayan bacci riga da wando da kuma hula a saman kanta, kitson gabanta sun ɗan rufe mata gefen fuskarta da ta ɗaura jikin ƙaton teddyn da ɗazun aka siya mata a mall, a bakin madaidaicin gadon kalar na yara aunty Kubra ta zauna tana ci gaba da kallon Salma da ke yin bacci hankali kwance, ta ɗan dauki lokaci tana kallon fuskarta yayin da a cikin zuciyarta ba abun da take yi face kukan zuci, yanzu shike nan dole ta rabu da yarinyar nan ta mayar da ita wurin iyayenta, dama tamkar ara mata ita aka yi saboda tsananin ƙaunar ta da take yi, gashi wa'adin da ta ɗauka na ruƙonta ya cika, ko ba haka ba, dole ta haƙura ta maida ta wurin iyayenta ko don saboda yawan sa6anin da zamanta ke haddasa masu da mijinta, ƙiri-kiri yake nuna yana yin kishi da yarinyar, a cewarsa Kubra ta fi fifita yarinyar fiye da kula da shi, ko da yaushe a cikin ƙorafi yake kan tafi bawa abu biyu muhimmanci, wato aikinta na asibiti kasantuwar ta babbar nurse, sai kuma Salma, a cewarsa koda yaushe idan tana gida to lokacin ta na Salma ne ba shi ba. Ta san duk ba komai bane ya sa take matuƙar ƙaunar yarinyar face haihuwa da Allah bai ta6a bata ba gashi har ta ɗan fara manyanta, idanunta ne suka ciko da ƙwalla, daga baya ta kifa kanta a saman gadon tana yin kuka a hankali, da sauri ta ɗago bayan ɗan lokaci jin an dafa mata kai, suka haɗa ido da Salma wadda ta farka tana kallonta da idanunta dake ɗauke da bacci, "Aunty Kubranah mi aka yi maki kike kuka?" Salma ta tambaya da muryarta da bacci bai saka ba, da sauri Kubra ta kai hannu tana share hawayen fuskarta tare da gyara zamanta, ɗan murmushi ta yi mata ta ce, "Ba abun da aka yi mani baby, ba kuka nake yi ba." Salma ta bita da ido ta ce, "Ba na ji kina yin kuka ba, kuma har kina share ƙwalla. Daddy ne ko?" Fuskar Kubra kamar zata ci gaba da yin kukan ta girgiza mata kai alamar a'a, "To don Allah autynah tell me, mi yasa kike yin kuka?" Ta kai maganar itama kaman zata fara yin kukan, ta san idan har bata faɗa mata ba itama kukan zata yi, hakan ya sa ta ƙara matsawa tare da kamo hannunta, cikin karyayyar murya ta ce, "Ba wani abu bane baby, kawai na ji har na fara missing ɗin ki ne, za ki tafi ki bar ni." Ɗan shiru Salma ta yi tana kallonta, sai kuma ta ce, "To idan baki son in tafi zan zauna nan ba zan koma ba." Da sauri ta girgiza mata kai, "No baby, iyayenki da ƴan'uwanki suma suna son ki a kusa da su, idan baki koma ba zan zama mai son kai, ke kan ki rayuwarki a nan cikin kaɗaici kike yin ta, koda yaushe daga ni sai ke, ga zarya da nike yi da ke wani lokacin sai dai in tafi da ke asibiti wani lokacin in kai ki gida, can kuwa kin ga kina da ƴan'uwa, zaku yi wasa ku ci abinci tare ku yi hira, gara ki koma cikin ƴan'uwanki don suma suna muradin ki a kusa da su, musamman Sageer, duk muka yi waya kin ga sai ya tambayi yaushe zaki koma." Shiru Salma ta yi tana kallonta, aunty Kubra ta ci gaba da kwantar mata da hankali, a hankali Salma ta ce, "To ki daina yin kuka aunty Kubra, ai zan rinƙa zuwa hutu nan, kuma zamu rinƙa yin waya har da vedio call." Da sauri ta ce mata ta bari ba zata ƙara yi ba, ɗan yatsa Salma ta miƙa mata ta ce ta yi mata promise ba zata ƙara yin kuka ba, faffaɗan murmushi Kubra ta yi, har da irin yadda yarinyar itama ta damu da ita ke ƙara mata ƙaunarta, yatsanta ta bata suka yi promise ɗin, tambayarta Salma ta yi daddy ya zo ta ce mata a'a yau ba nan zai kwana ba, Salma ta ce, "To ki kwanta a nan." Aunty Kubra na murmushi ta ce, "To ai zan takura maki kin ga gadon ƙarami ne, sai dai mu je can ɗakina mu kwanta." Salma ta ɗaga kai, dama duk idan ba a gidan mijin aunty Kubra ɗin zai kwana ba da yake yana da wata matar, a ɗakin aunty Kubra suke kwana, safkowa suka yi don tafiya bedroom din nata, aunty Kubra ta duƙa ta ce ma Salma ta hau bayanta, dariya Salma ta saka tare da hayewa saman bayan nata, bayan ta miƙe Salma dake ta dariya ta ce, "Aunty Kubra har yanzu wai ba ki jin nauyi na da kike goya ni?" Tana dariya itama yayin da take nufar kofa ta ce, "Ko kin fi haka zan goya ki babyna." Daɗi ya kama Salma ta kwantar da kanta saman bayanta daga haka suka fita. Five years later (bayan shekaru biyar....) Abuja Nigeria. Nnamdi Azikwe International Airport. Wednesday, 11:30am Iskar safiyar laraba tana kaɗawa cikin natsuwa, a hankali gudun private jet ɗin da ya sauka ya fara ragewa yayin da yake yin tafiya akan hanyarsa, hasken ranar da ya haske jikin farin jirgin ya sa shi sai sakin sheƙi yake. A gefe guda cikin tarmac ɗin wasu mutane ne a tsaitsaye, wanda daga gani tarbar wani suka zo kuma mutanen masu matsayi ne kasantuwar ba kowa ake bari ba ya je wurin da jirgi ke sauka. A hankali ƙarar jirgin ta fara raguwa, yayin da yake neman tsayawa, bayan da jirgin ya tsaya sai da aka ɗan dauki lokaci kafin ƙopar shi ta fara sauka a hankali tana buɗewa, jim bayan ɗan lokaci a nutse wani matashin saurayi ya sako kai waje daga cikin jirgin, dakatawa ya yi a bakin ƙopar jirgin ya ɗan ɗaga kansa tare da lumshe idanunsa ta cikin baƙin gilashin fuskarsa, wai aka ce komai daɗin wuri gida daban ne, a hankali ya buɗe idanunsa wani irin nishaɗi da kwanciyar hankali yake ji na ziyartarsa. A yanayin halitta, matashin saurayin dogo ne amman ba irin tsawon da ya wuce misali ba, fatar shi fara ce tas irin farin nan mai tafiya bai ɗaya, daga fatar tasa zaka fahimci hutu ya zauna masa sosai yadda take sumul, yana da kyawun fuska wadda da idanu sun kalla zasu shaida hakan, kwantaccen sajen dake zagaye da fuskarsa ya ƙara ƙawata kyawun fuskar tasa, duk da gashin baida cika sosai wanda hakan ya sa ana iya ganin ɗan lotsawar da gemun shi ya yi wato yana da chin dimple, sumar kansa da gani tana da tsawo yadda aka yi baya da ita ta kawo har saman wuyansa baƙa wuluk da ita sai sheƙi take alamar ta sha gyara, a jikinsa yana sanye da tailored suit farare ƙal, maƙale a jikin wuyan kayan bow tie ne kalar green mai ɗan duhu haka a jikin aljihunan jacket ɗin kayan nan ma an yi adon kalar green, daga jikin ƙasan zagayen hannun kayan nan ma akwai ratsin green, ƙafafunsa na sanye da haɗaɗɗun rufaffun fararen takalma, haka wutsiyar hannunsa na ɗaure da rantsattsar farar agogo, saman kan agogon sai sheƙi yake yana ɗaukar ido tare da bada launin green. Shin wanene wannan matashin mai cikar halitta da ya gaji da haɗuwa? NURADDEEN IBRAHIM AMBASSADOR ke nan, wanda fitacce kuma ƙwararran ɗan wasan ƙwallon ƙafan Turai ne dake buga wasa a babbar ƙungiyar ƙwallon kafa ta IMPERIAL LONDON FC (ILFC) dake a England. Asalin tushen shi ƙasar Nigeria ne duk da ba anan aka haife sa ba, mahaifinsa Alhaji Ibrahim Nuraddeen ɗan asalin jahar Katsina ne haifaffen garin Funtua. Kakansa marigayi Alhaji Nuraddeen Ambassador ɗan asalin garin Funtua ne wanda tushen family ɗin su babban family ne da suka yi gadon arziƙi a garin. A lokacin da Alhaji Nuradden na raye ya yi aiki a ma'aikatar harkokin waje wato Ministry of Foreign Affairs inda ya yi aiki a wasu ƙasashe da dama har ya kai matakin ambasada kafin ya yi ritaya. Yaran Alhaji Nuradden da ya haifa biyar amma ukku ne yanzu ke raye a duniya, Alhaji Sa'ad shine babban ɗan shi wanda yanzu haka yana zaune a garin Funtua tare da iyalinsa. Alhaji Sa'ad ya gaji mahaifinsa ta bangaren aiki in da shima ya yi aiki a ma'aikatar harkokin waje har zuwa yin ritayarsa, yanzu yana harkar kasuwanci da kuma noma wanda dama gadon family ɗin su ne. Mahaifinsu wato Alhaji Nuradden Ambassador lokacin da yake raye babban manomi ne da ya mallaki manya da ƙananun gonaki a sassa daban-daban a cikin ƙasar nan, suna da ma'aikata da dama dake aiki a ƙarƙashin su, yayin da wasu gonakin nasu kuma ake yin hayar su. A duk shekara ba ƙaramin noma ake yi a gonakin nasu ba, akwai gonakin da irin su auduga kawai ake nomawa da waɗanda ake noma sauran abubuwa daban-daban, kuma musamman akwai manyan kamfanoni da ke siye amfanin da aka noma da zarar an gama wanda ba ƙananun kuɗi suke samu ba. Bayan noma kuma suna yin kiwo a manyan gidajen gonakin da suka mallaka. Alhaji Sa'ad yana da yara shidda, Fahad shine babban ɗansa wanda yanzu haka likita ne dake aiki a Zaria, daga shi sai Sadeeya tana karatu a ABU Zaria, akwai Ibrahim suna ce masa Khalil sai Abubakar Sadeeq da Fatima suna ce mata Binafa sai auta Muhammad Ayden. Alhaji Ibrahim shine na biyu wanda yanzu haka ɗan majalissar tarayya ne dake zaune a garin Abuja shi da matarsa Hajiya Jameela suna da yara guda biyar, Nuraddeen wanda ya ci sunan kakansu shine babba sai Omar da Haleema suna ce mata Leemarh don sunan kakarsu ta wurin uwa aka saka mata wato mahaifiyar Hajiya Jameela, sai Sa'ad wanda ya ci sunan yayan mahaifinsu suna ce mashi Sultan sai autar su Fateema wadda ta ci sunan kakarsu ta wurin uba suna ce da ita Batool. Aunty Murja ita ce ta ukku, Malamar Jami'a ce tana aure a garin Kano tana da yara ukku, biyu mata sai namiji ɗaya. Hajiya Binta ita ce matar marigayi Alhaji Nuraddeen Ambassador wadda yanzu haka take zaune a cikin garin Funtua, ta kasance dattijuwa mai matuƙar kirki da karamci, tana da mutunci sannan ga alheri musamman ga mutanen da take rayuwa da su, ta kasance a koda yaushe burinta ta saka farin ciki a cikin zukatan al'umma musamman marasa ƙarfi, mutanen gari suna yi mata laƙabi da Hajiyar Ambasada haka ƴan cikin unguwar da take suna kiran gidanta da gidan Hajiyar Ambasada. Dangane da yadda Deen ya zamo ɗan wasan ƙwallon ƙafan Turai kuwa, akwai ƙanwar mahaifiyarsa mai suna Aunty Safnah da suke zaune a London ita da mijinta Maleek sai ɗiyarsu guda ɗaya Basma wadda ita kaɗai ce Allah ya basu. Maleek ya kasance babban abokin mahaifin Deen wato Alhaji Ibrahim, ta sanadiyar abotar su ne har ya haɗu da ƙanwar Hajiya Jameela ya aureta. Maleek ya kasance ƙwararren injiniyan fasaha da ya mallaki babban kamfani a birnin London, tun bayan da Deen ya kammala karatunsa na ƙaramar secondary anan Nigeria ya koma wurin su da zama, bayan saka shi a makaranta don ƙarasa karatunsa na secondary, lokacin malamansu suka fahimci yana da baiwar ƙwallo, don yadda yake bada himma a kan ƙwallo baya ba karatu himma, hakan ya sa malamin su na wasanni ya fara magana kan idan aka goya mashi baya zai zama babban ɗan kwallo har suka tuntu6i mahaifinsa mai ruƙonsa wato Maleek, bayan ya tuntubi Deen don jin ra'ayinsa, ya nuna masa yana son zama ɗan ƙwallo, hakan yasa Maleek ya tsaya masa da taimakon malamin nasu aka maida shi makarantar koyon ƙwallo, cikin lokaci ƙankani ya fara samun ƙwarewa sosai. Tun yana buga kwallo a junior team har ya koma yana bugawa a senior team, yana a shekara 17 ya yi signing da babbar kungiya ta farko da ya fara buga ma wasa a nan London, daga baya ya koma wasu kungiyoyi biyu har kawo kungiyar da yake buga ma wasa a yanzu, wadda Tsohuwar ƙungiya ce kuma sananna. Laƙabin da ake yi ma ƴan kungiyar shine The Imperials ko The Lions of London, suna da babban filin wasa mai ɗaukar dubbanin mutane mai suna Imperial Crown Stadium. Yanayin launin rigarsu ta gida wato jersey shine fari da ratsin golden wanda ke nuna daraja da iko, rigarsu ta waje kuma tana da launin baki da ja, sai kalar rigarsu ta ukku mai launin shuɗi mai duhu. Kungiyar Imperial London FC ta samu manyan nasarori masu tarin yawa daga manyan gasannin ƙwallo, an san su kuma da yin kasafin kudi mai tsada wajen sayen fitattun ƴan wasa daga ko'ina cikin duniya. Sannan club din na da salon suna mai ɗauke da alamar ƙarfi, mulki, da tarihi, irin wanda ke da alaƙa da masarautar Birtaniya. Ba ƙaramar shahara Deen ya yi ba a harkar ƙwallo don ya iya ta sosai ya san duk wasu dubarun cin ƙwallo, mutane na kiran sa da ɗan baiwa, da wuya ka ga an yi wasa da ƙungiyarsu bata ci ba saboda ta haɗa zaratan yan ƙwallo, hakan ya sa ƙungiyarsu tana ɗaya daga cikin wadanda ake jin shakka. A shekaru Deen ba wani babba bane don bai wuce 26 ba, sai dai in ka gan shi sai ka ce ya wuce wannan shekarun sosai saboda ƙirar jikin shi irin ta zaratan ƴan kwallo ce. Wannan ke nan game da fitaccen jarumin ɗan ƙwallo, wanda a duniyar ƙwallo aka fi sani da DEEN JR. Wasu kuma suna kiran shi da NUREE JR. Cigaban labari..... Maida idanunsa ya yi kan mutanen da suka zo tarbarsa, a hankali ya saki wani ƙayataccen murmushi tare da gyara zaman jacket ɗin shi kafin a nutse ya fara taka matattakalar jirgin yana saukkowa cikin aji, daga yanayin shigar kayan jikin shi zaka fahimci ya yi shigar ne don nuna girmamawa da kuma ƙauna ga ƙasar shi don kayan na ɗauke da kalolin tutar ƙasar Najeriya ne wato kore da fari. Daga yanayin yadda kayan suka amshi jikinsa zaka fahimci musamman shi aka ƙera ma kayan kuma ba ƙaramin kyau shigar ta yi masa ba. Tun kafin ya ƙaraso ƙannansa Leemarh da Batool suka rugo wurin sa, ganin su ya sa shi ware masu hannu yana sakar masu murmushinsa mai saka mutum shagala wurin kallon sa, ɗan rankwafawa ya yi lokacin da suka ƙaraso jikinsa ya haɗe su tare da rungume su, ɗagowa ya yi suna kallon juna cikin washe masa baki suka furta, "You are welcome big bro." Amsa masu ya yi. "Thank you my lovely sisters, Leemarh and Batool, I'm so glad to see you guys." Suna ta washe baki suma suka ce sun ji daɗin ganin shi, Leemah wadda ke da ɗan tsawo ta kai hannu ta cire glasses ɗin da ya rufe idanunsa, tsarki ya tabbata ga ubangijin da ke tsara halitta, abun da na ayyana a raina ke nan a lokacin da na yi tozali da kyawawan manyan idanunsa da suke farare tas tamkar an ɗiga zaiba, ƙwayar cikin su baƙa ce wuluk har sheƙi take yi. Kama hannuwansu ya yi suka nufi wurin sauran mutanen. A cikin waɗanda suka zo tarbar shi akwai mahaifinsa Hon. Ibrahim Nuraddeen Ambasada sai mahaifiyarsa Hajiya Jameela da sauran ƙannansa, ministan wasanni na tsaye daga gaba cikin shigar baƙaƙen suit, tare da shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasa (NFF President), sai jami'an ƙwallon ƙafa, akwai wakilan wasu manyan kamfuna dake da alaƙa da harkar wasanni, sai manyan ƴan jarida da kuma shuwagabannin ƙungiyar matasa masu son ƙwallon ƙafa. Suna isowa wurin sauran mutanen ya saki hannuwan ƙannan nasa ya nufi mahaifinsa dake ta sakin murmushin farincikin ganin tauraron ɗan nasa, rungume juna suka yi dad din ya furta, "Welcome home, son." Ya yi maganar yana shafa bayan shi, ɗagowa Deen ya yi yana murmushi ya yi ma mahaifin nashi godiya tare da furta yana farin cikin ganin su, cike da jin daɗi Dad din ya furta suma sun yi matuƙar farin cikin ganin sa, maida idon shi ya yi kan mahaifiyarsa dake gefe ta yi shiga ta hamshaƙan manyan mata, doguwar rigar rantsattsiyar lace ce Abuja boubou a jikinta ta soke ɗaurin kallabi ya zauna daram akanta, saukar da gyalenta ya yi saman kafaɗa ya bayyana yalwataccen gashinta dake tufke ƙasan kanta, lokacin da idanuna suka sauka a kan fuskarta har saida na furta Ma sha Allah ganin irin tsantsar kyawun halittarta, mace ce irin giant ɗin nan wato tana da tsawo da jiki, gata fara ce jajur da ita sannan ta bangaren fuska abun ba a magana don irin matan nan ne masu manyan kyau wanda kana kallon su ko ka hango su tun daga nesa zaka shaida kyawun su, tana da manyan idanuwa da dogon hanci wanda daga ƙasa ya ɗan yi faɗi kaɗan, haka bakinta ma madaidaici ne da zanen labbanta suka fita raɗam, daga yanayin gashin girarta ma zaka fahimci tana da yalwatacciyar suma, ɗan ɗigon baƙin dake gareta a gefen gemunta ya ƙara ƙawata kyawun fuskar tata, gaba ɗaya tun daga wuyanta, kunnuwanta zuwa hannuwanta duk gold ne. Hajiya Jameela ta kasance jinsin mutanen nan da ake kira da sadakar yalla, mahaifinsu Deen ya auro ta ne daga jahar Kano wanda asalin tushen su ba ƴan nan ƙasar bane. Wani kallo Mom ɗin nasa ta yi mashi mai kama da harara, murmushi Deen ya sakar mata don ya fahimci dalilin kallon saboda ba ita ya fara runguma ba, nufar ta ya yi ya ɗan rungumo ta tare da fadin, "I missed u sweetheart." Murmushi ta saki, ya ɗago suka haɗa ido shima da murmushi akan fuskar tasa ta ce, "Welcome home, my pride." Godiya ya yi mata kafin ya ɗaura idanunshi akan ƙannansa Omar da Sultan, duk suka yi mashi sannu da zuwa cikin nuna farinciki duk ya rungume su, wurin ministan wasanni ya nufa, cikin washe baki ministan ya ba Deen hannu suka gaisa, cikin nutsattsiyar muryar shi mai taushi da daɗin sauraro ya ba ministan haƙuri kan rashin zuwa wurin su da wuri, da fara'a ministan wanda kirista ne ya furta, "Don't worry, first things first, and family is always first." Gaba ɗaya mutanen wurin suka yi murmushi tare da jinjina kai alamar gamsuwa da abun da minista ya faɗi, cikin nuna farin ciki NFF President ya ba Deen hannu tare da faɗin, "Nigeria is proud of you. Welcome home our champion." Da murmushi Deen ya yi masa godiya, haka duk ya gaggaisa da sauran mutanen suka yi masa barka da zuwa tare da nuna farin cikin ganinsa da yabon shi kan irin ƙoƙarin da yake yi a harkar ƙwallon ƙafa, ƴan jarida nata ɗaukar su hotuna da vedios. Sun ɗan dauki lokaci suna gaisawa da yin hotuna, kafin daga baya suka nufi hanyar barin tarmac ɗin wasu daga cikin security personnel ɗin Dad ɗin sa ne suka jawo jakunkunan kayansa da aka fito da su. Suna cikin tafiyar ne minista ke ƙara jinjina ma Deen Jr. kan irin ƙwazon shi a harkar ƙwallo da irin yadda yake saka ƙasa alfahari, yana maganar yana nuni da hannuwansa yayin da Deen ke ɗan murmushin jin daɗi. Lokacin da suka iso arrivals hall nan ma wasu tarin masoyan shi ne da masu goyon bayan ƙungiyarsa da suka zo tarbarsa, nan hayaniyar masoya ta cika wurin, cike da farin ciki suka shiga ɗaga hannuwa cikin ɗaga murya suka shiga yin sowar farin cikin ganin shi tare da koɗa shi da kuma kungiyarsa ta ILFC, har da masu rera waƙokin club din su, wasu daga cikin mutanen na ruƙe da babbar banner mai ɗauke da hotonsa jikinsa sanye da kayan ƙungiyarsu ya ɗaura ƙafarsa guda a saman ƙwallo yayin da bakinsa ke a buɗe, daga yanayin yadda ya rankwafa a cikin hoton zaka fahimci yana cikin yin gudu a cikin filin wasa aka yi shi, wasu kuma suna ruƙe da placards gaba ɗaya an yi rubutun barka da zuwa tare da yabo da jinjina a gare shi, da kuma masu ruƙe da tutar tambarin kungiyarsu mai dauke da shield wato garkuwa mai launin fari da zinari, daga tsakiya akwai zaki mai riƙe da ƙwallo wanda ke nuni da jarumta da jagoranci, daga saman tambarin akwai ƙaramin kambu(crown) wanda ke nuni da haɗin kulob din da masarautar Biritaniya. A ƙasan tambarin an rubuta a Latin, "Virtus et Gloria" (wanda yake nufin ƙarfi da ƙwazanta) tutar sai shawagi ta ke a sama. Gaba ɗaya wurin ya karaɗe da hargowar masoyan Deen hakan ya jawo hankalin sauran mutane dake kai kawo a cikin arrivals ɗin duk hankulansu suka dawo kan fitaccen ɗan ƙwallon, tuni ƴan jarida sun zagaye shi wasu na mashi tambayoyi yayin da wasu ke ɗaukar hotunansa da video, ƙayataccen murmushi ne akan fuskar Deen yana ta ɗaga ma masoyan nashi hannu tare da yi masu godiya, cike da alfaharin ɗan nasu iyayensa da ƴan'uwansa ke ta sakin murmushin jin dadi ganin yadda mutane ke nuna haukan son shi, mutane sai tutsetseniya suke don ganin sun samu saka hannunsa wato autograph wasu kuma hoto suke son yi da shi, cikin sakin fuska yake saka ma masoyan nashi hannu a wurare daban daban, wasu a jikin rigunansu, wasu a jikin hanky wasu a jotter da sauran su, wasu 'Deen Jr.' yake rubuta masu yayin da wasu yake rubuta masu, 'Nuree Jr." Wasu ma, 'Ambassador Jr.' yake saka masu a autograph din. Da ƙyar jami'ai suka dakatar da mutanen suka wuce da shi. Bayan sun fito daga cikin arrivals din kai tsaye wurin da motocin da suka zo da su suke suka nufa, anan ya yi bankwana da minista da sauran muƙarrabanshi bayan sun sanar da shi game da welcome dinner da aka shirya mashi da daddare a Transcorp Hilton Hotel. A jere motocin suka fita daga cikin airport ɗin kowa ya kama hanyar da zai nufa. A cikin wata dankareriyar baƙar jeep wadda gaba ɗaya glass din ta yake baƙi baka iya hango wanda ke cikin motar Deen da ƙannansa ke a ciki, yayin da iyayensu suke a motar dake biye da bayan ta su, gaba da bayan su motocin escort ne a jere suke tafiya. _Bossladieswriter_ *_✨A CIKIN RAYUWA✨_* *_Dedication_* _Ga duk wanda ya taɓa fuskantar zafi amma har yanzu yana murmushi,_ _To everyone who has loved deeply and lost painfully,_ ga duk wanda ya faɗi,_amma hakan bai hana sa tashi ba, this story is for you._ _A cikin rayuwa, kowace ƙaddara tana da dalili, every tear carries a hidden lesson, and even in the darkest nights, there’s always a light waiting to shine again._ _May this story remind you that nothing in life is wasted, duk abinda Allah Ya bari ya faru, has a meaning that only time can explain._ _Zainab Bature (Zeelaluh)_ Page 2 .....Lokacin da motocinsu suka ƙaraso bakin katafaren gate ɗin gidan Alhaji Ibrahim Nuraddeen dake a maitama, tun a bakin gate za ka fara sakin baki tsabar haɗuwar sa, bayan jami'an dake a bakin gate sun buɗe masu kai tsaye motocin suka kutsa ciki, al'ajabi ne ya kama ni ganin irin luxurious mansion ɗin tamkar ba a Nigeria ba, fassalta tsaruwar ginin gidan ba ƙaramin aiki bane saidai a ɗan kwatanta, gidan na da girma sosai sannan an tsara shi da shuke-shuken fulawoyi masu matuƙar kyau da tsari, ƙasan gidan kan shi ba irin wanda idanu suka saba gani ba ne, wani irin design aka yi ta yadda wani bangare na ƙasan wani irin abu mai salƙi ne tamkar in ka taka zai kada ka, wani bangaren ƙasan kuma an kawata shi da shukar korayen ciyayi gwanin burgewa, gidan ya ƙawatu matuƙa ta yadda duk wanda ya tsinci kan shi a gidan zai tabbatar da naira ta sha kashi a wurin ƙera gidan. Kai tsaye entryhall din gidan motocin suka nufa a tare suka faka, cikin escort ɗin wasu suka fito tare da nufar motocin da iyalan suke suka bubbuɗe masu ƙofofi, lokacin da Deen ya fito wani irin lumshe ido ya yi fuskarsa ɗauke da murmushi ya furta, "Home, sweet home." Ƴar dariya duk suka yi Dad ɗin shi ya dafa kafaɗarsa ya ce ya yi missing ɗin gidan ne, buɗe kyawawan idanunsa ya yi akan Dad din nasa ya furta sosai ma, "Ba dole ya yi missing gida ba, almost 3 years fa rabon shi da 9ja." Mom ɗinsa ce ta faɗi hakan, nufar hanyar shiga cikin gidan suka yi hannuwansa ruƙe da na Sultan da Batool, wani irin katafaren falo ne da ya gaji da haɗuwa suka shigo, falon ƙarshe ne wurin tsaruwa akwai duk wani abu da za a samu a cikin falon masu kuɗin da suka amsa sunan masu kuɗi, to uba kuɗi ɗa kuma kuɗaɗe ko ban faɗa ba an san dole gidan ya kasance aljannar duniya ne. A ɗaya daga cikin rantsattsun saitin kujerun da ke a katafaren falon suka zauna wanda akwai saitin kujeru daban-daban na gani na faɗa sun kai ukku, bayan babban falon kuma akwai wasu ƙananun faluka a wasu bangarorin cikin gidan, sannan akwai matattakalar benen hawa sama wadda ita kanta yadda ta tsaru abun tsayawa kallo ce, daga bangaren da kayan kallo da na sauti suke akwai hotunan iyalan gidan da na sauran ƴan uwansu musamman masu muhimmanci a gare su, akwai hotunan dad ɗin su da aka yi mashi wasu zaune a majalissa wasu tare da shugaban ƙasa da sauran ƴan majalissa. Kafin Deen ya zauna saida ya fara cire jacket din jikin shi Leemah da Batool suka cire mashi takalmansa, a saman kujera mai mazaunin mutum ukku suka zauna, Deen ne a tsakiya su Leemah da Sultan suka saka shi tsakiya ya ɗaura Batool a saman kafafunsa, a kujerar gefen shi mai mazaunin mutum ɗaya ƙaninsa mai bi mashi wato Omar ya zauna, daga ɗayan gefen saman kujerar dake fuskantar su mai mazaunin mutum biyu nan mom da dad ɗin su suka zauna, Gaba ɗaya iyalan cikin farin cikin zuwan Deen ɗin suke saboda daɗewar da ya yi bai zo Nigeria ba, saidai su in sun je can su haɗu, da yake suna yawan zuwa saboda ƙanwar mom da abokin dad dake can. Maganar abinci mom ta yi masa wanda tuni an shirya mashi a dining room, ya ce mata a ƙoshe yake ya ci a cikin jirgi sai dai zuwa anjima, umarnin akawo mashi drink ta bada ta hanyar landline ɗin cikin falon, bada jimawa ba wata ƴar babbar mace ta shigo jikinta sanye da farar apron da hula irin na chef wato masu yin aikin abinci, chef Alima ke nan wadda ƴar dattijuwar bayerabiya ce, ita ce babba a cikin ƴan aikin gidan, bayan ta gaishe da su a nutse cike da taka tsan-tsan gudun masifar uwar ɗakin nata sanin bata raina abun masifa ta ɗaura luxury tray ɗin saman ƙaramin table dake a gefen kujerun, matso da taburin ta yi fuskarta ɗauke da faffaɗan murmushi ta ɗaura idonta kan Deen ta furta, "You are highly welcome sir." Da ɗan murmushi ya jinjina mata kai ya yi mata godiya, ƙokarin zuba mashi lemun ta fara, ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu ya ce ta bari ba yanzu zai sha ba in zai sha zai zuba, ɗagowa ta yi har lokacin da murmushi akan fuskarta wanda na farin cikin ganin shi ne domin suma duk suna son shi, idan ana yin ƙwallo da kungiyarsu suna cin albarkaci su zauna tare da iyalin gidan anan cikin babban falo su kalla, duk da a bangarensu na ƴan aiki akwai kayan kallon amman ta fi masu daɗi in suna kallo tare da iyalin, godiya ta yi ma shi kafin ta juya, saida ta tambayi mom ɗin cike da ladabi ko akwai wani abu da zata ƙara yi ta ɗan girgiza mata kai alamar babu sannan ta bar falon, hira suka shiga yi cike da nishaɗi, "Ya dad da mom ɗin ka na can?" Mahaifinsa ne yake tambayar shi Maleek da Safna, "They are all doing well, suna gaishe da ku." Ya bashi amsa cikin turancin shi na yan can, hatta hausar shi ma in ya yi zaka ji yanayin sautin kamar turanci, "How about Basma? Da kun zo tare ai." Mom din shi ta faɗa, yanayin fuskarsa ne ya ɗan sauya ya bata amsa da basu samu hutun school ba, "Bro amman zaka daɗe ko?" Leemah ce ta tambaya, a taƙaice ya bata amsa da ba zai daɗe ba sosai yana da wasanni da zai buga, kallon Omar ya yi ya tambaye shi ya karatunsa da yake yi a ƙasar Cyprus, amsa mashi ya yi da Alhamdulillah ya kusa komawa, kai Deen ya jinjina, maida idon shi ya yi kan Sultan ya tambaye shi miyasa basu je school ba, Leemah ce ta bashi amsa da saboda suna son su tarbe shi yasa suka ƙi zuwa. Saida Mom ta yi mashi magana kan juice da aka kawo masa sannan Leemah ta zuba mashi ya sha kaɗan, Dad ne ya yi mashi magana kan yakamata ya je ya kwanta ko ya huta gajiya, ya bashi amsa da ba wani gajiya ya yi ba sosai don ya kwanta a cikin jirgi. Suna nan zaune har aka fara kiran sallar azahar, tare da Dad da sauran ƙannansa maza suka tafi masallaci wanda yake a jikin gidan. Ko a masallacin bayan gama salla haka mutane sukai ta zuwa suna gaisawa da shi tare da yabon sa da kuma yi masa fatan alkhairi, wasu ma ba masu kallon ƙwallo bane amman saboda yadda yake burge mutane ya sa suke ta zumuɗin ganin sun gaisa da shi. Bayan dawowar su daga masallaci suka zauna zaman cin abinci a dining room wanda shima ya tsaru sosai da tsadaddan dining table da kujerun sa guda takwas, akwai kuma wasu set ɗin daban a can bangare ɗaya, abinciccika ne birjik a saman teburin cikin luxury warmers da sauran abubuwan zuba abinci na ƙawa, masu aiki biyu ne a tsaye suke serving na su yayin da suke cin abincin a nutse, gaba ɗaya idanun ƴan aikin na akan Deen yadda yake cin abincin shi cikin aji da jan hankali. Bayan gama cin abincin gaba dayan su suka taru a bangaren Deen dake a saman bene, bangaren na da girma akwai babban falo da ya ji kujeru leathers sai kayan kallo da kayan sauti, akwai manya-manyan hotuna wanda yawanci duk na shi ne a wurin ƙwallo sai na ƴan gidan su, akwai hoton abokin mahaifinsa wanda yake wurin shi wato Maleek tare da iyalinsa, sam falon baida hayaniya amman kana kallon kayan ciki zaka san masu tsada ne kuma ba gama garin kaya ne ba da zaka iya samu a ko ina, daga wurin bangon da kayan kallo suke wani irin design ɗin gini aka yi na gidajen da za a iya saka abubuwa, a cikin gidajen wasu daga cikin lambobin yabo da kyaututtuka masu daraja ne da ya samu a ciki gwanin burgewa, duk da ba wai iya su kaɗai bane kyaututtakan akwai tarin wasu a gidansa na London. Zazzaune suke a saman kujerun cikin falon suna ta hira, mom ɗinsu ta canza kaya zuwa doguwar riga navy blue da ta ƙara fiddo da haskenta fayau, Dad din su ma jallabiya ce a jikin shi, su Leemah dai kayan da suka je tarbar shi ne airport ƙananun kaya riga da wando, haka ma Omar da Sultan duk ƙananun kayan ne a jikinsu, shima Deen ya canza kaya zuwa na shan iska riga mara hannuwa da gajeran wandonta da ya kai mashi gwiwa, murɗaɗɗun hannuwansa sun bayyana, "Bro, mom ta ce nima ina gama secondary school zan koma wurin Aunty Safnah a can zan ci gaba da karatu." Leemah ce ta faɗa tana murmushi. "When will you be done with secondary school?" Deen dake kishingiɗe ya tambaya, "Yanzu ina a S.S 2 going to 3 nan da one year zan gama." Kai ya jinjina kawai. "Ni ina ganin ba gara ki yi karatunki anan ba, in kika tafi nesa Batool ba za ta ji daɗi ba ita kaɗai ba ƴar'uwa mace." Dad na rufe baki Mom ɗin su ta ce, "No, can zata tafi saboda Basma ta matsa tana son ta koma can itama ta samu sister, ita Batool ai autan mom ce muna tare ko yaushe ba za ta damu ba." Ta yi maganar idonta a kan Batool dake manne da jikin Deen, ta ɗage mata gira tare da tambayarta ai ba za ta damu ba tana tare da mom ko, kai Batool ta jinjina mata tana murmushi, shiru Daddynsu ya yi ya san kawai ita ke ra'ayin Leemah din ta je can, shi kuma yana tunanin hakan kamar bai kamata ba, ganin Deen na zaune a wurin su duk da yanzu yana da gidan kansa amman ai kusan a wurin su ya taso, kuma har yanzu in dai yana a London a gidan su yake zama, bayan wannan kuma shi bai son Leemah ta kasance tare da Basma su samu kusanci sosai don ya san yarinyar bata jin magana an sangartata da yawa, duk da ya san iyayenta suna ƙoƙari wurin tarbiyarta, sai dai kasancewar ita kaɗai Allah Ya basu ya sa take samun gata sosai. "Bro Deen, pls gobe ka kaimu school friends dina na ta son su gan ka da na faɗa masu zaka zo, wasu ma sun ce sai sun zo nan gidan sun gan ka ku gaisa." Shiru ya yi idonsa akan Leemah da ta yi maganar yana ɗan murmushi, magiya ta shiga yi masa akan ya kai su, Sultan ma ya ce shima abokansa na son shi sosai kuma suna ta son ganin shi, haɗuwa suka yi suna roƙon shi akan ya kai su makarantar, Leemah har da duƙawa ƙasa a gaban sa, su Dad sai dariya suke masu, amsa masu ya yi da zai duba ko da ba goben ba zai kai su, sallamar da suka ji an yi ce ta saka su kai idanunsu gaba ɗaya kan ƙofar shigowa, wani matashin mutum ne ya shigo, a yanayin halitta dogo ne kusan zasu iya yin kai ɗaya da Deen, baida jiki yanayin shi irin na ƴan gayun fulani da hutu ya zauna masu, amman kuma duk da rashin jikin shi sam baida sirantaka, jikinsa na da ɗan cika ta yadda riga da wandon jeans din da yake sanye da su sun kar6e shi sosai, yanayin hasken fatarsa da kuma sumar kansa sun fallasa kasancewar shi bafullatani, duk da bai kai hasken su Deen ba amman kuma shima ba baƙi bane, saidai ya fi wasu daga cikin ƴan gidan su Deen ɗin haske kamar Omar da Sultan hasken mutumin ya fi nasu, ba kamar Deen da Leemah ba da suka fi kowa fari a gidan don sak kalar fatar mahaifiyarsu suka ɗauko, itama Batool tana da haske tafi su Omar da Sultan amman kuma ba ta kai hasken Deen da Leemah ba, Leemah da bata kai ga miƙewa daga durƙuson da ta yi a gaban Deen, tana ganin mutumin da ya shigo ta yi saurin miƙewa, nufar shi ta yi muryarta da alamun mamaki ta furta, "Ya Fahad!" Bin ta da wani mugun kallo mom ɗin su ta yi ganin yadda take rawar jikin ganinsa, ba tun yanzu ba tana jin haushin yadda Leemah ke rawar ƙafa duk in ta ga Fahad, kwanaki can baya har tsare ta ta ta6a yi kan ta faɗi mata ko akwai wani abu a tsakaninsu, Leemah ɗin ta ce mata ita ba wani abu kuma miye don tana nuna murna in ta ganshi ba ɗan'uwanta bane, kuma matsayin yayanta tun da ɗan yayan mahaifinta ne, a lokacin kashe ma mom ɗin nasu baki ta yi da amsar da ta bata dama kuma Leemah tsagera ce. Deen na ganin wanda ya shigo shima ya yi saurin miƙewa yana sakar masa murmushi ya nufe shi, dad dake zaune sai murmushi yake ganin Fahad ɗin, tsaye Leemah ta yi a gaban shi tana sakar mashi murmushi ta ce, "Sannu da zuwa yaya Fahad, ashe zaka zo?" Kai ya ɗaga mata alamar eh, Deen na ƙarasowa ya nufe shi tare da ɗan rungumo shi yana yi mashi sannu da zuwa, bayan ya ɗago Fahad ɗin ya amsa mashi tare da yi masa an zo lafiya, kamo hannunsa ya yi yana faɗin su shiga ciki, gaba ɗaya falon ya karaɗe da kamshin turaren jikinsa mai daɗin ƙamshi da sanyaya zuciya yayin da suke ƙarasa shigowa ciki, a saman kujera ɗaya suka zauna, dad dake kallon shi fuskar shi ɗauke da murmushin ganin ɗan yayansa, da ido kawai mom din su ta bi su saidai a cikin ranta sam bata jin daɗin yadda su Deen ke rawar jiki akan Fahad din, "Daddy ina wuni." Fahad din ya gaishe da shi a nutse, da faffaɗan murmushi ya amsa. "Lafiya lau son, ya hanya? Ya ka baro duk mutanen Funtua?" Amsa masa ya yi da Alhamdulillah duk suna lafiya suna gaishe da su, maida idon shi ya yi kan mom din su Deen itama ya gaishe da ita. "Yauwa, an zo lafiya." Ta amsa babu yabo babu fallasa, ba tare da ya maida idonsa a kanta ba a taƙaice ya amsa mata da lafiya lau, kallon Deen ya yi suka sakar ma juna murmushi, "Our football star, sai ga ka a ƙasarmu." Fahad din ya faɗa, ƴar dariya Deen ya yi ya ce, "I thought zan ganka cikin wanda suka zo welcoming ɗina a airport." Hannu ya kai ya ɗan shafi gashin fuskarsa da ke a kwance ya sha gyara tare da ɗan gyara zamansa ya ce mashi aiki ne ya ruƙe shi ya yi ƙoƙarin ya taho da wuri, "Daga wurin aikin ma ka taho ke nan?" Dad ya tambaya, Fahad ya ɗaga kai ya bashi amsa da eh, "To ya aikin? Ana dai ƙoƙari yadda ya kamata ko?" Kai ya jinjina ma Dad alamar eh, addu'ar Allah ya taimaka ya yi masa suka amsa da Amin har da Deen, Leemah ce ta shigo hannunta ruƙe da madaidaicin tray a saman shi glass jug ne ɗauke da ruwan lemu da cup, kallon mamaki mom ta bita da shi don ba wanda ya lura da lokacin da ta fice daga falon, ɗan tebur ɗin dake a gefen kujera ta dauko ta ɗaura tray ɗin, da kanta ta tsiyaya masa lemun ta miƙa mashi tana murmushi ta ce gashi ta san yana buƙatar shi tun da ya yo tafiya mai nisa, jin abun da ta ce ya sa shi kallonta suka haɗa ido ya sakar mata murmushi kumatunsa duk suka ɗan lotsa alamar yana da dimples, amsar cup ɗin lemun ya yi tare da yi mata godiya. "Daɗi na da Leemah wani lokacin akwai hankali." Da sauri ta kalli daddynsu da ya yi maganar, ɗan tura baki ta yi, "Daddyyy, you mean wani lokacin bani da hankali ke nan?" Ta tambaya ta ɗan ɗaure fuska tare da tura baki, "Haka ne mana." Kafin Dad ɗin nasu ya bata amsa Omar ya faɗi hakan, kallo mai kaman harara ta wurga masa dama ita ke bi mashi ba su cika jituwa ba, a faɗace ta ce, "To an ji ɗin." Gaba ɗaya Omar ɗin ya bata haushi don sai ta ji an muzanta ta a gaban Fahad, kallon dad din su ta yi ganin yana ƴar dariya ta ƙara ƙulewa kaman zata yi kuka ta ce, "Dad, you are the one who caused it and yet you are laughing." Maganar tata duk ta basu dariya, yana kallonta ya ce to shi mi ya yi ai ba a ji ya ce bata da hankali ba Omar ne ya faɗi hakan, tura baki ta yi tana ƙyaƙkyafta idanu, ta nufi jikin hannun kujerar gefen da Fahad yake ta zauna, ganin ya ruƙe lemun bai fara sha ba ya sa ta ce mashi ya sha mana, ya kai cup ɗin bakin shi ya fara kur6a a hankali, mom dai bakinta ya mutu sai bin Leemah take da ido ganin yadda take nema ta wuce gona da iri, sai ka ce ita kaɗai yake ɗan'uwanta da za ta yi ta faman rawan jiki haka, "Amman dai ya Fahad kwana zaka yi ko?" Shiru ya ɗan yi ya dakata da shan lemun, kallonta ya yi bayan ya kawar da idonsa ya ce mata yau zai koma saboda aiki gobe, a shagwa6e ta ce, "To ba sai ka ɗauki excuse ba, yaushe rabon da ka zo nan gidan ka kwana." Ɗan murmushi kawai ya yi, Deen ya ce, "Pls ka bari sai gobe, dama akwai welcome dinner da aka shirya saboda ni sai mu je har da kai..." Tun kafin ya rufe baki mom ta tari numfashinsa, "To in bada shirin kwanan ya zo ba miyasa zaku matsa masa ne sai ya kwana? Ba ku ji ya ce daga wurin aiki ya taho nan ba, na san kayan jikin shi ne kawai ya taho da su, in ya tsaya ina zai samu wanda zai canza?" Duk kallonta suka yi irin na mamakin jin abun da ta ce, Fahad dai idonsa na ƙasa, a hankali ya ɗan yamutsa fuska jin maganarta, ba yau ne ta fara masa irin wannan kora da halin ba, shi ya sa bai son zuwa gidan ko da ya shigo Abuja bai wuce ya zo su gaisa ba, koda kwana zai yi in ya zo gidan daddy ya ce masa ya tsaya ya kwana wani lokacin sai ya ce mashi a ranar zai koma ko kuma ya ce sun zo wani taro ne an kama masu wurin da za su kwana, kusan in har ya zo gidan ya kwana to Deen na nan ne, "Mom kaya ai ba problem bane, akwai clothing stores available da za a siya nan take ma a saka." Leemah ta faɗa tana watsa hannuwa, hannu Deen ya kai ya shafi sumarsa yana kallon Fahad da har lokacin kansa yake sadde ƙasa, ya ce masa ya ma kira wurin aikin ya ɗauki excuse anan zai kwana dama shima zai je Funtua ko goben sai su tafi tare, wani kallo mom din shi ta yi masa ba ta dai ce komai a. "Bro Deen yanzu sai mu je a siya kayan da zai saka na dinner ɗin ko?" A ɗokance Leemah ta faɗa, kai Deen ya girgiza ya ce mata ba sai sun je sun siyo ba akwai kaya da ya siyo mashi daga can, daɗi ne ya kamata ta shiga sakin murmushi. "Fahad, ya Hajiya fa? Wllh ina ta so in je don na kwana biyu ban leƙa ta ba sai dai ta waya, amman kwanan nan zan yi ƙoƙari in sha Allahu in samu in je dai." Tun kafin Fahad ya ce wani abu mom ta yi karaf ta ce, "To ai rashin zuwan ba laifin ka bane, kowa ya san yanayin aikin ka, ɗan siyasa dama ina ya ga wani isasshen lokacin da zai rinƙa yin tafiya a duk lokacin da ya so, kuma itama Hajiyar ba ta so a rinƙa ganinta ba ko yaushe, tun da ai har nuna kana son ta dawo nan ka yi amman ta ƙi amincewa, don haka ka ga sai dai ta rinƙa yin haƙuri sai lokacin da ta ganka kawai." Ta ƙarashe maganar tare da maida bayanta ta jingina da jikin kujera, yadda ta yi maganar ko a jikinta saima ta ɗauki waya tana latsawa, Fahad da Deen kuwa gaba ɗaya wutar su ce ta ɗauke jin kalamanta, shi ma dad ɗin shiru ya yi bai ce komai ba, wani abu ne ya tokare wuyan Fahad jin yadda Daddyn ya yi shiru, duk da dama bai yi zaton zai ce mata wani abu ba, saboda ba yau ta fara danƙara magana irin haka ba ba tare da ya tsawatar mata ba, ƙiri-ƙiri take nuna bata son danginsa su ra6e su, ta fi son ya rinƙa hidimta ma danginta kawai. Kowa na danginsu ya san bata son suna ra6ar shi sai ka ce ba ƴan'uwansa ba, abun takaicin ma hatta mahaifiyarsa bata ƙyale ba, ji dai yanzu maganar da ta faɗa, a cikin ran Fahad ayyanawa yake da a ce mahaifiyarsa ce ta yi maganar nan tabbas sai ta gane kuskurenta a wurin abbansu, amman shi duk irin abubuwan wulaƙanci da cin kashin da take ma danginsa ya zuba mata ido, yadda take cin karenta babu babbaka ba tare da ya iya yin wani katabus ba akai abun na basu mamaki, ko don tana da kyau ne ya sa ya ƙyale ta take abun da ta ga dama? Amma in haka ne, ai itama mahaifiyar su Fahad tana da kyau don bafullatana ce kuma jinin sarauta amman hakan bai sa abbansu ya bata damar da zata wulaƙanta na shi ba, dama kuma mahaifiyarsu Hajiya Amina mutuniyar kirki ce bata da halin wulaƙanta mutane. In ba don alaƙar aure ta haɗa Hajiya Jameela da nasu ba wllh bata kai matsayin da za ta taka wani daga cikin ahalin su ba ba tare da ta gane kuskurenta ba, matar da ahalinta duk talakawa ne kawai kyawun sura da Allah ya yi masu ne ya rufa masu asiri suke auran masu kuɗi, dama kuma iyayensu mukwaɗaita ne mugun son abun duniya gare su, hakan ya sa suka maida ƴaƴannasu jari. Deen ya lura da yanayin fuskar Fahad akwai alamun 6acin rai dama kuma ya san shi da zuciya, kamo hannunsa ya yi ya ce mashi su je ɗaki zai nuna mashi abu, hakan ma mom ɗin sai da ta tanka, ta ɗaga murya tana faɗin su da ya bari anan ba don shi suka zo part ɗin nasa ba ko su basu da muhimmanci ne, Dad ne ya ce mata ta ƙyale su ta san kamar abokai suke da juna za su buƙaci ke6ewa su tattauna tun da sun daɗe ba su haɗu ba, Deen bai tsaya saurarar ta ba ya ja Fahad ɗin suka shige cikin bedroom, dogon tsoki ta ja tare da miƙewa ta nufi hanyar barin falon tana tafiya cike da isa, duk suka bita da ido, su kan su yaranta sun fahimci tana nuna bambanci tsakanin danginta da na daddynsu in suka zo ko suka haɗu da su, ko Funtua sai a daɗe bata je ba sai in wata hidima ta kama itama sau da yawa sai daddyn ya matsa mata sannan ta je, akwai part ɗin su da suke sauka a gidan Hajiyar Ambasada, haka za tai ta wulaƙanci tana yi ma mutane kallon rashin arziki, ko zaman da suke yi a gidan Hajiyar ba so take ba saida tai ta yi ma daddyn mitar ya gina masu gidansu daban kamar yadda yayansa wato mahaifin Fahad shima yake da gidansa daban, da ya tambaye ta miye illar zaman su gida ɗaya da Hajiya, sai ta fake da cewa unguwar da gidan yake ta yi ƙauye da yawa ba kamar unguwar da gidansu Fahad yake ba a bakin babban titi ba hayaniya da cunkoso, kawai ta faɗa masa hakan ne amman saboda bata son yadda danginsu da mutane suke zuwa in suka je ne, wani lokacin bata samun damar yi masu wulaƙanci saboda Hajiya na taka mata burki, shi ya sa take son ya gina masu gida daban su rinƙa sauka yadda zata ji daɗin taka duk wanda ta ke so. Duk suka je sai ta yi ta mashi mitar ya gina masu gida, sai dai ya amsa mata da zai gina masu, har dai daga baya sai da ta yi nasarar saka shi ya fara yi masu ginin katafaren gida amman har yanzu ba a kammala ba. Batool na ganin mom ɗinsu ta fita ta miƙe ta bi bayanta, Sultan da Omar ma duk suka miƙe suka fita, miƙewa shima dad ya yi zai tafi, ganin Leemah ta yi zaune bata da niyyar tashi ya ce mata ta tashi su je, tana yamutsa fuska ta ce mashi tana son su yi hira da ya Fahad ne, ce mata ya yi ta bari zuwa anjima in sun gama tattaunawa tun da anan zai kwana sai su yi hiran, fuskarta a yamutse ta tashi ta bi bayan shi suka fita. *Littafin A Cikin Rayuwa kashi na farko zai zo maku a kyauta, ga mai buƙatar kashi na biyu zai biya 500 kacal. Domin neman ƙarin bayani a tuntubi waɗannan lambobin ta hanyar aika saƙon whatsApp kawai banda kira, 09013804524, 08169856268* _Bossladieswriters_ *_✨A CIKIN RAYUWA✨_* _By Zainab Bature_ Page 3 .......Bayan sun shiga cikin bedroom ɗin Deen wanda shima babba ne, sam ɗakin baida hayaniya amman ya tsaru da tsadaddun furniture, tun daga kan yadda aka tsara ɗakin zuwa kayan dake ciki irin na turawa ne, akwai tafka tafkan glass windows a wurare daban daban na bangon ɗakin, girman windunan in mutum ya tsaya a jiki za a iya hango kusan gaba ɗaya jikinsa, a jikin windunan akwai labulaye masu kyau da inganci kalar ruwan madara, sauran kayan cikin ɗakin ma duk kalar ruwan madara ne, akwai gado king-size bed with stylish high-end bed frame with built-in headboard, sai bedside drawers a saman su haɗaɗɗun fitilu ne, akwai tebur ɗin gaban gado ɗunɗumeme, daga ƙasa wani irin lallausan carpet ne mai gwa6i yana da gashi-gashi masu ɗan tsawo shima kalar ruwan madara, can ɗan gaba da gadon akwai lounge chair daga bayanta akwai tafkekiyar window wadda kana zaune a kan kujerar wurin kana hango waje, akwai dressing table da kujerar shi can gefe ɗaya, sai walk-in closet da ke acan cikin ɗakin, yadda aka tsara closet ɗin wurin ya yi kamar wurin sayar da kaya wato boutique, banda wurin kayan sakawa akwai wuraren ajiye takalma, daga tsakiyar closet din akwai dresser da chest of drawers a ciki su agoguna ne da sauran kayan gayun maza. A saman kujerar zama dake gaban gadon suka zauna, kowa ya yi shiru fuskar Deen tattare da damuwa yake kallon Fahad da ya jingina bayansa jikin kujerar ya ɗan ɗage kai yana kallon gefe guda, a hankali Deen ya kai hannunsa ya ɗaura a saman hannun Fahad ɗin dake ajiye saman cinyarsa, juyo da fuskarsa ya yi ya kalli Deen, "I'm sorry Yaya Fahad.." Deen ya faɗa fuskarsa tattare da damuwa, ɗan murmushi Fahad ya yi masa kawai, "I don't know why mom is acting so inappropriately...." Ya faɗa looking worried, shiru Fahad ya yi tare da kauda idanunsa gefe, kasancewar shi mai zuciya ba tun yanzu ba abubuwan da mahaifiyarsu Deen ke yi ma danginsu ke ci masa tuwo a ƙwarya, ba don karfin zumuncin dake tsakaninsu da ƴan'uwansu ba da tuni sai ta fuskanci 6acin ransa kan abubuwan da take yi, duk irin yadda suke janye jiki da gidan gudun wulaƙancinta hakan bai sa sun tsira ba, da alama so take kwata-kwata su daina zuwa gidan wanda hakan abu ne kuma da ba zai yuwu ba, suna ƙaunar junansu shi da sauran ƴan'uwansa, musamman Deen da Fahad akwai shaƙuwa mai ƙarfi a tsakaninsu tun tasowar su, mahaifin Deen ya so Fahad ya zauna gidan tare da su saboda ganin yadda suke ƙaunar juna, saidai mahaifiyarsa firr ta ƙi amincewa ta nuna bata son ya zauna a gidan, a nan gidan Fahad ya yi karatunsa na secondary cike da ƙyara da kuma hantara daga wurin mom, idan dad baya a gidan haka zata mayar da shi kamar wani yaron gida, shine gyaran gida da su aike duk da a lokacin Deen ba wani girma ne da shi ba, yana nuna mata rashin jin daɗin hakan da take yi amman hakan bai sakawa ta bari, ya sha cewa sai ya faɗi ma Dad abubuwan da take masa amman Fahad ke hana shi ya ce masa in har ya faɗi ma dad to za su 6ata kuma zai tafi ya bar gidan, hakan yasa Deen bai ta6a sanar ma dad ɗin nasu ba, duk da a lokacin shima dad din yana ɗan fahimtar ƙuntatawar da take ma Fahad ɗin, sai dai ko ya yi mata magana sai ta nuna ita mi take yi masa kuma tun da matsayin uwa take a wurin sa ba dole ta rinƙa tsawatar masa ba kan abun da ba daidai ba, kawai dai dad na yin shiru ne don ba wani katabus zai iya yi ba kan hakan amman ya san tana takura masa, hatta iyayen Fahad a lokacin sun fahimci zaman takura yake a gidan ba kamar da suka san halin mom ɗin su Deen na rashin mutunci, saidai ko an tambaye shi kan irin zaman da yake yi idan ya je hutu gidansu sai ya nuna masu lafiya lau yake zaune, a lokacin bai son su san halin da yake ciki ne ba don komai ba sai don ka da su raba shi da Deen sanin ba zai jure hakan ba, wani lokacin idan ta kai Fahad ɗin bango ya gaya mata magana da yake yana da zuciya har bugunsa take. Lokacin da Deen ya gama ƙaramar secondary ne ta matsa kan tana son ta maida shi London wurin ƙanwarta ya ƙarasa karatunsa a can, ba don komai ta yi hakan ba sai don ta raba shi da Fahad wanda a lokacin shi ya kammala karatunsa na Secondary, jin haka yasa dad ɗin Deen ya ce su tafi tare da Fahad sai shima ya ci gaba da karatun nasa a can, aikuwa ta hau sama ta dire kan sam hakan ba zai yuwu ba ya koma gidansu shima mahaifinsa ya nema mashi makarantar da zai ci gaba, lokacin ya so ya kafe kan ra'ayinsa amman sai ta fake da nuna mashi abun zai yi yawa a ce sun je can har su biyu sun zauna a wurin su, ya nuna mata ai ba dole sai su duka sun zauna ba sai shi Fahad ya zauna a makaranta amma ta dage kan ya san dai irin shaƙuwar da suka yi ba yadda za ai suna a ƙasa ɗaya su zauna a wuri daban-daban. Ƙarshe dai sai da ta yi nasarar yadda ta sa shi janye ra'ayin kai Fahad can. Deen ya sha kuka lokacin da za su rabu da Fahad, tare da daddynsu suka raka shi Funtua da zai koma, a can ma ganin yadda Deen ya shiga damuwa kakarsu Hajiyar Ambasada sai da ta ce ma Alhaji Ibrahim mi zai hana a tura su tare da Fahad din amman sai shima ya fake da faɗi mata irin abun da mom ɗin su Deen ta faɗa, a lokacin ta fahimci matarsa ce bata son hakan, da yake ita ba mai shiga ta yi karan tsaye cikin al'amuran ƴaƴanta ba ce, tsakaninta da matayen su sai in abu ya wuce gona da iri take shiga hakan ya sa ta ƙyale su, ƙarshe Deen yana ji yana gani aka raba shi da yayansa da yake matuƙar ƙauna a cikin zuciyarsa suka koma Abuja ba tare da shi ba. Bayan tafiyar Deen London shima Fahad mahaifinsa ya nema masa makaranta a ƙasar Malaysia ya tafi yin karatun likitanci. Duk da sun yi nesa da juna hakan bai sa sun daina zumunci ba, suna ziyartar juna duk suka samu hutu, ba kamar Deen da yake ɗan gatan Maleek ne ba ƙaramin ji yake da shi ba saboda bai da ɗa namiji, duk abun da yake so yana masa hakan yasa duk lokacin da ya nuna yana son zuwa Malaysia wurin Fahad sai ya samu lokaci ya kai shi da kansa, dama kuma akwai kamfanonin da yake yin hulɗar kasuwanci da su a can, hakan ma sai da mom ɗin Deen ta yi ƙoƙarin hana ziyartar junan da suke yi ta hanyar yi ma Maleek magana kan ya daina biye ma Deen, ta ce ko ya ce yana son zuwa wurin Fahad ya daina kai shi, sai dai bata yi nasara ba don Maleek ɗin nuna mata ya yi ai hakan ba wani abu bane kuma abun da suke yi yana da kyau ƙarfafa zumunci ne, da bata yi nasara ta bangaren sa ba sai ta koma kan wadda take da iko da ita wato matarsa ƙanwarta Safna, tsawatar mata ta yi a kan ta hana Maleek kai Deen da yake yi wurin Fahad, a lokacin Safna ta nuna mata zata yi hakan, amman da yake itama tana tsananin son Deen duk abun da yake so tana yi masa bata hana ɗin ba, ƙarshe dai dole mom ɗin ta kyale su ta ƙarata da baƙin cikin hakan. Juyowa Fahad ya yi ya kalli Deen da har lokacin 6acin rai ke kwance akan fuskarsa, dafa kafaɗarsa ya yi cikin kwantar da murya ya ce, "You shouldn't worry yourself about dat, hakan na faruwa, wasu mutane suna yin abun da ake ganin ba daidai ba, su kuma a wurin su basu ganin hakan a ba daidai ba, so hakan ya daina damun ka." Ɗan yamutsa fuska Deen ya yi, "Amman ita mom ta san abun da take yi ba daidai bane tun da ba kowa take ma hakan ba. Tun ba yanzu ba Ya Fahad bana jin daɗin the way take treating duk dangin daddy, kaman sun mata wani abu?" Ya ƙare fuskarsa a yamutse, ɗan murmushi da ya fi kama da na takaici Fahad ya yi jin har yaranta sun san tana yi ma danginsu ba daidai ba, ƴar ajiyar zuciya Fahad ya sauke, "Zai iya yuwuwa akwai abun da ya faru da ya sa hakan ke faruwa." Fahad ya faɗa ba don yana zaton hakan bane ya dai ce ne kawai. Duk da yana yaro sosai aka aurota bai tunanin akwai abun da ya ta6a faruwa tsakaninta da danginsu da har ya haifar da hakan, dama can tun da ya taso yake jin ana ƙorafi game da halinta. "Ya Club ɗin na ku, wani wasa zaku buga in ka koma?" Da murmushi Deen ya faɗi masa ya ce, "Ko ka zama football fan ne? Da fa kana son ƙwallo sosai, ka tuna lokacin da muke yi a cikin compound kai ta fyaɗa ni da ƙasa, in kafe sai na rama ƙarshe da kuka muke gamawa ka dawo kana rarrashi na" Ya ƙarasa yana sakin faffaɗan murmushi, dariya Fahad ɗin ya yi tunowa da lokacin, gyara zama ya yi ta yadda ya ɗan zamo jikinsa ya kwanta kansa a jikin kujerar, "Yanzu ma ina ɗan kallon wasu match ba sosai ba, amman duk wasan ku ina kallo." Kai Deen ya jinjina, ya yarda da abun da ya faɗa don duk suka yi wasa suka yi nasara sai ya taya shi murna ta chat ko kiran waya, koda basu yi nasara ba sai ya yaba masa tare da ƙara ƙarfafa masa gwuiwa. "Yanzu na fi kallon boxing sosai." Fahad ya faɗa yana ɗan shafa sajensa, "Ka ce ka fi son kallon mugunta, Allah Ya sa ba kana koya bane watarana ka karya ma wani jaw." Dariya sosai Fahad ɗin ya yi, "Wani lokaci ne dinner da ka ce?" Fahad ya tambaya yana kallonsa, faɗi masa lokacin ya yi tare da venue kafin Deen ya ce masa yana zuwa ya nufi cikin ɗakin, walk in closet dinsa ya shiga, bada jimawa ba ya fito hannunsa ɗaya jaye da suitcase kalar ruwan ƙasa da wata yar babbar jaka a ɗayan hannun masu kyaun gaske, gadon shi da ya sha gyara an shimfiɗa zanen gado mai kyau sai duvet mai laushin tsiya da aka rufe rabin gadon da shi gaba ɗayan su kalar kayan ɗakin ne suma wato ruwan madara, ɗaura akwatin ya yi saman gadon ya haye sama ya zauna, kallon Fahad ya yi ya ce masa ya zo ya gani, a nutse ya taso yana gyara rigarsa ya nufo shi, a ɗayan bangaren gadon ya zauna ta yadda sun saka akwatin tsakiya, buɗe akwatin ya yi wanda kayan sakawa ne cike a ciki, daddaɗan ƙamshi haɗi da na sabuntar kaya ne ya gauraye wurin, a tsanake yake fiddo da kayan yana nuna masa yana ajiyewa a gefe, bayan ya gama fiddo da kayan ɗayar jakar ya jawo itama ya buɗe ta, a ciki takalma ne ƴan ubansu tsadaddun gaske, akwai agoguna da turarurruka harda kayan shan iska da underwear na maza, bayan duk ya gama fiddo su ya kalli Fahad ya ce gasu nan nashi ne ya san duk za su yi masa tunda ya san size ɗin sa duk da ya ga kaman ya ɗan ƙara jiki ko ya daina motsa jiki ne, da murmushi Fahad ɗin ya ce masa yana yi, da zolaya Deen ya ce to cinye ma mommy abinci yake yi ke nan tun da ya ƙi ya yi aure, ƴar dariya Fahad ya yi kafin ya mayar da idanunsa kan kayan dake jibge a saman gadon ƙirar manyan kamfuna, ko ba a faɗa ba ya san kaya ne masu tsadar gaske, kallon Deen ya yi ya ce, "Miyasa zaka kashe kuɗi haka, kayan sun yi yawa ai." Shima yana murmushi ya bashi amsa, "Ina da kuɗin ne, ko da bani da su zan nema don in siya maka." Ɗan faffaɗan murmushin jin daɗin maganarsa Fahad ya yi, har da irin hakan ke ƙara masu ƙaunar juna, shima Fahad ɗin ya na yi ma Deen alkhairi duk da ya san ya fi shi kudi sosai, ko lokacin da ya fara amsar albashinsa na farko sai da ya tura ma Deen wani kaso a ciki kuma Deen ya ji daɗin hakan. Hira suka ci gaba da yi zaune saman gadon gwanin burgewa, kana kallon su ka ga zaratan maza waɗanda hutu ya zauna a jikinsu. Leemah na barin part ɗin Deen ƙasa ta sauka ta nufi ɗakinta ta shige, ɗakin ba laifi yana da ɗan girma akwai simple modern furniture, komai na cikin ɗakin kalar ruwan toka ne, kana ganin ɗakin kasan na ɗiyar masu hannu da shuni ne don harda tv stand kalar setin kayan dakin manne da madaidaiciyar plasma suna fuskantar gadon ɗakin. Kai tsaye toilet ta nufa don ta yi wanka bayan ta rage kayan jikinta, ba da jimawa ba ta fito ƙirjinta ɗaure da tawul da ya kawo mata tsakiyar cinyoyinta da suka bayyana jajur da su ko ɗan tabo babu, ba tare da 6ata lokaci ba ta hau shirya kanta. Bayan ta gama yin shafe-shafe ta gyara gashinta da yake da tsawo ga santsi, wurin ƙatuwar wardrobe ɗinta dake a jikin bango ta nufa don ta ɗauko kayan da zata saka, saida ta yi ruwan ido wurin zabar kayan da zata saka don kaya ne ciki gasu nan birjik iri- iri, ƙarshe wani baƙin lace mai adon fulawowi peach da ratsin golden ta dauko, kana ganin leshin ba sai ma an faɗi maka zai yi kuɗi ba yadda aikin jikinsa ya saƙu sosai, bayan ta saka kayan wanda fitted gown ce da ta kama jikinta daga ƙasa ta buɗe haka hannun rigar ma dogo ne daga ƙasan shi ya ɗan bude an yi ado da bakin leshin, wuyan rigar irin mai zagayayyar kwala ne, ta matuƙar yin kyau kayan sun amshi jikinta ta fito a ƴar matashiyar budurwa, duk da bata ida zama babbar budurwa ba alamun tana da diri mai kyau ya bayyana, dama jikin momynta ta biyo duk da a fuskarta akwai ɗan yanayin daddynsu amman ta fi kama da momynsu sosai, tana da tsawo sannan bata da jiki amman kuma ba siririya bace, daga yanayin jikinta akwai alamun da ta ƙara girma ko ta yi aure zata iya ƙara jiki, gaban madubi ta tsaya tana kallon kanta fuskarta ɗauke da murmushi ganin yadda rigar ta amshi jikinta, dama kayan sababbi ne bata ta6a saka su ba suna cikin kayan da aka yi masu saboda zuwan yayan su Deen, ko ƙananun kayan da suka je tarbar sa da su suma sababbi ne gal yau suka fara saka su, ɗan jujjuyawa ta yi ta kai hannu tana shafa hips ɗinta, ta ji daɗin ganin yadda suka fito, kai idonta ta yi kan ƙirjinta da suma sun fito ɗas duk da har da ƙarin bra da ta saka yasa suka cika, kallabin kayan ta shiga ɗaurawa bayan ta ɗaure gashinta da ribbom jelar ta sauka har wuce saitin kafaɗarta, tana cikin yin ɗaurin ta ji an buɗe ƙofar ɗakin, ta cikin madubin ta kai idonta wurin ƙofar, har sai da gabanta ya ɗan faɗi ganin mom ɗin su ce ta shigo, Idonta akan Leemah dake ci gaba da yin ɗaurin kallabinta ta nufo cikin ɗakin, gefenta ta tsaya tana bin ta da kallo mai cike da mamaki, sai da ta kammala yin ɗaurin sannan ta juyo ta kalli mom ɗin na su da murmushin ƙarfin hali kan fuskarta ta furta, "Mom na yi kyau ko?" Bata amsa mata ba da alamun mamaki ta ce, "To wannan ɗin na minene?" Ta yi maganar tana nuna ta daga ƙasa har sama, ɗan tura bakinta da ya sha dark peach din jambaki ta yi da yanayin shagwa6a ta ce kwalliya ce kawai ta yi, wata uwar harara ta wurga mata da alamun 6acin rai ta ce, "Ke nan wanccan mutumin ki kai ma kwalliyan?" Bata rai Leemah ta yi, "Mom ni fa kawai na yi kwalliyana ne, kuma ai ba yau na fara yi ba ko." Bin ta da kallo mom ta yi sheƙeƙe, fuska a yamutse ta ce, "Eh ba yau kika saba yin kwalliya ba, amman ba irin wadda kika saba yi ɗin ba ce ai kika yi. Wato dai zargin da nike yi a kan ki Leemah ya zama gaskiya ko! Idan ba akwai wani abu tsakanin ki da wanccan yaron ba uban miye to na yin kwalliya haka? Ko yayanki da ya ɗau tsawon lokaci bai zo ba sai yau baki yi irin wannan kwalliyar ba don tarbar sa, soyayya kike da Fahad ko!" Ta tambaya cikin kwatsa tsawa, tura baki Leemah ta yi rai 6ace ta ce, "Wai mom sau nawa zan ce maki ni ba soyayya muke yi da shi ba, kuma in ma soyayyar muke yi ai ba haramun bane tun da akwai aure a tsakanin mu..." Uwar tsawa ta daka mata ta ce, "Kar ma ki fara wannan tunanin wllh! In ma soyayya kuke yi to tun wuri ki datse ta idan ba haka ba zan datse ta da kai na, matuƙar ina numfashi ba zan bari hakan ya faru ba wllh, ai zaren bai yi daidai da kalar yadin ba, bai kai matsayin da zai iya auren ki ba!" Ta ƙarasa tana ɗan jujjuya kanta ta ƙanƙance idanunta, cikin ƙuna-ƙuni Leemah ta ce, "In haka ne, to ai kema mom ke da daddy zaren bai yi daidai da kalan yadin ba ko kuma ya aure ki, kuma ai ya Fahad bai da wani aibu yana da kyau kuma yana da aiki mai kyau sannan danginsu masu arziƙi ne, ke kuma ai dangin ku ba masu kuɗi bane amman a hakan suka amince dad ya aure ki, sai ke kuma zaki ce ba za ki amince ma wani nasu ya auri ɗiyar ki ba." Tana maganar tana ɗan ja da baya, da alama ta kashe bakin mom ɗin nasu, tsananin al'ajabin abun da Leemah ta faɗa ne bayyane akan fuskarta, Cikin murya mai kaushi ta furta, "Leemah ni kike faɗi ma wannan maganar!" Ta faɗa tare da nuna kanta da yatsa, "To ai gaskiya na faɗa ko mom, ba ta inda na fi ƙarfin ya Fahad, in ma don kina ganin daddynmu mai kuɗi ne shima ai daddynsa yana da kuɗi, ko da don kina tunanin dad ya fi abbansu kuɗi ne kin manta da cewa dad ɗin namu ƙanin mahaifinsu ne?" Wani kallon takaici mom take bin ta da shi ta yamutsa baki, Leemah na kikkafta idanu ta ƙara cewa, "In dai ina son shi shima yana sona sai mun auri jun...." Da sauri ta goce ma marin da mom ta kawo mata, tana huci ta furta, "To don ubanki, ko shi ɗanɗan ƙaruna ne baza ki aure shi ba don ba ɗan shaye-shaye na haifa ma ke ba! Sannan ko wadda take iko da ubanki bata isa ta sa ya aure ki ba balle shi uban naki! Gara ki dawo cikin hayyacin ki tun wuri." Tana ƙarasa maganar ta juya ta nufi barin ɗakin, ta san Leemah ba kunya ta ishe ta ba, in ta biye mata haka zatai ta saka ta hargowa tana ƙara ƙunsa mata bacin rai, "In har Allah Ya ƙaddara shi mijina ne sai na aure shi, ba wanda zai iya hana hakan." Ta faɗa cikin tura baki, lokacin mom ta kama ƙofa zata fita ta tsinkayi muryar Leemah, juyowa tayi cikin sakin shu'umin murmushi ta furta, "We shall seee..." Daga haka ta fuce tare da rufe ƙofar da ƙarfi ta bada sauti. Bakin gado ta nufa ta zauna dabas fuskarta a jagule kamar zata sa kuka, sam bata ji komai ba da mom ta kira Fahad da ɗan shaye-shaye, ba tun yau ba tana jin hakan saidai ita bata ta6a ganinsa ba yana shan wani abu da ya danganci haka, takaicinta ita ba ma soyayyar suke da shi ba, kawai dai tana jin wani abu a ranta game da shi wanda ta san son shi take amman shi bai ma san halin da take ciki ba. Gaba ɗaya mom ta lalata yanayin farin cikin da take aciki, ji take kamar ma ta cire kayan ta fasa fita, sai dai son ta yi hakan ya rinjaya a cikin zuciyarta. Ta ɗan ɗauki lokaci zaune tana ta ƙunci kafin daga bisani ta miƙe ta koma gaban madubin ta ɗan ƙara gyara fuskarta bayan ta gama ta ciro takalma flat kalar peach ta zura kafafunta ta nufi hanyar fita. Kiran dad da ya shigo wayar Deen ya sanar da su cewa lokacin sallar la'asar ya yi su fito su tafi masallaci ya tashe su daga hirar da suke yi. Bayan sun dawo suna shigowa falo Deen ya ce ma Fahad su je dining room ya ci abinci, suna zuwa tsakiyar falon Leemah dake zaune tana jiran dawowar su ta nufo su, ganinta ya sa su tsayawa ta ƙaraso gaban su da ɗan murmushi ta yi masu sannu da dawowa, fuskar kowannan su da murmushi suka amsa mata. "Leemah, an zama ƴan mata." Deen ya faɗa da murmushi, hannuwanta ta sa ta rufe fuska alamar kunya, buɗe fuskar ta yi suka haɗa ido da Fahad dake ɗan yin murmushi, "Ya Fahad mu je ka ci abinci gashi can na kai maka dining, tun da ka zo baka ci komai ba." Ta faɗa tana ɗan rausayar da kai. "Good, dat's why i love u Leemah, kina da hankali da sanin yakamata." Deen ya faɗa, "Amman ɗazun dad cewa ya yi wai wani lokacin nike da hankalin." Ta tura baki, da alama bata ji daɗin maganar ba, kuma ba don komai ba sai don an faɗi hakan a gaban Fahad, satar kallon shi ta yi suka haɗa ido. "Suna maki wasa ne ai." Fahad ne ya faɗa idonsa a kanta, ɗan murmushi ta yi ko ba komai ta ji daɗi da ya ɗauka wasa suke, Deen dake ta kallon su yana ɗan murmushi don ya so ya fahimci wani abu, ya ce ma Fahad su je Leemah ta yi serving na shi zai je part ɗinsa ya ɗauko wayansa ya san yana da tarin saƙonni, kuma yana son yin magana da manager ɗinsa, nufar dining room suka yi suna tafiya a jere shi da ita yayin da Deen ya nufi upstairs jikinsa sanye da farar jallabiyar da ya saka da za su je masallaci ya yi kaman balarabe... *Littafin A Cikin Rayuwa kashi na farko zai zo maku a kyauta, ga mai buƙatar kashi na biyu zai biya 500 kacal. Domin neman ƙarin bayani a tuntubi waɗannan lambobin ta hanyar aika saƙon whatsApp kawai banda kira, 09013804524, 08169856268* _Bossladieswriters_ *_✨A CIKIN RAYUWA✨_* _By Zainab Bature_ _Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._ Page 4 Bayan sun isa dining room, a ɗaya daga cikin kujerun ya zauna Leemah ta shiga yin serving na shi, bayan ta gama ta zagayo kujerar dake fuskantar tashi ta zauna, a nutse ya fara cin abincin yayin da take ɗan satar kallon sa, ita dai bata san ya akai ba komai nashi burgeta yake ba tun yanzu ba, ba kamar kwantaccen sajen shi da irin gyaran da ake mashi burgeta yake sosai, tana cikin kallon nashi maganganun da suka yi da mom ɗinta suka shiga dawo mata, jikinta ne ya yi sanyi tasan halin mom ɗinsu, idan har ta nuna bata son abu to fa ba a isa ba a yi, tasan tun da ta nuna bata son alaƙar soyayya a tsakanin su to kuwa mawuyacin abu ne in ma sun fara yi ta bari su auri juna. Ta yi nisa a duniyar tunani ya ɗago ya kalle ta, daga yanayin fuskarta ya fahimci kamar wani abu na damunta, ɗan gyaran murya ya yi shiru bata dawo hayyacinta ba, "Leemahh..." Ya kira ta da wani irin sauti, ɗan firgit ta yi ta kalle shi, "What's wrong with you?" Ya tambaya bayan ya ajiye cokalin hannunsa, ɗan kikkafta idanu ta shiga yi bata san mi zata ce mashi ba, "Tell me, mi ya faru?" Cike da nuna kulawa ya tambaya, sauke idonta ta yi tana ci gaba da kikkafta idanu, ɗagowa ta yi ta kalle shi ya kafe ta da nasa idanun alamar amsarta yake jira, motsa baki ta fara, slowly ta furta, "Mom ce..." Ta faɗa kaman zata yi kuka, shiru ya yi yana ci gaba da kallon ta, bai ji yana son ya tambaye ta abun da ya faru ba saboda ya san tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi, da wuya abun da ya haɗa ta da ita in ba akan shi bane. "Ki yi hakuri, they're our parents komai suka yi mana sai dai mu yi haƙuri, and sometimes suna yi mana abu ne for our own good." Shiru ta yi fuskarta a ɗan ɗaure, ɗage mata gira ya yi alamar ta ji, a hankali ta jinjina masa kai, murmushi ya yi tare da ɗaukar cokalin ya ci gaba da cin abincin, after a while ya ƙara dakatawa tare da kallon ta ya ce mata ta zuba abincin itama, "Na ƙoshi, bamu daɗe da muka ci ba ka zo." Ta faɗa da murmushi, "Shine ni kika tsare ni don ki ga yadda nike yin loma ki yi mani sharri?" Dariya ta yi har fararen haƙoranta suka bayyana, "Ai nasan baka yin loma Ya Fahad." Ɗan murmushin gefe ya yi kafin ya ci gaba da cin abincin, ganin ya tsaya yana ƙoƙarin zuba lemu ta miƙe da sauri ta zuba mashi, miƙa masa ta yi ya kar6a tare da yi mata godiya, bayan ya sha ya ajiye glass cup ɗin, kallon ta ya yi suka haɗa ido ya ce, "Ya school, an kusa gamawa ko?" Kai ta jinjina tare da faɗi mashi lokacin da ya rage, "Da an gama sai a ci gaba ko, mi kike son karanta ne?" Tsintar kanta ta yi da kasa bashi amsa ta bishi da ido tana kikkafta su, shiru ya yi yana nazarin ta, can ya ɗan yi murmushi slowly ya furta, "Ko aure zaki yi?" Har saida gabanta ya faɗi jin abun da ya faɗa, nan ma kasa bashi amsa ta yi, ganin kallon da yake mata ya sa ta sunnar da kanta tana ɗan motsa baki, "Leemah..." Ɗagowa ta yi ta kalle shi, "Speak your mind, ai ba laifi bane in shi kike son yi abu ne mai kyau." Motsa baki ta yi da ƙyar ta ce, "Duk abun da Allah Ya za6a mani." "Amman kin fi son ki yi aure?" Abu ta haɗiya kafin ta ce, "Ni da ko saurayi bani da Ya Fahad." Ya yi ɗan murmushi, "In kin yi saurayin za ki yi auren ke nan?" Shiru ta ɗan yi tana kallon sa tana ɗan murmushi yayin da zuciyarta ke ta tunzura ta kan ta fallasa mashi sirrinta, kai ta jinjina, ta ce, "In muna son juna." Dariya ya yi duk dimples ɗin sa suka lotsa, "Allah Ya tabbatar da alkhairi, Ya baki saurayi na gari wanda zai so ki saboda Allah ya kula mana da ke sosai." A hankali ta amsa da Amin tare da sauke idanunta, ji take kamar ta faɗa mashi cewa tana son shi saidai tana jin fargabar hakan ba kamar da yake matsayin yayanta kada ya ƙi amincewa ya kuma tsawatar mata kan hakan, a nutse ya ci gaba da cin abincinsa tana ta ɗagowa tana satar kallon shi, "Amman na yi mamakin jin baki da saurayi, yadda sister nawa take tubarkalla, ko dai ke ce baki amincewa in an ce ana son ki....? Ko da yake kamata ya yi dama yanzu ki focus kan karatun ki ba wannan ba, gashi kuma kin ce aure kike so to kuma ba boyfriend, ya za a yi ke nan?" Ya ƙare yana sakin murmushi, tura mashi baki ta yi a shagwa6e ta ce, "Ni fa Ya Fahad ba cewa na yi banson karatu ba ko, ba kai ne ka matsa in faɗi maka ba har ka ce abu mai kyau ne, ni shiyasa na ce ina so kuma na ga ko an yi aure ana iya yin karatu." "To yanzu ya zamu samo boyfriend en?" Ya faɗa yana ɗan shafa gemun shi da hannunsa na hagu, wani kallo ta yi masa ta ce, "Ai ina da wanda suke cewa suna so na, wasu yaran friends ɗin mom ne wasu kuma na dad, amman ni duk bani son su, akwai wanda nike so amman shi bai sani ba..." Ta ƙare maganar ƙirjinta na ɗan bugawa, "You should tell him.." Ya faɗa tare da ɗan ƙanƙance ido ya shigar da lip ɗin sa na ƙasa, "I'm scared he might reject me...ban so na zubar da ƙima ta." Da ƙyar ta faɗa tana ta ƴan kame-kame, ƙayataccen murmushi ya saki ya bita da wani irin kallo da yasa duk ta sha jinin jikinta, lokaci guda ta ji kallon na neman haifar mata da kasala, ta kasa tsaida idanunta akan shi sai ƴan kifce-kifce take tare da kallon ƙasa, "Bana tunanin akwai namijin da zaki furta ma hakan ya ƙi amincewa, with your beauty inside and out, I'm sure he will adore you. Kawai yanzu kamata ya yi ki maida hankali kan karatu, forget about any relationship for now, lokacin hakan zai zo, and you will meet the right person to marry " Ɗan jinjina mashi kai ta yi kafin ta sunnar da kanta ƙasa, hannu ya kai ya ɗauki glass ɗin lemu ya kai baki, a hankali yake kur6ar ruwan lemun idanun shi akan Leemah kamar mai nazarin wani abu. Bayan Deen ya dauko wayarsa, babban falon ya dawo ya zauna a ɗaya daga cikin saitin kujerun ciki, bayan ya shiga shafukan shi na sada zumunta waɗanda yake da mabiya miliyan ɗaruruwa, tarin sharhin masoyansa ya taras, a nutse yake bi yana dubawa, yawanci fatan alkhairi ne suke mashi kan ziyarar da ya kai ƙasarsa, da masu gwarzanta shi da nuna yadda suke ƙaunar shi, akwai tarin saƙonni daga wasu ƙananu da manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Nigeria suna roƙon shi da ya kai masu ziyara su yi wasa tare da shi, wasu kuma roƙon shi suke kan ya basu dama don su haɗu da shi. Yayin da yake ci gaba da bin saƙonnin, ɗan murmushi ne akan fuskarsa, wasu yana basu amsa wasu kuma ya yi liking dama shi ba mutum bane mai shariya ga masoyan sa, da wuya ya share in an turo mashi saƙo mai muhimmanci, yana matuƙar ƙoƙari wurin ganin ya samu lokaci ya bada amsa ga saƙonnin da suka dace. Duk da wasu abubuwan da yawa da suka shafi social media accounts dinsa personal manager din sa ne ke kula da su. KATSINA STATE Funtua L.G.A Madaidaicin gida ne irin wanda kana gani zaka fahimci mamallakan shi masu ƙaramin ƙarfi ne, akwai ɗakuna guda biyu masu baranda a gaban su daga 6angaren hagu, daga 6angaren dama akwai ɗaki ɗaya ware yana kallon barandar wanccan ɗakunan, idan ka shigo gidan daga ƙofar waje akwai rufaffan zaure daga ciki akwai ƙofa da taga irin ɗakin zaure, kana shigowa cikin gidan daga bangaren hagu gefen baranda anan wani ɗan ɗaki ne mara girma yana da buɗaɗɗun ƙofa da taga daga yanayin shi zaka fahimci kitchen ne, daga bangaren gefen ɗakin da ba a cikin baranda yake ba ɗan fili ne, akwai rijiya a wurin da wurin yin wanke-wanke sai wani zagayayyen ɗaki mara rufi akwai kofa a jiki da gani banɗaki ne. Gaba ɗaya tsakar gidan malale yake da siminta sannan ginin gidan bai ji jiki ba sosai. Daga can gefen rijiya wata matashiyar budurwa ce zaune akan kujera ƴar tsugunno, daga gabanta roba ce mai ɗan faɗi tana yin wanki ta gicce, ta yadda robar ba a tsakiyar kafafunta take ba a gefenta take, a jikinta tana sanye da doguwar rigar atamfa yayin da kanta ke sanye da hula daga tsakiyar kanta ya yi tudu sosai alamun tana da gashi ko kuma ƙaton ribbom ne ta saka, saidai kana kallon gaban kanta da suma ta kwanta zaka fahimci tana da gashin, yanayin kalar fatarta warm caramel ce, irin kaman wankan tarwada amman wadda ta fita daban da ake kira fata mai tsada don ba kasafai aka fiye samun masu ita ba musamman mu a nan, yadda ta juyar da fuska ta ɗan sadda kanta ya bayyanar da hancinta wanda ke da tsawo sosai tamkar an tsaga kara. Daga can gabanta saman tudunkar baranda wani matashin saurayi ne da a shekaru zai iya kai wa shekara ashirin da ukku zuwa da huɗu, duk da girman namiji in ka gan shi sai ka ce ya wuce wannan shekarun ma, jikin shi na sanye da riga mara hannu irin ta shan iska da wando tiri kwata, daga gaban shi tsakankanin ƙafafuwansa plate ɗin abinci ne dauƙe da shinkafa da wake da mai da ya ji har da salat, hannun shi na dama na ruƙe da cokali da yake cin abincin da shi yayin da hannun hagun shi ke ruƙe da waya android yana ɗan latsa ta, yana yi yana kai idonsa akan abincin in zai ɗebo ya kai baki, Wani matashin saurayin ne ya shigo cikin gidan yana sanye da singileti da gajeran wando, da alama daga cikin ɗakin zaure yake, a shekaru zai kai shekara ashirin zuwa da ɗaya, wurin inda matashiyar budurwar take ya nufa hannunshi ruƙe da wasu kaya, daga gabanta ya tsaya tare da sakin kayan ƙasa ya ce, "Salma ɗan wanke mani su yanzu ki shanya mani su bushe, muna da match anjima su zan sanya." A hankali ta ɗago da fuskarta ta jefa mashi wani kallo mai kama da harara, ma sha Allah! ganin irin kyawun fuskarta, baya ga dogon hancinta tana da madaidaitan idanuwa farare tass da su, idan ka ƙura mata idanu zaka fahimci ƙwayar idanun nata baƙin su bai ciza ba sosai ta yi ɗan kalan ruwan ƙasa, haka ma labbanta kalar su brown ne da ya ɗan ciza, da kallo ɗaya zaka fahimci kyawunta, kana ci gaba da kallonta za kai ta ƙara ganin ƙaruwar kyawun nata. "Ni fa gaskiya Sageer na gaji, duka yaushe na dawo daga makaranta, ba don uniform ɗin nawa sun yi datti ba da bama zan yi wankin ba hutawa zan yi, gashi ka kawo mani kayan ƙwallo masu dauɗar tsiya, safar ma sai wari take yi wllh." Ta ƙarasa tana kallon kayan tare da tura baki, harara ya jefa mata ya ce, "Dole ki wanke su!" Yana faɗin haka ya juya zai bar wurin, bin shi ta yi da harara, tunanin abun da zata yi ta fanshe fushinta ne ya zo mata a rai, wata ƴar dariyar gefe ta yi ta buɗe baki ta fara yin waƙa, "Delu ƙanwar maza, ta fi mazan wayau...." Idanunta akan saurayin dake zaune yana cin abinci wanda sam bai kalle ta ba kamar ma bai ji mi take cewa ba, kallon Sageer dake nufar zaure ta yi shima bai bi ta kanta ba, ganin haƙarta bata cimma ruwa ba ya sa ta ƙara ɗaga muryarta mai daɗin sauraro ta ƙara yin waƙar, "_....Ni Delu ƙanwar maza, duk na fi mazan wayou...._" Tana rufe baki matashin dake zaune yana cin abinci ya kai hannunshi ɗaya ya ciro ƙaton takalmin robar dake ƙafarsa, ɗagowa ya yi tare da saita ta ya jefo mata shi, da sauri ta goce tana dariya, shi kuwa Sageer maimakon ya fice sai ya nufi ƙofar kicin dake gefe, fitowa ya yi hannunsa ruƙe da muciya ya nufo ta yana faɗin, "Yau zaki gaya mani ubanwa kika fi wayou..." Tana ganin abun da ya ɗauko ta yi zumbur ta miƙe, miƙewar da ta yi ainihin suffar jikinta ta bayyana, sam ba gajera bace za a iya kiranta da doguwa, jikinta dum-dum bata da sirantaka sosai, daga wurin ƙugunta ya ɗan buɗe alamar tana da hips ba laifi, hakan ya sa straight gown ɗin jikinta ta fitar da shape ɗin ta gwanin burgewa, nufar wurin ƙofar banɗaki dake wurin ta yi cikin ɗaga murya ta shiga faɗin, "Wayyo Innarmu! Ga yaya Auwalu da Sageer nan zasu kashe maki ni...." Bada jimawa ba ƙofar ta fara yin ƙara alamar za a buɗe, wata mata ce ta fito daga ciki, a yanayin shekaru zata iya kai shekaru arba'in zuwa da ɗaya, sam jikinta bai nuna manyantaka ba, ta fuska ne zaka ɗan iya fahimtar hakan, tana da tsawo sannan bata da jiki, yanayin fatar ta za a iya kiranta da wankan tarwaɗa, jelar kitson dake a kanta ta sauka a tsakankanin kafaɗunta alamar tana da gashi ba laifi, akwai ɗan yanayinta a tattare da yaran dake wurin duk da tafi mazan haske don su baƙaƙe ne ba kamar Auwalun, shi Sageer ɗin ya ɗan daukko haskenta amman ita kuma Salmar tafi ma uwar haske koma in ce sam kalar fatar su ba ɗaya bane. Bayan mahaifiyar tasu ta je ta 6oye tana leƙen Sagir da ya tsaya hannunsa ruƙe da muciya ya ɗaure fuska, "Mi ya haɗa ku da ita?" Innar ta tambaya da ɗan murmushi akan fuskarta, "Innarmu ba kina jin ta ba, mu sa'aninta ne da zata rinƙa yi ma wannan waƙar!" Ya faɗa cikin fushi, "To ai da wasa take yin waƙar..." Katse Innar ya yi, "Wllh ba wani wasa, kuma mu ai ba tsaran wasanta bane, kawai don kina goya mata baya ne ya sa duk ta bi ta raina mu, ko Auwalu bata ƙyale ba balle ni, in kuma za a ɗauki mataki a kanta ki hana shiyasa ai take ci gaba da yi ma mutane iskanci." Ya ƙare yana ta hura hanci, daga bayan innar tasu ta leƙo da kyakkyawar fuskarta tana ƴar dariya ta ce, "In haka ne kaima ai ka raina yaya Auwalu ba gashi nan ko yaya baka iya ce mashi..." Bata ƙare maganar ba ganin ya yo kukan kura yana ƙoƙarin kwaɗa mata muciyar, ihu ta saka tare da ƙara ƙanƙame innar tasu kamar zata kayar da ita ƙasa ta shiga fadin, "Wallahi idan ka doke ni sai na faɗa ma aunty Kubra, ka san kuma ba ƙyale ka zata yi ba (Aunty Kubra ita ce wadda ta riƙe ta ta yi karatun primary a wurinta, kuma cousin ɗin innarsu ce, wato mahaifin innarsu yayan mahaifin aunty Kubra ne. Aunty Kubra ita da iyayenta suna zaune a garin Kaduna, saidai mahaifiyarta ta rasu, yayin da ita kuma innarsu iyayenta na zaune a nan garin Funtua, sannan mahaifin aunty Kubra dan boko ne kuma ma'aikacin gwamnati sa6anin mahaifin innarsu Salma da ba ɗan boko bane manomi ne) Dariya innarsu ta shiga yi ta tare Sageer ɗin tana cewa, "Sageer kana da hankali kuwa! Kashe min ita kake son ka yi dama kana ganin ita kaɗai Allah Ya bani yar mace...." Cikin huci muryarshi da 6acin rai ya ce, "Wallahi innarmu duk ke kika sa ta raina mu, ko muna tare da abokanmu rashin kunya take mana don ta san ba ki bari mu hukunta ta." Girgiza kai Innar ta yi tana ci gaba da yin dariya ta ce, "Duk fa yadda Salma ta kasance kai ne sila Sageer, nan yarinyar nan ta taso ba ruwanta shiru-shiru da ita magana ma sai ta kama take yi, amman ka dage sai ka canza ta kana ce mata sakarya, ba dama daga waje a yi mata abu ta yi kuka sai ka hau yi mata faɗa kana cewa in bata ramawa sai ka duke ta. Har fa yadda zata rinƙa yin dambe kake koya mata a cikin gidan nan, sai yanzu kuma da ta ɗauki horon ka ta kasance yadda kake so ka ce kuma zaka hukuntata kan hakan?" Gyaɗa kai Salma da ta leƙo da kanta ta yi alamar atoh, cikin 6acin rai Sageer ya ce, "Amman dai ai ban koya mata ta rinƙa yi ma na gaba da ita rashin kunya ba ko?" "A'a, ai Salma bata yi ma na gaba da ita rashin kunya, ku ma don kawai ta ɗauke ku kamar abokanta ne shiyasa take maku hakan matsayin wasa, kuma hada ƙarin bata da ƴan'uwa mata sai ku." Daga bayan Innar Salma ta furta, "Hakane innarmu..." Harara Sageer din ya watso mata ta saka dariya, shi dai Auwalun bai ma ƙara bi ta kan su ba ya ci gaba da cin abincin shi, dama shi ba kamar Sageer yake ba bai cika hayaniya ba sai ta kama, Sageer ne dai sarkin zuciya abu kaɗan ya fara hargowa, ko cikin abokansa baya ɗaukar rainin wayo yanzu ya dambace da mutum gashi yana da ƴar ƙirar ƙarfi a jikinshi saboda yawan ƙwallon da yake yi. Suna cikin haka aka yi sallama daga bakin ƙofa duk suka kai idanunsu wurin, wani babban mutum ne ya shigo wanda a shekaru ba zai gaza yin arba'in da biyar ba. Malam Bashir ke nan wanda shine jigon wannan iyali, da shi da matar tashi duk ba wani manyanta suka yi ba da yake irin auran wurin nan ne suka yi, mahaifiyarsu tana gama makarantar sakandare ta aure shi lokacin duka bai fi shekaru ashirin da ukku ba, lokacin da ya auri innarsu wato Fiddausy shima ya kammala karatun shi na sakandare, saidai bai ci gaba da karatu ba sai sana'ar kafintancin da yake yi wadda ta kasance gadon gidansu ce, suna da babban gareji da suke yin sana'ar shi da ƴan'uwanshi da kuma mahaifinshi wato kakan su Sageer kafin Allah ya yi mashi rasuwa, da wannan sana'ar da har yanzu ita yake yi yana da ɗan rufin asirin shi da yake kula da iyalinsa kuma daidai gwargwado yana ƙoƙari wurin sauke hakkokin su da ke kan shi. Hannunshi ruƙe da babbar leda ya shigo cikin gidan, jikinsa sanye da ƙananun kaya riga mai dogon hannuwa da ma6allai da wando irin na magidanta, amsa mashi sallamar shi suka yi ya ƙaraso cikin gidan, kallon saitin da suke ya yi innarsu na murmushi ta ce mashi sannu da zuwa ya amsa, fitowa Salma ta yi ta nufe shi da sauri, a gaban shi ta tsaya tana murmushi ta ce, "Sannu da zuwa babana." Shima murmushin ya yi ya amsa mata, "Yauwa mamana. Ya gidan? Mike faruwa na gan ku kun yi tsaye cirko-cirko?" Satar kallon Sageer da ya ƙaraso wurin tare da innarsu ta yi tana murmushi, maida idanunsa ya yi kan innarsu Salma dake mashi sannu da dawowa, amsawa ya yi tare da kallon Sageer da shima ya ce mashi sannu da zuwa, ganin yadda ya ɗaure fuska kamar bai ta6a yin dariya ba yasa baban nasu tambayar innar mike faruwa, "Ba komai, kawai ƴan diramar gidan namu ne suka fara." Yana jin haka ya gane Salma da Sageer take nufi don ya san sune koda yaushe cikin rigima suke ko don suna mabiyi da mabiyi, "Mamana mi ya haɗa ki da yayan naki.?" Dariya ta kama yi tana kallon Sageer da har lokacin ya ƙi ya saki fuska, ganin ta ƙi bashi amsa ya kalli Sageer ya tambayi mi ya haɗa su, cikin 6acin rai ya ce, "Wllh baba yarinyar nan ta raina mu, kuma in muka zo zamu hukunta ta inna ta hana, don ta ga kuna goya mata baya kuna hana a ɗauki mataki a kanta ya sa take ma mutane rashin kunyar da ta gadama." Ya ƙarasa yana hura hanci, Ƴar dariya baban ya yi jin har da shi ake zargi cikin wanda ke goya ma Salma bayan abun da take yi, "Mamana faɗa mun abun da kika yi masa." Ya faɗa yana kallon Salma da ɗan murmushi, itama murmushin take ta ce, "Wai daga na yi waƙa, kuma ni da wasa nike..." A fusace Sageer ya ce, "To mu abokan wasan ki ne? In ni kin raina ni kina ɗaukana tsaran ki duk da na baki shekaru shi Auwalun tsaran ki ne? Baba, wannan ƴar iskar waƙar take mana tana cewa wai ko ita kande ƙanwar maza duk tafi mazan wayau...ko a gidan ubanwa ta fi mu wayau, yarinyar da inda ba don na taimaka mata ba da yanzu a sakarya ta taso wllh." Gaba ɗaya suka saka dariya har Auwalu dake can gefe saida ya ɗan dara, "Mamana mi ya sa kike tsokanar su?" Ɗan kikkafta idanu ta shiga yi tana murmushi ta ce ita da wasa take yi masu. "Tun da sun nuna basu so ki daina kin ji, koda zaki yi masu wasan ki rinƙa yi masu wanda baza su ga kin yi masu rashin kunya ba, banson ana cewa mamana bata da kunya." Tana yar dariya ta ce, "To babana na daina daga yau." Ya furta yauwa, harara Sageer ya wurga mata ya ce da dai wata ba ita ba, baban nasu ya ce tun da dai ta ce ta bari yasan bazata ƙara ba, "Ka dawo an ƙi bari ka shiga ciki ma ka huta." Innarsu ta faɗa tana murmushi, amsa mata ya yi da to ya zai yi dole ya tsaya ya kashe wutar da mamanshi ta kunna, nufar wurin ɗakunan suka yi Salma na ruƙe da ledar da ya shigo da shi, yana ƙoƙarin shiga cikin barandar ya kalli Auwalu ya ce, "Auwalu an dawo daga makarantar?" Kai ya ɗaga cikin girmamawa ya ce, "Eh baba, sannu da dawowa." "Yauwa, to ba a haƙuri a ajiye wayar sai an gama cin abincin a lallatsa, ko kuwa sai ka je ka tura a cikin hanci." Ya faɗa yana ƙoƙarin tsallake tudunkar barandar, duk su Salma suka ɗan yi dariyar maganar tashi, tabarma innarsu ta ɗaukko daga cikin ɗaki ta zo ta shimfida mashi a cikin barandar, bayan Salma ta ajiye ledan, can ƙarshen barandar daga gefen kicin ta nufa, a saman wani tebur dake ɗauke da kwandunan kayan wanke-wanke ta tsaya, bayan ta ɗauki wani ɗan babban farantin roba mai kyau ta wuce cikin kicin, bada jimawa ba ta fito ta ɗauro wata kula da sauran abubuwan dake ɗauke da mahaɗin abincin a sama, gaban baban nasu ta je ta ajiye kafin ta miƙe ta koma ta ɗauko plate da cokali ta kawo mashi, sake miƙewa ta yi ta je ta kawo ruwa, bayan ta ajiye tana murmushi ta ce, "Bismilla babana ga abincinka nan, bari na zuba maka." Jinjina kai ya yi da murmushi, zuba mashi komai ta yi bayan ta gama ta ce to ga shi nan ya ci, godiya ya yi mata tare da saka albarka a nutse ya fara ci. "Yanzu dai Salma kin hana in rinƙa samun ladan kawo ma baban ku abinci, kullum yana dawowa ke ce zaki sauri ki kawo masa." Innarsu ta faɗa da sigar wasa, Salma na dariya ta ce ai itama ladan take so ta samu kuma itama ba tana samun ladan a wasu abubuwan ba, ko jiya da daddare ai ta yi mashi gugan kayan shi ko, "Ba wani neman lada, neman suna dai kawai." Sageer ya faɗa yana harararta, "Kai ka ta6a ganin inda uwa ta yi neman suna a wurin ɗanta?" Babansu da ya dakata da cin abincin ya faɗa, kafin Sageer ya ce wani abu wani ɗan matashin yaro wanda zai kai shekara sha biyar da alama shi yake bi ma Salma ya fito daga can ɗakin dake ƙarshe ya ƙaraso wurin, tsugunnawa ya yi ya ce, "Sannu da dawowa baba." Da murmushi ya amsa mashi, "Yauwa Imrana, dama kana gidan?" Kai ya ɗaga, "Eh, ina can ina yin Assignment ne ban san ka dawo ba, sai daga baya na jiyo muryar ka." Kai baban ya jinjina ya ce Allah Ya bada sa'a suka amsa da Amin. "Ina Hamza, da Usman autan baba? Su ban gan su ba." "Duk suna can suna bacci, shi Hamza tun bayan da ya dawo daga makaranta ya ci abinci ya kama yin bacci, gashi ma lokacin islamiyya ya taho dole ya tashi." Kai baban ya jinjina ya ce ya kwaso gajiyar makaranta ne shiyasa yake bacci, hannu ya kai ya ɗauki cokalin ya ci gaba da cin abincin, miƙewa Imrana ya yi zai tafi, kallon shi Salma ta yi da murmushi ta ce, "Yau ba a gayyata ta yin assignment ɗin.?" Shima murmushi ya yi ɗan kyakkyawa da shi sak komai na mahaifiyarsu ya ɗauko har haskenta, amsa ya bata da assignment ɗin baida wuya ya ga zai iya yi shiyasa bai kawo mata ta nuna ma shi ba, kai ta ɗaga mashi ya wuce. "Salma da Allah tashi ki je ki wanke mani kayan lokaci na ƙurewa gashi har so nike su bushe." Yamutsa fuska ta yi, "Allah Sageer ko na wanke su ba lalle har su bushe ba, gara ma kayan, amman wancan murtikekiyar safar bazata bushe ba, kamata ya yi ma a jiƙa ta ta kwana don ta yi dauɗa sosai har wari take yi." Ce mata ya yi to ta je ta wanke mashi kayan sai ta jiƙa safar yana da wata da bata yi datti sosai ba sai ya saka. "Kowa yana zaune yana hutawa miyasa zaka takura mata ka saka ta wanki a cikin ranar nan." Babansu da ya dakata ya faɗa, "Ai daman wankin take cikin yi na bata ta haɗa." Cikin sigar shagwa6a Salma ta ce ma baban nasu wllh haka yake takura mata ko da ba wankin take ba sai ya kawo kayan ƙwallon shi ya ce sai ta wanke mashi, harararta Sageer ɗin ya yi ya ce a da kafin a rinƙa kai kayanta wanki bashi ke wahalar wanke mata ba... "Ke nan ba don Allah ka yi ba?" Innarsu ta faɗa tana ƴar dariya. "Don Allah na yi, amman dai dole a rama ma kura aniyarta." Ganin ta ƙi tashi ta je ta yi wankin ya kai hannu zai buge ta ta miƙe da sauri, innarsu ta ce mashi shi yake ja take mashi abu kuma ya zo yana faɗin ta yi mashi rashin kunya, wucewa Salmar ta yi don ta je ta ƙarasa yin wankin..... _Bossladieswriters_ *_✨A CIKIN RAYUWA✨_* _By Zainab Bature_ _Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._ Page 5 .....Bayan Salma ta gama yin wankin, cikin barandar ta dawo, har lokacin duk suna a zaune itama ta koma gefen babansu ta zauna, hira suka ci gaba da yi don lokacin ya gama cin abincin, "Auwalu yau bazaka je can wurin aikin bane?" Baban ya tambaya idanunsa akan Auwalu dake lallatsa wayar shi shima tuni ya gama cin abincin, ɗan sosa kai ya yi ya ce mashi wllh ya dawo daga makaranta ya gaji ne yau sun sha lectures kuma gashi yana da assignment da zai yi saidai zuwa gobe in Allah ya kaimu, jinjina kai baban ya yi ya amsa da Allah Ya kai mu. "Kai Sagiru gaba ɗaya ma so kake ka watsar da karatun naka ko? Yanzu kusan fin shekara da ka kammala karatunka na sakandare amman ka tsaya shiririta ka ƙi ka maida hankali ka ci gaba." Ɗan kikkafta idanu Sageer ya shiga yi yana dan murmushi bai ce komai ba. "Shi wai nan babban ɗan kwallon ƙafa yake son zama." Salma ta faɗa, jinjina maganar baban ya yi tare da maimaita abun da aka ce yana son zama, "Dama ka tsayar da hankalinka ka yi karatu, ka dai san a ƙasar nan sai mutum yana da hanya, akwai waɗanda suka iya ƙwallo sosai, da in aka taimaka masu ba ƙananun ƴan ƙwallo zasu zama ba, amman saboda basu da hanyar hakan gasu nan sun kare da bugawa a cikin unguwanni suna wahala basu samun komai." Auwalu ne ya faɗa cikin nuna girma. "Ka ji abun da ɗan uwanka ya faɗa, don haka ka daure ka ci gaba da karatun ka kada a yi biyun babu, idan Allah Ya ƙaddaro zaka zama abun da kake so ko ba yanzu ba zaka zama, amman yanzu ka yi ta zama haka nan bai kyautu ba, ga ɗan uwanka nan ya dage da karatu kuma yana zuwa wurin sana'a, amman kai gaba ɗaya ka ƙi ka maida hankali kan sana'ar sosai. Rayuwa gudu take yi nan da ɗan lokaci kaɗan zaka ga an kai munzalin tara iyali, gara tun kan lokaci ya ƙure ma mutum ya samu madogara, don ajiye iyali bai yuwuwa ba tare da mutum yana da hanyar da yake samu ba, in kuwa ba haka ba mutum ya ce zai tara iyali ba wata ƙwaƙkwarar sana'a tabbas zai jefa kan shi a matsala babba, wahalhalun rayuwa su taru su yi mashi katutu, ina amfanin mutum ya tara iyali madadin ya ji da su dadi sai su ƙare da shan wahala." A nutse Sagir ya ce, "In sha Allahu zan maida hankali in ci gaba da karatun, dama ina jira a fara sayar da form na Jamb zan siya in yi." "To Allah Ya bada sa'a. Ku daure ku dage wata rana zaku ci ribar karatun, tun da mu bamu samu muka yi ba shiyasa muke son ku ku yi. Duk da Alhamdulillah, dai dai gwargwado da sana'a Allah Ya rufa mana asiri, amman in mutum ya haɗa da aikin zai fi wadatuwa, ita kanta sana'a in aka haɗa da ilimi tafi faɗaɗuwa, mutum zai ƙara sanin hanyoyi da dubarun da zai inganta sana'ar ta samu karbuwa ba a iya inda yake ba a fadin duniya baki daya." Duk sun natsu suna sauraren shi, ba tun yanzu ba ya saba zama ya yi masu nasiha kan abun da zai amfani rayuwarsu, akwai kyakkyawar mu'amala tsakanin shi da iyalan nashi, "Ke mamana ba zaki siya form na Jamb ɗin bane.?" Kai ta ɗaga mashi ta ce, "Eh, abun da nike son karanta ba sai an yi ta ba." "Ita ka san Auntynta Kubra take so ta gado, itama karatun aikin jinyar take son yi, a yadda ma suka tsara can Kaduna zata je ta yi karatun in ta ci jarabawa." Kai mahaifin nasu ya jinjina jin bayanin innarsu Salma yana murmushi, "To sai ki dage, duk da nasan baki wasa da karatu. Allah Ya yi maku albarka, Ya baku sa'ar duk abun da kuka saka gaba na alkhairi, Allah Ya ƙara shiryar da ku a bisa tafarkin manzo (S.A.W)." Gaba ɗaya suka haɗa baki wurin amsawa, "Ameen." Kowanne fuskarsa ɗauke da murmushi, suna matuƙar jin daɗi in mahaifin nasu na yi masu addu'a haka. "Yau baza ku yi awaran bane?" Auwalu ne ya tambaya yana kallon Salma, kafin ta bashi amsa baban nasu ya ce, "Af, ka ga na shafa'a ma, Sagir jeka waje akwai sauran katakai dana tattaro masu suna nan a bayan mashin." Cike da jin daɗi Salma ta ce yauwa dama tafi son yin amfani da sauran katakan akan gawayi. "Amman mamana ai gawayin kaman ya fi sauki ba hayaki ko?" Ta ce matsalar gawayin in ya cinye sai mutum ya ta saukewa yana girgijewa ya ƙara, shi kuwa icce ko katako kawai sai dai ta iza. Shigowa Sagir yayi hannuwan shi ruƙe da katakan da aka ɗaure, a gaban kitchen ya ajiye Salma na ganin su da ɗan yawa ta fara washe baki, "Gasu nan, amman waɗannan biya na za a yi gaskiya, sai in ta kawo abu ana yin sana'a amman ba a bani komai, kuma nima ai siyo katakon muke yi." Dariya duk suka yi jin maganar baban. "Amman ai kana cin awaran ko, kullum sai an ɗibar maka mai yawa, sannan kuma idan babu wasu abubuwan kamar magi da gishiri da sauran abun abinci ba Innarmu take badawa ba a siyo, watarana ma har abincin da za a dafa take bayarwa a siyo." Salma ta faɗa tana dariya, hannu baban nasu ya kai ya ruƙe ha6a ya ce, "Tohh, abun yau gori za a mani ke nan." Suka saka dariya gaba ɗaya, "Yau mun ji tsakanin ku, gashi nan duk yadda ka ke ji da ita amman ta yi maka gori." Hararar Sagir da ya yi maganar Salma ta yi ta ce, "To an ji, kanwa uwar gami." "Ba abun da ya shiga tsakaninmu, ai tsakanin uwa da ɗanta sai Allah." Ƴar ƙarar daɗi Salma ta saka ta fara yi ma Sagir gwalo tana fadin an gwasale shi. Hira suka ci gaba da yi cikin nishaɗi gwanin burgewa, sallar la'asar da aka fara kira ya tashe su, baban nasu ya yi masu sallama don komawa wurin aiki daga can in ya yi salla, suma kowa ya miƙe. Malam Bashir ya kasance mutumin arziki ba ga iyalinsa kaɗai ba, hatta mutanen da yake mu'amala da su suna yi mashi shaidar hakan, shi ɗin abun koyi ne ga duk wani magidanci mai iyali, rayuwar shi da iyalan shi ta kasance abun bada misali. Duk da bashi da wadata sosai amman yana da wadatar zuciya sosai, a ganin malam Bashir in har mutum zai tara iyali ya bari rayuwarsu ta tagayyara to miye amfanin tarawa, kullum ƙoƙarin shi ya wadata iyalansa ta bangaren abinci da sutura, gaba ɗaya yaran shi sun fita daban a cikin layin su, tun tasowar su haka zaka gan su tsaf-tsaf cikin sutura ta kirki bai barin su cikin tsumma, ta bangaren karatunsu da lafiyarsu nan ma a tsaye yake yana bakin ƙoƙarin shi, shi yasa sam yaransa basu da damuwar komai, tun tasowar su ba a ta6a kama su da laifin sun ɗauki abun wani ba saboda sun wadata, itama mahaifiyarsu ba zaune take ba tana yin ƴan sana'oin da take tallafa ma mijin nata sun taru sun rufa ma kan su asiri. ABUJA. Tun bayan gama sallar magrib su Leemarh suka fara yin shirin tafiya dinner da aka haɗa ma Deen. Tsaye yake gaban dresser idanunsa na kan madubin gaban shi yana gyara zaman waistcoat ɗin jikinsa, wato irin riga mara hannuwa da ake ɗaurawa saman riga ƴar cikin suit mai kaman falmara bayan ya saka ta cikin baƙa mai dogon hannuwa, yayin da Fahad ke can gefe saman kujerar gaban gado ya ɗan zamo jikinsa yana latsa wayarsa, shima da alama ya shirya yana sanye da baƙaƙen suit sai salƙi suke, daga gaban kayan zuwa ƙasan hannunsa farar rigar ciki ta fito don bai saka ma6allan kayan ba, yayin da wuyansa ke sanye da necktie baƙi, damtsen hannun shi ya ɗaura silver din agogo itama sai salki take, haka ƙafafunsa ya saka dress shoes wato rufaffun baƙaken takalma da suka matuƙar ƙara ƙawata shigar tashi, a kallo ɗaya in ka yi masa zaka yanke hukuncin yana daga cikin matasan Abuja da suka taso cikin hutu da jin daɗi saboda yadda shigar ta amshi jikinsa, sumar kansa da ta fuskarsa sun sha gyara sun kwanta luf. Shigowa ta yi cikin ɗakin ko sallama babu, motsin da Fahad ya ji ya saka shi ɗaga ido ya kallo ta suka haɗa ido, mom ɗin su Deen ce ta shigo, da alama itama ta shirya tana sanye da wata jigunanniyar abaya maroon mai duhuwa, kallo ɗaya in ka yi mata sai ka firgita da kyaun da ta yi a cikin rigar, ta matuƙar amsar jikinta farinta ya fito sosai wani fayau, saman kanta ta naɗa gyallen rigar yayin da fuskarta ta yi makeup har da janbaki kalar rigar wato maroon, ƙafafunta tana sanye da takalma half cover masu dan tsini kalar aikin rigar wato golden, haka hannuwanta ta riƙe purse wadda da gani mahaɗin takalman ce itama golden, ta dai yi kyau sosai ba ƙarya. Cikin ɗakin ta shige ba tare da ta ƙara kallon in da Fahad yake ba, shima ganin bata bi ta kansa ba yasa shi maida kan shi ya ci gaba da danna wayarsa ba tare da ya tanka mata ba, gaba ɗaya ɗakin ya ƙara karaɗewa da ƙamshin turarenta sai ka ce ba matar aure ba, kuma a haka zata je ta shiga cikin mutane, wurin da Deen yake ta nufa tana tafiya cike da isa da izza, tun da ta taho Deen ya hango ta ta cikin mudubi har ta karaso ta tsaya daga bayan shi ta gefen shi, haɗa ido suka yi ta cikin madubin ya ɗan yi mata murmushi, itama shi ta mayar masa kafin ta maida idanunta akan sumar gemun shi da yake ƙara gyarawa sai ƙyalli take, ganin bata yi mashi magana ba yasa shi maida hankali kan shirin shi, wani box mai kyau dake ajiye a saman dresser ɗin ya ɗauko ya buɗe, kan shi kwalin abun kallo ne balle kuma abun da ke a ciki, saida ya cicciro wasu fararen takardu masu kauri kaman kati da wani mai kaman ɗan littafi kafin ya kawo in da abun da ke ciki yake, wata rantsattsiyar agogo ce ya fiddo silver bayan ya warware abun da aka naɗe ta da ita, nan take ta fara walainiya da gani ba sai an faɗa ba sabuwa ce lokacin aka fara buɗe ta kuma jikinta ya bayyana mai tsada ce, yana ƙoƙarin ɗaura ta a hannunsa mom ɗin shi ta matso tare da miƙa mashi hannu alamar ya bata, dakatawa ya yi ya bata ta shiga jujjuya ta a hannunta, "Amman da gani agogon nan zata yi tsada sosai ko?" Ta tambaya tana ɗage gira, kai ya ɗaga mata tare da faɗi mata kuɗinta, ɗan waro idanu ta yi jin miliyoyin da ya faɗa. "Ku dai ƴan ƙwallo da alama kuɗin ku duk a wurin siyan kaya masu tsada suke tafiya, komai ka siya sai a ji shi da uban kuɗi!" Ta ƙare da alamun mamaki, murmushin gefen fuska ya saki still ta cikin madubin yake kallon ta cikin sautin muryan sa mai daɗi ya furta, "Ta hakan muke samun wasu kudin." Da alamun rashin fahimta ta ce, "What do you mean...?" "Kaman muna yin talla ne, and, wasu kamfunan muna da hannun jari in aka gani a jikin mu za a siya kayan, sannan muna ƙara samun followers saboda gayun." Ya ƙarasa yana ɗan murmushi, jinjina kai ta yi idonta akan shi yana ta ƙara gyara zaman bowtie ɗin wuyan rigars, "Suma followers ɗin biyan ku ake da su ko?" Kai ya jinjina mata alamar eh, "Wato harkar ƙwallon nan dai ba ƙaramin kuɗi ake samu da ita ba, ba kamar in mutum ya ɗaukaka, shi yasa na so a ce ka taimaka ma Omar shima ya zama kamar kai amman ka ƙi bada goyon bayan hakan." Ta faɗa da ɗan alamun bacin rai, hannunsa guda akan gemunsa yana ƙara gyara sumar wurin da alama dai yana ji da ita, a taƙaice ya furta, "Ba abun a tare da shi ne." Yamutsa fuska mom ɗin ta yi, tun farko lokacin da ta nuna tana son Omar ya zama kamar shi ya faɗi mata cewa bai da baiwar hakan don ya gwaggwada shi, ko ya fara yin ƙwallon ba inda zai je. "To shi Adam fa? Shima ka ƙi ka ɗaura shi a hanya kuma yana son zama ɗan ƙwallo sosai, kuma shi dama ko a Kano yana bugawa, har tura shi na yi London wurin ka amman shima still baka goya mashi baya ba." Shiru ya yi jin tana magana akan ƙaninta, ko ta ina zai zama wani babban ɗan ƙwallo mutumin da babu abun da ya sa a gaba sai shiririta tuni ya kashe rayuwar shi da shaye-shaye har da neman mata. "Ka yi mani shiru!" Ɗan yamutsa fuska ya yi, "To mi zan ce mom? I thought mun gama wannan maganan since." Ta6e baki ta yi, a hankali ta juya ta kallo wurin da Fahad yake, saidai bata hango shi ba a inda ta gan shi zaune da alama fita ya yi daga cikin ɗakin, juyowa ta yi a cikin ranta tana ayyana daga ganin kayan da ta gani a jikinsa masu tsada ne sosai. "Can i have it?" Ya faɗa tare da miƙo mata hannu alamar ta bashi agogon. "Suma su Omar ka kawo masu kayan ne?" Ɗan yamutsa fuska ya yi ba tare da ya bari ta gani ba don ya gane saboda kayan da ta gani ne a jikin Fahad ya sa ta yi mashi tambayar. "Bai nuna maki bane?" Ya faɗa yana ɗaura agogon, yamutsa fuska ta yi ta ce, "Yea na gani, Allah Ya sa masu kuɗi ne ka siyo masu, don na san ka iya fifita bare akan jininka." Wani guntun murmushin gefe ya yi, wai ya iya fifita bare, ko waye baren? Ya faɗa a cikin ransa, ganin ta kafe shi da ido fuska a haɗe ya sa shi ɗan juyowa ya kalle ta ya ce, "You can google to check their prices." Daga haka ya wuce can wurin closet ɗin shi ya shige, bai ɗauki lokaci ba ya fito daga ciki hannunsa ɗaya rataye da navy blue ɗin jacket ɗin kayansa yana tafiya cike da ƙasaita saidai shi ba da wani abu yake yin hakan ba haka tafiyarsa take, haɗaɗɗun rufaffun takalman kafarsa wanda su kan su miliyoyin naira suke sun ƙara fito da kyawun shigar tashi, sai faman baza ƙamshi mai narkar da zuciyar wanda ya shaƙa yake, wurin ta ya nufo ya tsaya daga gabanta yana ƙoƙarin saka jacket ɗin, bayan ya gama saka ma6allan mom ɗinsa da ke ta faman bin shi da ido ta ce, "Kyau a ce Basmah tana a gefen ka, da sai gayun naka ya fi fitowa." Lokaci guda ya ji wani abu ya ziyarci ransa mai kama da 6acin rai, ya yi shiru bai ce mata komai ba, "Duk da ka ce wai saboda makaranta yasa baka taho tare da ita ba, da ka so ai zaku iya tahowa duk da hakan, I don't know why baka bata muhimmanci yadda yakamata, and she's your fiancee yakamata ace kuna samun kusanci da ita sosai ko ina ya kasance kuna tare, kamar yadda zaka ga wasu sanannun mutane suna nuna matan da suke so, ko za su aura, amman kai bana tunanin ma an san da ka tsaida matar da zaka aura." Shiru ya yi yana ta kallonta har ta gama maganar, a ransa ya ayyana matar dai da aka tilasta masa ya aura, ƴar ajiyar zuciya ya sauke ya ɗan yamutsa fuska ya ce, "Mom, yanzu ya za ai a ce duk inda nike mu kasance tare da ita, is that even possible? Kuma miye amfanin mutum ya yi ta bayyana ma duniya ga wadda zai aura? I think idan lokacin da zamu yi auran ya yi dole za a sani no need sai na bayyana hakan yanzu." Ganin yanayin da fuskarsa ta nuna kaman bai ji daɗin maganan ba ya sa ta sassauta muryarta ta ce to amman ai ko nan ɗin da sai ya taho da ita su ganta tun da sun kwana biyu basu gan ta ba, ci gaba da saka ma6allan rigarsa ya yi, ya bata amsa da idan lokacin da suke zuwa vacation ya yi za su zo ne sai su ganta, ta yi sototo tana kallon sa don duk wasu alamu na rashin son ya kusanta kan shi da Basma sun riga sun bayyana, sai dai ta sha alwashin matuƙar tana raye bashi da mata in ba Basma ba, kallon ta ya yi bayan ya gama daidaita rigan a jikin shi, ɗan murmusi ya yi mata tare da ɗage gira ya ce, "Can we go?" Ƴar harara ta wurga mashi ta ce wato ta zo ta ishe shi da haushi ko, still murmushin ne akan fuskarsa ya ɗan lanƙwasa mata hannunshi, tana ganin haka ta ɗan saki murmushi ta saƙa nata hannun a cikin nasa kamar yadda turawa saurayi da budurwa suke yi suka nufi hanyar barin ɗakin, duk da kasancewar mom ɗin tasu mai tsawo kuma ga takalma masu tsini amman sai gashi Deen ɗin ya ɗara ta tsawo ko don tana mace. Bayan Fahad ya fito daga part ɗin Deen, kai tsaye matattakalar bene ya nufa don sauka ƙasa, a natse yake taka matattakalar daidai ya kai tsakiya sai ga Leemarh ta ƙaraso zata hawo benen, a kusan tare suka tsaya cak suna kallon juna, wato ni kaina na girgiza da ganin matuƙar kyawun da ta yi, abun ka da farar mace kuma sai ta yi shigar red hakan ba ƙaramin kyau ta yi a cikin shigar ba, doguwar rigar ɗanyen jan material ce ta saka, rigan straight gown ce ta kamata hakan yasa shape ɗin ta ya fito, hannun rigar na material ɗin ne ba a saka wani abu a ciki ba hakan yasa ana hango jikin hannun nata amman ba sosai ba don daga yanayin material ɗin yana da ɗan kauri, sosai material ɗin ya haɗu duk da bashi da kwalliya sosai wasu gashi-gashi ne a jikin shi masu salƙi daga gani zai yi taushi, a hannunta hadaddiyar purse ce silver sai takalman ƙafarta mahaɗin jakar ne, duk da ba gajera bace takalman nata masu tsini ne irin wanda daga sama suke da maɗauri, a wuyanta yar ziririyar sarƙa ce tare da ƴan kunnayenta sai ka ce na diamond wataƙil ma su ne, a hannunta guda ta ɗaura agogo itama silver, a saman kanta jan head ne wanda ba irin yadin material din bane wani material din ne daban, shi kan shi ɗaurin ba ƙaramin kyau ya yi ba, ɗauri mai steps aka yi mata ta yadda daga gaban kan gashinta da aka tsaga tsakiya ya ɗan fito an faka shi ta baya, musamman ƙwararriyar mai yi masu make-up ta zo ta yi masu ta kuma shirya su. A hankali suka shiga sakar ma juna murmushi ba tare da sun motsa ba, Fahad ne ya ci gaba da saukowa idon shi akan ta har ya iso bakin benen ya sauka ƙasa, fuskantar juna suka yi sam kowa ya kasa magana sai murmushi kawai, "Who could resist this beauty?" Bayan ɗan lokaci ta ji Fahad ɗin ya furta, kunya ce ta kama ta don ta fahimci dalilin da ya sa ya faɗi haka, saboda maganar da ta yi masa lokacin da yake cin abinci na akwai wanda take so amman tana tsoron ya ƙi amincewa in ta sanar da shi, shine yanzu ya yabe ta ta hanyar cewa 'waye zai ƙi wannan kyawun?" Hannunta guda ta sa ta ɗan rufe fuskarta alamar kunya, ga jan lallen da aka yi mata dama na zuwan Deen mai kyau mara yawa ya bayyana ya yi ja shar gwanin burgewa. "Kin yi kyau sosai. U look like a bride." Cire hannun da ta rufe fuskar ta yi, tana murmushi ta ce, "Thank you ya Fahad. Kai ma ai ka yi kaman ango." Ɗage gira ya yi ya ce ango da irin shigan shi, "Eh, kaman groom ya yi shigan dinner." Ɗan faffaɗan murmushi ya yi ya ce, "To ko angon ne? Dama gashi shigan dinner ɗin na yi, amman kuma ba bride en, ko idan muka je sai in samu a can?" Ƴar dariya ta yi ta ce, "Ya fi dai ka tafi da amaryan." Dariya ya yi dimples dinsa suka lotsa, ya riga da ya gama fahimtar ta, da hannu ya yi mata alamar su je cikin falon, suka jera suna tafiya a nutse sai ka ce ango da amaryan yadda suka dace, duk da Leemarh ba wata babba bace amman shigar da ta yi ta ƙara mata girma. Saman kujera mai mazaunin mutum biyu suka zauna suka ɗan karkata ta yadda suke fuskantar juna, hira suka shiga yi yawanci shine ke mata tambayoyi akan karatun ta da wasu abubuwan. Lokacin da suka ƙaraso bakin matattakalar Deen ya saki hannun mom ɗin nashi suka fara saukowa, suna kaiwa tsakiyar benen idanun mom suka sauka akan Fahad da Leemah dake ta hirar su cikin nishaɗi suna ta murmushi, wani baƙin ciki ne ya tokare mata maƙoshi ta ɗaure fuska tamkar ta ga wani mugun abu, a cikin ranta ta shiga cin alwashin sai ta raba su koda a ce ba soyayya suke ba sai ta kawo ƙarshen wannan shirin nasu don ba shi take haifa ma yaran ba da kowa zai rinƙa shiri da shi suna son shi sosai, kafin su ƙarasa safkowa ƙasa Batool ta fito daga hanyar bangaren su itama doguwar rigar material ce a jikinta ruwan madara, an yi mata makeup itama an gyara mata gashinta ya sauko har bayanta an ɗaura mata net ya yi kaman hula ta fito a yar matashiyar mace yar shekara sha biyu, tana hango su mom ɗinsu ta ambaci sunanta tare da nufar wurin su, a tare Fahad da Leemah suka juya jin sunan mom da Batool ta kira, miƙewa suka yi ganin sun nufo cikin falon, wata muguwar harara mom ta shiga wurga mata, Leemarh ta yamutsa mata fuska tana ɗan tura baki, wani irin ƙamshi ne ya gauraye wurin kasantuwar kowa da kalar abun kamshin da ya shafa, murmushi Fahad ya shiga sakar ma Deen ganin yadda ya yi kyau sosai, shi kan shi ya burge shi, hannu ya ɗan dunƙule ya miƙa ma Deen shima ya yi ma nashi hakan suka ɗan buga irin gaisuwar gayu, Fahad ya ce, "You are looking sharp! You are the GOAT, on and off the pitch!" Yar dariya Deen ya yi jin yabon da Fahad ɗin ya yi masa har yana kiransa da suna mai matuƙar girma wanda samun sa ba ƙaramin aiki bane a duniyar ƙwallo, amsa ya bashi da, "Tukunna dai, Ya Fahad." Ya faɗa tare da ɗan jinjina kai yana murmushi. "Ya Deen, in sha Allah you are going to break all the records, trust us you are going to be the GOAT (Greatest Of All Time)" Leemarh ta faɗa tana murmushi, ita kanta gayun na shi ya tafi da ita, dama ba tun yanzu ba sun san yayan nasu da iya ɗaukar wanka, wanda har da hakan ke ƙara mashi masoya musamman mata ba ƙaramin tafiya yake da imanin su ba, gaba ɗaya duk suka amsa ma maganar da Leemah ta yi suma suka furta in sha Allah har da mom ta furta ƙasa ƙasa, yana murmushin jin daɗi ya yi masu godiya. Suna haka sauran yan gidan su Omar da Sultan duk suka fito suma duk wankan suit suka yi sun yi kyau ma sha Allah, daga ƙarshe Dad ɗin su shima ya fito daga bangarensa ya nufo cikin falon jikinsa sanye da suit ruwan toka, sosai kayan suka amshi jikinsa ya fito a babban mutum mai ƙwarjina da haiba, duk idanunsu na akan shi fuskokinsu ɗauke da murmushi har ya ƙaraso wurin su shima yana masu murmushi, "Wow! Gaskiya dad ka tashi kaina! Ka gan yadda ka yi kyau sosai?" Leemarh ta faɗa ta ɗan buɗe ido, yana murmushi ya yi mata godiya ya miƙo hannu ya ɗan rungumo ta ta gefe. "Dad, wllh ka yi kaman su ya Deen." Batool ta faɗa tana dariya tare da noƙe kai, itama ya janyo ta jikinsa yana yar dariya ya ce mata ke nan ya koma ɗan saurayi, ta ɗaga mashi kai tana dariya. "Ki ce wataƙil ma wata ta yaba da wankan nawa in samo maku aunty a can ke nan." Duk suka saka dariya ban da mom da ta hade fuska, ya saci kallonta bayan ya yi maganar suka haɗa ido ta wurga mashi harara, ɗan murmushi ya yi shima yasan ya faɗa ne kawai. "Are we good to go?" Dad ya tambaya yana kallon Deen da murmushi ganin yadda ɗan nashi ya yi kyau sosai, kallon agogon hannunsa ya yi kafin ya kalli dad din ya ce mashi zasu iya tafiya kusan lokacin ya yi, gaba ɗaya suka nufi hanyar barin falon suna tafiya cikin natsuwa, kana kallon su ka ga waɗanda hutu da jin daɗi ya zauna musu sosai. Tuni an jera motocin da za su tafi da su a gaban entryhall, bayan sun fito aka shiga bubbuɗe masu, Deen da Fahad wata haɗaɗɗiyar baƙar Mercedes S-Class ce suka shiga sai uban sheƙi take irin na sabunta, motar tashi ce ba a jima da kawo ta ba kafin ya zo, dama akwai wasu motocin da ake amfani da su a gidan waɗanda shine ya siye su, dad da mom ɗinsu suma mota ɗaya suka shiga sai sauran yaran har da Omar suka shiga cikin wata ƙatuwar baƙar jeep, tsaye Leemarh ta yi har saida ta ga mom ɗin su ta shiga cikin mota sannan ta yi saurin nufar motar su Deen ta buɗe kofar baya za ta shiga, Fahad da Deen dake zaune a bayan a tare suka kalle ta, ta ɗan yamutsa fuska ta sigar shagwaba ta ce masu a motar su take son tafiya, ɗan murmushi Deen ya yi ba tare da ya ce komai ba ya fito daga bayan ya yi mata alamar ta shiga da hannu, shi kuma ya koma kujerar gaban motan ya shiga, bayan duk sun gama shiga a tare aka tashi motocin suka nufi hanyar gate abun gwanin sha'awa, dama ga su duka motocin baƙaƙe ne sai sheƙi suke yi, daga bayan su kuma motar jami'ai ce ke take masu baya...... *_✨A CIKIN RAYUWA✨_* _By Zainab Bature_ _Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._ Page 6 Zaune suke a tsakar gida bayan sallar isha, da yake yanayin zafi ne ba a cikin barandar suke zaune ba, daga gaban ɗakin dake kallon barandar wanda ɗakin Salma ne a nan suka yi shimfiɗa, dama duk in ana zafi anan suke zama don ya fi iska, gaba ɗayan su suna zaune akan ƙatuwar tabarma suna cin abinci, Salma tare da innarsu suke cin tuwon gaban su sai ɗan autansu dake manne a jikin innar tana bashi a baki, daga gefen su Imrana ne tare da Hamza suma suna ci a wuri guda, gefe daga gaban su yayan su Auwalu ne zaune akan tudun baranda shima tuwon yake ci a cikin plate da cokali, sun natsu suna cin abincin jefi-jefi suke yin magana banda Auwalu da ya tattara hankalinsa akan wayar shi, da alama ya yi sabo da yana cin abinci yana latsa waya. Suna tsaka da cin abinci suka jiyo ƙarar kwaramniyar kwanuka kaman daga cikin kicin, da dan ɗaga murya innarsu ta tambayi waye a nan. "Ƙilan awakan gidan su Bello ne suka shigo." Imrana ya faɗa da tuwo a bakin sa. "Ba wasu awakai, mai hankalin gidan ne, ina ganin lokacin da ya shigo daga cikin zaure ya shige kicin." Salma na faɗin haka suka fahimci Sagir take nufi, fitowa ya yi ya nufo su jikin shi daga shi sai gajeran wando ko vest babu, hannun shi ya ruƙo wata yar madaidaiciyar kular abinci, tsaye ya yi akan su fuska da alamun 6acin rai ya ce, "Wai fisabilillahi baza a yi ma mutane abinci ba sai wannan? Da me mutum zai ji, da zafin da ake kokuwa da wannan da zai danƙara ma cikinsa?" Gaba ɗaya dariya suka saka banda Auwalu da hankalinsa na akan waya, itama innarsu ɗan murmushi ta yi ta ce, "To da yake ma ba wanda aka ma dole ai sai ya ci ko?" Yamutsa fuska ya ci gaba da yi yana mitar kullum ai ta abu ɗaya sai ya kashe mutum. "Amman yaya Sagir ai ba ko da yaushe ake yin tuwo ba da daddare, ko shekaranjiya ba taliyar hausa yaya Salma ta dafa ba muka ci da daddare..." Imrana ne ya faɗa tare da kai lomar tuwo bakinsa. "To ubanwa ya tambaye ka! Kuma ba an fi yin tuwon ba, sai a jera kusan sati ana yin shi kafin a canza wani abun. "Ai dama baka wahalar da bakinka ba Imrana, ko ka faɗa ba yarda zai yi ba, ka san shi da gardamar tsiya kaman makahon jaki, in banda sharri ko yaushe ake yin sati ana yin tuwo...." Salma da ta ɗauko maganar bata ƙarasa ba Sagir dake niyyar zama a gefen Auwalu ya aje kular tuwon hannunsa ya yo kukan kura kanta, yana zuwa ya tangare mata ƙeya da ƙarfi har saida hular kanta ta cire, tufkar kitson shaden dake kanta ta baje har gadon bayanta, a fusace ya ce mata uban waye makahon jakin! Da sauri ta janye jikinta gefe tare da kare kanta tana dariya ta ce, "To ai dai bani na fara faɗan haka ba ko, innarmu ce ke cewa ka cika gardama kamar maka...." Kanta ya yo yana fadin, "Wllh kika ƙara faɗar maganar nan sai na fasa maki baki!" Innarsu dake dariya ta ce mashi kada ya sake ya ƙara ta6a ta, rai a bace ya ce to ta ce ma Salmar kada ta ƙara ce mashi haka in ba haka ba sai ya gota ta Allah, kallon Salma ta yi ta ce mata kada ta kara faɗin haka ta gyaɗa kai tana ta dariya, ƙwafa Sagir ɗin ya yi ya koma inda ya ajiye tuwon ya zauna ya fara ci, ganin yadda yake ta buga loma Salma dake kallon shi cike da tsokana ta ce, "Ah, man Sagir ya na ga kana ta buga loma kuma, ai na yi zaton tun da ran ka bai son tuwon zaka ɗan tsakura ne kawai don dole..." Ganin yana laluben takalmi yasa ta yi shiru ta 6oye a gefen innarsu tana ƙyalƙyata dariya, cikin ɗan ɗaga murya innarsu ta ce mashi kada ya jefo masu takalmi cikin abinci, fasa ɗaukar takalmin ya yi ya ci gaba da cin tuwon yana yi yana leƙo abun da Auwalu ke kallo a wayarsa. "Yau mutumina Habu bai leƙo ba da daddare." Salma ta faɗa tana ci gaba da cin tuwon, "Ai gara ma da bai zo ba, ni wllh bani son yana zuwa, kullum bai tashi zuwa sai lokacin da muke cin abinci kamar ya san lokacin da ake gama mana abinci, kuma duk in ya zo innarmu sai ta bashi abincin, wani lokacin ma in babu sai ta kwashe cikin namu ta bashi." Imrana ne ya yi maganar yana tura baki, da ɗan murmushi innar tasu ta ce, "Ai yanzu ma in ya shigo babu tuwon, cikin naku zan ɗebar mashi..." Da sauri ya ce, "Kam, Allah ni dai ba za a ɗibar mashi ba, in kuma mu bamu ƙoshi ba fa, saidai yaya Salma ta bashi dama ita ta saba haƙura da abincinta in ya shigo babu ta bashi har ta ce ya je su ci shi da ƙannanshi..." "Munahukar ba, tana nuna kamar ita ta Allah ce mai tausayi, dama tun da wurin soya awara tana samu ta ci ta ƙoshi ta kuma zame wasu cikin cinikin ta siya abun da take so ba dole ta rinƙa yin neman suna da abincinta ba." Sagir da ya maido da hankalinsa akan su ya faɗa yana ci gaba da cin tuwon gaban sa. "Kai Sagir! Banda sharri, ba wata awara da Salma ke ci, kuma koda ta ci sai ta sanar mani, sannan ko ta nawa na saka mata haka zata kawo mani kuɗina daidai ba tare da ta ɗauki ko naira biyar ba sai in ni ce na bata. Ita haka Allah ya yi ta da tausayi abun ta bai dame ta ba, kuma hakan abu ne mai kyau don duk abun da ka bada shine naka, idan kana badawa sai Allah Ya yi ta buɗa maka shi yasa itama bata rasawa, ko ban bata kuɗi ba bata rasa ƴan kuɗaɗenta da zata siya abun da ranta ke so cikin wanda Auntynta Kubra ke turo mata." Murmushi kawai Salma ke yi jin abun da innarsu ke faɗa game da ita, mita Sagir ɗin ya ci gaba da yi yana faɗin dama bata ganin laifinta shiyasa zata ce haka amman shi ya san tana cinye mata awara kuma tana zarar kuɗi cikin ciniki. "Bara Ubannan...!" Bayan ɗan lokaci Suka ji Sagir ɗin ya furta tare da ƴar zabura idon shi akan wayar Auwalu, "SubhanAllahi! Sagir wane irin furuci ne haka? Mi ya faru?" Ɗan girgiza mata kai ya yi yana washe baki ba tare da ya kalle ta ba ya ce mata ba komai, a ƙagauce ya ce ma Auwalu, "Wai mutumin har ya iso ke nan?" Kai Auwalu ya ɗaga masa alamar eh, a ɗokance Sagir ɗin ya ci gaba, "Wllh ni ban san ya iso ba, nasan dai da maganar zai zo Najeriya, da yake tun jiya ban hau online ba banda data, ɗazun kuma ban samu zuwa fili da wuri ba kuma match zamu buga ina zuwa muka fara dama ni ake jira shiyasa na san ban ji zancen zuwan nashi ba." Yadda yake maganar kana gani zaka fahimci ba ƙaramin dadin zuwan wanda yake magana akai ya ji ba, "Waye kuke magana akai ne?" Innarsu ta tambaya, da sauri Sagir ya bata amsa da, "Tauraron ɗan ƙwallon mu na ƙasar waje Nuree Jr." Bin shi ta yi da ido ta ce shine yake ta wannan rawar jikin? "Ba zaki gane bane innarmu, ina mugun yin shine wllh, bama ni kaɗai ba, yanzu a duniyar kwallo yana ɗaya daga cikin taurarin dake lokaci, mutanen da basu haɗa komai ma da shi ba sun mutu akan shi balle kuma ni..." Da yanayin mamaki Salma ta ce, "To kai ɗin ma wani abun ka haɗa da shi ne?" "Ah! Ka ji yarinyar nan, ai kuwa na haɗa wani abu da shi tun da ɗan ƙasata ne ƙarewa garinmu ne tushen shi, uwa uba kuma gidansu a unguwarmu yake." "Wai ba jikan Hajiyar Ambasada ɗan kwallon nan kake magana ba?" Innarsu ce ta tambaya, ya bata amsa da shi fa. "Ma sha Allah, ka ce dai shima ya ɗaukaka..." Auwalu ne ya ɗago ya bata amsa, "Daukaka sosai ma, don yanzu dai a duniyar ƙwallo yana ɗaya daga cikin waɗanda ake ji da su ake kuma maganar su saboda ya iya ta sosai.." Sagir ya yi saurin kar6ewa, "Ai tukunna ma dai, ko na yi rantsuwa ba zan yi kaffara ba Nuree Jr nan gaba ba ƙaramar shahara zai yi ba sai ya samu title din GOAT in sha Allah. A yanzu ma da ba wasu shekaru sosai ya ɗauka a duniyar kwallon ba ya fara breaking records, ko gasar Champions league da ba a daɗe da gamawa ba team din su ne suka ƙara ci, kuma shi ya ƙara samun kyautar Golden boot wato kyautar ɗan kwallon da ya fi zura kwallo a raga, kuma ba wannan ne na farko ba dama ya taba samu ban da wanda ya samu a gasar premier league, haka bayan kammala kakar wasannin bara ya samu Ballon d'or nomination, duk da bai samu kyautar ba, amman in sha Allahu muna saka ran zai samu bada daɗewa ba in dai ba an saka son kai ba kasancewarsa ɗan Africa ...." Haka ya ci gaba da faɗi ma innar tasu nasarorin da Nureen ya samu daban-daban, gaba ɗaya ma ya dakata da cin tuwon, ita dai Salma tana ta cin tuwon ta don abun da suke magana a kai ba damunta ya yi ba hasalima in suna hirar ƙwallon a gidan wani lokacin a ɗakin su na soro su da abokansu yadda suke hargowa da waƙe- waƙe haushi suke bata ta ji kamar ta je ta hau su da bugu. "Allah Ubangiji Ya ƙara ɗaukaka shi Ya kare shi. Ni da yake ba sanin ta kan kwallon na yi ba ban san haka ya shahara ba, kawai dai na san ana faɗin ya iya ta sosai ba kamar lokacin da ya ci ma Nigeria wata ƙwallo bansan dai ko wacce ba ce akai ta maganar shi..." Innarsu ta faɗa bayan Sagir ya gama bata labarin. "AFCON kike magana, wannan gasar zakarun nahiyar Africa ce da ake yi duk bayan shekara biyu, itace ya taba ci ma Nigeria, sai kuma gasar cin kofin duniya FIFA World cup, itama ya ta6a buga ma Nigeria sau ɗaya duk da basu yi nasara ba amman sun yi ƙokari sosai don sai da suka kai har quaterfinals wato mataki na biyun ƙarshe..." Auwalu bai kai ƙarshen maganar ba Sagir ya kar6e, "Ai duk kokarin da suka yi a lokacin shine ya yi shi, to lokacin ma bai kai gogewar da ya yi yanzu ba, nasan yadda ya ƙara ƙwarewa muna da hope din in sha Allahu a gasar cin kofin duniya da ke zuwa nan da shekara ɗaya zai ci ma Nigeria bi'iznillAh...Ai Nuree ɗan baiwa ne a ƙwallo, nima ina fatan wata rana in zama kamar sa, koma ban kai shi ba nima dai ina roƙon Allah Ya sa in zama shahararran ɗan kwallon kafa.." Innarsu na murmushi ta amsa mashi da Amin Ya Allah in hakan alkhairi ne a gare shi, Auwalu ma ya amsa da Amin kafin ya ɗaura da fadin, "Shi Nuraddeen harda farinjini da Allah Ya yi masa, yana da kyau na fuska da jiki ma sha Allah, bana tunanin akwai ɗan ƙwallon da ya kai shi kyau sai dai ko a samu mai irin ƙirar jikinshi amman dai kyawun fuska gaskiya da ƙyar ne." Cikin washe baki Sagir ya ce, "Ai kyaun fuska dai babu ma, kuma Nuree akwai physique, he is strong, powerful and fast, in ya kama ƙwallo ba kyau, Allah dai ya haɗa mashi komai wllh, gashi yanzu shima yana cikin jerin ƴan ƙwallo masu samun kuɗi sosai, kuma ba laifi yana da alkhairi, tun da ko da ba anan yake zaune ba yana tallafa ma mutane musamman matasa ta gidauniyarsa. In sha Allahu wannan karon sai na yi yadda na yi na samu na yi magana da shi tun da na san tabbas sai ya zo nan garin, ina son ya bamu shawarwarin yadda zamu inganta harkar ƙwallon mu ya kuma taimaka mana yadda za mu ci gaba." Amsa mashi Auwalu ya yi da Allah Ya bashi iko, ya ɗaura da faɗin amman dai hakan da wuya don ya san dole ya kasance cikin tsaro sosai, ita dai innarsu murmushi kawai take in ya yi addu'a ta amsa mashi da Amin, ita kuwa Salma tuni har hirar tasu ma ta fara gundurar ta ta fara yamutsa fuska, ƙarshe ma miƙewa ta yi bayan ta gama cin tuwon ta tafi wanko hannu. Abuja. Mutane ne tsaitsaye cikin harabar katafaren tsadaddan hotel ɗin sun kewaye Deen bayan da suka isa, kowa ka gani fuskar sa a washe suna ta gaisawa da shi, ba wasu mutane sosai don dinner din private ce iya masu ruwa da tsaki a harkar ƙwallo da manyan masu muƙamai ne za su halarta sai makusantan su kamar iyalansu da sauran su, duk wanda ka ga ya samu zuwa to yana da hanya da wani babba a harkar ƙwallo ko kuma shima wani babban ne a ƙasa. Bayan sun gama tarbar shi suna niyyar shiga cikin hotel ɗin ƙarar jiniya ta dakatar da su kowa ya kai idanun shi kan babban gate ɗin hotel din wanda daga nan ƙarar jiniyar ke fitowa, kai tsaye jerin wasu motoci na gani na faɗa gaba ɗayan su baƙaƙe ne suka shigo, wadataccen hasken wurin ya haske su sai sheƙi suke yi, motocin jami'ai ne a farko sai wasu manyan jeep guda ukku a ƙarshe wata motar jami'ain ce ta rufo masu baya, suna tsayawa jami'an suka shiga dirowa suna nufar ɗaya daga cikin jeep ɗin, yayin da wasu jami'an masu ƙirar ƙarfi suka ja layi tun daga farko har zuwa ƙarshen motocin gaba ɗaya jikinsu na sanye da kaki sun riƙe bindigu, idanun minista akan motocin tun kafin wanda aka buɗe mawa ya fito ya gane ko waye sakamakon ya san da sun kai mashi katin gayyata kasantuwar shi masoyin ƙwallon ƙafa ne sosai kuma yana yin Deen, "It's vice-president." Minista ya faɗa tare da ɗan kallon Deen yana murmushi, kai ya jinjina mashi shima da ɗan murmushin, bayan an buɗe ma mataimakin shugaban ƙasan ya fito jikinsa sanye da baƙaƙen suit, gaba ɗaya manyan mutanen wurin har da Deen suka matsa don su tarbe shi, cike da girmamawa suka shiga gaishe da shi tare da yi mashi sannu da zuwa fuskarsa da murmushi yake amsa masu, daga baya ya maida idanunsa kan Deen bayan ya dafa kafaɗarsa ya yi mashi sannu da zuwa ƙasar tare da yabonsa, bayan gama gaishe- gaishe kai tsaye suka nufi shiga cikin hotel ɗin, jami'ai ne a gaba sai Deen da Minister da VP na a biye, daga bayan su dad ɗin Deen ne tare da wasu abokansa ƴan majalisa, daga bayan su wasu daga cikin masu ruwa da tsaki ne a harkar ƙwallo sannan su mom ɗin Deen, Leemah na jere da Fahad sauran mutane suka rufa masu baya, yayin da ƴan jarida ke ta aikin ɗaukar rahoto, wani abun burgewa tun daga in da aka tarbo Deen din har zuwa ƙopar shiga cikin hotel din red carpet ne aka shimfida suke tafiya a sama wanda hakan ke nuna Deen wani mai muhimmanci ne. Wurin da za a yi dinner ɗin ballroom ne wato babban ɗaki kamar hall da akan yi a manyan tsadaddun hotels, saidai irin wurin ya fi tsaruwa fiye da irin hall da aka saba yin hidindimu, ɗakin an kawata shi don yin taruka na musamman, kana shiga wani irin ni'imtaccen sanyin Ac ne zai tarbe ka, tun daga kan ginin ɗakin zuwa kan yadda aka tsara shi da decoration abun kallo ne ga wanda bai saba tsintar kansa a irin wurin ba, adon da aka yi a ciki mai aji ne ba mai hayaniya ba kalar na taron waɗanda suka jiƙu da kuɗi, suna shiga sauran mutanen da ke a cikin wurin gaba ɗaya suka maido idanuwansu kan hanyar shigowar suna masu mararin ganin tauraron ɗan kwallon, lokacin da ya shigo wasu har da miƙewa fuskokinsu ɗauke da murmushin farin cikin ganin sa, nan fa aka shiga ɗaukar shi hotuna da vedio, a nutse yake ɗaga ma mutane hannu yayin da suke nufar cikin wurin, jami'an dake tsaron su na biye da su wasu daga gaban su wasu a gefe da gefe yayin da suke nufar wuri na musamman da aka ware ma manya, irin tsarin zaman cin abinci aka yi ma kujerun wurin wato tebur a tsakiya sai kujeru a zagaye da shi gaba ɗaya an lullu6e su da yadi kalar decoration din wurin, daga saman kowanne tebur an yi ado da fulawoyi masu kyau saman ɗan stand da aka yi ma adon wasu sarƙoƙi masu ƙayatarwa, wurin da aka ware ma su Deen za su zauna na daga gaba. A can babban gate ɗin shigowa hotel din jami'ai ne sun kasa sun tsare suna bincike mutanen dake shigowa cikin hotel ɗin, koda baka daga cikin waɗanda za a gudanar da dinner din sai an bincika ka, a bakin kopar shiga ɗakin da za a yi taron nan ma wasu samudawan jami'ai ne jikinsu da hannuwansu ɗauke da manyan makamai yayin da rabin fuskarsu ke a rufe iya idanuwansu ne ake iya gani wanda ko haɗa ido da su ka yi sai ka shiga taitayinka, duk wanda zai shiga wurin sai an bincike shi tun daga sama har ƙasa saboda tsaro. Ba tare da 6ata lokaci ba bayan dinner guests ɗin kowa ya zauna an natsu mai girma ministan wasanni ya fara jawabi bayan ya miƙe an bashi lasifika, cikin harshen turanci ya fara bayanin dalilin taruwar su,"Ladies and gentlemen, distinguished guests, it is our pleasure to welcome home our very own football superstar, DEEN JR.!" Ya ƙare maganar tare da dafa kafaɗar Deen hakan ya sa shi miƙewa tsaye fuskarsa cike da annuri, gaba ɗaya ɗakin ya ɗauka da ƙarar tafin mutane. Ministan ya ci gaba da cewa, "Your achievements on the pitch have brought joy and pride to our nation. Tonight we gather to celebrate your success and express our gratitude for being an inspiration to our youth." Ya ƙare maganar idon shi akan Deen yana yi mashi murmushi. Shima Deen murmushin yake na jin daɗin yabon da ministan ke yi masa, yayin da mutane suka ƙara saka tafi, cikin natsuwa yake ɗaga ma mutane hannu alamar ya ji daɗin tafin da suke masa. Bayan ministan ya gama jawabin nashi mai girma mataimakin shugaban ƙasa shima ya yi wanda yabo ne da kalaman ƙarfafa guiwa ya yi ma Deen, haka wasu a cikin masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa suma suka yi nasu jawabin wanda yabo ne akan irin ƙoƙari da jajircewar Deen a harkar ƙwallo da kuma yadda yake saka ƙasa alfahari. Bayan gama duk jawabe-jawaben aka fara ciye-ciyen abinci da abubuwan makulashe, daga can bangare guda na cikin ɗakin anan aka jere iyayen kayan abinci da masu aikin zubawa da rarraba ma mutane jikinsu sanye da uniform, sai abun da mutum ke so za a kawo mashi a cikin abubuwan cin abinci da kofuna na ƙawa sai walainiya suke, kowa saida aka zuba mashi duk abun da yake so duk da haka masu aikin raba abincin nata zagayawa suna tambayar mutane ko akwai abunda suke so akawo masu, iyayen Deen na daga can gaba daga bayan inda su Deen suke a zaune, Fahad da Leemarh da Omar suna a wuri guda gefe da su mom ɗinsu, an natsu ana ta ciye-ciye baka jin ƙarar komai sai ta cokulla dake haɗuwa da plate ɗin ƙarau, kowane tebur bayan kayan abinci an ajiye masu kwalin tissue mai kyau don goge hannu da baki, kowa ka gani fuskarsa cike da annashuwa wasu suna ci suna ɗan yin hira, kamar Fahad da Leemarh suma suna cin abincin suna ɗan ta6a hira, suna haka ta ɗan debo ta kai bakin shi yana murmushi ya buɗe baki ya amsa, itama ya ɗebo ya kai bakinta hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba dama saboda tana son ya bata a bakin yasa ta fara bashi, duk abun da suke mom ɗinsu na kallo baƙin ciki ya turnuke ta kamar ta je ta shaƙe Fahad take ji, gaba ɗaya fuskarta ba walwala ta haɗe rai, lura da yanayinta da ya canza da kuma saitin da take yawan kallo ya sa dad shima ya juya ya kalli wurin su Fahad ya ga yadda suke ba juna abinci duk da a lokacin shi har da Omar ya ga Leemarh ɗin ta ba abincin a baki hakan ne ya sa shi bai fahimci miye dalilin da ya sa mom ɗin daure fuska haka ba. Bayan an yi nisa da fara cin abinci wasu ma har sun gama ci don abu ne na ƴan gayu da yawa ba wani sakin baki suke su yi ta cin abinci ba, wasu abu kaɗan suke tsakura shike nan sun ƙoshi tun da dama an saba cin mai dadi sa6anin talaka bawan Allah wani abincin sai dai ya gan shi a hoto sai kuma idan Allah Ya ci da shi ya tsinci kansa a hidima irin ta masu hannu da shuni ya samu ya ci. Kwatsam! mutane suka ga hasken cikin ɗakin ya ɗauke, har hayaniyar mutane ta ɗan fara karaɗe cikin ɗakin ana tambayar abun da ya faru suka ga an kunna wasu ƙananun fitulu ba masu haske ba sosai a can sama, basu gama mamakin dalilin ɗauke ainihin hasken wurin ba suka ga wani hasken mai yawa ya fara bayyana daga can sama yake saukowa ta gaban ɗakin taron inda mutum ke hawa in zai yi bayani ko za a nuna ma mutane wani abu ko bada kyauta, lokaci guda suka fahimci screen ne da alama wani abun za a haska mutane su kalla kamar dai a cinema, fahimtar abun da ke faruwa yasa hankalin mutane ya kwanta kowa ya natsu yana jira ya ga abun da za a haska, wani mutum ne da alama m.c ne ya fara magana ta cikin lasifika ya ba mutane hakuri kan rashin sanar masu abun da za a yi ya ce hakan cikin bazata ne, nan ya sanar dasu cewa za a haska wasu daga cikin performance ɗin Deen ne a fagen ƙwallo, gaba daya ɗakin aka saka tafi raf, raf, raf murmushin farin ciki ya bayyana akan fuskokinsu. Wasu daga cikin manyan gasannin ƙwallo da ya buga kuma ya yi nasara aka shiga haskawa, nan fa ɗakin ya karaɗe da tafi da sowar mutane, tamkar a lokacin ake buga ƙwallon, idan ya ci haka zaka ji wasu sun saka ihu suna faɗin, 'Goallllll!' gaba ɗaya wurin sai ya koma kamar stadium kamar a nan take ake buga ƙwallon ba haskawa ake ba, kowa idonsa na akan screen, tuni masu cin abinci sun daina hankulansu sun koma can, shima Deen idonsa na akan screen yana kallo yana ta sakin faffadan murmushin jin dadin irin yadda mutane ke ta faɗin kalaman yabo kan yadda ya iya ƙwallo, wasu daga cikin matan dake wurin musamman ƴan mata ba wai yadda yake yin ƙwallon bane ke burge su don wasu ma ba masoya kwallon bane kawai shi Deen ɗin ne yake burge su, tun bayan fara taron wasu cikin yan matan dake a wurin idanunsu na akan duk wani motsin shi, hatta iyaye mata da wasu da yawa daga cikin mazan duk burge su Deen yake yi. Bayan an gama kallon perfomance din sa sai kuma aka shiga haska mabambantan lokutta da aka bashi kyaututtuka a harkar kwallon, daga karshe aka yi replaying wuraren da ya ci ƙwallo daban-daban in slow-motion, gaba ɗaya ɗakin ya ƙara harmutsewa da hayaniyar murna, ba kamar ƙwallon ƙarshe da ya ci a extra time a gasar cin kofin zakarun nahiyar africa wato AFCON wadda ita ce ta saka Nigeria yin nasara. Bayan an gama haskawa, hasken ɗakin ya dawo lokacin Deen din ya mike smiling humbly, sauran mahalarta taron ma duk suka miƙe suna mashi tafi fuskokinsu dauke da murmushin farin ciki, manyan mutane dake a kusa da shi suka shiga shaking hand da shi wasu suna patting bayan shi suna taya shi murna da kuma fatan alkhairi a harkar shi ta ƙwallo. Daga baya minister da sauran football officials suka karrama shi ta hanyar bashi lambar yabo tare da yi mashi godiya kan irin gudunmawar da yake ba harkar wasanni a Nigeria. Bayan karrama shi shima ya yi godiya cikin turancin shi mai dadin sauraro, "....Thank you everyone for this incredible honor. I'm proud to represent Nigeria on the global stage, and I'm committed to continuing to make our country proud." Gaba ɗaya aka saka tafi, daga baya ya yi godiya ga iyayensa da ƴan'uwanshi kan goyon bayan da suke bashi da yadda suke ƙarfafa mashi guiwa ya bayyana hakan na daga cikin sirrin nasarorinsa, daga karshe ya yi godiya ta musamman ga ɗan'uwan sa mafi soyuwa a gare shi wato Fahad, ya bayyana shi a matsayin mutumin da ya fara fito mashi da baiwar shi ta ƙwallo, ya ce duk da da bai manta yadda ya sha wuya a hannunshi ba in suna yin ƙwallon a cikin compound ɗin gidansu ya yi ta sa mashi kafa yana kayar da shi wani lokacin har ya yi fushi ya ce ba zai ƙara yin ƙwallon da shi ba, ƙarshe haka zai lalla6a shi ya rarrashe shi su ƙara yi kuma hakan ba zai hana ya ƙara cutar shi ba, ya ce sai dai a yanzu ya fahimci ba cutar shi yake ba a lokacin yana molding nashi ne to become who he is today, yana bayanin yana yin ƴar dariya idanunsa akan Fahad da shima yake yin dariyar, haka ma sauran mutanen dake saurara wasu dariya ce akan fuskokinsu wasu kuma faffaɗan murmushi, idan ka cire mom da ta tsuke fuska sam bata ji daɗin yadda yake yabon Fahad ba a gaban jama'a har da wani kiran shi dan'uwan shi mafi soyuwa a gare shi, kalmar ta matuƙar ƙona mata rai. Bayan Deen ya gama jawabin nashi shima Fahad ya miƙe ya yi kalaman yabo kan irin ƙoƙari da jajircewar dan'uwan nasa tare da yi mashi fatan alkhairi, daga nan shima Deen ya ba wasu daga cikin manyan da suka haɗa mashi dinner ɗin kyautar jerseys ɗin kungiyarsu mai ɗauke da lamba 7 da yake bugawa, daga baya aka shiga ɗauke-ɗauken hotuna tare da shi. Leemah na tsaye gefen Fahad bayan an yi masu hotuna da Deen wasu ƴan mata da suka gaji da haɗuwa suka ƙaraso wurin suna tafiya sai ka ce masu jin tausayin taka ƙasa, sun sha gayu da matsattsun dogayen rigunan lace ko mayafi babu da takalma masu uban tsini, kana ganin su ka ga ƴan mata zubin Abuja da alama ƴaƴan wasu manya ne a wurin, tun bayan da aka fara yin dinner ɗin hankalin ɗaya daga cikin su yake kan Deen don ba ƙaramin son shi take ba duk in za a yi kwallo da shi sai ta kalla, yau ne karo na farko da ta fara ganin shi a zahiri hakan yasa gaba ɗaya ya tafi da imaninta, a matuƙar ƙagare take da ta samu damar da zata yi magana da shi, ita kuwa ɗayar tun da ta ɗaura idanunta akan Fahad lokacin da Deen ke yabon shi ta ji ta afka kogin son shi, hakan ya sa suka yanke yin amfani da damar da suka samu ta yin hotuna da su sai su yi masu magana, cikin salon jan hankali budurwar dake son Deen ɗin ta ce mashi pls bari su yi hoto ya amsa mata da ok don duk wanda ya zo zai yi hoto da shi yana bashi dama duk da akwai jami'ai dake zagaye da shi don tsaron shi, lokaci guda Leemarh ta tamke fuska ganin ɗayar tana ma Fahad wani murmushi ta ce mashi tana son zata yi hoto da shi, aikuwa ba zato sai ji ya yi Leemah ta kama hannun shi ta riƙe gam, maido idanunsa ya yi kanta ya ga ta wani haɗe fuska tana farfari da idanuwa, ɗan murmushi kawai ya yi bai ce mata komai ba ya janye idanunsa, wani kallo budurwar ta yi ma Leemah don duk tana ganin abun da ke faruwa, fuskar budurwar ba yabo ba fallasa ta ce ma Leemah ta dan yi excuse nata za su yi hoto tare da Fahad, ta sakar mata wani kallo mai kamar harara ta ce mata ai bata hana ba ga wuri nan ta nuna mata gefenta, hakan ba ƙaramin ƙular da budurwar ya yi ba don sai ta ga ta ci mata fuska gashi tana ganinta ba sa'ar ta ba, ƙarshe dai dole a gefen Leemah ɗin ta tsaya aka yi masu hoton, sam Leemah ta hana kowace mace damar yin hoto da Fahad dole sai ta shiga tsakani, hakan ya sa wasu suka fara tunanin ko budurwarsa ce ita, ga shi ba yadda za a yi da ita don kana kallon fuskarta ba sai an faɗa maka ba zaka fahimci ƙanwar wanda aka yi taron domin shi ce don suna kama da Deen sosai, shi dai Fahad murmushi kawai yake ganin irin ƙarfin halinta. Alhamdulillah, dinner ta tashi lafiya kowa yana cikin farin ciki musamman masoyan Deen waɗanda ya kasance yau ne rana ta farko da suka fara yin tozali da shi har sun samu damar yin magana da kuma yin hotuna da shi. Kan ka ce mi tuni hotunan dinner ɗin sun karaɗe kafofin sada zumunta mutane nata tofa albarkacin bakin su, wasu daga cikin masoyan Deen da magoya bayan club ɗin shi ƴan Nigeria nata cika bakin wllh da sun san da za a yi dinner ɗin sai sun je ko da bala'e kuma sai sun shiga..... *_✨A CIKIN RAYUWA✨_* _By Zainab Bature_ _Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._ Page 7 ......Sanye da rigar bacci robe irin mai buɗaɗɗen gaba wadda ake ɗaurewa tsawonta iya gwiwa Deen ya fito daga cikin walk-in closet ɗin shi ya nufo cikin ɗakin yana tafiya a nutse da alama ya gama yin shirin kwanciya sai ƙamshi jikinsa ke saki, gadonsa ya nufo ya zauna daga gefe idon sa akan Fahad dake a kishingiɗe shima ya yi shirin kwanciya jikinsa sanye da pajamas, waya ce riƙe a hannunsa yana lallatsawa, a hankali ya ɗago idanunsa ya sauke su akan Deen suka yi ma juna murmushi, "Na yi zaton zan iske ka ka yi bacci saboda gajiyan dinner." Deen ya faɗa yana gyara zaman shi ya ɗan haye saman gadon kafarsa guda na a ƙasa, idon Fahad akan shi da ɗan murmushi ya ce, "Ba wani gajiya ai, kaine ma ke da gajiya an sha fama da mutane, yakamata by now ka yi bacci ka samu hutu sosai." Hannu Deen ya kai ya shafi yalwatacciyar sumarsa dake ta salƙi da alama a daren ma sai da aka gyara ta, "Da muka dawo ya ɗauke ni time ina duba saƙonni, amman yanzu zan kwanta ɗin." Kai Fahad ya jinjina mashi. "Gobe zamu tafi Funtua tare ina son je in ga sweety hajjanah." Ya faɗa da ɗan faffaɗan murmushi, "Da wuri haka, na yi tunanin zaka bari sai bayan kwana biyu in ka huta sosai." Fahad ya faɗa yana kallon shi. "No, gara mu tafi kawai, ko na tsaya ba wani hutun da zan yi, I received a lot of invitations from different football clubs, duk suna son in je mu tattauna game da yadda suke wasa. So, ina son in yi honour wasu daga cikin invitations ɗin kafin na koma." Kai Fahad ya jinjina masa, jin alamar shigowar mutum ya sa gaba ɗaya suka kai idanunsu kan ƙofar shigowa, mom din Deen ce ta shigo cikin ɗakin jikinta sanye da jar silky doguwar rigar bacci da ta fito da ƙirarta sosai kanta ta yafa ƙaramin baƙin gyale, nufo cikin ɗakin ta yi tana tafiya cike da isa yanayin fuskarta a ɗan ɗaure, tun kallo ɗaya da Fahad ya yi mata ya ɗauke idonsa tare da mayar da su akan wayar hannunsa, idon Deen na akanta cikin ransa yana ayyana ko miye dalilin zuwan ta ɗakin shi a irin lokacin, daga gefen shi ta tsaya ta bi Fahad da wani irin kallon rashin arziƙi wanda shi bai ma san tana yi ba idon shi na akan wayarsa, "Mom, baki yi bacci ba?" Deen ya tambaya yana kallonta, maido idonta ta yi kansa ta ƙara ɗaure fuskarta. "Ai kai zan ma wannan tambayar, mi kake baka yi bacci ba, kai da ka kwaso gajiya amman wani ne a kwance saman gadon kai a zaune!" Yadda ta yi magana ya bayyana ta ji haushin ganin Fahad da ta yi a kwance saman gadon, kallo Deen ya bita da shi ya ɗan yamutsa fuska ganin ta kafe shi da ido alamar amsar shi take jira, kamar bazai ce komai ba don ya ji haushin maganarta sai dai gudun kada ta ƙara kwa6o wata baƙar maganar ya sa shi cewa, "Ba wani dalili ya sa na zauna ba ni ke ra'ayin hakan, na tsaya yin wani abu, da kin zo bayan yanzu za ki iske ni a kwance ne." Daga yanayin yadda ya yi maganar ta fuskanci alamun bacin rai akan fuskar sa, ɗan ta6e baki ta yi ba tare da ta ce komai ba ta fara tafiya zata bar ɗakin, sai da ta yi taku biyu zuwa ukku ta dakata tare da juyowa ta kalli Deen da ya bita da kallo, cike da bada umarni ta furta, "Fallow me, I want to talk to u. " Daga haka ta ci gaba da tafiyarta, ɗan jim ya yi kaman ba zai tashi ba, kallon Fahad ya yi da har lokacin bai ɗago ba, shiru ya ɗan yi ya ma rasa mi zai ce mashi don duk da bai ga yanayin fuskarsa ba ya san dole maganar da mom ɗin ta yi ta 6ata masa rai, hannu ya kai ya ɗan ta6a ƙafar Fahad dake gefen sa ya furta, "Ina zuwa ya Fahad." Kai kawai Fahad ya jinjina masa ba tare da ya kalle shi ba, zuro gudar ƙafarsa ya yi ya sauka daga gadon ya bi bayanta. A hankali Fahad ya ɗago ya bi hanyar fita daga cikin ɗakin da kallo yanayin fuskar sa da ɗan alamun bacin rai, a cikin ransa yana jin ɗacin irin abubuwan da matar take mashi, shi dai ya san bai ta6a yi mata wani laifi da ya cancanci wannan tsanar ba daga gare ta, duk da ya san halinta ne bashi kaɗai take ma hakan ba amman nashi ya fi tsanani, sam bata son shi da Deen ga shi Allah Ya saka masu ƙaunar junan su kuma ga zumuncin da Allah Ya halarta a tsakanin su, ba don haka ba ai da tuni ya rabun mata da ɗa. Maida akalar tunaninsa ya yi kan Leemarh, daga abun da ya faru yau a wurin dinner ya tabbatar mashi da yarinyar son shi take kamar yadda yake hasashe, duk da shi bai ta6a tunanin ya yi soyayya da ita ba, amman in har ta bayyana mashi hakan to tabbas ba zai ƙi amince mata ba, duk da a yadda take ta yi mashi ƙaranta da kalar matar da yake son aura, a yadda yake so ya auri budurwa babba irin wadda ta gama karatun jami'a koma take aiki, amman duk da hakan yana jin zai iya auran Leemarh don tana da duk wani abu da namiji zai so a tare da mace, saidai ta ya hakan zai yuwu a tsakanin su a irin yadda mahaifiyarta ta tsane shi? Ana yin aure ne don samun farin ciki da natsuwa, amman baya tunanin hakan zai samu matuƙar aure ya kasance tsakanin shi da Leemarh, ƙarshe ya san madadin hakan ya ƙara masu danƙon zumunci yana iya lalata zumuncin wanda shi sam ba zai so hakan ba. Ahalin su babban family ne da suke da zumunci mai ƙarfi, suna da kyakkyawar alaƙa da kuma fahimta ba zai so a ce ta sanadiyyar auren su ba an zo an samu 6araka, don a yadda ya san rashin mutuncin mom Jameela to zata aikata abun da zai iya haddasa a samu babbar matsala matuƙar bata son hakan. Yin wannan tunanin ya sa shi fara tunanin hanyar da zai bi wurin ganin Leemarh bata furta mashi kalmar so ba duk da zai so a ce ya cika mata burinta, saidai baya tunanin hakan mai yuwuwa ne gara su haƙura kawai ko don a zauna lafiya. Bayan daukar ɗan lokaci yana tunane-tunane, saukowa ya yi daga saman gadon ya mike tsaye, cikin ɗakin ya nufa walking slowly, wurin da madaidaicin fridge yake ya nufa ya buɗe, bayan ya ɗauko lemu ya dawo cikin ɗakin riƙe da shi, a bakin gadon ya zauna har zai fara buɗe marfin lemun sai kuma ya dakata kamar yana ɗan tunani, wani abu yake son ɗaukowa a cikin motar shi sai dai yana tunanin ko su Deen na a cikin falon bai son ya je ya ratsa su suna magana, ɗan jimm yay can ya miƙe tare da ɗaura roban lemun a saman durowar gefen gadon, sai da ya buɗe durowan farko ya fiddo makullin mota kafin ya nufi ƙofar fita. Cikin sa'a bai iske su a cikin falon ba, har ya nufi ƙofar fita ya tuna da akwai wata kofa ta cikin falon da zata fidda mutum ta bayan gidan ta fi sauƙi zuwa inda parking space yake, juyowa ya yi ya nufi ƙofar cikin sa'a da makulli a jikinta ya buɗe ya fita. Lokacin da Deen ya fito ya yi tunanin zai ga mom ɗin ta shi a cikin falonsa amma sai ya ga akasin hakan, hanyar fita ya nufa da tunanin ko bangarenta ta koma, tsaye take ta ɗaura hannuwanta a saman ƙarfen bene idanunta na kallon cikin ƙaton falon na su dake a ƙasan bene ta haɗe rai, "Mom..." Ya furta bayan ya ƙaraso ya tsaya daga gefenta, shiru bata amsa ba bata kuma juya ta kalle shi ba, "Kin ce kina son magana da ni." Ya sake faɗa yana mai kallon ta ta gefe, a hankali ta juyo da fuskarta ta kalle shi kafin ta ƙarasa juyowa gaba ɗaya tana fuskantar sa, "Wai mike damun ka ne Deen?? Ta faɗa da amon bacin rai, ɗan buɗa idanunsa ya yi alamar rashin fahimta, ba tare da ta jira cewar sa ba ta ci gaba, "Har sai yaushe ne zaka dawo cikin hankalinka ne ka rinƙa yin abu yadda ya kamata?Yaushe ne zaka daina cutar kanka ka daina prioritizing buƙatun wasu fiye da naka? Yaushe zaka gane cewa wasu mutanen ba kamar yadda kake ɗaukar su bane, ba don Allah suke tare da kai ba face don amfanin kan su ba kamar saboda baiwar da Allah Ya yi maka, da zarar sun gama cin moriyar ka za su guje ka ne. I have been trying to make you understand all these things over and over again, but you just don't get it! Yakamata ka dawo cikin hankalinka, Deen!" Idanunsa akanta har ta gama maganganun nata, sai dai shi sam ya rasa gane kan maganganun balle ya fahimci akan mi take faɗan, "Mom, kina magana akan miye ne? I don't get u..." A ɗan fusace ta ce, "Dama ta ya zaka fahimce ni tun da an riga an makantar da kai, baka ji baka gani balle ka fahimta. Ina magana ne akan wancan mutumin mara tunani." Ta yi maganar tare da yin nuni da kofar part ɗin sa, da yanayin mamaki ya ce, "You mean ya Fahad! Minene ya yi na rashin tunani?" "Idan ba rashin tunanin ba ta ya yana ganin yau fa ka zo ƙasar nan, baka samu ka huta ba sosai maimakon ya taimaka maka ka kwanta ka huta amman shi ne a kwance a saman gadonka ɗare-ɗare ba ko kunya kai kuma bawansa a zaune!" Yanayin fuskarsa ne ya sauya zuwa yanayin bacin rai, bin ta ya yi da ido a ransa yana mai mamakin yanzu miye wani abu a cikin hakan da har zatai ta yin faɗa, "Oh, baka da ma abun da zaka ce mani ke nan? ka wani bi ni da ido ga mahaukaciya na magana ko?" Ɗan yamutsa fuska ya yi cikin alamun bacin rai ya ce, "To mi kike so in ce ne? Yanzu mom don Allah miye abun tashin hankali a ciki da zaki ta faɗa? I think i have already told you, ni ne ban kwanta ba na tsaya yin abu, ko kuwa ni ƙaramin yaro ne ban san ciwon kai na ba da sai wani ya faɗa mani in kwanta kafin na yi hakan? Idan shi yana buƙatar ya kwanta ya huta sai ya ƙi yin hakan saboda ni ban kwanta ba? Ko kuwa don yana gadona sai ya zama ya yi laifi don ya kwanta a sama? Dama abuna ba na shi bane, har akwai wani bambanci a tsakanin mu....? Have you forgotten that he is my brother? A gidan nan fa ya taso da har zaki ce wai da wani dalili yake tare da ni, idan ya gama cin moriyata zai guje ni. Ok mu dauka ma haka ne, to me, it's fine, zan yi faran ciki a ce ina da abun da ɗan'uwana zai amfana, koda ni zan rasa hakan bai dame ni ba, what would really hurt me is if he ever turns his back on me...that’s what would matter." A hasale ta katse shi, "Enough Deen! Saboda ina faɗa maka gaskiya zaka tsaya akai na kana mani wannan surutan! I'm your mother, dole na damu da kai na baka kulawa daga abun da nike ganin zai cuceka saboda tunanin mu ba ɗaya bane kai ba zaka gane abun da nike hango maka bane, sannan sam ni bani son tarayyarka da shi don zai iya saka ka ka lalata rayuwarka kamar yadda ya lalata tashi rayuwar da shaye-shaye..." Ɗan jujjuya kai ya yi jin abun da kuma zata fake da shi, yanayin idanunsa har sun ɗan sauya kala, wllh ya gaji da wannan halin na mahaifiyarsa, son kanta ya yi yawa, bai san mi yasa ta tsani Fahad haka ba wanda sam hakan bai mashi daɗi don kuwa idan akwai mutumin da yake jin shi a cikin ransa bayan su iyayensa to kuwa Fahad ne, "Mom, in kin san a in da nike rayuwa kin san da suwa nike tarayya? Kin san inda nike shiga a cikin duniyar nan? Kin san wani kalan mutane nike haɗuwa da su? Kin san irin abubuwan da idanuwana suke gani kunnuwana suke ji mom? Duk wannan basu lalata ni ba sai ya Fahad? Mutumin da zan iya rantsuwa akan ban ta6a gani ya sha wani abu da sunan ƙwaya ko abun maye a gaban idanuna ba, kuma kema na tabbata baza ki ce kin ta6a ganin hakan da idon ki ba. Mom, don Allah ina son in tambaye ki, and I don't want you to hide the truth from me, ya Fahad ya taba maki wani laifi ne da ya sa kika tsane shi, baki son shi a kusa na?" Fuska a yamutse ya yi mata tambayar, harara ta watsa mashi ta ce, "Yaushe mu ka yi da kai cewa na tsane shi? Kawai ni ina baka kariya ne daga duk abun da na hango zai cuce ka, ni ban yarda da shi ba, ba don Allah yake tare da kai ba kuma ban son tarayyar ku don zai iya jan ra'ayinka tun da kafi jin maganarsa akan ta kowa har mu iyayenka...." Ta ƙarasa maganar tana ƴan kame-kamen rashin gaskiya, ɗan murmushi wanda ya fi kama da a kira na takaici ya yi, kafin ya furta, "To na gode da kariyar da kike bani, amman Allah shi zai kare ni daga duk wani cutarwa ina roƙonsa hakan kuma ina da yaƙinin yana amsar addu'ana, don haka ina roƙon ki da ki ƙyale mu mu yi zumuncin da Allah Ya halatta a tsakanin mu..." Ni na tabbata ba don wani abu ya Fahad yake tare da ni ba, mutumin da tun da nike da shi bai ta6a buɗe baki ya ce na bashi kuɗi ba ko na siya mashi wani abu, ko kuma ya ga wani abu nawa ya ce na bashi. Duk abubuwan nan babu wanda ƴan'uwana basu tambayana har da ma wasu da ba ƴan'uwana ba, ke nan suma sai a ce duk cutata suke saboda ina basu abu? Dama idan Allah Ya buɗa maka don ka yi amfani kai kaɗai ya baka ne? Don ka ba wasu ne shi yasa yake ƙara baka, kuma idan kana badawa baka ta6a rasawa. If there’s nothing else you want to tell me, please allow me to go." Ya ƙarasa idanunsa na kallon gefe ya ɗaure fuska, bin shi da kallo ta yi ta lura da ran shi ya 6aci sosai, ta san yana da sauƙin kai da kauda ido, ba kowane abu ne ke saurin 6ata mashi rai ba, amman fa yana da zuciya idan ransa ya 6aci yana iya ɗaukar lokaci bai sauko ba, kuma zai iya yanke hukuncin da kowa zai iya shiga cikin damuwa, tunanin zai iya ma ya ce zai koma ne ya zo a ranta hakan yasa ta saki fuskarta, ɗan guntun murmushin da ba har zuci ba ta yi ta ce, "Ka yi hakuri yalla6ai na ta6a ɗan lelenka, wanda ya fi kowa muhimmanci a wurin ka gashi har na 6ata maka rai, watarana na san zaka fahimci abun da nike nuna maka." "Can I go?" Ya tambaya ba tare da ya kalle ta ba, ɗan yamutsa fuska ta yi ta ce, "Yanzu ke nan ku biyo zaku kwanta a saman gadon? Amman zaka iya takura ai, why not shi ya koma bangaren baƙi tun da akwai komai a can kowa ya fi sakewa..." Kafin ta rufe baki ya furta, "Shi ba baƙo bane, ba wani abu zamu kwanta tare. Gud nyt." Ya bata amsa a taƙaice tare da wucewa ya nufi komawa part ɗinsa yana tafiyarsa mai cike da natsuwa, bin shi da kallo ta yi ta tamke fuska tamau sai ka ce bata ta6a yin dariya ba har ya shige ciki ya maido ƙofa ya rufe, ɗan cije le6enta na ƙasa ta yi na ɗan lokaci kafin ta saki ta yi ƙwafa da ƙarfi ta furta, "Mu zuba ni da kai Deen!" Nufar sauka daga benen ta yi a cikin ranta tana saƙa cewa duk hanyar da zata bi sai ta ga ta raba tsakanin su, ba tun yanzu ba ta sha yin yunƙurin hakan lokutta daban- daban amman ta kasa yin nasarar hakan. Cikin falonsa ya shigo ya nufi kujera ya zauna, ransa a 6ace ya ɗage kansa sama tare da rufe idanunsa, ya yi hakan ne don ya samu sassaucin 6acin ran da yake ji kafin ya koma cikin ɗakin gudun kada Fahad ya fahimci wani abu. A hankali ya shiga tunano lokuttan baya irin yadda ta rinƙa yi ma Fahad izaya da yana a gidan amman duk da irin abubuwan da ta yi mashi hakan bai sa ko sau ɗaya ya janye masu ba a matsayin su na ƴan'uwansa, tunanin hanyar da zai bi ya ga ya yi maganin abubuwan da take yi ma dangin mahaifinsu ya shiga yi don hakan baya mashi dadi sam, a ganin sa har da laifin dad ɗinsu, shi yakamata a ce yana taka mata burki kan hakan amman baya ɗaukar matakin da ya dace shi yasa abun nata har ya girmama haka. Bayan ya ɗan ji sassaucin ransa ya mike ya nufi cikin ɗakin, yana shiga Fahad dake zaune a gefen gado ya jingina bayansa da jikin gadon ya ɗago idonsa ya kalle shi, nufar shi Deen ya yi yana ƙoƙarin daidaita yanayin shi gudun kada ya fahimci wani abu, a bakin gadon gefen shi ya zauna yana masa ɗan murmushi ya ce, "I thought zan iske ma ka yi bacci." Ɗan girgiza masa kai kawai Fahad ɗin ya yi ba tare da ya furta mashi komai ba, bin shi da kallo Deen ya yi ganin yadda ya yi shiru ya ɗan lumshe ido, tunanin ko ran shi ne ya 6aci kan abun da mom ta shigo ta faɗa ya shiga yi, a hankali ya kai hannu ya dafa cinyar Fahad ɗin fuska a ɗan marairaice ya ce, "Pls ya Fahad ka yi haƙuri akan abun da mom ke yi maka, na san hakan na 6ata maka rai sosai kawai kana kauda kai ne saboda zumuncin dake a tsakanin mu. Wllh sam bana jin daɗin abubuwan da mom ke yi ba tun yanzu ba, kawai na rasa yadda zan yi maganin abun, kuma ni ina ganin duk laifin dad ne, yakamata a ce yana tsawatar mata sosai..." Shiru ya yi yana kallon gaban sa fuskarsa da alamun baccin rai, sai da Fahad ɗin ya ɗan ɗauki lokaci kaman ba zai ce komai ba can ya ɗan yi yar ajiyar zuciya ya ce mashi ya daina damun kansa ai duk sun riga sun san halinta ne hakan, yadda ya yi maganar slowly ya sa Deen tunanin ko bacci yake ji, kallon shi ya yi ya ce mashi ya kwanta mana, shiru ya yi masa tare da lumshe idanunsa, kai idanunsa ya yi kan sauran lemun da ya sha ya rage, tunaninsa ya ƙoshi ne ya sa ya ajiye akan durowar, hannu Deen ya kai zai ɗauka ya ce bari ya ƙarasa shanyewa, yana kai hannu jikin robar ya ga Fahad ɗin ya yi saurin riƙe mashi hannu alamar hana shi ya ɗauka, da alamun mamaki Deen ya kalle shi sai kuma ya yi tunanin ko bai gama sha bane, fasa ɗaukar lemun ya yi ya ce mashi ya yi tunanin ya gama da shi ne tare da komawa ya zauna, bin Fahad ya yi da kallo ganin ya buɗe lemun ya kai baki, saida ya kwankwaɗe shi duka sannan ya cire robar ya maida marfin tare da mayar da ita saman durowan, a hankali yake ta lumshe idanunsa yana buɗewa, lokaci guda Deen dake kallon shi ya fara zargin kamar akwai abun da ke a cikin lemun shiyasa ma ya hana shi ɗauka kuma ya ƙi sakin jiki ya yi magana da shi sosai sai faman lumshe ido yake. Ya san da gaske ne Fahad na amfani da ƙwayoyi sai dai bai ta6a sha ba a gaban sa, haka idan ya sha bai sakin jiki sosai don kada ya gane, ya lura da irin kallon da Deen ke yi masa hakan ya sa shi ƙarasa hayewa saman gadon ya kwanta tare da ba Deen ɗin baya, jimm Deen ya yi na ɗan lokaci yana kallonsa kafin ya kai hannu ya ɗauko robar ya buɗe, kai bakinta ya yi saitin hancinsa ya ɗan sunsuna, daga ƙamshin da ya ji a ciki ya tabbatar masa da zargin da yake, mayar da robar ya yi ya juya yana kallon bayan Fahad, har cikin ransa tausayi yake bashi saboda shaye-shayen ƙwayoyin da yake yi, wanda a da sam hakan ba halinsa bane daga baya ƙaddarar ta haye mashi, hannu ya kai ya ta6a jikinsa tare da kiran shi a hankali, shiru bai amsa mashi ba ya san yana jin shi tun da bai daɗe da kwanciya ba, hakan yasa shi fara yin magana cikin kwantar da murya, "Ya Fahad, ka yi haƙuri idan abun da zan faɗa maka zai 6ata maka rai, duk da this is not the first time da na fara maka magana kan hakan, kuma wannan ba shine karo na ƙarshe ba, zan ci gaba da yi maka magana akan haka har zuwa ranar da Allah zai amsa addu'ana in ga ka daina. Please ya Fahad, you really should stop using drugs, a matsayin ka na medical doctor ka san irin illar da suke yi ma lafiyan mutum, hakan kuma yana da matuƙar haɗari ga aikin ka. Ba zan boye maka ba abun yana damuna sosai bro. I wouldn't want this to jeopardize your future." Fuska a yamutse ya ƙarasa magana, shiru Fahad ɗin ya yi bai tanka masa ba idanunsa na a rufe. Koma ya yi bacci bai sani ba? Tunanin da Deen ya yi ke nan, sai dai yana kokonton in ya yi bacci saboda ya san a duk sanda zai mashi magana kan shan ƙwayoyin da yake yi bai cika tanka masa ba sai dai ya yi shiru, wani lokacin kuma yana bashi amsa da zai daina in sha Allah Ya taya shi addua. Matsawa ya ƙara yi kusa da shi a hankali ya kwantar da kansa a saman jikinsa, Fahad da yana jin duk abubuwan da ya faɗa jin shi a jikinsa ya sa shi runtse idanunsa sosai, har cikin ransa bai jin dadin ganin yana saka mutane damuwa saboda abun da yake yi, saidai duk yadda ya so ya daina abun ya ci tura saboda ya kama mashi jiki sosai. "Ya Fahad, I think wannan teacher ɗin fa ya haukace, ya bani wannan assignment din ba daidai ba, that's why inata wahala amman ya ƙi ya yi daidai." Kaman daga sama Fahad ya tsinkayi muryar Deen a cikin kansa, duk da ya ɗan fita hayyacinsa amman komai na zuwa mashi a cikin kansa kuma yana fahimta, ɗan murmushi ne ya bayyana akan fuskarsa tunowa da can baya lokacin suna yara, duk aka ba Deen assignment ya kasa yi sai ya iske shi ya yi mashi wannan maganar da ya yi, da yake lokacin Fahad ɗin na yawan yi mashi faɗa kan yadda bai maida hankali sosai akan karatu ya fi mayar da hankali akan kwallo, to shine idan ya kasa yin assignment ya kawo mashi, gudun kada ya yi masa faɗan sai ya fake da cewa malami ya haukace ya bashi assignment ba daidai ba, You are the one who has gone mad, shiyasa ka kasa yin shi yadda aka koya maka." Fahad ɗin ne ya faɗa slowly, faffaɗan murmushi Deen ya saki ya ji dadin yadda ya bashi irin amsar da yake bashi a lokacin, duk da a yanzu bai kama mashi kunne ba kamar yadda yake mashi a lokacin, ɗago kai Deen ya yi yana kallon fuskarsa ya ce, "I thought ka yi bacci da na yi magana na ji baka ce komai ba." Ɗan shiru Fahad din ya yi kaman ba zai ce komai ba, "In sha Allah na kusa dainawa. Ka taya ni da addu'a Pls" Ya ji ya faɗa ba tare da ya juyo ba. "Ina yi maka addu'a a koda yaushe, ba akan wannan ba kaɗai, kuma zan ci gaba da yi maka har ƙarshen rayuwana, In sha Allah." Kai ya ɗan jinjina masa tare da ce mashi ya gode. "Ya Fahad yaushe zaka yi aure ne? Yakamata a ce zuwa yanzu kana da mata har ma mun samu baby, ka ga nima na samu wanda zan rinƙa nunawa a matsayin yaro na." Deen ya faɗa yana ɗan murmushi, ganin Fahad ɗin na kokarin juyowa ya sa shi gyara zaman sa, bin shi ya yi da kallo da lumsassun idanunsa a hankali ya furta, "Kai nike jira ka yi mani." Yar dariya Deen ya yi ya ce, "Serious, idan kana so sai in yi maka, ko gobe ma lafiya lau za a iya ɗaura maka aure. Who's the girl you want to marry?" Hannu Fahad ya ɗan yarfa ya ce mashi babu, amman tun da shi ne zai mashi auren sai ya samo mashi matar, "Samun matan ba matsala bane ai, na san akwai babes dake son ka, ɗazun ma a wurin dinner ai na ga ka samu, a cikin gidan nan ma na ga alamun ka yi kasuwa..." Ya karasa yana sakin faffaɗan murmushi, shima Fahad ɗan murmushi ne akan fuskarsa, ya fahimci akan Leemarh yake magana, bin shi kawai ya yi da kallo still idanunsa na ɗan lumshewa yana buɗa su. "Idan kana son Leemarh ka shirya ma auren ta let me know, zan sanar ma dad, tun da lafiya lau ta isa aure sai ta yi completing karatunta a gidan ka." Ɗan girgiza masa kai Fahad ya yi ya ce ba soyayya suke ba kawai shaƙuwa ce, "Da alama dai so kake in riga ka yin aure tun da ni ina da wadda zan aura, ko kuma in ce wadda aka za6a mani in aura." Yadda ya ƙarasa maganar zaka fahimci abun ba da son ranshi bane, kallon shi kawai Fahad yake yi can ya ɗaga hannu ya dafa shi ya ce, "You should not worry about that, idan Allah bai ƙaddara ita ce matar da zaka aura ba baza ka aure ta ba." "You're right. Idan ita Allah Ya za6a mani na kar6a, Allah Ya sa hakan ya zama alkhairi." Amsa mashi Fahad ya yi da Amin, suka ɗan yi shiru kafin Fahad ya ce mashi ya je ya kwanta dare ya yi gashi ya ce gobe tare za su tafi, miƙewa ya yi ya nufi ɗaya bangaren gadon, yana cikin tafiya yake tambayar Fahad gobe zai je wurin aiki ne, amsa ya bashi da ya so ya yi sammako don ya fara tsayawa wurin aikin to amman tun da tare za su tafi hakan ba zai yuwu ba, zai kira ya ƙara bada uzuri kawai sai su wuce Funtua, Deen ya ce kada ya yi haka goben idan Allah Ya kaimu da wuri za su tafi sai su fara tsayawa wurin aikin nashi kafin su wuce Funtua, Fahad ya amsa da ok, daga haka suka kwanta bayan Deen ya yi masu addu'a gaba ɗaya. Lumshe ido ya yi yana tariyo abun da ya wakana tsakaninsa da mom, a ransa yake raya gara ma ya yi tafiyar sa Funtua ya san a can zai fi samun peace of mind. _Bossladieswriters_ *_✨A CIKIN RAYUWA✨_* _By Zainab Bature_ _Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._ Page 8 Bayan mom ɗin Deen ta koma hamshaƙin katafaren ɗakinta da ya sha royal furniture kai kace wani ɗakin ƴar hamshaƙan masu kuɗi ko masu sarauta ne, a bakin gadonta da ya sha lafiyayyar katifa da shimfidar zanen gado mai kyau ta zauna, hayewa ta ƙarasa yi sama ta zauna tare da jingine bayanta da kan gado sai faman cika take tamkar zata fashe, bata da wani buri a cikin ranta face ta ga ta raba tsakanin Deen da Fahad, sam ta tsani ta gan su tare gani take kamar juya mata ɗa Fahad ke yi yana cin dukiyarsa son rai, ta ɗauki tsawon minti talatin a haka tana ta faman yin tufka da warwara, jin motsin shigowar mutum ya sa ta ɗaga ido ta kallo kofar shigowa, dad ɗin su Deen ne ya shigo yana sanye riga da wando na bacci, ya fito a babban mutum, cikin ɗakin ya nufo idanunsa akanta yana kallonta da ɗan yanayin mamaki, tun ɗazu yana a part ɗinsa yana jiranta, har kiranta ya yi a waya ba a daɗe ba ta sanar da shi tana zuwa tana yin wani abu ne, da ya ji shiru shine yanzu ya biyo bayanta don har sake kiran wayarta ya yi bata ɗaga ba, ganinta zaune ba tare da tana yin wani abu ba ya sa shi yin mamaki. Daga bakin gadon ya tsaya yana kallonta ita kuma tun da ta kalle shi sau ɗaya ta kauda idonta gefe, daga yanayin fuskarta ya gane tana cikin fushi, jikinsa ne ya ɗan yi sanyi don ya san idan tana a cikin irin halin bata saurarar shi, ƙoƙarin zama ya yi daga gefenta idonsa akanta, "Gimbiyata, ashe kina nan zaune kin ce mani kina zuwa ina ta jira." Ko kallon shi bata yi ba sai ma ta ƙara juyar da fuska tare da ɗan tura baki, jimm ya yi yana ta kallonta, ya san in dai yana son ta saukko to dole sai ya lalla6ata, "Ya aka yi ne my love? Mi ya faru na ga bacin rai a tattare da ke bacin bada jimawa ba mun yi magana lafiya lau. Pls tell me idan wata damuwar ce zan yi maganinta, in sha Allah." Ya ƙarasa maganar cike da tabbatar mata da abun da ya faɗa, sai lokacin ta ɗan juyo ta kalle shi amman bata saki fuska ba, hannu ya kai ya kamo nata ɗaya ta sigar lallashi ya ce mata yana jin ta minene matsalan, "Deen ne! Ban san mike damun shi ba, sam bai jin maganata, ban isa in nuna mashi abun da nike ganin shine daidai ba ya ji, abun da ransa ke so shine zai yi!" Ta ƙarasa a hasale. "SubhanAllah! Wai Deen ɗin? To ya aka yi haka, a yadda na sani Deen yana jin maganarmu sosai har ma ya fi duk sauran ƴan'uwan shi, ba laifi yana yi mana biyayya..." Da sauri ta katse shi ta ce, "Idan ba akan ɗan lelensa ba ko? Ai ba a isa a yi mashi magana ba idan dai ta shafi Fahad ya ɗauka." Shiru dad ya yi yana kallonta, dama ya san tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi, matuƙar aka ce Fahad ya zo gidan dama aka zatai ta taƙalo abubuwa tai ta faman maganganu, yar ajiyar zuciya ya yi ya ce mata wani abu Fahad ɗin ya yi, kaman tana jira ta hau faɗa mashi ƙabli da ba'adi ta ce wai ta je ɗakin ta iske shi Deen a zaune har yana ɗan gyangyaɗi amman shi Fahad ɗin yana baje saman gadonsa sai sharar baccin shi yake, kuma ta san saboda Fahad ɗin na kwance ne yasa Deen bai kwanta ba ga gajiya a tattare da shi, shine daga ta kira shi a waje don kada ma Fahad ɗin ya ji ransa ya 6aci, ta yi mashi magana kan mi zai hana Fahad ya tafi part ɗin baƙi ya kwanta shima ya fi sakewa ya kwanta sosai, shine fa ya hau yin maganganu yana faɗin wai ta tsani Fahad bata son su a tare, shi dai ta bar su su yi zumuncin su...haka tai ta faɗi ma dad ɗin karya da gaskiya, bayan ta gama maganar shiru dad ya yi yana ɗan jinjina kai, sam bai yarda da maganganun nata ba, idan ba neman abun magana ba tun farko mi zai kaita part ɗin Deen a lokacin bayan ta san yana jiranta, sanin halinta in har bai goya mata baya ba to kuwa ba zai samu ta sauko ba har ta kula shi ya sa shi nuna mata bai ji dadin abun da Deen ya yi ba, "Ban ji daɗin hakan da Deen ya yi ba, in baya ga abun shi ba don duk jin daɗin su saboda kada su takura ya sa kika bashi shawaran hakan ba, shine zai faɗi maganganu marasa daɗi haka. Ki ƙyale ni da shi, idan Allah Ya kaimu zan tsawatar masa kan hakan, ya kamata yana fahimtar abu yadda yake, kuma dama duk lokacin da Fahad ya zo gidan ba a part ɗin baƙin yake sauka ba..." Caraf ta amshe maganar, "Wataƙil ai kai in ka gaya mashi ya fahimta, ni dama a koda yaushe tawa zafi take balle har a fahimce ni, kuma ni kaina ai har da ganin a can din yake sauka yasa na ce ya koma can ba wani abu ba...." Matsawa ya fara yi kusa da ita har lokacin yana riƙe da hannunta guda, ɗan janyo ta ya yi zuwa jikinsa farko ta ɗan toge, saida ya ɗan sa ƙarfi sannan ya rungumo ta ta gefe cikin kwantar da murya ya ce, "Kada ki damu gimbiyata, na ce zan tsawatar masa na san zai ji ba zai sake ba, kuma kin san Deen ba wasu shekaru ne da shi sosai ba kawai har da girman jiki, shiyasa wani abun ba zai yi nazari ba balle har ya fahimci abun da ake nuna masa." Tana jin ya faɗi haka ta samu damar amayar da wani abu daga cikin ainihin abun da ke a ranta, "Har da hakan ya sa ni sam ban cika son ma yana samun kusanci da Fahad ɗin ba sosai wllh, ka dai san halin Fahad na shaye-shaye tsaf zai iya jan hankalin sa kan hakan tun da Deen ɗin yana ji da shi sosai yana ɗaukar maganar shi." Shiru ya yi yana juya maganarta a cikin ransa, ya san da Fahad na shaye-shaye don a can baya lokacin yana cikin yin karatu a Malysia abun ya fi yin ƙamari sosai, akwai lokacin da har saida ya samu matsala da karatunsa saboda hakan, har ta kai sun samu sa6ani tsakanin sa da mahaifinshi ya yi fushi da shi, har da shi cikin wanda suka yi kokarin ganin komai ya daidaita, amman a tunanin shi in da Fahad ɗin zai ja ra'ayin Deen har ya koya mashi shaye-shayen da tuni hakan ya faru tun da ba yau suke a tare ba, "Ki kwantar da hankalinki, In sha Allahu hakan ma baza ta faru ba tun da ai ba yau suke tare ba, kuma yanzu sai a dade ma basu kasance tare ba. Mu gode ma Allah, domin Deen nutsattsen yaro ne, a irin sana'ar da yake yi ta yawo ƙasashe daban daban, yana haɗuwa da mutane iri-iri daga masu tarbiya zuwa marasa tarbiya, amman babu abun da ya canza na daga kyawawan halayensa. Duk da ba a tare muke da shi ba in da halinsa ya gurbata zamu sani, har Maleek na kan yi mashi magana da ta shafi halayen Deen saboda kula, amman koda yaushe yana nuna mani halayen shi lafiya lau ba matsala kuma yana yabon Deen ɗin kan yadda ya tsare mutunci bai bari ɗaukakar da Allah Ya yi mashi ta ruɗe shi ga aikata sabon Allah ba, kamar yadda da yawa waɗanda suka ɗaukaka suke yin amfani da damar wurin gurbata rayuwarsu. Mu ci gaba da yi mashi addu'ar neman shiriyar Allah har da ma shi Fahad ɗin, saboda zumuncin Allah da ƴan'uwantaka ba zai yuwu a raba su ba." Shiru ta yi ta ɗan tura baki tana ƙara jin bacin rai ganin haƙarta bata cimma ruwa ba, a rashin tunaninta yadda ta so dad din ya goya mata baya su raba tsakanin su. "Don't worry my queen, na ce zan tsawatar masa ba zai sake ba ehen..." Ya yi maganar yana cusa fuskarsa tsakankanin wuyanta, ganin yana ƙoƙarin haɗe fuskokinsu ta yi saurin janye tata fuskar ta fara ƙoƙarin cire jikinta daga na shi, dakatawa ya yi daga abun da yake ƙoƙarin yi ya kalle ta fuskar shi da ɗan yanayin bacin rai, a marairaice ya ce mata miyasa take haka...fuska a yamutse ta ce mashi ya yi haƙuri an 6ata mata rai she isn't in the mood ya bari wani lokacin ko zuwa gobe da safe ne, Bin ta ya yi da kallo yana jin ran shi ya fara ƙuna, ya gaji da irin wannan halin nata, sau da yawa haka take hana shi hakkinsa idan ya nema, ba dama ai mata abun da ranta zai baci shike nan sai ta hana shi hakkin shi kuma sau tari ita ke janyo a yi abun da ran nata zai baci, da yawan lokutta yana cutuwa da hakan kawai daurewa ya ke. A can baya akwai lokacin da ya gaji da irin wannan halin nata har ta kai ya kai ƙararta wurin Hajiyar shi wato Hajiyar ambasada domin ta bashi shawara, a lokacin ta nuna mashi zaman tare dama sai an yi haƙuri balle kuma an ɗauki shekaru ana tare an tara zuria, ta faɗi hakan ne don bata son shiga cikin sha'anin gidan yaranta amman sarai ta san yana cikin matsala a gidan shi don sam bai yi dacen mata ba, ba kamar yayansa Alhaji Sa'ad ba wato mahaifin Fahad. A lokacin ya roƙi hajiyar kan ta sama mashi wata wadda zai aura, ya yi hakan ne da tunanin idan ya je ma mom ɗin su Deen da zancen cewa mahaifiyarsa ce ta sa shi ya ƙara auren zata yi haƙuri ta bari, don ya sha yin yunƙurin cewa zai ƙara aure ƙarshe ba a wanyewa lafiya tsakanin su har sai ya janye maganar, hajiya ta so bijire ma buƙatar shi don ta san ba lalle a kwashe ta lafiya ba, ta nuna mashi idan yana son ƙara auren shi to ya je ya nemi matar da kan shi, a marairaice ya nuna mata saboda ya yi hakan da farko ya nemi auren Jameela da kansa, gashi yanzu bai jin daɗin zama da ita shiyasa yanzu yake son ta zaba mashi wataƙil ya dace, dama sai da suka ƙalubalanci auren shi da ita, tun farko saida Hajiya ta nuna mashi ga mata nan a familynsu waɗanda an san su an san asalin su amman ya bijire lokacin idon shi ya rufe mugun son Jameela yake kamar me. Aikuwa ƙarshe ba a kwashe ta lafiya ba bayan da hajiya ta nemo mashi mata a cikin family ɗinsu wadda bazawara ce haihuwarta ɗaya mijinta ya rasu, ko da mom ɗin su Deen ta ji aikuwa ta daka tsalle ta tuma ta ce wllh bai isa ba duk da ya faɗi mata hajiya ce ta sa shi, amman hakan bai sa ta saurare shi ba, ƙarshe ma sai cewa ta yi ai dama ƴan family ɗinsu sun tsane ta har da hajiyan shiyasa ta saka shi ya ƙara aure inda tana sonta baza ta sa ba Ƙarshe har Funtua ta je gidansu matar ta ja musu kunnen kada su sake su bari a yi auren in ba haka ba ta sha alwashin sai ta halaka ta in ya so itama ai mata hukunci, har gidan hajiya ta je itama ta gaggaya mata magana kan wai ta tsane ta shiyasa zata sa a yi mata kishiya, itama hajiyar sai da ta sha mata alwashin in dai aka sake aka yi auren to sai ta kashe yarinyar wllh. Lokacin jin abun da ta aikata dad ɗin ya ce ma hajiya sakinta zai yi, hajiyar ce ta hana ya yi hakan ta ce mashi ya haƙura da ƙara auren a lokacin ya bari sai ya fara gyara gidan shi tukunna. Ba don Allah Ya sa shi ɗin mai tsoron Allah bane yana tsoron aikata zina saboda sanin hukuncin ta da tuni ya afka ga aikata hakan, ba kamar yadda Allah Ya hore mashi yana da hali da matsayin da duk kalar macen da yake so za a kawo mashi har in da yake. "Miyasa a duk lokacin da kika san ina tsananin buƙatar ki sannan zaki fara kawo wani uzuri mara dalili kina ja mani rai Jameela?" Rai a 6ace ya faɗi hakan tare da sakin jikinta, ita kanta ta san ran shi ya 6aci tun da har ya kira ta da ainihin sunanta. Ashe ba daɗi? Kai ma ai ka iya ja ma mutun rai idan yana son abu a wurin ka ko?" Wani kallo mai cike da takaici yake mata, ita kuwa sai wani jujjuya ido take tana yamutsa baki, "Wani abu kika nuna mani kina so na ja maki rai? Bana tunanin akwai abun da zaki buƙata a wurina ba tare da na yi maki ba..." Tarar numfashinsa ta yi, "Ai dama ban ce baka yi ba, amman wani lokacin sai ka ja ma mutum rai saboda yana nema a wurin ka, sai ran mutum ya gama 6aci.." Ta ƙarasa idon ta na kallon gefe ta ɗaure fuska, shiru ya yi yana ta kallonta ya ɗan ƙanƙance idanu, wannan halin nata na kawo tata buƙatar a lokacin da ya buƙaci hakkinsa ya tsane shi wllh. "Yanzu miye kike so?" Ya tambaya bayan ya sauke yar ajiyar zuciya, "Ka san mi na tambaye ka ai, maganar kuɗin da na yi maka zan tura ma Ammi." Wani kallon takaici yake wurga mata, wani lokacin har mamakin irin son kuɗinta yake, a koda yaushe cikin kawo masa buƙatun kuɗi take, duk da yana bata kuɗaɗe ba yan kaɗan ba, ban daAa kuma Deen da shima tana samun kuɗi a wurinsa bana wasa ba. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke ya ce, "In don wannan ne ai kin san zan baki tun da duk kika kawo mani wata buƙata da ta shafe su ina yin bakin ƙoƙari na, na ce ki ɗan jira ni kaɗan, yanzu babu isassun kuɗi ne a wuri na, cikin satin nan na tura ma injiniya da suke mana aikin gidanmu na Funtua kuɗi, aikin gidan yana da cin kuɗi sosai saboda gidan da kika nuna kina so ne ake yi duk don in faranta maki." Yamutsa fuska ta yi, "Amman dai ai baka cewa kwata-kwata baka da kuɗi, ko rabi ne sai ka bani." Kallonta yake yayin da ransa ke suya, ta saba haka nan ta kawo mashi buƙatar danginta ta kuma sa rigima idan ya nuna baya da hali, ba zata bar hankalin shi ya kwanta ba har sai ya yi mata abun take so, Allah kaɗai ya san adadin buƙatun kuɗin da ya yi ma danginta tun daga kan iyayenta zuwa ƙannanta. Sanin idan fa bai yi mata yadda take so ba to shima ba zai samu yadda yake so ba ya sa shi ce mata su tafi part ɗinshi zai tura mata rabin wayan shi na can, tare suka sauka daga saman gadon suka tafi tana ta cika tana batsewa, ni kam dai mai rubutun na ce 'A Juri Zuwa Rafi...'. Allah Ya kyauta Ya raba mu da son zuciya. LONDON Belgravia, (unguwar da aka fi sanin ta masu arziƙi a London...) Gida ne bene hawa biyu na alfarma, yana da faɗi tare da ginin zamani mai ɗauke da gilasai. Ginin gidan na da manyan tagogi da aka yi da gilasai masu nuni da tsari na zamani tamkar ginin kamfani. Kana shiga cikin gidan zaka tsinci kanka a cikin wani falo mai girma zubin na turawa cike da alfarma. Bangon gaba ɗaya fari ne mai sheƙi, an ƙawata bangon ta hanyar ɗora masa manyan zane-zanen fasaha na zamani. Ƙasan falon an rufe shi da Persian rug na Turai mai kauri da tsananin taushi a ƙafa wanda yake yin ɗan ƙyalli idan aka yi tafiya a kai. Kujerun cikin falon ɗuma-ɗuman leathers ne wato na fata kalar baƙi da ratsin golden mai haske, suna da tsananin taushi ko a ido. A saman falon akwai babbar fitila (chandelier) mai ƙyalli, girmanta tamkar zata rufto ma mutum, wadda aka yi da gilashin lu'ulu'u masu haske, tana kwaranya haske ta kuma bai wa falon kyan gani fiye da yadda ake tsammani, akwai kuma wasu ƙananun fitilun a can sama. A gefe ɗaya na falon an sa babbar talabijin mai siffar bango (wall screen) wadda a girma ta wuce inci ɗari, da sauran kayan sauti masu bada sautin gaske da ke sa mutum ya ji kamar yana a cikin cinema. Daga hannun dama kuwa akwai na'urar kula da gida (smart home system) da aka ɗaura a kan bango tana sarrafa fitilu, talabijin, sauti da ma kofar shigowa, duk ta hanyar danna madanni ko amfani da murya. Daga ƙasan tagogin falon akwai na'urar ɗumama iska da na'urar sanyaya iska, wanda suke aiki da kansu idan yanayi ya sauya. Duk in da ka kalla a cikin falon, zaka ga alamar zamani, daga na'urar ƙara haske (smart lighting) wacce take canza launi da dare, zuwa na'urar magana (voice assistant) da take iya amsa tambayoyi cikin harshen turanci. Tabbas gidan ya amsa sunan aljannar duniya, ko da gidan yake a Turai kana gani ka san bana ƙaramin mai arziƙi bane. Akwai bangaren cin abinci wato dining area dake cike da alfarma da fasaha, haka akwai bangaren karatu wato study corner mai ɗan girma, akwai babbar shelf mai ɗauke da littattafai, nan ma bangaren an ƙawata shi da abubuwan fasaha irin su smart speaker dake amsa tambayoyi tana kula da smart home devices, kamar kunna fitilu ko sauran na'urorin lantarki, sauraran kiɗa, podcasts ko audiobooks, saita tunatarwa kamar alarm, kira da kuma aika saƙonnin murya. Zaune a saman kujerar fata mai mazaunin mutum biyu dake cikin ɗakin karatun, Maleek ne jikinsa sanye da farar jallabiya ƙal, idanunsa na a cikin farin gilashin screen, kana ganinsa ka ga mutum mai lafiyayyen jiki wanda ba zaka iya tantance ainihin shekarunsa ba, ƴar hurhurar dake a gashin gemunsa da kuma saman kansa ke ƙara bayyana manyantakarsa, fuskarsa na da cika mai nuni da kwanciyar hankali da arziki da kuma tsananin ƙwarjini, a saman teburin da ke gaban sa manyan litattafai ne tare da laptop sai wata fitilar karatu mai kyau, daga gefe wireless charging pad ne da ake ɗaura waya a sama ta yi caji, ya dukufa yana duba wani babban littafin fasaha, lokaci bayan lokaci yake ɗan dakatawa tare da kai hannunsa ya ɗan tatta6a kwamfuta ɗin kafin ya ɗaura da duba littafin. Shigowa ta yi cikin babban falon tana sanye da riga da wando na bacci masu santsi kalar ruwan madara sai sakin kamshi mai ratsa zuciya take, ta rufe kanta da madaidaicin farin gyale da ya ɗan zame gaban kanta mai ɗauke da baƙar suma mai santsi ya bayyana, kallo ɗaya zaka yi mata ka tabbatar da ita ɗin kyakkyawa ce ta gaske, tun daga fuskarta zuwa dirin jikinta masu ɗaukar hankali ne, bin cikin falon ta yi da kallo kamar tana neman wani abu, hanyar da zata kai ta study corner ta nufa tana yin tafiya dake bayyana nutsuwarta, tana zuwa bakin ɗakin idanunta suka yi tozali da wanda take nema, wani ƙayataccen murmushi ne ya bayyana akan kyakkyawar fuskarta mai ɗauke da jan labba tamkar ta shafa jan baki sai dai kuma haka halittar su take, nufar shi ta yi tana yin tafiya a hankali kamar sanɗa yadda ba zata yi sautin da zai gane ta shigo ba, ta bayan shi ta zagaya tana zuwa ta kai hannuwanta ta saƙalo su ta kafaɗarsa tare da ɗaura kanta a gefen wuyansa, a nutse ya ɗago da fuskarsa mai cike da haiba yana murmushi ya kallo ta ta gefe, cikin sigar jan hankali ta kashe mashi ido tare da furta, "Sanyin idaniyar Sapnah kana nan ke nan, ka bar ni ni kaɗai." Ɗan lumshe ido ya yi yayin da ɗumin bakinta mai tattare da daddaɗan ƙamshin mouth spray ɗin da ta fesa ya bugi fuskarsa, a hankali ya furta, "Baki yi bacci ba?" ƙoƙarin zagayowa ta yi ta dawo ta gabansa, a saman cinyoyinsa ya yi mata masauki suna kallon juna cikin ido fuskokinsu tamkar zasu haɗe ta bashi amsa da, "Ta ya zan iya yin bacci mai saka ni in yi baccin baya kusa da ni." Yar dariya ya yi, slowly ya matso da bakinsa ya yi kissing reddish lips ɗinta ta lumshe ido, "I'm sorry, ina wani bincike ne mai muhimmanci da muke buƙatar sa da gaggawa." Ta ɗan kashe masa ido tare da furta, "Don't worry honey, kana da amincewar Sapnah a koda yaushe." Ya lumshe mata ido can ƙasan maƙoshi ya furta, "Thank you mah luv." Ta kai bakinta ta sumbaci kuncinsa kafin ta sauka daga jikinsa ta zauna gefensa ta ce ya ci gaba da aikin. A nutse take taka matattakalar benen yayin da take saukowa daga sama ƙafafunta na sanye da slippers masu taushi irin wanda ake yawo a cikin gida, cikin babban falon ta shigo tana sanye da nightgown iya gwuiwa da ta bayyana ɗan dirinta na matashiyar budurwa, kanta ta saka hula yalwatacciyar sumarta ta fito gefe da gefen kanta ta ƙulle ta da ribbom ta baya, kunnawanta na sanye da ƴar barimar diamond. A yanayin halitta ba za a kira ta fara ba, kana kallon ta ka san baƙa ce, sai dai daga yanayin fatarta yadda take sakin sheƙi ta fallasa ba ƙaramin hutu da jin daɗi take a ciki ba, sam ba wata kyakkyawar a zo a gani bace amman kuma ba za a kira ta da mummuna ba, tana da ƴar doguwar fuska mai ɗauke da ƙananun idanu da madaidaicin hanci da bashi da tsawo sosai, tana da ɗan babban baki mai ɗauke da manyan labba, yadda yanayin shape ɗin labbanta suka fita sun yi kalan ƴan gayu. Bin cikin falon ta yi da kallo sai kuma ta ci gaba da yin tafiya, bangaren mom ɗinta ta nufa, ɗan madaidaicin falo ta shigo da shima ya tsaru da kayan zamani, ganin bata a ciki ta wuce bedroom ta buɗe kofar ta shiga, nan ma wata aljannar duniyar ce guda, duk da ɗakin baya da hayaniya amman an zuba tsaddaddun kayan alatu a ciki, ganin nan ma mom ɗin bata nan ta nufi bakin kofar toilet ta ƙwanƙwasa tare da furta, "Mum, are you in there?" Jin Shiru ta ƙara kiran sunan mum ɗin, nan ma shiru hakan ya sa ta gane bata ciki ta juya ta nufi hanyar fita, babban falon ta dawo ta wuce kaitsaye zuwa study corner don ta san bata wuce tana can, tana shiga ta hango su zaune ta tsaya daga bakin ƙofa, cikin sigar shagwa6a ta furta, "Mum, dad..." A tare suka juya suka kalli direction ɗin da take, lokaci guda murmushi ya bayyana akan fuskokinsu ganin ɗiyarsu ɗaya tal da Allah Ya basu wadda ta kasance mafi soyuwa kuma sanyin idaniyarsu, hannu Maleek ya miƙa mata ta nufo su, a gefen shi ta zauna bayan ta kama hannun nashi, yana kallon ta ya ce, "Baby, haven't u slept yet?" Ta ɗan yamutsa fuska ta furta baccin ya ƙi zuwa, cike da kulawa idanunsa akan fuskarta ya ce ko wani abu na damunta? A hankali ta ɗan girgiza masa kai tare da kwantar da kanta a gefen kafaɗarsa, Sapna da ta maido duk attention ɗinta kan ɗiyar tata, tana ɗan murmushi ta ce, "Ko dai duk missing ɗin Deen ne?" Ɗan murmushi ne ya bayyana kan fuskar Basma ta maida idanunta ƙasa ba tare da ta ce komai ba, "Haka ne baby?" Maleek ya tambaya yana ɗan leƙen fuskarta, ɗago idonta ta yi da ɗan alamun damuwa ta ce har yanzu basu yi magana ba tana ta kira da daren nan but no response, kallon juna suka yi shi da Sapna, ba sai an faɗa masu ba sun san yadda take tsananin son Deen, hannu ya kai ya dafa kanta yana murmushi ya ce kada ta damu ya san ya yi busy ne sosai shi yasa bai samu damar su yi magana ba, musamman da ya ɗan daɗe bai je Nijeriya ba gashi a daren nan aka yi masa welcome dinner, "Yakamata ma ki saba da hakan, tun da ko yana a nan ba wani cika samun lokacin kan sa yake ba." Nodding kai Basma ta yi jin maganar mum ɗinta, har da hakan nema ya sa take yawan yi masa uzuri tana ɗaukar rashin bata kulawan da yake har da lokaci da bai da shi sosai. "Na tura maki saƙo kin gani." Maleek ya tambayi Basma, ta ɗago tare da ɗaga mashi kai ta ce masa thank you, Sapnah ta tambaye shi saƙon miye, ya ce ba wani abu bane ta ce tana buƙatan kuɗi ne shine ya tura mata, wani kallo ta yi ma Basma da itama take kallon nata cike da kama kai, mamakin mi zata yi da kuɗi ne Sapna ta shiga yi don ba a fi kwana biyar ba da ta buƙaci kuɗi a wurinta kuma ta bata masu yawa, bayan haka duk ƙarshen wata kowa a cikin su ke tura mata kuɗi don yin buƙatun kanta. Tabbas ta san kashe kuɗin Basma yana yin yawa, amma sanin ɗiyar tata na da son yin gayu da tsadaddun kaya ga kuma kyauta da take da ita musamman ga ƙawayenta yasa bata damuwa ta san duk anan kuɗin ke tafiya, wannan tunanin ya sa ta share bata ce komai ba, itama ta yi ma Maleek godiya da fatan ninkuwar arziƙinsa, yana murmushi ya ce ai su nauyinsa ne komai ya yi masu hakkinsa ne don haka no need sai sun rinƙa masa godiya, Sapna ta ce duk da hakan ai an ce yaba kyauta tukuici to godiyan ne yake serving as tukuicin, murmushinsa na dattako ya yi kafin ya ce su je su sha coffee, Sapna ta ce "Amman ba ka ce aikin da kake mai muhimmanci bane kuma na gaggawa, ka ci gaba da aikin ka, bari in raka baby part ɗinta." ƙoƙarin miƙewa ya fara yi yana riƙe da hannun Basma ya bata amsa da, "All work and no play...." Basma ta ƙarasa masa karin maganar da faɗin, "....makes Jack a dull boy." Gaba ɗaya suka yi ƴar dariya, itama ta kama ɗayan hannun Basma ta yadda sun saka ta a tsakiyar su suka nufi ƙofar fita gwanin burgewa.... *Littafin A Cikin Rayuwa kashi na farko zai zo maku a kyauta, ga mai buƙatar kashi na biyu zai biya 500 kacal. Domin neman ƙarin bayani a tuntubi waɗannan lambobin ta hanyar aika saƙon whatsApp kawai banda kira, 09013804524, 08169856268* *_✨A CIKIN RAYUWA✨_* _By Zainab Bature_ _Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._ Page 9 ....Bayan sun fito cikin babban falon, kaitsaye tea corner dake a wani bangaren falon suka nufa, nan ma wurin kan shi wata duniyar ƙawa ce, akwai babban teburin gilashi mai salo na zamani, saidai ba irin tebur bane da aka saba gani, wannan interactive glass coffee table ne, teburin yana da touchscreen surface gaba ɗaya. Idan aka taba saman gilashin sai haske ya kunnu ta ƙarƙashin glass ɗin, ya bayyana ƙananun menu icons tamkar wayar hannu, ana iya amfani da shi wajen buɗe Internet wato mutum zai iya browsing, duba email ko labarai kai tsaye a saman teburin. Sannan ana iya kallon hotuna ko bidiyo daga wata na'ura kaman waya, ta hanyar yin connecting ɗin bluetooth ko Wi-fi su bayyana a saman teburin, sannan za a iya matsar da hotunan ko vedio da yatsa, a zagaya ko a faɗaɗa su. Banda waɗannan kuma za a iya kunna waƙa da bidiyo, sannan teburin yana haɗe da tsarin sautin gidan (surround system), ta yadda idan aka kunna waƙa daga teburin sauran kayan sautin gidan suma za su kama ko ina za a ji. Ana iya yin wasanni wato games ta teburin sannan akwai app dake bada damar kashe fitilu,daidaita labule ko kunna AC duk daga saman gilashin. Ta ko ina dai a gidan fasaha ce ke aiki. Bayan sun iso cikin tea corner ɗin, Maleek ya ce su zauna shi zai haɗo masu coffee, a saman kujerun dake zagaye da coffee table ɗin suka zauna, Basma ta ce mashi ita hot chocolate take so ya ɗaga mata hannu ya ce, "Alright baby...." Hannu ta kai saman glass ɗin teburin da idan ba a cikin yin amfani dashi a ke ba yana nuna wasu artistic wallpaper, wato wani zane mai motsi tamkar ruwa da kuma mai kaman walƙiya, wanda hakan yana sa shi ya zama abin kallo ko da ba a kunna shi ba, game ta buɗe ta ce ma mom su yi kafin a kawo masu, gefe a cikin wurin Maleek ya nufa wanda a wurin akwai na'urar haɗa coffee da sauran abubuwan sha, da kuma china cabinet dake ɗauke da kufuna iri-iri da kayan haɗa abubuwan sha daban-daban, komai na wurin dai ya gama tsaruwa, within few minutes ya gama haɗa masu, Basma ya fara kai ma hot chocolate ɗin ta, bayan ta amsa ta furta, "Thank you, one and only dad." Ya wani kashe mata ido, a waje wanda bai san shi ba zai ce bai da irin barkwanci haka saboda yadda fuskarsa ke cike da ƙwarjini da haiba, bayan ya ɗauko masu coffee ɗinsu shi da Sapnah, a nutse duk suka fara sha, bayan wani lokaci ya kai hannu saman teburin, menu icons suka bayyana ya buɗe in da jerin karatuttukan alqurani suke, karatun alaramma Ahmad Sulaiman Kano ya kunna don tana daga cikin ƙira'oin da yake su gashi kuma ɗan garinsu, kan ka ce me gaba ɗaya kayan sautin falon suka kama karatun cikin madaidaicin sauti mai kwantar da zuciya da saka natsuwa.... Bayan sun gama Basma ta kwashe mugs ɗin da suka yi amfani ta je ta saka a wani injin dake a wurin wanda ke wanke maka kayan da aka yi amfani fess, ta maida su wurin ajiye su sannan ta dawo, Maleek ya ce ma Sapnah su je su raka baby part ɗinta ta amsa da ok, kafin su tafi ta hanyar wannan glass table ɗin ya rage hasken gaba ɗaya cikin falon zuwa mai duhu ya kuma gyara duka labulayen falon, abun dai kamar siddabaru! Kamar lokacin da za su zo yanzu ma saka Basma tsakiya suka yi suka kama mata hannu, lokacin da suka fara hawa matattakalar benen sai ma suka ɗaga ta sama ba tare da tana taka steps ɗin ba, Basma nata ƴar dariya suma duk ita ce akan fuskokinsu har suka haye da ita sama, kana ganinsu ka ga happy family, ɗakinta dake a saman benen suka kaita wanda shima yake da zubi irin na zamani, an tsara shi da tsadaddun furniture daidai da matashiyar budurwa, har saman gadonta da ya sha lallausar shimfiɗa suka kai ta tare da kwantar da ita, gaba ɗayansu suka yi mata addu'oi kafin duk suka sumbace ta a goshi suka yi mata sai da safe, tana murmushi ta furta, "Gud nyt mom, gud nyt dad, I luv u so muchhh." Hannunta Maleek ya kama ya sumbaci bayan shi ya furta, "We luv u too, our happiness." Ya ɗan kanne mata ido, sai da ya rage mata hasken ɗakin daga mai haske zuwa mai duhu kafin suka fita suna yi ma juna bye-bye, tana ganin sun tafi ta ɗago ta kai hannunta saman side drawer ta ɗauko wayarta don ta duba ta ga ko Deen yana online. Su Maleek na fitowa daga ɗakin nata ya duƙa ya ce ma Sapnah ta hau, dama duk zai ɗauke ta ya fi goya ta, don a cewarsa ƙirar jikinta ta saka ta yin nauyi, tana dariya ta kuwa haye bayan nashi, a tunaninta za su koma ƙasa ne sai ta ga ya wuce da ita part ɗinsa dake a nan saman benen don duk suna da part a nan, har Deen ma a nan saman part ɗinsa yake a gidan. A can hawan ƙarshe kuma ba ɗakuna bane, anan akwai Home Cinema wato babban wurin yin kallo kamar gidan kallo, an saka babban screen a jikin bango da manyan kayan sauti, akwai kujeru masu motsi dake ɗauke da wurin ɗaura kofin abun sha, akwai kuma Entertainment Zone wanda ɗan madaidaicin wuri ne don yin game, bayan su akwai kuma Mini Lounge inda ke da mini bar an saka glass shelves masu ɗauke da drinks kala-kala, Sai Relaxation Spot wanda area ɗin balcony ne aka yi ma ado ta hanyar zagaye sa da glass, akwai kujeru da table masu matuƙar jan hankali da fulawoyi masu tsari. Musamman akwai glass elevator da ke kai mutum can sama ba tare da an sha wahalar taka matattakala ba. Tabbas gidan Maleek ya amsa gidan mammalakin kamfanin fasaha, abu mafi ƙayatarwa shi ne yadda aka haɗa duk na’urorin gidan da smart home system, ta yadda ake iya sarrafa su ta amfani da murya ko kuma ta wayar hannu. Ganin sun nufi part ɗinsa, Sapnah ta tambaye shi ba aikin zai je ya ci gaba da yi ba, ya ce mata bai son shiga haƙƙinta su je ya sakata ta yi bacci idan ya tashi da dare zai ci gaba, ba ƙaramin daɗin hakan ta ji ba ta lafe a bayansa sai ka ce wata ƙaramar yarinya, koda yake gaba ɗayansu basu ɗaukar kansu a masu shekaru wurin nuna ma juna soyayya, a koda yaushe soyayyar su ga junansu sabuntuwa take yi kamar dai yadda ma'aurata turawa suke, yawan shekaru baya hana su nuna ma juna soyayya. Maleek mutum ne mai tsananin bawa iyalinsa kulawa tare da ƙoƙarin sauke masu hakkokin su duk da kasancewar sa mutum da yake yawan kasancewa busy. Sai dai ba iyakar iyalinsa kawai yake kyautata mawa ba, shi mutum ne mai tsananin alkhairi ga mutanen dake kewaye da shi, waɗanda ya sani da ma waɗanda bai sani ba alkhairinsa na isar masu, kamfaninsa na ɗaya daga cikin manyan kamfuna dake bada gudunmawa da tallafi a ƙasar, haka ma a Nigeria, yana ɗaya daga cikin mutanen da ake neman tallafi a wurinsu idan buƙatar hakan ta taso, kamar 6angaren gina makarantu, masallatai, hanyoyi da sauransu. Da zarar ƙafarsa ta dira a garinsa wato Kano, mutanen unguwarsu suke cika da farin ciki sanin cewa suna cikin alkhairi dumu-dumu, sannan duk da kasancewarsa mai tsananin arziƙi da yawan uzururruka hakan bai hana sa kula da addininsa, yana da ruƙo da addini sosai, a duk daren duniya indai yana da ƙoshin lafiya sai ya yi ibadu, a ganinsa in dai zai rinƙa tashi yana yin aiyukan da suka shafi aikin sa to ba shi da uzurin da zai hana sa yin ibada, wani lokacin sai ya gama yin ibadunsa sannan ya dasa da aiki, ko kuma bayan ya gama yin aikin, haka iyalinsa ma yana matuƙar ƙoƙari wurin saka ido kan abun da ya shafi ibadarsu. ABUJA A zazzaune suke a dining area suna yin breakfast, gaba ɗaya sun shirya dad ɗinsu na sanye da ƴan cikin manyan kaya na light blue ɗin shadda, babbar rigar su na can part ɗinsa sai ya gama in zai tafi aiki zai saka, a sauran kujerun su Leemarh ne da ƙannanta duk sun shirya cikin uniform don tafiya school, babu Omar a ciki don shi ba in da za shi ba da wuri zai yi breakfast ɗin ba, mom ɗinsu ma na zaune jikinta sanye da baƙar abaya mai buɗaɗɗan hannu ta yafa ƙaramin mayafin rigar a saman kanta, itama lokacin zata karya don zata fita da wuri ne zata je yin wani uzuri. Dama kuɗin da ta amsa jiya a wurin daddynsu ƙarya take ba wani Ammin su da zata tura mawa don buƙatar kanta ne ta amsa, ba a daɗe da ta sa ya bata miliyoyin kuɗi ba wai zata ƙara ma zinaranta girma, shiyasa yanzu ta fake da Ammin su na da buƙata. A natse suke cin abincin an shaƙe tebur ɗin da kayan breakfast kala-kala, wanda duk cin su baza su iya cinye su duka ba, Leemarh tana cin abincin amman hankalinta na kan Fahad ta ƙosa ta saka shi a idanunta saboda ba da su suke yin breakfast ɗin ba, saboda an san ya yi wuri da yawa shiyasa ba a yi masu maganar su fito su yi breakfast ɗin ba, daga gefen su masu aiki biyu ne a tsaye suna serving nasu abun da kowa ke so. Leemarh ce ta fara miƙewa ta ce ta ƙoshi, tana barin wurin ta nufin hanyar bene tana sanye da ɗan gajeran skirt da iyakar shi gwiwa na kayan makaranta, sai doguwar farar safa data kawo har bakin inda skirt ɗin ya tsaya, ƙafafunta na sanye da rufaffun baƙaƙen takalma na makaranta masu ɗan karen kyau, kanta na sanye da ƴar hijab himar sosai kayan suka yi mata kyau sai faman sakin kamshi take, lokacin da ta isa bakin bedroom ɗin ta tsaya ta yi sallama, sai dai kusan sau biyar tana yi shiru ba a amsa mata ba hakan yasa ta yanke ta leƙa ta gani ko basu tashi bane, bin ɗakin ta yi da kallo da ɗan alamun mamaki lokacin da ta hango gadon wayam ba kowa, sai dai alamun ba a daɗe da tashi daga sama ba don zanen gadon da duvet ɗin a ɗan yamutse suke, ƙarasa shiga ta yi tana tafiya a hankali kamar mai yin sanɗa tana bin cikin bedroom ɗin da kallo, a tsakiyar ɗakin ta tsaya tana yin ƴan waige-waige ko zata hango wani cikin su, har can ciki wurin closet ta duba amman bata gan su ba, har bakin toilet ta tsaya tare da ɗan yin knocking nan ma shiru bata ji alamun mutum ba, hanyar fita ta nufa a cikin ranta tana mamakin to ina suka tafi da sassafen nan, bayan ta fito falo har ta nufi ƙofar fita ranta ya bata to ko suna a sashen baƙi? Yin wannan tunanin ya sa ta juya da sauri ta nufi ɗayar ƙofar da zata sada ka da bayan gidan wanda ta nan ya fi kusa da sashen baƙin, lokacin da ta je a rufe ta iske part ɗin alamar ba kowa a ciki, komawa ta yi cikin gidan tana ta tunanin ina suka tafi, bayan ta shigo ciki hanyar dining area ta nufa har lokacin suna a zazzaune basu ƙarasa yin breakfast ɗin ba, "Mom, wai ina su ya Deen da ya Fahad suke?" Ta tambaya bayan ta tsaya daga gefen mom ɗinsu, ba tare da ta kalle ta ba hannunta riƙe da tea cup tana sipping ta ce Deen ba yana a part ɗinsa ba, "To ai yanzu daga can nike amman ban iske kowa ba, har cikin bedroom na shiga nan ma wayam ba su nan." Dakatawa mom ɗin ta yi ta kai idanunta kan ta, "To ina Deen ɗin zai tafi da sassafe?" Hannu Leemarh ta yarfa mata alamar itama bata sani ba, shiru mom ɗin ta yi alamar tunani, a ranta ta ayyana ko saboda maganar da ta yi ma Deen ya sa shi jan Fahad suka koma bangaren baƙi, kallon Leemarh ta yi ta ce tana jin Deen ɗin yana a part din baƙi, yadda take ba Leemarh amsa sam bata sakawa da Fahad sai ka ce ba su biyu ta tambaya ba, "Ai har can ma na je amman ba su nan, part ɗin ma a kulle ya ke fa." Jimm mom ta ɗan yi, lokaci guda zuciyarta ta ayyana mata ko dai hasashenta na jiya ya tabbata ran shi ya 6aci ya yi tafiyar shi har da Fahad ɗin! Da sauri ta ajiye cup ɗin hannunta har sai da ya yi ƙara, kallon dad ta yi ta ce, "Ko ka san in da Deen ya ke?" ɗan ɗage ido ya yi alamar tunani, "ehumm..tare dai muka je masallaci da su, bayan mun dawo ne suka wuce part ɗin Deen nima na wuce nawa." Wata zabura da ta yi kamar wadda shock ɗin lantarki ya ja, da sauri ta fita daga cikin kujerar da take ta nufi cikin falo tana tafiya jikinta na amsawa dama rigar jikinta irin abayar nan ce mai fidda shape, a tsiyace take taka matattakalar benen gabanta har ɗan faɗuwa ya ke, ita bawai ma in komawar ya yi ba ce tafi ɗaga mata hankali, tunanin tare ya koma da Fahad ne ya sa ta wannan ruɗewar, da ƙarfi ta bangaza ƙofar part ɗin shi ta shige, kamar yadda Leemarh ta iske shi haka itama ta iske wayam, cikin ɗakin ta kutsa tana faman ƙwala masa kira, "Deen! Deen...!!" Ba in da bata duba ba amman babu alamar su, tsaye ta yi tare da ruƙe ƙugu tama rasa tunanin da zata yi na inda suka tafi, walk-in closet ɗin shi ta sake shiga tana ƙara dudduba kayan ciki, lokacin da ta fahimci ba wasu daga cikin akwatunan da ya zo da su jiya wani irin tsinkewa zuciyarta ta yi, har wani duhu-duhu take gani lokacin da ta fito ta nufi sauka ƙasa da sauri kaman za ta tashi sama, ko kallon in da su Leemarh suke bata yi ba bayan ta saukko kai tsaye ta nufi hanyar fita daga cikin falon, duk da ta san falon na su yana da girma amman sai take ganin kaman ya ƙara girma ganin ta ƙi kaiwa kofar duk da saurin da take zubawa, a cikin entryhall ta ja tunga ta fara ƙwala kira cikin tsananin ɗaga murya tana faɗin "Officer, officer at the gate! Call the officer at the gate!!" Ta ba wani jami'i dake tsaye gefen jibgegiyar baƙar jeep umarni, da sauri ya amsa mata da ok ya nufi hanyar gate, ba a ɗau lokaci ba wani jami'i jikinsa sanye da uniform yana riƙe da hularsa a hannu ya tunkaro ta yana tafiya da sauri, yana zuwa cikin girmamawa ya ce, "Good morning ma," "Did you see Deen go out of the house??? Ta jefa mashi tambayar ba tare da ta amsa gaisuwar da ya yi mata ba, "Yes, sun fita lately tare da brother na shi." Wani mugun kallo ta watsa masa, "Wane brother ɗin?" Sai ka ce bata san wa yake nufi ba, "I mean, his cousin brother Fahad." Wani gauron numfashi ta saki ta ɗan cije baki, "Sun faɗi maka ina suka tafi?" "Yes, da na gan su har da kaya shine na tambaye su za su yi tafiya ne suka ce za su je Funtua." Da tsananin mamaki ta maimaita, "Funtua...?" Amsa mata ya yi da yes can Deen ya faɗi mashi za su tafi, har za ta juya ta dakata ta tambaye shi Deen ya tafi da jami'ai ya amsa mata da a'a su biyu kawai suka tafi, wata irin juyawa ta yi tamkar zakanya ta durfafi komawa cikin gidan, officer dake tsaye ya bi jikinta dake amsawa da kallo baki a buɗe har ta shige, a cikin falon ta haɗe da su Leemarh sun taho har da dad ɗinsu ya saka babbar rigar shi yana tafiya yana gyara zaman hular shi, "Ka ga irin abun da nike faɗi maka ko! Yanzu Deen har ya kai ya yi tafiya ba tare da ya sanar mana ba! Rashin amfanin mu har ya kai haka a wurin shi? Ko da yake nasan wannan duk aikin ƙanin ubansa ne wanda ya riga ya gama mallake shi sai yadda ya yi da shi!" Shiru dad ya yi yana kallon ta yadda take zazzaga masifa har rufe ido take, sarai ya san da su Deen ɗin sun tafi Funtua, bayan dawowar su daga sallar asuba ne ya faɗi mashi zai bi Fahad, anan har yake mashi magana kan abun da mom ɗinsu ta sanar da shi, Deen ya kwashe komai ya faɗi mashi har lokacin da 6acin rai a tattare da shi, ya ce ma dad din ya yi tunanin in ya zo zai samu kwanciyar hankali tun da ya daɗe bai zo ba amman tun yanzu mom dinsa ta fara ɗaga mashi hankali shiyasa gara kawai ya tafi Funtua ya san zai fi samun kwanciyar hankali a can, jin hakan ya sa dad ɗin nashi goya mashi bayan hakan, amman saida ya yi mashi magana kan yakamata su tafi da security saboda tsaro, Deen ɗin ya nuna mashi ba sai ya tafi da jami'ai ba in sha Allahu za su je lafiya, anan suka yi bankwana har da Fahad, ya ce mashi ya faɗi ma yayansa Alhaji Sa'ad wato mahaifin Fahad ɗin yana nan zuwa bada daɗewa ba. Da alamun kamar bai san komai ba ya tambaye ta ina suka tafi ne, a hasale ta faɗi mashi in da aka ce sun tafi, "Tohh..Funtua suka tafi ke nan, kuma tun da sassafe kamar waɗanda aka kora, maimakon in ma tafiyar za su yi su bari gari ya waye sosai bayan sun yi breakfast sai su tafi." Wata uwar ƙwafa mom ta yi rai a matuƙar 6ace ta ce, "Wannan duk aikin Fahad ne, kuma wllh sai na ɗauki mataki akan hakan, in ba shi da bai da hankali ba ta ya daga zuwan shi zai ja shi su tafi wata Funtua, kuma ya san halin rashin tsaron da ake fama da shi shine zai ja shi ba tare da jami'ai ba, wato komai zai same shi ma ya same shi. Wama ya sani ko wani setup ne shiyasa ya ja shi suka tafi su kaɗai, dama ai an ce makashin ka yana tare da kai, abun da ke faruwa ke nan yanzu da na jikin mutum ake cutar da shi...." "Subhanallahi! In sha Allahu hakan ma ba zai faru ba, ki rinƙa faɗin alkhairi pls." Dad ne ya faɗa jin irin maganganun da take faɗa mara sa daɗi, fuska a yamutse Leemarh take kallonta, wani 6acin rai take ji a cikin ranta jin yadda mom ɗin ke faɗan maganganu marasa daɗi akan Fahad, ga damuwar ya tafi ba tare da ta gan shi ba, kwantar mata da hankali dad ya shiga yi kan ba abun da zai faru in sha Allahu za su je lafiya, ganin ta wuce ciki ya sa shi tambayar ba taren za su fita ba? tana nufar cikin falon ta ɗan ɗaga masa hannu ta ce su tafi kawai ta fasa fita, ɗakinta ta nufa ta ɗauki wayarta ta shiga kiran wayar Deen sai faman jijjiga jiki take ta kasa tsayuwa a wuri ɗaya, Zaune suke cikin motar Fahad suna tafiya kan hanya, Fahad ne ke yin driving yayin da Deen ke a kujerar gefen sa, Fahad yana sanye da brown dress suit pant wato dogon wando ruwan ƙasa sai baƙar dress shirt ya yi tucking rigar a cikin wandon ya saka baƙin belt, ƙafafunsa sanye da luxury loafers irin rufaffun takalma marasa igiya, da gani ba sai an fada ba takalman masu tsada ne daga laushin jikin su da yadda suke salƙi, a nutse yake juya sitiyarin motar wutsiyar hannun shi na ɗaure da baƙin agogo shima sai salƙi yake, yayin da shi kuma tauraron ɗan kwallo wato Nuree yake sanye da farar high-end dress shirt tare da farin jeans ya ɗan matse daga ƙasa, a saman rigar ya ɗaura baƙar tailored blazer wato riga mai kaman jacket ta kawo mashi zuwa ƙasan kugunsa, bai saka ma6allan rigan guda biyu dake daga can ƙasa ba hakan yasa ana ganin farar ta ciki da ya yi tucking ɗinta da baƙin ubansun belt da kan shi ke wani irin ƙyalli, shima irin takalman dake ƙafar Fahad ne a tashi kafar iri ɗaya ya siya masu, hannun shi guda na ɗaure da agogo Rolex yayin da baƙar sumarsa ya yi baya da ita ya ɗaure ta daga ƙasa, Ya Allah! Yadda ya yi sai ka rantse hausa baza ta fito daga bakinsa ba, gaba ɗaya kana ganinsu ka san ba ƙananun kaya bane suka saka, yadda kayan suka yi fitting na su so well abun ba a magana sai daddaɗan ƙamshi ke tashi daga jikinsu, gaba ɗaya ya karaɗe cikin motar ya haɗe da sanyayyan iskan A.c, shima Fahad sumar shi ta sha gyara sai salƙi take, daga gaban Deen hular shi ce baseball baƙa ajiye wato irin hular da ake kira da face cap, tana da tambarin premium brand da aka yi ta daga gaba. A hankali sautin ƙira'ar da Fahad ya kunna ke tashi, dama shi haka yake da wuya ka ga yana driving ya kunna waƙa, duk da wani lokacin yana kunna music idan yana tafiya ba mai nisa ba ko cikin gari haka, Deen na zaune ya ɗan zamo jikinsa kaɗan ta yadda ya kwantar da kanshi a jikin seat ya lumshe idanunsa, idan ka gan shi zaka yi tunanin bacci yake, saidai ba haka bane yana bin ƙira'ar da ke tashi ne a cikin zuciyarsa, jefi-jefi suke yin magana tsakanin su sa6anin lokacin da suka taso hira suke sosai, yanzu da suka yi nisa ne suka rage yin magana ba kamar Deen da ya fara gajiya da zaman motan, har magana Fahad ya yi mashi na ko ya kwantar da seat ɗin ya ji daɗin zaman ya ce mashi a'a yadda yake ma lafiya lau. Tun da suka taho basu tsaya ba sai a checkpoint biyu da aka tsayar da su gaba ɗaya kuma da suka tsaya jami'an sun san fuskan Deen kuma dama suna da labarin zuwan shi, don akwai masu supporting team ɗinsa, hakan ya sa sun ɗan 6ata lokaci kaɗan a wurin gaisawa da su har da waɗanda suka yi hotuna da shi, Sautin zazzaƙar muryar mace ne ya karaɗe cikin motar daga wayar Deen, irin muryar na'ura ne ke faɗin, "Sweetheart is calling..." Saida muryar ta sake maimaitawa sannan Deen ya buɗe idanunsa, ɗagowa ya yi tare da gyara zaman shi ya kai idanunsa kan wayar tashi da ke ajiye gefen shi, lokacin da ya kai hannu ya ɗauko ta muryar ta sake sanar da shi contact mai sunan sweetheart na kira, a nutse ya furta, "Tell sweetheart I'm not available, am out of reach." Yana gama faɗin haka ya ɗaura wayar saman cinyar shi tare da mayar da kansa jikin headrest, daga sunan da aka sanar da shi ya san mom ɗinsa ce ke kira, kuma ko ya ɗauka ya san 6acin rai ne shi yasa ya ce a sanar da ita haka, _"Message sent: ' You're not available, you're out of reach."_ Muryar ta sake karaɗe cikin motar tana sanar da shi cewa ta tura saƙon abun da ya ce a faɗi ma sweetheart, shiru ya ɗan yadda suka yi da ita a daren jiya na sake dawo masa. Lokacin da saƙon da Deen ya ce a fadi mata ya riske ta na cewa baya available tamkar ta kurma ihu ta ji, sam ta kasa zama har lokacin sintiri take ta yi bata da burin da ya wuce Deen ya ɗauki wayar ta bashi umarnin ya juyo kada ya ƙarasa Funtua, sau wurin ukku tana kira duk saƙo ɗaya ake turo mata cewa he's out of reach, sanin cewa yana akan hanya ya sa bata kawo komai a ranta ba ta yarda da abun da ake faɗa mata, ranta ne ya bata ta gwada kiran Fahad tun da suna tare wataƙil shi ta same shi, hannunta har ƴar rawa yake wurin kokarin kiran Fahad, wanda ba zata iya tuna yaushe ne ƙarshe da ta yi waya da shi ba, akasi! Shima dai sanar mata ake da cewa baya available duk ta kira. Dama sanin zata iya kiran Fahad ya sa Deen ɗaukar wayar Fahad ɗin ya saka ta a flight mode shiyasa shima ta kasa samun shi. Ƙarshe jefa wayar ta yi saman gado tsabar takaici ta zauna a baki tana ta huci kamar zakanya. Lokacin da suka iso Kaduna Fahad ya yi mashi maganar bari su je wani eatery su yi breakfast, Deen ya ce mashi a can Zaria ba eatery mai kyau, Fahad ɗin ya amsa mashi da akwai har a cikin asibitinsu, Deen ya ce mashi ok lafiya lau shi baya jin wata yunwa sosai za su iya bari su ƙarasa in dai ba shi yana jin yunwa ba, "Kai dai ka faɗi gaskiya idan kana jin yunwa, na san ƴan ƙwallo cin abinci gare ku sosai." Fahad ya faɗa tare da ɗan murmushi idanunsa akan hanya yayin da suke tafiya cikin garin Kaduna, ɗan murmushi Deen ya yi jin abun da ya faɗa, kuma gaskiya ne shi kan shi baya wasa da abinci, ce mashi ya yi lafiya lau zai iya kaiwa Zaria ai still safiya ne, suka ci gaba da tafiya...... *_✨A CIKIN RAYUWA✨_* _By Zainab Bature_ _Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._ Page 10 Alhamdulillah sun iso Zaria lafiya. Kaitsaye ABUTH dake Shika suka nufa, inda anan Fahad ke aiki matsayin Specialist a Family Medicine, bayan sun isa cikin asibitin, General Outpatient Department (GOPD) suka nufa, Fahad ya parker motan a inda aka tanada don hakan, Deen ya ɗauki hularsa ya saka kafin ya fito, yadda gashin shi da ya faka ya ɗan fito daga baya ba ƙaramin kyau ya yi ba, Fahad da shima ya fito yana kallon sa da dan murmushi ya yi masa sannu da gajiyan hanya, shima murmushin ya mayar masa ba tare da ya ce komai ba suka nufi shiga wurin, nan fa Deen ya zama abun kallo a wurin mutanen da ke kai kawo a arean, duk da ba a gane ko waye saboda hular shi ta ɗan yi curved daga gaba kuma ya ɗan sauke fuskarsa, idan ba ya ɗaga kai ba ba a ganin fuskar tashi sosai, duk in da suka wuce sai sun bar ƙamshin jikinsu sai faman kallon su ake, hatta mutane masu aji kallon su suke, suna shiga block ɗin suka haɗu da wani likita ya yi shigar light blue ɗin dress shirt da dogon baƙin wando sai nicktie, a wuyansa ya rataya stethoscope, gaisawa suka yi da Fahad cikin harshen turanci, dama bayerabe ne sunan shi Dr. Hakeem kamar yadda Fahad ɗin ya kira shi da suna gaisawa, yana ɗaura idanunsa akan Deen za su gaisa ya gane shi, da alamun ɗan mamaki ya kalli Fahad da har za su wuce ya ce, "This man looks like your footballer brother?" (Wannan mutumin kaman ɗan uwanka ɗan ƙwallon ƙafa?" "Yes." Fahad ya amsa mashi fuska a sake. "Ahhh! Nice to meet you. I am a huge fan of yours and support your club, I love your playing style." Dr Hakeem ɗin ya faɗa ya ɗan kama bakin shi dake a washe cike da farin cikin ganin Deen, da ɗan murmushi Deen ya yi mashi godiya ya nuna shima ya ji daɗin haɗuwa da shi, yadda Dr. Hakeem ɗin yake magana da yake yana da budaɗɗiyar murya hakan ya jawo hankalin wasu dake wurin da basu lura da shigowar su Deen ɗin ba, kan ka ce mi, ai Dr. Hakeem har ya fara shelar zuwan Deen, gaba ɗaya hankulan mutanen wurin ma'aikata da wanda suka zo ganin likita ya dawo kan su, nan fa aka shiga zuwa ana gaisawa da shi kowa yana nuna farin cikin ganinsa tare da yabon shi, nan fa wurin ya cika da ma'aikata manya da ƙananu har da mata, daga bangarori daban daban na asibitin ake ta zuwa ganin Deen, mutane sai yin hotuna suke da shi, Fahad dai na tsaye gefe yana murmushin jin dadin yadda ake ta nuna haukan son ɗan'uwan nasa, ana haka sai ga Medical Director (MD) na asibitin, babban mutum ne ya ɗan manyanta kuma yana son kwallon ƙafa, sannan yana goyon bayan kungiyarsu Deen, yana kuma bala'en yin Deen sosai, yana shigowa wurin aka shiga bashi girma ana gaida shi, cike da zolaya yake ce ma mutane shi bata so yake ba su matsa ya ga tauraron shi, duk mutane suka yi dariya, yana zuwa wurin Deen ya jawo shi jikin shi tare da rungume shi, bayan ya ɗago shi cike da farin ciki yake faɗi mashi yadda yake son wasan shi da kuma kungiyarsu, sosai ya shiga yabon Deen da ke ta sakin murmushi, hotuna ya saka aka shiga yi masu da wayarsa, bayan an gama janye Deen ɗin ya yi ya ce duk mai son ganin shi ya zo office ɗin shi, tafiyar su taba Fahad damar fara yin abubuwan da ke gaban shi, workstation ya nufa don shirya fara duba marasa lafiya. Bayan zuwan su office din MD a can ya sa aka kawo ma Deen lafiyayyun abincin breakfast suka ci a tare dama MD din yana cikin cin abinci aka sanar da shi game da zuwan Deen ya tashi ba tare da ya ƙarasa. Fahad bai daɗe sosai ba yana duba marasa lafiya a consultation room ya tashi, dama bashi kaɗai bane akwai wasu likitocin a sauran ɗakunan da suke duba wasu marasa lafiyan, office ɗin MD ya wuce wurin Deen, a can shima ya yi breakfast duk da rana ta riga ta yi, saida suka yi sallar azahar da lokacinta ya yi kafin suka hawo hanya zuwa Funtua. Wuraren ƙarfe biyu saura suka iso garin Funtua, lokacin Deen ne ke yin driving ɗin, tun bayan da za su baro Zaria ya amsa har Fahad na ce mashi zai iya driving mai tsawo kuwa a titin Nigeria, yana murmushi ya ce mashi lafiya lau zai iya, ga shi har Allah Ya kawo su lafiya. Daga cikin wani ɗan lungu ta 6ullo, tana sanye da uniform riga da wando sai ƴar madaidaiciyar hijab wadda daga bayan saman kanta ya yi tudu sosai, tsaf-tsaf da ita duk da daga gani lokacin tashin su aka yi, amman sam ba datti a tare da kayan jikinta, a hannunta na hagu ƙatuwar baƙar jakar makaranta ce sargafe, yayin da ƙafafunta ke sanye da baƙaƙen takalma sneakers, kana ganinta ka ga ƴar makaranta mai natsuwa da tsafta. Tana ƙarasowa bakin hanyar ta tsaya tana dubawa ko akwai abun hawan da ya taho, bata hango wani abu ya taho ba bayan mashin ɗin da ya wuce daga 6angaren hagu, sai kuma motar da ta hango ta taho daga 6angaren dama, ganin kamar motar na ɗan nesa har ta tsallaka ba tare da ta ƙaraso ba ya sa ta hau hanyar da sauri a ƙoƙarinta na ta tsallaka, da alama idanunta sun hango mata ba daidai ba, don tana kaiwa tsakiyar hanyar motar da ta taho da matsakaicin gudu ta cimmata, kiɗimewa ta yi ta ruɗe ta rasa in da zata nufa tsakanin ƙarasa tsallakawa ko kuma komawa jin horn ɗin da aka shiga sakar mata a jere, ƙarar uban burkin da motar ta ci a dab da ita ne ya sa ta ƙara gigicewa ta saki jakarta tare da durƙushewa a wurin, gaba ɗaya ta saka tafukan hannuwanta ta rufe fuskarta gam, duk a tunaninta motar ta tashi da ita jikinta sai faman kerma yake, kamar yadda idanunta ke runtse haka ma Deen ya runtse idanunsa ganin haɗarin da ya kusa afkuwa, gaba ɗaya hannuwansa na riƙe da sitiyari gam, yayin da gaban shi ke ɗan faɗuwa, tun da suka taho lafiya lau yake driving ɗin shi bai haɗu da wata matsala ba sai yanzu. Da yake hanyar ba babban titi bane ba wasu ababen hawa sosai sai jefi-jefi, sai kuma wasu ƴan mutane da ke a ɗan can bakin hanya wasu a bakin shaguna, hakan ya sa ba idanun mutane sosai a kan su, sai waɗanda suka hango suka saki salati ganin abun da ya faru, horn mai ƙara da aka yi mata ya sa ta saurin ɗagowa, tana ganin gaban motar dab da ita bata ta6a ta ba ta yi saurin miƙewa, ko ta kan jakarta bata bi ba ta ƙarasa tsallakawa ta tsaya har lokacin jikinta bai bar kerma ba, cike da 6acin rai Fahad ya buɗe ƙofar motar ya fito idanun shi a kanta, "Ke baki da hankali ne? Baki ganin abu ya taho zaki hawo saman hanya!" Cikin yar tsawa ya yi mata maganar, kikkafta idanu ta shiga yi ta fara motsa baki sam ta kasa magana sai nishi take, "Baki ji ana maki magana!" Ya kwatsa mata tsawa ganin ta kafe shi da ido, "K...ka yi haƙuri, na yi zaton har zan tsallaka bata ƙaraso ba ne..." Katse ta ya yi a hasale ya ce, "Da yake baki da hankali, ko ke dabba ce? shiyasa kika kasa gane ko motan zai ƙaraso wurin ki?" Duk da halin da take ciki sai da ta ji maganar a cikin ranta, yanayin fuskanta ne ya sauya ta ɗan daure fuska, "C'mon go take your stupid bag ko mu take ta mu wuce, idiot." Wannan karon ɗan buɗe baki ta yi alamar al'ajabi, zata iya cewa tun da take ba wanda ya taba kiranta da waɗannan sunayen sai yau, motsa baki ta shiga yi tana ɗan gunaguni tana yi mashi wani kallo mai kaman harara ba tare da ta motsa daga inda take ba, "Zagi na kike yi??" A fusace ya tambaya, da yake rainon Sagir ce ya koya mata rashin tsoro da kuma kada a yi mata abu ta kyale, rai bace ta ce, "Ni ba zagin ka nike ba, kawai ya zaka ce mani mara hankali dabba kuma idiot bacin tun farko na baka haƙuri..." Mamaki ne shimfide akan fuskar shi jin yadda ta maida mashi magana tana yarinya ƙarama, "To an ce maki dabban ma, da akwai abun da zaki iya yi ne? Ai gara ma dabba dake don ita ba yadda za ai ta bari har mu ƙaraso mu same ta a saman hanyan." Rai 6ace ya yi maganar dama abun ka da mai zuciya, ƙwarjini ya yi mata ta kasa ce mashi komai sai ɗan ƙunƙuni da take yi, tafiya ta fara a hankali don ta je ta ɗauko jakarta, tsoki ya ja ya ce, "Ƙaramar mara kunya kawai..." Cak ta dakata da yin tafiya ta kalle shi a ɗan harzuƙe murya na rawa kaman zata yi kuka, "Ni dai ba mara kunya bace, kuma ni ba dabba ba ce wllh, koda na yi shiru ai ba don ina jin tsoron ka bane, kawai dai na san idan mutum ya kira ka da sunan abu kuma kai ba abun bane to..." Sam ta kasa ƙarasa maganar don sosai ya yi mata ƙwarjini, ko maganganun da take yi kawai ƙarfin hali ne, kashe shi da mamaki ta yi yanzu, daga yadda yanayin fuskarsa ya canza zaka fahimci hakan, ɗan ƙanƙance ido ya yi tare da ɗan yamutsa baki irin yaro bai san wuta ba sai ya taka, "Ni ne dabban ke nan?" Ya faɗa ya ɗan ɗage gira, juyar da kai ta yi tana ɗan motsa baki, ƙarasa fitowa ya yi daga jikin marfin motan yana faɗin bari ya zo sai ya ji da kyau abun da take faɗa, Deen na jin haka ya fara kiran sunan shi yana faɗin ya ƙyale ta pls amman bai bi ta kan shi ba, ya san abu mara daɗi na iya faruwa hakan ya saka shi saurin kai hannu ya buɗe motar, Fahad na zuwa kusa da ita ya ɗaga hannu zai zabga mata mari, bata yi ko gezau ba duk da ta fahimci abun da yake ƙoƙarin aikata mata, saidai ta ɗan tsorata da hakan da sauri ta runtse idanunta, "Pls ya Fahad let her be..." Deen da ya tare hannun nashi ya faɗi, sam baya son attention ɗin mutane ya dawo kan su saboda ya lura da wasu mutanen idanunsu na akan su duk da ba lalle in sun fahimci abun da ke faruwa ba, daddaɗan sautin muryar da ta ji ya ziyarci cikin kunnanta ne ya sa ta yi saurin buɗe idanunta don ta ga waye ya yi maganar, ita bata ma san su biyu bane a cikin motar ba saboda tinted ce ba a ganin wanda ke a ciki, kuma saboda ruɗewar da ta yi tun farko da motan ta kusa buge ta ya sa bata ma iya ta tantance Fahad ko daga bangaren direba ya fito ba, bin su da ido ta yi lokacin Deen ya kama hannun Fahad sun juya, saida ya kai shi har bakin mota ya roƙe shi ya yi haƙuri kada su zamo center of attention, bayan ya Fahad din ya shiga Deen ya juyo don ya koma side ɗin shi, lokacin da suka haɗa ido da ita har saida gabanta ya yi wani irin bugu da ƙarfi ganin irin tsantsar kyawun halittar shi, kallo ɗaya ya yi mata ya ɗauke idanun shi ya wuce, tamkar rainon sakarai haka ta ɗan saki baki ta bishi da ido, ba komai ya fi jan hankalinta tattare da shi ba face sumar shi da ya faka, kokonto ta shiga yi a cikin ranta na shine ya yi maganar da ta ji ko kuwa, sai take ganin wannan ai kaman baya jin hausa ma, sai da ya kai bakin ƙofar motar ya dakata tare da kallo ta, "Ki je ki ɗauki school bag ein ki ko mu bi ta kan shi mu wuce!" Cike da bada umarni ya yi maganar fuskarsa a ɗan ɗaure, mamaki ne ya cika ta jin da gaske shi yake yin magana da hausa, wucewa ta yi ta ɗauko jakar ta juyo suka haɗa ido ya shige cikin motar, tsaye ta yi a bakin hanyar tana bin motar da kallo har suka wuce, ita kam a rayuwar ta zata iya cewa tun da take bata ta6a ganin mutum mai kyau ba a zahiri kamar shi, sai dai ko a fina-finan ƴan ƙasar waje amman duk da haka gani take wannan kyawun na shi ma na musamman ne, tunanin ko su ɗin su waye ta shiga yi sai kuma take jin kamar ma ta ta6a ganin fuskokinsu ba kamar wanda ya kusa marin ta, wata zuciyar ce ta raya mata a ina zata ta6a ganinsu daga ganin su ba ƴan Nigeria bane ba kamar mai gashi a ƙulle, to amman suke yin magana da hausa? Ta jefa ma kanta tambayar, wataƙil suna zaune anan ne shiyasa suka iya ko kuma shi wanda ya kusa marin nata ne ɗan nan ƙasar, mai gashin a ƙulle ɗan ƙasar waje ne to sai ɗayan ya koya mashi hausar, haka ta dingi yin tunane-tunane a cikin zuciyarta tana tafiya sukuku da ita, a karon farko take jin kaman bata kyauta ba abun da ta yi masu, to amman koma miye wanccan ya ja duk da ta bashi haƙuri ya ce mata dabba, fuska a tur6une take tafiya tana raya hakan a cikin ranta. Lokacin da ta zo daidai bakin wani shago da wani ɗan magidancin mutum ke a tsaye yana kallon duk abun da ya faru ya ce mata, "Salma lafiya, mi ya faru ne tsakanin ki da waɗannan mutanen da suka wuce?" Fuska a yamutse ta kalle shi ta bashi amsa da ba komai sun kusa buge ta ne, daga haka ta wuce yayin da zuciyarta ke ta tariyo mata da fuskokinsu. Tun da suka ci gaba da tafiya Fahad ke ta ɗan jan tsoki tare da yin ƙwafa, ya so Deen bai hana shi ba da ya wawwanka mata marikan da gobe bazata sake yi ma wani rashin kunya ba, haƙuri Deen dake driving ke bashi yana ce mashi ya manta kawai irin yaran haka suke basu da ɗa'a, "Mtsww, ban san mi yasa su dad zasu bar hajja tana rayuwa a irin wannan local unguwan ba, ba komai a cikinta sai tarin illiterate mutane." Ya faɗa yana ƙara daure fuska, Suna wuce wata kwana dake a 6angaren hagun su, a daidai bakin gida na farko dake a bakin hanyar ya fara ƙoƙarin karya kan motar, cikin wasa ya ce Allah Ya sa nan ne gidan hajjan bai manta ba, yanayin fuskar Fahad ne ya ɗan canza kaman zai yi murmushi ba tare da ya ce komai ba sanin da wasa ya yi maganar, kana gani kasan ba ƙaramin babban gida bane yadda katanganar shi ke da tsawo a bakin hanyar, jami'ai biyu ne zaune a bakin tangamemen baƙin gate ɗin shiga gidan, daga yanayin yadda aka tsara ginin katangar gidan ma zaka san cikin gidan ma ba ƙaramin haɗuwa ya yi ba, akwai shuke-shuken fulawoyi masu kyau da tsari da fitulu a wajen, daga waje kana hango wasu shuke-shuken dogayen fulawoyi dake a cikin gidan. Jami'an na ganin motar ɗaya ya miƙe daga saman bencin da suke zaune don ya je ya buɗe masu gate sanin motar ko ta wacece, yana gama buɗewa motar ta kutsa kai jami'an na ɗaga ma motar hannu don duk a zaton su Fahad ne kawai a ciki. "Ko dai shine ya iso?" Wani matashin mutumi ne ya faɗi hakan daga bangaren daman dake kallon gidan suna zaune su ukku a bakin wani shago, "Anya kuwa, idan shine ai ba zaka ganshi ya zo a mota ɗaya ba kuma ba tare da jami'ai ba, sannan bana ma tunanin zai hawo waccan motar sai dai wadda ta fita." Guda ne a cikin su ya furta. "Ai bama shi bane, waccan motar ta wannan jikan gidan likita ce, ya ma sunan shi...yauwa, Fahad ɗin nan." Wanda shine mai shagon ya faɗa. Su nan duk ƴan ƙwallo ne zaman dakon zuwan Deen suke tun da suka gani a facebook cewa yana a Zaria, shine suke tunanin daga can ƙilan nan Funtua zai wuto. "Amman bakwa gani ko tare suke? Ai dama hoton da muka ga ni ɗazun an yaɗa a Zaria ne suka yi shi kuma tare da likitoci suka yi shi." Wanda ya fara yin magana tun farko ne ya sake fadin hakan, cike da kokonto na biyun ya ce gaskiya dai ƙilan shi likitan bada motar ya je wurin aiki ba don ba yadda za ai Nuree Jr ya yo irin wannan shigowar, haka dai suka yi ta faɗin hasashen su. Kai tsaye babban parking space ɗin gidan suka nufa wanda zai iya ɗaukar motoci shidda, bayan sun faka a kusan tare suka fito Deen na riƙe da hular shi a hannu, ƴar miƙa ya yi tare da faɗin Alhamdulillah, Fahad dake kallon shi daga ɗayan bangaren da ɗan murmushi ya ce halan ya gaji, "Sosai, it has been a long time ban yi driving haka ba, and tuƙi a Nigeria sai mutum ya saka kula sosai saboda yanayin hanyan ba kyau." Murmushi kawai Fahad ɗin ya yi, officern da ya buɗe masu gate yana gab da rufewa ya ga sun fito, dakatawa ya yi yana kallon Deen cike da mamaki, sam bai kawo ma ransa zai ganshi ya fito daga cikin motar ba, duk da suma sun ga hotunan shi da aka wallafa cewa yana Zaria, da sauri ya juya kan abokin aikin shi ya sanar da shi ga Nuree nan sun zo tare da Fahad, yana jin haka ya yi saurin miƙewa yana tambayar shi da gaske, tare suka shigo cikin gidan suka nufo su, da ɗan ɗaga murya guda ya fara faɗin, "Barka da zuwa yalla6ai...." Ya yi hakan ne don ya dakatar da su ganin suna ƙoƙarin shiga cikin gidan, cikin washe baki suka shiga gaisawa da shi suna mashi an zo lafiya, yana amsa masu cikin sakin fuska Fahad na daga gefe shima suka yi mashi sannu da zuwa, bayan sun gama gaisawa har za su wuce, ɗaya daga cikin officers ɗin ya ce mashi pls bari su ɗan yi hoto yana fiddo waya, Deen ya basu damar hakan, bayan sun yi hoton suka wuce suma su officer ɗin suka nufi komawa gate cike da zumuɗin zuwa su yaɗa labarin zuwan shi da hoton da suka yi. Harabar gidan na da girma sosai, bangare biyu ne a cikin gidan, akwai bangaren iyayen Deen wanda ƙaton ginin bene ne yana daga can ciki amman tun a bakin gate kana shigowa zaka hango ginin saman benen, 6angaren hajiya shine a farko wanda shima babban flat ne mai kyawun gaske, daga gefen ginin hajiyan ana hango wani 6angare na jikin ginin su Deen kuma ta nan ake bi zuwa can bangaren. Page 11&12 WAIWAYE Lokacin da Hajiya Binta ta auri mijinta marigayi Amb. Nuraddeen, duka bata wuce shekaru goma sha huɗu ba, lokacin iya karatun ƙaramar sakandire ta yi, sai bayan shekaru da yin auren su lokacin suna zaune ƙasar waje ta samu ci gaba da karatun ta in da har ta kai matakin digiri na biyu a fannin kasuwanci, hakan yasa ta kasance babbar ƴar kasuwa ce dake yin kasuwancinta tsakanin ƙasashe daban-daban, ta kasance tana siyar da furniture na ƙasashe daban- daban da kayan sakawa da su akwatuna, jakunkuna, takalma, tana da plaza fin ɗaya dake da manyan shaguna na kaya da ake kula mata da su anan Funtua da kuma Zaria, haka kuma tana da motoci da ake haya manya da ƙananu da kuma keke napep da mashina, sannan kuma itama tana gonaki da ake mata noma sosai. Koda yanzu Hajiyar Ambasada ta tsufa har yanzu kasuwancinta na saro kaya daga ƙasar waje na tafiya lafiya lau don ta kafu sosai, tana da connection mai ƙarfi da kamfunan da take sarar kaya na ƙasashen waje, kuma tana da amintattun mutane dake mata hidimar komai. Mahaifin su Fahad ne ɗanta na farko da ta haifa bayan shekaru ukku da yin aurenta, a yanzu yana cikin shekara ta hamsin da bakwai, sakamakon ya fara yin aiki da wuri hakan yasa ya yi retire kafin ya kai shekaru sittin. Lokacin da ya kammala karatun shi na degree mahaifin su babban ma'aikacin ma'aikatar harkokin waje ne hakan ya sa aiki bai mashi wuyar samu ba. Sai mahaifin su Deen wanda a cikin shekarar da ake yake cika shekaru hamsin da biyu, gaba ɗaya karatun su ba anan ƙasar suka yi shi ba hakan yasa suke kammalawa da wuri. Bayan mahaifin su Fahad ya fara aiki bada jimawa ba yana da shekaru 27 aka yi auren shi da Hajiya Amina, auren zumunci ne aka yi masu don ƴar'uwar su ce matsayin cousin ɗinsa take, tun kafin ya kammala karatun shi soyayya mai ƙarfi ta ƙullu tsakanin su a zuwan da suke yi, anan Funtua mahaifin shi ya gina mashi gida wanda shine har yanzu suke a ciki, bayan shekara ɗaya daidai da yin auren aka haifi Fahad. Daga baya lokacin da Alhaji Sa'ad ya yi kuɗi sosai ta hanyar aiki da sana'ar noman da suke yi ne ya ƙara faɗaɗa gidan da suke tare da ƙawata ginin daga flat ya koma babban ginin bene. Da yake irin aikin mahaifin shi ne ya yi hakan yasa suma sun ɗan zauna a wasu ƙasashen sai dai basu kai yawan ƙasashen da mahaifinsu ya yi aiki ba, kuma shi bai samu kaiwa matsayin Ambassador ba ya ajiye aiki amman ya kai daga cikin manyan matsayi a aikin. A bangaren Jameela mahaifiyar su Deen, ta kasance ita ce babba a gidan su, sai mai bi mata wato Sapna, Bashir shine na ukku sai mai bi mashi Naila, akwai ƙanwar su ta biyar Aseeya sai ɗan autan su namiji Adam dama su shidda ne a gidan su. Su Jameela sun kasance ƴan Kano duk da asalin tushen su ba ƴan nan ƙasar bane daga Nijar suke, ahalin su sun kasance nau'in mutanen da ake kira da sadakar yalla, wanda suke wani rukuni daga cikin mutanen da ake kira buzaye. asalin garin kakanninsu a Nijar ya kasance ɗan karamin gari a hamada, inda rayuwa take matuƙar wahala, sun shigo Najeriya cikin ayari da ya ƙunshi dangi da kuma wasu ƴan garin su don samun sauƙin rayuwa. A lokacin iya yayan mahaifin su Jameela mai suna Amadu kawai suka haifa, daga baya a nan Kano aka haifi mahaifinsu Jameela wato Abdullah, sai ƙanwarsa wadda ita ce kuma ta ƙarshe a ɗakin su babansu mai suna Maryam. Mahaifiyar su Jameela wato Haleema ta kasance yar'uwar babansu ce, matsayin ɗiyar ƙanin babanshi ce, kuma har da iyayen nata aka zo garin Kano. Itama Haleema a nan Kano aka haife ta kuma ita kaɗai iyayenta suka haifa, mahaifiyarta na da cikinta Allah ya yi ma mahaifinta rasuwa sanadin mota da ta buge shi, bayan watanni da haihuwarta itama mahaifiyar tata ta rasu, hakan yasa rainon ta ya dawo hannun mahaifiyar baban su Jameela. Farkon zuwan kakannin su Kano, sun kasance basu da taƙamaiman matsugunni, daga baya suka fara aikin gadi a wuraren da ake manyan gine-gine ana basu wurin zama. Amadu yayan babansu Jameela ya kasance jajirtacce mai ƙoƙarin neman na kai, tun yana ɗan matashi yake bin kasuwanni yana yin aikin yaron shago da dakon kaya, daga baya ya fara yin sana'oi irin su sayar da turare, ƴan kunne, zabba da sauran su, sa6anin mahaifin su Jameela da ya taso a malalaci saidai komai Amadu ya yi masa. Sosai Allah Ya buɗa ma Amadu har ya siya ma iyayensu ɗan madaidaicin gida gaba ɗaya suka koma, ya kuma saka mahaifin su Jameela a makaranta tare da ƙanwarsu sai mahaifiyar su Jameela da iyayen su ke riƙo wadda kusan sa'ar Maryam ce. Daga baya Amadu ya auri wata bahaushiyar yarinya da suke soyayya yar nan Kano mai suna Hafsa, wadda da ƙyar iyayenta suka yarda ta aure shi saboda asalin sa. Ƙanwar su Maryam na aji ukku na sakandire wani alhaji ya fito neman aurenta aka bashi musamman ganin yana da kuɗi, a lokacin ne shima Abdullah ya bayyana ma iyayensu cewa yana son auren Haleema, farko ta nemi bijire ma auren shi saboda tana ganin Maryam ta samu babban mutumi mai kuɗi, shi kuma ta raina ma girmansa gashi bai da komai ya ƙi kuma tsayawa ya yi sana'a, duk in da ya fara aiki ba a ɗaukar lokaci ake sallamarsa saboda maular tsiya ga rashin gaskiya, ga kuma shaye-shaye da ya fara sakamakon biye ma abokan banza. Duk da Haleema ta nuna bata son auren Abdullah, haka iyayen shi suka tursasa mata har da su gorin rainon ta da suka yi, tana ji tana gani aka yi mata auren dole da shi, suka tare a ɗakinsa dake a gidan, ita kuwa Maryam gidan da aka kaita mai kyau har da gate. Farko Haleema ƙin amince ma Abdullah ta yi, sai da ta kai sai ya haɗa mata da bugu sannan abu ke shiga tsakanin su, da ta yi mashi laifi sai ya kai ƙarar ta wurin iyayensu a yi ta mata faɗa, a haka ta samu cikin Jameela ba wata kulawa da take samu ta buƙatun mai ciki daga wurin shi, sauƙin ta Amadu da ke taimaka mata, dama duk shine ke ɗaukar dawainiyar su, wanda a lokacin babbar mota yake ja yana kai kaya da ɗaukowa daga kudu, ta 6angaren Maryam ma tana taimaka masu bakin gwargwado. Lokacin da cikin Haleema ya kai wata tara ta haifo santaleliyar ɗiyarta, tun a asibiti ake ta santin kyawun Jameela, haka ma mutanen unguwa musamman jin yadda ake zuzuta kyawun jaririyar wasu ke zuwa barka, tun da Allah Ya sa Haleema ta ɗaura ido kan kyakkyawar jaririyar tata wata irin ƙaunar yarinyar ta shiga zuciyarta, wannan dalilin ne kuma ya sa ta yada duk wasu makaman ƙiyayyar da take ma Abdullah ta saki jiki suka ci gaba da rayuwa irin ta ma'aurata. Ba irin ƙoƙarin da Amadu bai yi ba wurin ganin ya ɗaura Abdullah hanyar da zai gyara rayuwarsa ya kama kwakkwarar sana'a ba kamar da ya fara aje iyali, sai ya yi kaman ya canza sai kuma ya koma gidan jiya. Bayan wasu shekaru kakannin su Jameela duk suka rasu, lokacin Maryam sun bar Kano sun koma Lagos da zama kuma tana ci gaba da taimakon su musamman da kuɗi. Akwai wani makwabcin su mai suna Alhaji Mahmud, ya kasance attajirin mai kuɗi ne da ke yin kasuwanci ƙasashe daban-daban, lokacin da su Jameela suna yara mahaifin su ya ta6a yin aikin gadi a gidan Alhaji Mahmud ɗin, wanda gidan katafaren gida ne na gaske, daga baya ne Alhajin ya sallami mahaifin su Jameela saboda ya gaji da halin shi na maula, duk da albashin shi da ya tsare mashi yake bashi akan lokaci sannan da wasu alkhairan da yake mashi kamar na kayan abinci haka in salla ta yi har kuɗi yake bashi don ya yi ma yaran shi kayan salla amman hakan bai isa ba, duk wata matsalar shi sai ya kawo ma alhajin, ko iyalan shi ne basu da lafiya alhajin ne zai biya kudin asibiti ko magani, ganin gaba daya ya maido mashi nauyin iyalinshi da kuma yadda su Jameela suka mayar mashi da gida tamkar na su, a nan suke wuni su ci abinci wani lokacin har kwana, sau da yawa sai ya yi ma matarshi hajiya Aisha magana kan ta sallame su su koma gidansu sannan wani lokacin suke tafiya, waɗannan dalilan ne suka sa Alhaji ya sallami babansu daga yi mashi aikin gadin ya nuna mashi a yadda yake da iyali kamata ya yi ya nemi wata hanya da zai rinƙa samun isassun kuɗin da zai rinƙa ɗaukar nauyin iyalan shi, har da jari ya bashi don ya fara yin sana'a, sam baban su Jameela bai so hakan ba don ya saba da samun komai bati, ƙarshe dai ba wata sana'ar kirki da ya kama haka suka cinye kuɗin ya koma yin maulan da ya saba da kame-kamen sana'oi, aka ce zama da maɗaukin kanwa, itama matar tashi ta yi aikatau a wasu gidajen masu kuɗi, sai dai duk abu ɗaya ke sa bata daɗewa ake sallamarta, ita ban da maula da rashin gaskiya har da munafunci, ƙarshe ta koma yin sana'ar kitso, gidanta ya koma matattarar gulma da ɗaura mata kan gur6atacciyar hanya. Duk da mahaifin su Jameela ya bar aiki a gidan Alhaji Mahmud hakan bai sa sun daina zuwa ƙwaƙwa ba, ba kamar Jameela da take ƙawance da ɗiyar Alhajin wadda tsararta ce mai suna Safiyya suna kiranta da Soffy. A haka su Jameela suka taso a wannan gidan, saidai iyayen su sun kasance ba irin iyayen nan bane masu bama tarbiyyar ƴaƴansu muhimmanci, hakan yasa suka sake su suna abun da suka gadama, rashin halin iyayensu yasa wasu daga cikin yayan suka raina ma arzikin iyayen suka zama masu kwaɗayi da hangen na wani, sun kasance irin waɗanda basu da gashin wanccan su ce sai sun yi kitson wance, hakan yasa suke liƙe ma yaran masu kuɗi ga yin samarin tsiya, da yake Allah Ya yi masu baiwar kyau, gaba ɗaya yaran gidan su ba munana bane saidai kyawun wani ya fi na wani, saboda kyawun dake gare su hakan yasa suke yin samari masu kuɗi ko yaran masu kuɗi, a wurin su suke samun kuɗaɗen da suke fantamawa suke yin rayuwa tamkar yaran masu hannu da shuni, wanda idan baka san su ba aka faɗa ma iyayen su talakawa ne har rantsewa kana iya yi cewa ƙarya ne aka faɗa maka, to da yake suma iyayen nasu masu shegen son abun duniya ne hakan yasa sam basa kwa6ar su kan yadda suke samo kuɗi, ba kamar da yake suma suna yagar rabon su kuma ana kawo masu kayan daɗi suna ci, gaba daya sun maida yaran nasu kamar jari har hure masu kunne suke yi kan yadda suke da kyawu kada su sake su rinƙa kula maza marasa kudi, har huɗuba suke masu idan aka ce ana son su da aure kada su amince su yi aure da wuri su bari sai sun gama cin ƙuruciyar su in ba haka ba da an aure su zasu daina samun duk alherin da maza ke yi masu su koma sai yadda aka yi da su. Da yake wani lokacin a gida akan samu wanda ya fita zakka, to suma a gidansu Sapna wadda ita ce ke bi ma Jameela ta fita zakka, tana da kamun kai da natsuwa gata tana son karatu kuma ba laifi tana da ɗan ƙoƙari, sa6anin Jameela da sauran ƙannansu waɗanda sam basu wani fahimtar karatu, Allah dai ya basu kyawun sura amman ƙwalwarsu yadda kasan dusa ce a ciki saboda rashin fahimtar karatu, ita Sapna karatu kawai tasa a gabanta sam bata kula samari, ba kamar Jameela ba da tun tana firamare take da samari kuma suke bata kuɗi, wani lokaci har faɗa iyayensu suke ma Safna akan rashin kula samarin da take yi, suna cewa wai tana masu baƙin cikin alherin da zata sama masu kamar yadda suke samu da ƴar uwarta Jameela, sam bata biye ma huɗubar iyayensu duk faɗan da zasu yi mata, karatunta na boko da islamiyya kawai ta saka a gaba, saboda rashin kula samarin da take yi yasa wani lokacin in ta kawo masu buƙatar da ta danganci karatunta sai su ƙi yi mata, su rinƙa cewa da tana kula samari tana samun kuɗi ai da ta rinƙa biya ma kanta buƙata har ma da nasu buƙatun, da yake tana son karatunta bata son abun da zai yanke mata shi hakan ya sa wani lokacin take tambayar Jameela kuɗi, idan ta ci sa'a ta bata, wani lokacin kuma idan Amminsu na kusa sai ta hana Jameela ta bata wai duk don ta ji matsi ta rinƙa kula samari amman hakan bai sawa ta canza. Akwai wani lokaci da ta rasa ina zata samu kuɗin da zata siya littafai don nata duk sun cika sai dai ta samu paper ta yi rubutu sai ta sa cingam ko kuma ta je jikin wata bishiyar makarantar su ta samo ƙwaro sai ta haɗe paper din da karshen littafin, har ta kai bata da sauran paper din da zata rinka yagowa, data rasa mafita gashi gida an ƙi bata kuɗi ta siya, ƙarshe a 6oye ta je gidan su Soffy wurin mahaifiyarta Hajiya Aisha, tana ƙwalla ta sanar da ita halin da take ciki game da karatunta, saidai bata faɗi mata cewa saboda bata kula samari ya sa iyayensu basu bata kuɗin siya ba, kawai ce mata ta yi sun ce basu da kuɗi, lokacin Hajiya Aisha ta ji tausayinta sosai musamman yadda ta san halin Safna ɗin ba irin na sauran yan uwanta bane, bata da kwaɗayi ko ta saki baki ta faɗi matsalan da ta danganci kanta ko gidan su da sunan a taimaka mata, wannan ne karo na farko ma da ta kawo kukanta wajenta, a lokacin Hajiyar ta ce mata ta je gida zata bada a kawo mata littafan, amman sai ta nuna mata ba a san da ta zo ta fadi mata ba bata son hakan ya sa a buge ta in aka ji ta zo ta roƙe ta, Hajiyar ta fahimce ta ta ce mata shike nan ta je zuwa anjima sai ta dawo, bayan tafiyarta ne ɗiyarta Soffy ta shiga bata labarin irin wahalan da Safna din ke yi akan karatu, ta ce mata kullum a ƙafa take zuwa makaranta ta dawo, kuma wani lokacin ko kuɗin break ma ba a bata ga kayan makarantarta duk sun tsufa sun yage, Hajiya ta ƙara jin tausayinta ya kama ta dama ta na son yarinyar saboda natsuwarta. Bayan Sapna ta dawo da daddaren Hajiya ta sa ta zauna a falo, lokacin dad ɗin su Soffy na nan ta iske shi a falo, bayanin Sapna ta yi mashi ta roƙe shi kan ya taimaka mata a karatun ta, farko ya nuna shi ya yi masu duk abun da zai iya tun da ya ba mahaifinsu jari, wanda inda ya jajirce ya yi kasuwanci ai da duk ya ɗauki wata ɗawainiyar su, cikin lallami da kwantar da kai ta shiga nuna mashi yarinyar ta fita daban da yan'uwanta kuma tana son karatu, ta roƙe shi kan ya taimaka mata tun da su iyayen nata ba ɗaukar ilimin suka yi da mahimmanci ba, cikin nasara ta ja hankalinsa ya amince da zai taimaka ma karatun Sapna. Daga ranar Hajiya ta sa ta rinƙa zuwa da safe idan driver zai kai yaran gidan makaranta sai a tafi da ita a sauke ta a tasu makarantar, sannan duk wata buƙata ta karatunta ta ce ta rinƙa zuwa tana faɗa mata, har sabbin kayan makaranta da jaka da takalma suka siya mata, Sapna ta ji daɗin hakan kuma sosai ta ci gaba da maida hankali akan karatunta ba ruwanta da kula samari. A shiriri ce Jameela ta kammala karatun ta na sakandire, daga nan bata ƙara bin ta kan karatu ba sai biye ma samari. Duk halin da suke ciki yayan baban su Amadu ya sani, kuma yana tsawartar ma iyayansu sosai kan rashin kula da tarbiyyar yaransu, ƙarshe sai suka maida shi tamkar abokin gabansu, Amminsu ta zuge abbansu wai baƙin ciki yake masu Allah Ya basu yara kyawawa suna samun alheri da su ba kamar nashi yaran ba, har da cewa baya son ci gaban su ya fi son kullum su yi ta zama ƙarƙashin shi yana taimaka masu, ƙiri-ƙiri suka yanke zumunci da shi, hatta yaran nasu suka dasa masu haushin shi a zuciya, ita dai Sapna ba ruwanta ba abun da ya canza daga bangarenta tana zumunci da su, hakan ba ƙaramin ciwo ya yi ma Amadu ba ya shiga damuwa sosai, matarsa Hafsa ta rinƙa kwantar masa da hankali ta ce ya rabu da su kawai tun da ya yi bakin ƙoƙarin shi ya sauke hakkinsa na ɗan'uwan su. Bayan ɗan lokaci da hakan Amadun ya haɗu da haɗarin mota wanda ya yi sanadiyyar rasa rayuwarsa, a lokacin yana da yara biyar. Lokacin da Soffy ɗiyar Alhaji Mahmud ta fara karatu a jami'ar BUK hakan ya ja hankalin Jameela ta ji tana son itama ta fara yin karatun jami'a, da yake a lokacin ta zama babbar yarinya idan ka ganta zaka yi tunanin ta girme ma shekarunta saboda tana da ƙira irin ta manyan mata masu diri, hakan ne ma ke ƙara jawo mata samari saboda kyawun surar ta, akwai wani babban mutum ɗan siyasa da take tare da shi a lokacin, tun farkon haɗuwar su ya nuna yana son aurenta amman ta ƙi amincewa ta nuna mashi ita gaskiya ba yanzu zata yi aure ba saboda yarinya ce ita ba wata babba ba, da yake yana samun yadda yake so a wurinta hakan yasa yake sakar mata kuɗi duk abun da take so yana yi mata. Lokacin shi ta yi ma maganar tana son ci gaba da karatu, saidai koda aka amso result ɗinta gaba ɗaya Waec da Neco abun ba kyawun gani duk F9, a lokacin alhajin nata ya ce mata ba yadda za ai ta samu ci gaba da karatu da wannan sakamakon, ganin ta shiga damuwa sosai ya kwantar mata da hankali da cewa hakan ai ba wata babbar damuwa bace, ya nuna mata su da suke da hanya za a canza mata wata jarabawar bama sai ta sake yi da kanta ba. Haka kuwa aka yi sai gashi an yi mata wata jarabawar kuma duk ta ci, ba tare da wata wahala ba sai gashi ta samu admission itama a BUK. Lokacin data fara karatun ita Soffy har ta shiga shekara ta biyu, amman duk da haka manne take da ita, duk ƙawayen Soffyn ta maida su itama ƙawayenta musamman da yake duk yaran masu kuɗi ne, cikin ɗan lokaci sai gashi ta yi suna a makarantar, ba iya yan set ɗinta da na Soffy ba, har cikin manya yan shekarar ƙarshe tana da abokai maza da mata, da yake abu mai kyau na da jan hankali hakan yasa duk waɗanda take manne mawa ta nuna tana son ƙawance da su basu gudun ta ko hantarar ta sai ma son ta da suke yi. Sam Jameela bata wani maida hankali akan karatu sai shiriritar abokai da samari, wani lokacin har makarantar ake zuwa a ɗauke ta, hatta cikin lakcarorin su tana da samari, gata yar ina da biki ce da ta ji cikin abokanta ana maganar biki sai ta je ko ba a gayyace ta ba har da su ƙarfin halin yin anko, ba kamar in ta ji bikin masu kuɗi ne ta dingi faman zura jiki har sai ta samu shiga. Da yawa waɗanda basu santa ba a makarantar sun yi zaton ɗiyar wani ce saboda kyawunta da yadda take saka suturu, wasu a tunanin su ita ɗin ƴar'uwar su Soffy ce, kuma sam Soffyn ba ta fallasa ko ita wacece, sai wasu daga cikin ƙawayen Soffy da suke tare tun kafin su zo jami'a kuma sun san gidan su da kuma alaƙarta da Jameela, sune suke fallasa ko wacece ita ganin irin yadda take rawar kai tana nuna kamar ɗiyar uban wani ce ita. Ganin suna karatu jami'a ɗaya da Soffy yasa ta koma tana tarewa a gidan su, ta ci abinci ta yi wanka har aron kayan Sophia ɗin take waɗanda za su yi mata don ta fita garin jiki, duk da yawanci ma in ta arar mata kaya cewa take ta bassu, da yake mahaifiyar su Sophia din mutuniyar kirki ce sam bata da matsala hakan yasa Jamila ke cin karanta babu babbaka a gidan, saidai mahaifin Sophia ɗin bai cika son yana ganinta a gidan shi ba, har ƙawancen da take da ƴar shi baya so saboda duk an san yaran gidan su basu da tarbiyya, akwai lokacin da har magana ya yi ma mom din Sophia, kan baya son ƙawancen da take da ƴar shi bai son ta gur6a ta mata tarbiyya, lokacin mom din Sophia ta nuna mashi cewa raba su lokaci guda abu ne mai wuya tun da tare suka taso, kuma za a iya raba su su zagaye su koma a tare ta bayan fage, kuma hakan na iya haifar da abun da ake gudu, ta nuna mashi gara a ƙyale su su ci gaba yadda suke ana saka ido ana sanin wane hali suke ciki. Lokacin ya ɗauki shawararta, saidai ita kanta Jameela ta fahimci baya son zuwa gidan shi da take don duk ta zo ta iske shi ta gaishe shi haka yake amsa mata ba yabo ba fallasa, hakan ya sa sam bata sakewa yadda ta saba in har yana a gida, da yake kuma mahaifin Sophia bai cika zama ba yana yawan fita ƙasashen waje harkar kasuwancin shi, har da wannan ke bata dama take sakata ta wataya son ranta, har wasu cikin samarinta yaran masu kuɗi nan take kawo su a zuwan nan gidan ƴan'uwanta ne anan take zaune, da yake kuma maigadin gidan Garbati mayen son kuɗi ne, kuma shima dai ba wani na kirki bane sosai hakan yasa yake bata goyon bayan da take so ba kamar da tana bashi kuɗi masu yawa, wani lokacin da taimakon mai gadin wasu cikin samarinta har shiga take da su cikin gidan su zauna a cikin rumfunan shaƙatarwar dake a can gefe guda ba tare da sanin masu gidan ba har su yi zancen su su gama. Akwai wata rana da tana cikin yin zancen a gidan mahaifin Sophia ya ritsa da ita, ranshi ya 6aci sosai ganin har zance take mashi a gida, inda ta ci sa'a a ranar bai yi mata magana ba a gaban saurayin, sai da ya shiga ciki ya balbale mom ɗin Sophia da faɗa duk da ta nuna mashi bata da masaniya akan hakan amman bai yarda ba, shima mai gadin sai da ya sha faɗa sosai ya yi ta ba Alhajin haƙuri, yana cewa ya ga an bata dama tana zuwa gidan sosai shiyasa bai hana ta shigowa da samari ba a zaton shi Hajiya ta sani, lokacin alhajin ya gargaɗe shi akan kada ya sake bari ta shigo mashi da wani a gida in ba haka ba zai ja ma aikin shi, ya ƙara da cewa ko ɗiyar shi ya hana ta kula samari saboda karatu yake son ta yi akan me wata zata riƙa shigo mashi da ƙattakai cikin gida, jin hakan yasa Garbati mai gadi ya ce ma Jameela ta yi haƙuri ba zai ci gaba da barinta tana kawo samarinta ba kamar yadda suka saba ya faɗa mata yadda suka yi da Alhaji, sam a lokacin bata ji haushin alhajin ba don ta san gaskiya ya faɗa, ɗiyar shi Sophia ba ta kawo samarinta gidan duk da tana da su saidai su yi waya ko su haɗu a wasu wuraren. Akwai wata rana bayan Alhaji Mahmud ya dawo daga tafiyar da ya yi ya ɗan kwana biyu baya nan, lokacin ya je masallacin dake a jikin gidan shi, bayan gama yin sallar ne suka gaggaisa da mutane da yake shi ɗin mutumin kirki ne da ya san hakkin makwabtaka, yana da taimakon mutane sosai musamman waɗanda basu da shi ko aka zo neman taimako wurin shi, bayan sun gaisa da limamin masallacin ne ya ce mashi in ba damuwa yana son za su ɗan tattauna wani batu mai muhimmanci, jin hakan yasa Alhaji Mahmud fasa tafiya ya zauna tare da tattara hankalinsa akan liman, a nutse ya fara yi mashi magana, "Wato Alhaji Mahmud dama magana nike son yi maka game da wani abu da ke faruwa, ina hango cewa idan aka yi sake al'amarin na iya haifar da gagarumar matsalar da ba a fata, hakan ya sa na yanke shawarar tunkararka da maganar a matsayin gyara kayan ka. Kuma ganin ana zama na amana da juna bai kamata a ce in an hango wani abu da ka iya zamewa matsala ba ai shiru ko don a fita hakkin juna...Dama game da ƴar wajenka ne Safiyya da kuma yarinyar gidan Abdullah Buzu..." Wani irin faɗuwa gaban Alhaji Mahmud ya yi jin abun da liman ya ce, dama sam hankalinshi bai kwanta da tarayyar su biyun ba, gyara zama ya yi sosai ya ce ma Liman wace matsala ce ya gani don Allah Ya faɗa masa kuma kada ya ji nauyin faɗa masa komai, "Su ƴa'ƴa da Allah Ya bamu Amana ne a gare mu Alhaji Mahmud, kuma tabbas Allah zai tambaye mu akan yadda muka kula da wannan amanar, a matsayin mu na iyaye ya kamata muna kula sosai akan al'amuran yaranmu, mu kasance muna masu basu kariya daga dukkan wani mummunan abu da muka hango yana tunkaro su...Duk mun san irin halayen yaran dake a unguwar nan, ba zancen ganin ido ba Alhaji kowa ya san yarinyarka Safiyya tana da kyawawan halaye, kun yi ƙoƙari matsayin ku na iyayenta wurin ganin kun bata tarbiyya duk da kasancewarka ba mazauni ba, sai aka ci sa'a da mahaifiyarta ma jajirtatta ce wurin hakan...Ba sai na fito fili na bayyana maka irin halayen yaran Abdallah buzu ba don hakan a bayyane yake, kuma kai zaka ma fi mu sanin halayyar su tun da kusan a unguwar nan sun fi shiga gidan ka akan na kowa tun lokacin da mahaifin su yana aiki a ƙarƙashin ka..." A nutse cikin kwantar da murya ya shiga nusar da Alhaji illar da yake hangowa a ƙawancen Safiyya da kuma Jameela, ya kuma nuna mashi irin ƙarfin tasirin da abokai suke yi wajen canza halayyar junan su wanda ko iyaye basu cika yin wannan tasirin ba, ya haɗa da kawo mashi hadisai dake magana kan abokantaka da irin mutanen da ya kamata a yi abota da su. Hankalin Alhaji Mahmud ya ƙara tashi, har zuciyar shi ta fara saƙa mashi tunanin kodai wani mummunan abu ya faru da bashi nan an 6oye mashi, kasa haƙura ya yi sai da ya yi ma malam Liman tambaya kan hakan, ya roƙe shi akan don Allah Ya sanar mashi in dai da abun da ya san ya faru da bashi nan, Liman ya tabbatar mashi da ba wani mummunan abu da shi dai ya ji ya faru, sai dai hango hakan na iya faruwan ne ya sa ya yanke yi mashi magana kamar yadda ya faɗa tun farko. "Nagode sosai malam Liman, haƙiƙa kai masoyi nane na gaskiya da har ka hango illa da ka iya shafar ahalina ka sanar mani don daukar matakin guje ma faruwar hakan, haƙiƙa nima tun ba yanzu ba hankalina sam bai kwanta da tarayyar su ba, na so in raba su tuni, to sai mahaifiyar yarinyar ta nuna gara a ƙyale su ana saka masu ido akan a raba su, don suna iya zagayewa su koma tare ba tare da sanin mu ba, to wannan shawarar tata ita na ɗauka ya sa ka ga na ƙyale su amma ba wai don hankalina ya kwanta da hakan ba." Alhaji Mahmud ya yi bayanin da damuwa shimfiɗe akan fuskarsa, "Ba wani abu Alhaji, ai duk yi ma kai ne, kuma fita hakkin juna ne a matsayin mu na maƙwabta. Sannan dama mu malamai a koda yaushe aikin mu ne idan mun hango wata matsala in muna da ikon gyara ta sai mu yi hakan, idan kuma bamu da wannan ikon sai mu tuntu6i wanda ke da ikon gyarawar don a ya gyara, idan ya ɗauka Alhamdulillah hakan muke so, idan kuma akasin hakan to mu dai mun yi aikin mu. Shi kan shi Abdullah Buzun na yi mashi nasiha ba sau ɗaya ba akan halayen yaran shi amman sam baya dauka, ƙarshe ma sai gaba ɗaya ya ɗauke ƙafa da zuwa wannan masallacin, wannan dalilin ne ya sa nima na rabu da shi, duk da mutane na yawan zuwa mani da ƙorafin yaran shi, to saidai in faɗi masu cewa na yi abun da zan iya sai dai kawai mu yi masu addu'a Allah Ubangiji Ya shirya su da zuri'ar mu baki ɗaya." Amsawa Alhaji ya yi da Amin, ya ƙara da cewa shima ya sha yi mashi magana akan hakan sai ya nuna kamar ya ɗauka, ƙarshe da ya fahimci ba ɗaukar shawara ko nasihar yake ba sai ya tattara ya rabu da shi. Tun akan hanyar komawar Alhaji gida ya gama yanke shawarar matakin da zai ɗauka kan hakan, bayan ya isa gidan a falon shi ya kira Hajiya Aisha, tun da ta kalli fuskarshi ta fahimci akwai damuwa tare da bacin rai tattare da shi, ta shiga tambayar shi abun da ke faruwa, duk abun da suka tattauna da malam Liman ya sanar mata, anan ya ce mata ya gama yanke shawarar matakin da zai dauka, shine zai maida Safiyya ƙasar Turkey can wajen yayanshi dake zaune acan yana aiki da kasuwanci, sam hajiya bata ja da shawarar da ya yanken ba, don tun farko dama can ya so ya tura Soffyn ta yi karatu ita ce ta roƙe shi kan ya ƙyale ta ta yi karatun ta anan ta nuna bata son ta yi nesa da ita, to shima da yake bai cika son yaranshi su yi nesa da gida ba hakan yasa a lokacin ya ƙyale ta, fatan Allah Ya sa hakan ya fi zama alkhairi ta yi ya amsa da Amin. A daren ranar ya kira Soffy ya sanar da ita kan ta fara shirin tafiya Instanbul a can zata ci gaba da karatu, ta ji ba daɗi amman bata shiga damuwa ba sosai saboda gidan yayan mahaifin nata dake can tamkar gida yake a wurinta, shima yana da yara har da sa'ar ta da suke ƙawaye, sannan kuma akwai ɗan shi Lukman da suke cikin yin soyayya da juna. Lokacin da Jameela ta ji zancen tafiyar Soffy ba ƙaramar damuwa ta shiga ba, saboda ba ƙaramin amfanuwa take da ƙawancen da suke ba, sannan kuma sun saba sosai da juna don tun suna yara suke tare, a lokacin ta ji inama ta bita ƙasar wajen itama sai ta ci gaba da karatunta na shiririta a can, sai dai ta san hakan ya fi ƙarfinta don ko cikin samarinta bata tunanin akwai wanda zai iya ɗaukar mata nauyin hakan, dama honorouble ne mai sakar mata bakin aljihu yadda ya kamata, to shima a lokacin ya ɗan ja mata baya tun da ya ce mata baya son tana kula samari sai shi kaɗai amman ta ƙi bin umarnin shi. Bayan tafiyar Soffy haka Jameela ta ci gaba da shiririta a wurin karatun ta don saima abun da ya ci gaba. Ana haka ne su Ibrahim wato mahaifin Deen suka zo biki Kano, a lokacin bikin yayan abokinshi Maleek mai suna Saleem, wanda asali suma Maleek ƴan Funtua ne amman a kano iyayen su suke zaune, sai dai basu cika zama a Kanon ba suma sun fi zama a ƙasashen waje saboda irin aikin iyayensu ɗaya, dalilin ma da ya haɗa iyayen nasu kenan har suke abota suma kuma yaran nasu suka zama abokai, kusan duk sun zauna a ƙasashe guda kuma tare suka yi karatu tun suna yara, hakan ne ya sa Ibrahim bashi da babban abokin da ya wuce Maleek, shima Sa'ad abokin Saleem ne wanda suka zo bikin shi. A ranar da za a yi dinner party lokacin Jameela ta zo duk da gayyar soɗi ta zo don bata haɗa komai da masu bikin ba, wata ƙawarta ce ƴar jami'arsu ita ce ƴar'uwar su amaryar shine ta biyo ta, a wurin dinner ɗin idan ka ga Jameela bazaka ta6a yin tunanin cewa bata haɗa komai da masu bikin ba, yadda ta ci uban gayu zaka ce bikin nasu ne don har da su anko ta yi har ma tafi ƙawartata da ta biyo iya yi, ba ƙaramin jan hankalin samari ta yi ba a wurin kamar dai a kowane biki da take zuwa. Tun da Ibrahim ya ɗaura idanun shi akanta ya ji ya kamu da tsananin son ta, sai da ya yi yadda ya samu yin magana da ita tana ta faman yauƙi kai ka ce ɗiyar uban wani ce, ba tare da 6ata lokaci ba ya bayyana mata shi dai ya ganta kuma ya ji ya kamu da sonta, a nan ya bayyana mata kan shi da kuma alaƙar shi da masu bikin, ai fa tana jin cewa ba zaune suke a ƙasar nan ba ya ja hankalinta har ta saurare shi sosai musamman da ta ga tare yake da ƙanin angon wato Maleek, kuma dama ta fahimci angon ɗan masu arziƙi ne daga yanayin shi da dangin shi. Bayan gama dinner din ya amshi lambarta ya ce washe gari zai zo gidansu su gaisa da iyayenta, gudun ya je ya ga gidan su yasa ta ce mashi ya bari ai zata zo wurin bikin gobe sai su haɗu, duk yadda suka so su maida ta gida bayan gama dinner ɗin sai da ta zille masu. Washe gari don ƙarfin hali sai gashi ta je gidan bikin, anan suka sake haɗuwa da Ibrahim har ya nuna ma yayanshi Sa'ad ita matsayin budurwar da ya yi, ya so ma ya kai ta ta gaisa da hajiyar su amman ta ƙiya ta nuna mashi ya yi wuri da yawa, har kusan magrib ta na nan, a motar Maleek suka ɗauke ta da za a tafi kai amarya. A ranar duk yadda ta so ta zille masu ta kasa, su suka ɗauke ta don maida ita gida, tana ta zullumin kada idan suka ga gidansu ya guje ta, wannan tunanin ya sa ta yanke ƙin kai su gidan su, a bakin gidan su Soffy ta sa suka ajiye ta ta ce masu anan take da zama amman ba nan ne ainihin gidan su ba, saida suka so ta shigar da su don su gaisa da mariƙan nata amman ta ƙiya, ta yi masu ƙaryar babanta mai ruƙonta baya barinta kula samari su bari daga baya zata yi masu hanyar da za su gaisa. Bayan gama bikin da kwana biyu a ranar da za su koma Funtua ya buƙaci yana son su haɗu, a wani haɗaɗɗan wurin cin abinci ta yi masu mahaɗa, a nan ya sanar mata shi fa son ta yake da aure, idan ta amince yana komawa gida zai sanar da iyayen shi, ya ce mata so yake kafin su bar ƙasar a gama magana tsakanin iyayen su, tabbas ta ji tana son shi da aure musamman kuma saboda ya tafi da ita ƙasar waje kamar yadda ƙawarta Soffy ta tafi ta barta, lokaci guda ta ce ta amince zata aure shi. Bayan komawar su Funtua ne ya yi ma hajiya maganarta tare da nuna mata hoton ta a wayar shi, ta tambaye shi game da iyayenta, ya ce bai san wanene mahaifinta ba amman ɗan'uwan mahaifinta ne ke ruƙonta, har ya sanar mata cewa yayan shi Sa'ad ya ganta har sun gaisa, a lokacin nuna mashi ta yi shi da yake son ci gaba da karatun shi kuma ya zai kawo batun aure, ba kunya ya nuna mata ya canza ra'ayi saboda yana son yarinyar idan ya aureta ya ci gaba da karatun, hajiya ta yi mamakin yadda ya kamu da son yarinyar lokaci guda, ta ce mashi ya bari zata yi magana da mahaifin su. Bayan sun tattauna da mahaifin nashi ne suka sanar da shi cewa sai sun fara yin bincike game da yarinyar kafin akai maganar aure. Lokacin da ya sanar da Jameela hakan hankalinta ya tashi har ta yanke faɗa mashi gaskiya cewa ita fa ɗiyar talakawa ce, ya bata amsa da shi ai ita yake so ba wani abu ba don haka ba ruwan shi da hakan, ta ji daɗi sosai don bata fatan a ce bata aure shi ba, ta samu Ammin su dama tuni ta sanar mata game da Ibrahim, cike da damuwa ta sanar mata yadda suka yi da shi na cewa za ai bincike akanta, ta ce ita tana tsoron su yi binciken a faɗi masu wani abu da zai sa su ƙi yarda a yi auren, Ammin ta so ta ja ra'ayinta kan ta haƙura da shi kawai, amman Jameela ta nuna ita gaskiya tana son shi da aure da kuma manufarta na auren shi, jin hakan ya sa Ammin tana sakin shu'umin murmushi ta ce mata kada ta damu su yi binciken tana tabbatar mata ko sun yi ba abun da za su ji da zai sa a fasa saidai ko don saboda su talakawa ne, sosai Jameela ta ji daɗi don ta san wacece Ammin su a 6angaren hatsabibanci ga bin bokaye, ko farin jinin samarin da suke da shi ba haka nan bane. Mahaifin su Maleek wato Alhaji Usman Karaɗuwa shi daddyn su Ibrahim ya tuntu6a da maganar ya ce yana son ya saka a yi masu bincike game da yarinyar, da yake abu ne na manya ba 6ata lokaci ya wakilta wani kan hakan, bayan an tambayi Jameela ta faɗi sunan unguwar da take da kuma mahaifinta. Sam hajiya Binta bata ji tana son al'amarin ba bayan da aka sanar da su sakamakon binciken suka ji asalin Jameela da iyayenta, ba kuma don sun kasance talakawa ba don su basu gudun talaka, kawai daga yadda ta ji asalin na su ne akwai rauni, a hakan ma wai don basu ji halin su ba don Ammin su tasa an yi mata surkulle an rufe bakin mutane, kuma Allah Ya ara masu sa'a don kwata-kwata a binciken ba a faɗi wani abu mara kyau game da halin ƴan gidan ba. Hajiya bata goyi bayan auren ba ta ce ma Ibrahim ya haƙura da yarinyar nan shima ya yi auren zumunci kamar yayanshi, dama akwai ƙanwar Amina matar Sa'ad ita suke son su haɗa su, har ta nuna mashi in don kyawu ne itama tana da shi daidai gwargwado tun da fulanin asali ne, shima Alhaji Nuraddeen ya goyi bayan ra'ayin matar shi ya nuna ya haƙura kawai, aikuwa sun sha ruwan mamaki, don Ibrahim tubure masu ya yi kan shi dai ita yake so har da su kwanciya ciwo ya yi ta koke-koke, cikin lokaci ƙanƙani sai gashi ya rame, a haka lokacin komawar su ya yi suka tafi, ta bangaren Jamila itama hankalinta ya tashi jin iyayen shi basu amince ya aure ta ba, ta shiga damuwa sosai itama har da su kwanciya ciwo saboda ta ƙwallafa rai kan tafiya ƙasar waje, har da ita ke ƙara tayar ma Ibrahim ɗin hankali, in suna waya tai ta yi mashi kuka tana faɗin miye aibunta da iyayen shi za su ƙi amincewa da ita, idan don su talakawa ne ba shi ya ce hakan ba damuwa bane, sai da ta yi nisa a son shi ta rabu da duk samarinta masu son auren ta sai kuma a ce shima ba zai aure ta ba, waɗannan kalaman nata ke ƙara tayar mashi da hankali, sai gashi ciwo sosai ya yi mashi rigis, hankalin su Hajiya ya tashi lokacin da aka tabbatar masu da ya samu high bp, a lokacin likitansu wanda yake bature ya basu shawarar su bashi abun da yake so kada a rasa shi. Ƙarshe dole suka haƙura, wasu daga cikin dangin mahaifin shi dake Funtua aka wakilta su je nema mashi aure, Jameela ta yi farinciki kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha da ta ji zancen, dama sai da Ammin su tai ta ce mata ta kwantar da hankalinta, idan dai ba son su rasa yaron su suke ba to tabbas sai sun amince, don kuwa har da sharrinta ya sa son Jameela ya tsananta a zuciyar Ibrahim. Watanni kaɗan aka saka na bikin, zuwa bayan babbar salla za a yi, dama duk hutun karshen shekara suke zuwa sai kuma wani lokacin suna yin azumi anan amman duk babbar salla anan suke yin ta saboda sun fi son su yi layya anan, lokacin da aka yi bikin Saleem yayan Maleek har ya haɗu da Jameelar lokacin dama sun zo hutun ƙarshen shekara ne. A kwana a tashi har lokacin bikin ya yi, gaba ɗaya hidimar bikin a Kano aka yi ta gidan su Maleek suka zauna har aka gama aka ɗauko amarya zuwa Funtua, dama kafin bikin mahaifinshi ya gina mashi flat a cikin gidansu daga baya, wanda da babban fili ne har noma ake masu da damuna a ciki. A ranar da aka kawo Jameela da daddare bayan sallar isha Sapnah ƙanwarta ta fito daga part ɗin da suke na amarya ta nufo bangaren su hajiya, tana tafiya cikin harabar a nutse jikinta sanye da abaya ta ɗaura gyalen rigar a saman kanta, ita kanta bata san ina zata je ba ta dai fito ne kawai har ta iso gaban gidan, a daidai lokacin ango Ibrahim suka dawo daga masallaci tare da Maleek da wasu abokan su ƴan'uwan Ibrahim guda biyu, gaba ɗaya sun sha shadda sun fito a matasan samari yan hutu sai sakin ƙamshi suke, tun da suka shigo Maleek ya hango ta a tsaye daga gefen ginin, suna ƙarasa shigowa ciki ya gane fuskarta, har za su shige ya ce masu su je yana zuwa ya nufo ta, tana ganin ya nufo ta ta shiga yan kame-kame har zata juya ta bar wurin ya ƙaraso, "Assalamu Alaiikum.." Sautin daddaɗar muryar shi ya sauka a kunnanta, ɗago idanunta tubarkallah ta yi ta ɗan kalle shi kamar tana tsoron amsawa ta amsa ƙasa-ƙasa, haɗa ido suka yi ya sakar mata murmushinsa mai burgewa, dama Maleek ba daga baya ba kyakkyawan saurayi ne sosai gashi dogo mai ɗan kaurin jiki, "Sannu ko." Kai ta ɗaga mashi kawai. "Zamu wuce ne na hango ki tsaye na yi tunanin ko kina neman wani ne?" Muryar shi ba dai daɗi ba, kana jin yadda yake magana kuma zaka fahimci turanci ya zauna mashi, baki ta fara motsawa tana kame-kame sam ta kasa magana saboda yadda ya kafe ta da idanuwa, tun lokacin da ake cikin hidiman bikin ya fara ganin ta, kuma ya fahimci bata da hayaniya sannan tana da natsuwa sosai, don lokacin da aka yi dinner yana ganin yadda ta natsu a wuri ɗaya bata tashi ta yi rawa ba kamar sauran ƴan mata ba, kuma an yi mata ɗinkin mutunci a ankon dinner ɗin, "Tell me if you need something." Ya faɗa tare da ɗage mata gira, da ƙyar ta buɗe baki cikin nutsattsiyar muryarta ta ce, "D..dama ina son in saka cajin wayana ne bansan na manto caja na a gida ba." Murmushi ya yi jin muryarta a karon farko, "Yanzu kina buƙatan caja ke nan?" Shiru ta ɗan yi kafin ta ce eh in akwai inda ake sayarwa, "Baki son in ara maki nawa?" Yanayin fuskarta kamar zata yi murmushi ta ce, "To ai bansan ko kaima zaka yi amfani da shi ba ne." "Ko zan yi amfani da shi sai in haƙura in baki tun da ke baƙuwarmu ce, kuma an ce ka karrama baƙon ka." Dan faffaɗan murmushi ta yi duka kumatun ta suka lotsa, sosai ya ga ta ƙara yi mashi kyau murmushin da ta yi, tambayar ta ina wayar tata ya yi ta ɗago ɗayan hannunta dake riƙe da ita ta miƙa mashi, bin wayar ya yi da kallo bayan ya amsa ba wata babba bace kuma da gani ta ɗan kwana biyu, ɗagowa ya yi ya kalle ta suka haɗa ido, da sauri ta sunkuyar da kanta, haka nan ta ji kunya ta kama ta, murmushi ya yi kamar ya fahimci dalilin sunkuyar da kan nata, "Charger na ba zai yi ma wayan ba, amman idan ba damuwa mu je sai a siyo irin nata." Ɗagowa ta yi ta kalle shi, da yake tana tsananin buƙatar ta yi cajin saboda karatun jarabawar Jamb da take yi hakan ya sa ta amince, tare suka nufi parking space ya nuna mata ɗayan side ɗin motar da yake ƙoƙarin buɗewa, ita tama yi tunanin a ƙafa ne za su je siyowa, da yake ta san shi tun da aka fara hidiman bikin take ganin shi, hakan ne ya sa bata ji tsoron ta bishi ba, "Ya sunan malamar ne?" Suna cikin tafiya bayan sun hau hanya ta ji ya tambaya ta ce mashi Sapnah, "Nice name.." Kallon shi ta ɗan yi a hankali ta ce mashi ta gode. "Ni baki son sanin nawa sunan?" Bayan ɗan lokaci ta ji ya tambaya, "Ina so.." Ta faɗa, "No, baki so ai da kin tambaya." "Da gaske ina so." Ta sake faɗa tana kallon shi, shiru ya yi idon shi akan hanya kamar ba zai faɗa ba, "Suna na Maleek Usman Karaɗuwa, ni best friend ɗin ango ne kamar ma dai ƴan'uwa muke da shi, don iyayen mu ma abokai ne sosai." Kai ta ɗan jinjina bata ce komai ba, kallon ta ya ɗan yi ya tambayi ita miye alaƙarta da amaryan, ta ce mashi yayarta ce uwa ɗaya uba ɗaya. Daga haka suka fara sabawa bayan an siyo caja sai da ya ɗan zagaya da ita wai ta ga gari ya siyo mata kayan ƙwalam sannan suka dawo gida, kafin su rabu sai da ya amshi no ɗin ta. Washe gari bayan an yi walima aka shirya maida dangin amarya, kafin su tafi saida suka yi sallama da juna ya kawo abu a cikin leda ya bata ya ce kyauta ce ya bata sai ta je gida sannan ta buɗe, ya yi mata hakan ne don daga yanayin ta ya fahimci idan ta san ko miye ba lalle ta amsa ba, haka kuwa aka yi sai da suka koma gida sannan ta buɗe ta ga sabuwar haɗaɗɗiyar waya a cikin kwalinta, ita tsoron ma wayar ta ji don wannan ne karo na farko da ta amshi abu irin haka a wurin wani namiji, ko wayar hannunta tsohuwar ta Jamila ce ta bata, aikuwa da ya kira ta sai da ta yi mashi ƙorafin wayar, ta ce wai zata bada a maido mashi ita bazata amsa ba tun da tana da ita, ya ce ya san da tana da itan ya bata kuma ai kyauta ce, da ta kafe kan sai ta maido mashi ya ce mata aikuwa idan ta yi hakan za su 6ata ba zai ƙara kiranta ba, tun da ta nuna mashi bai isa ya bata abu ta amsa ba duk da yanzu su kamar ƴan'uwa suke, jin hakan ya sa ta bashi haƙuri ta nuna mashi ba haka bane kawai ta ga tana da wayan ne, daga baya ta yi mashi godiya. A hankali sabo mai ƙarfi ya shiga tsakanin su, har bayan su Maleek sun bar ƙasar yana kiranta akai-akai suna gaisawa har su yi hira don ta sake da shi, daga baya har kuɗi yake turo mata ya ce ta yi buƙatunta na karatu da za ta fara...... *_✨A CIKIN RAYUWA✨_* _By Zainab Bature_ _Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._ Page 13 A 6angaren amarya da ango suna ta shan soyayyar su, saidai tun ba a je ko'ina ba hajiya ta fara fahimtar wasu daga cikin halayen Jameela, ƙiri-ƙiri take nuna bata son dangin su dake zuwa a fakaice take yi masu wulaƙanci da kora da hali, farkon kawo ta sosai take ma Hajiya biyayya kullum sai ta je ta gaishe da ita ta tambayi ko akwai abun da za ta yi mata, ko da hajiyar ta ce mata babu komai sai ta je kicin ta taya mai aikinta wani abun, a hankali ta fara janye ƙafa sai ta gadama sannan ta je ta gaishe da ita, sanin tana zuwa ya sa idan Hajiya ta ga an kwana an wuni bata je ba sai ta tambayi Ibrahim ko lafiya idan shi ya je gaishe da ita, wani lokacin har ƙarya yake mata ya ce Jameelar ce bata jin daɗi, daga baya hajiya ta fahimci hakanan ganin dama ne ya sa bata zuwa gaishe ta kaman yadda ta saba sai itama ta fita batun ta, iyaka idan Ibrahim ɗin ya je ta tambaye shi suna lafiya. Sai da ta kai har sai ya matsa ma Jameelar sannan wani lokacin zata je gaishe da hajiyan. Watan su biyu da yin aure ta samu juna biyu, a lokacin sai abun da ya ci gaba na iskancin ta, farko ma bata yi murna da cikin ba wai ita ba yanzu take son samun ciki ba gaskiya karatu take son ci gaba da yi, lalla6a ta ya yi ya rarrashe ta kan ta yi haƙuri ta haifi wannan daga shi sai su bari bayan ta kammala karatun sai ta sake haihuwan. Ba ƙaramin wahalar da shi take ba da buƙatun cikin, gaba ɗaya ta daina yin girki dama ba wani cika yi take ba sai ta gadama don ana kawo masu daga part ɗin hajiya, ga ƙazantar tsiya ko jikinta bata damu da ta gyara ba, gashi irin laulayin tofar da yawu take haka zata tofar a duk in da ta samu, yalwatacciyar sumar kanta ma duk ta barta ta harmutse bata gyarawa, ba uwar da take yi daga kwanciya sai cin abun da ta ga dama, ko wanka ma sai an ci sa'a dole Hajiya ta sa aka samo mata mai aiki, wani lokacin in hajiya ta je duba ta ita zata matsa mata kan ta daure ta tashi ta gyara jikinta, haka za ta tashi tana ta ture-turen baki, ba ƙaramin jin jiki Ibrahim yake ba akan cikin don kuwa hakkin shi ma wannan ba a maganar shi gaba ɗaya ta hana shi wai bai tausaya mata. Tun ana gama bikin Alhaji Nuraddeen ya koma wurin aikin shi, ita hajiya ta ce zata ɗan zauna saboda su Ibrahim ɗin, Jameela na a cikin halin laulayin take ma Ibrahim maganar wai yaushe za su bar ƙasar ai ya ce mata ba su cika zama anan ba, ya ce mata yana jira sai hajiya ta yi maganar lokacin da za su tafi, ganin har cikin ya kai kusan wata biyar ba ai zancen tafiyar na su ba ya sa ta matsa mashi lamba wai ita tafi son ta ci gaba da rainon cikin a ƙasar waje kuma ta haihu hannun ƙwararrun likitoci, ganin ta matsa ya sa shi samun hajiya ya yi mata zancen tafiyar su, a lokacin ta ce mashi tun da juna biyun matar shi ya fara girma bari ta yi ta sauka, jin haka ya sa shi ce mata wai da ya fi son su koma saboda tafi samun kulawa kuma ta haihu a hannun ƙwararrun likitoci, duk da bai fito fili ya bayyana hakan ra'ayin Jameela bane hajiyar ta so ta fahimci hakan, cikin ɗan murmushi ta ce mashi duk nan ƙasar ba ƙwararrun da za su duba mashi matar tashi ne, ko yayan shi ba a nan aka haifa mashi yaron shi ba, bai dai ce mata komai ba a lokacin itama bata bashi tsayayyar magana kan komawar ta su ba, koda Jameela ta ƙara mashi magana kan hakan ya faɗa mata Hajiya ta ce anan zata haihu, aikuwa ta shiga yin tijara iri-iri, gaba ɗaya ta hana mashi zaman lafiya har tana cewa ita ta yi zaton ma suna yin auren za su tafi honeymoon ƙasashe amman an zo an jibge ta a ƙauye, ga yayan shi can da iyalinshi suna ƙasar waje sai ita don tana bare shine za a ƙi yi mata abun da take so, duk ƙoƙarin shi na ya fahimtar da ita shi Sa'ad aikin shi yake a can ta ƙi sauraren shi. Lokacin da cikin ya isa fara zuwa awo hajiya ta yi mashi magana, ya yi ma Jameela maganar amman fir ta ƙi fara zuwa wai ai ba a damu da lafiyar abun cikin nata ba shiyasa za a barta ma'aikatan asibitin ƙauye su duba ta, da abun ya ishe shi kawai sai ya kira dad ɗin shi ya roƙe shi kan yana son ya taho da Jameela don bata jin daɗi, ya ce cikin na wahalar da ita sosai yasan zata fi samun kulawa anan, hajiya ta yi mamaki lokacin da dad ɗin ya yi mata maganar, dama tun lokacin da ya fara neman auren Jameela ya fara ja da maganarta, bayani ta yi ma dad ɗinsu ta ce mashi ba wata wahalar da take sha kawai dai shine ya fi son hakan kuma ta bari cikin ya yi ƙwari sosai sai su taho, ya ce mata to in tana ganin ba matsala kawai su taho da itan dama itama yakamata ta dawo hakanan. Farin ciki a wurin Jameela ba ya misaltuwa lokacin da ta ji zancen tafiyar su ƙasar Australia da a lokacin nan dad ɗin yake aiki, Ammin su na jin zancen tafiyar tasu bayan ta sanar mata sai cewa ta yi wai ta tafi da Naila, haka ta sanar ma Ibrahim din cewa tana son tafiya da ƙanwarta don ta rinƙa taimaka mata, lokacin da ya yi ma hajiya maganar ranta ya 6aci ganin yadda Jameelar ke son mayar da su shashashu, cikin yanayi na 6acin rai ta ce mashi ba za a je da wata ƙanwarta ba ko ta ɗauka tafiyan kaman zuwa Kano ne, duk wata kulawa ai zata samu a can tun da anan ma bata rasa hakan ba, a karon farko da ta fara magana akan tsakanin shi da iyalinshi cikin ƙoƙarin ankarar da shi ta ce, "Ibrahim, yakamata ka isa da gidanka ka zama namiji, ba baki zan maka ba amman muddin ka ci gaba da sake ma iyalinka, ka ce duk abun da take so sai ka yi mata koda kai zaka takura da hakan to kuwa watarana zaka yi kuka da hakan, saboda mata ba a sake masu gaba ɗaya don abun zai ta ƙara gaba ne har ya kai girman da lokacin da zaka so ɗaukar matakin gyara hakan ya fi karfin ka..." Cikin kwantar da murya ta ci gaba da nusar da shi illar dake tattare da hakan, cike da nuna gamsuwa da maganar ta ya yi mata godiya. Jameela ta ji haushin jin ba za a tafi da Naila ba, haka tai ta faman fushi ya bata haƙuri tare da nuna mata tafiyar da itan ne ba zai yuwuwa ba tun da ba a shirya hakan ba. Ba tare da wani ɗaukar lokaci ba aka gama yi ma Jameela duk wani shiri na tafiya, lokacin da ya rage saura sati ɗaya su tafi suka shirya zuwa Kano don ta yi bankwana, kuɗi masu yawa ta buƙata a wurin shi wai zata ba iyayenta tun da tafiya zata yi, ya nuna mata bashi da su tun da bai riga ya fara aiki ba dama yawanci ɗawainiyar su iyayen shi ke yi masu, rufe ido ta yi ta kama yi mashi masifa har tana faɗin ita da ta san irin rayuwar da zata fuskanta ke nan a gidan wllh da bata aure shi ba, a tunaninta zai yi mata duk abun da take so ta yi rayuwar aure mai daɗi, har da ce mashi tana da masu son aurenta da in ta auri wani cikin su ta san zata yi rayuwa mai dadi fiye da ta gidan shi, hankalin Ibrahim ya yi matuƙar ƙololuwar tashi jin kalamanta a lokacin, ba irin lallashinta da bai yi ba yana nuna mata in dai zata yi mashi adalci shima mai ta nema a gidan shi ta rasa, duk wani abu da take son ci shi ko sha tana samu, haka bata yin komai musammaman aka samo mata mai aiki, sannan duk ta buƙaci kuɗi yana bata, kawai wannan da ta buƙata ne sun yi yawa bashi da su a lokacin, amman ta yi haƙuri da ya fara aiki duk wata buƙatar ta ta kuɗi zai rinƙa yi mata, ya ce shi siyasa ma yake shirin fara yi don haka ma ya yanke yin master's degree ɗin shi akan political science. "Amman ai kuna da kadarori, ba ka faɗa mani har gonaki kana da su naka ba da ake maku noma, a sanina noma ana samun kuɗaɗe sosai to su ina suke da bazaka rinƙa yi mana amfani da su ba?" Ta tambaya fuska a ɗaure ta wani ƙanƙance idanu kanta ko kallabi babu sai baƙar sumarta tum, ƴar ajiyar zuciya ya sauke ya ce, "Tabbas ba ƙarya na faɗa maki ba, sai dai su waɗannan kuɗaɗen dama ba su shigowa hannuna suna wurin dad da su ne yake mana hidindimun da suka shafe ni..." Tun kan ya ƙarasa ta katse shi. "Wannan ai rashin ƴanci ne, kuɗi dai naka ne kuma yanzu ai ka mallaki hankalin kan ka tun da har kana da iyali, sai a damƙa maka hakkin ka ka rinƙa yin hidindimun ka, don haka sai ka kira dad ɗin ka nuna mashi kana buƙatan kuɗi sai ka bani." Shiru ya yi idon shi akan ta yayin da yake a tsaye ita kuma tana zaune a bakin gado ta juya mashi kai, cikinta har ya fito jikinta ya ƙara yin kyau sosai fatar nan kamar ka ta6a jini ya zubo, duk fa abun da ya ja wannan taƙaddamar kawai don ya zo yana neman ta bashi hakkinsa ne wanda tun da ta samu ciki sai ta gadama take bashi daman hakan, ya san indai ba yi mata yadda take so ya yi ba shima ba zai samu abun da yake so ba, tunanin yadda zai tunkari mahaifin shi da buƙatar kudi har miliyan ɗaya yake yi, yasan koda zai bashi to sai ya ji mi zai yi da su, jiki a mace ya nufi hanyar barin bedroom ɗin ta juyo ta bi shi da kallo fuska a ɗaure, ƙwafa ta yi bayan ya fita a fili ta ce wllh in dai ana son zaman lafiya to dole a yi mata abun da take so, kuma duk fa abun nan ba kowa ne ya haddasa shi face Amminsu, dama tun bayan auren take sata ta tura mata kuɗi daga dubu ɗari, ɗari da hamsin, dubu ɗari biyu, kuma duk yana bata, wannan karon sai ta ce wai ta sa ya bata miliyan ɗaya saboda tafiya zata yi buƙatu na iya haye masu. A falo ya zaune yay zugudum bawan Allah, haƙiƙa har ya fara gajiya da halayen Jameela, saidai kuma son da yake mata ya sa baya iya yin wani katabus kan hakan, ya ɗauki tsawon lokaci yana wasi-wasin kan shawarar da ya yanke ta kiran dad din su, cike da fargaba ya ɗauki waya ya kira shi, bayan sun gaisa ya yi shiru, dad ɗin ya fahimci da maganar da yake son yi ya kasa ya tambaye shi lafiya, da ƙyar ya ce mashi dama kuɗi yake so miliyan ɗaya, ɗan jimn dad ɗin ya yi kafin ya tambaye shi mi zai yi da kudi haka, cikin in ina ya ce mashi dama yana son zai ba wife ɗin shi wasu in sun je bankwana ta ba iyayenta sai kuma akwai uzururrukan da zai yi da sauran, bayan ya gama yi mashi bayani dad ɗin ya ce zai yi mashi magana suka yi sallama, suna gama yin wayar ya kira matar shi hajiya dama tsakaninsu ba su 6oye ma juna komai, ya sanar mata game da buƙatar Ibraheem ya ce mata in tana ganin lafiya lou ta tura mashi kuɗin, cike da 6acin rai ta ce mashi ya ƙyale shi ba za a bashi kudi ba haka, daga yanayin yadda ya yi magana ya fahimci da wani abu, ya tambaye ta mike faruwa, ta ce mashi Ibrahim so yake ya zama shashasha wanda mace zata rinƙa juyawa, ta tabbatar matar ce ta buƙaci waɗannan kuɗaɗen, in ba haka ba har wani uzuri ne gare shi na kuɗi da ba zai iya yi da kuɗaɗen hannun shi ba, nan ta shiga faɗa mashi irin abubuwan dake faruwa har da buƙatar da ta kawo na a taho da ƙanwarta, ɗan murmushin dattako ambasada ya yi don ya daɗe da sanin kowace uwa bata son ta ga mace na juya mata ɗa, kwantar mata da hankali ya yi ya ce shi yana ganin a bashi kuɗin kawai tun da dama na shi ne, yama yanke shawarar zai mallaka mashi dukkan dukiyar shi ta ci gaba da kasancewa a wurin shi tun da ya mallaki hankali har ya aje iyali, hajiya bata nuna amincewa akan hakan ba ta ce mashi maganar ya mallaki hankali da saura tun da ya bari mace na juya shi, yana murmushi ya ce mata so ne ya ja mashi hakan ta rabu da shi a hankali zai dawo cikin hayyacin shi. Ƙarshe Jameela ta yi nasarar karbar kudin. Bayan sati guda suka tafi ƙasar Australia, farin ciki a wurin Jameela kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha ganin ta a ƙasar waje, sosai ake kula da ita bayan ta fara zuwa asibiti, sai dai duk yadda take murna da zuwan ta ƙasar saida murnar ta so komawa ciki saboda yadda take muzanta sakamakon rashin iya turanci, kowa ya ganta bai yin tunanin bata iya turanci ba haka zatai ta faman raba idanu idan ana yi mata saboda bata iya komai ba in ba irin su 'Yes, come, thank you..' da sauran irin ƴan guntayen kalmomi, dole koda yaushe tana tare da Ibrahim saboda haka, ko a gida in suka yi baƙi haka zata yi wuriri sai dai hajiya ce ke zame mata tafinta in ana mata magana, hakan yasa duk ta bi ta raina kanta. Ba a ɗau lokaci ba ta roƙi Ibrahim kan ya rinƙa koya mata turanci, da yake tana tsananin son ta iya ta hakan ne shima yake samun yadda yake so a tare da ita ba tare da ta ja mashi rai ba, cikin daɗin rai ya fara koya mata, amman daga baya abun ya fara gundurar sa saboda yadda kan nata baya saurin ɗauka, daga baya kawai sai ya samo mata baturiyar malama da take zuwa tana koya mata, ita kanta malamar ba a ɗau lokaci ba ta fahimci kan Jameela baya saurin ɗaukar karatu, haka dai tai ta ƙoƙari tana koya mata tun da biyanta ake. Bayan cikinta ya kai wata tara Allah Ya sauke ta lafiya ta san6alo santalelen jaririnta kamar ɗan aljanu tsabar kyau, hatta turawa haka sukai ta yabon kyawun yaron, bangaren uwar yaron wato Jameela kuwa ba a magana sam fuskarta ta kasa boye farin ciki da zumuɗin babyn, ba kamar da farko ba da bata so samun cikin ba, ita kanta kakar shi wato Hajiya ba ƙaramin farinciki ta shiga ba da ganin kyakkyawan jikan nata tamkar ɗan balarabe, a Nigeria ma duk wanda ya ga hoton babyn sai ya yaba da irin kyawun shi sai murna dangi suke. Bayan yin haihuwar da kwana ukku Sa'ad suka iso ƙasar daga kasar France da a lokacin can yake aiki tare da matarsa Amina da kuma yaron su Fahad wanda a lokacin yake da shekaru ukku da ƴan watanni, shima Fahad tubarkalla kyakkyawa da shi don ya ɗauko haske da kyawun mahaifiyarsa duk da akwai kamanin Sa'ad a tare da shi, kuma shima mahaifin na shi yana da kyau ba laifi, tun da Fahad ya ɗaura idanun shi akan babyn ya fara son shi ya maƙale mashi, koda wani lokaci yana a wurin baby da an yi yunƙurin ɗaukar shi zai kama kuka sai da ƙyar ake raba shi da babyn ko idan ya yi bacci. Bayan sati ɗaya da yin haihuwar gaba ɗaya suka taho Nigeria, nan yan'uwa da abokan arziki suka shiga zuwa barka, da sati ya zagayo aka yi taron suna inda yaro ya ci sunan kakan shi wato Nuraddeen (Deen) A lokacin Jameela ta ji haushin ƙin bin ra'ayin ta da ba a yi ba na a saka sunan mahaifinta ko kakanta, dad ɗin Deen ya bata haƙuri kan in suka ƙara haihuwar namiji sai a saka mashi, ƴan'uwanta na Kano duk sun zo har da Ammin su, suna na gani na faɗa aka yi inda saboda jin daɗin saka sunan Ambasada da aka yi ya bada ƙaton shanu aka yanka ma baby, ba ƙaramar zalama dangin Jameela suka nuna ba a wurin sunan inda duk suka kwashe naman suka ba su Hajiya ɗan kaɗan, kowa kuma ya fahimci abun da suka aikata har da shi kan shi dad ɗin Deen, amman ba wanda ya tanka masu don sun fi ƙarfin hakan, bayan gama suna haka suka ƙi tafiya har da Ammin ta su sai bayan kwana biyar sannan suka tafi, Amminsu duk ta tattare kayan suna da Jameela ta samu abun takaici har da kayan baby da aka kakkawo mashi don zalama su basu kawo ba amman sun kwasa. A lokacin an bar ma Jameela ƙanwarta Naila ta zauna mata duk da akwai dattijuwa da hajiya ta sa aka kawo mata tana kula da ita, lokacin Naila bata wuce shekaru tara ba amman bata jin magana tsagera ce ta gaske sam bata da kunya, ƙiri-ƙiri idan ƴan'uwan hajiya suka zo barka sai su hana su ganin jaririn koda yana a hannun wani tsakanin Jameela da Naila basu ba da shi a gan shi, akwai watarana da wasu ƴan'uwan hajiya suka zo daga ƙauye hajiya ta saka ƴar aikinta Asabe ta rako su part din su Ibrahim don su yi barka, a wulaƙance Jameela ta tarbe su, a lokacin ba don ganin idon ƴar aikin hajiya ba da ba abun da zai sa ta bari su zauna mata akan kujera, yadda take bin su da ƙasƙantaccen kallo tana yamutsa fuska sai ka ce ta ga kashi, dama lokacin tubarkalla jikinta ya ƙara cikowa ta yi dumurmur, suka gaisa ta amsa masu a daƙile, bayan ɗan lokaci ɗaya daga cikin matan ta kalli Naila dake zaune riƙe da Deen ko kallon su dama bata yi ba tun da suka shigo idonta na akan tv, dama ba iya gaida mutane ta yi ba, da yar fara'a matar ta ce mata ta kawo masu jaririn su gani ta yi kamar bata ji ta ba, sai da Asabe mai aiki ta sake maimaitawa ta ce bata ji ana mata magana, sannan ta juyo ta yi masu kallon hadarin kaji bata da niyyar tasowa ta kawo shi, ganin haka yasa Asabe ta nufe ta da niyyar kar6o masu shi, aikuwa Jameela ta yi saurin dakatar da ita cikin haɗe rai ta ce ita ta hana ta rinƙa ba mutane shi saboda idan baƙi suka ɗauke shi sai ya yi ta kuka har kan shi yay ciwo, gaba ɗaya sai da suka ɗan buɗe ido mamakin jin furucinta, Haka suka taso jiki a mace suka baro part ɗin, bayan dawowar su 6angaren hajiya, ɗaya cikin su ta kasa haƙuri ta gaya ma hajiya irin wulaƙancin da aka yi masu, ran hajiya ya 6aci sosai nan Asabe ta ƙara faɗa mata cewa ba wannan ne karo na farko ba don ko ranar da wasu danginsu suka zo ta saka ta raka su suma haka ta yi masu, bayan sun baro part ɗin su baƙin ne suka roƙe ta kan kada ta sanar ma hajiyan, Asabe na rufe baki hajiya ta miƙe, wata a cikin baƙin ta fara mata magiya kan ta rabu da ita kawai yayin da wadda ta faɗi ma hajiyar abun da aka yi masu cikin 6acin rai ta ce ta ƙyale ta, gara ta je ta ja mata kunne in ma zata rinka wulaƙanta mutane to ban da su da suke dangin su. Jameela na ganin yanayin fuskar hajiya bayan ta isa falon ta sha jinin jikinta, tsaye ta yi a tsakiyar falon ba tare da ta zauna ba, Asabe da suka taho tare na daga gefen ta a baya, cikin yanayi na bacin rai tana kallon Jameela ta ce mata don me take hana mutane su ga Deeni kuma ma har da waɗanda suke dangin shi! Nan ta shiga ƴan kame-kame tana kifce-kifcen idanu ta ce tun kwanaki da wasu suka zo aka basu shi bayan sun tafi ya yi ta kuka har jijiyoyin kan shi suka fito, da ta rasa mike damun sa sai ta kira Ammin su ta sanar mata, shine Ammin ta tambayi wani malami dake a layin su ya ce a daina ba ko wane mutane shi don mayya ce ta so kama shi, baki a kwa6e hajiya ke kallon ta har ta gama, sam bata ma yarda da zancen nata ba, daga yanayin fuskarta da yadda take yin maganar zaka fahimci karya take faɗi, bayan ta gama bayanin cikin ɗaure fuska hajiya ta ce mata to su kaf dangin su babu mai maita, kuma ba wannan bace haihuwar da kaɗai aka ta6a yi a familyn su da za a ce maitar bata ta6a shafar wani ba sai shi, don haka daga yanzu kada ta sake jin wai ta hana wani yaro koda bacci yake indai aka zo ganin shi to a ɗauko shi a ba mutane, in ba haka ba ranta zai 6aci, "Asabe je ki kar6o shi!" Cike da bada umarni ta ce ma Asabe, nufar Naila ta yi ta je ta amso babyn, juyawa hajiya ta yi tana faɗin Ibarahim ɗin zai dawo zata ji in har da shi ya bada goyon baya ake ma dangin shi hakan, Jameela da Naila suka bi su da kallon harara har suka fuce. Bayan wata ɗaya da yin haihuwar Maleek ya zo daga ƙasar India da a lokacin a can yake aiki da wani kamfani da ya danganci fasaha, kuma sannan yana ci gaba da yin karatun degree ɗin shi na biyu wato master's degree. A gidan su na Kano ya sauka, a ranar da daddare ya shirya zuwa wurin Sapna wanda shine karo na farko da zai fara zuwa gidan su tun bayan da suka shaƙu da juna, har abun ya juye ya koma soyayya mai ƙarfi a tsakanin su, sai dai ba wanda ya sani sun bar abun a tsakanin su, Sapna ta yi farin cikin jin zuwan shi lokacin da ya kira ta ya sanar mata, duk da ta wani 6angaren tana ɗan jin fargaba saboda bata san yadda zata tarbe shi ba, a wata haɗaɗɗan ash din mota ya isa gidan su bayan la'asar, jikin shi sanye da jeans da t-shirt, kiranta ya yi ya sanar da ita ya iso, ba a ɗauki lokaci ba ta fito tana sanye da brown ɗin doguwar riga ta ɗaura ƴar ƙaramar baƙar hijab mai tattara a ƙasa, ta yi kyau sosai cikin shigar haskenta ya fito fayau, yana ganin ta ya sauke glass ɗin motar ya zuba mata ido yayin da take nufo motar tana tafiya a nutse, tun da suka haɗa ido ta sadda kanta ƙasa tana murmushi, yana daga abun da yake ƙara mashi son ta yadda take da kunya ga kamun kai, daga gefen ƙofar da yake ta tsaya tana kallon shi, haka shima idanunsa na a cikin nata suka shiga sakar ma juna murmushi, sam ta kasa yi mashi magana don tun da abun su ya juye zuwa soyayya basu ga juna ba, "Ko dai ba a murnar gani na?" Ya faɗa da muryarsa mai cike da natsuwa, ɗan girgiza mashi kai ta yi still tana ta murmushi, ɗage gira ya yi ya ce gashi nan ta ƙi yi mashi magana idan ta ji daɗin ganinsa ai baza ta ƙi yin magana ba, "To ai saboda murnan ne na kasa magana." Ta faɗa da ƴar zazzaƙar muryar ta, har saida ya ɗan lumshe ido yana murmushi, ce mata ya yi ta shigo cikin motan, ta yi ɗan jim tare da ɗan wawwaigawa ganin ba mutanen dake kallon ta ya sa ta zagaya ta shiga, wani ni'imtaccen sanyi haɗi da kamshi mai daɗi suka ratsa ta, gaishe da shi ta yi tare da yi mashi an zo lafiya ya amsa yana kallonta cike da so da kauna, shima ya tambayi yadda take tare da ƴan'gidansu ta amsa da duk suna lafiya, hira suka shiga yi irin ta masoya duk da ita bata cika yin magana sosai ba sai dai murmushi kawai, har yake tambayarta ya babyn su na wurin sister ɗinta ta amsa da duk suna lafiya, ya ce bai samu zuwa ya ganshi ba lokacin da aka yi haihuwar yana yin exams ne, kai ta ɗaga ba tare da ta ce komai ba, ce mashi ta yi bari ta kawo mashi ruwa ya yi saurin dakatar da ita ya ce akwai ruwa a motan, ta ce to bari ta kawo mashi lemu, shima ya ce mata ta barshi, da ɗan yanayin shagwa6a ta ce ke nan yana nufin ba zai sha komai ba, murmushi ya yi ya fahimci ta iya shagwa6a duk da kunya na hanata yi sosai, tambayar ta ya yi ita ta haɗa lemun, "A'a na shago ne, ban san da yau zaka zo ba dana haɗa maka, kuma lokacin da ka kira ni ka ce zaka zo nan ba time sosai." Ta faɗa tana yi tana sauke idanunta, "Siyo mani kikai ke nan?" Kai ta ɗaga mashi, "Ok, tun da saboda ni aka siyo idan zan tafi sai a ɗauko mani." Kai ta jinjina mashi suka ɗan yi shiru, "Ya maganar karatun ki, yaushe ne zaki fara tun da kin samu points mai kyau?" Ta ce,"Yanzu ina jiran lokacin da zamu yi post utme ne." Kai ya jinjina suka ɗan ƙara yin shiru, "Ai ina tunanin ci gaba da karatun ma anan babu shi..." Da sauri ta kalle shi, ya ci gaba, "I think ya kamata mu yi aure, da yadda na tsara sai na gama karatuna sannan, amman i have changed my mind." Da sauri ta sadda kanta ƙasa jin maganar aure da ya yi, ƴar dariya ya yi, "Ko baki shirya mu yi aure ba yanzu?" Tana a yadda take ta girgiza mashi kai, ce mata ya yi ta ɗago sosai su yi magana wannan serious abu ne, ɗagowa ta yi tana kallon shi ya tambayi miye ra'ayin ta kan hakan, "Duk yadda ya yi maka nima ya yi mani, amman tun da ka ce kafi son sai ka gama karatunka ko ka bari idan Allah Ya kaimu ka gama ɗin." Iska ya ɗan furzar tare da shafa lallausar sumar kan shi ya ce, "Ai My Sapnah na ga nema kike ki hana ni maida hankali akan karatun, tunanin ki yana yi mani yawa gashi karatun mu baya son wasa, that's why I just decided in mallake ki ki kasance a tare da ni ko na tsayar da hankalina wuri ɗaya, idan muka yi auren a can sai ki ci gaba da karatun kawai." Wani irin daɗi ne ya lullube ta ta shiga yin murmushi dake bayyana hakan, tambayar ta ya yi ta amince su yi auren ta ce mashi eh, a nan suka gama magana ya ce zai sanar da mahaifin shi a zo nema mashi aurenta tun da yana a gari ko mi ake ciki zai mata magana, da zai tafi ya bata tsarabar da ya yo mata. Cike da farin ciki Sapna ta ƙarasa yinin ranar duk da a cikin zuciyar ta tana zullumin kada a ƙi amincewa da maganar auren nasu. Bayan ya samu dad ɗinsa da maganar ya ce mashi ya jira zai neme shi, mahaifin su Ibraheem dad ɗin Maleek ya kira ya shaida mashi game da auren da Maleek ɗin ke son a nema mashi na yar'uwar matar Ibrahim, ya tambaye shi shawara game da hakan, a nan ambasada ya ce mashi ya bari za su yi magana da hajiya don ita tafi shi sanin abun da ya dangance su, hajiya ta yi mamakin jin Maleek yana son auren ƙanwar Jameela, saidai ita kanta ta fahimci Sapna ta sha bambam da sauran ƴan gidansu tun daga bikin Ibrahim ta gane hakan, ko lokacin da suka zo bayan ta haihu ita kaɗai ce ke zuwa ta gaishe ta safe da yamma har aiki take yi mata, koda ta ce ta bari sai ta yi kamar gyara mata falo da taya Asabe aiki, har Ibraheem ta kira ta tambaye shi game da halayen Sapna ya tabbatar mata da ta fi kowa kyawun hali a gidansu Jameela, anan yake ji a bakin hajiya cewa Maleek ne ke son auren ta, aikuwa ya yi mamaki sosai don shi kawai ya san dai suna mutunci da juna amman bai san abun ya juye zuwa soyayya ba. A bakin shi Jameela ta ji zancen, aikuwa cikin rawar jiki ta kira Ammin su da maganar ta nuna ita bata san ma da Sapnah ɗin na soyayya da shi ba, cike da zumuɗi Jameela ta ce mata ta tashi tsaye duk yadda za ai kada ta bari a samu matsalar da zata sa a fasa auren nan, in ba haka ba za su yi babbar asara don iyayen Maleek sun fi na Ibrahim kuɗi kuma shi kan shi Maleek din a yanzu yana da kuɗi sosai, kuma idan aka yi auren India zai tafi da Sapna ɗin, nan fa jikin Ammin ya kama rawa har tana faɗin wllh da a ce Naila ta girma da sai ta sa an juye al'amarin ya koma kanta don bata tunanin za su rinƙa samun wani abun arziƙi idan aka yi auren da Sapna tun da ita sakarya ce bata son su da arziƙi, anan Jameela ta shiga bata shawarar ta ja Sapna ɗin a jiki ta yi ƙoƙarin canza mata hali, idan bata canza ba bayan an yi auren kawai ta saka bokanta ya yi aikin da za a canza mata ra'ayi ta rinƙa yin abun da ake so, sosai Ammi ta ji daɗin shawarar ta ce haka kuwa za a yi. Bayan sun gama yin wayar haka ta rufe Sapnah da faɗan wai don me bazata sanar masu ba a yi mata shiri sosai yadda abun zai tabbata ba tare da wata matsala ba kamar yadda aka yi na Jameela, Sapna ta san abun da take nufi da a yi mata shiri don tasan tana biye biyen bokaye kuma ta tsani hakan, nan fa Ammin tasu ta shiga rawar jiki haka ma babansu bayan ta sanar mashi, har da cin alwashin zuwa wurin bokanta washe gari tana faɗin ba abun da zai sa a fasa auren, Sapna har nuna mata ta yi ita dai bata son ta saka a yi ma Maleek wani abu idan Allah Ya ƙaddara shi ɗin mijinta ne ba abun da zai hana ta aure shi, Ammin ta hau surfa mata masifa tana faɗin bata da wayau, yanzu waya faɗi mata abu irin wannan ana tsayawa wai a zura ido kowa tashi yake tsaye ya nemi taimako da sa'a, har da bata misali da ba ga ƴan mata nan ba da iyayen su suka lanƙwashe hannu basu nema masu taimako duk sun yi kwantai ba mazajen auren ba, ita dai Sapna duk da hakan ta nuna bata son ta je wani neman taimako. A daren ranar hajiya ta sanar ma ambasada game da bincikin da ta yi da kuma abun da ta sani na halayen Sapna, shi kuma ya kira Alhaji Usman ya shaida mashi. Cikin dare Sapnah ta tashi ta yi nafilfili ta roƙi Allah kada ya ba Amminsu sa'a a duk abun da zata sa a yi, tana ƙwalla ta roƙi Allah Ya bata Maleek a matsayin miji idan tana da rabo. Ikon Allah, washe gari Ammin ta tashi bata jin daɗi, duk yadda ta so ta fita ta kasa ba don ta so ba ta bari sai ta samu sauƙi. Bayan dad ɗin Maleek ya ƙara sakawa an yi mashi bincike anan Kanon aka tabbatar masu da cewa Sapna tana da halayen kirki ta fita daban a yaran unguwar ma baki ɗaya, mahaifiyar Maleek ce ta so ta ƙi goyon bayan abun saboda wata ɗiyar ƙawarta take son ya aura, dad ɗinshi ya ce mata tun da ya nuna Sapna yake so kuma an yi bincike bata da wani hali mara kyau kawai su ƙyale shi ya aure ta, ya ce mata ta san yaran zamani in aka ce za a hana su abun da suke so ko aka ce za ai masu dole kan abun da basu so abu mara daɗi na iya faruwa, har ya bata misali da lokacin da aka hana Ibrahim auran yayarta abun da ya biyo baya. Bayan dad ɗin ya sanar da Maleek cewa ya faɗa ma yarinyar iyayensa za su zo su gana da nata iyayen, a daren ranar ya kira Sapna waya ya sanar mata, baiwar Allah tamkar ta zuba ruwa ƙasa ta sha saboda farin ciki har sujjadar godiya ga Allah ta yi, suma iyayenta sun yi farin ciki kamar me, duk da haka Ammin tasu bata haƙura da zuwa wurin bokan da ta yi niyya ba. Ana zuwa neman aure aka saka rana gaba ɗaya wata ukku masu zuwa. Bayan Jameela ta yi arba'in har ta je Kano ta dawo ta yi ma Ibrahim zancen komawar su ƙasar waje don ta ci gaba da karatun ta, a nan yake sanar da ita baza su koma ba gaba ɗaya anan za su ci gaba da karatun shima zai yi master's degree ɗin shi kan political science don yana son fara yin siyasa, tubure mashi ta yi kan ita bata yarda ba gaskiya a can take son yin karatunta, ta ce idan ma shi anan zai yi to sai shi ya tsaya ita ta tafi, lalla6a ta ya shiga yi yana nuna mata manufar shi na su tsaya anan din ba don komai ba sai don su saba da mutane sosai yadda ba zai samu matsala a ƙi za6ar shi saboda ba zaune yake ba anan idan ya fito takara, ya nuna kuma dole sai itama ta tallafa mashi kan hakan 6angaren da ya shafi mata, ta ɗan ji tana goyon bayan shiga siyasar da yake son yi, sai dai ta wani 6angaren tana jin kishin yayan shi Sa'ad da matarshi dake a ƙasar waje ga kuma Sapna ma da an ɗaura auren su za su bar ƙasar, kasa 6oye abun da ke ranta ta yi ta ce mashi amman ita hakan ci baya ne a wurinta ga Amina can har ta yi degree ɗinta a ƙasar waje haka ma Sapna za ta je ta ci gaba da karatunta sai ita za a dankwafe ta anan ta ci gaba da karatu, nuna mata ya yi hakan duka na ɗan lokaci ne ai da zarar ya fito takara ya ci sai ƙasar da take so zata je, har ya bata misali da ai tana ganin yadda matan ƴan siyasa masu muƙamai suke fantamawa yadda ransu ke so, tana jin hakan ta ce mashi shike nan ta amince amman ta ya zata ci gaba da karatu a wannan ƙauyen garin, ya ce mata ta kwantar da hankalinta ya tsara masu komai, dad ɗinshi na da wani babban gidan gona a Zaria kuma akwai gida mai kyau a ciki can za su koma sai su ci gaba da karatun a ABU Zaria, cike da nuna gamsuwa ta ce mashi ta amince kuma zata taimaka mashi sosai a harkar siyasar shi amman sai ya yi mata alƙawarin idan ya fito takara ya samu duk abun da take so zai yi mata, yana murmushi ya ce mata ya yi mata alƙawarin hakan. A kwana a tashi bayan watanni ukku aka yi bikin Sapna da Maleek ana gamawa suka wuce India, kamar yadda Ibrahim ya tsara masu haka aka yi suka koma Zaria a can suka ci gaba da karatu ya yin da ya shiga shirye-shiryen fara shiga siyasa. Bangaren iyayen Fahad duk bayan lokaci suna zuwa Funtua wani lokacin ma anan yake barin su shi ya koma daga baya sai su bi shi. A kwana a tashi bayan shekaru biyu da wasu watanni dad din Deen ya kammala karatun shi ya tsunduma harkar siyasa yayin da Jameela ke cikin yin karatun degree dinta, cikin sa'a ta ubangiji a karon farko da Ibrahim ya fito takarar kujerar majalissar jaha sai gashi ya ci, don ya samu farin jini a wurin mutane duk da nasarar ta shi na da nasaba da mahaifinshi wanda yake mutum ne mai kyautata ma mutane sosai, zo ka ga murna a wurin Jameela ganin haƙarta ta fara cimma ruwa an zama matar ɗan majalisa, haka ƴan'uwa da abokan arziƙi suka yi ta zuwa taya murna, bayan rantsar da su suka kama aiki, a lokacin dole ya raba ƙafa bai a Katsina bai a Funtua haka Zaria da har lokacin Jameela ke a cikin yin karatu. Abu na farko da ta fara buƙatar ya siya mata ita ce danƙareriyar mota, ba tare da ya gardama mata ba ya siya mata saboda ya san ta taka rawa sosai wurin ganin ya ci za6en, nan fa Jameela a ka fara fankama ba kama hannun yaro, bayan wani lokaci ta buƙaci ya siya ma iyayenta gida shima bai ƙi ba ya siya masu gida mai kyau a can Kano, a hankali ta fara saka shiririta a karatun ta duk da ta yi nisa ta fara mashi ƙorafin ya za ai tana matar ɗan majalissa ana ganin tana karatu hakan ma sai ya ja mata raini, ƙiri ƙiri ta aje karatun ta matsa sai dai ta koma ƙasar waje ta yi, hakan kuma aka yi sai dai ya rinƙa zuwa ko kuma in ta samu hutu su zo. Suna gab da kammala tenure ɗin su ta farko Jameela ta gama karatunta ta dawo Nigeria, saidai ko da ta dawo matsa mashi ta yi kan sai ya siya masu gida a Abuja duk da a yadda ya so su koma Katsina da zama amman fir ta ƙi dole sai dai Abujar ya siya masu gida suka koma, son kai irin na Jameela a gabanta in dai ta ga zai yi ma dangin shi alkhairi sai ta yi ƙoƙarin hanawa, ta rinƙa ƙorafin shike nan don ya samu muƙami kowa ya dauƙo buƙatar shi sai ya kawo mashi ai koda aka za6e shi don ya yi ma al'umma aiki ne ba wai kowa ya zo da bukatarsa ba, amman kuma ita kullum cikin kawo mashi baƙatun da suka shafi danginta take. Bayan shekaru huɗu tenure ɗin su ta ƙare aka sake yin za6e, jam'iyarsu ta sake samun nasarar cin zaben hakan yasa duk suka samu yin tazarce, a lokacin Deen na cikin shekara ta bakwai, sosai suke son junansu shi da Fahad in suka haɗu kamar kar su rabu, a lokacin Fahad na cikin shekara ta goma, a wani zuwa da su Deen suka yi Funtua lokacin suma su Fahad suna a Funtua, gaba ɗaya Fahad ya dawo gidan hajiya anan wurinta suke wuni tare da Deen don tun a lokacin Fahad yake fuskantar tsangwama daga wurin Jameela shiyasa yake zama wurin hajiya, lokacin da su Deen za su koma Abuja haka yaron ya dingi kuka yana cewa a tafi da Fahad shima, da ƙyar aka raba su da yake shi Fahad ya ɗan girma sai dai ya yi ta zubar da ƙwalla. Ganin irin shaƙuwar da suka yi ne ya sa Hajiya ta yi ma Ibrahim magana kan ya ɗauki Fahad hakan zai saka su taso da zumunci mai ƙarfi, koda Jameela ta ji zancen da buɗar bakinta sai cewa ta yi a bari mana idan iyayenshi sun mutu sai a ce su ɗauke shi, amman yanzu ga iyayensa a raye miye na wani cewa ya dawo wurin su in ba son ɗaura masu ɗawainiya ba yaro ai sai iyayen shi, shi dai dad a lokacin nuna mata ya yi ba zai iya musanta ma maganar hajiya ba saboda haka ta yi haƙuri, wannan ne sanadiyar komawar Fahad gidan su Deen har suka ci gaba da yin karatu a makaranta ɗaya. A 6angaren Sapnah tuni ta kammala karatunta na medicine a india, daga baya kuma Maleek ya koma ƙasar America ya ci gaba da yin aiki da wani babban kamfanin fasaha. Sapna ba ƙaramin gata take samu a wurin Maleek ba, gaba ɗaya ta canza kana ganinta kasan hutu ya zauna mata idan ma aka ce maka a Nigeria aka haifeta anan ta taso har ta girma sai ka ƙaryata, sai dai har lokacin basu samu rabo ba ko batan wata bata ta6a yi ba, tun suna a India aka binciki lafiyar su gaba ɗaya inda aka tabbatar matsalar daga wurin Sapnah take, ba ƙaramar damuwa ta shiga ba amman shi Maleek sam bai nuna damuwar shi ba duk da yana son ya ga ya samu rabo, shine yake rarrashin ta yana nuna mata ko da a ce bazata ta6a haihuwa ba yana son ta a haka kuma za su ci gaba da rayuwa ba tare da wata matsala ba har ƙarshen rayuwar su, 6angaren danginta lokacin da suka ji zancen matsalar rashin haihuwar tata sun shiga damuwa sosai musamman Ammin su da kuma Jameela, Ammin har tambayarta ta rinƙa yi sun tabbatar an yi binciken sosai kuwa? Sapna ta tabbatar mata da ƙwararru ne suka yi binciken, sosai Ammin tasu ta shiga baƙin ciki don ba abun da ke a ranta face yanzu shike nan idan bata haihu ba Maleek na iya ƙara aure matar ta zo ta hayayyafa idan ya mutu su cinye gado, wannan dalilin ne ya saka ta damuwa sosai ta shiga bin bokaye ido rufe kan a yi mata aikin da Sapna zata samu ciki ta haihu, saidai kuma shiru Allah bai sa ta samu cikin ba. Bayan wasu shekaru, abubuwa da dama sun faru, ciki har da yin ritaya da ambasada ya yi suka dawo gida Nigeria da zama a lokacin shima mahaifin Fahad an maido shi aiki Nigeria. Cikin iko na Allah bayan shekaru goma da auren Sapna da Maleek Allah ya azurta su da samun rabo inda ta haiho ya mace wato Basma. Bayan yin ritaya ɗin ambasada da shekara ɗaya shugaban ƙasa na lokacin ya sake bashi muƙamin ambasadan Nigeria a ƙasar Spain, yana riƙe da muƙamin ne bayan wasu shekaru ya kwanta ciwon da ya zamo ajalin shi ya rasu, ba ƙaramin alhini ahalin shi dama al'ummar garin Funtua suka shiga ba na rashin dattijon arziƙi. Rayuwa ta ci gaba da gudana yayin da arziƙin iyayen su Fahad ya ninninku, mahaifin su Deen ya ci gaba da gudanar da harkokin shi na siyasa inda daga baya ya sake tsayawa takarar kujerar ɗan majalissar tarayya ya yi nasara. CIGABAN LABARI...... *_✨A CIKIN RAYUWA✨_* _New story from the writer of 'A Sanadin Makwabtaka',_ _ZAINAB BATURE_ _Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._ Page 14 Ƴar tafiya kaɗan Deen da Fahad suka yi daga parking space ɗin suka ƙaraso bakin babbar kofar shiga 6angaren, falo ne babba mai ɗauke da haɗaɗɗun kujeru royal kalar blue mai duhuwa, yadin kujerun na daga wurin da ake zama yana da zane-zanen kalolin blue mai haske da ruwan madara har da ɗan ratsin brown, akwai hadaddun labulaye masu inganci da babban carpet da ke shimfiɗe a tsakiyar kujerun saman tiles din da aka malala cikin falon, gaba daya komai na cikin falon kalolin su ya hau sun ƙawata cikinsa, akwai kayan kallo da na sauti da sauran na'urorin wuta da kayan ƙawata falo, akwai manyan hotunan ahalin gidan a wurare daban-daban, sosai falon ya haɗu tun daga kan ginin yadda ya tsaru kai ka ce ba falon tsohuwa ba. Zaune a saman kujera mai mazaunin mutum biyu Hajiya Binta ce tana sanye da cotton ɗin doguwar riga irin wadda ta dace da yanayin da ake ciki na zafi, don ma akwai sanyin Ac ya karaɗe ilahirin cikin falon, kanta ta saka hula, a yanayin halitta bata da jiki sosai amman kuma ba siririya can bace, kana ganinta kasan ta manyanta sosai don a shekaru za ta yi saba'in da ɗoriya amman da gani da ɗan ƙwarinta, tana da kyawun fuska doguwa mai dauke da dogon hanci da madaidaicin baki, daga yanayin jikinta yadda yake ƙem zaka fahimci ta haɗa iri da fulani duk da yanayin fatarta ba fara ce, za a iya kiranta da wankan tarwaɗa. Idanunta dake sanye cikin glasses na akan tv tana kallo, yayin da daga gabanta saman madaidaicin center table plate ne an yanka kankana a ciki, a hankali take ɗauka da fork tana kaiwa bakin ta, daidai zata kai kankana bakinta, sallamar da ta ji an yi ya sa ta kai idanunta saitin kofar shigowa tana amsawa, tana yin tozali da waɗanda suka shigo, da sauri ta mayar da kankanar saman plate tare da washe baki ta fara ƙoƙarin miƙewa, nufo cikin falon suka yi Deen ne a gaba yana ta sakar mata faffaɗan murmushi, yana zuwa gabanta ya ware mata hannuwa ta nufe shi da sauri ya rungumo ta yana murmushi, tare da lumshe idanuwan jin daɗin ganin kakar tashi da ya ɗauki lokaci bai gani ba, ɗagowa ta yi suna kallon juna da murmushi ta kai idanuwanta kan Fahad dake tsaye a gefe yana mata murmushi, "Wannan wane irin zuwan bazata ne haka!" Ta faɗa tana washe baki, "Yea, It's a suprise." Deen ya faɗa yana ƙoƙarin zama saman kujera tare da ita, kallon Fahad ta yi ta ce ya zauna mana ya yi tsaye, a saman kujera mai mazaunin mutum ɗaya ya zauna daga gefen su ya ɗaura duka hannuwansa a saman hannun kujeran, "Ɗan ball, Allah Ya yi an samu an leƙo ƙasar tamu ke nan, ai na yi zaton ma sai ka ɗan kwana biyu ka huta zaka zo nan." Ta faɗa tana ta murmushin jin dadin ganin jikan nata da ta dade bata sanya shi a idanunta ba, sai dai ta waya ko a tv in tana kallon wasan shi, amsa ya bata da ba zai iya jurewa ba yana ƙasar ya bari har sai bayan wasu kwanaki sannan zai zo ya ga sweety ɗinshi da yake missing sosai, ta washe bakin jin dadin maganar. "To ya ball ɗin, ai ina gani in kuna yi a tv, kana ƙoƙari sosai, ana ta ƙara ƙwarewa. Allah Ya ƙara taimakawa ya kuma tsare." A tare suka amsa mata da Amin, "Kun ga da kun sanar da zuwan naku da an shirya maku sosai, yanzu ba wani shiri da aka yi maku, na san dai jiya mun yi sallama da Fahad akan zai tafi tarbarka amman ba wanda ya sanar da ni yau zaku taho nan, don haka sai ku yi haƙuri duk abun da ya samu da shi za a tarbe ku." Gaba ɗaya ɗan murmushi suka yi Deen ya ce mata no problem, mai aikinta Balaraba ta shiga ƙwala ma kira, fitowa ta yi daga cikin wata ƙofa ta nufo cikin falon, ƴar babbar mace ce jikinta sanye da riga da zane na atamfa, tana fitowa idanunta suka hango Deen nan ta shiga washe baki, ƙarasowa ta yi gaban su cike da girmamawa ta ce ma hajiya gata, kafin ta faɗi mata dalilin kiran nata ta kalli Deen cikin washe baki ta yi mashi sannu da zuwa tare da gaishe da shi, ya amsa mata da ɗan murmushi, gaishe da Fahad ta yi ya ɗaga mata kai, "Baƙo ne muka yi ya yi mana zuwan bazata, akawo masu abun da za su sha sai ki shirya masu abinci a table." Amsa mata ta yi da to ta juya, Deen na murmushi ya ce mata shine baƙon, hajiyar na dariya ta ce mashi eh mana mutumin da za a yi shekaru ba a gani ba ai ya zama baƙo, yar hayaniya suka fara jiyowa daga waje hajiya ta kai idonta kan ƙofar shigowa tana faɗin kamar hayaniyar mutane take ji, miƙewa Fahad ya yi ya nufi kofar ya leƙa, juyowa ya yi yana faɗin a gate ne ya san su officer ne suka sanar da zuwan Deen, hajiya ta ce ai Deen ɗin ne yana da masoya har zuwa ake ana tambayar ta yaushe zai zo, zama Fahad ya yi tare da ciro wayar shi ya yi sending kira, magana ya yi da officer ya bashi umarnin kar a bar kowa ya shigo sai Deen ya huta ko zai ga mutane, cire wayar ya yi daga kunne yana faɗin dole sai an ƙara security a gate, hajiya ta ce gaskiya don ta san yanzu mutane za su cika gidan. Bayan Balaraba ta gama shirya masu abincin ta zo ta sanar da su, Deen ya ce ma hajiya ta taso su je su ci abincin ta ce ai ita tuni ta ci abinci shiyasa ma ta zauna tana shan kankana, ya ce to ta taso su je ta bashi a baki ya yi missing hakan, tana murmushi ta miƙe, Fahad ma ya tashi, Deen ya kama hannunta suka nufi wurin table tana faɗin ita yaushe rabon ma da ta zauna cin abinci a can ta fi jin daɗin ta zauna kan kujera ta ci, balaraba ce ta yi serving na su abincin hajiya ta ce dole a ƙara sama masu wani abun su ƙara ta amsa mata da to, bayan ta gama ta bar wurin, a nutse suka fara cin abincin hajiya ta fara ba Deen a baki kamar yadda ya buƙata suna ta murmushi, lumshe ido ya yi yana tauna abincin ya furta ya yi missing ɗin wasu abinci na nan, "Ko dai santi kake yi?" Hajiya ta faɗa tana faffaɗan murmushi, amsa ya bata da in ma ya yi santin ba laifi bane don cook ɗinta ta iya abinci sosai, "Ko kana son in baka ita idan ka yi aure sai ta rinƙa dafa maku abincin, ko kuwa ka fi son na matar ka?" Hajiya ta tambaya bayan ta bashi abincin yana taunawa, Fahad ya ɗaga ido ya kalle shi da ɗan murmushi, shima murmushin kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba, a ranshi ya ayyana baya ma tunanin Basma ta iya ko ruƙe tukunya balle akai ga maganar iya yin girki. Bayan sun gama cin abincin Fahad ya ce ma hajiya ta sa mai aikinta ta ɗauko masu jakunkuna a cikin mota kafin suka wuce bangaren da ɗakin da Fahad ke zama a gidan don su huta, hajiya kuma ta koma cikin falo bayan ta kirawo Balaraba ta bata umarnin ɗauko jakunkunan. Da sallama ta shigo cikin gidan, saida ta ƙara yin wata da ɗan ɗaga murya sannan ta jiyo muryar innarsu tana amsa mata daga can cikin ɗaki, nufar ɗakin innar tasu ta yi tana haye tudun baranda lokacin innar ta fito jikinta sanye da doguwar rigar atamfa, tana ganin Salma ta saki faffaɗan murmushi tare da faɗin, "Alhamdulillahi, hasken gidanmu ya dawo." Washe bakin jin daɗi Salma ta yi ta nufe ta da sauri tana ƙarasawa innar ta buɗe mata hannu ta faɗa jikinta, ɗagowa ta yi tana kallon innar ta ce, "Innarmu ina wuni, ya gida?" "Lafiya lau tauraruwata, ya makarantar, kin dai ci abinci ko?" Tana ƴar dariya ta ɗaga mata kai, dama kullum ne idan ta dawo daga makaranta sai ta tambaye ta ta ci abinci, "Je ki rage kayan jikin ki, bari na kawo maki abinci." Kai ta ɗaga mata ta wuce inda ɗakinta yake innarsu kuma ta nufi kicin, ba a jima ba Salma ta fito ta cire hijab ɗinta sai riga da wandon uniform kanta ba kallabi sai tufkar kitsonta dake naɗe, wata irin suma gare ta mai kyaun gaske daga gaban kanta ta kwanta mata luf luf, cikin barandar ta dawo lokacin innar ta iso gabanta riƙe da plate ɗin abinci ta saka mata cokali ta bata, "Thank you best mom." Murmushin daɗi innar ta saki Allah Ya sani tana tsananin jin son ƴar tata, ita ɗin kyautar Allah ce a gareta don gani take kamar bata isa ta haifi kamar ta ba, ganin tana ƙoƙarin zama akan tudun baranda ta nuna mata tabarmar dake a shimfiɗe ta ce ga wuri nan ta zauna, Salma ta ce lafiya lau bari ta zauna anan ɗin, ita kuma innar ta zauna a saman tabarmar. "Ban ga su Imrana ba, ba dai basu dawo ba har yanzu?" Salma ta tambaya tana kai abinci baki, "A'a sun dawo, na aiki Imrana kantin Mubarak ya siyo mani ɗan tsami shine Hamza ya bishi." Kai ta gyaɗa ta sake cewa, "Halan bacci Usman ke yi?" Innar ta bata amsa da kamar ta sani, ƴar dariya Salma ta yi ta ce ai kusan kullum ne idan ta dawo daga makaranta yana bacci, tana cikin cin abincin ta ƙware ta dafe ƙirji tana tari, a ruɗe innarsu ta miƙe ta nufi hanyar kicin da sauri, dawowa ta yi hannunta riƙe da ɗan babban kofi ta kawo mata, da kanta ta bata ruwan a baki, bayan ta gama sha ta ce mata ta yi haƙuri ta manta bata haɗo mata da ruwa ba, Salma tana murmushi ta furta, "Innarmu kina ji da ni sosai, shiyasa Sagir yake kishi da ni." Dariya innar ta saki tana komawa wurin zamanta ta ce to ba dole ta ji da ita ba ƴar macen tata guda ɗaya tal, "Ai zaki ƙara haifo mana wata in sha Allahu." Waro ido innar ta yi, "Haihuwar lafiya kuma Salma, ai na gama ina laifin ku da na haifa, mun bar ma yara dai." "Ai innarmu kema ba wani girma kika yi sosai ba, kamar ma baki haife mu ba Allah." Tana dariya ta ce ta girma mana tun da ta kai shekara arba'in. "Amman dai Allah innarmu baki girmi haihuwa ba, kina da kyawun jiki ba wanda zai ce kin kai shekara arba'in." Shiru innar ta yi bata ce komai ba tana yar dariya. "Ina mutumina man Sagir ko an shige gari." Salma ta tambaya, innar ta bata amsa da bada jimawa ba ya shigo ya ɗauki abinci ta tambayeta ta duba ɗakin su ne baya nan, Salma ta ce da ta shigo ta ga an ɗan turo ƙofar ɗakin shiyasa bata leƙa ba, innar ta ce to ba mamaki yana ciki yana bacci, wayar innarsu dake a cikin ɗaki ce ta fara yin ƙara, Salma har ta yunƙura zata je ta ɗauƙo mata innar ta dakatar da ita ta ce ta ci gaba da cin abincinta bari ta je ta ɗauka, lokacin da ta shiga ɗakin har kiran ya yanke, ɗauko wayar ta yi tana kokarin duba wanda ya kira ta, daidai tana fitowa wani kiran ya sake shigowa, zama ta yi akan tabarmar tare da ɗauka ta kai kunne, sallama ta yi kafin cike da girmamawa ta gaishe da wanda ya kira ta da fara'a har da ɗan rankwafawa, ɗan saurarawa ta yi kafin ta amsa da yaran duk suna lafiya gasu nan duk sun dawo daga makaranta. "Eh hajiya....to lafiya lau ba matsala za a samu dama cikin yin ta nike yanzu haka." Ɗan saurarawa ta yi kafin ta sake cewa, "Lafiya lau hajiya bakomai a basshi." Da sauri kuma ta ƙara cewa, "A'a ba a yi haka ba hajiya." Shiru ta yi tana sauraren hajiyar da ta kira ta, daga baya ta furta to zata faɗi sai an gama, daga haka suka kammala yin wayar ta cire daga kunnanta tana murmushi tare da faɗin, "Ina ruwan hajiya.." Salma dake kallon ta ta tambayi wace hajiya ce? "Hajiyar Ambasada ce, awara take so ta rabin tiya, wai baƙi ne suka yi mata zuwan bazata ba a shirya masu wani abincin kirki ba shine take son a haɗa masu awarar da sauce ta san za su ji daɗinta, to wai da ta tambayi kuɗin na ce ta basshi shine ta ce man to nima na bar awarar tawa." Ƴar dariya Salma ta yi, "Mutumin da haka nan ma kullum cikin yi maka alkhairi yake, duk aka yi mata awara haka zata bada kuɗi fin abun da aka faɗa ai ba wani abu bane don an ce ta barshi." Innar ta faɗa tana ta murmushi, "Yanzu wata za a yi mata daban?" girgiza kai innar ta yi ta ce, "Kawai bari sai a bata cikin wadda aka yi tun da sauri ake kada a 6ata mata lokaci, ke sai ki soya ragowan kawai." Kai Salma ta ɗaga, su Imrana ne suka dawo daga aiken, suna ganin yayarsu ta dawo suka nufo ta suna murmushi, ware ma hamza hannu ta yi ya faɗa jikinta yana dariya ta ce masu ya makaranta duk suka amsa, kallon Imrana dake tsaye gefe ta yi da murmushi ta ce, "Malam Imrana ya, yau akwai assignment ne?" Kai ya ɗaga mata kafin ya ce mata amman bashi da wahala zai iya ta jinjina kai. Bayan innar ta amshi saƙon aiken ta koma kan aikin awaran Salma ma ta bita don ta taya ta, innarsu na ta basshi ita da ta kwaso gajiyar makaranta kuma anjima zata fita suyan awara, Salma ta bata amsa da ai yau awaran bashi da yawa bazata gaji ba. Zuwa bayan sallar la'asar sun gama awaran Salma har ta yi wanka, fitowa innar su ta yi daga ɗaki ta ƙwala ma Salma kira, bayan ta amsa ta ce mata ta fito ta kaima hajiya awaran ta san zuwa yanzu ta tsane, amsawa ta yi da to daga cikin ɗakin, ba a jima ba ta fito jikinta sanye da doguwar rigar material ta yafo madaidaicin baƙin gyale a saman kanta, nufar inda innarsu take a duƙe tana maida awaran cikin roba ta yi ta ce mata gata, nuna mata robar ta yi bayan ta ɗauka ta ɗago ta ce ma innar idan ta tambayi kuɗin ya zata ce mata, "Jeki kawai, idan ma ta tambaya ki ce kawai ban faɗi maki ba." Amsawa ta yi da to ta wuce hanyar fita. A nutse take tafiya ta rungume robar awaran a gefen cikinta, da alamun mamaki take kallon ƙofar gidan hajiyar da yake danƙam da mutane ga motar jami'an tsaro an faka daga can gefe, yayin da a bakin gate ɗin gidan jami'ai ne sun kai guda shidda sun tare mutane, a cikin ranta ta shiga raya ko lafiya? wani 6angare na zuciyarta ne ya bata ƙilan wannan ɗan majalissar ɗan hajiyan ne ya zo, tabbatar ma kanta ta yi da hakan ne ma, tsallaka titin ta yi tana ci gaba da tunanin ko ma za a barta ta shiga, da ƙyar ta samu kaiwa bakin gate ɗin inda jami'an suke, wani officer ne ya tambaye ta ya aka yi? A ɗarare ta ce mashi aiko ta aka yi ta kawo ma hajiya saƙo, tambayar miye acikin robar ya yi saboda a rufe take, hannu ta kai ta cire marfin ya gani ya ce ta wuce, wani a cikin sauran officers ɗin ya buɗe mata ƙaramar kofa ta wuce, tana shiga nan ma cikin harabar wasu dandazon mutanen ne daga can gefen parking space sun kewaye wurin sai hargowa suke yi, nufar shiga cikin gidan ta yi tana yi tana waiwayen mutanen har ta isa ƙofa ta shige, falon wayam ba kowa sai tv dake ta aiki, shiga ta yi ta tsaya daga tsakiyar falon ta fara yin sallama, sai da ta yi sau ukku sannan ta ji an amsa mata, Balaraba ce ta fito tana amsawa, tana ganin mai yin sallamar ta nufo cikin falon da murmushi, "Salma ke ce?" Tana murmushi ta amsa mata, "Eh Aunty Balaraba, ina wuni." Amsa mata ta yi da lafiya lau ta tambayeta ya makaranta har an dawo ta ce eh, faɗi mata saƙon da aka aiko ta ta yi Balarabar ta ce har an kawo awaran ke nan to bari ta yi ma hajiya magana ta nuna mata kujera ta ce ta zauna, ba a jima ba ta fito daga bangaren hajiyan ta ce mata gata nan zuwa, ba a ɗauki lokaci ba hajiya ta fito ta nufo cikin falon, "Salma ce?" Ta tambaya da murmushi tana ƙarasowa, miƙewa Salma ta yi ta amsa da eh tare da gaishe da hajiya, amsa mata ta yi ta tambaye ta ya karatu, ganin ta miƙe ta ce mata ta koma ta zauna, "Wai nikam hayaniyar mi cece nike ji tun a cikin ɗaki sama sama?" Hajiya da har zata zauna ta dakata tana tambayar Balaraba, "Mutane ne da yawa a can wurin ajiye motoci, a waje ma wurin gate akwai wasu sosai ofisoshi sun hana su shigowa, nima na ɗauka baza su barni ma in shigo ba." Salma ce ta faɗa, nufar hanyar babbar window hajiya ta yi ta leƙo wajen, jinjina kai ta hau yi kafin ta juyo ta dawo tana faɗin, "Mutanen Deeni ne. Wannan ma ai har ya fi mahaifin shi tara jama'a. Su dai maza Allah Ya yi su da jarabar son ƙwallo." Dawowa ta yi ta zauna kan kujera tare da kallon Balaraba ta ce mata ta ɗauki awaran ta je ta fara aikinta ta amsa da to bayan ta ɗauka ta tafi, "Duk ya ƴan'uwan naki." Hajiya ta tambaya tana kallonta da murmushi, "Suna nan lafiya lau." Ta amsa itama da murmushi, "Nawa ne ta ce kuɗin?" Amsa ta bata da bata faɗi mata ba kawai ta ce ta kawo, ɗan kwa6e baki hajiya ta yi bata ce komai, gaba ɗaya maida hankalin su suka yi akan tv suka ci gaba da yin kallo a tare, after some minutes suka ji an yi sallama, a tare suka kai idanun su wurin ƙofa, Deen ne ya shigo jikin shi ya sauya shigar da ya zo da ita zuwa farar jallabiya mai gajeran hannu ta fito da suffar shi ta ƙaƙƙarfa, cikin falon ya nufo ya nufi can gefen hajiya saman kujera ya faɗa ya kai hannu ya shafi goshin shi tare da huro iska waje, hajiya dake kallon shi tana murmushi ta ce halan mutanen na shi sun tara mashi gajiya, amsa mata ya yi da wallahi ai bai ma iya gama ganin su ba ya gaji sai wani lokacin, tun lokacin da ya shigo Salma ta kafe shi da ido tana bin shi da kallon al'ajabi, tabbas in dai ba ƙarya idanunta ke nuna mata ba wannan shine mutumin nan na ɗazu, abun da ya ƙara tabbatar mata da hakan sumar kan shi duk da a yanzu ba a fake take ba ya sake ta ta kwanto a wuyanshi, sai kuma muryarsa da bata tunanin zata ƙara jin irinta ba tare da gane ba don ta fita daban, sam bai kalle ta ba bayan ya gama yi ma hajiya magana wayar shi ya shiga latsawa, Fahad ne ya shigo da sallama shima ya canza kaya zuwa jeans da t-shirt dama bayan sun yi wanka ne suka fita yin sallar la'asar da lokacin ta ya yi shine fa mutane suka hana su shigowa ciki sai yanzu, wani iri faɗuwa gaban Salma ya shiga yi lokacin da ta kallo mai shigowar idanunta suka yi tozali da Fahad suka haɗa ido, da sauri ta janye idanun nata ta koma kallon ƙasa, cikin falon ya shigo ya nufi kujera ya zauna hajiya ta ce mashi an shigo ya ɗaga mata kai, bin Salma ya yi da kallo tun da ya shigo suka haɗa ido ya so ya gane ta, a hankali ta ɗago zata saci kallon shi aikuwa karaf idanunsu suka haɗu, kasa janye idanun nata ta yi duk ta bi ta kama kanta ta shiga kikkafta idanu yayin da bugun zuciyarta ya tsananta, ji take kamar ta tashi ta tafi amman ta rasa ƙwarin gwuiwar yin hakan, ganin irin kallon da yake jefa mata yasa ta sauke idanunta da sauri tana yamutsa yatsun hannunta, "What the hell are you doing here?!" Kallon Fahad hajiya ta yi jin yayi magana duk da bata fahimci mi ya ce ba, ce mashi ta yi magana yake ne, ganin direction ɗin da yake kallo yasa ta juya ta kai idonta kan Salma da itama shi take kallon tana ɗan motsa baki, kasa fahimtar kallon mi suke ma juna hajiya ta yi ta sake kallon Fahad, a daidai lokacin ya miƙe ya nufo wurin da Salma take ta miƙe da sauri, bayan ya tsaya daga gabanta, fuska a ɗaure tamkar bai ta6a yin dariya ba ya sake furta, "Mi ya kawo nan!" Cikin yar tsawa ya yi maganar, hakan ne ya jawo hankalin Deen da ke latsa waya ya maido hankalin shi kan su, "Baki ji maganan da nake maki ba, uban me ya kawo ki gidan nan??" Jikinta ne ya shiga yin rawa don a fusace yake mata maganar, cikin rawar murya ta ce, "D..dama aiko ni aka yi wurin hajiya..." "Get out of this house! Idan na sake ganin ki a gidan nan sai na tattaka ki." Da sauri ta juya zata tafi hajiya da gaba ɗaya ta ruɗe da ganin abun da ke faruwa da sauri ta miƙe tana faɗin, "Fahad wai mike faruwa ne? Ka san Salma ne? Mi ya haɗa ka da ita?" Shiru bai bata amsa ba idon shi na kan Salma da ta fara tafiya da sauri za ta bar falon, "Ke Salma dakata, zo nan!" Hajiya ta faɗa, tsayawa ta yi ta juyo a ɗarare ta dawo ta tsaya daga gaban su, tambayar ta ta yi miya haɗa ta da shi, motsa baki ta shiga yi ta kasa cewa komai, kawai sai gani hajiya ta yi Fahad ɗin ya kai hannu cikin zafin nama zai wanka ma Salma marin da yayi niyya yi ɗazun, da sauri Salma ta goce duk da haka saida ya ɗan same ta, ruɗewa ta yi ta fashe da kuka gyalenta ya zame daga saman kanta, salati hajiya ta rafka tana ce ma Fahad mike damun shi? Mi ta yi mashi wai?" "Hajiya just ta bar gidan nan yanzu, and I don't want to see her again, idan ba haka ba yanzun nan zan sa officers su kama ta su je su kulle ta." A zuciye ya yi maganar, wani salatin hajiya ta ƙara zabgawa hakan ya ja hankalin Balaraba dake a cikin kicin ta fito bakin ƙofa tana kallon abun da ke faruwa, yunƙurin barin falon Salma ta sake yi hajiyar ta dakatar da ita tana tambayar wai mi ya haɗa su, "Fahad wai bazaka buɗe baki ka gaya mani abun da ya haɗa ku bane? A ina ka san Salma kuma mi ta yi maka ne? Wuri na fa aka aiko ta." Ba tare da ya ce komai ba ya juya ya tafi, hajiya da Balaraba suka bi shi da ido cike da al'ajabi har ya shige ciki inda ɗakuna suke, maido kallon ta ta yi kan Salma ta matsa tare da dafa ta ta ce ta faɗi mata mi ya haɗa su, sam ta kasa magana sai kuka take yi tare da ƴar ajiyar zuciya, hajiya ta fahimci jin nauyin faɗi mata take yi, kallon inda Deen yake zaune yana kallon duk abun da ke faruwa ta yi ta ce, "Ko ka san abun da ya haɗa su ne?" Ɗan yamutsa fuska ya yi ya ce ba komai ya sani ba amman ita yarinyan ai ta san mi ya haɗa ta da shi ta faɗi mata mana, zaunar da Salma ta yi saman kujera mai mazaunin mutum biyu itama hajiya ta zauna, hannunta akan kafaɗarta cikin sigar rarrashi ta ce mata kar ta ji komai ta faɗi mata abun da ya haɗa su zata fahimta, dakatawa ta yi da murzar idon da take yi da gyalenta tana ci gaba da yin kukan cikin zuciya tana kikkafta ido, a hankali take bin mutanen cikin falon da kallo har da Balaraba dake a can bakin kicin, tsaida idonta ta yi akan Deen daidai lokacin ya yi mata kallon ƙasan ido, da sauri ta kauda idonta don sai ta ga kamar ya harare ta, "Ina jin ki Salma.." Hajiya ta faɗa, Cikin rawar murya ta fara magana, "D...dama ɗazun ne lokacin da na dawo daga makaranta...shi..ne zan tsallaka titi na hango motar su can nesa, to..na yi tunanin har zan tsallaka basu ƙaraso ba..shine suka kusa buge ni da mota, to...shine ya leƙo yana mani magana...shi..ne..." Kasa ƙarasawa ta yi ta ci gaba da yin ajiyar zuciya tana murzar ido, hajiya ta so ta fahimci sa6ani ne ya shiga tsakanin su da abun ya faru shiyasa Salma ta kasa faɗi mata, miƙewa ta yi ta ce mata kada ta tafi ta jira tana zuwa daga haka ta nufi cikin hanyar da Fahad ɗin ya bi, gaban Salma ne ya ci gaba da bugu don ta gane wurin shi hajiyar zata je kuma ta san zai iya faɗi mata komai, ƙasa ƙasa ta ci gaba da yin kukan gyalenta a fuska, "Kina ma wa kuka? Ko wani ya sa ki ne ki yi mashi rashin kunyan?" Kamar daga sama ta tsinkayi muryar Deen ya faɗi hakan, cire gyalen ta yi daga fuskarta ta kalle shi da jiƙaƙƙun idanuwa, ɗage mata gira ya yi ya sake cewa, "You caused it, so what's the point of crying now?" Cikin muryar kuka ta ce, "Ai ni ba rashin kunya na yi mashi ba wllh, tun farko saida na bashi haƙuri amman shine ya ce mani dabba mara hankali, kuma farko ni bance mashi komai ba shine ya sake ce mani mara kunya..." Shiru ta yi tana kikkafta ido tana ɗan nishin kuka, "Sai kika nuna mashi ke mara kunyan ne?" Ya ɗage mata gira, girgiza masa kai ta yi tana motsa baki, ta sa gyale tana goge ƙwallan da suka zubo mata ba tare da ta ce komai ba, ɗan ta6e baki ya yi ya ci gaba da ta6a wayan shi....... *Littafin A Cikin Rayuwa kashi na farko zai zo maku a kyauta, ga mai buƙatar kashi na biyu zai biya 500 kacal. Domin neman ƙarin bayani a tuntubi waɗannan lambobin ta hanyar aika saƙon whatsApp kawai banda kira, 09013804524, 08169856268* *_✨A CIKIN RAYUWA✨_* ZAINAB BATURE _Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._ Page 15 Dawowa hajiya ta yi ta nufo cikin falon tana gyara zama glasses dinta tare da faɗin, "Kai, abun dai bai yi dadi ba sam, ni bana son abun tashin hankali wllh..." Tsayawa ta yi ba tare da ta ƙaraso cikin falon ba ta ce, "Salma ta so kin ji." Miƙewa ta yi tana gyara gyalenta ta nufi hajiyar, kama hannunta ta yi suka koma hanyar da ta fito, cikin corridor ɗin da ɗakuna suke suka nufa, wata ƙofa hajiya ta tura suka ta shiga tana riƙe da hannun Salma, wani irin sanyin ac da ƙamshi ne suka karade cikin ɗakin, gaban Salma ne ya faɗi ganin Fahad ɗin kwance a saman lafiyayyan gadon ɗakin ya kwanta rigingine tare da rufe idanun shi, "Zo ki bashi haƙuri, ai durƙusa ma wada ba gajiyawa bane, balle ma wannan ba wadan bane, shi bin na gaba bin Allah ne." A ɗarare Salma ta matsa daga bakin gadon ta durƙusa ƙasa, idanunta cike da ƙwalla cikin rawar murya ta furta, "D...don Allah Ka yi haƙuri." Shiru kaman bai san da su a wurin ba don ko motsawa bai yi ba, "Fahad, baka ji ana magana ba."Hajiya dake tsaye bakin gadon ta faɗa idanunta akan shi, sai da aka ɗan ɗauki lokaci sannan ya bude idanunsa da har sun ɗan sauya kala, nuni hajiya ta yi mashi da Salma ta ce mashi gata nan tana bashi haƙuri, ɗaura idanunsa ya yi akanta still tana durƙushe suka haɗa ido ya wani ƙara tamke fuska, "Ka yi haƙuri don Allah..." Ta faɗa tana sussune kai tare da kai hannu tana ta6a gefen fuskarta, ɗauke idanun shi ya yi ba tare da ya ce komai ba, hajiya ce ta ƙara ce mashi ya yi shiru sannan a taƙaice ya ce, "Ta je." Sanin yana da zuciya ya sa hajiya yin ɗan murmushi ta ce, "Ka haƙura ko?" Shiru ya ɗan yi kafin ya ɗan ɗaga hannu, hajiya ta ce, "Ba shike nan ba, taso to Salma." Miƙewa ta yi suka nufi ƙofa, a hankali ya juya yana kallon bayan su har lokacin fuskar shi a ɗaure take, can ƙasan maƙoshi ya ɗan ja guntun tsoki bayan sun fita. Cikin falon suka dawo Deen ya ɗaga ido yana kallon su, wuri hajiya ta nuna ma Salma ta ce ta zauna itama ta zauna, "Ta bashi haƙuri ba shike nan ba, dama duk sharrin zuciya ne ba wani abu ba, da kuma shaiɗan da bai son ya ga an zauna lafiya." Hajiya ta faɗa tana daga hannu idanunta akan Deen, ɗan murmushin gefe Deen ya yi ya ɗauke idonsa daga kan su, bayan ɗan lokaci Salma ta miƙe tana kallon hajiya ta ce mata zata tafi gida, "To shike nan Salma na gode. Komi ya wuce kada ma ki yi maganar a gida kin ji ko. Kuma daga yau kada ki sake yi ma babba haka, idan babba ya yi maka abu ka rama people will see you as disrespectful, don haka koda abu bai yi maka daɗi ba, in dai babba ne ya yi maka ka yi haƙuri ya fi kuma hakan ba faɗuwa bane, kin ji?" Kai ta ɗaga a sanyaye ta ce, "In sha Allahu ba zan ƙara ba." Hajiya ta ce, "Yauwa Salma, dama na san ba halin ki bane, kawai sharrin zuciya ne." Shiru Salma ta yi kafin a hankali ta ce mata sai anjima ta juya ta nufi kofa, "Salma ɗan dakata, bari a kawo maki robar...koda yake je ki ma kawai zan aiko a kawo harda saƙo." Kai ta jinjina ta ci gaba da tafiya, tana zuwa ƙofa zata fita, a hankali ta juya da niyyar ta saci kallon Deen, kamar an ce shima ya ɗago karaf suka haɗa ido da sauri ta juya ta fuce, ya yi kaman zai yi murmushi ganin yadda ta yi. Miƙewa ya yi zai bar falon hajiya ta ce halan ya gaji da zaman, shafa sumar shi ya yi ya ce mata zai je ya shirya ne za su je gidan su Fahad, "Ko ku bari zuwa bayan magrib don ga awara can ana haɗa maku kuma tafi daɗi mutum ya ci ana gama soyawa, na san dai ba wani ƙoshin kirki kuka yi ba, bama kamar kai nasan ka baka wasa da abinci, dama ana cewa ƴan ƙwallo cin tsiya ne da ku. To dama yadda kuke jijjige jiki ma ai dole ku ci abinci." Murmushi kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba ya juya ya nufi hanyar corridor. Cikin sauri take tafiya bayan da ta fito daga cikin gidan, lokacin da ta shigo kwanar gidan su ta hango su Sagir acan saman dandamalin gidan dake kallon gidansu, su da yawa suna ta hargowa, ashe baya a gida, tun yana gama cin abinci bai daɗe da kwanciya ba wani abokinsa ya kira sa yake sanar masa game da zuwan Deen, aikuwa wuff ya tashi, rigarsa ma a ƙofar gida ya ƙarasa saka ta, lokacin da Salma ta shiga gidan hajiya yana a cikin mutanen da ta gani a wurin parking space don da bala'e sai da ya yi yadda ya samu suka shiga, zaman da suka yi a nan tattaunawa suke akan ganawar da suka yi da Deen ɗin inda ya yi masu albishir da zai kafa sabon club ɗin shi anan Funtua shine ya basu za6in sunan da suke son a saka ma club din shine fa ake ta musayar ra'ayi kamar za su tashi sama don daɗi, ko kallon su Salma bata yi ba lokacin da ta ƙaraso saitin su ta wuce zata shiga gida, "Ke, Salma zo nan..." Banza ta mashi ko juyowa bata yi ba, "Ba ki ji ina kiran ki! ga Aliyu nan shine ke son magana da ke." Wani irin 6acin rai ta ƙara ji ya kama ta, Aliyun abokin shi ne yake haɗa ta da shi wai son ta yake, ita kuma ta ƙi kula shi don harkar samari bata a gabanta karatunta ta saka a gaba, bama Aliyun kaɗai ba ana yawan cewa ana son ta amman bata sauraran wani saurayi, burinta ta gama makaranta ta wuce ta yi karatun nursing ta zama kamar auntynta Kubra, kuma har da ita Kubran ta yi mata huɗubar kar ta biye ma samari ta maida hankali kan karatun ta don in dai tana son zama nurse sai ta yi karatu sosai. Bata iske kowa ba a tsakar gidan bayan ta shiga, kai tsaye hanyar banɗaki ta nufa, a bakin rijiya ta ɗauki buta wadda ke da ruwa a cikinta, ƙarar motsin da innarsu ta jiyo ya sa ta ɗaga murya daga cikin ɗaki tana tambayar waye anan ta bata amsa da ita ce, "Salma kin dawo?" Ta ce mata eh, tana ƙoƙarin shigewa cikin banɗakin daidai innar ta fito sai dai ta ga shigewar ta, tana shiga ciki ta yi tsaye tare da jingina da bango zuciyarta ta shiga dawo mata da abun da ya faru, ƙwalla ne suka shiga zubo mata ta fara yin kuka a hankali, bata ta6a dana sanin abu kamar wannan ba, maida akalar tunaninta ta yi kan Deen, yanzu ta gane shine ɗan ƙwallon da su Sagir ke maganar shi, ita sam bata san shi ba, ko Fahad bata ta6a gani ba, dama bata fi shekara biyar da ta dawo garin ba daga Kaduna, kuma basu daɗe da suka fara yin hulɗa da hajiyar ambasada ba sanadin Balaraba da ke kawo a yi masu awara, kuma ba kasafai ta cika zuwa gidan ba don wani lokacin idan aka gama Balaraba ce ke zuwa ta amsa ko kuma a aika su Imran su kai, ita zuwanta gidan ma za a iya ƙirga shi, fuskar Deen ce ta shiga dawo mata, ita kanta ta gasgata kyawunsa sosai, ga shi komai nasa mai burgewa ne, ba ƙaramin daɗi maganar shi ke yi mata ba, _"Kina ma wa kuka? Ko wani ya sa ki ne ki yi mashi rashin kunya....."_ Maganar da ya yi mata ta tuno, a ranta ta ayyana yanzu shike nan kallon mara kunya suke mata, idanuwanta ne suka cicciko da ƙwalla ta ƙura ma wuri ɗaya ido, ta ɗauki mintuna a haka kafin ta duƙa ta wanke fuskanta da ruwan cikin butar da ta shigo da ita, dama ba wani abu za ta yi a banɗakin ba kawai bata so innar su ta fahimci wani abu ne. Lokacin da ta fito daidai innar su itama ta fito daga cikin kicin, tsayawa ta yi da murmushi tana jiran ƙarasowar ta, daga gefe Salma ta tsaya ta ce mata hajiyar ta ce zata aiko da robar da kuma saƙo innarsu ta ce to, shiru suka ɗan yi Salmar tana kallon gefe, "Salma..." Har saida gabanta ya bada rass jin yadda ta kira sunan ta, juyowa ta yi suka haɗa ido, "Ya aka yi ne?" Ƙaƙalo murmushi ta yi ta ce mata ba komai, "Ah saidai idan abun da baki yi mani zaki fara, amman daga ganin fuskar ki akwai abun da ke damun ki, kamar ma har kuka kika yi ko?" Shiru ta yi tana kikkafta ido, tunowa ta yi da gargadin da hajiya ta yi mata kuma ko ba haka bama bata jin zata sanar da ita abun da ya faru don ta san itama ta yi ba daidai ba abun da ta yin, dabara ce ta faɗo mata cikin ɗan yamutsa fuska ta ce, "Ba wanccan Sagir ɗin bane." Tana jin ƴar ajiyar zuciyar da innar tasu ta sauke alamar hankalinta ya kwanta, "To mi kuma ya haɗa ki da shi ku da baku gajiya?" "Wai yanzu na taho zan shigo shine ya kama yi mani maganar wannan Aliyu, kuma ya san na ce mashi ya daina haɗa ni da shi ban so amman ya ƙi dainawa." Yar dariya innar tasu ta yi ta ce to in banda abun ta miye laifin wanda ya nuna yana son ka, cikin tura baki ta ce ita dai bata so kuma ma ba aunty Kubra ta hana ta yin wata soyayya ba ta ce ta maida hankali akan karatu, "Haka ne, shike nan ki bari zan gargaɗi Sagir ɗin kan hakan. Kin ma tuna mani da baki nan mamar taki Kubra ta kira waya tana tambayar ki na ce mata kin fita idan kin dawo kya kira ta." Lokaci guda ta washe baki jin maganar, Allah Ya sani tana son Aunty Kubra sosai saboda itama tana nuna mata ƙauna, wani lokacin har mamaki Salma ke yi yadda take tsananin ƙaunarta, duk da dalilin hakan kusan a bayyane yake bai rasa nasaba da rashin haihuwar da Allah bai bata ba, tambayar innar tasu ta yi ina wayar ta kira ta ta ce mata tana cikin ɗaki, ta wuce da sauri don ta je ta kira ta. Bayan sallar magrib su Deen suka fito cikin falo don tafiya gidan su Fahad, yana sanye cikin ƙananun kaya farar t-shirt sai overshirt ja irin riga da ake ɗaurawa a saman wata mai budaddan gaba da ana ganin ta ciki, wandon jikinsa dark-washed jeans ne sai ƙafafunshi ya sanya takalma fararen gucci ace, hannun shi haɗaɗɗan agogo ce mai duhu da ta hau da kalan wandon jikinshi, ya yi kyau har ya gaji sai faman baza ƙamshi yake, shi kuma Fahad ƙananun kayan da ya canza ɗazun ne a jikin shi, gaba ɗaya falon ya karaɗe da kamshin jikinsu, hajiya dake zaune ta kalle su da murmushi ta ce sun fito Fahad ya amsa mata, Balaraba ta ƙwala ma kira ta fito, umarnin ta ɗauko saƙon ta bata ta amsa da to kafin ta juya ta koma cikin kicin, fitowa ta sake yi hannunta riƙe da wani ɗan madaidaicin kwando kalan na ƴan gayu a cikin shi warmer ne guda biyu yar madaidaiciya sai mai bi mata, "An ce so so ne, amman dai son kai ya fi, gashi nan ku kai ma baban naku." Murmushi suka yi gaba ɗaya, Fahad ya ce amman dai ta san zata haɗa rigima ne, tana dariya ta ce ai ta san zai samma su, Fahad ya ce ma Balaraba ta je ta kai basket ɗin wurin motar shi ta amsa mashi da to cikin ladabi duk da da gani ta girme mashi, sallama suka yi ma hajiya ta ce su gaishe mata da kowa. A motar Fahad da suka zo da ita suka fita, lokacin da suka fito wajen gate ɗin akwai wasu mutane a tsaye da alama Deen suke son gani ba a basu dama ba, "Mutanen nan fa baza su ƙyale ka ba, duk da ka faɗa masu baza ka samu ganin su ba ka ga still suna nan." Deen ya ce Allah ma ya sa basu san yana a motan ba ya san har biyo su suna iya yi, ya ce zai yi ƙoƙari ya samu isasshen time ya gan su. Bayan wasu mintuna suka ƙaraso gidan su Fahad dake a bakin babban titi wanda babban gida ne na gaske, karya kan motar Fahad ya yi ya tunkari tangamemen gate ɗin gidan, yana yin horn maigadi ya leƙo ta ƙaramar ƙofa, yana ganin motar da sauri ya koma ciki ya fara buɗe masu, ciki suka shige mai gadin na ɗaga ma motar hannu duk a tunanin shi Fahad ne kawai, bayan sun shiga cikin harabar gidan mai girman gaske kai tsaye katafaren ginin gidan motar ta tunkara basu nufi inda parking space yake ba, a bakin entryhall motan ta tsaya a tare suka fito, maigadi dake can bakin gate yana ganin sun fito su biyu ya ƙara ware ido a ranshi ya shiga ayyana ko dai tare suke da Deen, nufo su ya yi da ɗan sauri yana ƙara wara ido don ya tabbatar ma kan shi ko Deen ne, tun kafin ya ƙaraso ya gane shi ɗin ne saboda hasken dake akwai a wurin, washe baki ya shiga yi bayan ya iso ya shiga faɗin, "Barka da zuwa yalla6ai...barka da zuwa, dama sai da na yi tunanin ko kai ne wllh." Sam ya kasa rufe baki sai kace yaro ya tsinci haƙori, amsa mashi Deen ya yi ya ce mashi ya aiki, da sauri maigadin ya ce, "Aiki Alhamdulillahi gashi muna akan shi muna ta ƙoƙari. Yallabai ya naku aikin ai kaima gaskiya ba ƙaramin ƙoƙari kake ba wllh muna matuƙar yaba maka, da yake nima ɗan club ɗin ku ne duk wani wasa da zaku yi sai na kalla, da a wayata nake kallo lokacin ina da andiroyin kafin ta lalace in koma mai madannai, amman duk da haka duk idan za a yi ƙwallon ku akwai wani ɗan ƙauyen mu da ke anan shi nake sawa ya zo ya tsare gate ɗin in je gidan kallo in kalla. Wllh ai duk muna yin ka yalla6ai..." Sai faman washe baki yake kai ka ce wanda aka ma albishir da gidan aljanna, murmushi ne akan fuskan Deen ya yi mashi godiya, Fahad da ya fara gajiya da tsayuwa ya ce mashi an gode daga haka ya kama hannun Deen suka wuce, maigadin nata hargowa yana faɗin a fito lafiya yallabai, ɗan ɗaga mashi hannu Deen ya yi ya ce zai ganshi da sauri ya amsa mashi da to, nufar komawa bakin gate ya yi a ranshi yake ayyana ina ma wayan shi andiroyin bata lalace ba da sai ya roƙe shi sun yi hoto ya watsa a fesbuk, a yanzu ma ɗin ma alla alla yake ya je ya fara kiran abokansa da suke kallon ƙwallo tare ya yaɗa masu labarin zuwan shi, Tun a walkway ɗin shiga cikin gidan zaka fara shaida tsaruwar shi, har da wani haɗaɗɗan console mirror da manyan flower vases masu ɗauke da tafka tafkan fulawoyi, wani babban falo suka shigo mai ɗauke da light purple ɗin kujeru, komai na cikin falon kalar light purple ne wasu abubuwan an yi ratsin dark purple, hatta hasken fitulun cikin falon wasu na bada launin purple, a saman luntsuma luntsuman kujerun dake ciki wasu daga cikin ƴan gidan ne ke yin kallo, autar su Binafa ce ta shigo cikin falon zata nufi wurin da sauran suke, tana hango su Fahad da suka shigo ta nufi wurin su, tun kafin ta ƙarasa idanunta suka sauka akan Deen, cikin ƙaraji ta furta, "Laa, ga yaya Deen ɗin ball nan wllh!" Hakan ne ya jawo hankalin sauran kan su, da gudu Binafa ta nufi Deen ya wara mata hannu yana sakin faffaɗan murmushi, tana zuwa ya ca6e ta tare da ɗaga ta sama ta shiga ƙyalƙyata dariyar farin cikin ganin shi, Sadeeq ne ya rugo shima yana washe baki, Deen ya sauke Binafa shima ya ca6e shi ya ɗaga shi yana faɗin, "My man ka ƙara girma ka yi nauyi da yawa.." Duk suka yi dariya, Binafa ta ruga tana faɗin bari ta je ta faɗo ma momy ga ya Deen ɗin ball ya zo, bayan ya sauke Sadeeq kallon Khaleel dake tsaye yana ta sakin faffaɗan murmushi ya yi ya miƙa mashi hannu suka gaisa, cike da zolaya Khaleel ɗin ya ce shi ba za a ɗaga shi irin na su Sadeeq, Deen na murmushi ya ce, "Ai kai ka girma da yawa, kama kusa kamo ni tsawo." Duk suka yi dariya Khaleel ɗin ya yi mashi an zo lafiya ya amsa mashi, yayarsu Sadeeya wadda ita ce ke bima Fahad ta ƙaraso wurin tana sakin murmushi jikinta tana sanye da straight skirt da riga na atamfa, a yanayin halitta bata da tsawo sosai amman tana da diri kuma tana da kyawun fuska, akwai kamanceceniya sosai tsakaninta da Fahad duk da haskenta bai kai na Fahad ba, "What a surprise visit! You'are highly welcome my lil bru." Ta yi maganar tana miƙo mashi hannu alamar su gaisa, Deen na kama hannun ya murɗe shi ba arziƙi ta saki ƙara tare da duƙewa, cikin jin zafi ta furta, "Mi na yi maka kuma, daga abun arziƙi na yi welcoming naka." Yana murmushin ƙeta ba tare da ya saki hannun ba ya ce, "Who's ur lil bru?" Cikin nuna alamun jin zafi ta furta, "Ƙarya na yi to kai ba ƙanin nawa bane..." Bata ƙarasa ba ta ƙara sakin ƙara da ƙarfi sakamakon ƙara lanƙwasa hannun nata da ya yi, "Ahhh...kar fa ka karya mani hannu Deen, kasan dai wanda zan aura soldier ne zaka tsinci kan ka a guardroom wllh." Yana ƴar dariya ya ce tun da ita yayar shi ce ba sai ta ƙwace hannun ba, su Fahad dake tsaye suna ta murmushi, hajiya Amina ce ta shigo cikin falon tana tafiya a nutse irin ta manyan mata masu cikar kamala, tana da ƙwarjini sosai a fuska gata jajir da ita, doguwar riga ce a jikinta ta yafa mayafi a saman kanta daga gaban kanta kitson da aka yi ma baƙar sumarta ya ɗan fito, da murmushi akan fuskarta ta iso wurin, Sadeeya na ganinta ta ce, "Momy kin gani zai karya ma ɗiyar ki hannu ko, pls ki ce mashi ya sakar mani hannu." Dariya ta yi ta ce ita ba ruwanta dama ai sun saba kuma ta san ita ce ta ja shi. "Welcome my son." Ta faɗa da murmushi, ɗan rankwafar da kan shi ya yi ya gaishe da ita ta amsa tare da yi mashi an zo lafiya, "Pls ka sakar mani hannu wllh fa ina jin zafi." Yar harararta ya yi, ya ce, "Sai kin faɗa da bakin ki ni yayan ki ne." Tura baki ta yi ta ce, "To wai a ina ka zama yayan nawa ba na girme ka ba, ko don ka ga ka zama jibgege shine zaka fara yin runton shekaru." Ɗan girgiza kai momy ta yi jin yadda basu gajiya da yin musun shekaru duk in suka haɗu, "Bari in raba gardaman, rigima ne kawai naki Sadeeya amman kin san Deen ya girme ki, duk da ba wani nisa ne sosai tsakanin ku ba, ya baki shekara ɗaya." Dariya duk suka yi Deen ya ce mata small girl, tana dariya ta ce ta ji to ya sakar mata hannu, ƙin saki ya yi ya ce sai ta faɗa a gaban kowa shi yayanta ne, ƴar hararar shi ta yi aikuwa ya ƙara murɗe hannun ta saki ihu tana faɗin, "Don Allah Ya Deen ka yi haƙuri wllh zaka karya mani hannu fa." Gaba ɗaya suka saki dariya jin ta yada makaman nata ta kira shi da yaya, yarfe hannun ta shiga yi bayan ya saki tana faɗin kamar da hannun ƙarfe ya riƙe ta, "Wllh ya yi maki ma da sauƙi yaya Sadeeya, da ya kama ki sosai to sai kin yi acawi a jiki." Dariya duk suka yi jin kalaman Sadeeq, momy ta ce mutum ya zo sun ƙi bari ya shiga ya je ya zauna, kallon Deen ta yi ta ce, "Let's go in my son." nufar ciki suka yi duk suka zazzauna a saman kujeru, ƙara gaisawa suka yi da momy ta tambaye shi ya zo lafiya da kuma iyayensa na can, "Yaya Deen ai duk in kuna yin ƙwallo muna ganin ka." Binafa ce da ta maƙale a jikinsa ta faɗi hakan, ɗage mata gira ya yi ya tambaye ta da gaske, ta ɗaga mashi kai ta sake cewa, "Kuma ka iya sosai, idan ka ci ball sai mu yi ihu mu ce, 'A goalll..' har rawa muke yi, idan kuma baku ci ba sai bamu jin daɗi, mu yi ta tsoki har mu zagi waɗanda suka ci ku." Momy da ke zaune ta ce 'assha' duk suka yi dariya, ƙara rungume ta Deen ya yi ya ce mata ai haka wasa yake ba kowane lokaci nasara ke a wurin naku ba su daina damuwa. Hira suka ci gaba da yi Sadeeya ta iso wurin su tana riƙe da tray an ɗaura jug da glass cup a kai, a saman wani babban haɗaɗɗan center table na glass wanda ke bada launin purple ta ɗaura tray din, wani ƙarami ta ɗauko a can gefe ta aje daga gaban Deen ta sauko tray ɗin ta ɗaura sama, tsiyaya mashi lemun ta yi ta bashi tare da faɗin gashi don ba halin shi na mugunta ba, yana murmushi ya kar6a ya ce, "Thank you my lil sis." Ƴar hararar shi ta yi tana murmushi ta zauna a saman kujera, "Son, ka yi mana zuwan bazata, ban yi tunanin zamu gan ka yanzu ba, I thought sai ka ɗan kwana biyu a Abujan, gashi ba a shirya maka abu na musamman ba nasan ka yi missing food din nan. Koda yake ƙilan ai mom ɗinka na can na yi maku irin su." Ta ƙarasa da murmushi a kan fuskarta, amsa mata ya yi da ba komai ai sun ma jima da zuwa suna gidan hajiya, kallon Fahad ta yi ta ce miyasa bai kira ya sanar da zuwan su ba, dakatawa ya yi da latsa wayan da yake ya ɗan kalle ta ya ce ya manta bai yi tunanin hakan ba, "Akwai tuwo, kasan dad din naku ƙa'ida sai ya ci tuwo da dare, amman idan baka son shi sai Sadeeya ta yi preparing maka wani abincin." Momy ta faɗa da murmushi, ce mata ya yi lafiya lau yana son tuwon ya daɗe bai ci shi ba, "Yaya Deen a can ba a yin tuwo?" Binafa ta tambaya, kallonta ya yi ya bata amsa da mom Sapna na yi masu idan ya je gidan amman wani lokacin yana daɗewa bai samu zuwa ba idan sun tafi wasa, umarnin zubo mashi tuwon momy ta ba Sadeeya ta tafi, kafin ta dawo daddy ɗin su ya shigo cikin falon ya nufo inda suke, Alhaji Sa'ad mutum mai dattako da haiba yana sanye da riga da wando na brown ɗin shadda, da ganin kayan ƴan cikin babbar riga ne amman bai saka babban rigan ba, sannu da zuwa mutanen cikin falon suka shiga yi mashi yana amsawa yayin da ya nufi Deen da murmushi, miƙewa Deen ya yi yana gaishe da shi dad ɗin ya miƙa mashi hannu suka gaisa, "Mutan turai barka da zuwa, fatan ka zo lafiya" Amsawa ya yi da ɗan faffaɗan murmushi, daddy ya ce mashi ya zauna shima ya nufi kujera ya zauna, "To ya ƙasar taku, ya kuma tamolan. Ai ina ganin yadda ake ta ƙoƙari, Allah Ya ƙara taimako Ya kuma tsare." Gaba ɗaya suka amsa da Amin, Deen na murmushi ya ce, "Daddy ashe kana kallon ball." Dariya daddy ɗin ya yi, ya ce, "Can baya dai ina kalla amman sai na bari, yanzu kuma tun da yarona na yi ai dole in rinƙa kallo." Duk murmushi suka yi, Binafa ta ce, "Ai tare ma muke kalla, kasan mi yaya Deen?" Kai ya girgiza mata alamar a'a, ta ci gaba, "Idan muna kallon ball en ka ka ci sai daddy ya ce, 'goalll, that's my son, I'm very very proud of you Deen, ya yi ta jin daɗi yana dariya. Idan kuma kuka gama yin ball baku winning ba sai bai jin daɗi, fuskan shi ya yi haka, sai ya ce, 'dama wasa ya gaji haka sai haƙuri." Ta ƙarasa tana ƙyalƙyata dariyar kwaikwayon daddy ɗin nasu da ta yi, kowa dariya ya yi har da daddy ɗin, hannu ya kawo alamar zai kamo ta yana faɗin,"Zo nan ummina, wato kina nan kina karantar duk yadda nike yi ko, har na zama abun zolaya." Hayewa ta yi kujera ta lafe jikin Deen tana ta dariya, Sadeeya ce ta iso hannunta riƙe da tray mai ɗauke da kayan abinci, tambayar Deen ta yi ko ta kai mashi dining area ya ce eh ta juya, "Ba dai tuwo zaku ba mutamin turai ba, koda yake watakil ya daɗe ma bai ci shi ba, ƙilan ya ji dadin shi." Momy na murmushi ta ce haka ya ce ya daɗe bai ci shi ba, ce mata ya yi to shima akai mashi nashi can dining ɗin sai su ci tare da son don an daɗe basu ci abinci tare ba, sai lokacin Fahad ya tuna da saƙon da hajiya ta bada, kallon Khaleel ya yi ya ce mashi ya je motanshi a backseat akwai basket ya ɗauko, after few minutes ya dawo hannun shi riƙe da basket ɗin, Fahad ya kalli daddy ya ce mashi ga saƙo nan in ji hajiya, "Ni aka ce akawo ma saƙon?" Daddy ya tambaya idonsa akan basket ɗin Fahad ya ce mashi eh, gyara zama ya yi yana faɗin to bari ya ga saƙon miye hajiyan shi ta bada a kawo mashi, da sauri Binafa ta taso tana faɗin bari ta buɗe mashi, maƙe kafaɗa daddy ya yi ya ce shi zai buɗe abun shi, zama ta yi a kusa da shi yayin da ya duƙo yana kokarin buɗe warmers ɗin, yana buɗewa ƙamshin abun ciki ya dakar mashi hanci har sai da ya ɗan lumshe ido yana murmushi, waro ido Binafa ta yi tare da washe baki, Sadeeya da ta dawo falon ta matso tana faɗin bari ta ga miye aka kawo ma daddy din, "Ya Fahad anya baka yi kuskure ba bamu hajiya ta ce akawo mawa ba?" Sadeeya ta faɗa, ɗan murmushi ya yi ya ce na daddy ne, momy dake murmushi ta tambayi miye aka kawo ma daddyn? Binafa ta yi saurin cewa awara ne da chicken sauce, awaran daddy ya ɗauko guda ɗaya bayan ya dankwalo sauce ya kai baki, lumshe ido ya yi tare da furta, "Uwa mai daɗi. Allah Sarki hajiyana, Allah Ya ƙara maki lafiya da nisan kwana masu albarka." A tare duk suka amsa da Amin, rufe warmer ɗin ya yi ya fara kokarin miƙewa yana faɗin shi yama fasa cin tuwon bari ya je part ɗin shi ya ci abun da mamanshi ta aiko mashi, aikuwa da sauri Binafa ta riƙe basket ɗin tana faɗin to su fa, ɗaure mata fuska ya yi ya ce to su aka aiko ma da shi ne, suma idan suna so momynsu ta yi masu, "Wayyo daddy, amman ya za a ce ido guba." Sadeeya dake tsaye ta faɗa, miƙewa Khaleel da Sadeeq suka yi suma suka je suka zagaye daddyn abun gwanin ban dariya, "To wai ku ma ba tana aiko maku da abu ba ina saka maku ido ne, sai yanzu don nima an kawo mani zaku yi mani taron dangi. Ga momynku nan idan kuna so sai kuma ta baku kamar yadda nima momyna mai sona ta bani." Tura baki Binafa ta yi ta ce to ai dai suma hajiyan kakarsu ce ko, miƙa ma Sadeeya ya yi ya ce ta ba kowa tun da basu son ya ci ya ƙara ƙiba, amsar basket ɗin ta yi tana dariya ta ce, "Daddy dama ai kaza mai ƴa'ƴa bata maiƙo." Yana yar dariya ya ce kawai dai sun cika son kai. Kowa ya yaba da daɗin awaran bayan sun ci har da daddy ɗin ma, Deen da Fahad su basu ci ba cewa sukai sun ƙoshi sun ci a can gidan hajiya, Sadeeya ta ce gaskiya suma za su yi irinta gobe, momynsu ta ce to sai a kira hajiya a yi mata magana tun da dama idan suna son awaran daga can unguwarsu ake yo masu. Bayan sun gama cin awaran, gaba ɗayansu har da daddy da Deen suka wuce dining area don cin abincin dare dama duk basu ci ba, Binafa da Sadeeq dai cewa suka yi yadda suka ci awara mai daɗi baza su ci tuwo ba sai dai su haɗa cornflakes da madara su sha, momynsu ta ce su dai suka sani da gulma tuwon ma ai special tuwo ne. Bayan sun gama cin abincin Fahad ya wuce da Deen zuwa part ɗinsa dake a can saman bene...... *_✨A CIKIN RAYUWA✨_* ZAINAB BATURE _Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._ Page 16 Bayan sun isa part ɗin Fahad a falo suka zauna wanda madaidaicin falo ne mai ɗauke da kujeru leathers da kayan sauti da su hotunan family ɗin shi, yar hira suka ta6a kafin Fahad ya miƙe ya ce mashi bari ya je ya watsa ruwa ya rage kayan jikinsa, maida hankali Deen ya yi akan tv bayan ya kamo sport channel wato tashar dake haska wasanni, yana cikin kallon ya ji wayar shi na sanar da shi sweetheart na kira, ɗan jimm ya yi tare da lumshe idanunsa, ya san ko ya ɗaga ba lalle su kwashe ta ta daɗi ba shi da mahaifiyar tashi, sai bayan da kiran ya yanke sannan ya kai hannu ya ɗauki wayan a gefensa ya fara kokarin kiran ta, kamar jira ta ke wayan na fara yin ringing ta yi picking, "Ai da baka neme ni ba Deen a sannan zan san ka cika ɗa, wato rainin da ka yi mani har ya kai haka! Ka tsallake ka tafi ba tare da ka sanar mana ba a matsayin mu na iyayenka, da izinin wa ka tsallake ka bar garin nan? Wai yaushe ka canja ne haka Deen? Gaba ɗaya ka daina ganin girman mu, wani ya fi mu matsayi a gun ka da zai saka ka yi abun da kasan zai 6ata mana rai, alhalin shi ko da wasa ba zai ta6a aikata abu makamancin wannan ba ga na shi iyayen. Ina wayonka da tunaninka suka tafi Nuraddeen!" Shiru ya yi tare da ɗan cize leben shi na ƙasa, daga yadda ta kira ainihin sunan shi ya fahimci ba ƙaramin harzuƙa ta yi ba don ba zai iya tuna when last da ta kira sunan shi haka ba. Sigh ya yi calmly ya ce, "I am sorry mom, ni ban yi haka don in 6ata maku rai ba, ki daina tunanin wai na canza ko na raina ku bana fatan hakan ya kasance, kuma ki daina zargin yaya Fahad ne ya sa na zo nan ba ruwansa ra'ayin kai na ne..." "Ka ce ra'ayin kan ka ne Deen? Ra'ayin ka ne ka 6ata mana sannan ka ce wai in daina cewa ka canza?" Ta faɗa bayan ta katse shi, "Ki yi hakuri idan haka da na ce baki ji daɗi ba, ina so ne in fahimtar da ke yaya Fahad bashi da hannu a tahowana nan, shi bai ma goyi baya ba da na ce zan zo nan, a tunaninsa zan bari sai na huta, ni ne na ga is better in taho nan..." Shiru ta ɗan yi da alama nazarin abun da ya faɗa take, kafin ta ce, "Har nan ya fi maka ke nan a kan gidan iyayen ka, haka kake nufi Deen?" Juyar da kan shi ya ɗan yi yana riƙe da wayan a kunnan shi, "Mom I won't hide it from you, bana jin daɗin yadda abubuwa suke faruwa, na daɗe ban zo ba I thought zan samu complete happiness amman sai na ga ba haka ba. Yaya Fahad brother nane, yadda kuke farin cikin zuwa na shima haka ne, shiyasa ya zo wuri na ba wani abu ba amman hakan ya zama abun tashin hankali.." Shiru ya yi bai ƙarasa ba, daga yanayin voice ɗin shi ta tabbatar da gaske ne abun da ya faɗa, yar ajiyar zuciya ta sauke cikin ƙoƙarin daidaita natsuwarta tare da kwantar da murya ta ce mashi shike nan ya yi haƙuri ba zata ƙara yin abun da zai 6ata mashi rai ba. ta ce, "Yanzu yaushe zaka dawo nan don muna son ka a kusa da mu saboda mun yi missing naka sosai." Ɗan murmushi ya yi ya ji daɗin yadda ta yi mashi magana, amsa ya bata da zai ɗan kwana biyu anan saboda yana shirin buɗe club ɗin shi. "To yaushe zaka je can Kano wurin su Ammin suma?" Shiru ya ɗan yi, ba wai bai son zuwa wurin na su ba, kawai akwai abubuwan da suke mashi da baya jin daɗin su bama a zahiri ba ta waya ma, yasan idan ya ce ba zai je ba hakan zai zama wani issue hakan yasa shi ce mata zai je kafin ya koma tun da zai yi 2 weeks kafin ya tafi gaba ɗaya, ta amsa mashi da ok. "Have u called Basma?" Ta tambaya, ɗan jimm ya yi yana shakkar amsar da zai bata don shi yama manta da Basmar balle ya neme ta, sai ɗazun da yamma a gidan hajiya da ya ga missed calls nata bayan ya fito daga wanka kuma bai bi kiran ba. "Nah, I wanted to be well settled sai mu yi magana da ita sosai." Amsa mashi ta yi da ok kafin ta ce mashi yanzu sai yaushe za su yi expecting nashi, ya bata amsa da zai yi kaman kwana biyar sai ya dawo, ta ce mashi to ko kawai ya wuce Kano daga nan ma, ya ce mata dole sai ya dawo nan tun da bada mota ya taho ba kuma yana son zai bi jirgi ne zuwa Kanon, saida ta jaddada mashi game da ya kira Basma sannan suka yi sallama. Bayan sun gama wayan shiru ya yi tare da ɗan lumshe idonsa, yana haka Fahad ya fito ya shirya da brown din jallabiya mai gajeran hannu, a kusa da Deen ya zauna yana kallon shi ya kira sunan shi, slowly ya buɗe idon shi tare da kallon shi, gyara zaman shi ya yi ya ce ya fito Fahad ya amsa mashi da eh yana bin fuskarsa da kallo, "Is everything alright?" Cike da kulawa Fahad ya tambaya, ɗan yamutsa fuska Deen ya yi ya ce, "Mun gama magana da mom ne ta yi faɗa akan na taho ban sanar masu ba, amman ba wani abu." Ya ƙarasa with a smile on his face, shiru Fahad ya ɗan yi yana kallon shi kaman yana nazarin wani abu, sigh ya yi ya furta, "I guess ta yi maka magana akan yarinyan da zaka aura?" Juyowa Deen ya yi ya kalle shi tare da yin dariyarsa mai tsada ya furta, "You guess right. Amman ya akai kasan ta yi mani maganan?" Dan ta6e baki Fahad ya yi yana gyara zaman shi ya ce, "Yakamata ta yi maka maganan ne, ina lura da kai tun a Abuja baka yi waya da ita ba, ɗazun a gidan hajiya ta kira ka lokacin kana bathroom and I thought you will call her back da ka fito sai baka yi hakan ba, nasan dole ta kai ƙarar ka." Dan murmushin gefe Deen ya yi ya kai hannu ya shafi sumar shi. "Na kasa in saba da ita ne a matsayin wadda nike dating, still ina mata kallon sis dina ne." Gyara zama Fahad ya yi tare da cewa yakamata ya saba da hakan, remote Deen ya ɗauko ya sake canza wata sport channel kuma cikin sa'a ɗaya daga cikin wasannin su ne da suka buga a kakar wasanni da ta wuce ake sake nunawa, bayan wani lokaci Deen ya duba agogon hannunsa ya ce ma Fahad bari ya zo ya tafi yana son ya kwanta da wuri don ya huta sosai, kallon shi Fahad ya yi ya ce mashi ya kwana a nan mana, "Ba zaka je aiki gobe ba?" Deen ya tambaya, amsa ya bashi da zai je amman ai gidan ba baƙon shi bane da zai ce sai yana nan zai zauna, murmushi kawai ya yi Fahad ya kai hannu ya ɗauki wayan shi da ya ajiye a gefe ya ce bari ya sanar ma hajiya anan zai kwana kada ta yi ta jira Deen ya furta ok, bayan Fahad ya gama yin wayan ya ce ma Deen ya je ya yi wanka don ya kwanta ya huta, miƙewa ya yi ya nufi bedroom Fahad ya ɗan ɗaga murya yana ce mashi idan ya gama sai ya ɗauki kayan bacci cikin closet ya ɗaga mashi kai. Wayar Fahad ce ta fara yin ringing ya kai duban shi kan screen ɗin ta, mom dinsa ce ya ga tana kira ya ɗauka, tambayar shi ta yi amman anan Deen zai kwana ko ya amsa mata da eh, ta ce ya tambaye shi ko yana buƙatar tea ko coffee ta san turawa da sabo da shan su da dare, murmushi ya yi ya sanar mata ya shiga wanka sai ya fito zai tambaye shi ta amsa da ok. After some minutes Deen ya fito jikinsa sanye da bathrobe, shiryawa ya yi ya saka kayan bacci riga mara hannuwa da wandonta iya gwiwa, yana cikin gyara sumar shi ya ji wayar shi na sanar mashi da ana kira tare da sunan mai kiran wato Basma, sai bayan da ya gama abun da yake yi sannan ya nufi inda wayan take, zama ya yi a bakin gadon ya ɗauki wayan lokacin tuni kiran ma ya tsinke, ya san ko ya kira ta cewa za ta yi su yi vedio call don ta fi son hakan duk za su yi waya, komawa ya yi ɗayan 6angaren gadon ya ɗan kishingiɗa tare da jingina bayansa da kan gadon, vedio call ya shiga kiran ta yana shiga ta ɗauka, lokacin da ya yi arba da ita har sai da ya ɗan kauda idonsa gefe, ita dai tana son saka fingilallun kaya, har magana sai da ya ta6a yi mata can baya kan irin shigan da take yi idan yana a gida, lokacin sai ta nuna wai miye ai shi yayanta ne, ya yi ƙoƙarin fahimtar da ita duk da haka bai kamata tana saka kowane irin kaya ba saboda shi ba muharraminta bane amman ta ƙi ta bari. Bayan da maganar aure ta shiga tsakanin su sai ma abun da ya ci gaba, bata jin komai ta saka kowani irin kaya, wani lokacin idan ya je gidansu har sai ya nuna mata 6acin ran shi sannan take canza kaya, duk da wasu kayan ko ta canza duk uwar ɗarin ce amman dai wasu da ɗan dama. Itama a kishingiɗe take tana sanye da wata vest kalar ruwan ƙasa da ko rufe mata mara bata ƙarasa yi ba, da wando casual short, irin ɗan guntun wandon jeans da iyakarsa tsakiyar cinyoyi, a kunnanta ta saka manyan zagayayyun ƴan'kunne dake da stones masu sakin ƙyalli, ɗayan hujen kunnan da take da ta saka ɗan kunne barima. Shiru ta yi tana kallon shi tare da ɗan kikkafta idanunta dake ɗauke da dogon gashin ido masu gazar-gazar, Ɗan murmushi ne akan fuskar Deen ganin kallon da take bin shi da shi irin na kana tuhumar mutum da laifi, "Basma, How are you doing?" Ɗan kauda ido ta yi, sam bata jin daɗin yadda ya ƙi daina kiranta da sunanta ya rinƙa kiran ta da sunan da ke nuna akwai soyayya a tsakanin su, maido idonta ta yi suka shiga cikin na shi, "Do you even care how I’m doing?" Ta tambaya da ɗan yanayin fushi, yadda ta yi maganar cikin salo da sarrafa labbanta, still murmushin ne akan fuskarsa yana kallon ta ba tare da ya ce komai ba, "Now that you are settled after arriving at your destination yesterday, i thought you would want to catch up on how I’m doing. It feels like I’m not a priority." Ta faɗa da London accent, Shafa sumar kansa ya yi ya ce, "Don't think that way, I'm not fully settled yet. Na daɗe ban ziyarci nan ba, and you know my career as a footballer keeps me busy with so many things." Har ta ji sanyi a ranta hakan da ya faɗa, shiru ta yi tana jefa mashi kallo mai cike da so da ƙauna, "Ya dad da mom?" Amsa mashi ta yi da suna lafiya, ta tambayi suma bai tuntu6e su bane tun da ya bar nan? ya bata amsa da sun yi magana, "Ni ce baka samu lokacin ka yi magana da ni ba?" Ta yi maganar tana mashi kallon tuhuma, da ɗan murmushi kan fuskarsa ya ce mata no ba haka bane ya bari ya samu isasshen lokaci ne da za su yi magana, su dad kawai sun gaisa ne, har ta ji daɗi daga murmushin da ta yi. "Ya hutun ka? Are u enjoying it?" Kai ya jinjina mata alamar yana jin daɗin hutun, ta ce, "Mom ta faɗa man kana garin su dad, ta ya za ka ji daɗin hutu a nan ƙauyen?" Murmushin gefe ya yi, ya bata amsa da ai sai ya fi jin daɗin hutu a nan tun da bai saba da irin wurin ba sosai, ta6e baki ta yi kafin ta tambayi yaushe zai koma ya faɗa mata, "Ba don bana son zuwa 9ja ba da zan biyo ka ne, ko da ba a yi hutun skul ba." Ta faɗa tana kanne mashi ido, tambayar ta ya yi saboda mi ba ta son zuwa? "Kawai bana jin daɗin zama a country ɗin." Ɗan jinjina kai ya yi, ya ce "Yakamata kuwa ki koyi jin daɗin zama tun da kaman ƙasar ki ce, parents ɗin ki nan ne asalin su." Ta6e baki ta yi ba tare da ta ce komai ba. Magana suka ci gaba da yi, yawanci duk ita ce ke yin maganar ya bata amsa, jin alamar an shigo ya sa shi kallon wurin kofar ɗakin, Fahad ne ya shigo ganin waya a hannun shi ya dakata daga bakin ƙofar tare da tambayar shi yana waya ne Deen ya ɗaga mashi kai alamar eh, amsa masa ya yi da ok bari ya gama, "Da wani abu ne?" Har zai juya ya ji Deen ya tambaya, dakatawa ya yi ya ce mashi dama mom ce ta ce a tambaye shi ko yana buƙatan wani abu na ci ko sha, ɗan murmushi ya yi ya bashi amsa da no ai sun ci abinci. "Ba ka buƙatan tea ko coffee? Ta ce ta san ku turawa kun yi sabo da shan su kafin ku yi bacci." Ɗan faffaɗan murmushi Deen din ya yi ya ce kamar kuwa ta sani ya yi sabo da shan coffee kafin ya kwanta, amma ba sai sun wahalan da kan su ba, Fahad ya ce to miye abun wahala ko Sadeeya sai ta haɗa mashi, "Ba kana kan waya bane?" Fahad ya tambaya, Deen ya ce, "Yea, Basma ce." "Ka ce kai da amarya ne ake shan luv na zo na katse ku." Wani kallo Deen ya yi mashi wanda nan take Fahad ɗin ya fahimci mi kallon ke nufi, ɗan murmushi Fahad ya yi tare da juyawa ya fice, tambayar shi Basma ta yi waye suke magana bayan ya maida fuskarsa kan screen ɗin wayan ya bata amsa Fahad ne, da yake ta san Fahad ɗin ta ce yana ina su gaisa, wani kallon baki da hankali ya jefa mata ganin da irin shigar da ke jikinta take cewa za ta gaisa da wani, ya san a wurin ta hakan ba wani abu bane, amman koda ba wani jin ta yake a ransa ba nan da ɗan lokaci za ta zama iyalinsa dole ya yi kishin a gan ta haka, amsa ya bata da Fahad ya fita ta amsa da ok, ƴar hira suka ƙara yi kaɗan ya ce mata yana son ya kwanta ya huta sai sun ƙara yin magana, ba don ta so su gama yin wayar ba a lokacin, ta ce sai yaushe za su ƙara yin magana ta san sai bayan wasu kwanakin kuma, gudun jan maganar ya sa shi ce mata da ya samu lokaci zai kira ta, ta amsa da tana jira idan kuma ta ji shiru ita za ta neme shi dama ta fi damuwa da shi, murmushi kawai ya yi ya ce mata good night, "Just gud night? Ta tambaya ta dan ƙanƙance ido, gaba ɗaya ya ƙosa da wayan ya san idan bai yi mata yadda take so ba ba za a gama wayan ba, ya sake ce mata, "Gud night. I luv u." Murmushi mai fadi ta yi ta farfara mashi ido itama ta ce mashi, "Luv u more honeypie. Gud nyt and dream of me." Ta faɗa cike da salo da kisisina, lumshe ido ya yi tare da ɗan ɗaga mata kai daga haka ya kashe, wurgar da wayan ya yi gefe ya ɗage kan shi a jikin gado tare da rufe idanunsa kamar mai yin tunani, turo kofar ɗakin aka yi Fahad ya shigo hannuwansa ruƙe da kofuna tiriri na fitowa, sauke kai Deen ya yi yana kallon shi ya ƙaraso bakin gadon tare da miƙa mashi kofi ɗaya, "Thank u mah friend." Deen ya faɗa yana murmushi bayan ya amshi mug ɗin, a gefen shi bakin gadon ya zauna yana rike da ɗayan kofin, tambayar shi ya yi har ya gama shan luv din, Deen ya yi faffaɗan murmushi tare da shafar sumar gemunsa, a tare suka fara sipping coffee din, Deen ya ɗan dakata yana tambayar Fahad shima yana shan coffee ke nan da daddare, "No, jefi-jefi. Na fi shan black tea." Wayar Fahad ce ta fara ruri ya kai idonsa kan ta, ɗan murmushi ne ya bayyana akan fuskarsa ganin mai kiran nasa wato Leemarh, a saman bedside drawer ya ɗaura kofin coffee din, ɗaukar kiran ya yi ya kara a kunne a nutse ya furta bari ya kira ta, katse kiran ya yi ya sake kira, jin ta yi shiru bayan ta yi picking ya ce, "Sis Leemarh..." Ciki-ciki ya ji ta amsa, murmushi mai ɗan faɗi ya yi don ya fahimci dalilin amsa masa hakan da tayi, "Hope kuna lafiya?" Ya tambaya, yadda ta amsa da ya kira sunan ta yanzu ma haka ta ba shi amsa da eh, "Tell me, ya aka yi ne na ji muryan ki haka?" Ya tambaya still da murmushi akan fuskarsa, kamar ba za ta yi magana ba sai kuma ya ji ta fara cewa, "Ba kai bane..." Hannu ya kai ya shafi sajen shi ya ce, "Uhuym, ina ji mi na yi?" "Ai ka sani...shi ne zaka tafi without saying goodbye." "Eyya, I am sorry for dat idan baki ji daɗi ba. Amman ai dama kin san ba da shirin kwana na zo ba, kuma ke ce kika roƙi in tsaya in kwana, dama ba zan wuce yau ba." "Na sani, amman sai kawai ka tafi ba za ka bari mu tashi mu yi bankwana ba." Murmushi ne bayyane akan fuskarsa. "Ok na amshi laifi na, ina son zuwa wurin aiki ne shi ya sa muka taho da wuri." "To yaushe za ka ƙara zuwa?" Shafa sumar kan shi ya yi, "Sai wani lokacin kuma." Da sigar shagwa6a ta ce ita dai ya faɗa mata lokacin da zai ƙara zuwa, faffaɗan murmushi ne akan fuskarsa ya ce mata da a ce Deen na nan Abuja ne to sai ya ƙara zuwa wurin shi, amman yanzu suna tare. "Shike nan, ni idan aka yi mana hutu zan zo nan." A cikin ransa ya ayyana Allah Ya sa wannan mom ɗin taku ta amince, a fili ya ce hakan ya yi za su jira ta, tambayar shi ta yi zai ji daɗin zuwan nata? ya bata amsa da sosai ma ya san kowa ma gidan zai yi farin cikin zuwanta, "What are you doing now? Ko kana chat da girlfriend ɗin ka?" Murmushi mai ɗan sauti ya saki jin tambayar da ta yi mashi, ya ce, "Ga ni tare da Deen muna shan coffee. Ni bani da girlfriend ai" Tambayar shi ta yi da gaske? ya bata amsa "yea," "To yaushe zaka yi?" Still d murmushi ya bata amsa da sai ya shirya yin aure sannan don bai son wasting time din shi da na wata, ƴar hira suka ƙara yi kaɗan ta ce bari ta bar shi ya sha coffee ɗinsa suka yi sallama. Haɗa ido suka yi da Deen dake sipping coffee a natse, ɗage mashi gira ya yi ya ce, "An gama luv en?" Ƴar dariya Fahad ya yi don ya gane tsokanar da ya yi mashi ɗazun ce shima ya rama, ɗaukar coffee ɗin shi ya yi tare da bashi amsar cewa ai ya faɗa mashi ba soyayya suke da Leemarh ba, kawai sun shaƙu da juna ne, miƙewa Deen ya yi yana faɗin in ma da abun da suke 6oyewa ai lokaci zai bayyana ya wuce toilet don ya wanke baki, lokacin da ya fito Fahad ya gama shan coffee ɗin, "Ina zaka je ne?" Fahad ya tambaya ganin ya miƙe da kofunan da suka gama shan coffee, ya ba shi amsa da zai fita da mugs ɗin ne, dakatar da shi ya yi ya ce ya bari Sadeeya zata zo ta ɗauka...... *_✨A CIKIN RAYUWA✨_* _New story from the writer of 'A Sanadin Makwabtaka',_ ZAINAB BATURE 17 Washe gari da wuri Fahad ya wuce wurin aiki, misalin ƙarfe sha ɗaya da rabi Deen ya saukko ƙasa ya shirya cikin t-shirt da wando jeans sai faman baza kamshi ya ke, yadda rigar ta ɗan kama shi ta bayyana ƙirar ƙirjinsa dake a bude, yana ƙarasa saukowa suka haɗu da momy ɗin su Fahad da ta nufo hanyar benen, da murmushi ta furta, "Good morning my son." Shima murmushin ne akan fuskarsa ya ce, "Morning Momy..." "Hope you slept well?" Ya bata amsa da, "Yea, Alhamdulillah." ta sake cewa, "Ai da yanzu nike niyyar zuwa in taso ka ka yi breakfast kada yunwa ta kama mana baƙon turai, duk da na san dama ba lalle kana yin breakfast da wuri ba, kai ya ɗaga yana murmushi ya ce mata ba da safiya sosai yake cin abinci ba sai dai idan zai je wani wuri, jinjina kai ta yi tare da yi mashi nuni da dining area ta ce an shirya mashi table bari ta turo Sadeeya sai ta yi serving nashi, ya yi mata godiya ta wuce. Ba da jimawa ba Sadeeya ta shigo cikin falon tana sanye da ƙananun kaya riga da skirt kanta ta saka hula, wurin Deen dake zaune saman kujera yana latsa waya ta nufa, "Good morning bru." Ɗago fararen idanunsa ya yi tare da sakar mata murmushi, ya ce, "Morning my lil sis.." Ƴar harararsa ta yi ya ɗage gira ya ce ko tana da ja kan hakan, da sauri tana girgiza masa hannu ta ce, "Ni dai ai baka ji na ce wani abu ba ko, balle ka ji daɗin yi mini mugunta dama ga shi daga ni sai kai a cikin falon." Ƴar dariya ya yi ba tare da ya ce wani abu ba, ta ce mashi su je ya ci abinci ya miƙe suka nufi dining area. "Ina Basma budurwarka ko in ce wife to be ɗin ka?" Sai da ya cinye abincin bakinsa ya bata amsa da tana can tana lafiya, Sadeeya ta sake cewa, "Yaushe ne za mu sha bikin to? Amman dai a nan za a yi shagalin bikin ko?" Amsa ya bata da sai ta ƙarasa gama karatu yanzu tana a year 2, ta ce, "To ba kawai sai a yi bikin ba sai ta ci gaba da karatun a gidan ka" Ɗan murmushi kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba ya kai chips ɗin da ya ɗebo da fork baki, shiru Sadeeya ta yi tana zaune a saman ɗaya daga cikin kujerun wurin, a kaikaice ta ke satar kallon Deen ɗin a cikin ranta tana raya sam Deen bai dace da auran yarinyar ba, a yadda yake tubarkalla kamata ya yi ya auri mace da ta amsan sunan mace, ita fa a da ma tana crushing nasa da ta ji cewa yarinyar zai aura ta cire shi a ranta dama ba wanda ya san da hakan, tana cikin kallonsa ba tare da ta ankare ba ya ɗago idanunsa suka haɗa ido, da sauri ta wayance ta shiga yin ƴar dariya ta ce haka ya iya loma ashe shiyasa ya koma jibgege tubarkalla, murmushin gefen baki ya yi ba tare da ya kawo komai ba a ransa ya ce dama dalilin da ya sa ta zauna ke nan don ta yi masa kallon ƙurulla, sipping tea ya yi bayan ya shanye ya kalle ta ya ce, "Ya baki je school ba, or have you already graduated?” Amsa mashi ta yi da a'a tana dai a final year sun samu hutu ne, ya ce, "Sai aure ke nan idan kika gama?" Ɗan juyawa ta yi gefe ta juyo ta jinjina mashi kai alamar eh tare da kanne masa ido, dariya ya yi har haƙoransa suka ɗan bayyana ya ce, "So you're very eager to get married right?" Ɗage masa gira ta yi tana dariya, ya dan girgiza kai kafin ya sake cewa, "Wannan soldier ɗin da kika turo mani picture na shi da shi za a yi auren, miye ma sunan shi?" "Captain Junaid.." Ta bashi amsa, ya ce Allah Ya nuna masu ta amsa da Amin, ɗaga fork ɗin hannunsa ya yi kaman zai jeho mata ya ce ita bata da kunya ne, ta duƙe tana dariya ta ce shi ne za ta ji ma wani kunya. Bayan ya kammala yin breakfast ɗin ya ce ma Sadeeya yana son zuwa gidan hajiya ko akwai motan da zai yi amfani da shi, ta bashi amsa da akwai ya ce ok, kafin ya sake tambayarta dad na nan ya je su gaisa ta ce mashi eh, tare da ita suka nufi bangaren dad, bayan sun gaisa ne Sadeeya ta yi mashi maganar Deen yana son motan da zai je gidan hajiya, dad ya ce mashi ba zai jira zuwa anjima ba idan suka yi sallan juma'a sai ya tafi, Deen ya amsa mashi da to sai kuma dad ɗin ya ƙara cewa ko da yake ya san ba lalle zaman gidan ya yi masa daɗi ba tun da abokin nashi baya nan, makullin mota ya bashi Deen ya yi masa godiya, lokacin da zai miƙe har dad ɗin na tambayar wai zai iya tuƙin saboda titunan nan ba kamar na can ƙasar su ba, da murmushi ya ce masa eh lafiya lau ko jiya ma shi ya kawo su nan daga Zaria, dad ya yaba masa kan hakan duba da yana daɗewa bai yi tuƙi a nan ba. Bayan sun dawo cikin falon ya je ya yi ma mom sallama suka fito tare da Sadeeya ta rako shi har bakin mota ta ce ya gaishe mata da hajiya tana nan zuwa within the weekend yanzu don za su yi online group discussion da ta bi shi, tana tsaye har ya ja motar cikin ɗaga murya take faɗin, "Ka kula sosai my lil bru." Ya sakar mata horn tana dariya ta juyo ciki. Hajiya zaune a falo ta yi gayun juma'a tana sanye da doguwar rigar shadda ruwan toka da aka yi ma aiki mai kyau, falon ma ya sha gyara sai ƙamshi ke tashi, jin sallama ya sa ta kai idanunta kan ƙofa, ganin Deen ta saki murmushi ya nufo ciki a nutse, a gefen ta saman kujera mai mazaunin mutum biyu da take kai ya zauna yana murmushi ya gaishe da ita ta amsa, ta ce, "Ai ban yi zaton ganin ka ba yanzu, na yi tunanin sai zuwa bayan sallan juma'a." Kwantar da kansa ya yi jikin kujera ya ce mata haka nan ya taho ya zo ya ganta." Murmushin jin daɗin maganar ta yi ta ce to ta gode ga ta ya gan ta, tambayar ta tashi lafiya ya yi ta amsa mashi da lafiya lau Alhamdulillah, tare da tambayar suma sun tashi lafiya ko, "Ya iyayen naka da ƴan'uwanka duk suna lafiya?" Ya bata amsa da lafiya lau, hajiya ta ce, "Sai suka ga ka yi masu zuwan bazata." Ya ɗaga mata kai yana murmushi ya ce sun ji daɗin ganinsa sosai, hajiya ta jinjina kai tana murmushi. "Za ka ci abinci a shirya maka ne?" Kai ya girgiza ya ce mata bai daɗe da ya yi breakfast ba sai dai zuwa anjima ta amsa da to, ya faɗi mata saƙon gaisuwar Sadeeya. "Ai jiya da daddare ta kira ni suna son awara, na ma isar da saƙon nasu wurin mai yi, na san zuwa yanzu ma ƙilan ta kusa gama masu." Labarin yadda aka ci awaran jiya ya bata tana dariya ta ce, "Ahaf, dama ni na san sai an yi rikici kan awaran in dai suka gani, dama ita haka take abun marmari ce, ai gata nan za a yi masu har ta tiya ɗaya sai su ci su ƙoshi. Fahad yana wurin aiki ne?" Amsa ya bata da eh ta ɗaga kai, kafin ta sake cewa, "Ko kana son awaran a sake yi maka?" Hannu ya kai ya shafo sumar kansa da murmushi ya ce idan akwai yana so ya ji daɗin shi da ya ci ta jinjina kai, bayan ɗan lokaci ya miƙe ya ce zai shiga ciki, har ya fara tafiya ta dakatar da shi ta hanyar sanar da shi cewa ta saka an gyara mashi part ɗin shi na can 6angaren su ko zai yi amfani da shi, ya yi mata godiya kafin ya wuce, wayarta ta ɗauka ta kira layin Innar su Salma, bayan sun gaisa cikin girmamawa innar ta ce mata ai ga aikin awaran nan ana gaf da gamawa, hajiya ta ce to in an gama za su aiko daga can gidan a amsar masu, kafin ta sake cewa dama tana son wata ta rabin tiya ne idan za a samu, baƙonta ya ji daɗin ta jiya shi ne za a ƙara yi mashi, cikin fara'a Innar ta ce mata eh lafiya lau za a samu dama da ta sauke wannan za ta ɗaura wata, hajiya ta ce to shike nan ba sauri take ba ko zuwa yamma ne idan an gama a ba Salma ta kawo, ta amsa mata da to suka yi sallama. Misalin ƙarfe ɗaya Fahad ya zo nan gidan hajiya dawowarsa ke nan daga aiki ya ɗauki Deen suka koma gidan su don su je sallar juma'a, bayan sun je Fahad ya ba Deen kayan da zai shirya wanda sabbabi ne a cikin leda ta brand din kayan, bayan ya saka kayan wanda shadda ce sky blue riga da wando da aka yi masu aiki kalan na ƴan gayu, tubarkallah sosai kayan suka amshe shi, shi ma Deen ɗin murmushi ya shiga saki yayin da yake kallon kan sa a madubi bayan ya gama saka kayan, shi ma Fahad shiryawa ya yi cikin shadda ruwan toka irin ɗinkin ɗaya da na Deen suma kayan sababbi ne tare ya siyo masu. "Kayan ya yi kyau sosai." Deen ya faɗa yana gyara zaman hular da ya saka wadda take mahaɗin kayan ce itama sabuwa ce sai salƙi take, "When last ka saka kaya irin wannan?" Fahad ya tambaya yana ɗaura agogo a hannunsa, amsa Deen ya bashi da ba zai iya tunawa ba don an daɗe rabon da ya saka manyan kaya. Bayan sun gama shiryawa suka nufi ƙasa sai baza uban ƙamshi suke, idan ka gan su sun fito a zaratan samari tamkar ka sace su. "Wow, ma sha Allah, ƙanina wannan wanka haka!" Sadeeya dake zaune cikin falo ta yi gayun juma'a da jan lace ta faɗa tana nufo su, "Yaya Deen ka yi kyau sosai!" Binafa ta faɗa tana washe baki, tambayarta ya yi da gaske ya yi kyau ta ce eh wllh, hannun Ayden ya kamo yana masa murmushi don jiya da ya zo basu haɗu ba ya yi bacci, yana ta kallon Deen ɗin don bai saba da shi ba sosai. "Tubarkallah ma sha Allah, son ka ƙara matuƙar kyau cikin kayan nan." Mom ɗinsu Fahad ce ta yi maganar yayin da take nufo inda suke tana sanye da doguwar rigar shadda ta yi ɗauri mai kyau, godiya ya yi mata yana murmushi, haka sauran mazan da duk suma sun yi gayun juma'a duk suka yaba gayun Deen, dad ne ya shigo cikin falon ya sha manyan kayan farar shadda, nufo su ya yi yana tambayar su Sadeeq duk sun shirya ko don sun kusa makara, yana ganin Deen ya yi faffaɗan murmushi tare da faɗin, "Ma sha Allah yarona, kayan nan sun matuƙar amsar ka. A can ma kana saka kaya irin wannan?" Amsa ya ba dad ɗin da yana da su amman yana daɗewa bai saka ba wannan ma Fahad ne ya kawo masa, "Amma gaskiya sun yi maka kyau sosai, yakamata kana saka irin su ko a can don za ka burge mutane sosai." Godiya ya yi ma dad ya ce zai rinƙa sakawa in sha Allah, hoto Sadeeya ta ɗauke shi tana faɗin dole ta watsa wankan nan daga haka suka tafi masallaci. Zaune take a saman tabarma cikin baranda tana cin abinci, bata daɗe da dawowa daga makaranta ba ta yi wanka tana sanye da riga da skirt na atamfa, daga gefen ta su Imrana ne suma suna cin abincin su basu daɗe da dawowa daga sallar juma'a ba duk suna sanye da yadi mai kyau kala ɗaya, daga can saman tudun baranda yayansu Auwalu ne zaune shima yana cin abincin yana latsa waya, "Ina zaka je?" Innar su ta ɗaga kai tana tambayar Sagir da ya shigo gidan ya nufi hanyar kicin yana sanye da wandon yadi ya cire rigar sai farar singlet. "Zan ɗan ƙaro abincin ne ban ƙoshi ba ni da su Aliyu muka ci." "To ina ruwan wani da tare kuka ci, kowa kason shi aka zuba masa, saboda ma an san kafi kowa ci wanda aka zuba maka ya fi na kowa yawa kuma shine zaka zo ka kwashe sauran..." Salma bata ƙarasa ba ya nufo ta zai ƙwala mata cokali yana faɗin, "Ke wai uban mi yasa kika raina ni ne..." Da sauri ta 6oye a jikin innarsu, "Sagir kada ka sake ka buge ta, ai gaskiya ta faɗa, abincin da aka zuba maka ya fi na kowa, ba a hana ka ci da wasu ba, amman kuma ba zancen ka zo kai ta kwashe ma mutane abinci, idan kuma ya ƙare aka yi tuwo da daddare ka fi kowa yin tsegumin za a kashe ku da tuwo." Innar su ta faɗa da ɗan ɗaure fuska, ya ce, "Innarmu kaɗan zan ɗan ƙaro." Ya faɗa ya na nufar kicin, "Kai dai ka sani, abinci dai har dare aka yi shi, idan ka kwashe ka nemi abun da zaka ci da dare, don ba wani abincin da za a ƙara dafawa." Bayan ya zubo abincin innarsu ta ce ya kawo ta gani, ya tsaya ɗan nesa da ita ya ɗan karkato mata da kulan yadda ba za ta gani ba sosai, "Kam! wllh innarmu cuko ta ya yi." Imran ya faɗa, da sauri Sagir ɗin ya fice yana dariya innar ta ce za su haɗe da dare ne. "Allah wanda ya rage mu za a zuba mawa da daddare ban da shi." Imrana ya faɗa yana tura abinci baki, "Su Imrana mala'ikun tauna..." Salma ta faɗa tana dariya. "Habu shigo mana ya zaka lafe a nan." Gaba ɗayan su suka kai idanuwansu kan ƙofa jin maganar da innarsu ta yi, lokaci guda Imrana da Hamza suka ɗaure fuska ganin wanda aka kira da suna Habu, "Shigo mana mutumina." Salma ta faɗa tana masa murmushi, nufo ciki ya yi yana tafiya kamar mai jin tsoron shiga, yaro ne da ba zai wuce shekara bakwai ba, jikinsa yana sanye da wani koɗaɗɗan yadi da ba a iya tantance ainihin kalarsa saboda tsufa, daga ɗan nesa da su ya tsaya sai da Salma ta sake cewa ya zo wurin ta sannan ya ƙarasa, nuna mashi gefen ta ta yi ya zauna, "Har an dawo daga makaranta?" Salma ta tambaye shi, kai ya girgiza mata, a hankali ya ce, "Ba mu je ba." "Saboda me baku je makaranta ba." Kan shi a ƙasa ya ce mata ai sun daina zuwa saboda kayan makarantarsu duk sun yayyage kuma basu da littattafai shi ne baban su ya ce su zauna gida sai ya samu kuɗi zai siya masu, ɗan girgiza kai Salma ta yi, har cikin ranta tana jin tausayin halin da yaran suke ciki na rashin wadatuwa, ba kamar a baya ba lokacin da mahaifinsu ke aiki yana kula da su bakin gwargwado, tun bayan da ya aje aikinsa na ɗan sanda kuma wurin biyan shi hakkinsa na gama aiki aka samu wasu azzalumai suka zabtare masa kuɗin aka biya shi ba yadda ya kamata ba shike nan silar shigar su wahala, gashi yana da iyali matansa ukku da yara sun kai sha bakwai, yana da wata ƴar gonarsa da yake nomawa sai kuma sauran ƴan buge-bugen da yake yi don bai da wata tsayayyar sana'a, ya yi niyyar idan kudin shi suka fito lokacin ya kama ƙwaƙƙwarar sana'a, har suma matansa ya basu babban jari to sai abu ya zo ba yadda ya zata ba, tun a biyan basussukan da ake bin su kuɗin suka tafi, ya dai samu ya canza tsohon babur ɗinsa ya siya wani da yanzu har sana'ar aca6a yake duk da manyanta da ya yi. "Salma je ki samu wuri ki zuba mashi abinci ya je ya ci shi da ƙannansa." Innarsu ta faɗa, amsawa Salma ta yi da to tana ƙoƙarin miƙewa, wani kalan tamke fuska Imrana ya yi jin za a kwashe masu abincin dare, Salma da ta kalle shi ganin yadda ya yi kicin-kicin da fuska ta nufi kicin tana mashi dariya. Bayan Salma ta zubo mashi ya amsa zai tafi, cikin tsawa Imrana ya ce, "Ba zaka ce an gode ba!" "Imrana miye haka ne, kai ka basa abincin da zaka ce sai ya yi godiya!" Salma ta daka mashi tsawa, kallon Habu ɗin ta yi ta ce, "Je ka Habu." A hankali kamar zai yi kuka ya ce mata an gode ya tafi, yana haura tudun barandar zai nufi ƙofa Auwalu ya ɗaga kai ya kira shi, bayan ya je ya saka hannu a aljihu ya fiddo kuɗi dubu biyu ya bashi ya ce ya kai ma innarsu ya ce ta basu kuɗin aski a ciki, shima sai da ya ce mashi an gode sannan ya tafi, kallon Imrana ya yi cikin ɗaure fuska ya ce masa idan ya ƙara ganin ya hantari yaron sai ya zane shi, ya shiga kwatanta mashi kowa ma zai iya shiga irin halin da suke a ciki ba wai don Allah Ya fi son su bane ya sa su ya wadata su, idan Allah Ya buɗa ma mutum har da don ya taimaka ma wanda bashi da shi ne, Salma da innarsu nata jinjina kai cike da jin daɗin abun da Auwalun ya yi, innarsu tana alfahari da irin halin yaran nata na tausayin wanda bashi da shi, duk da irin rashin kirkin Sagir shima wani lokacin yana taimakon su da kuɗi, shima Imrana ta san har da yarinta ke damunsa. Wuraren ƙarfe biyar na yamma innarsu ta gama aikin awarar da hajiya ta buƙata, ƙwala ma Salma dake a cikin ɗaki kira ta yi ta amsa tare da fitowa, "Yauwa zo ki kai ma hajiya awaran nan." Turus Salma ta yi jin in da zata je, "Inna ko ki ba Imrana tun da ga su can suna yin kallo, ni wani assignment ne nike yi." Ta faɗa cikin rashin son zuwa. Innarsu ta ce, "Da shi zan aika, sai na tuna hajiya da kanta ta ce a baki ki kai, ai tun da ba wani nesa bane kawai miƙawa zaki ki dawo, je ki ɗauko mayafin ki." Bayan ta ɗauko mayafi ta ɗauki robar ta wuce, tun da ta tunkaro gate ɗin gidan ƙirjinta ya fara bugawa da ƙarfi, fargabarta kada ta iske su Fahad, ganin mutane a bakin gate ɗin ya ƙara saka mata fargaba don ta san wurin jikan hajiya ɗan kwallon nan suka zo da alama yana nan ke nan, bayan ta wuce gate ɗin ta nufi ciki tana ta saƙe-saƙen ko shima wannan ɗayan yana nan. A bakin kofar shiga falon ta haɗe da hajiyar ta yo ma wasu magidanta su ukku rakiya da alama ziyara suka kawo mata, sai da suka gama yin sallama sannan ta dawo kan Salma da murmushi ta ce, "Salma..." "Na'am hajiya, ina wuni." Amsa mata ta yi da lafiya lau ta ce su shiga ciki, bayan ta zauna ta nuna ma Salma kujera ta ce ta zauna, "Gashi innarmu ta ce in kawo." "To, awaran ce an gama." Ƙwala ma Balaraba kira ta yi don ta zo ta ɗauka, bayan ta fito suka gaisa da Salma ta ɗauka ta wuce, "Salma ya makaranta, an dawo tun ɗazu ko?" Hajiya ta tambaya tana kallonta, ta amsa da eh tana wasa da yatsun hannunta, hajiya ta ji daɗin ganin yadda ta saki jiki dama saboda abun da ya faru jiya ya sa ta ce a ba Salmar awaran ta kawo, tayin abinci hajiya ta yi mata Salma ta ce mata ta ƙoshi yanzu nan ta gama ci, shiru suka yi gaba ɗaya idanunsu na akan tv, sallamar da aka yi ta sa duk suka kai idanunsu kan ƙofar shigowa........ *_✨A CIKIN RAYUWA✨_* ZAINAB BATURE _Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._ 18 Salma na ganin waɗanda suka shigo ta yi saurin maida idanunta ƙasa, ƙirjinta ya hau bugu da ƙarfi, ta shiga zullumin abun da zai biyo baya ganin Fahad, sam ta kasa ɗaga kai ta sake kallon saitin ƙofar yayin da suke shigowa ciki, ƙamshin turaren su ne ya karaɗe ilahirin cikin falon, cikin washe baki hajiya ke kallon Fahad da Deen da suka nufo inda suke, "Ma sha Allah angwayen hajiyar ambasada, wannan wanka dai ya yi min na yaba gaskiya." Ta faɗa tana bin su da kallo, jin furucin hajiya ya sa Salma ta ɗan ɗago kanta a hankali ta kalle su aikuwa idanunta suka shiga cikin na Fahad, ganin yadda ya ɗaure fuska ya sa ta yi saurin janye idanunta, sam ta kasa dauke idanunta daga kan Deen don ba ƙaramin kyau ya yi mata ba, "Wannan na san bai wuce aikin Fahad ko?" Hajiya ta faɗa tana ta murmushin jin daɗin ganin yadda jikokin nata suka fito, Deen ya bata amsa da shine ya kawo masa kayan, ta ce, "Amman kuwa sun matuƙar amsar ka. Kana ma saka kaya haka kuwa a can?" Ya bata amsa da ya daɗe, "Aikuwa ka rinƙa sakawa don ba ƙaramin burge mutanen can zaka yi ba." Da ɗan murmushi ya ce mata haka daddy ya faɗa, ƙoƙarin zama ya fara a kan kujera mai mazaunin mutum ɗaya, Fahad kuwa wucewa ya yi ciki Salma ta bi bayansa da kallo, maido idonta ta yi kan Deen suka haɗa ido, shi tun da ya shigo ma bai kalle ta ba sai yanzu ya ganta, a hankali ta sauke kanta ƙasa bayan ɗan lokaci ta sake ɗagowa lokacin idanunsa na akan wayarsa, "Ina wuni..." Ta faɗa da siririyar muryarta, sai da hajiya ta ce masa ana gaishe shi ya ɗago suka sake haɗa ido, a ɗan daburce ta sake gaishe da shi ya ɗaga mata kai ba tare da ya amsa ba, daga haka ya ci gaba da latsa wayarsa ita kuwa ta bi sumar kansa dake fake a ƙasa da kallo, bayan ɗan lokaci ya ɗago kansa yana kallon abun da suke kallo a tashar arewa 24, shi rabon da ya kalli channel ɗin hausa ma har ya manta, hajiya ta kai idonta kan sumar shi da ya juyo kansa ta ce, "Amman dai ba haka ka je sallar juma'an ba da gashi a ƙulle kaman mace." Juyowa ya yi fuskarsa a sake kaman zai yi murmushi ya ce mata haka ya je, "Wannan ai sai ka ɗauke ma mutanen dake salla a kusa da kai hankali tun da ba abu ne da suka saba gani ba namiji da gashi a ƙulle." Murmushi mai ɗan faɗi ya yi ya ce ai ya saka hula yana mota ne ya cire, Fahad ne ya fito suka maida kallon su kan shi, "Ba dai har zaka tafi ba?" Hajiya ta tambaya, ya bata amsa da eh ya samu kiran gaggawa ne daga private hospital ɗin da yake aiki a nan zai je ya duba wasu marasa lafiya, hajiya ta ce, "To amman zaka dawo ko, don kun zo ko abinci baku ci ba." Ya bata amsa da ya gama zai dawo ya ce mata a ƙoshe suke sun ci abinci a gida ta gyaɗa kai, kallon Deen ya yi ya bashi hannu suka yi sallama, Deen ya ce mashi sai ya dawo Allah Ya bada sa'a ya amsa da Ameen kafin ya wuce, hajiya itama ta yi addua'ar Allah Ya taimaka ya basu lafiya, bin bayansa Salma da ko kallon 6angaren da take bai yi ba ta yi da kallo, Deen na kallonta yanayin fuskarsa kamar zai saki murmushi don ya fahimci a tsorace take da Fahad sai ka ce ba ita bace mai tsaurin idon nan. "Wai kuwa ka ga mutanen dake ta son ganin ka tun ɗazun a bakin gate." Hajiya ta tambaya, ya bata amsa da eh sun yi magana sai zuwa dare zai yi ƙoƙarin ganawa da su. "Su kawun ka ma Hamida ɗazun sun zo nan suka ce sun ji labarin zuwan ka, na sanar da su kana can gidan baban naka. Yakamata ka samu lokaci ka kai ma ƴan'uwa na nan ziyara ku gaisa za su ji daɗin hakan sosai." Amsa mata ya yi da in sha Allah zai yi hakan. "Ko a shirya maka abinci ne?" Kai ya girgiza mata alamar a'a, ta sake cewa, "Ga awaran ma da ka ce kana so can Salma ta kawo Balaraba na haɗa maku." Kai idonsa ya yi kan Salma suka haɗa ido, sam ta kasa janye nata sai ƴan kame-kame da ta shiga yi tana kikkafta idanu. "Su suke yin shi ne?" Ya tambaya bayan ya maida idanunsa kan hajiya ta bashi amsa da eh, bai ce komai ba ya mayar da kallonsa kan waya, can ya miƙe ya nufi ciki Salma nata kallonsa, ita a wurin ta ganin shi da take yi hakan ba ƙaramar alfarma bace a wurinta, don in ba haka ba to ina zata samu damar ganin mutum mai kyau da ɗaukaka irin wannan? Ci gaba da kallon ta ta yi don ta san ko ta koma gida a lokacin ba wani abun da zata yi, dama ɗazun ƙarya ta yi ma innarsu cewa assignment take, kawai don bata son zuwa ne kada ta haɗu da Fahad, to ƙarshe ma sun haɗun ya nuna da ita da bola duk ɗaya. Motsin da suka ji ya sa duk suka kai idanunsu kan Deen da ya dawo cikin falon, ya canza kaya zuwa ƙananu na shan iska riga mara hannuwa da wandonta gajere dukkan su kalar ruwan ƙasa mai haske da ta hau da fatarsa, kayan na ɗauke da tambarin Louis Vuitton, "Jama'a ku taya ni kallo, mi nake gani ne a saman kan Deeni?" Hajiya ta tambaya tana kallon saman kan nasa da mamaki akan fuskarta, wadda za ta bata amsa bata wuce Salma ba tun da su biyu ne kawai, sai dai itama gaba ɗaya hankalinta ya tafi kan Deen ɗin da yanayin al'ajabi take kallon saman kan nasa, nufar kujeran da ya tashi ya yi ya zauna fuskarsa da ɗan murmushi don ya san abun da hajiyan ke ma mamaki, "Wai miye a kan ka Deeni kamar kitso?" Hajiya ta tambaya har lokacin da mamaki shimfiɗe a saman fuskarta, ba don bata ta6a ganin kitso a kan nasa ba, ta san yana yi musamman idan suna ƙwallo, to amman mamakinta waye ya yi masa kitson yanzu? hannu ya kai ya shafi kan nasa ya bata amsa da kitso ne, ta ce, "Ikon Allah! Waye ya yi maka kitso cikin ɗaki? ko kuwa shima kitson an yo injin da ke yin sa ne tun da Bature dai ba zai gaji da kashe mu da abubuwan al'ajabi ba?" Murmushinsa ne ya ɗan faɗaɗa jin zancen hajiya, ya ce, "Nah, ni ne na yi shi." Ya yi maganar yana jingina kansa da kujeran, "Kana nufin yanzu kai ne ka zauna ka kitse kan ka haka?" Kai ya jinjina mata ya ce eh, kafin ya ɗaura da cewa zafi ya yi yawa a nan gashi ya saka manyan kaya sun ƙara masa zafin, hajiya ta ce, "To ai dama ka san yadda weather ɗin tamu a nan take, a haka ma da sauƙi tun da damuna ta fara don ma dai ruwan bai zauna ba sosai. To mi zai hana ka aske gashin kawai ko kuma ka rage shi sai ka fi samun sauƙin jin zafin a kai, idan sumar kake so sai ka bari idan ka koma ka ƙara tara wata tun da gashin bai maka wuyar taruwa." Shiru bai ce komai ba sai ɗan murmushi da yake yi, Salma dai ta kasa ɗauke idonta akan nasa, al'ajabi ne bayyane a saman fuskar tata don ita tun da take bata ta6a ganin namiji da kitso a zahiri ba sai yau, gashi abun da ya fi ɗaure mata kai shine jin cewa da ya yi shi ya yi ma kan sa kitson, dama akwai mazan da suka iya kitso? hakan take ayyanawa a ranta, ko Sagir da take roƙa wani lokacin ya taya ta tsifan kanta bai ta6a jaraba cewa zai yi mata kitso ba, jin bai ce komai ba bayan hajiya ta yi masa maganar aske sumar ya sa ta ƙara cewa, "Ko ba a ko ina kake yin aski ba? Balle garin namu ƙauye ko?" Tana rufe baki caraf Salma ta ce, "Ai akwai wani wurin aski mai kyau a can bakin tasha, ƴan gayu masu kuɗi nan suke zuwa aski, ko wannan ɗan film ɗin na nan garin na taba ganin shi a can an masa ask..." Kasa ƙarasa maganar da ta ɗauko ta yi sakamakon ido da Deen ya ɗago ya yi mata wani kallo mai kama da kallon ni tsaran wasan ki ne? hajiya da ta lura da abun da ke faruwa a tsakanin su ta sa dariya, dama maganar Salmar ta bata dariya, cikin dariyan ta ce ma Deen, "To kai shike nan ma ka ji Salma ta san inda ake ma irin ku celebrity aski sai ta raka ka a yi maka." Maida idonsa ya yi kan Tv ba tare da ya ce komai, itama Salma tun da ta yi maganar ta sauke kanta ƙasa ƙirjinta na bugawa da ƙarfi, yayin da zuciyarta ke tsawatar mata kan ita ina ruwanta da shiga maganar su! sosai ta ji rashin daɗin su6utar bakin da ta yi masu, kunya duk ta lullu6e ta tana jin kaman ta nutse a wurin, bayan ɗan lokaci da ƙyar ta miƙe hajiya ta kalle ta ta ce ina zata je, cikin ƴar rawar murya ta bata amsa da gida za ta tafi, hajiya na murmushi ta ce, "Kina yin kallon ki muna hira, ki zaman ki." Shiru ta yi tana ɗan wasa da yatsun ta, "Deeni ka ga zaka korar mini baƙuwa." Kamar ba zai ce wani abu ba, slowly ya juyo idanunsa ya kalli Salma, janye idonsa ya yi ya mayar kan Tv tare da faɗin, "Ban kore ta ba. If I want to cut my hair, I have a clipper (Idan ina son aske gashina ina da abun yin askin)" Hajiya dake murmushi ta ce mata, "To kin ji, shi ba ruwan shi da ke ki zaman ki." A hankali ta ɗago kai ta kalle sa, daidai lokacin ya maido nasa kanta idanunsu suka haɗu, kawai sai gani ta yi ya ɗage mata gira tare da ɗan jinjina kansa alamar ta ji abun da ya ce? ɗan kikkafta idanu ta shiga yi tare da tsuke baki ta jinjina masa kanta alamar eh, ya kauda idanunsa daga barin kallonta, komawa ta yi ta zauna amman duk da haka ta kasa sakin jiki, after some few minutes ta sake miƙewa hajiya ta kalle ta, tun kafin ta ce wani abun Salma ta riga ta cewa, "Zan je in shirya ne, anjima zan fara tuyan awara." Da alamun rashin fahimta hajiya ta ce, "Dama ke kike tuyar awaran?" Kai ta ɗaga mata alamar eh, ta sake tambayar ta anan cikin gidan su? ta bata amsa da a ƙofar gida. "Amman ba kina da ƙannai ba?" ta ce mata eh amman duk maza ne, tambayarta ta yi maza basu tuyar awaran ne, tana ɗan murmushi tare da wasa da yatsunta ta ce suna yi kawai dai ita ce ke son tana yi, hajiya ta ce, "Amman Salma baki gudun samarinki su gan ki kina tuyar awara?" Still da murmushi ta ce ai ita bata da saurayi, kallon ban yarda da abun da kika faɗa ba hajiya ta yi mata, "Ya za ai budurwa kamar ke, ga ki kuma tubarkallah ki ce mani baki da saurayi Salma?" Ƴar dariya ta yi kanta a ƙasa ta ce ai ita ce bata saurarar su, "To saboda me?" hajiya ta tambaya tana kallonta da ɗan murmushi, cikin yar en-ina Salma ta ce, "I...idan na gama makaranta so nike in ci gaba da karatu shi ya sa." Kai hajiya ta jinjina alamar gamsuwa kafin ta ce, "Duk da haka dai idan akwai wanda ya zo da magana ta kirki mai nagarta, kuma kin ga ya yi maki yakamata ki saurare shi, saboda karatu baya hana ai a saurari saurayi, kuma ko da mace tana cikin karatunta zata iya yin aurenta ta ƙarasa a ɗakin mijinta. Ita mace akwai lokacin da zaki ga tauraruwarta ta haska samari sun yi mata caa har da masu son aurenta, to ya kamata ta yi amfani da damarta don wani lokacin in ta ce sai lokacin da ta shirya sannan sai ki ga samarin ɗibb babu su, duk da dai dama komai ya faru da bawa rubutacce ne. A dage a rinƙa yin addu'ar neman za6in Allah." Cikin muryarta mai tattare da natsuwa ta amsa da in sha Allahu. "Amman dai yakamata ki bar ma ƙannanki suna tuyar awaran nan, ko ba samari ba baki jin kunyar ƙawayen ki su gan ki kina tuyar awara?" Hajiya ta tambaya da zolaya, Salma ta yi ƴar dariya ta ce, "Ai ma duk ƙawayena sun san ina yin awaran, kuma ni bana jin komai tun da neman halak ne, ya fi ka je kana roƙon mutane." Da alamun burgewa a maganarta hajiya ta ce, "Wannan gaskiya ne Salma. Allah Ya ƙara rufa asiri." Ta amsa da Amin, duk abun nan Deen na saurarar su duk da ba za ka ce hankalinsa na a kan su ba don idanunsa na akan Tv, maganar Salma ta ƙarshe ba ƙaramin burge shi ta yi ba saidai ba alamar da ta nuna hakan. Bayan hajiya ta ƙwala ma Balaraba kira ta fito ta bata umarnin ta kawo ma Salma robar awaran ta ce ta zubo mata kayan itatuwan da aka kawo ɗazun daga lambu, after some minutes Balaraba ta kawo mata robar da lemu, mangaro, gwaba a ciki, hajiya ta ce ma Salma gashi nan su je su sha ta yi mata godiya, har za ta juya ta ji Balaraba ta ce, "Wai Salma ina fara ne, kwana biyu ko kin daina soyawa?" Tana murmushi ta ce, "Wllh anty Balaraba faran ne ta yi tsada sosai, idan na soya sai a yi ta cewa na yi tsada shi ya sa ma kawai na bari." Balaraba na murmushi ta ce, "Ai komai ma yanzu ya yi tsada abun sai dai addu'a kawai, amman idan kina fita ko ya ya ne kuma ana siya ai ya fi ki ci gaba da ki ce kin bari ɗin gaba ɗaya, tun da gaskiya kin iya soya fara ba ƙarya." Dariyar jin daɗin yabon ta yi, ta ce in sha Allah za ta ci gaba dama wasu na ta so, itama Balarabar ta ce to idan ta yi tana so ta kawo mata ta dubu ɗaya, hajiya dake sauraran su tana ta murmushi, juyawa Balaraba ta yi ta koma kicin Salma ta ƙara yi ma hajiya Sallama da godiya ta nufi hanyar barin falon, har ta kusa kai wa ƙofa ta juyo da niyyar satar kallon Deen kawai sai gani ta yi ashe idon shi na kan ta, da sauri ta juya ta tafi. Bayan sallar magrib Deen ya fara ganin mutanen dake son ganawa da shi, yawanci duk koke ne kan halin matsin rayuwa wasu kuma abun da ya shafi ƙwallon ƙafa, a wurin parking space ya zauna ana shigo mashi da mutane a nutse da yake bakin gate ɗin akwai jami'ai, sai da aka fara kiran sallar issha ya dakata tare da ba waɗanda bai samu gani ba haƙuri ya basu lokacin da zai gan su, cikin gida ya koma wurin Fahad wanda ya dawo da magrib, tare suka tafi masallaci yin sallan issha, bayan sun dawo suna shigowa haraban gidan aka kira Deen a waya ya ce ma Fahad ya shiga ciki zai shigo idan ya gama amsa kiran, a wurin da ya zauna ɗazun da yana ganin mutane ya zauna, ya ɗan ɗauki lokaci yana yin wayar wanda wani babban abokinsa ne ɗan team ɗin su bature ya kira shi suke tattaunawa game da hutun da suke yi da kuma shirin da za su yi don tunkarar next season, bayan ya gama yin wayar zaune ya yi a wurin idanunsa na kallon wuri ɗaya kamar mai tunanin wani abu, motsin da ya ji a ta gefensa ya sa shi kai idanunsa wurin, Balaraba ce ta fito tana ruƙe da wata babbar roba ta nufi hanyar bayan gidan, juyo da kansa ya yi ya shiga latsa wayarsa, ba a ɗauki lokaci ba ya sake jin motsi ya ɗago kai, ita ce ta dawo zata koma ciki, har ta kusa kai wa ƙofa ya dakatar da ita ta hanyar yin alamar kiran ta, da sauri ta aje robar a wurin ta nufo shi, kafin ta ƙaraso wurin sa a cikin ransa ya shiga tunanin to mi ma zai ce mata da ya kira ta? Daga gefensa ta tsaya cikin ladabi ta gaishe da shi ya ɗan jinjina mata kai, shiru ya ɗan yi na wani lokaci sai kuma ya gyara zaman sa ya ce mata dama yana son tambayarta ne a kan yarinyar nan da suke yin awara a nan unguwan suke? Da sauri ta amsa mashi da eh, ta ce ai basu da ma nisa da an fita, layin da ke tsallake yana kallo bangaren nan gidan anan ciki suke gidansu ne na ukku daga dama, kai ya jinjina mata ya ce ya gode za ta iya tafiya, sam Balaraba bata kawo komai ba a ranta illa ta yanke taimakon su wataƙil zai yi ganin yadda yake ta taimaka ma mutane, bayan ɗan lokaci ya miƙe yana tafiya a nutse jikinsa sanye da ƙananun kaya ya nufi gate, ganinsa ya fito officers dake bakin gate ɗin suka shiga faɗin, "Barka da fitowa yalla6ai..." Bayan ya amsa masu, ganin yana kallon bangaren da aka faɗi mashi gidansu Salma yake wani cikin jami'an ya ƙara cewa, "Ko da wani abu ne yallabai?" Ya bashi amsa da a'a, tunanin ko ya kamata ya yi abun da zuciyarsa ke horan sa akan ya yi ya shiga yi, hannu ya kai cikin aljihun wandonsa ya fiddo takunkumin fuska, tafiya ya fara yi bayan ya gama sakawa, wani jami'i ya ce mashi ko yana buƙatar rakiya ya ɗan ɗaga masa hannu tare da faɗin ba nisa zai yi ba, suna ta mamakin in da zai je ganin yana ƙoƙarin tsallaka titi, yana shiga layin idanunsa suka hango masa wani wuri inda wuta ke ci ga wasu yara a tsugunne, daga yadda aka kwatanta masa ya fahimci nan ne inda take tuyan awaran, a nutse ya tunkari wurin fuskarsa a ƙasa, daga ɗan nesa da su ya dakata yana kallon wurin. "Awara za a baka?" Ya ji ɗaya daga cikin yaran ya tambaya cikin ɗan ɗaga murya, hannu ya kai a hankali ya zame nosemask ɗin ganin wurin ba wadataccen haske, tambayarsu ya yi ina mai yin abun, yaron ya ce, "Yaya Salma ce ta shiga gida ta dawo, amman ko mu zamu iya saida maka." Shiru Deen ya yi daga yanayin zaƙin muryar yaron ya fahimci ɗan'uwanta ne, hannu Deen ya kai ya mayar da nose mask ɗin ganin wasu matasan samari sun nufo wurin, awaran suka siya bayan an sallame su yaron ya kalli Deen ya ce "Ka ji, ta nawa za a baka awaran?" Ɗan murmushi ya bayyana a kan fuskarsa ya ce masa bari ita mai abun ta dawo, miƙewa yaron ya yi da sauri yana faɗin to bari ya je ya kirawo ta, da ƴar sassarfa ya nufi gidan Deen ya ɗaga ido yana kallon inda yaron ya nufa, a daidai bakin zaure suka haɗe da ita har suna yin karo, ta ce, "Lafiya Hamza ka taho haka?" Da sauri ya ce, "Wani mutumi ne ya zo siyan awara na ce ta nawa za a bashi amman ya ce sai kin dawo." Da alamun mamaki ta maimaita abun da ya faɗa, ɗan leƙa kanta ta yi ta hango shi saidai bata iya gane ko wanene ba saboda ba haske ta dai hangi mutum a tsaye, "Ka san shi?" Ta tambayi Hamzan, kai ya girgiza mata ya ce, "A'a ya rufe fuskan shi, amman dai yana ta uban ƙamshi." Juya maganar Hamza ta shiga yi a ranta tana ƙoƙarin tuno wanda ta sani mai zuwa siyan awara yana ƙamshin turare sosai, fitowa suka yi tana biye da bayan Hamza jikinta sanye da hijab mai hannu ta tsaya mata daidai gwiwa, da sallama ta ƙaraso wurin ta tsaya ɗan nesa da shi tana kallonsa sai dai ta kasa tantance wanene don tana ganin kamar bata ta6a ganin wani mai irin suffar jikinsa ya zo siyan awara ba, ga shi ta gaskiyar Hamza sai baza uban ƙamshi mai ratsa zuciya yake duk ya cika mata hanci, "Ina wuni..." Ta gaishe da mutumin duk da bata san wanene ba amman ya yi mata ƙwarjini sosai, ganin bai da niyyar yi mata magana koda ta gaishe shi kai ya ɗaga mata, ta ce, "Awara za a baka ne?" Ta tambaya ta tsare shi da idanu, ta cikin mask ɗin ta ji ya ce za su yi magana tana a nan ne? ta gane yana nufin ta yi masa nisa, sam bata gane muryarsa ba saboda rufe bakinsa da ya yi, ɗan matsowa ta yi kaɗan a ranta tana mamakin wanene wannan mutumin mai aji haka? Jin bai ce komai ba duk da ta matso ya sa ta shiga yin tunanin ko har yanzu ta yi masa nisa ne shiyasa ya ƙi cewa komai, ƴan kame-kame ta shiga yi ta ce, "Uh..mm jikina yana yin ƙaurin wuta ne ban so in matso ka ji..." Ita kanta bata san dalilin faɗin hakan da ta yi ba, wataƙil saboda yadda ta ji yana sakin ƙamshi ya sa ta kama kanta, steps biyu zuwa ukku ya yi shi ya matsa ta kafe shi da idanu, a hankali ya kai hannu ya zame nose mask ɗin fuskarsa, duk da bata ganin fuskar sosai sai da gabanta ya faɗi, kallon ƙurulla ta shiga yi masa tana son gane waye, "Kina zama a kusa da wuta with this, ba ki tsoron ya kama wutan?" Ya yi maganan yana nuni da hijabin jikinta, damm! gaban Salma ya faɗi, ai ko a cikin magagin bacci ta ji muryarsa wllh sai ta gane, kokonton anya kuwa shine ta shiga yi, to mi zai kawo shi nan idan shi ne? Ya ma za ai ya san wurin? To amman kuma tabbas wannan muryarsa ce, tana cikin yin wasi-wasin wani mai mashin ya shigo cikin layin hasken babur ɗin ya haske mashi rabin fuska farar fatarsa ta bayyana, tabbas shi ne! zuciyarta ta gasgata hakan, ƙirjinta ya shiga yin bugu fat, fat, sai ta ji ma kamar ƙafafuwanta na barazanar kasa riƙe ta, ɗage mata gira ya yi ya ce bata ji abun da ya ce ba? ta shiga motsa baki da ƙyar ta tattaro kalaman bakinta ta ce mashi ai tana kula sosai, kauda kai ya yi ta ji ya ce It’s not safe to go near fire da dogon abu irin haka, kamar yar ƙadangaruwa ta gyaɗa kai ta ce mashi to ta gode za ta daina saka irin shi idan za ta yi tuyan, hannu ya saka cikin aljihun gaban wandon shi, miƙo mata abun da ya fito da shi ya yi ta matso ta amsa, lokaci guda ta gane kuɗi ne masu yawa, a dabarbarce ta ce, "Awaran bata kai ta haka ba, duka ma wadda ta rage bata da yawa." Ya ce mata ta raba ma mutane shi, daga haka ya maida mask ɗin, ganin yana ƙoƙarin juyawa da sauri ta ce, "To kuɗin sun yi yawa ai, duka awaran ma bata wuce ta dubu ɗaya ba idan ma ta kai..." A taƙaice ya ce ta kai kuɗin gida, daga haka ya yi gaba abun shi ba tare da ya tsaya sauraren abun da za ta ƙara cewa ba, tamkar rainon sakarya haka ta bi shi da kallo yayin da yake tafiya bakinta a buɗe tsabar mamaki..... *_✨A CIKIN RAYUWA✨_* _New story from the writer of 'A Sanadin Makwabtaka',_ ZAINAB BATURE 19 Da tsananin mamaki innarsu Salma ke juya kuɗin da ta kawo mata wanda rafar yan dubu dubu ce guda biyu. "Yanzu kika ce haka nan ya zo ya baki wannan uban kuɗin ya ce ki kawo?" Ta tambaya idonta a kan Salma dake tsaye a gabanta bakin baranda, kai ta ɗaga ta ce, "Wllh innarmu yadda na faɗa maki." Hannu ta kai ta riƙe haba ta ce, "To amman ya akai ya san nan gidan har ya zo?" Ta tambaya da mamaki a kan fuskarta, Salma ta ce, "Ni ma wllh abun da nike ta mamaki ke nan innarmu, kuma na faɗa maki ai maganganun da muka yi da hajiya ɗazun sam shi bai ma saka baki ba lokacin da take mani maganar tuyan awaran." Gyaɗa kai innar ta yi ta ce, "To wataƙil dai daga hiran taku ne yana sauraro, kuma ƙilan bayan kin taho ya tambayi hajiyan har ya san in da kike yin tuyar shine ya zo. Dama Sagir yana ta faɗin irin uban alkhairin da yake ta yi ma mutane, an gode Allah Ya saka masa da mafificin alkhairi ya ƙara masa ɗaukaka. Idan kuka sake haɗuwa sai ki yi masa godiya sosai." Amsawa Salma ta yi da to, tana shirin juyawa innar ta tambaye ta ina zata je ta ce mata za ta je wurin awaran ne, "To ku ƙarasa soya sauran sai ku rabar ma mutane tun da haka ya ce, ki ba Hamza ya kai gidansu Habu." Amsawa ta yi da to cike da jin daɗi ta nufi hanyar waje, ci gaba da juya kuɗin innar tasu ta yi tana mamakin irin kirkin Deen, haka nan ya ɗauki kuɗi masu yawa lokaci guda ya ba su! tabbas shi ɗin na daban ne ta ayyana a ranta tare da juyawa ta nufi ɗaki. Bayan Salma sun dawo gida suka zauna cin abinci har da su Sagir da suka dawo, suma sun yi mamaki sosai bayan da innarsu ta sanar masu zancen kuɗin da Deen ya basu, Sagir ya ce ai wannan ba wani abu bane a wurinsa, ya shiga basu labarin irin abubuwan alkhairi da yake ta yi ma mutane, gaba ɗaya suma su Auwalu sun yanke cewa maganar da Salma ta yi da hajiya ce ta sa ya zo ya bata kuɗin, sai dai sun yi matuƙar mamakin yadda ya iya takowa ya zo ƙofar gidan nasu, Sagir ji yake inama sun haɗu da shi. Bayan Salma ta gama cin abincin banɗaki ta wuce ta yo wanka, dama ta yi sallar isha tun lokacin da Deen ya zo aka ce tana cikin gida to salla ta je yi, sam bata wasa da salla da lokacin ta ya yi take barin abun da take yi ta je ta yi, shiryawa ta yi da doguwar rigar bacci ta saka hula a kanta jikinta na ta ƙamshin humra da ta shafa, littafinta ta ɗauko don ta yi karatun test da za a yi masu, sai da ta yi addu'a kafin ta kwanta a saman ɗan gadonta da ya sha shimfiɗar wankakken zanin gado, musamman babanta ya haɗa mata gadon da ɗan mirror har da ƴar wardrobe mai gida biyu, hannunta ɗaya riƙe da wayar innarsu keypad ta kunna torch tana haska littafin, sai dai tana fara yin karatun zuciyarta ta ƙi bata goyon baya ta hanyar jan akalar tunaninta zuwa faɗawa tunanin Deen, sai ma ta rinƙa ganin fuskarsa a jikin littafin, ƙarshe dole ta ajiye shi a gefe ta ci gaba da ba zuciyarta goyon baya, abubuwan da suka faru tsakaninsu yau ta shiga tunanowa tana sakin murmushi kamar wata zautatta, komai na shi ba ƙaramin burge ta yake ba, ba ƙaramin tafiya ya yi da ita ba lokacin da ya yi ma kansa kitson nan, ko ina ma kitson? ta raya don ba alamun shi lokacin da ya zo ƙofar gidansu, wata zuciyar ta bata amsa da ƙilan ya kwance da zai fita waje, jinjina irin kirkin sa ta shiga yi yadda har ya iya takowa kofar gidan nasu ya bata kuɗi, Fahad ne ya faɗo mata a rai nan take ta yanke hukuncin Deen ya fi shi kirki nesa ba kusa ba, a ranta take raya tabbas duk wadda ta aure shi wllh ba ƙaramin dacewa ta yi ba. Tana ta tunane-tunane a haka bacci ya yi awon gaba da ita. Washe gari Asabar, misalin ƙarfe tara saura na safe su Salma na zaune a ɗakin innarsu, wanda ba laifi ɗakin babba ne, akwai gado mai kyau da dressing mirror da side drawers ɗinsa, sai wardrobe mai gida biyu, daga farkon shiga dakin a gaban gado akwai kujeru mai mazaunin mutum biyu da masu mazaunin mutum ɗaya guda biyu, Salma na zaune a saman kujera mai mazaunin mutum ɗaya, yayin da Imran da Hamza ke zaune a tsakiyar kujerun saman ɗan madaidaicin carpet dake a saman ledar tsakar ɗakin, gaba ɗaya suna sanye da uniform ɗin islamiyya, kowannan su kofi ne a hannunsa suna yin karin kumallo, "Faka-faka, ina abun karin kumallo na?" Sagir da ya faɗo cikin ɗakin ya faɗa, ƙafafunsa na sanye da dogayen safuna sai wandon ƙwallo hannunsa na riƙe da rigar bai kai ga sakawa ba, duk suka kalle sa, zama ya yi a saman kujera kusa da Salma, "Innarmu ina nawa?" Tana kallonsa ta tambayi saurin mi yake yi haka? Amsa ya bata da, "Wllh gasa ce zamu yi gaba ɗaya team ɗin ƙwallon garin nan, a cikin waɗanda suka yi nasara Nuree Jr zai zabi ƴan wasan sabon club ɗinsa mai suna 'FT STRIKERS." Kai Innarsu ta jinjina alamar ta gane, "Tare da shi zaku yi ƙwallon?" Salma da ta kur6i kunu ta tambaya, ya bata amsa da a'a amman a gabansa za a yi gasar yana kallo, bayan an zuba masa kunnun ya ɗauka yana sha tare da ƙosai, ba tare da 6ata lokaci ba ya miƙe innarsu ta tambayi har ya gama ya ce mata eh, ta tambayi ko a ƙara masa ya ce mata a'a bai son ya cika cikinsa sosai ya kasa yin abun kirki, "To ni zan tafi innarmu ki yi mani addu'ar nasara, dama baba tun da muka je sallar asuba na sanar masa shima ya yi mani addu'a." Tana murmushi ta ce, "To Allah Ubangiji Ya baku sa'a Sagir." Da sauri ya amsa da Amin yana ƙoƙarin saka rigar kwallon, "To ni ba zaka ce in yi maka addu'ar ba?" Salma ta faɗa tana wurga masa yar harara, "Ke dalla wake ta wata addu'arki, ga mai kankat nan wadda da ta yi an kar6a ba shamaki." Gyaɗa kai Salma ta yi ta ce to shike nan, Innarsu dake murmushi ta ce, "A'a Sagir, wannan yarinyar tawa fa yar baiwa ce Allah, kada ka raina addu'arta don Allah na amsa mata addu'ointa." Bayan ya gama saka rigar ya kalli Salma yana ƴar dariya ya ce to ta yi masa addu'an, "Ban yi!" A fusace ta faɗa, hannu ya kai ya kama kanta yana dariya ya ce,"Haba my lovely sis, ni da ke ai bata 6aci kin san wasa nike maki ina buƙatar addu'ar ku ƴan'uwana." Tana murmushi ta ce masa Allah Ya basu sa'a, amsawa ya yi da Amin tare da sakar mata kai, sai kuma ya ce, "Da kar ki yi mini addu'ar ki ci na jaki." Harara ta wurga masa tare da faɗin, "Kamm! To na ma janye addu'ar tawa." Nufar ƙofa ya yi yana dariya yana faɗin ta baya ta rago, su Imrana suka ɗaga murya suna yi mashi Allah Ya bada sa'a ya amsa lokacin ya fice. Bayan Salma ta gama karin kumallon, ɗakinta ta koma ta sako hijab a saman kayan jikinta don tafiya islamiyyar hadda da suke yi asabar da lahadi kawai don ta yi sauka, "Innarmu zan tafi." Ta faɗa a daidai saitin ɗakin innar tana gyara hijab ɗinta, ɗaga labule ta yi ta fito da murmushi ta ce mata, "To, sai kin dawo Allah Ya bada sa'a." Ta ce, "Amin, yauwa ba kin ce kina son waken suya ba? Ko ki kawo idan aka taso sai in wuce bakin tasha in siyo." Ɗan jim innar ta yi kafin ta ce, "Je ki kawai a siyo ko gobe." Salma ta ce, "To wanda za a yi amfani yau fa?" "Anya a yi awara yau, a dai bari ko gobe idan Allah Ya kaimu, kada shi mutumin da ya bamu kuɗi ya gan ki kina yi yayi tunanin mun cika son kuɗi." Ta ƙarasa tana ƴar dariya, itama Salma murmushi ne akan fuskarta ta ce, "To ai neman halak ne, kuma da ya bamu bai ce kada mu yi ba." Kai innarsu ta ɗaga alamar haka ne ta ce amman dai yau ta huta, sallama suka yi ta wuce innarsu ta bita da kallo tana murmushi, tana kai wa bakin ƙofa zata fita ta juya ta yi ma innar tasu bye bye tare da yi mata alamar kiss, murmushin jin daɗi ne akan fuskar innarsu ta furta, "Ina son Salmata. Allah Ya raya mani ke ya albarkaci rayuwarki." Amsa mata ta yi da, "Amin uwata da babu irinta.." Daga haka ta fuce innarsu ta ɗan girgiza kai tare da juyawa ta koma ɗaki. Misalin ƙarfe sha biyu da rabi na rana su Salma duk sun dawo daga islamiyya suna zaune a tsakar gida, baka jin muryar kowa sai ta Sagir da ta karaɗe wurin yana basu labarin yadda gasar su ta wakana, jikinsa ko riga babu sai wandon ƙwallo daga gefensa takalman kwallon da ya cire ne tare da safar ajiye, Salma dake ta murmushin jin daɗin jin Sagir ɗin na cikin waɗanda aka za6a yau, ta ce, "Amman Sagir har da shi kuka yi ƙwallon?" Tambayarta ya yi wa? ta ce shi jikan hajiya da ya haɗa gasar, Sagir ya ce, "Farko bai shiga ba kallo ya yi, sai bayan da aka gama za6ar waɗanda suka ci zagayen farko na gasar muka buga tare da shi...kuturun uba! Kai, wanda ya iya dai ya huta wllh, ai duk yadda muke ganin mu nan ƙwararru ne gurin ƙwallo a garin nan ƙur'an duk sai da muka raina kan mu...wai kun ga yadda mutumin yake sarrafa ball kuwa....!" Dakatawa ya yi ya ɗauki wayarsa dake a saman cinyarsa ya ɗan lallatsa, miƙo ma Salma ya yi ya ce ta kalla ga wani video nan da ya yi lokacin da suke bugawa tare da second team da suka ci, da sauri ta yunƙuro ta zo ta amsa ta koma saman tabarmar da take zaune tana kallo, innarsu da su Imrana ma duk suka sako kai suna kalla, Deen na sanye da jersey ɗin club din su na gida, sosai kayan suka amshi jikinsa sun ƙara fito masa da hasken fatarsa, murmushi ne akan fuskar Salma yayin da take kallon ƙwallon, a cikin ranta ta raya ke nan sake yin kitson ya yi don ta ganshi akan sa yanzu, kamar innarsu ta san mike a ran Salmar ta ce, "Wai kamar kitso nike gani a saman kansa ko?" Ta ɗago tana kallon Sagir, ya ce, "Eh kitso ne mana, ai dama yana yin kitso. Ni ma indai na shahara a ball sai na rinƙa yin kitso tun da ai ba haramun bane." Yana rufe baki Salma ta ɗago da alamun mamaki ta ce, "A wannan kan naka kamar goruba ne zaka rinƙa yin kitso." Daƙuwa ya yi mata ya ce, "Eh don ubanki, shegiya, dama ni ne da irin gashin ki, ni na rasa yadda aka yi ma komai naki ya fi namu kyau, koda kike mace ai yakamata muma mu ɗebo wasu abubuwan irin naki, amman daga ke sai Hamza duk aka tara ma abubuwa masu kyau." Ƙyalkyale masa da dariya Salma ta yi tare da yi masa gwalo, innarsu na murmushi ta ce, "Ai kuma ma sha Allah ba munana bane." Imrana ya kai hannu ya shafi sumarsa ya ce, "Amman dai gara gashi na da na yaya Sagir wllh..." Da sauri ya yi shiru ganin Sagir ɗin na niyyar rarumar takalmin ƙwallonsa ya san kuma yana iya jefo masa. Bayan salar Azhar Deen ya shigo cikin falon kamar ko yaushe jikinsa sanye da kayan shan iska don ba karamin jin zafin yanayin da ake ciki a Nigeria yake ba, a haka ma wai ruwa ya fara sauka kuma koda yaushe yana a cikin Ac, hajiya na zaune ta ɗaga kai ta kalle sa tana murmushi, wurin da take ya nufo yana zuwa ya miƙa mata hannu ya ce ta taso su je waje zata ga wani abu, kama hannun nasa ta yi ta miƙe tana faɗin Allah Ya sa ta ga alkhairi ya amsa da Amin yana murmushi, wajen part ɗin suka fito hajiya nata wurga ido ko zata ga wani baƙon abu, wurin parking space ya nufo da ita sai lokacin idanunta suka ga wani mutum dake a tsaye gefen wata rantsattsar mota fara sol sai uban sheƙi ta ke, kana gani ba sai an faɗa maka ba ka san sabuwa ce, mutumin na ganin Deen ya shiga washe baki, suna ƙarasowa ya ba mutumin hannu suka gaisa tare da yi masa ya hanya cikin washe baki mutumin ke amsawa, daga baya ya gaishe da hajiya har da ɗan russunawa ta amsa masa a mutunce, bin motar Deen ya yi da kallo mutumin ya ce ko a buɗe masa ya ƙara gani ya jinjina masa kai, buɗe cikin motan ya yi wanda ya matuƙar tsaruwa, nuna masa abubuwa mutumin ya shiga yi yana ƙara yi masa bayani, fuska a sake Deen ke ɗan jinjina kai alamar yana fahimtar bayanin, duk da dama ya riga ya san abubuwa da suka danganci motan, hajiya dai ta zuba ido itama tana kallon motar da sauraran mutumin, bayan ya gama yi ma Deen bayanin ya ce shi zai wuce, Deen ya ce masa ba zai tsaya ya huta ba ya ci abinci, cikin washe baki ya sanar da shi tare suka zo da wani abokin kasuwancin su shima ya kawo wata mota Zaria za su haɗu ne suna son su koma Abuja yau kada dare ya yi masu, bayan sun yi sallama mutumin ya tafi don dama tuni sun gama duk wani ciniki da boss ɗin su, shi ma kuma mutumin lokacin da ya kira Deen ya sanar da shi shine zai kawo masa mota ya tura masa kuɗi masu yawa. "Ya kika ga motan, ya yi kyau?" Ya tambayi hajiya idonsa akan motar, kai ta shiga jinjinawa ta ce kyau ma ai ba a ma magana ita bata ma ta6a ganin irin motan ba, yana murmushi still holding her hand ya ce mata Avatr EV ce, wato motan da ake ma cajin lantarki, cike da al'ajabi hajiya ta ce, "Ikon Allah, yanzu nan sai a yi mata caji lafiya lau a yi amfani da ita?" Amsa ya bata da sosai, ta ɗan ta6e baki ta ce, "Bature dai ba zai bar mu mu huta da abubuwan al'ajabi ba, saura kuma jirgi mai caji shi ma na san ba wani babban aiki bane a wurin su." Yar dariya Deen ya yi ya ce mata ai wannan ba daga turawan bane daga yan China ne, hajiya ta ce ai dai duk taron su ne masu jan kunnuwa, zagayawa ya yi da ita ya buɗe mata ɗayan bangaren ta shiga da bismilla a bakinta, shima ya zagayo driver seat ya shiga yana ƙara kallon cikin motar, kai kawai hajiya ke jinjinawa tana ƙara yaba tsaruwar motan, screen ɗin dake a kusa da steering motan ya ɗan tatta6a kafin ya kalli hajiyan ta ciki ya ce mata, "Hi Sweety!" Hajiya ta gwalo ido cikin rashin fahimta, dariya ya saka ya yi mata playing vedion da mamaki ta ce wai camera ce a jikin screen ɗin ya ce mata eh, bayan ya rufo motan ya tashe ta suka fara zagayawa a cikin harabar gidan, su officer dake bakin gate duk sun leƙo suna ta kallon motan cikin washe baki sai kace bakunan nasu za su yage, tambayarta ya yi ko su fita su zaga gari ta ce a'a ya bari ta shirya tukun ko zuwa dare, bayan sun gama zagayawa ya dawo da su wurin parking, suna fitowa su officers suka ƙaraso cikin washe baki suka shiga yin santin motan tare da yin Allah Ya sa alkhairi, bayan su officer sun bar wurin hajiya ta ce, "Yanzu ita wannan motan amfani zaka yi da ita ne da ka siya?" Amsa ya bata da eh ya zo ba mota shi yasa ya siya ya yi amfani da ita a nan, hajiya na kallonsa ta ce, "Amman duk motocin dake a gidan nan Deeni? Idan ma na nan basu yi maka ba ai a can 6angaren iyayenka ba akwai wasu da bama amfani ake da su ba suna a lullu6e, in ma duk basu yi maka ba a can gidan ɗayan baban naku duk ba akwai motocin da zaka iya amfani da su ba kafin dai ka koma?" Murmushi ne akan fuskarsa ganin kallon da take masa mai kama da na tuhuma, ta ci gaba da cewa, "Ba laifi bane don mutum ya siya abun da ransa ke so, amman a rinƙa dubawa kada don an samu dama kuma a rinƙa yin almubazzaranci, tun da ai kana da motocin a Abuja da can ƙasar ma da kake, ai ina ganin su kala-kala a hotuna da video, har da wata mai suffa kamar ta wasan yara..." Dariya ya saka jin yadda ta fasalta motan ya kuma gane lamborghini ɗinsa take magana, "....Akwai abubuwa da dama masu amfani da ya kamata a rinƙa yi wanda har da dalilin hakan Allah Ya bada wadatar, duk da na san ana yi sosai." Murmushi ne akan fuskarsa don ya fahimci akan abun da take magana, tambayarsa ta yi yanzu wannan motan zata yi nawa, ya bata amsa da 85m wato miliyan tamanin da biyar, har da ce mata ai ba wata babba bace sosai a cikin jerin avatrs, kai ta jinjina tana ƙara kallon motar ta ce ta ci kuɗinta amman dai a rage yawan son ƙyale ƙyalen duniya a fi maida hankali ga yin zubin da za a ƙwasa a lahira. Gently ya ce, "In sha Allah sweetienah, wannan ma zan ɗan yi amfani da shi ne amman ba nawa bane, Fahad na siya mawa na ga yana son irin motan." Da mamaki hajiya ta kalle sa ta maimaita Fahad ya siya ma wannan motan? kai ya ɗaga mata yana murmushi, wani irin farin ciki ne ya lullu6e ta, tana matuƙar jin daɗin yadda jikokin nata suka haɗa kan su suke kyautata ma junan su, yadda suke taimakon juna ko iyayensu ba su yin hakan, duk da kowanne a cikin iyayen nasu yana hali daidai gwargwado, amman mahaifin Deen ya fi na Fahad arziƙi saidai bai yawan yi masa alkhairi kamar yadda ɗan nasa ke ma ɗan'uwansa Fahad, sai dai ta san hakan na da nasaba da rashin dacen mata da ya yi wadda ta san har da ita ke hana shi yi ma makusantan shi alkhairi yadda ya kamata. "Ban san ya zan misalta maka irin farin cikin da na ji ba Deeni, ina matuƙar alfahari da yadda kuke ƙaunar junan ku kuke taimakon juna. Allah Ubangiji ya ƙara haɗa kawunan ku ya sa ku ɗore da hakan ko bayan ba ran mu." Hannu ya kai ya rungumo kafaɗarta jikinsa yana murmushi ya amsa mata da, "Amin Ya Rabb. In sha Allah." Tana murmushi ta ce aikuwa ita zata yi ma Fahad wannan babban albishir ɗin, da sauri ya ce mata, "No, I wanna give him a surprise, ka da ki sanar masa cewa nashi ne yanzu." Ƴar harararsa ta yi ta ce, "Ke nan buƙulun goron albishir za ka yi mini." Yana yar dariya ya ce, "Idan wannan ne ni zan baki, ki faɗi duk abun da kike so." tana ƴar dariya ta ce, "To nima irin motan nike so." "No problem, zan sa akawo maki naki." Sanin da gaske yana iya sakawa a kawo mata ya sa ta yi saurin ce masa, "Ni wasa nike maka, in yi yaya da wannan motan ni da ake tuƙawa, wanda ke a kwai ma sun isa." yana murmushi ya ce, "But yana da kyau ka canza zuwa sabon abu if you have the means, sai ki bada wani da kike da shi." Tana murmushi ta ce ai duk motocin da ake mata amfani da su ba su wani tsufa ba akwai ma wadda ba a daɗe da aka kawo mata ba, ta ce tun da dai ya siya ma angonta hakan ya wadatar an gode ta san kuma zata rinƙa hawa, bayan sun gama ganin motar suka koma cikin gidan..... *_✨A CIKIN RAYUWA✨_* _New story from the writer of 'A Sanadin Makwabtaka',_ _ZAINAB BATURE_ _Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._ Page 20 Wararen ƙarfe ukkun rana Fahad ya dawo gidan hajiya, don bayan gama gasar ɗazun wanda da shi aka yi ta gida ya wuce ya shirya don sun yi da Deen da yamma zai je kai ma manyan garin ziyarar gaisuwa, sosai ya yaba da sabuwan motan Deen da ya iske an kawo, a ɗakin Deen suka zauna suka ɗan ƙara hutawa, ana gama sallar la'asar suka yi shirin tafiya, wani ɗanyen farin voile ne Deen ya saka da ya matuƙar amsar jikinsa, da ƙananun kaya zai saka hajiya ce ta kawo masa kayan ta ce manyan kaya yakamata ya saka, kansa ya faka sumarsa baya ba tare da ya saka hula ba don takura masa take yi duk da hajiya ta nemi ya sa hulan ya ce mata sai sun isa, shima Fahad farar shadda ce a jikinsa ya yi kyau sosai sai sakin ƙamshi suke yi, harabar gidan suka fito da wasu abokan su guda biyu da za su je tare , motoci ukku ne jere da za su yi tafiyar da su, ɗaya Deen da Fahad suka shiga, sai mota ta biyu ta abokan nasu ce, sai ta ƙarshe wasu daga cikin manya ne a harkar ƙwallon garin tare da ƴan jarida da suka zo da su, daga ƙarshe motar jami'ai ce da za su yi escorting na su, a jere motocin suka fita daga cikin gidan suka hau hanya duk idanun mutane a kan su, farko gidan ɗan majalissar jaha suka fara zuwa wanda yake a gari ya zo weekend, daga nan gidan chairman ɗin garin suka je, daga ƙarshe suka wuce fadar sarkin maskan Katsina hakimin Funtua, wanda da mahaifin kakansu ambasada da mahaifiyar hakimin yaya da ƙanwa ne, sannan hakimin shine mahaifin mommynsu Fahad. Duk in da suka je sun samu kyakkyawar tarba tare da nuna jin daɗin ziyarar ta Deen, sun yi hotuna tare da bashi lambobin yabo, shima kuma ya ba wasu kyautar jersey daga bisani suka dawo gida, nan da nan hotunan ziyarar tasa suka karaɗe shafukan sada zumunta, mutane na ta yabon halin kirkin Deen wasu kuma suna roƙon yaushe zai kawo masu ziyara suma. Bayan sallar isha su Salma na zaune a tsakar gida da yake yau bata yi awara ba, suna cin abinci da ita da innarsu da su Imrana, _"Duniyar nan sai da kuɗiii.. Allah Ka bamu kuɗɗiii...."_ Muryar Sagir ce ta karaɗe tsakar gida ya shigo yana rera waƙa, "Sallamar ke nan Sagir?" Innarsu ta tambaya, sai da ya zauna a bakin tudunkar baranda ya ce, "Bari innarmu, an gama tashin kaina ne qur'an, Allah dai ya yi mana arziƙi wllh dole tsiya ta ji kunya." Tana murmushi ta amsa da Amin Allah Ya bada arziƙin mai amfani, bayan ya amsa da Amin ya ce, "Wato wata arniyar mota ce Nuree Jnr ya faso da ita ɗazun, motar avatar ce wadda ake ma caji, wato innarmu sai kin ga motar nan...Innalillahi! Wallahi tallahi arziƙi ya yi, duk kuma wanda ya ce bai yi ba munafuki ne, idan ba aikin arziki ba an ce ɗazun nan aka kawo mashi motan, kuma wllh ta yi kusan miliyan ɗari." Da mamaki innarsu ta maimaita miliyan dari! Sagir ya gasgata mata haka ne. "Amman da ka ce caji ake mata kamar wai yadda ake ma waya caji?Sagir ya ce, "Eh mana, caji ake mata, dama ai an yi keke mai caji da mashin yanzu ga mota ma an yo." Imrana ya ce, "Innarmu bana baki labarin mashin mai caji ba wanda aka siya ma wani ɗan bokon mu, wllh nima ina son a siya mani irin mashin ɗin." Sagir ya ce, "Tabb, lallai yaro waye zai siya maka wannan mashin ɗin da ya yi kusan miliyan ɗaya, idan ba kuɗin shinkafar da ake siya mana muna ɗan yi ma talauci barazana kake son a tattare a siya maka ba." Tura masa baki Imrana ya yi, innarsu da ke murmushi ta ce Allah zai buɗa a siya masa, "Ka sha kuruminka Imrana, ka taya ni addu'a in sha Allah na zama nurse na fara aiki in dai ba a siya maka ba ko ya kai nawa ni zan siya maka." Kai ya ɗaga ma Salma da ta yi maganar, Sagir ya ce, "Sai ka ce zama nurse ɗin wata tsiya ake samu zaki wani cika ma mutane baki, ni zuwa lokacin in sha Allahu ai na sha kwana, irin mashin ɗin fin guda goma ma sai na siya masa, amman ko da ina da halin ma ba zan siya ba tun da ya iya yi ma mutane rashin kunya don uban shi." Wani kallo Imrana ya jefe masa bai dai ce komai ba, a haƙiƙance Salma ta ce wllh in dai har ta fara aiki matsayin nurse siyan wannan mashin ɗin ba zai gagare ta ba, innarsu dai nata bin su da murmushi sam basu gajiya da shan chapter. Bayan sallar isha Deen da Fahad suka fito da hajiya don su zaga gari a sabuwar motan, daga baya suka wuce gidansu Fahad, daidai lokacin da Deen ya faka motan a cikin gidan sai ga daddynsu da sauran yara maza sun dawo daga masallaci, cike da farin ciki yaran suka tarbi kakarsu haka ma daddynsu ya ji daɗin ganin mahaifiyar tasa sosai, bayan sun gama gaisawa hajiya na murmushi ta ce, "Sabuwar amarya Deeni ya yi shi ne aka fito da ni ɗani." Kai daddy ya jinjina gaba ɗaya idanunsu na akan motar tun bayan da suka shigo dama ta ja hankulansu, "Ma sha Allah son, motar ta yi kyau sosai. Kamar avatr ko?" Kafin Deen ya bashi amsa Khaleel ya yi saurin cewa ita ce, hajiya ta ce, "Ni ai ban ma san motan ba, sai yau na fara ganin irinta." Daddy na murmushi ya ce mata ba a daɗe da aka fara yayin ta ba a nan, hajiya ta sake cewa, "Yayin masu kuɗi ko, don na ji ba laifi motan akwai kuɗi, a haka ma Deeni ya ce wai ba mai kuɗi bace wannan sosai." Daddy ya ce amman ya san wannan bata rasa yin hundred million koma ta fi, hajiya ta ce kusan haka don miliyan tamanin da biyar Deeni ya ce ya siya, gaba ɗayansu suka jinjina kai, "Congrats bro, ta yi kyau sosai. Allah Ya tsare " Khaleel ya faɗa yana murmushi, Sadeeq ma ya ce, "Ya Deen Allah Ya sa alkhairi Ya tsare." Da murmushi ya amsa masu da Amin, Daddy ma ya yi mashi addu'ar Allah Ya sanya alkhairi ya tsare, Sadeeq ne ya ce bari ya je ya kira su mommy da yaya Sadeeya su zo su ga sabuwan motan yaya Deen ya ruga cikin gida, ba da jimawa ba sai ga su sun fito sun nufo wurinsu, da gudu Binafa ta nufi hajiya tana faɗin, "Oyoyo granny..." Tarbe ta hajiya ta yi tana murmushi ta ce, "Oyoyo ƙawalliyana..." Fuskar momy da murmushi ta yi mata sannu da zuwa, Sadeeya ta rungumo kafaɗar hajiya tana mata sannu da zuwa, "Wow, what a fabulous car!" Sadeeya ta faɗa bayan ta saki hajiya ta nufi motan tana kallo, "Kamar avatar ko?" Fahad ya bata amsa da ita ce, ta shiga shafa jikin motan tana zuba santi, momy dake murmushi ta ce, "Ma sha Allah son, motan ta matuƙar yin kyau sosai. Allah Ya sa alkhairi ya tsare ya ƙara arziƙi mai albarka." Duk aka amsa ma momy da Ameen, sakin hajiya Binafa ta yi tana kallon motan ta ce, "Ya Deen wannan motan mai kyau ka siya!" Kafin ya bata amsa hajiya ta ce ba tashi bace ta ta ce ta siya, wani kallo ta yi mata ta ce, "No na san ba taki bane, ai ke tsohuwa ce, ta yaya Deen ce." Jawo ta hajiya ta yi tana faɗin, "Zo nan ki gaya mini shi tsoho bai hawa mota mai kyau." Ta maƙe kafaɗa tana kyalkyala dariya haka sauran mutanen wurin, "Gaskiya yaron nan ka samu duniya!" Sadeeya ta faɗa tana murmushi tare da jinjina kai, "Lahira ma zai samu in sha Allah." Daddy ya faɗa duk suka amsa da in sha Allah, Deen ya ce ma Fahad ya yi testing nasu ya amsa da ok, Fahad ne ya shiga driver seat daddy na other side, baya Sadeeya da Khaleel da Sadeeq sai Binafa suka shiga suna ta santin tsaruwar cikin motar, cikin harabar gidan ya shiga zagayawa da su, Deen ya kira Fahad a waya ya ce mashi ya fita da su mana suka fita gate, after a while suka dawo itama mommy ta shiga aka zagaya da ita cikin harabar gidan, ba abun da suke sai yabo da son barka bayan sun gama ɗana motan, daga baya suka shiga cikin gidan, Fahad ya wuce part ɗinsa tare da Deen, a bakin gado Fahad ya zauna shi kuma Deen ya ɗan kishingiɗa tare da dafe forehead ɗinsa, Fahad na kallonsa ya ce ya gaji sosai ko don yau bai huta ba, yana murmushi ya bashi amsa da ai gajiyan ku san tare suka yi shi, "Yanzu zuwa wane lokaci ne za a yi launching club din?" Hannu Deen ya kai ya shafi sumar fuskarsa ya bashi amsa da shine yake son su zauna su tsara komai lokacin da yake da time, Fahad ya ce yana ganin ko zuwa gobe tun da ba aiki, Deen ya ce ok goben idan sun gama morning training zai zo, ya sake cewa "Ka ga da kaima kana harkan football sai ka zama manager ko kuma corch." Murmushi Fahad ya yi ya ce shi ai ba abun da ya haɗa shi da ƙwallo da dai abun da ya shafi bangaren lafiya ne, "Yauwa, ya maganar private hospital ɗin da kake so ka gina? Mun fara maganan baya..." Deen ya tambaya idonsa akan Fahad, gyara zama Fahad ya yi ya ce mashi maganan na nan yana son ya ƙara shiryawa ne sosai, "Amman already daddy ya baka plot so wani shiri yanzu ya rage?" With a smile on Fahad's face ya ce,"Kasan harkan gini yana bukatan a yi mishi shiri financially, idan ba haka ba sai ka ga abu ya zo yana delay." ɗan jinjina kai Deen ya yi alamar gamsuwa, sai kuma ya ce, "Idan wannan ne let's collaborate on it and get it done faster. Ka ga kai you provided the plot ni kuma sai in ɗauki nauyin aikin ginin" Wani kallo Fahad ya jefa masa sai koma ya janye fuskarsa gefe da ɗan murmushi, ya gama fahimtar Deen wato ya san idan ya nuna zai bashi kuɗi ba lalle ya amince ba shine ya 6ullo mashi ta hakan, kamar Deen ya san abun da ke a ran Fahad ya sake cewa, "Ka san nima I have the intention of building a hospital here, bari kawai mu yi amfani da wannan daman." Kallonsa Fahad ya yi da ɗan murmushi ya ce,"Amman ka san filin ba siya na yi ba?" Ɗan buɗa masa ido Deen ya yi ya ce, "But daddy ne ya baka,so ya zama naka ne ai." Fuskantarsa Fahad ya yi sosai, a nutse ya ce, "Deen, ka san aikin gini ba ƙananun kuɗi yake ci ba, ba kamar ginin asibiti dake buƙatan abubuwa da dama, ina ganin lissafin bai yi daidai ba a ce na bada fili kai kuma ka ɗauki nauyin ginawa." Ƴar dariya Deen ya yi don ya gane Fahad ɗin ya gane wayonsa, "Ba wani damuwa in sha Allah ba wani abu da zai gagara." Ya ƙare tare da ɗage ma Fahad gira, kafin ya ce wani abu aka yi sallama, "Assalamu Alaikuum..." Duk suka kai idanunsu kan kofan shigowa, Sadeeya ce ta nufo su tana murmushi, "Barkan ku da hutawa..." Deen ne ya yi mata murmushi tare da amsa mata, "Dama daddy ne ya ce a yi maku magana ku zo mu yi dinner." Fahad ya ce mata a kawo masu abincin nasu nan, ta ce,"Da hakan za a yi but sai daddy ya ce tun da duk an haɗu har da hajiya a yi dinner ɗin tare." Kai Fahad ya ɗaga, kallon Deen ta yi ta ce, "Gaskiya lil bru yakamata idan zan koma school ka fasa da ni a sabuwar motan can taka, na san zan tashi kan mutane over." Yana murmushi ya ce mata ta nemi lil bru ɗin nata sai ya kai ta, dariya ta yi ta ce, "To yaya Deen..." Shima yar dariyar ya yi kafin ya tambayi yaushe zata koma ta bashi amsa da ranar talata, ɗan jimm ya yi kafin ya ce ok zai duba yuwuwar hakan don yana da schedules ranan amman idan ma bai samu kai ta ba sai Fahad ya yi using motan su tafi tare idan zai je wurin aiki" Ta yi masa godiya tana murmushin jin daɗi, daga baya suka fita zuwa yin dinner din. Bayan an rako su za su koma gida, Fahad ya ce ma Deen akwai wani aiki da yake son yi a daren da sun tafi tare, Deen ya ce masa ba matsala gobe zai zo nan ya wuni su ƙara tattaunawa. Salma ta gama yin shirin bacci tana niyyar kwanciya saman gadonta wayar innarsu dake a hannunta ta fara yin ringing, duba mai kiran ta yi, murmushi ne ya bayyana akan fuskarta ganin sunan mai kiran, ɗauka ta yi ta kai wayar kunne a nutse ta fara magana, "Asslamu Alaikum..." Daga ɗayan 6angaren muryar mace ta amsa, "Wa'alaikumus salam, yaya Fiddausy barka da dare..." Yar dariya Salma ta yi ta ce, "Aunty Kubrah ba ita ba ce, baki gane muryata ba?" "Ahh..wllh sam ban ɗauki murya ba, da yake itama ba wata babban murya ne da ita ba, ashe babynah ce.." Tana murmushi ta amsa mata da eh, "Babynah ya kike? fatan kina lafiya." "Lafiya lau Autynah, ina wuni ya aiki." "Alhamdulillah, gani nan ban daɗe da dawowa ba ma, da yake evening na yi, gaba ɗaya na gaji yanzu nan na watsa ruwa gani nan na baje." Salma tana ƴar dariya ta ce, "Sannu Autynah.." Ta amsa mata da yauwa, "Bari in kai ma innar wayar..." Katse ta ta yi, "No ba sai kin kai mata ba, dama kiran naki ne ina son in ji muryan ƴar babynah ne.." Still da dariya akan fuskarta ta ce, "To na gode Autynah mai kaunata, ina missing en ki sosai.." "Allah Sarki my baby, in sha Allahu ai mun kusa mu kasanci a kusa da juna da zaran kin fara karatu a nan, yanayin aikin namu ne da mutum bashi da lokacin kansa sosai ina ta son nima in zo in gan ku...." Hira suka ci gaba da yi mai nuni da yadda suka damu da juna, daga baya ta tambayeta ko tana da wata matsala ta ce mata a'a, "Babynah na san halin ki sarai da nauyin baki, in baki sanar da ni buƙatunki ba to wa zaki sanar wa?" With a broad smile Salma ta ce, "Allah Aunty Kubra bani da wata buƙata, ko kuɗin da kika turo mani last time suna nan ban siya komai ba." Da alamun mamaki a muryar aunty Kubra ta ce, "Lahh..ke da na turo ma su don ki siya abun da kike so shine kike ta ajiyar su?" ta ce, "To ai Aunty Kubra ba wani abu da nike so yanzu." "Kina budurwa za ki ce ba abun da kike so, ina kika bar cosmetics? Su perfumes, roll on..." Cikin sigar shagwa6a Salma ta ce, "To ai Aunty Kubra duk ina da su fa cikin waɗanda kika aiko mani duk akwai saura." Salati Aunty Kubra ta saka, "Yau na bani..Salma ba dai jere kika yi da su ba baki using da su?" Da sauri ta ce mata wllh tana amfani da su, "To amman yakamata a ce by now sun ƙare ai, kuma dama abubuwa irin wannan wa ya ce maki bari ake har sai sun ƙare sannan a siyo wasu? Tun da products din ko da yaushe cikin yin su ake kala kala, yakamata mutum na bincikawa idan ya ji wani mai kyau da inganci sai ya yi trying nasu ya ga ko za su fi wanda yake using da kyau. Sannan su gyaran kai da jiki....wai ma Salma kina zuwa saloon kuwa?" Kame-kame ta shiga yi tana ɗan sosa ƙasan gashinta ta ce, "To ai ni Aunty Kubra kin san bani yin saloon." "Ina nufin kina zuwa wankin kai da su gyaran jiki, su lalle?" Ɗan zaro ido Salma ta yi ita yaushe rabon ta da yin wani lalle, kawai dai bata barin ƙumbunanta su yi fari fat, wankin kai kuwa dama sai idan ta je hutu Kaduna wurinta take kai ta amman a nan innarsu ke taya ta ta wanke "Kika yi shiru?" Amsa ta bata da a'a amman tana yin lalle sai dai ba akai akai ba, "To fisabilillahi baby kuma sai ki buɗe baki kina cewa ba abun da zaki da kuɗi? bacin duk ga abubuwan da ya kamata ace kina yi amman ba kya yi, ai an ce ko kana da kyau to ka ƙara da wanka, idan baki gyara kan ki sosai ta ya zaki samo mana surukin kirki? Ko so kike ki kwaso mana kwashikwaraf?" Tana ƴar dariya ta ce mata a'a. "To kuwa mace yanayin gyaranta yanayin mazan da za su rinƙa tunkararta. Daga yanzu karki ƙara wanke kanki a gida in ba so kike sumarki ta lalace ba, kina da gashi mai kyau tubarkallah, idan kina son ya ci gaba da bunƙasa to ba kowanne abu zaki na danƙara ma kanki ba wurin wanke shi, duk ƙarshen wata kije a yi maki wash and set da kuma ƙunshi, sai gyaran jiki ma duk bayan lokaci shima a rinƙa yi maki, zuwa da safe zan ƙaro maki kuɗi sai ki haɗa da wanda kika ce suna nan ki je a yi maki duk abun da na ce, har su kayan shafan ki je ki siyo ki daina jira sai sun ƙare, bari ma zan bincika maki skin care products masu kyau sai ki samo." Cike da jin daɗi Salma ta amsa mata da to tare da yi mata godiya, "Ba godiya zaki mani ba, ki tabbatar kin yi duk abun da na ce kin ji ni?" Kai ta daga, "Eh, in sha Allahu I will do as you instructed auntynah." Murmushi Aunty Kubra ta yi tare da faɗin, "That's my baby girl. Allah Ya ci gaba da raya mana ke ya ƙara yi ma rayuwarki albarka." "Amin Autynah, may Allah bless ur life too." Cike da jin daɗi aunty Kubra ta amsa mata, bayan sun ɗan ƙara yin hira daga baya suka yi sallama, Salma ta ajiye wayar gefe tana murmushin hirar tasu, don ma bata san cewa har yanzu tana yin awara ba ta san da sai ta yi mata faɗa, don tuni ta hana ta ta ce ta bar ma su Imrana suna yi to amman ita tana son yi, a ranta take raya Aunty Kubra tana matuƙar ƙaunarta ta san kuma don Allah bai ta6a bata haihuwa bane..... *_✨A CIKIN RAYUWA✨_* _New story from the writer of 'A Sanadin Makwabtaka',_ ZAINAB BATURE 21 Washe gari da safe Salma ta fito bayan ta gama yin shirin tafiya islamiyya, a bakin baranda ta tsaya tana yi ma innarsu sai ta dawo, fitowa innar ta yi tana murmushi ta ce, "Za a tafi?" Kai ta ɗaga mata alamar eh, da yake lokacin da suna yin karin kumallo Salma ta ba innarsu labarin wayar su da aunty Kubra jiya da daddare hakan ya sa innarsu ta ce, "Idan kika dawo sai in taya ki ki kwance kan ki je a wanke makin ko?" Ƴar dariya Salma ta yi ta ce to, sai kuma ta ce, "Ya maganar zuwa kasuwar? Ko ki bani kawai da an tashi sai in wuce ba sai na yi wahalar dawowa ba." ɗan jimm innarsu ta yi ta ce, "Ko dai a bari sai bayan kwana biyu sai a yi awaran?" Da sauri Salma ta ce, "A'a innar mu kawai ki kawo a siyo waken, shike nan don an bamu kuɗi sai mu daina yin sana'a? Ai kuɗin za su ƙare ko." Kai ta gyaɗa ta ce to bari ta bata, ɗaki ta koma bada daɗewa ba ta fito tana riƙe da kuɗi ta bata, bayan ta faɗi mata abubuwan da zata siyo ta ce mata sauran kuɗin ta yi amfani da su ta siya abun da take so, da sauri Salma ta ce, "A'a innarmu ki bar su, ai aunty Kubra ta ce zata turo mani kuɗi, ki yi amfani da waɗannan, na san ma duk a hidiman gida za su ƙare." Yar hararar wasa ta yi mata, "Ke ni ki amsa, na Kubra daban nawa daban, kuma bake kika samo mana su ba." Ƙin amsa ta yi tana noƙe kai tana ce mata ta bassu don Allah, Sagir ne ya shigo har zai nufi hanyar banɗaki ganin su ya fasa ya nufo su, "Wai Salma wasan da nike yi dake ne ya sa kika fara raina ni? Ya ina baki abu zaki ƙi amsa, kuma dama ba kin ce zaki siyo fara ba ki soya, to ba sai duk ki haɗa ki siyo ba." Innarsu ta faɗa da ɗan daure fuska, yamutsa fuska ta shiga yi tana marairaice mata tana faɗin ai tana da kuɗin da za ta siyo farar, "Ah lalle yarinyar nan gatan da kike samu ya yi yawa wllh, wato kuɗi ma ake baki kina ƙin amsa. Ni innarmu don Allah ki bani ina so..." Janye kuɗin ta yi ganin ya miƙo hannu ta ɗan ɗaure masa fuska, ya sake cewa, "pls innarmu wllh ina cikin buƙatan kuɗi, kuma dama baki bamu salalarmu ba a cikin kuɗin da Nuree jr ya bada." Wani kallo ta masa ta ce, "Ku da kuka ci gasan kana nufin baku samu komai ba a wurinsa?" "Ai ba a gama ba gaba ɗaya, na san sai daga ƙarshe zamu samu kyaututtuka." ta ce, "To amman wace buƙatan kuɗi ce da kai? ina bada daɗewa ba ka zo ka ce in cika maka kuɗi zaka siya sababbin kayan ƙwallo da takalma na ɗauka na baka? Bayan su wace buƙata ce kake da ita? Koda ka ga ina bata itama na daɗe rabon da in bata kuɗi ta siya abun buƙata kuma ba tambaya ta take ba." Ɗan sosa kai ya shiga yi ya ce mata shi dai don Allah ta bashi ba sai ta ji buƙatan ba, Salma ta ce, "Innarmu kar ki bashi, yanzun haka wannan Fa'izar zai kashe ma su, kuma wllh wahalar banza kake yi don wannan yarinyar ba samunta zaka yi ba, su da suna gama makaranta gidansu ake yi masu aure, kuma mate ɗita ce nan da shekara ɗaya zata gama, ko kana tunanin zaka iya aurenta zuwa lokacin?" Hannu ya ɗaga zai make ta innarsu ta dakatar da shi cikin ɗaga murya ta ce kada ya sake ya ta6a ta ai gaskiya ta faɗa, "Ni dai innarmu ki bani don Allah, ƙarya take mani don ni wannan yarinyar tuni ma na rabu da ita." Ta6e baki ta yi ta ciro dubu biyu ta miƙo masa ya amsa yana faɗin duka dubu biyu za a bashi, ta miƙo hannu tana faɗin, "Idan baka so to ka bani abu na, duk kuɗin ba a hidiman gida za su ƙare ba, babanku ma na bashi wasu a ciki." Tura kuɗin ya yi cikin aljihun wandonsa, ya kalli Salma cikin ɗaure fuska ya ce, "Munafuka yar hana ruwa gudu kawai, wllh saboda mugun halin ki har na fara ji na ƙosa ki yi aure ki bar gidan nan." Tana dariya ta ce, "Ka sha kuruminka man Sagir, bada jimawa ba ma ai zan tafi makaranta Kaduna." Yana hararanta ya ce, "Ai wannan still ba hutawa muka yi ba tun da za a rinka yi maki buƙatu kuma za ki rinƙa dawowa, amman idan kika yi aure shike nan ba ruwan mu da ke, duk nauyin ki ya koma kan mijinki sai kuma in kin kawo ziyara." Ɗan girgiza kai Salma ta shiga yi tana ɗan murmushi ta ce, "Allah Sarki Sagir, ka ga ni har zullumin abun da zai saka in rabu da ku nike yi, ba komai, amman ka rubuta ka ajiye wallahi duk ranar da na bar gidan nan da sunan aure sai ka yi kuka da idanunka." Tsoki ya buga ya nufi hanyar banɗaki yana faɗin Allah ya kyauta ya yi kuka don sun rabu da ƙaya, innarsu dake murmushi ta ce mata ta rabu da shi, da ƙyar Salma ta amsa kuɗin amman sai da ta rage ta mayar mata da wasu suka yi sallama ta tafi. Wararen ƙarfe sha biyu saura Salma ta nufi kasuwa bayan ta taso daga islamiyya, a nutse take tafiya a gefen hanya tana sanye da dogon hijab ɗin islamiyyarta, daidai lokacin da ta zo ƙarshen hanyar zata hau babban titi ta hango mota na tahowa ta hanyar da take, hakan ya sa ta dakata don motan ta wuce, lokacin da motar ta ƙaraso saitin ta sam Salma ta kasa ɗauke idanunta akan motar, bama ita kaɗai ba duk idanun mutane na akan motan, hatta waɗanda ke a saman ababen hawa kallon motar suke, a cikin rai Salma ke faɗin, "Wannan wata irin mota ce! Amman dai ta haɗu sosai...." Ita tun da take ma bata ta6a ganin mota irinta ba, ɗan gaba da ita motan ta tsaya da alama mai motan na jiran ababen hawa su gama wucewa ne ya hau kan babban titin, sam ba a ganin wanda ke a ciki hakan ya ɗarsa ma mutane mamakin waye mamallakin haɗaɗɗar motar wadda mafiya yawan mutanen garin basu ta6a ganin irinta ba, a maimakon motar ta tsallaka sai gani Salma ta yi ta ɗan yo baya hakan ya sa ta yi saurin ƙara matsawa gefe don ta ba motan wuri, sai da aka ɗan ɗauki lokaci sannan glass ɗin ta ya fara sauka ƙasa a hankali, bugawa ƙirjin Salma ya yi damm! lokacin da idanunta suka yi tozali da wanda ke a mazaunin driver, nan take ta dabarbarce ta shiga motsa baki don bata yi zaton shi zata gani ba, kallonta ya yi suka haɗa ido ta shiga kikkafta nata, da kai ya yi mata alamar ta zo, tamkar wadda babu laka a jikinta haka ta ɗan matsa sai dai bata yadda ta yi saiti da shi ba, "Ina..kwa...wuni." Ta faɗa cikin dabarbarcewa, kai ya ɗaga kawai ta sunnar da kanta ƙasa, kamar ba zai yi magana ba sai kuma ta ji ya ce, "Where are you going to?" Da sauri ta ɗago ta kalle shi sai ka ce bashi ya yi maganar ba, da ƴar rawar murya ta ce, "Kasuwa aka aike ni..." Shiru ya ɗan yi tare da ɗauke idanunsa, ƙasa-ƙasa ta ji ya ce, "Get in to the car.." Ta wani zaro ido sai ka ce wadda aka faɗa ma wani mugun abu, kokonto ta shiga yi na abun da ta ji ya faɗa haka ne ko kuwa dai kunnuwanta ne suka jiye mata ba daidai ba, after some seconds ya yi mata wani kallo ya ce, "Baki ji maganan da na yi ba?" Da sauri ta ce, "Cewa ka yi in shigo motan?" Kai ya ɗan ɗaga mata alamar yes, sumi-sumi ta zagayo ɗaya bangaren, sai da ta ɗan yi tunanin ina zata shiga tsakanin gaba da baya, ƙofar baya ta buɗe kafin ta shiga ta ɗan ɗago ta kalli mutanan dake a area ɗin, sai da gabanta ya ƙara bugu ganin gaba ɗaya idanun mutanen wurin na a kan ta, ruɗewa ta yi da ganin yadda ake kallonta da sauri ta kama handle ɗin ta ja ya buɗe ta shiga bugun ƙirjinta na ƙara tsananta tamkar wadda ta aikata wani laifi, wani irin ni'imtaccen sanyi ne tare da ƙamshi mai kwantar da zuciya suka tarbe ta, bin cikin motan ta yi da kallo at the same time al'ajabi ya bayyana akan fuskarta, ita dai ko a film bata ta6a ganin mota haka ba balle a zahiri, ɗaga kanta ta yi sama ta ɗan waro idanu ganin yadda take ganin kanta tamkar tana kallon madubi, tana cikin kalle-kallen ta sauke idanunta a kan madubin gaban motan karaf suka haɗa ido, da sauri ta sunne kanta ƙasa cike da jin kunya, duk yadda Salma ta so ta kama kanta ta kasa a hankali take ci gaba da bin cikin motan da kallo, tafiya suke suwet kamar ba a mota ba don ba wata ƙara ko irin gumin cikin mota da zaka ji wani lokacin haɗe da warin fetir, sauke idanunta ta yi akan screen ɗin da ke a kusa da sitiyarin motan, wani sabon mamakin ne ya kamata ganin duk abun da ke faruwa a bayansu ana gani ta cikinsa kamar vedio, "I don't know the place, zaki nuna mani..." Da sauri ta kai idanunta kansa jin ya yi magana sai dai bata ji abun da ya faɗa ba, daga yanayin kallon da ya ga tana mashi ta cikin madubi ya gane bata fahimci mi ya ce ba, haɗa ido suka yi ta madubin calmly ya sake faɗar abun da ya faɗa ta ɗaga mashi kai alamar toh, tafiya kaɗan suka ƙara suka zo roundabout, da sauri ta ce mashi da an ɗan wuce round ɗin ne wurin, bayan ya yi parking ya bi wurin da kallo, hannu ta kai za ta buɗe kofar saidai in da ta yi tunanin nan ne ake buɗewar ta ta6a amman kofan ta ki ta buɗe, juyowa ta yi da niyyar yi masa magana daidai lokacin shima ya juyo idanunsa suka shiga cikin nata ya ce mata, "But nan kasuwa ne?" Kikkafta idanu ta shiga yi ta ce, "A'a, amman da na ɗan ƙara gaba kasuwan take, a zagaye take mota bata shiga sai dai a aje a bakin hanya." nodding kai ya yi tare da juyawa, ganin bai gane ta kasa buɗe kofar ba ya sa innocently ta ce, "Ban san ya zan buɗe kofar ba..." Haɗa ido suka yi ta mirror ta yi saurin sunnar da kai, bata san ina ya ta6a ba kawai ta ji kofar ta yi wani ɗan sauti har sai da ta ɗan tsorata ta yi saurin kallon ƙofar ta ganta a buɗe, har zata fita ta juyo a hankali ta ce, "Na gode.." Kai ya ɗaga ba tare da ya kalle ta ba, tsaye ta yi bayan ta fito tana kallon motar ya ja ya tafi, sai da motar ta 6ace ma ganinta sannan ta ankare da irin kallon da mutane suke yi mata, da sauri ta juya ta fara tafiya ta gefen hanya, yayin da a cikin ranta take ta jinjina haɗuwar motar, ta raya a zuciyarta ba tantama ita ce motar da Sagir ya zo yana masu santi, ita cikin motar ya fi yi mata kama da irin cikin private jirgi da take ganin hoto , "Anya ba jirgi bane aka yi da suffar mota?" ta yi tambayar a ranta, ƙarshe zuciyarta ta yanke hukunci da alama ma hakan ne, maida akalar tunaninta ta yi kan yadda akai har ya ganta ya gane ta ya tsaya ya ɗauke ta, tunowa ta yi da screen ɗin nan dake nuna mashi komai dake faruwa a bayan shi ta raya ta san ta hakan ne ya ganta, tana ta tunane tunane har ta iso kasuwar. Bayan Deen ya isa gidansu Fahad ya yi parking motan, kai tsaye cikin gidan ya nufa, Sadeeya na zaune tana latsa waya ta hango shi ya shigo, miƙewa ta yi tana murmushi ta nufe shi tana masa welcome, hannunta ya kama bayan ya amsa suka dawo wurin kujerun, Khaleel dake kwance shima yana latsa waya ya miƙe zaune da murmushi ya ce, "Ya Deen sannu da zuwa." Da murmushi ya amsa mashi yana kokarin zama a saman 2 sitter Sadeeya ma ta zauna gefensa, tambayar su Binafa ya yi Sadeeya ta bashi amsa da suna islamiyya sai yamma, momy ce ta ƙaraso wurin su da fara'a ta ce, "Son, an shigo." Amsa mata ya yi kafin ya gaishe ta ta amsa tare da zama, "Ya hajiya da gajiyan ɗanin mota." Yana murmushi ya bata amsa da tana gida tana gaishe su, "Da jigunannar motar ka zo?" Sadeeya ta tambaya, ƴar dariya ya yi jin yadda ta kira motan ya ce mata eh, miƙewa ta yi tana faɗin bari ta je ta yi hotuna dama jiya don dare ne ya sa bata yi ba, miƙa mata makullan motan ya yi ta amsa da sauri tare da faɗin yauwa ta gode, kallon Khaleel ta yi ta ce ya zo su je ya yi mata hotunan ya amsa da toh tare da miƙewa, "Kafin ki tafi yin packaging ɗin ki fara samo mashi abun da zai ci." Momy ta faɗa tana murmushi, Sadeeya ta yi dariya tare da faɗin, "Kai momy, ai ba packaging bane tun da dai motan mallakinmu ce." Kallon Deen dake murmushi ta yi ta ce breakfast zata haɗo mashi kafin a gama abinci, ya ce mata no baya jin yunwa ya yi breakfast, ta ce to bari ta kawo mashi ko lemu shima ya ce ta basshi ta je, momy ta ce, "Son ka bari ta kawo maka wani abu mana kafin a ƙarasa abincin." Calmly ya ce mata yanzu baya jin yunwa a bari sai an gama abincin ta amsa da ok, bayan tafiyar su Sadeeya ya tambayi momy ko daddy na nan ya je ya gaishe shi, ta ce, "Eh yana nan, suna tare ma da Fahad a can part ɗin sa ina tunanin wani aikin suke yi." Miƙewa ya yi ya ce bari ya je part ɗin ya gaishe da shi ta amsa masa da ok, bin shi da kallo momy ta yi bayan ya nufi bangaren daddyn fuskarta da murmushi, tana son yaron saboda yana da hankali da natsuwa, duk da irin ɗaukakar da ya samu sam bai yada nasa ba ko ya canza masu, sam bai ɗauko ɗaya daga cikin halayen mahaifiyarsa ba, ta6e baki momy ta yi tunowa da irin munanan halayen mom Jameela, ba don ita ɗin tana da kyakkyawar zuciya ba ai ko kallon Deen ba zata yi ba balle ma ya ga murmushinta duba da yadda mahaifiyarsa ta yi maltreating mata yaro lokacin da yana wurin su. Da sallama Deen ya shiga falon daddy, a tare suka kai idanunsu kan ƙofa, da murmushi suka amsa masa ya ƙarasa ciki, daddy na zaune a saman kujera mai mazaunin mutum biyu, Fahad na zaune daga gefensa a saman carpet, system ce a gaban Fahad da wasu takardu a gefe, "Barka da zuwa son." Daddy ya faɗa idonsa akan Deen da ya zauna a ƙasa gefen Fahad, da murmushi ya ce, "Yauwa daddy, ina wuni." Amsa mashi ya yi ya tambayi hajiyarsa, kallonsa Fahad ya yi yana murmushi ya ce, "Sannu da zuwa..." Ya ɗaga masa kai, bayan shiru na ɗan lokaci dad ya kalli Fahad ya ce, "Ka ce gaba ɗaya lissafin ya kama nawa?" amsa ya bashi ya ce, "Abun da ya bada 135m." Kai daddy ya jinjina sai kuma ya ce, "Ka saka har da na waɗanccan kayan da na fada maka?" Kai Fahad ya jinjina ya ce yes, daddy ya jinjina kai tare da komawa ya jingina bayansa da jikin kujera yana murmushin sa na dattako ya ce, "Alhamdulillah, saura mu ga abun da kuma wannan damunar zata kawo mana. Allah Ya saka mata albarka." A tare Deen da Fahad suka amsa da Ameen. "Son, ka zo muna ta lissafi, haka hanyar samun namu ya koma tun da yanzu ba aikin gwamnati, wannan ne ya koma aikin office ɗin nawa." Ya ƙarasa yana ƴar dariya, shima Deen faffaɗan murmushi ne akan fuskarsa ya ce, "Allah Ya ƙara sama nema albarka daddy." ya ce, "Amin my son, Ya saka ma nemanmu baki ɗaya. Dama haka abun yake kowa da kalar hanyar samun sa, ga ɗan'uwanka nan shi rashin lafiyar mutane ne tasa hanyar samun, sa6anin kai kuma nishaɗin mutane ne naka hanyar samun." Gaba ɗaya faffaɗan murmushi ne akan fuskokinsu, "Kasuwanci yana da daɗi sosai, musamman idan Allah Ya riƙe maka, ba don kasuwancin nan da muke yi ba watakil yanzu abun da muke samu matsayin pension ba lalle ya iya riƙe mana iyali ba a yadda rayuwar ta yi tsada..." Ya ɗan dakata su Deen suka jinjina kai alamar tabbatar da gaskiya ne zancensa, ya ci gaba da cewa, "Shi ya sa yana da kyau bayan aikin gwamnati mutum ya samu wata kasuwa yana yi, hakan na da amfani sosai musamman a lokacin da ba aikin. Idan kuma kasuwancin kaɗai mutum ke yi yana da kyau ya bullo da wasu hanyoyi da dubaru da za su inganta sana'ar tasa, ya zama a koda yaushe ana tafiya da shi...." Dakatawa ya sake yi yana shafa sumar gemunsa dake haɗe da ƴar furfura, "Son, na san bayan tamolan baka rasa wata kasuwar da kake yi ko, kamar yadda na ga yawancin yan ƙwallo zaka ga suna wasu kasuwancin daban-daban." Deen ya ɗaga kai with calmness ya ce,"Yes daddy, ina da hannayen jari da wasu kamfuna daban-daban, sannan akwai wasu hanyoyin da muke samu da so da yawa." Kai daddy ya jinjina, "Ma sha Allah..." Gyara zama Deen ya yi ya ce, "Daddy idan ba damuwa dama ina son neman shawara a wurin ka." Ɗagowa daddy ya yi ya fuskance shi da kyau ya ce, "To Allah Ya bani ikon baka mai amfani." Amsawa ya yi da Amin kafin ya ce, "Ina son buɗe company ne a nan, shi ne nike son ka bani shawara abun da kake ganin zai samu kar6uwa kuma zai kawo ma mutane sauƙi." Jinjina kai daddy ya yi tare da yin shiru alamar yana nazari, after few minutes ya gyara zamansa tare da ɗan yin gyaran murya ya ce, "To a ganina cikin abubuwan da za su samu karbuwa idan aka bude companyn su akwai abinci, wato kamfanin da ya danganci sarrafa kayan abinci tunda shi wannan ba shi da wani lokaci da za a ce ba a tafiya da shi, saboda abinci abu ne wanda ake buƙatarsa sosai a koda yaushe. Sannan buɗe company da ya danganci abinci a nan za a samu sauƙin tafiyar da shi duba da yadda muke da albarkar noma a nan, akwai kamfuna da dama dake sarrafa abinci ciki da wajen nijeriya waɗanda a nan suke siyan kayan da suke sarrafawa. Ka ga dama an ce wai da arziƙi a garin wasu gara a naku, a nakun ma a cikin gidanku, idan namu ya buɗe kamfanin ai ba buƙatar siyar ma wasu kayan amfanin gona ke nan." Gaba ɗaya suka yi ƴar dariya, bayan shiru na ɗan lokaci ya ci gaba, "Sai abu na biyu da nike tunanin idan aka buɗe kamfaninsa zai samu kar6uwa shine kamar textile ko kayan sakawa, ka ga mu nan a arewa bamu da kamfuna irin haka, yawanci a kudu ake da su wasu kayan ma masu inganci sai dai a shigo mana da su daga ƙasar waje, kuma ka ga suma yawancin abubuwan da suke sarrafawar wasu duk a nan suke samun su, kamar auduga da sauransu. To ina ga cikin waɗannan biyun duk wanda aka yi zai samu karbuwa, kuma zai kawo sauƙi da ci gaba a arewa." Kai Deen ya jinjina alamar gamsuwa, Daddy ya ce "Sai ka natsu ka ga wanda ya yi maka, wanda kuma nauyin aljihunka ko in ce account ɗin ka zai iya yi." Ya ƙarasa yana ƴar dariya, Deen yana kallon daddyn da murmushi ya ce, "Zan duba duka in sha Allah." Dan waro ido daddy ya yi ya ce, "Duka son...!Hakan ba ƙaramin shiri yake buƙata ba musamman na kuɗi." Still da murmushi a fuskarsa ya ce, "In sha Allah ba zai gagara ba, ko ba duka ba a lokaci guda." Jinjina kai daddy ya yi, "Ma sha Allah, Allah Ya taimaka Ya tabbatar da hakan. In sha Allahu nima ba za a barni a baya ba zan bada duk wata gudunmawa domin tabbatuwar hakan idan Allah Ya nuna mana, kuma muna daga cikin masu saka hannayen jari, tun da muka ma saka ma wasu balle namu." Duk murmushi ne akan faces ɗin su, Deen ya dan rankwafar da kai ya ce, "Thank you daddy..." "Fahad kai ya maganar ginin asibitin naka?" Kallon daddy ya yi da murmushi ya ce, "Tana nan daddy, dama na bari in shirya sosai yadda aikin ba zai delay ba idan aka fara, but...jiya Deen ya ce we should collaborate on it." Kallon Deen ya yi ya ce, "Haka ne son?" Kai ya jinjina ya ce eh, daddy ya ce, "Hakan ya yi kyau, amman ka fara tuntu6ar iyayenka kan hakan." Shiru Deen ya ɗan yi a ransa yana raya ya san ko da mahaifinsa ya amince to mom ɗinsa ba zata ta6a amincewa da hakan ba, kallon daddy ya yi ya ce, "Daddy tun da kai ka sani ai duk ɗaya ne." Murmushinsa na dattako ya yi mai nuni da jin daɗin maganar Deen ya ce, "Duk da haka son, suma suna da hakkin ka sanar masu ko don ka samu sakawar albarkar su." Amsa masa ya yi da toh, kamar daddy ya san abun da Deen ya saƙa a ransa ya sake cewa, "Ka sanar da su before a fara gudanar da aikin don ka ji miye ra'ayin su a kai." Shiru Deen ya ɗan yi don a yadda ya yanke kawai sai bayan an gama gaba ɗaya aikin asibitin zai sanar da su, slowly ya furta"Okay daddy." "Allah Ya ƙara saka albarka a dukkanin abun da muka sa a gaba, nima da na ce ma Fahad filin da na bashi matsayin bashi ne idan komai ya kammala aiki ya kankama zai biya ni koda a hankali, a yanzu na janye batun bashin na mallaka maku shi kyauta matsayin tawa gudunmawar, sai ku yi haɗin gwiwa wurin aikin ginin, zuwa a kammala mu gani idan da gudunmawar da zamu ƙara baku." A tare suka haɗa baki wurin yi masa godiya da adduar Allah Ya ƙara girma da lafiya, bayan ya tambaye su ko akwai wani abu duk suka ce masa a'a ya sallame su, bin su da kallo ya yi yayin da suka nufi ƙofa, a ransa yana matuƙar jin daɗin haɗin kan su, suna tuna masa lokacin da suna matasa shi da mahaifin Deen, haka suke kansu a haɗe yake komai za su yi sai sun tambayi shawaran juna, sa6anin yanzu da komai ya canza a tsakanin su, duk da daddyn bai bari hakan ya zame masa damuwa ba, ya saka a ransa cewa kowa yana da iyalin da zai iya yin shawara da su. Bayan sun baro part ɗin daddy upstairs suka nufa zuwa part ɗin Fahad, suna fara taka staircases Sadeeya da ta shigo cikin falon ta kira sunan Deen, hakan ya sa shi dakatawa yana jiran ta ƙaraso, tana washe baki ta miƙa masa wayarta ta ce, "Duba ka gani don Allah yadda hotunan suka ɗauko, kuma packaging ɗin nawa ya yi, motan ta hau da ni sosai Allah..." Ta ƙarasa maganar tana dariya, Kallon hotunan ya shiga yi yana murmushi, da gaske sun yi kyau dama ga wayan tata iphone ce, bayan ya gama kalla ya ce, "Yakamata ai snapping naki ai kina driving yadda za a fi yarda naki ne." Ya faɗa yana ƴar dariya, ɗan waro ido ta yi ta ce bata yi gigin hakan ba don gani take kaman ba zata iya driving motan ba, miƙa mata wayan ya yi ya ce lafiya lau zata iya tuƙa ta mana ba ta iya driving ba, ta ce a'a gara dai idan ya fara nuna mata, ci gaba da hawa matattakalar ya yi yana faɗin ok idan ya fito zai nuna mata lokacin tuni Fahad ya wuce ya bi bayansa..... *_✨A CIKIN RAYUWA✨_* _New story from the writer of 'A Sanadin Makwabtaka',_ _ZAINAB BATURE_ _Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._ 22 Bayan sallar issha su Imrana na a ƙofar gida wurin tuyan awara shi da Hamza, ƙamshin da ya cika ma Imrana hanci ne ya sa shi saurin ɗagowa don ya gane irin ƙamshin mutumin da ya zo rannan har ya basu kuɗi ne, aikuwa shi ɗin ya hango a tsaye ɗan gaba da su, da sauri ya miƙe ya nufe shi ya tsaya daga gaban shi ya ce, "Ina wuni, awaran za a baka?" Kai Deen ya ɗan jinjina masa yana kallon sa yau ma fuskarsa na rufe da nose mask, "To ta nawa za a baka?" Imrana ya tambaya, shiru ya yi bai ce masa komai ba, ganin haka ya sa Imrana cewa, "Ko in kira maka yaya Salma?" Sai lokacin ya ɗan girgiza masa kai, hannu ya kai cikin aljihun wandon jeans din sa ya fiddo kuɗi ya miƙa masa, da sauri Imrana ya miƙo hannu har da ɗan kakka6e su kafin ya amsa, waro ido ya yi ganin kuɗin masu yawa, a ɗan ruɗe ya ce, "Ai awaran bata kai ta wannan uban kuɗin ba, duka ma wadda ta rage bata wuce ta dubu ɗaya ba fa." Har sai da ya sa Deen yin murmushi ta cikin mask ɗin ganin reaction din da fuskarsa ta nuna, hannu ya kai ya ɗan zame mask ɗin calmly ya ce masa ya kai kuɗin gida awaran da ta rage a raba ma mutane, da sauri ya amsa da to ya juya zan nufi gida, daidai nan Salma ta fito tana ƙwala ma Imrana kira jikinta sanye da doguwar rigar atamfa ta yafa ƙaramin gyale a kai, da ƴar sassarfa ya nufe ta sam bata lura da Deen ba, yana zuwa gaban ta ya miƙa mata kuɗin ya ce, "Yaya Salma kin gani wannan mutumin da ya zo shekaran jiya ne ya sake dawowa ya bada wannan kuɗin ya ce in kai gida, kuma a raba ma mutane awaran da ta rage." Har sai da gabanta ya faɗi jin abun da ya ce, da sauri ta tambaye shi ina mutumin yake ya juya yana nuna mata Deen da har ya juya ya fara tafiya, bin shi da kallo ta yi a ranta tana mamakin yadda yau ma ya dawo ya basu kuɗi, haka nan sai kuma bata ji daɗin zuwan da ya yi ya iske suna yin awaran ba, wani tunani ne ya zo mata a rai da sauri ta bi bayan shi, tunanin yadda zata tsayar da shi ta yi don bai ma san ta biyo bayansa ba, "Ya Deen..." Kawai sai ji ta yi ta kira sunansa da ɗan ɗaga murya ba tare da ta shirya ma hakan ba, cak ta tsaya ganin ya dakata tare da juyowa, slowly ta ɗan matsa kamar mai tsoron ƙarasawa gaban sa, jim ya ɗan yi yana kallonta kafin ya kai hannu ya zame mask ɗin fuskarsa, da yake akwai wutar nepa wasu gidajen layin suna da hasken globe a gaban su hakan ya sa suna iya ganin fuskokin juna ta hasken da ya ɗan haska, tana kikkafta idanu ta ce, "Ina wuni.." Kai ya jinjina sai kuma ta ji ya ce, "How are u?" Ta amsa da, "Lafiya lau," Kai ya ƙara jinjinawa suka ɗan yi shiru, wani irin ƙwarjini yake mata hakan ya sa ta rasa mi zata ce masa, "Any problem?" Ta ji ya sake tambaya, cikin ƴar in ina ta ce, "Dama yanzu ƙanina ya nuna mani kuɗi ya ce kai ka bashi ya kai gida..." Ya ɗaga mata kai alamar eh, "An gode Allah Ya saka da alkhairi....da innarmu ma ta ce kada a yi awaran yau, dama jiya bamu yi ba saboda wanccan kuɗin da ka bamu, ni ce na ce mata ai da ka bamu kuɗin ba cewa ka yi mu daina yin awaran ba..ita bata so a yi ba ni ce na nuna ina so a yi.." Cike da kama kai ta yi maganar ita kanta bata ma san miye amfanin yin wannan maganan ba, ɗan murmushi ta ga ya yi calmly ya ce, "Yea, ba don ku daina bane, it's just a gift." Ɗaga kai ta yi itama yanayin fuskarta kaman zata yi murmushi ta sake cewa, "Mun gode Allah Ya ƙara buɗi na alkhairi." "Ameen.." Ya amsa ƙasa-ƙasa, shiru suka ɗan ƙara yi kafin ta ji ya ce shike nan zai iya tafiya, da sauri ta ɗaga masa kai daga haka ya juya yana ƙoƙarin mayar da mask din, har zai fara tafiya da sauri ta ce, "Ko in zubo maka awaran?" Juyowa ya yi ya kalle ta ya girgiza mata kai ta cikin mask ɗin ta ji ya ce, "Thank you." daga haka ya juya ya ci gaba da tafiya cike da natsuwa, tsaye ta yi a wurin tana ta kallon sa a cikin ranta ba ƙaramin mamaki yake bata ba, juyawa ta yi bayan ta ga ya tsallaka hanya ta nufi gida, tana shiga ta ga innarsu a tsaye a bakin baranda tana riƙe da kuɗin da alama shigowar ta dama take jira, a sanyaye Salma ta ƙarasa wurinta, da alamun mamaki ta ce, "Salma ashe yau ma zuwa ya yi ya bada kuɗin kuma kamar na shekaran jiya yauma dubu ɗari biyu ne." Kai Salma ta ɗaga ta ce, "Nima ina fita Imrana ya nuna mani lokacin bai daɗe da ya bashi kuɗin ba don bai ma kai ga barin wurin ba, shi ne na bi bayansa na yi masa godiya." Shiru innarsu ta ɗan yi kafin ta ce,"Duk sai na ji wani iri wllh, kada a ce ganin ana yin awaran ne ya sa shi sake zuwa ya bada kuɗin." Itama Salma da irin tunanin a cikin ranta, sai kuma ta ce, "Ai bayan na yi masa godiyar sai da na faɗa masa baki so a yi awaran bama ni ce na ce da ya bamu kuɗin bai ce kada mu yi sana'ar ba, shi ne sai ya ce eh kawai matsayin kyauta ne ya bamu." Jinjina kai innarsu ta yi har ta ɗan ji hankalinta ya kwanta, "An gode Allah Ya saka masa da mafificin alkhairi. Gaskiya mutumin yana da kirki ba kaɗan ba kuma bashi da girman kai wllh, Allah Ya kara masa ɗaukaka." Salma ta amsa da Amin, "Inna yanzu a je a rabar da awaran?" Imrana ya tambaya, da sauri ta bashi amsa da eh, kallon Salma ta yi ta ce, "To shi bai son awaran? Na ji hajiya ta ce kaman yana son ta." Salma ta ce, "Ai sai da na tambaye shi in zubo masa awaran ya ce a'a." Ƴar dariya innarsu ta yi, ta ce, "In ban da abun ki Salma ta ya zaki tambaye sa haka, a tunanin ki zaki zubo masa abu ne ya riƙe ya tafi da shi?" Shiru ta yi tana ɗan murmushi itama sai yanzu ta gane shirmen da ta yi, "Yanzu kina ganin ko a haɗa masa sai ki je ki kai masa?" Kai ta ɗaga ta ce eh, "To yi sauri ki je ki ga idan Imrana bai ƙarasa soya ɗanyan da ta rage ba sai ki ɗebo nan mu haɗa masa da kan mu, dama akwai sauran cefane sai a yi masa yar sauce ko?" Da sauri Salma ta ce eh ta nufi hanyar fita, without wasting time suka shiga haɗa masa awaran ita da innarsu, suna cikin yin aikin ne Salma ta roƙi innarsu idan zai yuwu a cikin kuɗin da aka ƙara basu a bada a yi ma su Habu ɗinkin makaranta ko da ba su duka ba tun da suna da yawa, murmushi ne akan fuskar innarsu ta ce mata kamar ta shiga zuciyarta itama hakan ya zo mata a rai, idan babansu ya dawo zata yi mashi maganar sai a ga abun da za a ba su ya ba baban su Habu ɗin a siya masu kayan makarantar, hakan ba ƙaramin daɗi ya yi ma Salma ba. Ba tare da an ɗauki lokaci ba suka kammala, awara mai ƙwai da sauce suka haɗa gwanin kyau a ido sai ƙamshi ke tashi, har da ɗan coleslaw suka haɗa dama suna da mayonnaise, suna gamawa Salma ta je ta canza kaya duk da yau bata zauna sosai wurin tuyan awaran ba duk Imrana ne ya yi amman saboda aikin awaran da suka gama ya sa take ganin kaman kayan jikinta sun yi dauɗa, doguwar rigar material mai mayafi ta sako wanda kayan na daga cikin irin waɗanda auntynta Kubra ke aiko mata daga Kaduna, har da turare ta ɗan faffesa duk don ta fito fess yadda Deen ɗin zai ci awaran, don a yadda yake ta tabbatar ba zai rasa ƙyanƙyami ba, bayan ta fito innarsu ta fiddo mata da awaran da aka zuba a cikin wata ƴar madaidaiciyar kula mai kyau, daga cikinta akwai irin yar farar roba mai marfi a nan aka zuba sauce ɗin, sai coleslaw ɗin aka sa a cikin wata ƴar farar roba irin ta takeaway ana ganin abun da ke a ciki, "To a ina kike ganin za a saka kayan?" Innarsu ta tambaya tana kallonta, "A cikin leda ko?" Salma ta faɗa, "Amman kina ganin lafiya lau a saka a leda? Na ga su ƴan gayu zaki ga a ɗan kwando suke saka kayan abinci." Dariya maganar ta ba Salma ta ce, "To ai mu ba ƴan gayun bane bamu da kwandon, in dai ba a cikin riyon Usman za a saka ba matsayin kwandon..." Dariya ta saka kafin ta gama maganar ganin irin kallon da innar tasu take jefa mata, ta ce, "Ta ya za a saka kayan abinci a cikin riyo in banda abun ki, ai sai ma ya kasa cin abincin." Still dariya Salma take yi ta ce, "To kema innarmu tun da kin san babu kwandon kawai a saka a ledan mana ai ba wani abu bane." Amsa mata ta yi da to ta ce tana zuwa ta nufi hanyar ɗakinta da sauri, fitowa ta yi hannunta riƙe da wata farar leda mai ƙauri irin ta siyayya ta nufo Salma tana faɗin, "Ina ganin zai fi a saka a wannan ledan, dama ganin mai kyau ce yasa na 6oye ta." Kai Salma ta ɗaga, bayan an gama saka kayan ta ɗauka tana faɗin sai ta dawo, innarsu ta ce mata to, lokacin da ta kai bakin soro tana niyyar fita innar ta ɗan ɗaga murya ta ce, "Ki faɗa ma hajiya a yi mana godiya ya bamu kuɗi." Ta amsa mata da to daga haka ta fice. Hajiya zaune a falo ta kara waya a kunnanta tana waya fuskarta ɗauke da fara'a, da sallama Salma ta shigo cikin falon, bayan ta ƙarasa ciki ta tsaya ɗan gefe da hajiyan tana jiran ta gama wayan, bata daɗe da shigowa ba hajiya ta kammala yin wayar bayan ta ajiye a gefenta ta ɗago ta kalli Salma, da murmushi ta ce, "Salma ce..." Ta amsa mata, "Eh, ina wuni hajiya." Bayan ta amsa ta nuna mata kujera ta ce ga wuri ta zauna, zama ta yi ta ɗan yi shiru haka nan sai ta ji nauyin yadda zata faɗi abun da ya kawo ta, "Ya maman taku da ƴan'uwanki?" Da ɗan murmushi ta kalli hajiyan ta ce mata duk suna nan lafiya lau, hajiya ta ce, "Ma sha Allah." Shiru suka ɗan ƙara yi idon hajiya na akan tv, can ta juyo ta kalli Salma ta ce aiken ta aka yi? da sauri ta ce, "A'a, dama innarmu ta ce in kawo wannan a bawa yaya Deen, sannan ta ce in faɗa maki a yi mana godiya ya bamu kuɗi." Murmushi ne akan fuskar hajiya ta ce, "To, mi Deen ya samu?" Miƙewa Salma ta yi ta kai ledan gabanta tana faɗi mata abun da ke ciki, godiya hajiya ta yi ta ce bari a kirawo shi yana nan, wayarta ta ɗauka ta fara dannawa kafin ta kara ta a kunne, tana murmushi ta ce, "Ka zo falo ga saƙo an kawo maka." Daga haka ta cire wayan tana faɗin, "Tun ɗazun da ya dawo gidan yake a ɗaki, dana ji shirun ta yi yawa har leƙawa na yi na iske shi wai suna meeting ne da mutanensu yan ƙwallo ta kwamfuta." Ɗan murmushi ne akan fuskar Salma ba tare da ta ce komai ba, after few minutes sai gashi ya fito, wani irin faɗuwa gaban Salma ya yi ganin a yadda ya fito daga shi sai wando 3-quarter, da sauri ta sunnar da kanta ƙasa, daga gefen kujeran da hajiya take ya tsaya yana kallonta kamar yadda itama take kallonsa ta ce, "Sarkin jin zafi, har ta kai an cire riga ke nan." Ɗan murmushi kawai ya yi, nuna masa ledan dake gabanta ta yi ta ce gashi nan dama Salma ce ta kawo mashi awara in ji innarsu, ɗaura idonsa ya yi akan Salma da bata yarda ta ƙara ɗagowa ba, don a yadda ta gansa har tsorata ta yi ba wai don bata ta6a ganin namiji ba riga ba, wannan ma ta saba gani wurin su Auwalu da Sagir, sai dai akwai bambancin ƙirar jiki a tsakaninsu da Deen nesa ba kusa ba, gaba ɗaya a murɗe yake ga six-pack din cikinsa sun fito baro baro, fatar jikinsa fara tass da ita ba ko ɗan ta6o, yadda cikinsa yake a ɗame tamkar baya cin abinci, maido idonsa ya yi ya sake kallon ledan da ɗan alamun mamaki akan fuskar tasa, "Tukuici ne aka aiko maka, ta ce in taya su yi maka godiya ka basu kuɗi. Allah Ya saka da alkhairi." Sai da ya ji maganar da hajiya ta yi ya fahimci komai, ganin yana niyyar juyawa ta yi saurin cewa, "Ba zaka tsaya ka ci yanzu ba, awara ce na san kuma kana son ta." Hajiya ta faɗa idonta a kan sa, da hannu ya yi mata alamar zai saka riga ne daga haka ya koma ciki, sai da Salma ta tabbatar ya bar wurin sannan ta ɗago ta bi hanyar da ya koma da kallo, bayan ɗan lokaci sai gashi ya sake dawowa, singlet ce ya sako fara ƙal da ita kai ka ce a lokacin aka buɗe ta a ledarta ta kama jikinsa, a ɗayan 6angaren ya zauna yana ɗago fuskarsa suka haɗa ido da Salma, da sauri ta ɗan sunkuyar da kai tana gaishe sa ya ɗaga mata kai kawai, "Salma kai masa, sai ki je kitchen ki ɗauko masa plate." Ta amsa da to tana miƙewa, tana niyyar nufar dinning area ya dakatar da ita da hannu, ce mata ya yi ta matso masa da c-table ta ɗaura a sama, bayan ta yi kamar yadda ya ce ta wuce kitchen ta ɗauko masa plate sai da ta yi tunanin wanne yakamata ta ɗauko masa tsakanin spoon da fork, ƙarshe dukansu ta ɗauko bayan ta sake wanke su, fitowa ta yi ta nufo inda yake, bayan ta ɗaura abubuwan da ta ɗauko a saman table ɗin ta fiddo kulan awaran da roban coleslaw daga cikin ledan, har zata buɗe ta yi serving nasa wata zuciyar ta kwa6e ta da ya saka ta yin hakan? Dakatawa ta yi ta ɗago ta kalle sa ta ga shima ya kalle ta, slowly ta ce, "In zuba maka?" Kai ya ɗaga mata alamar eh, sannan ta buɗe kulan ta fiddo da roban sauce ɗin, da fork ɗin da ta ɗauko ta yi amfanin wurin zuba masa awaran, sai da ya dakatar da ita sannan ta daina zubawa, ta buɗe sauce ta sa cokali ta zuba masa da coleslaw ɗin, ɗagowa ta yi da ɗan murmushi ta ce masa gashi nan, ya ɗan lumshe ido tare da ɗaga kai a hankali ya furta, "Thank you.." Juyawa ta yi ta koma kujeran da ta taso ta zauna, "Wannan awara ta musamman ce aka haɗa maka, don daga jin ƙamshinta ba sai an faɗa ba zata yi daɗi." Hajiya ta faɗa tana murmushi, sadda kai Salma ta yi itama tana ɗan murmushi, tabbas yana da kula kan abincin da zai ci, amman ya ji lafiya lau zai iya cin abun da aka kawo masa saboda ya riga ya san awaran da ake haɗa masa yana ci sune suke yin ta, a hankali Salma take ɗan ɗagowa tana satar kallon shi yayin da ya fara cin awaran a nutse, "Salma ya makaranta, ko da yake weekend ne ba makaranta sai dai islamiyya ko." Maganar hajiya ta sauka a kunnanta, juyawa ta yi ta kalle ta da murmushi ta ce mata eh, ɗan jinjina kai hajiya ta yi ta ce Allah ya bada sa'a, bayan Salma ta amsa hajiya ta sake cewa, "Kin kwance kan ki ne?" Ta tambaya tana kallon kan Salma da ta saka hula bayan ya yi tudu sosai, "Eh, ɗazun na kwance." Kai hajiya ta ɗaga ta ce saura kitso ko, Salma ta ce, "Eh zan je a fara wanke mani sai a yi mani kitson." Jinjina kai hajiya ta yi tare da mayar da idanunta akan tv, bayan wani lokaci ta kalli Deen ta ce, "Saboda kai aka kawo mawa shine kuma ido guba?" Ba tare da ya kalle ta ba ya yi ɗan murmushi tare da kai awaran da ya ɗebo baki, sosai Salma ta ji daɗin yadda ya saki jiki yana cin awaran bai ma yi amfani da fork ba hannu ya saka, jinjina kai hajiya ta yi ta ce ya ci awara lafiya in dai ita ce zata rama ne, sai lokacin ya ɗan ɗago ya kalle ta still da ɗan murmushi a fuskarsa ba tare da ya ce komai ba ya maida idon shi kan awaran yana ci, sosai Salma ta shagala tana ta kallon shi don komai na shi na musamman, hatta yadda yake cin abinci da burgewa, bata ankara ba kawai ta ga ya ɗago sun haɗa idanu, da sauri ta sadda kan ta ƙasa gabanta na ɗan faɗuwa ganin ya kama ta tana kallonsa, still ya yi yana kallonta don ɗagowar da ya yi magana yake niyyar yi mata, rasa ta ya zai yi mata magana ya yi ganin ta sunnar da kai, after few seconds ta sake ɗagowa da niyyar kallonsa suka sake haɗa ido, tana niyyar kauda idonta ta ga ya yi mata alamar kira da kan sa, bin sa ta yi da kallo cikin alamun rashin tabbas ɗin idan gaske ne kiran nata ya yi, sai da ya sake yi mata alamar ta je sannan ta miƙe ta nufe shi walking slowly, tsayawa ta yi a gaban table ɗin ya ƙara ɗibar sauran awaran cikin kulan, bayan ya zuba sauce da coleslow ya ɗago ya kalli Salma ya ce mata ta ɗauki sauran ta kai ma hajiya, bayan ta yi kaman yadda ya ce hajiya na ɗan murmushi ta ce ai ta yi zaton ba zai batan ba, plate ta sa Salma ta ɗauko mata itama ta zuba mata sauran ta fara ci tana yaba daɗin awaran, bayan Deen ya gama cin awaran duba tissue ya yi a nan bai ganta ba ya tambayi hajiya, amsa ta bashi da ga ta can a dinning area ta kalli Salma ta ce ta je ta ɗauko masa, a saman table ɗin ta ɗaura tissue box ɗin bayan ta ɗauko ya yi mata godiya, ɗaukar kayan da ya yi amfani da su ta yi ta kai kitchen, sai da ta wanke su sannan ta dawo cikin falon ta koma ta zauna, after some minutes hajiya ta gama ta kalli Salma ta ce mata ta je ɗakin Balaraba ta kira ta ta zo ta wanke kayan, miƙewa Salma ta yi ta ce bari ta wanke hajiya na ɗan murmushi ta ce ta kawo masu abun daɗi kuma a barta da wanke-wanke, tana murmushi ta ɗauki kayan ta wuce kitchen, bada jimawa ba Salma ta dawo cikin falon bayan ta gama wanke kayan, hajiya ta yi mata sannu ta amsa da murmushi ta koma ta zauna, bayan ɗan lokaci hajiya ta miƙe ta ce zata ɗan shiga ciki, jin haka ya sa Salma miƙewa ta ce zata tafi, hajiya dake kallonta ta ce ba zata jira ta fito ba, tana ɗan murmushi ta ce ma hajiya ta ga dare ya yi ne, "Haka ne kuma, an gode sosai, itama maman taku ki yi mata godiya." Ta amsa da to, har zata juya ta tafi hajiya ta ce ina kayan da aka zubo awaran Salma ta ce suna a kitchen ta ce to ta je ta ɗauko ta tafi da su, wucewa ta yi zuwa kitchen ɗin hajiya kuma ta nufi hanyar shiga ciki, lokacin da ta fito Deen ne kawai a zaune idonsa na kan tv, ledan da aka sako kayan ta je ta ɗauka ta maida su ciki, kallon Deen ta yi daidai lokacin ya maido idonsa kanta, tsaye ta yi tana ƴan kifce kifcen idanu cike da ƙarfin hali ta yi ɗan murmushi a hankali ta ce masa, "Sai da safe..." Kai ya jinjina mata calmy ya ce, "Thank you, I appreciate it." Murmushi ne akan fuskarta ta ce, "Mu ma mun gode Allah Ya saka da alkhairi ya ƙara ɗaukaka." Kai ya sake jinjina mata da ɗan murmushi, juyawa ta yi ta nufi hanyar barin falon hannunta rike da ledan kayan, tana zuwa daidai bakin ƙofa ta ɗan juyo ta saci kallonsa, daidai yana ƙoƙarin miƙewa ganin haka ya sa ta yi saurin ƙarasa ficewa har ta kusa yin tuntu6e.... ✨A CIKIN RAYUWA✨ _New story from the writer of 'A Sanadin Makwabtaka',_ ZAINAB BATURE 23 Washe gari litinin bayan sallar la'asar su Deen suka gama yin shirin fita don kai ziyarar tallafi a ƙarƙashin charity foundation na Deen, a cikin tawagar har da hajiya da ta sha lifaya idanunta sanye da gilashi da kuma daddyn Fahad wato Alhaji Sa'ad shima ya yi shiga ta manyan mutane da kuma Fahad ɗin, daga nan kai tsaye gidan chairman suka nufa a nan suka haɗe da sauran mutanen da za a kai ziyarar da su ciki har da chirman ɗin, babban asibitin garin suka je inda suka samu kyakkyawar tarba daga manya da ƙananun ma'aikatan asibitin, bayan gaishe gaishe tare da gabatarwa da kuma bayanan da suka danganci asibitin, daga baya suka fara zagayawa suna duba marasa lafiya tare da basu tallafin kuɗi da kaya wanda suka haɗa da abinci da kuma barguna da gidan sauro duk a ƙarƙashin gidauniyar jin ƙai ta Deen, mutane da dama sun samu tallafin har da waɗanda ya biya ma kuɗin aiki da za a yi masu, daga cikin su akwai masu manyan lalurori da za a tura su Katsina a can za a yi masu aikin, haka kuma ya bada gudunmawar kuɗi masu yawa don magance wasu daga cikin matsalolin da asibitin ke fama da su, hatta suma ma'aikatan sun samu na su rabon, haka 6angaren marayu ma sun samu tallafin abinci, kaya da kuma kuɗi, ba ƙananun kuɗi Deen ya 6atar a ziyarar ba sai faman yabo da son barka ake. Tuni hotuna da bidiyon ziyarar suka karaɗe shafukan sada zumunta, haka ma kafafen sadarwar suna ta sanarwa game da ziyarar da kuma tallafin da ya bayar, haka akai ta turo masa da saƙonnin yabo, godiya da kuma fatan alkhairi, mutane suka yi ta ɗaurawa a shafukansu na sada zumunta gami da ambatun Deen ɗin da kuma kalaman yabo da nuna ƙauna a gare sa, mata da dama suka yi ta bayyana ra'ayin su na son Deen, gaba ɗaya social platforms Deen ne ke ta trending mutane na ta faman tambayoyi da bada bayanan da suka danganci rayuwarsa, wasu da dama da basu san komai da ya shafi harkar ƙwallo ba mamaki suke jin cewa shi ɗin asalin ɗan Najeriya ne ganin irin sufar shi da sam bata yi kama da ta ƴan nan ƙasar ba. A ranar Salma bata baro makaranta da wuri ba saboda ta tsaya wata ƙawarta da ta iya ƙunshi sosai ta yi mata zanen lalle baƙi da ratsin ja a hannuwanta, sosai ƙunshin ya yi kyau bayan ya bushe ta wanke suka baro makaranta, har da kuɗi ta ba ƙawar tata da ta yi mata, keke napep guda suka hawo aka ajiye Salma bakin kasuwa ita kuma kawar tata aka wuce da ita gida, wani shagon salon da take gani idan ta zo kasuwa ta je don a wanke mata kai, kusan wannan ne karo na farko da ta zo wankin kai shago a nan, amman idan ta je Kaduna hutu aunty Kubra na kai ta ana yi mata wash and set, cikin sa'a ba layi mai yin salon ɗin wadda bayerabiya ce musulma ta tarbi Salma cikin haba haba ta tambayi abun da za a mata, bayan ta sanar da ita ba 6ata lokaci aka fara shirin yi mata, saman wata kujera mai mazaunin mutum biyu Salma ta zauna ta cire hijabin uniform ɗinta tare da hular kanta, matar na daga wurin bakin kofa tana zuba ruwan da zata wanke mata kai, juyowa ta yi ta kalli Salma ta ce mata ta matso a wanke kan ta amsa mata da to, bayan ta zauna saman kujerar wankin kan matar na ɗan murmushi ta ce gashi da gani gashin nata yana da kyau, Salma ta yi ɗan murmushi ba tare da ta ce komai ba, hannu matar ta kai don ta cire ribbom ɗin da aka naɗe gashin da shi, da ɗan alamun firgici matar ta furta, "Ahh...!" Ganin irin tsawon gashin bayan ta cire mata ribbom, tsaye ta yi da alamun al'ajabi tana kallon gashin Salma da ya tarwatse ya yi mata rumfa tsawon shi har tsakiyar baya, hannu matar ta kai still da al'ajabi a kan fuskarta ta fara ta6a gashin baki buɗe, duk abun da take yi Salma na hango ta ta madubi dake daga can ciki, "Is this all ur hair?" Matar ta tambaya with shock, kai Salma ta ɗaga mata, "Kai ɗan garin nan ne?" Mai salon din ta sake tambaya, ta ƙara ɗaga mata kai, matar ta sake tambayarta wace unguwa, Salma ta faɗa mata, "Amman kai ba hausa ba ko? Are u an arab or an indian?" Har sai da tambayar ta ba Salma ƴar dariya, ta ce mata ita bahaushiya ce, "Ok babanka ko mamanka ne ba hausa ba? I mean you are biracial ba?" Kai Salma ta girgiza mata tana murmushi ganin yadda matar ta ruɗe tana ta faman tatta6a mata gashi ta ce ita iyayenta cikakkun hausawa ne, da yanayin shakku matar ta ce to amman dai a cikin grandparents nata dole akwai wanda ba bahaushe ba, Salma ta ce duk hausawa ne, mai salon dai ta kasa yarda ta ce to su fulani ne amma ba hausa ba, Salma da har ta fara ƙagara da tambayoyin matar ta ce mata kawai eh iyayenta fulani ne duk da ita dai a saninta iyayenta da kakanninta duk cikakkun hausawa ne, har gara ma kakarta ta 6angaren innarsu ita tabbas bafullatana ce sosai, da ƙyar ta samu matar ta fara yi mata wankin kan tana yi tana ci gaba da santin kyawun gashin ta faɗi mata cewa she had never come across hair like that so long and full tun da take sana'ar salon, ta ce duk da akwai masu gashi sosai dake zuwa, wasu gashinsu na da cika sosai amman ba tsawo, wasu kuma yana da tsawo ba cika, wasu kuma suna da yanayin irin gashin Salman amman bai kai nata ba, haka tai ta faman yi ma Salma surutu har bayan ta gama wankewa tana setting nashi, haka shima ƙunshin da aka yi ma Salma da ta gani sai da ta yi ta yaba shi, ita dai Salma murmushi kawai take abun da ya sa bata damu da surutan matar ba ta kan faɗi maa sha Allahu a cikin yabon nata, bayan an gama Salma ta siya lemu da biscuit da matar ke saidawa saboda yunwar da take ɗan ji, a nan ta ci bayan ta gama ta tambayi matar gaba ɗaya kuɗin, kafin ta faɗi mata ta yi mata tallar wasu mayukan gashi ta ce suna da kyau sosai daga Ghana ake kawo mata, Salma ta siya guda biyu ta haɗa da wasu ribbons masu kyau suma guda biyu, bayan ta faɗi mata kuɗin gaba ɗaya ta biya ta har da ƙari ta yi mata, aikuwa matar tai ta faman yi mata godiya tana washe baki, har da roƙon Salma kan ta ci gaba da zuwa nan ta ce tana yin komai na gyaran gashi Salma ta ce to, har da rakiya matar ta yo mata har waje, ita duk a ɗaukar ta Salma ɗiyar masu kuɗi ce ganin yanayin ta ga kuma cinikin da ta yi mata. Ajiyar zuciya innarsu Salma ta sauke bayan ita da Salma sun gama kallon vedion ziyarar da Deen ya kai da irin tallafin da ya bada, miƙa ma Sagir wayar shi da suka yi kallon a ciki ta yi ta ce, "Wai haka yake da kuɗi? Na ga ba ƙaramin tallafi ya ba mutane ba!" Ta faɗa da mamaki, wata dariya Sagir ya yi yana jinjina kai ya ce,"Yo innarmu wannan har wani abu ne a cikin irin kuɗin da yake da su a matsayinsa na ɗan ƙwallon kafan Turai, mutumin da a duk sati ake biyan su miliyoyin kuɗi, ai duk yadda zan faɗa maku irin kuɗin da ake samu a harkar ƙwallo ba zaku gane ba wllh, ku dai ku taya ni addu'a in samu irin damar shi, wllh da gaba ɗaya danginmu sun warke daga talauci." Salma da ke a gefen innarsu saman tabarma ta yi dariya ta ce, "Kamar gaske, kai idan Allah Ya sa ka samu dama har ka tafi ƙasar waje ai na tabbata can zaka samu matan turawa ka aura mu kuma sai mun gan ka kawai." Wani mugun kallo ya jefa mata ya ce, "Ke dai wallahi sakarya ce, maimakon mutum ya faɗi niyyarsa mai kyau ki yi masa fatan alkhairi sai zancen banza." Dariya ta shiga ƙyalƙyata masa ya yi ƙwafa tare da miƙewa da alama ya ji haushin maganar tata, "Sorry my brother, Allah Ya tabbatar maka da niyyar ka, ka ga ma sai kawai in koma wajen ka can ƙasar wajen in ci gaba da karatuna." Tsoki ya yi mata daga haka ya fice daga gidan innarsu dai bin su ta yi da kallo tana dariya don abun su ba shi da ranar ƙarewa. Bayan sallar magrib su Imrana suka fitar da kaya don fara tuyar awara, bayan Salma ta gama shiryawa don zuwa wurin awaran, ɗakin innarsu ta shiga ta iske ta zaune a bakin gado tana ninkin kaya, tana ganin Salma ta fara yi mata murmushi itama shine akan fuskarta, a saman kujera ta zauna ta yi mata sannu ta amsa, ta ce ma innar zata tafi wurin tuyar awaran, tana kallonta still da murmushi a kan fuskarta ta ce, "Ki yi zaman ki ki huta tun da ga su Imrana can suna yi." Ta ce mata a'a zata je, gyaɗa mata kai innarsu ta yi ta ci gaba da ninkin kayan, ganin Salmar ta yi shiru kuma bata tashi ta tafi wurin awaran ba kamar yadda ta ce ya sa ta dakata tana kallonta ta ce, "Ko da wani abu ne Salma? Na ga kamar da magana a bakin ki." Kallonta ta yi tana faffaɗan murmushi ba tare da ta ce komai ba, "Yaushe muka fara haka da ke? Minene kike son faɗa mini har kike jin nauyi haka?" ƴar dariya Salma ta yi ta ce, "Innarmu ba fa wani abu ba ne." ta ce, "To faɗa mini ina jin ki auta ta." Ta tattara duka attention ɗinta akan ta, ci gaba da murmushi Salma ta yi haka nan sai take jin nauyin abun da take son faɗa mata, zuba mata ido innarsu ta yi tana jiran ta ji mi zata faɗa ta ce, "Ko dai saurayi kika yi ne shi ne kike jin nauyin sanar mini?" Cike da zolaya innarsu ta faɗa, dariya sosai Salma take yi ta ce, "Kai innarmu wani saurayi kuma, ai in wannan ne ba zan ji nauyin sanar maki ba, kamar yadda kike ce mini idan har na yi saurayin da na ji ina son sa in sanar maki kar in 6oye maki." Kai ta jinjina mata alamar haka ne, ta ce, "To yanzu ma koma minene kar ki ji komai ki faɗa man zan fahimce ki." Salma na dariya ta ce, "Ba fa wani abu bane, dama cewa zan yi ko yau ma a yi ma yaya Deen irin awaran jiya na ga ya ci sosai ba har na faɗa maki yadda suka yi da hajiya ba da bai bata ba." Faffaɗan murmushi ne akan fuskar innarsu ta ce, "To dama wannan ne kika kasa sanar mani Salma, ai ba wani abu bane ni jin daɗina ne a ce ina da abun da zan bashi kuma ya amsa, mutum irin wannan komai ka yi masa baka faɗi ba saboda irin alkhairinsa, ko da ace alkhairin nasa bai je ma mutum ba zai je ma wani nasa ko wanda ya sani, kin san a cikin waɗanda ya biya ma kuɗin aiki a asibiti har da malam Rabi'u?" Shiru Salma ta ɗan yi alamar tunani ta yi saurin cewa, "Baban su Habiba?" Kai innarsu ta ɗaga, "Eh wllh..baki ji yadda na ji daɗi ba ɗazun da muna waya hajiyarmu ta sanar mani, dama bayin Allah sun shiga damuwa ana ta faman cuku cukun yadda za a haɗa kuɗin aikin sai gashi Allah Ya kawo mafita." Murmushi ne akan fuskar Salma a cikin zuciyarta fuskar Deen na mata yawo, "Daga can ƙasan mu ma na ji akwai wani mutumi mai fama da lalurar ƙoda shima yana cikin waɗanda suka samu tallafin aiki, ko baka haɗa komai da mutum ba ka ji ya samu mafita akan mayuwacin halin da yake ciki dole ka ji masa daɗi wllh. Allah dai Ya saka masa da alkhairi Ya ƙara masa ɗaukaka." Salma ta amsa da ameen with a smile on her face, innar ta ce mata ta je ta ɗebo awaran sai a haɗa dare na ƙara yi ta amsa da to ta miƙe, bayan ta dawo suka fara yin aikin tare kamar jiya, innarsu ta bada shawarar su canza yau a yi masa egg sauce. Deen yana kishingiɗe a saman gado hannunsa riƙe da wayarsa yana duba tarin saƙonnin da aka masa, wasu ya yi reply wasu ya yi liking, daga cikin waɗanda suka ɗaura ziyarar tallafin nasa a shafukan su har da mai girma gwamnan katsina ya yi masa kalaman yabo da godiya da kuma fatan alkhairi, shima Deen ya yi masa godiya tare da ɗaurawa a page ɗin sa, ɗayar wayarsa dake ajiye a gefensa ce ta fara yin ruri ya kai idanunsa kanta kafin ya ɗauka, ɗan murmushi ne ya bayyana akan fuskarsa ya yi picking call din a nutse ya furta, "Good evening dad.." Daga ɗaya 6angaren dad ɗin ya ce, "How are you my son?" Ya amsa masa da Alhamdulillah, dad ya ce, "Ma sha Allah, gani nan cikin farin ciki sosai ganin yadda al'umma suke ta jin daɗi da yabon abun da ka yi Deen, ba zan 6oye maka ba na ji daɗi sosai har bansan yadda zan bayyana maka ba, I am always proud of u my boy." Murmushi ne akan fuskar Deen ya ce, "Thank you dad." "Yaushe zaka dawo ne, ko Funtua ta yi maka daɗi nan zaka ƙare hutun naka?" Ya faɗa yana ƴar dariya, amsa Deen ya bashi da zai dawo akwai abubuwan da yake so ya ƙarasa kammalawa, hira suka ci gaba da yi dad na bayyana masa yadda shima mutane suka yi ta kiransa suna nuna jin daɗi da yabon abun da ya yi kafin daga baya suka yi sallama, ko minti biyar ba a yi ba sai ga kiran mom ɗin sa ya shigo, bin wayar ya yi da kallo kamar mai shakkar ɗaga kiran, sallama ya yi bayan ya ɗaga, ko amsa sallamar bata yi ba ta fara cewa, "Wai Deen mi yake damun ka ne? Yaushe ne zaka fara yin tunani yadda ya kamata? Ka je ka samu wuri ana ta tunzura ka kana 6annar kuɗi sai ka ce wanda bai son ciwon kansa ba. Kai baka da buƙatun kanka ne da zaka tare a biya ma wasu nasu? Idan taimako ne ai daidai gwargwado kana yi, ko ba dama kana yin taimakon a foundation ɗin naka da ita kakar taka take running maka ba? Wannan duk bai isa ba da sai an saka ka je kana ma wasu 6arin kuɗi, mutane da rashin godiyar Allah da mugun hali hakan kuma ba zai hana su bika da sharri ba ba kamar ganin Allah Ya ɗaukaka ka. Ai kana da family, idan kuɗin sun yi maka yawa ka biya ma ƴan'uwanka buƙatun su ba ka tare a hidimta ma wasu bare ba da yabawar da za su yi ba lalle har zuciya ba...." Shiru ya yi yana saurarenta fuskarsa ta bayyana yanayin 6acin rai, "Deen are you there?" Ta faɗa jin har ta ƙare maganganunta bai ce mata uffan ba, slowly ya furta, "Yea.." A ɗan fusace ta ce, "Ok, shine ka yi banza da ni in ƙaraci haushina?" Ɗan murmushi ya yi wanda ya fi kama da a kira na takaici, lumshe ido ya ɗan yi trying to calm himself kada ya fadi wani abu ba daidai ba, calmly ya ce, "Ki yi haƙuri mom, amman ni abun da na yi ra'ayin kai na ne ba wanda ya sani, kuma na yi ne saboda Allah not to seek people's praise, ban yi realizing hakan abu ne mara kyau ba ganin yadda kowa ke yabawa sai yanzu da ke kika nuna mani hakan." Shiru ta yi na ɗan lokaci da alama ya kashe mata baki, cike da kama kai ta furta, "Nima ai ba ina nufin hakan da ka yi abu ne mara kyau ba, kawai dai yakamata a ce kana yin tunani a duk abun da zaka yi, bai kamata ka tare a taimakon wasu bare ba kawai." Ɗan ta6e baki ya yi ya ɗan sauke ajiyan zuciya ya ce, "I thought yin taimako koda a wuri guda ne in dai ana buƙatan hakan ba laifi bane, kuma nan ne asali na, miye laifi don ina taimaka ma mutane?" A ɗan harzuƙe ta ce, "Ta ina nan ɗin ya zama asalin ka? A nan aka haife ka?" Shiru ya yi don ya san ko mi zai faɗa sai ta yi jayayya da hakan, ta ci gaba da faɗin, "Ka kama ka tare a nan, sai ka ce nan kaɗai kake da dangi, ga su Ammi can duk sun ƙagara su ganka sai tambayar yaushe zaka je suke yi, amman da yake su baka basu mahimmanci ba shi ya sa ba ta tasu ka ke ba, balle ka yi tunanin zuwa suma ka ji buƙatun su." Ɗan murmushi ne akan fuskarsa jin ƙarashen zancen nata, dama ya san tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi, ita bata ƙaunar ta ga an hidimta ma wani in ba danginta ba, sigh ya yi ya ce mata zai je can ɗin da ya kammala abubuwan da yake yi a nan, ta ce, "Allah Ya sa. Amman yakamata kafin ka je ka fara tura masu wasu kuɗi, za su ji daɗi su san ka damu da su kuma kana sane da su, tun da duk suna ganin irin 6arin kuɗin da kake yi akan wasu bare." A taƙaice ya ce mata zai yi hakan da tunanin faɗin hakan zai kawo ƙarshen korafin nata, sai kuma ya ji ta sake cewa, "Ita Basma kuna yin wayar ko itama ka shiga dangi masu muhimmanci ka manta da ita?" Runtse ido ya yi tare da yamutsa baki kafin ya bata amsa da ko jiya sun yi chat. Ajiye wayar ya yi bayan sun gama ya zuba ma wuri guda ido, duk da ya san halinta amma sosai bai ji daɗin maganganunta ba, ganin yadda kowa yake yaba masa kan abun da ya yi amman a ce sai mahaifiyarsa ce zata kushe, hannu ya kai ya dafe forehead ɗinsa tare da ɗan lumshe ido, bayan ɗan lokaci ya kai hannu ya ɗauki wayoyinsa, zuro kafafunsa ya yi ƙasa ya miƙe tare da nufar ƙofa ya fita. Bayan sun gama haɗa awaran, a cikin wata warmer mai kyau aka zuba awaran sai egg sauce ɗin a cikin ƙaramar warmer ɗin ta awaran, shiryawa Salma ta yi cikin doguwar rigar atamfa ta yi ɗaurin kallabi mai kyau gashinta dake a fake ya leƙo ta ƙasan ƙeyarta, fuskarta ta yi fresh duk da bata shafa hoda ba dama haka face ɗinta take zaka ga kamar ta shafa hoda saboda yadda fatar ta take sumul, iya ɗan lip gloss ta shafa ta yafa gyale, ita kanta ta ga ta yi kyau bayan ta duba madubi da yake akwai wuta, sai kuma ta kasa fita saboda kunya a cikin zuciyarta tana raya to ma wai duk miye na yin shirin, duk da jiya ma sai da ta canza kaya amman ita kanta ta ga ta fi fitowa tsaf tsaf yau, da ƙyar dai ta fita daga cikin ɗaki a zuciyarta tana zullumin kada innarsu ta zargi wani abu, dama ɗazun saida ta ji kunyar cewa a yi masa awaran da ta yi..... *_✨A CIKIN RAYUWA✨_* _New story from the writer of 'A Sanadin Makwabtaka',_ _ZAINAB BATURE_ _Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai._ 24 Da ƴar sallama ta shiga cikin falon, tana shiga idanunta suka sauka akan Deen dake zaune saman kujera mai mazaunin mutun biyu ya jingina bayansa tare da ɗan miƙar da ƙafafunsa, har ta ƙarasa ciki ta tsaya daga gefe sam bai ji shigowarta ba don idanunsa na akan tv yayin da ya toshe kunnuwansa da headphones, tun bayan da ya gama waya da mom ɗinsa ya fito nan ya zauna yana buga PS wanda ya kawo daga part ɗin su, kallon controller ɗin da yake riƙe da yana motsa hannuwansa a hankali Salma ta yi kafin ta kai idonta kan FIFA, wato game ɗin ƙwallon ƙafa da yake bugawa, bayan ɗan lokaci ta ƙara yin sallama ganin alamun bai san ta shigo ba, sai dai still bai juyo ya kalle ta ba, tunanin ko bai jin ta ne ta yi tana kallon headphones ɗin kunnuwansa ta raya ƙilan wani abun yake ji shi ya sa, ta shiga tunanin yadda za ta yi masa magana can ta maida idanunta tana kallon game ɗin da yake yi, after a while ya fara ƙoƙarin gyara zaman shi, ganin kamar mutum ta gefensa ya sa shi ɗan juyowa, daidai itama Salma ta maido idonta kansa jin motsin shi, haɗa ido suka yi ya bita da kallo mai kaman na mamaki, ɗan murmushi ta shiga yi tana kifce kifcen ido, hannu ya kai ya cire headphones ɗin ganin haka ta yi saurin ce masa, "Ina wuni." Kai ya jinjina mata tare da gyara zamansa, sauke idanunta ta yi ta rasa ta ina zata fara yi masa magana saboda ƙwarjinin da yake mata, ɗagowa ta yi suka sake haɗa ido cikin yan kame kame ta ce, "Ina ta yin sallama da na zo baka ji ba." Kai ya ɗaga calmly ya ce, "Sorry, nasa headphones." Kai ta ɗaga tana ɗan murmushi, "Hajiya tana ciki, let me call her..." Ya fara ƙoƙarin miƙewa, sam ta kasa sanar da shi wurin shi ta zo, bada jimawa ba ya dawo ya ce mata hajiya tana zuwa ta ɗaga masa kai, bayan ya koma ya zauna ya ci gaba da yin game ɗin sa ba tare da ya mayar da headphones ɗin kunnansa ba, hajiya ce ta fito ta nufo cikin falon tana sanye da dogowar rigan bacci da hula, "Salma ce.." Ta faɗa bayan ta ƙaraso, Salma ta ce, "Hajiya ina wuni." Amsa mata ta yi ta ce ga wuri ta zauna ta yi tsaye, "Yau na gaji sosai saboda fitar da muka yi, shi ya sa na kwanta da wuri " Hajiya ta faɗa tana yin hamma, a hankali Salma ta ce, "Sannu.." Ta amsa da yauwa, jimm ta ɗan yi kafin da ƙyar ta ce, "Ga shi an ce a ba yaya Deen." Ta faɗa tana ajiye ledan daga gefen kujeran hajiya, kallon ledan hajiya ta yi tana ɗan murmushi ta ce, "To yau ma wani abun daɗin aka kawo ma Deeni?" Salma tana ɗan murmushi ta ce mata awara ce, godiya hajiya ta yi ta kalli Deen ta ce, "Ashe ma wurin ka ta zo Deeni." Kallon hajiya ya yi ta nuna masa ledan tana ce mashi saƙon sa ne, da alamun rashin fahimta ya kalli ledan hajiya ta ce ma Salma ta kai masa, miƙewa ta yi ta ɗauki ledan ta kai gabansa ya bita da kallo, "Awara ce aka ce in kawo maka." Ta faɗa a hankali, kai ya ɗaga sai kuma ya ce, "Thank you..." hajiya ta ce masa, "Ka sa Balaraba ta kawo maka abinci ne?" Ya bata amsa da ta kai dining area, ta ce, "Ai da ka ci dare na yi, ko da yake ga awara nan sai ka fara ci, Salma je kitchen ki ɗauko wuri sai ki zuba masa." Amsawa ta yi da to ta wuce don ta yi abun da ta ce, bayan ta dawo ta zuba masa ya ce ta kai ma hajiya sauran, hajiya ta ce, "Anya zan ci awaran nan kuwa don na gama shirin kwanciya har baki na wanke, maida masa na san zai iya cinyewa duka." Ƴar dariya Salma ta yi ganin irin kallon da ya yi ma hajiya bayan ta mayar masa da awaran, a nutse ya fara cin awaran, "Miye wannan kake kallo ne?" Hajiya ta tambaya tana kallon game ɗin da ya tsayar, ya ce mata game ne tare da ɗaukar remote ya fita daga wurin ya maida masu kallo, a tare gaba ɗaya suka kai idanunsu kan ƙofar shigowa jin an yi sallama, ƙirjin Salma ne ya buga ganin wanda ya shigo cikin falon, bayan ya ƙaraso ciki hajiya ta ambaci sunansa tana murmushi, ya gaishe da ita tare da zama a gefen Deen, tun da Salma ta kalli Fahad da ya shigo bata yarda ta sake kallonsa ba, kallon Deen dake masa murmushi ya yi cikin muryarsa mai tattare da nutsuwa ya ce, "Acici...da alama wannan kafin ka koma sai ka cinye ma hajiya duk abincinta." Hajiya ta yi dariya ta ce, "Ban da nawa ma har ma da na maƙwabta, don wannan ɗin Salma ce ta kawo masa." Sai lokacin ya kai idanunsa kan Salma daidai ta ɗago suka haɗa ido nan take fuskarsa ta canza, gaishe shi ta yi ya amsa ba yabo ba fallasa tare da janye idonsa ya maida kan tv, "Akwai sauran awaran Salma ta zuba maka." Tamkar an faɗi masa wani mugun abu ya yi saurin ce ma hajiya a'a ya ƙoshi, Salma dai idanunta na a kasa duk ta sha jinin jikinta, jin motsi ya sa ta ɗan ɗago idanunta ta ga Deen ne ke ƙara awaran, haɗa ido suka yi ya yi mata ɗan murmushi don ya lura da rashin sakewarta tun bayan shigowar Fahad, itama ɗan murmushin ta yi masa ta janye idonta, bayan ɗan lokaci ta miƙe ta ce ma hajiya ta tafi, hajiya ta ce mata ai ya kusa gamawa ta bari sai ta tafi da kayan kawai, ba don ta so ba ta koma ta zauna, hajiya ta ce, "Fahad ga abinci can a kan table da aka shirya Deeni bai kai ga ci ba, ko kuma ya gama sai ku ci tare." Deen ya kalle ta ya ce, "Na ci wannan na ƙoshi." Cike da zolaya hajiya ta ce, "Kai dai, na san shima abincin ba zai rasa shiga ba, ko kunya kake ji kada Salma itama ta fahimci acici ne kai." Murmushi kawai ya yi ya ci gaba da cin awaran, wani kallo Fahad ya yi ma hajiya ganin kamar raini take ja ma Deen da ta yi maganar a gaban yarinyar, dama ya yi mamakin jin cewa ita ta kawo masa awara kuma yake ci, akan wani dalili? Da alama ransa ne ya 6aci ya sa shi miƙewa zai wuce ciki, hajiya dake kallon sa ta ce ba zai ci abincin ba? a taƙaice ya bata amsa da sai ya fito, Salma tabi sa da ido tun lokacin da hajiya ta yi magana ta saci kallonsa ta ga yanayin sa ya canza, jikinta ne ya yi sanyi don ta fahimci duk saboda saka ta a maganar da hajiya ta yi ne, ita har cikin ransa ta basa haƙuri lokacin da hajiya ta sata saidai ta fahimci ya nuna ya haƙuran ne ba har ransa ba, Deen da ya bisa da ido shima ya fahimci yanayin Fahad ɗin ya canza. Bayan ya gama Salma ta je ta tattara kayan ta kai kamar jiya ta wanke su sannan ta fito, sallama ta yi masu bayan ta saka kayan a leda hajiya ta ce ta gaishe da innarsu ta yi mata godiya, kallon Deen ta yi suka haɗa ido da ɗan murmushi shima ya ce mata ya gode ta ɗaga kai daga haka ta tafi, bayan Salma ta tafi kusan tare shi da hajiya suma suka bar falon bayan sun yi ma juna saida safe kowa ya wuce bangaren sa. Shirye shiryen bikin buɗe sabon club din Deen sun kankama, su Sagir ba zama anata shiri an yo masu jerseys na club ɗin kala biyu da takalma. Washe gari talata da yamma Salma ta shirya don zuwa gidan hajiya ta kai ma Balaraba faran da ta soya, wata coffee brown ɗin abaya ta saka a cikin irin kayan gayun da aunty Kubra ke siya mata, aikin jikin abayar mai kyau da stones kuma ta matuƙar amsar jikinta ta kuma ƙara fiddo da kyaun fatarta, yafa gyalen rigar ta yi saman kanta daga ƙasan ƙeyarta inda ta naɗe sumarta ya yi tudu, yayin da daga gaban kanta kwantacciyar sumarta dake a nannaɗe ta ɗan fito, sosai ta yi kyau idan ka ganta zaka yi tunanin ba daga nan gidan take ba ɗiyar masu kuɗi ce, bayan ta gama shiryawa ta fito, ɗakin innarsu ta nufa don ta sanar mata, haɗa ido suka yi da innarsu bayan ta ɗaga labulen ɗakin, tana zaune akan kujera ganin Salma ta fara sakin murmushi, daga gefenta Salma ta zauna itama murmushin ne akan fuskarta, innarsu ta ce, "Ka ga ƴan matana Masha Allah, ina zuwa?" Ƴar dariya Salma ta yi ta ɗan ɗaga mata ledan faran hannunta ta ce zata je kai ma aunty Balaraba fara, kai innarsu ta ɗaga mata ta ce, "Idan wanda bai san ki ba ya gan ki ba za a ta6a yarda cewa sana'ar tuyar awara da fara kike ba." Dariya sosai Salma take fararen haƙoranta sun bayyana, bayan ta dakata ta ce, "To ai dai innarmu sana'a ce ko, kuma yanzu har ƴan gayun masu kuɗi suna yin irin waɗannan sana'oin." Innarsu dake ƴar dariya ta ce, "Amman su tasu sana'ar zaki ga a wayance suke yin ta.." Salma ta tari numfashinta, "Kawai packaging ɗin abubuwan ne suke wasu su kai manyan kantuna ko supermarket, nima da sana'ar faran tawa ta kankama ai zan iya yin hakan." Murmushi innarsu ke yi tana bin ta da kallo mai cike da ƙauna, kallon ɗan plate ɗin dake gefenta Salma ta yi wanda ta zubo mata fara bayan ta gama soyawa ta ce, "Faran ya yi daɗi?" Ta ce sosai ma komai ya yi daidai, "Sai yaushe za a yi kitso? Ko kuma sai an gama gayu da shi?" Innarsu ta tambaya tana kallon kan Salma da gyalen ya zame, shiru ta ɗan yi tana mata murmushi sai kuma ta ɗaga mata kai alamar eh, still murmushi ne akan fuskar innarsu ta ce mata ai da yake sumar tata bata danƙarewa idan an barta a kwance ta sha gayun ta, dariya Salma ta yi ta ce, "Ke yaushe zan taya ki ki kwance naki?" Hannun hagunta ta kai ta kamo jelar kitson kanta guda ta ce ma Salma ya tsufa ko ta ɗaga mata kai alamar eh, innarsu ta ce, "To ni ai gashi na ba wani mai uban yawa bane zama ɗaya ma sai in kwance." Salma ta ce, "Duk da haka kema innnarmu kina da gashi tunda idan kika kwance har wuce kafaɗarki yake, kuma kema da za a yi maki wash and set ɗin ko saloon na san zai ƙara tsawo sosai." Innarsu ta ce, "Kai ni kyiwur zuwa shago nike a wanke mani kai, kuma nima bana yin saloon, ina ga sau ɗaya na ta6a ƙona sumata tun lokacin bikina da baban ku shima soda ce aka saka mani duk da lokacin gashina ya fi haka tsawo." Dariya Salma ta guntse jin ta ce tun bikinta da abbansu, itama innar tasu dariya take ta ce mata ta je ta kai mata yamma na yi ta gaishe mata da hajiya ta amsa da to tare da miƙewa, innarsu ta bita da kallo ya yin da ta nufi ƙofa har ta fita. Bayan Salma ta shiga cikin gidan, a cikin harabar daga can gefe ta hango Balaraba a bakin famfo tana wanke wasu manyan robobi, nufar inda take ta yi bayan ta isa kusa da ita ta ce, "Aunty Balaraba ina wuni." Balaraba da ta ɗago tana kallonta da murmushi ta ce, "Lafiya lau Salma, ya su innar ku?" Ta amsa mata da suna lafiya, "Ma sha Allah Salma kin yi kyau." Balaraba dake ta kallonta ta sake faɗa, tana murmushi ta ce mata ta gode kafin ta kai hannu cikin ledan ta fiddo roba guda ta fara ta ce mata ga shi, goge lemar hannunta ta yi ta amsa tana faɗin farar ce har ta soya, buɗewa ta yi ta ɗan de6o ta kai baki, bayan ta cinye ta ce, "Salma kin iya soya fara, ta yi daɗi sosai wllh." Salma dake murmushi ta ce mata ta gode, tambayarta ta yi ko hajiya na nan ta bata amsa da eh tana cikin gida ta shiga, tana shiga cikin falon ta ja ta tsaya sakamakon hango Deen da ta yi a zaune yau ma ya maƙala headphones a kunnansa hannunsa riƙe da controller da alama yau ma game ɗin yake yi, kasa shiga ciki ta yi saboda ganinsa da ta yi ba riga jikinsa sai wani neck scarf da ya rataya a wuyansa ha6ar ta rufe masa gefe da gefen ƙirjinsa sai wando 3-quarter, haka nan ta ji nauyin ta ƙarasa tana niyyar juyowa ta fito kawai ta ga ya juyo fuskarsa inda take suka haɗa ido, bin ta da ido ya yi ta shiga ƴan kame kame, ba yadda ta iya haka ta ƙarasa shiga cikin falon ta tsaya daga ɗan nesa da shi tana sauke idonta ƙasa, a hankali ta ɗan ɗaga ido ta ce masa ina wuni ya ɗaga mata kai, shiru ta yi batare da ta ƙara cewa komai ba idonta na kallon gefe, "Hajiya?" Nutsattsiyar muryarsa ta sauka a kunnanta, kallonsa ta yi tare da ɗaga masa kai, idonsa a cikin nata ya ce, "So you want to turn me into the one who has to call Hajiya every time you come, right?” Ya yi maganar tare da ɗage mata gira, rass ta ji gabanta ya faɗi da tunanin ko ya fara gajiya da zuwan da take yi gidan, cikin ƴar rawar murya ta ce, "Ka yi haƙuri, bari in tafi ko anjima idan ta fito na dawo." Tana faɗin hakan da sauri ta juya zata nufi kofa, "Hey..." Ya dakatar da ita ta juyo suka haɗa ido, ɗan murmushi ta ga ya yi calmly ya ce, "Just kidding...let me call her for u." Daga haka ya miƙe idonta akansa, yana juya bayansa zai nufi part ɗin hajiya ta yi saurin janye idonta don muscular jikinsa tsoro yake bata, ba a jima ba ya dawo tana jin dawowarsa bata kalle sa ba, ya koma wurin da ya tashi zai zauna ta ji ya ce hajiya tana toilet sannan ta ɗaga ido ta kalle sa tare da ɗaga masa kai, ci gaba da yin game ɗinsa ya yi after some seconds ya juyo suka haɗa ido ya ce mata ta zauna a hankali ta matsa kujeran kusa da ita ta zauna, kallon game ɗin ta ci gaba da yi tun bata fahimta har ta ɗan fara gane kan game ɗin daga yanayin da Deen ke nunawa akan fuskarsa idan ya yi winning, after some minutes hajiya ta shigo cikin falon, a kujeran da ta saba zama ta zauna Salma na kallonta ta ce, "Hajiya ina wuni." Fuska sake hajiya ta ce, "Lafiya lau Salam, ya ƴan'uwanki?" Ta amsa mata suna lafiya, ta ɗaga mata kai kafin ta kai idonta kan game ɗin da Deen ke yi, hannu Salma ta kai cikin ledan da take riƙe da, robar fara ta fiddo da ɗan murmushi ta miƙa ma hajiya ta ce, "Gashi hajiya." Kallon abun da ta miƙo mata ta yi ta ce, "To..mi na samu haka?" Salma ta ce, "Fara ce na kawo ma aunty Balaraba, shine kuma na kawo maku." Hajiya tana murmushi idonta akan robar farar ta ce, "To na gode, sai dai bansan ma yanzu ko zan iya cin fara ba saboda haƙora ba ƙwari abu kaɗan sai su fara ciwo." Ta yi maganar tana ƙoƙarin buɗe robar, ƙamshin faran ne ya bugi hancin ta ta ce, "Ma sha Allah, tun ban ci ba ma na san ta yi daɗi." Ta faɗa tana murmushi, kai da gangar jiki na farar ta fara ɗauka tana ci ta ce bazata ci cinya ba kada ta soke ta, Salma dake kallonta murmushi ne akan fuskarta na jin daɗin ganin tana cin faran, ruƙus-ruƙus ɗin tauna farar da hajiya ke yi da kuma yadda take ta yaba daɗinta su suka jawo hankalin Deen ya ɗan juyo ya kalle ta, tana kallon sa ta ce, "Ko zaka ci ne?" Ta ɗaga robar tana nuna masa, bin robar faran ya yi da kallo kamar bai fahimci abun da hajiyan ta ce ba, miƙa ma Salma robar ta yi ta ce ta kai masa, tana ɗan murmushi ta ce mata ai shima ta kawo masa hajiya ta ce to ta kai masa a ga in zai iya ci, miƙewa ta yi ta isa gabansa ta kai hannu cikin ledan ta fiddo wata robar fara ta miƙa masa tana murmushi, bin robar da take bashi ya yi da kallo kafin ya ɗaga ido ya kalle ta alamar bai fahimta ba, ta sake ce masa fara ce soyayya ta kawo masa, hannu ya kawo ya amshi robar ya buɗe, hajiya dake kallon Deen dariya ce akan fuskarta ganin yadda ya yi duruduru yana kallon farar kamar wanda ya ga wani abun tsoro, ta ce, "Spicy fried grasshoppers ce ka ci." Ɗagowa ya yi ya kalli hajiya da idanunsa tubarkalla, "Dama ana cin shi?" Ya jefa mata tambaya, still da dariya akan fuskarta ta ce, "Eh mana, da ba a ci zaka ga nima na ci, kuma tana da amfani sosai a jiki." Shiru ya yi ya maida idonsa kan farar yayin da ƙamshinta ke ta bugun hancinsa, kuma ƙamshin ya yi masa daɗi, ɗago ido ya yi ya kalli Salma da har lokacin take a tsaye tana murmushi, slowly ya ce mata ya gode ta ɗaga kai ta dawo inda ta tashi ta zauna, tana ta kallon shi don ganin ko zai ci farar da ya riƙe shi bai fara ci ba bai kuma rufe ba, after some seconds ya kai hannu ya ɗauko part guda na faran ya riƙe yana kallo kamar mai jin shakkar ci can dai ya kai baki, slowly ya fara taunawa har ya haɗiye, hannu ya ƙara kaiwa ya ƙara ɗaukowa ya sa baki, Salma dake kallonsa murmushin daɗi ne ya su6uce mata ganin yana ci, "Ka maida mana kallo tun da mu ba fahimtar game ɗin muke ba." Hajiya ta faɗa idonta akan tv, after a while Salma dake kallo ta ji hajiya ta ɗan ta6a mata hannu da sauri ta kai idonta kan hajiyar, tana ɗan murmushi da hannu ta yi mata nuni da Deen ta yi ƙasa da murya ta ce, "Kalli mutumin ki da kamar ba zai ci farar ba." Kallon saitin shi Salma ta yi ta ga yana ta cin farar a nutse kuma da alama ta yi masa daɗi, maido idonta ta yi kan hajiya tana murmushi ta ce ita bata ma yi zaton zai iya ci ba, hajiya dake ƴar dariya ta ce, "Wanccan hamburum burum ɗin, ai in dai ana cin abu kuma ya yi masa daɗi to zai ci." Faffaɗan murmushi Salma ta yi, sosai ta ji daɗin cin farar da ya yi, Balaraba ce ta shigo cikin falon ta nufo inda suke, hajiya ta ce, "Balaraba kin ganni ina cin fara Salma ta kawo mani." Tana murmushi ta ce, "Nima mun haɗu a waje ta bani." Kai hajiya ta ɗaga ta sake cewa, "Kuma ta yi daɗi sosai, komai ya yi daidai daidai har yajin bata cika ba, ga Deeni nan ma da bai ta6a cinta ba yana ci alamar ta yi masa daɗi." Balaraba ta ce, "Eh wllh, nima ta yi mani daɗi don kasa haƙura na yi a can bakin famfo na samu wuri na zauna ina ta ci." Duk suka ɗan yi dariya, kuɗin da ta ruƙo a hannunta ta miƙa ma Salma ta ce mata ga kuɗin farar, tana kallon Balarabar da murmushi ta ce mata ta ɗari biyar ce ta kawo mata sauran ala koro ne ta ƙara mata, Balaraba ta ce, "Ahh, ya za a yi haka kuma Salma?" Ta ce mata Allah kuwa suma su hajiya ala koron ta kawo masu." Hajiya ta ce, "To kuma in ana haka Salma ta ya za a maida kuɗi har a samu riba?" Ita dai murmushi kawai take ta ce ma hajiya ai duk da haka zata samu riba, hajiya ta ce uhmm ta dai faɗa ne kawai, duk yadda Balaraba ta yi da Salma taƙi ta amshi dubu ɗayan, sai da hajiya ta saka baki ta ce ta amsa to kuɗin ta Balaraba da kuma nata, Salma tana dariya ta ce, "To ai hajiya na ki alakoro ne kowa na kawo masa" hajiya ta ce, "Ai duk da haka na san tawan ta fi ta ɗari biyar kuma ga Deeni ma an basa, kin ga dai duk da haka kin bamu alakoron." Da ƙyar ta amsa dubu ɗayan ta yi ma aunty Balaraba godiya, wayar Deen ce ta fara yin ƙara alamar ana kira, tissue ya ciro a cikin tissue box ya goge hannunsa sosai kafin ya ɗauki wayan ya kai kunne, a taƙaice ya ba mai kiran nasa amsa da zai fito yanzu daga haka ya katse kiran, miƙewa ya yi hannunsa riƙe da robar sauran farar ya nufi shiga ciki, hajiya na tsokanarsa tana cewa ya kawo ta ajiye masa ya yi murmushi kawai, bayan ya koma bedroom ɗinsa toilet ya shiga ya wanke hannuwansa da bakinsa ya fito ya saka kaya, lokacin da ya fito idon hajiya a kansa ganin crazy jeans ɗin da ya saka ta ce, "Kai jama'a! Mutum ya ɗauki kuɗi da hannunsa ya siya kaya bana kirki ba da sunan gayu." Yana zuwa saitin ta ya kai hannu ya ɗan ja kumatunta ya ce mata kuɗin wandon zai siya gadonta, ƴar harara ta wurga masa ta ce ya san nawa gadonta yake da zai haɗa shi da yagaggen wando, ɗage mata gira ya yi ya ce tana zaune a ƙauye bata san gayu ba daga haka ya nufi hanyar fita yana murmushi, Salma dake ta bin sa da ido murmushi ne akan fuskarta a ranta tana ayyana ashe yana magana haka..... *_✨A CIKIN RAYUWA✨_* _New story from the writer of 'A Sanadin Makwabtaka',_ ZAINAB BATURE Page 25 Bayan Salma ta yi ma hajiya sallama, tana fitowa harabar gidan ta hango Deen a zaune saman plastic chair da wasu mutane za su kai su biyar a gefe wurin parking space, nufar gate ta yi tana tafiya a nutse, gab da zata isa bakin gate ta ji kaman ana mata magana hakan ya sa ta waiga, daga cikin mutanen da yake zaune da su wani ya yi mata nuni da ta je da hannu, tunkarar su ta yi kanta a ƙasa tana kusa zuwa inda suke Deen ya taso ya nufo ta, daga gaban shi ta tsaya tana kallonsa da ɗan murmushi, hannu ya kai cikin aljihun jeans ɗin sa ya fiddo kuɗi ƴan dubu masu yawa ya miƙo mata, kallon kuɗin ta yi kafin ta ɗago ta kalle sa da alamun rashin fahimta, calmly ya ce, "For the..." Shiru ya ɗan yi alamun sunan farar ya shige masa sai dai ya idasa faɗa da turanci, ta ɗan girgiza masa kai ta ce ai kyauta ta kawo mashi, shiru ya ɗan yi fuskarsa a sake ita kuma tana ta ɗan murmushi, "Ai ba a yin business haka, idan kina ba mutane kyauta how will you make profit?" Ya faɗa idonsa cikin nata, still murmushi ne akan fuskarta ta ce, "Ai ko wanda na bada ɗin ma riba ne." Ɗan murmushi ya yi ya ce ok ta amsa sai ta ƙara improving business ɗin, bin sa da kallon rashin fahimtar abun da yake nufi ta yi, ya gane hakan ya ce mata yana nufin kamar bangaren branding da packaging yadda business ɗin nata zai fi kar6uwa, shiru ta ɗan yi tana kallon kuɗin, ya ce ta amsa ta bar shi da abu a hannu, kallon shi ta yi tana kikkafta idanu ta ce, "To ka rage kuɗin sun yi yawa." Kai kawai ya girgiza mata alamar ba zai rage ba, ɗan langa6ar da kai ta yi tare da ɗan yamutsa fuska gyalenta ya zame baya, hannu ta kai tana gyarawa cikin marairaicewa ta ce masa don Allah Ya rage, ya yi mata wani kallo da ya sa ta yi saurin sauke idonta ƙasa, bin doguwar farar ƙafarsa dake sanye cikin baƙin LV designer sandal ta yi da kallo, ɗagowa ta yi a hankali ta kai hannu ta amshi kuɗin tare da yi masa godiya, ba tare da ya ce komai ba ya juya ya koma wurin mutanen ta bisa da kallo kafin ta juya ta tafi. Washegari da rana bayan Salma ta dawo daga makaranta, tana zaune a cikin baranda tana cin abinci, fitowa innarsu ta yi daga cikin daki ta zauna daga gefenta tana mata murmushi yayin da itama Salma shine akan fuskarta, "Dazun hajiya ta kira tana son awara." Innarsu ta fada, Salma ta gyada mata kai tana murmushi, "Wai nikam kwana biyu mutumin ki Habu bai leko ba, ina ga tun ranar juma'a bai kara shigowa ba." Bayan Salma ta cinye abincin bakinta ta ce, "Wllh nima yana raina, wama ya sani ko saboda abun da Imrana ya yi masa ne ranar shi ya sa bai sake zuwa ba." Innarsu ta ce, "Anya, ban tunanin haka, tun da ai ba lokacin ya fara masa haka ba kuma hakan bai hana sa sake dawowa." Gyada kai Salma ta yi alamar haka ne, innar ta ce Allah Ya sa to lafiya rashin zuwan nasa, "Bari idan na gama cin abinci zan je gidansu in duba ko lafiya." Salma ta fada. Kamar yadda ta fada bayan ta gama ko uniform din jikinta bata cire ba ta wuce gidansu Habu, da sallama ta shiga gidan wanda daga yanayin gidan kana gani kasan gidan iyali ne, wata yar matashiyar budurwa dake duke tana yin wanki a can gefe ta dago da murmushi tana amsa ma Salma kafin ta gaishe ta, Salma ta tambaye ta innarsu ta ce mata tana a daki, bayan ta shiga ciki sai da ta leka dakunan abokan zaman innar su Habu duk ta gaisa da su kafin ta wuce dakin su Habu, "Ah Salma ce, shigo mana." Innarsu Habu dake kishingide a bakin gado ta fada tana kokarin tashi zaune bayan Salma ta yi sallama, nuna mata bakin gado ta yi tace ta zauna, Salma bata zauna ba idanunta akan Habu dake kwance saman shimfida a ƙasa, da sauri ta nufe shi ta duƙa tare da kai hannu ta taba fuskarsa a hankali ya buɗe idanunsa da suka ƙanƙance, sai fitar da numfashi yake a wahalce, da yanayin ruɗu ta ɗaga kai ta kalli innarsu ta ce, "Innarsu Habu bai lafiya ne?" Fuskarta a yamutse cike da damuwa ta ce, "Wllh Salma baya lafiya kusan fin sati." Salma ta ce, "Amman ya je gidanmu ranar juma'a." ta ce, "Eh, ai farko a tsaitsaye ya fara yin ciwon kafin ya kwantar da shi haka." Tambayar abun da ke damunsa Salma ta yi innar ta bata amsa daga zazzabi dai abun ya yi tsanani haka, "To innarsu Habu ba a kai shi asibiti bane?" Hannu ta ɗan yarfa ta ce mata an kai shi chemist aka bashi magunguna daga baya da jikin ya yi tsanani har da ƙarin ruwa mai chemist ɗin ya zo gida ya saka masa amman jikin dai ba sauƙi abun sai ƙara gaba yake, cike da damuwa Salma ta kalli Habu wanda duk ya rame ƙasusuwan jikinsa duk sun fito, "Innar su Habu ai da an kai shi babban asibiti an duba shi sosai." Ɗan juyar da kai ta yi nan da nan idanuwanta suka canza cikin karewar murya ta ce, "Wllh Salma nima hakan na so to amman ba hali, ko ƙarin ruwan da aka saka masa bashin kuɗin na samo, na yi ma babansu magana shima ya ce mani bai da kuɗi sai ya samu, kuma dama ba Habun ne kaɗai bai lafiya ba su ukku ne kwance kawai dai ciwon na shi ya fi yin tsanani..." Ɗan dakatawa ta yi tana share ƙwallan da suka tarun mata, ta ci gaba, "Abun ne sai addu'a kawai Salma, har bashi na nema amman ban samu ba kowa sai ya ce bai da kuɗi, waɗanda ke ɗan baka har sun zo sun fara gajiya saboda rashin cika magana. Wllh har bincikawa na yi ko zan samu abun da zan sayar in kai sa asibitin amman babu wani abun kirki duk na siyar saboda halin rayuwa." Salma da tausayi idanunta har sun kawo ruwa, cike da damuwa tace, "Amman innarsu Habu da kin yi ma innarmu magana na san zaki samu kuɗin a wurinta." Ɗan rausayar da kai ta yi ta ce, "Wllh Salma kunya da nauyi ya sa ban je wurinta ba, ganin duka ranar lahadi babanku ya ba babansu Habu kuɗi masu yawa ya ce a mayar da su makaranta, kuma yana bashi kuɗin bai tsaya 6ata lokaci ba gudun kada su salwanta don da an samu kuɗi ta abinci ake, hakan ya sa ya je ya siya masu duk abubuwan makarantar da ake buƙata, har ya samu ragowar da muka ɗan ci abinci kwana biyu." Shiru Salma ta yi idanunta akan Habu da ya kama mata hannu, cike da tausayawa ta ce, "Sannu Habu ɗan gidana, Allah Ya baka lafiya." Kai kawai ya ɗaga mata, miƙewa Salma ta yi ta ce ma innarsu Habu tana zuwa ta nufi ƙofa ta fita. Sosai innarsu Salma ta shiga damuwa jin halin da ta zo ta faɗi mata Habu na ciki, sam bata ji daɗi ba da innar tasu bata zo ta sanar masu ba har jikin nasa ya yi tsanani haka, shiryawa Salma ta yi cikin doguwar rigar material ta ɗaura yar madaidaiciyar baƙar hijab roba, innarsu dake kallonta bayan ta fito ta tambaye ta wane asibitin zata kai shi ta ce mata babban asibiti, shiru ta yi tana kallonta ganin duk ta shiga damuwa dama haka take da tausayi, tana dawowa gidan bayan ta sanar ma innarsu rashin lafiyan Habu ɗin ta ce zata je ta kai shi asibiti, innar tasu ta ce bari ta ɗauko mata kuɗi, Salma ta ce ta bari ta riga ta ɗauka cikin wanda Deen ya bata, wayarta ta ba Salma ta ce mata ta je da ita duk halin da ake ciki sai ta kira ko da Sagir ne ta sanar masa ta ce mata to tare da ce mata sai ta dawo. Rungume Habu ta yi bayan ta shiga keke nepep sun hau hanya, lokaci bayan lokaci take ɗago fuskarsa ta ce masa sannu ya ɗaga mata kai, bayan sun yi nisa ta ga ya juyo yana ta kallonta, ta yi mashi ɗan murmushi ta ce, "Sannu Habu." Ya ɗaga mata kai sai kuma ta ji daƙyar ya ce mata yunwa yake ji, tambayar shi ta yi to mi yake son ci ya ce mata yoghurt, ɗago kai ta yi ta ce ma mai keken, "Malam don Allah idan ka ga wurin da ake siyar da yoghurt ka ɗan tsaya da mu zan siya masa." Mutumin ya amsa mata da to, yar tafiya kaɗan suka ƙara ya tsaya da su bakin wani shago Salma ta siyo masa yoghurt ɗin na roba, bayan sun ci gaba da tafiya da kanta ta rinƙa bashi a baki yana sha, "Ke ma ki sha..." Ya faɗa yana nishi bayan ya sha da ɗan yawa, tana murmushi ta ce mashi ta ƙoshi ya shanye duka, ya ɗaga mata kai ta ci gaba da bashi. Bayan sun isa babban asibiti cikin sa'a Salma ta samu ganin likita da wuri da taimakon wata nurse mai kirki, awo aka rubuta mata shima ba 6ata lokaci aka yi mata don mai yin awon yana ganin Salma ya ƙyasa, bayan ta kawo ma likitan result nan ya tabbatar mata da typhoid da malaria ne suka kama shi sosai don har bai da jini a jikinsa, nan ya buƙaci jini leda biyu da za a saka masa da gaggawa, Salma duk ta ruɗe ta ce a saka mashi nata idan zai yi, likitan mai kirki yana murmushi ya ce mata an fi buƙatar namiji ya bada, ƙarshe Sagir ta kira ta sanar da shi halin da ake ciki ya tambaye ta irin jinin Habu ɗin ta faɗa masa, ya ce lafiya lau zai iya basa, jin leda biyu ake so ya ce mata bari ya zo tare da abokinsa Aliyu shima irin group ɗin jininsu ɗaya. Ba tare da ɗaukar lokaci mai tsawo ba su Sagir suka zo a saman mashin ɗin Aliyu, bayan an duba jininsu zai yi aka ɗiba aka saka ma Habu, daga baya su Sagir suka tafi Salma kuma ta zauna da shi. Bayan komawar su Sagir ya je ya sanar ma innarsu Habu halin da ake ciki don bata da waya, ba a ɗau lokaci ba suka isa asibitin ita da baban Habu, bayan ganin ɗan nasu nan suka shiga yi ma Salma godiya suna saka mata albarka tana ce masu ba komai, bayan an kira sallar la'asar baban Habu ya tafi yin salla, da zai dawo ya taho ma Salma da chin-chin da ledan zobo guda biyu, da murmushi ya ce mata, "Ƴata Salma ga wannan ki ɗan ta6a ba yawa dai." Tana murmushi ta ce masa ba komai ai bata ma jin yunwa, matsa mata ya yi saida ta amsa, cin-cin ɗin bai wuce biyu ta ci ba da zobo ɗaya, ta miƙa ma Innarsu Habu sauran ta ce ta ci, "A'a Salma, baki ganin daga gida nike ke kau kin sha zama, don Allah ki ci." Ta faɗa tana murmushi, magiya Salma ta shiga yi mata kan ta amsa ta ci ta ce itama bata jin yunwa tana gama cin abinci ta kawo Habu, amsa ta yi da Salma ta matsa mata, dama baiwar Allah yunwa nata nanuƙarta saboda ba su ci abincin rana ba, babansu Habun bai daɗe da ya samo abun da za su dafa ya kai masu, lokacin ne kuma su Sagir suka je suka sanar da su halin da ake ciki, haka ta taho ba tare da an gama abincin ba, bayan ɗan lokaci baban su Habu ya tambayi Salma abun da aka kashe a asibitin, tana murmushi ta ce masa ai innarsu ce ta bada kuɗin kyauta ta kawo sa, ba yadda bai yi ba ta faɗa masa kuɗin da aka kashe ta ƙiya, ta nuna masa ragowar kuɗin dake a hannunta ta ce masa bama a kashe duka kuɗin ba akwai saura, jiki a sanyaye ya yi mata godiya, dama ƙarfin hali ne kawai ba wai yana da kuɗin ba kawai ya sa ran duk inda zai samo kuɗin zai nemo. Saura kaɗan ledan jinin da aka saka ta farko ta ƙare kawai suka ga Habu ya fara wata irin jijjiga, a ruɗe gaba ɗaya suka zagaye gadon suna tatta6a shi tare da kiran sunansa, Salma da ta gama ruɗewa ta ruga da gudu ta je ta faɗa ma wata nurse, bada daɗewa ba suka dawo tare da likita ya nufi gadon Habu da sauri, bincikar sa ya fara yi tare da yi masu tambayoyi suna bashi amsa, tambayoyi ya shiga yi ma Salma game da jinin da aka saka masa tana bashi amsa a ruɗe, ɗibar jinin da aka saka ma Habu likitan ya yi tare da ɗayar ledan da ba a kai ga saka masa ba ya ba nurse tare da faɗi mata abun da yake son ta yi ta amsa da sauri ta bar wurin.....Rafka sallama Imrana ya yi a bakin falon hajiya kan shi ɗauke da robar awara, hajiya dake zaune a cikin falon ta juyo tana amsawa ya shiga ciki, daga gefe ya tsaya yana gaishe da ita ta amsa da murmushi ya ce, "An ce ga awaran." Ta ce to tare da nuna masa kitchen ta ce ya kai ciki ya ce ma Balaraba ta juye ya amsa da to tare da juyawa, lokacin da Imrana ya dawo bayan an juyo ya yi daidai da shigowar Deen cikin falon daga ƙofar waje, bin Deen ya yi da ido kamar idanun nasa za su faɗo har ya ƙaraso ciki ya wuce kujera ya zauna, da rawar jiki Imrana ya gaishe shi ya ɗaga masa kai ba tare da ya kalle sa ba, gaba ɗaya hankalin Imrana ya koma kan Deen ya kasa janye idanunsa yayin da Deen ɗin ya ɗauki remote yana canza channel, maganar da hajiya ta yi masa ta tambaye shi an juye awaran ita ta sa ya maido hankalinsa kan hajiyan ya ce mata eh, ta ce to ya ce ma innar tasu ta gode, yana niyyar tafiya hajiya ta ce, "Ina Salma, yau bata zo ba, ita ta saba zuwa kawo awaran." Dakatawa ya yi ya ce mata tana asibiti, tambayarsa hajiya ta yi wake bai lafiya ko ita, ya ce mata a'a ɗan maƙwabtansu ne ta tafi kaiwa, jinjina kai hajiya ta yi sai kuma ta tambaye shi mike damun yaron, ai kaman yana jira ya fara kora mata bayani tun daga kan zuwa da Habu ke yi gidansu ana bashi abinci har da yadda Salma ke haƙura da nata abincin ta bashi, kaf A to Z sai da ya zayyane ma hajiya yana yi yana kallon Deen, duk abun da yake faɗa Deen na saurare duk da sai ka ce hankalinsa baya akan sau don idanunsa na akan tv, cike da nuna jimami hajiya ta tambayi Imrana babansu baya aiki ne ko kasuwanci, ya faɗa mata tsohon ɗan sanda ne yadda ya ji an ce ba a biya shi kuɗin sallamar shi yadda ya kamata ba bayan ya ajiye aiki, har da sana'ar aca6a da yake yi a yanzu, girgiza kai hajiya ta hau yi da alamun rashin jin daɗin maganar, bayan ta furta, "Allah Ya kyauta." ta ce ma Imrana ya je idan Salma ta dawo ya ce tana kiranta tana son ta san halin da jikin yaron yake ciki, Imrana ya amsa da to kafin ya tafi, kallon Deen hajiya ta yi da alamun ƴar damuwa ta ce, "Al'amarin ƙasar nan tamu dai sai addu'a kawai, mutum ya ɗauki tsawon shekaru yana bauta ma ƙasar sa amman ƙarshe a kasa biyansa hakkinsa yadda ya dace, hakan ba ƙaramin naƙasu zai haifar ma ƙasa ba, don ƙarshe hakan zai iya ja mutane su fara gudun yin aikin gwamnati, ba kamar jami'an tsaro wanda rasa masu shiga aikin babbar barazana ce ga tsaron ƙasa. Ba da daɗewa ba dama na gani a labarai yadda tsofaffin ƴan sanda suka gudanar da zanga-zangar kai koken halin da suke ciki da yadda gwamnati ta manta da su, al'amarin dai sai dai a ce Allah Ya kyauta." Slowly Deen da ya juyo yana saurararta ya amsa da Amin. Tun bayan da likita ya tabbatar masu cewa Habu ya rasu Salma ke ta faman rizgar kuka, baiwar Allah ita gani take tamkar ita ce silar mutuwar ta shi tun da ita ta ɗauko shi ta kawo shi asibiti, duk da halin damuwa da iyayen Habu ke ciki na rasuwar ɗan nasu su ke ta faman rarrashin Salma, bayan an sallame su suka baro asibitin baban Habu na rungume da gawar ɗan nasa ita kuma innar Habu ta rungumo Salma ta gefe, har suka fito daga cikin asibitin kuka Salma ke ta yi tana tafiya da ƙyar, keke nepep baban su Habu ya tsayar masu suka shiga ya ba innar gawan Habu ya ce su yi gaba zai biyo su a mashin, bayan sun hau hanya Salma na kuka tana kallon fuskar Habu tamkar zata ƙira shi ya buɗe idanu, abubuwa da dama ne suka shiga dawo mata game da yaron, tuno ɗazun lokacin da zata kawo sa asibiti ta siya masa yoghurt har ya ce itama ta sha ta yi, ashe ita ce magana ta ƙarshe a tsakanin su, tuna hakan ya sa ta sake fashewa da wani sabon kukan, innarsu Habu da mai keken suna ta bata haƙuri, wayar innarsu dake a cikin aljihun doguwar rigar jikinta ce ta fara ringing, bayan ta ciro ta ɗauka tare da kaita kunne, tun kafin innar tasu ta ce wani abu ta jiyo shasshekar kukanta, da alamun ruɗewa ta ce, "Salma lafiya na ji kaman kina kuka? Ya jikin Habun? Yanzu nike son tahowa duba shi Sagir ya faɗa mani sun zo sun bayar da jini an saka masa..." Bata ƙarasa rufe baki ba cikin kuka Salma ta ce, "Innarmu Habu ya rasu...." Innar tasu ta saka dogon salati.... *_✨A CIKIN RAYUWA✨_* _New story from the writer of 'A Sanadin Makwabtaka',_ ZAINAB BATURE 26 Lokacin da su Salma suka iso, wasu a cikin mutanen gidan su Habu na a waje suna dakon isowar su, keke napep ɗin na tsayawa shima baban su Habu ya ƙaraso hakan ya sa iyalan nashi nufo su, fitowa innarsu Habu ta yi idanunta cike da ƙwalla, bayan baban su Habu ya sauko daga saman mashin ɗinsa ya nufi 6angaren da Salma take, cikin kwantar da murya yake rarrashinta ya ruƙo ta ta fito, su Sagir da abokansa dake zaune daga can gaban wani gida dake kallon nasu suka taso zuwa wurin su, Salma na ganin Sagir sautin kukanta ya ƙaru, fuskarsa da alhini ya kamo ta ya rungume ta ta gefe yana rarrashinta ya nufi gida da ita, suna shiga cikin zaure daidai da fitowar innarsu tana gyara hijab, dakatawa ta yi tun kafin ta ce wani abu Salma ta nufe ta da sauri ta faɗa jikinta tare da fashewa da matsanancin kuka tana faɗin Habu ya rasu dama bata kai shi asibitin ba, kama ta innar tasu ta yi suka shiga cikin gida ta nufi ɗakinta da ita, bayan ta zaunar da ita a bakin gado itama ta zauna tare da rungumo ta jikinta ta shiga rarrashin ta tana kwantar mata da hankali. Ba'a ɗauki lokaci ba aka gama shirya Habu, a nan kofar gida aka yi masa salla har da su Sagir da baban su da ya dawo don halartar jana'izar, lokacin da aka gama sallar Hamza ya ruga cikin gida ya nufi ɗakin innarsu, Salma na kwance ta duƙunƙune a saman gado har lokacin kuka take ta yi, Hamza ya ce mata gashi can za a tafi a rufo Habu, tana jin hakan ta miƙe idanuwanta duk sun kumbura ta nufi hanyar waje, a cikin zaure ta tsaya tana leƙe yayin da take ci gaba da kuka ƙasa-ƙasa, tana ganin lokacin da aka wuce da shi ta duƙe nan wurin ta saka kanta a cikin gwiwuwinta ta shiga raira wani sabon kukan. Bayan sallar magrib duk suna zaune a cikin baranda, Salma na kwance a saman tabarma ta tada kanta a saman cinyar innarsu, babansu na daga gefe saman darduma sai Sagir da Auwalu na zaune a saman tudunkar baranda, basu jima da dawowa daga rufo Habu ba aka yi sallar magrib, bayan gama sallar ne duk suka shigo gida, gaba ɗaya jimamin rasuwar yaron suke, sauke ajiyar zuciya babansu ya yi ya ce, "Haka rayuwar take, dukkan mai rai mamaci ne, kowa da lokacin sa ya yi to ba makawa sai ya tafi ba tare da an ƙara ma mutum ko da sakan ba, shi yasa ake son mutum ya zauna a cikin shiri kuma ya kasance mai aikata aikin alkhairi sannan ka zauna da kowa lafiya. Yaron nan ina tunanin bai fi shekaranjiya ba da na je wurin mahaifinsa na gansa, yau gashi babu shi." Girgiza kai innarsu ta yi cike da jimami ta ce ko ranar juma'a ya shigo nan har aka bashi abinci ya je su ci da ƴan'uwansa ashe ƙarshen shigowar shi gidan ke nan, jin maganar innar tasu ya sa Salma fara yin kuka ƙasa-ƙasa, haƙuri iyayensu suka shiga bata, "Imrana yanzu hankalinka sai ya kwanta ko? Habu ba zai ƙara shigo maku gida ba har ya ci maku abinci." Sagir ya faɗa yana jifar Imrana da harara da yake akwai hasken kwai mai caji wurin ya yi fayau, duru duru Imrana ya yi ya kasa cewa komai, dama tun da ya ji Habu ya rasu duk jikinsa ya yi sanyi laƙwas, jin maganar Sagir babansu ya tambaye shi mi ya sa ya faɗi haka, nan ya kwashe yadda Imrana ke kyarar yaron saboda abinci ya faɗa masa, sam baban nasu bai ji daɗin maganar ba nan ya shiga yi ma Imrana nasiha kan ya rinƙa ɗaukar komai ba komai ba ya nuna masa duk abun da mutum ya bada shike da riba musamman ciyar da wanda ke jin yunwa ba ƙaramar falala hakan yake da, da alamu nasihar ta shiga Imrana sosai har da kuka ya yi tare da yi ma babansu alƙawarin ba zai sake ba, kiran sallar isha'i da aka fara ya sa duk suka miƙe, wurin Salma baban nasu ya nufa ya ɗan duƙa yana kallon ta ya ce, "Ki yi haƙuri mamana, ki daina saka damuwa a ranki, komai kika ga ya faru to dama can rubutacce ne, ko baki kai shi asibiti ba dama Allah Ya rubuta a yau zai bar duniya, abun da kika yi mai kyau ne kuma kina da lada, kada hakan ya sa ki sare ki ci gaba da taimakon duk wanda yake a hali kuma kika ga kina da ikon taimaka mashi." Kai Salma ta ɗaga ma mahaifinta tana kallon shi idanuwanta cike da ƙwalla, ya ce, "Yauwa mamana, pls ki cire komai a ranki kada damuwa ta sa ki kamu da ciwo, mu yi masa addu'a ita ce yake buƙata a yanzu, duk da muna kyautata masa zaton ya huta tun da yaro ne." Nan ma kai ta ɗaga masa, innarsu ta ce ai yanzu haka ma akwai zazza6i a jikinta kuma ta san bata rasa ciwon kai saboda kuka, miƙewa baban ya yi yana tambayar ta bata magani ta ce masa eh bayan ta dawo daga gidan gaisuwar ta bata, nufar hanyar fita ya yi yana faɗin In sha Allahu zata warware damuwa ce, daga haka suka tafi masallaci shi da duka yaran maza. Bayan Salma ta yi sallar isha ita da innarsu, a nan cikin barandar ta sake kwanciya innarsu kuma ta wuce kicin don ta ɗumama mata ruwa ta yi wanka, ita ta haɗa mata ruwa ta zo ta kama ta ta kai ta har banɗakin, bayan ta yo wankan ta saka wata doguwar riga tare da hula, sosai ta ji daɗin jikinta don dama tun wankan safe da zata tafi makaranta bayan ta dawo bata samu yin wani ba ta tafi kai Habu asibiti. Bayan mazan sun dawo daga salla anan cikin barandar suka zauna cin abinci, babansu bai shigo ba yana can wurin zaman gaisuwan, shi kuma Sagir ɗaukan nashi ya yi ya fita ƙofar gida, Auwalu nan ya zaune inda ya saba zama yana cin abincin yana latsa waya as usual, saida innarsu ta lalla6a Salma sannan ta ɗan ci abincin don da ta ce baza ta ci ba, "Yaya Salma na manta ɗazun da na kai ma hajiya awara ta tambaye ki, shi ne na faɗa mata kin tafi kai Habu asibiti ta ce idan kin dawo in ce maki ki je." Imrana da duk ya yi sukuku ko abincin ya kasa sakin jiki ya ci ya faɗa yana kallon Salma dake zaune ta jingina da bango, shiru ta yi bata ce komai ba innarsu dake kallonta ta ce, "To wannan anya ma kya iya zuwa, bari Imranan idan ya gama cin abincin ya je ya sanar mata baki jin daɗi don kada ta ji shiru." Ɗan girgiza kai Salma ta yi a sanyaye ta ce mata bari ta je, innar tasu ta ce zata iya ta amsa mata da eh, miƙewa ta yi ta nufi ɗakinta walking slowly, ƴar madaidaiciyar hijab ta ɗauro a saman rigar jikinta, bayan ta fito ta ce ma innarsu sai ta dawo, ta amsa mata da to sai kuma ta ce ko ta jira Imrana ya ƙarasa sai ya rakata, ta ce a'a bari ta je kawai dare na yi daga haka ta nufi ƙofa ta fita. Da sallama ta shiga cikin falon hajiya, yau ma Deen ne kadai zaune yana playing PS ya saka headphones jikinsa yana sanye da kayan shan iska riga armless da wandonta, yau ta ci sa'a tana shiga ya juyo ya kalle ta, kanta a ƙasa ta ƙarasa cikin falon ta tsaya ɗan nesa da shi daga gefe, gaishe shi ta yi da alama ya ji ba tare da ya cire headphones ɗin ba ya ɗaga mata kai, daga haka ta maida kanta ƙasa, motsin da ta ji ya sa ta ɗagowa ta ga ya kai hannu ya ɗauki wayarsa, kira ya yi ya kai kunne ta ji ya ce an zo wurinta hakan ya sa ta gane hajiya ya kira, after few seconds ya juyo yana niyyar ce mata ta zauna sai ga hajiya ta fito hakan ya sa shi fasa yin magana ya juya ya ci gaba da abun da yake yi, nufo cikin falon hajiya ta yi fuskarta a sake bayan ta ƙaraso ta ce, "Salma.." A hankali ta amsa mata tare da gaishe da ita idanunta a ƙasa, zama hajiya ta yi tana kallonta ta ce, "Ki zauna, kun dawo daga asibitin ke nan, ɗazun ɗan'uwanki da ya kawo awara ke faɗa mani kin tafi kai yaron makwabtan ku da bai lafiya asibiti, shine na ce idan kin dawo ya ce ki zo don ina son sanin halin da yaron yake ciki. To ya jikin yaron?" Kamar jira take ta tambaye ta game da jikin shi kawai sai gani hajiya ta yi ta fashe da kuka mai sauti, salati hajiya ta saka ta shiga tambayar ta lafiya miya faru ne, kukan da Salma take yi da maganganun hajiya su suka janyo attention ɗin Deen ya dawo kan su, kallon Salma dake a tsaye tana kuka ta rufe fuskarta da gefen hijab ya shiga yi ba tare da ya ce komai ba, miƙewa hajiya ta yi ta kamo hannun Salma guda tana tambayarta mi ya faru ne, cikin kuka Salma ta faɗa mata yaron ya rasu, dogon salati hajiya ta saka ta juya ta kalli Deen da idonsa ke akan su ta ce masa ya ji yaron da aka ce ta tafi kaiwa asibiti ɗazun ya rasu, ɗan buɗa ido ya yi hajiya ta jawo Salma jikinta tana rarrashinta tana cewa, "Ki yi haƙuri Salma, dukkan mai rai dama mamaci ne, lokacinsa ne ya yi. Allah Ya jiƙansa." Cikin kuka Salma ta ce dama bata kai shi asibitin ba...ɗan murmushi hajiya ta yi jin maganar da Salmar ta yi wadda ke bayyana yarintarta, kallon Deen hajiya ta yi still da murmushi akan fuskarta ta ce masa wai ita gani take har da kai shi asibitin da ta yi ne ya sa yaron ya mutu, shi ma ɗan murmushi ya yi kawai, zama hajiya ta yi da Salmar tana ci gaba da rarrashinta tare da nuna mata ba don kai shi asibitin da ta yi bane ko bata kai shi ba idan yau ne wa'adin da Ubangiji ya ɗaukar masa zai mutu, wayar hajiya da ta ajiye a gefe ta fara yin ringing alamar ana kiranta, kallon wayar ta yi ta ga wanda ke kira, sakin Salma ta yi ta ɗauki wayar, saboda shesshekar kukan da Salma ke yi yasa ta nufi hanyar ɗakinta ta ce tana zuwa, bayan tafiyar hajiya kife kai Salma ta yi a saman hannun kujera tana ci gaba da yin shesshekar kuka a hankali, duk abun nan idon Deen na akanta, can ya miƙe yana tafiya a nutse ya nufi wurin da take, ta gefen da ta ɗaura fuskarta ya tsaya yana kallonta wuyan hijab ɗin jikinta ya ɗan zame hakan ya bayyanar da baƙar sumarta, magana ya yi mata calmly saidai da alama bata ji shi ba, ɗan jimm ya yi yana ta kallonta sai kuma ya ɗan rankwafa, "Salmerh..." A karon farko ya kira sunanta, tana cikin kuka ta tsinci sautin daddaɗar muryar da bata iya tantance ko ta waye ba ta kira sunanta, da sauri ta ɗago kanta da alama ma ta tsorata da kiran sunan nata da ta ji an yi, wani bugu gabanta ya yi ganin shi a kusa da ita, bin kyakkyawar fuskarsa ta yi da kallo ƙirjinta na ci gaba da bugawa da ƙarfi, sai yanzu da ta samu kusanci da shi sosai ta ƙara ganin ainihin tsantsar kyawun shi, shima kallon cute fuskarta ya ke wanda yau ne ya ta6a ƙare mata kallo sosai, idanuwanta sun yi ja har lokacin da ɗan kumburi akan su, yayin da dogayen gashin idonta suka mammane ma juna saboda jiƙewar da suka yi da hawaye, bin juna suka ci gaba da yi da kallo shi ya kasa ce mata komai ita kuma tana ta ɗan kikkafta idanu tana sakin ƴar ajiyar zuciya, tun da ta yi arba da fuskarsa a kusa da ita ta nemi kukan da take yi ta rasa, hannunsa ya ɗago ta maido idonta kan abun da ya miƙo mata, kallon shi ta yi ba tare da ta amsa ba ya ɗan lumshe idanunsa with calmness ya ce, "Take it....wipe ur tears." Hannunta na ɗan rawa ta amsa hanky ɗin da ya bata, maimakon ta yi abun da ya ce sai ta bi hanky ɗin da kallo don a wurinta na musamman ne don wani irin taushi ne da shi ga wani sanyi sanyi da jikinsa ke saki kamar yana da lema kuma ba lemar ba ce, a hankali ta ɗaga ido ta kalli Deen ya yi mata alamar ta yi abun da ya ce da kan shi, kai hanky ɗin ta yi fuskarta wani irin ƙamshi mai nutsar da zuciya ya ziyarce ta, slowly ta shiga goge hawayen fuskarta har bata san tana ɗan lumshe ido ba saboda taushin hankyn, bata daɗe tana goge fuskar ba ta cire ta miƙo masa, bai amsa ba calmly ya fara mata magana, "Stop worrying, you didn’t cause his death. Kin yi abu mai kyau da kika taimake shi, it’s just that lokacinsa ya yi shi ya sa ya mutu." Tamkar yana biya mata karatu tana ɗauka yadda ta bisa da ido, ɗage mata gira ya yi alamar ta gane, tamkar yar ƙadangaruwa haka ta gyaɗa masa kai, miƙewa ya yi, ganin yana niyyar tafiya da sauri ta ce masa, "Ga shi.." Ba tare da ya kalli hankyn da take miƙo masa ba ya ce ta ci gaba da using da shi ya san ba gama kukan ta yi ba, da sauri cikin muryar kuka ta ce, "Na daina..." Ya ɗan juyo ya kalle ta da murmushi, ba tare da ya ce mata komai ba ya juya ya nufi hanyar shiga 6angaren da bedrooms suke ta bisa da kallo har ya shige, maido idanunta ta yi tana kallon hankyn tana ɗan yamutsa shi da hannunta, bai daɗe da shigewa ba sai ga hajiya ta dawo, zama ta yi a inda ta tashi kusa da Salma tana kallon ta ta ce, "Yi haƙuri Salma na bar ki zaune wata doguwar waya aka kira ni ne, kin daina kukan ko?" Kai ta ɗaga mata alamar eh ta ce yauwa haka yakamata, tambayoyi ta shiga yi mata game da gidan su Habu Salma tana bata amsa, bayan ta gama tambayar tata ta ce ko a zuba mata abinci Salma ta ce mata a'a yanzu tana gama ci ta taho nan, shiru suka ɗan yi can hajiya ta tambaye ta Deen fita waje ya yi ne Salma ta ce mata a 'a ciki ya shiga ta ce ok, Salma na ta jira ta ga Deen ya fito ta bashi hanky ɗinsa, har bayan wani lokaci bai fito ba gashi dare na ƙara yi, ƙarshe ta yanke tafiya kawai tun da bai fito ba, sallama ta yi ma hajiya ta ce zata tafi, miƙewa hajiya ta yi tana ƙara kwantar mata da hankali ta ce in sha Allahu gobe zata saka Balaraba ta rako ta ta yi gaisuwa gidan su yaron Salma ta amsa da to daga haka ta tafi. Tana tafiya kan hanya tana tunanin abun da ya wakana tsakaninta da Deen, ɗago hanky ɗin ta yi tana kallo, a hankali ta kai shi saitin hancinta, ɗan murmushi wanda bata san daga ina ya fito ba ya su6uce mata. Bayan ta koma gida innarta ke sanar mata aunty Kubra ta kira tana son magana da ita bayan ta ji abun da ya faru, amsar wayar innarsu ta yi ta tafi ɗaki bayan ta zauna a bakin gadonta ta kiran aunty Kubra, saida ta yanke sannan ta kira Salma ta ɗaga, "Hello baby!" Ta faɗa da alamun tashin hankali, murya can ƙasa Salma ta amsa tare da gaishe ta, amsa mata gaisuwar ta yi ta ce, "Na ji abun da ya faru, ai ba laifin ki bane baby ke da kika yi taimako kawai lokacinsa ne ya yi. Pls ki daina damuwa gashi na ji ance har zazzabi ya kama ki." Tana kikkafta idanu ta ce mata ai ta bari, "Yauwa my baby ki kwantar da hankalinki kin ji, Allah Ya jikansa ya sa mai ceton iyayensa ne, kema Allah Ya baki ladan taimako." Ta amsa mata da amin, "Yanzu ya jikin naki, har yanzu akwai fever ɗin?" Girgiza kai ta yi ta ce mata a'a ya sauka, "Kin ci abinci?" Ta ce mata eh, "To kin ci sosai kuwa, ko akwai abun da kike so in saka Sagir ya kawo maki?" Ɗan murmushi Salma ta yi ta ce mata a'a, "Kai babynah, nasan ki da nauyin baki feel free ki faɗa mani komi kike so." Still da murmushi akan fuskarta ta ce mata Allah bata son komai, "Ko kaza?" Wannan karon dariya maganar aunty Kubra ta bata ta ce mata itama bata so, waya suka ci gaba da yi tana ƙara rarrashinta kan ta kwantar da hankalinta ta cire damuwa a ranta, kafin su yi sallama sai da ta ƙara tambayar ko akwai abun da take buƙata ta ce mata ba komai ai ta faɗa mata game da kuɗin da Deen ya bata ta ce ta ƙi ma ta amshi wasu ciki, aunty Kubra ta yi murmushi ta ce mata a'a ta riƙe abunta ta yi abun da ya ce ta yi da su, daga baya suka yi sallama tana ƙara jaddada mata ta cire damuwa a ranta. Bayan sun gama yin wayar zaune ta yi a wurin kamar mai yin tunani, kai idonta ta yi kan hanky ɗin Deen da ta ajiye a gefe, a hankali ta kai hannu ta ɗauko ta ƙura mashi ido tana kallo, a cikin ranta take ƙara yaba irin kirkin Deen tana ɗan murmushi, after some minutes ta miƙe don ta kai ma innar su wayarta, ba da daɗewa ba ta dawo ɗakinta, gado ta nufa ta kwanta, ɗan tsoro ta ji na niyyar kamata saboda tunanin Habu da ya shiga dawo mata, ta yi saurin kauda tunanin ta koma tunano abun da ya faru tsakaninta da Deen, a hankali ta kai hankyn da take riƙe da shi hancinta tana shaƙar daddaɗan ƙamshin da yake saki tana jin wata irin natsuwa a cikin zuciyarta, slowly idanunta suka fara lumshewa a haka har bacci ya yi awon gaba da ita.... *_✨A CIKIN RAYUWA✨_* _New story from the writer of 'A Sanadin Makwabtaka',_ _ZAINAB BATURE_ 27 Washe gari misalin ƙarfe sha ɗaya na safe bayan hajiya ta gama yin breakfast suka fito don tafiya yin gaisuwa tare da Balaraba kamar yadda ta ce ma Salma, har da Deen za a je, bayan sun fito ya tambayi hajiya za su je da mota ne ta ce kamar ba sai sun hau mota ba tun da an ce maƙwabtan su Salma ne duk da ita bata ma san gidan su Salman ba ta dai san a unguwar suke, dama asali ta dalilin Balaraba ta san su Salma na yin awara har take sawa suna yi mata, tambayar Balaraba ta yi ko gidansu Salma da nisa ta ce mata a'a kusa ne da an fita tsallaken hanya, bayan sun fito su officers suka shiga gaishe da hajiya tare da Deen, bayan sun gama gaisawa suka tambayi unguwa za su je nan hajiya ta sanar masu nan tsallake gidan gaisuwa za su je, Officers guda biyu ne suka bi bayansu don yi masu rakiya, tun da suka fito mutane ke ta zuwa suna gaishe da hajiya ita da Deen har suka ƙarasa cikin layin su Salma, da yake gidan rasuwa ne suna shiga layin suka gane gidan dama kuma ga mutane masoyan Deen da suka rufa masu baya, mutanen dake zaune wurin amsar gaisuwan suna ganin su duk suka miƙe suka shiga gaishe da su suna yi masu sannu da zuwa, da fara'a hajiya ke amsawa haka ma Deen fuskarsa a sake yake amsa ma mutane gaisuwar da suke yi masa, hajiya ta tambayi mahaifin yaron mai rasuwa aka nuna mata baban Habu, gaisuwa ta yi masa haka ma Deen da Balaraba, hajiya ta ce zasu shiga su yi ma mahaifiyar yaron gaisuwa, da sauri baban Habu ya shige gaba, dama tun kafin su shigo wasu daga cikin yaran gidan tuni sun kai rahoton zuwan nasu, a nan waje Deen ya tsaya da jami'an da suka yo masu rakiya hajiya da Balaraba suka bi bayan baban Habu, lokacin da suka shiga a tsakar gida suka iske matan gidan da ƴan gaisuwa duk sun fito suna tsaye, cikin girmamawa suka shiga yi ma hajiya sannu da zuwa suna gaishe da su, duk da sun san hajiya mutuniyar kirki ce mai taimakon mutane ba su yi zaton ganin ta gidan da sunan ta zo gaisuwa ba, koda a ka yi mata tayin shiga ɗaki cewa ta yi a'a daga nan waje ma ya isa, da sauri baban Habu ya nufi dakinsa ya ɗauko wata yar babbar darduma ya zo ya shimfiɗa masu daga gefen ɗakunan, hajiya kawai ta zauna ita Balaraba a tsaye ta tsaya, bayan an nuna ma hajiya innarsu Habu dake tsugunne gefe ta yi mata gaisuwa tare da bata haƙurin rashin da ta yi, cikin girmamawa kan ta a ƙasa take amsa ma hajiya, bayan ta gama mata gaisuwan ta sanar da su yadda akai ta samu labarin rasuwan, maida kallonta ta yi kan baban Habu dake a tsugunne shima ta ƙara masa gaisuwa cike da girmamawa yake amsawa ta ɗaura da cewa, "Abu idan Allah Ya ƙaddaro ba makawa sai ya faru, amman idan al'amari ya tsananta sai a zo a nemi taimako, ni ina zaune ba sanin abubuwan dake faruwa nike yi ba sai idan an zo an sanar mani, ko yaya ne dai idan an zo an sanar ba a rasa abun yi ba." Cike da dattako take yin magana, kan baban Habu a ƙasa ya ce mata lokacin da ya ga jikin nasa ya tsananta sannan ga ƴan uwansa guda biyu suma duk a kwance sai da ya je da niyyar neman taimako a wurinta sau biyu, sai dai bai samu ganawa da ita ba saboda jama'a da suka yi yawa, ƙarshe dole ya haƙura ya siya masu magani da abun da yake da shi, kai hajiya ta jinjina daga yanayin fuskarta zaka fahimci bata ji daɗin hakan ba, ta ce masa da yake Deeni ya zo shiyasa jama'a suke yin yawa kowa da buƙatar da ta kawo shi, ƴan tambayoyi ta yi masa game da aikinsa da ya ajiye yana bata amsa a nutse, addu'ar Allah Ya ƙara rufa asiri ta yi ta ce In sha Allahu za a ga abun da za a yi, kallon Balaraba ta yi ta ce mata ta amshi lambar wayarsa daga haka ta miƙe, duk mutane suka rufo mata baya don yi mata rakiya, har ƙofar gida wasu suka biyo ta don su ga Deen, tana fitowa shima ya miƙe a lokacin mutanen dake tare da shi sun ƙara yawa har da su Sagir da sauran matasa ƴan sabon club ɗin sa, mutanen da ke zaman amsar gaisuwan ma bayan ta fito duk suka miƙe suna yi mata sallama da godiya, sai da baban su Habu ya rako ta har wurin gidan su Salma hajiya ta juya ta ce masa ya koma shi da ke amsar gaisuwa, kai a ƙasa ya yi mata godiya kafin ya juya, kallon Balaraba ta yi da ɗan murmushi ta tambaye ta ina ne gidan su Salma lokacin suna a saitin gidan, bayan Balaraba ta nuna mata ta ce bari su shiga yau a gaisa, Sagir na ganin gidan su suka nufa ya yi saurin riga su shiga don ya sanar da zuwan su, ganin Deen zai wuce hajiya ta tambaye sa gida zai tafi ya ce mata eh sai ta dawo, da murmushi ta ce shi ba zai zo su je tare ba ya yi godiyar hidimar awara da ake masa, ɗan murmushi kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba suka nufi gidan, a bakin kofar gidan jami'an da suka rako su suka tsaya tare da dakatar da mutanen da suke tare da su a nan, hajiya na shiga cikin gidan da sallama innarsu Salma da ta fito ta amsa cikin fara'a tana mata sannu da zuwa, gidan nasu fes da shi tamkar a zuba abinci a saman simintin tsakar gidan a ci yadda ya yi tas, dama duk safiya kafin Salma ta tafi makaranta take share gidan ƙwal sai innarsu ta ƙarasa sauran gyaran gidan, gaba ɗaya tsakar gidan ya karaɗe da ƙamshin tsintsiyar ƙamshi mai daɗi, "Sannun ku da zuwa hajiya, maraba..." Baban su Salma da bai kai ga fita ba ya shiga faɗa bayan ya fito daga cikin ɗaki, tana murmushi take amsa masu, innarsu Salma ta nuna masu ɗaki ta ce su shiga, hajiya ta ce, "A'a nan ma ya isa, dama daga gidan gaisuwa muke na tambayi Balaraba gidan na ce bari a shigo a gaisa mu yi godiyar hidiman awara da ake yi mana." Innarsu Salma dake ta fara'a ta ce ai ba komai, baban su Salma ne ya fito daga ɗakinsa da sauri yana riƙe da tabarma babba ya shimfiɗa a cikin baranda ya ce ma hajiya ga wuri tana ta tsayuwa, nufar cikin barandar ta yi tana faɗin dole dai sai ta zauna ke nan yana ta murmushi ya ce yadda za a gaisa sosai, kafin ta zauna ta kalli hanyar waje ta sanar da su tare suke da Deen, baban su Salma ya nufi hanyar zauren da sauri, sai ga su sun shigo tare har da Sagir dake ta faman washe baki kamar bakin nasa zai yage, ganin abun yake kamar mafarki Deen Jr yau a cikin gidan su, wanda idan da wani ya faɗa masa hakan abu ne da zai yuwu tabbas zai ƙaryata da babbar murya, a bakin barandar Balaraba ta tsaya shi kuma Deen ya ƙarasa kusa da hajiya ya zauna, innarsu Salma da ta tsugunna can gefe tana ta kallonsa don wannan ne karo na farko da ta ta6a ganinsa ido da ido, daga gefe shima baban su Salma ya duƙa yana gaishe da hajiya, Deen da tun da ya shigo kansa na a ƙasa ya ɗago yana amsa masu gaisuwar da suke masu a nutse, "Ai na ce shima ya shigo ya yi godiya anata masa hidiman awara." Hajiya ta faɗa idonta akan Deen tana murmushi, "A haba ai ba komai wllh, mu ma muna ta ganin abun arziƙi. Allah Ya saka da alkhairi Ya ƙara girma da ɗaukaka." Babansu Salma ya faɗa da fara'a, itama innar tasu ta ce ai ba komai ta yi ma Deen godiya, shi dai bai cewa komai sai ɗan murmushi dake a kan fuskarsa yana yi yana sauke idanunsa, "Ina Salma, ina ce dai ta warware ko? jiya da ta je tana ta kuka lokacin da ta sanar mani da rasuwan yaron." Hajiya ta faɗa, innarsu Salma ta ce, "Eh wllh haka tai ta faman kuka wai ita gani take don ta kai shi asibiti ne ya rasu, har sai da zazza6i ya kama ta, amman ta samu sauƙi har ta tafi makaranta ma." Hajiya dake murmushi ta ce ina ruwan Salma ai abu mai kyau ta yi lokacinsa ne ya yi, tambayar jikin nata da sauƙi sosai har ta tafi makaranta hajiya ta yi, baban su ya ce, "Ta samu sauƙi sosai, dama jiyan saboda kukan da ta sha ne sai kanta ya fara ciwo daga baya sai zazzabi ya rufe ta, bayan ta sha magani ta samu sauƙi, yau da safe har ta tafi makaranta, sai da aka ce mata ta bari ta ƙara warwarewa ta ce ta samu sauƙi, da yake Salma akwai son karatu ba ƙaramin dalili ne ke hana ta zuwa makaranta ba." Ya ƙarasa da murmushi, kai hajiya ta jinjina ta ce Allah Ya sa ma karatun albarka, duk suka amsa da Amin, "Daga gidan rasuwan muke muka yo ma iyayen yaron gaisuwa. Mutane ana cikin hali, irin wannan ba sani mutum ke yi ba idan ba an zo an faɗa ba, ko yaya ne idan an zo in faɗa halin da ake ciki ba a rasa taimakon da za a yi, duk da ya ce ya zo nan gida wuri na har sau biyu bai samu gani na ba, saboda mutanen da ke zuwa yanzu sun yi yawa saboda zuwan Deeni." Gyara zama baban su Salma ya yi ya ce wllh al'amurra yanzu sai godiyar Allah, nan ya shiga faɗa mata halin da mahaifin Habu da iyalinsa suke ciki duk sanadiyyar rashin yi masa sallamar kirki bayan aje aiki, bayan ya gama innarsu Salma ma ta ɗora da faɗin abubuwan da ta sani har da zuwan da Habu ke yi gidan da yadda wasu lokuttan Salma ke bashi abincinta su je su ci da ƴan'uwansa da sauran alkhairai, har da yadda ta sa a basu kuɗi a cikin wanda Deen ya basu don a mayar da yaran makaranta, ashe ba rabon shi Habun ya koma, hajiya da ke ta ɗan murmushi ta ce, "Maa sha Allah, hakan abu ne mai kyau, yadda take tausayi da kyautata ma mutane itama in sha Allahu Allah zai tausaya mata Ya kyautata rayuwarta." Duk suka amsa da Amin, innarsu Salma ce ta miƙe da sauri tana faɗin su yi haƙuri sun zo an barsu ba a kawo masu ko ruwa ba, dakatar da ita hajiya ta yi ta ce mata ba sai ta kawo ba ai safiya ne, sallama ta yi masu ta ce tun da an gaisa, Deen ya fara miƙewa suna ƙara yi masa godiya ya nufi hanyar fita Sagir na daga gefensa. Bayan sun koma gida Deen ya zauna da hajiya kan taimakon da yake son yi ma baban Habu, sannan ya nemi shawararta kan wani aiki da ya yanke yana son ba Salma a ƙarƙashin foundation ɗin shi, bayan ya bayyana ma hajiya aikin wanda abinci ne yake son za su nemo mutane da za su rinƙa dafawa ana raba ma mutane, ita Salma so yake ya ɗaura ta akan abun wato ta rinƙa kula da komai sannan ta rinƙa bincika masa mutanen da ta ji suna cikin buƙatar taimako sosai, hajiya ta goyi bayan hakan ta ce sadakar abinci yana da falala sosai duk da dama suna yi cikin azumi, ta ce kuma aikin dafa abincin zai taimaka ma matan da za su rinƙa yi tun da albashi za a rinƙa biyan su, har ta bada shawarar a saka wata daga cikin matan baban Habu a aikin idan suna so hakan zai taimaka masu sosai, sai dai a yadda ya bayyana mata kowacce rana za a rinƙa yin abincin ta bada shawarar a rinƙa yi sau biyu ko ukku a sati don yi kullum ɗin zai iya kashe ma wasu zuciya musamman magidanta, sannan ta nuna mashi akwai wasu buƙatun da ake taimaka ma mutane da su, daga baya ta tambaye shi aikin da yake son Salma ta yi yana ganin ba zai ta6a karatunta ba gashi an ce tana son karatu sosai kada a takura mata, ya ce yana ganin ba zai shafi karatunta ba tun da ita hajiya zata rinƙa providing masu komai na yin abinci ita Salma kamar zata saka ido ne kan yadda komai ke gudana kuma ita zata rinƙa zuwa wurinta tana amsar ma masu aikin abubuwan da ake buƙata, hajiya ta ce ta fahimta lafiya lau ya yi magana da Salma ta tuntun6i mahaifiyarta sai a ji idan suna son aikin, ya ce ok zuwa anjima ta sa a kira mashi Salmar tun da bai da lokaci sosai ya kusa tafiya. Wuraren azahar hajiya ta kira innarsu Salma ta tambayi ta dawo daga makaranta innar ta ce a'a ta dai kusa, hajiya ta ce mata to idan ta dawo ta huta zuwa anjima tana nemanta, bayan Salma ta dawo sosai ta yi mamakin jin hajiya ta zo nan gidansu kuma har da Deen, bayan ta ci abinci innarsu ta saka ta ta yi wanka don ta tafi kiran da hajiya take mata, shiryawa ta yi ta saka riga da skirt na atamfa glitter da ta yi mata kyau sosai, ta yi ɗaurin kallabi mai steps, bayan ta gama ta ɗauko mayafi wanda dama mahaɗin kayan ne ta yafa, lokacin da ta fito innarsu na a zaune tsakar gida da su Imrana, nan suka hau cewa ta yi kyau, tana ɗan murmushi ta ce ma innarsu ita da ba wata kwalliya ta yi ba ko powder bata shafa ba kawai puff ɗin powder ne ta goge fuskarta sai ɗan lip gloss da ta shafa, innar su ta ce, "To ai ke dama fatar ki kalar powder ɗin ce, ko baki shafa ba sai fuskar ki ta yi kaman kin shafa." Dan murmushi ta yi kawai ta ce mata sai ta dawo daga haka ta tafi. Balaraba ta fito daga kitchen jin ana sallama, ganin Salma ta yi murmushi ta ce, "Salma ce.." Ta amsa mata tare da gaishe da ita, bayan ta amsa Salma ta tambaye ta hajiya na nan ta ce eh tana ɗaki bari ta yi mata magana, bada jimawa ba ta fito ta ce mata tana bedroom ta ce ta shiga, Balaraba ta yi mata jagora zuwa ɗakin hajiya wanda yau ne karon farko da zata fara shiga, bin ɗakin Salma ta yi da kallo bayan sun shiga wanda babban ɗaki ne da ya tsaru da lafiyayyun furniture kai ka ce ba ɗakin tsohuwa ba, Salma taita kallon gadon hajiyan na alfarma, ba abun da ya faɗo mata a rai sai ranan nan da Deen ya ce kuɗin wandonsa zai siya gadon, a ranta ta shiga raya ko da wasa yake ganin katafaren gadon, suna shigowa hajiya dake a kwance saman gado ta yunƙura ta tashi zaune tana ɗan murmushi, nufar wurin gadon ta yi ta duƙa daga gefe tare da gaishe da hajiya ta amsa mata, wayarta da ke ajiye gefe ta kai hannu ta ɗauka ta fara latsawa kafin ta kai kunne, kusan sau ukku tana yin kira da alama ba a amsawa, ƙoƙarin sake yin kiran ta yi still ba a yi picking ba, a fili ta ce, "Ina Deeni ya shige ne...ina ta kiran waya baya ɗagawa." Kallon Salma ta yi ta tambaye ta lokacin da ta shigo ko ta ga Deeni? Salma ta ce mata a'a, ta sake tambayarta ta ga Sule dirabanta a harabar gidan Salma ta ce shima bata gansa ba, shiru hajiya ta ɗan yi alamar tunani can ta ce, "Ina tunanin yana a can part ɗin su don ɗazun da ya gama cin abinci ya ce mani jikinsa ya yi nauyi zai je can ya motsa don a can yake da kayan motsa jikin, ƙilan shi ya sa baya ɗaga kiran." Ita dai Salma shiru ta yi tana kallonta, "Dama shine yake neman ki, ko zaki je ki duba shi a can?" Da alamar rashin fahimta Salma ta tambaye ta ina zata je, kwatancen part ɗin su ta yi mata ta ce idan ta je sai ta ƙwanƙwasa kofar ta ga idan yana can ta san ma bai wuce yana can ɗin, amsawa Salma ta yi da to tare da miƙewa, tana tafiya a ranta tana tunanin ko neman mi yake mata, tun kafin ta ƙarasa part ɗin a ranta take yaba haɗuwar shi, a bakin tangamemiyar kofar part ɗin ta tsaya gabanta har ɗan faɗuwa yake, a ɗarare ta kai hannu ta fara knocking, tun tana yi a hankali har ta koma tana yi da ƙarfi, jin shiru ba a buɗe ba ya sa ta fara tunanin ko bai a part ɗin, bayan ta ɗan ƙara ƙwanƙwasawa ta yanke ƙilan baya nan, tana niyyar juyawa zuciyarta ta bata ta murɗa handle ɗin kofar ƙilan a buɗe take, kama handle ɗin ta yi ta murɗa daidai lokacin ta ji an ja kofar ta ciki, gaba ɗaya ta tafi sakamakon jan kofar da aka yi da ɗan ƙarfi, da sauri Deen ya kai hannuwansa ya tare ta ta hanyar dafe shoulders ɗinta, still ya yi yana kallon fuskar Salma da ta runtse idanu jikinta na ɗan rawa ya yin da idanunta ke ɗan motsawa daga gani ta tsorata sosai, a hankali ta fara buɗe idanunta suka shiga cikin na Deen dake ta kallonta, bugun da ƙirjinta ke yi ne ya ƙaru ganin a yadda yake daga shi sai wando 3 quarter ba riga, daga gani cikin motsa jikin yake don duk fatar jikinsa ta jiƙe da zufa, sumarsa ta manne masa a wuya, ya rataya ɗan madaidaicin farin towel, da sauri ta janye idanunta daga barin kallon shi, a hankali ya ɗauke hannayensa daga saman shoulders ɗin ta, daga yanayinta ya fahimci tsoro a tattare da ita calmly ya ce, "I'm sorry, kin ji tsoro?" Ɗan motsa baki ta yi ba tare da ta kalle shi ba a hankali ta ce, "Da na zo inata yin knocking ba a buɗe ba, na yi tunanin ko kofan a buɗe take shine na murɗa." Idonsa a kanta ya ce bai ji knocking ɗin bane saboda headphones da ya saka sai daga baya, ta ɗaga kai kawai, tana niyyar ƙara yin magana ya riga ta cewa hajiya ta turo ta? Lokacin ta ɗan ɗaga ido ta kalle sa ta ce mashi eh tana ta kiran shi a waya bai ɗauka ba, kai ya ɗaga kafin ya ce mata ta je daga can gefen part ɗin akwai rumfa a wurin ta zauna yana zuwa, a hankali ta ce masa to tare da juyawa ta nufi inda ya nuna mata still gabanta na ɗan faɗuwa saboda abun da ya faru.... *_✨A CIKIN RAYUWA✨_* _New story from the writer of 'A Sanadin Makwabtaka',_ ZAINAB BATURE 28 Sosai Salma ke ƙara yaba tsaruwar part ɗin yayin da take tafiya, tana zuwa ta ga rumfar irin ta shaƙatawa ce da kujerun zama, ciki ta shiga ta zauna a saman ɗaya daga cikin kujerun ta ɗaga ido tana kallon cikin rumfar wadda itama ta burge ta, Deen na komawa ciki without wasting much time ya watsa ruwa ya canza kaya, bata daɗe zaune ba ya fito, ƙamshin turaren da ta ji ya ziyarci cikin hancinta ne ya sa ta juyowa ta hango shi ya nufo rumfar jikinsa sanye da jallabiya mai gajeran hannu, gyara zamanta ta yi ta sauke idonta ƙasa, bayan ya ƙaraso ya ja kujera ɗaya ta 6angaren da ke kallonta tare da ɗaura wayoyin da ya riƙo guda biyu a saman table din tsakankanin kujerun da suke zaune, zama ya yi ya jingina bayansa da kujeran, a hankali ta ɗago suka haɗa idanu ta ɗan yi murmushi, calmly ya ce, "How is school?" A nutse ta amsa mashi da Alhamdulillah kafin ta ce masa, "Ina wuni." Kai kawai ya ɗaga mata, shiru ta biyo baya Salma ta sauke idanunta ƙasa don bata iya jure kallon shi cikin ido, "Ya kuka?" Kaman daga sama ta ji ya yi maganar, da sauri ta ɗaga ido ta kalle shi ta ga idanunsa na akanta da ɗan murmushi akan face ɗinsa, kunya ce ta kama ta ta ɗaga hannunta guda da har lokacin akwai zanen lalle ta ɗan rufe fuskarta, bayan ta cire tana ɗan murmushi ta ce, "Ai na bari." Shiru bai ce komai ba yana dai ta kallonta kawai, ɗayan hannunta da tun bayan da ta baro gida yake a cikin gyale ta fiddo, abun da ta riƙo ta miƙa masa ya kai idanunsa kan hannun nata, ta ce, "Ga shi, jiya na jira in baka sai baka fito ba, amman na wanke shi saboda na bata shi da ƙwalla." Ɗago idonsa ya yi ya kalle ta, kaman ba zai ce komai ba bayan ɗan lokaci ya ce, "Keep it, ki ci gaba da using da shi don na ga kaman kuka bai yi maki wuya." Ɗan waro ido ta yi da sauri ta ce, "A'a, kawai jiya na shiga damuwa ne sosai shi ya sa." Still da ɗan murmushi akan face ɗinsa bai dai ce komai ba, sai da ta ƙara ce masa gashi sannan ya ce ta ɗauka ya bata, sauke idonta ta yi a hankali ta ce ta gode, wayarsa ce ɗaya ta fara ringing, bayan ya ga mai kiran ya kai hannu ya ɗauka tare da kai ta kunne, ɗan saurarawa ya yi kafin ya furta, "Yea...we're together." Daga haka ya cire wayan, gyara zaman shi ya yi a nutse ya ce mata ta ji yana nemanta ko? Ta ɗaga masa kai alamar eh, a nutse ya soma yi mata bayanin dalilin kiran nata kamar yadda ya yi ma hajiya, ta natsu tana ta kallon shi sai ka ce yana biya mata karatu, ɗan murmushi ne akan fuskarta bayan ya gama magana ta ce shike nan zata sanar ma innarsu ɗin idan ta koma, yana kallonta ya tambayi ita nata aikin da yake son bata tana ganin ba zai affecting karatunta ba? Ɗan girgiza masa kai ta yi ta ce, "A'a, ai ba wani aiki bane mai ɗaukan lokaci sosai, zan iya." Kai ya jinjina kafin ya ce idan ta koma gida ta yi ma mom ɗin nata magana a bincika idan da waɗanda za su yi sai ta sanar masa don bai da lokaci sosai, Salma ta ce to, "Do you have a phone?" Ta ji ya tambaye ta, ɗan girgiza masa kai ta yi alamar a'a, ya ce, "Why? Ko baki so?" Tana murmushi ta ce, "Ina so, kawai dai ban isa riƙewa ba sai na gama makaranta." Shiru ya yi yana kallonta a ransa ya ɗan ji mamakin maganar tata, tambayarta ya yi ajin ta nawa ta bashi amsa da biyar, ya tambayi tama kusa gama school din ke nan, ta ce eh next year, ya gane sa'ar ƙanwarsa ce Leemarh saidai ita yana tunanin tun da ma ta fara secondary school take da waya, ya ce, "But at your age kin isa riƙe phone, kuma zai taimaka maki wurin karatun ki." Ɗan kikkafta ido ta shiga yi tana murmushi ba tare da ta ce komai, ya tambaye ta ko gida ne aka hana ta amfani da shi, ta ɗan girgiza kai ta ce, "A'a, ni ce na fi son sai na gama school, saboda ban son ta rinƙa ɗauke mani hankali ta hana ni karatu." Nodding kansa ya yi alamar ya fahimta, sai kuma ya ce mata amman ita ce zata tsara yadda ba zai rinƙa ɗauke mata hankalin ba, shiru ta yi bata ce komai ba, "Yanzu ba wani phone da zamu iya communicating kan maganan da muka yi?" Da sauri ta ce masa a'a akwai ta innarsu da take yawan amfani da, shiru ya ɗan yi kafin ya ce ban da shi ba wani? Ta ce akwai ta yayanta Sagir, ɗan maimaita sunan ya yi irin alamar kamar ya san mai sunan, tambayarta ya yi ta riƙe lamba ɗin shi ta ce eh, ya kai hannu ya ɗauki ɗayar wayarsa kafin ya miƙo mata ya ce ta saka lamba din Sagir, bayan ta saka ta bashi ya amsa ya yi saving, kiran shi aka yi waya ya ɗauka yana amsa kiran da turanci, ita dai Salma ta zuba masa ido don ya ɗan juyar da fuskar tasa, har yanzu tana jin mamakin wai shi ɗin bahaushe ne, yana cikin yin wayar ya ɗan janye ta daga kunnansa, ya kai ɗayan hannunsa kan ɗayar wayar wadda tun da ya ajiye ta bai ta6a ta ba, iya jikin wayar ma abun kallo ne glass din ta sai sheƙi yake, ba tare da ya ɗauki wayar ba ya ɗan buɗa tafin hannunsa a saman ta sai gashi ta kawo haske alamar ta buɗe kanta, mamaki ne ya kama Salma ganin yadda ya buɗe wayar wanda ita tun da take bata ta6a ganin an buɗe waya haka ba, ɗan daddana wayar ya yi na ɗan lokaci da alama abu yake dubawa, maida wayar da yake amsa kiran yayi kunne ya ci gaba da yin wayar da yake yi, idon Salma na akan wayar da ya gama ta6awa bayan ɗan lokaci ta yi duhu alamar ta rufe kanta, tana ta kallon wayar can ta ɗaga ido ta kallo Deen ta ga idanunsa na a gefe yana ci gaba da yin waya, a hankali ta kai hannunta itama ta buɗe tafin hannunta a ɗan saman wayan yadda ta ga ya yi, ganin bata kawo haske ba ya sa ta yi tunanin ko hannun nata ya yi nesa da screen ɗin wayar, hakan yasa ta ɗan ƙara matsawa da tafin hannun, ta shagala tana ta ƙoƙarin buɗe wayar kamar daga sama ta ji muryarsa ya ce, "It only unlocks with my Palm ID." A ɗan firgice ta ɗaga ido ta kalle shi suka haɗa idanu, kunya ce ta kama ta ta yi saurin janye hannunta tare da sauke idanunta ƙasa, tafin hannun nashi ta ga ya kai saman wayar ta buɗe, turo mata ita ya yi ta ɗaga ido ta kalle shi, ya ce mata gashi ya buɗe, da sauri ta ce a'a ba wani abu zata yi da ita ba kawai dama haka nan ta yi yadda ta ga ya yi, murmushi kawai ya yi bai ce komai ba ya ɗauke idanunsa yana latsa wayar dake a hannunsa, tana ta kallon screen ɗin wayar da ke ɗauke da hotonsa da kayan ƙwallo ya sa ƙafarsa zai buga ball ɗin, daga gani suna cikin yin wasa ne aka yi hoton, sosai hoton ya yi mata kyau, ɗagowa ta yi da niyyar yi masa magana amman ta kasa, kamar ya ji tana kallonsa ya janye idonsa daga kan wayar hannunsa ya kalle ta, daga yanayin ta ya fahimci da magana a bakinta, ɗage mata gira ya yi ba tare da ya ce komai ba, cikin kama kai ta ce, "Dama cewa zan yi zan iya kallon hotuna?" Yadda ta yi maganar ya so bashi dariya amman bai yi ba, kai ya ɗaga mata alamar eh, sai dai lokacin da ta kalli wayar har ta rufe kanta, hannu ta ga ya kawo ya buɗe ya ɗauka ya ɗan daddana kafin ya miƙo mata, tana amsa ta ga ya buɗe mata daidai gallery ɗin wayan, folder daban-daban ta gani ta shiga ta farko wadda ke ɗauke da sunan 'My Fam' tana shiga hoton farko da ta fara cin karo da na wata mata ne wadda sai da Salma ta ɗan tsorata da ganinta saboda tsantsar kyawunta, yanayin yadda ta yi kallo a jikin hoton ya bayyana kaifin idanuwanta, sai dai kana kallon fuskarta zaka shaida kammaninta sosai da Deen, bin hoton Salma ta yi da kallo na ɗan lokaci kafin ta ɗago a hankali ta kalli Deen, ta ce, "Is she ur mom?" Ɗago idonsa ya yi ta juya mashi hoton, ɗan murmushi ta ga ya yi ya ɗaga mata kai alamar eh, Salma ta ce, "Kun yi kama sosai." Calmly ya ce mata thank u, hoto na biyu tana buɗe shi ta gane mahaifinsa ne don ta san shi ɗan majalissar garin su ne, hoto na gaba ta buɗe wanda gaba ɗaya ƴan gidansu ne har da mom da dad din su hakan ya sa ta gane, hoton Leemarh ta buɗe wanda take ita kaɗai, bin hoton ta yi da kallo don ta yi mata kyau sosai kuma kana ganinta zaka ga kammanin Deen a tattare da ita, juya wayar ta yi ta ce mashi, "Ur sis right?" Kallon hoton ya yi ya ɗaga mata kai, ta ji ya ce, "Leemarh...she's ur age mate." Shiru ta yi tana kallonsa a ranta ta ɗan ji mamakin yadda ya ce su sa'anni ne." Daga yanayin fuskarta ya gane ta yi mamakin maganarsa, ya ce mata itama next year take gama sec school ɗinta, sai da ta ji haka ta gane ta ɗaga masa kai, kan hoton wani babban mutum ta zo ya yi shigar baƙaƙen suit yana zaune a cikin wani haɗaɗɗan office, mutumin yana da matuƙar ƙwarjini da haiba, sam jikinsa bai nuna yawan shekarunsa ba, daga gashin kansa da na gemunsa da ke haɗe da yar hurhura ne zaka iya gane cewa ya ɗan manyanta, sosai Salma ta yaba da kyawun suffar mutumin wanda da gani naira ta zauna masa kuma ɗan gayu ne na gaske, kasa haƙura ta yi sai da ta tambayi Deen wanene shi, daga murmushin da ya bayyana akan fuskar Deen zaka fahimci yana ji da mutumin, ya bata amsa da daddy Maleek a wurinsa ya taso a London, hoton gaba mutumin ne da wata kyakkyawar mata, daga yadda ya rungume ta ta gane matarsa ce, lokaci guda kuma a ranta ta yanke matar baturiya ce ko kuma yar indiya duk da ta ga kamanninta da mom ɗin Deen, hoto na gaba sune sun rungume wata matashiyar yarinya da suka saka a tsakiya, bin budurwar Salma ta yi da kallo a ranta tana ayyana ko wacece don bata ga kamanin su da ita ba, duk da kana ganin yarinyar zaka gane yar hutu ce kuma wayayya, kasa haƙuri Salma ta yi ta tambayi Deen wacece ita, ɗan kallon hoton ya yi ya janye idanunsa tare da bata amsa da cousin sis ɗin shi ce Basma, jin ya ce cousin sis ya sa Salma sake tambayar shi ke nan daddy Maleek ɗin ɗan'uwan mahaifinsa ne, ya ɗan girgiza mata kai ya ce shi aminin mahaifinsa ne mom ɗinta ita ce ƙanwar mom ɗin sa, sake kallon hoton Salma ta yi tana ɗan mamakin yadda Basma ta fi iyayenta baƙi duk da mahaifinta ma ba fari bane amman ya fita hasken fata, ƙarshe zuciyarta ta bata ai hakan na faruwa sosai, ci gaba da kallon hotunan ta yi daga baya ta fita daga cikin folder ta bude ta wata da aka saka 'Bdays' bayan ta shiga hotunan ahalinsa ne a ciki na bikin murnar ranar haihuwar su, kusan kowa cikin waɗanda ta gani akwai hotunan bdays ɗinsu har da iyayensa da kuma shi kansa Deen ɗin, sosai hotunan suka burge ta ba kamar na Deen wasu tare da yan team ɗinsa na kwallo ya yi celebrating wasu a wurare daba-daban, wata folder ta shiga ita kuma an rubuta 'Lifestyle' nan kuma duk hotunan Deen ne a wurare daban-daban, akwai waɗanda ya yi a ƙasashe daban daban da ya je on vacation, wasu a bakin ruwa shi da abokansa fararen fata suna yin barbecue, wasu a snow yana skiing, wasu yana swimming, wasu yana driving a haɗaɗɗun motoci, wasu a saman bike, wasu a cikin jirgi na sama da na ruwa, har da wanda ya yi a gaban ka'aba, Salma ta shagala tana ta kallon hotunan nashi da suka yi matuƙar tafiya da hankalinta, kiran wayar da aka yi ma Deen ya sa ta ɗaga kai ta kalle shi, faɗin inda suke zaune ta ji ya yi a ranta ta raya ƙilan hajiya ce ke tambayarsa da ta ji shiru, bayan ɗan lokaci da yin wayar tasa kamar ance Salma ta ɗaga idanunta, ganin wanda ya nufo inda suke ya sa gabanta wani irin faɗuwa, da sauri ta ajiye wayar da ke a hannunta hakan ya sa Deen kallonta, Fahad na gab da ƙarasowa ta yi saurin miƙewa ta ce ma Deen za ta tafi, shiru ya yi yana kallonta noticing how nervous she looked, Fahad na ƙarasowa ta bar wurin ko ƙara kallon Deen bata yi ba, sai lokacin Deen ya fahimci dalilin canzawarta, miƙewa Deen ya yi yana kallon Fahad da murmushi ya miƙa masa hannu ya ce, "Welcome ya Fahad." Kai ya ɗaga masa ya ɗan juya yana kallon hanyar da Salma ta bi kafin ya juyo ya kalli Deen, zama suka yi fuskarsa babu yabo babu fallasa ya ce ma Deen, "What is dat gal doing here?" Dan murmushi ne akan fuskar Deen ya ce masa shine ya kira ta, wani suspicious look ya ma Deen ɗin jin abun da ya ce bai dai ce masa komai ba, dama ya yi mamakin awaran da ta kawo masa ranan nan har ya zauna yana ci, don ya yi clearing any doubt ya yi ma Fahad bayanin dalilin kiran ta da ya yi, shiru ya ɗan yi sai kuma a taƙaice ya ce Allah Ya tabbatar da alkhairi, bayan Deen ya amsa da Amin yana kallonsa ya ce, "How is work?" Amsa masa ya yi da Alhamdulillah, dama daga wurin aikin yake yanzu, hira suka ci gaba da yi bada jimawa ba aka fara kiran sallar la'asar hakan ne ya tashe su don zuwa yin salla. Lokacin da Salma ta koma gida innarsu bata nan ta tafi gidan gaisuwa kamar yadda Imrana ya sanar mata, jin haka itama ta bita can gidan bayan ta cire gyalen jikinta ta saka hijab, sai bayan da aka gama sallar la'asar suka dawo, sai da suka yi salla sannan Salma ta iske innarsu a ɗakinta nan ta sanar mata dalilin kiran ta da hajiya ta yi, da mamaki innarsu ta maimaita maganar aikin da Deen ɗin ke son badawa Salma ta ƙara tabbatar mata da hakan, daga yanayin fuskarta zaka fahimci ba ƙaramin daɗin maganar ta ji ba, ta ce, "Shi dai wannan mutumin ya ji daɗi wallahi, da Allah Ya hore masa sai shima yake taimaka ma mutane, dama haka Allah Yake so idan ya baka kai ma sai ka bayar. Sadakar abinci ba ƙaramin taimako bane za a yi ma mutane Salma musamman a lokacin nan da mutane ke cikin hali." Salma da ke ɗan murmushi ta ce, "Wallahi kuwa, ya ce duk yadda muka yi da ke sai in sanar masa, kamar yana son jin amsa da wuri in za a yi ko ba za a yi ba don ya ce bai da lokaci sosai." Da sauri innarsu ta ce, "Yi kai, Salma a yadda mutane ke cikin hali ai duk wanda aka ma tayin aikin nan ban tunanin zai ƙi amsa, ni kaina ina cikin masu yi tun da ko ba komai aikin lada ne, zan yi ma innarsu Habu magana duk dama tana cikin alhinin rasuwa, to amman tun da sauri ake zan je in yi mata bayani tun da abu ne na ƙaruwa, sai dai kuma kada sauran abokan zaman nata su ga an ware su ko su yi tunanin an yi masu baƙin ciki." Ta ƙarasa idonta akan Salma, tambayarta ta yi kamar mutum nawa ake buƙata da za su yi aikin, Salma ta bata amsa da bata sani ba sai dai a tambaye shi, innar ta ce to ta yi hakan idan babansu ya dawo za su yi magana da shi. Bayan sallar isha lokacin da baban su Salma ya dawo innar tasu ta yi masa bayanin aikin na Deen, shima ya yaba sosai da hakan tare da yin fatan alkhairi, suna cikin tattaunawar ne aka yi sallama daga waje, da yake jiya da yau basu yi awara ba saboda rasuwar da aka yi duk yaran na nan, Imrana ne ya je ya dubo mai yin sallamar, bayan ya dawo ya ce masu baban su Habu ne, miƙewa baban su Salma ya yi ya nufi hanyar wajen, tare suka dawo cikin gidan da baban Habun, yaran suka shiga gaishe da shi da fara'a yake amsa masu, miƙewa innarsu Salma ta yi daga kan tabarmar da take tana mashi sannu da zuwa tare da gaishe da shi, a saman tabarmar suka zauna shi da baban su Salma ita kuma innarsu ta koma daga gefe ta zauna kan kujera, kallon su Imrana ya yi duk ya kira sunayen su kafin ya tambayi ina Salma, fitowa ta yi daga cikin ɗakinta ta zo daga bakin barandar tana murmushi ta gaishe da shi, yana murmushi ya ce, "Salma ya ya? An daina kukan ko?" Maida idonta ta yi ƙasa tana ɗan murmushi ta ce mashi eh, "Yauwa haka yakamata. Ya makaranta." Ta amsa da Alhamdulillah, wasu ƴan matasan maza ne guda biyu suka shigo ɗauke da wasu kaya babansu Habun ya ce su kawo su nan bakin baranda, bayan sun ajiye suka gaishe da su baban Salma kafin suka tafi, kowa kallon kayan da aka ajiye ya yi wanda kayan abinci ne da alamun rashin fahimtar na miye akan fuskokinsu, a nutse baban su Habu ya fara magana, "Dama zuwa na yi in sanar da ku abun arziƙin da ya same mu, in kuma yi maku godiya musamman Salma don kusan ita ce silar komai, yanzu bada jimawa ba Hajiyar Ambasada ta kira ni dama ta amshi lambar wayata, sha tara na arziƙi suka mani wllh, an bani buhun shinkafa da na masara da gero, sai katon din taliya da macaroni kowanne biyu har da jarkar mai, sannan ita ta bani dubu ɗari biyar shima jikan nata ɗan kwallon nan ya bani dubu ɗari biyar an ce in nemi wata sana'a in fara yi, suma iyalina kowacce jikan nata ya bata dubu ɗari su ɗan samu sana'a da za su fara yi. Ni dai tsabar farin ciki ma kuka na kama yi masu." Ya ƙarasa tare da kai hannu ya matse kwallan da suka taho mashi, babansu Salma ba abun da yake faɗi sai, "Alhamdulillah, Allah Ya saka da alkhairi..." Haka innar su Salma farin ciki ne ya lullu6e ta, cikin karyayyar murya ya ce, "Ku ma na gode maku ƙwarai, Allah Ya saka da alkhairi Ya sa kyautata ma maƙwabta ya zamo silar shiga aljanna." Gaba ɗaya suka amsa mashi da Amin har da su Imrana, kallon Salma ya yi, "Ke ma Salma Allah Ya saka maki da alkhairi, Ya albarkaci rayuwar ki, Allah Ya baki miji na gari da zai kula da rayuwar ki..." Kallon su Imrana ya yi suma duk ya saka masu albarka, kuɗi masu yawa ya fiddo daga aljihun shi ya miƙa ma babansu Salma yana murmushi ya ce ga wannan su ma sai su saka albarka, da sauri baban su Salma ya ce, "A'a, ka bar su, kai da aka ba ka yi sana'a, Allah Ya saka masu albarka Ya sa silar arziƙi ne." Matsa mashi baban Habu ya yi kan ya amsa, yana murmushi ya ce, "Wallahi malam Umaru ba zamu amshi kudin nan ba." Bin shi ya yi da kallo fuskarsa ta nuna rashin jin daɗi ya ce ya zai yi rantsuwa haka, sai kuma ya ce, "Tun da haka ne, nima wallahi wanccan kayan sai kun amsa, daga cikin kayan abincin da aka bani ne." Daga haka ya miƙe, baban su Salma yana ƴar dariya ya ce wato shine zai yi rantsuwa ya ɗaure su, yana saka takalmi ya ce to ai kowa ya iya yin rantsuwar, su Salma dai na ta murmushi, innarsu ta yi masa godiya haka su Salma da sauran yaran, tare da babansu Salma suka fita... *_✨A CIKIN RAYUWA✨_* ZAINAB BATURE 29 Washe gari Friday Deen ya zama busy sosai saboda gobe asabar ne bikin buɗe sabon club ɗinsa, da yamma wasu daga cikin baƙin da za su halarci bikin suka fara zuwa, yawanci ƴan kwallo ne na clubs daban daban daga wasu jahohi, tuni an kama masu masaukin da za su zauna dama, da daddare bayan sallar isha'i Salma ta zo gidan hajiya, tana shigowa harabar ta hango Deen daga can gefe wurin parking space zaune da wasu mutane, nufar hanyar shiga cikin gidan ta yi, "Salmerh.." Kafin ta ƙarasa ta ji an kira sunanta ta juya, Deen ta gani ya nufo ta ta tsaya idonta akan sa, a cikin ranta raya bata ta6a jin wanda sunanta yake daɗi a bakinsa ba irin shi, daga gabanta ya tsaya tana ɗan murmushi ta gaishe da shi, bayan ya amsa ya ce mata hajiya sun fita ba kowa a ciki, ledar hannunta ta ɗago ta ce, "Gashi aka ce in kawo maka." Kallon ledan ya yi ya maido idon shi kanta ya ce, "Awaraa?" Murmushin kan fuskarta ya ɗan fadada saboda yadda ya faɗi sunan ta ce mashi eh, kai ya jinjina ya ce mata thank you kafin ya ce ta kai mashi ciki idan ya gama da mutanen da yake tare zai je ya ci, ta amsa da to har za ta juya ta dakata ta ce, "Maganar aikin an samu mutum ukku da za su yi, amman innarmu ta ce a tambaye ka yanayin yawan abincin da za a rinƙa yi don a san mutane nawa za a ɗauka." Shiru ya ɗan yi kafin ya ce su yi magana da hajiya ita zata faɗi yanayin yadda za a rinƙa yi har da salary da za a rinƙa ba su, Salma ta ce to ta na murmushi ta ce bari ta kai mashi abun ciki, ya amsa da ok tare da ce mata, "Gud nyt." Daga haka ya juya ya koma wurin mutanen, bayan ta kai mashi kamar yadda ya ce ta fito ta wuce gida. Washe gari asabar misalin karfe sha ɗaya na safe aka fara bikin buɗe sabon club ɗin a stadium ɗin garin, wanda ya samu halartar ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na wasu states da ma waɗanda ba ƴan kwallon ba masoyan Deen, cikin manyan mutane masu muƙami da suka halarta har da commisioner matasa da wasanni na jahar Katsina, da Executive Director Katsina State Sport Council da wasu stakeholders, hikimin garin, ɗan majalissar jaha da sauran manya masu muƙamai a garin duk sun halarta, dad ɗin shi ya so zuwa amman wani uzuri ya taso mashi a can Abuja da ya sa bai samu halarta ba amman daddyn su Fahad ya halarta kuma shine matsayin wanda ya wakilci mahaifinsa, hajiya da momyn su Fahad da sauran ƴan gidan duk sun zo, tare da sauran ƴan'uwa da abokan arziƙi, wuri ya cika da al'umma wasu ma don kawai su ga Deen suka zo, su Sagir ƴan wasan sabon club duk sun yi shiga cikin sabon jerseys da takalma, bayan buɗe taron da addu'oi an gabatar da jawabai daban daban wanda suka ƙunshi yabo, ƙarfafa gwiwa da fatan alkhairi, an yi abubuwan nishaɗi da suka haɗa da kaɗe-kaɗe sannan an gabatar da wasannin gasa tsakanin wasu ƙungiyoyi da sabon team ɗin inda a ƙarshe suka samu nasarar zuwa na biyu, an bayar da kyaututtuka sannan an rarraba abubuwan ci da sha, daga ƙarshe Deen ya yi bayani game da dalili da kuma abubuwan da yake burin cimmawa a sabon club din, ya bayyana burin sa na faɗaɗa tare da inganta club ɗin ta yadda ba a iya ƙasar kawai za su rinƙa buga wasa ba, ya kuma bayyana niyyar sa ta gina ma club ɗin stadium mai zaman kansa a garin ba da jimawa ba. Alhamdulillah taro ya tashi lafiya, bayan kammala taron ne manyan baƙi da kuma shuwagabannin sabon club ɗin da ƴan wasa suka yi walimar cin abincin rana, an ci an sha an gode ma Allah. Sagir zaune a tsakar gida sam ya kasa rufe bakin sa, kasancewar sa a sabon club ɗin Deen a ganinsa mafarkinsa na zamowa shahararren ɗan ƙwallon ƙafa ya fara tabbata, gaba ɗaya ƴan gidan da wasu sun halarci bikin suna a kewaye da shi dukkan su suna cikin farin ciki sosai, Salma nata murmushin farin ciki tana kallon kyaututtukan da aka bashi kasancewarsa ɗaya daga cikin ƴan wasa da suka nuna hazaƙa wanda suka haɗa da kayan ƙwallo da takalma har da lambar yabo, "To, Allah Ubangiji Ya sa albarka, Ya sa an hau matakin nasara. Allah Ya albarkace ku Ya inganta rayuwar ku baki ɗaya." Babansu ya faɗa da faffaɗan murmushi, kusan a tare suka haɗa baki wurin amsa addu'ar mahaifin nasu, itama innarsu ta yi masu addu'a baki ɗaya, saboda farin cikin da suke ciki abinci na musamman aka yi a gidan har da kaji da lemuna, su Imrana ba baka sai kunne, bawan Allah saboda sadudar da ya yi da suna cin abincin har cewa ya yi da a ce Habu na nan sai ya di6ar masa cikin abincin shi ya kai mashi har gida, maganar shi ta ta6a zuciyoyinsu musamman Salma sai da ta ji ƙwalla sun tarun mata a ido, Sagir ne ya ce, "Da yana nan ɗin ba za kai hakan ba, sai dai da ana dawowa." Wani kallo Imrana ya yi masa bai ce komai ba. Washe gari lahadi wuraren ƙarfe sha biyun rana Sagir na cikin yin bacci a ɗakinsu ringing ɗin wayarsa ya tashe shi, ɗan tsoki ya yi don ya ji haushin katse masa baccin da kiran ya yi, ganin bai san lambar da ake kiran da ita ba ya sa shi saka wayar a vibrate, komawa ya yi ya kwanta bayan kiran ya yanke sai ga wani ya sake shigowa, kamar ba zai ɗauka ba sai kuma ya ɗago tare da ɗaukar wayan ya yi picking, yana niyyar yin magana ya ji an yi sallama da wata nutsattsiyar murya, daidaita zaman wayar Sagir ya yi kafin ya amsa shima a nutse sa6anin farko da ya yi niyyar yin magana a fusace, "Sageer, how are you doing?" Ɗan waro ido Sagir ya yi sai kuma ya yunƙura ya tashi zaune sosai yana amsawa, "Pls idan ba damuwa ina son yin magana da Salmerh if she is around." Kan Sagir ne ya ƙulle jin ana neman Salma ta wayarsa abun da ba a ta6a yi ba, yana son tambayar wanene amman kuma ya kasa don muryar ta yi masa ƙwarjini sosai, sai dai kuma a wani 6angare na zuciyarsa yana jin kamar ya san muryar kuma bai sha wahalar gane muryar da ta wa ta yi mashi kama ba, sai dai bai tunanin abu mai yuwuwa ne a ce Deen Jr ya kira wayarsa yana neman kuma Salma, dama su basu da lambarsa iya manyan ƙungiyarsu ne ke tuntu6arsa game da komai, miƙewa ya yi ya nufi cikin gidan bayan ya ce ma mai kiran bari ya kai mata, yana akan kiran bai yanke ba har Sagir ya shiga cikin gidan ya fara ƙwala ma Salma kira, innarsu dake a tsakar gidan ta ce mashi tana ɗakinta, a daidai bakin ƙofa suka haɗu ya miƙa mata wayar ya ce ana son magana da ita, ɗan jim ta yi tana kallon screen ɗin wayar, ta kalli Sagir ɗin a hankali ta ce masa waye, ya ɗan ta6e baki haɗi da ɗage kafaɗa ya ce mata oho, a ɗarare ta kai wayar kunne tare da yin sallama, tana jin muryarsa ta gane nan take ta saki ɗan murmushi, da hannu Sagir ya yi mata alamar waye ta ƙi ta ce komai ta shige cikin ɗakinta, after few seconds sai gata ta fito daga cikin ɗakin ta nufi Sagir da ke a kusa da innarsu bayan ta kira shi tana tambayar wa yake kiran Salma ya ce mata bai sani ba, miƙa masa wayar ta yi kafin ya ce wani abu innarsu ta riga shi cewa, "Waye ya kira ki?" Tana murmushi ta ce, "Yaya Deen ne wai cewa ya yi idan bani komai yana son gani na." Waro ido Sagir ya yi with surprise all over his face ya ce, "Deen!" Kai Salma ta ɗaga masa still tana murmushi, da alama mamaki ya kashe Sagir, ya sake cewa, "Ke, miye haɗin ki da shi da har yake neman ki ta waya?" Ganin yadda mamakinsa ya bayyana ya sa Salma yin dariya ta ce, "So na yake..." Wani kallan kallon kina hauka zaki fadi haka ya jefa mata, innarsu da ke kallon su dariya ce akan fuskarta, Salma ta ce, "Da gaske nike..." Wata dariyar kin raina mini wayo ya yi ya ce, "Baki da hankali yarinya, Deen ɗin ne zai so ki?" Sai lokacin innarsu ta saka baki ta ce, "Ka raina ta ne kake ganin ba zai iya son ta ba? Mace ce fa." Yana dariya ya ce, "Yo innarmu in dai mata ne wannan ya saba ganin su kala-kala, ƙarshe ma shi da yake rayuwa a cikin turawa, mata masu aji da kyau rububin shi suke sai ya tsaya cewa yana son wannan." Innarsu ta ce, "Ai abun baya a nan Sagir, sai ka ga duk su bai ga kyaun so ba sai ita, kuma dai kaima kasan Salma ba daga baya ba indai kyau ne, sannan shi so wani lokacin ba ruwansa da kyau, sai ka ga wani abun daban ne game da ita ya burge shi." Wata dariya Sagir ya yi ya ce, "Innarmu ko mi zaki ce ba zan ta6a yarda wai Deen Jr zai iya son wannan yarinyar ba." Ƴar hararar shi Salma ta yi tana murmushi ta ce, "Ka raina ni, kana ganin ba zan iya sa shi ya kamu da so na ba?" Yana dariya sosai ya ce, "Har abada kuwa ba zaki iya sa Deen wai ya so ki ba, idan kuma har kika iya yin nasarar hakan ni kuma na rantse da Allah daga lokacin zan koma ce maki yaya Salma." Dariya ce akan fuskar Salma irin ta ka san ba zaka iya abu ba ka dai faɗa ne kawai, innarsu ta ce, "Ki je wataƙil jiran ki yake kada ki biye ma Sagir." Juyawa ta yi ta koma ɗakinta don ta shiryo, matsa ma innarsu ya yi sai da ya ji dalilin da yasa Deen ke kiran Salma, gyale ta yafo saman doguwar rigan jikinta ta fito tana kallon Sagir da ke mata dariya irin ta ka raina ma mutum wayo, ya ce, "Ni wllh nama gode maki da kika bashi no ɗina, kin ga na rinƙa gaisawa da shi." Ƴar harara ta wurga mashi ta ce ai dai da ya koma ƙasar waje shike nan ba zai iya samun shi da layin ba, yana dariya ya ce mata matsalar shi da ita ƴar ƙauye ce waya ce mata ba ya iya amfani da layin a can, sai ta dawo ta yi ma innarsu ta ce mata to daga haka ta nufi kofar fita Sagir ya bi bayanta yana mata shegantaka kan alwashin da ya sha na kiranta yayar shi. Tun kafin ta ƙarasa gidan hajiya ta hango mutane dadda6e a bakin gate ɗin, bayan ta ƙarasa wani daga cikin jami'an dake tsaron gate ɗin ya dakatar da ita yana tambayar ta wurin wa zata je, tana niyyar bashi amsa wani jami'i da ya san ta tana zuwa gidan ya ce mashi ya bar ta ta wuce, tana shiga ta hango Deen daga can cikin parking space yana zaune a saman kujera ya ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya, daga gefensa wani jami'i ne a tsaye gefensa tarin kayan abinci ne masu yawa, wurin da yake ta nufa ganin yana cikin magana da wani dattijon mutumi dake zaune akan kujera ya ɗan rankwafa ya sa ta tsaya tana jira ya gama da shi, bata daɗe da zuwa ba mutumin ya miƙe hannunsa riƙe da kuɗi da Deen ya bashi muryar shi kamar zai yi kuka yake faɗin, "Allah Ubangiji Ya saka maka da gidan Aljanna Ya ƙara maka ɗaukaka, Allah Ya sa ka gama da iyayenka lafiya..." Haka ya yi ta jero addu'oi har muryarsa na karewa, kai Deen ke jinjina masa a hankali bakinsa ke motsawa alamar yana amsa addu'an, "Taho baba." Jami'in da ke tsaye ya faɗa, da sauri dattijon ya nufe shi kamar zai faɗi, kallon mutumin jami'in ya yi kafin ya ce, "Anya kuwa baba zaka iya ɗaukar kayan nan?" Da sauri dattijon ya ce to akwai yaron shi da suka zo tare ba a barsa ya shigo ba yana a bakin gate, sunan yaron jami'in ya tambaya ya bashi amsa, ɗaga murya jami'in ya yi yana faɗin, "Officer Kamal, allow one Sabi'u to come in..." Matashin yaron ne ya shigo ciki officer ya ɗaga murya ya ce mashi ya zo da sauri ya nufe su da sassarfa, madaidaicin buhun shinkafa da kwalin taliya da macaroni officer ɗin ya nuna masa ya ce su zai ɗauka, taimaka masa ya yi ya ɗaura masa shinkafar sai kwalin taliyar, dattijon ya ce a bashi ma macaronin, sai da yaron ya ɗan rankwafa ya yi ma Deen godiya kafin suka tafi farin ciki kwance akan fuskokinsu, kallon officer ɗin Deen ya yi ya ce a dakata da shigo da wani sai ya yi magana, ya amsa masa da ok tare da nufar bakin gate, kallon Salma dake tsaye ya yi suka haɗa idanu, ɗan murmushi ta shiga yi masa da hannu ya yi mata alamar ta ƙarasa, nuna mata kujera ya yi ta zauna, tana kallon shi a nutse ta ce, "Ina kwana." Ya ɗaga mata kai, shiru ta ɗan biyo baya, gently ta ji ya ce, "How can I help u?" Waro ido ta yi jin tambayar da ya yi mata, mamaki ya bayyana akan fuskarta a ranta ta fara kokonton ba shi ya kira ta ba? Ganin yana ta kallonta alamar ita yake jira ta yi magana ya sa ta fara kikkafta idanu ta ce, "Kai ka kira ni.." Shiru bai ce komai ba yana ta kallonta kawai ta shiga yan kame kame, ɗan murmushin da ta ga ya yi ya sa itama ta yi don ta gane wasa yake mata, "Baki je school ba?" Tana kallon shi ta ce, "Islamiyya?" Kai ya ɗaga mata, ta ce, "Ban yi haddar da aka bamu ba shi ya sa ban je ba." Ya ce, "Why baki yi ba?" Tana murmushi ta ce, "Saboda rasuwan da aka yi ban samu na zauna na yi ba, amman yanzu ma ina cikin yi ka kira ni." Nodding kai ya yi ba tare da ya ce komai ba, hannu ya kai gefensa ya ɗauko wata ƙaramar bag ya ɗaura saman tabur ɗin da ke a tsakanin kujerun da suke zaune tare da tura ta gabanta ya ce, "It's ur phone, zamu rinƙa communicating da shi kada a takura ma brother ɗin ki, but ka da ki bari ya ɗauke maki hankali ki daina karatu." Murmushi ta yi ta maida idanunta kan ledan, kallon shi ta yi ta ce, "Na gode Allah Ya saka da alkhairi." Slowly ya amsa da Ameen, shiru ta ɗan ƙara biyo baya kafin ta ji ya ce, "Aikin da zaki yi ni ne zan rinƙa baki salary, tell me how much you want, and whether you want it to be weekly or monthly" Zaro ido ta yi jin tambayar da ya yi mata, a ranta take raya dama idan mutum zai yi aiki shi ake tambaya kuɗin da yake so a rinƙa biyan sa da kuma lokacin da yake so? Jin ta ƙi cewa komai ya ce ita yake sauraro yana son ya ci gaba da attending mutanen da ke waje, a daburce ta ɗan watsa hannu ta ce ai aikin ba wani aiki bane ya basshi ba sai ya rinƙa biyanta ba, ɗage mata gira ya yi ya ce dama ana yin aiki haka? Shiru ta yi kawai tana ɗan murmushi, gyara zaman shi ya yi ya ce mata idan ba zata rinƙa amsar salary ba a bar aikin, waro ido ta yi sai kuma ta ɗan marairaice fuska ta ce, "A'a yaya Deen zan yi tun da kana so." Ya ce ok yana jinta ta faɗi kuɗin da take so, ji ta yi duk ya ɗaure ta ta rasa ya zata ce, can ta ce bari ta je to ta tambayo innarsu, ya ce mata ai ita zata yi aikin kuma bashi da isasshen lokaci don gobe da safe zai tafi ga mutane na jiran shi, slowly ta ce, "Can ƙasar da kake?" Ya ce mata a'a zai koma Abuja after a week zai koma London, ta yi shiru tana kallon shi, ya ɗage mata gira alamar ita yake sauraro, sauke idonta ta yi ƙasa a cikin zuciyarta tana tunanin ita ya zata ce masa, can dai ta ɗago cike da jin nauyi ta ce, "Ka rinƙa bani dubu biyar." Shiru ya ɗan yi sai kuma ya tambaye ta weekly ko monthly, a sanyaye ta ce monthly wato duk ƙarshen wata, wani guntun murmushi ta ga ya yi ya ɗan juyar da fuskarsa, ta yi shiru tana kallon shi kamar mai son karantar yanayin fuskarsa, "Zan rinƙa baki 100k..." Tun kafin ya rufe baki ta wani zaro ido tare da kai hannunta guda ta rufe baki, idon shi akan ta ya ce ya yi mata ko a ƙara, da sauri ta janye hannunta ta hau girgiza masa kai cikin rawar murya ta ce, "S..sun yi yawa sosai gaskiya." Ya ce to haka yake son bata, marairaice mashi ta yi kan ita dai sun yi yawa, ganin ya ƙi amincewa ya rage kamar yadda take so sai kawai ta saka mashi kuka, mamaki sosai ya kama Deen ganin ta rufe idanunta da hannunta, shi bai ta6a ganin in da ake gudun kuɗi ba sai a kanta, ya ɗage gira ya ce, "Mi ye na kuka?" Janye hannunta ta yi ta kalle shi da idanunta da suka jiƙe cikin muryar kuka ta ce, "Kuɗin sun yi yawa wallahi, ko gida ma haka za a ce." Yana murmushi ya ce yanzu ya take son a yi, da sauri ta ce ya rinƙa bata kamar yadda ta ce, ɗan jimm ya yi kafin ya ce mata hakan ai ya yi kaɗan kuma monthly, ta ce to shike nan ya rinƙa bata dubu goma, ɗan murmushi kawai ya yi yana ci gaba da kallonta ta sauke idanunta ƙasa, tunanin ko ya rinƙa bata yadda hajiya ta ce da ya tambaye ta shawara wato dubu talatin, sai dai shi yana ganin sun yi kaɗan, sigh ya yi ya ce "Ok I will be giving you 50k, idan baki yarda da hakan ba a bar aikin kawai." Ɗago idanunta ta yi ta kalle shi, ganin yanayin fuskarsa ta nuna da gaske yake abun da ya faɗa ya sa bata ce komai ba, shiru na ɗan lokaci can ya ce mata idan tana da wani matsala ta faɗa mashi, ɗan girgiza masa kai ta yi ta ce bata da wata matsala, daga haka ya ce mata zata iya tafiya sai sun yi magana, godiya ta yi masa ya ɗaga mata kai ta ɗauki ledan wayan, har zata miƙe sai kuma ta dakata a sanyaye ta ce mashi goben da safe zai tafi, ya ɗaga mata kai sai kuma ya ce ko akwai wani abu, a hankali ta girgiza mashi kai alamar a'a, ganin yana ta kallonta ya sa ta ce, "Dama na yi zaton ko bada sassafe zaka ta fi ba in soya maka fara, yanzu ba lalle har in yi ba zuwa dare." Murmushi ya yi ya ce, "Don't worry, na gode, wani lokacin idan na sake zuwa." Ta yi shiru tana kallonsa sai kuma ta ce, "Za ka sake zuwa?" Still da murmushi ya ce mata eh ai nan garin shi ne, ta ce, "Amman tun da na dawo nan ban ta6a ji ka zo ba." Tambayar ta ya yi daga ina ta dawo nan, ta ce, "A wurin auntyna Kaduna na yi primary school, bayan na gama na dawo nan yanzu shekara biyar." Kai ya jinjina mata ya ce shekaru ukku da ya zo kuma lokacin bai zo nan Funtua ba iyakar sa Abuja, ta ce, "Yanzu ma idan ka tafi sai an daɗe zaka ƙara zuwa?" Ya ɗan yi shiru idonsa akanta itama kallon nashi take duk da bata iya jure ma kallonsa cikin ido amman sai ta kasa janye idanun nata, slowly ya ce bai tunanin zai daɗe sosai kafin ya ƙara zuwa, kai ta ɗaga ta ce, "Allah Ya tsare Ya kiyaye hanya." Ya amsa da Ameen daga haka ta miƙe ta nufi hanyar gate idonsa a kanta..... *_✨A CIKIN RAYUWA✨_* _New story from the writer of 'A Sanadin Makwabtaka',_ ZAINAB BATURE Page 30 Bayan Salma ta isa gida, ɗakin su Sagir da ke a cikin zaure ta nufa jin sautin waƙa na tashi, daga bakin kofa ta yi sallama ba a amsa ba, sai da ta ƙara yi sannan cikin ɗaga murya Sagir ya ce, "Waye?" Ta bashi amsa da ita ce, tasowa ya yi ya leƙo yana ganinta ya fara dariya cike da zolaya ya ce, "Budurwar Deen Jr...ya har kin yi nasarar sa shi ya kware makin?" Murmushi kawai ta yi bata ce komai ba, tana niyyar juyawa ya ce mata miye a ledan ta ce mashi ina ruwan shi, hannu ya kawo zai warci ledar ta yi saurin shigewa cikin gida da ɗan gudu, innarsu da ke zaune a cikin baranda har lokacin ta ɗago tana kallon ta, ganin ta shigo da guda ta tambayi lafiya, tana ƴar dariya ta ce ba wancan Sagir ɗin bane, wurin innar tasu ta nufa ko zama bata yi ba sai ga Sagir ɗin ya biyo bayanta yana faɗin bata isa ba sai ya ga ko minene aka bata a cikin ledar, da sauri ta miƙa ma innar tasu ledan tana dariya ta ce idan ya isa ya kar6a a wurin innar tasu, riƙe ledar innarsu ta yi tana kallon Sagir da murmushi ta ce ina ruwansa da ko minene a ciki tun da ba shi aka bamawa ba, Sagir ya ce, "Innarmu ko ba ni aka ba ba, tun da gidanmu aka kawo ai dole in gani." Miƙa ma Salma ledar ta yi ta ce ta amshi abun ta, tana ta murmushi ta ce ma innar tasu ta buɗe ta gani, buɗewa ta yi ta ciro kwalin da ke ciki, bin hoton wayar da ke a jiki ta yi da kallo, da sauri Sagir ya miƙo hannu ya ce ya gani, jujjuya kwalin wayar ƙirar samsung ya shiga yi tare da ɗan waro ido, kallon Salma ya yi ya ce, "Wayan waye?" Tana murmushi ta ce tata ce, "Kina nufin Deen ɗin ya baki?" Ta ɗaga masa kai alamar eh, "Ke! Kin san kuwa wannan ba ƙaraman waya bace, akan mi zai baki wannan babbar wayan?" Dariya maganar tasa ta ba Salma, ta ɗage masa gira ta ce ba ta faɗa masa son ta yake ba ya ƙi yarda, wani kallo ya yi mata mai kama da harara ya ce shi fa ba zai ta6a yarda ba, ta ce to shike nan, kallon innarsu ya yi ya ce, "Innarmu kin ji wai shi ya bata, kuma kin san mi wannan wayar wllh ta kusa miliyan ko bata ida ba kaɗan ke babu." Daga innar tasu har Salma duk suka zaro idanu jin abun da ya ce, da sauri innarsu ta maimaita abun da ya ce ya tabbatar mata da hakan, kallon Salma ta yi ta ce, "Ya akai ya baki wannan wayan?" Da ɗan ruɗewa ta ce, "Ni dai kawai cewa ya yi gashi nan da ita zamu rinƙa magana kan aikin da ya bani don kada a takura ma Sagir." Mamaki ne duk ya bayyana akan fuskokinsu Sagir na dariya ya ce, "Shi bai san ni son ya rinƙa kiran wayan tawa nike ba." Ita dai innarsu ta yi zuru da alama ta rasa abun cewa jin kuɗin wayar da aka faɗa, "Kuma ya ce wai dubu hamsin zai rinƙa biyana duk wata kuɗin aikin." Duk suka ƙara waro idanu suna kallonta, "Wane aikin ne za a biya ki dubu hamsin?" Sagir ya tambaya da mamaki, ta ce mashi wanda ya ce zata rinƙa mashi, dariya ya yi ya ce, "Lalle Deen bai ɗauki kuɗi wani abu ba, yanzu har wani aiki ne wannan da zai rinƙa baki har 50k! Kawai saka ido bama da ke za a rinƙa dafa abincin ba, sai in kin ji wani na cikin matsala sosai ki sanar masa, shike nan aikin amman zai rinƙa biyan ki kuɗi har haka" Innarsu ta ce, "Amman Salma wannan kuɗin ai sun yi yawa a wannan aikin, ko dai gaba ɗaya har da na dahuwar yake nufi?" Ta ɗan girgiza mata kai ta ce, "Ai wannan ba cewa ya yi hajiya zata rinƙa badawa ba har da kayan abincin da za a rinƙa amfani." Shiru innarsu ta yi da alama abun ya fi ƙarfinta, tambayar Salmar ta yi ko ita ce ta ce ya rinƙa bata hakan, da sauri ta ce mata a'a wllh nan ta faɗi mata duk yadda suka yi da shi, wani sabon mamakin ne ya bayyana kan fuskar innarsu jin wai da dubu ɗari zai rinƙa bata, Sagir ya ce, "Ba fa ma wani abun mamaki bane ko dubu ɗarin ya rinƙa bata, wannan da kuke gani ba ƙananun kuɗi yake samu ba, na gaya maku duk sati miliyoyin kuɗaɗe ake biyan shi ban da wanda yake samu a wasu harkokin, ke kawai kakar ki ta yanke saƙa kin zama babbar yarinya, dubu hamsin duk wata ba wani nauyi a kan ki, lalle nan gaba kaɗan ba lalle ma ki rinƙa ganin girman mu ba, dama yanzun ma ya aka cika." Ita dai Salma kallon shi take kawai tana dariya, innarsu da ta yi jigum ta ɗan yi murmushi ta ce ai ya san ba haka take ba kuɗi ba za su canza ta ba, Sagir da ke dariya ya ce, "Pls ki bar man ita mu yi musanya in baki tawa don na san ke ƴar ƙauye ce ba lalle ki iya amfani ma da ita ba." Ƴar hararsa ta yi ta ce a cin zalinta da yake zata bashi, ita dai innarsu murmushi kawai take amman a can ƙasan ranta kokonton yakamata a amshi wayan take. A ranar ma basu yi niyyar yin awara ba, amman saboda tafiyar da Deen zai yi Salma ta roƙi innarsu a yi, bayan sallar magrib babansu ya dawo har da Auwalu, suma sun jinjina wayar da aka ba Salma da kuma albashin da aka ce za a rinƙa bata, ita dai innarsu ta nuna a mayar masa da wayar a ce ya canza mata wadda bata kai wannan ba, shima baban ya goyi bayan hakan, amman Auwalu da Sagir suka nuna basu goyi bayan hakan ba tare da nuna ma iyayen nasu shi fa a wurin shi wannan ba wani abu bane, da yawa ma haka nan yake masu alkhairin da ya fi wannan ita kuma aiki ne zata mashi, ƙarshe iyayen nasu suka amince tare da yin addu'a da kuma fatan alkhairi, har da nasiha baban nasu ya yi ma Salma kan ta zamo mai gaskiya da amana a aikin kuma ta kula da kanta ta guji aikata duk wani abu da ta san ba daidai bane, ka da ta bari zuciya ruɗe ta kan duk abun da ba daidai ba, daga ƙarshe ya haɗa su duka ya yi masu nasiha tare da basu misali da wannan alkhairin da ya samu Salma yana da nasaba da taimakon da take yi, ya ja hankalinsu da su zamo masu zuciyar taimako, itama innarsu ta yi mata yar nasiha, ƴan'uwanta duk suka yi mata addu'a da fatan alkhairi. Bayan sallar issha ta tafi kai ma Deen awaran, yau ma tana shiga gate ta hango shi zaune da mutane za su kai biyar, ɗauke kai ta yi ta nufi hanyar shiga cikin gida, tana cikin tafiya ta ji muryar Deen ya kira sunanta, dakatawa ta yi ta juya tana kallon in da suke, ya yi mata alamar ta je, tunkarar su ta yi ta sauke kanta ƙasa, daga ɗan gefen su ta tsaya ta ɗago ta gaishe su duka, lokaci guda ta ji gabanta ya faɗi sakamakon haɗa ido da ta yi da Fahad wanda shi kaɗai ne bai amsa gaisuwar da ta yi ba, sauran mutanen guda ukku wanda duk abokan su ne suma duk hutu ya zauna masu sai ƙamshi ke tashi wurin, duk suka amsa mata gaisuwarta, Deen ya ce mata hajiya bata jin daɗi ta sha magani ta kwanta yana tunanin yanzu tana bacci, a hankali ta ce to ta ɗan yi shiru duk ta kama kanta, ganin idanun sauran mutanen na akanta idan ka cire Fahad dake kallon direction daban, ɗan matsawa ta yi daga inda Deen yake ta miƙa masa ledan ta ce gashi, kai ya ɗaga ya ce ta kai mashi ciki tare da yin godiya, juyawa ta yi ta wuce cikin gidan ƙafafunta har ɗan harɗewa suke, bada jimawa ba sai ga ta ta fito ko kallom inda suke bata yi ba ta nufi gate, "Deen wannan fa?" Ɗaya daga cikin abokan nasu ya tambaya bayan Salma ta fita daga gate, ya bashi amsa da a makwabta take, "Amman dai she is beautiful gaskiya, ban yi tunanin a area irin wannan ana samun beb mai kyau haka ba." Sauran abokan biyu ma duk suka yaba da kyawun Salma, ɗaya cikin su ya ce da gani kuma tana da natsuwa da wayewa, na farko da ya fara magana ya ce shi ya ji ma ta yi masa anya ba zai neme ta ba, sai lokacin Fahad ya saka baki ya ce mashi kar ya fara yarinyar bata da kunya, kallon Fahad ya yi ya ce, "Da gaske?" Kafin Fahad ya bashi amsa Deen na ɗan murmushi ya ce mashi ya ɗan samu misunderstanding da ita amman yarinyar tana da hali mai kyau ba yadda Fahad ke tunani ba, Fahad ya ce ai halin mutum da ya bayyana da shi ake shaidar shi, Deen bai sake cewa komai ba haka shima abokin nasu don ya fahimci kamar Fahad bai yin yarinyar. Bayan komawar Salma gida aka kira Aunty Kubra aka sanar mata game da waya da aikin da Deen ya bata, sosai ta yi farin ciki tana faɗin ita dama ta san ta yi sa'ar ɗiya akwai alkhairi tattare da rayuwarta wasu nasarorin ma na zuwa in sha Allah, da innarsu Salma ta sanar mata game da diramar da Salma ta yi da Sagir har da alwashin da ya sha, sai da aunty Kubra ta sa aka ba Sagir waya ta ce, "Sagir raina ɗiyar tawa ka yi da kake tunanin ba zai iya son ta ba? Kai ma ka san wllh Salma ba daga baya ba, kuma shi so ba ruwan shi tsaf sai ka ga Salma ta siye zuciyarsa cikin sauƙi." Yana dariya ya ce, "Maganar gaskiya aunty Kubra Deen ba zai iya son ta ba, mutumin da mata masu kyau da aji ƙarewa ma farar fata ke rububin shi mi zai ci da wannan." Ƙwafa aunty Kubra ta yi ta ce, "Ka rubuta ka ajiye wannan maganar da ka yi don ubanka, in sha Allahu akwai ranar tado ta don ma kada ka ce ka manta, ba dai za su kasance tare ba za ta yi masa aiki, bi'iznillah sai Allah Ya nuna maka ikonSa kuma wallhi sai ka rinƙa kiranta da yaya." Gaba ɗayansu dariya suke har da sauran ƴan gidan don a speaker aka saka kiran, bayan ta gama yin magana da shi ta ce ya ba Salma, bayan ta taya ta murna itama ta yi mata nasiha kamar yadda iyayenta suka yi mata, daga baya ta tambayi Salmar tana a ina ne ta ce mata tana a tsakar gida ta ce ta je ɗaki su yi magana, bayan ta sanar mata ta shigo ɗakinta aunty Kubra da ke akan waya ta ce, "Kina ji na baby, so nike mu ba wancan shegen Sagir ɗin kunya, don haka ki dage da gyara kan ki, ki rinƙa yin kwalliya na san wataƙil har video call za ku rinƙa yi, sannan ki kasance mai gaskiya da riƙon amana, ki tsare mutuncin ki, ki zamo mai natsuwa ba kamar yayin da kike magana da shi, kuma ki zamo mai kauda kai kada ki rinƙa nuna kwaɗayi ko haɗama duk da na san dama wannan ba halin ki bane, to kada ki sake ki koyi hakan ba kamar ganin kin samu dama, sannan ki zamo mai kunya don tana tasiri sosai a kan maza ba kamar shi da yake rayuwa a cikin waɗanda ba sa da kunya sai ki ga hakan ya zamo yana burge shi a tattare da ke...." Shiru Salma ta yi tana ta sauraran auntyn tata tana ɗan sakin dariya, ita duk abun da ake yi ta ɗauke sa wasa amman ita aunty Kubra ta dage tana son hakan ya zamo gaske wanda bata tunanin hakan abu ne da zai yuwu tana dai saurarenta ne kawai tana amsa mata. Washe gari wuraren karfe bakwai na safe Deen ya isa gidansu Fahad bayan ya yi sallama da hajiya da tuni ta fara jin kewar jikan nata, su ma gidansu Fahad bankwana ya yi masu duk aka rako su waje har da daddynsu da yaran gidan da basu kai ga tafiya school ba, tare da Fahad za su tafi shi zai kai shi Kaduna a can zai bi charter flight sai ya dawo Zaria wurin aikinsa, addu'oi da fatan alkhairi duk suka yi ma Deen yana ta murmushi yake amsa masu, a sabuwar motar shi za su tafi Fahad ne ya zauna a driver seat Deen yana a ɗayan side ɗin, yana ta ɗaga masu hannu da suma suke ɗago masa a haka motar ta bar gidan. Suna tafiya suna hira tsakanin su har suka iso Kaduna wurin karfe goma da wasu mintuna, kai tsaye airport suka nufa har wurin da zai hau jirgi Fahad ya sauke shi, duk a tunanin Fahad a nan Kaduna Deen zai bar motar a bishi da ita Abuja, bayan sun fito Deen ya miƙa mashi hannu yana murmushi ya yi masa bankwana, Fahad da shima murmushin ne akan fuskarsa ya ce, "Saduwar alkhairi bru. Allah Ya tsare, sai mun yi magana." Deen yana murmushi ya ce, "Thank you for everything ya Fahad, amman dai zamu sake haɗuwa before I leave for London?" Shiru Fahad ya ɗan yi haka nan bai son abun da zai sake kai shi Abuja gidansu, amman shima zai so ya sake ganawa da ɗan'uwan nasa kafin ya tafi don za a a iya ɗaukar lokaci bai sake ganinsa ba, amsa ya bashi da zai yi ƙoƙarin zuwa idan zai tafi, Deen ya yi mashi godiya tare da sake miƙa masa hannu suka yi musabaha, lokacin ya saka ma Fahad makullin motan, bayan ya zame hannunsa yana murmushi ya ce masa, "Dama motan taka ce, na ɗan yi amfani da ita ne kafin na tafi." Daga haka ya kai hannu ya kama suitcase ɗinsa da jaka ya nufi jirgin da ke a ɗan can gaban su, tsananin mamaki ya sa Fahad kasa cewa komai sai ido kawai da ya bi Deen da ke tafiya da shi, sai da zai shige cikin jirgin ya juyo tare da ɗaga ma Fahad hannu, jiki a matuƙar sanyaye Fahad shima ya ɗaga masa hannu daga haka ya shige. Fahad na driving bayan ya ɗauki hanyar komawa zaria, a cikin ransa mamakin kyautar motar kawai yake, ba wannan ne karo na farko da ya ta6a yi mashi kyauta mai girma ba, amman wannan ne karo na farko da ya yi mashi kyauta mai darajan da ta kai haka, Bai san wane irin so Deen ke mashi ba haka, yana driving yana ɗan murmushi wani lokacin ya ɗan girgiza kan sa yayin da yake tunawa da wasu abubuwan. Bayan Deen ya sauka Abuja daddynsa tare da ƙaninsa Omar suka je tarbo sa, sun nuna farin cikin dawowar shi daga baya suka nufo gida, yana shiga cikin falo suka yi ido huɗu da mom ɗin shi da ke saukowa daga bene jikinta sanye da doguwar riga ta ɗaura mayafin a saman kanta, daga bakin benen ta tsaya suka ƙarasa wurinta, fuskarta babu yabo babu fallasa take kallon Deen da ke mata murmushi, daddy ya ce, "Ga yaron ki ya dawo sai hankali ya kwanta ko." Ya yi maganar yana ƴar dariya, ta ɗan ta6e baki ta juyar da fuskarta gefe, Deen ya fahimci fushi take yi da shi daga yanayin fuskarta, dama ya yi zaton ganinta ta je tarbarsa a airport sai ya ga akasin haka, a hankali ya ce, "Mom, I'm back." Ya yi maganar da murmushi, ba tare da ta kalle shi ba ta ƙara ta6e baki a daƙile ta ce ai da ya koma tun da can ya za6a, shiru ya ɗan yi yana kallonta can ya juya tare da yi ma Omar dake riƙe da jakar shi alamar su je, "Deen ina za ka?" Dad din su ya tambaya da sauri ganin ya juya, dakatawa ya yi ya kalli dad ɗin a sanyaye ya ce, "Zan koma ne dad, since I'm not welcome here." Yana juyawa kafin ya ƙara step a fusace mom ɗin shi ta ce, "Don't you dare walk out of this house Deen! Idan ba haka ba wllh ranka sai ya 6aci." Juyowa ya yi ya kalle ta ta ɗaure fuska, da ɗan murmushi ya ce, "But, ke kika ce in koma ai." A faɗace ta ce, "To ka tafin who cares! Ai dama bamu da muhimmanci a wurin ka shi ya sa ka ɗauki ƙafa ka tafi just kwana ɗaya da dawowar ka, shekara nawa baka zo ba? Ka san yadda muke mararin ganin ka? Do you know how eager we are to sit and talk with you?" As your parents, we're ready mu baka dukkan lokacin mu, mu ji idan kana da problems mu yi ƙoƙarin ganin mun magance maka, idan kana buƙatan shawarwari mu baka, siblings ɗin ka suma a koda yaushe burin su ɗan'uwansu wanda ake ɗaukar lokaci basu gan shi ba ya dawo, ka basu lokaci ku yi hira, ku yi raha, ka ji matsalolin su, But unfortunately wasu ne daban suka samu dukkan wannan muhimmancin...you're free ka tafi, ka koma ka ci gaba da faranta ma wasu can bare Deen!" Tun da ta fara maganar idon shi na akanta yanayin fuskarsa ya nuna rashin jin daɗin maganganun da take furtawa, tana gama maganganun ta juya zata haye saman benen, da sauri Deen ya kamo hannunta, ta juyo a fusace ta ce, "Leave my han..." Bata ƙarasa ba ya jawo ta jikinsa ya tungume ta sosai, uwa daban ce ko da tana yin abun da rai bai so, sosai ransa bai ji daɗin 6acin ran da ya gani a tattare da ita ba, slowly ya ce, "I'm sorry mom, don Allah ki yi haƙuri, fushin ki akai na zai iya affecting nawa. It's not as you think mom, my family is always first, you are my number one priority....do forgive me pls." Ba ita da yake gaya ma maganganun ba hatta su dad da Omar sai da jikinsu ya yi sanyi da ganin abun da ke faruwa, sun ɗan ɗauki lokaci haka dukkan su kowa ya rufe ido, sai da ya tabbatar ta sauko sannan ya sake ta idanunsu cikin na juna, slowly ya ce, "Pls ki yi haƙuri, I realize my mistake and it won’t happen again In sha Allah." Ɗauke idonta ta yi ta koma tana kallon gefe tana ɗan far far da idanunta, juyowa ta yi ta kalle shi a tausashe ta ce, "It's Okay, ya wuce." Murmushi ya saki tare da furta, "Thank you my world." Ƴar harara ta sakar masa ta ɗan yi murmushi, su dad da Omar ma duk murmushin ne akan fuskokin su, Jameela ke nan, tana da matuƙar wuyar sha'ani, amman idan ta so wani lokacin tana da sauƙin sha'ani, haka dad ɗin su ke rayawa a cikin ransa, cikin falon suka koma duk suka zauna Omar ya wuce upstairs part din Deen don ya kai mashi kayan shi, hira suka shiga yi tun mom ɗin bata saki jiki ba har ta dawo ta saki jiki sosai, bayan ɗan lokaci dad ɗin su ya yi masu sallama zai koma wurin aiki dama daga can ya tafi tarbo Deen, abinci mom ta ce mashi gashi can an shirya a table su je ya ci, duk da ba wata yunwa yake ji ba haka ya miƙe gudun ya ce ba zai ci ba hakan ya zama wata matsala kuma, da kanta ta yi serving na shi bayan ta gama ta zauna shi kuma ya fara cin abincin a nutse, haka ta shiga jero masa ƙorafe-ƙorafe ciki har da maganar rashin zuwa Kano wurin su Amminta, bayan ya gama cin abincin ta so su zauna a falo su yi magana, ya nuna mata ya gaji yanzu yana son ya je ya huta ta yi haƙuri zuwa anjima zai bata isasshen lokaci su yi duk maganar da za su yi, jin haka ta amince ya nufi part ɗin shi, yana zuwa wanka ya yi ya canza kaya zuwa na shan iska daga haka ya haye gadon shi wanda ke a gyare, bada jimawa ba bacci ya ɗauke shi..... *_✨A CIKIN RAYUWA✨_* ZAINAB BATURE 31 Lokacin da Deen ya farka daga baccin da ya ɗauke shi mai nauyi har an gamma sallar azahar, anan ɗakinsa ya yi salla bayan ya gama ya duba wayarsa ya taras yana da missed calls ciki har da na hajiya da kuma Fahad da daddy Sa'ad, gaba ɗaya ya kira su suka yi mashi ya ya isa, Fahad ya yi mashi godiya sosai da addu'oi, bayan ya gama bin kiran da zai bi sake kwanciya ya yi don ji yake baccin bai ishe sa ba, bai daɗe da rufe ido ba ya ji an buɗe kofar ɗakin hakan ya sa shi buɗe ido, Leemarh ce ta nufo shi da faffaɗan murmushi akan fuskarta da gani bata daɗe da dawowa daga school ba don ko uniform bata cire ba, a bakin gadon ta zauna tana kallon Deen cike da farin ciki ta ce, "Ya Deen ashe ka dawo?" Kai ya ɗaga mata tare da miƙa mata hannunsa ta kama tana ta murmushi ta ce, "Ai da na san yau zaka dawo ba zan je school ba." Ya ɗage gira ya ce, "Why?" Tana ta murmushi ta ce, "Don a je da ni welcoming naka airport." Murmushi kawai ya yi ba tare da ya ce wani abu ba, farin cikin da yake gani akan fuskarta ya sa maganganun mom ɗin su suka dawo mashi, tana son ta tambaye shi Fahad amman haka nan take jin nauyin hakan, can dai ta ce, "Ya Deen ina Yaya Fahad?" Gyara kwanciyarsa ya yi still hannunsa na a nata ya bata amsa da a Kaduna suka rabu shi ya yi dropping nashi, shiru ta ɗan yi sai kuma ta sake cewa, "Dama ya biyo ka kun dawo nan tare." yana ɗan murmushi ya ce, "Aikin shi fa?" Dan yamutsa fuska ta yi a shagwabe ta ce, "To ai sai a daɗe kafin ya zo nan, ga shi ya zo kuma duka kwana ɗaya ya yi ko sallama da shi ba a yi ba ya tafi." Dan murmushi mai faɗi Deen ya yi zuwa yanzu ya riga ya gane tana crushing Fahad ne, "Idan kina son ganinsa sosai ba sai ki je can ba." Haɗa ido suka yi jin yadda ya yi maganar ya sa ta yi saurin kama kanta ta ce, "Ai ba shi kaɗai ba duk ina missing kowa na can an daɗe ba su zo ba." Deen ya ce mata idan suka samu hutun school sai ta je, da sauri ta ce dama niyyanta ke nan, turo ƙofar aka yi Batool ta shigo itama tana sanye da kayan makaranta, da gudu ta nufo gadon Deen na ganinta ya saki hannun Leemarh tare da tashi zaune ya ware mata hannu, hayewa ta yi saman gadon ta faɗa jikinsa ya rungume ta, cikin muryarta mai tattare da shagwaba ta ce, "Yaya Deen welcome back." Yana kallonta da murmushi ya ce, "Thank you my Batool, how's school?" Ta amsa, "Lafiya lou." Ya ce tana dai karatu sosai ko ta daga masa kai, kallon shi ta yi ta ce, "Amman dai ya Deen ba zaka ƙara tafiya ko ina ba ko?" Shiru ya ɗan yi ya kai hannu yana shafa gefen fuskarta ya ce mata zai je Kano ya yi kwana ɗaya daga nan idan ya dawo ba zai sake zuwa ko ina ba har sai lokacin da zai koma London, murmushin jin dadi ta saki ta ƙara shigewa cikin jikin sa, haka nan yake jin zancen mom ɗin su kamar gaskiya ne yan'uwansa basu samu lokacin shi ba sosai, hira ya shiga yi da su suna haka bayan ɗan lokaci aka sake turo ƙofar duk suka kai idanunsu wurin, mom ɗin su ce ta shigo ta sha ado da haɗaɗɗar applique atampa ɗinkin riga half gown da zani ta wani coge ɗaurin kallabi, gaskiya ba ƙarya Jameela ba ƙaramar kyakkyawa kuma dirarrar mace ba ce dole take murza kambunta yadda ta ga dama, kana ganinta ka ga matan Abuja masu cikakken capacity, cikin tafiyarta mai tattare da isa ta nufo cikin ɗakin, ganin su ya sa ta shiga sakin murmushi har ta ƙarasa gaban gadon ta tsaya, gaba ɗaya wurin ya karaɗe da ƙamshin da jikinta ke saki mai matukar daɗi, kallon Deen ta yi ta ce, "Hakan suke bukata a wurin ka." Ya dan yi nodding kai, kallon su Leemarh ta yi da suma ita suke kallo ta ce sun ji daɗin ganin big bro ɗin su ya dawo ko duk suka ce mata eh suna murmushi, "Momy kin yi kyau." kallon Batool da ta yi maganar ta yi ta ɗage mata gira ta ce, "Thank u mah gurl." tare da kissing nata daga nan, "Shi ya sa dad ya kasa yi maki kishiya saboda yadda kike kashe shi da gayu." Wani kallo ta jefa ma Leemarh da ta yi maganar tana dariya, ɗan yamutsa baki ta yi ta ce ya ma yi, shi dai Deen ɗan murmushi kawai yake yi, ce ma su Leemarh ta yi su tashi su je su cire uniform ɗin jikinsu, bayan sun tafi ta kalli Deen ta ce an sha bacci ya ɗaga mata kai, "To ka taso food is ready on the table." Ya ce mata ba ya jin yunwa, tana kallon shi ta ce, "Ka dai taso haka nan ka je cikin ƴan'uwanka ku ci tare za su ji daɗi." Kai ya ɗaga mata alamar to ta miƙa mashi hannu alamar ya ta so, kama hannun ya yi ya sauko daga gadon ya ce zai wanke baki yana zuwa ta tafi. Gaba ɗayansu har da mom suka zauna cin abincin amman ban da dad ɗin su don bai dawo ba, ba wani da yawa ya ci ba amman ya zauna wurin har sai da ƴan'uwan nasa duk suka gama daga baya suka dawo falo. Bayan Salma ta dawo daga makaranta, sosai ta yi mamaki ganin uban kayan abincin da aka aiko masu daga gidan hajiya in ji Deen, jiki a sanyaye ta nufi dakinta, a bakin gado ta zauna tana kallon wuri guda, haka nan take jin wani yanayi a tattare da ita mai kamar na kewar Deen ɗin, kyakkyawar fuskarsa ta shiga dawo mata a rai, ji take kamar ta kira shi, sai dai sabuwar wayar tata na a wurin Sageer da ya amsa idan ta dawo zai nuna mata abubuwa kuma yanzu bata iske shi a gida ba, a hankali ta kwanta tare da rufe idanunta, kiran da ta ji innarsu na yi mata kan ta fito ta ci abinci ya sa ta tashi, bayan ta canza kaya ta nufi kofa ta fita. Su Leemarh na cikin yin hira Deen ya ce masu idan ba wani abu da za su yi su je su shirya su fita outing, sosai suka nuna jin daɗin hakan ba kamar mom ɗin su, ba tare da 6ata lokaci ba duk suka shiryo cikin kananun kaya har da shi Deen ɗin, ita mom gyale kawai ta ɗauro a saman kafaɗa suka fito, a cikin wata jeep za su fita, Omar ne ya zauna driver seat zai ja su, sai Deen a gefe, baya mom da Leemarh sai Sultan, Batool na manne jikin mom, a cikin wata ƙaramar mota security suka yi masu jagora. Duk wani babban park a Abuja sai da suka je, sun yi nishaɗi sosai wuraren ƙarfe shidda ya kai su wani babban mall ya ce kowa ya za6i abun da duk yake so, mom baki ya ƙi rufuwa dama burin ta ke nan a yi masu sai kuma nata kaɗai, siyayya bata wasa suka yi a mall ɗin ba har sai da hakan ya ja hankalin mutane kan su aka ankare da Deen akai ta yin hotuna da shi har da ma'aikatan wurin, sai bayan gama sallar magrib suka dawo gida a gajiye, a nan falo duk suka baje kayan suna sake daddubawa, suna haka dad ɗin su ya shigo ya iske su shima ya zauna yana ganin kayayyakin, cikin marairaicewa ya ce shine aka yi masa wayo aka tafi ba da shi ba kuma ba wanda ya tuna da shi balle a siyo masa komai, yadda ya yi maganar duk ya saka su dariya, Deen na murmushi ya ce mashi shima za su je sai ya za6i duk abun da yake so, dariya dad ya yi ya ce, "No son, ina maku wasa ne, ni bana buƙatar komai, nasu da ka siya masu ya isa kuma na ji daɗi sosai ina alfahari da kai, Allah Ya sa a mizanin kyautatama ƴan'uwa, Allah Ya shi albarka ya ƙara dafa maka." A tare duk suka amsa da Ameen, kiran sallar isha'i da aka fara yi ya tada su. Salma zaune a cikin ɗakinta bayan ta gama yin sallar issha, idanunta akan wayarta da tuni Sagir ya buɗe mata ya kuma nunnuna mata abubuwa, ya buɗe mata account a social media platforms ya kuma yi mata following handles ɗin Deen, dama ta iya abubuwa ba laifi duk da bata da waya, hakan ya sa abubuwan ba su yi mata wahalar iyawa ba, tun ɗazun take son kiran Deen ta yi ma shi ya ya koma amman ta kasa, haka nan take jin nauyin yin hakan, ta ɗan ɗauki lokaci tana wasi wasin yin hakan a cikin zuciyarta, ƙarshe ta yi ƙarfin halin kiran shi ta layin da ya kira Sagir, saida ta yi masa kira biyu amman bai ɗaga ba hakan ya sa ta ƙyale bata sake kira ba. Bayan dawowar su Deen masallaci suka zauna cin abinci gaba dayansu cikin nishaɗi, ko da suka kammala sake zama suka yi a babban falo suna hira a nan kuma Deen ya ce ma ƴan'uwan nashi in da mai wata buƙata ya sanar masa, Omar ne ya fara faɗin tashi buƙatar ya ce mota yake so a siya mashi a can ƙasar da yake karatu saboda sai dai ya yi order ɗin ride ko kuma ya yi amfani da ta abokai, Shiru Deen ya ɗan yi kafin ya ce mashi ya san tuƙi a irin ƙasashen suna da ka'idoji don haka ya bari zai je ya same shi idan ya koma sai ya siya mashi a yi komai, mom ta yi saurin cewa, "Yaushe har zaka samu zuwa, kai da baka da wani isasshen lokacin kanka, ina ganin kawai ka yi masa abun da ya ke so, ai shi ya san yadda ake komai." Dad ya yi saurin cewa, "Ni ina ganin zai fi ya je ɗin komai sai ya fi yuwuwa cikin sauƙi ba kamar tun da shi kusan ko ina yana da alfarma." Deen ya ce mata zai samu lokaci ya je, ba don ta so ba ta ce Allah Ya sa kada ya bar Omar ɗin ya yi ta jira, bayan buƙatar mota ya sake cewa yana son ya canza mashi iphone nashi zuwa latest one da kuma laptop ɗin sa, wani kallon baka da tausayi Leemarh ta yi mashi ba ta dai ce komai ba, Deen ya jinjina mashi kai alamar zai yi masa hakan, "Leemarh, you..." Deen ya faɗa bayan ya maida idanunsa a kanta, murmushi ta yi ta ce, "No, I don't need anything ya Deen, wannan da ka siya mani sun isa na gode Allah Ya saka da alkhairi Ya ƙara maka ɗaukaka." Dad da ya ji daɗin yadda ta yi maganar hankali ya amsa mata da, "Ameen.." Mom wani kallo ta yi mata ta ce, "Ke baki son a can za maki phone en na ki?" Dan yamutsa fuska Leemarh ta yi ta ce, "No, wannan nawa ɗin ya isa, sabuwan ma bata da wani bambanci sosai da wannan duk wasting kuɗi ne." Wani kallon ƙasan ido Omar ya yi mata dama ita ke bi masa sun cika ƴar tsama, fuska a ɗaure ya ce, "Wai ke don a ce kina da hankali ko, ai dai suna da bambancin kuma kowa na son ci gaba ba ai ta barin sa a baya ba, ƴar ƙauye kawai." Harararsa Leemarh ta yi a tsiwace ta ce, "Eeeeh ɗin, na ji ƴar ƙauyen ne ni, kuma su masu kamfanin iphone ɗin sune ke ci gaba suna ƙaruwa da mu shiyasa duk shekara suke yin sabo, mu kuma mu yi ta kwasar kuɗi muna siya instead of muma mu yi investing kuɗin mu ta yadda zuwa wani shekaran mu samu riba, ai rubibin siyan iphone ɗin ma shine ƙauyancin idan baka sani ba." Faffaɗan murmushi ne akan fuskar dad ɗin su sosai ta burge shi da zurfin tunaninta, fuskar mom ɗin su a ɗan tamke tana mata wani kallo ta ce, "Ai There is nothing wrong with mutum ya siya abun da ransa ke so idan yana da hali, hakan zai sa a rinƙa ganin kana ci gaba." Ɗan ta6e baki Leemarh ta yi dama ta san ba zata goyi bayan maganarta ba, wani lokacin har tunani Leemarh ta ke yi anya mom ɗin su na tausayin yaya Deen kuwa yadda take yawan faɗa masa buƙatu tana amsar maƙudan kuɗaɗe a hannunsa, "Ki faɗa masa abun da kike so bani son munafurci." mom ta faɗa da yar tsawa, yamutsa baki Leemarh ta yi, "To ni mom na faɗa bani buƙatan komai." Harara ta wurga mata ta ce, "Kina mace kuma budurwa zaki ce baki buƙatan komai!" Shiru Leemarh ta yi tana ɗan tura mata baki, dad ya ce tun da ta ce bata buƙatan komai ta ƙyale ta, duk da haka sai da ta ce ma Deen ya bada kuɗi ta ƙara ma gold din Leemarh girma ya ce to, shiru kawai dad ya yi shi kan shi yana ganin rashin tausayi a al'amurranta game da Deen, da aka zo kan Sultan shi cewa ya yi so yake a canza mashi ipad ɗin sa, shi dama bai da damuwa in dai zai yi games, lokacin da aka zo kan Batool tana dariya ta ce, "Labubu nike so zan saka shi a school bag ena." Ta faɗa tana noƙe kai, kallonta dad ya yi ya ce miye kuma lanbubu, duk suka ɗan yi dariya jin bai faɗa sunan yadda Batool ta faɗa ba, Leemarh ta ce masu teddy ne, wani kallo suka yi ma Batool, Omar yana ƴar dariya ya ce duk ta rasa abun da zata ce tana so sai teddy, dad ma ya ce ba akwai teddies a gidan ba, mom ta ce a ƙyale ta tun da shi ranta ke so, Leemarh ta yi saurin cewa, "Tsada ma gare shi fa akwai har na 250k." Ɗan wara ido dad ya yi ya ce teddyn ne ke dubu ɗari biyu har da hamsin! ta ce eh kuma salon ma a siya mata ya faɗi ko a ɗauke, mom ta ce a dai kyale ta tun da tana so, ta ƙara ce ma Deen itama sai ya bada kuɗi ta canza mata gold nan ma ya ɗaga mata kai alamar toh, ko da ya tambayi mom ɗin ita mi take so, wani murmushi ta yi ta ce ita ya bari za su yi magana daga baya, a cikin rai Leemarh ta ce, "Allah Ya cece ka ya Deen.." Ko da ya tambayi dad ɗin su shim bun da yake so, da sauri ya ce, "Ah ni bana son komai son, abubuwan da ka je ka yi a garina sun wakilci duk wani abun da nike so.." Tarar hanzarin sa mom ta yi ta ce, "Ya je dai ya yi bannar kuɗi kuma kana goya masa baya, yanzu ina amfanin wani club da ya je ya buɗe a wannan ƙauyen? Ina wani riban da zai samu a nan, maimakon in ma club ɗin yake son ya buɗe ya je Kano in da yake birni kuma harkar take da ƙarfi zai samu riba sosai, kuma ga Bashir shima ɗan ƙwallo ne sosai a can ko ba komai zai kula masa da club din ba tare da wata matsala ba." Duk kowa ya yi shiru bayan ta gama, sigh dad ya yi ya ce a can ɗin ma in sha Allah za a samu abun da ake buƙata, shiru ta yi ta ɗan tabe baki tare da kawar da kanta gefe, bayan shiru na ɗan lokaci Deen ya yi deciding sanar da su game da asibitin da za su buɗe da Fahad kamar yadda daddy Sa'ad ya ce masa ya yi, sosai dad ɗin su ya bayyana farin ciki da goyon bayansa, bayan ya sanar da su dad ya ce hakan tunani ne mai kyau da za su haɗa hannu wurin ginin asibitin, ita kuwa mom wani kallo ta bishi da shi lokacin da ya sanar da su, wani baƙin ciki ta ji ya zo mata wuya ba kamar da Deen ya ce daddy Sa'ad ya ce ya sanar da su, ke nan da ba lalle ya sanar da su ba? Ina! Sam basu isa su mallake mata yaro ba zata nuna masu iyakar su, dad ɗinsu na rufe baki a kausashe ta ce, "Ni ban goyi baya ba, ban kuma amince ba!" Kallon mamaki dad da Deen har da Leemarh suka yi mata, "Amman na ga abu ne mai kyau wannan suke da niyyar yi, asibiti ne fa za su yi haɗin gwiwa su gina." A fusace ta ce, "Shine abun da ban amince ɗin ba! If he wants to build a hospital, miyasa ba zai yi abun shi shi ƙaɗai ba, ai yana da halin da zai yi, kuma dole sai a can, komai su zai tare yana yi mawa ke nan, ya gina nashi a nan mana, akwai in da ya kai gina private hospital a Abuja ne, wace riba zai samu idan ya gina asibiti a ƙauye?" Sunkuyar da kai Deen ya yi ba tare da ya ce komai ba, Leemarh wani kallo take jifar mom ɗin nata da shi, Omar da Sultan da Batool su dai sauraro kawai suke, dad ɗinsu ma kallonta kawai ya ke har ta gama zazzaga masifar tata, ƴar ajiyar zuciya ya sauke, ya ce, "Yanzu miye laifi ko illa don ya haɗa hannu da ɗan'uwansa sun yi abun ci gaba, kuma a bayanin da ya yi su ba ribar da za su samu ta kuɗi suke hanga ba, suna kwaɗayin samun lada ne ta hanyar sauƙaƙa ma al'umma." Wani kallo take bin dad ɗin da shi, bayan ya gama magana ta ce, "Kai kana tunanin idan suka haɗa hannun hakan ba shi da wata illa? Ni na san cutar shi kawai za a yi kamar yadda aka saba ya kasa fahimta, ina Fahad yake da wani halin da zai iya haɗa hannu su gina asibiti da Deen? Don haka a matsayina na mahaifiyarsa ban amince ba wllh." Wannan karon ta fara ƙular da dad, fuska ɗaure ya ce, "Shi Fahad laifi ya yi maki ne ko kuwa baki ɗauke shi naki ba shi ya sa kike tunanin zai cuci Deen? Ina ce yanzu kika gama magana akan club kina cewa maimakon ya je ya buɗe a Kano Bash ya kula masa saboda yana harkar, shi baki tunanin zai iya cutar shi ba ko a samu matsala sai Fahad? Idan kin ce shi Bash yana harkar ƙwallo shima Fahad likitanci ne profession ɗinsa, kuma ba wanda ba zai iya cutar da shi ba a cikin su biyun, haka idan ma wani baren ya ɗauka ya saka a harkar babu tabbacin ba za a cuce shi ba, don haka gara ya kasance na jikinsa ne ko da ma za a cuce shi hakan zai iya zuwa da sauƙi, wanda bana ma tunani za a iya haɗa kai da Fahad a cuci Deen balle kuma a ce shi da kansa ne zai yi hakan, maganar hali kuma dama ba lalle percentage ɗin ya zama ɗaya ba, sai dai kowa a cikin su akwai 6angaren gudunmawar da zai bada da zata fi ta ɗaya, idan shi Deen ya fi hali shi kuma Fahad ya fi shi ilimi da experience a harkar lafiyan. Yakamata ki rinƙa yin tunani kafin ki yi magana, irin waɗannan maganganun da kike yi za su sa yaran ki su fahimci abun da bai kamata su fahimta ba, kawai ki yi mashi fatan alkhairi." Da alama dad ya kashe mata baki, wani kallo ta shiga bin shi da shi wanda ke bayyana ranta ya 6aci sosai da kalamansa, Leemarh kuwa ɗan murmushin jin daɗin taka mata burkin da dad ya yi mata ta shiga saki, shi dai Deen kansa na ƙasa, sam bai ji daɗin exchanging words din da suke yi da juna ba, wani shu'umin murmushin gefe mom ta saki tare da miƙewa tsaye, duk suka kai idanunsu kan ta, tana kallon dad da idanuwanta masu kaifi ta furta, "Sai ya je ya yi abun da ransa ke so..." Daga haka ta juya ta nufi hanyar part ɗin ta tana tafiya mai cike da isa, duk suka bi ta da kallo har ta shige part ɗin ta, miƙewa Batool ta yi ta bi bayan mom ɗin, Sultan ma ya bita daga baya Omar shima ya tashi, kallon Leemarh da ta yi zaune fuskarta duk ta nuna rashin jin daɗi dad ya yi ya ce ta je ta kwanta, a hankali ta ce, "Pls dad ka yi haƙuri.." Dan murmushi ya yi mata tare da jinjina mata kai ya ce ba komai ya wuce, bayan tafiyar ta Deen ya ɗago tare da kallon dad ɗin su da ke kallon 6angare guda, slowly ya ce, "I'm sorry dad..." Juyo fuskarsa ya yi ya kalli Deen ya ce, "Ba komai ka da ka damu, kai ma ka ci gaba da haƙuri da abubuwan da take yi, kasan akwai mutane da suke yin abu ba daidai ba amman su koda yaushe gani suke akan daidai suke, to itama haka ne akan ta, zan yi ƙoƙarin shawo kanta, sannan ka da ka sare ka ci gaba da yin ayyukan alherin ka a duk in da ka yi niyya matuƙar kana da hali. Ɗazun babanku na can Funtua ya kira ni har yake mani godiyar mota da ka ba Fahad, bai san ni bani da masaniya ba akan hakan, amman dai kawai na nuna masa hakan ai ba wani abu bane kyautatawa ce tsakanin ka da ɗan'uwanka." Sauke kai ƙasa Deen ya yi don shi bai yi niyyar sanar da su ba gudun abun da zai iya biyo baya, tsinkayar muryar dad ya yi yana cewa, "Ba wanda zai hana ka kyautata ma ƴan'uwanka, saidai ina son ka bar abun tsakanin ku kawai, kada ka bari ita mom ɗin naku ta sani gudun matsala ganin kuɗin motan na da yawa, na san dai su ba wanda zai yi magana game da hakan da ita." Jinjina kai Deen ya yi alamar zai yi yadda ya ce, addu'oin ƙarin buɗi na alkhairi ya yi masa kafin ya ce mashi ya je ya kwanta ya san yana tattare da gajiya, shiru Deen ya ɗan yi kafin a hankali ya miƙe ya ce ma dad ɗin sai da safe, ya amsa mashi da Allah Ya tashe su lafiya daga haka ya nufi matattakalar bene ya haye zuwa part dinsa.... *_✨A CIKIN RAYUWA✨_* ZAINAB BATURE 32 Zaune dad ya yi shi kaɗai a falon ya ɗage kan sa sama, ya gaji da halin Jameela gashi ya rasa ta yadda zai yi maganinta, yanzu ya san wannan fushin da ta yi haka zata yi ta gasa masa aya a hannu, sanin shi zai cutu ya sa shi fara tunanin ta hanyar da zai bi ya shawo kan ta cikin lalama har ta amince da buƙatar Deen, bayan wani ɗan lokaci ya fara sakin ɗan murmushi da alama ya samu mafita, miƙewa ya yi ya nufi hanyar 6angarenta. Deen zaune a bakin gadonsa yana riƙe da ɗayar wayarsa da ya bari a nan ɗaki lokacin da ya zo yin alwala, duk missed calls da ya iske yana da saving contacts ɗin banda baƙuwar lamba ɗaya da ya gani, a ƙa'ida baya ɗaga baƙon kira idan ba ya san da za a kira sa ba hakan ya sa bai bi kiran ba. Dad na shiga cikin ɗakin mom ɗin su Deen ya hango ta zaune a gaban dressing mirror tana mulke jikinta da mai, da alama wanka ta yi ta saka yar yaloluwar doguwar rigar bacci mai siraran hannuwa, sumarta a warware ta yi mata rumfa har tsakiyar bayanta, jin motsi ya sa ta ɗan waigawa don gashinta bai bari ta ga bayanta, tana yin arba da dad ta wani tamke fuska tare da juyowa tana ci gaba da abun da take yi, tsaye ya yi daga ɗan nesa da ita yana kallonta, bayan ta gama shafa man ta shafa roll on sannan ta shiga fesa turarurruka kamar da gayya, bayan ta shafa ma gashinta wasu mayuka ta feshe shi da hair spray kafin ta tattare shi ta tufke, ɗaukar wayarta dake ajiye a gefen madubin ta yi ta juya ta nufi gado tana latsa ta, yadda take tafiya jikinta na juyi zaka san da gayya take yin hakan, saman gadon ta haye ta tada kanta da pillow tana ci gaba da lallatsa wayarta, nannauyar ajiyar zuciya dad da ke a tsaye kaman an dasa shi ya sauke still idanunsa na akanta, "Jameela..." Calmly ya kira sunanta, ko kallo bai ishe ta ba tana ci gaba da ta6a wayar, ɗan jim ya yi kafin jiki a sanyaye ya zagaya ta gefen inda take ya zauna a bakin gadon, "Jameela baki gan ni bane?" Sai lokacin ta yi mashi wani matsiyacin kallo a ɗan harzuƙe ta ce, "Idan na ganka goya ka kake son na yi?" Shiru ya yi kawai yana kallonta ta ɗauke idanunta, a nutse ya fara magana, "Yanzu a cikin maganganun da na yi miye abun bacin rai Jameela?" Kamar tana jira ta yunƙura ta tashi zaune a masiface ta ce, "Taya zaka ga abun 6acin rai a ciki Ibraheem!" Har saida fuskarsa ta kasa 6oye mamaki jin yadda ta kira sunansa gatsau, duk da ba wannan ne karo na farko ba, idan ya yi mata abu ranta ya baci sosai kiran sunansa take kai tsaye, a tausashe ya ce, "Ni ban yi maganar da na yi ba don na 6ata maki rai, baki fahimce bane, ina ƙoƙarin nusar dake irin yadda wasu lokuttan kike wasu maganganun akan abun da ya shafi relatives ɗin yaran nan bai kamata ba, za su iya fahimtar kamar kina yin bangare ɗaya kawai which hakan ba zai masu daɗi ba ko kuma ya haifar da matsala a zumuncin su." Wani kallon ɗibar albarka take bin shi da shi har ya gama, tana yamutsa fuska ta ce, "Shine zaka zauna a gaban yara ka ci mani fuska, idan fahimtar da ni kake son yi tun da bani da fahimta a gaban su yakamata ka yi mani magana? Dama ai ba yanzu ka fara nuna mani iyakata ba akan dangin ka, shine shima Deen ɗin kake ƙoƙarin koya masa hakan, kuma abun da ba zai yiwu ba ke nan matuƙar ni ce na haife shi dole ne na yi iko da shi akan abun da bani so ko na hango zai iya cutar da shi, ba wanda ya isa ya hana ni! Ai ina da dalilin yin maganar da na yi, akan mi zai tare can ya yi ta masu bauta, wasu abubuwan ma da ya je ya yi gwamnati ce yakamata a ce ta yi amma bata yi ba, sai shi da bai san ciwon kan sa ba ya je yana 6arnatar da kuɗin da yake wahala kafin ya samu, da yake garin ka ne yake ma bauta naka za su amfana ai shi ya sa baka ganin hakan a ba daidai ba kake goya masa baya, ni kuma ba zan zauna in zuba ido ba wllh tun da ba su na haifa ma shi ba." Ta ƙarasa tana mai tabbatar da abun da ta faɗa, shiru dad ya yi kawai yana ta kallon ta, can ya ɗan girgiza kan shi, bayan ya sauke yar gajerar ajiyar zuciya cikin kwantar da murya ya fara magana, "Baki fahimce ni bane Jameela, bani da wata manufa wai ta koya ma Deen ko ya raina ki ya ƙi jin maganar ki akan abun da ya shafi dangina, a wuri na da naki dangin da nawa ba wani bambanci tun da ni da ke mun riga mun zama abu ɗaya, sannan koda kika ga ina goya masa baya akan duk abubuwan da yake yi a can saboda hakan abu ne mai kyau, kuma shi taimako ko da a wuri ɗaya mutum ke yi ba laifi bane in dai ana da buƙatar hakan kuma zai samu lada, sannan kuma da na yi wani dogon tunani ta wani 6angaren muma hakan amfanin kan mu ne Jameela." Wani kallon ban gane me kake nufi da hakan ba ta jefa masa, gyara zaman shi ya yi ya ci gaba da magana, "Ke kike ta ƙarfafa mani guiwa tun da daɗewa kan kina son na fito takarar kujerar gwamnan jahata, sai nike ganin wannan abubuwan da Deen ke yi tamkar sharar fage ne yake yi mana, yanzu baki ganin idan na fito takara waɗannan ayyukan alherin da yake yi a jahata za su yi matuƙar yin tasiri wurin kai ni ga yin nasara ehem?" Jim ta yi idonta a kansa ya ɗan jinjina mata kai alamar ta yi tunani, juyar da fuskarta ta yi zuwa ga duban wani direction daban da alama nazarin maganarsa take, wani murmushin nasara dad ya shiga saki a fakaice, dama ya san haɗamarta akan mulki shi ya sa tunanin shawo kanta ta wannan hanyar ya zo masa a rai ya san tabbas zai yi nasara a kanta, slowly ya kai hannu ya dafa cinyarta da rigar jikinta ta lafe a kai, juyowa ta yi ta kalle shi ya ɗan sakar mata murmushi ya ce, "Ke ya kika gani game da hakan?" Ɗan juya idanunta ta yi ba tare da ta ce komai ba, ɗan cije lebanta na ƙasa ta yi ta ce, "Amman ai da sai ka fahimtar da ni daga ni sai kai ba a gaban yara ba." Da sauri ya ce, "Ok na kar6i kuskure na, I'm sorry my queen ba za a ƙara irin haka ba." Wani kallo mai kaman harara ta wurga masa ya saki ƴar dariya, ƙoƙarin ƙarasa hayewa saman gadon ya fara ta yi masa wani kallo ta ce ina zai je, a ɗan marairaice ya ce to ba sun sasanta ba ta haƙura, tana yatsina ta ce suka yi da shi ta haƙura, ya ƙara marairaice mata, sai da ta mula sannan ta ce a haka zai hau mata gado ba tare da ya freshen up ba, ya ce mata duk zumuɗin gimbiyarsa ta haƙura ne, saukowa ya yi daga saman gadon yana faɗin bari ma kawai ya yi using toilet ɗin ta, ya nufi hanyar toilet ɗin a ransa yana faɗin, "Jameela zuma, ga daɗi ga harbi..." zuba ma wuri guda ido ta yi tana ƙara nazarin maganarsa da kyau, ya akai ita sam wannan tunanin bai zo mata a rai ba, tabbas kuwa ayyukan alkhairin da Deen ke yi ba ƙaramin taimaka masu zai yi ba idan dad ɗin nasu ya tsaya takarar gwamna, yanzu tamkar campaign ne yake masu, dole kam ta rinƙa kauda kai akan wasu abubuwan ko da ranta bai so, wani shu'umin murmushi ta shiga saki yayin da zuciyarta ke hasko mata ta zama first lady ɗin Katsina, gyara kwanciyarta ta yi ta ɗan tada kanta a ranta tana raya ba ma iya first lady ɗin Katsina ba, burinta ta zama har first lady ɗin Nigeria kuma sai ta yi duk yadda zata yi gurin ganin haƙarta ta cim ma ruwa. Tun Salma tana saka ran Deen zai biyo kiranta har dai ta fidda rai ganin an ɗauki lokaci, bayan ta kwanta tunani iri iri suka shiga zuwa mata a rai game da dalilin ƙin biyo kiran da bai yi ba, a ƙarshe ta bar ma ranta wataƙil wani uzurin ne ya hana sa kiran nata. Washe gari a hanyar su Deen ta dawowa daga sallar asuba dad ɗin sa ya sanar da shi ya kwantar da hankalinsa su ci gaba da shirin su na gina asibitin ya shawo masa kan mom ɗin su, sosai Deen ya ji hankalinsa ya kwanta don dama bai san ta ya zai fara sanar da su Fahad cewa ya fasa haɗin gwiwar ba dole za su zargi ƙin amince masa aka yi. Deen da kansa ya kai su Leemarh school a ranar ya yi masu bankwanar tafiya Kano da zai yi suka yi mashi Allah Ya tsare da fatan dawowa lafiya. Misalin ƙarfe sha ɗaya na safiyar ranar Deen ya sauka a Kano, kyakkyawar tarba ya samu daga manyan masu ruwa a harkar ƙwallon ƙafan jahar tare da manya da ƙananun ƴan'kwallo da kuma fans ɗin shi ciki har da jaruman fina-finai, an cika arrivals hall ɗin don welcoming ɗin sa, bayan gama gaishe gaishe da ɗauke ɗauken hotuna kai tsaye suka wuce da shi babban hotel ɗin da suka yi masa masauki don ya huta kafin lokacin da za su fara gasar da aka shirya wadda wasu kamfanoni a jahar suka ɗauki nauyi. Deen na kwance saman gado a ƙayataccen ɗakin da aka kama masa yana yin bacci, ringing ɗin wayar sa ne ya tashe shi, duba mai kiran ya yi ya ga mom ɗin sa ce, ɗauka ya yi ya kai kunne tare da yin sallama, ta amsa masa kafin ta yi masa ya isa lafiya, ya ce Alhamdulillah, "Ina ka sauka ne? Yanzu muka yi waya da Ammi ta ce mani sun ga ka isa garin amman ba can ka je ba." Shiru ya ɗan yi kafin ya bata amsa da yana a hotel, ta ce, "To miye na kama hotel room ba sai ka sauka a can ba tun da dai akwai wadataccen wuri." Ya ce mata football officials na nan ne suka kama masa, "Ok, yanzu sai yaushe zaka je can don sun ƙagara su ganka kada su ga kaman kana ta ja masu rai tun da suna ganin kana zuwa wurare." Amsa ya bata da idan aka yi sallar azahar zai je, ta ce to amman a can zai kwana ko, ya bata amsa da a'a don za su fara tournament da aka gayyace shi kuma tun yamma za su fara har zuwa dare, "Ka ce dama dai zuwa Kanon ma ba don su ka yi ba ke nan." Ya ce, "No, na zo gaba ɗaya ne." Shiru ta ɗan yi tana ƙoƙarin dannar zuciyarta kada ta cika yi masa ƙorafi kamar yadda ta tsara, ta ce, "To ka dai daure pls ka je kuma ka basu lokaci sosai ka ji buƙatun su ka biya masu." Ya amsa mata da in sha Allah, daga haka suka yi sallama, duba agogon wayarsa ya yi ya ga azahar ɗin ma ta kusa, yana son ya je gym na cikin hotel ɗin ya ɗan motsa jikin shi duk da a can Abuja kafin ya taso ya yi, saukowa ya yi daga saman gadon ya nufi toilet, bayan ɗan lokaci ya fito ya ɗauki abun da zai ɗauka dama kayan shan iska ne a jikinsa ya nufi kofa ya fita. Bayan sallar azahar ya yi wanka ya shirya cikin ƙananun kaya ya ɗaure sumarsa ta baya sai sakin ƙamshi yake, abincin rana aka kawo masa ya zauna cikin falo ya ci, bayan ya gama ya fito harabar hotel ɗin dama already ya sanar da driver da aka sa zai rinƙa tuƙa shi za su fita, har da jami'ai da za su bashi kariya aka haɗa shi tun da ya zo, bayan ya shiga cikin motar mai kyaun gaske ya sanar da driver anguwar da zai kai shi suka tafi motar da jami'an ke ciki ta bi su a baya, bayan sun iso layin da gidan yake, wani babban flat Deen ya nuna ma driver ɗin ya ce nan za su shiga, karya kan motar ya yi tare da yin horn sau biyu sannan wani mutumi da gani mai gadi ne ya leƙo, driver ya yi mashi bayanin wanda ya zo yana jin haka cikin rawar jiki ya shiga wage masu gate ɗin motar ta kutsa ciki tare da ta jami'an, bayan sun tsaya a cikin harabar wani a cikin jami'an ya fito ya buɗe ma Deen ƙofa, zuro ƙafarsa dake a cikin haɗaɗɗun takalma ya fara yi kafin ya ƙarasa fitowa, fuskarsa ta yi wani fresh sai sakin annuri take yi, mai gadi na ganinsa ya durƙushe ƙasa yana yi masa sannu da zuwa kai kawai Deen ke ɗaga masa, ya ce ma jami'an da driver sai ya fito suka amsa masa, mai gadin ya yi gaba da sauri ya nufi cikin gidan don ya je ya sanar masu isowar Deen, a daidai bakin main kofar shiga cikin gidan wani matashi ya fito kana ganin fuskarsa ka san ya girmi Deen don zai kai shekaru talatin da ɗoriya, fari ne sosai sai dai fuskarsa duk ta yi ƴan tabbuna tabbuna sannan la66ansa sun nuna alamar yana shaye-shaye, yana da tsawo da kuma ɗan kaurin jikin, akwai yanayin kammani da mom din su Deen akan fuskarsa, cikin washe baki ya tarbi Deen tare da miƙa masa hannu suka gaisa, da ƴar buɗaɗɗiyar muryarsa ya ce, "Ai tun ɗazun muke ta dakon zuwanka, na so zuwa tarbar ka airport wani uzuri ya sa na makara ban samu zuwa lokacin da ka iso ba." Ɗan murmushi ne akan fuskar Deen yayin da yake sauraron uncle ɗin nasa wato Bashir, jagora ya yi masa suka shiga cikin gidan wanda kana gani ka san akwai ƙarancin tsafta a tattare da shi, Ammi da abban su mom ɗin shi ne suka tarbe shi cike da nuna farin ciki bayan sun ƙarasa cikin falon, kujerun cikin falon manyan leathers ne amman duk sun fita hayyacin su da datti, haka dakakken carpet ɗin da ke a shimfiɗe shima dai duk ya yi datti, bangon falon kuwa da ya sha wallpaper itama duk tayi dabbare dabbaren dauɗa da su jirwaye wani wurin ma ta babbako daga jikin bangon, haka nan dai Deen ya zauna asaman ɗaya daga cikin kujerun, cikin natsuwa da ladabi ya gaishe da kakannin nasa suka amsa masa cikin washe baki suna ƙara masa sannu da zuwa, "Ai mun yi zaton nan zaka fara sauka tun bayan da Jameela ta sanar da mu tahowarka muka shirya ma tarbar ka, amman sai Bash ke sanar da mu wai a hotel ka sauka." Ammi ce ta yi maganar, ya ce mata eh can aka sauke shi, ta gyaɗa kai, Bash da ke ta washe baki yana ɗaukar Deen bidiyo a kaikaice don ya yaɗa, dama ba ƙaramin tutiya yake ba da kasancewar matsayin Deen a wurinsa, "Deeni ya can ƙasar taku, ai muna ganin irin kokarin da kake yi wllh..." Abban su mom ɗin sa ya faɗa yana washe baki da haƙoransa tuni sun gama fita hayyacin su da dattin taba da goro, amsa mashi ya yi da Alhamdulillah, ya ce "Ma sha Allah, Allah Ya ƙara taimako ya sa kafi haka." Deen ya amsa da Amin, fitowa Ammi ta yi ɗauke da tray a sama an ɗaura lemun kwali da glass cup sai robar ruwa, a saman center table da duk glass ɗin sama ya tsattsage ta ɗaura ta maido shi gaban Deen tana faɗin ga lemu ya sha kafin a kawo abinci ya yi mata godiya, "Wai ina Aseey ba na ga bata je makaranta ba?" Bash ya tambaya yana kallon Ammi ta ce, "Eh, tun ɗazu take ta zaman jiran zuwan Deen, daga baya da ta ji ba a nan zai sauka ba shine ta ɗan fita na san ba da daɗewa ba zaka ganta, koma bara na kira ta na sanar da ita ya zo." Ta ƙarasa tana laluban wayarta a gefe, "Deen ka sha lemun mana, ko in zo in zuba maka ne, ka san fa kai babba ne." Bash ne ya yi maganar yana washe baki, ɗan murmushi Deen ya yi kawai ya ɗauki lemun gudun ya ce ba zai sha ba hakan ya zama wani issue, in da so samu ne ma ya sha a cikin kwalin ba sai ya yi amfani da cup ɗin ba don shi yadda ya ga gidan har ɗan kyankyami ya kama shi, a can ƙasan ransa kuwa mamaki yake yadda akai gidan ya kasance haka wanda ya san ba a jima ba mom ɗin sa ta amshi kuɗi masu yawa cewa su Ammin za su yi gyaran gida, sai dai bai ga alamun an yi wani gyara ba a gidan, "Salaamm.." Muryar mace ta furta, da sauri ta ƙaraso cikin falon tana washe baki idonta akan Deen, Aseeya ce wadda a shekaru ta kusa talatin, itama tubarkallah jajir take tana da kyau ba laifi sai dai sam bata kai kyawun mom ɗin su Deen ba, sanye take da wata straight gown da ta yi matuƙar kama jikinta, kai kace idan ta yi kwakkwaran nishi rigan zata iya yagewa, kanta ta tsigara ɗaurin kallabi da ya bayyanar da yalwatacciyar baƙar sumarta da ke fake a baya, daga gaban rigan kusan rabin ƙirjinta a waje yake fatar wurin ta fito fari fat da ita, nufo inda Deen ya ke ta yi tana ci gaba da washe baki ta wurga yar jakar da take rike da a wata kujera, ta zame ɗan ziririn gyalen da ke rataye a kan kafaɗarta guda, zama ta yi a kujerar da ke kusa da ta Deen cike da zumuɗi ta ce, "Welcome ɗana, ai tun ɗazun na yi ta zaman jiran ka sai baka zo ba." Dan kallon fuskarta ya yi ba tare da ya yarda idanunsa sun sake kallon jikinta ba, murmushi ya yi mata ya ce, "Thank you, ya karatu?" Ta amsa masa da Alhamdulillah ta ce ai yau saboda zuwan sa ma ta ƙi zuwa makaranta tana son ganin sa don ya daɗe bai zo ba sun yi missing nasa." Shi dai ɗan murmushi kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba, sam bai yi mamakin ganin irin dressing ɗin jikinta ba sanin irin halin sakaci da rashin kula na iyayen su, "Aseey ki shirya ma ɗan naki abinci." Ta amsa ma Ammi da to tare da miƙewa da sauri, Deen kamar ya ce a bar shi amman ya san sai sun yi tsegumi idan ya ƙi cin abincin, dawowa Aseey ta yi ɗauke da wani babban tray an ɗauro warmers babba da ƙaramarta sai plates da cukulla, a saman center teble ɗin ta ɗaura da yake yana da faɗi, serving nashi abincin ta fara yi wanda farar shinkafa ce da miya ta sha naman kaza sai coleslaw, "Deeni ga abinci nan, an so ma a yi maka fin haka to mai aikin tamu ce ta je gida wai mamanta bata lafiya, nima kuma ba isassar lafiyan ce da ni ba, wannan ma ɗin duk kusan Aseeya ce ta yi." Ammi ta faɗa, godiya ya yi mata tare da addu'ar Allah Ya bata lafiya, sai da Aseey ta ƙara masa magana game da cin abincin ganin ya ƙi fara ci, sannan ya kai hannu ya ɗauki spoon ya fara ci..... ✨A CIKIN RAYUWA✨ ZAINAB BATURE 33 Deen bai wani ci abincin da yawa ba ya ce ya ƙoshi, Ammi ta ce, "Amman ai baka wani ci na kirki ba kuma don kai aka yi shi." Da ɗan murmushi ya ce mata ya ci abinci a hotel kafin ya taho, ta ɗan 6ata rai ta ce, "To ai da gangan ka ci abinci tun da ka san nan dole za a shirya maka ko, kuma yaushe rabon ka da nan ɗin fisabillillah, kamata ya yi a ce ka sauka anan amman baka yi hakan ba, kuma sannan abincin ma ka ƙi sakin jiki ka ci, ta ya zamu ji daɗin hakan." Haƙuri ya bata ya ce ba shine ya kama hotel din ba, ya yi mata bayani, Bash ma ya ɗaura da yi masu bayani game da gasar ƙwallon da aka shirya za a yi, ta nuna ta fahimta tare da yi mashi fatan nasara, kakansa ma da har lokacin yana zaune a falon ya yi masa addu'ar nasara, Bash ya ce ai ya ga bashi kaɗai ya zo ba har da jami'ai sai a kai masu abincin su ma, Ammi ta sa Aseey ta kira mai gadi ya zo ya ɗauka masu bayan an ƙara masu abincin, mom ɗin Deen ce ta kira Ammi tana tambayar ta ko Deen ya zo ta ce mata eh gasu nan ma tare da shi a falo har ya ci abinci duk da bai ma wani ci sosai ba wai ya riga ya ci a otel, bayan sun gama wayar sai ga kiran mom ɗin tashi ya shigo wayar shi shima, ya san tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi, abun da ya zo masa a rai zata ce masa shi ɗin ta jaddada masa wato ya tambaye su buƙatun su ya biya masu ya amsa mata da to, bayan gama yin wayar a nutse ya ce masu yana son tafiya don nan da dan lokaci za su fara wasa, Ammi ta ce,"To amman dai zaka dawo ko?" Ya amsa mata da eh, duk da bai da tabbacin hakan don yana son zuwa gidan ƙanwar dad ɗinsa wato Aunty Murja da ke nan, ce masu ya yi su faɗi buƙatun da suke da su aikuwa zo ka ga washe baki da gyara zama, Ammi ce ta fara faɗin buƙatar ta, farko ta ce kuɗi take so akwai wani fili da aka mata talla tana son siya, sannan tana son zata koma wani ƙwararren private hospital a duba ta da kyau rashin lafiyan da take yawan yi to asibitin yana da tsada sosai, sannan tana son ya bata jari tana son fara yin kasuwanci mai ƙarfi yadda zata rinƙa yin wasu buƙatun ba sai an ta takura masa da mom ɗin shi ba, a ƙalla ta nuna tana buƙatar kusan miliyan ashirin, gashi duk buƙatun ma kame kame ne, Deen ya ce mi zai hana ta je Abuja maganar binciken lafiyarta tun da akwai asibitoci masu ƙwararrun likitoci, tarar hanzarinsa ta yi da sauri ta ce ai wannan asibitin ma da take son zuwa nan likitocin ƙwararru ne don har da turawa ba sai ta je har Abuja ba ya amsa mata da to, da aka zo kan Abba yana washe baki ya ce yana buƙatar kuɗi wanda zai yi gyaran gidan har da bene yake son a ɗaura, sannan kuma yana son zai je kasar su ziyarar dangin su don ya daɗe bai je ba kuma idan ya je zai yi masu alkhairi, dangin da tuni ya yafe su, taƙamaimai ma bai san inda wasu dangin nasu suke ba tun da shima a nan aka haife sa, ƙarshe ya ce motarsa ta tsufa tana bashi matsala yana son a canza masa wata, shiru Deen ya yi yana kallonsa har ya gama magana, da kamar ya share amman kuma sai ya dake ya ce, "But kwanaki mom ta amshi kuɗi a hannuna ta ce zata turo ma Ammi a gyara gida, ko bata ba ku?" A tare Ammi da Abba suka kalli juna, daga kallon da yake mata zaka gane shi bai san ma da maganar ba, murmushin yaƙe Ammi ta shiga yi cike da kama kai ta ce, "Ah...eh tabbas an yi haka, to amman kuma wani uzuri na kuɗi ya gifta lokaci, ka san uzururrukan rayuwa basu ƙarewa kuma ba shawara suke ba kafin su zo, dole da kuɗin aka yi amfani." Deen bai ce komai ba, Bashir ya gyara zama ya fara nashi bayanin, shima mota yake son a canza mashi ya faɗi kalar wadda yake so, sannan ya ce shagon shi na sayar da kayan su atamfofi da shaddoji da laces wanda Deen ɗin ne ya bashi jarin da ya buɗe shi, wai duk ya yi ƙasa saboda buƙatun yau da kullum da yake yi ma kansa da gidan nasu, gashi har yau karatun shi bai kammala ba balle ya samu aiki, karatun da shekara da shekaru ya fara shi amman gamawa ta gagara, kallon ƙarya mutum ke shirgawa iyayen nashi suka shiga bin sa da shi, mutumin da da ƙyar suke amsar kuɗi a hannunsa suma ba masu yawa ba, ba abun da ya saka a gaba sai sharholiyar shi da mata duk akan su ya ƙarar da kayan shagon, gashi akwai son yin ƙarya cikin abokai, koda yaushe yana nuna shi ɗin wani ne yana tutiya da yayarsa tana auran ɗan majalisa a Abuja sannan ɗanta shahararren ɗan kwallon duniya ne, ga kuma wata yayar tasa da ke auren babban injiniyan fasaha da ya mallaki company a ƙasar waje. Shima babansu ba abun da ya saka a gaba sai neman mata da shaye-shaye duk anan yake 6annatar da kuɗi har caca yana yi, ku san duk halayyarsa ce Bash ya ɗauko, a 6angaren Ammin su kuwa ita wannan shahararriyar mai bin bokaye ce, komi ƙanƙantar matsala sai ta kai wurin boka, ita a wurinta ta yi imanin dukkanin hasken da take gani a rayuwarta to sanadiyyar aikin da ake mata ne, duk a wurin bokaye kuɗaɗenta ke tafiya, gashi ta iya wulaƙanta mutane musamman talaka, sannan akwai ta da son nuna ita wata ce, da tsiya ta kutsa kanta tana abota da matan masu kuɗi da manyan ƴan siyasa da kuma mata ƴan duniya. Da aka zo kan Aseeya ta faɗi abun da take so cewa ta yi sabuwar iphone da aka yi take so ya canza mata sannan wai duk kayanta sun tsufa tana son ta yi canjin wardrobe, Ammin su har da ce mata ita ke nan buƙatar da zata faɗa ga harkar ɗawainiyar karatun ta Aseey ɗin ta ce ta manta, bayan su da suke a gida sun gama faɗan buƙatun su har da na Adam autan su da baya nan a cewar su yana makaranta shima sai da aka zayyano nasa buƙatun, sannan Ammi ta ɗaga waya ta kira Nailah da suka ce itama ta yi tafiya, bayan ta sanar mata game da zuwan Deen ta ce ta faɗi buƙatar ta a sanar masa, ta saka aka ba Deen wayar suka gaisa ta yi mashi an zo lafiya, daga baya kai tsaye ta ce mashi miliyan goma take so ya tura mata zata yi wata buƙata ya amsa mata da ok, a ƙalla buƙatun da suka kawo masa sun yi na kusan miliyan ɗari, kuma bai isa ya ce ba zai yi ba ya san suma za su kafa hujja da abubuwan da ya je ya yi a Funtua tun da ya san sun gani, kuma zai fuskanci 6acin ran mom ɗin sa in bai yi ba, tambayar su ya yi a account ɗin wa za a saka kuɗin, da sauri su dukansu kowa ya ce a tura mashi a account ɗin sa sanin halin junan su akan kuɗi. Bayan ya sallame su ya yi masu sallama dukansu suka rako shi harabar gidan sai faman washe baki suke kakar su ta yanke saƙa an cika masu account da kuɗaɗe, shima maigadin su saida ya bashi kuɗi masu yawa ya yi ta masa godiya, ku san a tare Bash da Abbansu suka kai hannu cikin rawar jiki don su buɗe ma Deen mota, bayan ya shiga ya ƙara yi masu sallama suna ta yi masa godiya da addu'oi, Bash na ce mashi sai sun haɗu a stadium daga haka motocin suka bar harabar gidan. Deen na zauna a bayan mota ya ɗage kansa sama bayan sun hau hanya, sam bai ji komai ba da kuɗin da ya basu, sai dai har cikin ransa baya jin daɗin wasu abubuwan musamman yadda suke yawan kawo masa buƙatu idan ya biya masu kuma basu tattalawa, sam dangin dad ɗinsa ba su yi masa hakan, a gaba ɗaya familyn su bashi da wanda suka shaƙu sosai suke matuƙar ƙaunar juna irin Fahad, amman bai ta6a buɗe baki ya tambaye shi wani abu ba, haka ma sauran en familyn dad ɗinsa ba wanda yake tambayar sa kuɗi sai dai idan shi ya yi masu alkhairi, ko hajiya bata tambayar sa abu sai dai ta kawo masa shawarar ya yi ma wasu alkhairi cikin dangin dad ɗin sa idan da buƙatan haka, ko lokacin da zai baro funtua da ƙyar daddy ɗin su Fahad da momynsa suka amshi kuɗin da ya tura masu, duk da haka sai da daddy Sa'ad ya rage wasu ya mayar masa a cewarsa kuɗin sun yi yawa. Bayan wani lokaci ya sauke kansa ƙasa ya duba agogon da ke ɗaure a hannunsa, ya so a lokacin ya ziyarci Aunty Murja, sai dai ganin lokaci ya ja ya sa shi fasawa sai wani lokacin. Misalin ƙarfe ukku da rabi aka zo ɗaukar Deen zuwa babban stadium ɗin garin da anan ne za a yi gasar, ya shirya tsaf yana sanye da jersey ta club ɗin da zai wakilta, yadda aka shirya tournament ɗin iya clubs na cikin gida ne za su yi, amman daga baya wasu clubs na wasu jahohin suka shiga hakan ya ƙara faɗaɗa gasar. Ɗumbin mutane masoya ƙwallon ƙafa da ma waɗanda ba sa harkar ƙwallon kawai don su ga wasan Deen ne suka halarta, wasu mutanen ma daga wasu jahohin suka taso suka zo don su kalla, su kan su mashiryan gasar basu yi tunanin gasan zata yi haka ba, yayin da aka fara wasan ba ka jin komai sai hargowar mutane, wasu suna waƙen goyon bayan clubs ɗin da ake wasan da su, wasu suna sakar ma club ɗin adawar su habaice habaice, gaba ɗaya Deen ne tauraron wasan har waɗanda basa goyon bayan club ɗin da yake ma wasan sai faman washe baki suke ba tare da sun san suna yi ba, ainihin ƙwarewa a ƙwallon ƙafa mutane ke a gani a wurin Deen, muryoyin mutane sun karaɗe stadium ɗin da faɗin sunan Deen Jr, tuni videos da hotunan wasan suka karaɗe kafofin sada zumunta, mutane nata comment wasu suna jin tamkar su yi tsuntsuwa su gan su a wurin. Lokacin sallar magrib aka dakata da wasan, sai bayan da aka gama sallar issha aka kuma dasa wanda suka kai har ƙarfe goma na dare kafin aka gama. Farko yadda aka tsara tournament ɗin na kwana ɗaya ne, amman yanzu dole ya zama na kwana biyu kuma an ƙara lokuttan bugawa saboda gasan ba zai kammalu cikin kwana ɗaya ba. A matuƙar gajiye Deen ya koma ɗakinsa na hotel bayan an maida shi, wanka ya fara yi sannan ya yi sallar shafa'i da wutiri, da ƙyar ya fita falo ya ɗan ci abincin da aka kawo masa ba da yawa ba, ya so ya ɗan zauna a nan ya duba tarin saƙonnin da yake da tare da missed calls da ya tarar a wayansa da niyyar abincin da ya ci ya bi masa jiki, sai dai ya gaji sosai kawai so yake ya ji sa a kwance hakan ya sa shi wucewa cikin ɗaki, already kayan bacci ne a jikinsa ya nufi gado idanunsa na lumshewa. Salma zaune a ɗakinta bayan ta yi shirin kwanciya, tunani ne iri-iri ke mata yawo a cikin zuciya, tun bayan da ta gama kallon vedios na wasan Deen a Kano da ke ta yawo a social media ta ji tana son ta yi waya da shi, sai dai wata zuciyar na hana ta yin hakan duba da jiya ta kira shi bai ɗauka ba kuma bai biyo kiran ba, don haka yanzu ma ko ta kira hakan ne zai sake faruwa, wannan tunanin ya sa ta fasa kiran nasa ta haye gado ta kwanta, ko da ta kwanta ta kasa yin bacci kuma son kiran Deen ɗin ya ƙi fita daga ranta, hannu ta kai a hankali ta ɗauko wayarta ta latsa power haske ya kawo, ƙura ma hotonta tare da innarsu dake a wallpaper ɗinta ido ta yi tana kokonton ko ta kira, bayan ɗan lokaci ta kai hannu gabanta na ɗan faɗuwa ta danna masa kira, Deen bai daɗe da kwanciya ba wayarsa ta fara ringing, a hankali ya buɗe idanunsa da bacci ya fara cin ƙarfin su sun ɗan yi ja, kallon wayar da ke ta yin ringing ya yi bacin da ya ci karfinsa ne ya sa bai saka ta a silent ba, a hankali ya kai hannu ya ɗauko ta da niyyar ya saka ta a silent ɗin, bin lambar da ake kiran da ita ya yi da kallo ya gane ita ce aka kira sa har sau biyu jiya da daddare, ɗan jim ya yi kamar yana tunani a haka har kiran ya tsinke, jiki a sanyaye Salma ta bi wayan da kallo bayan kiran ya yanke, zuciyarta na jaddada mata ai dama ta ce ko ta kira ba zai ɗauka ba, ajiye wayan ta yi a cikin ranta ta yanke wataƙil ba kowane kira yake ɗauka ba, ƙilan shi ne zai rinƙa kiranta, tunani ta yi ko ta yi masa magana ta whatsApp, har zata yi hakan sai kuma ta fasa ganin dare ya yi ta yanke gobe idan Allah Ya kaimu sai ta yi mashi, bayan kiran ya yanke Deen ya ji yana son sanin wanda ke kiransa da lambar, a kasalance ya maida ma lambar kira, Salma har ta rufe idanuwanta jin ƙarar wayarta ya sa ta yi saurin buɗe su, mamaki ne ya kama ta ganin Deen ne ke kira, da sauri ta tashi zaune gabanta na ɗan faɗuwa ta kai hannu ta ɗauki wayan, kamar mai jin tsoron yin picking a ɗarare ta ɗauki kiran, shiru ta yi bayan ta kara ta a kunne ƙirjinta na ci gaba da ɗan bugawa, sam ta kasa yin magana sai ɗan motsa baki take kamar mai ƙoƙarin tattaro abun da zata faɗa, "Hello, Assalam alaikum..." Ta ji daddaɗar muryarsa a cikin kunnanta, har sai da ta ɗan rufe ido murmushi ya bayyana a kan fuskarta, a hankali ta ce, "Wa'alaikumus salam. Ina yini.." Jim ya ɗan yi ba tare da ya amsa ba, tunani ta fara yi ko bai gane ta ba ne ko kuma bai ji ta ba, hakan ya sa ta ɗan ɗaga murya ta sake cewa, "Yaya Deen ina yini." Daga ɗayan 6angaren ta ji ya furta, "Salmerhh.." Bata san lokacin da ta saki faffaɗan murmushin jin daɗin ya gane ta ba, a hankali ta amsa masa da na'am, "How are you?" Ta ce, "Alhamdulillah." Shiru ya yi, ta ce, "Dama tun jiya na kira in yi maka ya ka isa sai baka ɗauka ba, shine dama yanzu na sake kira." Ta faɗa tana ƴan kame-kame, calmly ya ce, "Ok, I'm sorry bana ɗaukan bakon no, na isa lafiya. Thank you." Shiru ta yi tana ci gaba da yin ɗan murmushi tare da ɗan wasa da yatsun hannunta wanda ba da shi ta riƙe wayar ba, "Any problem?" Ta ji ya tambaya, da sauri ta girgiza kai ta ce, "A'a dama shike nan." Tambayar ta ya yi layin ta ne wannan don wayar da ya bata babu layi, ta amsa mashi da a'a ɗayan na innarsu ne ta bata take amfani da shi, ya ce ok zai iya saving nashi ta ce eh da shi zata rinƙa amfani, bayan ya amsa mata da ok ya ce mata za su yi magana ya gaji ne sosai don har ma ya fara yin bacci, da sauri ta ce mashi to tare da yi masa sai da safe, bin wayar ta yi da kallo bayan ta cire ta daga kunnanta, haka nan take jin wani nishaɗi wayar da ta yi da shi don ita komai da ke faruwa tsakanin su ɗaukar shi take a matsayin alfarma yake mata sanin ya fi ƙarfin hakan da ita. Matasa ne guda ukku zaune a saman benci a gaban wani shago wanda rubutun da aka yi a sama ke nuna shagon sayar da provision ne, gaba ɗaya sun cika wurin da hargowa suna hirar gasar da aka yi yau da irin yadda Deen ya iya sarrafa ƙwallo, daga cikin shagon wani matashin saurayi ne jikinsa sanye da ƙananun kaya ya ɗan kwanto saman kantan gaban shagon yana saurarar su, daga yanayin da fuskarsa ta nuna zaka gane yana da interest kan hiran don har ɗan murmushi yake, a kallo ɗaya idan ka yi ma matashin zaka shaida kyakkyawa ne na gaske, launin fatarsa mai matuƙar kyaun gaske wanda ba kasafai aka cika samun mutane masu irinta ba, yana da dogon hanci da madaidaicin baki, idanuwansa na da ɗan girma masu haske da baƙar ƙwaya wuluk, yana da cikar gashin gira wanda zanenta ya fita raɗam da kwantaccen gashi, haka gashin saman kansa ma yana da cika gashi baki mai santsi ya kwanta luf, kana ganinsa zaka iya yanke cewa ba ɗan nan ƙasar bane don daga yanayin fatarsa da kyawun fuskarsa ya fi kama da irin mazan ethiopia, bayan ɗan lokaci samarin suka tashi ɗaya ya ce ma mutumin da ke cikin shagon ya bashi maganin sauro, ɗayan ma ya ce ya bashi indomie manya guda biyu da ƙwai biyu, bayan ya sallame su suka yi ma juna saida safe suka tafi, ɗayan da bai tafi ba ya ƙaraso cikin shagon yana kallon mai shagon ya ce, "Wai Mukhtar mi ya hana ka zuwa kallon gasar ne?" Ɗan murmushi Mukhtar ɗin ya yi ya shafi sumarsa cikin muryarsa mai tattare da natsuwa ya ce, "Ba komai Tasiu, haka nan na ƙi zuwa." Tasi'u ya ce, "Amman kana son ƙwallo balle wannan babbar gasa ce, uwa uba kuma har da ɗan'uwanka wanda duniya ta san da shi a harkar ƙwallo." Shiru Mukhtar ya yi yana kallon Tasi'u kawai, daga yanayin fuskarsa zaka fahimci ɗan yanayin damuwa da ya bayyana, Tasi'u da ya san miye damuwarsa ya ce, "Da nine kai zan je kuma sai na yi yadda na yi na samu yin magana da shi." Wani murmushi wanda ya fi kama da a kira na takaici Mukhtar ya yi ya ce, "In ce masa mi Tasi'u? Mutumin da bai damu da kai ba kamar ma bai san da Allah ya yi ka ba...." Tasi'u ya yi ɗan jim, shi fa a yadda yake ji da shine yake da alaƙa ta jini da Deen wllh duk yadda za ai sai ya samu ya yi magana da shi, amman da yake ya san halin Mukhar mutum ne mai kauda kai hakan ya sa bai ta6a tunanin ya nemi Deen ba tun da shi ma bai neme su ba, Tasiu ya ce, "Amman ni abun nan na ɗaure mani kai wllh, mutumin nan ana yabonsa da halin kirki, amman a ce bai ta6a tunanin ya neme ku ba matsayin ku na danginsa, duk irin alkhairin da ya ke ma mutane wasu ma can bare amman ku bai ta6a yi maku ba, abun nan da mamaki." Shiru Mukhtar ya yi can ya sauke ƴar ajiyar zuciya ya ce, "Wataƙila bai san da mu a matsayin danginsa bane." Tasiu ya yi masa wani kallo ya ce ta ya hakan zai yuwu da mahaifinsu da mahaifin mahaifiyarsa uwa ɗaya uba ɗaya, su fa matsayin cousin ɗin mahaifiyarsa ne amman a ce bai san da su ba a matsayin danginsa, shiru kawai Mukhtar ya yi amman shi ya san dalilin da ya sa ya faɗi hakan wanda abu ne mai sauƙi hakan ta kasance, jin bai ƙara cewa komai ba Tasiu ya ce don Allah gobe ya zo su je tun da ba a gama ba, Mukhtar ya ce masa zai duba yuwuwar hakan, bayan Tasiu ya siya biredi da madara suka yi sallama ya tafi, bayan tafiyarsa zuba ma wuri guda ido Mukhtar ya yi yana tunanin abun da ya faru can baya tsakanin shi da Ammin su mom wanda har ta yi masa iyaka da zuwa gidan su, ranar da abun ya faru ya je unguwar su gidan su wani abokinsa bayan sallar azahar, bayan ya gama ya biya don ya gaishe da ita kamar yadda duk bayan lokaci yake yi, duk da su sam basu yin zumunci da su hakan bai dame shi ba a wurinsa yana yin hakan ne don Allah, kuma halin ko in kulan da suke nuna masu bai dame sa ba, da sallama ya shiga falon Ammi na zaune tana cin abinci ta amsa masa babu yabo babu fallasa, bayan ya zauna kan kujera ya gaishe da ita, shiru ya yi Ammi ta tambayesa ƴan gidan su ya ce mata duk suna lafiya, "Ga shi ka zo abinci ya ƙare ba a san da zuwan ka ba." Ta faɗa tana mashi wani kallon rashin arziƙi, ya yi murmushi ya ce, "Ah ba komai dama zuwa na yi in gaishe ku." Ta ce, "To an gode." Daga haka ta ci gaba da cin abincinta, motsin shigowar da suka ji ya sa duk suka kai idanunsu kan kofar shigowa, Aseeya ce ta shigo cikin falon tana wata irin tafiya jikinta sanye da riga da skirt na lace da suka yi matuƙar matse jikinta, sosai kayan suka fito mata da shape din jikinta tamkar an zana ta, hannunta riƙe da ƴar jakarta da kallabinta, saman kanta wani ɗan yalolon gyale ne mahaɗin kayan sharara da shi hakan ya bayyanar da sumarta dake a baje, bin ta da ido Ammi ta yi har ta ƙaraso ta zauna a kujeran kusa da ita, Ammi ta ce, "Sai yanzu zamu gan ki? Daga zuwa wurin biki shiru tun jiya kin sa hankalin mu duk ya tashi, ga shi anata kiran wayarki tun tana shiga ba a ɗagawa har ta dawo a kashe." Kamar bazata tanka ta ba sai faman wani lumshe ido take, can kamar magana na mata wuya ta ce, "Ba a tashi dinner ɗin da wuri ba, shine kawai muka wuce gidan su amaryan muka kwana." Shiru Ammi ta yi tana kallon ta don ta so fahimtar kamar ƙarya take ba gidan su amaryar ta kwana ba, tun da idan can ta kwana miye na ƙin ɗaga waya kuma ba sai ta kira ta faɗa ba, ganin Mukhtar na a falon ya sa ta yi shiru bata ƙara ce mata komai ba, "Zaki ci abinci ne?" Ammi ta tambaya, ɗan girgiza mata kai ta yi ta ce a ƙoshe take, "Ba ki ga yayan ki Mukhtar ba." Ta wani ɗaga ido ta kalle shi suka haɗa ido, a daƙile ta ce masa sannu ya ɗaga mata kai kawai, wayarta ce ta fara yin ringing ta kai hannu ta buɗe jakarta ta fiddo, lokacin Ammi ta miƙe ta bar falon riƙe da plate ɗin data gama cin abinci, murmushi Aseey ta shiga saki tana amsa wayar, daga yanayin yadda take amsa wayar Mukhtar ya gane koma wanene suke magana ta waya da shi suka kasance duk in da ta kwana, ko nauyin Mukhtar ɗin bata ji ba yadda take yin wayar, sadda kai Mukhtar ya yi jikinsa ya yi sanyi sosai, duk da dama ya san halin da yaran gidan suke ciki amman jin irin maganganun da Aseeya ke yi a gabansa hankalinsa ya tashi sosai, lokaci guda wani 6angare na zuciyarsa ya fara saƙa masa wani abu yayin da ɗayan 6angaren ke gargaɗinsa kan hakan, tunawa ya yi da ita ɗin ƴar'uwarsa ce yana da hakkin da zai yi hakan, bayan ta gama yin wayar miƙewa ta yi ba tare da ta ɗauki gyalenta da ya zame daga kanta ba, iya jakarta kawai ta ɗauka zata nufi ciki, "Aseeya..." Mukhtar ya kira ta yana kallonta, dakatawa ta yi ta juyo tana kallon sa ba tare da ta ce komai ba, "Idan ba damuwa ina son yin magana da ke ne." Tsaye ta yi kamar bazata tanka masa ba, sai kuma ta matso daga gabansa ta ce tana ji, nuna mata kujerar gefensa ya yi ya ce ta zauna, wani kallo ta yi masa sai kuma ta yi yadda ya ce ɗin, duk da yadda gabansa ke ɗan faɗuwa saboda fargabar abun da zai iya biyo baya, amman haka ya tattaro ƙwarin gwiwa cikin kwantar da murya ya fara mata magana, "Aseeya...dama magana ce nike son yi maki ko kuma in ce nasiha da ta shafi rayuwar ki a matsayina na ɗan'uwanki...ina fatan zaki fahimce ni, ina son in ja hankalinki ne Aseeya, kada ki bari ruɗin zamani ya yi tasiri a kan ki, a matsayin ki na mace Allah ya yi maki daraja, kada ki bari wannan darajar ta ki ta zube, mutuncin kowace ƴa mace ɗakin mijinta, yadda kike tubarkalla na san kina da masu son ki da aure, kada ki bari damar ta wuce ki, ki yi aure domin hakan shine zai fi zama alkhairi a rayuwarki, ki rabu da duk wasu maza masu zuwa wurin ki ba da alkhairi ba ko zancen aure, domin da sun samu abun da suke so a wurin ki za su bar ki kuma ba lalle su aure ki ba, shi namji duk abun da ya yi ado ne, ita kuwa mace abu kaɗan ke ta6a matuncin ta...." Tun da ya fara maganar ta ke bin sa da wani kallo irin na mamaki ta ɗan yamutsa baki, can ta katse shi a harzuƙe ta miƙe tana faɗin, "Ban gane inda ka dosa ba Mukhtar, mi kake nufi? Wani abu ka ga na aikata da zaka zauna kana mani waɗannan maganganun, ko kuwa kana son ka ce su iyayena ba su kula da tarbiya ta shine zaka zauna kana mani wani nasiha..." Yadda take yin maganar tana wani fizge fizge sai ka ce Mukhtar ɗin ba matsayin yayanta yake ba, maganganun da take yi ne cikin ɗan ɗaga murya da alama suka jawo hankalin Ammi ta fito, nufo su ta yi tana tambayar mike faruwa, Aseeya ta juya tana faɗa mata maganganun da Mukhtar ɗin ya yi mata, cikin ɗaure fuska Ammi ta juya ta kalli Mukhtar da ya sadda kan sa ƙasa, a harzuƙe ta ce, "Wato dama zuwan da kake yi gidan nan ba don Allah bane da wata manufar ne ke nan." Da sauri ya ɗago tare da girgiza mata kai cikin sanyin murya ya ce, "A'a Ammi, Allah ne shaida na ni don zumunci nike zuwa." Ammi ta ce, "Da kuma saka ido ko? Wato yadda mahaifinka kafin Allah Ya ɗauki ransa ya saka mana ido, ƙiri ƙiri ya rinƙa nuna mana hassada baya son ci gabanmu, ya fi son mu ci gaba da zama a ƙarƙashin sa muna roƙonsa yana taimaka mana, shine kai ma yanzu zaka dasa daga inda ya tsaya ko?" Shiru Mukhtar ya yi idanunsa a ƙasa, ta ci gaba, "To ni ba zan lamunci a saka ma zuri'a ta ido ba, don muma ba wanda muka saka ma ido, hasali ma bamu san ya kuke gudanar da rayuwar ku ba, don haka ka cire idanuwanka daga kan rayuwar iyalina, ku ma ai ba wanda ya san abun da kuke aikatawa a 6oye, sai mutum ya rinƙa nuna shi na Allah ne alhali Allah kaɗai ya san mugun abun da yake aikatawa a baɗini. Kuma da kake mata maganar ta yi aure ita ƙanwarka Fadeela ba tana zaune a gida ba har yanzu bata yi auren ba, ita miyasa baka saka ta ta yi auren ba tun da ka san shine alkhairi a wurin mace? To daga yau in dai ka san abun da ke kawo ka gidan nan ke nan kada ka sake zuwa, zumuncin da ka yi mana mun gode Allah Ya bada lada, shima mahaifinka ku san hakan ce ta faru a tsakaninmu da shi, ba dalili bamu saka ma kowa ido ba mu a saka mana, sam ni ban lamuntar hakan. Ka gaida gida." Tana kai wa nan ta ja hannun Aseeya suka nufi ciki tana ƴan maganganu, ba ƙaramin sanyi jikin Mukhtar ya yi ba, da ƙyar ya miƙe ya ja kafafunsa da ya ji sun masa nauyi ya fita, yana saman mashin ɗinsa bayan ya kamo hanya, a hankali ya ke kai hannu yana goge ƙwallan da ke zubo masa, ba komai ne ya sa shi zubar da ƙwalla ba sai jin ƙazafin da Ammi ta yi ma mahaifinsu, wanda Ummansu ta basu labarin irin jajircewar da ya yi wurin tallafa ma rayuwar su amman shine suka saka masa da hakan. Tun daga wannan ranar bai ƙara zuwa gidan ba, farko bai yi niyyar abun da ya faru ya sa shi yanke zumunci da su ba, amman saboda maganganun da ta yi akan mahaifinsu ne ya sa ya haƙura da zuwa gidan, ko Ummansu da sauran ƴan'uwansu bai sanar da su abun da ya faru ba, don bai son gaba ɗaya su yanke zamunci da su, duk da dama ita ummansu tuni ta fita sha'anin su, suma sauran ƴan'uwan shi ba wani zumunci suke da su ba sosai, da Sapna tana tallafa masu sosai, wani lokacin idan ta zo har gidan take zuwa ta yi masu alkhairi mai yawa, itama daga baya basu san mi ya faru ba ta janye masu jiki ta daina yi masu duk abun da take masu, amman ƙanwar mahaifinsu Maryam wadda a yanzu ba a ƙasar suke zaune ba tana tallafa masu sosai kuma idan suka zo ƙasar tana ziyartar su ko kuma su su je. Nannauyar ajiyar zuciya Mukhtar ya sauke bayan ya gama tunano abun da ya faru, ji ya yi gaba ɗaya jikinsa bai masa daɗi hakan ya sa shi fita ya kulle shagon, gidansu da ke a gefen shagon ya shiga, gidan nada ɗan girma ba laifi kuma yana da kyau, gaba ɗaya tsakar gidan broken tiles ne kuma ginin bai ji jiki ba duk da tun gidan da mahaifinsu ya rasu ya bar masu ne, amman ana mashi gyara lokaci bayan lokaci. Bayan rasuwar mahaifinsu ummansu ta ƙara yin wani aure bayan wasu shekaru, amman ba ta bar gidan ba har Allah ya yi ma mijin da ta aura rasuwa shekarun baya, tun daga nan bata sake yin wani aure ba yanzu ma har ta manyanta, gaba ɗaya sun taru sun rufa ma kan su asiri sun jajirce suna yin sana'oi sannan akwai masu yin aiki a cikin su, dama su biyar ne mahaifin su ya bari, babban yayan su da mai bi mashi sai mace guda duk sun yi aure, yanzu daga Mukhtar wanda ya kammala karatunsa na degree bai kai ga samun aiki ba, sai autar su Fadeela da ke cikin yin karatu a BUK suka rage a gidan, itama Fadeela da tuni ta yi aure don tana da samari masu son ta da yake suma yaran gidan tubarkalla kyawawa ne sosai, wasu farare ne tas yayin da wasu farin nasu ya gauraya da kalar mahaifiyarsu da take wankan tarwaɗa hakan ya sa hasken su ya fita daban, sam Fadeela bata sauraran masu son ta don ita ba wanda Allah Ya jarabe ta da son shi sai Bashir na gidan su mom, ba ƙaramar wahala zuciyarta ke bata ba akan son shi, gashi shi kuma sai faman gara ta yake yi, ba irin faɗan da ba a yi mata ba a gida kan ta rabu da shi amman ta kasa, yanzu haka cikin dagar da ake ta yi da ita ke nan a gida kan ta rabu da Bashir ta fidda miji a cikin masu sonta amma abu ya ci tura...... ✨A CIKIN RAYUWA✨ ZAINAB BATURE 34 Washe gari tun safe aka ci gaba da yin gasar da su Deen ke yi wadda ta kai har zuwa yammacin ranar, ƙarshe dai waɗanda suka haɗa gasar sune suka lashe kofin wato babban club ɗin da Deen ya buga mawa, ba wanda kuma ya ja da hakan don Deen sam bai sarara ma abokan karawar sa ba, dama kowa ya riga ya saka a ransa club ɗin su Deen ne zai yi nasara saboda kasancewar sa a cikin su, an bayar da lambobin yabo ga ƴan wasan da suka yi nasara da kuma sauran clubs da suka yi na biyu da na ukku, ban da wannan Deen ya karɓi babbar lambar yabo ta Player of the Tournament, bayan da ya kuma zama Man of the Match a wasan ƙarshe. Baya ga manyan lambobin yabo da ya samu a tournament ɗin, wasu daga cikin kamfanonin da suka ɗauki nauyin gasar sun karrama shi da lambobin yabo na musamman, suna yabon girmamawarsa, tasirinsa da ƙwarewarsa, tare da kuɗaɗe da kayayyaki masu tsoka, har da gwamnan jihar wanda ya kalli wasan ƙarshe kuma ya karrama wasu da suka yi nasara shima ya yi ma Deen karramawar sa. Bayan jawabin godiya daga Deen anan take ya sadaukar da kudaden da aka bashi ga team ɗin guragu da ke buga ƙwallon ƙafa, ya nuna yabawarsa a gare su kan yadda nakasar su bata saka sun kasance cikin ƙunci ko kuma za6ar su rinƙa yin bara a tituna, wannan tallafi da Deen ya bayar ba ƙaramin daɗi ya yi ma mutane ba da ƙara masa farinjini, a nan wasu manyan kamfanoni suka gabatar masa da tayin hulɗa daban-daban da suka haɗa da tayin zama jakadan kamfani wato Brand Ambassador offers, Sponsorship and Partnership offer da sauransu, in da ya nuna zai duba wasu. Bayan komawar sa hotel shiryawa ya yi cikin shiga ta musamman don kai ziyara babban asibitin gwamnatin garin tare da rakiyar jami'ai da wasu football officials da manyan ƴan kwallon jahar, da suka je asibitin kamar yadda ya ba marasa lafiya tallafi a Funtua haka nan ma ya ba marasa lafiya tallafin kuɗaɗe da biya ma wasu kuɗin aiki. Bayan sun gama daga nan gidan ƙanwar mahaifinsa aunty Murja ya wuce don gobe zai koma Abuja ita kuma tana zuwa aiki malamar jami'a ce bata nan da safe, daga shi sai jami'an da ke tare da shi suka je gidan dake a Nasarawa G.R.A, bayan motocinsu sun faka a cikin harabar gidan wanda yake babban flat ne mai kyau, aunty Murja da maigidanta tare da yaran su ukku da ke dakon zuwan shi bayan da ya kira ya sanar mata, suka tarbi Deen cikin nuna farin cikin ganin sa, shima murmushi ne akan fuskarsa ya gaishe da su, ɗan side hug aunty Murja ta yi masa kana ganinta zaka ga kamanin hajiyar ambasada akan fuskarta, "You are highly welcome tauraron ɗana." Ta faɗa bayan ta sake shi, mijinta Dr Mustapha shima ya yi mashi sannu da zuwa, "You are welcome yaya Deen." Babbar ɗiyarta mai suna Fateema da ake ce ma Zarah ta faɗa tana murmushi idanunta sanye cikin glass, a yanayin shekaru zata yi shekaru ashirin da ɗoriya, ta biyun mai suna Nabeela da ba zata wuce shekara sha takwas zuwa sha tara ba tana sanye da abaya itama ta yi mashi sannu da zuwa tana murmushi, sai na ukkun wanda shine auta wato Nabeel shima a shekaru zai yi shekara sha biyar yana sanye da ƙananun kaya riga da wando, ya nufi Deen da murmushi ya faɗa jikinsa yana mashi sannu da zuwa Deen ya rungume shi, gaba ɗaya iyayen kana ganin su ka ga wayayyun ƴan boko, haka yaran nasu ma jikin su ya nuna hutu, kana ganin su ka ga ƴan gayu tun daga kan yadda suke magana, sannan ba laifi suna da kyau sam ba munana bane, Zarah doguwa ce sannan bata da jiki, a yanayin fatar ta tana da ɗan haske ba sosai ba, sai Nabeela ita ta ɗan fi Zarah jiki sannan bata kai haskenta ba, Nabeel kuma sam ba shi da jiki don duk ya fi so sirantaka sai dai kuma shi kana ganinsa fari ne, bayan sun gama welcoming na shi Dr ya ce su shiga ciki. A babban falon gidan da ya sha lafiyayyun leather chairs tsaf da shi suka zauna aka shiga sake yi ma shi sannu da zuwa, miƙewa Zarah ta yi ta nufi ciki bada jimawa ba ta dawo hannuwanta riƙe da tray a sama lemu ne da cup, a saman center table ta ajiye a gaban Deen tana murmushi, bayan ta zuba masa ta ce mashi gashi ya ɗaga mata kai tare da yi mata godiya, "Deen ya ka baro mom da dad din ka, mun yi ma waya da shi ɗazun da safe." Aunty Murja ta fada, a nutse ya bata amsa da suna lafiya suna gaishe da su, ta jinjina kai tana murmushi kafin ta kara cewa, "Ya can ƙasar taku da kuma iyayen ka na can." Ya amsa mata da suna lafiya, "Deen ya ball?" Dr ya tambaya shima da murmushi, ya amsa masa da Alhamdulillah, Dr ya ce, "Ma sha Allah, ai duk muna kallon wasan ku, kuna kokari sosai, Allah Ya ƙara taimakawa Ya tsare, Ya ƙara ɗaukaka." Gaba ɗaya suka amsa da Ameen, "Ya Deen jiya da kuka fara tournament a stadiun mun je kallo ni da wani friend ɗina, na so in yi magana da kai amman ba a gama ba muka taho saboda dare ya yi, ɗazun da yamma da aka gama muna wurin ban samu damar da zan yi maka magana ba." Nabeel ya faɗa da muryarsa mai tattare da yanayin sangarta, murmushi kawai Deen ya yi masa, aunty Murja ta ce ai suma duk sun kalla a Tv tare da yaba masa kan tallafin da ya bayar har a Funtua ta yi masa addu'oi, shima Dr ya yaba sosai tare da yin nasa addu'oin, "Zarah kin kawo lemu saura ki shirya ma yayan naki abinci a table, ko a kawo maka nan son?" Aunty Murja ta tambayi Deen, ya ce mata ya ci abinci baya jin yunwa, "Amman ka san ba zan barka ka zo ka tafi baka ci abinci ba, yaushe rabon ka da gidan nan, it's been a long time sai kuma ka ce ba zaka ci abincin zumunci ba, ka dai ci ko ɗan yaya." Murmushi kawai ya yi, Zarah da ta miƙe tana kallon sa tana murmushi ta ce ta shirya masa a table ɗin ko ta kawo nan, kallon ta ya yi ya ce duk yadda ta yi ta amsa da ok, zata wuce cikin zolaya ya ce ta bi a hankali kada ta zubar da abincin don ya ga ta zama makauniya, dakatawa ta yi ta ɗan rausayar da kai tare da ɗan tura baki ta ce, "Kai ya Deen, a ina ka ga na makance don na saka medical glasses ai ina gani." Duk suka yi ƴar dariya shima Deen murmushi ne akan fuskarsa, wucewa ta yi tana faɗin in da ita makauniya ce ai da baƙin glass zai ganta, hira aunty Murja ta shiga yi masa bayan Zarah ta dawo ta sanar masa ga abincin can ta kai masa bata zubar ba, ya yi ɗan faffaɗan murmushi tare da yi mata godiya, tambayar game da karatun su ya yi Zarah ta ce masa tana a level 2 zata je 3 tana karantar medicine a jami'ar da mom ɗinta ke koyawa wato BUK, Nabeela ta ce ita tana a level 1 itama zata je 2 tana karantar English Language itama a nan jami'ar, Deen dake fuskantar su yana sauraron su ya ce ita mi yasa bata ɗauki medicine ba ko don bata son ta sha wahala, tana dariya ta ce ai shima English ɗin yana da wahala Allah, gyara zama Nabeel ya yi da aka zo kansa ya ce shi yanzu yana a aji huɗu na secondary wato s.s one zai je two, idan ya gama school of aviation zai tafi don pilot yake son zama wato matuƙin jirgi, Nabeela na dariya ta ce, "A haka zaka zama pilot ɗin, cikin kai da jirgin waye zai ja wani." Ya jefa mata harara tare da cewa an faɗa mata abun a jiki yake." Deen da ke murmushi ya ce ai idan ya ƙara girma zai ƙara jiki, a hasale Nabeel ya ce, "Kyale ta yaya Deen, sauƙin abun dai ni ba acici bane, yaya Deen ka ganta nan rumbu ce, duk ita ke cinye abincin gidan nan, har namu idan muka rage duk wawushewa take." Dariya Nabeela ke yi ta ce, "Lafiya gare ni shi ya sa, kuma ba gashi da bambanci a tsakanin mu ba abincin na mani aiki, wani ma yana ci amman kaman baya ci." Dariya suka sa Deen har fararen haƙoran sa suka ɗan bayyana, suma iyayen nasu dariyar suke, aunty Murja ta ce, "Son ka ƙyale wannan biyun haka suke kullum faɗa kaman kaji, ka je ka ci abincin ka." Yana murmushi ya ce mata haka Leemarh da Omar suke duk suka zauna tare, "Haka ne dama yawanci zaka ga tsakanin sako da sako ba su cika jituwa ba. Allah Sarki my daughter Leemarh an daɗe bamu haɗu ba sai ta phone, dama ita ce take ɗan zuwan mana lokaci bayan lokaci idan ta zo hutu nan." Miƙewa Zarah ta yi ta ce su je ta yi serving na shi, bayan ya miƙe suka nufi hanyar dining area ɗin yana tafiyar shi mai tattare da natsuwa, duk idanun mutanen falon na akan shi Nabeela sai ɗan murmushi take yi ta kasa janye idonta akan shi, miƙewa Nabeel ya yi mom din su ta tambayi ina zai je ya ce zai taya yaya Deen hira, wani kallo ta yi masa ta ce, "Dama idan ana cin abinci ana hira ne? Za ka je dai ka takura masa, koma ka zauna ka jira ya gama." Hararar Nabeela dake masa dariya har da ɗan gwalo ya yi kafin ya koma ya zauna, bayan Zarah ta yi serving na shi abincin zama ta yi a kan ɗaya daga cikin kujerun ya yin da ya fara ci a nutse, jefi jefi suke ɗan yin magana da juna, kallonta ya yi ya ce itama ta ci abincin tana murmushi ta ce duk sun ci tun kafin ya zo, ba wani mai yawa ya ci ba Zarah na roƙonsa ya ƙara ya ce mata shima ya riga ya ci abinci ne kafin ya zo. Cikin falon suka dawo aunty Murja na murmushi ta ce har ya gama Zarah ta ce ai ba wani da yawa ma ya ci ba, zama suka yi Deen ya ce ya hana su kwanta ya yi zuwan dare, Dr na murmushi ya ce kada ya damu dama wani lokacin suna kai wa dare haka musamman idan kowa na da aikin da zai yi a daren, shiru na ƴan wasu daƙiƙu ne ya biyo baya kafin Deen ya kalli su Zarah ya ce masu kowa ya faɗa mashi abun da yake so, ɗan zaro ido suka yi tare da kallon juna suna ɗan murmushi, ya ce Zarah ta fara faɗa tun da ita ce babba, ɗan motsa baki ta shiga yi tana murmushi ta kasa magana, sai bin mutanen cikin falon take da kallo da suma duk idanunsu na akanta kowa yana jira ya ji mi zata ce, sam ta kasa magana Deen da ke kallonta da murmushi ya ce ko glasses za a ƙaro mata, ɗan tura baki ta yi a shagwabe ta ce, "Kai yaya Deen wai mi glass ɗina ya yi maka, ni fa ina gani kawai da dare ne vision na ke raguwa, sai idan zan duba paper especially white paper." Yana ɗan murmushi ya ce ashe dai makauniyan ce ita, a shagwabe ta ce ita wllh ba makauniya ba ce sai dai ko fiancee ɗin shi ce makauniya idan glasses ɗin ya yi masa ne sai ta bashi ya kai mata, iyayen su na ta ƴar dariya, shi Dr har da mamaki ya ke don bai zata Deen ɗin na iya yin wasa haka ba, ce mata ya yi yana jin ta ta faɗa mashi duk abun da take so ai shi ne ya tambaya, ƴan kifce kifcen idanu ta shiga yi tana satar kallon mom da dad ɗin su, da ƙyar ta ce mashi mota take so da zata rinƙa zuwa school, "Zarah! Wani irin mota kuma, ina bani ce ke tafiya da ku ba gaba ɗaya." Aunty Murja ta tari hanzarinta da faɗin hakan, ɗan yamutsa fuska Zarah ta yi ta ce, "Amman mummy wasu lokuttan ai bamu samun tafiya tare idan muna da bambancin lokacin lectures, kina riga na tafiya sai dai in je daga baya ko kuma ni na riga ki tafiya." Tana mata wani kallo mai kaman harara ta ce, "Wani time en ba daddyn ku na kai ku ba, ko kuma idan ba taren zamu tafi ba in saka Shuaibu ya kai ku, duk miye na wani a siya maki mota kuma?" A marairaice ta ce to amman wani lokacin ba sai dai ta hau abun hawa ba, kallon Deen aunty Murja ta yi ta ce, "Son ka rabu da ita ba wani motan da za a siya mata." Shi dai murmushi kawai yake, tambayar Zarah ya sake yi sai mi take so? A sanyaye ta ce ba komai motan ma a bari tun da mummy bata so, dariya Nabeela ta fara yi tana sunne kai lokacin da itama ya tambaye ta abun da take so, tsoron ta ta faɗa itama mummy ta taka mata burki, jin Deen ya ce sai ta faɗa masa abun da take so ta yi ƙarfin halin ce mashi waya iphone take so, aikuwa itama mummy ta daka mata tsawa ta ce, "Shi wayan naki da ya yi mi? ina ce samsung gare ki kuma waya ce mai kyau, ku wai mi yasa baku da tunani da lissafi ne, gaba ɗayan ku unnecessary abubuwa ne kuke faɗa, ce maku akai bashi da abun da zai yi da kuɗi ne ko kuwa injin buga kuɗi ne da shi, wahala yake yi kafin ya samu shima." Juyawa ta yi kan Deen ta ce, "Don't mind them son, ka rabu da su ba wani mai wani kwakkwaran buƙata." Yana murmushi calmly ya ce mata, "Aunty, wannan tsakanin ƴan'uwa ne, would you mind giving us some space?" Ɗan wara ido aunty ta yi jin abun da ya ce Dr ya saka dariya, jinjina kai aunty ta yi ta ce ta ji ɗin amman duk da haka bazata fita a maganan ba ta san duk unserious buƙatu za su faɗa, tambayar Nabeela ya yi sai mi take so tana murmushi ta ce mashi shike nan, ana zuwa kan Nabeel gaba ɗaya suka ga ya juya ta yadda ya ba mummy ɗin su baya yadda kar ma ya kalle ta ta hana shi faɗin buƙatar sa, sun fahimci mi hakan da ya yi ke nufi duk suka yi dariya, aunty Murja ta ce ya yi ya gama in dai ba wani abun kirki bane shima ba bari zata yi ba, abu na farko da ya ce yana so shine ya canza masa PS ɗin sa da ya lalace kuma an gyara amman yana ta bashi matsala Deen ya ce ok, ya ƙara tambayar sa sai mi, ya ce sai mashin mai caji, cikin ɗaga murya mummy ta ce, "Shi mashin ɗin naka da ya yi mi za a canza maka, ku ji fa don Allah! in ba son a yi almubazzaranci ba ga mashin naka lafiyan sa lau ka ce wai kana son a siya maka wani." Juyawa ya yi ya kalle ta a shagwabe ya ce, "Mummy to ai ba iri ɗaya bane ko wannan mai caji ne nike so." Tana hararansa ta ce, "Ina mai cajin da mara cajin duk buƙata ɗaya suke yi?" Tura baki ya yi ya ce to amman dai ai shi ne na yayi wanccan roba roban yanzu duk an daina ya yin shi." A ɗan harzuƙe ta ce, "Yayin banza, kuma ƙarya kake har yanzu an fi amfani da shi irin nakan, idan don ya yi ne shima electric ɗin yayin nasa zai wuce ne." A shagwabe yake faɗin shi dai shi yake so kuma duk friends ɗin sa yanzu duk irin shi gare su sai shi zata hana a siya mashi ba yaya Deen ɗin ne ya ce su faɗi komi suke so ba, shi dai Deen murmushi kawai yake, sai dai sun burge shi ta wani 6angaren yadda komai suka saka hankali a ciki, a wurin shi ba su faɗi wasu buƙatu da suka wuce kima ba amman duk da haka mummynsu sai da ta tsawatar masu, ba kamar yadda ta kasance a gidan su mom ɗin shi ba, wayar sa ya ɗauka ya fara daddanawa bada jimawa ba ya ɗago ya kalli aunty da murmushi ya ce mata ga saƙo nan ya tura a account ɗinta nasu ne ita da Dr, kallon Zarah ya yi ya ce mata za a kawo masu saƙon su zuwa gobe, ta ɗaga masa kai tana murmushi haka ma su Nabeela duk farin ciki ne akan fuskokin su, lokacin da aunty ta duba kuɗin da ya tura ɗagowa ta yi ta kalli Deen ta ɗan waro idanu ganin suna da yawa, da sauri ta ce, "No son, kuɗin nan sun yi yawa gaskiya, su ma kuma kada ka biye masu pls, hidindimun da yawa ai ba su kaɗai bane." Ya ce mata ba wani abu ai dama saboda su yake neman kuɗin kuma basu kaɗai ne ya yi mawa ba kada ta damu, ƙarshe sai dai suka yi masa godiya da addu'oi, daga haka ya yi masu sallama zai tafi, har aunty na ce mashi ya tsaya nan mana kawai ya kwana ya nuna mata akwai abubuwan da zai yi don gobe zai wuce Abuja. Gaba ɗayan su suka rako shi waje yana riƙe da hannun Nabeel da ya kasa rufe bakin sa saboda farin ciki, a bakin mota suka tsaya suna ƙara yin bankwana da shi aunty Murja na faɗin sai kuma Allah Ya sake ƙaddara saduwar su, su Zarah duk suka yi masa godiya, bayan ya shiga cikin mota ya kira Zarah ta je bakin motar tare da ɗan rankwafawa suna yin magana, bayan ɗan lokaci ta ɗago tana murmushi tare da ɗaga masa hannu tana masa bye bye, suna ta ɗaga masa hannu har aka ja motar suka tafi, daidai bakin gate suka ga motar ta tsaya da sauri mai gadin da ya buɗe gate ya nufi bayan mota in da Deen ya ke gilashin ya ɗan sauka, magana suka ɗan yi kafin maigadin ya ɗan ja baya, da alama godiya yake yi har yana ɗan rankwafawa, bayan gilashin ya ɗaga sama aka ja motar mai gadin na ta ɗaga masu hannu har suka fuce.... *_✨A CIKIN RAYUWA✨_* ZAINAB BATURE 35 Suna komawa cikin falo wayar Zarah dake riƙe a hannunta ta fara yin ringing, murmushi ne ya bayyana akan fuskarta ganin Deen ne ke kira, bayan ta ɗauka ta kai kunne tare da yin sallama, ɗan saurarawa ta yi can ta ce, "Kai yaya Deen kuma, ai da ka bar shi pls." Tana murmushi ta ce mashi sun gode Allah Ya ƙara ɗaukaka, cire wayar ta yi ta kalli mummy ɗin su da duk idanunsu na akan ta jin ta ambaci sunan Deen, murmushi ta shiga yi ba tare da ta ce komai ba, aunty Murja ta tambaye ta ya aka yi, ta ce wai kuɗi ne ya turo ta account ɗinta ya ce su raba da su Nabeela da Nabeel, mamaki ne ya bayyana kan fuskar aunty Murja ta ce kuma bayan saƙon da ya ce za a kawo gobe na su, zama ta yi kan kujera kusa da Dr tana yaba hali irin na Deen, ta ce, "Wallahi ina son yaron, akwai hankali da natsuwa, wasu idan suka samu ɗaukaka sai su guji nasu amman shi sam ba haka yake ba, burin shi a koda yaushe ya yi ma nashi har ma da wanda ba nashin ba. Allah ya ba yaya Ibrahim ɗa ɗaya tamkar da dubu." Dr Mustapha ya ce, "Ni abun da ya fi burge ni da shi natsuwar shi, sam ɗaukakarsa bata sa ya gur6ata rayuwar sa ba, duk da ba tare da shi muke ba amman da gani bana tunanin yana aikata wani abu ba daidai ba, kuma ina ganin yadda mutane ke yabon halinsa a social media." Aunty Murja ta ce ai gaskiya zata iya shaidar sa kan hakan, basu jima ba suka bar falon kowa ya nufi 6angarensa, saman gado Nabeela ta faɗa tana ta faman washe baki ta ce, "Nima dai zan yi iphone in huta da wulaƙancin da kike mani idan na ce ki bani aron naki in yi pics, ko idan zan je wani wuri na ce ki ara mani in je da shi don in yi pictures." Ƴar dariya Zarah ta yi ta ce itama ta huta da takura matan da take yi, "Gaskiya ya Deen yana da kirki, wallahi ba ƙaramin burge ni yake yi ba, ga kyau, ga kuɗi, ga ɗaukaka, ga kuma kirki duk shi kaɗai." Zarah ta faɗa tana murmushi bayan ta zauna a bakin gado, "Ni kin san mi ya fi burge ni a tattare da shi?" Nabeela ta faɗa, Zarah ta girgiza mata kai, "Wannan gashin na shi, da ni zai aura wllh har kitso zan rinƙa yi masa." Dariya Zarah ta yi ta ce, "Yanzu idan ya ce yana son ki zai aure ki zaki amince." Nabeela ta ce, "Da gudun tsiya ma, ke idan ya ce yana son ki ba zaki amince ba." Zarah ta ɗan rausayar da kai ta ce, "Zan amince mana, ai bana tunanin akwai wata mace da zai ce yana so ta ƙi amincewa wllh, dole a tattare da shi akwai abun da zai saka mace ta so shi." Tashi zaune Nabeela ta yi tana kallon Zarah ta ce, "Amman an ce ai yana da wadda zai aura ko?" Kai Zarah ta ɗaga, "Yea, cousin ɗin sa ce wadda yake zaune wurin su a London, kuma wllh baki ganta ba, ba zan ce bata da kyau ba amman don a can take ne, da ace anan ƙasar take to sam basu dace da juna ba nesa ba kusa ba." Shiru Nabeela ta dan yi don ita wallahi bata ƙi ya ce yana son ta ba to da sai ta aure shi, "Kina da pic ɗin ta?" Ta tambaya, Zarah ta ce mata da dai tana da amman yanzu babu, Nabeela ta ce, "Zan so in ganta, gaskiya ta dace." Zarah ta ce ta bari zata yi ma Leemarh magana ta tura masu, cike da zaƙuwa ta amsa da ok. Bayan Deen ya koma hotel shirin kwanciya ya yi don ba ƙaramar gajiya yake tattare da ita ba, bayan ya kwanta ya ɗauki wayarsa yana ɗan duba saƙonnin dake gare sa, bai yi mamakin ganin saƙon yabon tallafin da ya yi ba daga wurin mom ɗin sa, ya san saboda garinta ne, har da saƙon gaisuwa da Salma ta turo masa ta whatsApp ya yi mata reply ɗin godiya, bai jima ba ya ajiye wayan saboda baccin da yake ji. Washe gari kafin Deen ya bar Kano sai da ya siya ma su Zarah dukkanin abubuwan da suka ce suna so tare da shi aka kai gidansu lokacin ma duk basu nan, dama maganar kawo saƙon ce ya yi ma maigadi a jiya da zai bar gidan, shima maigadin sai da ya yi mashi kyautar kuɗi masu yawa da har sai da ya zubar da ƙwalla, kamar ba zai koma gidansu mom ba daga baya dai ya je ya yi masu sallama. Wuraren ƙarfe biyar ɗin yamma ya baro kano, lokacin da ya iso Abuja gaba ɗaya ƴan gidansu ne suka zo tarbarsa har da mom ɗin shi. A cikin kwanakin da suka rage Deen ya koma London sosai ya ba su Leemarh lokaci, a nan Abuja ma sai da aka ƙara yin wata gasar ƙwallon da shi. Ranar asabar da yamma sai ga Fahad ya yi masu zuwan bazata don yin bankwana da Deen da zai tafi washe gari lahadi, farin ciki sosai Leemarh ta yi har ta kasa 6oyewa, a 6angaren mom ɗinsu kuwa kamar dai ko yaushe babu yabo babu fallasa ta tarbe shi, koda ta ji cewa don ya yi bankwana da Deen ya zo har da cewa ai da ba sai ya zo ba in don wannan ne a waya ma za su iya yin bankwanar, shi dai bai biye ta ba dama har da gudun matsala ya sa shi bai zo da motar da Deen ya bashi ba, don ya san muddin ta ganta sai ta ɗarsa zargi a zuciyarta kuma sai ta bi diddiginta. A daren ranar Fahad da Deen da su Leemarh suka fita outing, zagaya gari suka yi suka je wurare daban daban cike da nishadi, har da haɗaɗɗu kuma tsadaddun wuraren sayar da kayan ƙwalam da maƙwalashe suka je suka siya abubuwa, daga baya suka wuce babban mall Deen ya ƙara yi masu shopping, har Fahad ma sai da ya siya masu abubuwa, sai wuraren goma na dare suka koma gida, bayan sun koma kowa part ɗinsa ya wuce ba wanda ya nemi abinci don duk a ƙoshe suke, Fahad tare da Deen suka wuce part ɗin sa kowa ya yi wanka, Leemah na zuwa part ɗinta itama wanka ta shiga, bayan ta fito ta shirya cikin doguwar rigar bacci, da ta gama shiryawa ta fito ta wuce kitchen, Fahad da Deen na zauna a cikin falonsa a saman kujera mai mazaunin mutum ukku, dukkan su kayan bacci ne a jikinsu Fahad riga da wando Deen kuma robe da ta bayyanar da faffaɗan chest ɗinsa, gaba ɗayansu sun ɗan kishingiɗa a saman kujeran idanuwansu akan tv suna kallon ƙwallo, jin an turo ƙofa ya sa a kusan tare suka kai idanuwansu direction ɗinta, Leemarh ce ta shigo ciki hannuwanta riƙe da ɗan tray a sama mugs ne tiriri na ɗan fitowa, nufo ciki ta yi idanunta akansu ta fara yin ɗan murmushi, tana zuwa kusa da su gyalen da ta ɗauro a saman kanta ya zame ta fara ƙoƙarin ganin bai faɗi ba, sai dai ta kasa tsayar da shi saboda abun da take riƙe da a hannunta, miƙewa Fahad ya yi ya tarbe mata gyalen kafin ya ƙarasa faɗuwa ƙasa, ɗagowa ya yi suka haɗa ido tana murmushi ta ce, "Thank you ya Fahad." Ya ɗaga mata kai, miƙa ma Deen da ke kallon su mug ɗaya ta yi ta ce, "Ya Deen ga coffee na haɗa maku." Amsa ya yi da murmushi akan face ɗinsa ya yi mata godiya, juyawa ta yi ta kalli Fahad da ke tsaye gabanta riƙe da gyalenta shima ta miƙa masa ɗayan mug ɗin ya ɗauka ya miƙa mata gyalen, tana ta murmushi ta ƙara yi masa godiya, komawa ya yi ya zauna tare da nuna mata gefensa alamar ta zauna, Deen da ya fara kur6ar coffee ɗin ya ɗan dakata yana murmushi ya ce, "Albarkacin Ya Fahad nima na samu coffee ɗin ke nan." Da sauri ta saka hannunta ɗaya ta ɗan rufe bakinta tana dariya, bayan ta cire ta ce, "No yaya Deen kawai na haɗo maku ne, kuma na san ai kana sha duk dare." Ya ɗage gira ya ce, "Amman ai baki haɗa mani." Cikin kame kai tana ɗan murmushi ta ce to ai bai saka ta ta haɗo mashi shi yake haɗawa ko ya saka chef Alima ta haɗa masa, Fahad da ke kallonta murmushi ne akan fuskarsa yana shan coffee ɗin, kallon shi ta yi suka haɗa ido duk kunya ta kama ta kan maganar da Deen ya yi, bayan ɗan lokaci aka kira Deen a waya ya ɗauka yana amsawa tare da miƙewa hannunsa riƙe da mug ɗin ya nufi hanyar bedroom ɗinsa, shiru na ɗan ƙalilan din lokaci bayan tafiyar Deen, Leemarh ta juya ta kalli Fahad da har lokacin bai ƙarasa shanye coffeen ba, janye idonsa ya yi daga kan tv ya maido su kanta suka haɗa ido, tana murmushi ta ce, "Ya Fahad dama ina son maka godiya.." Ɗan ɗage gira ya yi tare da janye mug ɗin daga bakinsa calmly ya ce, "Na mi?" Ta ce, "Na kayan da ka siya mana." Shiru ya ɗan yi yana kallonta kawai, can ya ce, "Kin yi ma Deen godiyan shima?" Da sauri ta girgiza masa kai alamar a'a, "Then why ni zaki yi mani." Shiru ta yi kawai tana ɗan murmushi don ya ɗaure ta, "Ko muna da bambanci ne ni da shi?" Da sauri ta girgiza masa kai, ɗan murmushi kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba. Mom ta tura kofar ɗakin Leemarh ta shiga tana sanye da kayan bacci, daga bakin ƙofar ta tsaya tana bin cikin ɗakin da kallo, ganin wayam bata ganta a ciki ba ta kai idanunta wurin da toilet yake, ciki ta ƙarasa shiga ta nufi kofar toilet ɗin ta ɗan dakata kafin ta kai hannu ta yi knocking, bayan ta ƙwanƙwasa kusan sau ukku ta tura kofar a hankali, nan ma wayam ta gani babu kowa a ciki, jawo kofar ta yi ta dawo cikin ɗakin ta nufi gaban dressing mirror, kayan shafan da Leemarh ta yi amfani da su mai da turare da roll on ta bi da kallo waɗanda da gani ba a daɗe da yin amfani da su ba, jim ta yi tare da ɗan ƙanƙance idanunta alamar tana tunanin wani abu a ranta, juyawa ta yi ta nufi ƙofa ta fita daga cikin ɗakin, fitowa ta yi cikin falon daidai lokacin chef Alima ta taho hannuwanta riƙe da tray mai ɗauke da warmers a sama da ta ɗauko daga dining area bayan basu umarnin su kwashe abincin da suka kai ƴan gidan ba za su ci ba, tana zuwa kusa da mom ta dakata cike da ladabi ta gaishe da ita, "Have u seen Leemarh?" Mom ta jefa mata tambaya ba tare da ta amsa mata gaisuwarta ba, da sauri ta ce mata eh ɗan ɗazu bada jimawa ba ta zo kitchen ta haɗa kofin coffee biyu, ɗan yamutsa fuska mom ta yi jin zargin da ya zo mata a rai ya tabbata, da hannu ta ba Alima umarnin tafiya ita kuma ta juya ta nufi bene, tuni Fahad ya gama shan coffee ɗin suna yin hira da Leemarh, har lokacin su biyu ne a cikin falon da alama Deen ya basu space ne shiya sa bai dawo ba, idan ka gan su yadda suke zaune zaka ce masoya ne a zahiri don sun yi matuƙar dacewa da juna, turo kofar da suka ji an yi ya sa a tare suka kai idanunsu wurin, Leemarh na ganin wadda ta shigo har sai da gabanta ya ɗan faɗi ta yi saurin gyara zamanta daga ɗan kishingiɗar da ta yi a saman doguwar kujerar da suke zaune tare da Fahad, shigowa ta ƙarasa yi cikin falon tana jefa masu wani irin kallo fuskarta babu yabo babu fallasa, daga ɗan nesa da su ta tsaya idonta akan su, cikin kama kai Leemarh da ke kallonta ta furta, "Mom..." Shiru bata amsa ba, Fahad ya ɗaga ido a hankali ya gaishe da ita, kaman baza ta amsa ba can ƙasan maƙoshi ta furta lafiya, "What are you doing here?" Ta jefa ma Leemarh tambayar tare da ƙara ɗaure fuska, da ɗan murmushi ta ce, "Ba komai, na kawo ma su yaya Deen coffee ne." Tana ɗan harararta ta ce, "Ina Deen ɗin a nan?" Leemarh ta ce, "Ya tafi bedroom amsa call." Wani kallo ta yi mata har zata juya sai kuma ta dakata ta sake cewa, "Ke baki da abun yi da kika zo ki ka yi zaune a nan?" Bin ta da kallo Leemarh ta yi sai kuma ta ɗan kalli Fahad da kansa ke a ƙasa yana latsa wayansa da ya ɗauka, ɗan ɗaure fuska Leemarh ta yi ta amsa mata da eh hira suke da yaya Fahad, ba tare da ta ce wani abu ba ta juya ta nufi bedroom ɗin Deen, shiru Leemarh ta yi tana kallon Fahad da har lokacin kansa ke a ƙasa, slowly ta kira sunan shi, "Yaya Fahad..." Ya ɗago idanunsa ya kalle ta ya ɗan sakar mata murmushi, ba da jimawa ba mom ta dawo ta nufi hanyar fita Leemarh ta bita da kallo, bayan ta kama handle ta juya da ɗan ɗaga murya ta ce, "To zaki kwana anan ne?" Ɗan tura baki Leemarh ta yi ta ce, "Bana jin bacci, zan taho idan muka gama hiran." Wani mugun kallo ta sakar mata kafin ta ce mata ta taso su tafi, yamutsa fuska Leemarh ta shiga yi alamar bata son tafiya, ɗan ɗago kai Fahad ya yi suka haɗa ido ya yi mata alamar ta je da kai, ba don ta so ba ta miƙe tana tura baki ta ce mashi sai da safe ya ɗaga mata kai, wani murmushi mom ta yi tare da ɗan jinjina kai alamun mamakin wato sai da Fahad ya ce ta tafi sannan, tana gaba mom ɗin na a baya tana yi tana waiwayenta, kana ganin fuskarta ka san bata ji daɗin tahowa ba, har abu ta sako a cikin aljihun rigar baccinta da ta siya ɗazun a mall take son bama Fahad ɗin, tana niyyar idan sun gama hira zata taho sai ta bashi gashi mom ta 6ata mata shirinta, har ɗaki mom ta bita, ta na shiga da sauri ta kai hannu zata rufe ƙofar ɗakinta mom ta bangaje kofar don ta fahimci mi take ƙoƙarin yi, shiga ta yi cikin ɗakin fuska a ɗaure Leemarh dake tsaye tana bin ta da kallo, "Wato Leemarh kin raina ni ko!" Mom ta faɗa a fusace, ɗan yarfa hannu ta yi fuska a yamutse ta ce, "To mi kuma na yi mom?" "Ban sani ba! Duk maganar da na yi maki akan Fahad baki ji ba ko?" Wani kallo mai tattare da mamaki Leemarh ta yi mata ta ce, "Yanzu mi na yi mom? Kawai fa coffee na kai masu har da yaya Deen, sannan na zauna muna hira, mi ye ne laifi a ciki?" Shiru mom ta ɗan yi tana ci gaba da kallonta cikin fushi, "Na gargaɗe ki akan idan ma soyayya kuke tun wuri ki datse ta baki ji ba ko?" Yarfa hannu ta yi ta ce, "Amman mom I have already told cewa ni ba soyayya nike da shi ba..." Ta katse ta, "To shisshige masa na miye?" Leemarh ta ce, "To shi ba ɗan uwana bane? Yadda yaya Deen yake a wuri na haka shima na ɗauke shi, miye laifi to don na shisshige masa." A harzuƙe mom ta ce, "Ke kaɗai ce yar'uwarsa? Ko su Omar suna masa haka ne." Leemarh ta ɗan ta6e baki ta ce, "Kowa da yadda ya ɗauke sa, ni na faɗa maki tamkar yaya Deen na haka na ɗauke sa, duk abun da zan yi ma yaya Deen shima zan masa." Ta ƙare tare da watsa hannuwa alamar gaskiyarta take faɗa, "To bana son wannan shisshige masan da kike, kuma as I warned u, idan ma kin san da wani abu na soyayya tsakanin ku ki yanke shi." Tana ƙarasawa ta juya ta nufi ƙofa Leemarh ta bita da kallo mai kaman na takaici har ta fice, jiki a sanyaye ta nufi bakin gadonta ta zauna, ji ta yi ranta duk ya jagule don ita dai ta san tana son yaya Fahad kuma burinta aure ya shiga tsakaninsu, zuciyarta ta shiga tunzurata kan ta faɗa masa tana son sa kawai, idan ya so maganar ta fasu kowa ya sani a family duk abun da zai faru ma ya faru, sai dai kuma wani 6angare na zuciyarta baya bata ƙwarin gwiwar yin hakan musamman tunanin kada Fahad ɗin ya ƙi kar6ar soyayyar tata, a hankali ta kai hannu cikin aljihun rigar ta, bin haɗaɗɗun chocolates ɗin da ta ɗauko a mall don ta bashi ta yi da kallo, a tunaninta idan ta bashi zai fahimci wani abu game da son shi da take yi saboda chocolates ɗin na ɗauke da kalmar love da hoton heart a jiki, kokonton ko ta bashi ta shiga yi, bayan wani lokaci ta ajiye su daga can bakin gado ta ƙarasa hayewa ta kwanta, zuba ma wuri guda ido ta yi a cikin ranta maganganun mom ɗinsu na dawo mata, mi ya sa mom ta tsani yaya Fahad sosai? ta san ba shi kaɗai take ma haka ba a familyn dad ɗinsu amman dai na shi ya fi yawa, mi ye aibun sa da zata ce bazata bari ta aure shi ba, ita dai a ganinta yaya Fahad bai da wani aibu, yana da duk qualities da za su saka mace ta so shi, gaskiya ita dai tana son shi sai dai komai zai faru ya faru...., haka ta yi ta tunane-tunane da yin tufka da warwara har bacci ya yi awon gaba da ita.... ✨A CIKIN RAYUWA✨ ZAINAB BATURE 36 Washegari kasantuwar ranar lahadi ne ba aiki, gaba ɗaya iyalin gidan bayan sun gama yin breakfast suka nufi backyard sports field ɗin gidan kowa yana sanye da kayan wasa, wasanni iri-iri suka yi cike da nishaɗi har da dad ɗinsu, mom ɗin su ce kawai bata wani saki jiki ta yi annushuwa ba, ba don komai ba sai don Fahad da ya kasance a wurin, wasanni irin su basketball, volleyball, badminton har da favourite wasan dad wato golb suka yi, gaba ɗaya duk Deen ya iya su sosai har shima Fahad, su Leemarh ma duk sun iya kasantuwar dama suna yi sun ƙware, ba ƙaramin kyau suka yi a cikin kayan wasannin ba, ba kamar Leemarh da ta saka jajayen tracksuit kanta ta saka jar sun cap irin hula mai kaman face cap mai buɗaɗɗan sama ta yadda gashinta ya bayyana ta ƙulle shi a baya, idan ka ganta zaka yi tunanin hausa bazata fito a bakinta ba, abun da ya ƙara ƙular da mom ɗinsu a wurin shine ganin yadda Leemarh da Fahad suke ɗaga ma junansu suna yin nasara, bayan wani lokaci dad ya sa chef Alima da sauran ƴan aiki da suna a wurin suna kallon wasannin aka kawo abubuwan ci da sha, sai bayan da lokacin sallar azahar ya gabato sannan suka tashi daga wasannin kowa yana cike da nishaɗi da annashuwa idan ka cire mom. Ko da suka zauna cin abincin rana bata zauna cikin su ba duk don saboda Fahad. Da daddare wuraren ƙarfe tara gaba ɗaya ahalin gidan suka rako Deen airport, Deen na tsaye sanye da jeans da T-shirt kan sa ya saka face cap, dad na kallonsa da murmushi ya ce, "Son, sai kuma yaushe za mu ƙara saka ran ganin ka anan ƙasar?" Deen na murmushi ya ce masa in sha Allah zai zo da ya samu lokaci, "Ya Deen pls kada ka ƙara daɗewa baka zo ba." Leemarh ta faɗa da sigar shagwaba ya ɗaga mata kai, kallon mom da ke sanye da abaya ruwan ƙasa mai shegen kyau ya yi yana murmushi ya ce, "Mom, I'm leaving, sai na ƙara zuwa." Itama murmushi ne akan fuskarta ta ce, "Allah Ya tsare hanya Ya ƙara kare mana kai, ka gaida su Sapnah." Ya amsa mata, kallon Fahad ya yi suka sakar ma juna murmushi ya miƙa masa hannu suka yi musabaha ya ce, "Ya Fahad sai wani lokaci." Fahad ya ce, "Ok, Allah Ya tsare sai mun yi magana." Kallon Omar ya yi ya ce masa sai ya shigo Cyprus ya amsa masa da ok tare da yi masa addu'ar Allah Ya tsare, daga haka ya saki hannun Sultan da Batool da yake riƙe da, Leemarh ta rumgume shi tana jin har ta fara kewar ɗan'uwan nata saboda ko zuwa suka yi London ba wani samun isasshen lokaci suke yi da shi ba in dai ba a lokacin hutun shi bane, bayan ya saki Leemarh ya nufi mom ɗinsa itama suka rungume juna, haka duk sai da suka rungume juna da mutanen wurin kafin ya nufi jirgin ƙungiyarsu da tuni ya hallara don ɗaukar sa har an shiga da kayan sa, suna ta kallon shi yayin da yake tunkarar jirgin cikin tafiyarsa mai cike da natsuwa, bayan ya kai matakalar ƙarshe ta shiga ciki ya juyo yana kallon su shi kan shi ya fara jin kewar su, ɗaga masu hannu ya yi a karon ƙarshe kafin ya juya ya shige, bayan ɗan lokaci ƙofar jirgin ta fara ɗagawa tana rufewa, akan idon su jirgin ya fara tafiya kan hanyar sa har ya tashi sama ƙoli ya tafi. Cike da jin kewar Deen suka nufi inda motocin su suke, dakatawa Fahad ya yi bayan sun ƙaraso idon shi akan dad da ke niyyar shiga mota ya yi mashi sallama cewa zai tafi, da yanayin mamaki dad ya ce, "Ba dai Funtua kake nufin zaka tafi ba a cikin daren nan? Kamar an kore ka son, mu je gida ka kwana idan Allah Ya kai mu ba sai ka yi asubanci ba in ma saboda aiki ne." Fahad na ɗan murmushi ya ce, "No daddy ba can zan tafi ba, akwai wani colleague ɗina a nan mun yi da shi zan je gidansa ne in kwana sai mu wuce Zaria da safe." Daddy ya jinjina kai alamar gamsuwa kafin ya ce, "Shi abokin aikin naka yana da iyali a nan ke nan?" Fahad ya ɗaga masa kai ya ce eh, "To kai sai yaushe zaka yi iyalin kai ma a rinƙa zuwa gidan ka?" Ɗan sunkuyar da kai Fahad ya yi yana dan murmushi ba tare da ya ce komai ba, mom ta shiga jifar sa da wani kallo mai kaman harara, daddy ya ce, "Yakamata dai ai niyya son, shekaru tafiya suke yi, kuma kana da aikin ka mai kyau to mi ake jira? Aure yana ƙara ma mutum natsuwa da kamala kuma shine cikar mutum. Ka ga shi ɗan'uwanka yana da mata da lokaci ya yi zai yi aure, amman kai ban ta6a jin an ce akwai wacce kake tare da ita ba da zaka aura, ko kuwa so kake mu yi maka auren dole?" Ɗagowa Fahad ya yi still da murmushi a nutse ya ce mashi in sha Allah zai yi, dad ya ce gara ya yi harama pls ko sun fara samun grandchildren, sosai kunya ta kama Fahad ya sunkuyar da kai ba tare da ya ce komai ba, sallama suka yi da sauran ƴan'uwan nasa har da mom da ta amsa a daƙile, Leemarh duk fuskarta ta nuna alamar rashin jin daɗi, ta so idan suka koma gida su yi hira da shi har ta bashi chocolates din da bata samu bashi ba jiya, bayan sun gama yin sallama da juna duk suka shiga cikin mota ban da Leemarh, matsawa ta yi gaban shi idanunta suka shiga cikin nasa, da alamun damuwa ta ce, "Yaya Fahad mi yasa baza ka koma gida ba sai ku haɗu da shi da safen?" Yana kallonta cikin ido ya ce mata sun riga sun gama magana da shi, ta ce ita dai bata ji daɗi ba da ba gidan su zai sake kwana ba, yanzu shima idan ya tafi sai an daɗe kafin su sake ganin shi, yadda ta ƙarasa maganar kamar zata yi kuka, calmly ya ce, "I'm sorry Leemarh, in sha Allah ba za a daɗe ba zan samu time in zo, hakan ya yi maki?" Ta ɗaga masa kai tana ɗan kikkafta idanu, tana niyyar sake yi mashi magana ta ji muryar mom ɗinsu a kausashe tana faɗin ita za su tsaya jira, sai da fa dad ya ce ta ƙyale su su gama magana amman ta ƙi bari, Fahad ya ce mata ta je sai su yi magana ta waya daga haka ta nufi mota ta shiga, sai da ya ga tafiyar su sannan shima ya shiga motar sa ya tafi, sai dai ba wani gidan abokinsa da zai je, kai tsaye daga nan hotel ya nufa, dama ya yanke Deen na tafiya kwanciyar hankalinsa kada ya koma gidan nan, hakan ya sa shi yanke zuwa hotel ya kama ɗaki. Bayan Fahad ya fito daga wanka a hotel room din da ya kama, shiryawa ya yi cikin kayan bacci ya buƙaci a kawo masa baƙin shayi kawai don sun ci abincin dare kafin su raka Deen airport, ba tare da bata lokaci ba aka yi knocking kofar dakin da yake ya mike ya je ya buɗe, black tea da ya buƙata ne aka kawo masa a cikin tea cup mai kyau saman saucer, daga gefe cokali ne a nade sai kuma sikari don ya sa yadda ransa ke so, amsa ya yi ya dawo ciki ya ɗaura a saman side drawer, abun ka da likita sai da ya je ya wanko cokalin duk da a naɗe yake kafin ya dawo ya yi amfani da shi, a nutse yake shan shayin yana kallon american movie a tv ɗin ɗakin, bayan ya gama ya wanko bakinsa ya dawo ya kashe kayan kallon, sai da ya kwanta sannan ya tuna da ya ce ma Leemarh za su yi magana, lokacin da kiransa ya shigo wayarta tana kwance a saman gado ta gama shirin kwanciya tana ta dakon kiran nasa har ta fara fidda ran zai kira, wani daɗi ta ji lokacin da kiran nasa ya shigo ta yi saurin miƙewa zaune kafin ta ɗaga, "Leemarh..." Ya kira sunanta jin ta yi shiru, a hankali ta ce, "Na'am ya Fahad." Ya sake cewa, "Ko har kin fara bacci?" Da sauri ta ce mashi a'a tana jira ne da ya ce za su yi magana, ya ce mata ok ta yi haƙuri ya ɗan shafa'a ne, ta ce, "Dama na yi tunanin haka da na ji shiru, kuma kamar in kira." Yana murmushi ya ce to mi ya sa bata kira ba, tana wasa da dogayen yatsunta ta ce, "Haka nan, kada in takura maka." Sigh ya yi ya ce, "Dama ɗan'uwa na takura ma ɗan'uwansa ne Leemarh?" Ta yi shiru tana murmushi, a hankali ta ce, "Yaushe zaka ƙara zuwa?" Ya ɗan yi shiru kafin ya ce mata zai sanar mata lokacin, tambayarta ya yi ba ta ce zata zo Funtua hutu ba ko ta fasa, ta ce, "Kana so in zo?" Ya bata amsa da sosai don an daɗe bata je ba, amsa ta bashi da zata zo suka ɗan yi shiru, can ta ce, "Yaya Fahad yaushe zaka yi auren? Na ji dad ɗazun ya yi maka magana ka ce masa zaka yi." Gyara kwanciyarsa ya yi yana murmushi ya ce mata bai san ya zai ce masa bane shine ya bashi amsar, "To ba zaka yi auren ba?" Ya ce, "No, zan yi in sha Allah, amman ba yanzu ba don bani da wadda zan auran." Muryata da alamun rashin yarda ta ce, "Kai yaya Fahad kai ne zaka ce baka da wadda zaka aura kuma na san ai kana da wanda kuke soyayya da su." Ya bata amsa da yin soyayya da mace ba shine ke nufin lalle ita ce mutum yake son aura ba, kuma shi bai ma 6ata lokacin shi kan hakan, ta ce, "Yanzu ke nan ba wadda kake son aura?" Ya yi ɗan jimm kafin ya ce, "Kamar akwai wata da nike jin hakan akan ta, amman kuma bata sani ba don ba komai tsakanin mu." Har sai da gaban Leemarh ya ɗan faɗi jin abun da ya ce, a ranta take raya ke nan ma yana da wadda yake son aura, "Leemarh are you there?" Fahad ya faɗa jin shiru kamar bata kan wayar, cikin ƙoƙarin daidaita natsuwarta ta ce mashi eh, tambayarta ya yi yanzu wace shawara zata bashi kan hakan, baiwar Allah duk ta daburce daga yanayin muryarta ya gane hakan, ta ce mashi kawai ya sanar da ita in dai ta yi mashi ta san ma bazata ƙi amincewa da hakan ba, Fahad ya ce, "Are you sure hakan yakamata in yi?" Farko shiru ta ɗan yi, murya a sanyaye ta ce masa eh, ya yi mata godiya ya ce zai jaraba yin hakan, daga haka bata sake cewa komai ba, daga baya ta ce mashi sai da safe zata kwanta gobe akwai school ya amsa mata da ok ya ce mata good nyt, da murmushi akan fuskarsa yake kallon screen ɗin wayar bayan ya cire daga kunnansa, kife fuskarta ta yi a saman gwiwowinta tana jin wani iri a cikin zuciyarta, yanzu shike nan burin ta na son auren yaya Fahad ba zai cika ba, hakan take rayawa a cikin zuciyarta, wani 6angare na zuciyarta ya shiga ƙarfafata cewa ai bai riga ya tsayar da waccan da ya ce matsayin wadda zai aura ba, tana da damar da zata iya cimma burinta, amman ta yaya? Ta raya hakan, zuciyarta ta shiga tunzurata kan kawai ta sanar masa abun da ke a cikin ranta, to amman idan kuma ya zamana shi bai son ta fa? Wata zuciyar ta raya mata ko don matsayin ta na yar'uwarsa zai iya amincewa da soyayyarta ya aure ta, sai dai ita kuma ta fi son a ce yana son ta kamar yadda take son shi su yi aure ba wai ya aure ta don tana yar'uwarsa ba kawai ba tare da akwai son ta a zuciyarsa ba, ƙarshe zuciyarta ta ci gaba da karfafa mata cewa lokaci bai ƙure ba zata iya saka mashi son ta a cikin ransa har ta cimma burinta, wayarta ta ɗauka ta tura masa saƙo cewa don Allah idan zai yuwu gobe da safe su haɗu, ta yi sending saƙon cike da fatan Allah ya sa bai yi bacci ba, bayan ɗan lokaci sai ga kiransa ya shigo, picking ta yi tare da yin sallama, bayan ya amsa ya tambaye ta lafiya dai ko take son su haɗu, ta ce mashi lafiya lau dama saƙo ne take son bashi, ɗan jim ya yi kamar yana yin nazari, ya tambayi a ina za su haɗu ta ce mashi ko in zai iya zuwa nan gida kafin su tafi school tun da ya ce da sassafe za su wuce Zaria, tambayarta lokacin da suke zuwa school ya yi ta faɗa masa, ya ce zai yuwu su haɗu a school din? ta ce, "Eh zaka iya shigowa, ko kuma in tsaya a wurin gate." Ya ce ok idan ba matsala su haɗu a bakin gate ɗin zai yi ƙoƙarin zuwa da wuri, ta ce, "Ok ya Fahad na gode, hope ban takura ka ba, ka ce da wuri zaku tafi." Ya ce mata no problem sai goben suka yi sallama, saƙe-saƙen yadda zata kasance tsakanin su goben ta shiga yi, a ranta take jin anya hakan da ta yi daidai ne, don kawai ta bashi chocolates zata saka shi ya zo alhalin ya shirya tafiya da sassafe, wata zuciyar ta ƙarfafe ta kan wannan ce damar ta ta fara cusa masa son ta a cikin rai don haka kada ta bari ta rasa ta, a haka bacci ya yi awon gaba da ita. Washe gari Leemarh bata iya tsayawa ta yi breakfast sosai ba, saboda ƙagarar da ta yi su haɗu da Fahad duk da a gefe guda tana jin fargaba a cikin ranta, ƙarfe bakwai daidai suka bar gida saboda makarantar ta su tana da ƴar tazara daga gidansu, sanin ranar monday ce dole za a samu cunkoson ababen hawa ya sa Fahad baro hotel ɗin da wuri, kai tsaye makarantar su ya nufa, su Leemarh na zuwa kusa da bakin gate ɗin makarantar ta ce ma driver ya ajiye ta a nan, da yake makarantar tasu babba ce motoci na shiga da ɗalibai, Batool ta kalle ta sanin ciki ake shiga da su ta ce mata miyasa zata sauka a nan, "Za a kawo mani wani saƙo ne, ku shiga yanzu nan da na amsa nima zan shigo." Ta faɗa tare da kai hannu ta buɗe ƙofar motar ta fita, da yake bakin gate ɗin akwai tarin motoci da ke ta shiga da fita hakan ya sa ba wanda hankalinsa ke a kanta har jami'an dake a bakin gate ɗin, tana tsaye can gefe guda tana ɗan waige-waigen hanya, ba a jima ba ta hango motar Fahad ta shigo titin ta ji wani sanyi a ranta, yana shigowa hanyar ya hango ta kasantuwar ita kaɗai ce a tsaye daga gefe, a gabanta ya yi parking glass ɗin gefen da take ya sauka ƙasa, haɗa ido suka yi da shi sai ta ga fuskarsa ta ƙara yi mata wani fresh, tambayarta ya yi ya fito ne ko za ta shigo, ɗan waigawa ta yi ta ga ba wanda hankalinsa ke a kanta ta kai hannu da sauri ta buɗe ƙofar gaban motan ta shiga, sanyi haɗe da daddaɗan ƙamshi ne suka karaɗe cikin motar, tana ɗan murmushi ta ce, "Good morning ya Fahad." Murmushin ya mayar mata ya ce, "Morning sis Leemarh, how was ur nyt." Ta amsa da Alhamdulillah, shiru ta ɗan yi ta kasa bashi saƙon da ta ce shi kuma yana ta kallonta alamar yana jiran saƙon, tambayarta ya yi Batool da Sultan ta ce an shiga da su cikin school ya ɗaga kai, kauda idonsa ya yi ya koma kallon gabansa ya lura kamar tana jin nauyin wani abu, kallonta ya ƙara yi for the second time ya ce, "Miye saƙon da zaki bada?" Cike da jin nauyi ta ɗago ƙatuwar school bag ɗinta mai kyau ta buɗe zip, kwaso chocolates ɗin ta yi gabanta na ɗan faɗuwa tana tsoron yadda zai reacting idan ya ga shine saƙon, bin abun cikin farin hannunta da ta miƙo mashi ya yi da kallo, ya ɗago idonsa da alamun rashin fahimta ya kalle ta, cikin ƴar rawar murya ta ce, "Dama wannan ne...tun da muka je mall na ɗauko nike son baka, ranan da daddare ban kai ga baka ba mom ta zo, jiya kuma ba a gida ka kwana ba." Da ƙyar ta ƙarasa maganar, sake kallon chocolates ɗin hannunta ya yi, a hankali ya ɗago hannunsa alamar ta bashi ta zuba mashi, bin su ya yi da kallo kana gani kasan masu tsada ne, ba komai ya fi jan hankalinsa ba face sunan da ke jikinsu wato LOVE tare da zanen red heart, lokaci guda ta ga ya yi ɗan murmushi tare da ɗago idanunsa ya kalle ta, yan kame-kame ta shiga yi tana ƙifce-ƙifcen idanu, da ɗan murmushi a fuskarsa slowly ya furta, "Thank you, I appreciate it" Har ta ji sanyi a ranta, ta yi ɗan murmushi sai kuma ta ce, "Ka yi haƙuri idan na 6ata maka lokaci." Still da murmushi ya ce, "No, you are important to me, so har fasa tafiya ina iya yi saboda buƙatan ki." Fuskarta har ta kasa 6oye yadda ta ji daɗin maganar, shima murmushi mai faɗi ya yi yana ci gaba da kallonta, "Ina colleague ɗin naka, ko ba yanzu zaku tafi ba?" Janye idanunsa ya yi daga kanta, haka nan ya ji baya son sake yin ƙarya kan hakan, juyawa ya yi suka haɗa ido calmly ya ce, "Ba wani colleague ɗina da zamu tafi tare, I have no option shi ya sa na faɗa ma dad haka." With confusion akan fuskar Leemarh ta ce, "To yaya Fahad ina ka kwana?" a hankali ya bata amsa da hotel, fuskarta ta bayyana yadda ta jinjina abun a ranta, cikin nuna ƴar damuwa ta ce, "Amman ya Fahad why zaka je hotel ka kwana kuma ga gida?" Shiru ya yi kawai ya ɗan shigar da lips ɗinsa, tana kallon shi ta ce, "Saboda mom ne ko?" Still bai yi magana ba, ɗan yamutsa fuska ta yi ganin mom na neman zame mata matsala, ta san saboda ita ne ya sa bai son zuwa gidansu tuntuni, wanda da yana zuwa tuni soyayya a tsakanin su ta ƙullu, "Ka yi haƙuri da duk abubuwan da mom ke yi maka yaya Fahad, wllh duk we are against it, ba kamar ni bana so cause you are important to me as well, shiyasa take yin faɗa da ni kan hakan." Cike da damuwa kamar zata yi kuka ta ƙarasa, idonsa akanta yana ɗan murmushi ya ce, "She is your mother ki daina yin faɗa da ita." Ta ɗan yarfa hannu muryarta na ɗan yin rawa ta ce, "To ai ni bana son abubuwan da take yi maka ne it hurts me." Ƙwalla ya gani sun cika idanunta, ta ɗan juyar da kai tana kokarin ganin basu zubo ba, "Leemarh..." Gently ya kira ta, ta amsa a hankali, "Look at me." Ta juyo suka haɗa ido, calmly ya ce, "Ki daina damuwa da hakan kin ji?" Ta ɗaga masa kai kafin ta ce, "To kai ma yaya Fahad pls ka daina damuwa da abubuwanta, haka halinta yake." Ya ɗan lumshe ido ya ce, "Na bari in sha Allah. I appreciate your concern for me, lovely sis." Murmushi ta saki tare da sauke idanunta, did he just call her lovely? Duk da ta san hakan ba wani abu bane zai iya zama yabo amman ta ji wani abu a ranta, muryarsa ta ji ya ce ta je kada ta yi latti sai sun yi magana, ta ɗago ta kalle shi ta ce to, har zata buɗe kofar ya sake cewa ya ga ai ana shiga ciki ko ta ce eh, ya ce bari ya shiga da ita daga haka ya tashi motan suka nufi cikin makarantar, bayan jami'ai dake bakin gate sun ɗan bincike shi, a babban wurin da ake tsayawa da motoci ya tsaya ya ɗan bi cikin makarantar wadda ta yi masa kyau sosai da kallo, juyowa ya yi suka kalli juna tana murmushi ta yi mashi godiya, ya ce bari ya bata kuɗi ta siya abu idan an yi break ta yi ƴar dariya ta ce ai su ba a basu kuɗin break duk a cikin kuɗin makaranta ake sakawa sai dai su je su ci duk abun da suke so, ya ɗan buɗe ido ya ce lalle su ƴan gata ne shi lokacin da suka yi school a nan Abuja shi da Deen da abinci suke tafiya, sallama suka yi ya ce sai sun yi magana ta amsa da to, har ta kama ƙofar sai kuma ta juyo ta kalle shi ta ce, "Allah Ya kiyaye hanya Ya tsare man kai yaya Fahad." Ya lumshe mata ido tare da amsawa da, "Ameen, take care." Ta ɗaga kai daga haka ta buɗe ta fita, ya ɗan bita da kallo ta cikin glass itama tana tafiya tana waiwayen shi..... ✨A CIKIN RAYUWA ZAINAB BATURE 37 Bayan Fahad ya baro makarantar su Leemarh ya hau hanyar tafiya Zaria, yana driving yayin da a zuciyarsa yake tunanin abubuwan da suka wakana tsakanin shi da Leemarh, yanzu ya tabbatar da yarinyar son shi take yi, dama kuma ya riga da ya fahimci hakan, wata zuciyar ta raya mashi yanzu ya ke nan zai yi? lokaci guda ya yanke a ransa cewa ba zai karya mata zuciya ba, matuƙar ta fito fili ta bayyana tana son shi kuma da aure zai amince da hakan, a da yana tunanin hakan ba mai yuwuwa bane saboda mom ɗinta, amman yanzu yana jin ya shirya ma duk wani ƙalubale da zai fuskanta daga gare ta matuƙar ba Leemarh ɗin ce ta janye ra'ayinta akansa ba, sai dai a yanzu ya yanke shawarar ba zai nuna mata ya gane komai ba zai fi su ci gaba da tafiya a yadda suke saboda now isn't the right time a ce soyayya ta shiga tsakaninsu musamman da bata kammala karatunta na secondary ba, sai dai idan ita ce ta fito ta bayyana masa tana son sa to bai da za6in da ya wuce ya yi accepting soyayyarta. A gajiye Salma ta shigo cikin gida bayan ta yi sallama, daga cikin ɗaki ta jiyo muryar innarsu can ƙasa tana amsa mata, ɗakin ta nufa ta ɗaga labule ta shiga, murmushi ta sakar ma innarsu da ta yunƙura ta tashi daga kwancen da take, a saman kujera Salma ta zauna ta ajiye ƙatuwar jakarta a saman hannun kujera, "Sannu da dawowa." Innarsu ta faɗa tana ɗan yin murmushi, Salma ta amsa da yauwa, tambayar su Imrana ta yi innarsu ta bata amsa da sun fita bayan sun ci abinci, "Ki je kema ki ci abinci sai ki huta ko." Salma ta amsa da to kafin ta ce, "Amman innarmu kaman wani abu na damun ki?" Ta tambaya cike da kulawa, ɗan murmushi ta yi ta ce mata a'a ba abun da ke damunta, Salma ta ce, "Ko dai baki son faɗa mani innarmu, gashi nan na ga alamun damuwa a tattare da ke. Ko baki jin daɗi?" Ɗan murmushi kawai innar ta yi, ta riga ta san matuƙar akwai abun da yake damunta to Salmar tana ganewa kamar yadda itama duk yadda Salma ta so 6oye mata abu a ranta sai ta gane saboda yadda suke bawa juna kulawa, "Don Allah innarmu ki faɗa mani mike damun ki, ko nima so kike in shiga damuwa ne." Salma ta faɗa har yanayin fuskarta ya sauya, sanin idan ba ta faɗa mata ba hankalinta ba zai kwanta ba ya sa ta ce, "Ba wani abu bane, amman dai ta wani 6angaren abu ne mara daɗi, dama bada jimawa ba muka gama yin waya da auntynki Kubrah shine take sanar mani cewa aurenta ya mutu." A ɗan zabure Salma ta kai hannu ta dafe ƙirji tare da ɗan waro idanunta, da ɗan ruɗani ta furta, "Wannan ne na ukku fa innarmu?" Cike da jimami innarsu ta ɗan girgiza kai, cikin raunin murya Salma ta ce, "Wai mi yasa ake mata haka don Allah, don kawai bata haihuwa? Ai ba ita ce zata ba kanta ba ko." Har idanunta sun kawo ruwa, innarsu ta gyaɗa kai ta ce, "Ku san dai wannan matsalar ita ce ke haddasa mata mutuwar aure, tun da ni dai a iya sanina Kubra bata da wani mummunan hali da zai sa a rinƙa rabuwa da ita, mutum ce mai tsananin kirki ga iya zama da mutane, tana da aikinta mai kyau da take biya ma kanta buƙatu bata damu da ta tsaya sai miji ya yi mata abu ba balle ya ga ta zamar masa jidali. Kawai dai kin san mutane kowa da irin kalar tunanin sa, kuma kowane bawa akwai ta inda Allah Ke jarabtar shi, ita kuma ta nan jarabawar tata take, sai dai mu taya ta da addu'a Allah Ya bata ikon cinye dukkan jarabawar da yake mata." Salma tana share hawaye ta amsa da Amin, rarrashinta innarsu ta yi kan ta daina kuka ta yi mata addu'a, bayan wani lokaci ta miƙe tare da ɗaukar jakarta zata fita innarsu na ƙara bata baki, dama ta san sai abun ya saka ta damuwa musamman yadda ta damu da auntyn tata. Dakinta ta nufa ta zauna a bakin gado tare da ajiye jakarta a ƙasa tana ci gaba da goge ƙwallan dake zubo mata, sosai take jin tausayin aunty Kubra kan rashin haihuwan da Allah bai bata ba wadda kusan ita ce ke haifar mata da matsala a gidajen aurenta, wayarta ta ji tana yin ringing ta miƙe ta nufi inda ta ajiye ta a cikin drawer ɗin mirror dama bada ita take zuwa makaranta ba, tana ɗauko ta ta ga aunty Kubran ce ke kira da alama ƙilan sun yi magana ne da innarsu yanzu, komawa ta yi ta zauna tare da ɗaukar kiran ta kara a kunne a hankali ta yi sallama, amsa mata aunty Kubra ta yi ta ce, "Baby an dawo school ɗin?" Ƙasa-ƙasa ta amsa mata da eh, "Ya na ji voice ɗin ki kamar kina a cikin damuwa, kamar ma kuka kike yi ko?" Ai kaman Salma tana jira ta yi mata tambayan ta saka mata kuka, da ɗan alamun tashin hankali ta shiga rarrashinta tana tambayarta mike damunta ta faɗa mata, cikin kuka ta ce yanzu bayan ta dawo innarsu ta sanar mata abun da ya faru da ita wllh bata ji daɗi ba, murmushi mai sauti aunty Kubra ta yi ta ce, "To kuma baby shine abun kuka sai ka ce yau aka fara ehem? Ki kwantar da hankalinki pls, ba wani abu, bawa baya wuce ƙaddararsa, ni wllh kin ganni sam ban damu ba, tabbas mutuwar aure bata da daɗi to amman idan Allah Ya ƙaddaro ma bawa ya zai yi? Sai haƙuri, ki taya ni da addu'a Allah Ya bani ikon cinye jarawabar hakan na fi buƙata kin ji baby?" Kai ta ɗaga cikin muryar kuka ta ce, "Koda yaushe ina maki addu'a auntynah, in sha Allahu in dai saboda haihuwa ne suke maki haka Allah zai baki, ƴan biyu biyu ma zaki rinƙa haihuwa." Dariya mai sauti aunty Kubra ta yi ta ce, "Na gode baby, amman ni wllh idan ma Allah bai ƙaddaro zan haihu ba na kar6i ƙaddarata hannu biyu, kuma sunan ban haihu bane amman tuni Allah Ya yi mani kyautar ƴa'ƴa a ciki kuma ya bani ɗiya ɗaya tamkar da dubu wato babynah farin cikin zuciyana." Murmushin jin daɗin kalamanta ne ya bayyana akan fuskar Salma, ta ce, "In sha Allahu ma zaki ƙara haiho wasu, ke ce ma zaki mani yar ƙanwa mace." Tana dariya ta ce, "To Amin, amman ni gaba ɗaya ma aure ya fita daga raina baby, ba za a ce dai ai ban yi ba ko, gaskiya na haƙura da sake yin aure, zan ci gaba da yin wasu ibadun, wadda muka yi ta aure kuma Allah Ya kar6a ya yafe mana kurakuranmu." Jikin Salma ne ya yi sanyi da jin kalamanta, tambayarta ta yi ko tana da wata buƙata, Salma ta ce, "A'a aunty Kubra, bani da wata buƙata, kuma kin manta yaya Deen har ya fara turo mani kuɗin albashin da ya ce zai riƙa bani." Aunty Kubra ta ce, "Wannan naki ne baby, kuma hakan ba zai hana mu sauke responsibilities din mu ba ai." Salma na ƴar dariya ta ce to ita ya zata rinƙa yi da waɗannan kuɗin masu yawa, aunty Kubra ta ce ita ta san mi zata yi da abun ta, cike da zolaya Salma ta ce to bari ta rinƙa tarawa sai a siya mata kayan ɗaki idan zata yi aure, dariya mai sauti aunty Kubra ta yi ta ce, "Baby ko dai aure kike so ne?" Da sauri ta ce, "A'a wllh auty Kubra ni wasa fa nike." Aunty Kubra ta ce, "In sha Allahu kayan ɗakin ma da kuɗin mu zamu yi maki su na gani na faɗa, fatan mu a koda yaushe Allah Ya baki miji na gari mai zuciya da zai kula da rayuwarki. Ko har an samu?" Da sauri ta sake ce mata a'a tana dariya, "Ina shi ɗan ball ɗin, kin fara karkato hankalinsa kan ki?" Ɗan waro ido Salma ta yi don ta gane Deen take magana, ta ce, "A'a, ni tun da ya tafi ma bai fi sau biyu muka yi magana ba shima ta chat, kuma tambayata kawai yake idan da wani abu kan aikin da ya saka ni." Aunty Kubra na ƴar dariya ta ce wasa take yi mata dama, hira suka ci gaba da yi kafin daga baya suka yi sallama aunty Kubra na jaddada mata kan kada ta sake ta saka damuwa a ranta. Maganar da suka yi da aunty Kubra kan Deen ta sa ta hawa facebook ta shiga page ɗinsa tana dubawa, ta ga bada daɗewa ba an yi posting hotunan match ɗin da suka yi a pre season shi da teammates ɗin shi, duk da kasancewar sauran da yawa duk fararen fata ne amman Deen ya fita daban a cikinsu, gaba ɗaya ya kere su kyau da ƙirar jiki, idan ka gan shi bazaka ta ba kawo wa wani abu ya haɗa shi da Najeriya ba balle ya kasance ɗan nan, yadda ya ƙulle gashin sa a tsakiyar kai wasu suka ɗan zubo daga gaban kansa ba ƙaramin kyau ya yi mata ba, a ranta take raya yanzu wannan ne zata iya jan hankalinsa wai ya so ta? To ta ina ma, mutumin da ta ga yadda mata ke rububinsa amman baya kula su har ana alaƙanta shi da sunan ɗan ƙwallo mai izza da jan aji, musamman yadda ta ji cewa shahararrun mata da duniya ta sani kama daga mawaƙa, yan film, models da sauran su ke yi masa tayin soyayyarsu amman sam baya da wata budurwa da yake tare da, kamar yadda yawanci shahararrun ƴan ƙwallo suke tarayya da fitattun mata, amma shi an ce sana'arsa kawai ya saka a gaba, sai dai kuma halin sa na ƙin kula matan na burge mutane da yawa musamman musulmai, ana masa kallon ɗan ƙwallo musulmi nagari mai kiyaye dokokin Allah. Ko zancen yana da matar da zai aura duniya bata sani ba sai ahalinsa kawai, ba irin ƙorafin da Basma bata yi masa kan yadda bai bayyanata ta hanyar ko da ɗaura hotunanta ne, idan har ka ga ya ɗaura hoton ta a social media to sai dai idan na family ne amman bai ta6a ɗaura ta ita kaɗai ba ko shi da ita balle har ya bayyana wacece ita ko mutane su zargi akwai wani abu a tsakaninsu. A hankali wata mota mai kyau ta ƙaraso bakin tangamemen gate ɗin gidan ta tsaya ba tare da an kashe motar ba, ƙofar side ɗin driver aka buɗe wani gajeran baƙin babban mutum mai ɗan jiki da tumbi, fuskarsa sai naso take a haka kuma daga yanayin motar ka san a Ac ya fito, zagayowa ya yi ɗayan 6angaren da sauri tumbinsa har ɗan rawa yake yi, buɗe ƙofar gaba ya yi fuskarsa da ɗan murmushi ya tsaya yana riƙe da kofar alamar wani zai fito, sai da aka ɗan ɗauki lokaci kafin aka zuro wata ƙafa waje wadda da gani ta mace ce fara fat da ita, ƙafar na maƙale da sarƙar ƙafa wadda da gani ta zinari ce, ƙafar na sanye da wasu matsiyatan takalma masu ɗan banzan tsini irin masu igiya da ake ɗaurewa, daga baya aka zuro da ɗayar ƙafar kafin mai ƙafafun ta ƙarasa fitowa, Ma sha Allah! wata kyakkyawar mata ce wadda koda mutane marasa cikakkar lafiyar idanu suka kalle ta sai sun shaida kyawunta, fara ce sol tana da kyawun fuska sosai, a yanayin halitta doguwa ce mai ɗan dogon wuya, sanye take da wata matsiyaciyar straight gown ta haɗaɗɗan lace da duwatsun jiki ke sakin wani irin kyalli, rigar ta bayyana dirinta wanda yake mai matuƙar ɗaukar hankali, daga wurin ƙugunta ya buɗe sosai yayin da cikinta yake a ɗame kai ka ce bata cin abinci, ƙirjinta a cike yake fam cleavage din ta a bayyane fatar wurin fara tass da ita, saman kanta ta soke ɗauri da ya zauna ɗas, walwatacciyar sumar kanta da ta fi kama da tata daga yanayin halittarta wadda take baƙa wuluk mai santsi ta zubo da ita ta gaba gefe guda, yayin da sauran ke a zube bayanta wanda tsawon sumar ya wuce kafaɗunta ta kawo har ƙirjinta, tun daga kan kunnanta zuwa wuyanta da sarƙar da ke a maƙale a ƙafarta guda da kuma nose ring da ke a maƙale a gefen hancinta, sai zobban dake a wasu yatsun hannun damanta da hagu gaba ɗaya duk zinari ne, sam babu mayafi a jikinta sai wata yar ƙumbulallar purse da take riƙe da wadda da gani mahaɗin takalman kafafunta ce, wani irin masifaffan ƙamshi take bazawa ta ko ina dai ta cika mace, sai dai a yanayin shigarta ba zaka iya tantance shin musulma ce ko kuwa ba musulma ba? Bayan ta fito ta kalli mutumin da ke a tsaye kamar an dasa shi da idanunta da suke farare tass da su masu kaifi, cikin salo kamar bata son yin magana ta furta, "Thank you." Washe baki ya yi ya ce, "No ai ni yakamata in yi godiya ranki ya daɗe." Wani mayen kallo mai tada tsigar jiki ta sakar masa, ganin tana niyyar tafiya ya yi saurin cewa, "Am..ranki ya daɗe baki bani phone number ɗin naki ba da kika ce zamu yi magana daga baya." Ɗan juya idanunta ta yi ta ce ok ta manta, buɗe purse ɗin hannunta ta yi ta fiddo da wayar ta latest iphone ta miƙa masa yatsun hannunta zara-zara masu ɗauke da zaƙo- zaƙon ƙumbuna dake shafe da jan farce kalar da ya hau da kayanta, da gani ta ƙara ƙumbunan kanti, ce mashi ta yi ya saka mata number ɗinsa, still baki a washe ya ce a'a ta bashi tata lambar ba sai ta yi wahalar kira ba, ta ce masa kada ya ji komai ya bata tashi lambar, amsar wayar ya yi wadda ita kanta ƙamshi take saki, bayan ya saka ya miƙa mata fuskarsa da ɗan alamun kokonton kiran nasa da ta ce zata yi ya ce,"pls ranki ya daɗe ki cika alkawari kada a shanya ni in ta jira koma a manta da ni." Wani ɗan murmushin gefe ta yi ta ce, "Kar ka damu." Ta yi maganar tare da ɗan ɗage gira, daga haka ta nufi gate ɗin tana taku tamkar wata tarwaɗa yayin da tsagar bayan rigarta ta kawo har kan layin bayan gwiwowinta, shi kuwa mutumin bin ta ya yi da wani mayen kallo tamkar zai lashe ta, tana tunkarar gate ɗin hannunta na latsa wayarta ba tare da 6ata lokaci ba ta shiga goge lambar da mutumin ya saka mata, a cikin ranta tana raya ya yi zaton ita ɗin haka take da arha, daga ya samu ta shiga motar sa ya kawo ta shike nan zai zira jiki, bai san ita tana da test a maza ba, ba kowa ne take iya yin hulɗa da shi ba, balle shi da gani ba wani wayayye bane can da suffarsa kamar wani bijimin sa, sannan da gani ba wasu shahararrun kuɗi ne da shi ba, kawai don bata son hawa taxi ya sa lokacin da ya yi mata tayin shiga motar bayan ta fito daga hotel ɗin da take ta amince har ya ɗauko ta, shi kuwa mutumin ya yi tsaye kamar gaula har sai da ya ga ta shige gidan da ya ajiye ta ta ƙaramar ƙofa sannan ya koma cikin mota a ransa yana mai fatar ta kira sa ɗin sannan haƙarsa kanta ta cim ma ruwa, lalle da ba ƙaramin morewa zai yi ba, ya ƙarasa tunanin tare da ɗan cije lebansa, tana shiga cikin gidan suka kusa yin karo da wani mutumi mai sanye da kayan jami'an tsaro da ke niyyar fita waje, ta ra6a ta gefensa zata wuce ba tare da ta ko kalle sa ba, da sauri ya dakatar da ita da cewa, "Sannu hajiya," Ta yi masa wani kallo ta furta, "Kai ma haka." Tana niyyar wucewa ya sake cewa, "Wa kike nema ne?" Dakatawa ta yi tana mashi wani kallon rashin arziƙi ta gefe, ɗage masa gira ta yi ta ce, "Dole sai na sanar da kai wurin wanda zan je?" Shi bai ma yi zaton zai ji hausa ta fito raɗam daga bakinta ba, ɗan murmushi ya yi tare da gyara tsayuwarsa ya ce, "Tabbas, don saboda haka ne aka ɗauke ni aiki ai." Ɗan yamutsa baki ta yi ta ce, "To kuwa sai dai shiga ta ta yi sanadiyyar korar ka daga aikin idan sai na sanar ma wurin wanda na zo." Ƙoƙarin wucewa ciki ta fara yi ya yi saurin shan gabanta ya ce, "Hajiya abun duk ba na faɗa bane, amman dole sai kin sanar mani wurin wa kika zo hakan aiki nane." Wani mugun kallo ta jefa masa, 6acin rai ya bayyana a saman fuskarta a fusace ta ce, "Zaka kauce daga gaba na ko sai ka ji tafin hannu na a saman kuncin ka!" Mamaki ne ya bayyana akan fuskar officer ɗin jin abun da ta ce wai shi za ta mara, wanda tun da yake aiki bai taba fuskantar irin wannan humiliation ɗin ba, ɗan jinjina kai ya yi da ɗan murmushi ya ce, "Mari kuma??" Ta ɗage gira ta ce, "Ko kana kokonton hakan ne?" Kafin ya bata amsa wani officer ya ƙaraso wurin daga cikin gidan, yana ganin matar ya washe baki ya ce, "Barka da zuwa ranki shi daɗe." Sauke idanunta ta yi a kansa fuskarta babu yabo babu fallasa ta amsa masa, ya ce, "Hajiya ki shiga mana." Ya faɗa yana nuna cikin gidan, tana kallon shi ta nuna ɗayan officer da ya dakatar da ita ta ce, "Wannan baƙo ne a nan?" Ya bata amsa da eh bai daɗe sosai da fara aiki ba, wani kallo ta yi masa ta ce, "Be careful, idan ba haka ba aikin ka zai su6uce maka a cikin sauƙi." Ta ɗan haɗe yatsunta ya yi sauti daga haka ta kaɗa kai ta nufi cikin gidan duk suka bita da kallo, juyowa ɗayan officer ɗin ya yi ya kalli abokin aikinsa ya ce, "Mi ka yi mata ne." Dan tabe baki ya yi ya ce, "Mi na yi mata kuwa, kawai don na ce sai ta sanar mani wurin wanda ta zo, shine har da cewa wai zata mare ni." Dariya wanccan ya saka ya ce, "To kai ma baka ga kamaninta da hajiyar gidan bane?" Ya ce, "To ko na gani ni dai ba aikina na yi ba, ko kuwa don tana kama da hajiya daga zuwanta sai kawai na ƙyale ta ta shiga bacin ba saninta na yi ba. Kawai don mutum na aiki a ƙarƙashin masu kuɗi ko mulki sai kowa nashi ma ya nemi taka shi." Wanccan da ke ƴar dariya ya ce to ya za su yi tun da ƙasar tasu ce, wajen gate ɗin suka fita suka zauna a wurin da suke zama, wanccan officer ɗin da maganar marin da aka ce za a yi masa ta tsaya masa a rai ya ce, "To su duk dangin hajiyar haka suke basu da mutunci?" Dariya ɗayan ya yi ya ce, "Wallahi kusan haka, ni dai duk wanda na sani suna zuwa gidan nan duk basu da mutunci." Tabe baki ya yi ya ce, "Allah Ya kyauta, koda yake abun ne ya yi masu yawa dole su rinƙa taka mutane yadda suka so, ga kyau ga kuɗi, yanzu ji dai wannan kamar ita ta yi kanta, saidai da gani ba tarbiyya, wannan shigar da ta yi wa zai ce musulma ce don Allah." Ɗayan ya ce, "Haka ne, itama hajiyar gidan baka ga yadda take ba masha Allah." Baƙon officer din ya sake cewa, "Yanzu ita wanccan ɗin budurwa ce ko bazawara?" Dariya ɗayan ya yi ya ce, "To wllh ban sani ba haka dai nike ganinta duk da tana daɗewa ma kafin ta zo, amman da gani ai ba sai an faɗa ba kasan ba matar aure bace, sai dai budurwa ce ko bazawara Allah masani. Ni in da zan samu waccan ai har aikina ina iya haƙura da shi wllh." Wani kallo baƙon officer ya yi masa kafin yay ƴar dariya ya ce, "To da wannan aikin naka ma waccan ba iya tarayya zata yi da kai ba balle kuma a ce baka da aikin." Gaba ɗaya suka saka dariya. Kai tsaye ta shiga cikin falon ta tsaya a tsakiya inda kujeru suke tana latsa wayarta, ta ɗan ɗauki lokaci a haka kafin wata ƴar matashiyar mace ta shigo cikin falon, hango baƙuwar da ke a cikin falon ya sa ta nufo ta, daga ɗan gabanta ta tsaya cikin hausarta da bata nuna ba sosai ta ce, "Sannu da zuwa ajiya." Tana ta latsa waya sai da ta gadama sannan ta ɗago kanta suka haɗa ido, "Ina matar gidan?" Ta tambaya a taƙaice, cikin girmamawa matashiyar ta ce mata tana part ɗinta lokacin baccin ta ne yanzu, wani kallo ta watsa mata jin abun da ta ce, cike da bada umarni ta ce, "Je ki taso man ita!" Tana niyyar juyawa ta nufi kujera ta ji matashiyar ta ce, "Sorry ajiya, ba a tada ta idan tana bacci." Cak baƙuwar ta dakata tare da juyowa ta ɗan ƙanƙance ido tana kallon matashiyar, ba tare da ta ankara ba ta ji ta ɗauke ta da wani wawan mari ta ce, "Ni kike faɗa ma haka don ubanki!" A gigice matashiyar ta saki ƙara tare da dafe kuncinta lokaci ɗaya jikinta ya fara yin rawa ta shiga ɗan ja da baya da gani marin ya shige ta sosai, ƙarar da chef Alima ta jiyo ya sa ta leƙowa cikin falon, tana hango su ta nufo ciki da sauri don ta ga alamun akwai matsala, tana ganin baƙuwar cike da girmamawa ta ce, "You are welcome hajiya." Maimakon ta amsa sai ta nuna matashiyar yarinyar ta ce wannan bata san ita wacece ba? Da sauri ta ce mata eh baƙuwa ce bata jima da fara aiki ba, kallon Alimar ta yi da ta ɗan russunar da kai gabanta duk da koda bata haife ta ba ta girme mata nesa ba kusa ba ta ce ta je ta tado mata matar gidan, ba musu ta ce mata to ta nufi hanyar part ɗin mom Jameela, duk da ta san ƙa'idarta ba a tada ta idan tana yin bacci amman ta za6i ta karya dokar tata akan ta karya ta baƙuwar don itama ta ta6a shan marinta, nufar kujera baƙuwar ta yi zata zauna hakan ya sa matashiyar juyawa zata wuce ciki har lokacin tana dafe da kuncinta ƙwalla na zubo mata, "Did I tell you to leave?!" Cikin yar tsawa baƙuwar ta yi magana, da sauri ta juyo murya na rawa ta ce, "Sorry hajia." Zama ta yi akan kujera ta ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya fararen ƙafafunta suka bayyana saboda tsagar rigar da ke da tsawo. Saida Alima ta yi knocking kusan sau biyar a ƙofar ɗakin mom Jameela sannan ta jiyo muryarta daga ciki a ɗan fusace tana tambayar waye ne? Cikin ɗaga murya ta ce, "Hajiya it's me Alima, kin yi baƙuwa ne." wani uban tsoki ta buga daga ciki ta ce ma Alima ta shigo, tura ƙofar ta yi ta tsaya daga bakin kofa tana yan kame kame kamar munafuka, mom da ta ɗago da fuskarta ta ɗaure ta tamau ta ce, "Ban hana idan ina yin bacci ba a tashe ni ko waye ya zo?" Cikin yar rawar murya Alima ta ce, "Pls sorry ma, ki gafarce ni, dama sis naki ne ta zo and she insists sai an tado ki, har ta mari Rashidat da ta ce mata ba a tada ki idan kina bacci." Alamun mamaki ne ya bayyana akan fuskar mom ta maimaita sis ɗinta, da sauri Alima ta ɗaga mata kai, shiru ta ɗan yi kafin ta ce mata ta je gata nan zuwa, da sauri ta ce, "Thank you ma.." Ta juyo ta futo daga ɗakin a ranta tana gode ma Allah da na hajiya bai yi zafi ba, bayan ta dawo cikin falon daga gefen kujeran da baƙuwar ke zaune ta tsaya cikin girmamawa ta ce mata ta ce tana zuwa, baƙuwar ta ɗan ɗaga mata kai kawai ba tare da ta kalle ta ba, tsaye Alima ta yi tana gudun tafiya ta yi laifi, sai da aka ɗan ɗauki lokaci sannan ta ɗan ɗaga mata hannu alamar ta je, godiya ta yi mata har za ta juya sai kuma ta dakata cikin ɗan rusunawa ta tambaye ta kalar lemun da za ta kawo mata don shima bata manta ba ta ta6a yi mata laifi akan lemun, kamar baza ta tanka ta ba tana ta pressing phone ɗinta, ƙasa ƙasa ta ji ta ce mata ta je idan tana buƙata za ta yi magana, Alima ta yi mata godiya kafin ta wuce tana ɗan yi ma Rashidat kallon tausayawa...... ✨A CIKIN RAYUWA ZAINAB BATURE 38 ....Mom Jameela na fitowa bakin part ɗinta idanunta suka sauka akan baƙuwar, ɗan guntun murmushin gefen fuska ta yi ganin wacce dama ta yi zaton zata gani daga bayanin da chef Alima ta yi mata, cikin falon ta nufo tana sanye da doguwar riga ta ɗaure gyalen ta a kai, bayan ta ƙaraso cikin falon, a kujerar kusa da ta baƙuwar ta zauna idon ta akan ta ta furta, "Nailah manyan gari, yau an shigo Abj ke nan?" Gira ta ɗaga mata idanunta akan wayarta, "Yau kika shigo ne?" Ta girgiza mata kai kafin a taƙaice ta ce, "Jiya." Idanun mom Jameela akanta ta ce, "Ok, ya su ammi, ko ba daga Kano kike ba?" Sai lokacin ta ɗago ta bata amsa da daga can take suna lafiya, "Wani abu kika zo yi, ko kuwa mu aka kawo ma ziyara." Mom Jameela ta faɗa da ɗan murmushi, slowly ta girgiza mata kai ta bata amsa da tayo rakiya ne, kallon Rashidat da har lokacin ke a tsaye mom ta yi sai kuma ta maido idanunta kan Nailah ta ce halan laifi ta yi, ta ɗage gira ta ce, "Ask her." Maida idonta ta yi kan Rashidat ta tambayi mi ta yi, cikin rawar murya ta faɗa mata, mom ta kalli Nailah still da ɗan murmushi ta ɗan yi ƙasa da murya ta ce, "Ki yi haƙuri baƙuwa ce bata san ki ba." Shiru kaman bata ji ta ba ta maida idanunta kan waya, saida mom ta sake mata magana sannan ta ɗan ɗaga hannu, mom ta ce ma Rashidat ta je ta kawo mata lemu da sauri ta amsa da, "Okey ma." Kitchen ta koma, lokacin da ta shiga chef Alima bata a ciki, sai da ta ɗan yi jimm bayan ta buɗe fridge tana tunanin lemun da zata kai gudun ta sake yin wani laifin, ƙarshe ta ɗauko babbar robar Fanta, a saman ɗan tray mai kyau ta ɗaura ta ɗauko glass cup mai kyau ta haɗa, bayan ta koma cikin falon, ɗan ƙaramin table dake a gefen kujerun ta ɗauko ta ɗaura tray ɗin, hannunta har ɗan rawa yake tana buɗewa, tsiyayawa ta yi a cikin kofin ya ɗan wuce rabin kofin sannan ta rufe robar ta ajiye, tsaye ta yi tana bin su da kallo ganin ba wanda ya bi ta kanta, a ɗan tsorace ta furta, "Ga lemun ajiya." Tamkar bada ita take ba, kallon Nailah mom Jameela ta yi ta ce mata ga lemu nan an zuba mata, sai da ta ɗan ɗauki lokaci kafin ta ɗago idanunta ta kalli cup ɗin lemun, hannu ta kai ta ɗauka kawai sai gani suka yi ta watsa shi a jikin Rashidat, wata irin firgita Rashidat ta yi saboda sanyin lemun, rawa jikinta ya shiga yi ta shiga ja da baya tana yarfewa, da sauri mom Jameela ta kalli Nailah ganin abun da ta aikata sai dai bata ce mata komai ba, "Daga yau ki riƙe ko ni wacece, sannan kada ki sake kawo mani lemu kalar ƴan ƙauye!" Baiwar Allah jikinta na kerma ta ɗaga mata kai, "Kuna da La casera a gidan?" Ta tambayi mom Jameela ta ce mata kaman akwai, kallon Rashidat ta yi ta ce mata akwai La casera ɗin ta ce mata eh, "Je ki kawo mata." Ta juya da sauri ta nufi kitchen tana ɗan yarfe hannuwa, without wasting time ta kawo mata lemun, tana niyyar buɗewa ta zuba mata a wani glass cup da ta ɗauko, hannu Nailah ta ɗaga mata alamar kada ta buɗe, Rashidat ta ja baya ta tsaya kanta a ƙasa, "You can go." Nailah ta faɗa bayan ta kai hannu ta ɗauki lemun, "Thank you ajiya." Rashidat ta faɗa tare da juyawa da sauri ta tafi, tana komawa cikin kitchen ta iske Alima ta dawo dama baya ta je, tana ganinta ta nufe ta da sauri tana zuwa gabanta ta fashe da kuka, "Rashidat, what happened?" Cikin kuka ta shiga fada mata abun da Naila ta yi mata, Alima ta ta6e baki tare da kai hannu ta dafa shoulder ɗinta ta yi ƙasa da muryarta ta ce, "Kada hakan ya dame ki, haka halinta ya ke bata da kirki, ni kaina ta ta6a mari na." Da alamun mamaki Rashidat ta maimaita ta mare ta, Alima ta tabbatar mata da abun da ta faɗa, "Shike nan don bamu da kuɗi sai mu zama abun wulaƙantawa? Kuma ba kyauta suke biyan mu ba aiki muke yi masu." Dan murmushi Alima ta yi ta ce mata kada hakan ya dame ta, ta ɗauka wurin neman halak dama sai an sha wahala. Bayan Nailah ta buɗe lemun, yar purse ɗinta da ke ajiye a saman hannun kujera ta dauko ta buɗe ta, wani abu ta ciro kaman sachet ɗin magani ta ballo guda biyu, marfin lemun da ta buɗe ta cire ta saka abun, maida marfin lemun ta yi ta tufe ta dauka tare da ɗan girgiza shi, aje lemun ta yi ta maida sachet ɗin cikin purse, bayan ɗan lokaci ta buɗe lemun ta fara sipping a nutse, duk abun nan mom Jameela na zaune tana bin ta da ido, juyawa Nailah ta yi ta kalle ta da wani shu'umin murmushi ta ce, "Ko zaki sha ne?" Da sauri mom Jameela ta ce, "Wa! wannan ai naku ne manya." Naila ta yi mata wani kallo ta ce, "Au haba? Ni zaki ma pretending, kin manta na san har da auren ki kina using na su, ko sai na tuna maki lokacin da na zauna wurin ki lokacin da kika haifi Deen a Funtua, a gabana kike komai, kin ɗauka bani da wayau ban san komai ba. Kuma na san tun lokacin ba bari kika yi ba." Ta ƙarasa tare da ɗage mata gira, mom Jameela ta wani tamke fuska, Nailah ta shiga sakin wani murmushin rainin wayou, cikin haɗe rai mom Jameela ta ce, "Wannan kina magana ne akan can baya ba yanzu ba, na bari since, so bana son kina kawo maganar." Nailah ta ɗan ta6e baki tana ci gaba da shan lemun ta tana wani juya ido, kauda ido mom ta yi zuciyarta na tuno mata da can baya lokacin da take amfani da irin drugs ɗin da ta koyi sha a lokacin da ta fara karatu a Buk, kauda tunanin ta yi ta kalli Naila dake ta sipping lemun and pressing her phone at the same time, tambayarta mom Jameela ta yi akawo mata abinci ta ɗan girgiza mata kai ta ce ta ci kafin ta fito, "A ina kika sauka ne?" a taƙaice ta bata amsa da "Transcorp..." mom Jameela ta ce, "Ke da waye kuka zo." Kamar baza ta bata amsa ba, ta ce, "Wani ne, baƙo ne daga ƙasar Ghana ya zo Kano muka haɗu ya buƙaci na rako sa nan." Aunty Jameela da ta bita da idanu sam bata yi mamakin jin namiji ta rako ba don duk sun san barikinta take bugawa a fili, ba kasafai ma ta cika zama a gida ba can Kano, mom Jameela da ke kallonta ta ce halan mai arziƙi ne mutumin shiyasa har ta amince ta biyo shi, wani bazawarin murmushi ta saki ta ce, "Wato ni ga lashe money ko, koda yake gaskiya ne, zan amince na biyo sa ne ba tare da kaya a hannunsa ba, yana da arziƙi kam tun da ko ɗaki da ya kama 2m per day" Mom Jameela ta ɗan jinjina kai ba tare da ta yi ja akan hakan ba don ta san a Transcorp hilton hotel har ɗakin da ya fi hakan kuɗi a rana ɗaya akwai, shiru ta ɗan yi wani abu na mata yawo a rai, cikin son tabbatarwa tana kallonta ta ce, "I thought ma da Alhaji Muhmud kuka zo kamar yadda kika saba, Allah Ya sa dai baku tare yanzu." Nailah ta ɗan buɗa ido sai kuma ta yi yar dariya ta ce, "Rabuwa kuma! Ni da babyn nawa, yadda nike ji da man ɗin nan ai ban iya rabuwa da shi, yana daga cikin mazan da suka iya tafiyar da ni yadda nike so." Da wani expression da ya bayyana yar damuwa akan fuskar mom Jameela ta ce, "Amman dai Nailah wllh abun da kike baki kyautawa, yakamata ki rinƙa tunani kuma ki yi hallaci, mutanen nan wani irin alkhairi ne basu yi mana ba a rayuwa? A lokacin da abbanmu ke aiki a gidansa ba irin alkharin da basa yi mana shi da matarsa, amman a ce ki rasa da wanda zaki yi tarayya sai mijinta, abun takaicin ma kuma ta sani, haba!" Dakatawa Nailah ta yi da shan lemun ta jefa mata wani kallo ta ce, "To miye laifi na anan don na so mijinta, ko kuwa don yana mijinta sai ya haramta in yi tarayya da shi taƙamar ta yi mana wani alkhairi, ina itama cin arziƙi take, don haka nima sai a bar ni in ci rabo na." Wannan karon da ƴar fusata mom Jameela ta ce, "Amman ai bata hanyar da ya dace kike yin soyayyar da shi ba, ya fi ma a ce auren shi kika yi da irin wannan tarayyar da kike yi da shi." Nailah ta yamutsa fuska ta ce, "Duk wannan abun saboda yana baban ƙawarki ne, farko ba auren nashi na so yi ba ita matar tashi ta nemi yi ma mutane iskanci, shine ai muka nuna mata ita jaririya ce a bangaren, ba a auri mijin nata ba tun da hakan take so, amman kuma tana ganin ana juya shi ba yadda ta iya. Next week ma zamu tafi Dubai da shi." Ta kai maganar tana juya fararen idanunta tare da sipping lemunta, baƙin ciki da takaici ne ya turnuƙe mom Jameela, ba tun yanzu ba ta tsani tarayyar su biyun, gashi yanzu arziƙin alhaji Muhmud din ya fi na da sosai, ba karamar hidima yake ma Nailah din ba don har ƙasar waje ya fitar da ita ta yi karatu, sannan dalilin ta sam yanzu bai damu da matarsa ba hajiya Aisha, baƙin ciki kawai take ƙunsa dalilin tarayyar da Nailah ke yi da mijinta, saboda wannan dalilin ne ya sa ƙawancenta da Sophie ɗiyar alhaji Mahmud tuni ya lalace, kuma bata ga laifin ta ba da ta daina alaƙa da ita don iyaye ba wasa bane, tuno irin alkhairan da suka yi masu ta shiga yi, Sophie mutum ce da har abada ba zata manta hallacin da ta yi mata ba a rayuwa kuma tana jin ta a ranta har yanzu, wanda yanzu ita Safiyyar tana a ƙasar Turkey inda ta yi karatu tana auren cousin ɗinta Lukman wanda ta zauna a gidan su, cikin tsananin 6acin rai mom Jameela ta ce, "Wallahi ki dai ji tsoron Allah Nailah, ki sani Allah baya bacci, aje a dawo watarana zai tona asirin abun da kika yi masa ne." Ɗan buɗa ido Nailah ta yi, da yanayin mamaki ta furta, "Wow! Dat's nice, aunty Jameela ke ce kike ce ma wani ya ji tsoron Allah!...hhhhh...to nima na ce Allah Ya tona ma kowa asirinsa and I dare you to say amin if you think ke ɗin you're a saint." Shiru mom Jameela ta yi tare da kawar da fuskarta gefe, Nailah ta tabe baki ta ci gaba da kur6ar lemunta, bayan ɗan lokaci ta miƙe mom Jameela ta maido idanunta kanta, "I need to use the bathroom." Kai kawai ta ɗaga mata, ta nufi hanyar part ɗin ta tana tafiya tana wani rausaya, mom Jameela ta bita da ido har ta shige, kauda idanunta ta yi ta bi wuri guda da kallo, tana sauraron zuciyarta da ke gargaɗinta kan Nailah, ta sani duk gidan su ba wanda ya kaita rashin kunya da iya rashin mutunci, so gara ta lalla6a ta su rabu lafiya. Bayan ta fito daga bathroom ɗin kai tsaye kitchen ta nufa, tun kafin ta shiga su chef Alima suka jiyo ƙamshin turarenta, kowannen su ya kai idon shi saitin ƙofa da sauri, daidai lokacin ta shigo ta tsaya daga bakin kitchen tana jifar su da kallon rashin arziƙi, duk suka shiga taitayin su, Alima ta nufo ta ta tsaya ɗan gefe da ita da ɗan murmushi ta yi mata sannu, ta tambayi ko tana buƙatar wani abu ne, tana yar yatsina ta ce mata suna da small chops? Chef Alima ta yi saurin cewa eh akwai tare da lissafo mata wanda ke akwai, ta faɗi wanda za a kawo mata falo tare da juyawa ta fita, Rashidat da tun bayan da ta shigo ta ƙame a wuri guda kamar wata soja ta ɗago bayan ta fita, chef Alima ta kalle ta tare da yin ƴar dariya ta ce, "Da alama kin tsorata da ita." Ta ɗan zaro ido ta ce, "Wllh sosai, da ta mare ni sai da na ga wani farin wuta fa...but she's beautiful." Alima ta jinjina kai tare da faɗin, "Very, very beautiful, ai duk ƴan familyn su suna da kyau gaskiya, amman duk kyaunta hajiya ta nan gidan tafi ta, kawai don ita wannan tana cikin ƴan matanci ne, ita kuma hajiya ta manyanta kuma ta haihu da yawa, but still kana gani ka san tafi wannan sis nata kyau." Rashidat ta ce, "Ni fa idanun hajiya ta nan gidan suna bani tsoro, suna yin kaman irin na matan da ke acting as snakes a movies, especially indian movies." Yar dariya Alima ta yi ta ce haka ne, itama shi ya sa da wuya ta kalli cikin idanunta, "Wai aunty Alima wannan ɗin duk nata ne?" Ta faɗa tana nuna saitin ƙugunta alamar tana nufin ƙugun Naila duk nata ne, Alima ta ce mata nata ne mana bata ga itama hajiyar gidan yadda take da su ba, Rashidat ta jinjina kai kafin ta ce, "Wasu in ka gan su sai ka ga kaman sune suka yi kan su wllh....Ah! tana jira a kai mata abu fa a falo..." Yadda ta ƙarasa maganar a zabure har sai da ya ba Alima dariya. "Yauwa gara da na tuna, ina son kuɗi ne." Nailah ta faɗa bayan ta ɗauko slice ɗin chocolate cake da fork ta kai baki, mom Jameela da ke kallonta ta ce, "Mi kuma zaki yi da kuɗi, ke da kika zo tare da alhaji mai arziƙi, na san ba ƙananun kuɗaɗe zaki samu a wurin sa ba." Bayan ta cinye cake din bakinta ta ce, "To kuɗi suna yin yawa ne? Ina da hidindimu da yawa da zan yi, kuma ina so idan muka je Dubai da baby zan yo siyayya, sannan ga iyalai na da nike son sallama kafin na tafi." Wani kallo mai kaman harara mom Jameela ta bita da shi, ta san da biyu don ta ƙunsa mata baƙin ciki ya sa ta kira Alhaji Mahmud da sunan baby, sharewa ta yi ta ce, "Wane iyalin gare ki? Na san dai ba su Ammi kike nufi ba." Tana wani murmushi ta ce, "Yea basu nike nufi ba, nima ina da nawa iyalin..." Shiru mom Jameela ta yi tana kallonta don ta fahimci inda maganar tata ta dosa, maganar kuɗin da take buƙata ta sake faɗa mata tare da adadin da za ta bata, mom ta ce, "Ni gaskiya yanzu bani da kuɗi har haka, ban daɗe da na ƙara gold ba." Wani kallon ban fahimce ki ba Nailah ta jefa mata ta ce, "Yanzu sai ya ke nan?" Ɗan jimm mom Jameela ta yi ta san muddin ba ta bata kuɗin ba baza a zauna lafiya ba, ƴar ajiyar zuciya ta yi ta ce, "Bari zan kira Sapnah mu ji ko zan samu a wurinta. Amman duka fa ba a daɗe ba da Deen ya je ya baku kuɗaɗe masu yawa almost 100m fa, kuma har da ke a ciki." Tana yatsina ta ce, "Lokacin da ya je ina gidan ne? Kema dai kin san idan kuɗi suka shiga hannun Ammi fitar su sai hali, sai da ma muka sayar da hali sannan na tsira da 5m kawai." Fuska a turbune mom Jameela ke kallonta, sam bata yi mamakin maganar da ta yi ta saida suka sayar da hali da Ammi ba, saboda rashin mutuncin nata har akan iyayen nasu, "Yanzu dai ke nike jira don't keep me waiting, daga Dubai ɗin ma ina tunanin zan wuce Uk." Da sauri mom Jameela ta ce, "Mi zaki je yi can?" Tana mata wani kallo ta ce, "Bangane mi zan je yi can ba? Ina da sis uwa ɗaya uba ɗaya, ga ɗiyarta wadda idan da kara kamar tawa take, sai kuma har ki ce mi zan je yi?" mom Jameela ta ɗan yi jim tana kallonta sai kuma ta ce, "Ni dai pls in dai kin san zuwa zaki yi ki hana mata kwanciyar hankali kada ki je." Ta ɗan tabe baki ta ce, "Ya ina son in je in ga muradin raina zaki wani ce kada in je." Ta ƙarasa tana wani yin dariyar rainin wayou, shiru mom Jameela ta yi kawai, Nailah ta sake cewa, "Har yanzu su daughter Leemarh suna school ne? Na ga rana ya yi." mom ta bata amsa da sai ƙarfe shidda suke dawowa suna yin har da islamiyya, "Dad ɗin su fa?" Ta bata amsa da shima bai dawo daga aiki ba, Nailah ta ce, "An daɗe ban gan shi ba, ranan kaman zan yi masa magana ta chat sai kuma wani abun ya ɗauke man hankali, may be ya dawo ina nan mu gaisa." mom Jameela ta gyaɗa kai kawai, bayan sun ƙara yin ƴar hira mom Jameela ta miƙe ta ce mata za ta ɗauko wayanta a bedroom, tana shiga ɗakinta ta maida ƙofar ta yi locking nata da makulli, nufar gadonta ta yi ta zauna tare da kai hannu ta ɗauko wayanta da ke a saman side drawer, bayan ta ɗan lallatsa ta kara a kunne, magana ta fara yi da dad ɗin su Leemarh ta tambayi yaushe zai dawo, on the other hand ya ce mata da la'asar, ta yi ɗan jimm don la'asar ɗin ta kusa, ta ce "Ok, amman pls bani son ka dawo gida yanzu, ko ka wuce guest house kawai." muryarsa da alamun mamaki ya tambaye ta lafiya da bata son ya dawo, ta bashi amsa da lafiya lau kawai wata baƙuwa ce ta yi bata son su haɗu, yar dariya mai sauti dad ya yi cike da zolaya ya ce, "Hala budurwa ce ko bazawara, baki son in ganta ko na sama maki abokiyar zama." Ta wani ɗaure fuska ta ce, "Da yake abun da ke a ranka ke nan ko, to ba wannan ne dalili ba, wata friend ɗina ce wadda mijinta ya rasu, kwanaki ba na baka labarinta har ta nemi in tallafa mata saboda an barta da marayu tana da yara ukku, wadda har na faɗa maka game da ita ka bada kudi na bata." Ya ɗan yi jimm alamar tunani kafin ya ce mata ya manta cause mutanen da yawa, ya tambayi yanzu to mi ya faru, ta ce, "Ita ce wai kuma ta zo tana neman wani tallafin, tana ta wani lissafo buƙatun yaranta sai ka ce basu da dangin uba, shine na ce mata ka yi tafiya." Ya ce, "Ok na fahimta, amman ai da an tallafa matan tun da ko ba komai friend ɗin ki ce, kuma kin san yadda nauyin kula da yara yake, sannan ba lallai idan dangin mahaifin nasu suna kulawa da su ba." Fuskarta a ɗaure ta ce, "Kai baka san irin mutanen ba, wani lokacin kawai rashin godiyan Allah ne da iya maula, kai da ka ganta ka san basu wani cikin hali tun da har aiki fa tana yi, yanzu da an ƙara tallafa mata to an sake bata daman da za ta ƙara dawowa ne." Ya ɗan sauke gajerar ajiyar zuciya ya ce ya fahimta tare da tambayar ta yanzu to har sai yaushe zai dawo gidan, ta ce zata kira sa a waya idan ta tafi, ya amsa da ok tun da hakan take so, cire wayar ta yi bayan sun gama, ta zuba ma wuri guda ido ta haɗe rai, ba wai tana zargin Nailah ɗin bane kan mijinta, kawai ta ji bata son ya dawo ya ga Nailah da wannan ƴar iskar shigar da ta yi, ko ita da take mace sai da shigar ta ɗauki hankalinta balle kuma namiji, a yadda yanzu duniyar ta lalace fitintinu suka yi yawa komai zai iya faruwa, ta ƙarasa tunaninta tare da ɗan girgiza kanta, kamar ta kira Sapnah ta sanar mata game da zuwan da Nailah ɗin ta ce zata yi Uk, sai kuma ta yi tunanin kada Nailah ɗin ta ji ta shiru, fasa kiran ta yi lokacin ta miƙe ta nufi kofa hannunta riƙe da wayarta...... *✨A CIKIN RAYUWA✨* ZAINAB BATURE HAPPY NEW YEAR 2026🎇 Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai. 39 Komawa falon mom Jameela ta yi ta zauna kan kujeran da ta tashi idanunta akan Nailah da ke yin waya, cikin ɗan haɗe rai ta furta, "Kawai sai in ta zama a hotel room kada na fito na sha iska?" Ɗan saurarawa ta yi kafin ta sake cewa, "Oh ke nan zargi kake wurin wani na je baka yarda da ina gidan sis ɗina ba." Ta ɗan yi shiru tana ƙara haɗe rai, can ta cire wayan tana faɗin, "Ka ji mani mutum da shegen kishin tsiya sai ka ce aure na yake, don ka zo da ni shike nan ban da ƴancin kaina, bai san ni ba haka nike ba, duk kuɗin namiji bai isa ya ce zai juya ni ba." Ta yi maganar tana pressing phone ɗin ta, ɗago kai ta yi ta kalli mom Jameela da ke tambayar ta ya aka yi ne, "Mutumin da na zo tare da shi ne, wai ya koma hotel din bai same ni ba shine zai wani tutsiye ni, har da wani wai akan mi zan fita ban sanar masa ba, sai ka ce irin ya biya sadaki na. Ni fa har da irin wannan abun ya sa har yanzu ko sha'awar aure bana yi, don bana jin zan iya tsayawa namiji ya rinƙa nuna mani iko." mom Jameela ta ɗan ta6e baki kafin ta tambaye ta ba shine ya kawo ta nan gidan ba ke nan, ta ce mata a'a, after some minutes sai ga kira ya shigo wayarta ta duba, ba tare da ta ɗauka ba ta ɗago ta kalli mom Jameela ta ce, "Shine ya zo ɗauka na." Miƙewa ta yi tana gyara rigarta, mom Jameela da itama ta miƙe tana kallonta da murmushi ta ce mata zata sake zuwa kafin ta bar garin, ta ce mata bata sani ba sai yadda ta kama, amman ko don ta ga su Leemarh za ta yi ƙoƙari ta dawo idan basu wuce ba, tare suka nufi hanyar barin falon, lokacin da suka fito motar mutumin da ya zo ɗaukar nata na a cikin harabar don yana sanar da su officer ita ya zo ɗauka suka bar shi ya shigo, bin motar mom Jameela ta yi da kallo wadda wata haɗaɗɗiyar baƙar jeep ce sai sheƙi take, gilashin motar tinted ne hakan ya sa ba a ganin wanda ke ciki, mom Jameela da ta ji tana son ganin mutumin, bayan sun tsaya daga gaban motar ta ce mata, "Baki yi masa magana mu gaisa." Ta furta ok tare da juyawa ta kai hannu ta ɗan ƙwanƙwasa glass, na gaban motar ne aka ɗan sauke, ta leƙa ta ɗan yi magana kafin ta juyo, ƙofar 6angaren driver aka buɗe mutumin ya fito, babban mutum ne don zai yi sa'an mijin mom Jameela koma ya ɗan ɗara shi shekaru kaɗan, kana ganinsa ka ga attajiri tun daga kan shigar da ya yi, ya sha manyan kayan farar shadda idan ka gansa kaman duka ke nan, tun daga kan hulansa da takalminsa da agogon hannunsa kana gani ka san za su yi tsada, mom Jameela na ta kallonsa a ranta tana raya, "Dube sa kaman na Allah..." Gefen Nailah ya tsaya da fara'a ya gaishe da mom Jameela ta amsa masa da ɗan murmushi, Nailah ta yi masa wani kallo kalan na waɗanda suka jiƙu da duniyanci ta furta, "Ko har yanzu ɗin baka yarda da inda na zo ba?" Ya wani bita da wani mayen kallo yana sakar mata murmushi ya ce, "Ai na yarda dama." Da yanayin hausarsa ba irin ta nan ba, ta ɗan jefa masa harara, ya yi ƴar dariya ya ce, "I'm sorry beauty, na koma room ne da muradin son in gan ki, sai na iske you weren’t there.", kuma bamu yi zaki je wani wuri ba." Ta ɗan ta6e baki kawai, mom Jameela ta ɗan kauda kai a ranta ta raya, "Yawancin maza dai duk munafukai ne, matarsa ko matansa na can Allah kaɗai ya san halin da suke ciki a gidansa." Ya sake ce mata, "Zamu iya tafiya? I have got a suprise for you when we get there." Ta ɗaga gira ta ce na minene, yana mata murmushi tamkar zai jawo ta jikinsa ya ce mata ta bari sai sun koma hotel zata gani, yadda yake mata magana ko kunyar mom Jameela baya ji, ko da yake Nailah ta riga ta bayyana masa daga wane irin kalan gida ta fito, kallon mom Jameela ta yi ta ce, "Aunty Jameela sai mun yi magana. Pls ki gaishe mani da su daughter Leemarh, ban ji daɗi da ban gan su ba." mom Jameela ta furta ok, sai kuma ta yi saurin cewa, "Yauwa na tuna, ina son baki saƙo wurin Aunty Shafa maganar ankon nan kada ta ɗauko da ni, don gaskiya bani da halin yin sa yanzu, ankon sun yi kuɗi almost 10m, ni kuma yanzu ba wani isassun kuɗi a wurina just last week na yi order kayan business ɗina as I told you." A kaikaice Nailah ta sakar mata wani kallon baki tsoron Allah aunty Jameela, sai kuma ta ɗan yi guntun murmushi ta furta, "To ki tambayi daddy mana, ba daɗi ace kowa zai yi ankon amman ban da ke." Ta ɗan yamutsa fuska ta ce, "Kawai na ga yakamata mutum na saka tunani, shine ya ƙara mani kuɗin da na yi order ɗin kayan, kuma yanzu sai in ƙara bijiro masa da wata buƙatar ai sai mutum ya ga ka raina ƙoƙarinsa. Ki bari kawai, I will see what I can do, idan kuma Allah Ya sa kayan sun iso kafin bikin na san zan samu ciniki sai in yi." Nailah ta gyaɗa kai da murmushi ta ce ok sai sun yi magana, duk abun nan alhajin na tsaye yana sauraran su, mom Jameela ta yi masa sallama yana murmushi ya yi mata godiya, har zata juya kuma sai ta tsaya ta ce ma Nailah ta manta ko lemu ba a kawo ma baƙon nata ba ko za su shigo, da sauri cikin fara'a ya ce mata no problem akwai lemu ma a cikin mota, daga haka ta nufi komawa ciki ya bita da ido, juyowa ya yi ya kalli Nailah ya ce gaskiya komai na su ya yi kama, ta ɗaga masa gira ta ce ita ce elder sis ɗin su. Bayan mom Jameela ta koma ciki, tana niyyar zama saman kujera ta ga Nailah ta shigo, fasa zaman ta yi ta nufe ta tana tambayar ta yi mantuwa ne? Dariya ce akan fuskar Nailah ta ce, "Wllh aunty Jameela kin fini bala'e wurin son kuɗi, you're the real lashe money, wato ke kina ganinsa har kin ga business." Itama dariya ce akan fuskarta ta ce, "Kin san ni ai bani wasa da dama ko kaɗan." Nailah ta ɗan girgiza kai ta ce, "To kin sayar, ya tura mani kuɗi a baki." Mom Jameela ta ɗan wara ido ta ce, "Are you serious?" Nailah ta ɗaga mata gira, "Har nawa?" Mom Jameela ta tambaya, Nailah ta ce, "Nawa kika ambata kuɗin ankon a gabansa." Ɗan jimm alamar tunani mom Jameela ta yi can ta ƙara wara ido da mamaki ta furta, "10m!" Nailah ta ɗaga mata gira, Mom Jameela ta ce, "Kai, da alama dai mutumin nan ba ƙaramin mai kuɗi bane, da na sani ma fin hakan na ambata." Nailah ta yi ƴar guntuwar dariya ta ce, "Saboda son kai ko, ke kaɗai kike son a tattare kuɗin a ba ke nan." mom Jameela ta sa dariya, Nailah ta sake cewa, "Kin ga yana jira na, ce masa na yi mantuwa na yi, dama don in zo in faɗa maki, sannan 50-50 za a yi, don haka zan turo maki 5m." Wani kallo mom Jameela ta yi mata, "Kamar ya 5m? Ba kin ce 10m ya bada a bani ba?" Nailah ta ɗage gira ta ce, "Yea, amman kin san ai bake kaɗai zaki samu kuɗin ba, tun da ni na kawo maki business ɗin dole nima na ɗauki share ɗina." mom Jameela ta 6ata fuska ta ce to amman tun da shi ita ya ba sai ta bata duka ita sai ta bata abun da ta yi niyya, Nailah ta ɗan girgiza mata kai ta ce dole yadda ta ce za a yi, idan kuma bata so shike nan zata yi amfani da duka kuɗin, sanin halinta ya sa mom Jameela ta ce, "Shike nan, amman dai ba maganar wanccan kuɗin da kika buƙata a wurina." Ta wani jefa mata kallo mai kaman harara ta ce, "No, wanda na buƙata daban, ina kuma jira. Idan kuma ya yi maki in riƙe 5m ɗin da zan turo maki ki ciko mani sauran, let me know." Daga haka ta juya ta nufi hanyar fita, mom Jameela ta bita da kallo, idan ka ganta zaka yi tunanin ta yi BBL ne yadda ƙugunta da mazaunanta suka fita sosai, amman kuma ba wani aikin hakan da aka ta6a yi mata, a cikin rai mom Jameela ta yanke kawai zata yi ma Sapna magana ta turo mata kuɗi sai ta cika mata ba sai ta amsa 5m ɗin ba, dama kawai ƙyashin ta fitar da kuɗinta ta ba Nailah ɗin take amman ba wani wai bata da kuɗi. Fahad zaune a falon daddynsa saman carpet yana rubutu a saman wasu takardu, ɗagowa ya yi ya miƙa ma daddynsa takardar da ya gama yin rubutun, alhaji Sa'ad dake zaune saman kujera idanunsa sanye da gilashi ya kar6i takardan yana dubawa, bayan ɗan lokaci ya ajiye ta a gefensa ya furta, "Komai ya yi daidai." Fahad ya jinjina kai, shiru suka yi na ɗan lokaci kafin alhaji Sa'ad ya yi ɗan gyaran murya ya fara magana, "Kwanaki can baya mun yi magana da kai kan yakamata ka fito da mata ka yi aure, ka ce zaka yi hakan, gashi yanzu almost a year da yin maganar amman shiru." Fahad ya ɗago suka haɗa ido da dad ɗin nasa, slowly ya maida kansa ƙasa, "Ka yi shiru." Daddyn ya sake faɗa, ba tare da Fahad ya ɗago ba ya ce, "Ban tsayar bane daddy." alhaji Sa'ad ya ce, "Why?" Still kansa na ƙasa ya ka sa bashi amsa, daddy ya ce, "Nasan dai ai baza ka ce babu ƴan matan da kake tare da su ba." Fahad ya amsa mashi da bai samu wadda yake son aura ba, alhaji Sa'ad ya ce, "Ke nan duk cikin ƴan matan naka babu wadda ta yi maka?" Shiru Fahad ya yi bai ce komai ba, daddy ya ce, "To ko mu mu nema maka matar auren ne, ko a cikin family ma za a iya samu." Fahad ya ɗan ɗago ya kalle sa ba tare da ya ce komai ba, daddy ya ci gaba da cewa, "Ga ƴar'uwarka Zarah ma, ko itama ina ganin lafiya lau kaman bata da matsala in zaku daidaita, dama gashi irin abun da ka karanta itama take karanta ka ga zaku taimaka ma juna sosai." Shiru Fahad ya yi har saida daddyn ya ce bai ce komai ba, dagowa ya yi ya ce, "Daddy ina bukatan a dan kara mani lokaci." daddy ya ce, "Itama Zarah bata yi maka ba ke nan?" Fahad ya ce, "No, akwai wadda nike shirin fitarwa, tana cikin karatu ne yanzu, amman nan da zuwa next year zata gama." Daddy ya ɗan jinjina kai kafin ya tambaye shi wacece ita? Fahad ya ce, "Itama a cikin family take, idan muka gama daidaitawa I will let you know." Daddy ya ɗan yi shiru kafin ya ce mashi yana ganin za su daidaita da itan, "In sha Allah, already mun fara fahimtar juna da ita." Da ɗan murmushi daddy ya ce, "Allah Ya tabbatar mana da alkhairi, nan da shekara mai zuwa ai kaman gobe ne idan muna da rabon gani. But, bana son jin wani uzuri kuma, idan ba haka ba zan yanke decision din dana ga ya yi akan ka." Fahad ya ɗan ɗago da ɗan murmushi ya ce in sha Allah za su ji abun da suke son ji, daga haka daddy ya sallame shi ya tafi. Mom Jameela zaune a dining area ita da su Leemarh da dad ɗinsu suna yin breakfast kasantuwar weekend ne, kowannen su ya yi shiga mai kyau don duk sai da suka yi wanka kafin suka zauna cin abinci, abinci kala kala gasu nan sai abun da mutum ke so zai ci, gaba ɗaya wurin ya karaɗe da aroma ɗin abinciccikan ga kuma ƙamshin da jikinsu ke saki, Leemarh ta kai chips baki, bayan ta gama ci ta ɗan dakata tare da ajiye fork ɗin tana kallon dad ɗinsu ta ce, "Dad next week zamu fara exam, muna gamawa zan tafi Funtua a can zan yi hutu." Kafin dad ɗin da ya kai tea cup baki ya ce wani abu mom Jameela ta yi saurin cinye abun da ke bakinta ta ce, "Na faɗa maki baza ki je ba!" Leemarh ta ɗan 6ata rai tare da tura baki, "But saboda me?" Dad ɗin su ya tambaya bayan ya ajiye tea cup ɗin hannunsa, "Kano zata tafi, su Ammi har sun yi magana." Dad ya bita da ido kawai, Leemarh tana tura baki ta ce, "Ni ba zan je can ba, kuma yawanci duk hutu ba Kanon nike zuwa ba." Dad ya ce, "Ki barta ta je Funtua ɗin tun da can take son zuwa, kuma suma za su ji daɗi tun da an daɗe ba wanda ya je a cikin su." Wani kallo ta yi masa ta ce, "Ita Ammin da har ta yi magana sai a ce mata ya ya ke nan? Ko sai a ce mata bazata je wurin su ba Funtua za ta tafi, kana tunanin hakan daidai ne?" Shiru dad ya yi tare da kallon Leemarh, ganin ya yi shiru ta san ƙarshenta goyon bayan mom ɗin zai yi ya sa ta fara yamutsa fuska tana faɗin ita wllh Funtua zata je ba Kano ba, mom ta yi mata wani kallo ta ce, "Sai ki je ɗin." Leemarh ta dangwarar da cokalin da take riƙe da, ta mike tana ƙunƙunin ita bazata je Kano ba ta nufi hanyar ɗakinta. Bayan barin Leemarh wurin, dad ɗinsu bai ce komai ba, amman a ransa ya bari zai lalla6a mom ɗin daga baya kan ta barta ta je Funtua. Leemarh na shiga ɗakinta ta nufi gado ta faɗa, ƙwalla ne suka ciko idanunta, a hankali suka fara gangaro mata, a fili ta shiga faɗin, "Ni wllh ba wani Kano ɗin da zan je, ko dama can da nike zuwa wani lokacin ba da son raina bane mom take matsa mani..." A cikin ranta ta shiga tuna maganar da ta yi ma Fahad na cewa zata je hutu can, yanzu kuma sai ta dawo ta ce mashi mi? Kuma ita dai har cikin ranta tana son zuwa can ɗin ko ba don kowa ba don shi, tunanin mafita ta shiga yi sanin halin mom ɗinsu idan bata son abu to kuwa ba a isa a yi ba, da sauri ta yunƙura ta tashi zaune bayan zuciyarta ta bata shawarar abun da ya kamata ta yi, ta ɗauki wayarta ta fara dannawa... Hajiyar ambasada na zaune a saman kujera, bata daɗe da fitowa ba bayan Balaraba ta gama gyara falon ko ina fes sai ƙamshi ke tashi, idanunta akan Tv tana kallon labaru, wayarta dake ajiye a gefenta ta fara ringing, kai idonta ta yi kan screen ɗin wayan, ɗan murmushi ne ya bayyana akan fuskarta ganin mai kiran nata, bayan ta ɗauka ta kara a kunne ta furta, "Assalamu alaikum, Haleematu." Daga ɗayan 6angaren Leemarh ta ce, "Na'am, hajiya ina kwana." Hajiya ta amsa mata da lafiya lau tare da tambayarta duk ya suke, Leemarh ta amsa mata da lafiya lau daga haka ta yi shiru, hajiya da ta fahimci kaman da wani abu ga shi ta ji muryarta can ciki ta ce, "Haleematu ya aka yi, lafiya dai ko?" Kaman tana jira cikin muryar kuka ta ce, "Ba mom ba ce..." Hajiya ta gyara zama don wannan ne karo na farko da ta kira ta da sunan kawo ƙorafin mom din nasu, "Ina ji, mi ya faru ne?" hajiya ta tambaya, bayan ta sanar mata ɗan murmushin dattako ne ya bayyana akan fuskar hajiya, cikin alamun rarrashi ta ce, "To ki yi haƙuri Haleematu tun da ta riga ta yanke can Kano zaki je, tun da ba gama karatun kika yi ba idan Allah Ya kaimu wani hutun sai ki taho nan, idan ma ni kike so sai in zo in taho da ke." Cikin ƙuna ƙuni Leemarh ta ce, "Ni dai bana son zuwa Kanon, kuma duk yawanci duk hutu ba can nike zuwa ba, yaushe rabon da mu zo nan, ni dai nan zan zo in ma ta ƙi bari na zan je car park in hawo mota ba tare da ta sani ba." Hajiya ta ɗan buɗa ido jin maganar Leemarh, sai kuma ta yi dariya ta ce, "Shike nan ki bari zan yi magana da iyayen naki, amman kada ki sake ki ce zaki baro gida ba tare da sanin su ba." Bayan sun ɗan ƙara yin magana suka yi sallama, hajiya ta ɗan kwa6e fuska tana kallon gabanta, dama ta riga ta san rashin zuwan su nan har da mom ɗinsu, shi kuma mahaifin nasu dama ta san ba wani tsawatar mata yake ba, ya riga ya sake mata tana yin duk abun da ta ga dama, duk da bata son shiga harkar iyalin yaran nata, ta ji dole ta yi magana tun da har ga furucin da Leemarh ta yi na tahowa ba tare da sanin su ba. Dad ɗinsu Deen na cikin cin abinci wayarsa dake ajiye gefe ta fara ringing, kai idanunsa ya yi kan screen ɗin, ganin hajiyarsa ce ke kira ya sa shi yin saurin ajiye fork ɗin hannunsa ya kai hannu ya ɗauki wayar, a nutse bayan ya ɗauka ya gaishe da ita kafin ya ce mata bari ya kira, mom da ta bisa da ido tun bayan da kiran ya shigo wayarsa ta janye idanun nata don ta gane wadda ke kiran nasa daga yanayin yadda ya amsa, bayan ya kira cikin girmamawa ya shiga gaishe da ita, shiru ya yi yana sauraranta kafin ya ce, "Nima na ce a barta ta zo tun da nan take son zuwa, to ita mom ɗin tasu ta ce sun riga sun yi magana da su can suna son ta je." Mom ta juya ta yi masa wani kallo don ta fahimci zancen Leemarh suke, ɗan ta6e baki ta yi ta ci gaba da cin abun gabanta, can dad ya ce, "Eh, gata nan." Cire wayar ya yi ya miƙa ma mom Jameela, ta wani kalle sa fuska a ɗan yamutse ta tambayi waye kamar irin bata san wanda ya kira ba, ya bata amsa da hajiya ce ke son magana da ita sannan ta amsa, da ɗan girmamawa ta gaishe da ita ta yi shiru tana sauraranta, yanayin fuskarta ne ya sauya ta ce, "Ba haka bane, Ammi ta riga ta buƙaci ta je masu hutu ne, yanzu idan kuma aka ce bazata je can ba ga inda zata je tana iya ganin ba a yi mata daidai ba kan abun da ta isa da shi." Daga ɗayan 6angaren hajiya ta ce, "Ni kuma Jameela ba zan ga an yi mani ba daidai ɗin ba? Yaushe rabon da yaran nan su zo nan? Yanzu kuma wata a cikin su ta nuna tana son zuwa nan sai a hana ta? Mi hakan ke nufi?" Da ɗan sauri mom ta ce, "No hajiya, ni fa ba ina nufin komai ba, kawai don ita Ammin da kanta ta riga ta buƙaci ta je can ne, idan aka yi wani hutun sai ta zo nan ai." Hajiya ta ce, "Tun da ta nuna nan take son ta zo kuma sun ɗauki lokaci basu zo ba, bari zan yi magana da Ammin na san zata fahimta." mom ta ɗan yi shiru jin abun da hajiya ta ce na zata yi magana da Amminsu, dama duk shirinta ne hakan ba wata Ammin da ta buƙaci Leemarh ta je hutu, hakan ya sa ta ɗan yi saurin cema hajiya shike nan Leemarh ɗin zata zo ita zata yi magana da Ammin, cikin haɗe rai ta ajiye wayar bayan sun gama, ta watsa ma dad wani kallo kafin ta miƙe ta bar wurin. Dakin Leemarh ta nufa, sai dai koda ta kai hannu zata tura ƙofar sai ta ji ta a kulle, dama tun da Leemarh ta ji hajiya ta ce zata yi magana da su ta rufe ƙofar sanin abun da zai iya biyo baya, buga kofar ta shiga yi tana ce ma Leemarh ta san tana jin ta ta buɗe ƙofar idan ba haka ba ranta sai ya 6aci, Leemarh dake kwance saman gadonta tana tura baki a ranta take faɗin Allah bazata buɗe ba, ƙarshe mom da ta gaji da knocking ta yi ƙwafa da ƙarfi ta furta, "Zamu haɗu ne!" Daga haka ta bar wurin, sosai ranta ya 6aci don bata ƙaunar Leemarh ta je Funtua don ta san har da saboda Fahad ya sa ta tsiri cewa zata je hutu can..... *✨A CIKIN RAYUWA✨* ZAINAB BATURE Page 40 Yau tun bayan da Salma ta dawo daga school tana kwance a ɗaki don da ciwon ciki ta dawo, dama ta saba duk zata yi period sai ta yi ciwon cikin, imnarsu na zaune daga gefenta bayan ta sa ta ɗan ci abinci ta bata magani, akai akai take yi ma Salma sannu, tana kwance jikinta sanye da doguwar rigar material kanta ba kallabi, gaba ɗaya mazan gidan lokacin sun tafi masallaci kasantuwar ranar juma'a ne. Innarsu na a ɗakin Salma har lokacin da yaran gidan suka dawo daga masallaci, kowa sai da ya shigo ya ƙara yi ma Salma sannu da jiki har da mahaifinsu, Sageer ne na ƙarshe da ya dawo, ɗakin ya shigo yana sanye da riga da wando na shadda, daga bakin gado ya tsaya yana kallon Salma dake kwance ya ce, "Sannu patient, ya jikin?" Kai ta ɗan ɗaga masa kawai kana ganin fuskarta ka san bata lafiya, ledar da ya shigo da ita ya miƙa ma innarsu ya ce, "Ga abun ciwo nan na kawo mata." Amsa ta yi tare da dubawa, kallon Sagir ta yi tana ɗan murmushi ta ce, "Yanzu ka rasa mi zaka kawo mata abun ciwon sai gyaɗa?" Yana ƴar dariya ya ce, "To innarmu ina laifi, ni da ma na damu da ita har na kawo mata gyaɗan." Still da murmushi akan fuskarta ta ce, "To ita dake fama da kanta ta ya zata iya wani zaman cin gyaɗa." Sageer ya ce sai ta rinƙa 6ara mata tana bata tun da dama jinyar ta take, innarsu ta ce, "In dai ka damu da ciwon nata kamata ya yi ai ka kawo mata ko kaza." Ya ɗan buɗe ido yana dariya ya ce, "Kaza innarmu, ni da nike fama da kaina, kuma ita yanzu ai ita ce hajiyar gidan nan, wake samun irin kuɗin da take samu." Innarsu ta ce amman dai kuɗin ai ba ita kaɗai ke cin su ba, kowa na amfana tun da duk cikin hidiman gida ake haɗawa, yana dariya ya kalli Salma ya ce, "Zaki ci kaza?" Bin shi ta yi da kallo da ɗan murmushi, Sageer ya ce tun da ta ƙi magana bata son ci, cikin muryarta da ta ɗan disashe ta ce mashi ƴan shilan da yake siyowa take so, ya ɗan harare ta ya ce, "Kina ciwon ma sai kin yi kwaɗayi, to ai yanzu ba su fara gasa su ba, sai ki bari sai bayan magrib." Kai ta ɗaga masa daidai lokacin ciwon cikin nata ya motsa ya cize baki tare da kai hannu ta dafe mara, da sauri innarsu ta shiga yi mata sannu tare da dafa ta, Sageer da fuskarsa ta ɗan canza alamar tausayi ya ce, "To wai innarmu shi wannan ciwon bashi da magani ne? A ce duk wata mutum sai ya yi ta wahala." Shiru innarsu ta ɗan yi kafin ta ce ana samun maganin da ke yi musamman na hausa anata jarabawa har Allah Ya sa a dace, Sageer ya gyaɗa kai ya ce Allah Ya sa a dace, bayan ɗan lokaci ciwon ya lafa ta lumshe ido. Bayan Sageer ya baro ɗakin Salma, kicin ya wuce ya ɗauko abincinsa kafin ya wuce ɗakinsu, cire rigar shaddar jikinsa ya yi ya zauna da vest ya fara cin abincin, bayan ya gama ya ƙarasa hayewa saman katifarsu yana yin chatting, can ya ɗan waro ido ganin Deen ya turo masa saƙo, hannunsa har rawa yake yi wurin saurin buɗewa, sakon juma'a da Sageer ɗin ya saba tura masa ne ya yi masa reply, daɗi ne ya kama Sageer don yawanci idan ya tura masa bai wuce ya yi masa react ba, wani lokacin ma sai an daɗe sannan zai buɗe saƙon kuma ba zai yi ko react ɗin ba, amman yau ya amsa saƙon, ganin yana online a lokacin ya sa Sageer saurin tura masa, "Yaya Deen ina wuni." almost a minute sai gashi ya buɗe saƙon, ya yi masa reply da, "Lpy Alhamdulillah." Ƙara waro ido Sageer ya yi tare da washe baki, saurin gyara zama ya yi irin abun na yi ne ɗin nan, saƙo Sageer ya tura masa na yabo kan kokarin da suke a gasan premier league da suke cikin yi, shima bayan ɗan lokaci ya yi masa reply din godiya, daga haka bai ƙara tura masa komai ba shima Deen ɗin bai ce masa komai ba, har Sageer ya fita daga chat ɗin nasu sai kuma ya ga ya sake tura masa saƙo, da sauri ya buɗe, "Where is Salmerh?" shine abun da ya turo, da sauri Sageer ya tura masa da, "Tana nan, bata ma lafiya tana can kwance ɗakinta." Ya buɗe saƙon amman bai ce masa komai ba, sai ga vedio call ɗinsa ya shigo, har saida Sageer ya ɗan zabura ganin abun da bai zata ba, da sauri ya shiga daidaita zaman sa, har da kai hannu ya ɗan goge fuskarsa kafin ya ɗauka, faffaɗan murmushi Sageer ya shiga saki bayan ya yi tozali da Deen dake a ɗan kishingiɗe saman kaman gado kaman kuma kujera yana sanye da baƙar t-shirt, sumarsa a sake a wuyansa, gaida shi Sageer ya sake yi, a nutse ya amsa mashi kafin ya tambaye shi mi yake damun Salmerh? Sageer ya faɗa mashi ciwon ciki take yi, tambayar ta je asibiti Deen ya yi, bakin Sageer da ba control ya ce mashi ai dama ta saba yin ciwon duk wata, bata zuwa asibiti sai dai ta sha magani, shiru Deen ya yi ba tare da ya ce komai ba, take kuma ya fahimci wane irin ciwo ne take yi, tambayarsa ya yi zai iya kai mata wayan don ya kira ta yanzu bata yi picking ba, da sauri Sageer ya ce, "Ƙilan wayan bata kusa da ita ne, don da ciwon ta dawo daga makaranta, dama bata zuwa da wayan school." Kai kawai Deen ya jinjina, da sauri Sageer ya shigo cikin gidan ya nufi ɗakinta, tuni ta samu bacci har innarsu ta bar ɗakin, nufar ta ya yi ya ɗan rankwafa yana tashin ta ta hanyar kiran sunanta, a hankali ta buɗe idanunta da suka ɗan sauya ta kalle shi, ɗan ɗaure fuska ta yi har zata fara yi masa ƙorafin tashinta da ya yi don baccin sauƙi ne a gare ta, kawai sai ya kanga mata wayar shi yana faɗin, "Ga yaya Deen yana son magana da ke." Wani faɗuwa gabanta ya yi lokacin da ta kalli screen ɗin suka haɗa ido da shi, satar kallon Sageer ta yi ganin haukan da ya yi mata, yana kallon a yadda take daga ita sai riga kanta a buɗe amman ya wani kanga mata waya, tashi ta yi ta zauna ta riƙe wayar Sageer ya juya ya tafi, ɗan murmushi ta shiga yi tana ƴan kame-kame, kanta an yi mata kitson gaba dama tun tana yarinya tana son shi, jelar kitson sun zubo mata a gefen fuska, "Yaya Deen ina wuni." Ta faɗa da disasshiyar muryarta, kai ya jinjina mata, suka yi shiru ta kasa tsayar da idanunta akansa, "Ya jikinki?" Ta ɗaga ido ta kalle shi ta ce, "Na samu sauƙi." suka ɗan ƙara yin shiru, "Mi yake damun ki ne?" Ta ji ya tambaya, ta bashi amsa da kanta ne yake ciwo tun a school, bin ta ya yi da kallo jin ta faɗi akasin abun da Sageer ya sanar da shi, daga yanayin da fuskarta ta nuna bayan ta faɗa mashi abun da yake damunta ya fahimci kunyar sanar da shi ainihin mi yake damun nata take yi, a karo na ukku da ya ji wani abu dangane da ita ya burge shi, na farko jijircewarta wurin sana'a, na biyu tausayinta kan abun da ya faru na Habu, yanzu kuma kunyar ta, wadda sam Basma bata da ita, ita duk idan period ɗin ta ya zo sai ya sani, haka zata yi ta mashi complaining ɗin ciwo duk da ba wani ma ciwon cikin take ba saboda mom ɗinta na kula da hakan matsayinta na likita, "Kin je hospital?" Ya tambaya, ta girgiza masa kai ta ce, "A'a, na sha magani na ji na samu sauƙi." Shiru ya ɗan yi kafin ya ce ok, sai kuma ya sake ce mata amman idan ta ji bai daina ciwon ba yakamata ta je asibiti ta ce masa to, "Where is ur phone?" Ta bashi amsa da tana cikin drawer ba da ita take zuwa school ba, kuma ta dawo da ciwo bata ɗauko ba, shiru suka ƙara yi, yana lura da yadda duk ta kasa sakewa, sai faman kai hannunta da ya sha zanen lalle take tana ɗan rufe gefen kitson gabanta alamun kunya, haka nan yau Deen yake jin komai na fuskarta na burge shi wanda a da da yake ganinta a zahiri bai jin hakan, hatta yadda kitson gabanta ya zuba ya ɗan rufe mata gefen fuska ya burge shi, duk ta ɗaga ido ta kalle shi sai ta ga ita yake ta kallo, can ta ce, "Na ga kuna yin gasan ko premier....Allah Ya bada sa'a." Ya yi ɗan murmushi tare da amsa mata da Amin, tambayarta ya yi tana kallon ƙwallo ke nan, da ɗan murmushi ta ce, "A'a da ban kallo, saboda kai ne na fara kalla, farko banma gane abubuwanta sai na tambayi yaya Sageer sai ya yi mani bayani." Yana ta kallonta tana yin maganar har ta gama, ya ɗan jinjina kai alamar ya fahimta, ta ji ya ce, "Thank you..." Murmushi kawai ta yi ba tare da ta ce komai ba, bayan ɗan shiru ta ji ya ce, "Ina faraa." Ƴar dariya ta yi saboda yadda ya faɗi sunan, ta ce, "Nama kwana biyu ban yi ba." Ya yi shiru bai ce komai ba idonsa akanta, ta ce, "Kana son ci ne?" Slowly ta ga ya ɗaga mata kai alamar eh, ta ce, "To ai ka yi nisa da na yi maka, in da kana Abuja ne sai in yi in bada saƙon mota a kawo maka." Dan murmushi ta ga ya yi sai kuma ta ji ya ce nan ma zata iya aiko mashi, Salma ta ɗan waro ido alamar mamaki ta ce, "Ana bada saƙo ta jirgi ne?" Ya ɗan ɗaga mata kai, shiru ta yi mamaki shimfiɗe akan fuskarta don ita dai bata taba sanin cewa ana bada saƙo ta jirgi ba kamar yadda ake yi ta mota, ba wannan ne ya fi ɗaure mata kai ba yadda zata bada saƙon fara ta jirgi, ita da ko airport ma bata ta6a zuwa ba, ko lokacin da tana wurin aunty Kubra da zata je makka gida aka maido ta, kasa daurewa ta yi ta ce, "Kuma har faran za a iya bada saƙon ta ta jirgi a kawo maka?" Shiru ya yi yana ɗan murmushi kaman ba zai ce komai ba ita kuma tana ta kallon shi alamar tana jiran amsa, ɗan gyara kishingidar sa ya yi calmly ya ce, "I don't know ko har shi za a iya bada saƙon shi, amman ina wasa ne, wani lokacin idan na zo sai ki yi mani." Ta ɗaga kai, shiru suka ɗan ƙara yi kafin ta ji ya ce, "Is there any problem?" Da sauri ta ɗan girgiza masa kai alamar a'a, ya ɗan yi shiru yana ta kallon ta ita kuma sai ɗan murmushi take yi tana sauke idonta, "Let me know if you need anything." Ta ji ya faɗa, ta sake girgiza masa kai, softly ya ce, "Mi yasa baki son faɗi mani?" Da sauri ta ce, "Allah da gaske nike yi bani buƙatan komai." Ya yi shiru yana kallonta, ita ce mutum ta farko da duk lokacin da zai tambayi idan tana da matsala ko tana buƙatan wani abu ta ke ce masa babu, ganin yadda yake kallonta ya sa ta yi tunanin ko bai yarda da abun da ta faɗa ba, tana kallonsa ta ce, "Ai kana bani albashi duk abun da nike so da su nike yin amfani." Kamar ba zai ce komai, sai kuma calmly ya ce, "But 50k a wata ba komai zai iya yi ba, and you also have your family to support" Ta ɗan langa6ar da kai tana ɗan faffaɗan murmushi ta ce duk 50k ɗin na isarta, wani kallo ta ga ya yi mata da sauri ta sa hannunta guda ta rufe rabin fuskarta, ya bita da kallo, sigh ya yi ya ce ya saka an tada ita tana bacci kuma ya san baccin relief ne a wurinta bari ya barta ta ƙara hutawa, tana kallon shi ta ce, "Yanzu na san sai bayan wani lokacin zamu ƙara magana." Ya ce, "Why do you say that?" ta ce, "Ba komai, kawai na ga kana zama busy sosai, ko saƙo na tura maka wani sai ya daɗe kafin ka duba." Kai ya ɗan ɗaga alamar haka ne kafin ya ce bai cika samun lokacin kan sa bane a irin wannan lokacin da suke yin gasanni sosai, ta ɗaga masa kai alamar ta fahimta, ta ji ya sake cewa, "I will send you another number, duk lokacin da kike son magana da ni ki yi amfani da shi, personal manager na ke kula da shi, I will tell him about you and he will help us get in touch when i'm available ." Ta jinjina masa kai sai kuma ta tambaye shi kira zata yi, ya ce duk yadda ta yi amman zai fi mata sauƙi ta kira whatsApp call ko ta sending masa message, idonta cikin nasa ta ce masa to, tambayarta ya yi shike nan ta yi saurin ɗaga masa kai ta ce, "Nagode, Allah Ya sa ku yi nasara." Ya ɗan lumshe ido tare da yin ɗan murmushi ya ce, "Amin thank you, Allah Ya baki lafiya." Ta amsa da Amin, ya ƙara cewa, "Take care." Ta ɗaga masa kai daga haka ya yanke kiran, Salma ta bi wayar da kallo bayan sun gama fuskarta da ɗan murmushi, bata yi tunanin zai iya kiranta vedio call ba kuma har su yi magana haka sosai, don tun da ya tafi ma basu yi magana ta kira ba sai dai ta chat, shima ba kowane sako in ta yi masa yake bata amsa ba wani lokacin sai daga baya, kuɗin albashinta dai da yake bata wannan da lokaci ya yi take ganin an turo mata ta account ɗinta, har tana tunanin kaman wani yasa yake tura mata, amman Sageer ya ce zai iya yuwuwa shine ya sa direct daga banki ake turo mata duk idan lokaci ya yi, ajiye wayar ta yi a gefe, har zata kwanta sai kuma ta sauko daga gadon tana tafiya a hankali ta nufi wurin dressing mirror, drawer ɗin farko ta buɗe ta saka hannu ta ciro wayarta, dawowa ta yi wurin gadon ta hau ta ta6a wayan ta kawo haske, bin saƙon da ta ga an turo mata a notification daga bankinta ta yi da kallo, hannu ta kai ta buɗe wayar ta shiga saƙon, lokaci guda ta zaro ido ganin kuɗi masu yawa da aka tura mata har miliyan ɗaya, kuma ta gane daga Deen ne don ta account ɗin da ake turo mata albashi ne, ɗan jimm ta yi tana ta kallon saƙon ƙirjinta har ɗan bugawa yake, tunanin mi yakamata ta yi ta shiga yi zuciyarta ta bata kawai ta kira shi ta yi masa godiya, sai dai ko da ta kira layin nashi baya shiga, whatsApp ta shiga ta kira sa voice call, har kiran ya ƙare ringing ba a ɗaga ba, kuma tana ganin kamar yana online don har ya turo mata lambar da ya ce ta nan, sake kiran sa voice call ta yi ta ga an katse kiran, kawai sai gani ta yi ya turo mata saƙo ya ce, "Just use it." Iya abun da ya rubuto mata ke nan, ta yi shiru tana ta kallon saƙon, ƙarshe ta tura masa saƙon godiya kafin ta miƙe ta nufi hanyar fita don ta je ta nuna ma innarsu. Har su Leemarh sun fara yin terminal exams din su, dad dinta ya sanar da ita da shi za su je Funtua bayan sun gama sai ya baro ta can ta yi hutu, ba ƙaramin farin ciki ta shiga ba, har ta kira Fahad ta sanar da shi, shima ya nuna jin daɗin hakan, ya kuma ce ta maida hankali sosai kan jarabawarta ta yi masa alƙawarin yin hakan. London. Galleliyar baƙar mota ce dake ta sheƙi ta ƙaraso bakin gate ɗin, nan take gate ɗin ya buɗe da kan shi kasantuwar automatic gate ne, cikin katafaren gidan motan ta kutsa kai. Katangar gidan bata rufe gidan gaba ɗaya ba, bangon bashi da tsawo ya kasance rabin katanga da aka yi da farin dutse mai sheƙi, daga sama kuma aka cike ta da ƙarafan alfarma masu launin baƙi da golden, waɗanda ke ƙyalli idan rana ta hasko su. Babban gate ɗin shiga gidan ya kasance na ƙarafa mai kyan gani, wanda aka ƙera jikin shi da salo na zamani. Kana shiga cikin harabar gidan iska zata busu maka ƙamshin furanni da aka k Ƙawata wurin da su cikin tsari mai matuƙar ƙayatarwa, hanyar da zata kai ka wurin harabar motoci ta kasance mai fadi, an yi ta da fararen duwatsu masu tsabta. A gefen dama akwai ƙaramin tsari na shuke-shuken ƙananun bishiyoyi da aka tsara cikin salo, yayin da gefen hagu kuma aka sa fitilu masu kyan gani. Ƙasan gidan gabaɗaya yana sakin sheki, an yi shi da farin dutse da gilashi, wanda yake ɗaukar hasken rana ya maida shi kamar wani ginin sarauta. Duk wanda ya tsaya a gaban ƙofar gidan ba sai an ce masa mai gidan attajiri bane don ginin da kansa ya nuna alfarma da darajar dake cikinsa. Kaitsaye gaban ginin gidan motar ta nufa ba parking space ba, tana tsayawa ƙofar 6angaren driver ta buɗe, wani gajeran baturen mutum ne ya fito jikinsa sanye da suit, da sauri ya zagayo ɗayan 6angaren motan, yana kokarin kai hannu ya buɗe ƙofar baya aka buɗe ƙofar daga ciki, fitowa ya yi jikinsa sanye da grey ɗin tom ford suit, ƙafafunsa na sanye cikin dakakkun rufaffun takalma, a fuskarsa ya rufe idanunsa da baƙin designer glasses, sosai ƙwarjininsa ya bayyana, kayan sun matuƙar amsar jikinsa kasancewarsa mutum mai matsakaicin tsawo da kuma ɗan kaurin jiki wanda da gani yana motsa jiki, ta cikin gilashin fuskarsa ya kalli mutumin da ya yi niyyar buɗe masa kofar, da ɗan murmushi ya furta, "Thank you, James." Mutumin ya ɗan rankwafar da kai, kai tsaye Maleek ya nufi gidan, a nutse ya fara tattaka steps ɗin da za su sada ka da ƙofar shiga, bayan ya isa gaban kofar wadda take mai matuƙar kyau da tsari, ɗan tsayawa ya yi yana fuskantar ta, after few seconds ta yi wata ƴar ƙara tare da sakin ɗan jan haske ta wani wuri mai kaman na'ura, ƙofar na ɗauke ne da na'urar tsaro mai tantance fuska (Facial recognition security system). Cikin falon gidan ya shigo wanda yake tsit ba kowa a ciki sai na'urori dake aiki, kuma yana shigowa fitilun cikin falon suka kawo haske wanda a da ba wadataccen haske a falon, hanyar da zata kai shi 6angarensa da ke a nan ƙasa ya nufa, wata gajerar baturiyar mata ce ta fito ta wani 6angare ta shigo cikin falon, tana ganin Maleek ta fara sakin murmushi tare da nufar sa, bayan ta iso daga ɗan gaban sa ya dakata, cikin fara'a da girmamawa ta ce, "Oh, sir welcome back...." Maleek ya jinjina mata kai tare da furta, "Thank you mrs. Helen." Still da fara'a a fuskarta ta ci gaba da cewa, "....The security system triggered an alert, i was in the kitchen so i came out to check." Ya yi ɗan faffaɗan murmushi ya ce mata,"Thank you mrs Helen. I appreciate your attentiveness." Ta jinjina kai tana murmushi, tambayarta ya yi akwai wani matsala ta ce masa a'a, daga haka ya wuce, ita kuma ta juya zata koma kitchen, taku biyu zuwa ukku ya yi ya dakata tare da kai idanunsa kan Helen da har ta fara tafiya ya ce, "Has my love returned home?" Yana tambayar ko Sapna ta dawo, Helen da ta dakata ta bashi amsa da, "No Sir, but Basma is back." Maimaita sunan Basma da ta ce mashi ta dawo ya yi kafin ya ce ok daga haka ya ci gaba da tafiya, ya ɗan yi mamakin jin Basma ɗin ta dawo, kasantuwar ranar asabar ne da kanshi ya ajiye ta a makarantar islamiyya, da yake duk weekend baya daɗewa a wurin aiki, da safe idan zai tafi yake tafiya da ita ya yi dropping nata, ƙarfe biyu ake tashin su shima kuma bai wuce lokacin sai ya je ya ɗauko ta su dawo gida, gaba ɗaya sauran wunin ranar za su kasance a tare a can hawan bene na ƙarshe su huta tare da yin abubuwan nishaɗi, wani lokacin kuma bayan gidan suke tafiya inda ke da swimming pool da liluna, akwai madaidaicin garden mai ɗauke da shuke-shuke masu tsari, sannan kuma akwai sports field inda suke yin wasannin motsa jiki, itama Sapna duk asabar bata daɗewa a wurin aiki, wani lokacin idan ya ɗauko Basma suke biyawa su ɗauko ta, wani lokacin kuma idan ta gama aiki da wuri tana rigan su dawowa, ko kuma su riga ta dawowa idan bata gama aikinta ba ranar lahadi kuwa gaba ɗaya shi da Sapna ɗin basu zuwa wurin aiki sai in abu na gaggawa ne ya taso da ke buƙatar dole su je, sanin cewa dama wani lokacin Basmar tana dawowa kafin lokacin tashin su daga islamiyya ta ce ko bata jin daɗi ko kuma wani uzurin, hakan ya sa shi yin tunanin yanzu ɗin ma wataƙila wani uzurin ne ya sa ta dawo. Kai tsaye 6angarensa ya nufa ya shige, ya dauki wasu mintuna masu ɗan tsayi kafin ya fito hannuwansa riƙe da wasu files yana tafiya yana duba su, dama abun da ya zo ɗauka ke nan don lokacin tasowarsa bai yi ba duka lokacin ƙarfe sha ɗaya da wasu mintuna na safiya, yana shigowa cikin falon ya yi tunanin zuwa ya duba Basma don ya ga ko lafiya ta dawo, saboda bai son ya 6ata lokaci kaitsaye daga wayarsa ya buƙaci elevator ya sauko, shiga ya yi ya nufi saman benen da shi, bayan ya tsaya ya fito ya nufi 6angaren da ɗakin Basma yake, yana zuwa bakin ƙofar ya cire glasses ɗin fuskarsa tare da kama handle ɗin zai buɗe ya ji ƙofar a rufe take, har zai yi knocking sai kuma ya fasa ya ɗaura babban yatsansa jikin wani ɗan wuri dake a hannun ƙofar nan take ƙofar ta buɗe, a nutse ya saka kai cikin ɗakin fuskarsa da ɗan murmushi, lokaci guda Maleek ya tsaya cak kamar an latsa masa pause, nan take murmushin fuskarsa ya gushe tamkar bai wanzu ba, zaro idanu ya yi cike da razani nan take hannunsa ya fara yin rawa bai san lokacin da ya saki files da glasses ɗin hannunsa ba, da wata irin muryar kiɗimar abun da idanunsa ke gane masa ya furta, "BASMA....!" Kai tsaye kiran ya daki dodon kunnen su, a firgice suka saki juna, idanu a zazzare Basma take kallon dad ɗin nata ta fara ƙoƙarin lalubar rigarta, duvet ta janyo ta rufe jikinta yayin da ɗayar ta yi saurin sauka daga saman gadon ta 6oye a jikin ɗayan 6angaren gadon, hannun Maleek na kerma ya nuna Basma fuskarsa a hautsine yayin da furucin bakinsa suka ƙafe sam ya kasa furta kalma, itama Basmar kerma jikinta ke yi sosai tana ƙara dukunkune kanta da duvet ɗin, wane irin bala'e ne wannan idanuwansa suka gane masa! Wace irin musiba ce wannan ke faruwa under his roof! Cikin karewar murya da tashin hankali da ƙyar ya furta, " “Basma… me nake gani haka?!” Ya faɗa his voice breaking in disbelief, Basma ta kasa magana jikinta sai faman kakkarwa yake, yayin da zuciyarta ke bugawa da ƙarfi, wani irin tsoro da bata taɓa fuskanta ba na ratsa ta, tunanin cewa mahaifinta ya gan ta a wannan hali ya matuƙar gigita ta, da ƙyar Maleek ya iya jan ƙafafunsa ya juya ya fita daga cikin ɗakin ko bin takan takardun da suka faɗi bai yi ba....sai lokacin Basma ta fashe da wani irin matsanancin kuka, ɗayar da ta 6oye a gefen gado tana jin alamun ya fita da sauri ta ɗago tana zare idanu, ba zata wuce sa'ar Basma ɗin ba, sai dai ita fara ce jajur kuma tana da gashi mai launin coffee brown, ta jawo kayanta dake a gefe guda saman gadon, cikin rawar jiki ta fara sakawa wanda riga da wando ne, ta ɗauko wata doguwar riga ta ɗaura a sama, jawo gyalen rigar ta yi ba tare da ta bi ta kan jakar ta ba ta nufi ƙofa da sauri kana ganinta ka san a firgice take, da yake a saman benen akwai hanyar da zata fitar da kai ta bayan gidan kuma ta san da ita don sun sha biyowa ta nan, nufar hanyar ta yi tana tafiya kamar zata kife ƙasa. Sosai Basma ke ta yin kuka, wllh ta yi dana sanin ganinta da mahaifinta ya yi a halin, bata san ya aka yi ba bata ankare da na'urar tsaron gidan da ke sanar da shigowar mutum ba, wadda dama da ita take amfani tana gane idan wani ya shigo gidan duk tana aikata hakan, shi ya sa asirinta bai ta6a tonuwa ba a wurin iyayenta sai yau da aka samu 6acin rana.... *✨A CIKIN RAYUWA✨* ZAINAB BATURE 41 ....Da ƙyar Basma ta jawo kayanta ta fara sakawa, saukowa ta yi daga saman gadon har lokacin jikinta kerma yake sosai, tsaye ta yi ƙwalla na ci gaba da zubowa daga idanunta, tana son tabi bayan dad ɗinta sai dai tsoro da fargaba sun cika zuciyarta, ta ɗauki lokaci a tsaye tana ta saƙe-saƙe a zuciyarta, da ƙyar ta yi ƙarfin halin nufar ƙofa ta fita, a hankali take yin tafiya kamar mai yin sanɗa, kana ganinta ka san a matuƙar tsorace take, bugun da ƙirjinta ke yi yana ƙara tsananta yayin da take ta ƴan waige-waige, bakin bene ta iso ta tsaya tana kallo cikin ƙaton falon ƙasan bata ga kowa a ciki ba, ɗago idonta da ya yi sharkaf da ƙwalla ta yi ta kallo 6angaren dad ɗinta da ke a saman benen, jim ta yi tana ta kallon wurin, can ta fara tafiya a hankali ta nufi part ɗin, tana isa bakin ƙofar shiga ta tsaya sakamakon hango Maleek da ta yi ta cikin ƙofar wadda take ta glass, zaune yake a saman kujera ya sadda kansa ƙasa yayin da yasa duka hannuwansa ya tallabe kansa, ko takalman ƙafarsa bai iya ya cire ba, wasu sabbin hawaye ne suka fara zubo mata, ta yi takaicin yadda ta saka dad ɗinta mai matuƙar ƙaunarta a cikin damuwa haka, a karon farko a rayuwarta da ta ji tana tsoron kusantar mahaifin nata, summoning every ounce of courage she had ta shiga ciki, har ta kai tsakiyar falon bai ɗago ba da alama ma bai san ta shigo ba, can nesa da shi ta tsaya tare da duƙawa ƙasa, cikin rawan murya ta fara magana, "Dad, please I'm sorry… I swear it was a mistake, I was not thinking please forgive me..." Shiru bai ko motsa ba yana a yadda yake, ƙwalla ne suke ta malala daga idanuwanta, "Don Allah dad...na san na yi abu mara kyau, It was the devil's work...Dad please… i promise it will never happen again." Ta faɗa tare da haɗe hannuwanta pleadingly, Still ba alamar zai ɗago balle ya tanka mata, haka ta ci gaba da roƙonsa, bayan wani lokaci ta ga ya ɗago kan sa ya kalle ta, abun da ta gani a fuskarsa ya matuƙar ƙara tayar mata da hankali, dad ɗinta yau ke zubar da ƙwalla, wanda tun da take bata ta6a ganin hakan ba, ko lokacin da mahaifiyarsa ta rasu bata ga ya yi kuka ba duk da tarin damuwar da ya shiga a lokacin, yau ita ce ta saka dad ɗinta mai ƙaunarta kuka, subhanAllah! "Basma...." Ya kira sunanta da yanayin tsoro da rashin yarda muryarsa na karyewa, kallon da yake mata shi kaɗai ya isa ya karya dukkan ƙarfin gwiwar ta, haɗe hannuwanta ta yi tana ci gaba da yin kuka tana bashi haƙuri tare da faɗin kuskure ne, "I can't believe what my eyes just saw...what have you done Basma?" Ya faɗa yana yi mata kallo mai cike da shakku, "Dad don Allah ka yafe ni… wallahi kuskure ne, ban san me nake yi ba. Ka yafe ni don Allah!” idanunsa jiƙe da hawaye ya furta, "Kuskure? Kina kiran wannan kuskure? Kin san abin da wannan yake nufi a addini? A al'ada? A cikin sunan iyalin nan?" shiru bata ce komai ba tana ta haɗe hannuwanta tana ci gaba da yin kuka, maida kallonsa ya yi gefe, idanuwansa har sun yi ja, cikin ɗan jinjina kai ya furta, "This kind of thing under my roof! After all the love and trust we gave you..." Ya yi maganar ba tare da ya kalle ta ba muryarsa ta yi rauni sosai, magiya Basma ke ta ci gaba da yi masa kan ya yi haƙuri ya yafe mata tare da alƙawarin bazata sake aikata hakan ba, wayar sa dake yashe gefe ce ta fara ringing, sai da ya ga kiran James sannan ya tuna da ya barsa a waje za su koma office, saidai a halin da yake ciki bai jin zai iya komawa wurin aikin, ɗaukar wayar ya yi cikin ƙoƙarin daidaita muryarsa ya sanar da James cewa ya je kawai shi ba zai samu komawa office ɗin ba, shiru ya yi bayan ya gama wayan yana kallon gefe, akwai maganganun da yake son yi amman saboda ɗacin da yake ji a bakinsa ya kasa, a cikin ransa yake ta faman jinjina al'amarin wanda yake gani tamkar mafarki, tabbas ƙaddara bata kara, duk yadda ya kasance yana mai kula sosai kan tarbiyyar Basma hakan bai hana wannan mummunan ƙaddarar samun su ba, tunaninsa yadda akai ta koyi wannan mummunan ɗabi'ar, ko hakan yana da nasaba da wani sakaci nasu? A hankali ya kai idanunsa kan Basma dake ta shar6ar kuka jin furucin da take na roƙon kada ya sanar ma mom ɗinta, janye idanunsa ya yi a ransa yana mai tunanin idan Sapna ta ji wannan labarin ya san har matsala zata iya samu a zuciyarta idan ma bata samu attack ba, "So, kin san abu ne mara kyau kike aikatawa, kuma kin san hakan zai jefa mu a cikin damuwa, amman baki yi tunanin guje ma aikata hakan ba gudun halin da zamu shiga...wannan ne sakayyar mu daga gare ki Basma! Miye kika nema kika rasa? Mi ye bamu yi maki? Wani riba ne zaki samu da kika za6i wannan hanyan da zai lalata rayuwarki?.....Is this what happens when love is given too much? wataƙila mune muka ja hakan, saboda soyayyan da muke nuna maki, muna yi maki duk wani abun da kike so sakamakon ke kaɗai ce Allah Ya bamu...sai dai na san mu bamu ɗora ki hanyan da rayuwarki zata gur6ace ba, muna bakin kokarin mu wurin ɗaura ki a hanyan daidai tare da nuna maki abu mai kyau da mara kyau...ban san daga ina matsalan yake ba..." Ya ƙarasa maganar cikin raunanniyar murya tare da ɗan jinjina kansa, yayin da hannunsa da ya dunƙule ya ɗaura a saman bakinsa ke ƴar kakkarwa, kuka wiwi Basma ke ta faman yi tana bashi haƙuri, bayan ɗan lokaci ya sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da kai idonsa kanta ya ce, "Allah Ubangiji Ya fi mu sanin dalilin da ya sa ya jarabe mu ta wannan hanyan. Allah Ya bamu ikon cinye jarabawan, Ya kuma shirya mana ke." Sadda kanta ta yi ƙasa tana jin wani irin ɗaci a zuciyarta, ce mata ya yi ta tashi ta tafi, ta ɗago ta kalle shi cikin muryar kuka ta ce, "Pls dad ka yafe ni....ba zan sake ba...I promise you." Shiru ya yi idonsa a kanta yana mata kallo mai nuni da alamar mamakin mutum, ita kuma ta kasa tsayar da idanunta kansa, juyar da kansa ya yi daga barin kallonta ya ce mata ta je za su yi magana later, ta miƙe jiki a sanyaye ta nufi hanyar barin falon, juyo fuskarsa ya yi ya bita da kallo, zuciyarsa ta shiga dawo masa da hoton halin da ya riske ta, da sauri ya runtse idanunsa tare da kai hannu ya dafe goshinsa da ke wani irin sara masa tun faruwar abun. Misalin ƙarfe ukku saura Sapna ta shigo cikin gidan, tana sanye da riga da wando na wani silky yadi mai kyau kalar ruwan ƙasa da ya hau da fatarta sosai, kanta ta yi rolling gyale kalar kayan, hannunta tana riƙe da doguwar baƙar jacket sai yar babbar bakar jaka, mrs Helen ce ta fito ta tarbe ta da fara'a, bayan sun gaisa ta amshi jacket da jakan nata suka nufi shiga ciki, "Ko honey da baby sun dawo? Na kira wayan shi bai ɗauka ba." Sapna ta tambayi Helen da turanci yayin da suke tafiya cikin falon, amsa ta bata da eh sun dawo tun ɗazun, ta gyaɗa mata kai, part ɗinta ta ce ta kai mata kayan ita kuma kai tsaye ta nufi part ɗin Maleek dake nan ƙasa, ganin baya a nan ta fito ta nufi saman bene, tana shiga cikin falonsa ta ci karo da wayarsa dake ajiye a saman kujera, ta ɗan yi mamakin ganin wayan a nan ba tare da shi ba, sai kuma ta yi tunanin ko ya zauna a wurin ne ya shiga ciki yin wani uzurin, bedroom ɗinsa ta nufa tana shiga ta ja ta tsaya daga bakin ƙofa tana kallon haɗaɗɗan gadonsa fuskarta da ɗan alamun razana, da sauri ta shiga cikin ɗakin ta nufi gadon muryarta da yanayin tashin hankali ta furta, "Honey! Mi yake faruwa..." Hannu ta kai da sauri bayan ta ƙarasa bakin gadon ta yaye lallausan farin bargon da ya lullube har kansa da shi, a hankali ya buɗe idanunsa da suka yi ja ya kalle ta, a ruɗe Sapna ta kai hannu ta ta6a fuskarsa, jin zafi a jikin nasa da sauri ta ce, "Honey what's wrong with you? Baka lafiya?" Kai ya ɗan ɗaga tare da lumshe ido, "But...why didn't you call me ka sanar mani?" Shiru ya ɗan yi yana kallonta, cike da ƙarfin hali ya ɗan yi murmushi ya ce, "Bana son in tayar maki da hankali ne..." Ta katse sa fuska a yamutse ta ce, "Haba honey...to miye amfani na?" Hannu ya ɗago ya shafa fuskarta ta sigar rarrashi ya ce, "Sorry..ba wani rashin lafiya bane sosai..." cire hannunsa ya yi daga fuskarta ya dafe kan shi ya ce, "Kai na yake mini ciwo sosai." Ya yi maganar yana ɗan nishi, "And you are running a temperature too." ta faɗa tana ƙara taba jikinsa, shiru ya yi yana kallonta, "Where is baby?" Ta tambaye shi ganin bata ga Basma ba a kusa da shi, ɗan janye idonsa ya yi bayan ya lumshe idanun ya bata amsa da suna tare shi ya ce mata ta je ta kwanta ganin ta tada hankalinta saboda rashin lafiyan da yake, ta jinjina masa kai alamar gamsuwa kafin ta tambayi ya ci abinci ya ce mata bai jin yana son cin komai, sumbatar bayan hannunsa ta yi ta ce dole ya daure ya ci abinci sai ya sha magani, bayan ta yi maganar ta miƙe tana faɗin bari ta je ta samo mashi abun da zai ɗan mashi daɗin ci, bin ta da kallo Maleek ya yi yayin da ta nufi ƙofa da sauri, wani irin tausayinta ne ya ratsa masa zuciya, ya runtse idanunsa yana mai jin inama abun da ya faru mafarki ne ba gaske ba. Tana fitowa 6angaren Basma ta nufa, har sai da gabanta ya ɗan faɗi bayan ta shiga ciki ganin itama Basmar a kwance ta lullu6e har kanta da duvet, da sauri ta nufe ta ta zauna a bakin gadon tare da kai hannu ta buɗe mata fuska, ta furta, "Baby...." Ɗan firgit Basma ta yi ta buɗe idanunta, tun bayan data baro 6angaren dad ɗinta itama zazza6i ya rufe ta, bayan ta sha uban kuka ne bacci ba mai nauyi ba ya ɗauke ta, "Baby are you okey?" Sapna ta tambaya da alamun tashin hankali, shiru Basma bata yi mata magana ba sai idanu da ta bita da su gabanta na bugu da ƙarfi, tsoronta kada a ce dad ya faɗa mata, duk da bata ga alamun ta san abun da ya faru ba a tattare da mom ɗin tata, hannu Sapna ta kai tana shafa fuskarta, ta san dama in dai dad ɗinta baya lafiya haka zata shiga damuwa, itama wani lokacin har ciwo take yi, hakan ya sa Sapna yin tunanin saboda ciwon Maleek ɗin ne itama ta shiga wannan yanayin, matsawa ta yi kusa da kanta ta ɗaura kan nata a saman jikinta ta shiga rarrashinta tana faɗin, "It's okey, zai samu lafiya dad ɗin naki, ki daina damuwa pls, kin ga kema har ciwo ya kama ki." Bin ta da kallo Basma ta yi da alamun razana jin maganar ta, ke nan dad ɗinta baya lafiya saboda abun da ya faru? ta faɗa a cikin ranta, "Ko nima kina son damuwa ya yi mani yawa saboda halin da kuke ciki har ciwo ya kama ni?" Sapna ta faɗa fuska a yamutse ganin Basma ɗin taƙi cewa komai, da sauri ta girgiza mata kai ta yi saurin kife fuskarta a jikin mom ɗin nata jin kuka ya taho mata, shafa sumarta da ke a tarwatse Sapna ta shiga yi tana ƙara rarrashinta, bayan ɗan lokaci ta ce mata bari ta je zata haɗa ma dad ɗinta abun da zai ci ya sha magani, tambayarta ta yi mi take son ci itama ta haɗa mata, ta girgiza mata kai alamar bata son komai, Sapna ta ce mata dole ta daure ta ci abinci sai itama ta sha magani, daga haka ta sauka daga saman gadon tana faɗin zata turo mrs Helen ta kawo mata abincin kafin ta gama haɗa ma dad ɗinta ta daure ta ci, tana fita Basma ta kife fuskarta a jikin pillow ta saki kuka, yau ita ce silarta dad ɗinta ya kwanta ciwo, abun sam bai mata daɗi ba, ta ji gaba ɗaya ta tsani kanta, a haka ma don mom dinta bata sani ba ita bata san wani irin hali zata shiga ba, amman tabbas ta san sai ta fi dad ɗinta shiga mawuyacin hali. Wunin ranar haka ta kasance ma Maleek da Basma ba daɗi, sa6anin yadda suke yin hutun ranakun ƙarshen sati cike da nishaɗi da annashuwa, ita kanta Sapna duk ta shiga damuwan halin da suke ciki, don ma Maleek nata ƙarfin halin nuna ya samu sauƙi saboda halin damuwan da Sapna ta shiga. Washe gari lahadi duk suna a gida, har sannan Maleek baya jin daɗin jikinsa daurewa kawai yake yana nuna ya samu lafiya, gaba ɗaya duk a ɗaki suka yi breakfast, tun jiya da abun ya faru tsakanin shi da Basma ba wanda ya sake fitowa daga part ɗinsa, sai Sapna ce ke ta faman kai kawo tsakanin parts ɗin su. Bayan sallar azahar lokacin Sapna tana a bedroom ɗin Maleek ta yi bacci, fitowa ya yi daga part ɗin sa jikinsa sanye da farar jallabiya, a wajen part ɗin ya tsaya idanunsa na kallon hanyar zuwa 6angaren Basma, a karon farko da ya ta6a jin shakkar zuwa 6angarenta, after a while ya sauke ƴar ajiyar zuciya ya fara tafiya a sanyaye ya nufi 6angaren nata, lokacin da ya kama hannun ƙofar har saida ya ɗan runtse idanunsa jin yadda fargaba ta kama sa ƙirjinsa nata bugawa da ƙarfi, yayin da zuciyarsa ta shiga dawo masa da abun da ya gani a ɗakin, da sauri ya saki handle ɗin kansa a ƙasa, bayan ɗan lokaci ya dake ya sake kai hannu ya tura ƙofar, tsaye ya yi a bakin kofar bayan ya shiga idanunsa a kan Basma dake kwance ta lullube jikinta, dama ba bacci take ba tana dai kwance kawai, jin kamar an shigo cikin ɗakin ya sa ta buɗe fuskarta, tana yin arba da wanda ke a tsaye, a razane ta yi saurin tashi zaune tana zazzare idanunta, kallon shi ta shiga yi da alamun tsoro akan fuskarta, ganin kallon da yake jifar ta da shi ya sa ta sauke idanunta ƙasa, gabaɗaya ta takure jikinta gabanta sai duka yake, cikin rashin ƙarfin jiki ya nufo cikin ɗakin, duk da bata kalle shi ba ta gane shigowa ya yi ta shiga ƙara zazzare idanunta, daga ɗan nesa da gadon ya tsaya yana kallonta, "Have you prayed?" Ta ji saukar muryarshi yana tambayarta ta yi salla, ɗago ido ta yi suka shiga cikin nasa ta ɗaga masa kai alamar eh, kauda nasa idanun ya yi, ya yarda da ta yi sallan don ga abun salla da hijab nan a wurin da ta saba yin salla, kallon shi ta ci gaba da yi fuskarta a marairaice, ta lura da ko kallonta baya son yi abun da bata ta6a tunanin hakan zata kasance a tsakanin su ba, kneel down ta yi a saman gadon cikin rawar murya ta ce, "Dad pls ka yafe ni, na yi alƙawarin ba zan ƙara ba....na tuba don Allah kada ka yi fushi da ni..." Ɗan lumshe ido Maleek ya yi, idan ya ce yana jin daɗin hakan dake kasancewa a tsakanin sa da gudan jininsa mafi soyuwa a garesa ya yi ƙarya, to amman ba yadda ya iya dole ne yasa ta gane ta aikata laifi mai girma da muni, "Pls dad...." Ya ji ta sake faɗa, slowly ya maido idanunsa kanta, da sauri ta haɗe hannuwanta ƙwalla na zubo mata tana kikkafta idanu, "Kin san cikin irin halin da kika jefa ni Basma..." Cikin raunanniyar murya ya faɗi hakan, shesshekar kuka ta shiga yi tana kallonsa, "Har yanzu ina tantamar idan da gaske ke ce kika aikata hakan..." Ya jinjina kansa, still tana akan gwiwowinta cikin kuka ta ce, "Aikin shaiɗan ne dad, don Allah ka yafe min. Na san na yi kuskure, kuma ba zan sake ba....wallahi ba zan sake ba." Yana kallonta ya ce, "Ke kika ba shaiɗan ɗin goyon baya, kin za6i aikata hakan da iliminki, kin san abu mai kyau da mara kyau." Sauke idanunta ta yi ƙasa ƙwalla na ci gaba da saukar mata tana yamutsa yatsun hannunta, "I will ask you some questions, bana son ki yi mani ƙarya." Da sauri ta kalle sa tare da jinjina masa kai, shiru ya yi idanunsa na kallon direction daban, bai da yadda zai yi da zai mata tambayoyin amman ba don yana son hakan ba, "Who is the other girl?" Bayan ɗan lokaci kamar ba zai yi magana ba ta ji ya tambaya muryarsa ƙasa, da sauri ta maida idanunta ƙasa bugun ƙirjinta na ƙara tsananta, ita kanta tambayar ta saka ta jin ba daɗi a cikin zuciya, da ƙyar ta furta, "It's Huda." Ɗan runtse ido Maleek ya yi don ya san Huda ɗin best friend ɗin ta ce, bai ta6a zaton a tarayyar su suna aikata abu mara kyau ba, itama Huda mahaifiyarta likita ce ƴar nijeriya kuma ƙawar Sapna, amman mahaifinta Bature ne ɗan nan ƙasar kuma a kamfanin Maleek yake aiki, sau da yawa Basma tana tambayar iyayen nata kuɗi ta ce zata siya ma Huda abu, ko kuma idan aka siya mata kaya ta fidda wasu ta ce Huda ɗin zata ba, har ta kai wani lokacin idan suka yi mata siyayya har da Huda ɗin suke siya ma wasu abubuwan, dalilin shaƙuwar yaran nasu ya sa suma iyayen suke mutunci sosai da juna, har ma ta kai sun zama tamkar ƴan'uwa, kuma Maleek na yi ma dad ɗin Huda alkhairi mai yawa duk dalilin abotar yaran nasu, sai da Maleek ya ji kamar ba zai iya ci gaba da yi mata tambayoyin ba saboda zullumin da ya kama sa na kada ya ƙara jin abun da zai ƙara girgiza masa zuciya, amman ba yadda zai yi dole ya binciki yadda aka yi ta fara aikata hakan, "Ban da ita sai wa kuke yin hakan tare?" Ba tare da ta kalle sa ba ta ce masa ita kaɗai ce, ya ce mata ya ce bai son ta yi masa ƙarya, still ba ta kalle sa ba ta ce wallahi ita kaɗai ce, "Waye ya koya maku?" Bugun ƙirjin Basma ya ƙaru, cikin raunin murya ta ce, "Wata cousin sis ɗin Huda ce da ta zo hutu daga U.S." Maleek ya yi shiru tun da ya fara mata tambayoyin bai kalle ta ba, "Tun yaushe ne kuke yi?" Saida ta haɗiyi miyau kafin ta basa amsa da an yi shekara guda, Maleek ya girgiza da jin cewa shekara guda suna aikata hakan ba tare da asirin su ya tonu ba, tambayarta ya sake yi a ina suke aikatawa, ta ce masa a nan gidan ko a can gidan su Huda, ya ce kenan duk dawowar da take yi daga makaranta ba tare da lokacin tashin ta ya yi ba ta faɗi wani uzurin abun da take dawowa yi ke nan, murya na rawa ta ce wasu lokuttan amman ba duka ba, wani lokacin da gaske idan ta ji bata jin daɗi sai ta dawo, shiru ya yi ya ɗan cije lebensa na ƙasa tare da rufe idanunsa, jin bai ƙara cewa komai ba ya sa ta ɗago idanunta da suke jiƙe tai ta kallon sa tana jin wani iri a cikin ranta, after a while ya sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da juyawa ta ji ya ce ta sako veil ta biyo sa daga haka ya nufi ƙofar fita, hannu ta kai ta ɗauki gyalen ta dake a gefe saman gadon kafin ta sauka daga saman gadon, bayan ta ɗaura gyalen a saman dogowar rigar jikinta cikin sanyin jiki ta bi bayansa, sauka ta gansa ya yi ƙasa itama ta fara taka mattakalar benen ta sauka, babbar kofar fita daga gidan ya nufa tana biye da shi, bayan sun fito motar da Sapna ta dawo da ita daga aiki da ke ajiye a nan gaban gidan ya nufa ya buɗe driver seat, sai lokacin ya kalli Basma suka haɗa ido, da hannu ya yi mata alamar ta shiga cikin motan, ta kai hannu ta buɗe back door ta shiga, abun da bai ta6a faruwa ba a tsakanin su zama wuri daban daban a cikin mota, koda gaba ɗayan su ne za su fita har da mom dinta, ita ke zama a gaba don yawanci idan fitar da ta dangance su ce shine ke driving nasu, wani lokacin hannunsa guda a cikin nata, amman yau the reverse was the case..... ✨A CIKIN RAYUWA✨ ZAINAB BATURE 42 Bayan sun fito daga gida sun hau hanya, Basma na ganin hanyar da suka bi ƙirjinta ya shiga bugawa don ta fahimci gidan su Huda suka nufa, bayan tafiyar mintoci suka ƙaraso unguwar su Huda, cikin harabar katafaren ginin suka shiga, babban ginin bene ne mai hawa da yawa, wurin da aka tanada don ajiye motoci ya nufa ya parker motar, babban ginin na ɗauke da apartment da dama na mutane masu matsakaicin ƙarfi, kasantuwar ranar hutun ƙarshen mako ce, a kowane wurin da aka tanada don ajiye motoci na ɗauke da motoci, bayan ya kashe motar fiddo wayansa dake a cikin aljihun jallabiyarsa ya yi ya fara latsa ta, kai wayar ya yi kunne sai da ya yi ƙoƙarin daidaita natsuwarsa kafin ya fara magana, gaisawa suka yi da wadda ya kira wato mahaifiyar Huda ya tambaye ta ko Hudan na nan, bayan ta bashi amsa ya ce mata ta turo ta suna nan a waje shi da Basma, tambayar mi ya sa ba za su shigo ciki ta yi ba, yana ɗan murmushi ya bata amsa da yana sauri ne dama hanya ce ta biyo da su shine Basma tasa su tsaya ta gaisa da Huda, bayan sun gama yin wayar ya ajiye ta gefe tare da jingina kansa jikin seat ya ɗan lumshe ido, Basma dai na zaune a baya gabanta na ci gaba da bugawa tamkar ana mata luguden ta6are, after some few minutes Huda ɗin ta fito daga cikin ginin tana sanye da doguwar riga ta ɗaura ɗan mayafi a saman kai, kana ganin yanayin fuskarta kasan ba a nutse take ba, don tun da mummynta ta sanar da ita game da zuwan su kuma ba za su shigo ba ta san zuwan na da nasaba da abun da ya faru jiya, Maleek da idonsa na akan ginin ya ga lokacin da ta fito, ya kai hannu ya buɗe ƙofar motar ya fita yadda zata gan su, tana hango shi gabanta ya tsananta bugu, tamkar wadda aka zare ma laka ta nufo su, tana kusa ƙarasowa wurin motar Maleek ya yi mata alamar ta shiga baya ba tare da ya kalle ta ba ya koma cikin motan, hannunta har ɗan rawa yake ta kama handle ɗin kofan baya, tana buɗe ƙofar zata shiga suka haɗa ido da Basma, tana ganin yanayin Basman ta sha jinin jikinta tare da sauke idanunta ƙasa, jiki a sanyaye ta zauna saman seat ba tare da Maleek ya kalle ta ba ya ce ta rufo ƙofar, shiru suka ɗan yi cike da ƙarfin hali murya na ɗan rawa Huda ta ce, "Goo..d...after..noon daddy.." Shiru bai amsa ba idanunsa na kallon waje ta glass ɗin motan, ɗan jim ta yi da tunanin ko bai ji ta ba, ƙara gaishe sa ta yi still bata ji ya amsa ba, a hankali ta ɗago ido da niyyar ta saci kallonsa suka haɗa ido ta madubin motan, da sauri ta sauke idanunta ƙasa gabanta na ci gaba da faɗuwa don ta gane yana jinta ya yi mata shiru, a kausashe ta ji ya ce, "I'm very disappointed in you Hudah!" Gabanta ne ya buga da ƙarfi ta ƙara sunne kanta ƙasa, "Dama abun da kuke aikatawa ke nan ke da Basma?" Ta ji ya jefo mata tambayar, kasa ce masa komai ta yi kuma bata ɗago ta kalle sa ba, "Mun yi tunanin kuna tarayya da juna da gaskiya, kuna ƙaunar juna tsakani da Allah ashe ba haka bane mummunan abun da kuke aikatawa ke nan?" Dukkan su idanunsu na a ƙasa suna ƴar shesshekar kuka, tambayar Huda ya yi tun yaushe suke aikata hakan kuma waye ya koya masu, kamar yadda Basma ta faɗa mashi itama irin amsar ta bashi, ya sake tambayarta su nawa suke yi ta ce masa su biyun ne kawai, "Do your parents know about this?" Kanta a ƙasa ta girgiza masa kai alamar a'a, ɗan shiru ya yi idanunsa na kallon gaba, sigh ya yi ya ce, "Then I have no choice but to inform them..." Tun kafin ya ƙarasa rufe baki a kiɗime Huda ta ɗago ta zaro idanunta da suka jiƙe da ƙwalla, ta shiga girgiza mashi kai cikin rawar murya ta ce, "No dad.. Pls don't tell them, idan suka ji za su shiga damuwa, mummy zata kashe ni..." Gaba ɗaya ta gigice don ta san mummy ɗinta tsaye take a kanta, duk da ƙaunar ta da take sosai bata wasa kan abun da ya shafi tarbiyyarta, Maleek ya ɗan jinjina kai tare da juyowa ya kalle ta ba alamun sassauci akan fuskar sa ya ce sun san suna tsoron a sani amman suke aikatawa, a tare suka haɗa baki suna roƙon shi kan ya yi haƙuri sun yi alƙawarin ba za su sake ba, Maleek ya ɗan lumshe idonsa, gaba ɗaya kan sa ya ɗaure ya rasa ta inama zai 6ullo ma al'amarin, ya san tabbas iyayen Huda suka ji dole su shiga tsananin tashin hankali, sai dai kuma ba daidai bane idan ya 6oye masu ko don su ɗauki matakin da ya dace don magance matsalan, tunanin mafita ya shiga yi a cikin ransa, after a while ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, a nutse ya shiga yi masu nasiha tare da nuna masu illar abun da suke aikatawa, ya ce wannan ba ɗabi'ar mutanen kirki ba ce kuma idan suka ci gaba da aikatawa sun ɗauki hanyar lalata rayuwar su ne, kuma matuƙar suka mutu suna aikata hakan tabbas za su haɗu da azabar Allah, daga baya ya yi masu faɗa sosai tare da saka su su yi masa alƙawarin ba za su sake aikata hakan ba, ya ɗaukar masu alwashin matuƙar ya gano ba su bari ba zai ɗauki mummunan matakin da ba su ta6a zato ba akan su, kuma zai sanar da iyayen Huda da mom ɗin Basma duk su sani, Huda kuka sosai take yi don nasihar da ya yi mata ta shige ta sosai, cikin kuka ta yi masa godiya tare da yi masa alƙawarin ta daina, ya jinjina kai tare da cewa, "May Allah guide you all." Duk suka amsa da amin, ya sake ce masu kowannen su idan ya yi salla ya riƙa yi ma kansa addu'ar neman shiriya kan hakan dama duk wani sa6on Allah suka amsa mashi, tissue ya ciro ya miƙa ma Huda ya ce ta goge fuskarta don kada idan ta koma gida a gane ta yi kuka, hannunta na rawa ta amsa tana gogewa, gaba ɗaya tausayin yaran da su kansu iyayensu ya kama shi don wannan musiba ce ta same su, bayan ta gama ya ce ta koma gida, bayan ta fito a parking space ɗin Huda ta saƙe jikin motan mummynta ta shiga yin wani sabon kuka, duk sai ta ji ta tsani kanta da ya kama su suna aikata hakan, dama ita tun farko ranta baya so Basma ce ta koya mata, lokacin da ta fara ƙoƙarin saka ta a hanyar sai da ta nuna mata abu ne mara kyau baza ta yi ba, amman haka tai ta faman ƙoƙarin jan ra'ayinta tana kashe mata kuɗaɗe a haka har saida ta yi nasara a kanta, maganar da suka faɗa ma Maleek cewa cousin ɗinta ce ta koya masu ba gaskiya ba ce, tun jiya Basma ta kira ta ta tsara mata hakan. Akan hanyar komawar su gida sai da Maleek ya ƙara yi ma Basma nasiha sosai, ta nuna masa ta yi masa alƙawari ba zata sake aikata hakan ba, bayan sun iso gida cikin sa'a har lokacin Sapna tana bacci don jiya bata samu ta yi isasshen bacci ba saboda halin ciwon da su biyun suke ciki. Sosai Maleek ya yi ƙarfin hali wurin ci gaba da yin harkokinsa kamar ba wani abu, sai dai a can ƙasan ransa abun na damunsa sosai duk da ya ɗauki hakan a matsayin ƙaddara, sannan ya saka ma Basma ido sosai tare da yi masu addu'oin neman shiriya, duk da suna pretending kamar ba abun da ya faru sam su biyun sun kasa sakar ma juna jiki kamar yadda suke a da, amman ba su bari Sapna ta fahimci wani canji a tsakanin su ba, Basma ce ma ke ɗan shan jinin jikinta idan suna tare gaba ɗayansu amman shi Maleek yana ƙoƙarin sake ma Basma ɗin kamar yadda ya saba, wani lokacin har ta yi ta masa kallon mamaki. Bayan kwanaki da faruwan hakan, da daddare Sapna na kwance saman gadon Maleek ta tada kanta da ƙafafunsa, yayin da shima yake a kishingiɗe hannunsa guda a cikin sumarta, magana yake son yi mata da ta shafi Basma amman yana zullumin kada ta yi tunanin wani abu, sai dai ganin maganar na da muhimmanci kuma zata taimaka wurin ƙara saka mata ido ya sa shi tattaro ƙwarin gwiwa a nutse ya ce, "My love...ina son zamu yi magana da ke ne da ta shafi Basma." Ɗago fararen idanunta ta yi ta kalle shi tare da furta ok, dan jimm ya yi kafin ya ci gaba, "I think...kaman kuɗi da muke bata suna yawa, so yakamata mu rage idan so samu ne ma gaba ɗaya a daina bata kuɗi in dai ba da wani ƙwakkwaran dalili ba." Zuba masa ido Sapna ta yi da ɗan alamun mamaki akan fuskarta, "Wani abu ya faru ne?" Ta tambaya tana ta kallonsa, da sauri ya ce, "No, ba wani abun da ya faru, kawai dai na yi nazari ne duba da tana yawan kawo mana buƙatar kuɗi kuma wasu lokuttan muna bata ba tare da sanin mi take yi da su ba, kin san kuɗi suna saurin yin tasiri wurin canza mutum, wannan dalilin ne ya sa na ga ya dace mu saka kula kan hakan ba kamar yadda yanzu rayuwar ta lalace, kana ma yaron ka tarbiya wani abun sai ya zo ya 6ata hakan." Shiru ta yi tana ta kallon sa, can ta yunƙura ta miƙe zaune jikinta sanye da wata hadaddan rigar bacci iya gwiwa, zama ta yi saitin sa da yanayin shakku ta ce, "Honey ko dai akwai abun da kake 6oye mani? Basma ta aikata wani abu ne? Pls tell me.." Da sauri ya kamo hannunta cikin ƙoƙarin kwantar mata da hankali yana murmushi ya ce, "Ba wani abu kar ki tashi hankalin ki, kawai na yi tunanin hakan ya dace ne, idan ta kawo buƙatar kuɗi a rinƙa sanin mi zata yi da su kuma a tabbatar da abun da ta ce ɗin ta yi da su, zai fi ma a rinƙa siya mata duk abun da ta ce tana so zata siya kan a bata kuɗin, ko kuma a ɗauke ta akai ta ta siya, duk hakan a matsayin ƙara saka kula ne akan tarbiyarta musamman da ya kasance ita kaɗai Allah Ya ba mu." Shiru Sapna ta yi tana kallonsa yayin da wani 6angare na zuciyarta ke a cikin fargaba don sai take ganin kaman akwai wani abu da yake 6oye mata duba da bai ta6a kawo magana irin wannan ba, wani 6angare kuma na ganin zai yuwu ba da wani dalili bane kawai ya ga hakan ya dace ne kamar yadda ya ce, kuma ita kanta ba tun yanzu ba ta fahimci kashe kuɗin Basma yana yin yawa, shima Maleek shiru ya yi a ransa yana kokonton idan shawarar da ya bada ta ƙarshe zata zama mafita, yana ganin akwai buƙatar koda an siya mata abun da take so ɗin a tabbatar da ita ɗin ce zata yi amfani da abun, tabbas ya san a halin da ake ciki akwai buƙatar saka ido kan Basma daga wurin mahaifiyarta don ita ce ta fi kusanci da ita ta wasu 6angarorin, shi ba koda wane lokaci yake samun isasshen lokacin kasancewa da su ba, ban da aiki kuma yana yawan yin tafiye-tafiye, to idan shi kaɗai yake kula da ita a lokacin da baya nan hakan na iya bata dama, shirun da ya yi yasa Sapna bin sa da ido tana karantar yanayin sa, sam bata ji ta yarda da ba wani abu da yake boye mata ba, fuskantar sa ta yi sosai ta kama duka hannuwan sa cikin marairaicewa ta ce, "Honey pls ka sanar da ni abun da ke faruwa, na yi maka alƙawarin zan fahimta ba zan tada hankalina ba." A cikin ransa ya fara tunanin ta yadda zai bayyana mata ba tare da hankalinta ya tashi ba, dubara ce ta faɗo masa ya daidaita natsuwarsa ya ce, "Ok let me get you straight into the point...dama yau a wurin aiki ne na lura da wani a cikin ma'aikatan na a cikin damuwa sosai, shine na gayyace shi office don in ji damuwarsa, a nan yake sanar da ni cewa abu mara daɗi ne ya faru da su game da yarinyar su, ita kaɗai ce ɗiyar su mace sauran yaran su duk maza ne, hakan ya sa suke mata gata duk abun da take so suna yi mata, ya ce tana yawan tambayar su kuɗi su bata ba tare da tunanin komai ba, sai yanzu da Allah Ya bayyana masu abun da take aikatawa ba tare da sanin su ba..." Shiru ya yi don abun nauyi yake masa a zuciya, Sapna da ta kafe sa da idanunta tubarkalla a ɗan razane ta ce masa mi take aikatawa? Da ƙyar Maleek ya faɗi mata abun da take yi da ƙawarta, Sapna ta wani zaro idanu tare da kai hannu ta dafe ƙirjinta, kana ganinta ka san hankalinta ya tashi da jin hakan, to ina ga kuma ta ji cewa ɗiyarta ce ke aikatawa, cikin kwantar da murya Maleek ya ce, "Mun tattauna da shi sosai na bashi shawarwarin da nike ganin sune mafita, a cikin shawaran da na bashi har da wannan yanzu da na kawo don muma mu yi hakan akan Basma matsayin gyara kayanka, duniyar ta lalace, kana ba yaron ka tarbiya wasu na lalatawa ba tare da sanin ka ba, dole idan Allah ya baka yara yanzu sai ka jajirce sosai wurin kula da tarbiyar su, ba zancen wai ka yarda da yaron ka ka ƙi saka masa ido komai zai iya faruwa, al'amurra yanzu sai an dage da addu'a, Allah Ya shirya mana zuriya ya taya mu kula da tarbiyan su." A sanyaye Sapna ta amsa da amin duk jikinta ya yi sanyi laƙwas, hannu ya kawo ya jawo ta jikinsa ganin yadda duk ta yi sukuku, ya shiga kwantar mata da hankali ya ce su dage wurin saka ido kan Basma tare da addu'a in sha Allahu ba abun da zai faru, ta ɗaga masa kai tana lafe a jikinsa, Maleek ya ɗaura fuskarsa a saman gashinta tare da lumshe idanunsa, yanzu ya ɗan ji wani bangare na damuwar da yake ciki kan hakan ya ragu don ya san itama zata saka ido akan Basma, nan take a cikin rai Maleek ya yanke tafiya Umra tare da su, don ya ji yana son ya je gaban ka'aba ya roƙa masu shiriya musamman yadda ita Huda iyayenta basu sani ba balle su yi mata addu'a su kuma saka mata ido, duk da yana da tarin ayyuka a gabansa amman yana ganin wannan matsalar ta girmi duk wani aiki dake a gabansa. Bayan wasu kwanaki suka tafi saudia, Maleek ya yi amfani da labarin da ya ba Sapna na abun da ya faru da ɗiyar abokinsa ya ce mata su roƙa ma Basma shiriya sosai dama sauran yaran musulmi, itama Basma tun kafin su zo sai da ya faɗa mata ta yi masu addu'a sosai, yanzu ma bayan sun zo sai da ya jaddada mata hakan ta yi masa alƙawarin zata yi. Dalilin tafiyar tasu ne ya sa Nailah bata samu zuwa wurin su ba kamar yadda ta yi niyya, bayan da ta kira Sapna kan zata zo ta sanar mata da basu nan sun tafi Umra. Ranar Juma'a Leemarh suka ɗauko hanyar Funtua, tana zaune a bayan danƙareriyar baƙar Jeep tare da dad ɗinta, yayin da a gabansu motar jami'ai ce, Leemarh tana sanye da wata haɗaɗɗar baƙar abaya kanta ta yafa gyalen rigan, yayin da baƙar sumarta ta ɗan fito daga gaba, a fuskarta ta saka baƙin glasses da ya matuƙar yi mata kyau, a kallo ɗaya idan ka yi mata zaka yanke balarabiya ce ko kuma ba'indiya yadda haskenta ya fito sosai a cikin shigar, gaba ɗaya a ƙagare take da su ƙarasa Funtua musamman don ta ga yaya Fahad, dama tun da suka ɗauko hanya ta kira shi ta sanar masa ya ce yana wurin aiki amman zai taso da wuri. Suna shigowa cikin garin Funtua mutane ƴan siyasa suka yi ma motar su ƙawanya suna hargowar tarbar ɗan majalissar tarayyan nasu, gaba ɗaya aka ɗan sauke glass ɗin ƙofofin bayan motan dad na ɗaga ma mutane hannu cikin fara'a, ta cikin glasses ɗin fuskar Leemarh take bin mutanen da kallo, har da ita suke ta ma barka da zuwa tana ɗan ɗaga masu kai a hankali, har suka ƙaraso gidan hajiya mutane na biye da su, a bakin gate motan jami'an ta tsaya yayin da tasu leemarh ta kutsa cikin gidan, a cikin harabar gidan aka faka motar jami'in dake a gaba ya fito da sauri ya buɗe ma dad ƙofa, lokacin har Leemarh ta buɗe ta fito, Sule direban hajiya ya ƙaraso cikin girmamawa yana masu sannu da zuwa, Leemarh ta ce mashi ya fiddo boxes a booth ya kawo ciki da sauri ya amsa da to ta nufi shiga cikin gidan, hajiya ce ta fito daga ɗaki tana sanye da leshi mai kyau, cikin falon ta shigo tana faɗin, "Ko ƴan tafiyan ne suka ƙaraso na ji kaman hayaniya..." daidai lokacin Leemarh ta shigo cikin falon, hajiya na ganinta ta shiga washe baki, da sauri Leemarh ta nufo ta hajiya ta wara mata hannuwa tana ƙarasowa gabanta suka rungume juna, cike da farin ciki hajiya ke faɗin, "You are welcome ƴar hutuna." Dariya Leemarh ta yi tare da ɗagowa ta kai hannu ta cire glasses ɗin fuskarta, gaishe da hajiya ta yi bayan ta amsa ta kama hannunta ta ce su zauna yadda za su gaisa da kyau, shigowa Sule ya yi janye da boxes guda biyu masu kyau hajiya ta ce ya kai ciki ya amsa tare da wucewa, "Haleematu mutanen Abuja, duk ya kika baro su." Tana ta dariya ta ce mata duk suna lafiya suna gaishe da ita, "Daga ke sai baban naku kuka zo ke nan, ya ba a taho mani da takwarata ba da kuma maigidana." Leemarh ta gane Batool da Sultan take nufi ta ce mata za su je Kano ne da mom hajiya ta ɗaga kai, ƙwala ma Balaraba kira ta yi ta fito tare da nufo cikin falon, tana ganin Leemarh da fara'a ta yi mata sannu da zuwa ta amsa mata tare da gaishe da ita, hajiya ta ce, "Ga ƴar hutun mu nan ta iso, a kawo mata abun sha, sun sha hanya." Balaraba ta amsa da to tare da juyawa ta koma kitchen, fitowa ta yi hannuwanta riƙe da madaidaicin tray a saman glass jug ne da cups masu kyau, a saman center table ta ɗaura ta ɗauki jug ɗin dake ɗauke da lafiyayyan kunun aya da ya ji kwakwa a ciki ta zuba a cup, miƙa ma Leemarh ta yi hajiya ta yi saurin amsa tana faɗin bari ita zata bata a baki duk suka yi dariya, barin wurin Balaraba ta yi hajiya ta shiga ba Leemarh kunun ayan a baki suna ta ƴar dariya, sallamar da aka yi yasa Leemarh ɗaga idanunta suka shiga cikin na Fahad da ya shigo, lokaci guda ta shiga sakar masa murmushi shima idanunsa na akan ta yana mata ɗan murmushi yayin da yake ƙarasa shigowa jikinsa sanye da ƙananun kaya, a saman kujerar dake gefe da wadda suke ya zauna, hajiya ta kalle shi tana ƴar dariya ta ce, "Gani nan ina lelen baƙuwata, saboda murnar zuwanta ka ga ma a baki nike bata abun sha." Faffaɗan murmushi ya yi ya ce, "Hakan ya yi kyau." Sannu da dawowa ta yi masa ya amsa tare da maida idanunsa kan Leemarh, tana murmushi ta ce, "Ya Fahad sannu da zuwa, ina yini." Dan jinjina kai ya yi ya ce, "Kun zo lafiya." Ta amsa da lafiya, "Kun gaisa da baban naka ne?" Hajiya ta tambaya, ya ce mata a'a yana tare da mutane, yana rufe baki sai ga dad ya shigo, jikinsa ya yi shigan manyan kayan farar shadda ya fito a babban mutum wanda naira ta zauna masa, Fahad na ganinsa ya miƙe yana masa sannu da zuwa da murmushi ya amsa masa, ya ƙarasa daga gaban kujeran da hajiya take ya tsugunna, a nutse cikin ladabi ya gaishe da ita, tana murmushi ta amsa masa tare da yi mashi an zo lafiya, ta ce "Ya aka baro iyali?" Yana murmushi ya ce, "Duk suna nan lafiya lau suna gaishe da ku, suma suna nan zuwa in sha Allah." Hajiya ta ce Allah Ya yarda, miƙewa ya yi bayan sun gama gaisawa idanunsa akan Fahad ya nufe sa tare da miƙa masa hannu suka gaisa, bayan ya zauna akan kujera ya ce ma Fahad ya zauna, "Fahad ya aiki?" dad ya tambaya, ya ce, "Alhamdulillah, daga can ma nike yanzu." dad ya jinjina kai ya ce, "Allah Ya ƙara taimakawa." Fahad ya amsa da Amin, Hajiya na kallon dad ta ce, "Sai ga ƴar hutuna, saboda murna yanzu na gama bata abun sha a baki." Dad ya yi ƴar dariya tare da kallon Leemarh da itama dariyar ta ke, ya ce, "Ai da bata zo Funtua ba da hankalin kowa ba zai kwanta ba." Hajiya ta yi dariya ta ce, "Ta kwana biyu bata zo bane." Dad ya ce, "Hakane, na so ma su zo gaba ɗaya, to sai mom ɗinsu ta ce za su fara zuwa Kano da yake can ma sun ɗan kwana biyu ba su je ba." Hajiya ta ce ba komai za su zo ne wani lokaci, Leemarh ta kai hannu ta ce ma dad bari ta zuba mashi kunun aya ya yi daɗi sosai, hajiya ta ce ta bari a kawo masa wani, dad ya ce lafiya lau a zuba masa wannan ɗin, bayan ta zuba masa a cup ta miƙa masa, Leemarh ta kalli Fahad da fuskarsa ke kallon direction daban, zuba wani kunun ayan ta yi tare da miƙewa ta nufe shi ya juyo ya kalle ta, daga gefen sa ta tsaya ta ce gashi shima ya sha, ya yi mata murmushi ya amsa, bayan ya sha ya cire cup ɗin daga bakinsa, ta ɗan rankwafa ta yi ƙasa da murya ta ce, "Yaushe zaka je gida?" idonsa a cikin nata ya tambayi tana son zuwa ne ta ɗaga masa kai, ya ce ok ko yanzu idan ta shirya sai su tafi, miƙewa ta yi ta ce to bari ta ɗauko abu, hajiya dake kallon su ta ce ya aka yi ne Fahad ya ce tana son zuwa can gidansu ne, bada jimawa ba Leemarh ta dawo cikin falon tana riƙe da wata babbar farar shopping bag, hajiya na kallonta ta ce, "Baki bari ki ƙara hutawa, gashi ko abinci ma baki ci ba." Tana murmushi ta ce mata idan ta je can sai ta ci, dad dake kallonta da murmushi ya ce, "Kin ƙosa ki ga yan'uwan naki ne?" Ta ɗaga masa kai, hajiya ta yi mata sai ta dawo daga haka suka nufi ƙofa sun jera da Fahad, suna kusa isa ƙofa ya kai hannu zai amshi ledan hannunta, ta juyo ta kalle shi ya ɗan yi mata murmushi, hannu guda na ledar ta sakar masa suka kama tare daga haka suka fita daga cikin falon..... *✨A CIKIN RAYUWA✨* ZAINAB BATURE Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai. 43 Bayan sun fito a motar Fahad sun hau hanya, a hankali yake ɗaga ido ta cikin madubin gaban motan yana kallon Leemarh da ta mayar da glasses ɗinta tana kallon hanya, sosai ta yi masa kyau har wani girma ya ga ta ɗan ƙara, a hankali ya ga ta juyo ta kalle sa ta cikin glasses ɗin, ɗan juyawa ya yi shima ya kalle ta calmly ya furta, "Kin yi kyau sosai." ta yi murmushi tare da sauke kanta ƙasa, ɗagowa ta yi ta kalle shi ya mayar da idanunsa kan hanya, ta ce, "Kai ma ka yi kyau." Ya ɗan buɗa ido ba tare da ya kalle ta ba ya ce, "Ina wani kyau a wurin wanda ya dawo daga aiki." Tana murmushi ta ce masa ya aikin, ya bata amsa da, "Ba daɗi." ta ce, "Why ka ce haka?" Da ɗan murmushi ya ce "Mutum koda yaushe yana kai da komowa kan hanya, kullum cikin gajiya..." Tana ta kallon shi ta cikin glasses din a hankali ta ce, "Sannu..." Ya ɗan ɗaga kai, sai kuma ya ji ta ƙara cewa, "Idan ka yi aure gajiyan zai ragu." Ya ɗan juyo ya kalle ta ya ce, "Ta yaya?" Ta ɗan yi shiru tana murmushi sai kuma ta ce, "Idan ka dawo daga aiki wife en ka zata taimaka maka, kamar ta haɗa maka ruwan wanka, ta taimaka maka ka shirya, ta shirya maka abinci har ma ta baka da kanta, da sauran abubuwa, kuma sannan ma...zata maka massage don rage gajiyan." Tana ƙarasa maganar ta yi saurin juyar da fuskarta tana kallon gefe, Fahad ya ɗan buɗe ido tare da juyowa ya kalle ta, maida idonsa ya yi kan hanya yana ɗan murmushi, duk da ya san ta isa ta san komai game da aure ya ɗan ji mamakin yadda ta iya faɗa masa hakan. Bayan sun iso, Fahad ya parker motan a gaban ginin, tare suka fito sai lokacin Leemarh ta kalle shi tun bayan da ta yi maganar ɗazun da suna hanya, murmushi suka sakar ma juna ya zagaya inda take tare da yi mata alamar su shiga, sai da ta ɗauko ledan da ta taho da ita a back seat wadda ke dauke da tsaraban da ta yi masu, falon gidan suka shigo wanda yake tsaf sai ƙamshi ke tashi, Khaleel na kwance saman doguwar kujera yana latsa waya basu daɗe da zuwa gidan ba weekend shi da Sadeeya daga makaranta, yana ganin Leemarh ya ɗan buɗa ido tare da tashi zaune, yana mata murmushi ya ce, "A surprise visitor saukan yaushe?" Itama murmushin ne akan fuskarta ta nufo shi, a kusa da shi ta zauna ta ce, "Bamu daɗe da zuwa ba ni da dad." Khaleel ya ce yanzu ko ya ga labarin zuwan dad ɗin ashe tare suke ta ce masa eh kafin ta gaishe da shi, bayan ya amsa ya tambayi sauran yan gidansu ta ce masa suk suna lafiya suna gaishe da su, Binafa ce ta shigo cikin falon ta yi gayun juma'a, tana hango Leemarh ta zaro ido tare da nufo ta da sauri, da mamaki ta furta, "Yaya Lermarh ke ce?" Dariya Leemarh ta yi mata ta ɗaga mata kai, aikuwa ta nufo ta da gudu suka rungume juna, ɗagowa Binafa ta yi still da alamun mamaki akan fuskarta ta ce, "Yaushe kika zo?" Ta bata amsa da yanzu suka zo tare da yaya Fahad daga gidan hajiya, miƙewa ta yi da sauri tana faɗin bari ta je ta gaya ma su mommy ta zo, dawowa ta yi tare da Sadeeq tana faɗin ga momy nan zuwa, Sadeeq ya gaishe da Leemarh yana murmushi, ita ma shine akan fuskarta ta amsa masa tare da tambayar sa ya karatu, momy ce ta shigo cikin falon tana sanye da hadaddan atamfa ɗinkin doguwar riga ta yi ɗaurin kallabi mai kyau da ya bayyanar da tufkar kitsonta dake a naɗe, da faffaɗan murmushi ta nufo Leemarh tana faɗin, "Oyoyo, welcome my daughter..." Leemarh ta miƙe tana murmushi, momy na ƙarasowa wurinta ta rungume ta, ɗago ta ta yi ta ce, "Daughter sannu da zuwa, saukan yaushe?" Leemarh ta bata amsa da basu daɗe da zuwa ba ita da dad, momy ta tambayi sauran yan'uwanta da mom ɗinsu ta ce mata duk suna lafiya suna gaishe da su, momy ta ce ta zauna tare da kallon Binafa ta ce mata ta je kitchen ta sa akawo ma Leemarh abun sha ta amsa tare da nufar kitchen, momy ta zauna tare da kallon Fahad ta yi masa sannu da dawowa ya amsa, ƴar hira ta shiga yi da Leemarh kafin Binafa ta dawo riƙe da tray mai ɗauke da jug da cup a sama, bayan ta ajiye a saman center table ta zuba ma leemarh, momy dake murmushi ta ce ma Leemarh ta sha zobo ta amsa tare da yin godiya, sosai zobon ya yi ma Leemarh daɗi tana murmushi ta kalli momy ta ce mata ya yi daɗi, momy ta ce mata ta ƙara mana dama ba a daɗe da aka haɗa shi ba ta gaji da lemu shine ta saka aka haɗa, bayan Leemarh ta ƙara sha ta juya ta kalli Fahad dake zaune yana ta bin su da ido ta ɗan yi masa murmushi, sai kuma ta zuba zobon ta tashi ta miƙa masa tana faɗin, "Yaya Fahad ga shi kaima ka sha." Amsa ya yi tare da yi mata godiya, momy ta yi murmushi, Sadeeya ce ta shigo falon tana sanye da rigar wanka da hula, lokacin da Binafa ta je sanar mata game da zuwan Leemarh ta shiga wanka, nufo cikin falon ta yi cike da murna cikin ɗan ƙaraji take faɗin, "Oyoyo my namesake..." Miƙewa Leemarh ta yi tana ƴar dariya ta nufe ta suka rungume juna, gyalen rigan Leemarh ya zame ƙasa hakan ya bayyanar da baƙar sumarta da ke a fake an lanƙwashe ta, cikin washe baki Sadeeya ta ɗago ta ce, "Ina wanka ban san kin zo ba, ke da wa kuka zo? Ko ku duka?" Leemarh ta bata amsa da ita da dad ne kawai, Sadeeya ta tambayi dad ɗin ta ce yana gidan hajiya, "Amman na ji daɗin zuwan ki sis irin sosai ɗin nan don an kwana biyu ba a haɗu ba. Ina su Omar su ya basu zo ba, ko baya ƙasar?" Leemarh ta ce, "Ya Omar yana nan ya ce zai zo, su Batool kuma za su je Kano ne da mom, amman suma dad ya ce duk za su zo bada daɗewa ba." Sadeeya ta ɗaga mata kai tana ta mata murmushi kafin ta kuma cewa, "Hope dai hutun kika zo mana kamar yadda yaya Fahad ya faɗa cewa za ki zo nan hutu." Leemarh ta ɗaga mata kai alamar eh, Binafa ta ce, "To ina box en kayan ki?" Leemarh ta ɗan buɗa mata ido ta ce, "Ban zo da su ba, na ki zan rinƙa sakawa." Binafa ta ɗan waro ido sai kuma ta yi dariya ta ce ai kayanta ba zasu yi mata ba sai dai in na yaya Sadeeya suma kuma ba lalle su yi mata ba saboda ta fita jiki, Leemarh ta yi murmushi ta ce mata wasa take kayanta na gidan hajiya, a ɗokance Binafa ta ce to sai su je a ɗauko, Sadeeya ta kama hannun Leemarh ta ce su je ɗakinta ta shirya, momy ta ce ya zata ja ta ko abinci bata ci ba, Sadeeya ta ɗaga mata hannu tana faɗin ai shiryawa kawai zata yi su fito, suna kai wa daidai za su shige inda bedroom suke Leemarh ta juyo da niyyar satar kallon Fahad, idanunsu suka shiga cikin na juna ashe shima bin ta ya yi da kallo, a tare suka sakar ma juna murmushi mai taushi. Sageer tsaye a tsakar gida idanunsa akan wayarsa yana latsa ta ya ci gayu da shadda ruwan ƙasa, ya saka hula da takalma har da agogo ya yi tsaf da shi, bayan ɗan lokaci ya ɗago kai a ɗan harzuƙe ya ce, "Da Allah malama kina 6ata ma mutane lokaci, wllh idan baki fito ba zan yi tafiya ta in barki...." Innarsu dake tsaye a bakin baranda tana murmushi ta ce, "Aikuwa da Kubra ta maido ka tun da dai dama ita ce ƙarfin tafiyar." Ƙwafa Sageer ya yi ya ce, "Wllh ba don ina son zuwa Kadunan ba da zan ƙyale ta ne ta tafi ita kaɗai ai tana iya zuwa." Innarsu na yar dariya ta ce tun da dai shi aka ce ya kaita dole taren za su tafi, fitowa Salma ta yi daga cikin ɗakinta hannunta guda riƙe da trolley, tana sanye da riga da skirt na lace ta yafa gyale da ya hau da kayan, kafafunta ta saka takalma half cover masu ɗan tsini, ɗayan hannun ta riƙe yar madaidaiciyar jaka da ta hau da takalmanta, sosai ta ƙara kyau a cikin shigar, nufo su ta yi idanunta akan Sageer da ya tamke mata fuska dama duk tana jin abubuwan da yake faɗa, daga gefen shi ta tsaya tare da ajiye trolley ɗin tana ƴar dariya ta ce, "Man Sagir gani na fito." Ya wurga mata harara, Imrana dake tsaye sukuku da shi yana kallon ta ya ce, "Yaya Salma sai yaushe zaki dawo?" Hannu ta kai tana murmushi ta dafa shoulder ɗinsa ta ce, "Ai dai yanzu ba makaranta tun da an yi hutu balle ka damu da ba mai yi maka assignment, da hutun ya ƙare ai zan dawo." Fuska a yamutse ya ce, "Ni ai ban son ki tafi wllh, gashi innarmu ta ƙi bari a je da ni." Ya ƙarasa yana ɗan kallon innar tasu, tana ƴar dariya ta ce aikuwa ba za a je da shi ba ai a yi abu na hankali mana sai su kwasa har su ukku su tafi, "Dalla malama ki wuce mu tafi ko so kike mu yi dare a hanya, dama ga hanya ba kyau salon ki ja aje a ƙwamushe mutum." Dariya Salma ta saka ta ce, "Kada ka damu idan ma an ɗauke ka zan tara kuɗin fansar ka." Hannu ya kai zai ranƙwashe ta yana faɗin, "Shegiya dama ai na san ba ƙauna ta kike ba." Innarsu dake ta dariya ta ce, "In sha Allahu ma lafiya za ku isa." Hannu Salma ta kai ta dafa kan Hamza ta ce masa sai ta dawo shima duk ya yi sukuku ya ɗaga mata kai, kuɗi ta fiddo a cikin jakarta ta basu innarsu na ta kyale su ko jiya ba ta basu ba, tana dariya ta ce ai daga yau kuma sai ta dawo, Sageer ya kalli innarsu ya ce mata sun tafi, tana ɗan murmushi ta shiga yi masu addu'oin Allah Ya tsare ya kai su lafiya, Salma ta kalle ta tana murmushi ta ce mata sai ta dawo, "To Salmata Allah Ya kiyaye hanya." Salma ta amsa da Amin, ta kama trolley ɗin innarsu ta ɗauki wata babbar leda da ke ajiye suka nufi ƙofar fita gaba ɗayan su, bayan Sageer ya dauko jakar shi a ɗaki ya fito, suna fitowa waje wani napep ya zo wucewa Sageer ya tsayar masu, Salma nata ɗaga ma innarsu da su Imrana hannu ta shiga cikin napep ɗin, Imrana da Hamza na ganin za su tafi suka fara kuka, jikin Salma duk ya yi sanyi tana ta kallon innarsu, lokacin da mai napep ɗin zai ja ta ɗan ɗaga murya ta ce, "Innata, Imrana, Hamza, I will miss you all." innarsu ta ɗan girgiza kai kawai tana dan murmushi, a can ƙasan ranta kuwa tuni har ta fara jin kewar ɗiyar tata. Suna kan hanyan zuwa tasha Salma ta ce ma Sageer don Allah su tsaya garejin su babansu dake a kan hanya ta ƙara yin bankwana da shi da Auwalu duk da sun yi da safe, suna zuwa daidai wurin Sageer ya ce ma mai napep ɗin ya ɗan tsaya da su, fitowa Salma ta yi tana kallon baban su dake cikin yin aiki, cikin ɗan ɗaga murya ta kira shi, yana ganinta ya ajiye abun da yake yi ya yi ma Auwalu magana a tare suka nufo inda suke, Salma nata masu murmushi bayan sun ƙaraso baban su ya ce, "Mamana za a tafi?" ta ɗaga masa kai, addu'oin Allah ya kiyaye hanya ya shiga yi masu haka shima Auwalu, babansu ya kalli Sageer dake tsaye ya ce, "Don Allah Sageer ka kula da ita sosai." Yana murmushi ya ce, "To ni kuma wa zai kula da ni baba?" Duk suka ɗan yi dariya, baban ya ce ai shi kamar matsayin jagoranta ne a tafiya, sallama babansu ya yi masu ya ce su tafi kada dare ya yi masu, kuɗi ya fiddo daga cikin aljihunsa ya miƙa ma Salma ya ce su sha ruwa a hanya, tana murmushi ta ce ya bar su akwai kudi a wurinta, ya ce duk da haka dai ta amsa, bayan ta kar6a ta yi masa godiya daga haka suka koma cikin napep ɗin, suna ta ɗaga ma juna hannu har suka tafi, bayan sun iso motor park cikin sa'a suka samu motan dake lodin Kaduna kuma mutum ukku suka rage yanzu saura passenger ɗaya kawai su tafi, bayan an shiga da kayan su Salma ta shiga ta zauna, tunawa ta yi da idan ta ɗan daɗe bata yi tafiya ba wani lokacin tana yin amai, ta windown motan ta leƙa ta kira Sageer da bai shiga cikin motan ba yana tsaye yana latsa waya, waigowa ya yi kafin ya matso saitin ta ya tambayi ya aka yi, kuɗin hannunta da babansu ya bata ta miƙa masa ta ce, "Don Allah na ga mai lemu a bakin tashan ka ɗan siyo mani, ka san idan na daɗe ban yi tafiya ba wani lokacin ina yin amai." Wani kallo ya yi mata ya ɗan yamutsa fuska ya ce, "In an gan ki dai kamar wata wayayya amman ƴar ƙauye ce mai yin amai a mota." Salma ta ɗan ɗaure fuska ta ce, "To ai dai lalura ce kuma ba kaina farau ba." Ya ce to bai siyo lemun, daga haka ya bar wurin ba tare da ya amsa kuɗin ba, komawa ta yi cikin motan tana tunanin ko ta fita da kanta ta siyo duk da ba lalle ta yi aman ba amman lemun zai taimaka mata saboda tashin zuciya, muryar Sagir ta ji ya kira sunanta ta juya ta kalle shi ta windown motan, ledar lemu ya miƙo mata ta amsa tare da yin murmushi ta ce, Thank you my bro, I love u" ɗan harararta ya yi ba tare da ya ce komai ba, bada jimawa ba aka samu cikon passenger guda ba 6ata lokaci suka hau hanya sai fatan Allah Ya sauke su lafiya. Da sallama daddy Sa'ad ya shigo cikin falon, hajiya ta juya tana amsawa ganin su ta shiga yin murmushi, dad Ibrahim yana riƙe da wayar hajiya yana yin waya da ƙanwarsu hajiya Murja bayan ta kira hajiya shine aka bashi suke magana, ya ɗaga ido da murmushi yana kallon yayan nasa dake ƙarasowa ciki, daga gefen hajiya alhaji Sa'ad ya ɗan rankwafa ya gaishe da ita tare da yi mata barka da juma'a, fuskarta da murmushi ta amsa masa, kallon su Sadeeq ta yi tana amsa gaisuwar da suke yi mata ta kai hannu ta kamo Ayden zuwa jikinta tana tambayarsa ana ta shan hutu ba school ko yana murmushi ya ɗaga mata kai, daidai lokacin da daddy Sa'ad ya miƙe dad ya gama yin wayar, miƙewa ya yi da faffaɗan murmushi ya miƙa ma yayan nasa hannu yana gaishe da shi, da fara'a dad Sa'ad yake amsa masa tare da yi mashi an zo lafiya, a saman kujerar da yake ya zauna shima dad ya koma ya zauna, dad Sa'ad ya tambayi iyalinsa ya amsa masa da duk suna lafiya suna gaishe da su, Sadeeq ya matsa ya ce, "Daddyn Abuja ina wuni, an zo lafiya." Dad ya miƙa masa hannu ya ce, "Sadeeq my boy, lafiya lau, ya school koda yake an yi hutu ko?" Sadeeq ya ɗaga masa kai, kallon Ayden dad ya yi ya miƙa masa hannu yana cewa ya zo su gaisa hajiya ta ce masa ya je, shima Ayden ya gaishe shi dad ya kama hannunsa da faffadan murmushi ya ce masa ana ta hutun school ko ya ce masa eh. "Sai ku ka ga ƴar hutu." Hajiya ta faɗa idanunta akan daddy Sa'ad, da murmushi ya ce, "Haleematu, aikuwa suna can ita da ƴan'uwan suna ta farin cikin ganin juna." Hajiya ta ce, "Allah Sarki, an kwana biyu ai ba su ga juna ba." Hira daddy Sa'ad da dad suka shi ga yi, hajiya nata kallon su fuskarta cike da ƙauna, tana jin daɗin ganin yaran nata a tare, Balaraba ce ta shigo cikin falon, ta ɗan rankwafa da gaishe da daddy Sa'ad ya amsa mata cikin sakin fuska, wurin hajiya ta nufa cikin ladabi ta sanar da ita ta shirya abinci a table, hajiya ta jinjina mata kai, kallon su ta yi ta ce masu ga abinci can an shirya, ganin sun yi shiru ta ce ko sai sun dawo daga salla, daddy Sa'ad ya duba agogon wrist ɗin sa ya ce ai lokacin sallan ma ya yi, dad ya ce ko a bari sai sun dawo daga sallan hajiya ta ce to. Tun da su Salma suka hau hanya lokaci bayan lokaci aunty Kubra ke kira tana yi masu ya hanya tare da tambayar sun zo ina, daga ji ta ƙagara su isa, lokacin da suka isa Kaduna suna shiga cikin motor park ta sake kira Salma ta sanar da ita ga su yanzu sun iso tasha, ta ce ok itama gata nan daidai zata shigo cikin park ɗin, Salma na fitowa daga mota lokacin motan aunty Kubra ta shigo ciki, murmushi ta shiga saki aunty Kubra da ta hango ta ta nufo in da take, bayan ta faka motan gefe ta buɗe ta fito, tana sanye da Abaya mai kyau ta naɗa gyalenta fuskarta ta saka glasses ta fito a wayayyarta, da sassarfa Salma ta nufe ta itama aunty Kubra ta nufo ta ta wara mata hannu, Salma ta faɗa jikinta tana dariyar farin cikin ganin auntynta, sosai aunty Kubra ta rungume Salma tana jin wani irin farin ciki a ranta, ɗago ta aunty Kubra ta yi ta cire glasses din fuskarta, cike da farin ciki ta furta, "Welcome babynah, I'm so glad to see you." cikin washe baki Salma ta ce, "Nima haka aunty Kubrana." Ƙara rungume ta aunty Kubra ta yi tare da ɗan lumshe ido, "Da alama ita kaɗai kike murnar gani." Sagir ya faɗa yana tsaye kusa da su, jin maganar shi ya sa aunty Kubra ta ɗago Salma daga jikinta ta kai idanunta kan Sagir da ya ɗan ɗaure fuska, dariya ta yi tare da kai hannu ta taba kafaɗarsa ta ce, "I'm sorry man Sagir nawa, ka san idan na ga babyna idanuwan nawa rufewa suke." Sagir ya ce, "To ai da ba a gayyaci mutum ba..." Dariya ta saka tare da ɗan bugun shoulder ɗinsa ta ce, "Wai har yanzu baka daina kishi da baby ba ke nan." Dan murmushi ya yi ya ce wani abun ba dole mutum ya yi kishin ba, ta gayyato shi ya kawo ta amman ta ba banza ajiyarsa kamar Salman ce kaɗai ta zo, dariya sosai aunty Kubra ke yi ta ce, "To tuba nike kada in ja a ce baza a ƙara kawo mini ita ba." Tambayar shi ta yi kayan su ya nuna mata su a gefe an fito da su, tare da ita suka ɗauki kayan suka saka a cikin boot din motar ta, a seat ɗin gaba aunty Kubra ta sa Salma ta zauna shima sai da Sagir ya yi mita, aunty Kubra tana dariya ta ce mashi ya yi haƙuri ya zauna a bayan shi da ma aka bar ma gaba ɗaya back seat ɗin yadda zai wataya, Salma dai dariya take ta yi ganin yadda Sagir ke ta nuna jin haushin abubuwan da aunty Kubra ke mata, bayan Sagir ya shiga baya aunty Kubra ta shiga driver seat ta ja suka bar cikin tashar..... 09013804524, 08169856268 for more info. *✨A CIKIN RAYUWA✨* ZAINAB BATURE Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai. 44 Bayan sun iso gidan aunty Kubra ta saka Sagir ya fita ya buɗe masu gate, ta kutsa motar cikin gidan, Salma data fito ta bi gidan da kallo don ba shine gidan da ta san auntynta a ciki ba, Sagir ya kulle gate ya nufo su shima yana kallon gidan wanda ƙaramin estate ne mai ɗauke da gidaje biyu, boot aunty Kubra ta buɗe ita da Sagir suka fiddo da kayan su, koda Salma ta zo zata ɗauka hana ta ta yi ita ta kama trolley ɗin ta shi kuma Sagir ta ce ya ɗauko jakarsa da ƙatuwan ledan, da ɗayan hannunta ta kama na Salma suka nufi cikin gidan inda part ɗinta yake, bayan sun shiga cikin falo nan ma Salma ta bi shi da kallo, aunty Kubra tana murmushi ta ce, "Baby kin ga gidan da nike yanzu ba wanda kika sani ba." Salma ta ɗaga kai ta ce, "Amman yana da kyau." aunty Kubra ta ce, "Eh ba laifi, 2 bedroom ne sai kitchen da store." Salma ta ɗaga kai, aunty Kubra ta tambayi Sagir kayan sa ya ce mata jakar hannunsa ce, nuna masa ɗayan bedroom ɗin ta yi ta ce ya kai ciki nan ne ɗakin da zai zauna, kallon ledan da ya ajiye ta yi zata ɗauka da trolley ɗin hannunta ta kai ɗakinta wanda anan Salma zata zauna, Salma ta ce mata tsarabar ta ce a cikin ledan hakan ya sa ta ajiye ta a nan tana faɗin ta gode bari ta fito ta ga tsaraban da aka yi mata, Salma ta bita ɗakin tana fadin bari ta yi salla suka shiga tare, shima Sagir sai da ya yi salla sannan ya fito, a nan cikin falon saman carpet aunty Kubra ta baje masu kayan abincin da ta haɗa masu, ita kuma tana zaune tana duba uban kayan tsaraban da aka yo mata fuskarta cike da jin daɗi tana ta yabawa, wayarta dake a gefe ta fara yin ringing, bayan ta yi picking call ɗin ta kai kunne, daga ɗayan 6angaren innarsu Salma ta amsa mata sallamarta kafin ta ce, "Kubra sun iso kuwa? Inata kiran wayar Sagir a kashe ita kuma Salma wayar tana ta yin ringing amman bata ɗagawa" Yanayin muryarta akwai alamun damuwa, Aunty Kubra da idanunta ke akan su Salma tana ɗan faffaɗan murmushi ta ce, "Har yanzu basu ƙaraso ba yaya Fiddausy, kuma yadda kike ji nima hakan ne idan na kira." Cike da damuwa innarsu ta ce, "To Allah Ya sa dai lafiya, wllh baki ji ba har hankalina ya fara tashi." Jin da gaske a yanayin muryarta akwai alamun damuwa ya sa Aunty Kubra yin dariya ta ce, "Wasa nike maki yaya Fiddausy kin gan su nan tuni ma suka iso ga su suna cin abinci, shi Sageer wayarsa ta mutu ga ta can ya saka caji, ita kuma baby tata tana can cikin jakarta a ɗaki." Tana jin yarda innar tasu ta saki ajiyar zuciya tare da furta Alhamdulillah, aunty Kubra na dariya ta ce, "Su yaya Fiddausy mai ƴaƴa wato har hankalinki ya tashi." Innarsu ta yi dariya ta ce, "Ba dole hankalina ya tashi ba Kubra abu har da ƴar zuƙeƙiyar budurwar ɗiyata." Dariya sosai aunty Kubra ta saka, Sagir da ya tura abinci baki duk suna jin abun da innarsu ke faɗi saboda a speaker aunty Kubra ta saka kiran cikin ɗaga murya ya ce, "Wato innarmu damuwarki akan ta ne ko, ni kuma ko oho in kin rasa ni." Daga cikin wayar innarsu tana dariya ta ce, "Ba haka bane Sagiruna, saboda ita kaɗai ce yar macen tawa na faɗi hakan amman ba ina nufin kai ban damu da kai ba." Sagir ya ce, "Uhmm, ni ai da yake akwai wasu ke nan ko." Tana dariya ta ce a'a shima ta damu da shi, aunty Kubra ta ce wai haka take fama da kishin Sagir akan baby, innarsu ta ce uhm ai don ma ba tare suke ba da ta ga abu sai ka ce wata kishiyarsa, yar hira suka ƙara yi kafin suka yi sallama. Ba ƙaramin daɗin kasancewar su Sageer aunty Kubra ke ji ba, koda yaushe ta je aiki ta dawo zata iske gidan tsaf sun gyara mata shi har abinci Salma ta yi, sai dai ta ci ta huta, cikin ranakun da ba aikin rana take ba ko kuma tana off haka zata ɗauke su a mota su fita zaga gari har ta yo masu siyayyar kayan ƙwalama, sai da Sageer ya samu filin da yake zuwa yana buga ball a unguwar, sosai ya yi farin jini wurin waɗanda suke yin ball ɗin tare da sauran mutane ƴan kallo ba kamar da suka ji yana a cikin sabon team ɗin Deen Jr na Funtua. Satin Sageer biyu ya shirya komawa Funtua, kafin ya tafi aunty Kubra ta ɗauke su suka je kasuwa ta yi masa siyayya mai yawa har da su innarsu da su imrana duk sai da ta siya masu abubuwa, ranar da zai tafi a motar aunty Kubra tare da Salma suka raka shi tasha, sosai aunty Kubra ta yi masa godiya da addu'an Allah Ya kai shi lafiya, Salma na dariya ta ce, "Man Sagir Allah Ya tsare hanya sai na dawo." Ya yi mata wani kallo mai kaman harara ya ce, "Dama ki zauna a nan kowa ma ya huta." Aunty Kubra dake yin dariya ta ce, "Cika baki kawai, ka dai san ni hakan nike so ai, amman ba zaku bar min ita ba, nan lokacin da take wurina kafi kowa azalzalar mutane kan ta koma." Sagir na dariya jikinsa sanye da sababbin jeans da t-shirt a cikin kayan da aunty Kubra ta saya masa har takalman kafansa duk sababbi ne, ya ce, "Allah aunty Kubra yanzu idan kina son ta zauna mun bar maki." Aunty Kubra ta ce, "Saurin mi kake yi, in sha Allah next year by now muna tare." Sallama suka yi da juna don an fara sanarwar fasinjoji su shiga cikin mota za a tafi, Salma nata ɗaga masa hannu har ya shige cikin mota, sai da suka ga tashin su sannan suma suka shiga mota suka tafi. Leemarh tana ta shan hutun ta a Funtua gidan su Fahad, wani lokacin tana zuwa gidan hajiya ta kwana ko ita da Binafa, sosai ƴan gidan su Fahad ke jin daɗin kasancewarta a gidan ba kamar yadda ta sakar ma yaran jiki sosai ta maida Binafa kamar wata ƙawarta, shaƙuwa sosai ce ke ƙara shiga tsakaninta da yaya Fahad, har ta kai wani lokacin bata cin abinci sai ya dawo daga aiki su ci tare, wasu lokuttan idan ya dawo da wuri haka zai ɗauke ta da dare su fita su zaga gari ya siya mata abubuwan ƙwalama, part ɗin shi ma ita ce ke gyara masa, koda yaushe ya dawo haka zai iske shi fes yana ta ƙamshi, har ƙananan kayansa take wanke masa a washing machine idan sun bushe ta goge masa, duk da yana ce mata ta daina wahalan hakan amman ta ƙi bari sai dai ya yi mata godiya da nuna jin daɗin abubuwan da take masa, ko a wurin aiki lokaci bayan lokaci take kiran sa ta yi masa ya aiki, hakan ya sa shima da ya samu lokaci sai ya kira ta ya ji ya take, ku san koda yaushe idan zai dawo daga aiki sai ya dawo mata da wani abu matsayin tsaraba, ku san dai soyayya suke da juna ba tare da sun furta ba, hatta ƴan gidan sun fahimci shaƙuwar su har mom ɗin su. Da yamma suna zaune a falo gaba ɗaya waɗanda ke a gidan ban da Sadeeya da Khaleel da suke makaranta, duk idanunsu na akan babbar tv ɗin falon suna kallon indian drama har da momy, sallamar da suka ji an yi ta sa suka kai idanunsu wurin ƙofan shigowa, lokaci guda Leemarh ta saki ƙayataccen murmushi ganin wanda ya shigo, miƙewa ta yi ta nufe shi jikinta sanye da riga iya gwiwa da wandon ta da ya matse daga ƙasa kanta ta saka hula, daga gabansa ta tsaya tana murmushi ta ce, "Sannu da dawowa ya Fahad." Shima murmushi ne akan fuskarsa ya amsa mata tare da yi mata ya gida, ɗan juyawa ta yi kafin ta maido idonta kan shi ta yi ƙasa da murya ta ce, "Duk wani iri nike ji ba daɗi saboda baka nan." Still da murmushi akan fuskarsa ya yi mata wani kallo ya ce to gashi ya dawo, hannu ta kai ta amshi yar jakar hannunsa suka ƙarasa cikin falon, duk su Binafa suka yi masa sannu da dawowa ya amsa, a kujeran gefe ya zauna ya kalli mom ɗinsa ya gaishe da ita, tana murmushi ta amsa ta yi masa ya aiki, Leemarh dake tsaye ta kalle shi ta ce, "Na shirya maka abinci?" Yana kallonta ya ce mata ta bari sai ɗan anjima baya jin yunwa yanzu, miƙewa ya yi ya miƙo hannu zai amshi jakar tana murmushi ta ce bari ta kai mashi sama ya ce ta basshi ba sai ta yi wahala ba tun da saman zai je, mom dai ta ɗauke idanunta daga kan su tana ɗan murmushi don zuwa yanzu ta fara zargin shaƙuwar tasu da wani abu, bayan ya amshi jakar ya bude, fiddo wata farar leda ya yi mai tambari a jiki ya miƙa mata, ta amsa tana murmushi tare da yi masa godiya, ya nufi bene ya haye zuwa part ɗinsa, buɗe ledan Leemarh ta yi ta fiddo abubuwan da ke ciki, su tuwan madara, peanuts, gullisuwa, popcorn da sauran tarkace dai wanda dama yana kawo mata su, buɗewa ta yi suka fara ci har da momy don ko ta ce baza ta ci ba haka zata matsa mata sai ta ci, shiyasa yanzu da ta bata abu take amsa ta yi godiya, suna cin abubuwan suna yin kallo, after some minutes Fahad ya sauko cikin falon da alama wanka ya yi ya saka jallabiya mai gajeran hannu sai ƙamshi yake saki, Leemarh ta ɗaga ido tana kallon sa da murmushi har ya ƙaraso ya zauna, miƙewa ta yi ta kai mashi sauran abubuwan ta ce gashi shima ya ci, tuwon madara guda biyu kawai ya ɗauka ya ce mata ya isa, zata koma ta zauna ya ce ta kawo masa lemu mai ɗan sanyi, tana kallon shi ta ce akwai wanda ta haɗa masu ɗazun bari ta kawo masa ya ɗaga kai, bin ta ya yi da kallo ya yin da ta nufi kitchen, mom ta ɗan saci kallon sa ganin yadda ya bi Leemarh da ido ta juyar da fuskarta tana ɗan murmushin tabbatar da zargin da take yi, dawowa Leemarh ta yi riƙe da tray ta ɗauro glass jug ana ganin ruwan lemun ciki da cup, bayan ta zuba a cup ta bashi ya amsa yana murmushi ya yi mata godiya, komawa ta yi inda ta tashi ta zauna ta ci gaba da yin kallon, "Yaya Fahad ya yi daɗi ko?" Binafa ta tambayi Fahad ganin yana ƙara lemun ya ɗaga mata kai kawai, "Ai daughter masha Allah ta iya abubuwa masu daɗi." Momy ta faɗa tana kallon Leemarh da murmushi, Leemarh ta kalle ta tana murmushi ba tare da ta ce komai ba,, "Ban yi tunanin ma kina yin girki ba a gida." Momy ta sake faɗa, Leemarh ta ce, "Eh ba a saka ni, kawai ni ce ke son yi shine wani lokacin nike zuwa ina koya a wurin su chef Alima." Momy ta jinjina kai ta ce, "Aikuwa hakan abu ne mai kyau sosai, don iya girki shine cikar mace, ba zaki gane amfanin hakan ba sai idan kin yi aure, don yana ƙara ma mace ƙima da daraja a wurin mijinta." Leemarh ta sunkuyar da kai tana murmushi, a hankali ta ɗaga ido ta saci kallon Fahad ta ga ita yake kallo, ya saki ɗan murmushi tare da janye idanunsa, "Yauwa yaya Leemarh ga ƴar indiyan nan da muka ce maki kuna kama." Sadeeq ya faɗa da sauri, Leemarh ta ɗaga ido tana kallon wadda yake magana a tv, momy ta ce ai da gaske suna kama sosai, Binafa ta ce, "Har gashin ku ma tsawon shi ɗaya." Leemarh na murmushi ta ce anya wannan bata fita gashi ba, hannu Binafa ta kai ta cire mata hula tare da zame ribbon ɗin data naɗe sumarta tana faɗin bari a ga wanda ya fi gashi tsakaninta da ƴar indiyan, gashin Leemarh ya baje a bayanta, duk kowa ya ce kusan tsawon gashin su ɗaya da ita, "Amman daughter bakya yin kitso ne kwata kwata?" Momy ta tambaya idanunta akan gashin Leemarh, ta ɗan yamutsa fuska ta ce, "Ina daɗewa ban yi ba, saboda yawan gashin ina jin wahalan zama a yi mani kitso, idan aka yi mani sai in kasa kwance shi kan lokaci, shiyasa ma ban cika son yi ba." Momy ta gyaɗa kai alamar ta fahimta, ta ce ai da yake gashin nata kamar ba mai lalacewa bane idan ana barin shi ba kitso, Leemarh ta ce eh baya komai da ta gyara shi ta saka mai shike nan, "Dama ni ke da irin gashin ki yaya Leemarh " Binafa ta faɗa tana tatta6a gashin, momy ta ce da kuwa an ga kankamba duk suka yi dariya, "Ai da wani na iya cire gashi ya ba wani da na cire na baki, don ni takura mani yake yi, inda ba laifi mutum ya yanke gashi da na yanke shi na bar shi iya shoulders ena." Leemarh ta faɗa, momy da ke murmushi ta ce, "Ah daughter ki bar gashin ki, ai shima cikar kyawun mace ne." Murmushi kawai Leemarh ta yi, momy ta ce ma Binafa tatta6a gashin ya isa hakanan ta ƙulle mata abu, duk Fahad na kallon abubuwan da ke faruwa, bayan ɗan lokaci Sadeeq ya ce, "Yaya Leemarh yau wani abinci mai dadi zaki yi mana mu ci da dare?" Kafin ta ce wani abu momy ta riga cewa, "Yau ba wanda zai wahalar da ita, idan ba zaku ci tuwo ba ku bari, sai dai idan ita ce bata son tuwon." Tura baki Binafa ta yi sai kuma ta yi saurin kallon Leemarh ta ce, "Ai yaya Leemarh kema baki son tuwon ko?" Ƴar dariya ta yi ta ce tana son shi yana mata daɗi don ba a cika yi masu shi ba mom ɗinsu bata so sai idan dad ya ce yana so ake yi, roƙon ta suka shiga yi kan ta yi masu wani abun kamar yadda take masu duk dare ta haɗa masu wani abu mai daɗi saboda basu son cin tuwo, tambayar su ta yi akwai dankalin turawa ta ga kaman jiya ya kusa ƙarewa, da sauri Binafa ta ce ai an kawo ɗazun, ta ce to bari ta yi masu Sultan Chips, miƙewa suka yi tare da Binafa za su wuce kitchen, momy ta kalli Sadeeq ta ce shima ya bi su a yi wahalan da shi tun da sun hana ta ta yi kallonta, har Leemarh ta wuce sai kuma ta nufi wurin Fahad ta ce, "Zaka ci kai ma in yi da kai?" Ya bita da kallo kaman ba zai ce komai ba sai kuma ya ɗan ɗaga mata kai alamar eh, ta yi murmushi ta ce ok, mom dai ta kauda idonta, ba da jimawa ba aka fara kiran sallan magrib momy ta miƙe ta nufi part ɗinta shima Fahad ya fita zuwa masallaci. Bayan sallan issha Leemarh ta shigo cikin falon Fahad tana riƙe da madaidaicin tray, Fahad na zaune a saman doguwar kujera ya miƙe kafafunsa yana yin kallo ya juya yana kallon ta har ta ƙaraso, sauke ƙafafunsa ya yi ta daura tray ɗin a saman kujeran tana faɗin bari ta matso da table, tambayarta ya yi ita ta ci ne ta ce a'a tare ta zubo masu, nuna mata ɗayan side ɗin kujeran ya yi ya ce su ci a nan, zama ta yi ta yadda sun saka tray ɗin a tsakiya, buɗe plate da ta rufo abun ta yi nan da nan ƙamshin shi mai daɗi ya karaɗe wurin, a ido ma ya yi mashi kyau sosai, miƙa masa fork ta yi ya amsa suka fara ci a natse, lokaci bayan lokaci suke ɗaga ido su kalli juna cikin ido tare da sakar ma juna murmushi, bayan sun yi nisa cikin cin abincin ta ga ya dakata tare da ajiye fork ɗin ta ɗaga ido ta kalle sa, calmly ya ce "Why kike son ki yanke gashin ki?" Ɗan buɗa ido ta yi alamar mamakin ashe ya ji maganan ɗazun, da sigar shagwa6a ta ce, "Gashin ne ke takura mani gashi ina jin wahalan zaman kitso saboda yawan shi." Shiru ya yi yana ta kallonta, ta ɗaga mashi gira ta ce, "Ko baka son in rage ɗin?" Ɗan murmushi ta ga ya yi slowly ya ɗaga mata kai, sai kuma ya ce yana ƙara mata kyau, tana murmushi ta ce to bazata yanken ba ai dama babu kyau, "Zan koya yadda ake kitson sai in rinƙa yi maki idan kina so." Ta ɗan wara ido alamar mamaki, ba ta yi zaton zai iya furta mata maganar ba, ɗage gira ya yi ya ce ko bata so, tana murmushi ta ce tana so, sai kuma ta ce, "Yaushe zaka rinƙa yi mani tunda da hutu ya ƙare zan tafi." Ya yi shiru kaman ba zai ce komai ba yana ta kallonta, itama idanunta na a cikin nashi, ya yi ƙasa da murya ya ce, "Bada jimawa ba zamu kasance tare." Shiru suka yi suna ta kallon juna cikin ido, kasa jure ma kallon Leemarh ta yi ta sunkuyar da kai zuciyarta na bugawa da sauri, ji take kamar ta furta masa kalmar da ta maƙale mata a baki, gani ta yi ya kawo fork din chips bakinta, ta ɗaga ido ta kalle shi kafin slowly ta buɗe baki ya saka mata......Aunty Kubra ta turo kofar bedroom ɗin ta shigo, dama bayan Sageer ya tafi Salma ta koma tana amfani da shi duk da tare suke kwana da aunty Kubra a ɗakinta, Salma dake zaune a bakin gado tana latsa wayarta ta juya tana kallonta da murmushi, ɗan zamanta a nan har wani fresh ta kara yi, tsayawa aunty Kubra ta yi gefenta jikinta sanye da fararen kayan aiki ta ɗaura baƙar after dress sai ƴar ƙaramar farar hijab, hannunta guda tana riƙe da ƴar babbar baƙar jaka, "Baby kin shirya?" Salma ta ɗaga mata kai alamar eh, sai kuma ta ɗan langa6ar da kai ta ce, "Aunty Allah zan iya kwana ki tafi." Wani kallo ta yi mata ta ce, "Ta ya zan bar ki ke kaɗai ki kwana a gida." Salma ta ce, "To ai ga su maman Esther a ɗayan block ko." Aunty ta ce, "Wannan da bata dawowa daga shago sai cikin dare, ni dai taso mu tafi ai ba yau na fara zuwa dake aikin ba." Dariya Salma ta yi tunowa da can baya lokacin da tana wurin ta wani lokacin idan tana aikin dare sai dai ta tafi da ita, ɗaukar gyalenta da ke ajiye gefe saman gadon ta yi ta sauko tare da yafawa a saman dogowar rigar jikinta, bayan sun fito cikin falo aunty Kubra ta nuna mata wani food carrier dake ajiye saman carpet ta ce ta ɗauko daga haka suka nufi ƙofa suka fita... 09013804524, 08169856268 For more info. *✨A CIKIN RAYUWA✨* ZAINAB BATURE 45 Bayan sun iso asibitin, aunty Kubra ta faka motar a wurin da aka tanada don haka, a tare suka fito daga cikin motan Salma ta buɗe back door ta ɗauko food carrier ɗin, cikin maternity ward din da aunty Kubra take suka nufa, suna shiga staff suka shiga gaisawa da aunty Kubra daga gani suna girmama ta, wani matashin mutum ne ya fito ta wata ƙofa jikinsa sanye da baƙin wando da maroon riga mai ma6allai ya yi tucking rigar cikin wandon, wuyansa rataye da stethoscope, tsaf tsaf da shi sai sakin ƙamshi yake, a yanayin shekaru zai kai talatin da wani abu, wankan tarwaɗa ne kyakkyawa da shi da ganin fatarsa ka san hutu ya zauna masa, kana ganinsa ba sai an faɗa ba zaka gane likita ne, dakatawa ya yi gaban aunty Kubra da murmushi ya gaishe da ita, ta ce, "Dr Hisham barka da dare, kana on call ne?" Amsa ya bata da eh, "Tare zamu kasance ke nan." Ta faɗa tana murmushi, kallon Salma da ke gaishe da shi ya yi ya amsa mata da murmushi, maida idonsa ya yi kan aunty Kubra ya ce, "Aunty Kubra baƙuwa muka yi ne?" Ta ce masa eh tare suka zo, kai ya jinjina ya ƙara kallon Salma suka haɗa ido, "Aunty Kubra wacece ita don ban ta6a ganin ta kin zo da ita ba." Aunty ta yi ɗan faffaɗan murmushi ta ce, "She's my daughter." Sake kallon Salma da ke ɗan murmushi ya yi ya maida idonsa kan aunty ya ce ɗiyar ƴar'uwarta ko ɗan'uwanta? Aunty ta ce, "I mean my biological daughter" Ɗan kai idonsa ya yi kan Salma kafin ya kalli aunty da yanayin shakku, tana ƴar dariya ta ce, "Baka ga muna kama ba." Still sai da ya ƙara kallon Salma kafin ya ce gaskiya basu kama, "Na fi ta kyau ko?" Aunty ta tambaya, Dr Hisham yana ɗan murmushi ya ce in dai gaskiya za a faɗa Salma ta fita kyau, Aunty ta saka dariya ta ce, "Ka dai duba da kyau Dr, ni da nike fara ka kuma san fari kyau ne." Dr Hisham ya ce, "Aunty ai yanzu fari ba ya a cikin kyau tun da har na kanti ana siyarwa, kuma ita kalanta ma mai tsada ne ba a cika samun shi ma a cikin mutane ba sosai balle a kanti." Salma dai murmushi kawai take tana ɗan sauke idonta ganin yadda Dr ɗin ke yawan kallon ta, sake tambayar aunty ya yi game da Salma ta sanar da shi ɗiyar cousin sister ɗinta ce ta zo mata hutu ne, kuma itama tana son zama nurse kamar ita, Dr ya jinjina kai tare da kallon Salma ya ce, "You are welcome baƙuwar mu." A hankali ta yi masa godiya, aunty ta ce bari su kai kayan hannun su ciki sai sun haɗe a ward round ya ce ok ya wuce suma suka nufi ciki, bakin wata ƙofa suka zo aunty ta buɗe suka shiga, ɗan madaidaicin ɗaki ne akwai gado da yar side locker kalan na asibiti sai kujerar zama ta roba da ɗan madaidaicin fridge, a jikin window ɗin ɗakin an saka labule yayin da ƙasan ɗakin gaba ɗaya tiles ne, a saman drawer ɗin gefen gadon aunty ta ɗaura jakar hannunta, kallon Salma ta yi ta ce ta ajiye food carrier din ta nuna mata kujera ta ce ta zauna, wata ƙofa dake a cikin ɗakin aka buɗe suka kai idanun su wurin, wata ƴar dattijuwar mata ce ta fito hannunta riƙe da bucket da ƴar jarkar liquid soap a ciki, tana ganin aunty ta yi murmushi tare da gaishe da ita, aunty ta amsa tare da tambayar ta wanke toilet ɗin aka yi ta ce mata eh, sannu aunty ta yi mata matar ta amsa daga haka ta nufi ƙofa ta fita, jakar da ta ajiye ta kai hannu ta buɗe tare da fiddo wani ɗan madaidaicin zanen gado, farin yadin dake a saman gadon ta kai hannu ta cire bayan ta kakkabe gadon ta fara shimfiɗa wanda ta fiddo, Salma ta miƙe ta ce bari ta shimfiɗa ta bata ita kuma ta juya ta shiga toilet bayan ta cire rigar saman uniform ɗinta, bayan ta fito ta ce ma Salma za su je ward round sai ta dawo ta ɗaga mata kai, bayan ta kai ƙofa ta juyo ta ce, "Ga ruwan zafi nan a flask idan zaki haɗa tea, idan kina jin bacci ki kwanta a gadon." Salma ta amsa da to tare da yi mata sai ta dawo, bayan tafiyar aunty komawa ta yi saman gadon ta ɗan kishingiɗa tana latsa wayarta don bata jin yunwa ta riga ta ci abinci kafin su taho, after some few minutes da tafiyar aunty ta ji an yi knocking kofar ɗakin, ɗagowa ta yi tana kallon ƙofar jin an ƙara yin knocking ta ɗan ɗaga murya ta ce ƙofar a buɗe take, turo ƙofar aka yi tana ganin wanda ya shigo ta tashi zaune sosai tana kallon sa kamar yadda shima kallon nata yake, ɗan murmushi ya yi mata ya ce, "Baƙuwarmu ke kaɗai?" Kai ta ɗaga masa, ya tambayi aunty ta ce masa ta fita ta ce za su je ward round, kai ya ɗaga mata daga haka ya juya, sai kuma ta ga ya dakata tare da juyowa ya kalle ta ya ce, "Amman zaman ke kaɗai ba za ki ji kaɗaici ba?" Ta yi ɗan murmushi ta ce masa a'a, ya ce, "Ko da yake ai ga phone nan zata ɗebe maki kewa kafin ta dawo." Ita dai murmushi kawai ta yi, ya sake cewa, "Amman tun da fannin mu kike son karanta ai kamata ya yi aunty ta tafi da ke ward round ɗin ki fara samun experiance." Shiru ta yi tana kallon shi bata ce komai ba, "Idan kina so mu je sai ki fara ganin yadda abubuwan suke ko." Ya faɗa idonsa akanta yana ɗan murmushi, shiru ta ɗan yi sai kuma ta ji tana son ta je ɗin, saukowa ta yi daga saman gadon ta saka takalmanta ya yi mata alamar su je suka nufi ƙofa, bayan sun fito ya cire stethoscope ɗin wuyansa ya miƙa mata ya ce ta riƙe masa ta amsa sannan suka tafi, yana gaba tana biye da shi bayan sun fito nan suka haɗe da aunty Kubra ta taho wuyanta rataye da stethoscope, hannunta ɗaya wasu files ne ɗayan kuma na'urar auna BP, tsayawa suka yi aunty ta kalli Salma sai kuma ta kalli Dr ta ce, "Ko nema na take ne?" Yana murmushi ya ce mata a'a ya je wurinta ne ya iske bata nan sai ita kaɗai shine ya ce ta zo su je a yi ward round ɗin da ita don ta fara samun experience, aunty ta yi ƴar dariya ta ce kuma haka yakamata daga haka wuce, wani babban ɗaki suka shigo wanda gaba ɗaya majinyatan mata ne masu fama da lalurori daban-daban da suka shafi ciki da haihuwa, su ukku suka fara duba marasa lafiyan ita dai Salma tana biye da su, lokaci guda kuma jikinta ya yi mugun sanyi laƙwas saboda tausayin halin da marasa lafiyan ke ciki, lokaci bayan lokaci Dr Hisham ke ɗan kallo ta da murmushi yayin da yake bincikar majinyantan ya ce mata tana ganin yadda suke aikin ta ɗaga masa kai, sai dai a yadda take ji ma gaba ɗaya ta sare kamar ba zata iya jure ganin yadda suke duba marasa lafiyan ba, bayan sun gama da 6angare guda za su nufi ɗayan bangaren, aunty ta kalli Salma ganin ta ja ta tsaya, tana murmushi ta ce mata ya aka yi ne, cikin rawar murya ta ce, "Ɗakin zan koma." Dafa shoulder ɗinta aunty ta yi tana tambayar mi ya sa zata koma ko ta gaji ne, kawai sai gani ta yi ta fashe da kuka ta rufe fuskarta a jikinta, Dr Hisham da har ya fara duba wata ya ɗago yana kallon su, dawowa wurin su ya yi yana tambayar aunty lafiya mi aka yi mata, ɗago fuskarta aunty ta yi ta ce, "Mi ya faru ne baby?" cikin muryar kuka ta ce bazata iya ci gaba da bin su ba ɗaki zata koma, ƴar dariya aunty ta yi ta kalli Dr ta ce, "To Dr baƙuwar mu mai koyon sanin makamar aiki tausayi ba zai bari ta ci gaba da koyon aikin ba." Ɗan buɗa ido ya yi sai kuma ya yi yar dariya ya ce, "To baƙuwar mu a haka zaki yi irin aikin namu, dole aikin mu sai an cire tausayi sannan za a iya shi." Shiru Salma ta yi ta sauke idanunta ƙasa, aunty ta tambaye ta zata iya ci gaba da sauri ta girgiza mata kai alamar a'a, aunty ta kalli Dr ta ce pls bari ta maida ta ɗaki she will be back now, ya jinjina mata kai still da ɗan murmushi akan fuskarsa ya yi ma Salma sai da safe, ba tare da ta kalle shi ba ta ɗaga masa kai suka tafi, aunty bata daɗe ba bayan ta kai Salma ɗaki ta dawo, Dr na murmushi ya tambaye ta ya Salma ta ce tana can ta kai ta ɗaki, ya ce amman dai tana da tausayi sosai, aunty na ƴar dariya ta bashi amsa da haka take tausayi ne da ita sosai, Dr Hisham ya ce to wannan ma zata iya aikin asibiti, aunty ta ce da ta fara karatun dole zata bar tausayin. Salma ta ɗaga ido ta kallo ƙofa jin an turo, aunty ta gani ta shigo da alama sun gama ward round ɗin, nufo ciki ta yi tana kallon Salma da ta tashi zaune daga kwancen da ta ke tana kallon ta, daga gefenta saman gado ta zauna da ɗan alamun mamaki ta ce, "Wai baki bacci ba har yanzu?" Salma ta ɗaga mata kai duk ta yi sukuku da ita, aunty da ta lura da har lokacin a sanyaye jikinta yake ta kai hannu ta dafa nata hannun da ɗan murmushi ta ce, "Kin ga abubuwan da suka tada maki hankali ko, irin abubuwan da mata ke going through ke nan yawanci duk sanadiyar haihuwa....amman a haka wasu mazan basu da abun wulaƙantawa irin mace, wata ma don bata haihun ba ake wulaƙanta ta, ba don sanin ƴaƴa rahama ne ba wa zai yarda ya sha baƙar wahalan da ake sha wurin haihuwan..." Dakatawa ta yi tare da juya fuskarta tana kallon wuri daban, Salma nata kallonta tana jin tausayin ta a rai, can aunty ta sauke ƴar gajeruwar ajiyar zuciya ta ce, "Allah Ya sa kowace mace ta ci ribar haihuwa, ni dai na gode ma Allah don tuni na fara cin riban hakan..." Ta juyo ta kalli Salma tana murmushi, itama Salma murmushin ta yi don ta gane da ita take, hannu aunty ta kai ta kwanto da ita jikinta ta yi mata side hug, cikin sanyin murya ta ce, "Allah Ya ƙara ma rayuwar ki albarka baby, kullum addu'ata a gare ki Allah Ya baki miji wanda zai ƙaunace ki, ya kula da rayuwar ki ya ji tausayin ki." Salma ta yi saurin lumshe ido jin hawaye na niyyar taho mata, bata san wace irin ƙauna auntyn tata ke yi mata ba, ta damu da ita sosai wanda ko iyayenta iya damuwar da suke nuna mata ke nan, ɗan leƙen fuskarta aunty ta yi ta ce bata ce Amin ba, buɗe ido Salma ta yi tare da yin ɗan murmushi, aunty ta fahimci kunyar amsawa take, ta ce mata ta amsa ai addu'a ce aka yi da ta shafi rayuwar ta ba batun kunya, a hankali Salma ta ce, "Amin Ya Rabb, na gode da ƙaunar da kike mani aunty Kubra, ina roƙon Allah Ya biya maki dukkanin buƙatun ki na alkhairi." Aunty tana murmushi ta amsa mata da Amin tare da ɗan shafa fuskarta, "Kin sha shayin ne?" Salma ta girgiza mata kai alamar a'a, aunty ta ce, "Zaki sha in haɗa mana?" Kai ta ɗaga mata alamar eh, ɗago ta aunty ta yi ta ce tana zuwa, miƙewa ta yi ta nufi jakar ta ta bude ta ɗauki abu bayan ta rufe ta nufi toilet idanun Salma akanta, after some minutes aunty ta fito tana ɗaure da zani saman rigar aikinta ta yafo ɗan gyale a kanta, fuskarta da hannunta ɗauke da lemar ruwa, bayan ta zauna ta buɗe food carrier ta ciro flask ɗin ruwan zafi da cups ta fara haɗa masu tea. Washe gari da safe bayan aunty ta tashi daga aiki tare suka fito zuwa inda motarta take, nan suka haɗe da Dr Hisham shima zai tafi, dakatawa ya yi wurin su suka gaisa da aunty, ya kalli Salma suka haɗa ido, a hankali ta gaishe da shi ya amsa yana murmushi ya ce, "Baƙuwar mu kin daina kukan ko?" Ta ɗan ɗaga masa kai tare da sauke idanunta, ya ce haka yakamata ta yi masu addu'a Allah Ya basu lafiya, ta ɗaga masa kai ba tare da ta kalle sa ba, kallon aunty ya yi ya ce mata sai anjima ta amsa tare da yi mashi Allah huta gajiya, ya amsa yana nufar motarsa, Salma ta ɗago tana kallon navy blue motar da ya buɗe ya shiga mai kyau da ita, bayan aunty ta buɗe motarta suka shiga suma suka tafi. Sai da aunty ta biya da su wani babban wurin siyar da abinci da ta saba zuwa tana siyan abinci musamman idan ta taso daga aikin kwana, waina da miya da nama ta siya masu, ta tambayi Salma ko tana son wani abu a siya ta ce mata a'a wainar ma ya isa, bayan sun gama suka nufi gida. Ranar Asabar wuraren ƙarfe goma saura Leemarh ta gama shiryawa cikin wani haɗaɗɗan sky blue lace da ya matuƙar yi mata kyau, gaba ɗaya gyale da takalma da jaka kalar golden ta saka wanda shine adon leshin, ta yi kyau kamar a sace ta, bayan ta fito daga ɗakin da take zaune ita da Binafa, 6angaren momy ta nufa don ta yi mata sallamar tafiya Zaria da za su yi ita da Fahad, momy na zaune a falonta ta ɗaga ido tana amsa sallamar ta, ciki ta ƙaraso ta zauna akan kujera momy nata kallonta tana murmushi, gaishe da ita Leemarh ta yi momy ta amsa tare da cewa, "Daughter an gama shiryawa?" Ta ɗaga mata kai tana murmushi, momy ta sake cewa, "Ma sha Allah kin yi kyau sosai." Murmushinta ya ɗan faɗaɗa ta ce mata ta gode, tambayarta ta yi Fahad ɗin ya fito Leemarh ta ce a'a sai dai ta yi mashi magana, momy ta ce bari kawai ta kira shi, wayarta ta ɗauka ta fara kiran shi, bayan ya ɗaga ta kai kunne ta ce mashi idan ya gama ga Leemarh nan tana jiran sa, ba a jima ba ya shigo cikin falon, ya yi shigar aiki don zai shiga asibiti duk da ba ranar aiki ba ce yana da aikin da zai je yi shine za su tafi tare da Leemarh zai kai ta makarantar su Sadeeya kamar yadda Sadeeya ɗin ta roƙe sa ya kai mata ita, Binafa ma ta so a tafi da ita amman ranar suna zuwa tahfiz tuni ma har sun tafi, cikin falon ya ƙaraso sai faman sakin ƙamshi yake yi fuskarsa ta yi wani fresh, sumar kan shi da ta fuska sun sha gyara sai ƙyalli suke yi, idanun Leemarh na akan shi har ya ƙaraso cikin falon ya zauna kan kujera, cikin ladabi ya gaishe da momy ta amsa mashi, a hankali ya juya ya kalli Leemarh ta yi masa murmushi ta gaishe da shi ya amsa, bin juna suka yi da kallo kowannan su na ɗan murmushi Fahad ya ce mata ta yi kyau, kunya ce ta kama Leemarh saboda momy dake a wurin ta sauke idanunta, ita dai momy tuni ma ta janye idanunta daga kan su ta maida kan tv, miƙewa Fahad ya yi ya ce mata sai sun dawo itama Leemarh ta miƙe, momy ta kalle su ta ce bari ta ɗauko saƙon da za a kai ma Sadeeya, bayan ta fito da saƙon a cikin wata ƴar babbar leda Leemarh ta kai hannu zata amsa momy ta yi murmushi ta ce ta bar shi bari ta raka su, matsawa Leemarh ta yi saida ta bata ledan ta riƙe sannan suka tafi ta raka su har waje tana masu Allah Ya tsare hanya. A nutse Fahad ke driving gaba daya cikin motan ya karaɗe da daddaɗan ƙamshi haɗi da sanyin Ac, lokaci lokaci yake juyawa ya kalli Leemarh su haɗa ido tare da sakar ma juna sanyayyan murmushi, wasu lokutan ta cikin mirror yake satar kallonta ya yin da idanunta ke kallon hanya, ba ƙaramin kyau ta yi masa ba, a yanzu ji yake ya shirya ma kowane irin ƙalubale zai fuskanta akanta don tuni son ta ya kanainaiye masa zuciya, komai game da ita ya yi masa ɗari bisa ɗari, kyawunta, tsabtarta, iya girkinta, iya kwalliyarta, sauƙin mu'amallarta, gashi ya fahimci ba ƙaramar kulawa zai samu a wurinta ba, don a yanzu ma da basu furta ma juna so ba ba ƙaramar tarairaya yake samu daga wurinta ba, da duk bai yi tunanin hakan daga gare ta ba ganin ta ba wata babba ba. Bayan sun iso Zaria Fahad ya ce su je su yi ma Sadeeya siyayya, wani mall ya kai su tare suka shiga da Leemarh, idan ka kalle su sai ka sake kallon su yadda suka yi kyau kana ganin su ka ga waɗanda hutu ya zauna masu, siyayya mai yawa suka yi, bayan sun fito har da fruit suma masu yawa ya siya sannan kai tsaye suka wuce Abu, a wuraren da hostel ɗin su Sadeeya yake ya faka motan ya kira ta a waya, ba a ɗauki lokaci ba sai gata ta nufo in da suke tare da wata friend ɗinta, cike da farin ciki ta ƙaraso wurin motar ta rungume Leemarh da ta fito tana faɗin, "Welcome my beautiful sis." bayan sun saki juna Leemarh ta gaishe da ita tare da ƙawarta da ta kafe Leemarh da ido sai kallonta take don Sadeeya ta sanar mata ko wacece Leemarh, Sadeeya ta leƙa ta ƙofa ta gaishe da Fahad ya yi mata ya karatu, tambayarta Khaleel ya yi ta ce ɗazun suka tafi Kaduna da wasu friends ɗinsa za su dubo mamar wani abokin su da bata lafiya amman anjima za su dawo, ƙawar Sadeeya itama ta ɗan duƙa ta ƙofa ta gaishe da Fahad ya amsa tare da yi mata ya karatu, "Amman ya Fahad nan zaka barta sai gobe ko?" Dan girgiza mata kai ya yi ya ce anjima da yamma zai zo ya ɗauke ta, a marairaice Sadeeya ta ce, "Tun da weekend ne ka bar mani ita sai ka dawo gobe ka dauke ta pls." Fahad ya ce to miye amfanin ta kwana a nan, idan ta wunin mata ai ya isa, dole Sadeeya ta haƙura amman ta ce masa to sai magrib zai dawo ɗaukar ta shi dai bai ce komai ba, nuna ma Sadeeya kayan dake a seat ɗin baya yai ya ce ta ɗauka, bayan ta fiddo su ta yi masa godiya, leƙawa Leemarh ta yi suka haɗa ido tana murmushi ta ce masa sai ya dawo, ya ɗan yi shiru yana kallonta cikin ido, ya yi ƙasa da murya ya ce, "Ko kina son ki kwana?" Saida ta ɗan saci kallon inda Sadeeya ta ke sannan ta juyo ta ɗan girgiza masa kai alamar a'a, murmushi ya yi don daga yadda ta yi ya fahimci saboda shine bata son kwana, slowly ya ce, "Ok, till I come back, take care." Ta ɗaga masa kai, Sadeeya da friend ɗinta suka ɗauki ledojin kayan, ta kama hannun Leemarh da ɗayan hannunta suka nufi hostel, ƙawar Sadeeya ta kasa janye idanunta akan Leemarh sai murmushi take mata, suna zuwa cikin hostel Ruƙayya ƙawar Sadeeya ta fara yayata ma ƴan hostel zuwan Leemarh da ko ita wacece, ai fa nan aka fara tururuwar zuwa ganin ƙanwar Deen Jr, mutane sai santin kyawun ta suke suna faɗin kamanninta da Deen, har daga wasu hostels ake ta zuwa ganin Leemarh anata yin hotuna da ita, sam an ƙi bari ma Sadeeya ta samu lokaci da ita su zauna su yi hira daga a ja ta nan sai a ja ta nan, ƙarshe da Sadeeya ta ga idan ta zuba ido ba za a bari ta samu lokaci da Leemarh ba sai ta sa wata ƙawarta da ta iya kitso sosai ta yi ma Leemarh yadda duk mai son ganinta sai dai ya zo ɗakin su ya ganta, sai da ana yin kitson ne ta samu suka yi hira har take tambayarta Binafa ta ce da sun zo tare, Leemarh ta ce itama ta so su zo tare amman saboda islamiyya kuma exams suke shiyasa ba su zo ba, haka akai ta kawo ma Leemarh abinci kala kala daga ɗakunan students, Sadeeya da ta yi niyyar yi mata girki sai dai ta fasa. Wuraren sallar la'asar su Khaleel suka dawo, tun yana can Sadeeya ta sanar da shi zuwan Leemarh kuma ya ga hotunanta da wasu students mata suka ɗaɗɗaura, kai tsaye hostel din su Sadeeya ya nufa ya kira Leemarh, lokacin har an gama mata kitson, shima hostel ɗin su ya nufa da ita aikuwa nan students maza suka yi mata dafifi a gaban hostel sai ka ce ita ce Deen ɗin, tun abun na ba Leemarh nishaɗi har ta fara gajiya, da kanta ta ce ma Khaleel ya maida ta wurin yaya Sadeeya. Misalin ƙarfe shidda Fahad ya zo ɗaukar ta, ƴan hostel ɗin su Sadeeya kusan fin goma suka yo mata rakiya, bayan sun ƙaraso wurin motar Fahad, Sadeeya ta buɗe back seat ta sassaka ledojin uwayen kyaututtukan da aka tara ma Leemarh, sallama suka yi da Sadeeya ta ce ai next weekend tana nan zuwa gida, suma ƙawayen Sadeeya suka yi sallama da ita ta yi masu godiya, tun da ta shiga cikin mota Fahad ya zuba mata ido yana kallon kitson da aka yaryara mata, har da na gaba ya zubo har zuwa wuya sannan kuma aka lanƙwashi shi aka haɗe dana baya aka kulle da ribbon ya sauka bayanta, Sadeeya ta leƙo suka yi sallama da Fahad ta yi masa godiya, kamo hannun Leemarh ta yi tana sake yin sallama da ita lokacin Fahad ya tashi motar, suna ta ɗaga ma juna hannu har da ƙawayenta a haka suka tafi. Bayan sun hau hanya sosai Fahad ya kalle ta suka haɗa ido, calmly ya ce, "Kitson ya yi kyau sosai." Murmushinta ya faɗaɗa ta ce, "Har da irin shi zaka koya ka rinƙa yi mini." Idonsa akan hanya yana murmushi ya ce, "To ai ban san irin style ɗin ba." Hannu ta kai ta zame kallabinta ta ce gashi ya gani, ya juyo yana kallon kitson da ya saƙu raɗam tsagar ta fita sosai farar fatar kanta ta fito, da sauri Fahad ya maida idanunsa kan hanya jin sitiyari na neman ƙwace masa, ya ce, "Kin ga zaki ja in sa mu yi accident saboda kyan kitson." Ƴar dariya Leemarh ta yi ta ce da gaske ya yi kyau, ya ɗan jinjina kai idanunsa a hanya ya ce sosai, "To da gaske kake zaka koya kitson ka rinƙa yi mani?" Ya ɗaga ido ya kalle ta suka haɗa ido ta cikin mirror, slowly ya jinjina mata kai tare da ɗan lumshe ido, murmushi ta yi ta sauke idanunta ƙasa. Bayan sun iso Funtua gidan hajiya Leemarh ta ce masa su biya ta gaishe da ita, a can ma hajiya sosai ta yaba da kitson Leemarh har ta ce mata ta rinƙa daurewa ana mata don ya ƙara mata kyau sosai, sai bayan sallar issha suka baro gidan suka nufi gidan su Fahad.... 09013804524, 08169856268 for more info. *✨A CIKIN RAYUWA✨* ZAINAB BATURE 46 Aunty Kubra ta shigo ward din da take sanye da uniform ta ɗaura after dress, shigowarta ke nan aiki bayan ta juya aikin rana hakan ne ya sa bata taho tare da Salma ba tun da da dare zata koma gida, wata staff ce ta zo wucewa ganin aunty Kubra ta tsaya suna gaisawa, "Aikuwa aunty Kubra ɗazun Dr Hisham ke tambayar ki na ce baki kai ga shigowa ba." Staff din ta faɗa, aunty ta tambaye ta ina Dr Hisham din ta ce mata yana office, kai tsaye office ɗin aunty ta nufa, bayan ta kwankwasa daga ciki aka bata izinin shiga, office ne ɗan babba irin na likitoci that's well equipped daidai da matsayinsa na specialist gynaecologist wato likita ƙwararre a 6angaren lalurorin da suka shafi mata, daddaɗan ƙamshi haɗe da sanyin Ac sun karaɗe ilahirin ofishin, Dr Hisham na zaune yana rubutu a saman desk ɗin gabansa, ɗago kai ya yi yana ganin aunty ya ajiye pen ɗin hannunsa yana amsa sallamarta da murmushi, a saman ɗaya daga cikin kujerun gaban desk ɗin da yake ta zauna ta ce, "Dr barka da rana." Ya ce, "Yauwa aunty Kubra an shigo." Ta amsa masa da eh, "Ya baƙuwar mu, ko tare kika zo da ita?" Ya tambaya da ɗan murmushi, aunty ta bashi amsa da tana gida dama saboda idan tana night ba kowa gidan shiyasa take tahowa da ita, Dr ya ɗan jinijina kai, "Yanzu ake ce mani kana nema na." ɗan murmushi ya yi ya kai hannu yana ɗan shafa kansa ya ce ai da ta bari ya iske ta, aunty da itama murmushin ne akan fuskarta ta ce ai ba wani abu don ta iske shi tun da anan shine babba, Dr ya ce, "To ai aunty baki san ko neman da nike maki bai shafi nan ɗin ba." Aunty ta yi ƴar dariya ta ce ta sani ko wani alkhairi ne ai gara kar ta tsaya jinkiri, shiru Dr ya yi yana ɗan murmushi aunty da ke kallon shi ta so ta fahimci kamar yana ɗan jin nauyin maganar da zai mata, sigh ya ɗan yi ya ce, "Nama rasa ta ina zan fara aunty." Tana faffaɗan murmushi ta ce ko ta ina ya fara lafiya lau, gyara zama ya ɗan yi a nutse ya fara magana, "Aunty dama dai ƙaninki ne ya ga abu a wurin ki to kuma ya ji zuciyarsa ta kamu da son abun, shine na ce bari in kawo ƙoƙon barana ko Allah zai sa in dace a bani." Aunty Kubra ta ɗan buɗa ido da ɗan murmushi ta ce, "To Dr miye abun, in dai nawa ne in sha Allah zan baka." Shiru ya ɗan yi still murmushi ne akan fuskarsa haka ma aunty dake jiran ya faɗi abun, "Aunty ƙanwata Salma nike so idan an amince za a bani..." Aunty Kubra ta ɗan jinjina kai tare da kauda fuskarta, dama dai ta so ta zargi hakan a game da shi tun ba yanzu ba ganin yadda yake nuna kulawa akan Salma, "Aunty ko na makara? don na san yadda take tubarkalla ba za a rasa wanɗanda suka kawo irin buƙata ta ba, kuma ƙilan ma an riga an ba wani." Juyowa aunty ta yi ta kalle shi tana murmushi ta ce, "Ba zan ce baby bata da masu son ta ba, amman dai ban tunanin akwai wanda aka ba ita, saboda na san ita sam soyayya ma bata gabanta, karatu take da burin yi sosai hakan ne ma ya sa ko kula samari bata yi." Dr ya ɗan yi faffaɗan murmushi alamar ya ji daɗin maganar, tana kallon sa ta ce, "Amman Dr kai wane irin so kake mata?" Dr ya ce, "Son ta nike da aure, ko yanzu aka amince mani a shirye nike." Aunty ta ɗan zaro ido sai kuma ta yi dariya ta ce da sauri haka, Dr ya ce, "Ai aunty da zafi zafi ake dukan ƙarfe, yanzun nan da na yi sanya sai kika an zo an mani overtaking." Aunty dai ta yi shiru tana ɗan murmushi, tabbas ta san idan Dr Hisham ya auri Salma ta yi dacen miji don ta san yana da kyawun hali kowa na yabon sa kan hakan, kawai abu ɗaya dangane da shi da ya sa ta ɗan ji bata goyon bayan hakan shine kasancewarsa yana da mata, duk da ta san hakan ba wani aibu bane amman kuma bata ma Salma fatan fuskantar matsalar kishiya, jin ta yi shiru Dr ya ce mata ko dai da wani abu ko kuma bata goyon bayan hakan, da sauri aunty ta ce, "No Dr. Hisham, abu irin wannan ai mutum bai zai ƙi goyon baya ba indai ba da wata matsalar ba tun da bamu san abun da Allah Ya ƙaddaro kan hakan ba, kawai dai abun da na sani shine gaskiya ba a shirya yi ma Salma aure ba duba da karatu ta saka a gaba, kuma gaba ɗaya ba wata babba bace don har yanzu ma bata ƙarasa cika 18yrs ba, ga shi ko secondary school ma bata gama ba." Dr Hisham ya ce, "Aunty ai wannan ba matsala ba ce, rashin gama secondary school ba shi ke nufin mace bata isa aure ba, kuma karatu ko a ɗakin miji ana yin sa, gashi dama abun da take son karanta is related to my profession, kin ga kasancewarmu tare matsayin ma'aurata zan taimaka mata sosai wajen samun ilimi da ƙwarewa, amman idan an fi son sai ta fara yin karatun ko ta gama sannan, lafiya lau zan iya jiranta in dai za a bani." Aunty ta yi shiru don gaba ɗaya kanta ya ɗaure ta rasa shawaran da zata yanke kan hakan, boyayyar ajiyar zuciya ta sauke ta ce, "Shike nan Dr, Allah Ya za6a abun da ya fi zama alkhairi, yanzu abun da ya fi shine ka bayyana mata ra'ayinka a kanta, idan kun fahimci juna ta amince maka lafiya lau ko yaushe mu sai mu sha biki." Murmushin jin daɗi Dr ya yi yana shafa kansa ya ce shike nan zai gwada sa'ar shi, aunty ta kasa danne abun da ke ranta ta ce, "Amman Dr ka san kana da mata, yakamata ku fara fuskantar juna kan hakan, ka fara tabbatarwa ba za a samu matsala ba a tsakanin su idan har al'amarin ya yuwu, don gaskiya ba zan 6oye maka ba, ina jin Salma a raina sosai, ita ɗin tamkar ɗiyar dana haifa a cikina take, bana mata fatan fuskantar ƙalubalen kishiya ba kamar a yadda take da ƙananun shekaru gaskiya." Dr ya jinjina kai tare da tabbatar ma aunty cewa ba za a samu irin ƙalubalen da take nufi ba a gun matarsa duk da ya san wasu matan ba a gane suna da matsala sai hakan ya faru, amman in sha Allahu zai yi bakin ƙoƙarin ganin ba wata matsala da zata faru, kuma ko da ya auri Salma ba gida ɗaya zai haɗa su ba, idan ta kama ma har gari yana iya raba masu, aunty ta ji hankalinta ya ɗan kwanta sanin yana da halin da zai yi hakan, addu'ar Allah Ya tabbatar da alkhairi ta yi ya amsa mata, bayan ta tambaye shi shike nan zata iya tafiya ya amsa mata da eh, har ta miƙe yana ɗan shafa sumarsa ya ce, "Aunty yanzu to ya za a yi ke nan." tana ƴar dariya ta ce, "Idan namiji ya ga mace yana so ya ake yi?" ya ce, "Zai je wurinta ne ya bayyana mata tare da neman soyayyarta." Aunty ta ce, "To kai ma hakan zaka yi." ya ce to ya zo gidanta ke nan, ta amsa masa da eh tana dariya, ya ce ok zai yi hakan amman kafin ya zo pls ta fara masa sharan hanya, tana dariya ta ce to daga haka ta tafi. Washe gari da safe aunty Kubra na zaune da Salma a dining area suna yin breakfast da suka haɗa a tare, lokaci lokaci take kallon Salma a ranta tana tunanin ta in da zata fara mata maganar Dr Hisham don ta san ba soyayya ta iya ba, bayan sun gama Salma ta kwashe kayan da suka yi amfani ta nufi kitchen, sai da ta wanke komai sannan ta fito lokacin aunty na zaune akan kujera, nufo ta Salma ta yi jikinta sanye da doguwar rigar material ta rufe kanta da hula, a kujerar kusa da ita ta zauna tana mata murmushi, itama aunty Kubra shine akan fuskarta ta ce, "Akwai abun da zaki yi ne yanzu?" Salma ta girgiza mata kai ta ce a'a sai dai idan lokacin yin abincin rana ya yi, aunty ta ce, "Akwai maganan da nike son zamu yi ne." Salma ta ce to tare da tattara hankalinta akanta, a nutse aunty ta fara mata bayani game da maganar da suka yi da Dr Hisham, lokaci guda gaban Salma ya fara faɗuwa ta sauke kanta ƙasa, aunty dake kallonta jin ta yi shiru tana murmushi ta ce, "To kin yi shiru baby ni da nike son jin miye ra'ayinki kan hakan?" Shiru Salma ta yi bata ce komai ba kuma bata ɗago kanta ba, hannu aunty ta kai ta ɗago fuskarta kawai sai gani ta yi ta runtse ido da sauri, dariya abun ya ba aunty ta ce, "To miye kuma abun kunya, ki buɗe baki ki faɗa mani ra'ayinki kan hakan ai ba wani abu bane, dama matsayin ki na mace ai dole ne watarana a zo kan wannan ga6ar, don ma ba kula samari kike ba ai da tuni ma an wuce wannan wurin ƙilan ma har an haifa mani grandchild." Da sauri Salma ta sa hannuwanta ta rufe fuska, "Yanzu dai ina son in ji miye ra'ayin ki game da Dr." Da ƙyar idanunta na kallon gefe ta ce, "Ni ai aunty kin san karatu nike son yi, kuma kema ba kina ce mani kar in rinƙa kula samari ba in maida hankali akan karatu." Aunty tana murmushi ta ce, "Hakane, amman kuma hakan ba yana nufin idan Allah ya kawo saurayi na kirki a ƙi kula sa ba, duk dai a yi karatun ƙarshe dole ai a yi aure, kuma aure baya hana karatu, mace tana ɗakin mijinta ma zata iya yin karatun ta lafiya lau. A koda yaushe addu'ar mu ita ce Allah Ya baki abokin rayuwa nagari, Dr Hisham yana da halin kirki hakan nema ya sa har na kawo maki maganarsa, don da na san ba mutumin kirki bane tun lokacin da ya yi mani maganar zan san yadda zan yi in dakatar da abun. A zamanin nan da maza na kirki suke wahala tabbas na san idan kika samu Dr matsayin miji kin dace, kawai inda nike hangen matsala shine da ya kasance yana da mata, to amman ya tabbatar mani da ba za a samu matsala ba da matarsa, ya ma nuna ba haɗa ku zai yi ba in har ya aure ki har gari ma zai iya raba maku, duk da dai hakan bai sa a guje ma sharrin wasu kishiyoyin, to amma dai idan bawa ya dogara da Allah ya isar masa, sai dai kuma idan baki son shi ba wanda zai maki dole." Shiru Salma ta yi kanta a ƙasa, wasu cikin maganganun aunty sun tuno mata da shawarar da hajiyar Ambasada ta ta6a bata, "Baby ke nike sauraro, ki faɗi mani miye ra'ayin ki kan hakan don tun wuri in san abun yi." A hankali Salma ta ɗago kai ta kalle ta, cikin sanyin jiki ta ce, "Duk yadda kika ce aunty zan amince." Aunty Kubra ta yi saurin girgiza kai ta ce, "A'a baby, wannan abu ne da ya shafi rayuwarki bai kamata wai wani ya yanke maki hukunci ba akai, mu iyaka dai mu baki shawarar da muka ga zata maki amfani." Shiru Salma ta yi don ta rasa mi zata ce, aunty ta lura da kanta ya ƙulle hakan ya sa ta dafa kafaɗarta ta ce, "Ina son ki samu lokaci ki natsu ki yi tunani a cikin zuciyarki, duk abun da kika yanke kada ki ji nauyin sanar mani kin ji." Kai Salma ta ɗaga mata duk jikinta ya yi sanyi, sam bata yi tunanin a lokacin nan za a zo mata da maganar aure ba, kiran aunty aka yi a waya ta miƙe ta nufi ɗakinta tana amsawa, itama Salma miƙewa ta yi ta nufi ɗakinta, bayan ta shiga gado ta nufa ta zauna tana kallon wuri guda yayin da zuciyarta ta shiga dawo mata da fuskar Dr Hisham. Bayan kwana biyu da yin maganar su da aunty Kubra, Salma tana zaune a cikin ɗakinta bayan ta gama sallar issha tana latsa wayarta, turo ƙofar ɗakin aka yi ta ɗaga ido tana kallon aunty da ta shigo, nufo ta ta yi ta tsaya daga gabanta tana murmushi ta tambaye ta mi take yi, Salma ta ce mata ba komai kawai tana ɗan duba waya ne, shiru aunty ta ɗan yi kafin still da murmushi ta ce, "To kin yi baƙo." Har saida gaban Salma ya faɗi jin abun da ta ce, "Dr Hisham ne ya zo yana nan ya shigo ki je ki same sa." Kallon ta kawai Salma ke yi ta kasa cewa komai, aunty ta ce, "Koda baki ji ya yi maki ba ki tsaya ki saurare sa, daga baya zan san yadda zan masa bayanin da za a rabu lafiya." A hankali Salma ta ɗaga mata kai, saida aunty ta ce mata ta je ta same sa dare na ƙara yi sannan ta miƙe, dama riga da skirt ne na atamfa a jikinta, wurin kayanta ta nufa ta ɗauko ɗan babban mayafi da ya hau da kayan ta yafa, walking slowly ta nufo ƙofa zata fita, aunty dake kallonta tana ɗan murmushi ta ce, "Haka za a je wurin saurayin ba za a ɗan gyara fuska ba." Salma ta wani ɗan yamutsa fuska har saida ta sa aunty yin dariya ta ce mata ta je, gabanta na ta ɗan faduwa ta fito haraban gidan, hango motarsa da ta yi a wurin gate ya sa bugun da ƙirjinta ke yi ƙaruwa, kamar mai jin tsoro haka ta ƙarasa bakin motar ta yi tsaye, Dr Hisham da tun da ta fito yana kallonta ta cikin motar da yake harabar akwai haske sosai, ganin ta yi tsaye ya sa shi buɗe motar ya fito, yana tafiya a nutse ya zagayo inda take, nan da nan wurin ya karaɗe da ƙamshin turaransa mai daɗin gaske, tsaf da shi kana ganinsa ka ga ɗan gayu, yana sanye da ƙananun kaya da suka amshi jikinsa, idan baka sani ba baza ka yi tunanin ma yana da aure ba, daga gefenta ya tsaya ya jingina da ƙofar gaban motan, idonsa akanta da ɗan murmushi cikin nutsattsiyar muryarsa ya ce, "Baƙuwarmu..." A hankali ta ɗaga ido ta ce masa ina yini, ya amsa mata yana ta kallon ta, bayan ɗan lokaci ya ce, "Sai kika ji saƙona a wurin aunty Kubra ko?" Kai ta ɗaga ba tare da ta kalle sa ba, hannu ya kai ya shafi sumarsa ya ɗan sauke numfashi ya ce, "Haka Allah Ke ikonSa..." ita dai bata ce komai ba kanta na ƙasa, "To ina son in ji na samu shiga ko kuwa sai dai in yi haƙuri in je na yi jinyar zuciyana." Shiru ta yi bata da niyyar yin magana, duk wani iri take ji don wannan ne kusan karo na farko da ta tsaya da namiji haka, duk da akwai samarin da ke zuwa gida da sunan sun zo wurinta suna son ta, sai dai bata ma tsayawa har su yi magana, wani lokacin ma su Imrana take saka wa su je su ce bata nan, "Salmah.." A karon farko da ta ji ya kira sunanta, a hankali ta ce, "Na'am." ya ce, "Kin yi shiru.." a sanyaye ta ce, "To ai ban san mi zan ce ba." Gyara tsayuwarsa ya yi ya ce, "Ina son ki faɗa mani miye ra'ayinki game da ni?" Shiru kamar bazata yi magana ba, da ƙyar ta ce, "Ka yi ma aunty Kubra magana duk abun da ta ce shike nan." Ɗan murmushi mai faɗi ya yi ya lura da yadda ta kasa sakin jiki da shi, amman tuna maganar da aunty Kubra ta faɗa masa na bata kula samari ya sa bai ji komai ba, "Wannan ba hurumin aunty Kubra bane da zata yanke hukunci tun da abu ne da ya shafi rayuwarki, kamar yadda na faɗa mata, zuciyata ta kamu da son ki kuma son aure nake maki, kin ga ke ce zaki yanke ma kan ki hukuncin za6ar wanda zai zamo abokin rayuwarki. Kar ki ji komai, duk abun da kika yanke game da ni zan fahimce ki." Har saida Salma ta ɗan runtse ido, ita gaba ɗaya ta rasa wace shawara zata yanke game da hakan, Dr Hisham dake ta kallonta ya fahimci kanta ya ƙulle, calmly ya ce, "Salmah.." Ta amsa masa idonta a ƙasa, ya ci gaba, "Ko kina buƙatar in baki lokaci ne ki yi shawara da zuciyar ki?" Da sauri ta ɗaga masa kai, yana murmushi ya ce, "Ok, yanzu kamar zuwa yaushe ke nan zan samu jin amsa daga gare ki?" ta ce masa zata dai yi shawaran, "Shike nan zan jira, amman pls kada a wahalar da ni, kin san jiran tsammani kan shi cuta ne." A hankali ta ɗaga ido a karon farko ta kalle shi suka haɗa idanu ta yi saurin janye idonta, "To miye labari?" ta ji ya faɗa, Hannu ta ɗan watsa ta ce babu, Dr ya ce bai yarda ba sai dai in shima labarin rowa za a masa, tana ɗan murmushi ta ce, "Da gaske babu wani labari, ni da kullum ina a cikin gida sai idan mun fita da aunty." Dr ya ce, "To ai labarin ba dole sai na nan ba, ko na can Funtua sai a bani ina so." Ɗaga ido ta yi ta sake kallonsa wannan karon bata janye idanunta ba ta ce to ai babu wani labari na can ɗin ma, Dr ya ce ya za ai ta ce ba wani labari da zata bashi game da garin su in da take yin rayuwa, shiru Salma ta yi don ita bata san wani labari zata bashi ba, "To ki bani labarin gidan ku, I mean na ƴan'uwan ki haka." Ta ji ya faɗa ta ɗago ta kalle shi, shiru ta ɗan yi kafin ta ce, "Ƴan gidanmu duk maza ne ni kaɗai ce mace." Dr ya ɗan buɗe ido ya tambaye ta da gaske ta ɗaga masa kai, tambayar su nawa ne a gidansu ya yi ta ce masa su shidda ta faɗa masa sunayen sauran ƴan'uwan nata, "Lalle ki ce ƙanwar sojoji ce ke, dole in lalla6a ki idan muka yi aure in ba haka ba in fuskanci 6acin ransu, kin san ƙanwar maza ba a taba masu ita su ƙyale fa." Ƴar dariya Salma ta yi ba kowa ya faɗo mata a rai ba sai Sageer, shi zai ci zalinta amman wani na waje da ya mata ba daidai ba sai ya fuskanci fushin sa, Dr ya ce saura ta bashi labarin ƙawayenta, ta ce "Ni ai bani da ƙawaye, kawai sai ƴan makarantar bokon mu da islamiyya, kuma abotar mu a makaranta ne sai idan wani abu ya faru muna zuwa gidan juna, amman bani da ƙawaye na daban, saboda ma ba a can na taso ba duk wanda muke tare a iya secondary school ne muka haɗu." Dr Hisham ya jinjina mata kai, sosai yake jin daɗin yadda ta ɗan saki jiki tana mashi magana yanzu, ya lura kunyar zancen sonta da ya zo da shi take yi shiyasa farko ta ƙi sake masa jiki, "Amman yadda baki da ƴar'uwa mace da kina da wata kamar best friend haka zata zame maki kamar ƴar'uwa, kuma zaki ɗan rinƙa samu nishaɗi daga wurin ta, I mean zaku rinƙa yin hira ku je wurare tare tun da su ƴan'uwan naki mazan ba lalle ki yi haka da su ba." Salma ta ɗan girgiza masa kai sai kuma innocently ta ce, "Suma muna yin hiran da su sosai, kuma ma ina yin sana'a hakan na saka ni nishaɗin." Dr ya ɗan gyara tsayuwarsa yana ta kallonta bayan ya tambayi sana'ar da take yi ta bashi amsa, ba wai sana'ar tata ta bashi mamaki ba, kawai yadda ta ce masa a ƙofar gida take yi ne ya ɗan sa shi jin mamaki, ganin yadda take tubarkalla kyakkyawar budurwa mai natsuwa amman take iya zama a ƙofar gida tana tuyan awara, yana murmushi ya ce mata bata jin kunya ta zauna a waje ta yi awara ba ya fi a cikin gida ba, ta ce masa ai haka ta saba yi kuma ita bata jin wata kunya tun da neman halak ne, Dr ya jinjina kai, sai kuma ya ji ta sake cewa, "Har da fara ma nike saidawa." Fuskarsa a sake ya tambaye ta wani irin fara tana wasa da yatsunta ta ce masa irin wadda ake soyawa, ya ce, "Ke kike soyawan?" Ta ɗaga ido ta kalle sa tare da ɗaga masa kai alamar eh, ɗan jinjina kai ya yi yana murmushi ya ce, "Ni ban ta6a cin shi ba, ina dai gani mutane na ci, amman kuma tana da amfani sosai a jiki don tana ɗauke da sinadarai masu mahimmanci irin su protein, fat, fiber, iron zinc da sauran su." Salma ta kafe sa da ido don ita dai haka nan take cin fara don kwaɗayi ba tare da sanin tana da wani muhimmanci ba a jiki, "Amman tun da kina soya shi dole in koya ci. Yaushe za a bani?" Tana ɗan murmshi ta ce to ai ba a nan take soyawa ba saboda itama aunty bata ci, Dr ya ce, "Sai idan na je Funtua ke nan?" ta ce masa saboda faran zai zo Funtua, Dr ya ce, "No, tun da ina burin mallakar ki matsayin matata ai dole in je gaisuwa da roƙon iri wurin su yaya Sageer." Yadda ya canki sunan Sageer kamar ya san tsakanin su da Salman, ganin ta yi shiru ta sauke idanunta ya ce ko bata son ya je, batare da ta kalle shi ba a hankali ta ce a'a, daga haka kuma kamar ya rufe mata baki bata ƙara cewa komai ba, shi dai yana ta kallonta don komai nata burge shi yake, can ta ɗaga ido ta ce masa zata shiga gida ta fara jin bacci, Dr ya ce kodai ya cika ta da surutu shiyasa zata masa kora da hali, da sauri ta ce masa a'a da gaske bacci take ji, ya ce ok tare da tambayar yaushe take maraba da shi ya dawo, ta ɗan yi shiru sai kuma ta ce duk sadda ya dawo, ya ce shike nan tare da ce mata ya gode, sai da safe ta yi masa har zata tafi ya dakatar da ita, back door ya buɗe ya fiddo wasu ƴan manyan ledoji guda biyu ya miƙa mata suka haɗa ido ya ce, "I got you this..." Ta ƙi amsa ta ce ya bar shi, "Sai in yi yaya da su tun da ke na kawo mawa? Kuma ai ba a maida kyauta balle kuma ta wanda ke son ka." Sauke idonta ta yi ta amsa ta ce masa ta gode, Ya ce, "Gud night, sleep tight." Ta ɗaga ido ta kalle shi idanunsu suka haɗu daga haka ta juya ya bita da kallo, Dr ya ji ta ƙara burge shi saboda halinta na ɗaukar rayuwa da sauƙi, musamman yadda bata ji komai ba ta faɗa masa sana'oin da take yi, nan take a zuciyarsa ya yanke in dai Allah Ya nufa suka yi aure kafin ta ci gaba da karatu, zai canza mata ra'ayi daga karatun nursing ta karanci medicine kuma ƙasar waje zai kaita kamar yadda shima ba a nan ya yi karatu ba, daga haka ya koma motarsa ya tafi....... *✨A CIKIN RAYUWA✨* ZAINAB BATURE 47 Aunty Kubra na duba abubuwan da Dr ya kawo ma Salma bayan ta shiga cikin gida, leda ta farko kayan ciye-ciye ne har da manyan chocolates masu kyau kana ganin su za su yi tsada, ɗayan ledan kuma kayan shafe shafe ne da manyan turarurruka suma dai da gani duk masu tsada ne, ita dai Salma tana zaune gefe tana bin kayan da kallo, aunty ta ɗago ta kalle ta da ɗan murmushi ta ce, "Lalle Dr da gaske yake, su baby an fara samun alkhairin saurayi." Kauda kai Salma ta yi tana ɗan murmushi tare da ɗan tura baki, aunty ta ce, "Ko a can akwai saurayin da ya taba kawo maki abu irin haka?" Salma ta juyo ta kalle ta a hankali ta ce, "Ai ban saurarar su ma, amman dai Aliyu yana aiko mani da ƴan abubuwa, da ban amsa ma innarmu ce take cewa in amsa." Aunty ta tambaye ta waye Aliyu, ta ce abokin Sageer ne, wani kallo aunty ta yi mata ta ce, "Ana maganar samarin kirki, abokin Sagir ai daga ji ba wani saurayin kirki bane tun da shima Sagir ɗin ya yake." Dariya Salma ta saka, itama aunty dariyar take ta ce da yana kusa ta faɗi hakan da sai ya masu tijara, "Ya ku ka yi da shi Dr ɗin?" Ta tambaya tana kallonta, dan shiru Salma ta yi kafin ta ce, "Kawai ya tambaye ni wai ra'ayina akan shi, to ni dai rasa yadda zan ce masa na yi, shine ya ce ko ya bani lokaci in yi shawara na ce eh." Aunty ta jinjina kai ta ce hakan ya yi sai ta natsu ta yi shawara da zuciyarta ko mi ta yanke ta sanar mata Allah Ya za6a abun da ya fi zama alkhairi. Bayan Salma ta gama yin shirin kwanciya tana sanye da rigan bacci daidai gwiwa ta hau gado, ɗan lallatsa wayarta ta yi kafin ta ajiye ta gefe, bayan ta yi addu'a daga haka ta rufe ido, ringing ɗin da wayarta ta fara alamar shigowar kira ya sa ta buɗe ido da sauri ta fara tunanin waye ya kira a lokacin, bin baƙuwar lambar da ake kiran da ita ta yi da kallo, kamar bazata ɗaga ba can dai ta kai hannu ta yi picking tare da kara ta a kunne, daga ɗayan 6angaren ta ji an yi mata sallama nan take kuma ta gane muryar Dr Hisham ce, "Salmah..." Bayan ta amsa sallaman a hankali ta ji ya kira sunanta, "Hope kin gane mai magana." Ta amsa masa da eh, ya ce, "Dama tun da ba a kira ni aka ji ya na koma ba shine na ce ni bari na kira in ji ya kika shiga gida." Ɗan buɗa ido Salma ta yi sai kuma ta ɗan yi murmushi ta ce, "Ai bani da number ɗin ka ne." Ya ce, "Ai in an damu da aji ya na koma zaki amsa a wurin aunty kamar yadda nima na yi." Shiru ta ɗan yi sai kuma a hankali ta ce, "Ka yi haƙuri to" Da sauri ya ce, "No ai ba laifi kika yi ba, duk yadda kike so haka za a bi." Shiru ta yi kawai, can ta ji ya ce, "Ɗazun na tambaye ki kin bani labarin ƴan'uwanki har da business da kike yi, amman ni you didn't ask anything about me, ko baki son sanin komai akai na ne?" Salma ta ɗan yi shiru can ta ce, "Ai na san aunty Kubra ta san komai akan ka." Ya ce amman ai waƙa a bakin mai ita ya fi daɗi ko, ta dai yi shiru bata ce komai ba, sigh ya yi ya ce mi take yi ne yanzu, ta bashi da amsa da ta kwanta, ya ce ko har ta fara yin bacci ya tashe ta, ta ce, "Zan dai fara yin baccin ne ka kira." Ya ce, "Ok afuwan, bari in barki to ki yi baccin. Gud nyt, I love u" Ba shiri Salma ta runtse ido, jin bata ce komai ba ya kira sunanta, ta gane dalilin bata amsa masa abun da ya ce bane ya sa shi kiran nata, da ƙyar ta ce, "Na gode...." Tana jin sautin ɗan murmushin da ya yi daga haka ya kashe wayan, bin screen ɗin wayan ta yi da kallo bayan ta gama na ɗan lokaci, ajiye wayan ta yi tana niyyar rufe idonta ta ji ƙarar shigowar saƙo a wayar, airtime na dubu biyar ta ga ya turo mata, Salma ta yi shiru gaba ɗaya ta rasa ma tunanin da zata yi, wata zuciyar ta bata ta kira sa ta yi masa godiya, a sanyaye ta kira layinsa sai dai har kiran ya katse bai ɗaga ba, ƙyale sa ta yi bata sake kira ba, tunanin mi zata yi da kati har haka ta shiga yi, a haka tana ta tunane-tunane har bacci ya yi awon gaba da ita. Washe gari suna zaune suna yin breakfast da aunty, tunanin ta sanar da ita game da katin da Dr ya turo mata ya zo ranta, bayan sun gama kamar ko yaushe ta kwashe kayan ta kai kitchen, sai da ta wanke komai sannan ta dawo cikin falon ta zauna a kujerar kusa da wadda aunty ke zaune, "Baby ya aka yi ne?" Aunty ta tambaya tana ɗan murmushi ganin kamar Salman na son yin magana, "Dama zan faɗa maki Dr ɗin nan jiya bayan na kwanta ya kira shine har ya tura mani airtime na 5k." Aunty ta ɗan yi murmushi ta ce, "Dr ke nan kin gode, dama shi haka yake da son yin alkhairi, ko nan asibiti yana taimakon patients sosai, wani lokacin har kuɗin aiki yana biya ma wasu wanda suka kasa biya, haka idan azumi ya zo ma kullum ne sai ya saka an yi ma patients da masu jinyar su sadakar abun buɗe baki, hatta mu abokan aikinsa duk yana mana alkhairi lokaci lokaci, da yake dai bayan aikinsa suna da arzaƙi gaskiya, kuma babansa senator ne nan Kaduna." Ita dai Salma ta yi shiru tana saurarar ta, "Kin yi masa godiya ko?" Salma ta ce lokacin da ya turo ta kira ta yi godiyar amman bai ɗaga ba, Aunty ta ɗaga kai ta ce, " Shike nan daga baya kya masa godiyan." Salma ta ɗan yamutsa fuska ta ce, "To ni aunty ya zan yi da kati har na dubu biyar." aunty na dariya ta ce ta yi amfani da shi mana, ta ce, "To ai ni idan zan yi amfani da kati ina sakawa." Aunty ta ɗan ɗage gira ta ce, "Na fa manta ɗiyar tawa babbar yarinya ce mai kwasar salary, to yanzu da baki nan ma ya ake ciki da aikin?" Salma ta ce mata Sageer ne ya ci gaba da kula da komai, aunty ta ɗaga kai ta ce "To shi ɗan ball ɗin kuna magana da shi?" Salma ta ce mata ba sosai ba kawai sai idan da wani abu kan aikin da ya saka ta shine take masa magana, kuma shima yawanci saƙo ne take tura masa kuma wani saƙon sai a daɗe ma kafin ya duba, sai kuma wani lokacin tana tura masa saƙon gaisuwa, aunty ta yi shiru tana kallon Salma bayan ta gama maganar, haka nan daga yanayin da fuskar Salma ta nuna bayan ta kawo maganar Deen sai take ganin kamar da wani abu a ranta game da shi, aunty ta ji tana son ta san ko akwai wani abu a ranta game da Deen, cikin kwantar da murya ta ce, "Baby ko dai kin fara son shi?" Salma ta yi saurin kallon aunty, ɗan murmushi ta yi tana kikkafta idanu ta ce, "Aunty saboda mi zaki ce haka." ta ce mata haka nan ta tambaya, shiru Salma ta yi ita kanta ta kasa gane yanayin da take ji a zuciyarta game da shi, ganin yadda aunty ta kafe ta da ido ya sa ta ɗan yi murmushi wanda ya fi kama da na yaƙe ta ce, "A'a aunty...kuma wannan ma ai ya fi ƙarfi na da zan ce ina son shi." Aunty ta yi wani murmushi ta ce, "Ba wani fin ƙarfin ki da ya yi, yadda kike tubarkalla baby ba wani namiji da ba zaki iya siye zuciyarsa ba, ga dai misali nan kan Dr, ba ƙaramin son sa ƴan matan nurses da doctors ke yi ba, amman ke daga ganin ki ya kamu da son ki kuma son ma da aure." Ita dai Salma ɗan murmushi kawai take, "Allah Ya tabbatar mana da abun da ya fi zama alkhairi, rabon bawa baya ta6a wuce sa, idan shi ɗin rabon ki ne kina zaune zai furta maki so har ya aure ki idan shi ne mijin ki." Da sauri Salma ta ce, "Ni fa aunty ban ce son shi nike ba." Aunty na murmushi ta ce ai itama bata ce hakan ba, Salma ta sauke idonta ganin aunty nata murmushi, wayarta da ke gefe ta fara yin ringing ta kai hannu ta ɗauka, ganin yadda ta yi ɗan jimm aunty ta tambayi waye ke kiran ta, a hankali ta ce mata shine, aunty ta yi saurin cewa, "Ɗan ƙwallon?" har saida ta sa Salma yin ƴar dariya ta ce mata a'a Dr, aunty da itama murmushi ne akan fuskarta ta ce to ta ɗauka mana idan kuma kunya take ji ta tafi ɗaki, miƙewa ta yi jiki a sanyaye ta nufi hanyar ɗaki, aunty ta bi ta da kallo har ta shige. Tun Salma bata sakar ma Dr jiki a hankali har ta fara saki, akai akai yake kiran ta su yi waya, ko bai zo ba wasu lokuttan zai ba aunty idan ta je aiki saƙo ta kawo mata, katin waya da data kuwa har yawa suke mata a waya, haka idan aunty tana aikin kwana suka je tare asibiti indai shima lokacin yana duty to da ita yake ward rounds ko kuma su zauna office ɗin sa yana aikace aikacen sa sun yin hira, duk da ba sosai take sakin jiki ba, da ya gane tana son karatu sosai yawanci ya fi yi mata hira kan abun da ya shafi karatun nursing da take son yi ta hakan ne take sakar masa jiki sosai, amman har lokacin bata faɗa masa ra'ayinta game da shi ba, daga baya da ya matsa kan son jin ra'ayinta kan aurenta da yake son yi, sai ta samu aunty Kubra ta sanar da ita cewa ita gaskiya ba yanzu take son yin aure ba sai ta fara karatu koma ta gama, to itama aunty da yake ta 6angare guda tana jin zullumin auren nasu ba kamar da take ganin Salman ta yi ƙarama da kishiya, da kanta ta yi ma Dr magana kan ra'ayin Salma game da aure, ya nuna mata ba komai zai jira, tare da roƙon alfarmar ba sai ta gama karatun ba tana cikin yi sai ya aure ta ta kammala a gidansa, a haka aka bar maganar. Bayan Leemarh ta yi wata guda a Funtua mom Jameela ta takura mata kan ta dawo gida haka nan, ita kuma ta ce bazata koma ba har sai hutun su ya ƙare nan da sati biyu, har dad ɗinsu ta yi ma magana kan ya sa a je a ɗauko ta, shima koda ya yi mata magana kan dawowa ta nuna masa sai hutun ya ƙare zata dawo, da ya yi ma mom magana kan ta ƙyale ta ai sati biyun kaman gobe ne, haka ta ƙaraci fushinta akansa. A kwana a tashi har Salma ta yi sati shidda a Kaduna lokacin kuma hutun su ya ƙare har ta fara shirin komawa gida, ana saura kwanaki ta tafi Dr Hisham ya ɗauke ta ya kaita wani babban mall, ganin ta ƙi sakin jiki ta ɗauki kaya ya sa da kansa ya shiga ɗaukar mata, kaya masu yawa ya siya mata, duk da Salma ta marairaice masa kan sun yi yawa ya ce ai ba roƙon sa ta yi ba, ita kanta aunty Kubra sai da ta masa maganar yawan kayan bayan ya maida ta gida, ya ce mata ba komai ko ba wani abu tsakanin su ita tamkar ƙanwarsa ce, ƙarshe saidai suka yi masa godiya, a yadda ya so ma shi zai maida Salma Funtua, ya ce ma aunty yana son ya je ya gaishe da iyayenta ya gabatar masu da kansa, duk da dama sun riga sun san da maganarsa don aunty ta sanar masu, aunty Kubra ta ce masa tare take son su tafi ta maida ta sannan ta ɗan kwana biyu don ta jima bata je ba, ta ce ko ya bari daga baya sai ya je ya amince da hakan, ita kanta aunty sosai ta siya ma Salma kaya har da sababbin ɗinkuna ta yi mata kamar dai yadda dama ta saba yi mata idan ta je hutu. Leemarh ta fito cikin falon tana sanye da atamfa mai kyau ta yafa gyale, hannunta ɗaya tana janye da trolley Binafa na biye da ita da wata jaka, cikin falon gidan suka ƙaraso duk ƴan gidan suna a nan zaune har da Fahad, mommy ta kalle ta da murmushi ta ce, "Daughter an gama shiryawa?" Leemarh da duk ta yi sukuku da ita saboda tafiyar da zata yi cikin sanyin jiki ta ɗaga mata kai, Khaleel da suka zo weekend ya kalle ta yana murmushi ya ce, "Sis Leemarh sai kuma yaushe?" Ta kalle shi a sanyaye ta ce in aka yi wani hutun in sha Allah, ya jinjina mata kai, "Ya Leemarh za mu yi missing ɗin ki wllh." Ta kai idonta kan Sadeeq da ya yi maganar ta ɗan yi murmushi kawai, Sadeeya ce ta shigo cikin falon ta nufo su, gaban Leemarh ta zo tana murmushi ta miƙa mata ƴar babbar ledan data ruƙo ta ce, "Sis Leemarh ga wannan kya yi amfani da su." Leemarh ta amsa ta yi mata godiya, Fahad da shine zai maida ta Abuja ya ce, "Shike nan zamu iya tafiya?" Mommy ta ce bari a sanar ma daddyn su za su tafi, Sadeeq ne ya tafi sanar masa, bada jimawa ba suka dawo tare da daddy yana sanye da jallabiya, daga gefen Leemarh ya tsaya yana murmushi ya dafa shoulder ɗinta ya ce, "Daughter za a yi mana halin baƙo?" Ta ɗaga ido ta kalle shi ta yi ɗan murmushi kawai, "Allah Ya tsare Ya kai ku lafiya. Mun gode kwarai Allah Ya bada ladan zumunci." A hankali ta amsa da Amin, "Za a sake zuwa mana wani hutun ko?" Ta ɗaga masa kai alamar eh, kallon Fahad daddy ya yi ya ce ya tashi su je lokaci na tafiya, Fahad ya miƙe ya zo ya kama trolley ɗin da ta fito da shi, Khaleel ya ɗauki wani box da ke anan falo, Sadeeya ta ɗauki jakar da Binafa ta fito da ita, gaba ɗayansu suka rako su harabar gidan, Fahad ya bude boot ya saka trolley ɗin duk sauran kayan ma aka saka, daddy ya kira Fahad daga gefe ya kai hannu cikin aljihun jallabiyar jikinsa, kuɗi masu yawa ya fiddo ya miƙa ma Fahad suka ɗan yi magana kafin ya koma wurin motan ya buɗe driver seat, Mommy ta kalli Leemarh tana murmushi ta ce, "To daughter Allah Ya kiyaye hanya Ya kai ku lafiya. Mun gode sosai, za mu yi missing naki." Leemarh ta matsa ta faɗa jikin mommy tana ƙoƙarin hana ƙwallan da suka taho mata zubowa, momy na murmushi take ɗan shafa bayanta, bayan ta ɗago haka ta bi sauran matan suka rungume juna, Sadeeq ma suka ɗan rungume juna, Khaleel ya kama hannunta yana murmushi ya yi mata Allah Ya tsare, Fahad dake tsaye ya dafa motan yana kallon su, ɗan murmushi ne akan face ɗinsa, a zuciyarsa yana raya ya san idan suka yi aure ba ƙaramar fahimtar juna za a samu ba tsakaninta da family ɗinsa, ta 6angaren su baya hango za a samu wata matsala, jiki a sanyaye Leemarh ta nufi motar, tsayawa ta yi daga gaban kofar ta juya tana kallon su ta ɗaga masu hannu, suma duk suka ɗago mata har da daddy, tuni Binafa ta fara yin hawaye, ta so a tafi da ita to sai dai shi Fahad ɗin idan ya maida ta gobe idan Allah Ya kaimu zai taho ya tsaya wurin aiki, bayan ta shiga cikin motar shima Fahad ya shiga daga haka ya tashi motar, suna ta ɗaga ma juna hannu yayin da motar ta tunkari gate har suka fice, a hankali Leemarh ta kai hannu tana goge ƙwallan da suka zubo mata, Fahad ya ɗaga ido yana kallonta ta cikin madubi. Bayan sun baro gidansu Fahad gidan hajiya suka wuce, duk da jiya da dare ya kai Leemarh ɗin ta yi mata sallama amma hajiyar ta ce kafin su tafi yau su biyo, lokacin da suka shiga cikin falon ba kowa, Fahad ne ya nufi ɗakinta don ya yi mata magana, tare suka fito hajiya ta nufo Leemarh da ke a tsaye, daga gabanta ta tsaya tana murmushi ta ce, "Haleematu baƙo zai yi halinsa?" Kai Leemarh ta ɗan jinjina mata, "To Allah ubangiji Ya tsare hanya Ya kai ku lafiya." nan ma kai Leemarh ta ɗaga mata don ji take da ta yi magana kuka zai taho mata, Balaraba hajiya ta ƙwala ma kira ta fito ta nufo su, hajiya ta ce, "Ƴar hutun mu ce zata tafi." Balaraba ta kalli Leemarh da ɗan murmushi ta ce, "Allah Ya tsare Haleematu Ya kai ku lafiya." a hankali ta amsa mata, hajiya ta ce ta je ɗakinta ta dauko akwati na nan gefen gado, bayan Balaraba ta kawo akwatin ta ce zata ɗauko ma Leemarh abu, kicin ta nufa bada jimawa ba ta dawo tana rike da wani package, miƙa ma Leemarh ta yi tana murmushi ta ce, "Haleematu ga snacks da na yi maki kya ci a hanya." Leemarh ta amsa ta ce ta gode, nuna ma Fahad akwatin hajiya ta yi ta ce ya ɗaukar mata, hajiya na riƙe da hannun Leemarh suka fito Balaraba na biye da su, hajiya ta ce, "Haleematu sai an ƙara zuwa mana wani hutun ko?" Kai ta jinjina mata sai kuma ta yi saurin faɗawa jikinta jin kuka ya taho mata, hannu hajiya ta sa tana ɗan bubbuga bayanta tana murmushi tare da rarrashinta tana faɗin ta kwantar da hankalinta ai ba ta gama zuwa hutun ba ke nan, da ƙyar ta saki hajiya ta shiga mota, suna ta ɗaga ma juna hannu a haka suka fito daga gidan. Tun da suka hau hanya Leemarh was so silent, ta jingina kanta a jikin kujera tana ta kallon gefen hanya, lokaci lokaci Fahad ke ɗaga ido ya kallo ta ta mirror ko kuma ya ɗan juya, bai tanka mata ba ganin yanayinta saboda ya riga ya san abun da ke damunta, tun ana saura kwanaki zata tafi take faɗa masa game da yadda zata yi missing ɗin su musamman shi, bayan sun yi nisa a tafiya ganin shirun nata ya yi yawa calmly ya kira ta ta juya ta kalle shi, da ɗan murmushi ya ce, "Ya aka yi ne?" Shiru ta yi tana kallon shi, bayan ya juyo sun haɗa ido ta ɗan girgiza masa kai ta ce ba komai daga haka ta juya ta ci gaba da kallon hanya. Lokacin da suka iso Kaduna lokacin sallar azahar ya fara shiga hakan ya sa Fahad ya tsaya wurin wani masallaci ya ce mata bari ya yi salla ta ɗaga masa kai, after some minutes ya dawo ya buɗe driver seat ya tsaya ba tare da ya shiga ba ya ce mata ko itama zata yi sallan ya ga akwai 6angaren mata, slowly ta girgiza masa kai ta ce bazata yi ba, shiru ya yi yana kallonta nan take kuma ya gane bata yin sallan ne, shiga ya yi ciki ya zauna yana ƙoƙarin kunna motan ya ce bari su samu wani eatery sai su ci abinci, kallon shi Leemarh ta yi a sanyaye ta ce, "Ni ba wani yunwa nike ji ba." Fahad ya juya ya kalle ta ya ce, "Amman dai ai ba har mu je Abuja ba zaki ci komai ba." Ta ce to ai ga snacks da aunty Balaraba ta bata ko shi sai ta ci, ɗan jinjina kai ya yi ya ce ok bari to a samu lemu sai ta haɗa, bayan sun fara tafiya ta kalle shi ta ce to shi ba zai ci abincin ba, idanunsa akan hanya ya ce lafiya lau shima sai ta samma shi snacks ɗin ya ishe shi. Tun da Leemarh ta ga sun kusa isa Abuja yanayinta ya ƙara sauyawa, damuwa ta bayyana akan fuskarta, haka nan take jin bata son komawa, Fahad dake kallonta akai akai ta mirror har ya gane damuwar da ta ƙara bayyana akan fuskarta, ɗan kallonta ya yi ya kira sunanta ta juya ta kalle shi, calmy ya ce, "What's wrong?" Kai ta ɗan girgiza masa ba tare da ta ce komai, ta langa6ar da kanta tana kallon gefe, bayan ɗan lokaci ta yi saurin juyowa ta kai idanunta kan hannun Fahad da ta ji ya kama nata hannun da ta ɗaura akan lap ɗinta, bin hannun nashi ta yi da kallo ya yin da ƙirjinta ke ɗan bugawa, don tun da ta zama budurwa ya daina ta6a ta ba kamar lokacin da take yarinya ba, ɗan kallon shi ta yi idonsa na akan hanya yana driving da hannu guda, sauke idonta ta yi tana ta kallon hannun nashi, after a while still yana riƙe da hannun nata ta ji muryar shi ya ce, "Idan kuka samu wani hutun da gaske zaki ƙara zuwa?" kallon shi ta yi a ranta tana jin rashin tabbacin hakan saboda yadda ya faru tsakaninta da mom ɗinta kafin ta zo wannan hutun, amman tana jin komai zai faru idan aka ƙara yi masu hutu nan zata zo, a hankali ta ɗaga masa kai ta ce eh, shiru ya ɗan yi sai kuma ta ji ya tambaye ta hutu nawa za su ƙara samu kafin su yi graduation, ta bashi amsa da biyu ya ɗaga kai idanunsa akan hanya, "Zaki iya dawowa Funtua da zama?" Da sauri Leemarh ta kalle shi jin tambayar da ya yi mata, juyowa ya yi suka haɗa ido ya ce, "I mean....dawowa na har abada" Kallon shi tai ta yi ya maida idonsa kan hanya, ɗan kallonta ya yi ya ɗage mata gira, slowly ta jinjina masa kai alamar eh, sakin hannunta ya yi ya ci gaba da driving ba tare da ya ce komai ba, maida kanta ta yi gefe ta ɗan yi murmushi don ta fahimci inda maganar tashi ta dosa, hakan kuma ya sa ta ɗan rage jin damuwar dake a ranta, nan take ta ji inama zata iya janyo lokacin.... *✨A CIKIN RAYUWA✨* ZAINAB BATURE 48 Wuraren la'asar su Leemarh suka iso Abuja, lokacin da suka isa gida, cike da farin ciki su Batool da Sultan har da daddyn su suka tarbe su a haraban gidan, ciki suka nufa daddy na yi ma Fahad ya hanya, su Batool sun kakkama Leemarh sosai suke ta murnar dawowar ta, a nan cikin babban falon suka zauna daddy na faffaɗan murmushi idonsa akan Leemarh ya ce, "Leemarh ƴan hutu, hankali ya kwanta ko an sha hutu a Funtua." Murmushi kawai ta yi masa, Batool ta ce, "Yaya Leemarh da muka dawo daga Kano saida muma muka ce muna son zuwa Funtua wurin ki momy ta ce bamu zuwa." Daddy ya yi saurin cewa, "Ai saboda hutun ya kusa ƙarewa ne, ku ma zaku je idan aka ƙara yi maku hutu." Leemarh dai ta yi shiru a ranta tana tunanin yadda itama za su ƙare da mom ɗin idan aka ƙara yin wani hutu ta ce zata Funtua, bayan ɗan lokaci ta tambayi Batool ina mom bata ganta ba ta ce mata tana part ɗinta, shiru Leemarh ta yi tana tunanin bata san ta dawo bane da bata zo ta tarbe ta ba, dad ya ce ma Leemarh ta je ta yi ma chef Alima magana ta shirya abinci ba a san ko Fahad na jin yunwa ba, Fahad na ɗan murmushi ya ce ai baya jin yunwa, miƙewa Leemarh ta yi ta nufi kitchen, cikin fara'a su chef Alima suka tarbi Leemarh tare da yi mata an dawo lafiya, bayan ta sanar da su a kai abinci dining ta fito ta wuce bedroom ɗin mom ɗinta, kwance ta iske ta hannunta riƙe da wayarta tana amsa kira wanda aka yi mata ya tashe ta daga baccin da take yi, tsayawa gefe Leemarh ta yi tana jiran ta gama, bayan dan lokaci ta gama yin wayar ta ɗaga ido ta kalle ta kafin ta janye idanun nata, bayan ta ajiye wayar ta maida kanta saman pillow ta kwanta, jikin Leemarh ne ya yi sanyi ganin halin ko in kulan da ta nuna mata, kamar ta juya ta fito daga ɗakin sai kuma a sanyaye ta ce, "Mom baki ga na dawo ba?" Ɗago ido ta yi ta watsa mata wani kallo ta ce, "To idan na ga kin dawo sai in yi maki mi? Ai da kin zauna can kawai ba sai kin dawo ba." Leemarh ta yi shiru tana bin ta da kallo can ta ce, "Ki yi haƙuri." Shiru bata ce mata komai ba, jiki a sanyaye Leemarh ta nufi barin ɗakin, mom ta yi ƙwafa rai 6ace ta ce, "Zan ɗauki mataki ne, ba zan zuba ido duk a mallake mani ko ba da kowa idan ya je sai ya samu wuri bai sai dawowa, don munafunci yaushe kika ta6a zuwa Kano hutu kika zauna haka." Duk Leemarh na jinta har ta ƙarasa ƙofa ta fita, lokacin da ta dawo falo Batool kawai ta iske ta sanar da ita cewa su dad sun tafi salla, itama Leemarh ta wuce zuwa ɗakinta, jikinta duk ya yi sanyi duk da ta san halin mom ɗin nasu amman bata ji daɗin abun da ta yi mata ba. Bayan sun dawo daga masallacin ta fito suka zauna cin abinci tare da Fahad, kaitsaye 6angaren mom dad ya nufa, har lokacin tana a kwance amman ba bacci take ba, ta ɗaga ido ta kalli dad da ya shigo kafin ta janye idanunta, daga bakin gadon ya tsaya ya ce, "Ashe idanun ki biyu, baki ga lokacin salla ya yi bane." Shiru bata ce masa komai, ya ce, "Ga su Leemarh sun iso tun ɗazu, yakamata ki fito ku gaisa da Fahad." Nan ma bata tanka sa ba, sai da ya ƙara ce mata bata ji yana magana ba sannan ta wurga masa wani kallo ta ce Fahad ɗin wani babban baƙo ne da dole sai ta taso sun gaisa, shiru dad ya yi fuskarsa ta nuna alamun 6acin rai, ganin haka ta sake cewa, "Ba yana a gidan ba ko yanzu zai tafi, idan na fito mun gaisa." Shiru bai ce mata komai ba sai ma ya juya ya nufi barin ɗakin ta bi sa da wani kallo. Da daddare bayan dad sun dawo daga sallar magrib tare da Fahad, a nan main falo suka zauna dad ya kira Leemarh ta waya ya ce ta je ta gyara ma Fahad part ɗin Deen, koda Leemarh ta je a kulle ta iske part ɗin, ta dawo wurin dad ta sanar masa, da ɗan alamun mamaki dad ya ce waye ya rufe part ɗin ta ce itama bata sani ba, ya ce ta je ta tambayi mom ɗinsu ko makullin part ɗin na wurinta, bayan Leemarh ta iske ta a ɗakinta ta tambaye ta, fuska a haɗe ta ce bata san inda yake ba, shiru Leemarh ta yi tana kallonta kafin ta juya ta tafi a cikin ranta tana mai zargin ita ce ta rufe part ɗin ta 6oye makullan, koda ta koma ta sanar ma dad shima shiru ya yi a ransa yana zargin mom ɗin ce zata dauke makullan don in ba ita ba waye zai aikata hakan, Fahad da ke zaune ya ce ma dad lafiya lau zai yi amfani da part ɗin baƙi tun da ba ga keys ɗin ba, shiru kawai dad ya yi ya san ko ya je ya yi mata magana ba bada makullan zata yi ba. Bayan sallar isha suka zauna cin abinci har da dad amman ban da mom da har lokacin bata zo sun gaisa da Fahad ba, bayan sun gama Fahad ya wuce part ɗin baƙi da dad ya sa an gyara masa. Bayan Leemarh ta gama yin shirin kwanciya ta ji tana son zuwa wurin Fahad su yi hira don gobe da safe zai wuce, fitowa ta yi zata je wurinsa sai kuma ta tuna da yana shan baƙin shayi duk dare, don da tana Funtua ma ita ce ke haɗa masa, kitchen ta wuce ta fara haɗa masa, bayan ta gama ta zuba a cikin wani ɗan madaidaicin flask ta daura a saman tray ɗinsa ta haɗa da cup da spoon sai sugar, tana riƙe da tray ɗin jikinta sanye da doguwar rigar bacci ta yafa gyale a a saman kai ta fito ta nufi ƙofar da zata fita baya, tana kusa kaiwa kofar ta ji muryar mom ɗinsu tana tsaida ita, juyowa ta yi tana kallon mom da ta nufo ta jikinta sanye da riga da wando na bacci, wani kallo ta jefa mata bayan ta iso gabanta ta ce mata ina zata je, Leemarh ta ce, "Zan kai ma yaya Fahad ne." mom ta ɗaure fuska ta ce, "Dama aikin ki ne hakan idan aka yi baƙo?" Ɗan ɗaure fuska Leemarh ta yi ta ce, "To ai shi ba baƙo bane ko." Mom ta watsa mata wani kallo ta ce, "Idan ba baƙo bane shi minene? Ko nan ɗin gidansu ne?" Leemarh ta yi ɗan kasa da murya ta ce eh ai nan kaman gidan su ne, "Idan sai ke ce zaki kai masa sai dai idan kada ya sha, je ki maida su kitchen!" Tura baki Leemarh ta yi zata yi magana mom ta kwatsa mata tsawa tare da nuna mata hanyar kitchen, tsaye mom ta yi a bakin ƙofar kitchen ɗin har saida ta je ta ajiye kayan ta fito, bayan ta fito fuska a ɗaure ta wuce ba tare da ta kalli mom ɗin ba ta nufi komawa ɗakinta, mom ta ɗaga murya tana faɗin, "Wllh idan kika je kai masa abun nan ranki sai ya 6aci." Leemarh bata ce mata komai ba bata kuma juyo ba, bayan ta koma ɗakinta a bakin gado ta zauna ranta a 6ace, har cikin ranta tana son ta je wurin shi su yi hira ba kamar da zai tafi gobe, ta ɗauki ɗan lokaci a haka, can ta kai hannu ta janyo wayarta, kiran sa ta yi bai ɗaga ba har ta tsinke, sai gashi ya biyo kiran, bayan ta ɗauka ya ce, "Leemarh..." A sanyaye ta amsa, "Baki yi bacci ba?" Ta ce masa eh, ya ce, "Yakamata zuwa yanzu kin yi bacci don ki ƙara hutawa sosai, ga gobe zaku yi resuming school." Shiru ta ɗan yi sai kuma ta ce, "Kawai bana jin baccin ne, ina tuna da a Funtua ne yanzu muna tare muna hira, ko kana aiki ina taya ka zama muna yin hira." Tana jiyo ɗan murmushin da ya yi ya ce, "Ko har kin fara missing hakan ne?" A hankali ta ce eh, "Idan kina so sai in zo mu yi hiran." Har sai da ta ɗan buɗa ido alamar jin daɗi ta ce masa ba abun da yake yi ne, ya bata amsa da eh kawai yana kallo ne, ta ce to idan bata takura mashi ba, bayan sun gama ta miƙe fuskarta da murmushi ta nufi ƙofa ta fita, tana zuwa cikin babban falon sai gashi ya shigo ta kofar baya jikinsa sanye da pajamas, murmushi suka shiga sakar ma juna har ya ƙaraso inda take ya zauna akan kujera, ta ce bari ta kawo masa shayi ya ɗaga mata kai, bayan ta dawo a saman table ta ɗaura ta haɗa masa don har yanayin yadda yake son sugar ta sani, itama ta haɗa wani ta zauna a kusa da shi a saman 2 seater da yake zaune, a nutse suke shan shayin su suna ɗan yin hira, after a while sai ga mom ta shigo cikin falon, tsayawa ta yi daga bakin part ɗinta tana bin su da kallo da alamun mamaki da kuma 6acin rai, wato Leemarh ta raina ta har haka, data hana ta kai mashi shine ta kira shi nan, gashi kana ganin a yadda suke zaune dole ma ka zargi akwai soyayya a tsakanin su, aikuwa zata nuna ma Leemarh iyakarta, a fusace ta nufo su tana kusa zuwa inda suke Leemarh ta lura da ita nan take ta sha jinin jikinta, ganin in da Leemarh ke kallo da yadda yanayin fuskarta ya sauya ya sa Fahad juyawa suka haɗa ido da mom wadda tun da ya zo sai yanzu ya ganta, daidai tana zuwa in da suke dad ya shigo cikin falon dama fita ya yi, tsaye ta yi ta fasa yin abun da ta yi niyya, Fahad ya gaishe da ita ta amsa masa a daƙile, ƙarasowa dad ya yi wurin su da murmushi akan fuskarsa yana kallon Leemarh ya ce mata bata yi bacci, cikin jin daɗin zuwan nashi tana murmushi ta ce, "Eh, yaya Fahad nike tayawa hira." dad ya jinjina kai ya ce ya yi kyau, kallon mom data yi tsaye kamar an dasa ta fuska a haɗe ya yi, ya tambaye ta ya aka yi ne, ta ɗauke kai tare da ce masa ba komai ta zo ta ce ma Leemarh ta je ta kwanta don gobe za su je school, dad ya ce, "Ki rabu da ita tun da bata jn baccin, ta ce tana taya yayanta hira ne." Ya yi maganar yana murmushi ya ce mata su je ciki, fuska a daure ta kalle shi kaman bazata tafin ba, harara ta wurga ma Leemarh kafin ta juya suka tafi, murmushi ne akan fuskar Leemarh don ta ji daɗin taka mata burkin da dad ya yi, shi dai Fahad shiru ya yi don ya fahimci abun da mom ɗin ta yi niyyar yi, sai dai a ransa yana jin ya shirya ma kowane irin abu da zai fuskanta a wurinta don yanzu sosai yake jin son Leemarh a cikin zuciyarsa. Washe gari da safe a tare gaba ɗaya suka yi breakfast kasantuwar ranar monday ne amman ban da mom, bayan sun gama Fahad ya yi sallama da dad a tare gaba ɗaya suka fito, dad zai wuce wurin aiki shi kuma Fahad ya ce zai yi dropping su Leemarh a school kafin ya wuce, bayan sun iso school ɗinsu Leemarh, har da kukanta da za su rabu, ya ji duk wani iri kamar ya koma da ita sai dai ya san hakan ba mai yuwuwa bane, rarrashinta ya yi ya ce mata idan suka samu wani hutun da kan shi zai zo ya ɗauke ta, hakan ya sa ta ɗan ji sanyi a ranta suka yi sallama cike da nuna za su yi kewar juna ya tafi. A ranar da daddare bayan sun gama cin abinci , Leemarh ta sa Batool da Sultan suka taya ta fiddo da kayayyakin da aka bata a Funtua, gidan su Fahad akwati guda aka yi mata na sababbin ɗinkakkun kaya har da su Batool, da su gyale da takalma har da su sarƙa da yan kunne, ledar da Sadeeya ta bata kuma nan underwear ne sabbabi da su perfume da roll on, shima Fahad tsadaddun sets ɗin mayukan shafawa da na gashi ya siya mata har da abayas masu kyau, sai kuɗi dubu ɗari da daddy ya ba Fahad ya bata, dama wasu daga cikin kayan da aka ɗinka masu daddy ne ya bada kuɗin, 6angaren hajiya itama akwatin kaya ta yi masu da Sultan da Batool har da su takalma da inner wears, dad ya bi kayan da kallo fuskarsa ta nuna jin dadi sosai, kallon mom ya yi ya ce, "Kin ga kaya kaman wani lefe." Babu yabo babu fallasa ta ce unhm, da yake mutum idan yana hali sai ya ɗauka ma kowa irin sa ne, mom gani take da gayya suka haɗo masu wannan uban kayan, sosai yaran suke ta farin cikin kayan, duk da hajiya ta saba aiko masu da kaya amman Leemarh ta ji daɗin wadannan sosai don bata ta6a zuwa hutu aka haɗo ta da kaya haka ba, dama Kano ne take yawan zuwa, can kuwa wani lokacin ita ake buƙatar wani abun ma a wurinta, wasu abubuwan ma nata ƙiri ƙiri idan ta je ake nuna ana so a raba ta da su, dad ya kalli mom a karo na biyu ya ce, "Yakamata ki kira su sai ki yi masu godiya." Wani kallo ta jefa masa, fuska a haɗe ta furta, "Ba don Allah aka yi masu ba da sai an yi godiya." Dad ya ce, "Wace irin magana ce haka, ko don Allah aka yi wanda ya yi ma naka wannan hidimar ai ya cancanci ka kira sa ka yi masa godiya." Ɗan tabe baki ta yi ta kauda fuskarta gefe, can ta miƙe tana faɗin ai ko shi zai iya kira ya yi masu godiyan, daga haka ta nufi hanyar part ɗinta, dad ya bita da kallo rai a matuƙar 6ace har ta shige, haka Leemarh da duk ta ji abun da ta faɗa ta bita da kallo fuskarta a haɗe, janye idonsa dad ya yi bayan ta shige, har cikin ransa yanzu ya gaji da halin Jameela, ya rasa gane ita ɗin wani irin hali ne da ita, wani mutum zaka ga idan aka ɗauki shekaru yana canza hali, amman ita kusan halin nata ƙaruwa yake koda yaushe, a da yana haƙuri da kauda kai a dukkanin abubuwan da take masa saboda son ta da yake sosai, to amman yanzu ta fara kai sa wuya kuma yana jin yana son ɗaukar mataki akanta, to amman ta yaya? Duk lokacin da ya yunƙuro zai ɗauki mataki kanta ƙarshe kasa ta6uka komai yake, ƴar ajiyar zuciya ya sauke bayan ya gama tunanin da yake, wayarsa ya ɗauka ya kira hajiyarsa, bayan ta ɗaga kiran cikin girmamawa ya gaishe da ita daga baya ya yi mata godiyar hidimar da aka yi ma su Leemarh tare da addu'oi, bayan ya gama yin godiyar tashi ya ba su Batool da Sultan suma duk suka yi mata godiya har suna ce mata idan aka yi masu hutu suma za su zo, hajiya ta ce to Allah Ya kaimu Ya kawo su lafiya tana jira, Leemarh ma ta amsa wayar ta ƙara yi mata godiya ta ce mata wllh duk tana missing nasu, bayan sun gama yin waya da hajiya, dad ya kira daddy Sa'ad shima suka yi masa godiya, bayan sun gama ya kira mommyn su Fahad itama duk suka yi mata godiya, Leemarh ta amsa itama ta ƙara yi mata godiya, ta sigar shagwa6a ta ce, "Wllh mommy duk na yi missing ɗin ku, ina jin kaman na dawo." Tana jiyo sautin ƴar dariya da mommy ta yi ta ce, "Muma daughter muna missing naki, musamman yadda kike cika mu da abubuwan daɗi, yanzun nan su Binafa ma suka gama magana wai da kina nan da kin haɗa masu abun dadi." Leemarh ta yamutsa fuska tana jin kaman ta ganta a Funtua, dad nata kallon ta suna wayar cike da jin daɗi, bayan sun gama dad ya kira Fahad ya ƙara yi masa godiya da ban gajiya, duk da ɗazun ma ya kira sa ya yi masa ya hanya lokacin ya sanar mashi har ya isa Zaria, suma yaran duk sai da dad ya basu suka yi masa ya ya isa, Leemarh ma ta ƙara yi mashi ban gajiya da godiya duk da sun yi waya da shi har sau biyu bayan tafiyarsa. Bayan Shekara Ɗaya...... *✨A CIKIN RAYUWA✨* ZAINAB BATURE 49 A Year Later.... A kwana a tashi ba wuya a wurin Ubangiji, cikin nasara har Salma ta kammala karatun secondary ɗinta, yanzu haka tana a Kaduna wurin auntynta Kubra tana zaman jiran result ɗin su ya fito ta ci gaba da karatu, a 6angaren aikin da take yi ma Deen, har yanzu tana yin aikin sai dai ku san aikin ya koma hannun Sageer tun da ita bata nan, a duk wata yake turo mata da albashinta, sai dai har yanzu ba wani lokacin yin magana da shi take samu ba, har yanzu idan ta tura masa saƙo wani sa'in sai an ɗauki lokaci yake dubawa ya yi mata reply, ko da ya bata number din da ya ce idan tana son magana da shi ta yi amfani da ita, sam bata wani yin amfani da layin sosai don gani take koma ta yi amfani da number ɗin to mi zata ce masa, dama dai ko saƙo zata tura masa bai wuce kan aikin da take yi masa ba sai kuma gaisuwa, hakan ya sa tafi yin amfani da layin da ta saba yin magana da shi kawai. A 6angaren Dr Hisham kuwa har yanzu suna tare, duk da har lokacin bata wani sakin jiki da shi sosai kuma bata buɗe baki ta faɗi masa tana son sa ba, amman dai tana kula shi kuma duk hidindimun da ya saba yi mata bai fasa ba sai ma abun da ya ci gaba, yanzu haka jira yake result ɗin ta ya fito ya ɗauki nauyin karatun ta. Maleek na riƙe da hannun Sapna da Basma suka fito wajen gidan, James da ke a tsaye bakin mota yana jiran Maleek ya fito ya kai sa airport ya nufo Sapna ya kar6i jakar Maleek da take riƙe da, dama tuni an fito da suitcase ɗin kayansa an saka a boot, jikin Maleek na sanye da bakaƙen suit masu kyau ya kalli Sapna da murmushi ya furta, "Sai na dawo my love." Cikin marairaice fuska ta ce, "We will miss you honey. Allah Ya tsare Ya kai ka lafiya." Ya amsa da Ameen tare da yin hugging ɗinta ya sumbaci gefe da gefen fuskarta, sakin ta ya yi ya maida kallon sa kan Basma suka haɗa ido, cikin sanyin murya da turanci ta furta, "Sai ka dawo dad, Allah Ya kai ka lafiya." Kai ya jinjina mata tare da kai hannu ya rungumo ta jikinsa, ƙasa da murya ya furta, "Take care..." Daga haka ya ɗago, Basma ta kalle shi cikin ido tana tuno da maganganun da ya yi mata jiya da daddare, daga haka ya nufi motar suna ɗaga ma juna hannu, bayan James ya buɗe masa back seat ya shiga ya zauna, shima ya zagaya 6angaren driver ya shiga, suna ta ɗaga ma juna hannu yayin da motar ta fara tafiya har suka fita daga cikin gida, Sapna ta juya ta kalli Basma, kama hannunta ta yi suka nufi komawa cikin gidan. Wuraren ƙarfe ukkun rana wata napep ta faka a gefen titi, bayan ɗan lokaci wata budurwa ta fito daga ciki, a yanayin halitta tana da matsakaicin tsawo sam ba gajera bace, sannan ba za a kira ta da siririya can ba don tana da ɗan cikan jiki, fatarta fara ce tas irin farin nan mai tafiya bai ɗaya, tana da kyawun fuska wadda take round face mai ɗauke da manyan idanu da dogon hanci tare da ƙaramin baki, daga yanayin gashin idonta da na girarta zaka fahimci tana da yalwatacciyar sumar kai, a jikinta tana sanye da doguwar riga A-shape ta atampa mai kyau, ɗaurin kallabin dake a kanta ya bayyana sumarta dake a naɗe, ta yafa gyale da ya hau da kayanta a saman kafaɗa ta rataya jaka, juyawa ta yi tana kallon ginin da aka ajiye ta a gaban shi wanda rabin katangarsa aka yi fencing mai kyau, tafiya ta fara yi a nutse ta nufi gate ɗin shiga wurin wanda shima yake mai kyau ta shige, harabar wurin na da girma sannan an ƙawata ta da rumfuna masu ɗauke da kujeru da tebura masu kyawun gaske, akwai tsarin shuke-shuke na fulawowi masu matuƙar kyau da ƙayatarwa da suka sanyaya wurin, wasu cikin flowers ɗin sun yi ma rumfunan wurin ƙawanya gwanin burgewa, rubutun da ke a saman ginin wurin ya bayyana cewa wurin shaƙatawa ne da kuma cin abinci, a saman kujerun da ke wurin akwai mutane maza da mata, wasu suna cin abubuwan ci da sha, wasu suna hira, wasu kana ganin su ka san masoya ne, daga can gefen ginin swimming pool ne da aka ƙawata wurin da rumfuna da kuma kujerun kwanciya wato sunbeds, ba ƙarya dai wurin ya ƙawatu iya ƙawatuwa, yayin da matashiyar budurwar ta shigo ciki tana tafiya a nutse, wasu daga cikin samarin dake zaune a wurin sun kasa ɗauke idanunsu akanta, har da masu yi mata magana suna mata tayin kan su, ita dai bata kula kowa ba tafiyar ta take idanunta na kallon gabanta, bayan ta kai ƙarshen hanyar da take bi ta ɗaga ido tana kallo cikin veranda din ginin in da nan ma wasu kujeru da teburan zama ne, hango wanda take nema ta yi a zaune, dama yawanci nan take yawan samun sa, lokaci guda ta ji jikinta ya yi sanyi don tare da mace ta hango sa zaune, duk da tama saba da iske shi tare da mace wani lokacin bama ɗaya ba, a sanyaye ta nufi steps ɗin hawa veranda ɗin, tana shiga suka haɗa ido da shi ta nufi inda suke tana tafiya a hankali, daga gefe ta tsaya suna kallon juna, cikin muryarta mai tattare da natsuwa ta ce, "Yaya Bash ina yini." Amsa mata ya yi, idon shi a kanta ya ce, "Ya school, daga can ma kike ko?" Kai ta ɗaga masa ta ce eh, juyawa ya yi ya kalli wadda suke zaune ya ce, "Zee meet my cousin sis Fadeela." Zee ɗin wadda kana ganinta ka san farinta na kanti ne, gashi ta yi wata shiga wadda idan ba ka santa ba ba zaka gane ita din musulma ce ko akasin haka, ta ɗan yamutsa fuska ta furta ok tare da ɗan ɗaga hannu tana bin Fadeela da wani kallo mai kaman na kishin mutum ya fika ɗin nan, "Fadeela have a seat." Bash ya faɗa yana kallonta, jim ta yi ba tare da ta zaunan ba, ganin hakan ya ce, "Ko da wani abu ne?" Idonta akan shi a hankali ta ce, "Ina son yin magana da kai ne." Shiru ya ɗan yi sai kuma ya ce ok, kallon Zee da ta wani haɗe fuska ya yi ya ce mata ta ɗan bashi lokaci yana zuwa, miƙewa ya yi tare da yi ma Fadeela alamun su je da hannu, fita suka yi daga cikin veranda ɗin suka nufi harabar wurin, a saman kujerun dake a wurin ya zauna itama Fadeela ta zauna suna fuskantar juna, "Mi kike so a kawo maki?" Tana kallon shi cikin ido ta ɗan girgiza masa kai ta ce ya basshi, shiru suka ɗan yi ta kasa tsayar da idanunta wuri guda kamar irin ta rasa ta ina zata fara masa magana, "Ina jin ki, kin ce kina son yin magana da ni." Ya faɗa tare da ɗage gira, ɗago fararen idanunta ta yi ta kalle shi, cikin sanyin murya ta ce, "Dama ba wani abu bane, kan maganan da muka yi da kai ne, ka ce zaka zo gida amman shiru baka zo ba, kuma na kira ka ka ƙara ce mani kana nan zuwa, gashi yanzu har an yi sati guda..." Bin ta ya yi da ido yana mata wani kallo, can ya ɗan kauda idon shi tare da ɗage gira ya ce, "Yanzu zuwa kika yi ki ji dalilin rashin zuwan nawa ke nan?" Kaman bazata ce komai ba sai kuma a hankali ta ce masa eh, juyowa ya yi suna kallon juna cikin ido ya ce, "Dama ba zuwan zan yi ba, kawai na faɗa maki hakan ne don ki bar ni na huta." Fadeela ta ɗan buɗa ido alamar mamakin maganar, sauke idonta ta yi na ɗan lokaci kafin ta ɗago idanunta da har sun cika da ƙwalla, cikin rawar murya ta ce, "Ya Bash mi yasa kake wulaƙanta ni? Kawai don ina son ka shine laifi na?" Tana kai maganar ƙwallan suka zubo mata sharr, hannu ta kai tana gogewa tare da juyar da fuskarta, Bash da ke kallon ta ya ɗan yamutsa fuska ya ce, "In da ina wulaƙanta ki Fadeela ba zan rinƙa baki lokaci na ba ina saurarar ki ba, kuma ni ban ce son da kike mani laifi bane saboda nima ina son ki, kawai na gaji da yadda kike sa muke ta maimaita abu guda ne, koda yaushe kina nuna kina sona, amman just abu ƙarami na buƙata a wurin ki kin kasa bani, a hakan kuma kike son in yarda da kina so na, bayan idan har da gaske ana son mutum ko mi ya buƙata bashi ake." Juyowa ta yi ta kalle shi cikin raunin murya ta ce, "Amman ya Bash kai ma ka san ba zaka ce bani son ka ba, saboda kai ne ko saurarar masu cewa suna so na bana yi...abun da ka buƙata a wurina miyasa ba zaka bari mu yi aure ba, lokacin gaba ɗaya ma zan zama taka." Ɗan ta6e baki ya yi ya ce, "Miye don na buƙaci hakan yanzu a wurin wadda zan aura?" Ta ce, "Amman ya Bash ka san hakan haramun ne tun da ba auren juna muka yi ba." Yana mata wani kallo ya haɗe fuska ya ce, "Ke matsalar ki ke nan, komai ki ce zaki nuna kin fi mutum sanin daidai, a tunanin ki kema akan daidai kike? Yanzu haka a tattare da ke akwai abubuwan da ba daidai bane, kin fito da gashin kan ki, kin yafa ɗan gyale, sannan jikin ki na ƙamshi, dukkan wannan abubuwan suma haramun ne kin kuma san da hakan, amman saboda abubuwa ne da zamani ya kawo an mayar da su daidai ne. Yanzu ba wani abu bane don mutum ya buƙaci sanin wadda zai aura, wasu ma tun suna fara tarayya da juna suke sanin juna har su yi aure, ai zamani ne ba wani abu ba. Wama ya sani ko already kin riga kin ba wani daman hakan shiyasa ni kika ƙi amince mani don kada in sani in canza ra'ayina akan ki." Ɗan juya kai ta yi tare da yin murmushin takaici ta ce, "Allah shine shaida na ya Bash, wllh ni ban ta6a ba wani namiji damar koda riƙe mani hannu ne da son raina. Ni a gani na idan ka so ko nan da wata ɗaya ne zamu iya yin aure." Ɗan girgiza kai ya yi ya ce, "Ban shirya yin aure nan da wata ɗaya ba, a tsarina akwai abubuwan da sai na kammala su sannan ko zan yi aure, ciki har da ginina da zan fara." Fadeela ta ce, "Ni ya Bash na amince ko gidan haya ne ka kama mani, sannan koma lefe ba sai ka yi mani ba." Wani kallon kina da hankali ya jefa mata ya ce, "Allah Ya kyauta na zauna wai a gidan haya, ai hakan ma ƙasƙanci zai ja mani yadda mutane ke ɗauka na, ni a tsarina sabuwar amarya ƙerarran sabon gida nawa na kaina." Fadeela ta ce, "Ka ce sabuwar amarya, taya zan zama sabuwar amarya idan ka samu abun da kake buƙata daga gare ni." Wani ɗan iskan murmushi ya yi ya ce, "Ai wannan tsakani na da ke ne kawai, a wurin kowa ke sabuwar amarya ce, ko kina tunanin wai idan na samu abun da nike buƙata a wurin ki zan yi dumping naki ne?" A hankali ta ɗaga masa kai, ya ce "To kima daina wannan tunanin, don hakan sai ma ƙara mani son ki da zai yi saboda na san ke ɗin tawa ce ni kaɗai, kuma idan ma na guje ki ai kaina na yi mawa tunda ke matsayin ƙanwata ce, ko wani ya yi maki hakan to sai in da ƙarfi na ya ƙare wurin kwatar maki hakkin ki." Shiru ta yi tana kallon shi, kafe ta ya yi da wani mayen kallo, burinsa kawai ta amince masa don ba ƙaramar shawarta ya ke ba, kuma ita ce mace ta farko da ya sha wahalan samun hakan daga gare ta, ɗage mata gira ya yi tare da yin ƙasa da murya ya ce, "Kin amince?" Shiru ta yi tana ta kallon shi yayin da gaban ta ke bugu sosai, gaba ɗaya fargabar amsar da zata bashi take tsakanin amincewa ko akasin hakan, nasihar da ummanta ke yawan yi mata kan riƙe maraicinta da kula da mutuncinta ta shiga yi mata yawo a kai...hannu Bash ya kai ya kama hannunta yana bin ta da wani mayaudarin kallo, ya yi ƙasa da murya ya ce, "Idan kin amince ko sau ɗaya ne na yarda." Shiru ta yi tana ta kallon farin hannunsa da ke riƙe da nata yayin da ƙirjinta yake ƙara tsananta bugu, "Zamu iya tafiya hotel yanzu?" Da sauri ta ɗago da manyan idanunta ta kalle shi, ganin duk tsoro ya bayyana a tare da ita ya ce, "Ki kwantar da hankalin ki, ba wanda zai san da hakan, akwai nose mask a mota sai ki saka yadda ba wanda zai ga fuskar ki." Nan ma shiru bata ce komai ba sai ido da take ta bin sa da shi, wani murmushi ya saki tare da miƙewa ya ce mata yana zuwa bari ya sallami Zee, har ya juya ya ji muryar ta ta ce, "Ya Bash...." Juyowa ya yi ya kalle ta, cikin rawar murya ta furta, "Ka...yi haƙuri...ba zan iya amincewa mu aikata hakan ba tare da mun yi aure ba." Wani ɗaure fuska ya yi yana jefa mata wani kallo da alamun 6acin rai, can ya ɗan ɗage kafaɗarsa ya ce duk yadda ta so, fita ta yi daga cikin kujerar zata tafi, har ta juya ta ji ya ce, "Fadeela..." Dakatawa ta yi ta juyo ta kalle shi, a kausashe ya ce, "Daga yau na yanke alaƙar soyayyar da ke tsakanin mu, don na fahimci ƙaryar so na kike, kada ki sake bibiyana, idan ba haka ba komai na yi maki ke kika siya da kuɗin ki." Yana kai wa nan ya juya ya nufi komawa in da ya taso, tsaye ta yi a wurin tana ta kallon shi har ya haye cikin veranda ɗin, jiki a matuƙar sanyaye ta juya ta nufi hanyar fita daga wurin, yayin da maganganun da ya yi suke ta mata yawo a cikin kai, sosai take ta ƙoƙarin hana hawayen da suka taho mata zubowa saboda mutanen da ke a wurin, lokacin da ta kai bakin gate ɗin wurin ta ɗan dakata tare da juyowa tana kallo saitin da Bash ɗin yake duk da bata hango shi, tsaye ta yi tana sauraran 6angarori biyu na zuciyarta dake tafka muhawara, ɗaya na goyon bayan ta amince masa tun da ya ce ko sau ɗaya ne, yayin da ɗayan 6angaren ke hana ta aikata hakan ta hanyar nuna mata haramcin hakan da kuma tuna mata da nasihar mahaifiyarta a gare ta, ɗan lumshe ido ta yi hawayen da suka tarun mata suka zubo sharr, a sanyaye ta juya ta fita daga cikin wurin. Tun bayan da Fadeela ta hau keke napep lokaci lokaci take kai gefen gyalenta tana goge ƙwallan dake zubo mata, ta rasa ya zata yi da son Bash da ke ta azalzalar ta a zuciya, yanzu da abun nan ya faru a tsakanin su maimakon ta cire shi a ranta sai ma ta ji son nasa ƙaruwa yake a ranta, mai keke napep ɗin sai ɗan kallon ta yake ta cikin madubi, a ransa yake ayyana gata dai mace har mace amman Allah kaɗai ya san mike damunta, daga baya kuma ya raya yanzun hakan namiji ne silar damuwar tata tun da ya ga daga bakin in da ya ɗauko ta, a ransa ya ce shi da Allah zai bashi wannan a matsayin mata ai an gama masa komai, can dai ya kasa haƙuri ya ce, "Malama ban san ko zaki ga na yi maki katsalandan ba, amman don Allah ki yi haƙuri, ki fawwalawa Allah al'amuranki, dama A CIKIN RAYUWA mumini dole ne ya fuskanci jarabawa saboda Allah yana son sa, kuma idan kika ji damuwar wani zaki ga ke taki ba komai bace, babban arziƙin shine da Allah Ya barki da lafiya da hankali, sai ki yi amfani da hakan ki dage wurin roƙonsa ya yaye maki damuwar ki, ya baki ikon cin jarabawar da ya yi maki." Gefen gyalenta ta kai ta share hawayen ta, a sanyaye ta ce, "Na gode da shawara, in sha Allahu zan yi amfani da ita." Mai keke napep ɗin ya yi saurin cewa, "Ah ba komai, nine da godiya da kika fahimce ni har kika ɗauki shawara ta." Koda suka iso gida ta bashi kuɗin napep ɗin cewa ya yi ta bar su duk da nisan daga in da ya ɗauko ta, ƙarshe da ya ƙi amsa ta yi masa godiya ta nufi gida. Bayan kwanaki da tafiyar Maleek U.S, Basma na zaune a cikin ɗakinta, gaba ɗaya ji take duk ta takura, dama idan ta je makaranta ne take samu tana yin abun da ranta ke so, gashi yanzu sun samu hutu tun kafin dad ɗinta ya yi tafiya, kuma yanzu itama mom ɗinta tana saka mata ido sosai, can baya har tunani ta yi ko dai dad ɗinta ya faɗa mata abun da ya ta6a kama ta tana aikatawa, to amma da ya gaya mata zata gane ta sani, ta yi tunanin wataƙila wani abun daban ya faɗa mata shiyasa take saka mata ido, yanzu duk in da zata je mom ɗin ke sakawa a kaita a kuma maido ta, wani lokacin ma ita da kanta take kai ta, dama makaranta kai ta ake a ɗauko ta, mafi yawancin lokutta ma iyayen nata ne ke kai ta su ɗauko ta, gaba ɗaya duk shawaran da Maleek ya ba Sapna akan Basma can baya ta ɗauka, yanzu basu bata kuɗi sai da dalili, komai take buƙata siya mata ake yi kuma su tabbatar da ita ɗin ce ta yi amfani da abun. Gaba ɗaya tun lokacin da abubuwa suka canza mata take jin ta a matuƙar takure, har ta kai tana ɗaukar abubuwanta masu daraja tana zuwa da su school ta bada a saido mata. Yanzu da take zaune kokonton ko ta aikata abun da zuciyarta ke raya mata take, duk da tana jin tsananin son aiwatar da hakan amman bata san ta yaya ba don ba zuwa school zata yi ba, gashi ko da mom ɗinta bata nan baza ta iya fita ba, don ta saka dokar hana ta fita ba tare da izininta ba kuma da ta fita sai ta sani, a gefe guda kuma tana tuna jan kunnen da dad ɗinta ya yi mata kafin tafiyarsa, ta ɗauki lokaci tana ta saƙe-saƙe a rai, can ta ɗauko wayarta dake ajiye gefe ta ɗan yi jim tana kallon screen ɗin, ta6a wayar ta fara yi kafin a ɗarare ta kai ta kunne, magana ta fara yi da wata da ta kira da suna Lily, tambayar ta ta yi ta koma gida ko tana a gari, bayan ta bata amsa, Basma ta ce mata pls ko zata taimaka mata ta zo gidan su, ɗan saurarawa ta yi sai kuma da sauri ta ce mata ok zata bata kuɗin amman sai idan ta zo don bata da isassun kuɗi a account ɗinta sai dai cash, amman idan ta zo kada ta shigo ta gate ta tsaya ta baya sai ta kira ta, daga haka ta yanke kiran, ɗan jimm ta yi sai kuma ta miƙe ta nufi ƙofa ta fita daga cikin ɗakin, kana ganinta ka san a tsorace ta ke ta nufi bakin bene ta tsaya tana kallo cikin falon ƙasa, ta san mom ɗinta ba yanzu zata dawo daga wurin aiki ba don bata ma daɗe sosai da tafiya ba lokacin duka ƙarfe goma da wasu mintuna na safiya, tunani ta shiga yi ko mrs Helen na a kitchen duk da tana ganin kamar lokacin da take yin girkin abincin rana bai yi ba, a hankali ta fara taka matakalar benen tana yi tana ƴan waige waige, ƙasa ta sauko ta nufi hanyar kitchen tana tafiya mai kaman sanɗa, lokacin da ta ƙarasa bakin kitchen ɗin ta leƙa bata ga kowa ba a ciki, juyowa ta yi tana kallon hanyar da ɗakin mrs Helen yake, nufar ɗakin ta yi tana ci gaba da yin ƴan waige-waige, daga bakin ƙofar ta tsaya ta yi ɗan jim tana saurarawa, kafin ta kai hannu a hankali ta kama handle ɗin cikin sa'a ƙofar a buɗe take, a hankali ta ɗan tura ƙofar ta kai idonta tana leƙa ciki, hango mrs Helen ɗin ta yi a saman madaidaicin gadon ɗakin wanda yake matsayin nata tana yin bacci, wani daɗi Basma ta ji, sakin ƙofar ta yi ta juya da sauri ta koma kitchen, wani ɗan dogon stool ta ɗauko tare da floor wiper ta fito ta nufi hanyar da zata kai ta bayan gidan, a ƙofar shigowa ta baya akwai Cctv Camera haka ta gaban gidan ma, dama iya wajen gidan ne ke da kamerorin tsaro banda ciki saboda nan akwai na'urorin dake sanar da shigowar mutum, da yake camera ɗin irin wadda ake juyawa ce, ana kuma control ɗinta ta computer ko waya, da stool ɗin ta yi amfani bayan ta hau ta saka sandar floor wiper ɗin ta juyar da camera ɗin ta koma kallon wani direction, dama tana yin hakan a lokuttan baya da asirinta bai tuno ba, ɗaukar stool da wiper ɗin ta yi ta ajiye su gefe wurin flowers, a nan ta tsaya tana dakon isowar ƙawar tata gaba ɗaya kana ganin ta duk a tsorace take.... *✨A CIKIN RAYUWA✨* ZAINAB BATURE 50 Gaba ɗaya hankalin duniya na kan gasar kwallon ƙafa ta cin kofin duniya wato FIFA world cup da ke gabatowa nan da ƴan watanni, wanda a wannan karon ƙasar Saudiyya ce ta ɗauki nauyin shirya gasar. Kasantuwar Deen zai wakilci Nijeriya a gasar hakan ya ƙara saka shi ya zama busy sosai, saboda suna cikin buga Premier League ga kuma wasu daga cikin qualifiers da zai buga ma Nijeriya wato wasannin neman cancanta a gasar cin kofin duniya a lokuttan international break, yanzu gaba ɗaya Salma bata samun lokacinsa, ko ta yi masa saƙo ba ya responding, dama yawanci saƙon gaisuwa ne, sanin cewa zai buga ma Najeriya a gasan world cup ya sa ta yi tunanin shiyasa bai da lokaci, hakan ya sa gaba ɗaya ma ta daina tura masa kowane saƙo, dama yanzu komai na aikin da take masa ya koma hannun Sageer tun da ita bata nan, shima Sagir ɗin ba samun lokacin Deen ɗin yake ba, iyaka dai duk abun da ya shafi aikin abincin da ake yi da har yanzu ana bama mutane hajiyar ambasada ake tuntu6a ita take bada komai. Ranar Juma'a lokacin satin Maleek ɗaya daidai da yin tafiya ya dawo, cike da farin ciki iyalin nasa suka tarbe shi, duk sun sha ado da kayan mu na gida, Sapna ta saka doguwar rigar wani rantsattsen jan leshi da ya bala'in ƙara mata kyau, itama Basma riga da skirt na lace ne a jikinta, su duka ba ƙaramin kyau suka yi a cikin kayan ba, shima Maleek ya nuna farin cikin ganinsu sosai, bayan gama tarbar sa a tare suka zauna cin abinci wanda har da Sapna aka yi aikin girka abinciccikan musamman saboda dawowar tasa. Bayan gama cin abincin part ɗin shi ya wuce tare da Sapna ta taimaka masa ya yi wanka ya kwanta ya huta. Da daddare bayan sallar issha Maleek ya fito daga part ɗin sa jikinsa sanye da farar jallabiya, a bakin bene ya tsaya tare da ɗaura duka hannuwansa ya dafa saman ƙarfen benen da ya zagaye sama, shiru ya yi yana kallon gabansa kana gani ka san tunani yake yi, he stood there for a while his mind elsewhere, can ya ɗan sauke gajerar ajiyar zuciya ya juya, walking slowly ya nufi hanyar part ɗin Basma, bayan ya isa hannu ya kai zai buɗe ƙofar sai kuma ya fasa, knocking ya ɗan yi kusan sau biyu sannan ya tura, Basma dake zaune a saman gado tana latsa wayarta ganin dad ɗinta ne ya sa ta yin saurin gyara zaman ta tare da ajiye wayan, ciki ya nufo ya tsaya ɗan nesa da ita yana kallon ta kamar yadda itama idonta na akan sa, a hankali ta ce, "Dad..." Kai ya ɗaga mata kawai, "Kin yi salla?" Da sauri ta jinjina masa kai alamar eh, shiru ya ɗan yi kafin ya ce, "Is there any problem?" Da sauri ta girgiza maza kai, ya ce, "Ya hutun?" Ɗan murmushi ta yi ta ce lafiya lau, daga haka bai sake ce mata komai ba, a fakaice Maleek ya kai idanunsa yana ɗan kallon wani direction a cikin ɗakin, can ya juya ya kalle ta tare da miƙa mata hannu ya ce ya ga wayarta, Basma ta ɗauka ta miƙa masa, kallo ta bishi da shi yayin da yake tatta6a wayar tata, bayan ɗan lokaci ya miƙa mata, ci gaba da bin sa da kallo ta yi ganin ya yi tsaye kuma bai sake cewa komai ba, can a hankali ya ce mata, "Gud night." itama ta ce masa haka ta bi shi da ido yayin da yake nufar ƙofa har ya fita. Bayan Maleek ya koma part ɗin sa, reading nook dake a cikin babban falon nasa ya nufa ya zauna, bin wata laptop da ke ajiye asaman teburi ya yi da kallo, kana kallon sa zaka fahimci yana zullumin yin wani abu, ya ɗan ɗauki lokaci a haka sosai yake jin fargabar aiwatar da abun da yake niyya, bai so ya ga wani abu da zai zo yai unsettle nasa duk da baya fatan ya ga abu haka, can ya dake ya kai hannu ya buɗe laptop ɗin, daddanata ya shiga yi bayan ya kunna, juyawa ya yi jin motsi, Sapna ce ta shigo cikin falon jikinta sanye da wata haɗaɗɗan doguwar rigar bacci data bi jikinta ta fito da shape ɗinta sosai, bin ta da kallo Maleek ya yi yayin da take ƙarasowa wurin da yake, lokaci guda wurin ya karaɗe da ƙamshin turarenta mai matuƙar daɗi da sanyaya zuciya, har Maleek bai san lokacin da ya lumshe idanunsa ba, hannu ya miƙa mata tana sakar masa lallausan murmushi ta kama, a saman cinyoyinsa ya yi mata masauki ta kwantar da kanta a ƙirjinsa, hannu ya kai cikin dogon sumarta da ta ɗaure ta a baya ba tare data rufe kan nata ba, ta sigar soyayya ya shiga yamutsa gashin nata da shima ya sha gyara yana ta sakin ƙamshi, ɗago ta ya yi tare da tura fuskarsa a tsakankanin wuyanta yana shaƙar ƙamshin da wurin ke saki, can ƙasan maƙoshi ya furta, "My love kin yi kyau..." Tana murmushi idanunta a lumshe a hankali ta furta, "Kai ma haka." Ɗago fuskarsa ya yi idanunsa a ɗan lumshe ya ce, "Wani kyau da wannan jallabiyan da kika saba ganina a cikin shi." Ƴar dariya ta yi bata ce komai ba, yanata bin ta da kallo don sosai ta yi mashi kyau duk da koda yaushe haka take yi masa kyau, "Mi yasa ne ke sam bakya tsufa?" Ta ɗan buɗa ido ta ce, "Tsufa kam ai na fara ɗaukar hanya tun da na wuce 40." Ɗan girgiza kansa ya yi ya ce, "Serious sam bakya tsufa Sapna, ba wanda zai gan ki ya ce ke kika haifi baby idan ba wanda ya sani ba, koda yaushe kina nan a yadda kike sai dai jikin ki kawai ya ɗan canza, kuma wannan ƙara maki kyau yake, kuma ba iya jiki ba still, like...." Shiru ya yi bai ƙarasa ba Sapna ta ɗage masa gira, kai bakinsa ya yi saitin kunnanta ya raɗa mata magana, dariya ta yi ta kwantar da kanta a ƙirjinsa, "Allah da gaske my love, har yanzu ina mamakin hakan, sai kuma in yi tunanin wataƙila wani siddabarun ne naku na likitoci kika yi shiyasa hakan." Ɗaga ido ta yi ta kalle shi kafin ta sauke ta bi wuri guda da kallo, jin ta yi shiru ya leƙo fuskarta suka haɗa ido, ɗage mata gira ya yi ya ce haka ne ko, ɗan murmushi ta yi ta ce wannan sirrinta ne, ya yi murmushi tare da kai hannu ya ɗan ja dogon hancin ta, ɗagowa ta yi daga jikinsa ta tambaye shi ko aiki ya ke ta bashi space, ya ce sai ka ce wani injin ya dawo daga tafiyar aiki yau kuma ya dasa wani aikin ai suma yakamata su samu lokacin sa kawai ya duba abu ne, hannu ta kai tana shafa gashin gefen fuskar shi ta ce, "Baka bani labarin trip ɗin naka ba." Ya ce ok bari su je bedroom ya bata, daga haka suka miƙe ya duƙa gabanta kamar yadda yake mata idan zai ɗauke ta, hayewa bayan nashi ta yi tana ƴar dariya, daga haka suka nufi bedroom ɗin sa ta kwantar da kanta jikinsa, tare da lumshe idanunta tana jin tsananin ƙaunar mijin nata na ƙara ratsa zuciyarta. Washe gari bayan sun gama yin breakfast Maleek ya koma part ɗin sa ya kwanta don ya ƙara hutawa, sai lokacin salar azahar ya farka daga bacci, bathroom ya shiga ya yi wanka bayan ya fito ya shirya cikin ƙananun kaya daga haka ya fita zuwa masallaci, ana gama sallan ya dawo gida kai tsaye part ɗinsa ya wuce, duk da fargabar da yake ji haka ya nufi reading nook ɗin ya zauna tare da buɗe laptop ɗin, ƙirjinsa ya shiga faɗuwa with every click, lokacin da zai buɗe abun da yake son dubawa har sai da ya ɗan runtse idanunsa, after gathering all the courage he had ya buɗe idanunsa tare da buɗewa, yadda ƙirjinsa ke ɗagawa a fili zaka fahimci ba ƙaramin tashin hankali yake a ciki ba, bayan ɗan lokaci ya wani zaro idanu tamkar idanun nashi za su faɗo ƙasa, kan ka ce mi jikinsa ya fara yin kakkarwa kamar wanda shock ɗin lantarki yake ja, da sauri hannunsa na rawa ya yi saurin kife laptop ɗin ya rufe ta, kaf, kaf, haka hannunsa da ke dafe da jikin system ɗin ke ta rawa, da ƙyar yake fitar da numfashi yayin da bakin sa ke ɗan rawa ya runtse idanunsa gam, a cikin ransa ba abun da yake maimatawa face "Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun...." Ya ɗauki lokaci mai ɗan tsawo a haka kafin ya buɗe idanunsa da har sun yi ja sosai, miƙewa ya yi a fusace ya nufi cikin bedroom ɗinsa, bada jimawa ba ya fito hannunsa ɗaya a cikin aljihun wandonsa, kai tsaye hanyar ɗakin Basma ya nufi idanunsa har rufewa suke yana haɗe hanya, yana isa ya kai hannu ya banka ƙofar ya shiga, a fusace ya furta, "Basma..!!!" Basma da ta miƙe daga gaban dressing mirror ta gama yin shafa tana tsaye bakin closet zata fiddo kayan da zata saka, da sauri ta kai idanunta kan dad ɗinta da ya shigo cikin ɗakin yana mata kiran da ta na ji ta san ba lafiya ba, sakin kayan da ta fiddo ta yi suka faɗi ƙasa ta fara ja da baya ganin yadda ya tunkaro ta, a ruɗe ta buɗe baki ta ce, "Dad...what's happ..." Kafin ta ƙarasa ta ji saukar waya a jikinta, wata gigitacciyar ƙara Basma ta saki yayin da raɗaɗin bugun ya ratsa ta, cikin fitar hayyaci Maleek ya ci gaba da zuba mata wayar ta ko ina, ihu kawai Basma ke saki jin azababben raɗaɗin da bata taba fuskanta ba a rayuwarta, gashi sam ya ƙi bata sararin da zata gudu, da ta yi yunƙurin guduwa ya ke fizgo ta ya hankaɗa ta, towel ɗin jikinta har kwancewa yake Allah ma ya sa ta riga ta saka underwear, da ƙyar Basma ta samu ta kubce masa ta fito daga cikin ɗakin, hanyar sauka ƙasa ta nufo da guda hannuwanta ƙanƙame da towel ɗin sai faman zabga ihu take, tana yi tana waiwayen Maleek da ya biyo bayan ta cikin sassarfa a fusace, gudu gudu take taka matattakalar, tana kaiwa tsakiya ta yi missing step gaba ɗaya ta tafi ta fara gangarowa har ta ƙundumo ƙasa, gigitaciyar ƙara ta saki a firgice cikin jin raɗaɗi ta ke faɗin, "Mom...mom...come and help me....dad want to kill me..." Gaba ɗaya ihunta ya karaɗe cikin gidan, mrs Helen ce ta fito cikin falon a ruɗe, tana ganin abun da ke faruwa da kuma furucin da Basma ke yi da gudu ta nufi 6angaren Sapna, tare suka dawo da Sapna wadda kana ganinta ka san daga bacci aka taso ta, wani irin zaro ido Sapna ta yi ganin abun da ke faruwa, Basma na ganin ta ta fara kokarin zuwa wurinta amman Maleek ya ƙi bata damar hakan, tuni bakinta da goshinta sun fashe duk jini ya wanke mata fuska har a saman towel ɗinta, cikin matuƙar gigicewa Sapna ta nufo su, tana zuwa ta shiga tsakankanin su tana ƙoƙarin kare Basma daga dukan Maleek, wani irin kuka mai sautin gaske Sapna ta saki ganin yadda yake ta kokarin ci gaba da bugun ta, cikin fitar hayyaci Sapna ta ke faɗin, "Are you okey honey....mi yake faruwa ne kake son kashe ta...mi ta yi maka ne don Allah...Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un..mrs Helen ki zo ki taimaka mani honey zai kashe baby!" Mrs Helen da ta yi tsaye gefe jikinta sai rawa yake yayin da take ƙwalla, duƙewa Sapna ta yi ta ƙanƙame duka ƙafafun Maleek ta shiga girgiza masa kai cikin kuka ta shiga faɗin, "Don girman Allah Maleek...don darajar manzon Allah...don darajar iyayenka...ka ƙyale ta, baka ganin ita kaɗai Allah ya bamu....so kake yi ka kashe mana ita ne..." Yadda take yin maganar kamar tana neman suƙewa idanunta sai ɗan lumshewa suke, ɗage kai Maleek ya yi yana kikkafta idanunsa, a hankali ya saki wayar hannunsa ya duƙe a wurin, zama ya yi dirshan a ƙasa ya sa duka hannuwansa ya tallabi kansa, ganin haka Sapna ta yi saurin miƙewa duk da jirin da take jin na neman kwasar ta, nufar wurin Basma dake ƙanƙame jikin Helen ta yi, hannu ta kai ta rungumo ta jikinta, tana jin yadda ta taho ta gane bata numfashi, a kiɗime ta ɗago kanta tana kiran sunanta, kallon Helen ta yi ta ce mata ta ɗauko mata ruwa ta amsa mata tare da nufar kitchen da gudu, bayan ta kawo ruwan ta zuba ma Sapna a hannu ta yayyafa mata a fuska nan take ta ja numfashi ta saki, wurin kujeru ta nufa da ita ta zauna a saman doguwar kujera tana ƙara rungume ta, Mrs Helen da ta biyo su tana tsaye daga gefe tana bin su da ido kana ganinta kasa duk a tsorace take don bata ta6a gani irin hakan ta faru a gidan ba tun da ta fara masu aiki, ɗago fuskar Basma ta yi tana kallo, ganin yadda fuskar tata ta yi ya sa ta sakin kuka mai sauti, cikin kukan ta ce, "What did you do to your dad baby?" Basma da idanunta ke ɗan buɗewa suna lumshewa a wahalce ta furta, "I don't know...." Kan Sapna ne ya ɗaure jin amsar Basma, bayan ɗan lokaci ta ce ma Helen ta zo ta kama ta, miƙewa Sapna ta yi ta nufi Maleek da har lokacin yana a yadda ta barshi bai ɗago kansa ba, zama ta yi a gabansa cikin zubar hawaye ta ce, "Maleek, mi baby ta aikata da ka yi mata wannan ɗanyen hukuncin....pls ka sanar mani...na san haka nan ba tare da dalili ba ba zaka yi mata wannan hukuncin ba...don girman Allah Ka sanar mani." Shiru kamar ba zai ɗago ba, a hankali ya ɗago kansa, abun da Sapna ta gani a fuskarsa ya matuƙar ƙara tayar mata da hankali, kuka ta ga yanayi hawaye sosai na bin fuskarsa, bin ta da kallo ya yi da jiƙaƙkun idanuwa, a ransa yana tunanin ta ina ma zai fara sanar da ita wannan al'amarin, sai dai ya san ba yadda zai yi dole a wannan ga6ar akwai buƙatar ya sanar mata, rokonsa ta ci gaba da yi kan ya faɗa mata, gyara zamansa ya yi cikin raunin murya ya ce, "I'm sorry Sapna..I'm sorry...I have no choice I will tell you this..." Jinjina masa kai ta yi ta kafe sa da idanunta da suma suke a jiƙe, yayin da tun bata ji mi zai faɗa matan ba bugun zuciyarta ya ƙaru, sai da Maleek ya tattaro duk wani ƙwarin gwiwar da ke gare shi sannan ya fara sanar da ita tun farkon al'amarin, har da ɗaukar ta da ya yi suka je gidan su Huda, ya sanar da ita labarin da ya bata kan abokinsa game da ɗiyarsa kawai ya faɗa mata hakan ne don kada hankalinta ya tashi, amman Basma ce ke aikata hakan, ya ce tun lokacin ya ke saka mata ido sosai, hakan ne ya sa ko tafiya ya rage yi in ba ta zama dole ba kuma bai wuce ƴan kwanaki, a wannan tafiyar da zai yi ne ganin zai yi har sati guda hakan ya saka sa zullumi kan Basma, shine kafin ya tafi ya saka camera a ɗakinta wurin gadonta ba tare da ta sani ba don yana son tabbatar da idan ta daina....cikin kuka mai sautin gaske ya ce mata ɗazun nan ya binciki video ɗin da camerar ta naɗa ya gan ta tare da wata daban suna aikata hakan a cikin ɗakinta. Jikinsa har jijjiga yake lokacin da ya ƙarasa faɗi mata, wani kalan zaro idanuwa Sapna ta yi, cikin ƙaraji ta shiga furta, "Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun....Allahumma ajirni fi musibati..." Haka ta shiga jera addu'oi duk jikinta ya hau yin rawa, kokowar fita numfashinta ya fara yi, duk ƙoƙarin ta na ganin ta hana abun da ke shirin faruwa da ita abun ya ci tura, gaba ɗaya ta tafi ta faɗa jikin Maleek, da sauri ya kama ta yana ambaton sunanta nan take ya gane sumewa ta yi, miƙewa ya yi ya kinkime ta ya nufi hanyar part ɗinta, duk abun nan idanun Helen da Basma na kan su tun lokacin da suka ji Sapna ta saka salati tana yin addu'oi, Basma na ganin haka ta gane ya sanar ma mom ɗin tata wani abu da ya danganci abun da ya taba kama ta tana aikatawa, duk tsoro ya bayyanar mata, nan take ta fahimci ya gane abun da suka aikata da Lily, cikin rashin ƙarfin jiki ta fara ƙoƙarin miƙewa, mrs Helen na ce mata ta zauna ta ƙara hutawa amman bata bi ta kanta ba, cikin jan ƙafafu ta nufi bene da ƙyar ta fara hawa, tana hayewa sama ɗakinta ta nufa, tana zuwa ta shige tare da garƙame ƙofar..... ✨A CIKIN RAYUWA✨ ZAINAB BATURE 51 A saman gado Maleek ya kwantar da Sapna ya nufi bathroom ɗin ɗakin da sauri, ruwa ya ɗebo ya dawo ya ɗan yayyafa mata a fuska, numfashi ta sauke kafin a hankali ta fara motsa idanunta, Maleek ya zauna gefen ta yana kallon ta tare da kama hannunta guda, a hankali ta fara buɗe idanunta, bin Maleek ta yi da kallo kamar mai son tuna abu, sannu da ya ce mata ta sa komai ya dawo mata akai hawaye suka fara zubo mata, "Why ka ƙi sanar mani tun farko honey? Wannan ba abu ne da ya kamata ka 6oye mani ba, da na sani zan fi ɗaukar matakin da ya dace..." Shiru ya ɗan yi shima ƙwalla sun cika idanunsa, cikin raunanniyar murya ya ce, "Ina gudun halin da zaki iya shiga idan kika ji ne." Ɗan girgiza kai ta yi ta ce, "Duk da haka da ka sanar mani, ai ni musulma ce na yarda da ƙaddara mai kyau da mara kyau." Shiru ya yi kawai yana ta kallon ta, juyar da fuskarta ta yi tana sake ambaton innalillahi....a hankali ta furta, "Ya aka yi baby ta koya wannan mummunan ɗabian?" Maleek ya ce shima abun da ke ta damunsa ke nan don ya gane duk abubuwan da ta faɗa masa a baya ba gaskiya bane, shiru Sapna ta yi idanunta na kallon gefe, wani irin faɗuwa gaban ta ya shiga yi lokacin da wani tunani ya zo mata, can ta yunƙura Maleek ya kalle ta da sauri ya ce mata ina zata je cikin muryarta da har ta ɗan disashe ta ce bathroom zata shiga, taimaka mata ya yi ta sauka daga gadon cikin rashin ƙwarin jiki ta nufi banɗakin ya bita da kallo cike da tausayawa, Sapna na shiga ta kulle ƙofar, gaban mirror ɗin kewayen ta tsaya tana kallon kanta lokaci guda ta saki sabon kuka tare da kai hannu ta toshe bakinta, wllh ta matuƙar girgiza da jin wannan abu, ta ɗauki tsawon mintuna a haka dama ba wani abu zata yi ba kawai ta rasa mike mata daɗi ne, wanke fuskarta ta yi ta nufi ƙofa, lokacin da ta fito bata iske Maleek ba a daƙin kamar yadda ta bar shi, bakin gado ta nufa ta zauna ta tsura ma guri guda ido yayin da ƙwalla ke ci gaba da gangaro mata, duniyar tunani ta afka can ta ɗan waro ido a cikin ranta ta raya, "Kada dai a ce halin wasu daga familynta ne ya shafi baby!" Tashin hankali ne ya bayyana sosai akan fuskarta da ta yi wani irin jajir alamar motsuwar jini, duk da rashin ƙarfin jikin da take ji haka ta miƙe ta nufi ƙofa ta fita. Lokacin da ta dawo main falon ba kowa a ciki, ɗakin mrs Helen ta nufa ta tambaye ta baby nan ta sanar mata ta koma ɗakinta, bayan ta fito bene ta nufa cikin mutuwar jiki ta fara hawa, ɗakin Basma ta nufa koda ta kai hannu ta tura ƙofar ta ji a rufe take, hannunta ta saka a na'urar jiki nan ma bata buɗe ba hakan ya sa ta gane ta kulle ta ciki, kiran sunanta ta fara yi tana cewa ta buɗe mata ƙofa, shiru har bayan wani lokaci ba alamar zata buɗe, hankalin Sapna ne ya ƙara tashi bayan tunanin kada a ce Basma ta aikata ma kanta wani mummunan abu ya zo mata a rai, da ƙarfi ta shiga bugun ƙofar tana kiran sunanta, "Baby...I know you can hear me...come and open the door I want to talk to you." Haka ta koma tana faɗi cikin ɗan ɗaga murya, sai can bayan wani lokaci ƙasa ƙasa ta jiyo muryar Basma tana magana, sai dai sam bata gane abun da take cewa, kanga kunne Sapna ta yi tana son ta ji abun da take faɗi, da ƙyar ta jiyo ta tana cewa, " I'm sorry mom...I promise....i won't do it again..." Cikin kwantar da murya Sapna ke ce mata to ta buɗe ƙofar tana son magana da ita ne ba wani abu ba, ta ji ta ce, "Kema na san zaki buge ni ne." Da sauri Sapna ta ce mata a'a ba bugun ta zata yi ba kawai magana take son za su yi...sai da Sapna ta yi fama da ita sannan ta ji ta buɗe ƙofar, lokacin da ta shiga cikin ɗakin, Basma har ta kai bakin bathroom tana ta zare ido alamar ƙiris take jira ta faɗa cikin banɗakin, bin ta da kallo Sapna ta yi, jikinta ta saka doguwar riga gashinta duk a hargitse kamar sabon kamu, har lokacin goshinta da gefen bakinta suna fitar da jini amman ba sosai ba, maimakon Sapna ta ji haushin ta sai ma wani irin tausayin ta da ta ji ya kama ta, Basma da take ƴar gayu yau ita ce a haka, jiki a sanyaye Sapna ta ƙarasa shiga cikin ɗakin ta zauna a bakin gado, da hannu ta yi mata alamar ta zo, cikin marairaicewa ƙwalla na zubo mata ta ce, "Za ki buge ni..." Sapna ta girgiza mata kai ta ce ba bugun ta zata yi ba, "To ki rantse ba zaki buge ni ba." Basma ta faɗa da muryarta da har ta shaƙe, da alama dai ta gigita da bugun da Maleek ya yi mata, koda yake abu ne da bai ta6a faruwa da ita ba, tun da take ko hannunta ba a ta6a ta6awa ba da sunan bugu, Sapna da ke ta kallon ta sai da ta rantse mata ɗin sannan ta matso, amman ɗan nesa da ita ta durƙusa kan gwiwunta a ƙasa, sauka Sapna ta yi itama ƙasa da sauri Basma ta ƙara ja baya, Sapna na fuskantar ta cikin raunanniyar murya ta ce,"Baby why....miyasa kika ɗauki wannan mummunan ɗabi'an...mi kika nema kika rasa baby...kin san girman laifin abun da kike aikatawa a addini...why baby...why kike son lalata rayuwan ki?" Shiru Basma ta yi ta sauke idanunta da suka kumbura ƙasa tana shesshekar kuka, "Now i want u to tell me the truth, kuma bana son ki yi mani ƙarya kaman yadda kika yi ma dad ɗin ki, a ina kika koyi hakan?" Ɗago ido Basma ta yi ta ji ba zata iya yi ma mom ɗin nata ƙarya ba, cikin rawar murya ta ce, "Ba wani ya koya mani ba...kawai na ji ina son yi ne." Da sauri Sapna ta juyar da fuskarta tare da ɗage kanta irin alamar mutum ya bani ɗin nan, a cikin ranta take nanata "Wllh jini ne..." Sake kallon ta ta yi ƙwalla sun ciko idanunta ta ce, "Tun yaushe ne kika fara aikata haka?" Miyau Basma ta haɗiya kafin ta ce, "...since I was in secondary school..." Wannan karon kuka mai sauti Sapna ta saki jin ta daɗe tana aikata hakan don yanzu tana a jami'a ne zata shiga shekara ta ukku da hutun su ya ƙare, cikin kuka Sapna ke tunanin ta ina ma za su tari al'amarin, itama Basma kukan take sosai ta sadda kanta ƙasa, "Yanzu baby ki faɗi mani ya kike so mu yi maki...komi kike so in dai zaki daina aikata hakan ki faɗi mani wllh zan yi maki, koda duka abun da na mallaka zai ƙare in dai hakan zai saka ki daina aikata hakan zan yi maki....tell me baby what do you want?" Ɗago kai Basma ta yi hawaye sun wanke mata fuska cikin muryar kuka ta ce, "Ina son Aure mom...ina son a yi mani aure da ya Deen." Shiru Sapna ta yi tana kallon ta da jiƙaƙƙun idanu, sam bata ji Basma ɗin wai ko ta yi rashin kunya ba da ta faɗi haka, a cikin ranta take tunanin ko dai Basmar na daga irin mutanen da ake halitta da ƙarfin desire, a ganinta wannan ba wata babbar buƙata bace tun da dama akwai maganar auren a tsakanin su, ke nan idan hakan ne komai zai zo da sauƙi, ajiyar zuciya Sapna ta sauke ta ce, "Kin tabbata zaki daina a yi maki auren?" Da sauri ta jinjina mata kai, hannu Sapna ta kai ta goge ƙwallan fuskarta, da hannu ta yi mata alamar ta zo wurinta, ganin yanayin Sapna ɗin ba a fusace take ba ya sa a ɗarare ta matsa wurinta, hannu ta kai ta ta6a jikin Basma ta ji da zafi sosai, dama daga yanayin ta ta fahimci kamar tana running a temperature, miƙewa ta yi ta ce mata yanzu zata dawo, kamar ta san abun da Basma ɗin ke niyyar yi bayan ta kai bakin ƙofa ta juyo ta ce mata kada ta rufe ƙofar, zaune ta yi a wurin tana ta faman zare ido, gaba ɗaya a tsorace take da kada dad ɗinta ya shigo, after some few minutes Sapna ta dawo hannunta riƙe da ɗan first aid box, a bayanta mrs Helen ce riƙe da tray mai ɗauke da kayan abinci, a nan ƙasa Sapna ta sa ta ajiye tray ɗin kan carpet kafin ta ɗago ta yi ma Basma sannu Sapna ta ce zata iya tafiya, mrs Helen ta nufi ƙofa har lokacin kanta a ƙulle yake dangane da wani irin laifi Basma ta aikata har dad ɗinta ya yi mata wannan jan bugun, da ƙyar Sapna ta tursasa Basma ta ɗan ci abinci ba sosai ba don da farko ta ce ba zata ci ba, bayan ta gama ta yi mata dressing ciwukanta tare da bata maganin zazzabi, sata ta yi ta hau gado ta kwanta, daga haka ita kuma ta nufi ƙofa ta tafi da niyyar zuwa ta iske Maleek kan maganar da suka yi da Basma ta son a yi mata aure da Deen. Bayan fitowar Sapna daga ɗakin Basma, 6angaren Maleek da ke nan sama ta nufa, ganin bata ganshi a nan ba ta fito ta sauka downstairs, part ɗinsa na nan ƙasa ta nufa bata gan shi a cikin falon ba, tana shiga bedroom ta iske shi a kwance saman gado, sai dai ba bacci yake ba don tana shiga suka haɗa idanu, yana dai kwance ne kawai duk abun duniya ya ishe shi, gaba ɗaya ji yake duniyar babu daɗi, farko a falo ya fara zama ya ji kamar yana akan ƙaya, shine ya taso ya dawo bedroom ya kwanta, itama dai kwanciyar ya yi ta ne kawai amman ba don yana jin daɗinta ba. A bakin gadon gefensa Sapna ta zauna suna kallon juna, yunƙurawa ya yi ya miƙe zaune cikin sanyin murya ya ce mata sannu ta ɗaga masa kai, shiru suka yi na ɗan lokaci, cikin raunin murya Sapna ta ce, "Na san wannan abu ne mara daɗi ya same mu da dole mu shiga damuwa, amman ba yadda zamu yi, mu ɗauke shi a matsayin ƙaddara..." Dakatawa ta yi tana share ƙwallan da suka zubo mata, hannunta guda Maleek ya kama ya ce, "I'm sorry da ban sanar maki ba tun farko, na yi gudun kada hakan ya ja ki faɗa mummunan hali, shiyasa na yi maki dubara ta yadda kema zaki saka mata ido, to ashe hakan ma duk a banza." Ɗan girgiza kai ta yi irin na takaici, sai dai tana jin inda tun farko ta sani to sai ta fi saka mata ido sosai, "Daga wurin babyn nike yanzu, mun yi magana da ita na tambaye ta ta faɗa mani gaskiyar yadda aka yi ta koya hakan...ta ce she just felt like doing it, na tambaye ta duk abun da take so da zai sa ta daina aikata haka...ta ce mani aure take so a yi mata da Deen..." Tun da ta fara magana Maleek ke bin ta da idanunsa da sukai ja sosai, ta ci gaba, "I think she has a high se*ual drive...ina ganin tun da already dama akwai maganan auren a tsakanin su a yi mata auren kawai shine mafita." Ta ƙare maganar a sanyaye, Maleek kamar ba zai ce komai ba, can ya ɗan juyar da fuskarsa ya koma yana kallon wani 6angare daban, ita dai tana ta kallon shi...bayan ɗan lokacin ta ambaci sunan shi ya juyo ta ce why ya yi shiru, motsi bakinsa ya fara yi yana ɗan kikkafta idanu kafin ya fara magana, "...Ina ganin su biyun yanzu basu dace da auren juna ba...ko da ba tare nike yin rayuwa da Deen ko yaushe ba, ina da yaƙini kan sa cewa baya aikata duk wani abu da yake haramun, to taya zamu haɗa shi aure da ita mun san tana aikata wannan halin?" Ya ƙare maganar tare da kafe ta da ido, wani irin faɗuwa gaban Sapna ya yi jin abun da ya ce, fuska a jagule ta ce, "Amman honey... shi da ita duk matsayin yaran mu suke, kuma bada son ran mu hakan ya kasance ba, kawai ƙaddara ne Allah Ya aiko mana." Maleek ya ɗan ɗage gira ya ce, "Don yana matsayin ɗan mu sai mu cuce shi? Ki ɗauki kan ki a matsayin mahaifiyar da ta haifesa, sai kika ji yana neman auren yarinyar da take aikata irin halinta a zuwan ba ɗiyar ki ba, shin zaki amince ya auri yarinya irin haka?" Sapna ta yi shiru tare da haɗiyar wani busasshen yawu, cikin ƙoƙarin fahimtar da shi ta ce, "....amma honey wannan duk abu na gida ne, kuma ba don mu cuce shi zamu yi masa hakan ba, shi ɗin matsayin ɗan'uwanta yake, koda ya san da tana aikata hakan zai iya rufa mata asiri ya aure ta." Ɗan murmushin takaici Maleek ya yi ya ce, "Sai su yi wani irin zaman aure?" Sapna ta ɗan kikkafta idanu sai kuma ta ce ai yanzu ba sani ya yi ba, Maleek ya ce, "Idan kuma bayan auren ya zo ya gane tana aikata hakan fa?" Shiru ta ɗan yi kafin ta ce, "Honey zata bari, ita da kanta ta faɗi hakan." Ɗan girgiza kai ya yi ya ce, "Farko dana fara kama ta tana aikata hakan the same abun da ta faɗa ke nan cewa ta bari, ba irin alƙawarin da bata yi mani ba, but ta bari ɗin? A lokacin ma ke baki san da hakan ba, yadda ta nuna tsoron bata son ki sani I thought ko shi zai sa ta daina aikata haka. We should not be selfish Sapna, ana yin aure don samun kwanciyar hankali, za mu cuci Deen idan muka aura masa ita ya zo ya san tana aikata hakan, wani hali kike tunanin zai shiga sanin wace irin mata ya aura? sannan auren ta da Deen ba lalle ya zama mafita ba, saboda yanayin career ɗinsa da ba kowane lokaci zai rinƙa kasancewa da ita ba, ƙarshe hakan zai rinƙa bata dama ne tun da gashi just sati ɗaya da bana a gidan ta samu daman aikata haka, to ina kuma ga Deen da sana'arsa ta yawan yin tafiya tafiye ce." Ya ƙarasa tare da rufe idanunsa ya ɗan ɗage kansa, idanun Sapna suka cicciko da ƙwalla, ita ba don wani abu take son auren nasu ba sai don hango masu mafita, kuma ba don tana son su cuci Deen bane, kawai tana ganin hakan matsayin ƙaddara, kuma tun da Deen ɗin ba sani ya yi ba a ganinta lafiya lau za su haɗa su auren, ta sigar rarrashi ta ce, "Honey..ka fahimce ni, ni ina ganin hakan ne kawai mafita... tun da dama shine zata aura kuma bai sani ba lafiya lau zamu iya masu aure." Shiru kamar ba zai tanka mata ba still idanunsa na a rufe tana ta kallon shi cikin marairaicewa, ba tare da ya buɗe idon ba ya ce, "Ke kike ganin hakan a mafita, amman ko an yi masu aure abubuwa ne za su ƙara lalacewa indai bata bar wannan halin ba..." Slowly ya buɗe idanunsa suka shiga cikin na Sapna, on a serious note ya ci gaba, "....In dai bata bar wannan halin ba ba zan ta6a goyon bayan ta auri Deen ba, don haka sai na tabbatar cewa ta daina ko zan amince ma auren su." Yana gama faɗin hakan ya zura ƙafafunsa ya sauka daga saman gadon ya nufi toilet ya shige, Sapna ta bi sa da ido gabanta na faɗuwa sosai, bayan ɗan lokaci ya fito fuskarsa duk ruwa da alama wanke ta ya yi, wurin side drawer ya nufa ya buɗe, hanky ya fiddo tare da makullin mota, bayan ya ɗauki wayarsa ya ɗan kalli Sapna ya ce mata ya fita daga haka ya wuce, ita dai da ido kawai take ta bin sa har ya fita daga ɗakin, ƙwallan da suka tarun mata ne suka fara zubowa, sam bata yi tunanin Maleek zai ƙi amincewa da maganar auren nasu ba, gashi ta san shi wani lokacin kaifi ɗaya ne a magana, yadda ya yi maganar ta hango har cikin ransa ne, yanzu ita ya zata yi? haka ta yi zaune a wurin kamar an dasa ta tana ta tunane tunane, da ƙyar daga baya ta yi ƙarfin halin miƙewa ta nufi ƙofa tana jan ƙafafu don tuni har zazza6i ya rufe ta. Maleek na fitowa daga gida a mota kai tsaye gidan su Huda ya nufa, bayan ya yi parking yau ma a waya ya kira mummy ɗinta bayan sun gaisa ya ce idan tana nan ta turo ta, bada jimawa ba Huda ɗin ta fito jikinta sanye da jeans da riga da ta kawo mata zuwa rabin cinyoyinta, kanta ta yafo gyale, a nutse take tafiya har ta ƙaraso parking space ɗin Maleek ya kai hannu ya buɗe mata front seat, shiga ta yi ciki ta zauna lokacin da suka haɗa ido da shi har saida gabanta ya ɗan faɗi don ta ga alamun damuwa a tattare da shi, a sanyaye ta ce, "Good afternoon dad." Kai kawai ya jinjina mata, Huda ta yi shiru tare da sauke kanta ƙasa a ranta tana tunanin ko wani abu ya faru, "Huda..." Da sauri ta ɗago jin muryarsa ya kira ta, da ƙyar ta ce, "Yes dad..." Juyawa yay looking at her in the eyes, a ɗan kausashe ya ce,"...I trusted you, but you lied to me!" Miyau Huda ta haɗiya ta zaro idanunta masu ɗauke da brown ƙwayar ido, cikin ƴar rawar murya ta ce, "Dad....yaushe na yi maka ƙarya?" Maleek ya ce, "Abubuwan da kika faɗa mani lokacin da na kama ku ke da Basma na gane duk ba gaskiya bane, kuma sannan kin yi mani alƙawarin kun daina amman kuka ci gaba da yi....kin ga yanzu dole nima zan sanar da iyayen ki, kuma zan ɗauki mummunan mataki akan ku kaman yadda na faɗa maku a lokacin." Gaba ɗaya Huda ta zaro idanunta, nan da nan jikinta ya hau yin kerma sosai, cikin rawar murya ta ce, "Dad na rantse da Allah ban ƙara yi ba tun daga lokacin...Wllh ban yi ba...ban yi ba dad." Kuka sosai ta sakar masa, Maleek ya yi shiru yana ta kallonta kamar yana nazarin wani abu tattare da ita, dama kawai ya faɗa ne don gano wani abu, amman tabbas a video ɗin ya ga ba ita ba ce, sigh ya yi ya ce mata ta yi shiru to su yi magana, idan ya gano gaskiya take faɗa masa shike nan ba zai sanar ma iyayen nata ba, da sauri ta gyaɗa masa kai tasa gyalenta tana goge hawayen, "Yanzu ina son ki sanar da ni gaskiyar abubuwan da na tambaye ki a baya, waye ya koya maku hakan da kuma tun lokacin da kuke yi." Miyau Huda ta haɗiya muryarta na rawa ta ce, "Ba cousin ena ce ta koya mana ba, Basma ne ta kira ni lokacin ta ce in faɗa hakan idan ka tambaye mu....ita Basma ita ne ta fara koya mani haka, farko ma na nuna mata ba zan yi ba saboda abu ne ba mai kyau ba amman sai da ta ja ra'ayina, kuma kamar yadda na faɗa maka gaskiya ne ni lokacin mun yi one year muna yi..." Fuska a hautsine Maleek ke kallon ta yana sauraron ta, cikin ƙarfin hali ya ce, "Bayan nan kuma na zo na gane kun ci gaba da aikatawa duk da alƙawarin da kuka ɗaukar mani." Da sauri Huda ta girgiza masa kai ta ce, "Wallahi Allah dad tun daga lokacin ban sake yi ba ka ji na rantse." Maleek ya ce, "Idan na ɗauko alqur'an na baki zaki rantse da shi?" Da sauri ta ɗaga masa kai ta ce eh, cike da barazana ya buɗe glove box, hannu ya kai ya fiddo wani madaidaicin alqurani, kallonta ya yi ya ce mata ta san hukuncin mutum ya yi rantsuwa da shi akan ƙarya, da sauri ta ce masa eh ta sani har da ƙoƙarin miƙo hannu ta amsa, Maleek ya yi shiru yana kallonta sai ya ji a ransa ya yadda da ita, janye alquranin ya yi don ya san koda mutum yana da gaskiya ba a son ya rantse da shi, tambayarta ya yi ko Basma ta ƙara buƙatar su yi hakan, ta bashi amsa da eh amman ita ta ce mata bazata ƙara yi ba, hakan ne ma ya sa yanzu ta rage shiri da ita, Maleek ya yi shiru, tabbas ya san shirin da suke ya ragu, to amma shi ya yi tunanin saboda kama sun da ya yi ne wanccan lokacin, tambayar ta ya sake yi ko ta san yadda aka yi Basma ta koya yin hakan ta ce masa bata sani ba, ya ƙara tambayar ta da su wa suke yi lokacin da ake yi da ita, ta ce ita da Basma ne kawai suke yi lokacin, Maleek ya maida kan sa ya jingina da kujera tare da rufe idanunsa, gaba ɗaya ya ji duniyar ta masa zafi, ba abun da yake maimaitawa a cikin ransa face innalillahi...wannan wace irin ƙaddara ce mai muni ta same sa, Huda nata kallon shi cikin ɗaurewar kai, tunaninta komi ya faru da ya sa ya zo yake mata tambayoyin, gashi ta fahimci yana cikin tashin hankali sosai, tausayi ta ji ya bata a hankali ta ce, "I'm sorry dad..." Sai lokacin ya buɗe idanunsa da har sun rine da ja, kallonta ya yi ya jinjina mata kai, hannu ya kai cikin glove box ya ciro wasu kuɗi masu yawa da shi kan sa bai san nawa bane ya miƙa mata ya ce ta amsa ta je gida, ta bi kuɗin da kallo sai kuma ta ce mashi a'a ya bar su, ya ɗan lumshe ido ya ce ta amsa kyauta ce ya bata, ta miƙo hannu ta amsa tare da yi mashi godiya, cikin raunin murya ya ce mata pls ta ƙara kiyaye aikata duk wani abu da yake sa6on Allah ne, Huda ta ce masa in sha Allah ba zata ƙara aikata abu mara kyau ba, ya jinjina kai tare da saka mata albarka, ya ce ta tafi ta gaishe masa da mom ɗinta, kuma idan ta tambaye ta dalilin zuwan shi ta ce mata tare suke da Basma sun tsaya su gaisa da ita, ta ce masa to ta ƙara yi masa godiya daga haka ta fita daga motar..... *✨A CIKIN RAYUWA✨* ZAINAB BATURE 52 Bayan Maleek ya baro gidan su Huda, driving yake amman gaba ɗaya hankalinsa baya a tare da shi, damuwa ta yi masa yawa sai faman girgiza kai yake yi, wayarsa da ta fara ringing ce ta maido sa hankalinsa, sai da ta kusa tsinkewa sannan ya ɗauka, daga ɗayan 6angaren mummyn Huda ta yi magana yadda take kiran sa, saida ya yi ƙoƙarin saita natsuwarsa kafin ya amsa mata, ta ce dama Huda ce ta dawo gida da kuɗi ta ce shine ya bata, so ta kira to confirm ko haka ne, ya bata amsa da eh shi ya bata, godiya sosai ta yi masa kafin suka yi sallama, Maleek ya ajiye wayan, nan take ya ji wani irin tausayin iyayen da ke tsaye akan tarbiyar yaransu ya kama shi, rayuwa ta lalace, kana jajircewa akan bawa yaron ka tarbiya amman hakan bai hana tarbiyan lalacewa, al'amarin tarbiya yanzu sai dai mutum ya yi iya bakin ƙoƙarinsa sannan kuma ya dage da roƙon shiriya daga wurin ubangiji. Gaba ɗaya Maleek ji ya yi bai son komawa gida, a bakin hanya ya parker motan ya fito, wani street bench irin kujeran zama na bakin hanya dake gefe ya nufa ya zauna, haɗe hannuwansa ya yi tare da ɗaura ha6arsa ya rufe ido, tunaninsa ne ya maida shi can baya, a cikin ransa yake raya miya sa yake fuskantar irin wannan munanan ƙaddaran, tunanin ko dai akwai abun da yake aikatawa da ya sa6a ma shari'a ba tare da sanin sa ba ya zo masa a rai, saidai a iya hangen sa bai iya hango wani abu da yake aikatawa da ya sa6a addini ba, gaba ɗaya Maleek ya ji duniyar bata masa daɗi...lalle A CIKIN RAYUWA da akwai tarin darussa, hamshaƙin mai kuɗi kamar Maleek yau shine ya za6i zaman bakin titi fiye da ya koma cikin daular da yake, wannan na nuna duk irin tarin arziƙin mutum Allah na iya jarabtarsa ta yadda arziƙinsa ba zai iya masa magani ba face shi ubangijin da ya ɗaura masa ƙaddaran, don haka mutum kada ya ga yana cikin ni'ima, a ko yaushe Allah ya so zai iya jarabtarsa ta yadda zai manta duk wani jin daɗi da yake ciki, kada ni'imar da mutum yake a ciki ta saka shi shagala da yin addu'ar neman kariya daga mummunan ƙaddara. Maleek ya ɗauki lokaci a wurin cikin tsananin damuwa, har sai da Sapna ta kira shi tana tambayar ina ya tafi tun da ba ranar aiki bane, sannan ya miƙe ya koma mota ya tafi. Haka kwanakin suka kasance ma iyalin ba daɗi, kana ganin su gaba ɗaya suna a cikin matsananciyar damuwa, ita Sapna ma ko aiki ta kasa zuwa tana gida duk don saboda saka ma Basma ido, gashi tun bugun da Maleek ya yi mata har lokacin bata da isassar lafiya, a yadda Sapna take ji har aikinta zata iya ajiyewa saboda Basma. Ba irin ƙoƙarin da Sapna bata yi ba wurin ganin ta shawo kan Maleek ya amince da auren su biyun amman ya kafe akan bakansa, ƙarshe ma da kansa ya je har ɗakin Basma wanda tun da abun ya faru bai sake zuwa ɗakin ba, ko haɗuwa a cikin gidan ma basu yi don yanzu har abinci kowa a 6angarensa yake ci, sun daina zama tare a falo ko wurin shan coffee, duk wasu abubuwa da suke yi a tare musamman na nishaɗi duk sun daina yi, a kausashe ya ce mata ta fidda rai da auren Deen, idan ma har zai amince ta aure shi to sai ya tabbatar ta shiryu ta daina aikata abun da take yi don ba zai cuci Deen ya aura masa ita ba bayan ta lalata rayuwarta, kuka wiwi Basma ta saka masa tana masa rantsuwar ta daina don Allah tana son Deen kada ya ƙi amince ma auren su, ya ce mata a baya ma ai haka ta yi masa rantsuwa da alƙawarin ta daina, don haka yanzu sai idan shi da kansa ya tabbatar da ta daina ta shiryu sannan ko zan amince. Ba ƙaramin tashin hankali Basma ta shiga ba da hukuncin da dad ɗinta ya yanke, haka ta kasance cikin matsananciyar damuwa kullum bata da aiki sai na kuka, a gefe guda kuma Sapna na matuƙar ƙoƙari wurin jan ta a jiki tana kwantar mata da hankali tare da ɗaura ta kan hanyar daidai, musamman saboda hakan Sapna ta ɗauki hutun aiki. Tuni Nijeriya ta samu tikitin zuwa gasar world cup bayan ta yi nasara a wasan neman cancanta wato qualifiers, wanda nasarar samun tikitin ya fito daga hannun Deen da ya buga mata wasannin biyun ƙarshe da ya kai su ga samun nasara. Gaba ɗaya idanun duniya sun koma kan ƙasa mai masaukin baƙi wato Saudiyya, wadda tuni an yi babban shiri don wannan gagarumin taro, shirye shiryen sun haɗa da ƙara samar da wadatattun kayan more rayuwa, sufuri, da sauran abubuwan da ake buƙata don shirya irin wannan taro, an kuma sabunta da kuma gina manyan stadiums a birane guda biyar da aka za6a don gudanar da gasar. Yadda aka tsara yin gasar, a Riyadh, Dammam, Alkhobar anan ne za a fara gudanar da matakin farko na gasar wato group stage, sai Jedda da Riyadh a nan za a gudanar da Quater and Semi final, sai Final za a yi ta a NEOM wanda yake sabon birni da aka tsara da fasaha, gine-ginen zamani, da tsari mai ban mamaki. Tuni al'umma masoya ƙwallon ƙafa daga yankuna daban-daban na faɗin duniya suka fara hallara a ƙasar Saudiyya don kallon gasar, Riyadh da a nan za a fara gudanar da gasar ko ina ka hanga haske zaka gani, an ƙara ƙawata birnin da abubuwa masu jan hankali da burgewa da suka haɗa da abubuwa da ke jaddada ƙasar addinin musulunci ce, wasu cikin baƙi musulmai sun yi amfani da damar don su jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, wato su kalli gasar kuma su yi umra, hakan ya sa ko ta ina mutane ne sun cika tituna da hotel hotel, tawagogin ƙwallon ƙafa da za su fafata a gasar suma duk sun hallara a masaukai daban daban. Tuni tawagar Nijeriya ma ta iso, in da Deen ya kasance shine wanda aka za6a matsayin captain wato jagoran tawagar Nigeria a ciki da wajen fili, shi ke da alhakin ƙarfafa gwiwar ƴan uwansa, yin magana da alƙali (referee), da tsara ƙwarin gwiwa lokacin da lamari ya yi zafi. An fara gudanar da gasar kamar yadda aka tsara, cikin sa'a Nigeria ta tsallake group stage ta samu zuwa Quater final, gaba ɗaya a cikin gasar Deen yana ɗaya daga cikin taurarin da suke haskawa, wanda mutane har so suke a zo kan wasan shi, mutane a duk faɗin duniya sai yabon ƙwazon da yake nunawa suke, sai dai a wannan matakin da Nijeriya ta kawo a gasar, mutane musamman ƴan Nijeriya sun shiga ɗar ɗar sanin ba lalle su iya tsallakewa ba don nan ne ƙarshen matakin da Nigeria ɗin ta ta6a tsayawa, duk da ganin irin ƙwazon da Deen yake nunawa ya saka ma mutane hope ɗin za su iya tsallakewa. Cikin sa'a ta ubangiji Nigeria ta tsallake ta kawo matakin semi-final wato mataki na biyun ƙarshe, wanda mataki ne da Nijeriya bata ta6a kawo wa ba a tarihin gasar cin kofin duniya, ita da ƙasar Morocco sune ƙasashen Africa biyu da suka samu nasarar kaiwa wannan matakin, saidai ita Morocco ta ta6a kaiwa matakin semi final a gasar.....Abun na Allah ne! Africa ta bada mamaki, irin mamakin da mutane basu ta6a yi ba a gasar cin kofin duniya bayan da ƙasar Nigeria ta kai final, wani abu da bai ta6a faruwa ba a tarihin world cup wato ƙasar Africa ta kai matakin final, tabbas duniya ta shaida cewa africa ba wai ta gaza bane a baya don rashin ƙwarewa, kawai lokacin samun nasararta ne bai yi ba, a wannan mataki ƙasashe biyu ne za su taka rawar gani, ban da Nigeria sai ƙasar Netherlands wadda ita a tarihin world cup ta kakkai matakin final ba sau ɗaya ba amma bata ta6a lashe kofin ba. Gaba ɗaya nahiyar Africa ta cika da farin ciki da alfaharin wannan mataki da ta kai, mutane na ganin ko a haka aka tsaya Africa ta yi nasara...kamar yadda Nijeriya ke kallon Deen a matsayin jaruminta da ya kai ta ga wannan matakin nasara, haka itama ƙasar Netherlands tana da nata jarumin da ƙasar ke alfahari da shi kuma ya kaita ga nasarar kai wa final, sannan suna da ƴan wasa masu ƙwazo da salon wasa mai kyau, yanzu kuma sai zaman jiran ganin yadda zata kaya a final, in da gaba ɗaya hankalin duniya na akan wasan da waɗannan ƙasashen biyu za su buga, ana son ganin ko wacce zata yi nasarar cin kofin duniya...a wannan lokacin ƙasar Saudiyya ta ƙara cika da mutane da suka zo domin ganin yadda za a fafata a gaban idanunsu, gaba ɗaya ƴan gidansu Deen sun zo, haka Maleek da iyalansa, a 6angaren gidan su mom, Nailah ma alhaji Mahmud ya kawo ta sun zo tare, sai Bash da shima ya zo, daga Funtua ma daddy Sa'ad da mommy sai Sadeeya da Khaleel duk sun zo, sai Fahad shi daga ƙasar India in da a yanzu yake cikin yin course a can ya zo, saboda course din da ya tafi ne India ya sa har yanzu bai kai maganar auren shi da Leemarh ba wurin iyayensa ya bari sai ya gama. A gida Nigeria, al'umma ta cika da fata da sa ran ita zata yi nasarar lashe kofin, duk da wasu suna ganin abu ne mai wuya, yayin da manyan masu muƙamai da manyan ƴan kasuwa. har da manyan celebrities ke ta yi ma ƴan wasan alƙawarurruka idan har Nigeria ta ɗauki kofin. Ana gobe za a yi final, ƙasar Morocco ta yi nasarar zuwa ta ukku a wasan 3rd place da suka buga, wannan ya ƙara saka ma mutane fatan Nigeria ma ta yi nasara..... Ranar ta zo..... Ranar da duniya ke dakon jira ta zo. A yau, ƙasashe biyu wato Nigeria da Netherlands ne suka tsayawa juna a wasan ƙarshe na gasar cin kofin duniya, duniya ta tsaya cak, gaba ɗaya hankali ya dawo birnin NEOM in da a nan za a fafata a wannan dare, babban filin da za a yi wasan ya yi kama da abin da aka ƙirƙira a mafarki saboda haɗuwar sa, a cikin filin musulmai har da ƴan wasan suka gabatar da sallar isha da raka'a biyu ta nafila don roƙon sa'ar kammala wasan lafiya, bayan gama yin salla aka shiga shirye shiryen fara wasan, su Deen da abokan karawar su sun tsaya a layin gaba, duk suna sanye da jerseys na team ɗin ƙasar su, a damtsen hannun Deen ya saka armband launin green da babbar farar C da ke nuna shine captain a tawagar ta su, yayin da sumar kansa ke dauke da manyan kitso, sosai ya yi kyau idan ba ka san game da asalinsa ba da wuya a yarda shi ɗan Nigeria ne, hannuwan kowannan su na a ƙirji yayin da aka fara rera taken Nigeria.....wasan ya fara da ƙarfi, kowanne 6angare yana buga ƙwallon da ƙarfin zuciya, mutane na kallon Netherlands na da dabaru yayin da Najeriya ke da zafi, da gaske Deen ke buga wasan da duk wata ƙwarewarsa...iya bakin ƙoƙarinsa yake yi wurin ganin sun ci da kuma hana abokan karawar tasu zura ƙwallo....gaba ɗaya ya zama tauraro da ake ji da shi, hargowar magoya baya da masu sharhi ta cika filin, ko ta ina sunan Deen Jr ke tashi....gaba ɗaya yan wasa sun jigata, kowannen su ya jiƙe da zufa, duk da ƙarfafa gwiwa da canjin ƴan wasa a haka har aka tafi hutun rabin lokaci ba wanda ya yi nasarar zura ƙwallo a raga...A Nigeria ko ina ya yi tsit, kallo ya koma kusan ko wane gida, haka gidajen kallo sun cika maƙil da jama'a kowa yana jira ya ga yadda zata kaya, su Sageer ƴan gani kashe nin Deen ana gidan kallon kwallo an kasa an tsare anata addu'ar samun nasara....A Kaduna ma Salma tare da Aunty Kubra suna zaune a falo suna kallon wasan....Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, wasan ya ci gaba da zafi fiye da baya, al'umma sun cika da fargabar su wa za su samu nasara, fili ya cika da waƙe waƙen ƙarfafa gwiwa daga magoya baya anata ɗaga tutocin ƙasashen biyu, cikin sa'a Netherlands ta samu zura ƙwallo a ragar Nijeriya, sai dai bayan wasu ƴan mintuna Deen ya rama ma Nigeria sakamako ya kama 1-1, hakan kuma ya ƙara jefa mutane cikin tsananin fargaba da zullumi ganin lokaci nata tafiya....Salon wasa ya canza, kowane 6angare da zafin nama yake buga wasan, filin NEOM ya cika da sautin ƙwallon da a ke bugawa, hayaniyar magoya baya ta cika sararin samaniya.....hajiyar Ambasada ta kai hannu ta dafa kujera tana ƙoƙarin miƙewa, Balaraba dake zaune suna kallon ƙwallon tare a falo ta ɗaga kai ta kalle ta, ganin zata bar falon cikin girmamawa ta ce, "Hajiya baza ki ƙarasa kallo ba?" hajiya ta ɗan girgiza kai fuskarta a jagule ta ce, "Ba zan iya ma fargabar nan ba Balaraba, kin ji yadda ƙirjina ke faɗuwa, ƙilan shiyasa ma ake cewa kwallo bata da kyau saboda yadda take tada hankali...kuma babu kyau tada hankalin musulmi ...ina jin ma sai na kai ga shan magani, don da ƙyar in ba jinin nawa ya hau ba, na samu kwana biyu ya daidaita.." Har sai da Balaraba ta ɗan yi murmushi jin maganganun hajiya da ta nufi hanyar ɗakinta tana faɗin Allah Ya ba masu rabo sa'a. Lokacin da ya rage saura mintuna goma kacal a wasan ƙarshe, Deen ya karɓi ƙwallo daga gefen hagu, ya ƙetare ƴan baya biyu, yana nufar ragar Netherlands cike da zafin nama, amma kafin ya kai tauraron dutch team ɗin ya shiga da ƙarfi ƙafafunsu suka yi wata irin haɗuwa, nan take ƙwallon ta watse, Deen ya faɗi ƙasa da ƙarfi ɗayan ɗan wasan ya faɗa saman shi, shiru ya mamaye filin, komai ya tsaya cak, babu ƙwallo, babu kaɗe kaɗe, babu hargowar magoya baya, Deen na kwance a ƙasa ya dafe kansa da hannunsa yayin da idanunsa ke rufe, kamar duniya ta tsaya cak, nan take referee ya dakatar da wasan, a cikin kujeru magoya bayan Najeriya duk suka mimmiƙe wasu sun dafe kai da hannayen su yayin da wasu har sun fara hawaye suna kiran sunan Allah, nan da nan aka zagaye Deen likitoci suka shigo filin da gudu suka fara duba shi. Ƴan mintunan da suka ɗauka suna duba shi a wurin mutane tamkar sa'o'i ne...gaba ɗaya duniya ta ƙosa da son sanin halin da yake ciki, ganin an shigo da stretcher cikin filin wato irin abun ɗaukar mara lafiya hakan ba ƙaramin tsinka zuciyar mutane ya yi ba, aka fara tunanin ko ya haɗu da wani mummunan haɗari ne, lokaci guda magoya baya suka sare, a Najeriya halin da Deen ya shiga ba ƙaramin jefa mutane cikin tsananin tashin hankali ya yi ba, mutane sai addu'ar Allah Ya sa ba wani mummunan abu ya same shi ba, su Leemarh da ke cikin ƴan kwallo tuni sun fara kuka, ita mom da karfin hali ma cikin filin ta fara ƙokarin zata je amman su dad suka hana ta....Salma da tashin hankali ya bayyana a fuskarta, har bata san lokacin da ta ɗaura hannu a saman kai ba tana faɗin, "Innalillahi...wayyo ya Deen, Allah Ya sa dai ba wani mummunan abu ya same shi ba..." Aunty Kubra da itama hankalinta ya tashi tana kallon ta ta ce, "In sha Allahu ba abun da ya same shi." Balaraba da ta ci gaba da yin kallon ita kaɗai, itama ba ƙaramin tashin hankalin ganin abun da ya samu Deen ta shiga ba, a ranta take ayyana gara ma da hajiya bata nan hakan ta faru, ta san da ba ƙaramin tashin hankali zata shiga ba...kowa dai ya shiga tashin hankali da zullumi. Ana ƙoƙarin ɗaukar Deen ya fara motsi, a hankali idanunsa suka buɗe, kokarin tashi ya fara yi amma likitoci suka hana shi saboda ba ƙaramar buguwa ya yi ba a kai, hannunsa guda na dafe da kansa yayin da ya miƙar da ɗayan hannun sama yana nuna alamar yana nan...nan take filin ya fashe da ihu, farin ciki ya bayyana a saman fuskokin mutane, cikin ƙaraji wasu cikin magoya bayan Nigeria larabawa suka shiga faɗin, "_Deen for life_..." aikuwa sai duk mutane aka ɗauka ana faɗin hakan, hada masu tsalle da yin rawa, farin cikin ba a iya filin ya tsaya ba, har da masu kallo na waje...cikin tsananin farin ciki Salma ta faɗa jikin aunty Kubra da itama ke ta sakin faffaɗan murmushi, a gidan kallon ƙwallo da su Sageer suke nan ma ihunsu ne ya karaɗe wurin kamar za su fasa bangon wurin, suma suka shiga fadin abun da magoya baya na cikin tv ke faɗi wato Deen for life. Likitoci sun yi ƙoƙarin hana Deen ci gaba da buga wasan, a cewar su yana buƙatar ya huta, amman Deen ya dage akan zai iya dole aka barshi, wasan ya ci gaba bayan referee ya ƙara mintuna goma matsayin injury time, kana ganin Deen kan san ƙarfin hali yake yana buga wasan don karsashinsa ya ragu ba kamar a baya ba, yana buga wasan wani lokacin yana kai hannu kansa, a haka dai har lokaci ya cika ba wanda ya ƙara ci, hakan ya sa aka ƙara extra time na mintuna talatin...haka dai aka ci gaba da fafatawa mai cike da ƙalubale da zullumi....sai da ya rage bai fi saura mintuna ukku ba lokacin da aka ƙara ya ƙare Netherlands ta samu bugun gefe, ƙwallo ta biyo iska ta shige ragar Nigeria, nan take shiru ya mamaye filin na ɗan lokaci, kafin allon sakamako ya nuna 2-1 daidai nan kuma lokaci ya cika, muryar stadium announcer ta karaɗe ilahirin filin da faɗin, "_Ladies and gentlemen, the moment you’ve all been waiting for… After an intense battle on the pitch, the winner of this edition of the World Cup is… the Netherlands! Congratulations to the Dutch team on their incredible victory....!_" Ihun magoya baya ya cika wajen, ƴan wasan Netherlands suka cika da tsananin farin cikin samun rabon da suka daɗe suna jira, yayin da ƴan wasan Nijeriya suka yi tsaitsaye, wasu suna ɗan murmushi wasu kuma sun ɗaura hannuwa a saman kai, Deen ya duƙe a ƙasa tare da saka hannuwansa ya rufe fuskarsa, ƴan'uwansa ƴan wasa suka ƙaraso wurin shi suma duk suka duƙa tare da kai hannu suka cire hannuwansa da ya rufe fuska, hawaye haɗi da kuma murmushi ne suka bayyana akan kyakkyawar fuskarsa, suma duk suka shiga sakin murmushi tare da haɗe kawunan su, koda ba su suka yi nasara ba sun san cewa sun ɗaga Najeriya sama, sun kaita wani mataki da bata ta6a kaiwa ba a tarihin ƙwallo, sun san hakan ma babbar nasara ce, kuma kasancewar Morocco ta ukku hakan ma abun alfaharin Africa ne na kaiwa wani mataki da nahiyar bata ta6a kaiwa ba a tarihi. Bayan kammala gasar aka shiga gudanar da closing ceremony, shagali ne mai tsuma zuciya da saka wanda ba ya a wurin jin tamkar ya yi tsuntsuwa ya gansa a wurin....Bayan da aka bada trophy da gold medals ga ƴan wasan da suka zo na ɗaya, Netherlands ta ɗaga shi, amma Nigeria ce ta ɗauki zuciyar duniya, su Deen da suka zo 2nd place suma aka saka masu silver medals a wuya, Marocco da suka zo 3rd place aka saka masu bronze medals, bayan medal Deen kuma ya samu kyautar Golden Ball, wato kyautar da ake bayarwa ga wanda ya kasance mashahurin ɗan wasa na gasar, haka kuma ya samu yabo da jinjina daga manyan mutane da shugabbanin ƙasashen duniya wanda suka hallaci wasan ƙarshen, ciki har da shugaban ƙasan Nigeria wanda shima ya je kallon final ɗin tare da wasu muƙarrabansa, ana ta gaisawa da Deen wasu suna rungumarsa, crown prince na nan Saudiyya har da wata haɗaɗɗar alkyabba ya saka mashi tare da rumgume shi, sai suka yi kaman jinsi ɗaya..... Salma na kwance a saman gadonta jikinta sanye da doguwar rigar bacci, wani irin farin ciki take ji yana ratsa zuciyarta sakamakon nasarar da su Deen suka yi, sai dai kuma a wani 6angare na zuciyarta tana jin tsananin son yin magana da shi, ta damu sosai da abun da ya same shi ɗazun, shiyasa take jin ina ma zata samu yin magana da shi don ta yi masa ya jiki, duk da tun bayan kammala gasar ta tura masa saƙon taya murna...sam ta kasa yin bacci sai faman juyi take, akai akai take ɗaukar wayarta ta duba saƙon da ta tura masa ko ya shiga, wani lokacin kuma ta shiga social media da gasar tasu ta karaɗe ko ina, mutane nata murnar nasarar da suka yi, ko ina hotuna da videos ɗin Deen na gasar ne ke ta trending ana ta yabon ƙwazon da ya nuna, hakan kuma ke ƙara ma Salma jin son yin magana da shi...a haka har dare ya raba Salma na abu ɗaya, bacci ba mai nauyi ba ke ɗan ɗaukar ta, kuma da ta fara sai ta farka ta jawo waya ta duba wai ko zata ga ya hau online, ƙarshe dai ta fidda rai dama ita kanta ta san ba lalle ta samu yin magana da shi ba a wannan lokacin, haka nan ma da ba lokacin gasa irin haka ba idan ta tura masa saƙo sai a daɗe bai duba ba, balle kuma yau da ta san dole bai da lokacin kan sa, tuna hakan ya sa ta haƙura, dama kawai zuciyarta ce ta ƙwallafa mata son yin magana da shi, ajiye wayar ta yi ta rufe ido, after some minutes ta sake buɗe idanun, sam bacci mai nauyi ya ƙi ya ɗauke ta, duk ta rasa mike mata daɗi, kallon wayarta ta yi kamar kar ta ɗauka sai kuma ta kai hannu ta ɗauko ta, power ta latsa haske ya bayyana, a sanyaye ta kai hannu ta buɗe whatsApp, bayan ta shiga bin contact ɗin Deen da ke a sama ta yi da kallo saboda shine mutum na ƙarshe da ta tura ma saƙo yau, ta yi shiru tana ta kallon saƙon da har lokacin tick ɗaya ya nuna alamar bai shiga ba, har zata fita daga whatsApp din kawai sai gani ta yi tick ɗin saƙon nata ya koma biyu alamar ya shiga amman bata san lalle idan an buɗe ba, wani daɗi Salma ta ji ya ziyarce ta, hannunta har ɗan rawa yake ta buɗe chat ɗin, shiru ta yi tana dakon wai ko zata ga ya yi alamar ya karanta, har bayan wani ɗan lokaci tana a haka, ranta ne ya bata ta san dole yau yana da tarin saƙonni ƙilan nata ma yana a can ƙasa ba lalle ya duba ba, tunanin ko ta sake tura masa wani saƙo yadda idan ma nata yana ƙasan zai dawo sama ya gani, cike da shakkun ko ta yi hakan ta kai hannu a ɗarare ta yi typing, "Ya Deen." iya abun da ta rubuta ke nan ta tura masa, fita ta yi daga chat ɗin ta bi contact ɗin nasa da kallo gabanta har ɗan faɗuwa yake, after few minutes sai gani ta yi ya turo mata sako...da sauri ta buɗe, "Salmerh." Shima abun da ya turo mata ke nan, wani kalan murmushi ne ya su6uce mata, ta sake tura masa, "Na'am, ya Deen ina yini." Sai da aka ɗan ɗauki lokaci ya maido mata, "Baki yi bacci ba?" Ta tura masa, "Eh.." Ba a ɗau lokaci ba ya maido mata, "Why?" Ɗan jim ta yi kafin ta maida mashi amsa, "Saboda kai, ina son in taya ka murna." Ya ce, "Ai na ga kin tura mani message, zan gani, da kin baccin ki." Ɗan jim Salma ta yi sai kuma ta sake tura masa, "Dama kawai na damu ne da abun da ya same ka da kuna yin ƙwallo, shi ne nike son in maka ya jiki idan ka hau online." Shiru bata ga ya maido mata reply ba kuma ta ga ya karanta....lokaci ɗaya Salma ta ɗan zaro ido ganin ya kira ta video call, mamakin da gaske shi ke kiranta video call ɗin ya cika ta, da sauri ta tashi daga kwancen da take, tunani ta yi ai ba zai ganta ba idan ta ɗauka saboda duhu, ɗan miƙewa ta yi ta kai hannu ta kunna fitilun ɗakin haske sosai ya gauraye ko ina, ɗaukar kiran ta yi gabanta nata ɗan faɗuwa, shiru ta yi tana kallon Deen da ɗan murmushi akan fuskarta, yana kwance a saman wani lafiyayyen gado, jikinsa yana sanye da farar riga yayin da rabin jikinsa ke lullu6e da farin lallausan bargo, shima bedsheet da pillow case din gadon da yake kwance duk farare ne tas, sumarsa na a sake ta tarwatse a saman pillow da alama ya kwance kitson kansa, kana ganin shi ka san har lokacin akwai alamun gajiya a tattare da shi, sai ɗan lumshe ido yake, a hankali Salma ta ce, "Ya Deen sannu..." Kai ya ɗan jinjina mata, kamar ba zai yi magana ba, a hankali ya buɗe ido ya kalle ta ya ce, "Miyasa zaki hana kan ki yin bacci har wannan lokacin, yanzu nan ba 3am ya yi ba?" Ta ɗaga mashi kai tare da fadi mashi karfe ukku da rabi a nan, shiru bai ce komai ba ita kuma tana ta ɗan murmushi, gani take abun kamar ba gaske ba, mutumin da yau duk duniya ake magana akan shi shine take magana da shi haka, "Ya Deen na taya ka murna sosai." Yana kallonta da ɗan murmushi ya ce mata ya gode, sai kuma ta ji ya ce amman basu suka yi nasaran ɗaukan cup ɗin ba, da sauri ta ce, "Ai kuma kun yi nasara yaya Deen, tun da na ji an ce Nigeria bata taba kai wa wannan matakin ba." Slowly ya furta, "Haka ne." ta ce, "Ya jiki?" Hannu ya kai ya ɗan shafi kan shi da murmushi ya ce mata ya samu sauƙi, ta ce mashi Allah Ya ƙara sauƙi ya tsare gaba ya amsa....tana ta kallon shi ganin yadda idanun shi ke ta lumshewa ta yi tunanin kada ta takura masa ko bacci yake ji, ta ce, "Yaya Deen ko bacci ka ke ji kada in takura maka." Buɗe idanun shi ya ɗan yi sosai yana kallon ta ya ce no bata takura masa ba ai shi ya kira ta, ya ce ya yi bacci sosai yanzu ma sallan asuba ya gama, kawai maganin da ya sha ne bai gama sakin shi ba, Salma ta ɗaga kai alamar fahimta, sosai take jin daɗin muryarsa tana jin kamar kar su daina yin maganan. "Ya school?" ta ji ya tambaya, Ta ɗan buɗa ido tana murmushi ta ce, "Ai na gama." Ya ce, "When?" "Kusan wata ukku ke nan." ta bashi amsa, idanun shi akanta ya ce,"Mi yasa baki sanar mani ba?" Tana ta ɗan murmushi ta ce, "Kawai na ga lokacin ka yi busy sosai saboda shirye shiryen wannan gasan." Ya ɗaga kai, sai kuma ya ce amman ai ya bata number din da zata riƙa reaching nasa out miyasa bata amfani da shi, ta ce haka nan kawai kada ta rinƙa takura ma manager ɗin nasa, kuma ta ga ta wannan number ɗin ma idan tana son yi mashi magana tana amfani da ita lafiya lau, shiru ya ɗan yi still yana ta kallonta, da alama zumuɗin kiran ta da ya yi yasa ta manta a yadda take, kanta a buɗe don tuni da tana juye juyen dakon shi a waya hulan ta ta cire, kanta na a kwance ba kitso ta yi fakin gashin ta nade shi a wuya, daga gaban kanta sumar wurin a kwance luff luff, "Yanzu sai aure zaki yi ke nan?" Ta ji ya jefo mata tambayar, da sauri ta girgiza masa kai ta ce, "A'a.." ta ji ya ce miyasa, "Karatu nike son yi, yanzu haka ma na dawo Kaduna wurin aunty na a nan zan ci gaba da karatun." ya ce mata mi yasa bata son yin aure, Salma ta ji tambayar ta yi mata nauyi, gashi ta ɗan ji mamakin ma yadda ya yi mata irin tambayar, kiran sunanta ta ji ya yi ta ɗaga ido ta kalle shi, ya ce miyasa ta yi shiru, da ƙyar tana sauke idanunta ta ce, "Haka nan, na fi son yin karatu." ya ce, "But, ko an yi aure ana karatu." Kanta a ƙasa Salma ta ɗan cije baki jin abun da ya ce, ta ɗaga mashi kai alamar eh, "Ke miyasa baza ki haka ba?" Ɗago idonta ta yi suka shiga cikin nashi, a hankali ta ce, "Kawai...ban sama rai na aure zan yi ba." Ya ɗan yi shiru still kallonta yake, ita kuma duk nauyin maganar auren take ji hakan yasa ta kasa tsayar da idanunta kan shi, softly ya ce "Ko baki da suitors ne?" Da sauri ta ɗaga ido ta kalle shi, sai kuma ta yi ƴar dariya ta ce, "Ina da su...kawai dai..." Ta yi shiru ba tare da ta ƙarasa ba don bata ma san mi zata ce masa ba, "Ko duk ba wanda ya yi maki da zaki aura a cikin su?" ya tambaya, Salma ta ɗan runtse ido kanta a ƙasa, tunanin wace amsa ma zata bashi ta shiga yi, ita da ba wani samari sosai gare ta ba saboda ba saurarar su take yi ba, tsayayye wanda zata iya aura bai wuce Dr Hisham ba, shi kuma har yanzu bata wani jin shi a ranta kawai dai tana tare da shi ne, kuma ta ga kaman aunty Kubra tana son ta da shi, kiran sunanta ta ji Deen ya yi, a hankali ta amsa ya ce ta bashi amsa, ta ɗaga mashi kai ta ce eh ba wanda ya yi mata da aure, shiru ya yi yana ta kallon ta ita kuma ta ƙi ɗago fuskarta, a cikin rai Deen yake jin kaman this is the right time da ya kamata ya sanar da ita abun da yake ji game da ita tun can baya, dama ya bari ne sai ta kammala secondary school ɗinta ko zai bayyana mata sanin tana da son karatu, kada hakan ya raba mata hankali, "Salmerh.." Har sai da ta ji gabanta ya faɗi don bada irin sautin da ya saba kiranta ya kira ta yanzu ba, murya ƙasa ta ce, "Na'aam..." ba tare da ta ɗago ba, shiru ya ɗan yi kafin ya yi ƙasa da murya ya ce, "Ni na yi maki?" Ƙirjinta ne ya wani irin buga, ba shiri Salma ta zaro ido tare da ɗago kai tana kallon Deen da idanunsa ke a lumshe tamkar ba shine ya furta maganar ba..... *✨A CIKIN RAYUWA✨* ZAINAB BATURE 53 Da sauri Salma ta sauke idanunta, ruɗewa ta yi a cikin ranta ta shiga kokonton anya shi ya faɗi abun da ta ji, ko dai kunnuwanta ne suka ji ba daidai ba.., "Kin yi shiru..." Ta ji saukar muryarsa, a hankali ta ɗaga ido ta ga kallonta yake, a ɗan dabarbarce ta ce, "Ba...ban gane abun da kake nufi ba." Gyara kwanciyar shi ya ɗan yi fuskarsa a sake ya ce mata abun da ta ji shi yake nufi, sauke idonta ta yi, ta kasa yarda idan yadda ta fahimci maganar hakan yake nufi, gently ya ce, "Idan nima ban yi maki ba, just tell me I will understand." Motsa baki ta shiga yi ta haɗiyi wani miyau, a hankali ta girgiza masa kai, ya ce mi hakan ke nufi, da ƙyar tana jin kamar zata nutse a wurin ta ce, "A'a..ka yi mani idan da gaske kake." Ɗan murmushi ya yi ya ce idan ba da gaske yake ba why zai yi mata irin maganan, shiru suka ɗan yi kafin ta ji ya ce it seems like she's not ready su yi maganan yanzu bari ya barta sai wani lokacin idan ta shirya, gabanta ne ya ɗan fadi zuciyarta ta kwa6e ta kan bari ta yi ma kanta ya yi tunanin ko bata son shi shike nan ya ki ƙara yi mata maganar, da ɗan sauri ta ce, "A'a ya Deen, kawai dai...ina jin kunya ne." Shiru ya yi still da ɗan murmushi akan fuskarsa, bai yi tunanin zai nuna yana son mace ta nuna masa kunya haka, duk da ita ce mace ta farko da ya fara furta ma magana irin wannan, sai dai shi mata su ce suna son shi, amman duk da haka kunyarta na burge shi, sigh yay ya ce, " I want you to tell me the truth Salmerh, do you love me?" Salma ta ɗan runtse ido ta jinjina masa kai alamar eh, calmly ya ce, "Taya zan yarda kin kasa ko kallo na." Shiru bata ce komai ba kuma bata ɗago kai ba, ya yi kasa da murya ya ce, "Idan kina son in yarda da gaske kina so na...look me in the eyes and say it." Zuciyarta ce ta shiga tunzura ta kan ta yi yadda ya ce kar ta yi ma kanta, da ƙyar ta ɗago kai ta kalli screen ɗin wayan suka haɗa ido da shi, motsa baki ta fara yi tana kikkafta ido, sam ta kasa faɗa masa hakan yayin da take kallon shi, kawai sai ta rufe idanunta muryarta na ɗan rawa ta ce, "I..love you..." Jin ya yi shiru bayan ta faɗi haka gabanta ya ɗan fadi, ta yi tunanin ko ma ya katse kiran tun da bata yi yadda ya ce ba, a hankali ta ɗan buɗe idanunta don ta tabbatar ko hakan ne, haɗa ido suka yi da shi yana ta kallonta, yadda ta runtse idanu ta faɗa masa hakan ba ƙaramin kyau ya ga ta yi masa ba shiyasa yake ta kallonta, ganin kallon da yake mata sai ta yi tunanin ko bai ji daɗi ba da bata yi yadda ya ce ɗin ba, sai da ta tattaro dukkan ƙarfin gwiwarta tana kallon cikin idanun shi a sanyaye ta ce, "I love you ya Deen." Wani kallan murmushi ta ga ya yi kawai ta yi saurin saka hannunta guda ta rufe fuskarta, daga haka ya ce, "Sarkin kunya, bari in bar ki ki yi bacci we will talk later." Ta ɗan ɗaga kai, ya sake cewa, "Make sure you get some sleep, I love u too." A hankali ta ɗan ɗago kai ta kalle shi ya sakar mata wani kallo da sai da duk jikinta ya amsa, daga haka ya yanke kiran, Salma ta kafe screen din wayan da kallo ta ɗan waro ido, ganin abun take kaman ba a gaske ya faru ba, ko dai mafarki take yi? hakan ta raya a zuciyarta, ƙoƙarin gasgata anya ba mafarkin take yi ba ta shiga yi, tunanin tun farkon lokacin da ta kwanta bacci zuwa yanzu ta shiga yi, hannunta ta ɗago ta kai shi gefen fuskarta ta ɗan mammari kanta a hankali, yadda wai in ma mafarkin ne ko zata farka, ganin tana nan dai yadda take ta sake kai hannu ta tsunkuli jikinta ta ji zafin ya ratsa ta, zuciyarta ta shiga tabbatar mata da duk abun da ya faru tsakaninta da Deen da gaske ne ba mafarki ba, faɗawa tayi kan gadon ta kwanta tana sakin faffaɗan murmushin farin ciki, wai ita ya Deen ke so she couldn't believe it! Wayarta ta ɗauka ta shiga Social media tana kallon hotunansa da videos dake ta yawo, wani farin ciki ne ya mamaye mata zuciya, duk da haka ta kasa yarda wai shi ne ke son ta, bayan ta gama kalle kallen hotunan ta ajiye wayan gabanta ta lumshe ido, zuciyarta ta shiga dawo mata da abun da ya wakana a tsakanin su, tana ta faman sakin murmushi a haka har bacci ya yi awon gaba da ita. Saboda rashin baccin da Salma bata yi ba da wuri, sai wuraren ƙarfe takwas saura ta farka, da sauri ta sauka daga kan gado ta nufi banɗaki ta yo alwala, bayan ta gama yin sallan zaune ta yi a wurin ta ɗaura kanta a gefen gado mafarkan Deen da ta yi na dawo mata, sai sakin murmushi take yi, da sauri ta juya jin an buɗe ƙofar ɗakin, aunty Kubra ce ta shigo tana sanye da rigar bacci da ta tsaya mata iya gwiwa kanta ta saka hula, cikin ɗakin ta shigo idanunta akan Salma da ta juya tana kallon ta itama fuskarta da murmushi, "Baby ba dai sai yanzu kika yi salla ba?" Salma ta ce, "Aunty makara na yi, ban daɗe dana tashi ba." Aunty ta gyaɗa kai ta ce, "Ai ban san baki tashi ba da asuba da na zo na tada ki. Halan social media kika shiga kallon abubuwan world cup shiyasa kika makara." Salma ta ɗaga mata kai kawai tana murmushi don bata san ta yadda zata sanar mata abun da ya faru tsakanin ta da Deen ba, juyawa aunty ta yi tana faɗin bari ta je ta haɗa masu breakfast dama ta ga bata fito bane shine ta shigo ta ga ko lafiya, Salma ta ce mata ta bari gata nan fitowa yanzu ta haɗa breakfast ɗin, aunty da ke niyyar fita ta ce ta yi zamanta kawai, bayan fitar aunty ci gaba da tunane-tunanenta ta yi, sai bayan wani lokaci sannan ta miƙe ta cire hijab ɗin da ta yi sallan ta ninke, fita ta yi daga ɗakin ta nufi kitchen. Bayan sun zauna yin breakfast, lokaci lokaci aunty ke kallon Salma da kana kallonta zaka ga alamun farin ciki akan fuskarta, wani lokaci har dakatawa take da cin abincin tana ɗan murmushi, bayan sun yi nisa cikin yin breakfast din, aunty ta dakata tana kallon Salma ta ce, "Baby ya aka yi ne, na ga alamun yau kina cikin farinciki." Salma ta kalle ta tare da sakin faffaɗan murmushi, itama aunty ta yi murmushi ta ce, "Mi ya faru?" Salma ta kasa magana sai murmushi kawai, aunty ta sake cewa, "Bani in sha mana babyna, Allah Ya sa alkhairi ne." Salma ta shiga motsa baki ganin yadda aunty ta kafe ta da ido tana murmushi, cikin jin kunya ta ce, "Dama jiya da daddare ne muka yi vedio call da ya Deen, shine...ya ce...wai yana sona." Ta ƙarasa tana sunne kai, aunty ta yi shiru a cikin ranta ta shiga tunanin waye Deen ɗin, tunanin mai suna Deen da ta sani ta shiga yi, wani Zaharadeen da suke matsayin cousin da ke a Katsina ya faɗo mata a rai, ta ce "Wane Deen? Ko Zaharadden ɗin aunty umma?" Salma ta girgiza mata kai alamar a'a, aunty ta ce wani ne a can Funtua? Salma nata murmushi ta ce, "Yaya Deen fa ɗan kwallo nike nufi." Aunty ta bita da wani kallo ta ɗan saki baki, da alamun mamaki aunty ta ce shi ɗin ne ya ce yana son ta, Salma ta ɗaga mata kai, aunty ta ce, "Amma dai mafarki kika yi ko?" Salma bata san lokacin data kyalkyace da dariya ba, "To in ba mafarkin ba baby taya kawai zaki ce mani ya ce yana son ki, bacin tare dake nan muka kalli wasan su da daddare. Sannan mutumin da yake cikin wannan hidiman yaushe har ya samu wani lokacin da zai kira ki ya ce yana son ki, sai dai idan wasan kakan da kike mani wani lokacin ne ya motsa zaki mani yanzu." Ta kai maganar tare da kai chips baki, Salma ta ce, "Allah aunty da gaske nike, bari mu gama in ɗauko wayata in nuna maki kiran da ya yi mani." Aunty dai ɗan murmushi kawai ta yi tana ci gaba da cin abincinta, a ganinta taya hakan zai faru tsakanin jiya da daddare zuwa yanzu da safe ganin halin da Deen ɗin yake ciki. Bayan sun gama yin breakfast Salma ta kwashe kayan ta kai kitchen ta wanke, lokacin da ta fito aunty na zaune a saman kujera ta bita da kallo, nufar hanyar ɗaki Salma ta yi, bayan ta fito tana riƙe da wayarta ta dawo wurin aunty ta zauna a gefenta, chat ɗinta da Deen ta shiga tana nuna ma aunty da kuma lokacin da suka yi magana, sannan ta je wurin whatsApp calls ɗinta ta nuna ma aunty contact ɗin Deen da ke a sama, shiga cikin kiran ta yi tana nuna mata lokacin da suka ɗauka suna yin video call, aunty data fara yarda da maganar Salma ta ɗan buɗa ido ta ce, "To da kuna yin video call ɗin sai kawai ya ce yana son ki?" Tiryan-tiryan Salma ta shiga bata labarin yadda komai ya faru, aunty ta ƙara waro ido sai kuma ta saki faffaɗan murmushi ta ce, "Babbar magana!" ta hau jinjina kai mamaki ya cika ta, after a while tana kallon Salma ta ce, "To yanzu idan ya fito zai aure ki, auren zaki yi ke nan?" Salma ta ɗan sunnar da kai sai kuma a hankali ta ɗaga mata kai alamar eh, aunty tana dariya ta ce, "To kuma ya zamu yi da Dr Hisham dake jiran lokacin da za a bashi dama?" Salma ta ɗan tura baki ta ce ita ai dama har yanzu bata ce mashi tana son shi ba ko yi mashi alƙawarin zata aure shi ba, aunty dake ta murmushi ta ce, "Da yake fa zuciya ta samu wanda take so ko?" Dariya Salma ta yi ta rufe fuska, "Yanzu dai ke nan kawai a dakata da shirin fara karatu, mu fara shirin kayan ɗaki. Amman baby anya baki ɗauko mana da girma ba?" Ta karasa tana jinjina kai, ita dai Salma ɗan murmushi kawai ta yi bata ce komai, ƴar ajiyar zuciya aunty ta yi ta ce, "Allah zai rufa asiri, kuma dai ai ya san wacece ke, ƙilan ma ki ga su ce basa buƙatar wasu kayan ɗaki, tun da na san da ƙyar idan kuka yi aure ku zauna a nan, koma dai ya aka yi ba abun da zai gagara in sha Allah." Bayan ta gama yin maganar ta yi shiru tana kallon wuri ɗaya, can ta saki wata dariyar bosawa ta ce, "Ko ba don komai ba na ji daɗin al'amarin nan saboda Sageer, gashi Allah Ya nuna masa ikonSa don uban sa...." Kallonta Salma ta yi tana dariya ta ce, "Aunty ashe baki manta ba." aunty ta ce, "Ta ya zan manta da wannan uban cika bakin da ya yi ma mutane, wani ba yadda za ai ya so ki, shi da yake ganin mata iri iri, wa ya mutu wa ya dawo, aikuwa zai ga ƙaryar iskancin sa wllh." Dariya duk suka yi, a sanyaye Salma ta ce, "Yanzu to aunty ya za a yi da Dr ɗin?" abun ya tsaya mata ne a rai tun ɗazun da aunty ta kawo maganarsa, "Ki bari na san ta yadda zan 6ullo ma al'amarin in sha Allah. In da na ji daɗin abun da ya kasance dama kina tare da Deen ɗin kina masa aiki ba yanzu daga baya kuka haɗu ba...zan dai san ta yadda zan fahimtar da shi a rabu lafiya, amman dai ba zan yi saurin yi mashi magana ba, mu jira mu ga abun ya kankama tsakanin ku tukun. Allah Ya tabbatar mana da alkhairi." A hankali Salma ta ce, "Ameen." Aunty ta ɗan waro ido ta ce, "Anya baby, wato saboda muradin ran ki ne ko ƴar al kunya ma baza a nuna mani ba." Salma ta yi saurin rufe fuska, bayan ta cire hannunta ta sigar shagwa6a ta ce, "To aunty bake kika ce in an yi addu'ar da ta shafi rayuwata in daina jin kunya in rinƙa amsawa ba." Aunty dake kallon ta da murmushi ta ɗan ta6e baki, shiru suka yi kowa da abun da ke masa yawo a rai, aunty gani take kamar Deen ya fi ƙarfin Salma, amman da ta tuna cewa a wurin Allah komai mai yuwuwa ne sai ta ji ƙwarin gwiwa. Bayan kwana biyu da gama gasar, ranar asabar wuraren sha ɗayan safe tawagar su Deen suka iso Nigeria, wurin saukar jirgin ta cika da mutane, kama daga manyan masu muƙamai, zuwa manyan ƴan kasuwa, manyan celebrities da sauran su, har da shugaban ƙasa da ya riga ya dawo, red carpet reception aka shirya masu da ƴan mata masu sanye da kaya launin tutar ƙasa sun jera a bakin jirgin suna riƙe da flowers abun gwanin burgewa, lokacin da ƙofar jirgin ta buɗe tawagar ƴan ƙwallon suka fara fitowa wuyan su rataye da medals da aka basu yayin da Deen ke riƙe da kyautar da ya samu, kowa fuskarsa ta cika da annuri, nan take band dake gefe suka fara kaɗa ganguna ana busa taken Nigeria, shugaban ƙasa ne ya fara tarbar su cike da farin ciki akan fuskarsa, haka sauran mutanen dake a wurin duk suka tarbe su cikin farin ciki da kuma yabawa, kowa so yake ya rungumi Deen ko ya gaisa da shi, ana ta jinjina masa kan ƙwazon da ya yi, fuskar Deen ta cika da annuri yana ta murmushi, sai da aka ɗauki lokaci kafin ya ƙarasa wurin su mom ɗin sa da suma suna a wurin tun jiya su suka dawo, mom Jameela ta kasa rufe baki sai faffaɗan murmushin farin ciki take saki cike da alfahari, ƴan jarida da ke a wurin suna ta aikin ɗaukar rahoto da kuma yaɗa shi kai tsaye ga mutane, har da drone camera da ke ta shawagi a sama tana ɗaukar bidiyo. Bayan gama tarbarsu duk aka shiga motoci aka nufi barin wurin. A titin barin airport ɗin nan ma masoya da jama’a sun taru, wasu na ɗaga tambarin team ɗin wasu kuma tutocin Nigeria, wasu na riƙe da manyan hotunan su har da masu sanye da riguna da ke ɗauke da hotunan su, ƴan wasan na a cikin motoci masu buɗaɗɗen rufi suna ta gaisawa da mutane ta hanyar ɗaga masu hannuwa, daga airport victory parade aka yi wato aka ɗan zaga gari da yan wasan mutane na gaisawa da su tare da nuna murnar nasarar da suka yi, daga baya aka wuce Eagle Square inda aka shirya bikin tarba da kuma karramawa. Biki sosai aka yi da su kaɗe kaɗe da raye raye, sababbin wakokin da aka yi musamman saboda gasar sun karaɗe wurin, daga baya shugaban ƙasa ya yi masu karramawa ta musamman da babbar lambar yabo ta OON. Sosai suka samu manyan kyaututtuka daga gwamnati da manyan ƴan kasuwa da suka haɗa da motoci, gidaje, da manyan kuɗaɗe. A ranar sai dare Deen ya samu zuwa gidan bayan sun yi dinner tare da shugaban ƙasa da muƙarrabansa a fadarsa. familynsa sun cika da farin cikin nasarar da suka yi, musamman mom da kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha ba kamar ganin irin kyaututtukan da ya samu masu tsoka. Bayan dawowar tasu wasu daga cikin gwamnoni suka gayyace su zuwa jahohin su suma suna son karrama su, ciki har da gwamnan Katsina. Lokacin da Deen ya je Katsina ya samu kyakkyawar tarba daga wurin gwamna tare da muƙarrabansa da kuma al'umma masoya ƙwallon ƙafa, a gidan gwamnati aka sauke shi, gwamna ya haɗa mashi dinner in da ya nuna farin sosai kan nasarar da suka yi da kuma ƙwazon da ya yi da ya kai su ga nasarar, ya bayyana yana alfahari da kasancewar Deen ɗan jaharsa, a nan ma Deen ya samu kyaututtuka daga manyan masu muƙamai da suka haɗa da motoci da kudaɗe, har da kyautar gida gwamna ya bashi a nan Katsina. Bayan Deen ya kai ziyarar gaisuwa masarautar Katsina, daga nan ya wuce masarautar Daura wadda take asalin masarautar hausa don kai gaisuwa da amsa saƙon gayyatar da sarkin Daura ya yi mashi, a nan sarkin ya bashi kyautar sarauta ta 'Zakin Wasannin Ƙasar Hausa,' Deen ya nuna jin daɗin sarautar sosai, nan aka saka lokacin da za a yi bikin naɗin shi...tuni hotuna da videon ziyara da kuma alkhairan da Deen ke ta samu duk suka karaɗe shafukan sada zumunta, mutane nata mashi laƙabi da mai sa'a, yayin da hakan ke ta ƙara zaburar da matasa masu burin zama kamar shi irin su Sageer. Daga Katsina Deen ya dawo Funtua, a satin ne suka tare a tamfatsetsen gidansu da Dad ya gina, babban ginin bene ne na zamani na gani na faɗa, wanda a duk garin babu kamar shi wurin kyau, ba don an san familyn su dad ɗin masu arziƙi bane da tabbas sai al'umma sun ce kuɗin su ya sata ya yi ginin, ƴan'uwa da abokan arziƙi anata zuwa ganin gida ana masu Allah Ya sanya alkhairi, su mom abun nema ya samu sai faman kauɗi take tana kallon mutane a ɗaɗɗage, musamman ganin mommyn su Fahad, dama sosai take kishi da ita, sai dai ita hajiya Ameena da yake ta yi gadon arziƙi da sarauta sam bata damuwa da duk abubuwanta, zumuncin da Allah Ya haɗa tsakanin su take yi da ita da zuciya ɗaya, duk abun nan Fahad baya nan, don bayan gama gasar world cup ƙasar India ya koma, amman duk abubuwan dake faruwa yana gani yana taya Deen murna. Bayan sati biyu da tarewar su sabon gidan Deen ya bar ƙasar don amsa gayyatar da wasu manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan turai suka yi mashi....A sanyaye Salma ta ajiye wayarta bayan ta gama kallon hoton Deen a ƙasar France da ya je, tun ranar da suka yi magana da shi har ya bayyana mata yana son ta basu ƙara yin magana ba, bayan da suka dawo daga gasar world cup da shugaban ƙasa ya karrama su ta tura masa saƙon taya murna, sai dai bai mata reply ba kuma ta ga ya duba saƙon, haka da aka bashi sarauta ma ta tura masa saƙon taya murna shi bata ma ga ya duba ba, duk da ta san yana cikin uzururruka, amman bata yi tunanin za su kai har yanzu ba tare da sun ƙara yin magana ba, gashi ya zo ya yi har kusan sati biyu ba tare da ya neme ta ba har ya koma, zuciyarta ce ta raya mata to ko dai ya fasa son nata ne? A tunaninta in dai kana son mutum ko yaya ne ai zaka samu lokacin shi, wannan tunani ba ƙaramin saka jikinta yin sanyi ya yi ba, gashi yanzu wani irin son shi take ji a zuciyarta, sai yanzu ta gane tun da ma ta kamu da son shi sai da shi ya bayyana mata hakan ta gane, ƙwalla ne suka taru a idanunta, a ranta take raya yanzu ita ya zata yi idan da gaske ya daina son nata, sharr hawayen suka zubo mata ta kai hannu tana gogewa, ƙarshe ta kwanta a saman gadon tare da rufe idanunta tana jin wani irin sabon son Deen na ratsa zuciyarta. Washe gari suna yin breakfast, aunty na lura da yadda duk Salma ta yi sukuku, ta ƙi sakin jiki ta ci abinci sosai, "Baby..." A hankali Salma ta ɗago idanunta ta kalli aunty jin ta kira sunanta, "Ya aka yi ne na gan ki duk wani iri, wani abu na damun ki ne?" Da sauri Salma ta ɗan girgiza mata kai a hankali ta ce a'a ba komai, shiru aunty ta ɗan yi tana kallonta kafin ta ce, "Baby yaushe kika fara 6oye mani damuwar ki? idan baki fada mani damuwar ki ba wa zaki faɗa mawa ehm?" Salma ta sauke idanunta tare da yin shiru, hakan ya sa aunty gane akwai abun da yake damunta, cikin kwantar da kurya ta ce, "Tell me baby minene?" Ɗago ido ta yi ta kalli aunty a sanyaye ta ce, "Ba wani abu bane aunty...dama yaya Deen ne na ga har ya tafi..." Shiru ta yi a ranta tana ganin miye amfanin faɗin hakan ma, "Can ƙasar da yake ya koma?" aunty ta tambaya, Salma ta ce, "Ban sani ba, na dai ga ya je France." shiru aunty ta yi tana kallon Salma da ta sauke idanunta, ta fahimci ta kamu da son Deen sosai, sai dai bata ga laifinta ba don bata tunanin akwai macen da zata ce bata son Deen balle kuma a ce shine ya furta mata so, ko rannan sai da ta tambayi Salma ko sun yi magana da shi ganin ya zo ƙasar Salma ta ce mata basu yi ba, "Har yanzu baku ƙara magana da shi ba?" aunty ta tambaya, ɗaga mata kai ta yi ba tare da ta ɗago ba, "Ke baki yi mashi magana bane?" Salma ta ɗan ɗago ta ce mata ta tura masa saƙo har sau biyu amman bai reply ba har yanzu, ɗan shiru aunty ta yi kamar mai nazarin abu, can ta ce, "Ina tunanin uzururrukan gasar da suka yi ne suka yi mashi yawa, na san ƙilan ya bari ne sai ya natsu sosai zai waiwaye ki, ki daina damuwa kin ji." Salma ta ɗan yi murmushi mai kaman na yaƙe ta yi saurin cewa, "Aunty nifa ba damuwa na yi ba..." aunty ta yi ɗan murmushi kawai ta ce mata ta ci abinci..... 09013804524, 08169856268 for more info. *✨A CIKIN RAYUWA ZAINAB BATURE 54 Bayan sati biyu Deen ya dawo Nigeria tare da daddy Maleek da iyalan shi, a gidan Maleek da ke nan Abuja su Sapna suka sauka. Bayan kwana biyu da dawowar Deen aka yi bikin naɗin shi a garin Daura, dama saboda naɗin ya dawo, sosai al'umma suka halarci bikin naɗin har da dad dinsa da daddy Maleek, ƙaninsa Omar ma da yana a ƙasar ya je, daga can Funtua ma daddy Sa'ad da su Khaleel da sauran ƴan'uwa da abokan arziƙi duk sun halarta, sosai hotuna da videon naɗin suka karaɗe kafofin sada zumunta, Deen ya yi wani irin kyau na musamman a cikin shigar sarauta mutane ana ta santin kyaun da ya yi, yayin da mata ke ta bayyana burin son mallakar sa matsayin miji. Bayan kwana biyu da yin naɗin aka shirya gagarumar dinner a Abuja, duk ƴan familyn su na Kano da Funtua sun zo, har Fahad ma ya zo saboda dinner ɗin, Leemarh ta yi farin cikin zuwan shi sosai, katafaren ballroom ne za a yi dinner ɗin a ciki, an yi ma wurin tsadaddan decoration mai aji, da tsarin zama na table a tsakiya da kujeru zagaye, tsarin da aka yi a wurin na da matuƙar ɗaukar hankali...ko ta ina a wurin ƴan madara zaka gani, da manyan mutane da naira ta zauna masu, dad ɗin Deen da daddy Sa'ad da Maleek tare da abokan su manyan mutane da masu muƙaman gwamnati 6angaren su daban, haka mom da nata jama'ar suma wurin su daban, har Ammin su mom da su Bash duk suna a wurin, haka hajiyar ambasada da wasu dangi ƴan Funtua suma suna a wuri guda, wasu cikin abokan Deen yan team ɗin shi turawa sun zo da kuma yan team din Nigeria da suka buga world cup duk suna a wurin, Leemarh da Omar ma duk sun yi inviting abokansu, wuri dai ya cika da mutane ƴan gayu da jikin su ya jiƙu da naira, matan wurin ankon tsadaddan lace suka yi, kalan na iyaye daban haka ƴan mata ma nasu kalan daban, suma mazan sun yi ankon tsadaddan yadi, Naila tare da ƙanwarta Aseey wasu irin matsiyatan fitted gown aka yi masu, gaba ɗaya an ci mutuncin tsadaddan leshin, duk in da suka yi sai sun ja hankalin mutane saboda surar su da shigan da suka yi, Basma da Leemarh ɗinki iri ɗaya aka yi masu straight skirt da riga da suka fitar masu da shape ɗin su, Sadeeya da su Zarah da Nabeela yaran aunty Murja ƙanwar dad su ɗinkin su da mutunci don dogayen riguna aka yi masu. Lokacin da Zakin Wasannin Ƙasar Hausa ya bayyana a wurin gaba ɗaya idanu suka koma kan shi aka shiga bin shi da kallo cike da burgewa, gaba ɗaya shigar fararen kaya da farin rawani ya yi, a sama ya ɗaura wata rantsattsiyar golden akyabba da ta gama haduwa tana ta ƙyalli, a hannun shi ya riƙe sanda irin na sarauta wadda daga samanta aka yi design ɗin kan zaki, idan ka ga sandar zaka yi tunanin ta gold ce saboda yadda take ɗaukar ido, watakila ma ta gold din ce dai, gaba ɗaya yan matan wurin sun kasa janye idanunsu daga kan Deen saboda yadda ya tafi da imaninsu, Basma jikinta har wani tsuma yake tsabar yadda ya tafi da ita, ta rinƙa jin ina ma a lokacin su ma'aurata ne...a wurin da aka tanadar ma Deen ya zauna gefe da gefen shi bodyguad ɗin sa biyu suka tsaya, wasu irin narka narkan mutane da su masu suffar ban tsoro, daga sama har ƙasa duk sun yi shigar baƙaƙe ko fuskar su ba a gani...gaba ɗaya cikin wurin ya karaɗe da sautin daddaɗar waƙar da aka yi ma Deen mai amshin sarautar shi ta Zakin Wasannin Ƙasar Hausa, sosai waƙar ta yi ma mutane daɗi ba kamar amshinta wasu har ɗan bi suke, a wuri ɗaya Nailah ta zauna tare da Basma, haka duk inda zata yi a cikin wurin tana tare da ita riƙe da hannunta, Leemarh ta so su zauna tare da Fahad sai dai yana tare da wasu abokansu ƴan Funtua sun zauna a wuri ɗaya, Nabeela ɗiyar aunty Murja hankalinta na akan Khaleel ƙanin Fahad da ke zaune tare da su Omar, lokaci lokaci suke kallon juna suna sakar ma juna murmushi don soyayya suke ba tare da an sani ba, shima Omar ƙanin Deen hankalinsa na kan Zarah, jefi jefi suke haɗa ido su yi ma juna murmushi, su ma ku san soyayya suke yi duk da bata yi nisa ba, ba a daɗe ba da ya fara nuna mata so, sai dai ita Zarah gani take kamar ya yi mata ƙarami saboda su ɗin ku san age mate ne, duk da dai tana jin son shi...a kowane table an ajiye menu wato katin da ke ɗauke da jerin sunayen abinciccikan da ke akwai a wurin, sai abun da mutum ke so za a kawo masa, shi kan sa katin na naɗin sarautar ne har da hoton Deen a jiki, ma'aikatan abinci nata kai kawon kai ma mutane, manyan mawaƙan arewa har da na kudu ne ke perfoming a wurin, komai na dinner ɗin cikin aji ake gudanar da shi...bayan gama yin bayanan taya murna da Allah sanya alkhairi daga bakunan wasu makusantan Deen aka shiga yin hotuna. A kafafen sada zumunta dinner ɗin ce ke ta trending mutane nata tofa albarkacin bakin su wanda duk yabo ne...jikin Salma duk ya yi sanyi laƙwas yayin da take zaune a saman gado tana kallon hotuna da videos na dinner ɗin, ita kanta yanzu shakku take kan anya aure zai yuwu tsakaninta da Deen ganin irin mutanen da ke kewaye da shi, duk da ta san dama su ɗin masu arziƙi ne, amman a yanzu sai take ganin shi ɗin ya fi ƙarfinta nesa ba kusa ba, amman kuma da ta tuna shi da bakinsa ne ya furta yana son ta sai ta ɗan ji ƙwarin gwiwa....a cikin hotunan dinner ɗin kawai sai ga hoton Deen da Basma an saki tare da bayyana dangantakar su da kuma kasancewar ta fiencee din shi, ai fa nan social media ta ɗauka mutane suka shiga cece ku ce, wasu suna faɗin sam basu dace ba don ya fi ta kyau nesa ba kusa ba, yayin da wasu ke cewa ai itama ba mummuna bace tana da kyaunta ga kalar fatarta mai tsada kuma daga ganinta arziƙi ya zauna mata, wasu suna faɗin ƙaton baki gare ta da ƙananun idanu, yayin da wasu ke nuna su shape ɗin bakin ma nata ya burge su, haka dai mutane ke ta faman musayar ra'ayi akan Deen da Basma....sosai gaban Salma ya shiga faɗuwa data ga hotunan Deen da Basma da kuma bayyana ta matsayin wadda zai aura da aka yi, gashi kana ganin hotunan ba zaka ƙarya ta hakan ba don hada waɗanda ta kama shi, sosai hankalin Salma ya tashi taita kallon hotunan hannunta har ɗan rawa yake, a zuciyarta take raya ke nan ita ba son ta ya ke ba da gaske, ƙilan haka nan ya faɗa mata hakan don ta ce ba wanda ya yi mata da zata aura a cikin masu son ta, to amman mi yasa zai ce mata hakan bayan yana da wadda zai aura, idanunta suka cicciko da ƙwalla yin wannan tunanin, ta raya ita ya zata yi yanzu don wani irin son shi ke addabar zuciyarta, ƙwallan ne suka fara zubo mata sharr, a hankali ta kai kwance ƙwallan na ci gaba da gangaro mata a fuska tana ɗan kai hannu tana sharewa, bayan wani lokaci ta miƙe tana ƙara goge idanunta, wayarta ta ɗauka ta sauka daga saman gadon tana tafiya jikinta kamar babu laka, aunty Kubra na zaune a saman gado ta jingina da kan gadon, jikinta sanye da kayan bacci hannunta tana riƙe da wayarta, ta ɗaga kai jin an buɗe kofar ɗakin, Salma ce ta shigo suka haɗa ido a hankali ta sauke kanta ta nufo cikin ɗakin, daga bakin gadon ta tsaya aunty nata kallonta ganin damuwa bayyane a kan fuskarta, a hankali ta ce, "Baby ya aka yi?" A sanyaye ba tare data kalle ta ba ta ce, "Dama zuwa na yi in nuna maki..." Ta faɗa tana miƙa ma aunty wayarta hannunta har ɗan rawa take, bayan aunty ta amsa wayar ta bi hoton Deen da Basma da kallo, ita kanta yanzu nan take ganin hoton, itama hankalinta ya tashi da ganin haka abun kuma ya ɗaure mata kai, ɗago idonta ta yi tana kallon Salma da har lokacin kanta na a ƙasa, hannunta aunty ta kama ta zaunar da ita a bakin gadon, cikin kwantar da murya ta ce, "Nima yanzun nan nike ganin hotunan nasu, na yi mamakin hakan....amman ke bai yi maki maganar wannan ɗin ba?" Salma ta girgiza mata kai ta ce yadda ta faɗa mata haka suka yi da shi, aunty ta yi shiru tana kallon wuri guda, bayan ɗan lokaci ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Ina ganin kada mu yi saurin yanke masa hukunci, da ba son kin yake da gaske ba haka nan ba zai furta maki hakan ba. Abu biyu nike tunani a raina, ko dai dama akwai maganar wannan ɗin, ko kuma daga baya maganar shi da ita ta taso tun da naga familyn su ɗaya, yanzu abun da ya fi mu jira mu ji daga gare shi, na san uzururruka ne suka sa bai neme ki ba." Ta ƙarasa tana kallon Salma da ta yi shiru idanunta ƙasa, aunty Kubra ta bi ta da ido ganin yadda duk ta shiga damuwa, hannu ta kai ta dafa shoulder ɗinta cikin kwantar da murya ta ce, "Don't worry my baby, ba abun da zai faru sai alkhairi, kaman yadda na faɗa maki a baya cewa idan shi rabon ki ne kina zaune zai furta maki so sai gashi kuma hakan ya faru, to haka ma idan Allah Ya ƙaddaro shi ne mijin ki, babu wani abu da zai zama shamaki ga faruwan hakan, mu ci gaba da addu'a Allah ya tabbatar mana da alkhairi." Salma ta ɗaga mata kai a hankali, shiru suka ɗan yi, aunty duk bata jin daɗin hakan dake faruwa a cikin ranta musamman ganin damuwar da babyn nata ke ciki, miƙewa Salma ta yi tare da ɗan kallon aunty ta ce mata sai da safe, aunty dake kallonta cike da kulawa ta ce ko ta kwanta a nan, Salma ta ce lafiya lau zata koma ɗakinta, sai da aunty ta rakata har ɗaki ta ƙara kwantar mata da hankali, bayan ta saka ta ta kwanta ta dawo ɗakinta duk itama ta shiga damuwa, a wannan daren bacci kusan ƙaurace ma Salma ya yi saboda damuwa da kuma zullumi da suka cika ta. Washe gari bayan sun yi breakfast aunty ta tafi aiki, haka Salma ta yi ayyukan gidan duk ta yi wani sukuku da ita. Wuraren la'asar aunty ta dawo, Salma ta tarbe ta tare da yi mata sannu da zuwa, a nan falo suka zauna aunty tana kallon ta da murmushi ta ce, "Sannu da gida baby." Salma ta amsa da ɗan murmushi, "Yau kin ga ban dawo da wuri ba ko, baƙi muka yi a asibitin namu, mai kama da ke tare da tawagar ta suka kawo mana ziyara shiyasa ban baro asibitin da wuri ba." Salma ta ɗan yi murmushi don ta gane matar gwamnan garin take nufi wato hajiya Aisha, ita ce ta ta6a bata kyautar kuɗi lokacin da ta gama primary a nan Kaduna, lokacin mijinta yana riƙe da muƙamin kwamishinan ilimi, yanzu kuma shine governor ɗin garin, ƙoƙarin miƙewa Salma ta fara tana faɗin bari ta kawo mata abinci, aunty ta ce, "Anya bar abincin nan, yanzu bana jin wani yunwa sosai sai dai ko anjima." Salma ta koma ta zauna tare da sauke kanta, kana ganin ta ka san tunani take dama daga jiya zuwa yau aikin da take ke nan, aunty ta bi ta da kallo, a hankali ta kira sunanta, Salma ta amsa tare da ɗagowa, "Har yanzu baki daina damuwan ba ko, ba na ce ki kwantar da hankalin ki ba." Salma ta ƙaƙalo ɗan murmushi a sanyaye ta ce, "Ba tunani nike ba aunty." Aunty ta yi shiru tana kallonta, tausayinta take ji a rai don ta fahimci son Deen ya yi mata mugun kamu, can ta miƙe tana faɗin bari ta je ta watsa ruwa, Salma ta ɗauki jakarta suka nufi ɗakinta, bayan ta kai mata jakan ta fito ta nufi ɗakinta, zama ta yi a saman gado ta yi shiru tana kallon wuri ɗaya, tun jiya ta kasa hawa social media saboda tana fargabar ta ga Deen da Basma, tana ta zaune can ta miƙe walking slowly ta nufi toilet, bata daɗe ba ta fito ta ji wayarta na ta ringing, gado ta nufo inda wayan take ajiye, sai dai kafin ta ƙaraso kiran ya yanke, zama ta yi ta kai hannu ta ɗauko wayar, kusan ƙamewa ta yi bayan da ta duba ta ga wanda ya kira ta, da gaske Deen ne ya kira ta ko kowa dai kiran nashi ne ke mata gizo, bata gama tantacewa ba sai ga wani kiran ya shigo, gabanta ne ya hau bugu ta bi kiran da kallo kaman ba zata ɗaga ba saboda zullumin da ya kama ta na abun da zai faɗa mata idan ta ɗaga, sai da kiran ya kusa katsewa ta kai hannu a ɗarare kaman mai jin tsoro ta ɗaga tare da kai wayar kunne, ta yi shiru ƙirjinta na bugawa da ƙarfi, saukar muryarsa ta ji ya yi mata sallama, ɗan runtse ido ta yi jin sautin daddaɗar muryar tasa a cikin kunnen ta, a hankali ta amsa sallaman ta ce, "Ya Deen ina yini." Bai amsa ba ta ji ya ce, "Salmerh." murya ƙasa ta amsa, ya ce mata, "How are you?" Ta amsa da lafiya lau, ɗan shiru ya yi sai kuma ta ji ya ce, "Is everything alright?" Ɗan yamutsa fuska ta yi lokaci guda ƙwalla suka fara taho mata, da ƙyar ta ce mashi eh, da alama ya fahimci wani abu daga muryarta ya ce, "Wani abu na damun ki ne?" Ta girgiza kai kamar yana ganinta sai kuma ta ce, "A'a, ba abun da ke damuna..." Ya furta ok, sai kuma ya ce, "I'm sorry bamu yi magana ba kaman yanda na ce, I have been so busy, na bari ne in samu natsuwa sosai." Ta ɗan jinjina kai har lokacin cike take da fargaba, a hankali ta ce mashi ba komai, ya ce, "Are you still in Kd?" Ta ce mashi eh, ta ji ya ce,"Ok, send me your address, zan zo in gan ki in two days" Ƙirjinta ya yi wani bugu da ƙarfi jin abun da bata yi zaton zata ji daga gare shi ba, da alamun mamaki ta ce, "Nan zaka zo?" Ya ce, "Yea, idan kina available." Ta yi shiru duk mamaki ya kama ta, "Ko baki so in zo ne?" Ta ji ya faɗa, da sauri ta ɗan girgiza kai ta ce, "A'a ya Deen...ina so." Calmly Ya ce, "Sai na zo. I love you." daga haka ya yanke kiran, Salma ta yi saurin rintse idanunta jin yadda kalmar I love you ɗin ta ratsa dukkan sassan jikinta, ciro wayar ta yi daga kunnenta, a hankali ta buɗe idanunta tana bin screen ɗin da kallo, ta rasa farin ciki zata yi ko kuwa, don still zullumin da take ji na nan, bata san idan ya zo mi zai ce mata ba, ko hakuri zai bata ya ce yana da wadda zai aura, wannan tunanin ya sa ta jin fargaba game da zuwan na shi, sai dai kuma ta wani bangaren tana jin farin cikin zuwan da zai yi, saukowa daga gadon ta yi ta nufi ƙofa don ta je ta faɗi ma aunty, lokacin da ta shiga cikin ɗakin, aunty na zaune a gaban dressing mirror ta gama sharce sumarta da ta kawo mata har ɗan wuce kafaɗa, ganin Salma ta dakata da ƙulle gashin tana kallon ta, Salma ta ƙaraso kusa da ita ta tsaya tana ɗan murmushi, aunty na ganin haka ta yi saurin cewa, "Ko ya kira ne?" Salma ta ɗan ɗaga mata kai, aunty ta washe baki dama tun da ta ga tana murmushi ta san bai wuce shine ya kira, "To ya ku ka yi da shi?" Ta tambaya tana kallon ta, Salma ta faɗi mata, aunty ta wani kalan zaro ido cike da mamaki ta ce, "Wai da gaske nan zai zo?" Salma ta ɗaga mata kai ta ce haka ya ce, aunty ta hau jinjina kai ta ce, "Lalle! Ki ce ban ga ta zama ba zamu yi babban baƙo haka, kika ce jibi ya ce zai zo?" Salma ta ɗaga mata kai, aunty ta ɗan yi shiru tana ta kallon Salma da itama ke kallon ta, "Kaina ma duk ya ƙulle na rasa da me zamu fara... miƙo mani wayana gata can saman gado." Bayan Salma ta kawo mata wayar, ta shiga latsa ta tana faɗin yakamata a yi mata gyaran jiki yau da gobe, kira ta yi ta kai wayar kunne, bayan an ɗauka tana murmushi ta ce, "Wa'alaikumus salam...sis Naja'atu ya gida ya su noor. Dama wai baby ce nike son zan kawo a yi mata gyaran jiki yau da gobe, ban san ko za a samu ba." ɗan saurarawa ta yi kafin ta ce ok lafiya lau suna hanya, bayan ta cire wayan ta kalli Salma ta ce, "Ai ba abun da kike yi yanzu ko?" Salma ta ce mata eh, aunty ta ce to ta shirya za su fita yanzu, Salma ta amsa har zata juya sai kuma ta dakata ta ce, "Aunty baki ci abincin ba, ko in zubo maki ki ci kafin mu tafi?" Aunty dake faffaɗan murmushi don ta ji daɗin kiran da Deen ya yi saboda Salma ta ce, "Ai bar abincin nan kawai baby, je ki dai ki shirya." Salma ta amsa da to tare da nufar kofa, itama aunty miƙewa ta yi don ta shirya. Bayan sun hau hanya aunty na a driver seat, Salma na zaune a front seat jikinta sanye da abaya, "Amman baby kaman mi kike ganin zamu yi na tarbar sa?Ina nufin abinci, ko kin san abinciccikan da ya ke so?" Salma ta kalli aunty da ta yi tambayar idanunta akan hanya, shiru ta dan yi tana kokarin tuna ko akwai abincin da ta san yana so, maganar da hajiya ta taba yi ta ce in dai ana cin abu ya yi masa dadi to zai ci, Salma ta ce, "Komai yana ci in dai ya yi masa dadi, haka na ji kakarsa hajiya ta ta6a faɗa...amman yana son awara sosai har da ma fara." Aunty ta ɗan yamutsa fuska ta ce, "Wani irin fara kuma, shi ɗin ne yake cin fara?" Salma ta yi yar dariya ganin yadda aunty ta yi ta ce mata eh tare da bata labarin awara da fara da ta rinƙa kai masa lokacin a Funtua, ɗan kyabe baki aunty ta yi tana driving ta ce, "Amman dai ta ya za a tarbe shi da wani fara, har gara ma awaran....bari idan na ajiye ki gidan sis Naja'atun zan wuce kasuwa kawai in siyo abubuwan da za yi amfani na abinci, daga nan sai in haɗo da waken suyan." Salma ta ɗaga kai ta ce ita zata yi awaran, aunty ta ce, "Yadda idan ya zo zai ji kina ta ƙaurin murhu ko." Salma ta yi dariya ta ce ai ba ranan da zai zo za a yi ba sai a yi gobe a ajiye a fridge, "To ke nan ma gyaran jikin banza za a yi maki tun da zaki ƙare a bakin murhu," Salma na murmushi ta ce ai tun da ba wani mai yawa za a yi ba lafiya lau zata iya yi a gas, aunty ta ce mata ba wani aikin awaran da zata yi ta bari akwai matar da ke yi a nan unguwarsu lafiya lau tana da tsafta sai a bata ta yi. Bayan sun iso gidan sis Naja'atun, aunty ta ce ma Salma ta shiga ta faɗa mata ta wuce kasuwa sai ta dawo...wajen Magrib aunty ta koma gidan sis Naja'atu, bayan ta shiga a falo ta iske yarinyar sis a zaune tana kallo ta ce, "Aunty Kubra ina yini." aunty da ke murmushi ta ce, "Lafiya lou Noor my daughter, how's school?" Ta amsa mata da, "Fine." "Ina mom ɗin ki?" aunty ta tambaya bayan ta zauna a kusa da ita, saukowa ta yi daga kujeran ta ce bari ta je ta kira ta, tare suka dawo da sis Naja'atu ta nufo aunty tana faffaɗan murmushi, bayan ta zauna kusa da aunty ta ce, "Ƙawata an dawo." aunty ta amsa mata, "Baby dazun ta ce kin wuce kasuwa, ina tsaraba na?" aunty na dariya ta ce mata tana boot idan sun fita zata bata, kafin ta ce,"Babyn fa?" sis Naja'atu ta bata amsa da tana ɗaki ta je yin salla, "Har an gama gyaran jikin?" aunty ta tambaya, ta bata amsa da eh basu daɗe da gamawa ba, "Mu je ciki ke ma ki yi sallan ko." Sis ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa, aunty na murmushi ta ce mata tata ta riga ta kai, sis Naja'atu ta koma ta zauna jin abun da ta ce, hira suka shiga yi irin ta manyan abokai, bayan ɗan lokaci Salma ta shigo cikin falon ta zo kusa da aunty tana murmushi, aunty dake kallon ta ta kama hannunta ta zaunar da ita a kusa da ita tana murmushi ta ce, "Ma sha Allah, gyaran jiki ya yi kyau, ji yadda face din ta ke wani glowing." Sis da itama take kallon Salma ta ce, "Ai skin dinta yana da kyau yana ɗaukar gyara sosai." aunty ta ɗaga kai, "Sai ma an yi na gobe za ki ga yadda skin ɗin nata zai ƙara sheƙi sosai, ban da kai za a gyara mata ne?" aunty ta ce oh ta manta har da shi fa, sis ta ce ai kawai wanke shi za ai ai setting ko don ta san ba a ƙona gashinta, aunty ta ce eh, "Ko za a turara mata shi?" sis ta tambaya, aunty ta yi wani murmushi ta ce, "Wannan sai Allah ya kaimu gyaran aure." Sis ta tambayi to shi wannan gyaran na miye ko haka nan, idon aunty akan Salma ta ce, "Na tarbar surukin mu ne." Sis ta ɗan wara ido sai kuma ta yi dariya ta ce, "Ma sha Allah, ki ce mu fara shiri mun kusa shan biki." aunty ta jinjina kai ta ce shiri sosai kuwa don biki mai sunan biki za su sha, "Ɗaga ina surukin namu zai zo ne?" Aunty ta bata amsa da Abuja, jinjina kai sis ta yi cike da zolaya ta ce Allah Ya sa babban kifi ne ta kamo masu, aunty ta saka dariya ta ce ƙundumeme ma kuwa, Salma ta 6oye fuska a jikin aunty, sis na dariya ta ce, "Su Kubra girma ya zo, da an yi auren nan da ɗan lokaci zaki gan ki da jika." Aunty da itama ke dariya ta ce, "Bari ƙawata, ai rayuwan nan na gudu ba kaɗan ba, wai baby ce har ta isa aure." Sis Naja'atu ta ce, "Ai abun sai dai addu'a kawai Allah Ya sa mu dace. Allah Ya sa ana yin auren 9 months mu samu jikoki twins kin ga sai a baki raino." aunty ta juya tana kallon Salma da ta rufe fuska a jikinta ta ce, "Baby zaki bani?" Miƙewa Salma ta yi zata ruga ɗaki, aunty ta ɗaga murya tana ce mata ina zata je tafiya za su yi, hakan ya sa Salma nufar ƙofar fita suka bita da kallo suna dariya. Bayan sun koma gida, tun a daren aunty ta fara yin wasu ayyukan abincin tarbar Deen, washe gari cikin sa'a off take, bayan sun gama yin breakfast ta ɗauki Salma ta kaita gidan sis Naja'atu don a ƙarasa yi mata gyaran jikin, har da lalle za a yi mata dama akwai mai yi nan kusa da gidan sis ɗin idan aka zo gyaran jiki wurin sis ana son lalle ita take kira ta yi. Bayan aunty ta kai Salma kai tsaye cikin gari ta wuce don akwai abubuwan da take son siyo ma Salma, daga can gida ta dawo ta ci gaba da yin ayyuka, sai yamma taje ta ɗauko Salma, idan ka ganta sai ka ce wata amarya, fuskarta sai wani sheƙi take ga wani ƙamshi mai daɗi da jikinta ke saki, a hannuwanta an yi mata jan zanen lalle mai kyau ba mai hayaniya ba, sumarta an gyara mata daga gaban kanta ta kwanta luff luff. Da daddare aunty sai da ta kammala duk wani abu da zata iya yi na abinci kafin gobe. Washe gari tun ana gama sallan asuba aunty ta fito ta fara gyaran falo, har labulaye ta canza ta saka wasu tsadaddu masu kyau, da yake dama ita irin matan nan marasa son jiki, duk da tana da ɗan jiki amman hakan bai hanata kazar kazar, bayan ta share falon ta goge komai na falon su windows, kayan kallo, frames, har da kujeru ta goggoge, sannan kuma ta yi mopping tiles, lokacin da Salma ta fito sosai ta yi mamakin ganin yadda falon ya sha uban gyara ya yi kyau ko ina nata ƙyalli, bayan ta yi ma aunty sannu ta ce ai da ta kira ta ta taya ta, koda ta ce zata haɗa masu breakfast farko hana ta aunty ta yi, sai da ta takura sannan ta barta ta ce amman kada ta yi amfani da ruwa sosai don kada lallen ta ya zube.... Bayan sun gama yin breakfast a nan falo suka zauna, aunty ta ce ma Salma sun yi magana da Deen ne ya faɗi mata lokacin da zai zo ta ce mata a'a tun da suka yi waya ya ce zai zo basu sake yin magana ba, aunty ta ce ai yakamata ta kira shi da nufin yi mashi ya hanya, Salma ta ce to tare da ɗaukar wayarta ta kira Deen gabanta har ɗan faɗuwa yake, har kiran ya yanke bai ɗaga ba, aunty ta ce ƙilan yana hanya duk da ta san idan ma a mota zai zo ba lalle shine zai driving ba, after few seconds sai gashi ya kira, a nutse Salma ta ɗauka ta gaishe shi, ta ce dama ta kira ne don ta yi masa ya hanya, bayan ya yi mata magana ta furta ok daga haka suka gama wayan, aunty da ke kallon ta ta ce, "Wai baby haka kike yin waya da shi sai ka ce har yanzu ba wani abu a tsakanin ku?" Salma da ke kallon aunty ta yi murmushi kawai, "Kina waya da shi kamar mai jin tsoro, ba zaki saki jiki ki yi mashi magana yadda ake ma masoyi ba." Salma ta yi dariya tare da sunne kai, aunty ta ci gaba, "Ba wai ina nufin ki zaƙe ba, amman yakamata yadda kike waya da shi da ya bambanta da yanzu." Tambayarta ta yi ya suka yi, Salma ta sanar mata ya ce ta yi expecting nashi after asr, aunty ta ce yauwa zuwa lokacin an gama komai, nan ta shiga koya ma Salma yadda zata rinƙa magana da shi, daga baya ta ɗauki wayarta ta kira wani Isyaku wanda wani matashin saurayi ne a nan unguwar, shi take aike ko ta saka shi ya yi mata wani aiki, magana suka yi ta ce idan yana nan ya zo tana son ganin shi, ba a jima ba sai gashi don bai wasa da kiran aunty Kubra saboda yana samun alkhairi daga wurinta, aunty ta ce mashi compound ɗin gidan take son ya share mata ya ce to, ita kuma ta wuce kitchen don ta ƙarasa harhaɗa abincin tarbar Deen. Lokacin zuwan Deen na matsowa yayin da zullumi ke ƙara cika Salma, duk yadda take jin farin cikin zuwan nashi da ta tuna da batun Basma sai jikinta ya yi sanyi...wajen ƙarfe ukku aunty ta gama komai har falon ta ƙara gyarawa ƙamshin turaren wuta mai daɗi ya karaɗe ko ina na gidan. Ana gama sallan la'asar aunty ta shigo cikin ɗakin Salma tana riƙe da wani ƙaton jaka mai tambari a jiki, Salma da ke zaune ta gama yin salla ta juya tana kallon aunty, "Baby kin gama sallan?" Ta ɗaga mata kai alamar eh, "To taso." Ta faɗa tana nufar dressing mirror, sawa ta yi Salma ta cire hijab ɗin jikinta ta ce ta zauna a saman stool ɗin gaban mirror, makeup aunty ta shiga yi mata ta ƙara gyara mata gashi, ba ƙaramin kyau Salma ta yi ba duk da ba wata kwalliya mai yawa aunty ta yi mata ba ɗan light makeup ne amman sosai ta yi kyau, jakan da ta shigo da ita ta buɗe ta fiddo wasu kaya da aka yi packaging nasu, buɗe ledan da suke ciki ta yi ta fiddo kayan nan da nan ƙamshin da kayan ke yi ya baza wurin , Salma tai ta kallon tamfatsetsiyan applique atamfan da aka rubuta farashin kayan a jikin ledan har naira 250k, sosai jikinta ya yi sanyi, ita dai bata san wani irin so aunty Kubra ke yi mata ba, warware kayan aunty ta yi wanda doguwar riga ce, ba wani kwalliya daban aka saka ma ɗinkin ba, da kwalliyan atamfan aka yi amfani amman fa ɗinkin ya tsaru ba ƙarya, dama Kaduna kankat ne wurin iya tsara ɗinki, aunty ta miƙa ma Salma rigan da ta yi zuru don farashin kayan ya girgiza ta ta ce ta saka, bayan ta gama sakawa sosai rigan ta amshi jikinta kuma ta yi mata daidai, aunty ta yi mata ɗaurin kallabi mai kyau, sarka da yan kunnenta na zinari ta saka ma Salma don ita iya ƴan kunne da zoben zinari kawai gare ta, wata hadaddiyar agogo ta ɗaura mata ta sa Salma ta ɗauko zobunanta guda biyu na zinari ta saka, aunty ta riƙe ƙugu tana kallon Salma ta ce, "Wow...Ka ga zakanyan zakin wasannin ƙasan hausa...." Salma ta saka dariya jin maganan aunty, "Ma sha Allah, baby kin gan ki kuwa, ni na san ta ko ina na gama yin dacen ɗiya wllh...." Salma ta kasa magana sai dariya take tana kallon kanta a cikin madubi, ita kanta ta ga kyaun da ta yi sosai, "Wannan kyau sai ka ce dai yau ne auren, ko da yake na san shigar yau nafila ce a kan ta ranar....amman kada fa yana ganin ki ya buƙaci a ɗaura auren yau ko gobe, sai dai baban Sageer ya ji an doka masa kira cewa ana son a ɗaura auren ki." Dariya sosai Salma ta saka, lokaci guda kuma zullumin da take ya zo mata a rai, a sanyaye ta kalli aunty ta ce, "Aunty ni sai in ta jin kaman idan ya zo zai ce....kaman zai yi mani maganar wanccan ne." Aunty da ta fahimci abun da take nufi ta ce, "Wai kina ganin zai ce ya fasa son ki, ai baby ba wani lafiyayyen namiji da zai iya rejecting naki, koda ma a ce ya zo da wannan niyyan ina tabbatar maki zai fasa ne, balle ma na san bada hakan zai zo ba, wataƙila dai ya yi maki bayanin wanccan ɗin ba wai ya ce ya fasa son ki ko auren ki ba, in sha Allah alkhairi zamu ji." Salma ta sauke idonta ba tare da ta ce komai ba, gyale da takalma duk sababbi aunty ta fiddo mata, tana ɗan ƙara gyaggyara ta suka ji wayar Salma ta fara ringing, aunty ta ce ta je ta duba ƙilan shine, gado Salma ta nufa sai ka ce wata amarya ta ɗauki wayan ta ga shi ɗin ne, aunty da ke kallonta ta tambayi shine ta ɗaga mata kai ta ce ta ɗauka, bayan ta yi picking kiran ta kai kunne tare da yin sallama, ɗan saurarawa ta yi kafin ta furta ok daga haka ta cire wayar, kallon aunty ta yi ta ce, "Wai ya ce ya zo address da aka tura mashi." Da sauri aunty ta kai hannu ta ɗauki wayarta tana faɗin bari ta kira Isyaku, dama ɗazun bayan ya gama yin shara ta sanar da shi cewa za ta yi baƙo ya kasance available watakil zai yo masa jagora zuwa gidan, bayan Isyakun ya ɗaga ta sanar da shi cewa baƙon nata ya iso, ya tambayi a mota suke aunty ta ce eh, kalan motan ya tambaya ta ce ba ta sani ba bari ta tambaya, sai kuma da sauri ta ji ya ce, "Aunty ga wata mota nan na ga ta shigo layin nan yanzu." Tambayar shi ta yi wace irin mota ce, ya ce, "Wllh aunty ban sani ba, haɗaɗdar farar mota ce ni dai bamma taba ganin kalan ta ba balle in san wace iri ce." Ya na maganar idon shi akan motan dake ta ɗaukar ido gashi ba zaka ce ga wanda yake ciki ba don glass din ta tinted ne kuma hatta lambar motar an rufe, aunty na jin haka ta yi tunanin Deen ɗin ne, aunty ta ce mashi motan ta tsaya ne ko tafiya take, Isyaku ya ce mata tafiya take amman a hankali da alama baƙon ne yake neman gidan bari ya je ya gani idan shine, nufar motar ya yi da yar sassarfa, daga wurin ƙofar gaba ya tsaya ya yi sallama duk da bai ganin wanda ke ciki, slowly glass ɗin front seat ya sauka, har saida gaban Isyaku ya faɗi lokacin da ya yi arba da mutumin da ke zaune a gaban, ganin shi wani jibgege mai ƙirar ƙarfi, ga shi gaba ɗaya jikinsa baƙaƙen kaya ne kansa ya saka baƙar hula face cap ya kuma rufe fuskarsa da baƙin takunkumi, a cikin rai Isyaku ya shiga kokonton anya kuwa baƙon auntyn ne, Isyaku bai san lokacin da ya ɗan rankwafa ba ya gaishe da mutumin ganin yana kallon shi, kai kawai mutumin ya ɗaga, cikin ɗan dabarbarcewa Isyaku ya ce, "Da...dama zan tambaya ne ko kai ne za a yi ma jagora zuwa gidan aunty Kubra?" Mutumin bai ce masa komai ba ya juya ya kalli baya kana gani magana ya yi da wani, juyowa ya yi ya jinjina ma Isyaku kai alamar eh, da sauri ya ce to ga gidan can ya yi gaba yana tafiya da sassarfa motan na bin shi a baya, yar tafiya kaɗan suka yi suka iso gidan, Isyaku ya kama gate ɗin gidan ya zuge tare da ja baya motan ta kutsa cikin gidan, rufe gate ɗin ya yi ya ƙarasa gaban motan yana ce ma mutumin bari ya sanar da ita gashi ya zo, nan ma mutumin kai kawai ya ɗaga masa, Isyaku ya nufi cikin gidan da sauri a ransa yana tunanin ko wane baƙo ne wannan aunty ta yi, amman kuma ya gane ba mutumin bane kaɗai a motan, ban da shi da wanda yake tuƙa motan akwai wani a baya....bayan Isyaku ya sanar ma aunty ya dawo wurin su ya sanar da su ya faɗa mata, nan ma dai mutumin kai ya ɗaga masa, har ya nufi gate zai fita ya ji an ce masa, "Hey..." Hakan ya sa shi juyowa, wanda ke a mazaunin driver ne ya yi masa magana, shima dai irin suffa da shigar ɗayan na gaban ke gare shi, Isyaku ya ƙarasa wurin shi tare da ɗan rankwafawa kamar mai neman gafara, bayan motan ya ga mutumin ya juya kafin ya juyo ya miƙo masa abu a hannunsa, hannu na rawa Isyaku ya karba ya ga kudi ne masu ɗan yawa, godiya ya shiga yi ma mutumin yana ɗan zaka kai a kokarin sa na ya hango wanda ke a bayan amman bai iya hango kowa ba, ya nufi gate yana ta mamakin kuɗin da aka basa da kuma wanda ke a bayan, wanda idan da Isyaku ya ga Deen wataƙil har kusan suma sai ya yi don daɗi saboda big fan ɗinsa ne....aunty ta shigo cikin ɗakin Salma bayan Isyaku ya sanar da ita isowar baƙon, tana murmushi ta ce, "Zakanya to ga Zakin naki ya iso." Salma ta ji gabanta ya faɗi, dama tun da ta ji an buɗe gate kirjinta ya shiga bugu da ƙarfi, aunty ta ɗauki gyalenta da ke ajiye gefe ta miƙa mata, Salma ta amsa tare da miƙewa ta yafa gyalen, aunty ta ɗan ƙara gyaggyara ta kafin tana murmushi ta ce mata ta je kada ya yi ta jira, Salma ta ɗan marairaice ta ce to ta raka ta, dariya aunty ta yi ta ce ya za ai ta raka ta gun saurayi, tare suka fito falo aunty na kallon ta da murmushi ta ce mata ta je ta kuma kula, Salma ta nufi kofar fita daga falon gabanta na faɗuwa...... *✨A CIKIN RAYUWA✨* ZAINAB BATURE 55 A nutse Salma ta fito haraban gidan, lokaci guda bugun da ƙirjinta ke yi ya ƙaru, sosai ta tsorata da mutanen da ke a gefe da gefen motar, ganin irin suffar su da shigar da suka yi, sai dai kuma ta gane bodyguards ne don a hotunan Deen na dinner wasu akwai su a gefen shi, a ɗarare ta ƙarasa wurin motan, mutumin 6angaren da ta ke ya ɗan sunkuya mata kai alamar gaisuwa kafin ya kai hannu ya buɗe mata ƙofar back seat, sai da Salma ta haɗiyi wani yawu kafin ta fara ƙoƙarin shiga, bayan ta shiga aka rufe motar, tana shiga idanunta suka sauka akan Deen da ke hakimce ɗayan gefen ya ɗan kwantar da jikinsa yana latsa waya, yana sanye da ƙananun kaya da suka matuƙar amsar jikinsa, kansa ya faka sumarsa ƙasa, ga wani irin ƙamshi mai narkar da zuciya da yake saki, gaba ɗaya cikin motan ya karaɗe da ƙamshin haɗe da sanyin Ac masu tsuma zuciya, sauke idonta ta yi bugun zuciyarta ya ƙara tsananta sakamakon ganin Deen, a hankali ta ɗago daidai ya janye idonsa daga kan wayan da yake latsawa suka haɗa ido, motsa baki ta shiga yi kaman mai tattaro abun da zata faɗa, da kyar ta ce, "Ya Deen... sannu da zuwa, ina yini." Yay nod kansa fuskarsa a sake yana ta kallon ta don ba ƙaramin kyau ta yi masa ba, kasa jure ma kallon shi ta yi ta maida kanta kasa, sosai ta ga ya ƙara yin wani irin kyau fiye da wancan zuwan da ya yi, Basma ce ta faɗo mata a rai, sai daga baya ta gane ita ce wadda ta ta6a ganin hoton ta a wayarsa har ya ce mata cousin ɗinsa ce kuma a gidan su yake zaune, idan har da gaske ita fiancee ɗin sa ce ta san mawuyacin abu ne bai aure ta ba, to ita anya kuwa Deen zai aure ta, don koda shi yana son ta dangin shi za su iya ƙin amincewa da ita saboda Basma, gashi ganin shi da ta yi yanzu wani irin sabon son shi ta ji ya mamaye mata zuciya, "Salmerh." Ya kira sunanta a hankali, ta ɗago ido ta kalle shi tana ƙoƙarin danne damuwar da ke a ranta, a hankali ta amsa, ya yi shiru yana kallonta can ya ce, "What's wrong, ko baki farin cikin zuwa na ba?" Da sauri ta girgiza masa kai tana ɗan murmushi ta ce, "A'a...ya Deen na yi farin ciki." Shiru ya yi yana ta kallonta kaman mai nazarin abu, "Mi yake damun ki ne?" Da sauri ta girgiza masa kai tana sauke idonta, daga yanayin ta ya so ya fahimci abu na damunta, saboda a ɗan sabawar da ya yi da ita wanccan karon a Funtua ya fahimci tana da ɗan yawan fara'a, in dai kuna magana za tai ta murmushi, yanzu kuma da ya kamata ya ga hakan koma fin yadda take yi a baya sai bai gani ba, dama tun lokacin da ya kira ta ya ce zai zo ya fahimci kaman tana cikin damuwa, calmly ya ce "Why kike boye mani abun da yake damun ki?" Dan kallon shi ta yi tana kikkafta idanu ta ɗan girgiza masa kai, duk yadda take son danne damuwarta zuciyarta ta ƙi bata goyon baya, in dai ba jin tsakanin shi da Basma da kuma matsayinta a wurin shi ta yi ba hankalinta ba zai kwanta ba, sigh ya yi ya ce, "I think zan koma ne idan ba zaki faɗi mani mi yake damun ki ba." Da sauri ta kalle shi tare da ɗan girgiza mashi kai cikin marairaicewa ta ce, "A'a ya Deen pls kada ka tafi." Gyara zama ya yi ya ce, "Ok, tell me mi yake faruwa?" Motsa baki ta shiga yi ta rasa ta yadda zata yi mashi magana, da ƙyar gabanta na faɗuwa da yar in ina ta ce, "D...dama kana da wadda zaka aura?" Tana yin maganar ta yi saurin sauke idonta ƙasa, Deen ya yi ta kallonta, sam bai yi tunanin wannan ne abun da yake damun ta ba, jin ya yi shiru ta ɗan ɗago kai ta kalle shi suka hada ido, janye idon shi ya yi ya koma yana kallon gaban shi, ya ce, "She is my cousin, akwai maganan aure tsakanin mu." Salma tai ta kallon shi yayin da bugun zuciyarta ya ƙara tsananta, zuciyarta ta shiga azalzalarta kan son sanin matsayinta a wurin shi, "Ni... ke nan ba aure na zaka yi ba..." tana yin maganar ta sauke idonta don ita kanta bata san lokacin da ta furta hakan ba, a hankali ya juyo fuskarsa ya kalle ta kaman ba zai ce komai, can ta ji ya ce, "Zan aure ta, ke ma haka..." Salma ta ɗaga ido tana kallon shi yayin da shima idanunsa ke akanta, "But ban san ko zaki iya aure na da wani matan ba." Salma ta ɗan yi shiru tana sauke idonta, ganin yana ta kallon ta alamar kamar amsarta yake jira, cikin yar rawan murya ta ce, "Zan aure ka...amman ita ban san ko zata amince ka aure ni ba." Ɗan murmushin gefe ta ga ya yi ya ce ba ita ce zata yanke masa haka ba, Jingina ya yi da seat yana kallonta, sam bai yi mamakin jin tsakanin shi da Basma ne damuwar ta ba, don ba ita kaɗai ba mata masu son shi duk sai da suka nuna mashi damuwar su game da hakan, har da wanda sukai mashi kuka jin cewa Basma fiencee ɗin shi ce. Sosai Salma ta ji sanyi a ranta duk da tana jin sauran zullumi don bata san ko family din shi za su yarda ya aure ta ba, ɗan juyawa ta yi ta kalle shi suka haɗa ido ta ɗan yi mashi murmushi, slowly ya ce mata damuwan ya tafi ke nan, da sauri ta kife fuskarta a jikinta alamar kunya, bayan ta ɗago ta sake kallon shi, ya yi ɗan murmushi ta ji ya ce, "Ko da wani damuwan?" Ta yi saurin girgiza masa kai, shiru ya ɗan yi kafin ya ce to ta bashi labari ya yi maganar yana maida idonsa kan waya, ɗan shiru ta yi tana tunanin wani labarin zata bashi, ta ce, "Na tura maka saƙo har biyu tun lokacin da kuka dawo world cup amman baka duba ba." Shiru ya yi yana daddana wayarsa, ta ji ya ce gashi ya ga ya duba saƙon farko na biyun bai ma gan shi ba sai yanzu, ɗago kai ya yi suka haɗa ido ya yi ƙasa da murya ya ce, "A yi hakuri idan na yi laifi." ta ɗan buɗa ido sai kuma ta yi murmushi tare da girgiza masa kai, daga yadda yake yin magana da ita zaka fahimci ba mai yawan magana bane, kuma da gani bai saba hirar soyayya ba, bayan ɗan shiru Salma na kallon shi da ɗan murmushi ta ce, "Kun sha dinner, ta yi kyau sosai." Idon shi akan waya ya ce, "Ke kuma kin sha kuka zaki rasa ni ko?" Ta ɗan buɗa ido sai kuma ta yi yar dariya, ya ɗago yana murmushi ya tambaye ta haka ne, sauke idon ta ta yi a sanyaye ta ce, "Na dai shiga damuwa sosai da na ga an ce fiancee ɗin ka ce ita...na yi tunanin ni ka fasa...so na." A hankali ta ɗago ta kalle shi jin ya yi shiru ta ga ita yake kallo, calmly ya ce mata ya so yai inviting nata dinner ɗin, sai ya yi tunani idan ta je zata zama uncomfortable saboda duk bata san su ba, tana ta kallon shi yana maganar, bayan ya gama ta ce, "Ni na yi zaton ma ko ka manta da ni ne, da na ga an ɗauki lokaci baka kira ni ba, har ka zo kuma ka tafi." Ya yi shiru yana kallonta, itama kallon nashi take tana yi tana sauke idonta, ƙasa da murya ta ji ya ce, "How can I forget someone who keeps appearing in my dreams...." Salma ta yi saurin kallon shi, janye idon ta ta yi don ta kasa jure ma kallon da yake mata, slowly ya tambayi shima tana yin mafarkin shi, ta ɗago ta kalle shi, lecture ɗin aunty Kubra ta shiga dawo mata a kai, cike da dakewa looking at him in the eyes ta ce, "You are in my dreams and in my heart always.." Ya yi shiru yana mata wani kallan kallo, duk yadda ta so ta jure ma kallon shi kasawa ta yi, ta ji kallon da yake mata na neman haifar mata da kasala hakan ya sa ta saurin sauke idonta, bayan ɗan shiru na wani lokaci ta ji ya ce, "Baki tambayi Fahad ba." Ita sham tama manta da wani Fahad sai yanzu da ya ambace shi, ta ɗan kalle shi ta yi murmushi kawai ba tare da ta ce komai ba, ya sake ce mata ina Sageer, ta ce "Yana nan, yana Funtua shine ma yanzu ke kula da aikin da ka bani, shima kwanaki ya ce mani ko ya tura maka saƙo baka reply, amman komai ake buƙata yana ma hajiya magana." Ya ɗan jinjina kai, "Ke kin dawo nan ke nan, ba zaki koma Funtua ba?" ta ce, "Eh a nan zan yi karatu sai dai in rinƙa zuwa idan mun samu hutu." Ya ɗan yi shiru can ya je, "Ba zaki yi karatun a London ba?" Ta yi saurin kallon shi ba ta ce komai ba don bata fahimci inda maganar tashi ta dosa ba, "Ko you are not ready ki koma can?" Dan murmushi ta yi ta sauke idonta, a hankali ta ce, "Waye zai kai ni." Ya bata amsa da shi, ta kalle shi sai kuma ta yi saurin saka tafin hannunta ta rufe fuska don ta fahimci abun da yake nufi, Deen ya yi murmushi don kunyarta na burge shi sosai, ba kamar Basma ba da sam bata nuna masa kunya a abun da ya shafi soyayyar su, yanzu haka ma cikin takura masa ta ke koda yaushe kan ya yi ma dad ɗinta magana cewa ya shirya auren ta, saboda har yanzu Maleek ya ƙi amincewa da maganar auren su biyun, a tunaninta idan shi Deen ɗin ya yi masa magana kan ya shirya auren ta zai amince, sai dai shi Deen bai san dalilin matsawar da Basman ke masa ba kan hakan. Salma ta ji tana son sanin abun da ya tsaya mata a rai, tana kallon Deen ta ce, "Amman ya Deen ya aka yi ka fara so na." Murmushi ta ga ya yi yana ɗan lumshe ido ya ce mata shima bai san yadda aka yi ba, wayarsa ya ɗan lallatsa ya miƙo mata ya ce , "I think daga wannan ne." Salma ta amshi wayan, mamaki ne ya bayyana akan fuskarta ganin hoton ta, taita kallon hoton tana son tuna yaushe ta yi shi, daga yanayin hoton da alama ma ba tare da sanin ta aka yi shi ba, a hoton ta ɗan juyo fuskarta ta yi murmushinta mai burgewa kanta a buɗe, yayin da sumarta ke a sake ta yi ma kanta rumfa, sai daga baya ta lura Sageer ne ya ɗaura hoton a status shine Deen ya yi screenshot, a jikin hoton an yi caption ɗin, "My beautiful sis...son kowa ƙin wanda ya rasa." Har da love emoji a caption din, a ranta ta raya Sageer ke nan, a fili ya bayyana yana son ta ya damu da ita amman kuma yai ta cin zalinta, kallon Deen ta yi tana murmushi tace ita bata ma san lokacin da aka yi hoton ba, "...daga nan sai ka fara so na?" Ta tambaya tana kallon shi, yana murmushi ya ce mata kawai dai hoton ya yi masa kyau shiyasa ya ɗauka, kuma kusan kullum sai ya kalli hoton to daga nan ya fara developing feelings akanta, dama akwai abubuwan da suke burge shi tattare da ita, Salma ta yi murmushi tare da ɗan langa6e kai tana kallon shi, ya ɗage mata gira ya ce ita ya akai ta fara son shi, ta ce, "Kawai kana bayyana mani na ji nima ina son ka, dama nima akwai abubuwan da suke burge ni a tare da kai." Ya yi mata wani kallo ta yi yar dariya....daidai nan wayarta da ke ajiye a jikinta ta fara ringing, dubawa ta yi ta ga aunty ce ta kira ta, bayan ta ɗauka ta kai kunne, daga ɗayan bangaren ta ji muryar aunty ta ce, "Love birds...haka ake yi sai ki riƙe mutum ba zaki shigo da shi ko ruwa ya sha ba." Ƴar dariya Salma ta yi bata ce komai ba, aunty ta ce mata ta shigo da shi ya ci abinci ta amsa da to, bayan ta cire wayan ta juya ta kalli Deen da ya jingina da seat ya ɗan lumshe ido, ta ce, "Auntyna ta ce mu shiga ciki." Slowly ya buɗe idanun shi kanta, ta ce mashi su je ya ɗan yi shiru sai kuma ya ce ok, tana kai hannu zata buɗe ƙofar ta ji an buɗe mata daga waje, shima Deen ta ɗayan bangaren aka buɗe masa, Salma ta fito tare da kallon mutumin da ya buɗe mata ƙofa, a ranta take raya ashe wai suna nan suna ta tsayuwa su kuma aikin su ke nan, zagayowa Deen ya yi 6angaren da take ya yi mata alamar su je suka fara tafiya a nutse sun jera, duk da Salma na da ɗan tsawo amman data jera da shi sai ta koma gajera don ko kafaɗar shi kanta bai ƙarasa ba, gashi sai ta yi ƴar ƙarama a tare da shi saboda ƙirar jikin shi. da ƴar siririyar sallama ya shigo cikin falon, Salma na gaba bayan sun shiga ta juyo tana murmushi ta nuna mashi kujera ta ce ya zauna bari ta kira auntynta ya ɗaga mata kai, tare suka fito da aunty Kubra tana biye da ita jikinta sanye da doguwar rigar lace, da murmushi ta ƙaraso wurin kujerun idonta akan Deen dake zaune ya ɗaura hannuwansa akan kafafunsa, aunty ta zauna a kujerar dake gefe da tashi fuska a sake ta ce, "Deen, sannu da zuwa." Cikin nutsattsiyar muryarsa ya amsa tare da gaishe da ita, "Ya ka baro familyn ka." aunty ta faɗa tana faffaɗan murmushi, ya amsa mata da duk suna lafiya, ta sake cewa, "Ma sha Allah...sannu." Shiru suka ɗan yi idon aunty akan shi shi kuma har lokacin bai kalle ta ba, ita kanta ganin abun take kamar mafarki mutumin da iya a tv da waya take ganin shi yau shine zaune a gabanta, aunty ta sake cewa, "Mun ga abubuwan alkhairi da suka wakana, Allah Ubangiji Ya ƙara ma rayuwa albarka, Allah kuma Ya ƙara bada sa'a Ya tsare." Sai lokacin ya ɗan ɗago ido ya kalle ta da ɗan murmushi ya ce, "Ameen Ya Rabb. Nagode sosai." Aunty ta ce ba komai, ta kalli Salma suka haɗa ido tana ta yin murmushi, aunty ta maido idonta akan Deen tana murmushi ta ce, "Sai kuma muka ji wani abun farin ciki a kan baby...Allah Ya tabbatar mana da alkhairi." A hankali ya amsa da Amin kafin ya ɗan kalli Salma suka haɗa ido suka ɗan sakar ma juna murmushi, aunty da ke kallon su ta janye idanunta still da murmushi kan fuskarta, juyowa ta yi ta kalli Salma ta ce, "Baby go with him and serve him some food." Salma ta amsa da to tana miƙewa, aunty ta kalli Deen a tausashe ta ce mashi ya je ya ci abinci, slowly ya amsa da ok tare da miƙewa suka nufi dining tare da Salma yana tafiyarsa mai cike da natsuwa, aunty ta bishi da kallo a fili ma sai ta ga ya fi kyau, a cikin rai take raya idan ka ganshi kaman ba zaka ji hausa ta fita daga bakinsa ba, miƙewa aunty ta yi ta nufi komawa bedroom a rai tana faɗin in dai baby ta aure shi lalle ba ƙaramin dace ta yi ba...Salma ta ja masa kujera tana kallon shi da murmushi bayan sun zo dining ɗin, ya yi mata wani kallo da ɗan murmushi kafin ya zauna, bubbuɗe abubuwan abincin masu kyau da aji ta shiga yi, ta ɗago ta kalli Deen tana dan langa6e kai ta ce mi yake so ya fara ci, ya ɗan lumshe mata ido ya ce komai ya yi mata, "Akwai awara ko in fara zuba maka ita?" Ya ɗan yi shiru yana kallon ta sai kuma ya ɗaga mata kai, awaran ta fara zuba mashi a cikin wani haɗaɗdan plate na ƙawa, tana cikin zubawa ta kalle shi ta ce, "Ka ƙara cin ta bayan da ka bar Funtua?" Slowly ya girgiza mata kai alamar a'a, enough ta zuba mashi, ta bude warmer ɗin chicken sauce ta zuba a wani bowl mahaɗin plate ɗin, ta zuba masa coleslaw, bayan duk ta zuba komai ta saka masa fork da kuma spoon ta ajiye komai a gaban shi, calmly ya furta, "Thank you." ta langabe kai tana kallon shi, wani irin son shi take jin yana ratsa zuciyarta, hakan ne ya sa take wasu abubuwan ba tare dama ta san tana yi ba, alamar ta zauna ya yi mata da hannu sannan ta zauna saman kujeran gefen shi, a nutse ya fara cin awaran ita kuma tana ɗan ta6a wayarta, bayan ɗan lokaci ya kalle ta suka haɗa ido ya ce itama ta ci abincin, tana murmushi ta ce ai ta riga ta ci tun kafin ya zo, maida idon shi ya yi kan abincin ta ji ya ce miyasa bata ci kaɗan ba idan ya zo su ci tare, ta yi shiru tana murmushi, bayan ya cinye wanda ya kai bakinsa ya ɗan kalle ta ya ce ko ita acici ce bata iya cin abinci kaɗan, Salma ta ɗan yi dariya ta ce, "Idan ni acici ce ka ga ke nan kai ne ka koya mani, don hajiya ta ta6a faɗin hakan akan ka." Ɗan buɗa ido ya yi sai kuma ya yi murmushi mai dan faɗi don ya so ya tuno lokacin...lokaci lokaci Salma ke ɗaga ido ta kalle shi, wani lokacin su haɗa ido ta sakar masa murmushi, sosai ta ji daɗin yadda ya saki jiki yana ta cin awaran kuma da alama ta yi masa daɗi, ganin ya kusa cinye wadda ta zuba mashi ta miƙe tana faɗin bari ta ƙara masa, da hannu ya dakatar da ita kafin ya ce wannan ta ishe shi ya ƙoshi, a ɗan shagwa6e ta ce, "To ai baka ci sauran abincin ba, kuma duk don kai aka yi." Yana bita da kallo yana cin awara a bakin sa, ta ce, "Bari to ko fried rice ɗin in zuba maka." Ba ta jira abun da zai ce ba ta buɗe warmer ɗin haɗaɗɗar fried rice da ta sha vegetables an yayyanka ƙananun nama sosai a ciki sai uban ƙamshi take, tana zuba kaɗan ya ce mata ya isa, ta ɗan yamutsa fuska tana kallon shi ba ta ce komai ba, yana ɗan murmushi ya ce mata ya ci abinci ne kafin ya zo, a shagwabe ta ɗan tura baki ta ce, "To miyasa zaka ci abinci ka san kuma nan dole za a yi maka." Still ya yi yana kallonta don ba ƙaramin tafiya ta yi da shi ba yadda ta yi maganar, ya ɗan lumshe ido ya ce, "I'm sorry princess....ai na ci awaraan sosai." Salma ta ɗan yi dariya don yadda yake fadin sunan awara na mata daɗi, bayan ta zuba mashi coleslaw ta tura plate ɗin gaban shi....sai da ya cinye awaran da ta zuba mashi duka, sosai ta yi masa daɗi ko don ya daɗe bai ci, fried rice ɗin ya fara ci, yana cikin ci suka haɗa ido da Salma, bayan ya cinye wadda ke a bakinsa ƙasa da murya ta ji ya ce ita ta dafa ta, Salma na murmushi ta ce ta yi mashi daɗi ne, a hankali ya ɗaga mata kai, "Aunty ce ta dafa, amman nima na iya yin irinta." Bayan ya cinye wadda ya kai baki ya ce kar wataran ya sata ta yi mashi irin shi ta kasa yi, ƴar dariya ta yi ta ce, "Wllh na iya girka irin ta." Ya ɗan jinjina kai ya ce zai sa ta yi mashi irin shi sai ya gane in da gaske ta iya, tana kallon shi cikin ido ta ce a ina zata girka mashi, ya ɗan dago ido a hankali ya ce, "Gidana..." Salma ta yi murmushi tare da sauke idonta, can kuma ta ɗago tana kallon shi ta ce, "Ba ma sai ka saka ni ba, kawai zaka ga na yi maka ita." Ya ɗan jinjina kai ba tare da ya ce komai ba...bayan ya gama ta miƙe ta zuba mashi drink a hadaddan glass cup, ta miƙa mashi tana faɗin wannan ita ce ta haɗa shi, ya yi murmushi ya amsa ya kai baki, bayan ya ɗan sha ya dakata ya kalle ta, ta ce masa ya yi daɗi ya ɗaga mata kai, "To hada shi zan yi maka." ya ce zata rinƙa yi mashi ai ba sau ɗaya ne za a yi ba, ta yi ɗan faffaɗan murmushi ta ce to, sai da ya shanye wanda ta zuba mashi, za ta kara ya ce mata ya isa ta nuna lemun kwali ta ce to bai sha wannan ba, yana kallon ta cikin ido ya ce bai san ina zai sa shi ba, ko don ta ji hajiya ta ce mashi acici ai yana ƙoshi, yar dariya ta yi, ya sa ta miƙa masa tissue box ya yaga ya goge baki, daga haka ya miƙe itama haka suka nufi cikin falon, Salma ta nuna masa kujera ya ce mata zai tafi ne, ta ce to bari ta faɗa ma aunty, tare suka dawo da ita aunty na murmushi ta ce, "Deen, har za a tafi." a nutse ya ce mata eh tare da yi mata godiya, itama godiya ta yi mashi ta ce amman dai ba Abuja zai koma ba yanzu ko ta ga yamma ya yi sosai, ya ce mata eh sai gobe zai tafi, daga haka suka yi sallama ya nufi ƙofa sun jera da Salma, aunty ta bi su da kallo fuskarta da murmushi har suka fita, zama ta yi akan kujera still tana murmushi a cikin ranta ta raya ko ya baby zata yi da wannan gabjejen mutumin...Salma ce ta dawo cikin falon aunty ta ɗaga ido tana kallonta, tambayar ta ta yi lafiya, Salma ta ce, "Aunty wai na ga awaran ta yi mashi daɗi don kusan ita kaɗai ya ci sosai sai fried rice ba sosai ba, shine na yi tunanin ko tun da akwai a zuba mashi ya tafi da ita." Aunty ta miƙe tana faɗin lafiya lau ai in dai zai tafin da ita, Salma ta ce zata sa ya tafi da ita bari ta dauko takeaway pack a zuba sai a saka a leda, da sauri aunty ta ce, "Ya za ai a zuba mashi a nan, bari a zuba a cikin warmer zai fi." Suka nufi dining, a cikin wasu warmers biyu masu shegen kyau aka zuba awaran, ɗaya aka zuba chicken sauce, ba a zuba mashi coleslaw ba a cewar aunty zai iya bugawa, Salma ta sa aka haɗa mashi da juice ɗin da ya sha bayan an zuba a wani glass bottle, wani basket shima mai kyau da aji aunty ta ɗauko aka zuba kayan a ciki Salma ta tafi, lokacin da ta fito haraban a bakin mota ta ganshi tsaye ya jingina yana latsa wayan shi, dama bayan sun fito kafin su iso wurin motan ne ta ce mashi tana zuwa shine ta koma ta yi ma aunty maganar, a gefen shi ta tsaya ya ɗago ya kalle ta, tana murmushi ta ce, "Aunty ce ta ce in kawo maka awaran ka tafi da ita don saboda kai aka yi." Ya ɗan buɗe ido ba tare da ya ce komai ba, "A ina ka sauka?" Ta tambaya tana kallon shi ya bata amsa da hotel, suka ɗan yi shiru kafin ta ji ya ce mata yana son za su fita gobe da rana idan zai yuwu, Salma da ke kallon shi ta ɗaga mashi kai, ya ce idan ta koma sai ta faɗi ma auntynta ta ce to, ɗaga kai ya yi ya kalli bodguard ɗin da ke a 6angaren da suke yana tsaye daga wurin boot ɗin motan, da turanci Deen ya ce mashi su fiddo abun da ke a cikin boot su kai ciki, cikin girmamawa ya amsa ma Deen da kai, Salma ta bi su da ido tana kallon wasu haɗaɗɗun akwatuna da suka ɗauko lokacin da za su wuce ciki, ɗaya yana riƙe da akwatunan guda biyu sai ɗayan kuma guda ɗaya da wata babbar jaka mai ɗauke da hoton Deen daga gani ta naɗin sarautar shi ce, Salma ta janye idanunta bayan sun wuce....aunty na zaune tana latsa wayarta ta ji murya an furta, "Excuse..." Ta yi saurin ɗagowa, har saida gaban ta ya faɗi ganin mutumin da ke a bakin ƙofar, miƙewa ta yi tana kallon shi kana ganin fuskarta ka san ta tsorata, mutumin ya ɗan ɗaga box ɗin hannun shi ta cikin takunkumin ya ce an ce su kawo, aunty ta ɗaga mashi kai ya kutsa cikin falon ɗayan na biye da shi, a nan gefen carpet suka ajiye kayan daga haka suka ɗan sunkuya ma aunty kai suka juya, aunty ta kasa furta masu komai ta bi su da ido suna tafiya a wani bubbuɗe sai ka ce wasu robot...bayan sun dawo Deen ya miƙe daga jikin motan ya ce mata za su wuce sai sun yi magana, ta ɗan langa6e kai ta ce ok sai kuma ta ce ta saka basket ɗin cikin motan ko boot ya ce ta saka a back seat kada ya manta da shi, ta nufi ƙofan 6angaren da suke shi kuma ya zagaya aka buɗe mashi ya shiga, daga gefe a back seat ta ajiye basket ɗin ta ɗago tana kallon shi, softly ya ce, "Thank you princess." tana murmushi ta ce, "Welcome ur highness." Deen ya yi ƴar dariya har fararen haƙoransa suka ɗan bayyana, ta ce, "Sai Allah Ya kaimu goben?" Ya ɗaga mata kai kafin ya ɗan lumshe mata ido slowly ya furta, "I love you." Kawai Salma sai gani ta yi itama ta ɗan lumshe ido yadda ya yi ta furta, "I love more..." Ita kanta bata san ya aka yi ta samu karsashin hakan ba, zuba mata ido ya yi yana jin sonta na ƙaruwan mashi a zuciya, Salma ta yi kokarin ta dake wurin mayar masa da martanin kallon amman ta kasa sakamakon yadda kallon nashi ya kashe mata jiki, a hankali ta yi murmushi tare da janye jikinta ta fita daga motan, ta ɗan ɗaga hannu tana yi ma Deen da ya jingina jikin seat bye bye, shi dai kallon ta kawai yake da ɗan murmushi, sai da bodyguards ɗin nasa suka ga ta fito sannan na mazaunin driver ya shiga, dayan ya zo ya kulle ma Deen ƙofa kafin shima ya shiga front seat, Salma na tsaye har motan ta juya ta tunkari gate, driver ɗin ne ya fito ya buɗe gate, bayan sun fita ya dawo ya rufe ya ɗan ɗaga ma Salma hannu alamar sallama....Salma ta ɗan sauke yar ajiyar zuciya bayan sun tafi ta juya ta nufi ciki, a falo ta iske aunty zaune, ta ɗaga kai tana kallon Salma, nufar ta Salma ta yi tana zuwa ta faɗa kanta, aunty ta saki faffaɗan murmushi tana tambayarta ya aka yi, jin shiru bata ɗago ba ya sa aunty ta kai hannu ta ɗago da face ɗin ta, lokaci guda aunty ta ɗan zaro ido ganin hawaye a idon Salma ga murmushi kuma tana yi, aunty ta yi dariya ta ce, "Duk farin ciki ne haka baby." Salma ta kasa cewa komai sai dariya take, zaunar da ita aunty ta yi tana kallon ta ta ce, "Sun tafi?" Ta ɗaga mata kai, ta ɗan yi shiru kafin ta ce, "To ya kuka yi da shi, ya yi maki maganar wanccan ɗin ne?" Salma ta bata labarin yadda suka yi, aunty na murmushi ta ce, "Ni dama na san har da uzururruka ya sa bai neme ki ba, kuma haka nan ba zai ce yana son ki ba kuma wai ya dawo ya ce ya fasa. Yanzu ke nan kin amince ya aure ku ku biyun?" A hankali Salma ta ɗaga mata kai alamar eh, aunty ta ɗan yi shiru tana kallon wuri guda, ganin haka ya sa jikin Salma yin ɗan sanyi, a hankali ta ce, "Amman...ni gani nike kaman dangin shi ba za su amince ba tun da ita yar'uwar shi ce." Kamar Salma ta san abun da ke ran aunty, kallon ta ta yi tana ƙoƙarin basar da tunanin da take yi ta dafa ta ta ce, "Kar ki damu, tun da bamu san ya dangin nasa suke ba, kuma kakarsa ai ta san ki kuna mutunci da ita. Mu ci gaba da yin addu'a, idan Allah Ya ƙaddaro shi mijinki ne kamar yadda na faɗa maki ba wanda zai hana hakan faruwa." Salma ta ɗaga mata kai, "Ya yi maki magana kan lokacin da yake son ku yi auren ne?" Salma ta ce, "a'a, ya dai ce karatu na a London zan ci gaba." Aunty ta ɗan gwalo ido sai kuma ta saki dariya ta ce,"Inyee, ki ce London zamu kai amarya." Salma ta yi ƴar dariya, aunty ta kalli akwatunan da aka ajiye ta ce mata na minene, Salma ta ce kawai ta ji ya ce a kawo, miƙewa aunty ta yi tana faɗin bari su duba, bayan ta jawo akwatunan ta shiga ƙoƙarin buɗe su amman ta kasa, kallon Salma ta yi da ɗan mamaki ta ce to ya aka yi zip ɗin ya ƙi buɗewa, Salma ta ce bata sani ba, itama Salma ta shiga ƙoƙarin buɗewa abun duniya ya gagara, aunty ta ce, "To ko dai zip din suna da matsala ne, tun da ai ga wurin rufe su nan kuma ba a rufen ba...amman kuma a ce gaba ɗaya zip ɗin su ke da matsala..to ko dai akwai yadda ake buɗe su ne bamu sani ba." Salma dai ta yi shiru....ba irin kokarin da aunty bata yi ba amman fir zip ɗin ya ƙi jawowa balle ya buɗe, ta kalli Salma ta ce, "Yau an bani an kawo ma ƴan kauye abu." Salma ta saka dariya, aunty ta fara dudduba jikin akwatin tana neman irin ɗan katin da ake sakawa na bayani, sai gashi ta gani a cikin wani ɗan aljihu, fiddo katin ta yi tana dubawa, lokaci ɗaya ta saki dariya bayan ta karanta yadda za a buɗe da sauran bayanai, kallon Salma ta yi ta ce mata ashe wai akwatunan smart suitcase ne, wato masu amfani da fasaha da ake ma caji, suna da na’urar gano wuri wato GPS da kuma bluetooth, sannan suna da USB port don cajin waya ko wata na’ura yayin tafiya, suna da kuma smart lock da za a iya kullewa ko buɗewa ta app ɗin waya, akwai kuma na’ura mai auna nauyi ta nuna maka nauyin kayan cikin akwatin, sannan suna iya bin ka kai tsaye ba tare da ka ja su ba, aunty nata dariya ta ce, "Wannan ai da ya bari sai kin je London ɗin ya siya maki irin su tun da mu nan duk ƴan kauye ne." latsa wurin da ta ga an sa ta nan ake buɗewa ta yi, sai gashi tana jan zip ɗin ya zuge, aunty ta ƙara sakin dariya tana faɗin ba don Allah Ya sa mutum ya yi ilimi ba aka kawo masa wannan da ya zai yi, da sai dai wurin kokarin budewa ya yi banna ko kuma ya haƙura ya bi su da kallo....wani irin ƙamshi ne ya baɗe wurin bayan aunty ta buɗe babban ciki, jinjina kai ta hau yi bayan ta ga uban kayan da ke ciki, hannu ta kai ta fara ɗaɗɗagawa, ubansun designer kaya ne a ciki, akwai Abayu guda biyar, sai engliss dress da za su kai kala bakwai, har da scarfs masu aji kusan biyar, sannan akwai sleeping dress, kana ganin kayan ba sai an faɗa ba kasan masu tsada ne sosai, ga su unique kaya ba irin wanda zaka iya gani ko ina ba, gaba ɗaya al'ajabin kayan ne ya kama su, akwati na biyu aunty ta buɗe nan kuma ubansun designer shoes and bags ne guda biyar abun sai wanda ya gani kawai ga takalman duk heels, sai turarurruka da mayuka na jiki da kai har da na tsabtar baki, ƙaramin akwatin ƙarshe nan earings ne wato ƴan kunne na ƴan gayu da su abun hannu, zobba, da agoguna har da hankys, gaba ɗaya kayan designers ne, kallon ƙatuwan jakar da ke dauke da hoton naɗin sarautar Deen aunty ta yi kafin ta buɗe ta, nan duk su abubuwan souvenirs ne na sarautar shi, kaya ne da yawa su table calander, jotter, pen, hanky, mugs, paper bags, key holders kowanne sun kai guda biyar biyar...nannauyar ajiyar zuciya aunty ta saki tare da juyawa ta kalli Salma da tai gwale jikinta duk ya yi sanyi ganin uban kayan, aunty ta jinjina kai ta ce, "Abun na yi ne? Kin ga kaya baby, wai nan tsaraba ce...to ina ga kuma lefe!" Salma ta kasa cewa komai da ido kawai take bin komai, "Yanzu ina ganin ya kamata a kira su yaya Fiddausy a sanar masu, dama na bari ne abun sai ya kankama." Sai lokacin Salma ta tuna da maganar fitan da ya ce za su yi gobe ta faɗi ma aunty, "Ina ya ce zaku je?" Salma ta ce itama bata sani ba ya dai ce ta tambaya, aunty ta ce to bari ta dakata sai an ga abun da zai wakana goben sannan ta kira Funtua ta sanar masu, suka yi shiru suna bin kayan da ƙamshin su duk ya karaɗe wurin da kallo...... *✨A CIKIN RAYUWA ZAINAB BATURE 56 ....Gaba ɗaya sauran yinin ranar Salma a cikin tsananin farin ciki ta kasance, ba kamar idan ta kalli kayan da Deen ya kawo mata da aunty ta sa suka kawo su nan ɗakinta, bata gajiya da tunanin Deen da abun da ya wakana a tsakanin su, kana kallonta zaka fahimci tana a cikin farin ciki. A daren ranar, bayan Salma ta gama shirin kwanciya sai ga kiran Deen ya shigo wayarta, dama ɗazun ta kira shi bayan ya tafi ta yi masa ya ya koma da godiyar kaya...soyayya suka sha sosai, har saida Salma ta yi mamakin yadda ya saki jiki, daga baya ya ce ta kwanta sai ya zo gobe, suka yi bankwana cike da nuna ƙaunar juna. Washe gari bayan sun tashi Salma ta yi duk ayyukan da ta saba yi duk da lokacin ma sai da aunty ta hana ta yin wasu abubuwan ba kamar wanda zata ta6a ruwa sosai, a cewar ta kada lallenta ya disashe tun da Deen ɗin ba tafiya ya yi ba gashi kuma za su fita tare...wuraren ƙarfe sha biyu ya kira ta ya sanar da ita bayan an gama sallan azahar zai zo ya ɗauke ta, suna gama yin wayar ta je ta sanar ma aunty ta ce ta je ta yi wanka, after some minutes ta fito tana tsaye a gaban mirror tana goge jikinta aunty ta shigo, cikin ɗakin ta nufa tana tambayarta ta fito wankan ta ce mata eh, ganin zata fara shafa mayukanta da ke a wurin aunty ta yi saurin cewa, "Ina waɗanda ya kawo maki?" Salma ta ce mata suna cikin akwatin, "To ai ba kawo maki yayi don ki ajiye ba ko, su yakamata ki yi amfani da su" Daga haka ta nufi inda akwatunan suke ta fara buɗewa, mayukan ta fiddo mata ta ce ta zo ta ɗauka, dama jiya duk sai da ta dudduba bayanan yadda ake amfani da komai, bayan ta zo ta kwashi mayukan ta koma gaban mirror ta fara shafawa, kana jin yanayin su ma a jiki ka san za su yi aikin su, har da na su tafin ƙafa da tafin hannu, wanda ake shafa ma gashi suma duk ta shafa, aunty ta nufo ta da wata Abaya da ta fiddo daga cikin kayan tana faɗin, "Wannan Abayan ta yi kyau over, ina ganin ki saka ta, shima idan ya ga kin saka cikin kayan zai ji daɗi." Salma ta jiyo tana kallon rigan, a gefen gado aunty ta ajiye ta ta nufo Salma, taimaka mata ta shiga yi ta gyara mata gashinta sannan ta yi mata light make up kaman jiya, bayan ta gama ta ce ma Salma ta saka underwear ta ce to tare da nufar wardrobe ɗin bango inda kayanta suke, aunty ta koma wurin akwatunan tana ce ma Salma ta zo su za6i jewellery da takalman da zata saka...aunty ta bi Salma da kallo tana ta sakin nurmushin jin daɗi bayan ta gama shirya ta, cike da sha'awa ta ce, "Ma sha Allah jiki ya ji naira, kin ga wani kalan kyau na musamman da kika yi baby, duk wanda ya gan ki sai ya yi tunanin ɗiyar wani babba ce a ƙasa, don da an ga kayan nan ansan ba ƙananun kaya bane." Ita dai Salma dariya kawai take tana ta kallon kanta a madubi, sosai ta yi wani irin kyau a cikin abayar wadda take ruwan madara, a jikinta wani irin design ɗin ado aka yi, sam kwalliyan rigar ba mai hayaniya bace amman tsarin kwalliyan da aka yi ya ƙawata rigan sosai, ga yadin ta shima na musamman, a jikin kwalliyan rigar akwai ratsin golden brown da wasu irin fararen stones masu sheƙi, takalman da ta saka kalan kwalliyan rigan ne da clutch bag mahaɗin takalman, aunty ta kai idonta kan takalman ta ce, "Baby anya kuwa zaki iya yin tafiya da takalman nan, na ga sun fi kalan wanda kika saba sakawa tsini." Salma dake ta faffaɗan murmushi ta ce zata iya ai suna da maɗauri, cike da shakku aunty ta ce, "Kada fa a je a yi abun kunya, kin san mutane irin shi public figure koda yaushe cikin ɗaura masu camera ake, bamu sani ba ko wani wurin mutane zaku je." Gaban Salma ya ɗan faɗi jin maganar aunty, ita sam tunanin ko wurin mutane za su je bai zo mata a rai ba, aunty tana ƴar dariya ta ce bari dai su ɗan yi little practice ɗin tafiyan saboda tsaro, daga farkon shigowa ɗakin zuwa ƙarshe ta saka Salma yin tafiya, tana yi tana gyara mata inda ke buƙatar gyara, sai da aunty ta ga tana yin tafiyan lafiya lau yadda ta nuna mata, sannan suka koma gaban mirror tana ƙara gyara ta kuma tana koya mata yadda zatai behave har da magana idan buƙatan hakan ta taso, suna haka suka jiyo ƙarar buɗe gate, aunty ta ce tana jin shine ya zo, tana rufe baki wayar Salma ta fara yin ringing ta nufi gado zata duba aunty ta bita da kallo cike da sha'awa tana sakin murmushin jin dadin ganin yadda babynta ta fito, bayan ta duba ta ga shine, cikin kwantar da murya suka yi magana ya ce mata ya zo, bayan ta gama ta ɗago tana murmushi ta ce ma aunty, "Shine ya zo." aunty ta nufo ta ta ce ta saka wayan a jakar da zata tafi da ita, tare suka nufi ƙofa da aunty ta kama mata hannu suka fita, har bakin falo aunty ta kai ta sannan ta saki hannunta tana kallon ta da murmushi ta ce, "Sai kun dawo babynah, ki kula pls." Salma ta ɗaga mata kai, sai kuma ta ce, "Ki raka ni ko bakin haraban." Aunty ta yi mata wani kallon hararan wasa, kafin ta ɗan yi murmushi ta ce, "Go on, don't keep him waiting..." Salma ta ɗaga hannunta da ya sha abun hannu mai matuƙar kyaun gaske ta yi mata bye bye itama aunty ta mayar mata daga haka ta tafi...a nutse ta nufo harabar tana tafiya, Salma ta bi danƙareriyar baƙar mercedes benz G- Class (G-Wagon) dake ta sheƙi da aka faka a gaban gate da kallo, sauke idonta ta yi tunowa da huɗubar da aunty ta yi mata na kada ta nuna ƙauyanci koda ta ga abun da ya ɗauki hankalinta, ta basar ko kuma ta yi al'ajabin a zuciya, a cikin rai take tunanin yadda aka yi yau ya canzo mota ganin ba da wannan ya zo jiya ba ko kuwa duka ya zo da su daga Abuja...tun da ta nufo motar idanun Deen na akan ta, da yake parker motan aka yi tana kallon ginin gidan ba tare da an rufe gate ɗin ba, tana kusa zuwa wurin motan mutumin da ke a gaban motan wanda da gani bodyguard ɗin jiya ne don irin shigar jiyan ce a jikinsa ya fito ya buɗe mata ƙofar baya tun kafin ta ƙaraso, kai ya ɗan sunkuya mata alamar gaisuwa itama ta yi masa haka, bayan ta shiga ya maida ƙofar ya rufe, har Salma bata san lokacin da ta ɗan lumshe ido ba lokacin da ta shiga cikin motan, haɗa ido suka da Deen da ke ɗaya 6angaren back seat ɗin, ya yi shigar fararen ƙananun kaya designers, farin jeans da riga fara mai ɗan ratsin baƙi sai farar hula face cap, a ƙafafunsa ya saka baƙaƙen takalma, haka hannunsa na ɗaure da wata rantsattsar baƙar agogo ta miliyoyin kuɗi, sai faman sakin ƙamshi mai narkar da zuciya yake, idan ka gan shi sam bazaka ta6a tunanin ya haɗa iri da hausawa ba ba kamar yadda sumar shi ta zuba a wuyansa, haɗa ido suka yi Salma ta sakar masa lallausan murmushi, softly ta ce, "Welcome...ina yini." Ya ɗan nod kan sa fuskarsa da murmushi, kasa jure kallon shi ta yi saboda kunyar hirar da suka yi da shi a daren jiya, don a hiran har da irin rayuwan da za su yi idan suka yi aure ya faɗi mata, itama ta tambaye shi abubuwan da yake son matarsa ta rinƙa yi mashi kamar shigar kaya da sauran su, ƙasa da murya ta ji ya ce, "Kin yi kyau sosai princess." A hankali ta ɗaga kai ta kalle shi ta ga ita yake kallo, a hankali itama ta ce, "Ai kai ne ka sa na yi kyau ɗin." Ya ɗan lumshe ido bai ce komai ba, mutumin na mazaunin driver ne ya tambayi za su iya tafiya Deen ya amsa mashi, bayan motan ta fita daga cikin gidan, ɗayan bodyguard ɗin da bai shigo cikin motan ba ya rufe gate din sannan ya koma ciki daga haka suka tafi....tun da suka hau hanya ba wanda ya ƙara cewa komai, idon Salma na akan hanya shi kuma Deen yana ta6a waya, bayan wani ɗan lokaci ta juya ta kalle shi, slowly ya dago kai shima ya kalle ta tare da yi mata murmushi, a hankali ta ce, "Kai ma ka yi kyau sosai.." Ya ɗan ɗage gira ya ce shima ita ce ta sa shi ya yi kyaun, Salma ta yi ɗan faffaɗan murmushi, tambayarta aunty ya yi ta ce mashi tana lafiya ta ce ma ta gaishe shi ya ɗaga kai, jefi jefi suka ci gaba da yin magana....bayan tafiyan mintuna masu ɗan tsayi suka iso wani wuri, duk yadda Salma ta so ta kasa ɗauke idanunta daga kallon ginin, duk da bata yi yadda zai yi ƙauyanci ba, tun daga tsarin ginin wurin da gate ɗin shiga masu matuƙar ɗaukar hankali ne, bayan sun shiga nan Salma ta ga ashe bata ga komai ba a wajen ginin, yadda ka san ginin ba a Nigeria ba yadda ya tsaru ga tafka tafkan gilasai ta ko ina a ginin benen, daga rubutun da ta gani a gaban ginin ta gane Restaurant ne, kuma kusan shine babban restaurant na garin, babban wurin parking ɗin motoci da ke can gefe na ɗauke da motoci masu numfashi, kai daga ganin wurin ka san ba wurin zuwan ƙananun mutane bane, ba su nufi parking space din ba ta gefen ginin suka bi, a daidai gaban wata babbar kofar glass da itama ta haɗu suka tsaya, bodyguard ɗin da ke a gaba ne ya ɗaga waya tare da yin magana da turanci, shortly after wani mutumi ya fito, kana ganinsa ka san farar fata ne tare da wasu mata yare guda biyu jikin su sanye da uniform na masu aikin wurin, a gaban motan suka tsaya bodyguards din suka fito, buɗe ma Deen da Salma kofan suka yi suma suka fito, cikin girmamawa mutumin ya gaishe da Deen da turanci ya bashi hannu, suma matan suka ɗan sunkuyar da kai suka gaishe da Deen, daga baya har da mutumin suka gaishe da Salma, mutumin ya yi masu alamar su shiga ciki da hannu, mutanen ne a gaba Deen da Salma a tsakiya sai bodyguards suka rufa masu baya, ashe Salma bata ga komai ba a tsaruwa sai da suka shigo ciki, a kaikaice ta ke kallon wurin ba tare da ta bari ta nuna ƙauyanci ba, bene suka nufa suka haye upstairs, nan ma wata duniyar tsaruwa ce, ƴar tafiya suka yi suka iso bakin wata ƙofa ta glass baturen mutumin ya buɗe masu tare da yi masu alamar su shigo, Salma ta ɗan bi cikin wurin da kallo wanda madaidaicin private dining room ne, wurin sam bai da hayaniya, tsarin da aka yi mai aji tun daga kan ginin, an saka labulaye masu kyau da aji a windows ɗin cikin ɗakin, haka a jikin bango an liƙa framed paintings in wooden frames da suka ƙawata ɗakin sosai suna kama hasken wurin, ga wani irin sanyin Ac da ƙamshi masu saka natsuwa a zuciya da saka masoya shauƙi, ɗan babban table ne a tsakiyar ɗakin da kujeru guda huɗu a zagaye da shi, cikin ma'aikatan mata da ke biye da su ɗaya ta ja ma Deen kujera tana kallon shi da murmushi, ɗayar matar ta ja ma Salma kujerar da ke kallon Deen amman sai ya yi mata alama da kujerar gefen shi wato a nan yake son ta zauna, kallon gulma suka yi da ido ita da ɗayar kafin ta zo ta ja ma Salma kujerar kusa da shi ta zauna tare da yi mata godiya, matar ta jinjina mata kai tana murmushi, gaba ɗaya ma'aikatan mamaki ne fal a ransu kan Salma, tunanin su wacece ita da kuma alaƙar ta da Deen, saboda suma sun ga ba ita ce aka bayyana ba matsayin fiancee ɗin shi, kuma daga alamun da suka bayyana soyayya ce a tsakanin su, sai dai suma duk sun ga kyawun Salma, kuma duk da basu san ita ɗin wacece ba suna ganin ta dace da take yin soyayya da Deen, bayan sun zauna cikin fara'a baturen mutumin ya ce ma Deen ga dukkan abunda aka buƙata nan an tanada sai ya duba ko akwai abun da bai yi ba ko za a ƙara, Deen ya jinjina masa kai, kiran ma'aikatan ya yi gefe ya gargaɗe su kan su kula da su sosai kada a samu wani matsala cikin girmamawa suka amsa masa, bayan ya yi ma Deen sallama ya fita, dama su bodyguards ɗin nasa suna a wajen wurin, Salma ta bi tarin uwayen abubuwan ci da sha da ke shake saman teburin da kallo, yayin da ma'aikatan suka shiga bubbuɗe abubuwan ƙawa da ke ɗauke da kalolin abinciccika na gida dana waje suna nuna masu tare da faɗin sunayen su, bayan sun gama nuna ma Deen cikin girmamawa suka tambayi abun da za su fara serving nasu, kallon Salma ya yi ya sakar mata lallausan murmushi, murya can ƙasa ya ce mi take son su fara ci, ma'aikatan suka wani kalli juna tare da ɗan buɗa ido, tun ɗazun da suke ta karakaina a gaban su ko kallon fuskar wata a cikin su Deen bai yi ba, fuskarsa ma basu wani ganinta sosai saboda face cap ɗin da ke a kansa, Salma sai da ta ɗan so ruɗewa wurin za6ar masu abincin ta rasa wanne zata ce, tana ganin kamar zata kwafsa idan ta faɗi kalan abincinmu da aka saba da shi, ƙarshe ta faɗi wani da ta riƙe sunan shi da suna gabatar masu, bata ma san kalan abincin ba haka nan ta zabe shi, gaba ɗaya wurin ya karaɗe da aroma daban daban, bayan sun gama serving nasu suka yi masu a ci lafiya tare da ɗan ja gefe alamar a nan za su tsaya suna serving nasu har su gama, a nutse Deen ya fara cin abincin, ita kuwa Salma ta ji duk ta takura da tsayuwar da ma'aikatan suka yi, har sai da Deen ya fahimci ta kasa sakin jiki, bayan ɗan lokaci da fara cin abincin Deen ya ɗaga kai a karon farko ya kalli ma'aikatan ya ce masu za su iya tafiya, da sauri ɗaya ta ce an saka su aikin yin serving nasu har su gama ne, ya ce mata ba komai za su yi serving kan su, daga haka suka yi masu sallama tare da fatan gama cin abinci lafiya, tun a bakin ƙofar fita suka buɗe baki za su fara gulma, suna yin arba da bodyguards ɗin da ke wajen suka yi gum suka wuce...duk da sun tafi Salma ta kasa sakin jiki sosai ta ci abinci, shi kuwa Deen cin abincinsa yake hankali kwance, can ya ɗago kai ya kalle ta suka haɗa ido, ya ce mata zai fi ta saki jiki don komai za su cinye, Salma ta ɗan wara ido sai kuma ta yi ɗan murmushi a sanyaye ta ce, "Ta ya zamu iya cinye wannan abubuwan duka." Deen da ya kai abinci baki bayan ya cinye ba tare da ya kalle ta ba ya ce mata ai tana tare da acici lafiya lau zai koya mata yadda za su cinye, ta yi ɗan faffaɗan murmushi kafin ta langabe kai ta ce, "Ai ko rabin su ba zamu iya ci ba." Bai ce mata komai ba, ta ga ya kawo abincin da ya ɗebo bakinta, slowly ta buɗe baki ya bata, wai sai da ta amsa kuma sannan ta sunne kai alamar kunya, shi dai ɗan murmushi kawai ya yi, daga baya ta saki jikinta ganin yadda yake ta cin abincin sa...da kanshi ya riƙa serving nasu, duk abun da zai zuba mata sai ya tambayi idan zata ci...duk idan ta nuna masa ta ƙoshi sai ya ce ai bata wani ci sosai ba ta ƙara, daga baya ta marairaice masa ta ce ta ƙoshi da gaske, cikin wasa ya ce mata so yake itama ta rinƙa cin abinci sosai kamar shi, Salma ta yi yar dariya ta ce, "To ni da ba yar ƙwallo ba." Yana cin abu ya ce, "Ai kin kusa zama." Ta ɗan yi shiru sai kuma ta tambaye shi mata ma na yin ƙwallon, ya bata amsa da eh ko club ɗin su akwai team na mata, "To da gaske nima ƴar ƙwallon zaka sa in zama?" Ɗan murmushi ya yi da alama bata fahimci nufinsa da maganar da ya yi ba ta ta kusa zama ƴar ƙwallo, "Idan kin zama yar ƙwallo, who will take care of our children?" Salma ta yi shiru tana kallon shi, ya ɗago ido ya kalle ta ta yi saurin sauke idonta, ta ji ya ce ta ci gaba da cin abinci, sai da ta marairaice masa sosai kan ta ƙoshi sannan ya ƙyale ta, ta maida idonta kan tv dake jikin bango shi kuma ya ci gaba da cin abincin shi, after a short while ta ga ya ɗauki waya yana latsawa ya kai kunne, ƴar magana kaɗan ya yi da ita bata ma ji mi ya ce ba ya cire wayan, bayan ɗan lokaci ba sai ga bodyguards ɗinsa sun shigo, Salma ta juya tana kallon na farkon da ya nufo su hannunsa riƙe da bouquet of flowers masu matuƙar kyau da tsari da kuma wata yar ƙaramar jaka, ɗayan kuma na biye da shi da wani ɗan faffaɗan kwali, Deen ya nuna masu gefe saman teburin suka ajiye kafin suka juya, Salma dai tai ta kallon abubuwa can kuma ta ɗauke kai tunowa da huɗubar aunty, idonta na kan tv ta ji ya yi mata magana ta juya, ƙwalin ya ɗauka ya miƙa mata ta amsa tana bin sa da kallon rashin fahimta ta ajiye a gabanta, yana kallonta ya ɗan lumshe ido slowly ya ce, "Open it..." Hannu ta kai zata buɗe a ranta tana tunanin miye a ciki, ƙamewa Salma ta yi tana ta kallon abun da ta yi arba da shi ƙirjinta yana ɗan bugawa da sauri, lokaci guda kuma ƙayataccen murmushi ya wanzu akan kyakkyawar fuskarta tana ci gaba da kallon cikin kwalin with astonishment, faffaɗan cake ne mai kyaun gaske daga saman shi an yi adon rubutu, abun da aka rubuta shine, "_Will you marry me?_" A hankali Salma ta juya ta kalli Deen da ya jingina da kujera yana bin ta da kallo da ɗan murmushi, ɗage mata gira ya yi alamar ta bashi amsa, slowly Salma ta hau jinjina masa kai kafin cikin ƴar rawar murya ta furta, "Yes I will..." Kawai sai ga ƙwalla sun zubo mata sharr, bayan hannunta ta saka tana goge ƙwallan tana kuma yin murmushi at the same time, ɗagowa Deen ya yi daga jinginar da ya yi ya kai hannu cikin ƙaramar jakan, wani ɗan ƙaramin jan akwati ya ɗauko tare da buɗe shi, tun Salma bata ga mi ke ciki ba ta ga ƙyallin abun, hannu ya sa ya ciro abun da ke ciki ya riƙe da dogayen yatsun shi ya ɗago yana kallon ta, Salma ta bi haɗaɗɗan zoben da kallo wanda kana gani na diamond ne, ɗago ido ta yi ta kalli Deen suka bi juna da wani kallo, alamar zai saka mata ya yi, hannunta har ɗan rawa yake ta miƙa masa yatsanta, Salma ta bi zoben da ya zauna a yatsanta ya yi mata daidai kamar an gwada da kallo, sosai ya yi ma hannunta kyau sai sheƙi yake yana ɗaukar hasken wurin, ɗago fuskarta ta yi tana kallon Deen da murmushi lokaci guda kuma ƙwalla suka ƙara zubo mata, kawai sai gani ya yi ta duƙe kanta alamar kuka ta ke, shi dai still yay yana ta kallonta da ɗan murmushi, ko bata faɗa masa ba alamu sun nuna tana son shi sosai shima kuma hakan yake ji game da ita, kusan ko wane lokaci son ta ƙaruwar mashi yake, slowly ya furta, "Salmerh.." Kanta na duƙe ta amsa, ya ce ta ɗago ta kalle shi, jimm ta ɗan yi kafin ta ɗago ta kalle shi sau ɗaya ta maida idonta ƙasa, hanky ta ga ya miƙo mata ta amsa tana goge hawayen a hankali, ɗan ɗago fuskarta ta sake yi suka haɗa ido ya ce mata mi yasa take kuka ta girgiza masa kai kawai, bai matsa mata kan sai ta faɗa masa ba don ya san kukan na farin ciki ne ba wani abu ba, tambayarta ya yi akwai abun da take buƙata nan ma ta girgiza masa kai, flowers ɗin ya ɗauka ya miƙa mata ta riƙe tana ta kallo fuskarta da yanayin farin ciki, wayarsa ya ɗauka yana latsawa bayan ɗan lokaci bodygurd ɗinsa ɗaya ya shigo, ya nuna masa kwalin cake ɗin alamar ya ɗauka, daga haka ya miƙe ya ce ma Salma su tafi, tana rumgume da flowers ɗin a gefen hannunta guda suka nufi ƙofa, bodyguard ɗinne ya riga su ƙarasowa wurin motan ya buɗe boot ya saka kwalin cake ɗin kafin ya zo ya buɗe masu kofofin, sai bayan da suka shiga cikin motan ɗayan bodyguad ɗin ya fito daga cikin wurin tare da wasu ma'aikata maza guda biyu suna biye da shi suma suna sanye da uniform, kowanne hannunsa na riƙe da ƴan manyan ledoji masu ɗauke da tambarin restaurant ɗin guda biyu, bayan an nuna masu boot suka saka ciki, daga haka bodyguards ɗin kowa ya shiga wurin zaman shi suka tafi...tun da suka hau hanya idanun Salma na ƙasa tana ta kallon flowers ɗin da suka burge ta sosai, a cikin ranta wani irin daɗi take ji, abun da take gani saurayi ya yi ma budurwa a kallo yawanci kuma ƴan ƙasar waje yau shine itama aka yi mata, har ɗan lumshe ido take yi tana shaƙar daddaɗan kamshin da suke saki, shi dai Deen idanunsa na akan wayarsa yana danna ta, lokaci lokaci yake ɗaga ido ya ɗan kalli Salma...bayan sun ɗan yi tafiya suka iso wata babban plaza, ciki suka shiga aka faka motar a wurin da aka tanada don haka, bodyguard ɗin da ke a front seat ne ya buɗe ƙofa ya fita, Salma ta bi sa da kallo yayin da ya nufi cikin plaza ɗin yana tafiya a bubbuɗe, maido idanunta ta yi kan flowers ɗinta bayan ta daina hango mutumin, can ta ji muryar Deen yana ce mata bata gaji da riƙe flowers ɗin ba, ta ɗaga ido ta kalle shi ya ce ta ajiye saman seat ta huta, ta yi ɗan murmushi tana sauke idanunta kafin a hankali ta ajiye gefen ta, after few minutes sai ga bodygurd ɗin ya dawo yana riƙe da wata yar shopping bag, 6angaren da Deen ya ke ya zagaya ya buɗe ƙofar tare da bashi jakan, bayan ya rufe masa kofan ya koma seat ɗin gaba da yake suka tafi. Kai tsaye gidan aunty Kubra suka dawo, bayan an buɗe gate motan ta kutsa ciki, gaba ɗaya bodyguards ɗin suka fita daga cikin motan ya rage saura Deen da Salma kaɗai, a hankali ta juya hannunta looking at the diamond ring sparkling on her finger, ɗago kai ta yi ta kalli Deen da ya jingina da seat yana kallonta, tana ɗan murmushi ta ce masa, "Thank you." Ya ɗan ɗage gira ya ce, "For..." Ta ce, "Proposing to me" Ɗan lumshe ido ya yi ba tare da ya ce komai ba, tambayar shi ta yi ya aka yi ya san wanda zai mata daidai har da kayan ma komai ya yi mata daidai, ya ce kawai ya ƙiyasta ne kuma tana ɗan yawan saka hannu ta rufe fuska ta nan ya san girman yatsunta, ta yi shiru tana murmushi, bayan ɗan lokaci ta ji ya ce, "I'm leaving today." Salma ta ji gabanta ya ɗan faɗi, bin shi da ido ta yi kafin a sanyaye ta ce, "Abuja zaka koma?" Ya ɗan girgiza mata kai, "Zan je Funtua kafin in koma Abuja." Salma ta yi shiru tana ta kallon shi, can ta ce, "Daga Abujan zaka koma London?" Ya ɗaga mata kai alamar eh, shiru ta yi tare da sauke idonta, haka nan ta ji jikinta ya yi wani irin sanyi, sai take jin kamar idan ya tafi shike nan zata rasa shi ne, lokaci guda ƙwalla suka fara tarun mata a ido, kiran sunanta ta ji ya yi ta ɗaga kai ta kalle shi tana kokarin maida ƙwallan, "Why kika yi shiru, ko da wani abu?" Girgiza kai ta hau yi kawai ƙwallan suka yi decieving nata sai ji ta yi sun zubo mata sharr, da sauri ta maida kanta ƙasa tana gogewa, ta ji muryarsa softly ya ce, "Don't you want me to go?" Ta girgiza masa kai a hankali, can ta ɗago ta kalle cikin rawar murya ta ce, "I..will miss you..." Tana yin maganar wasu ƙwallan suka taho mata, ita kanta ta rasa yadda aka yi ƙwallan ke zuwa, still Deen ya yi yana ta kallonta, shi kan shi mamakin yarinyar yake, yadda gaba ɗaya abubuwanta tafiya suke da shi tana ƙara dulmiya shi a son ta, ta ɗago ta kalle shi ganin ya matso a little closer to her, hanky ɗin da ta bashi da za su fito daga restaurant ya ɗago ya kai shi fuskarta yana goge mata ƙwallan da suka jiƙe idanunta dogayen lashes ɗinta sun makale ma juna, calmly ya ce, "Ki daina damuwa princess, ba zan daɗe ba zan dawo." Ta ɗago ido a sanyaye da ƴar sigar shagwa6a ta ce, "Yaushe zaka dawo to?" yana kallon cikin idanunta ya ce, "In two months time in sha Allah." Ta yi shiru tana sauke idanunta, in a whisper ya ce, "Zan je Funtua yanzu saboda ke....next time I come back we will be husband and wife, in sha Allah." Shiru ta yi tana kallon shi sai kuma ta yi murmushi tare da sauke idonta ƙasa, matsawa ya yi ya jingina da kujera yana kallonta, Basma ce ta zo mata a rai wanda ita mantawa ma take da su biyu zai aure, ta ji kaman ta tambaye shi lokaci guda zai aure su, wata zuciyar ce ta kwabe ta kan kada ta tambaye shi, ɗago kai Deen ya yi ya ɗaga hannu yana duba tsadaddan agogon hannunsa, kallon Salma ya yi suka haɗa ido ya ce, "I think I will take my leave now, kada yamma ya yi ." Salma ta ce, "Daga nan zaka wuce Funtua?" Ya ɗan girgiza kai ya ce zai koma hotel kafin ya wuce ta ɗaga masa kai, shiru ta ɗan yi sai kuma a sanyaye ta ce, "Allah Ubangiji Ya kiyaye hanya...Ya kai man kai lafiya ." Ya ɗan lumshe ido ya furta, "Ameen my love." Ta yi ɗan murmushi sai kuma ta langabe kai ta ce, "I love you so much..." Ya wani lumshe mata ido in a low voice ya furta, "I know..." Ta yi ƴar dariya, ɗan shiru suka yi kafin ya kai hannu ya ɗan ƙwanƙwasa glass ɗin ƙofa, bodyguard ɗaya ya zo ya buɗe ƙofan, Deen ya miƙa masa jakan da ya kawo masa ɗazun ya ce mashi a haɗa da kayan boot a kai ciki ya amsa tare da rufe kofar, ya juyo ya kalli Salma dake ta kallon shi yana ɗan murmushi ya ce ko ya tafi da ita, ta ce "Funtua?" Ya ɗaga mata kai alamar eh, ta gane wasa yake yi, ta ce auntynta ta ce za su je tare bada daɗewa ba ya ɗaga kai, lokacin da bodyguards din suka dawo ya ce mata ta je sai sun yi magana ta ɗaga mashi kai, suna ta kallon juna tana jin kamar kar su rabu, hannu ta kai zata buɗe ƙofar aka buɗe mata daga waje, har zata fita ta juyo ta kai hannu ta dauƙi flowers ɗinta, Deen da ke kallonta ya ce bata manta da su ba, ta ɗan girgiza kai kafin a hankali ta ce sune za su rinƙa rage mata kewan shi, ya sakar mata wani kallo tare da ɗan lumshe ido, Salma ta yi tsaye yayin da motan ke ƙoƙarin fita tana jin har ta fara kewar masoyin nata, lokacin da za a rufe gate ɗin ta ga glass ɗin back seat ya sauka, haɗa ido suka yi da shi jiki a mace ta ɗaga hannu tana yi masa bye bye shima ya ɗan yi mata, daga haka aka rufe gate ɗin tana jin tafiyar su...cikin gida ta nufa idonta akan flowers ɗin da ta rungume a hannu, tana shiga cikin falon ta iske aunty Kubra zaune tana latsa wayarta, juyowa ta yi tana kallon Salma da ta nufe ta da ɗan murmushi, aunty ta miƙa hannu ta kama nata tare da zaunar da ita kusa da ita, tana murmushi ta ce, "Baby kun dawo." Salma ta ɗaga mata kai, aunty ta bi bouquet ɗin da ta rungume da kallo tana ta murmushi ta ce, "Yau ma sai ga mutane ne masu kama da saƙago sun shigo mani." Salma ta ɗan yi dariya tana bin kayan da suka shigo da su da kallo har da basket ɗin awaran jiya aka maido, "Ya aka yi baby na ga kaman jikin ki duk a sanyaye?" Aunty ta tambaya tana kallon ta, Salma ta ɗan yi murmushi tare da girgiza mata kai alamar ba komai, yatsanta mai sanye da zoben ta ɗago ta nuna mata, lokaci guda aunty ta ɗan zaro ido don tana ganin zoben ta gane na diamond ne, kama hannun Salma ta yi da al'ajabi ta ce, "Baby wannan ai diamond ne!" Salma na murmushi ta ɗaga mata kai a hankali ta ce, "He proposed to me." Aunty ta ƙara zaro ido tana sakin faffaɗan murmushi, Salma ta ɗauko kwalin cake ɗin ta buɗe tana nuna mata, a bayyane aunty ta karanta rubutun, ta kai hannu ta dafe ƙirji cikin nuna shauƙi ta ce, "Of course yes..." Salma ta saki dariya ganin yadda aunty ta yi maganar, sauran ledojin aunty ta shiga dubawa ta ga duk kayan ciye ciye ne iri-iri, Salma ta ɗauko ƴar jakar da bodyguard ya kawo ma Deen da suka je plaza tana son ganin miye a ciki, ƙamewa Salma ta yi bayan ta fiddo abun da ke ciki ta ga latest iphone, da sauri ta juya ta kalli aunty da itama idanunta ke akan wayar ta hau jinjina kai mamaki ya cika ta, can ta sauke nannauyar ajiyar zuciya ta ce, "Wannan hidima ai har ta yi yawa ma." Salma da duk jikinta ya gama yin sanyi ta kasa cewa komai, aunty ta ɗauko ɗayan jakar da ta gani ta buɗe ta ga akwatin zoben ne a ciki ta fiddo, bin red velvet box ɗin ta yi da kallo tana ɗan jinjina kai, kallon Salma ta yi ta ce, "Wannan ma ba ƙaramin diamond ring bane baby, daga akwatin shi da kuma yankan da aka mashi." Ita dai Salma ta bita da ido don ba sanin yadda ake gane mai tsada take yi ba, aunty ta kalle ta ta tambayi Deen ɗin ya tafi ne, Salma ta ce mata eh ya ce ma Funtua zai wuce daga nan kuma saboda ita zai je, aunty ta zaro ido kafin da sauri ta kai hannu ta ɗauki wayarta tana faɗin bari ta kira yaya Fiddausy a shaida masu kada su ji abun kwatsam, sai dai koda ta kira layin aka sanar da ita a kashe yake, Sageer ta kira shima tana ta ringing baya ɗauka ta ce yanzu haka yana wurin ƙwallo, ta ce bari ɗan anjima zata sake kiran innar ta su. Bayan sallan magrib Sageer na zaune tare da abokan shi su Aliyu a gaban gidan dake kallon nasu in da suka saba zama, hira suke suna cin awara da suka siya a wurin Imrana da shine yanzu ke yin awaran, "Kai...wannan ba kamar Salma ba?" Wani abokin su Ibrahim da ke latsa waya ya faɗa, Sageer ya ce wace Salma, nuna masa hoton Ibrahim ya yi, Sageer ya bi hoton Salma da kallo wanda sam ita bata ma san da Deen ya yi mata shi ba ɗazun a restaurant, sai dai iya gefen fuskarta ne a hoton ta ɗan sadda kanta ƙasa tana yin murmushi dogon hancinta ya fito sosai, shima Sageer ya ga kaman ita sai dai yana shakkun hakan ba kamar ganin wanda ya ɗaura hoton, ɗagowa ya yi yana miƙa ma Ibrahim wayar ya ce kawai dai kama ce amman ba ita bace, Aliyu ya miƙo hannu ya amshi wayan yana faɗin ya ga hoton, yana ganin hoton da tsananin mamaki ya ce, "Wannan tabbas Salma ce, ka duba da kyau." Amsar wayar Sageer ya sake yi yana kallo still ya kasa gasgata ita ɗin ce duk da ya ga kammani sosai, ya ce, "Ta ya za a ce Salma ce, Deen ne fa ya ɗaura hoton, shi miye tsakanin shi da ita da har zai ɗaura hoton ta." Ibrahim ya ce, "Ba tana magana da shi saboda aikin da take mashi ba, ka sani ko sun fara soyayya ne. Kuma ka duba caption ɗin hoton da kyau." Sageer ya ƙura ma rubutun jikin hoton ido wanda capital S tare da heart emoji aka saka, ƙara bin hoton ya yi da kallo lokaci guda kuma ya zaro ido da al'ajabi ya ce, "Kai wllh kuma kamar fa ita." Cike da tabbatarwa Ibrahim ya ce ai itama ce S ɗin da aka rubuta farkon sunanta ne, shi dai Aliyu yana ta bin su da ido mamaki ya sa ya kasa yin magana don ya gane ita ce, da sauri Sageer ya miƙe yana faɗin bari ya ɗauko wayarsa da ya saka caji tun da zai je ƙwallo ya kira ta....Mom Jameela na zaune saman kujera ta ɗaura ƙafa ɗaya akan ɗaya a falonta dake a 6angarenta, basu daɗe da dawowa daga airport ba rakiyar su Sapna da za su koma London bayan sun je Kano sun kwana biyu, dama saboda naɗin sarautar Deen suka zo ba daɗewa za su yi ba, waya ce a hannun mom Jameela tana latsawa yayin da daga gabanta saman c-table yankakkun fruit ne a hankali take ɗauka tana sha, lokaci guda ta tsaya cak da tauna apple ɗin da ta kai baki, yanayin fuskarta ne ya sauya zuwa alamun al'ajabin abun da take kallo, hoton Salma ne da ke ta yawo ana bayyana ta matsayin sabuwar budurwar Deen Jr. Lokaci guda ta wani kalan haɗe rai tare da sauke ƙafarta, hannunta har ɗan rawa yake don ta je ta duba idan da gaske Deen ɗin ne ya ɗaura hoton a instagram kamar yadda take ganin anata faɗa....a wani kalan zabure mom ta miƙe bayan ta tabbatar da shi ɗinne da gaske ya ɗaura hoton, fuska a yamutsa ta ƙanƙance idanu ta shiga kiran Deen, ta kai wayan kunne yayin da ta fara yin ringing tana wani cije baki tare da ɗage kai sama, ta riƙe ƙugunta da ɗayan hannun.... ✨A CIKIN RAYUWA✨ BY ZAINAB BATURE A CIKIN RAYUWA_ (Kashi na farko) ya zo ƙarshe, domin ci gaba da kashi na biyu: *₦500 – Regular WhatsApp Group* *₦800 – Special Telegram Group* *Biyaa ta:* *Sterling Bank – 0121797114* *Zainab Bature* *Tura shaidar biya:* *WhatsApp: 08169856268 09013804524* *Telegram: 08032811442* Message only. No calls please. Page 57 Wuraren magrib Deen ya isa Funtua, kaitsaye gidan hajiyar Ambasada ya nufa ba sabon gidan su ba, sosai hajiya ta nuna farin cikin zuwan nasa don bata san da zai zo ba, bayan yayi sallar magrib ya ci abinci, ɗakinsa da yake zama a bangaren hajiya ya wuce don ya huta, a lokacin ne suka yi waya da Salma ya sanar mata ya isa lafiya, don lokacin da yake hanya sau kusan ukku tana kiransa tana mashi ya hanya, a shagwa6e ta bayyana masa cewa gata nan tana ta kewansa ya rarrashe ta tare da tabbatar mata da sun kusa kasancewa tare na har abada, a lokacin ne bayan sun gama yin wayan shauƙi ya kwashe shi har ya yi posting hotonta a shafin sa na Ig. Bayan sallar isha Deen na kishingiɗe a saman gado yana latsa wayarsa, lokacin kiran mom ɗinsa ya shigo, jimm ya yi yana ta kallon kiran, a jikinsa ya ji kiran bana alkhairi bane, kaman ba zai ɗaga ba, can lokacin kiran ya kusa katsewa ya ɗan rufe ido ya buɗe tare da ɗaga kiran...ko amsa sallama da gaisuwar da ya yi mata bata yi ba, cikin ɗaga murya ta ce, "Deen! who is that girl you posted a picture of on Ig? Miye tsakanin ka da ita?" Deen ya ɗan yi shiru kafin a hankali ya ce mata sunanta Salma a Funtua take...ba tare da ta bari ya ƙarasa ba a ƙagare ta ce, "I didn't ask you all dat, mi ke tsakanin ka da ita nike son ji." Deen ya ɗan lumshe ido tare da yin shiru kaman mai shakkar faɗi mata, har sai da a ɗan fusace ta ce, "Deen are you there?" Ya ɗan sauke boyayyan ajiyar zuciya, in a low voice ya ce, "I'm in love with her...." Sagir na shiga ɗakinsu ya nufi wayarsa da ya jona caji, bayan ya ciro yana dubawa ya ga missed calls ɗin aunty Kubra, da sauri ya shiga kiranta yana a tsaye, aunty da Salma na zaune a falo sun baje abubuwan ciye ciyen da aka kawo masu har da cake ɗin suna ta party abun su, Salma ta kai hannu gefenta saman kujera ta ɗauko wayarta jin tana ringing, aunty da ke kallonta ganin ta saki faffaɗan murmushi ta tambaye ta waye, "Sageer ne." Ta bata amsa, da sauri aunty ta miƙo hannu ta ce ta bata wayar, aunty ta daga kiran ta kai kunne, kafin ta ce wani abu daga ɗaya bangaren da sauri Sageer ya ce, "Salma..." Aunty ta bashi amsa da ba ita bace, jin muryar aunty ya gaishe da ita ta amsa, tambayar ta ina Salma ya yi, aunty ta ce, "Wacece haka." ƴar dariya Sageer ya yi sanin aunty na da barkwanci ya yi tunanin wasa take masa, ya ce mata, "Salma ƙanwata dake nan wurin ki." Aunty ta ta6e baki ta ce ita bata san wata Salma ba, Sagir na ƴar dariya a ƙagare ya ce, "Aunty don Allah tana ina, wani abu nike son tambayar ta." Aunty ta ce, "Ai baka shirya yin magana da ita ba." Magiya Sagir ya fara yi mata kan ta bashi Salma, duk a tunanin shi kawai cikin barkancin ta ne take masa haka, aunty ta fahimci bai gane inda maganarta ta nufa ba, ta ce masa, "Baka ga abun da ke yawo a social media ba ne?" Sagir ya zaro ido da sauri ya ce, "Na gani, ai abun da ya sa na kira ke nan in tambaye ta, aunty da gaske ita ce Deen ya ɗaura a Ig." Aunty na murmushi ta bashi amsa da ita ce, muryarsa cike da mamaki ya tambayi aunty mike tsakanin ta da shi, aunty ta ce mi yake tunanin zai sa shi saka ta a shafin sa, Sageer ya ce, "Aunty ke nan da gaske soyayya suke?" Ta ce masa kamar haka, a ƙagauce cike da mamaki ya ce mata amma ya aka yi ta fara soyayya da shi, aunty ta ce, "Oho, nima ban sani ba." Da sauri ya ce, "Aunty don Allah tana ina, ki bata in yi magana da ita." aunty da ta kai abu baki tana taunawa ta ce, "Ita wa?" Ya ce mata Salma, "Ashe baka shirya yin magana da ita ba, ai idan maye ya ci ya manta to uwar ɗa bata mantawa, idan ka ga na bata ka yi magana da ita sai ka tabbatar da alwashin da ka sha kanta." Nan take Sageer ya gane inda maganar tata ta dosa, dariya sosai ya saka ya ce ta manta da wannan kawai don Allah ta bata, aunty ta ce, "Karyar iskanci kake Sageer, Allah idan ka ga na bata sai ka ambace ta da yadda ka sha alwashin zaka rinƙa kiranta, Sagir nata dariya ya ce to ta bata, aunty ta ce , "In ba wa?" Cikin dariya ya ce, "Yaya Salma." Aunty ta saka dariya haka Salma da duk tana sauraran su itama dariya ta ke, aunty ta miƙa mata wayan, itama ta ɗauki tata dake a gafe ta miƙe ta nufi ɗaki don yin magana da innarsu Salma.....Sageer na gama yin magana da Salma jiki na rawa ya fito waje ya koma wurin su Aliyu, cikin washe baki yake tabbatar masu da abun da suka gani gaskiya ne soyayya Deen yake da Salma har ma sun yi zancen aure, suma duk suka cika da mamaki haɗe da farin ciki, Sageer da ya kasa rufe baki yana ta dariya cike da zolaya ya ce ma Aliyu, "Kai baka yin kishi ne, an ce budurwar ka na soyayya da wani har za su yi aure amman kake farin ciki." Aliyu da ke dariya ya ce, "Hauka ma ke nan nike da zan yi kishi, an gaya maka ana kishi da irin su Deen ne, koda a ce soyayya tsakani na da ita ta yi ƙarfi ya ce yana sonta, to zan goya bayan ta koma wurin shi ne balle ma dama ba wani shiga na samu yi a wurin ta ba." Gaba ɗaya suka babbake da dariya, Ibrahim ya ce, "Gara kar ka bari kanka ya yi murfi qur'an, ko banza kai ma ka dangwali arziki." Aliyu ya ce ai shine, Sageer dai fuskarsa ta kasa 6oye farin cikin da yake ciki, sai faman jinjina kai yake shi kaɗai ya san mi yake hange idan al'amarin ya kasance, can ya ɗaga hannuwa sama yana faɗin, "Allah Amin...Ya Allah Amin al'amarin nan ya tabbata su yi aure." Duk sauran suka amsa da amin.....Bayan aunty Kubra ta kira innarsu Salma kiran ya shiga, innar ta su ta ɗauka suka gaisa, aunty ta tambayi duk ya suke kafin ta ce, "Kira na yi don in yi maku albishir." Innarsu Salma ta ce, "To Allah Ya sa mu ji alkhairi." Nan aunty ta shiga yi mata bayani tiryan tiryan tsakanin Salma da Deen, mamaki ya sa innarsu kasa yin magana na ɗan lokaci, da tsananin mamaki ta furta, "Wai Kubra da gaske kike wannan maganar? Shi jikan hajiyan ambasada ɗin ne yake son Salma?" Aunty ta ce, "Wllh yaya Fiddausy yadda kika ji na faɗa maki, abun da ya sa tun farko ban sanar maku ba na bari ne in ga abun ya kankama tukunna, to yanzu zancen da nike maki ma daga nan da ya zo nan Funtua ya wuto, kuma saboda maganar auren su zai zo kamar yadda ya ce mata." Innarsu Salma was completely Speechless, jin abun take kamar mafarki sai faman jinjina maganar take a cikin rai, "Don haka sai ku kasance a cikin shiri." A sanyaye innar ta ce to, aunty ta ce, "Yaya Fiddausy ya na ji muryarki kamar baki farin ciki." Innar su Salma ta yi dariya ta ce, "Ina farin ciki mana Kubra, kawai abun ne...sai nike ganin kaman shi ɗin ai ya fi ƙarfin Salma nesa ba kusa ba." Aunty ta ce, "A wurin mu dama haka zamu gani, amman a wurin ubangiji duk ɗaya suke, don haka fatan alkhairi zamu yi." Innarsu Salma ta ce, "Haka ne to Allah Ya tabbatar mana da alkhairin." Aunty ta amsa da Ameen, Da ɗan shakku Innarsu Salma ta sake cewa, "Amman Kubra kina ganin danginsa za su amince, ba kamar da akwai maganar aure tsakaninsa da ƴar uwarsa?" Aunty ta ce, "To ai ya ce gaba ɗaya zai haɗa ya aure su, don haka mu yi addu'a kawai yaya." Innarsu Salma ta ce to, lokaci guda ta yi murmushi tunowa da alwashin da Sageer ya ɗauka a baya, ta ce, "Sageer kuwa ya san da maganar?" Aunty ta yi saurin cewa,"Ya sani, yanzun nan muka gama waya da shi, cike da zumuɗi ya kira baby yana son tabbatar da maganar soyayyan ta su da ya gani a social media, kin san wai shi har ya manta da alwashin da ya sha, ai kuwa na ce wllh ƙaryarsa ta sha ƙarya, sai da ya kira ta da yaya sannan na bata wayar." Innarsu Salma ta yi dariya kafin ta ce, "Ni lokacin koda na saka baki a maganar nike nuna masa zai iya ganin ya kamu da son ta, kawai na yi maganar ne a zuwan wasa ba wai don ina tunanin hakan zai yuwu ba." Aunty ta ce, "Gashi kuma kin ga ya yuwun, ai abu irin wannan mutum bai cika baki tun da komai na Allah ne." Innarsu Salma ta ce hakane, "Yanzu dai yaya sai ku zama cikin shiri, ki sanar ma baban su Sageer girma ya zo za a fara aurarwa." Inna na dariya ta ce to shike nan zata sanar masa, tambayar ina Salma innar ta yi, aunty ta ce, "Gata can a falo na baro ta suna magana da Sageer, kin ga cikin ma yin party muke da abubuwan daɗi da surukin namu ya kawo mana, har nike cewa Allah sarki nesa bata maganin kusa, da kuma kun ta6a abun arzikin surukin namu...yaya baki ga fa uban hidiman da ya yi mata ba, ubansun kaya ba ƴan nan ba, bari dama duk mun ɗauki hoton kayan, zan turo ma Sageer ku gani." Fuskar Innarsu Salma cike da farin ciki ta amsa da to, bayan sun ɗan ƙara yin magana suka yi sallama. Suna gama yin waya ta shiga kiran babansu Salma, tsananin mamaki ya shiga bayan ta sanar masa zancen, ya ce mata wannan ba maganar waya bace gashi nan dawowa gidan yanzu. Tun bayan da Deen ya gama yin waya da mom ɗin sa yake zaune ya yi shiru yana kallon wuri ɗaya, kausasan kalamanta ne ke ta masa yawo a kai, dama ba wai yana tunanin zata goyi bayan tsakanin shi da Salma bane, amma duk da haka kalaman da ta yi sun tsaya mashi, wayarsa da ke ajiye gefe ya kai hannu ya ta6a yana duba lokaci, da ya bari sai gobe zai yi ma hajiya maganar da ta kawo shi garin amman yanzu yana jin zai canza ra'ayi ya je ya yi mata magana yanzu tun da ya ga dare bai yi ba sosai, sauka ya yi daga saman gadon ya nufi ƙofa walking slowly, kana ganinsa ka san jikin sa a sanyaye yake, yana zuwa corridor zai nufi ɗakin hajiya ya hango ta zaune a falo, falon ya nufo hajiya da ke zaune saman kujera, da plate ɗin yankakkan kankana a gefenta tana sha ta ɗago kai tana kallon shi, a kujerar gefenta ya zauna fuskarta da ɗan murmushi, "Ai na ɗauka ka yi bacci." Hajiya ta faɗa idonta akan sa, ya ɗan girgiza mata kai alamar a'a, tayin kankanan ta yi masa nan ma kai ya girgiza masa alamar ba zai sha ba, shiru suka ɗan yi hajiya ta maida idonta kan tv, can ta juyo ta kalle shi, ganin kaman akwai alamun wani abu a tattare da fuskarsa ta ce, "Ya aka yi ne?" Sauke idonsa ya ɗan yi, kafin ya ɗago a nutse ya ce, "Ina son zamu yi magana ne." Hajiya ta ɗaga masa kai tare da tattara duk attention ɗinta kan shi, calmly ya shiga yi mata bayani ta natsu tana sauraran sa har ya gama, ɗan murmushi ne ya bayyana akan fuskar hajiya, ta hau ɗan jinjina kai tare da ɗauke idonta daga kansa bayan ta gama sauraran maganar da ya zo da ita, duk da ta san Salma tana yi masa aiki amman ta ɗan yi mamakin yadda har soyayya ta ƙullu a tsakanin su, sai dai ta san hakan ba komai bane a wurin ubangiji, ƴar gajeruwar ajiyar zuciya hajiya ta sauke ta kalle shi ta ce, "To amman ita fa waccan da batun aure ke tsakanin ku?" Deen ya ɗago fararen idanunsa ya kalle ta a hankali ya ce, "Zan aure su tare." Ta ɗan jinjina kai, murmushinta ya ɗan fadaɗa ta ce, "Ka ce zaka kafa tarihi a family, don ba wanda ya ta6a auren mata biyu lokaci ɗaya." Shi dai ya yi shiru tare da sauke idanunsa, jimm hajiya ta ɗan yi sai kuma ta ce, "Yanzu ita Salma kun gama daidaitawa da ita ke nan ?" Ya ɗaga mata kai, "To iyayenta sun san da maganar tsakanin ku?" Ya ce mata auntynta ce ta sani wadda take wurinta yanzu a Kaduna, hajiya ta jinjina kai ta ce ta san tana Kaduna, sauke numfashi ta yi ta ce, "In dai ta yi maka kana son auren nata kuma kun fahimci juna, to mu namu fatan alkhairi ne in dai an yi bincike ba wata matsala, duk da na san Salma tana da halaye nagari, kuma iyayenta ga dukkan alamu mutanen kirki ne. Yanzu zan yi ma babanka na nan magana kan zuwa nema maka auren, kaman yaushe ka shirya kake son a saka auren naku?" Deen ya ce mata zai koma London ya ƙarasa wasu abubuwa, nan da 2 months zai dawo lokacin yake son a ɗaura masu aure, hajiya ta ɗaga kai alamar fahimta idanunta na kallon wuri daban, bayan ɗan lokaci ta juya ta ce, "Amman to su iyayenka sun san da maganar neman auren naka?" Shiru Deen ya ɗan yi kafin ya ce mata bai yi magana da dad ɗinsa kan hakan ba amman mom ɗinsa ta sani, hajiya dake kallon sa ta ce to ita mom ɗin nashi ta amince ma auren nasu, yanayin fuskarsa ne ta ga ya ɗan canza, ya ɗan yi shiru muryar mom ɗinsa ta shiga yi masa amsa kuwwa a cikin kai yayin da take faɗin kausasan kalamai akan auren sa da Salma, "....._Deen! rainin da ka yi mani har ya kai haka...ni kake faɗa ma kana son wata kuma auren ta zaka yi...bacin ka san da maganar aure tsakanin ka da Basma....ba ka isa ka haɗa Basma da wata ba wllh, idan ma mafarki kake to ka farka...wato kai ka isa ka kai tun da kana da kuɗi ko, don haka kake tunanin duk abun da ka ga dama zaka yi, to komai kuɗin ka da isarka dole ne ka bi maganar mu tun da mune muka yi silar zuwan ka duniya, ka bari idan kai ne ka haiho kanka sai ka yi duk abun da ka ga dama, amman yanzu mune iyayenka masu iko akan ka, don haka ban amince da wai kana soyayya da wata zaka aure ta ba, already ka san da kana da wadda zaka aura don haka tun da wuri ka datse duk wata alaƙa da ke tsakaninka da wannan yarinyar, kuma ina umurtar ka da ka cire hoton ta da ka ɗaura yanzun nan_!" Lumshe ido Deen ya yi tare da sauke 6oyayyan ajiyar zuciya, hajiya da ke ta kallon shi ta ce, "Ka yi shiru Deeni." Kallon ta ya yi fuskarsa ta nuna alamun damuwa ya ce, "Bata amince ba." Hajiya ta yi ɗan murmushi na dattako, duk da ana saka ma mutum ran shiryuwa daga hali mara kyau da yake yi, dama bata yi tunanin Jameela zata amince masa game da auren ba, kallon shi ta yi ganin damuwa akan fuskarsa ta ce, "Dama ba lalle ta amince maka ba, duba da matsayin waccan, ita ɗin ɗiya ce a wurinta." Deen dake kallon ta fuskarsa a ɗan yamutse ya ce, "But I told her that I would marry both of them." Hajiya da ke murmushi ta ce, "Ai hakan ba zai saka ta amince maka ba sai ma ta ji zafin hukuncin naka, mu mata ba iya kan mu muke ma kishin abu ba, namu ma muna tayawa kishi." Deen ya yi jimm sai kuma muryarsa da yanayin amo na karyewar zuciya ya ce, "Amman yakamata ta goya mani baya akan abun da nike so, bani na zabi Basma a matsayin wadda zan aura ba, hakan zabinta ne kuma na amince don in faranta mata rai, why yanzu nima bazata mani hakan ba kan abun da raina ke so don ta faranta mani." Yana ƙarasa maganar ya sauke idanunsa, hajiya ta yi shiru tana ta kallon shi jin ya faɗi abun da sam ita bata san haka abun yake ba, duk ɗaukar ta soyayya ce ta shiga tsakanin su har ta kai ga maganar aure, gashi yanzu daga yanayin yadda ya yi maganar ta so ta fahimci kamar ma baya son Basman kawai dai ya amince ma auren ta don biyayya, tirƙashi! Wane irin halin son kai Jameela gare ta da har yaranta na cikinta bata ƙyale ba, a cikin rai hajiya take jin lallai zata yaƙi son kan Jameela wurin goya ma Deen baya kan abun da ransa ke so...nannauyar ajiyar zuciya ta sauke idonta akan Deen da har lokacin kansa na a ƙasa, cikin kwantar da murya ta ce, "Kada ka damu Deeni, idan Salma matarka ce ba wanda ya isa ya hana hakan kasancewa, kuma kana da goyon bayana matuƙar an tabbatar da ba wata matsala a auran ka da ita, amma duk da haka ina so ka yi ƙoƙari wurin shawo kan mahaifiyarka ta amince maka ko don samun albarkar al'amarin." A hankali ya ɗago kai ya kalle ta tare da ɗan jinjina kai, "Shi mahaifin naka ka bari zan yi magana da shi a daren nan ma." Deen ya ɗaga mata kai, ganin still da damuwa akan fuskarsa, cikin wasa a ƙoƙarin ganin ta kawar masa da damuwan ta ce, "Ka kwantar da hankalinka angon Salma, wai ni anya ma ba daɗin awara bane ya kwashe ka har ka fara son ta, ƙarshe ka yanke shawarar auren ta yadda zata rinƙa maka awaran duk lokacin da ka so ko?" Ƴar dariya ya yi har fararen haƙoransa suka ɗan bayyana, hajiya ta ji daɗin ganin dariyar da ya yi, sai kuma ta ce, "In ba ma don ka shanye ni ba, ta ya zaka zo mani da maganar yi mani kishiya ni kuma har da goya maka baya, ƙarshe ta zo ta ƙwace mani kai." Still da ƴar dariya akan fuskarsa ya ce mata saboda tana son shi ne ya sa ta goya masa baya, kuma kada ta damu ita matar shi ce ta ƙarfe ba za a raba su ba, hajiya dake ƴar dariya ta ce da daɗin awara ya kwashe shi zai watsar da ita, jingina ya yi da kujera yana faffaɗan murmushi ya ce mata da ya je Kaduna wurinta ma ta yi mashi awaraan mai daɗi, hajiya ta ɗan zaro ido ta ce ai kuma shike nan an riga ma an ƙwace mata shi ashe har Kaduna ya je, daga yadda yanayin sa ya nuna da suna maganar Salma hajiya ta fahimci yana son ta sosai don gashi damuwar da ta bayyana akan fuskarsa har ta washe, har cikin ranta ta ji itama tana son ya auri Salma don tabbas akwai abubuwan da in ba a tare da Salma ba ba lalle ya samu a wurin Basma ba duba da irin rayuwar da ta taso a cikinta. A cikin daren kan ka ce mi labarin soyayyar Deen da Salma ya karaɗe shafukan sada zumunta, tuni abokan Sageer sun yaɗa har da yadda alaƙar ta su ta samu asali daga aiki da take masa, wasu ma ƴan nan f Funtua musamman ƴan unguwarsu da suka san ta har da sana'ar awaran da take suka bayyana, nan fa al'umma suka shiga tofa albarkacin bakin su, yawanci duk yabon Deen suke kan yadda ya iya yin soyayya da Salma ana faɗin ba lalle a samu mutumin da ya shahara kamar sa ba da zai iya yin hakan, ana ta kuma yabon kyawun Salma da yake har da wasu hotunanta abokan Sageer suka watsa, Allah dai ya taimaka ba a samu wanda ya ɗaura hoton ta a wurin tuyan awara ba, da alama babu mai hoton ne da tabbas har shi sai an yaɗa, wataƙil har da don da daddare take yin awaran ya sa ba a samun hoton ba...Fahad na zaune idonsa akan wayarsa, mamaki ne sosai bayyane akan fuskarsa yayin da yake kallon abun da ake yaɗawa a social media na soyayyar Deen da Salma, kasa jurewa ya yi ya danna ma Deen kira don ya tabbatar, lokacin Deen bai daɗe da komawa bedroom ɗinsa ba ya fito daga toilet ya ji wayan sa na ringing, bakin gado ya nufa ya ɗauka a inda ya ajiye ta, ɗan murmushi ya yi ganin mai kiran, yanke kiran ya yi shi ya kira tare da hayewa saman gadon, bayan Fahad ya ɗauka suka gaisa Deen ya yi masa ya karatu, Fahad ya amsa mashi tare da tambayar yadda kowa yake a nan, duk da kwanan sa biyu da komawa India, ƴar magana suka yi kafin ya ji Fahad ya ce, "I want to ask about something." Deen ya gyara zama tare da furta ok he should go ahead, Fahad Ya ce, "Abun da na gani yana yawo social media is it true?" Ɗan murmushi Deen ya yi ya ce, "Yea." Shiru Fahad ya yi irin na mamaki ya kashe mutum, after few seconds ya ce, "Amman ya aka yi hakan ya kasance tsakanin ka da ita?" Deen ya ce masa kawai ya ji ya fara son ta kuma auren ta yake son yi, ɗan shiru Fahad ya yi kafin ya ce, "Ita kuma wadda maganar aure ke tsakanin ku fa?" Deen na murmushi ya ce zai aure su ne su duka, "Do you think it is as easy as you think?" Deen ya bashi amsa da in sha Allah zai iya handle na su, Fahad ya ɗan yi shiru can ya furta, "Allah Ya tabbatar da alkhairi." Deen ya amsa da Ameen, ƴar hira kaɗan suka yi Fahad ya yi masa sallama, ba ƙaramin mamaki Fahad ya yi ba jin da gaske ne, a ganin shi mi Deen zai yi da wannan yarinyar wadda har yanzu shi ɗaukar mara kunya yake mata, a ganin shi tausayi da taimakon da ta nuna akan Habu bai isa ya goge wanccan halin nata da ya bayyana ba. Mom Jameela ta ji kamar zuciyarta zata yi bindiga sakamakon ganin bayyana Salma da aka yi a mai tuyar awara, ji take Deen ya gama zubar masu da mutunci a idon duniya ya ƙasƙantar da su, sam ta kasa zama sai pacing up and down take a cikin ɗaki, Leemarh ce ta shigo cikin ɗakin jikinta sanye da kayan bacci tana riƙe da wayarta, mom Jameela ta juyo tana kallonta da fuskarta da ke a murtuƙe, ganin yanayin ta ya sa Leemarh shan jinin jikinta ta kasa furta abun da ya kawo ta, cikin ƙuncin rai mom ta ce ya aka yi ta zo ta kafe ta da ido, da ƙyar ta furta, "Dama zuwa na yi in nuna maki abun da ke ta trending...wai yaya Deen yana soyayya da wata mai awara kuma wai auren.." Wata uwar tsawa mom ta kwatsa mata ta ce, "Fita ki bani wuri Leemarh!" Leemarh ta yi saurin juyawa ta fita daga ɗakin, daga yanayin mom ɗin ta gane ta san da abun da ta je nuna mata...Dad ya shigo cikin ɗakin mom da sallama, nufo ciki ya yi idanunsa akanta kamar yadda itama ta juyo tana kallon shi, a bakin gado ya zauna ya ce, "Mi yake faruwa ne, kin kira ni kina son gani na kuma kamar hankalin ki a tashe..." Katse shi ta yi a fusace ta ce, "Ya hankalina ba zai tashi ba, ba ka ga abun da yake yawo akan Deen ba a social media?" Dad ya ɗan yi shiru yana kallon ta, shima ya gani kuma hajiyarsa ta kira sa sun yi magana kan neman auren yarinyar da yake, sauke numfashi dad ya yi cikin kwantar da murya ya ce, "Na gani, amman ni ina ganin wannan ba wani abun tashin hankali bane ai, tun da ya ji ya gani yana son yarinyar, sai mu yi masa fatan alkhairi." Wani matsiyacin kallo mom take wurga masa ta yamutsa baki, cikin ƙulewa ta ce, "Ke nan kai a wurin ka wannan ɗin ba abun tashin hankali bane? Ana yaɗa ɗan ka na soyayya da ƴar matsiyata mai tuyan awara hakan ne ba wani abu ba?" Dad ya yi ɗan murmushi ya ce, "To Jameela in dai an tabbatar yarinyar bata da wata illa da zata hana a aure ta ai hakan ba wani abu bane, kuma tuyan awara wannan ai sana'a ce ba bara aka ce tana yi ba, neman halak ne." Wani kallon mamakin baka za ci mutum zai faɗi abu ba ta shiga bin dad da shi, cike da 6acin rai fuskarta ta yi wani jajir ta ce, "Maganar in an tabbatar bata da illa kake yi, bacin illa a tattare da ita a bayyane take, yarinyar da ke tuyan wara a titi tana caccafkewa da kowani gardi ita ce zamu amince ɗan mu ya aura? Kuma da kake maganar sana'a, ai ni ban ga sana'a ba a yin wara face tambarin faƙiranci, kuma wllh ba zan ta6a amincewa ba Deen ya auri ɗiyar matsiyata, bama ita ba a duk Funtua ba sa'ar auren shi!" Still dad ya yi yana ta kallonta fuskarsa ta nuna alamun irin mamakin mutum, wai Jameela ce ke faɗin ɗanta ba zai auri ɗiyar matsiyata ba, ko ta manta ita yadda aka auro ta, gara ma ita wadda Deen ke so suna ƙoƙarin neman na kan su, ba kamar ita ba da babu abun da suka saka a gaba lokacin ban da garari, gani dad ya yi idan ya biye ta ransa ne zai 6aci hakan ya sa shi miƙewa yana faɗin, "To ni dai a wurina sana'a komi ƙanƙantar ta sana'a ce, kuma bata daga cikin abun da zai saka a ƙi auren mutum, don haka in dai an yi bincike akan yarinyar an tabbatar babu wata matsala a tare da su da zata sa a ƙi auren ta to ni ba zan ƙi amince masa auren ta ba." Yana kai wa nan ya nufi hanyar barin ɗakin, a masiface mom ke faɗin ai dama ta san tun da ƴar Funtua ce ba zai taba ganin illar ta ba, to wllh sai dai idan ba ranta zai auri yarinyan nan, dad dai bai bi ta kanta ba ya yi tafiyarsa, hakan kuma da ya yi ba ƙaramin ƙara ƙular da ita ya yi ba, ta kai zaune bakin gadon fuska a hautsine, wata irin tsanar Salma take ji a ranta irin tsanar da bata tunanin ta ta6a yi ma wani ita, mai wara Deen zai aura? Kai ina...wllh over her dead body! Ke nan ma so ake duk burinta akan auren shi da Basma ya tashi a banza, kuma ta san muddin ya auri wannan ɗiyar matsiyatan to sai sun handame komai na shi, ƙarshe ta zo ta haifa yara rankacabai don irin su ba control ɗin haihuwa gare su ba, wannan tunanin ya ƙara dugunzuma hankalin mom, ita mamakinta yadda aka yi ma Deen har ya faɗa soyayya da yarinyar, abun da ta ga an wallafa kan sanadiyar alaƙar su ne ya shiga dawo mata, tunanin tabbas da walakin goro a miya ne ya zo mata, lokaci guda ta gasgata zuciyarta kan ba haka nan suka bar Deen ba asiri suka yi masa, ta hanyar yin amfani da kusancin da yarinyar ta samu da shi, dama idan mutum na yin abu sai ya ga kowa ma na aikata abun, nan take mom ta yarda da zarginta, a ranta take raya aikuwa ba zata tsaya kallon ruwa ba kwaɗo ya yi mata ƙafa, zata nuna masu iyakar su...hannunta har ɗan rawa yake ta ɗauki wayarta ta fara kiran Amminsu.... ✨A CIKIN RAYUWA✨ BY ZAINAB BATURE ZEELALUH✍️ Page 58 Duk abun da ke faruwa su Sapna ba su sani ba saboda suna a halin tafiya, washe gari da rana Basma ta tashi daga baccin gajiyan tafiya ta yi wanka, bayan ta gama shiryawa cikin ƙananun kaya ta zauna tana latsa wayarta, a lokacin ne ta yi arba da zancen soyayyar Deen da Salma, tashin hankali sosai ya bayyana a fuskarta, jiki na rawa ta sauka daga saman gadonta ta nufi ƙofar fita, part ɗin Sapna na nan saman bene ta nufa, bata iske ta a falo ba kai tsaye ta wuce bedroom ɗinta, tana shiga ta ganta a kwance saman lafiyayyan gadonta tana bacci, nufar ta Basma ta yi ta rankwafa murya na rawa ta shiga kiran sunanta tana ɗan bubbuga shoulder ɗinta, a hankali Sapna ta buɗe idanuwanta masu ɗauke da bacci ta bita da ido, ganin yanayin fuskarta cikin muryar bacci ta ce, "Baby, what happened?" Kamar jira Basma ke yi ta tambaye ta kawai ta fashe mata da kuka, Sapna ta ɗan wara ido kafin da sauri ta fara yunƙurin tashi zaune, kamo Basma ta yi ta zaunar da ita tare da manna ta jikinta, da alamun tashin hankali ta ce mi yake faruwa ne ta sanar mata, hannu na rawa ta miƙa mata wayarta, Sapna ta kafe screen ɗin wayan da kallo with a little shock, can ta ɗago ta kalli Basma da ke ta kuka a hankali, kan Sapna ne ya ɗaure ta shiga tunanin da gaske ne Deen na soyayya da yarinyar kuma auren ta zai yi kamar yadda ta gani, to mi hakan ke nufi bacin ya san da maganar aure tsakanin shi da Basma? Kamar Basma ta san mi yake yawo a ran mom ɗin nata, tana kallonta cikin kuka ta ce shike nan hakan na nufin ya Deen ya fasa auren ta, ko dai dad ɗinta ne ya ce mashi ba zai aura masa ita ba shine ya samu wata, wannan maganar tata ta ja hankalin Sapna ta fara tunanin ko da sa hannun Maleek a faruwar hakan, rarrashin Basma ta yi ta ce ba lalle idan labarin gaskiya ne, amman bari ta je wurin dad ɗin nata ta ji idan ya san da hakan, ta sauko daga saman gadon itama tana sanye da ƙananun kaya da suka amshi jikinta sosai...kai tsaye 6angaren Maleek dake a nan sama ta nufa, tana shiga ta iske shi zaune a falo yana operating laptop dake a saman table ɗin gaban shi, ya ɗago kai yana kallon ta with a smile yayin da ta nufe shi, daga gefen shi ta zauna ya maida idonsa kan screen yana faɗin, "Har yanzu gajiyan hanyan ce bai sake ki ba, na shiga ai bada jimawa ba na iske kina ta bacci." Ta ɗan yi murmushin da iyakar sa lips ɗinta, jin ta yi shiru ya juyo ya kalle ta suka haɗa ido, cikin nuna kulawa ya ce, "Ya aka yi ne?" ta ɗan gyara zama kafin ta ce, "Ka ga abun da ke trending a social media?" Ya ɗan yi shiru yana mata kallon rashin fahimta, ya ce "Kan mi kike magana?" Wayar Basma da ta taho da ita ta miƙa masa, bin wayar ya yi da kallo kafin ta ga ya yi ɗan murmushi a nutse ya ce, "Na gani tun ɗazu." Sapna da ta kafe shi da ido ta ce, "So...is it true?" Maleek ya miƙo mata wayar yana faɗin, "Ku san hakan, don na ga posting ɗin da Deen ya yi na picture ɗin yarinyar before ya cire." Ya ƙare maganar yana ci gaba da latsa system ɗin gaban shi, fuska a jagule Sapna ta ce, "Amman ta ya zai yi hakan, ya san da maganar aure tsakanin shi da baby...ko kai ne ka goya masa baya?" Ɗan faffaɗan murmushi Maleek ya yi ba tare da ya kalle ta ba ya ce, "Sai na goya masa baya, kuma don akwai maganar aure tsakanin shi da ita shine ya zama bai da right ɗin son wata mace?" Sapna ta yamutsa fuska ta ce, "Amman itama gashi wai auren ta zai yi." Maleek ya ɗan ta6e baki ya ce, "In ma hakan ne a ganina ai ba laifi bane, ko kin manta mata nawa addini ya yardar masa ya aura." Sapna ta yi shiru tana kallon sa duk ranta ba daɗi, don gani take kamar Maleek ya 6oye mata ne amman da sa hannun shi a lamarin, bayan ɗan lokaci Maleek na ci gaba da latsa laptop ya ce, "Ni I'm very happy for him in dai auren yarinyar zai yi, dama haka yakamata ya samu wata nutsattsiya ya aura...tun da ita ta zabi lalata rayuwarta." Kana ganin yadda ya ƙarasa maganar zaka gane da ciwon abun a zuciyarsa, Sapna ta yamutsa fuska kamar zata yi kuka ta ce, "Honey ta bari, baby is a changed person now, ina tare da ita koda yaushe keeping an eye on her, tun da ka ce baza ka amince da auren ta da Deen ba ta daina aikata hakan gaba ɗaya, da kanta ta yi mani rantsuwar tun lokacin bata sake aikatawa ba kuma na yarda da ita." Maleek ya yi shiru idonsa akan screen, kamar ba zai ce komai ba can ya ɗan sauke gajeruwar ajiyar zuciya murya ƙasa ya ce, "Allah Ya sa da gaske ta bari." a hankali Sapna ta ce in sha Allah ta bari, jin ta yi shiru bayan ɗan lokaci ya juyo ya kalle ta, ganin damuwa duk ta bayyana a kan fuskarta ya ɗan yi murmushi ya ce, "Kada ki damu kan ki, tun da Deen ɗin ba cewa ya yi ya fasa auren ta ba, I think zai haɗa su biyun ne ya aura and I'm okay with it." Sapna ta yi zuru tana kallon shi kawai. Bayan sallar la'asar daddy Sa'ad ya zo gidan hajiya kamar yadda ta buƙaci ganinsa, a falo suka zauna ya gaishe da ita cikin ladabi, hajiya na murmushi ta tambaye sa iyalinsa shima da murmushi ya ce mata duk suna lafiya sun ce a gaishe ta ta ce tana amsawa, Balaraba ta sa ta kawo mashi abun sha mai sanyi, bayan ya sha a nutse hajiya ta ce sai ya ji kira tana neman shi, daddy na murmushi ya ce eh Allah Ya sa kiran na alkhairi ne, hajiya ta ɗan yi shiru idonta ƙasa still da murmushi fuskarta, ta ce, "In sha Allah, dama aiki ne ɗan ku Deen ya kawo maku." Daddy ya ɗago yana kallon ta da ɗan alamun rashin fahimta, ta ɗan juyo ta kalle shi ta ce, "Na zuwa nema masa aure." Faffaɗan murmushin da ta ga daddy Sa'ad ya yi, ya sa ta ce, "Ka ma san da maganar ko?" Daddy ya ɗan gyara zama a nutse ya ce mata ya ga maganar dai a kafafen sada zumunta amman bai da tabbacin ko gaske ne, hajiya ta ɗan jinjina kai ta ce mashi da gaske ne, "Ma sha Allah, a ina ita yarinyar take ne?" Daddy ya tambaya, hajiya ta ce, "A nan makwabta suke, ku san a nan gidan ma suka fara haɗuwa da ita, ana aiko ta kawo mani awara, sune masu yin awaran da ake aikawa can gidan." Daddy ya jinjina kai still da murmushi fuskarsa ya ce eh ya ga har da maganar sana'ar da ita yarinyar ke yi aka yaɗa, hajiya ta kai hannu ta kama ha6a da alamun mamaki ta ce, "Yanzu har sana'ar tata aka watsa, ni da yake kwana biyu na rage shiga kafofin sada zumuntan saboda ido." Daddy ya jinjina mata kai ya ce aikuwa har da sana'arta duk an yaɗa, hajiya ta ce, "Kai amman dai mutane kamar basu da aikin yi da komai sai an watsa yanar gizo." Daddy na ƴar dariya ya ce dama in dai mutum ya shahara to kuwa komai da ya shafe shi sai an watsa a idon duniya, hajiya ta ɗan jinjina kai ta ce Allah Ya sa mu dace, daddy ya amsa kafin ya ce, "Yanzu auren ta za a je nema masa, an yi bincike kan yarinyar da iyayen ta ne?" Hajiya ta ce ta ɗan fara yin bincike akan ahalin yarinyar amman ba mai zurfi ba, sannan a sanin da ta yi ma yarinyar tana da halaye masu kyau don ku san ma hakan ne ya sa Deen fara yin hulɗa da ita, sannan suma iyayen yarinyar a ɗan binciken da ta yi an tabbatar mata da mutanen ƙwarai ne, nan ta bashi labarin abun da ya faru game da marigayi Habu wanda har yayi sanadiyyar da Deen ya ba ita yarinyar aiki, daddy Sa'ad ya hau jinjina kai tare da faffaɗan murmushi a kan fuskarsa, daga labarin sai ya ji Salma ta burge shi, hajiya ta ce yanzu abun da ya kamata sai su ƙara yin bincike akan su idan an tabbatar ba wata matsala sai su fidda lokacin zuwa nema masa auren, daddy ya amsa sai kuma ya ce, "To ya maganar ita ɗayar ta can in da yake da aka ce akwai maganar aure a tsakanin su?" Hajiya ta ɗan yi shiru kafin ta ce ya ce duk su biyun zai haɗa ya aura, daddy ya jinjina kai ya ce Allah Ya tabbatar da alkhairi, tambayar game da mahaifin Salma ya yi da in da gidan su yake, hajiya ta kwatanta masa tare da faɗi mashi sunan mahaifin yarinyar Malam Bashir Kafinta wanda ɗa ne ga marigayi Alhaji Maikuɗi Kafinta, daddy ya ce kamar ya so ya san sunan kakan nata, hajiya ta ce ai tsohon babban kafinta ne a garin kafin Allah ya yi masa rasuwa, ta yi masa kwatancen inda garejin su yake daddy ya ce ya gane wurin, daga haka suka aje magana kan daddy zai kara yin bincike akan su kafin a je neman aure. Kwanan Deen biyu a Funtua ya shirya komawa Abuja, sai da ya ji kaman daga nan ya wuce direct Uk don ya san idan ya koma ba za su kwashe ta da daɗi ba da mom, sai dai dole ya koma can kafin ya wuce London...aikuwa abun da yake gudun ne ya faru, yana isa bayan la'asar tun a babban falo mom ta tarbe shi da masifa, ta in da take shiga bata nan take fita ba, tana ƙara tabbatar mashi da ba zai auri Salma ba, idan kuma ya ga ya aure ta sai dai idan bayan ba ranta, kuma ko bayan ba ran nata ya aure ta bata yafe ba, har tana cewa idan ma wasu ne suke ɗaure masa g*ndi suke sa yake ganin zai auri yarinyar to ya sani a matsayinta na mahaifiyarsa ba zata ta6a amincewa ba, ta ƙara jaddada mashi kan komai kudin da yake da su a ƙarƙashin ikon su yake, dole ne kuma ya bi umarnin su matsayin su na iyayensa..shi dai Deen kansa na a ƙasa, kalma ɗaya kawai ya furta mata ita ce ta yi haƙuri, duk su Leemarh suna jin faɗan da mom ɗin ke yi masa don duk suna a falon sun fito tarbar shi, hatta dad yana zaune ya haɗe hannunwansa tare da ɗaura ha6arsa, fuska a kwa6e yake bin mom da kallo bai dai ce mata ƙala ba, kuma ya san gogar zananta kan suwa ta yi, itama mom ɗin tun da ta fara sababin nata bata kalle shi ba don ma kada ya ce zai taka mata burki...sosai Leemarh ta ji tausayin yayan nata ya kama ta, fuska a yamutse take bin mom da kallo, ita dama neutral ce bata ji tana so ko ƙin auren shi da Salma ba, kawai dai ta yi mamakin jin yana soyayya da kamar Salma...haka mom Jameela ta ƙaraci bala'en ta ta juya ta nufi barin falon ko ina na jikinta na amsawa sakamakon yadda take yin tafiyan a fusace, shiru ne ya mamaye wurin na ɗan lokaci, su Leemarh nata kallon yayan nasu da kansa ke a ƙasa, bayan ɗan lokaci dad ya sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da ɗaura idanunsa kan Deen, yama rasa mi zai ce masa, cikin kwantar da murya ya ce, "Allah Ya kyauta. Ka je ka samu ka huta ka sha hanya." Slowly Deen ya ɗago kai ya kalli mahaifinsa ba tare da ya ce komai ba, sai da Leemarh ta ƙara ce mashi, "Ya Deen ka je ka huta." Ya ɗan yi murmushin ƙarfin hali ya miƙe ya nufi stairs walking slowly, kana ganin yadda yake yin tafiya kasan jikinsa a sanyaye yake....bayan ya isa part ɗinsa, a edge ɗin gado ya zauna tare da dunƙule hannuwansa ya ɗaura forehead ɗinsa sama, idanunsa a rufe yayin da maganganun mom ke ta masa yawo, ya kasa gane taƙamaimai dalilinta na ƙin auren sa da Salma, idan don Basma ne itama ai ya ce zai aure ta, wani 6angare na zuciyarsa ya shiga raya masa wataƙila Basma kawai take son ya aura, ya raya hakan na nufin shi bai da ƴancin da zai so wata ke nan saboda Basma? gashi a koda yaushe jin son Salma yake na ƙaruwa a zuciyarsa..ya ɗauki ɗan lokaci a haka ba tare da ya san taƙamaimai tunanin da zai yi ba, miƙewa ya yi ya nufi toilet, after some minutes ya fito waist ɗinsa ɗaure da farin towel ƙar, da wani short a hannu yana goge sumarsa ya nufi closet, farar singlet da short ya sako ya dawo cikin ɗakin ya nufi gado ya kwanta, ya ɗage kansa saman pillow tare da lumshe idanunsa, tunanin Salma ya shiga yi don koda yana a hanya sun yi waya da ita, slowly ya buɗe idanunsa jin an dan yi knocking ƙofar ɗakin tare da buɗewa, Leemarh ce ta shigo idanunta akan shi ta nufo cikin ɗakin, daga gefen gadon ta tsaya fuskarta da alamun ƴar damuwa ta furta, "Ya Deen..." Yana ta kallon ta ya yi mata ɗan murmushi tare da yi mata alamun ta zauna da hannu, a bakin gadon ta zauna tana kallon shi, ya tambaye ta da wani matsala, ta ɗan girgiza masa kai ta yi shiru, can ta ce, "Pls ya Deen I'm sorry kan abun da mom ta yi maka, wllh ban ji daɗi ba." Ta ƙarasa maganar kaman zata yi kuka, shiru ya yi yana ta kallon ta kafin ya yunƙura ya tashi zaune tare da jingina da gadon, calmly ya ce, "Nagode....amman ke miye ne ra'ayin ki kan hakan?" Leemarh ta sauke idonta ta ɗan yi shiru, ɗagowa ta yi ta kalle shi ta ce, "Ni kawai ina son ka auri sis Basma don tana son ka sosai, ta shiga damuwa saboda wannan da kake so yanzu, ko jiya da muka yi magana da ita har kuka ta yi." Deen ya ɗan yi shiru, a hankali ya ce, "I will marry them both." Ta ɗan jinjina kai sai kuma ta ce, "Hakan ya yi, in dai kana son ita wannan ɗin nima ina goyon bayan ka aure ta." Deen yay sigh ya ce, "Yea, I love her so much...but mom bata amince in aure ta ba." Leemarh ta ɗan yamutsa fuska tace, "Ina ganin kaman saboda sis Basma ne, ka faɗa mata su duka zaka aura?" Deen ya ɗaga mata kai alamar eh, ta ɗan yi shiru kafin ta ce, "Ban san mi ya sa bata son ka aure ta ba duk da haka....is it because they are not rich ko kuma don tana a garin su dad?" Ta ƙare maganar da sigar tunani, Deen ya bita da kallo, sai da ta yi maganar sannan hankalinsa ya fara kaiwa ga tunanin tabbas zai wuya ba ɗaya daga cikin wannan dalilin da Leemarh ta faɗa bane yasa bata son ya auri Salma. Da daddare bayan sallan isha Deen ya shigo falon dad ɗinsa kamar yadda ya buƙaci ganinsa ta hanyar kiran sa a waya, dad dake zaune saman lafiyayyan kujeran falon ya ɗaga kai yana kallon shi har ya ƙarasa ciki, yana ƙoƙarin zama a saman carpet dad ya nuna masa kujera ya ce ga wuri nan ya zauna mana, bayan ya zauna ya kalli dad a nutse ya yi masa barka da dare, dad na murmushi ya amsa masa, gyara zama dad yay ya fara magana, "Dama dalilin kiran ka da na yi, ina son na tambaye ka ne game da ita yarinyar ta Funtua..." A hankali Deen ya sauke kansa, dad ya ci gaba, "Da gaske ka tabbata kana son ta da aure?" Deen ya yi shiru kuma bai ɗago ba, dad yana ɗan murmushi ya ce, "Kai nake sauraro son, kana jin kunya shine har da ɗaura ta a shafin ka, sannan ka je wurin hajiya ka bayyana mata tsakanin ka da ita har da maganar aure." Deen ya ɗan ɗago ya kalli Dad da ɗan murmushi, dad ya ɗage masa gira ya ce ya bashi amsar tambayar da ya yi mashi, slowly ya furta eh yana son ta da aure, dad ya jinjina kai ya ɗan yi shiru, ƴar ajiyar zuciya ya sauke ya ce, "Shike nan, Allah Ya zaba mana abun da yake alkhairi. Ka kwantar da hankalin ka, in dai an yi bincike an tabbatar da ba wata matsala dangane da ita ni kana da goyon bayana akan auren ta. Yanzu jibin zaka koma can London ɗin?" Deen ya ce masa eh, "Hajiya ta ce nan da wata biyu ka ce kana son a ɗaura maku aure?" Deen ya ɗaga masa kai idonsa akan carpet, "To ita yar'uwar taka da ka ce duka zaka aure su, ke nan tare za a ɗaura maka auren da su lokaci guda ko kuwa ya ka shirya?" Deen ya ce mashi haka ya yanke shawara amman sai idan ya koma London zai yi magana da daddy Maleek, dad ya ce, "Ok, komi ke nan yadda kuka yi sai ka sanar mani, yanzu dai ka ce mu fara shirin shan biki kawai." Deen ya kalli dad yana murmushi, shima dad ɗin kallon sa yake yana murmushi, tausayin ɗan nasa yake ji har cikin ransa, ba kamar da hajiya ta faɗa masa cewa ashe Basma ba za6in ransa ba ce, kawai ya yi ma mahaifiyarsa biyayya ne ya amince da auren ta, hakan ne ya sa dad jin yana son goya masa baya akan wannan da yake so, "Amma...mom bata amince mani ba." Dad ya tsinkayi muryar Deen ya faɗi haka, kallon shi dad ya yi, daga yanayin fuskar ɗan nasa ya gane hakan na damun sa sosai, dad ya ɗan yi shiru kafin ya gyara zama ya ce, "Kada ka damu, zan yi ƙoƙarin shawo kanta in sha Allah." Deen ya jinjina kai feeling a bit relieved don ya san da yawan lokutta idan ta botsare akan abu dad ɗin na shawo kanta, bayan shiru na ɗan lokaci dad ya ce mashi idan ba wani abu shike nan zai iya tafiya, da alamun jin daɗi Deen ya ce, "Thank you so much dad for supporting me." dad ya yi ƴar dariya ya ce, "Kada ka damu, duk abun da kake so matuƙar bai sa6a shari'a ba kana da goyon bayana...kuma wannan kamar tarihi ne ke maimaita kansa, sai dai akwai in da bana son a kai" Dad ya ƙarasa yana dariya, Deen ya ɗaga kai yana kallon mahaifin nasa shima yana yin ƴar dariya don ya gane inda maganar tashi ta dosa, daga baya dad ya saka masa albarka suka yi sallama ya miƙe ya nufi hanyar fita idon dad akan sa, ɗage kai dad ya yi bayan Deen ya fita, maganganun da mom Jameela ta yi ɗazun na dawo masa, a ganinsa kalaman nata sun yi tsauri, kuma shi ya kasa gane wani irin son kai ne da ita, ta san ita ta matsa kan son ya auri Basma ya amince ba don son ransa ba sai don yi mata biyayya, yanzu ya zo ya nuna yana son wata amma firr ta ƙi ta amince masa, ai koda bata so yakamata ta amince masa don ta faranta masa rai kan biyayyar da ya yi mata, tunanin hanyar da zai bi don ya shawo kanta ya shiga yi, don dole akwai buƙatar amincewar ta matsayin ta na mahaifiyarsa ko don samun albarka a cikin al'amarin. Bayan kwana biyu Deen ya koma London, lokacin daddy Sa'ad ya yi duk wani bincike da ake yi da ya danganci neman aure, cikin sa'a ba a samu wata matsala da zata iya hana auren ba, sai ma yabo da shaida mai kyau da aka yi ma ahalin malam Bashir. Ba ƙaramin farin ciki iyalin suka shiga ba bayan da aka sanar da su zancen neman auren Salma da za a zo a ranar juma'a mai zuwa, gaba ɗaya ganin abun suke kamar mafarki ba gaske ba, Sageer ya fi kowa yin farin ciki tamkar zai zuba ruwa a ƙasa ya sha, ji yake kamar ya juya ya ciji kunnansa don daɗi, a yadda aunty ta shirya za su taho Funtua kafin ranar Friday don a yi shirin tarbar baki da ita, to sai baban su Salma ya ce ba a nan gidan za a tarbe su ba, a gidan yayan shi Alhaji Sani nan za a sauke su, kuma Alhaji Sanin ya ce a bar mashi duk wani shirin tarbar su can za su yi, hakan ya sa aunty ta bari sai ranar juma'a ɗin za su taho. Duk abun nan mom bata san da maganar za a je neman auren Salma ba, don ba yadda dad bai yi ba ya rarrashe ta ta amince ma auren amma ta rantse ta maya ba zai auri yarinyar ba. A can London kuwa bayan Deen ya koma ya samu daddy Maleek da maganar haɗa auren Basma da Salma, amman daddy ya ce mashi ya ci gaba da shirin auren Salma yanzu ita Basma ya bari za su yi magana daga baya, sosai Basma ta nuna masa tashin hankali bayan ya koma, tai ta yi mashi kuka akan Salma, ya samu ya rarrashe ta tare da sanar da ita cewa tare zai aure su, hakan ya ɗan sa hankalinta ya kwanta, dama ita ba wani zafin kishi ta sani ba saboda a irin rayuwar da ta taso, ita dai dama burinta kawai Deen ya aure ta. Rana bata ƙarya...ranar juma'a bayan an taso daga sallar juma'a daddy Sa'ad da kawu Hamida suka isa gidan yayan baban su Salma wato alhaji Sani, gidan ba laifi yana da ɗan kyau don Alhaji sanin ya fi baban su Salma wadata, a sitting room ɗin gidan aka tarbe su da abubuwan ci da sha, kuma daidai gwargwado an yi ƙoƙari, Alhaji Sani da wani ɗan'uwan su malam Lawan suka tarbe su, cikin mutuntawa da girmama juna aka gaggaisa daga baya suka shiga gabatar da abun da ya kawo su kamar yadda ake yi a al'ada, su daddy Sa'ad suka ce bayan neman aure har da saka rana suke so a yi idan zai yuwu, alhaji Sani ya bayyana farin ciki ya ce idan ma har da auren suke son a ɗaura a nan take su ba matsala a wurin su, cike da nuna jin daɗi su kawu Hamida suka yi godiya, nan suka bayyana nan da wata biyu suke son a saka auren amma ba sai an tsaida rana ba saboda yanayin aikin Deen, yadda suka tsara idan Allah Ya kaimu nan da wata biyun sai a kira rana kawai, su Alhaji Sani suka nuna amincewa da hakan, daga baya su daddy Sa'ad suka bada goro mai yawa da suka zo da su, sai kuma kuɗi miliyan ɗaya matsayin kuɗin neman aure da sauran abubuwan da ake kawowa na saka biki, wanda kuɗin daddy Sa'ad ne ya bada su don basu buƙaci komai ba daga wurin Deen ko mahaifinsa, bayan gama saka ranan daddy Sa'ad ya isar da saƙon da hajiya ta bashi na cewa ba a buƙatar komai da ya danganci kayan ɗaki, wannan magana ba ƙaramin daɗi ta yi ma su alhaji Sani ba, nan sukai ta yi masu godiya da addu'oin ƙarin girma da arziki, har da mahaifin su daddy Sa'ad da ke kwance ƙasa wato anbassador sai da ya sha addu'oi, bayan kammala saka ranan suka matsa masu sai da suka ɗan ci abubuwan da aka tanadar masu don da sun ce a ƙoshe suke ruwa da lemu kawai za su sha. Bayan tafiyar su daddy Sa'ad, alhaji Sani da malam Lawan suka kwashi goron da kuɗin da aka kawo a motar alhaji Sani suka nufi gidan su Salma, a nan cikin baranda aka yi shimfiɗa duk mutanan gidan suka zo suka gaishe da su, daga baya malam Lawan ya shiga yi masu bayanin yadda suka yi da su daddy Sa'ad, suka nuna masu goron da su Sageer suka shigo da su tare da basu kuɗin da aka bada, kowa ka gani a wurin bakinsa ya ƙi rufuwa tsabar farin ciki, sai ma da alhaji Sani ya sanar da su zancen ba a buƙatar komai na kayan ɗaki, wayyo daɗi! Farin ciki ne ya ƙara cika su, innarsu Salma har da ƙwallan daɗi, shima baban su sai faman murmushi yake yi yana ƙara godiya ga Allah, ana cikin haka sai ga su Aunty Kubra sun shigo, su Imrana suka saki ƙarar murnar ganin yayar su, da gudu suka nufo ta, Salma ta wara masu hannu tana ta dariya, jikinta ta sha gayu da ɗaya daga cikin abayas ɗin da Deen ya kai mata, jaka da takalman ƙafarta ma duk na cikin kayan ne da suka hau da rigan, sai ta yi kamar wata tauraruwa tsabar yadda ta yi kyau, Sageer ya nufo ta yana washe baki, yana zuwa gabanta ya kama hanci yana yin guɗar shaƙiyanci, duk ya saka mutane dariya, ya rungume Salma yana faɗin, "Welcome amaryarmu." Aunty Kubra na tsaye bakin baranda riƙe da hannun Imrana da Hamza, jikinta ta sha doguwar rigar leshi mai ɗan banzan kyau, ta yi wayayen ɗaurin kallabi yayin da idanuwanta ke sanye da bakin glasses da ya matukar ƙawata fuskarta ya ƙara fito da haskenta, ta kai hannu tana cire glasses ɗin tana amsa sannu da zuwan da innarsu Salma ke yi mata da fara'a, ƙarasawa suka yi cikin barandar tuni har baban su Salma ya yi mata shimfiɗa, ta zauna da faffaɗan murmushi suka shiga gaisawa da baban su Salma da su alhaji Sani suna yi mata an zo lafiya, Sageer ya ƙaraso cikin barandar yana riƙe da hannun Salma da ke ta bin kowa da kallo tana sakin murmushi, cire hannunta ta yi a na Sageer ta nufi innarsu, innar nata sakin faffaɗan murmushi tana kallon ta ta ce, "Salma.." Ta ce, "Na'am innarmu.." Ta faɗa jikin mahaifiyar tata tana murmushin daɗi don duk ta yi missing ɗin su, innarsu ta ɗago ta suka zauna, ta kalli baban su da ke ta kallon ɗiyar tashi fuskarsa cike da farin cikin ganin yadda ta canza, Salma ta gaishe da babanta tare da su alhaji Sani, duk suka amsa mata da fara'a suna kiran ta da amarya, ta yi saurin sauke kanta ƙasa tana ɗan murmushi, bayan gama gaishe gaishe innarsu Salma ta ce ma aunty ai sun yi zaton ganin su tun ɗazu, aunty ta ce mata wllh sun ɗan samu delay ne a motor pack basu taso da wuri ba, "Aunty ai da kawai kin tuƙo ku a motar ki." Sageer ya faɗa, tana murmushi ta ce har yanzu tsoron yin dogon driving take duk da daga Kadunan zuwa nan ba wani nisa sosai amman tana tsoron hawa babbar hanya, Auwalu da ke zaune a tudunkar baranda ya ɗan rankwafa kai yana gaishe da ita, ta amsa tare da ambaton sunan sa, alhaji Sani ya ce masu to su dai suna ganin za su tafi yanzu, aunty ta kalli kayan dake gefe ta ce, "Ko har baƙin ma sun zo?" Alhaji Sani ya ce mata eh har lokaci an saka, nan ya yi mata bayanin komai har da kayan ɗaki da aka ce ba a buƙata, tsabar daɗi aunty bata san lokacin da ta rangaɗa guɗa ba a wurin, duk aka saka dariya, cike da zolaya baban su Salma ya ce ashe wannan gajeran hancin nata zai iya guɗa haka, aunty ta juya tana kallon Salma da ta raku6e gefen innarsu, tana murmushi ta ce, "Babyna an zama amarya..." Da sauri suka ga ta miƙe ta shige cikin ɗakin innarsu duk suka yi dariya, "Ma sha Allah, Allah shine abun godiya, wllh tsabar farin ciki ji nake kamar na zuba ruwa ƙasa in sha...Allah Ya tabbatar mana da alkhairi ya nuna mana lokacin...Alhamdulillah, baby kam sai son barka don ta cika mai sa'a wllh." Aunty ta faɗa tana ta faman washe baki, Alhaji Sani ya ce, "Tabbas, don haɗa zuria da iyalan marigayi Ambasada ba ƙaramar sa'a ba ce, to bare kuma auran shi yaron, ban da ɗaukakar da Allah ya yi masa, ko'ina ana shedarsa da halin kirki, ai ba abun da zamu yi ma Allah sai godiya, Allah Ya kai mu lokacin da rai da lafiya." Duk aka amsa da Amin, malam Lawan ya ɗan gyara zama ya ce, "Ina son zan ɗan bada wata shawara....ina ganin zai fi a rufe al'amarin nan a bar shi iya dangi kawai, a bari koda za a bayyana sai lokacin ya zo, don yanzu rayuwar ta zama abun tsoro, kai kana zaune da kowa lafiya baka riƙi kowa da wata mummunar manufa ba, amman wani yana nan ba wanda yake jin haushi irin ka, kasancewar ka lafiya da ɗan rufin asirin da Allah Ya yi maka su suke ci masa tuwo a kwarya, wani kuma lafiya lau kuke da juna, amman wani abun arziƙin na samun ka sai wutar hassada ta ruru a zuciyarsa, har ta kai ya kasa jurewa ya fara neman yadda zai raba ka da abun ta ko wane hali, shiyasa yake da kyau a koda yaushe mu kasance muna masu yin addu'ar neman tsari da hassada..." Kowa ya amince da shawaran kawu Lawan, alhaji Sani ya bada misali da yadda akai ta yayata zancen soyayyar Salma da Deen a kafafen sada zumunta da maganganun da mutane sukai ta yi na nuna mamakin yadda ya iya yin soyayya da ita ana faɗin sana'ar da take yi, aunty Kubra ta juya ta kalli Auwalu da Sageer ta ce, "Kun ji ko, maganar saka ranar auren ta tsaya iya nan, kada wanda ya yaɗa a social media har sai Allah Ya kaimu lokacin." Duk suka ce ba zasu yaɗa ba, ta kalli Imrana da Hamza ta ɗan kama kunnanta alamar gargarɗi ta ce, "Ku ma kada wanda ya sake ya faɗa ma wani cewa an saka ma yayar ku Salma ranar aure!" Duk suka ɗaga kai suka ce ba zasu faɗa ba, daga haka su yaya Sani suka yi sallama, baban su Salma ya yi saurin cewa to ai ko abinci ba su ci ba, alhaji Sani ya ce kada ya damu duk a ƙoshe suke sun ci abinci a can gida kafin su taho, baban su Salma ya ce duk da haka nan ma yakamata su ci tun da saboda su aka yi, aunty ta yi saurin cewa a zuba masu sai su tafi da shi, innarsu Salma ta yi saurin miƙewa ta nufi kitchen, baban Salma ya ce to su ɗebi goron da aka kawo wanda za su yi amfani da shi, Sageer da Auwalu ne suka kai masu goron da abincin da aka zuba masu a coolers masu kyau zuwa mota, koda baban su Salma ya yi masu magana kan su ɗauki wani abu cikin kuɗin da aka kawo suka ce a'a wannan nasu ne su yi amfani da su wurin fara shirye shiryen bikin, aunty tace bikin da an ce ba a buƙatar komai, alhaji Sani na murmushi ya ce dole ai za a yi wasu hidindimun na kuɗi, da ƙyar suka amshi wani abu a cikin kuɗin matsayin na sauran abubuwan saka rana da za a siya, aka rako su har waje ana ƙara masu godiya suka tafi....bayan sun dawo cikin gida, cikin wasa baban su ya ɗan ɗaga murya yana faɗin, "Ina amaryar tamu ta shige ne?" Duk aka yi dariya, "Mamana kina ina?" Ya faɗa idonsa akan ƙofar ɗakin innarsu don ya san tana ciki, fitowa Salma ta yi kanta a ƙasa tana ɗan murmushi, ta tsaya daga gaban baban nasu ba tare da ta kalle shi ba, ya kai hannu ya matso da ita ya ɗan yi mata side hug, ya ce, "Duk kunya ce mamana." Salma ta noƙe kai bata ce komai ba, "Na taya mu murna sosai, Allah Ya sa alkhairi, Allah Ya nuna mana." Duk aka amsa da amin, ya kalli innarsu ya ce, "A kawo masu abinci suma tun da suka zo ko ruwa basu sha ba." Ta yi saurin amsawa tare da nufar kitchen aunty tana faɗin ai da yake ma ba wata yunwa suke ji ba, ya nuna ma Salma wuri ya ce ta zauna su ci abinci, yana ta kallonta ta nufi gefen aunty ta zauna, "Amman Kubra mi kike ba ɗiyar nan taki ne haka, ma sha Allah ta canza sosai, har girma ta ƙara." Aunty ta saka dariya kafin ta ce wani abu Imrana ya yi saurin cewa, "Fuskarta ma har ƙyalli ƙyalli take yi." Hamza ya ce kuma ta saka kaya irin na an indiyawa, duk aka saka dariya, aunty ta ce wannan duk aikin kayan gyaran fatan da angon nata ya kawo mata ne har da rigan ma, nan aka jere masu kayan lafiyayyan abincin da aka yi, farar shinkafa da lafiyayyan miya da ta ji nama, sai coleslaw da kuma peppered chicken har da lafiyayyan kunun aya da lemunan roba....bayan sun gama cin abincin aunty ta fiddo masu da tsaraban da suka yi kafin ta saka aka kai masu kayan su ɗakin Salma da tuni innarsu ta gyara shi, dama duk aunty ta zo a ɗakin babyn nata take sauka...haka iyalin suka kasance cikin farinciki sosai a wannan rana, da daddare bayan sallan issha nan suka baje cikin baranda har da baban su Salma da ya dawo da wuri ana ta hira cikin nishaɗi suna ciye ciye, Sageer sai cin goron saka ranar yake yana faɗin duk da baya cin goro ya zama dole ya ci wannan don na musamman ne, aunty da ke zaune jikinta sanye da doguwar rigar shan iska da hula itama goron take ta ci duk da bata ci tana faɗin ai cin wannan goro a gare ta ya zama wajibi, baban su Salma ya ce masu ɗazun bayan sallan magrib ya je gidan hajiyar ambasada ya yi mata godiya, aunty ta ce itama kuwa yakamata ta je, baban ya ce har kuwa tana tambayar Salma ya sanar mata da sun zo, aunty ta ce bari sai su je tare, Salma ta miƙe itama tana sanye da doguwar rigar bacci ta nufi ɗakinta, bada daɗewa ba ta fito hannunta riƙe da abu ta nufi innarsu ta zauna a gefenta, da murmushi ta ce, "Innarmu gashi, dama ke ce baki da waya android." Innarsu ta amshi wayan wadda tsohuwar samsung ɗin Salma ce da bata yi komai ba kamar sabuwa, tana murmushi ta kalli Salma ta ce to ta gode Allah Ya saka da alkhairi Ya ƙara ma rayuwa albarka, Sageer ya yi saurin cewa, "Amman dai kin san ni yakamata ki ba wayar nan, don tun lokacin da aka baki na nuna ina son ta." Aunty ta ce baƙin ciki zai ma innar tasu shi bai siya mata ba kuma an bata zai ce shi yakamata a ba, Sageer na dariya ya ce ba baƙin ciki zai mata ba yana nufin shi a bashi wannan sai ita ya bata tashi, Salma ta ɗan harare shi ta ce mi zata yi da wannan tsohowan wayar tashi da ta gama jin jiki, hannu ya kai zai rankwashe ta, da sauri aunty ta ce, "Wllh ahir ɗin ka Sageer, yanzu ba da bane, ka san dai waye zata aura in ka ci masa zalin mata ba ƙyale ka zai yi ba duk da kana yayanta, dama gashi yana da wasu gabza gabzan bodyguards da ni kai na lokacin da ya zo sai da na tsorata da na gan su." Duk aka yi dariya, baban su ya ce, "Ato kuma mu ba ruwan mu, ban da ma kuɗin yin belin ka idan aka kama ka." Sageer dai ya yi shiru yana kallon su yana dariya, a cikin ransa yana jinjina irin yadda Allah Ya ɗaukaka kanwar tasa, abun ka da uwa, innarsu tana murmushi ta miƙa ma Sageer wayan ta ce mashi gata ta bashi sai ya bata tashi ɗin, da sauri ya girgiza kai ya ce mata wasa fa yake, cikin kwantar da murya ta ce, "To ka amsa, ai ni na ce na baka, sai ka bani takan." Duk idanun kowa na akan Sageer da ke girgiza mata kai alamar ba zai amsa ba, aunty Kubra ta ce, "Koda yake ka ma cancanci a baka fa, don kai ne ka ɗaura hoton da ya yi silar ƙulla soyayyan." Sageer ya saki dariya don Salma ta faɗa mashi hakan, kuma ya gane hoton, shine ya yi mata shi kuma ba tare da saninta ba, lokacin innarsu ta gama taya ta tsafe mata kai an sharce shi, yana zaune gefe yana latsa waya ya yi mata hoton, shima lokacin hoton ya yi masa kyau sosai shine har ya ɗaura a status...sai da innarsu ta matsa masa duk su aunty suka saka baki sannan ya amsa tare da yi mata godiya, aunty ta amshi wayar shi tana dubawa ta ce, "Wayan taka ma ai ba wani tsufa ta yi ba, kawai glass ɗinta ne da ya ɗan tsattsage, kuma ai kaman ma akwai screen guard ko?" Sageer ya ce mata eh, dama ba ainihin wayan shi bace, wannan bai daɗe sosai da canza ta ba, kuma Salma ta san ba waccan tashin bace kawai sharrin ta ne data ce wayan tsohuwa ce, aunty ta ce gobe idan Allah Ya kaimu zata bashi kuɗi sai ya je a cire wannan screen guard ɗin a saka mata wani, sannan ya canza mata cover don wannan ta jiki innar tasu ba lalle ta ji daɗin amfani da wayan da shi ba, Sageer ya ce a'a lafiya lau ba sai ta bashi kuɗi ba zai kai a yi duk abun da ta ce, wayar Salma ce ta fara yin ringing duk suka kai idanunsu kanta, ta sadda kai tana kallon wayan wanda Deen ne ke kiran ta, "Mamana ba kiran ki ake yi ba?" Baban su ya faɗa, ta kasa bashi amsa kuma bata ɗago ba, aunty na murmushi ta ce, "Hala angon ne?" Salma ta ƙara sunne kai, baban su ya yi murmushi ya ce to ta ɗauka mana, ƙoƙarin miƙewa ta fara yi cike da jin kunya zata wuce ɗaki, Sageer ya kai hannu ya ɗan buge ta a jiki yana faɗin gulmamma wai su zata nuna ma ita mai kunya ce, baban su ya ce mashi ba dai zai kiyaye ba ko, aunty ta ɗan ɗaga murya tana ce ma Salma ta faɗa ma Deen cin zalin da Sageer yake mata, ita dai ta nufi ɗakinta ta shige....ba ƙaramar soyayya suka sha ba ta waya ita da Deen, sosai ta saki jiki har sai da ta ji inama ta janyo wata biyun bikin su..... A Cikin Rayuwa Book 2 is ₦500 for the Regular WhatsApp Group and ₦800 for the Special Telegram Group. Payment via Sterling Bank (0121797114, Zainab Bature) Send payment evidence to WhatsApp: 09013804524, 08169856268 or Telegram: 08032811442. Message only, no calls please. ✨A CIKIN RAYUWA✨ BY ZAINAB BATURE ZEELALUH Labarin na tafe da sabon salo mai matuƙar ban mamaki, kada ku bari a ba ku labari🔥 Page 59 Washe gari bayan sun gama yin break fast, wurin ƙarfe sha biyu saura suka shirya zuwa gidan hajiyan ambasada, aunty ta ci gayu da Abaya mai kyau, ta yi rolling veil ɗinta, fuskarta ta saka glasses da ta riga ta yi sabo da sakawa, Salma ma ta saka doguwar rigar atamfa, har da innarsu za a je itama ta saka doguwar rigar atamfa, lokacin da suka isa falon hajiya tana zaune bata daɗe da fitowa ba, bayan Balaraba ta gama gyara falon, sai ƙamshi ke tashi, hajiya ta ɗaga kai tana amsa masu sallama da ɗan murmushi, bayan sun ƙarasa ciki ta yi masu maraba tana kallon su ta nuna masu wurin zama, cikin girmamawa su aunty suka gaishe da ita ta amsa tana ta murmushi, sai da ta ɗaura idonta akan Salma da ke gaishe da ita sannan ta gane ta, ta ce "Ashe amaryarmu ce..." Ta yi maganar tare da miƙa ma Salma hannu, Salma ta taso ta iso gabanta kanta a ƙasa tana murmushi, hajiya ta zaunar da ita gefenta tana kallon ta ta yi mata an zo lafiya, Salma ta amsa da lafiya lau still kanta na a ƙasa, ɗagowa hajiya ta yi ta kalli innarsu Salma ta ce, "Ai farko ban gane ku ba sai da na ga Salma, duk ya yaran." Innarsu ta amsa da suna nan lafiya lau, hajiya ta ce masha Allah kafin ta ɗaura idonta akan aunty Kubra da ta cire glasses ɗin fuskarta tun shigowarsu, "Ita wannan ban gane ta ba." Hajiya ta faɗa tana ta murmushi, innarsu Salma ta ce ƴar'uwarta ce ita ce Salma ke wurinta a Kaduna, hajiya ta ɗaga kai tare da furta, "Allah Sarki, an zo lafiya." Aunty ta amsa mata da lafiya lau da murmushi, hajiya ta maida kallon ta kan Salma ta ce, "Ƴar kunya muka koma ne Salma da aka kasa kallo na, bayan kin saye mani zuciyar miji sannan zaki zo kina kunya ta" Duk su aunty suka yi dariya, ta ƙara cewa, "Ya Kadunan?" A hankali Salma ta ce lafiya lau, ɗan shiru suka yi kafin hajiya ta ce, "An tsaida lokaci kuma, Allah Ya sa alkhairi Ya nuna mana." Aunty ce ta amsa da Amin Ya Rabb, kafin a nutse ta sake cewa, "Dama zuwa muka yi mu yi godiya hajiya kan hakan da kuma abun arziki da aka yi mana na cewa ba a buƙatar kayan ɗaki, mun gode ƙwarai, Allah Ya saka da alkhairi Ya ƙara girma da arziƙi." Murmushi ne akan fuskar hajiya ta amsa da Amin, ta ce, "Ai ba wani abu bane, dama shi angon ne ya ce baya buƙatar komai, don da an ɗaura aure zai tafi da ita can in da yake, anan kuma gidan shi da zasu rinƙa sauka idan sun zo akwai komai, to babu wani amfanin yin kayan ɗakin." Duk suka jinjina kai, bayan ɗan shiru hajiya ta kalli aunty da murmushi ta ce, "Ke a Kaduna kike zaune ke nan, duk ya yara da maigida." A hankali aunty ta ce, "Eh a can nike aiki.." Daga haka ta yi shiru, innarsu Salma ta ce, "Da yake Allah bai bata haihuwa ba." Hajiya ta ɗan girgiza kai da ɗan nuna jimami ta ce, "Allah Sarki, komai lokaci ne, in da rabo za a samu in sha Allah." Innarsu Salma ta ce, "Haka ne...saboda matsalan ma ba auren yanzu." Hajiya ta hau girgiza kai tana kallon aunty da kanta ke a ƙasa, duk da bata ɗago kai ba kana kallon ta zaka gane maganar innarsu Salma ta saka ta a damuwa, cikin kwantar da murya hajiya ta ce, "Haka Allah yake ikonSa, idan ya so sai ya jarabi bawa ta kowacce hanya, ba don kuma baya son sa ba sai don ya jaraba imaninsa. Ki ci gaba da haƙuri, in sha Allah a gaba zaki haɗu da rabon da Allah Ya tanadar maki sakamakon imani da kika yi da ƙaddaran da ya aiko maki." A hankali innarsu Salma ta ce in sha Allah, aunty ta ɗago kai da ɗan murmushi ta ce, "Nagode sosai hajiya." Hajiya ta ce ba komai kafin ta ce an bar su ba a kawo masu ko ruwa ba, innar su Salma ta ce ai da yake ma rana bata yi ba sosai, hajiya ta ƙwala ma Balaraba kira, bayan ta fito bakin kitchen hajiya ta ce ta kawo ma baƙi ruwa da lemu ta amsa da to tare da juyawa, dawowa ta yi hannunta riƙe da tray ta ɗauro bottle water guda biyu da lemuna sai cups, sai da ta ƙaraso cikin falon suka haɗa ido da Salma da ta ɗago tana kallon ta da murmushi, bayan ta ɗaura tray ɗin a saman table ta ɗago tana kallon Salma da faffaɗan murmushi ta ce, "Salma an dawo.." Hajiya ta juyo tana kallon Salma ta ce, "Amaryar mu ce ta zo gaishe da kishiyarta da ta ƙwace ma miji." Salma ta sunne kai tana dariya, itama Balaraba dariyar ta yi ta ce ma Salma an zo lafiya ta amsa mata, "Ma sha Allah, sai na ga har ta canza." Balaraba ta faɗa tana ta kallon Salma, hajiya ta ce, "Eh, ba laifi har girma ta ɗan ƙara tubarkalla, gashi da gani auntyn tata kayan daɗi take bata, sai sheƙi take yi tun ma ba a ɗaura auren ba, wannan idan ban yi da gaske ba sai ta raba ni da shi gaba ɗaya." Duk suka yi dariya aunty na faɗin a'a baza ta yi haka ba don duk aje a dawo da tsohuwar zuma ake magani, Balaraba ta zuzzuba masu lemu, bayan ta ɗago hajiya ta tambaye ta ta gama abinci ne, ta ce a'a ta dai kusa, kallon Salma ta yi ta ce, "Salma an saka rana kuma, Allah Ya nuna mana." Salma ta yi shiru tare da sauke kai ƙasa, su aunty suka amsa da Amin daga haka ta nufi komawa kitchen, hajiya ta ce, "Haka Allah ke ikonSa, a nan gidan suka fara haɗuwa, gashi soyayya ta ƙullu har ana maganar aure." Duk suka yi murmushi, "Ya kuke da ita auntyn tata?" Hajiya ta tambaya idonta akan innarsu Salma, innar ta gane aunty Kubra take nufi, ta ce, "Da babanta da nawa uwa ɗaya uba ɗaya suke." hajiya ta jinjina kai ta ce alaƙa ce ma ta kusa sosai, ta sake cewa, "Ke nan itama ƴar nan ce?" Innar su Salma ta ce, "Eh a nan aka haife ta, amman iyayenta a Kaduna suke zaune, a can mahaifinta ya yi aiki, mahaifiyarta kuma Allah Ya yi mata rasuwa, sai itama yanzu nurse ce tana aiki a can Kaduna." Hajiya ta jinjina kai tare da furta, "Ma sha Allah, Allah Ya ƙara taimako Ya jikan mahaifiyar tata." Duk suka amsa da Amin, bayan ɗan lokaci hajiya ta ce, "Gashi muna ta magana ban san sunan ki ba." Aunty dake murmushi ta ce sunanta Khadija amman Kubra ake kiranta, hajiya ta ɗan jinjina kai ta ce, "Ki ce mai babban suna ce, sunan mahaifiyata ke nan Allah Ya jiƙan rai." Duk suka haɗa baki wurin cewa Amin tare da yin addu'ar rahama a gare ta, daga haka suka yi mata sallama za su tafi, ta ce ba za su tsaya su ci abinci ba an kusa gamawa, duk suka ce sun gode, kallon Salma ta yi cikin wasa ta ce, "To ke kin zo ke nan ko, ba sai an sha wahalan kawo mana ke ba." Salma ta sunne kai tana murmushi, miƙewa hajiya ta yi ta ce masu tana zuwa ta nufi hanyar ɗakinta, bada jimawa ba ta dawo hannunta riƙe da wata ƴar babbar leda, ta miƙa ma innar su Salma ta ce gashi nan a ba mamanta ta yi amfani da su, suka haɗa baki wurin yi mata godiya ta ce ba komai ai an zama ɗaya, daga haka suka yi sallama suka miƙe za su tafi, hajiya ta tambayi Salma ta zo ke nan har biki ko zata koma, aunty ta ce eh zata barta anan amman zata koma Kadunan kafin bikin sai ta dawo idan lokacin ya yi, hajiya ta jinjina kai ta ce to Allah Ya kai su lokacin da rai da lafiya, duk suka amsa daga haka suka tafi, hajiya ta bi aunty Kubra da kallo yayin da suka nufi ƙofa, a ranta take raya in baya ga wulaƙancin wasu mazan yanzu wannan koda bata haihuwa ai mutum ya zauna da ita yadda take tubarkalla mace har mace sai dai daman wasu basu iya samun dama ba. Bayan sun koma suka duba abun da hajiya ta ba aunty kubra, suka ga tsadaddan lace da kuma atamfa ne, sosai aunty Kubra ta ji daɗin kyautar ta kuma yaba da kirkin hajiya. Ranar lahadi aunty Kubra ta shirya komawa Kaduna, sosai ta ji zata yi kewan babynta don ba tare za su koma ba kamar yadda ta sanar da hajiya, sai bikin ya matso zata je can ta ƙara shirya ta, duk da ta faɗa ma innarsu bata buƙatar wasu magungunan gyara sosai saboda shekarunta, amman ta taho mata da maganin sanyi mai kyau da zata rinƙa sha, duk da ba wai ya bayyana tana da shi bane, sai dai a cewar aunty wani lokacin ba a gane yarinya tana ɗauke da shi sai bayan an yi aure, a zo ai ta fuskantar matsala a mu'amala daga yin aure, sannan kuma ta ce ma innar su a rinƙa bata abinci mai kyau da kayan itatuwa, itama Salma sosai ta ji har ta fara kewan auntyn tata. Bayan tafiyan aunty da kwana biyu, da daddare Salma na gaban wardrobe tana shiryawa da kayan bacci wayarta ta fara ringing, bayan ta gama saka hula akanta ta nufi bakin gado inda wayan ke ajiye, gabanta ne ya ɗan faɗi ta yi jimm tana kallon screen ɗin bayan ta ga wanda ke kiran ta wato Dr Hisham, sun ɗan kwana biyu basu yi magana da shi ba, duk da bata san ko aunty ta yi mashi wata magana ba, kamar ba zata ɗauka ba, can dai ta yi ƙarfin halin yin picking tare da zama a bakin gado, daga ɗaya 6angaren ta ji yayi mata sallama cikin nutsattsiyar muryar shi, a hankali ta amsa ta ji ya ce, "Salmah.." ta ce, "Na'am..ina yini, ya aiki." Ya amsa da Alhamdulillah, kafin ya tambayi yadda take da ƴan'uwanta ta ce mashi lafiya lau, shiru suka ɗan yi ta ji yay sigh ya ce, "Dama na kira ne in maki Allah Ya sa alkhairi, aunty ta sanar da ni an saka bikin ki." Salma ta ɗan runtse ido tare da ɗan cije baki, sai ta ji kamar ta yaudare shi, ta ji ya ce, "Salmah are you there?" Da ƙyar ta ce, "Uhm.." ya ce, "Ya aka yi kika yi shiru, ko baki son Allah Sanya alkhairin nawa?" Da sauri ta ce a'a sai kuma murya na ɗan rawa ta ce, "Don Allah Ka yi haƙuri..." Tana jin ɗan sautin guntun murmushin da ya yi ya ce, "Kin yi mani wani abu ne?" Ta ɗan yi shiru sai ta ji kaman da biyu ya yi maganar, ta ce, "Da..ban aure ka ba." Wani murmushin ya ƙara yi calmly ya ce, "Kada ki damu, ai na san wani baya auren matar wani, kuma aunty Kubra ta faɗa mani dama kina tare da shi kina mashi aiki daga baya soyayya ya shiga tsakanin ku, ni I'm very happy for you da irin mijin da zaki aura, duk da I won't hide it from you...na matuƙar son na mallake ki matsayin mata, amman na ɗauki ƙaddara, Allah Ya sa hakan ya fi zama alkhairi, yanzu kin zama kamar sister ɗina ta jini, in sha Allahu da mu za a yi bikin idan Allah Ya kaimu." Lokaci guda Salma ta ji hawaye sun ciko idonta, ita kanta ta san Dr Hisham na son ta sosai, amman ta rasa yadda aka yi ta kasa bashi damar auren ta, duk da daga baya har cikin ranta ta yanke zata aure shi ko don ganin aunty Kubra na son ta da shi, to kuma sai ga yadda abu ya zo ya kasance tsakanin ta da Deen, wataƙila dama shi ne Allah Ya ƙaddaro zai zama mijin ki shiyasa ma har kika kasa bashi damar auren naki, wata zuciyar ce ta raya mata hakan, Dr Hisham ne ya ƙara kiran sunanta ta amsa, jin yanayin muryarta ya ce, "Kada ki da mu kin ji." Ta ɗan ɗaga kai ta ce, "To...nagode." Ya amsa da, "Yauwa, bari in bar ki ki yi bacci, ki gaishe mani da angon naki and everyone at home, gud nyt." Daga haka ya kashe wayar, Salma ta bi screen ɗin da kallo, duk sai ta ji ba daɗi, jiki a sanyaye ta kai kwance tare da lumshe ido. Ranar Friday lokacin sati guda da saka auren Salma, bayan sallan juma'a suna zaune a cikin baranda dukkan su suna cin abinci har da baban su, bayan Salma ta gama ta kalli innarsu ta ce, "Wai inna an daina yin awara ne." Innar su ta ɗan yi murmushi ta ce, "Muna yi, wai na ga an saka biki ma ci gaba da yi kuwa." Salma ta ɗan tura baki tana murmushi kafin ta ce, "To mi zai sa a daina innarmu." Sageer da ya tura abinci ya ce, "Kawai sai a ga ana wata awara bacin an san wanda zaki aura." Salma ta juya ta yi mashi wani kallo ta ce, "To abun kunya ne yin awaran, kuma ba sana'a bace, sannan ai dama kowa ya san sana'armu ce ko." Kallon innarsu ta yi ta ce, "Don Allah Innarmu a ci gaba da yi, kar ki biye ma Sageer, tun da ai dai neman halak ne." Sageer ya sake cewa, "To in ma sana'a ce ba a iya canza wata, salon dai ja ma mutane surutu." Salma na mashi wani kallo ta ce to ita sana'ar awaran mi ta yi, kuma dai ai duk sana'a sana'a ce, kallon baban su dake ta sauraran su yana murmushi ta yi ta ce, "Don Allah babanmu dan an yi awara abun kunya ne, ba sana'a bace?" Yar dariya ya yi ya ce, "Haka ne mamana, sana'a sana'a ce, kuma ta fi yin roƙo ko maula, kawai shi abun da na fahimci yake nufi shine saboda wanda zaki aura shiyasa yake ganin kamar abun kunya ne idan aka ci gaba da yi, to sai dai kuma ai ba kowa ya san da an saka bikin ba, kuma dalilin hakan ba a ce a daina yin sana'a ba tun da ba kan shi zamu maida ɗawainiyar mu ba." Salma ta gyaɗa akai alamar ato, "Dama ai na san goyo mata baya zaka yi, amman dai ci gaba da yin wata awara ja ma kai ƙasƙanci ne." Yana rufe baki Auwalu ya ce, "Ita awaran ba ita ce ku san ta yi sanadiyyar haɗuwar ta da shi ba, kuma ai an san da ana yin sana'ar awaran amman hakan bai sa an ƙi amincewa ya aure ta ba." Salma ta yi ma Sageer gwalo, ta juya cikin marairaicewa tana ce ma innarsu don Allah su ci gaba da yin sana'ar su kar ta biye ma Sageer shi dama ɗan ƙarya ne, ya kai hannu zai ɗauki takalmi babansu ya yi saurin dakatar da shi ta hanyar ce mashi bai ji gargaɗin da aka yi mashi ba akan bugunta ko, Sageer ɗin ya mike yana faɗin kowa zata aura hakan ba zai hana shi hora ta ba idan ta yi mashi iskanci, ƙarshe innarsu ta amince kan zata ci gaba da yin awaran, ta ce ma Salma amma ba ita ce zata rinƙa yi ba sai dai Imrana da Hamza su ci gaba da yi. Tun bayan tsaida lokacin auren Deen dad ke tunanin ta yadda zai sanar da mom Jameela, da shi ya yanke ba zai sanar mata ba har sai bikin ya zo, amman hajiya ta ce masa ya sanar mata don tana da hakkin ta sani matsayinta na mahaifiyarsa, a cewar hajiya gara ta sani yanzu akan sai lokacin ya zo, hakan zai fi yi mata zafi ta ga an yi mata ba daidai ba, amman idan ta sani yanzu sai ya yi ƙoƙarin yadda zai shawo kanta ta amince. Ranar asabar lokacin sati guda da kwana ɗaya da saka bikin, wurin ukkun rana lokacin dad na gida ya nufi part ɗin mom Jameela, tana hakimce a saman kujera a falonta hannunta riƙe da waya, kallo ɗaya ta yi ma dad ta maida idonta akan wayan, a kujeran kusa da ita ya zauna, fuskarsa da murmushi ya ce, "My queen, hutawa ake.." shiru kaman bazata tanka shi ba, can ta ɗago manyan idanunta ta kalle shi tare da ɗage masa gira, yana murmushi ya ce ya yi kyau, shiru na ɗan lokaci kafin ya ce mata dama yana son za su yi magana ne, nan ma sai da ta ɗan ɗauki lokaci kafin ta kalle shi a taƙaice ta ce, "I'm all ears." Dad ya gyara zama tare da ɗan yin shiru kamar mai tattaro ƙwarin gwiwar yi mata magana, daga yanayin shi ta fahimci kaman abun da zai faɗa yana da nauyi, hakan ya sa ta maido hankalinta gaba ɗaya kansa ta kafe sa da idanunta masu kaman na macijiya, a nutse ya fara magana, "Dama ina son sanar dake ne cewa....an saka ranar auren Deen." Dumm mom ta ji kanta ya yi, ta bishi da kallo with shock and confusion, yamutsa fuska ta yi, "Wani Deen ke nan?" Ta tambaya, dad ya ɗan gyara zama don bai hango zata kar6i abun ta sauƙi ba, "Muna da wani Deen ne bayan ɗan mu?" Mom ta wani kallan buɗa ido tare ɗan karkata kai alamar mamaki ya kashe mutum, "Deen ɗana ne aka saka ranar auren sa ba tare da sani na ba?" Dad ya ce, "Amman ai kin san da maganar yana son yarinyar da aure ko." Ta wani kalan juya kai, kallon shi ta yi a zafafe ta ce, "Wllh wasa ne, ba wanda ya isa ya nuna mani iko da ɗan dana haifa, raina ni ma aka yi da har wai za a saka masa rana ba tare da sani na ba, to wllh ƙarya ne....ba wani isasshe da ya isa ya tsaya mashi ya auri yarinyar nan matuƙar ni ce mahaifiyarsa." Ta ƙare maganar tare da buga hannun kujera da ƙarfi, dad ya yamutsa fuska don ya fahimci inda maganar ta ta dosa, da ɗan amon 6acin rai ya ce, "Wai mi yake damun ki ne Jameela? Yaron nan ya nuna yana son yarinyar, kuma an yi duk wani bincike akanta an tabbatar tana da halin kirki, kuma suma iyayenta mutanan kirki ne, to akan minene zaki ƙi amince masa aurenta?" A fusace ta ce, "Akan bana son shi da yarinyar, saboda na riga na zaba masa mata, wllh muddin ina numfashi bashi da matar aure ban da Basma, kuma ita kaɗai ce matarsa a duniya don ita kaɗai ce na yarda tana son shi tsakani da Allah kuma bazata mallake mani ɗa ba, duk wata mace da zata so Deen ni na san ba tsakani da Allah bane, saboda arziƙi da ɗaukakar sa ne, don haka ban haifar ma kowace mace shi ba balle a cutar mani da shi ko a raba ni da shi." Dad ya yi gwale yana bin ta da ido, sai ya ji maganganun nata kamar izna ne a gare sa, sauke ƴar ajiyar zuciya ya yi ya ce, "Ke ta ya kike da tabbaci ita yarinyar ba tsakani da Allah take son shi ba? Jameela kada ki zama mai son kai saboda wani dalili naki mara hujja, idan ita Basma za6in ki ce, mi yasa shima ba zaki goya ma zabin shi baya ba ko don ki faranta masa saboda biyayyar da ya yi maki?" Ta wani kaɗa kai ta ce, "Ko mi zaka ce Ibraheem ba zan amince masa ya auri wannan ƴar matsiyatan ba wllh, ni ce na ɗauki cikin sa, na haife sa kuma na raine sa har ya girma, don haka ina da ikon in ce ga abun da nike so akan sa da wanda ban so musamman abun da nike ganin zai cutar mani da shi..." A ɗan fusace dad ya katse ta da faɗin, "Saboda kema hakan aka yi maki? Ki faɗa mani ke kin ta6a nuna kina son abu aka hana ki?" Ta kaɗa baki ta ce, "Ibraheem, yanzu magana ake ta ɗana, da kuma muradina akan sa." Dad ya ce, "Da kike ta wani maganar ɗan ki, ai ina ce bake ce kaɗai kika haife sa ba, don haka nima a matsayina na mahaifinsa da nike iko da shi ina goyon bayan zabinsa, muddin yana son yarinyar to sai ya aure ta, saboda nima ba a hana ni aure wadda nike so ba." mom Jameela ta saki wata bazawarar dariya ta ce, "Da aka kasa dai yin nasarar hana ka auren wadda kake so, sannan aka amince maka." Dad ya hau ɗan jinjina kai yana mata wani kallo cike da 6acin rai, nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, cike da 6acin rai ya ce, "Kin faɗi gaskiya, shima ki jira ki ga yadda hakan zata kasance akan sa, ai dama duk abun da ka yi will definitely come back to you." Yana kai wa nan ya miƙe ya nufi barin ɗakin, mom ta bisa da iso, sosai maganarsa ta ƙarshe ta dake ta, mi yake nufi da hakan? tunanin baya ta shiga yi lokacin da aka hana ya aure ta, yadda suka shiga suka fita har sai da ta aure shi, ke nan hakan zata iya kasancewa akan itama yarinyar, su shiga su fita har sai ta auri Deen, dama tun farko tana zargin cewa ba haka nan suka bar Deen ba, ta hanyar asiri suka yi nasarar saka soyayyarta a zuciyarsa....ina!! Sam bazata sa6u ba bindiga a ruwa, ba zata ta6a yin sakacin da hakan zai faru ba, dole ta nuna masu idan su asubanci suka yi a aikata ma Deen hakan to ita a hanya ta kwana don kare ɗanta, zumbur ta miƙe tare da ɗaukar wayarta ta shiga latsa ta yayin da take nufar wurin closet ɗinta, ta kara wayar a kunne ciki da bada umarni ta furta, "Get ready, we are leaving for Funtua now!" Daga haka ta cire wayan, sake yin wani kiran ta yi nan ma ta bada umarnin a shirya mota za su tafi Funtua yanzun nan...without wasting much time ta gama shiryawa cikin tsadaddan lace, ta zuba gwala gwalai a wuya da hannu ta fito a hamshaƙiyarta..lokacin da ta fito main falo ba kowa a ciki, kai tsaye ta nufi hanyar fita, a daidai gaban entry hall aka faka ƙatuwar baƙar jeep da za su tafi da ita, tana fitowa wani jami'i da ke tsaye a jikin motan ya yi saurin buɗe mata ƙofar baya tare da gaishe da ita, ko kallon sa bata yi ba ta shige, ya maida ƙofar ya rufe sannan ya buɗe front seat ya shiga, daga haka driver da ke zaune a driver seat ya ja motar suka tafi, sam dad bai san da tafiyarta ba, don bayan ya fito daga part ɗinta gidan gaba ɗaya ya bari ya wuce guest house ɗinsa ya je ya taushi zuciyarsa don ba ƙaramin 6ata mashi rai mom ta yi ba. Bayan sun ɗau hanya, gaba ɗaya mom Jameela a ƙagare take da ta gan ta a Funtua, sai ta ga tafiyar ta yi mata nisa, haushin ta da ba a zuwa garin a jirgi.... ✨A CIKIN RAYUWA✨ BY ZAINAB BATURE ZEELALUH✍️ Page 60 Bayan sallar issha suka iso Funtua, kai tsaye gidan hajiya ta sa suka nufa, bayan sun isa aka buɗe mata ƙofa ta fito, tsabar yadda take son ganinta a Funtua ya sa ko gajiyar tafiya bata ji ta yi ba, a gadarance ta shiga cikin falon hajiya, lokacin ba kowa a cikin falon, sai ga Balaraba ta fito daga cikin kitchen tana riƙe da wata roba, tana yin arba da mom Jameela sai da gabanta ya faɗi da ƙarfi, sanin ita ɗin tauraruwa ce mai wutsiya wadda mafi yawan lokutta babu alkhairi a ganin ta, da sauri ta ƙarasa inda take tsaye ta rankwafa tana gaishe ta tare da yi mata sannu da zuwa, ba tare da ta amsa mata ba a daƙile ta tambayi hajiya, Balaraba ta ce mata tana ɗaki tun da ta shiga da magrib bata fito ba, "Je ki faɗa mata gani na zo." Mom ta faɗa tana ƙoƙarin zama a kan kujera, Balaraba ta yi saurin amsa mata da to ta nufi hanyar part ɗin hajiya, bada jimawa ba ta dawo ta ɗan rankwafa ta ce ga hajiyan nan zuwa ta ɗan ɗaga kai, Balaraba ta wuce sumi sumi kamar mara gaskiya ta koma kitchen, fitowa ta yi riƙe da tray ta ɗauro ruwa da lemu da cup, bayan ta matsar da table gaban mom, cike da taka tsan tsan ta zuba mata lemu a cup, cikin girmamawa ta ce mata ga lemu, sai kuma ta tambayi ta kawo abinci, kamar abun faɗa mom ta bata amsa da, "Bana buƙata." Balaraba ta miƙe ta yi saurin barin wurin don ta fahimci a fusace take, daidai nan hajiya ta fito, idanunta akan mom tana kallon ta da ɗan alamun mamaki ta nufo cikin falon, kallo ɗaya mom ta yi mata ta kauda fuskarta, hajiya ta ƙaraso cikin falon ta zauna a can kujeran gefe, tana kallon mom ta ce, "Kune tafe." Mom ta amsa da unhm, ɗan juyowa ta yi ta kalle ta kamar an yi mata dole ta gaishe da ita, hajiya ta amsa tana dai ta bin ta da kallo, "Yaushe kuka zo?" Tana cika ta bata amsa da isowarta ke nan, hajiya ta ɗaga kai sai kuma ta ce, "Ke kaɗai kika zo ne?" nan ma ta bata amsa da unhm, hajiya ta ɗan yi shiru still kallon ta take don bata ga alamun arziƙi a tattare da ita ba, can hajiya ta ce, "To sannu da zuwa, duk ya aka baro yaran?" A taƙaice ta amsa da lafiya, daga haka suka yi shiru hajiya ta maida idon ta kan tv, can ta juyo ta kalli mom da idonta ke kallon gefe ta wani ɗaure fuska, hajiya ta ce, "Ki sha lemun mana, bari Balaraba ta shirya maki abinci." A dakile ta ce, "Na ƙoshi...ba don su na zo ba." Hajiya ta ɗan yi murmushinta na dattako tare da jinjina kai ta ce, "To don me kika zo Jameela?" Ta wani kalle ta fuska a haɗe ta fara magana, "Na zo ne kan maganar rana da wai aka saka ma Deen ba tare da sanina ba matsayina na wadda ta haife sa." Hajiya da ke kallon ta da murmushi ta ce, "Amman ai mun yi da Ibrahim zai sanar maki." A ɗan harzuƙe mom ta ce, "Eh ya sanar mani, amman bayan an yi gaban kai, shine na zo in sanar cewa a matsayina na mahaifiyarsa ban amince ya auri yarinyar ba, kamar yadda tun farko na sanar da shi Deen ɗin da mahaifinsa." Hajiya ta ɗan jinjina kai ta ce, "To yanzu ya kike son a yi ke nan?" Da sauri mom ta ce, "A warware saka ranan da aka yi, don ba zan ta6a amincewa da auren ba wllh." Hajiya ta ɗan ta6e baki tana bin ta da kallon mamaki, can ta sauke ƴar ajiyar zuciya ta ce, "Kema kin san mu ba ƙananun mutane bane, bamu yin magana mu dawo mu warware ta, musamman kuma magana da ta shafi aure. Mu tun da ya nuna mana yana son auran yarinyar to zamu goya masa baya in dai ba wata matsala aka samu da zata iya hana hakan ba, saboda mu bama hana namu abun da yake so matuƙar bai sa6a addini ba, koda kuwa mu abun bai yi mana ba muna yin haƙuri bama aiki da son zuciya, kuma ke kan ki shaida ce kan hakan, don haka idan kin ce ke baza ki amince ya auri yarinyar ba wannan ra'ayin ki ne, kuma ya rage tsakanin ki da ɗan ki ba mu ba." Duk da maganganun hajiya sun daki mom sosai bata nuna ba, ta yi ɗan murmushi mai kaman na yaƙe ta ce, "Shike nan, zan yi duk abun da ya dace don tabbatar da ra'ayin nawa." Hajiya ta gyaɗa mata kai ta ce Allah Ya taimaka, daga haka mom ta miƙe a taƙaice ta ce, "Sai Allah Ya kai mu." Hajiya ta ce, "Allah Ya tashe mu lafiya, ta bi mom da kallo ta ɗan kwa6e fuska har ta fita....mom na fita saura ƙiris su yi karo da Balaraba da zata shigo cikin falon, da sauri Balaraba ta ja gefe tare da sauke kanta ƙasa, har mom ta wuce sai kuma ta dakata tare da kallon ta ta ce mata ina ne gidan su yarinyar da aka ce Deen na so, Balaraba ta fara yi mata kwatance, cike da bada umarni ta ce mata su je ta kai ta gidan, har sai da gaban Balaraba ya faɗi, amman ta san bata isa ta ce ba zata je ba, ta yi saurin ce ma mom bari ta sako hijab, ta jefa mata wani kallo ta ce, "In tsaya jiran ki ke nan?" Balaraba ta girgiza kai, sai dai ta warware kallabinta ta yafa suka nufi gate, suna fitowa jami'in da ya zo tare da mom ya miƙe, da hannu ta yi mashi alamar bata buƙatan rakiyan, suka tsallaka hanya idanun officers ɗin bakin gate akan su, "Allah Ya kiyaye fitina..." Ɗaya cikin jami'an da ke tsaron gidan hajiya ya faɗa, "Kaima ka fahimci in da ta dosa ke nan." Wani shima ya faɗa, jami'in mom ya tambaye su ina zata je, ɗaya ya bashi amsa da da ƙyar idan ba gidan su yarinyar da ɗanta ke so zata je ba...suna shiga layin mom ta juyo ta ce ma Balaraba ina gidan, da hannu ta nuna mata gidan, ta ce mata ta koma ita kuma kai tsaye ta tunkari gidan, Balaraba ta yi tsaye gabanta nata faɗuwa, mom na zuwa saitin in da Imrana ke tuyan awara ta ɗan tsaya tana kallon shi fuska a yamutse, wani ƙululun baƙin ciki ya zo ya tokare mata wuya da ta gane ma idonta sana'ar awaran da suke yi da gaske ne, bayan Imrana ya sallami wani yaro ya ɗago ya kalli mom, innocently ya ce, "Awara za a baki?" mom ta ji tamkar ya ɗebo man tuyan waran ya watso mata, wani mugun tsoki ta bugu ta wuce gidan a fusace, Salma na zaune a saman tudunkar baranda, daga gaban ta farantin silver ne da roba tana yanka ma Imrana awara da zai zo ya ɗauka, tsaf tsaf da ita tana sanye da doguwar rigar atamfa, a hankali Salma ta ɗago ido jin kamar an shigo gidan, da sauri ta ƙarasa ɗagowa lokacin da ta yi arba da wadda ke tsaye a bakin ƙofar shigowa tana ƙare ma gidan kallon rashin arziƙi, duk da ba sosai take ganin fuskarta ba saboda hasken ƙwai mai cajin da ke cikin barandar ba ko ina ya haska sosai ba, hasken ya fi yawa a cikin baranda, ganin matar ta nufo ta ya sa Salma ta yi saurin miƙewa tsaye, ƙirjinta ya fara bugawa tana tunanin wacece wannan da ta shigo masu gida haka, sai da ta iso gabanta take ganinta sosai, nan da nan bugun ƙirjin Salma ya ƙaru sakamakon ganin fuskarta, a ranta ta fara raya ko dai aljana ce, amman kuma lokaci guda a ranta ta ji kaman ta san fuskar matar, mom ta bi Salma da kallo from head to toe, sannan ta bi farantin awaran da take yankawa da kallo tana yamutsa fuska sai ka ce ta ga kashi, ƙwarjini ta yi ma Salma sosai, a ɗan tsorace ta ce, "Sannu da zuwa..." mom ta sauke mata wani mugun kallo, duk da ba wadataccen haske ta gane ita ce yarinyar da Deen ke so, "Ina matar gidan!?" Ta tambaya a kausashe, Salma ta ce, "Innar mu?" Wani 6acin rai ya ƙara ziyartar mom jin yadda ta kira sunan mahaifiyarta, "Ban da ita akwai wata matar ne? koda yake na san mawuyacin abu ne a rasa wata matar, don talakan mutum ba a in da ya fi auki sai yin aure aure da tara yara sai ka ce ƴa'ƴan tumaki." Salma ta ɗan wara ido tare da ɗan buɗa baki, a hankali ta sauke idonta don ta ji bata iya jure ma kallon idanun matar, Salma ta shiga tunanin wace mata ce wannan da zata zo masu gida tana faɗin wannan maganganun...dammm! ƙirjinta ya yi wani bugu da ƙarfi lokacin da ta tuno da in da ta san fuskar mom wato a wayar Deen, da sauri ta ɗago ta kalle ta cikin rawar murya ta ce, "Ina yini..." mom ta dalla mata wata uwar harara, a tsawace ta ce, "Zaki kira mani matar gidan ko kuwa zaki tsaya kina mani munafunci." Da sauri Salma ta juya zata nufi ɗakin innarsu, daidai nan innar tasu ta ɗaga labule ta fito tare da faɗin, "Salma ke da wa, na ji kaman magana?" Salma ta tsaya cak ta kasa cewa komai, nufo bakin barandar innarsu ta yi, itama sai da gabanta ya ɗan faɗi lokacin da ta ga fuskar mom, innarsu Salma ta kasa cewa komai saboda yadda mom ta yi mata ƙwarjini gashi ta ɗaure fuska tamau, kallon Salma ta yi daga yanayin fuskarta ta fahimci ba lafiya ba, "Wacece?" Innar su ta tambaya a hankali, "Ni yakamata ai ki tambaya ba ita ba, ko tarbar baƙi ma ba a da basirar iyawa?" Innar su Salma ta ji maganar ta dake ta, amman sai ta ɗan yi murmushin ƙarfin hali ta ce, "A'a, ki yi hakuri hajiya, sannu da zuwa..ki shigo...bari in ɗauko tabarma don cikin akwai zafi ba wuta." Tana ƙoƙarin juyawa a tsawace mom ta ce, "Dakata malama...a tunanin ki kuna da wurin da zaku bani in zauna a cikin wannan akurkin gidan!" Innar su Salma ta bita da kallo da yanayin ruɗu, a ranta ta shiga tunanin to wai wannan wace irin baƙuwa ce suka yi haka, lokaci guda ta yanke anya baƙuwar su ce kuwa, ɗan murmushin yaƙe innar su Salma ta yi ta ce, "To Allah Ya baki hakuri hajiya, amman ina ganin kamar dai kin yi kuskuren kwatance ba nan kike nema ba." Kafin mom ta ce wani abu Salma ta ɗan matsa, ƙasa da murya ta furta, "Mom ɗin yaya Deen ce..." Ƙirjin innarsu ya buga da ƙarfi, mom ta yi wani guntun murmushi da baida alaƙa da farin ciki ta ce, "Good, gashi nan ɗiyar ki ta tabbatar mani ina a right place ban yi kuskure ba, kuma da a ce a cikin ku ba wanda ya san ni wacece hakan zai saka mani shakku a kan zargin mallake mani ɗa da kuka yi, yanzu kuwa na kara tabbatar da zargina...ban zo don in 6ata lokacina akan ku ba don baku cancanci hakan ba, idan mahaifinta na nan ki kira shi don yana buƙatar jin abun da ya kawo ni, idan kuma baya nan sai ki isar masa da saƙo idan ya dawo..na zo ne don in gargaɗe ku in kuma ja kunnan ku akan tun wuri ku raba ɗiyar ku da ɗana, ku janye batun wani aure a tsakanin su, kamar yadda bada sanina aka saka wai ranar aure tsakanin su ba, akan hakan zan ci gaba da kasancewa, wato ban san da zancen ba don ban haifar ma wata mai awara shi ba, bama ita kaɗai ba, a duk garin nan babu sa'ar auren shi..." Juyawa ta yi ta kalli Salma, da sauri Salma ta sauke idonta ƙasa bugun zuciyarta na ƙara tsananta sakamakon kalaman ta, tana sakin wani shu'umin murmushi ta ce, "Ƴan mata mai awara, a yi haƙuri a cire ran auran ɗana, domin wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa, yana da matar aure da na za6a mashi, warce take ƴar dangi, ƴar arziki, sannan ƴar gata gaba da baya, wadda ko matsayin mai aikinta ba zaki samu ba balle wai ki zama kishiyarta, don haka tun wuri ki sama ma kan ki salama, ki yi gaggawar cire shi a ran ki idan baki son ciwon zuciya ya yi ajalin ki, don wllh matuƙar ni ce mahaifiyarsa ba zai ta6a auren ki ba!" Lokaci guda Salma ta fashe da kuka ta yi saurin kai hannu ta rufe bakinta, daidai nan Imrana ya shigo ɗaukan awara, yana ganin abun da ke faruwa ga yayarsa tana kuka, da gudu ya koma waje, majalissar da su Sageer ke zama ya nufa, cikin rawan murya ya ce, "Yaya Sageeru ga wata mata can a gidanmu tana ta faɗin maganganu, har yaya Salma nata kuka." Wata zabura Sageer ya yi ya miƙe yana tambayarsa wace mata ce, Imrana ya ce shima bai santa ba, wata fara ce mai kaman aljanu, tare da abokan sa su Ibrahim da Aliyu suka nufi gidan, Sageer kamar zai tashi sama don kusan da taƙi taƙi yake yin tafiyan tsabar saurin ya isa gidan...mom ta koma kan innarsu Salma tana faɗin, "Ina mai ƙara jaddada maku da ku cire ran auren ƴar ku da ɗana, ku raba su babu shi babu ita, haka idan ma wani ƙulli kuka yi ma ɗana to ku yi gaggawar warware shi don na fi ku iya tijara...a yanzu cikin lumana na zo maku, idan kuma kuka ƙi ji to ba kwa ƙi gani ba, don zan ɗauki mummunan matakin da baku taba zato ba....idan ma baya ga matsiyacin mutum da shegen ƙarfin hali, ina ɗana ina wannan ƴar taku da har zaku yi tunanin haɗa alaƙa da shi ban da shegen ƙwaɗayin tsiya..." Da sauri Sageer da ya iso gaban su ya katse ta da faɗin, "A'a hajiya....gaskiya mu ba matsiyata bane...ai babu matsiyaci sai wanda bai san ubangijinSa ba balle yadda zai bauta masa, mun dai yarda mu talakawa ne, kuma hakan ba yana nufin mun zama abun wulaƙantawa ba, saboda Allah ne ke son ganin mu a haka, idan da ya so muma zai iya bamu arziƙin tun da nashi ne ba na wani ba, kuma da mai arziƙi da talaka ba wanda ya fi wani a wurinsa face wanda ya fi bauta masa, kuma Alhamdulillah a haka ma muma masu arziƙi ne tun da ya bamu rai da lafiyan bauta masa, sannan bamu rasa ci ba bamu rasa sha ba balle sutura...tabbas mu talakawa ne amman masu wadatar zuci, ki bincika a duk faɗin garin nan ba ma unguwar nan kaɗai ba, ba wanda muke zuwa mu roƙi wani abu a wurin shi ko mu yi masa maula, muna da ƙarfin zuciyan neman na kan mu bamu dogara da kowa ba, kuma ko shi ɗan naki zaki iya tambayarsa idan mun ta6a roƙon wani abu a wurin sa, balle har ki yi tunanin ƙwaɗayin abun sa muke....sannan mu ba mushirikai bane, bamu ta6a zuwa wurin malami kan wata buƙata ba balle kuma boka, mun wadatu da tauhid ta yadda duk wata buƙatar mu kaitsaye wurin ubangiji muke kai ta sanin shi kaɗai ake bauta mawa kuma ake neman taimako, kuma a cikin mu ba wanda ya roƙi Allah ya haɗa ƙanwarmu da ɗan ki, addu'ar za6in alkhairi muke mata a koda yaushe wurin Allah, shi ne ya haɗa ta da ɗan ki, don haka idan baki son alaƙar su wannan tsakanin ki ne da ubangiji ba mu ba, kuma ɗan ki shi ya ce yana son ta ba ita ba, tun da kina da iko da shi ai shi zaki sa ya rabu da ita ba mu ki zo mana nan ba, tun da mu miye namu a ciki, ku sa waɗanda suka zo neman auren ta su dawo su janye, ba abun da hakan zai rage mu da shi, kuma ai gari da yawa Allah zai kawo mata wani, ba wai don ɗan ki bai aure ta ba hakan na nufin zata rasa mijin aure...." Tun da ya fara maganganun innarsu ke ta ƙoƙarin dakatar da shi ta hanyar kiran sunan shi amman ya ƙi ya yi shiru sai da ya kai aya, fuskar shi a murtuke yana ta ɗan hucin 6acin rai, Salma sai kuka take yi itama tana ce mashi ya yi shiru don Allah, mom dai still ta yi ta zuba mashi kaifafan idanunta har ya gama, tana jin tun da take ba wani mai tsaurin idon da ya ta6a tsayawa gabanta ya gaya mata maganganun irin haka, gashi a wasu maganganun nashi ya yi sara a kan ga6a ba tare da ya sani ba, sai mom Jameela take ganin kamar ya san wani abu game da ita, shine ya yi amfani da hakan ya gaggaya mata magana, juyawa ta yi kan innar su dake ta bata haƙuri kan maganganun Sageer tana cewa yaro ne, wani shu'umin murmushi mom ta saki ta kai hannunta da ya sha gold ta ɗan kama kunnanta ta ce mata tana fatan ta ji gargaɗin da ta zo masu da shi, da sauri innar su Salma ta ɗaga mata kai, mom ta saki kunnanta tare da faɗin, "...Kowa ya zauna lafiya..shi ya so!" Daga haka ta juya kan Sageer da ke tsaye yana ta hura hanci, ta ɗan yi murmushi irin na yaro bai san wuta ba ɗin nan, ta ce, "Na ji duk maganganun ka, sai dai ka sani kaf dangin ku babu sa'ar yi na...amman ka jira, daidai da yin ka za su zo su same ka." Har zata juya sai kuma ta dakata tana kallon Salma da fuskarta ta yi sharkaf da hawaye, tana ɗan murmushi ta ce, "Ƴan mata mai wara, kin ji gargadin da na yi maki akan ɗana ko?" Salma ta ɗan yi shiru sai kuma ta ɗan jinjina kai, mom ta furta, "Gud...idan kunne ya ji, to gangar jiki ta tsira!" Daga haka ta juya ta nufi ƙofa, su Aliyu da ke tsaye suka yi saurin bata hanya, da sauri innar su Salma ta ce ma Sageer mi ya sa ya saka mata baki ya yi maganganun da ya yi, a zuciye cikin karyewar murya Sageer ya ce, "To wai innarmu shike nan shi talaka bai da galihu, da kowa ya sai ya nemi taka shi a lokacin da ya so, kamar shi ne ya zabi kasancewa talakan, ko kuwa su da Allah Ya ba arzikin dama ya basu ne don su wulaƙanta wanda bai ba ba, ina ya basu ne don su taimaki wanda bai da shi don samun rabauta, kuma shima wanda Allah bai ba ban aka san mi ya tanadar masa gobe, kuma ai mune masu babban arziƙi tun da bamu wulaƙanta kowa, mun san darajar ɗan adam....ta hana ɗan nata auren ta ta ga idan hakan zai rage mu da wani abu...wllh ba wanda zan zuba ido ya zo har gida ya nemi wulaƙanta mu akan abun da ba laifin mu ba don kawai muna talakawa, kuma daɗin abun ma ai bamu ta6a zuwa neman taimako ko maula a wurin mutum ba..." Duk maganganun nan da ya ƙara yi akan kunnan mom Jameela da ta dakata a bakin zaure, wata uwar ƙwafa ta yi daga haka ta fita daga gidan, Salma ta zame ƙasa akan gwiwuwinta ta shiga yin kuka sosai, a zuciye Sageer ke ce mata dalla kada ta damu kan ta, idan ta sa ɗan nata ya fasa auren ta Allah zai iya kawo mata wani wanda ma ya fi shi...mom Jameela na fita su Ibrahim suka rufa mata baya, tsaye suka yi a ƙofar gidan suna kallonta ya yin da take tafiya, gaba ɗaya wani irin haushinta ne ya turnuƙe masu zuciya, tana cikin tafiya ta buɗe ƴar jakar hannunta ta fiddo waya, kira ta yi tare da yin magana a taƙaice, daidai tana zuwa bakin hanya baƙar jeep ɗin da suka zo da ita ta faka gabanta, aka buɗe mata ƙofa ta shiga daga haka suka tafi, Ibrahim na ganin ta tafi ya shiga latsa wayarsa zai aiwatar da abun da ya shirya....bayan wasu mintuna Auwalu ya shigo cikin gidan, fuskarsa da alamun tashin hankali, innarsu da Salma har da Sageer duk suna zaune jugum a cikin baranda, har da Imrana da innarsu ta sa ya kwaso kayan tuyan awaran, har lokacin Salma kuka ta ke ta yi a hankali ta saka kanta a cikin ƙafafunta, ƙarasowa Auwalu ya yi ya tsaya daga gaban su ya ce, "Innarmu wai mi yake faruwa ne? Yanzu nan ake gaya mani wata mata ta zo ko kun yi faɗa da ita." Innarsu ta bi shi da kallo idanunta jiƙe da ƙwalla sun yi jajir, cikin hura hanci Sageer ya shiga faɗa masa abun da ya faru, Aliyu ne ya shigo cikin gidan da sauri ya nufo cikin barandan da yanayin tashin hankali ya ce, "Ga ƴan sanda nan wai sun zo tafiya da Sageer!" A tare gaba ɗaya suka kalle shi tare da miƙewa lokaci guda ban da Sageer, hankali a matuƙar tashe innarsu Salma ta furta, "Ƴan sanda..!" Aliyu ya ce mata eh har da mota suka so, ta saki salati da ƙarfi tare da fashewa da kuka, Salma da itama ta miƙe ta saki wani matsanancin kuka, haka Imrana da Hamza, Auwalu da ke kallon Aliyu ya ce, "To mi ya yi da za su kama shi?" Daidai nan suka ji an rafka uwar sallama daga waje ana faɗin Sageer ya fito idan ba haka ba za su shigo, Innarsu da duk ta gama kiɗimewa ta kalli Sageer tana faɗin bari ta kira baban su, Salma da itama duk ta gigice ta shiga yarfa hannu tana ci gaba da yin kuka, miƙewa Sageer ya yi yana cika ya ce ma innarsu bari ya je ai dai ba a isa a yi masa abun da Allah bai yi masa ba, Salma ta yi saurin riƙe masa hannu cikin kuka tana faɗin, "Don Allah Yaya Sageer kar ka je, tafiya fa za su yi da kai." Haka Imrana da Hamza ma suna kuka suna roƙon kada ya je, a hankali ya zame hannun Salma da ta so tsinka masa zuciya ya yi ɗan murmushin ƙarfin hali ya ce ta kwantar da hankalinta ba abun da zai faru da shi in sha Allah, daga haka ya nufi ƙofar fita Auwalu da Aliyu na biye da shi, gaba ɗaya su Salma suma suka rufa masu baya, yana fitowa ƴan sanda biyu dake tsaye a bakin zauren gidan suka tambayi shine Sageer ya ce eh, ɗaya ya ce, "Ok zamu tafi station da kai." Sageer da ya ɗaure fuska ya ce, "Akan mi, wani laifi na aikata?" Guda a cikin su wani ɗan baƙi tatirna ya ce, "Idan muka je can zaka ji laifin ka." Daga haka ya fara ƙokarin saka masa handcuff, da sauri Sageer ya janye hannuwansa yana masa wani kallo ya ce, "Sai ka ce dai wani criminal za a saka mani ankwa, kuma ni ban san laifin da na aikata ba ma." Ɗan sandan ya ɗaure fuska yana cewa ya tsaya ya saka masa, Sageer ya ce, "Gaskiya ni ba zaku saka mani ankwa ba ba tare da na san laifina ba, haka kawai salon mutane su fara zargin wani mummunan laifin na aikata, ko a ma yi tunanin kidnapper ne ni ko informer." Ɗan sandan ya bishi da wani kallo irin na ka ƙule mutum, Auwalu ya ce yakamata su faɗi masu laifin da ya aikata, ɗan sandan ya yi ƙwafa kafin ya ce ma Auwalu ai shi ya san laifin da ya yi ma matar ɗan majalissar tarayya kuma ita ta saka a zo a kama shi, haka suka tasa Sageer ba tare da ya yarda sun saka masa handcuff ɗin ba, wasu cikin makwabta har sun fiffito an fara tambayar mi ke faruwa aka kama Sageer, su innarsu duk sun yi tsaittsaye suna ta kuka, motar yan sandan na tafiya Salma ta zame ƙasa a bakin zauren tana rera wani sabon kuka, Auwalu ya hau mashin ɗin Aliyu ya ce su bi bayan su...zumbur Salma ta miƙe tare da rugawa cikin gida zata je ta kira Deen ta sanar masa abun da ke faruwa. Tun bayan da mom ta bar falon, hajiya ta yi zaune tana dogon tunani, ta san halin Jameela tana iya zuwa ta aikata abun da zai tada ma mutane hankali, lokacin Balaraba ta shigo cikin falon, har zata wuce kitchen sai kuma ta dawo ta tsaya daga gefen hajiya, ganin alamun kaman da magana a bakin ta hajiya ta tambaye ta ya aka yi, ta ce mata dama yanzu hajiya ta Abuja ta saka ta raka ta gidan su Salma, hajiya ta yi shiru tana kallon Balaraba jin abun da ta ce, can ta ce, "To mi ta je yi masu gida?" Balaraba ta ce itama bata sani ba don basu ƙarasa gidan ba ta ce ta dawo, daidai lokacin direban hajiya Sule ya shigo cikin falon duk suka ɗaga kai suna kallon shi har ya ƙaraso, da yanayin damuwa ya ce ma hajiya dama ya zo sanar mata ne ga hajiya can ta Abuja ta saka an kama Sageer yayan Salma, jin haka ya sa hajiya yin saurin miƙewa, nan da nan 6acin rai ya bayyana akan fuskarta ta ce ma Sule mi Sageer ɗin ya yi mata, wayar shi da ya ke riƙe da ya ɗago tare da miƙa ma hajiya, ta shiga kallon video ɗin da Ibrahim ya yi ma mom Jameela ba tare da sanin kowa ba, ta bayanta ya ɗauki video ɗin hakan ya sa ba a ganin fuskarta sai dai bayanta, daga lokacin da suka shiga gidan tare da Sageer videon ya fara, muryar mom Jameela ta fito raɗam lokacin da take ƙarasa yin maganganun da suka iske tana yi da kuma wanda Sageer ya mayar mata, shi Sageer ana hangen fuskar shi, amman Salma da innarsu basu fito ba don ta gefe ɗaya aka yi videon...6acin rai ne sosai ya bayyana akan fuskar hajiya bayan ta gama kalla, miƙa ma Sule wayan ta yi ba tare da ta ce komai ba ta juya ta nufi ɗakinta. Su Salma duk suna zaune a cikin baranda har da baban su da Auwalu, basu daɗe da dawowa daga police station ba sun je yin belin Sageer amman an hana su an ce sai mom ta bada izinin sakin shi, gaba ɗaya kana ganin su ka san suna a cikin tsananin tashin hankali, har lokacin innarsu da Salma da su Imrana basu daina matse ƙwalla ba, baban su ya sauke nannauyar ajiyar zuciya a karo na ba adadi, "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un..." Ya furta yana jinjina kai, tun da aka faɗa mashi abun da ya faru ba abun da yake face salati, fuskarsa a hautsine ya furta, "Da ina nan abun duk da bai kai haka ba wllh, kuma shima Sageer ya yi kuskure, da bai saka mata baki ba tun da ya san waɗannan mutanen sun fi ƙarfin mu." Cikin raunanniyar murya innarsu ta ce itama bata so ya saka mata baki ba amman ya san Sageer da zuciyar tsiya, baban su ya yi jigum ya rasa mike masa daɗi, gashi koda Salma ta kira Deen ta kasa samun shi, har saƙo ta tura masa amman baya online, kiran Auwalu aka yi a waya ya ɗaga tare da kai ta kunne, da sauri ya cire ya shiga lallatsa ta don duba abun da aka sanar da shi, "Gashi har an samu wani ma ya yi videon abun da ya faru ya ɗaura a social media." Ya faɗa idanunsa akan videon, da sauri duk suka kalli Auwalu da ya yi maganar, da sauri baban su ya tambayi miye aka ɗaura Auwalu ya miƙa masa, bayan ya gama kalla cikin tashin hankali ya ƙara rafka salati yana faɗin, "To waye kuma ya yi video har ya yaɗa, hakan ai ba abun da zai yi face rura wutar wata matsalar kuma." Duk fuskokin su innarsu suka nuna rashin jin daɗi da ƙarin tashin hankali bayan sun kalla videon, miƙewa baban su ya yi yana faɗin bari ya je ya samu yayansa Sani su san ta yadda za su 6ullo ma al'amarin....hajiya na shiga ɗakinta ta kai hannu ta warto wayarta dake a gefen gado, dad ta shiga kira, dakatawa ta yi tana jiran shi ya biyo kiran bayan ta ji ya yanke, after few seconds sai gashi ya kira, bayan ta amsa gaisuwar da ya yi mata, cikin tsananin fushi ta ce, "Dama so nike in ji da sanin ka matarka ta zo ta aikata abun da ta aikata?" Dad ya yi saurin cewa, "Wallahi hajiya ban sani ba, nima yanzun nan ake sanar mani kuma na kalla video ɗin, sannan kwata kwata ma ba da izini na ta zo nan ba, ni sam ban san ma ta taho Funtua ba wllh, kawai ɗazun bayan na sanar mata game da saka ranan auren Deen kamar yadda kika saka in yi, shine ashe ta kamo hanya ta taho, don ni tun bayan da na yi mata maganan abun ya nemi zama 6acin rai na bar gidan, har yanzu maganar da na ke yi maku ban koma gidan ba wllh sai dai kawai labarin tana Funtua ya riske ni...don Allah ku yi haƙuri." Sosai hankalin dad ya tashi musamman yadda ya ji hajiya ta yi magana da alamun tsananin bacin rai, gashi ya san tana da hawan jini, a kausashe ta ce, "To ka yi gaggawar bata umarnin ta sa a sakar masu yaro, laifin mi ya yi mata? Duk abun da ma ya yi mata ba ita ta ja ma kanta ba, in ba son ta zubar mana da mutunci ta mayar da mu ƙananun mutane ba miye hakan da ta aikata! kuma itama ba don saboda ɗanta ta je yi masu rashin mutunci ba, wanda kuma basu ne suka kira ɗan nata ya je ya so yarinyar su ba, sai shi kuma ya yi shiru tana ci ma mahaifiyarsa mutunci, ai hakan da ya yi mata shine daidai kuma haka ake son ɗan halak, don haka ka sata ta sakar masu yaro idan ba haka ba wllh zan ɗauki mummunan matakin da bata ta6a zato ba a kanta, don ba zan ci gaba da zura mata ido tana zubar mana da mutunci ba." Haƙuri dad yake ta bata tare da tabbatar mata da za a sake shi a daren nan, suna gama yin magana da shi ta shiga kiran daddy Sa'ad. Mom Jameela zaune a haɗaɗɗan falonta na sabon gidansu, hannunta ɗaya riƙe da glass cup mai ɗauke da ruwan lemu, cike da isa take sipping lemun, ta haɗe rai yayin da take latsa wayarta da hannunta ɗaya tana kallon video ɗinta da aka watsa, sai dai sam bata wani ji ta damu da hakan ba, don a yadda take ji ta shirya ma komai zai faru in dai akan Deen ya auri mai awaran nan, wayarta ce ta fara yin ringing, ta wani yatsina fuska ganin dad ne ke kira, sai da ya yi mata kira kusan ukku ba tare da ta yi picking ba, ƙarar shigowar saƙo ta ji ta kai hannu ta buɗe, dad ɗin ne ya turo mata saƙo da kausasan kalamai kan idan bata ɗauki wayan ba sai ya yi mummunan 6ata mata rai, bayan ɗan lokaci ya sake kiranta, tana cika tana batsewa ta ɗaga kiran, on the other hand a fusace dad ya ce, "What do you think you have done Jameela! Da izinin wa ma kika zo nan! Kuma akan mi zaki saka a kama masu yaro, a tunanin ki zaki je masu har gida ki ci masu mutunci su zuba maki ido? Kin san hakan da kika aikata zubar mana da mutunci ne..kin san kuma mi hakan zai haifar mani!? Ta wani sauke ƙafarta ƙasa a hasale ta ce, "I don't fucking care komai hakan zai haifar Ibraheem! magana ake ta muradina akan ɗana da na haifa, don haka sai in da ƙarfina ya ƙare wllh, ba wanda ya isa ya nuna mani iko akan ɗan da na ɗauki cikin sa na yi naƙudar sa har na kawo shi duniya, na san ai nufin ka hakan zai sa kasa mu matsala a siyasar ka ko, to a wannan ga6ar ban damu ba ko da zaka rasa kowane muƙami ne in dai akan cikar burina ne kan ɗana!" dad ya yi ƙwafa da ƙarfi ya furta, "To mu zuba mu gani, kuma ina mai umurtar ki da ki saka a saki yaron nan yanzun nan, idan ba haka ba zaki ga mummunan matakin da zan ɗauka akan ki, wanda ina mai tabbatar maki da sai kin yi da na sanin komai da kika aikata!" Daga haka ya yanke kiran, mom ta cire wayan tare da bin screen ɗin da kallo ta wani tamke fuska, ji take ai idan ma ta saka aka saki Sageer yanzu ya sha da ita, sannan hakan tamkar buɗe ma wasu ƙofar raina ta ne, sai dai kuma a wani 6angare na zuciyarta ta ɗan ji fargabar maganar dad ta ƙarshe ta kama ta.... A Cikin Rayuwa kashi na 2 ₦500 Regular WhatsApp Group, ₦800 Special Telegram Group. Za a biya ta Sterling Bank (0121797114, Zainab Bature). A tura shaidar biya ta WhatsApp: 08169856268, 09013804524, ko Telegram: 08032811442. Saƙo kawai ban da kira please.* Labarin na tafe da sabon salo mai matuƙar ban mamaki, kada ku bari a ba ku labari🔥